ABDUL_MALEEK by miss'Deejarh

Author :  miss'Deejarh Category :  Romance

Chapter   25 / 37

72K to 75K   out of 109K words

Inda take ya iso yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e saboda alwala, sunkuyowa yayi yasumbaci kumatunta sannan yafice yana fad'in saina dawo.
Batace komaiba saidai tasaci kallonsa tagefen ido tana murmushi, yana fita tatashi itama Dan d'auro alwala.
Saida yaje d'akinsa ya canja kayan barcinsa zuwa doguwar Riga sannan yafice masallaci.

Saida gari yayi haske sannan bobo yadawo, lokacin Rahma ma tana zaune akan sallaya tana addu'a bayan ta k'arasa karatun alkur'ani.
Zama yayi suka shafa addu'ar tare.
Kan Rahma ak'asa ta ce, ''ina kwana?."
Bazan amsaba saikin kalleni.
Murmushi tayi tareda rufe idanunta da tafin hannu, kamata yayi yamik'ar tareda zare hijjabin sannan yajata suka zauna a bakin gadon, my cute wai ita wannan kunyar bazata raguba haka?, nafa rage kusan 60% acikinta amma ank'i nunamin hakan.
Murmushi tayi kawai batareda tace komaiba, ya ce, "idan kinaso nakaiki gidan Appa yau saikin kalleni, yafad'a yana tsura mata mayun idanunsa.
Ahankali tad'ago k'yawawan idanunta masu kasheshi ta sauke akansa, kallon ido cikin ido sukema juna, suduka sunshagala cikin shauk'in so, bobo yad'an lumshe idanunsa yabud'e ahankali, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ina k'aunarki dayawa Rahma, tabbas da ubangiji bai sauya al'amuraba danayi asarar rashin kasancewarki matata, ALLAH na gode maka dakamin wannan k'yauta.
Rahma talumshe fararen idanunta, ta ce, "nice na cancanci gidema ALLAH ya *_Abdulmaleek_*, kaid'in namijine mai wahalar samu acikin maza, zanta godema ALLAH har k'arshen numfashina da kasancewarka mijina, Nawal d'iyata, tabbas kai alkairine ga rayuwata, hawaye yafara bin kumatunta na dad'i......
Ganin haka yasaka bobo fara bata Sumba ako ina najikinta, saida ya yamutsata San ransa, itakam dukda tsoron dake cikeda ruhinta haka tadake zuciyarta tana kar6ar sak'wanninsa.
Rungumeta yayi yana sauke numfashi asarek'e, muyi barci yafad'a ahankali yana gyara mata kwanciya.
Shiru tayi kamar tana barcin, shikam bobo mintuna kad'an barcin yay awon gaba dashi, ganin barcinsa yayi nisa tazare jikinta ahankali tamaida masa filo a madadinta.
Ficewa tayi domin had'amusu breakfast.
Cikin 'yan mintuna ta kammala komai ta gyara ko ina yad'auki k'amshi, abayinsa tayi wanka sannan tadawo d'akinta, mai tashafa tayi 'Yar kwalliya yau harda jambaki tasaka, aiko tayi k'yau tamkar kasaceta kagudu.
Siket dariga tasaka na atanfa fara da adon jajayen fulawoyi.
Masha ALLAH nafad'a araina Dan babu k'arya Rahma tahad'u.
Kum tad'auka tana taje kanta, wani d'an ruwa daya d'id'd'iga asaman gashin yafara tsalle harya sauka akan fuskar bobo.
Bud'e ido yayi ahankali yasauke akan Rahma dake tsaye agaban madubi tana faking d'in gashinta da jan ribom.
Lumshe ido yayi yabud'e yana murmushi aransa yace masha ALLAH.
Itakam dabatasan yanayiba tad'auk'i d'ankwali ta tayi d'auri mai k'yau na zamani, tad'auki 'yan kunne jajaye tasaka sannan takuma feshe jikinta da turarenta.
Juyowa tayi danufi fita saitaga idon bobo akanta, hannu tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, shima mik'ewa yayi zaune yana murmushi, yatako ahankali zuwa gabanta, hannunsa biyu yasaka yarik'o k'ugunta, muryarsa anarke ya ce, "beautiful Lady kinyi k'yau sosai, shine kikamin wayau ko?.
