Ba A Boran Namiji Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Abale Category :  Romance

Chapter   7 / 9

18K to 21K   out of 25.9K words

da takalman wambai da Rabi'u ya zuba mini a lefe sai wasu mayafai kamar abin tatar koko guda hud'u da wando da breziyya rabin dozin. Kayan kwaliyya masu sau'kin kudi.
Na shiga d'aki na ci kukana na 'koshi kuma ko da wasa babu wadda na gayyata daga cikin 'kawayena akan ta zo ta ga lefe na. Abinda na ajiye a raina shine; Rabi'u ya yi niyyar tozarta ni ne amma idan ba haka ba shekara biyu da wata shida da sa ranar auranmu ai ya kamata ace ya tanadi duk abinda ake bu'kata gurin neman aure.

Ranar d'aurin aure ya bada sadaki dubu goma sha biyar. Da shi aka saya mini zanin gado da ledar d'aki.
Saitin gado da kujeru da sauran tarkace Yaya Ibrahim da Usman suka had'u suka yi cikin rufin asiri aka yi mini jeren d'aki a gidan da Rabi'u ya kama haya wanda duk 'kafafarsa bai samu wanda zai zauna shi kad'ai ba, akwai wani a gidan. Sai yasa akayi masa katangar langa-langa aka zagaye mana gurinmu.falle-falle guda biyu sai kicin da band'aki sai d'an guntun tsakargidan da ba zai isa mu yi kwanciyar zafi ba.


PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank. A tura sheda 07084653262. Masu tambayar wannan karon babu Vip ne . Zan yi amma a talgram kawai za mu kammala littafin cikin kwana goma ko 'kasa da haka da ikon Allah. Wad'anda suke bukata kuma suna yin talgram din sai su yi mini magana domin jin abinda za su biya. 'Yan Nijar kuma dala d'ari katin airtel sai ku yi magana da momina kai tsaye babbar macace don Allah a kula.
*+227 88 13 77 40*

*GARKUWAR MATA.*
*BINTA ABBALE*
[12/17, 8:51 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*


Na yi nisa sosai a arewa books
*Binta Umar Abbale* https://www.arewabooks.com/chapter?id=67482a18ca3a075ba0996752


* *AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE*
_Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_nfection_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_

_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._
*08089965176*
*07084653262*



