Author : miss'Deejarh Category : Romance
pls.
Mizaisa na saurareki baseera?, aini yanzu kinfi k'arfina wlhy, keba k'awar rayuwa bace, tunda har kika iya cin amanar safna data d'auki sirrinta Dana gidansu tabaki duka, tonikam sai yaya kenan?, ALLAH abin tsoro kema baseera dole aji tsoron kaidinki, kecefa kika jefa rayuwar Safna a halinnan amma Ashe kina gefe kina cin dunduniyarta, haba baseera miye ribarki Dan ALLAH?, tundaga sanda iyayen safna sukace sun mata miji kika Shiga kika fita kika kanainaye rayuwarta, kin hana afad'a mata gsky bare ta fahimta, saboda son zuciya irin naku yanzu kun koma danku 6ata rayuwar auren k'anwarta, haba baseera kashe aurefa ba abin wasa bane, *_"ALLAH ne ya halatta aure da saki, amma shikanshi bayason sakin aure, duk sanda igiyar aure ta katse sai al'arshin ubangiji ta girgiza saboda kad'uwa, shaitan yakanyi farinciki awannan rana saboda yaraba aure, shin kuma kunaso kuzama daga jerin shaid'anu?."_*
Wlhy kuji tsoron ALLAH kutuba tun kuna da dama, idan kuka bari damarku ta su6uce kunci amanar kanku, kutuba tuba na gsky ALLAH zai iya yafe muku *_"domin shi gafurun rahimunne, kuma maji6incin al'amuran bayine."_*, kuma godema ALLAH daya fargar daku da wuri Dan yana sonku da rahmarsane.
Tunda zeenat tafara maganar baseera kuka takeyi, tabbas ta tafka babban kuskure kuma sharrin shaid'anne, wlhy tayi nadamar halayenta, tarik'o hannun zeenat tana hawaye ngd sosai zeenat kin tunatar dani abinda ban saniba kuma ngd wlhy kinsamu ladana Dan nayi nadamar abinda na aikata, kuma daga yanzu insha ALLAHU zan tuba, zan samu Safna na warware mata dukkan k'ulli, amma inaso ki taimakamin da nuna mata hanya itama, Dan inaso yanda natuba na dawo hanya itama ta tuba ta gyara kodan mugudu tare mu tsira tare.
Jinjina kai zeenat tayi tana murmushi had'eda sharema baseera hawayenta, karki damu 'Yar uwa ngd Nima dakika fahimceni kika kuma gane abinda nake nufi, ALLAH ya yafe mana gabad'aya ya kar6i tubanmu, ALLAH yasa mufi k'arfin zuciyarmu, ina fata yanda kika fahimta da wuri ALLAH yasa Safnama ta fahimta d'in.
Ameen zeenat ngd.
Karki damu muje Dan sir koba hakabane,😜 yakusa Shiga mana, muje muk'arasa lecture d'in muwuce gida.
Jinjina kai baseera tayi tana murmushi suka kama hannun juna suka nufi holl.
😁 _wlhy abinda yaburgeni kuma yamin dad'i masu karatu, ALLAH yasa safna itama ta fahimta kamar yanda baseera tagane kuma ta tuba.🙏🏻ameen._
Su Rahma duk suna kichin suna aikin soya cincin d'in gara, amma jitake zazza6i yana neman rufeta, ga k'asanta yana mata zafi har yanzu ko motsi bata sonyi ma, Ammi dake kallonta tun d'azun ta ce, "Rahma yaya dai?.
Murmushi yak'e Rahma tayi ta ce, " babu komai Ammi."
Aunty Sameera ta ce, "kai Rahma bakida lfy gsky, tun d'azun nima ina lura dake, aunty Rasheeda ta ce, " wlhy nima nakula tundama tashigo batada walwala kamarma tana d'ingishi, kokinji ciwo ak'afarne?.
Shiru Rahma tayi kanta ak'asa, jitake duk kunya ta isheta, itakam bobo yaja mata, yanzu hakama kowa yagane abinda yafaru........
Ammi CE ta katse mata tunani dafad'in tashi muje kisha magani.
Ahankali Rahma tamik'e tana duk'ar da kai, duk sukai mata sannu amma banda safna, azuciyarta ma sai tsinema Rahma takeyi.
Kama hannun ta Ammi tayi suka nufi d'akinta, ta zaunar da ita abakin gado sannan itama ta zauna tana fuskantarta, kallonta take cikeda nazari, ita kam Rahma kanta na k'asa tana wasa da zobenta.