Girgiza masa kai tayi haryanzu hannunta nakan fuska.
Ya ce, " to bud'e fuskar naga kwalliyar tawa ko?, akunyace tacire hannunta, woow my beautiful wife kwalliya namiki k'yau amma bak'yasonyi, todaga yau haka nakeso aringa tsantsaramin wadda zata ringa hanani fita office.
Yabata dariya Dan haka tatuntsure da dariya, shima dariyar yayi tareda rungumeta, bayan sund'an sarara ya ce, "to muje nima kimin wankan.
Idanu tazaro waje ta ce, ''rufamin asiri."
Asirinki arufe yake aii, shima yafad'a yanad'an zaro ido kamar yanda tayi.
Murmushi yayi, shikuma yafita yana fad'in tom bara naje nayi my cute, amma next time bazan d'aga miki k'afaba.
Murmushi Rahma tayi tareda d'aga hannunta sama tana fad'in ALLAH ngd maka daka daidaita al'amurana alokacin dabanyi zatoba.
d'akin tahau gyarawa cikin lokaci k'alilan takammala takoma falo tazauna jiransa yafito.
Shima baid'auki lokaci mai tsawoba yafito cikin k'ananun kaya wando 3Β½ da k'aramar Riga tashan iska duk farare tas, yasaka Jan silifas ak'afarsa, sai zabga k'amshin turarensa yake na alfarma.
d'agowa tayi tana kallonsa, yasakar mata murmushi itama ta mayar masa tareda mik'ewa, a dinning suka yada zango, tazuba musa abincin tana k'ok'arin zuba nata yarik'e hannunta tareda mata magana da ido.
Zama tayi danta fahimci inda yadosa, indai tak'aice muku dakansa yabata abinci itama tana basa, haka sukaci suka k'oshi tagyara wajen suka dawo falo suka zube.
Rahma takalli bobo ta narke murya, wai bazamuje gidan AMMIN ba?.
Ido d'aya ya kanne mata, ya ce, "a'a yau zamu huta agida musha soyayyarmu my cute.
Baki taturo kamar wata bebyn roba.
Zamewa yayi yakwanta bisa kujera yana murmushi.
Sallamar da akayice takatsema bobo maganar dayayi niyyar yi......
Rahma ta amsa tana maida kallonta ga k'ofa, ta ce, " kushigo.
Zeenat da baseera suka shigo da sallama, mik'ewa Rahma tayi taje ta tarbosu cikin farincikin ganunsu, zeenat ta ce, "oh ni Autar ummy amare.
Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana fad'in kai aunty zeenat, baseera ta ce, " Yar lukutar ummi kin k'ara kibafa, aunty baseera kema hadake ko?, Rahma tayi maganar cikeda shagwa6a.
Dariya sukayi tareda k'arasawa cikin falon, baseera da zeenat suka kalli juna Dan basuyi zaton bobo yana nanba.
Zama sukayi suna gaisheshi, baiko kallesuba ya amsa da lfy amma fuskarsa asake, mik'ewa yayi yana fad'in yakuke?.
Sukace lfy lau wlhy.
Fita yayi harabar gidan danya basu waje, dandanan Rahma tacika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa.
Zeenat ta ce, "nibanji motsin mutuniyarba.
Wai aunty safna?.
Sukace eh.
Lah tana gidansu ya Abdulmaleek aii, a can takwana wlhy. Dama tunda naganku nasan zuwantane tunda Baku ta6a zuwaminba.
Dariya sukayi baseera ta ce, " a'a dama gunki mukazo ko zeenat, gyad'a kai zeenat tayi tana dariya.
Daganan hira sukashigayi, bayan kamar minti30 suka mik'e tareda alk'awarin suma zasu halarci bikinsu khairiyya d'in.
Godiya tamusu tarakosu har harabar gidan, bobo nasaman mota zaune, suka masa sallama sannan suka tafi.
Dirowa yayi daga saman motar idonsa akan Rahma, batayi auneba taji yad'auketa cak kamar jaririya yanufi cikin falon da ita.
Direta yayi saman doguwar kujera suna dariya, yakwanta tareda d'ora kansa saman cinyarta suna kallon juna, ya ce, "wad'an nanfa daga ina?.
K'awayen aunty Safna ne?.
Baice komaiba, saima ya kauda zancen da d'akko wani daban.................