15&16.
Cikin rufin asiri aka yi hidimar biki. Sai dai kuma azahar tana yi wani irin zazzafan zazzabi ya rufar mini. Tun ina jarumtar boyewa har ya kada ni. Hak'ora na suka dinga karo da juna. Anti Jummai Yayarsa itace ta fara lura da yanayina tunda sai kai kawo suke yi a tsakanin gidajen namu biyu. Ta saka hannu ta tab'a jikina ya had'a zafi ainun. Da azama ta fad'awa Nene aka rufu a kaina. Amma ina abu sai tsananta yake yi. Dole aka samo a daidaita sahu muka yi asabitin Murtala tare da Inna Hauwa da kuma ita anti Jummai.
Kai-tsaye aka ba ni gado aka shiga ba ni taimkon gaggawa.
Gabadaya jikin mutanan da suka cika gidan ya yi sanyi, ana hidimar biki amarya kuma tana gadon likita. Ganin gado aka bamu ya sanya Inna Hauwa komawa gida dan d'auko abubuwan da zamu bukata.
Sai da magariba labarin ya samu Yaya Rabi'u. A sukwane ya isa asibitin. A lokacin na dan shiga hayyacina amma k'arin ruwa ake yi mini. A rikice yake fad'in "Jummai me ya sameta? Wanne irin ciwo ne da zai tashi ranar aurenta haka?"
A sanyaye ta ce "Likita ya ce jininta ne ya yi k'asa. Sannan akwai zazzabin cizon sauro da ya tsananta a jikinta."
Ya hura iska ya ce "Sallama ba yau ba ke nan?"
Ta ce "E, to da alamu. Tunda ga wata allura da suka ce , idan an yi takwas na dare, takwas na safiya ma zasu yi mata wata".
Ya saki gauron numfashi ya matso jikin gadon ya ce "Sannu Kulsum!
Na kalle shi kawai. Domin yadda ya ce Kulsum din har raina na ji ya bambanta da yadda yake fad'a a baya. Ban iya bude baki na amsa ba. Domin gabadaya jikina ciwo yake yi mini ga rashin k'arfi. Ya ce "ikon Allah! Ana cikin hidimar farinciki sai kuma murna take neman komawa ciki. Idan kin san jikin da sauki kawai zan nemi sallama mu wuce gidanmu, an shirya komai abin sha'awa. Gobe da kaina zan nemo kwararriyar ma'aikaciyar jinya ta duba ki tare da saka miki ruwan da sukace za'a saka miki d'in"
Ni dai da ido na bishi zuru. Ya ja kujerar gefen gadon ya zauna daf da gaban gadon.
Har wajen goman dare yana tukure bai tashi ba. Tun kafin tara kuma Inna Hauwa ta dawo da shirgi kayayyaki.
Ta zuba ido tana ganin rashin ta ido a wajen Yaya Rabiu. Ya kanannad'e komai. Da ta ga goma na shirin yi sai ta cire kawaicin da take yi ta ce "To tashi zan mu kwanta dare ya fara ja ".
Ya mik'e ba tare da ya iya cewa komai ba.
Ta kalli anti Jummai ta ce "Bi shi ku tafi ki kwana da yaranki. Idan Allah ya kaimu da safe kya zo".
A sanyaye ta ce "To Inna. Allah ya bata lafiya."
Ta amsa da ameen Jummai.
Suka tafi na bisu da kallo ba tare da na iya ce musu k'ala kanzil ba. Domin nauyin da jikina ya yi har harshena.
Yayin da Inna Hauwa ta dinga mita tana fad'in "Me za'a yi da halin wannan yaro. Allah ka rufa mana asiri kawai. Amma da ganin yadda idanuwansa suke a tsaye kyam tamkar nonon budurwar jiya, ba ta yau da duk a zube suke ba. Ba k'aramin artabu za'a yi da shi ba, ni kad'ai na gama nazarinsa kafaffe ne bayan rashin kunyar ma. Ta yi kwafa ta ja tsaki tare da cewa Malam Adamu bai kyauta mana ba, amma Allah yasa hakan ne alheri. Allah ya juyar da al'amarin zuwa kyakkywa."
A zuciyata na ji babu dad'i. Domin damuwar da ya shiga ta isa tasa inna ta fahimci cewar ba cushe na aka yi yiwa Yaya Rabi'u ba.
Kawai ya riga da ya saba da yin Abu a baibai.
Duk naci da tambayar da Yayah yake yiwa likitoci da sauran ma'aikatan lafiya akan za'a iya kula da ni a gida bai sa sun sallame ni ba sai da na kwana uku. Sosai ka yi treatment din maleria. Na warware ina takawa tare da cin abinci.
Ranar sallama kuwa shi so ya yi inna ta wuce da ni dakinsa. Yayin da ita ko kad'an hankalinta ma bai kai ga hakan ba.
Har muka fito bakin asibitin yana ta dibi-dibi ganin yadda take rike da ni da tamau.
Murya babu amo ya ce "Inna za ki wuce gidanki ne, ko sai mun fara zuwa can gidanmu?"
Yana rufe baki ta ce "Kai Rabi'u wanne irin gabo ne kai haka? Na kwana uku da yarinyar a asibiti sannan mu fito ka yi tunanin na barta a titi nayi tafiyata, ko dai ka manta cewar cikinmu d'aya da uwatata ne? ka fitine ni, ka hana ni skaat da rashin ta ido Wallahi."
Ya tumbatsa ya ce "Allahu ya huci zuciyarki Innarmu. Da wai ki wuce gida ki kintsa ki huta gajiyar zaman asibiti ne. Amma tunda baki fahimce ni ba, kin mini fahimtar da galibin jama'a suke yiwa Rabi'u to ki huce wa zai mance da matsayin surukursa ne Inna?"
Ta sassauta fushin ta ce "Wa yasan maka. Ai al'amarin naka ne na ga yana nema ya zama iyashege. To bazan tafi na huta din ba domin kuwa ban gaji ba, ko cewa zasu yi mu koma sai bayan wata guda Wallahi ba zan k'osa ko na gaza ba".
Da sauri ya ce "Haba Inna! Allahu ya Kyuata. Da ikon Allah ba zamu koma ba, daga nan sai d'akinta. Ai irin wannan abin ma da tausayi."
Ta yi jagale ta kasa cewa komai. Kawai ta tsayar da adaidaita ta ce Magashi. Muka hau tare da wasu cikin kayanmu muka tafi, muka bar shi da wasu kayan a gabansa.
A gida muka tarar da Babanmu. Ya dinga marabtarmu tare yi mana sannu gabadaya. Ni sannun ciwo ne, ita kuwa Inna sannun hidimar zama da ni ne. Cikin soyayya baba ya kalle ni ya ce "A a gawa ta ki rami. Da alamu kin fi ko wacce amarya zullimi tunda har kwanciya kika yi ranar aurenki. Allah ya baki lafiya. Sai hak'uri, gabadaya rayuwar ma hak'uri ce domin kalubalen da yake cikinta kabiran ne. Baka fita da ga wannan matsalar ba sai wata ta yanko maka. Ki tsananta addu'ar a sanya ki cikin bayi masu hak'uri domin shine jagoran dukkan arzikin duniya da lahira ".