Rahma kodai fad'a kukayi keda mukarram d'in?.
Girgiza kai Rahma tayi ta ce, "a'a Ammi bamuyi fad'aba."
To mike damunki?.
Ammi babu komaifa k'afatace kemin ciwo, shuru Ammi takumayi tana kallonta, zuwa can ta ce, "fad'uwa kikayine?, a'a, to ciwo kikaji kenan?.
Eh, Rahma tafad'a cikeda kunya, ga hawaye suncika idonta taf, bata fata ammi tasake tambayarta wani Abu kuma bayan wannan Dan batasan mizataceba kuma.
Ammi ma batasake cewa komaiba Dan sai yanzu tafahimci komai, amma tayi mamakin hak'urin mukarram dahar ya iya barin Rahma har zuwa yanzun, dawani yagaya mata bazata yardaba, amma gashi tagani da idonta, koda yake tasan duk cikin 'yayanta babu Wanda yakai mukarram kawaici saidai zuciya da masifar tsiya.
Bayi tashiga tahad'a ruwa mai zafi tareda magunguna masu k'au cikin wad'anda takema su khairiyya gyara, fitowa tayi tana fad'in Rahma taso kigani.
Rahma tamik'e tamkar wata muna fuka tanufi Inda ammi take tsaye, bayi ammi tanuna mata da hannu, kishiga ruwa na nan aroba kicire kayanki saiki shiga ruwan, amma saikin daure Dan yanada d'an zafi, idan yahuce kikuma Tarar wani ga maganin nan ajiye aroba saiki kuma shiga kinji, shima saiya huce insha ALLAHU k'afar zata daina ciwo sannu, nima idan k'afata na ciwo dashi nake amfani.
Sanyi Rahma taji aranta Dan duk tunaninta Ammi taganene, amma dataji tace itama dashi take amfani idan tana ciwon k'afa saitaji dad'i, risinawa tayi Tanama Ammi godiya.
Ammi tayi murmushi tana fad'in aii babu godiya tsakaninmu Rahma, kud'inma 'ya'yanane, matsayinku d'aya dasu mukarram araina.
Murmushi Rahma tayi tashige bayi tanamai jin k'aunar tsohuwar aranta, itama jinta take tamkar umminsu.
Ammi tana niyyar fita saiga ya hamza da bobo sunshigo d'akin da sallama.
Baya ammi takoma tana musu sannu, suka gaisheta sannan suka zauna abakin gado, shi boboma kwanciya yayi, Ammi ma zamatayi saman kujerar d'akin tareda jawo k'atuwar ledar dasu bobo suka ajiye, miye kuma anan?.
Ammi d'unkunanmune wlhy muka amso cewar bobo dake kwance male male agado.
Ammi tayi murmushi a alallai manyan yayye sun shirya, harkun kama d'inkinku ahannu?.
Ya hamza yay dariya to Ammi aigara haka, inba hakan mukayiba aiki cud'e mana zaiyi, Dan kinga daga yau babu hutu, sauk'inma banida lectures gaba d'aya satin nan, boboma nashi mai sauk'ine tunda zai iya d'aukar Hutu, ya sulaiman da ya ishaq nedai babu dama.
Hakane amma aii ansamu sauk'i tunda gaku, ALLAH dai yayi muku albarka.
Ameen Ammin mu.
Ammi appa bai dawoba?.
Eh bai shigoba, k'ila yau a can zaiyi sallar juma'a Dan yacemin sunada meeting.
Okey nima bara naje gida nayi wanka to kafin su ya ishaq su taso.
To shikenan saika dawo.
Bobo ya ce, "saika dawoto, bara nayi barci kona minti30 ne, plz idan kadawo katadani.
Humm ALLAH ya shiryaka kaikam, to kana nufin bazakayi wankan masallaciba?.
Ah zanyi mana, nikasan inada kaya anan gidan, to Dana tashi zand'an watsa ruwa na shirya, kafinma ad'akko yara school amusu wanka ashiryasu aina d'an huta.
Dariya ya hamza da Ammi sukayi, ya hamza ya ce, " Ammi wannan autan naki bansan yaushe zaisan yagirmaba?.
Bobo ya ce, "babu wani auta, kana ina ammi ta tureni daga sannan kujerar ta d'ora hibba.
Yanda yay maganar cikin shagwa6a yasaka Ammi da ya hamza yin dariya, ya hamza yafice yana fad'in bara na dawo sai azauna shari'a.