*_"Dan ALLAH duk masoyina yamin addu'a acikin sallarsa, ALLAH yabiyamin buk'atata ta alkairi, yakuma azurtani da abundana nake buri na alkairi."_*
πŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»





*_luv you oll_*
*_(((S))).......2017_*

πŸ‘©πŸ»β€πŸ’»typing........

❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣
_β€’{πŸ…±πŸ…ΎπŸ…±πŸ…Ύ}β€’_


*_NA_*
_*Bilyn Abdul*_

_sadaukarwa_
*_Abba Gana_*
*_Batul mamman_*
*_Billy giro_*

*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*
😭😭😭😭😭😭

6⃣0⃣

Wunin ranar gaba d'aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad'anjin kunyar bobo har yanzu.
Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?.
Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, "a'a ammi taji sauk'i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu.
Murmushi Ammi tayi ta ce, " toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita
To Ammi zataji.
Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, "ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH.
Murmushi yayma tareda fad'in kunyar wa zanji?.
Ta Ammi mana.
Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba.


.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.
Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.
Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk'i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe.
Amma yanzun data k'ara kusanci dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad'a amma sai anta6oshi yakeyi.

Safna kam abin duniya ya isheta, k'iriΒ² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad'aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak'aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone.
Yau tunda safe take tsumayensa amma yak'i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had'a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara.
Kad'an kad'an saita lek'a window d'akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki.
Khursiyya ta ce, "aunty safna lfy kuwa?.
Murmushin yak'e tayi tareda wayancewa ta ce, " wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak'o awanjensa.
Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k'ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu'a, k'ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran haka yakeyi.
Dammmmm safna taji gabanta yafad'i, azuciyarta ta ce, "soyayya kuma?, wani kululun bak'in ciki yatokare mata mak'oshi ta had'iyeshi dak'yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk'e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, " yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa'ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad'a da gudu zuwa waje.
Itama khairiyya ta take mata baya tana fad'in wlhy baki isaba saidai kowa yahak'ura mu badashi, daidai zasushiga d'akin Ammi bobo yashigo falon da sallama.
Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d'in bak'aramin feeting d'insa yayiba, masha ALLAH.
hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba.
Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?.
Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had'aku?!!.
suduka saida sukad'an razana da tsawar dayayi, sukad'anja baya khairiyya ta CE, "Yaya wandonefa nad'auka shine ta kwace tagudo.
Tsaki yayi ya ce, " wandon nawaye?.
Da Sauri khursiyya ta ce, "nawanefa, itama khairiyya ta CE, " Yaya k'arya takeyi nawanefa.
Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy...
Ammi tafito ta ce, "miya faru kuma tom and Jerry?.
Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani.....
Hannu Ammi tad'aga musu ta ce, " ainagaya muku kubar sayen Abu guda d'aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d'aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso.
Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d'auki rigar nitabani wandon amma tak'i yarda.
Hannu bobo yamik'a ya ce, "kubani wandon....
Jikin khirsiyya na Rawa tamik'a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba.
Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, " wlhy ALLAH yabaku sa'a kunsandai halin mukarram sarai ba bak'oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik'in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad'a itama tahaye saman Appa.
Jiki asanyaye suka koma d'akinsu, Safna ta kallesu tana fad'in kukuma lfy INA wandon?.
Baki Khairiyya ta turo ta ce, "bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba.
Zumbur safna tamik'e tana fad'in yazone?.
Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu.
Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k'amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad'i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito harabar gidan.
Ganin motarsa yasakata k'ara sakin wani murmushin, bud'e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba.

Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana.
Appa ya ce, "Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak'uri miyasa bazaka hak'ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?.
Appa idan na k'yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak'aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana 'Yar murya wai ayi hak'iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad'in baki akan kahanani kaisa kotu?.
Hakane mukarram amma ni aganina duk bak'in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k'ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok'eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok'ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk'urin cutar dawani namu saika d'auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan.
Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k'ulle k'ullen sacemin mata da 'ya.
Eh nasani Dan yafad'ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik'in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik'in Alhaji sunusi.
Shikenan Appa zanfad'ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad'a MASA najanye amma akwai shari'ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari'a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara.
Ranar dayaje office d'ina danyimin gargad'i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d'insa yak'atseshi.
Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, "a'a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari'ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k'ara kareka daga Sharrin mak'iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka.
Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa.
Daganan wani zancan suka d'akko.
Bobo yakalli agogo tareda mik'ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari'a yau k'arfe 11:30.
To ALLAH yabada nasara jarumin babammu.
'Yar dariya yayi yana k'ok'arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti.
To zasuji idan sun fito.
Ficewa yayi da hanzari, abakin k'ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo.
Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik'amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha.
Ya sulaiman ya ce, "yanzu nashigo muka had'u da idris zashi gaida su Ammi.
Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?.
Alhmdllh yaya komai normal munata fama.
To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti.
To ALLAH ya tsare yabada sa'a.
Ameen ngd.
Ya sulaiman ya ce, " yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad'an biyo ta asibiti dama inason ganinka.
Okey babu damuwa saina shigo.
Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad'a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito.

Motarsa yanufa hankali kwance yabud'e yashiga yana fad'in masha ALLAH yanzu kuma sai office.
Idan ka gama dani ko?........
Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?.
d'aure fuska yayi tareda fad'in miyasa kina shigarmin mota?, wama yabaki izinin shiga?.
Wani murmushi Safna tasaki tareda k'ara lafewa cikin kujerar tana shak'ar k'amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d'an d'aga gira.
Kauda kansa yayi daga kanta tareda k'ara had'e fuska, ke banason k'aramin iskanci fitarmin amiota.
Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice.
d'agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad'aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad'an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, " nabaki minti5 Dan inada abinyi.
Hawayen fuskarta ta share ta ce, "wlhy minti5 yamin kad'an pls ka k'aramin.
d'agowa yayi yad'an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak'ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak'arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d'aga miki k'afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak'anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak'anta jininaba.
Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, " sai anjima.
Jiki a sanyaye Safna ta bud'e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris.
Suduka cikin mamaki suke kallon Safna da kuma motar bobon.
Bobo dake kallonsu ya sulaiman ta madubi yad'anja tsaki, dama abinda yake gudu kenan, ganin ya sulaiman kamar yanufoshi yaja motar da

25 / 37