A sanyaye na ce "To Baba."
Daidai lokacin Yaya Usman ya shigo hannunsa dauke da ledar lemo da ayaba. Kai tsaye gabana ya ajiye yana ce wa "Daga asibitin nake na tarar an muku sallama."
Inna ta cafe da ce wa "Ai da basu sallamemu ba, da kaina zan nemi sallamar saboda azabar takura da Kwarzabar Rabi'u! Kai wannan yaro za'a yi azinanne".
Baba na jin haka ya yi maza ya shuri takalmansa yana cewa "Ki gaida gida sarkin daru, yau dai ba zamu yi fad'a ba, kin yi dawainiya bai kamata bacin rai ya biyo baya ba. Amma lamarinki sai an daure. K'anina Maalam Hassan yana hak'uri kan hak'uri da ke".
Ta ce "Wallahi Malam dawo mu yi fad'an, wacce hidima na yi? Dan uwa ta yi abin da ya kamata akan diyarta sai ya zama dawainiya? Dawo mu yi kawai, gara na fito na fad'a muku gaskiyar magana."
Ya yi dariya ya ce "To tattara gaskiyar ki fad'awa y'arki, amma abin da nake so ki fahimta d'aya ne. Aure dai na riga na d'aura. Har zuciyata kuwa so nake ya wanzu har gidan aljanna. Idan kyauta ta ji maganta ta zauna da mijinta lafiya, ta ninka hak'urinta da kowa ya santa da shi, duk runtsi, duk wahala sai ta ga sakayyar alheri domin ta yi mini biyayya, ta kuma mutuntata aure. Amma idan ta je ta tsiro da halayen banza dan tana jin kuna kushe dab'iun mijinta, to ta sani fa itama zata ga ba daidai ba. Domin Ubangiji da kansa ya girmama sha'anin aure, ya d'aga darajar miji akan mace. Ina rok'onku, ku fad'a mata hak'uri da juriya ne kawai a cikin ko wanne aure amma dad'insa kalilan ne."
Daga haka ya fice daga gidan gabadaya. Daga Nene har Inna kowa bakinsa ya mutu murus. Yaya Usman ne ya ce "Allah yasa alheri mai yawa ya biyo baya. Sannu KYAUTA".
Da kai na amsa shi tare da daukar ayaba na yi Bismillah na fara ci.
Ana haka Yaya Rabiu ya yi sallama ya shigo.da tarkacen kayan da muka bar masa.
Ya gaida Nene cikin mutunci, ya kalli Inna ya ce "Kun iso lafiya?"
Ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah".
Ya sassauta murya ya ce "Sannu Kulsum, ya k'arfin jikin dai?"
Murya babu amo na ce"Da sauki".
Ya mik'e yana addu'ar samun dauwamemmen sauki. Sannan ya tafi.
Sai da aka yi sallar la'asar Inna Hauwa ta tafi gidanta tare da shirgin kayanta da na biki.
Kwana biyu da sallamo ni, lafiya lau nake jina, amma gabad'aya jikin nawa babu k'arfi. Da na yi tafiya zan ji na gaji. Ganin hakan Baba ya jinkirta tariya. Ya hak'ura ya bar ni sai na ji k'arfin jiki.
Kullum kuma sai Yaya Rabi'u ya zo ya duba ni. A kwana na uku ya sassauta murya ya ce "kyauta kina da wata matsala ne da jikinki?"
A hankali na ce "kamar ya ya?"
Ya gyara tsayuwar da ya yi ya ce "To me kike yi a nan gidan. Ai ke Malama ce kinsan dai babu kyau a daura auren yarinya ta cigaba da zama a gidansu. Kin wani saki jiki kina ta marairaicewa. Ki tsananta jikinki, a saka ranar tariyar nan kyauta. Bar ganina haka nima na iya jinya da rarrashi sosai fa".
Na yi dariya na ce "Yayah ke nan.
Ina na rufe baki sai ji na yi ya saki baki ya ce "Kin san Allah akan gadonmu zan kwantar da ke na dinga bin sashe sashe ina yi miki tausa a hankali, ina kuma dunbular abin da yake tsole mini ido."
Gabadaya na ji na rikice, kunya ta ban mamaki ta yanko mini. A kidime na ja jikina na shige cikin gidan. Ya bude murya yana kirana da yake baifi taku biyar ba tsakanin zauren da tsakar gidan tunda gidan k'arami ne.
"Kyauta ki dawo ban fadi abin da na zo fad'a miki ba ai".
Nene da ke zaune a rumfa ta yi kamar bata fahimci yanayin da na shigo da shi na kunya na shige uwar dakin ba. Ga shi ya bude murya yana kirana babu ko kunyar gidan surukai yake.
Yana tsaye Ibrahim ya shigo zauren ya same shi. Suka gaisa. Sama-sama ya ce "Ya ka tsaya, ka shiga mana".
Rabiu ya dauke kai ya ce "Ban gane ba, kada ka mayar da ni wani irin mana, shikenan bazan yi kunyar surukuta ba. Kawai idan ka shiga ka turo mini ita, ban gama fad'a mata kalaman bakina ba ta tsere ta bar ni.".
Yaya Ibrahim ya jijjiga kai ya nuna kansa ya ce "Ni zaka aika na kira maka Kyauta Rabe?"
Ni ban zama surukinka ba ashe, wanne irin raini ka yi mini ne?"
Ya dauke kai ya ce "To ina ce kai abokina ne, kuma gaskiya kada ka sake ce mini Rabe! Ka sani, bana so, nifa Wallahi zan had'aka da Baban titi ya mana iyaka, ka bala'in matsa mini, tun sadda aka fara maganar aurena da Ummu Kulsum."
Ibrahim ya yi sakare yana kallonsa domin ya yi zaton auren da aka yi masa da kyauta zai sa Rabi'u ya sassauta ya rage rikice masa da gangan.
Suna haka Baban titi ya shigo ya ce "Halan yau ma cece kuce kuke yi."
Nan da nan Rabi'u ya ce "Yauwa Baban titi raba ni da Ibrahim ya matsa mini akan me zaice mini shu surukina ne, ba nine babba ba? Ance kwana araba'in na ba shi. To akan me zai titsiye ni wai sai na girmama shi akan shi yayan Kyauta ne. Ko Yaya Usman da ya yi mini fiko mai yawa bai mini hakan ba. Gaskiya ya rage shiga hancina".
Ya fad'a da sigar damuwa. Baban kuwa ya ce "Ibrahim ka daina zungurar Muhammad Rabi'u. Ba d'an uwanka ba ne? Ai ba auren kyauta ne ya had'a ku ba. Bana son rashin gaskiya."
Kan dole Ibrahim ya ce "To Baba zan kiyaye."
Ya juya ya tafi yana gunagunin takaici wanda na takaici yadda ba wanda ya ce masa ga ranar tariya.
Kaitsaye gidansu ya afka, babu sallama. Inno ta ganshi tamkar jifa sai huci yake yi.