Ammi ma mik'ewa tayi tafice zuwa kichin tana dariya.
Bobo yagyara kwanciyarsa yana murmushi, arayuwarsa yanason rayuwar irinta gidansu, Inda ace hakane akowane gida toda zuminci bai lalaceba, ALLAH yak'arama amminsu da Appa tsawon kwana.
Na ce, " ameen.
Lumshe idanu yayi dansonyin barci, baisan Rahma tana d'akinba.
Itakam tanad'anjin hirarsu sama sama, daga baya taji shiru duk zatonta sunfita gaba d'aya.
Tamik'e daga cikin ruwan da ammi tahad'a mata Dan har ya huce, wani takuma had'awa kamar yanda ammi ta umarceta, tasake shiga, nanma takai minti 15 aciki ruwan yana ratsata, yanzukam taji dad'i sosai, harma jitake wajen yabar zafi, wanka tayi kawai tafito.
K'arar bud'e k'ofarne yasaka bobo bud'e ido ahankali ya sauke akan Rahma.
Sosai yakuma bud'ewa Dan yayi mamakin ganinta, dama tana band'aki tun d'azun amma tayi muk'us kamar babu kowa?.
Shiru yayi bai motsaba Dan yakula batama gansaba.
Aiko Da gsk Rahma bata kula dashiba, tasa k'aramin tawul tatsane jikinta, jinta take wasai yanzun kamar iska zata d'auketa, kujerar madubi taja ta zauna tana mai fad'in kai ALLAH yabiyaki Ammi, Ammi uwa tagari, dabadankeba k'ilan saina had'a sati ina fama dazafin wajennan Dan wlhy ciwo yakemin, ALLAH yak'aramiki tsawon Rai Amminmu Dan zuciyata kullum k'ara k'aunarki takeyi wlhy.
Murmushi bobo yasaki danjin furucin Rahma ga mahaifiyarsu, jiyayi sonta yak'ara nunkuwa azuciyarsa.
Itadai hidimar shafa manta takeyi harda yaye yawul Dan ko kad'an hankalinta baikai akanshiba, tsaf tagama sannan tad'an gyara fuskarta dukda bawata kwalliyar kirki tayiba amma tayi k'yau.
Kayan su data d'akko ta d'auka tasaka, tayi d'as cikin siket da rigar na farin material mai d'igo d'igon bak'i.
Bobo dai yana kwance yana kallon ta cikeda k'auna, baimasan sanda yafurta woow my cite kinyi k'yau.
Arazane Rahma tajuyo tana kallonsa, tako wage baki zata tsala ihu Dan ita azatonta aljanine yay shigar siffar bobo yazo mata.
Da sauri bobo yajawota yarufe mata baki da lallausan tafin hannunsa...............
*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*
👩🏻💻typing........
❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_•{🅱🅾🅱🅾}•_
*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_
_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*
*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*
😭😭😭😭😭😭
5⃣9⃣
"K!, 'yammata karki taramin mutane mana, bobo yay maganar yana mai matse Rahma ajikinsa.
Sotake ta kwace kanta amma yak'i bata damar haka, ganinfa kamar da gsk atsorace take dashi yahad'e bakinsu waje d'aya, wata sassanyar ajiyar zuciya Rahma tasaki saidai har yanzun jikinta baibar k'yarmaba, saima k'aruwa dayayi Dan ayanzun ta shaid'a lallai bobone, to amma baya gudun Ammi tashigo tagansu?, kokuma wani daga cikin matan yayyensa.
Mintsininsa take amma yak'i sakinta, dole tahak'ura tazubama sarautar ALLAH ido wadda ta girma ta d'aukaka, daga kiss yafara kauce hanya, ayanzukam bazata iya jurewaba musaman idan ta tuno da azabar datasha adaren jiya wadda har safiyar yau wajen namata rad'ad'i, iya k'arfinta take turesa amma mutumin naku ko gazau sak'wanni kawai yakai son isarwa cikin nuna k'warewa.
Hawayene suka fara zurara akumatun Rahma Dan ayanzu kam batada wata hanyar ku6ta saidai kuka dan shikad'aine yarage mata.........
Da gudu khairiyya da khursiyya suka shigo d'akin suna kwala kiran aunty Rahma! Aunty Rahm.........
Suduka maganar tamak'ale amak'oshi Dan ganin abinda yafi k'arfinsu.