Ta sassauta ta ce "Menene kuma kai da har yanzu ba zaka daina fad'a irin na kumfar baki ba."
Tana d'isa aya ya ce "Inno na rantse ban tab'a ganin kaskantaccen ango Irina ba. Ta yaya za'a daura mini uare a saka ni kama gida, aje kuma a shirya shi, sai kuma a barni ni kad'ai? Na tabbatar ko kema ba ki tab'a ganin hakan ba."
Tsaki ta ja tare da mikewa ta bar shi tana fad'in shasha marar kunya kawai!
Ya yi sak'alo yana ayyana menene abin da ya yi na rashin kunya?
Ya make kafadarsa ya fito ya yi waje cikin kunci mai yawa.
**
Muna zaune a tsakar gida Nene na yin kad'ai da yake tana yin lagwanin risho Babanmu da Yaya Ibrahim suna tafiya mata da shi kasuwa, suna siyarwa.
Ta kalle ni ta ce "Yau dinma sai na ce ki debo maganin sanyin ki Sha? Wai ke wacce irin yarinya ce haka da ba Kya son magani? Kina dai Jin yadda innarki Hauwa ta fad'i kyawun maganin da ta yi kundubalar siyowa ta kawo miki, amma sai fama nake da ke ki sha. Shiyasa ban yi asarar kudina ba. Tunda ga wanccan hakkin dakan ma ki diba ki sha da madara amma kin k'i dad'in azanci. Na kyale ki, itama Hauwan ta ce na kyale ki, zaki nema da kanki ne."
Na yi k'asa da kaina domin tunda na fahimci amfanin hakkin dakan da take dirka mini nake jin matsananciyar kunyar na sha a gabanta. Gara na sanyi na kan sha, kawai ni ina cikin jerin mutanen da basa son magani ko wanne irin ne. Amma tabbas idan na sha na sanyin ina jin dad'in marata dama jikina, tunda hatta fitsarina canjawa yake yi. Haka kazar da aka dafa da Saiwowin chadi na cinye duk da dai ba ta dad'i ba ce, amma kuma bata da bauri ko kad'an.
Ku tuntubib wannan lambar 08032773332 don samun naku maganin sanyin sahihi cikin farashi mai rangwame.
Ba iya maganin sanyi ba, dukkan kayan gyara akwai wanda ake kawosu daga Chad.

A daren wannan ranar Baba ya ce gobe da yamma za'a raka ni dakina.
Ina dakina na ji wani irin matsananciyar faduwar gaba a dalilin maganar tariyata. Haka kawai nake shiga rudu da fargabar zan kad'aice daki d'aya da

7 / 9