Shima da sauri bobo yabar abinda yakeyi yad'ago, yayinda Rahma ALLAH yabata nasarar mik'ewa daga jikinsa.
Bobo ya k'ank'ance idonsa dasukayi jaa yana kallonsu khairiyya dasukayi tsuru², yasan tabbas idan yayi magana saiya fallasa asirin muryarsa, to amma bazai iya k'yale yarannanba.
Rahma tara6a tagefensu khursiyya zata fice yace karki fita.
Cak tatsaya cikeda mamakin wannan k'arfin hali irinnasa.
shikam kallonsa yamaida akansu khairiyya ya ce, "ku bakuda hankali Baku iya sallamabane idan zaku shiga waje?.
Yaya wlhy bamusan kana nanba munzata ita kad'aice Dan ALLAH kayi hak'uri bazamu sakeba.
Le6ensa yacije yama rasa mizaice musu, tsaki kawai yayi dallah kutashimin kai shashashu, haka za a kaiku gidan miji kunama mutane shirme.
Da sauri sukayi waje, suna fita khursiyya tarufe bakinta da hannu ta shek'e da dariya, itama khairiyya dariyar tasaka, suka tafa suna cigaba da dariyarsu, saidai sukayi mai isarsu sannan khairiyya ta ce, " kai ya bobo an iya mazuran rashin gsky, nakulafa yama rasa mizaice manane shine ya koromu, dariya suka kama tuntsurewa da ita.
Khursiyya ta ce, "yar uwa yau naga ruwan soyayya, dama irinsu ya Abdulmaleek akwai iya soyayya, amma akwai dai mazuran tsiya, badan karyaci ubanaba wlhy saina koma naga mi akeyi yanzu.
Idanu khairiyya tazaro ta ce, " tabd'i wlhy badaniba, kingama tafiyata baza'a kaini gidan miji da karyayyar k'afaba, haka kawai su sunacin tasu soyayyar da allura ni akaima mijina jiyya yakasa nunamin.
Rahma dake bayansu ta ce, "ALLAH ya shiryaku wlhy.
Da sauri suka juyo ganin Rahma yasasu nufowa gareta harsuna 'Yar rigerigen tambayarta ya aikayi tafito?.
Hararar wasa tamusu ta ce, saiya fito yaritsaku wlhy.
Da sauri suka bar wajen itakuma tabi bayansu tana murmushi.
Tundaga wannan lokacin Rahma bata sake bari sun had'a hanya da bobo ba har dare lokacin tafiyarsu yayi.
Bansan miya faruba Ammi tace safna tayi zamanta anan danta tayata wasu ayyukan.
Ina kallon bobo yayi wani murmushi mugunta, Rahma dai batace komaiba, Safna kam jitayi tamkar tafasa ihu Dan Bak'inciki.
Rahma ta ce, "ina Nawal mutafi.
Kinga d'iyata kuyi tafiyarku tunda weekend za'a shiga kuma dukan yaran nan za'a barsu.
Jiki a sanyaye Rahma ta ce, " to Ammi saida safe.
ALLAH yakaimu d'iyata kinji.
Tunda suka fita bobo yake wata 'Yar dariyar mugunta k'asa² itadai Rahma batace dashi k'alaba saidai jikinta duk yayi sanyi.
Da kansa yabud'e mata motar tashiga, shima yazagaya yashiga, har suka fice daga gidan baikuma cewa k'alaba, bayan yahau babban titi yana tuk'i ahankali yad'an juyo ya kalleta ya ce, "matsoraciya har an hau network d'in tsoronne?.
Shiru tamasa kamar batajiba, murmushi yayi yasaka hannunsa d'aya yakamo nata yana murzawa, d'ayan kuma yana tuk'i dashi, batace masa komaiba bakuma ta hanashi abinda yakeyiba.
Wai baza'amin maganaba ne my cute?.
Idanunta tad'ago ta kalleshi ganin hankalinsa nakan titi yasa takauda kai, miye kuma kike kallona?, bobo yay maganar har yanzu idanunsa atiti.
Nifa ban kallekaba, Rahma tafad'ad'a kamar zatayi kuka.
Humyim yarinya zaki maganane, ainasan hanyar dazansaki maganar bara mu Isa gida dai kigani.
Gaban Rahma ne yafad'i, saikawai hawaye yafarabin kumatunta, aranta ta ce, " wlhy ka k'aramin irinna jiya mutuwa zanyi.
Karya kwana yayi yashiga layin gidansu, anguwar shiru babu kowa sai haushin karnuka, yay hon mai gadi yabud'e masa gate bayan sun gaisa yashige ciki damotar.
Yana tsayawa ko kashewa bata tsaya yayiba tayi wuf tafice, sauri sauri gudu gudu tashige ciki bayan tabud'e k'ofar falon, kafin yak'araso harta shige d'aki ta kulle kanta.
Tabama bobo dariya danhaka yashige d'akinsa yana wata 'Yar dariya.
Tana Shiga d'akin tadafe k'irji tanama kanta dariya, wata zuciyarta ta ce, "kai Rahma akwai tsoro?, yo badole naji tsoroba, wlhy nabari mutuminnan idani zaiyi, afili tayi maganar Tanana kanta dariya.
Wanka ta shiga bayan tagama ta d'auro alwala tafito, shirin barci tayi sannan tahau abin sallah tayi shafa'i da wutiri, tayi addu'ointa tamik'e, aranta tana fad'in yaudai ba'a nemi shayin k'addaraba.
Gado tahaye ta kwanta hankalinta kwance taja bargo ta lullu6a.
Shimadai bobo yana Shiga d'akinsa wankan yashiga, yay shirin barci tsaf, duk abinda yakasance al'adarsa yagudamar sannan yajawo laptop akahau aikin k'a ida.
Har wajen k'arfe d'aya yana gaban laptop sai biyu saura yad'ago yana kallon agogon dake d'akin, mik'a yayi tareda hamma, yarufe laptop d'in yamik'e, dirowar gefen gado yabud'e ya d'au key da wayoyinsa yakashe fitilar d'akin yafice.
d'akin Rahma yanufa yasandai yanzu tayi barci, ahankali yabud'e k'ofar yashiga yamaida yarufe, kallonta yayi kwance akan gado ta k'udindine abargo, aransa ya ce, " yarinyar nan sai abarki, gakida bargo na gsky mai laushi kin 6uge da shiga bargon bogi.
Wayoyinsa yazube adurowar gefen gadon yahau yakwanta ahankali, bargon ya janye yashige ciki tareda rungumeta a faffad'an k'irjinsa mai yalwar k'amshin turare.
Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, Alhmdllh yafad'a azuciyarsa.
Rahma kam dabatasan yanayiba takuma gyara kwanciyarta sosai a k'irjinsa, ahankali tarink'a sauke numfashi mai d'umi ak'irjinnasa.
K'ara lumshe idanu yayi yana mai lashe la66ansa da k'yar ya iya control d'in Kansa yay barci.
_washe gari_
Da asuba Rahma tariga bobo farkawa, jinta kamar ajikin wani Abu yasakata saurin bud'e idanu, ganin bobo yasakata zare k'yawawan idanunta, aranta ta ce, "to yaushe yashigone?, mutum tamkar aljani?, k'yak'yk'yawar fuskarsa tazubama idanu, aranta ta ce, " mutumin nan akwai sirrin k'yau, babu Abu mafi d'aukar hankalinta ajikin bobo kamar Sajensa, tanason sajensa sosai danya k'awata sirrin k'yawun fuskarta, ahankali talumshe idanunta tareda kai hannu bisa k'yakykyawar fuskarsa tana shafa sajensa daya kwanta luf luf yanata tashin k'amshi mai dad'i kamar yanzun yasaka masa turaren.
Tunda tafara shafa masa fuska yafarka, ta k'asan ido yake kallonta, aransa ya ce, "ALLAH yabani magulmaciyar mata, anasona ana kaiwa kasuwa, Rahma tajanye hannunta tana murmushi Dan duk zatonta bai tashiba, k'ok'arin zare jikinta tafara daga NASA, jin haka yasa bobo k'ara rungumota, acikin kunnenta ya ce, " guduwa zakiyi kibarni?.
Shiru tayi wai ita a adole barci takeyi, ya ce, "humm nizakima pretending? Bayan kingama shafemin fuska kina shauk'i?.
Rahma ta cusa kanta ak'irjinsa tana dariya k'asa k'asa, shima dariyar yayi ya ce, " oh ni dama matana ta iya gulmar soyayya saikace matar k'auye?.
Itadai luf tayi ajikinsa Dan kunya.
Jin ana kiran assalatu yasashi yunk'urawa yatashi da ita ajikinsa, to madam pretending tashi muyi sallah.
Zame jikinta tayi daga nasa batareda tad'ago ta kalleshiba, shimadai mik'ewa tayi yashiga bayinta ya d'auro alwala,