Ba A Boran Namiji Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Binta Umar Abale Category :  Romance

Chapter   4 / 9

9K to 12K   out of 25.9K words

ta dakatar da ni daga barin abinda na ke yi. "E, wallahi Baba gata nan tana had'a kaya ta 'ki jin maganata kwana biyu Kulsumu bata mutuntuni, idan zan kafa doka a gidana itace take fara rusawa. Yanzu Baba daidai ne Kyauta ta dinga zage 'kwanji akan abokanan zamanta! Har sai da ta fasawa Nadiya baki fa."
Jikina ne ya yi kwata'kes jin irin sharrin da yake shirya mini a gurin mahaifina wanda nake ta jinsa yana salati da tu'ajibi.
Na sake tsinkayar maganarsa yana fadin." Wallahi kuwa Baba dama yau na ce zan zo na d'auke ka domin aje a basu ha'kuri ta dawo d'akinta ko saboda Yaranta."
Ban ji abinda Babanmu ya ce ba amma yanayin yanda yake magana a fusace da 'bacin rai shi ya kara tabbatar mini da cewa; Hud'ubar da Rabi'u ya yi masa ta samu gurbi a zuciyarsa.
Kashe wayarsa ya yi, ya kama hanya ya fita ya barni da akwati a gaba domin ya san abinda zai yi mini kenan ya dakusar da ni.
Akwatin na mayar Saman kwaba na duba agogo bakwai saura da sauri na tashi duk da ba girki na ba ne amma dole na sa Ido akan su Baffah dalili Nadiya da Aliya sun sa gilli a cikin zuciyarsu kowacce zata kimtsa Yaranta ne domin tafiya makaranta.
Kicin na nufa Jummai ta kammala musu abinci ta zubawa kowa a fulas. muka gaisa na tambayeta su Baffah nan take sheda mini ta yi musu wanka tun d'azu suna can suna shiryarwa.
Ina fitowa daga kicin na ji hayaniya na tashi daga gurin Nafisa. Gabana ne ya fad'i ban san ranar da zamu zauna lafiya ba a gidan nan. Nafisa 'korafi ne da ita, ita a haukanta ranar girkinta kada ya kula kowacce daga cikinmu saboda haka akace mata ana yi.
Fitowa ta yi hijabin wuyanta ya karkace tana share hawaye.
Da sauri na tari gabanta na ce." Nafisa menene haka da sanyin safyar nan?" Hannu ta d'aga mini a kufule ta ce." Kin ga Ummi kada ki yi mini wata magana tunda igiyar aurena a hannuki take sai ki sa almakashi ki datse d'ayar da ta yi saura dama biyun ma ke ki kayi sanadinsu."
Na tausasa harshe na ce." Nafisa don girman Allah ki koma d'akinki, ki yi ha'kuri da rayuwar nan kina kallo dai Hajajju ta yi wayo shekara goma Sha hud'u ga walida idan ku ka cigaba da irin wannan wallahi Khalid da Huzaifa ma da suke da k'ananun shekaru ba za su manta ba."
Yaran duk suka fito suka tsatstsaya da kayan makaranta a jikinsu. Da Ido na nuna mata su. Sai ta juya ta koma tana share fuska.
Na kalli Hajjaju dake share hawaye wato duk hatsaniyar da iyayen sukeyi a gaban yaran ne, na ce." Ke Hajajju ki ja su ku wuce ku tafi Adamu direba na jiranku."
Da sauri suka fita jikinsu duk a sanyaye."

Har na yi nufin tafiya gurina na sake tsinkayar wata sabuwar sa'insar a tsakaninsu.
Ban yi nazarin komai ba na kutsa kaina d'akin tana tsaye a kansa tana sakin kausasan kalamai tana kuka babu tauna harshe shi kuma yana zaune ya shirya tsaf Yana gyara link din hannuwan rigar dake jikinsa. Yun'kurin tashin da ya yi dukkaninmu ba mu yi tsammani ba kawai na ga ya d'auke fuskarta da wani bahagon mari! wanda sautinsa har sai da ya fita. Itama ta zabura ta matsa gefe hannunta dafe a kumatunta
Da sauri na shiga tsakaninsu bakina na rawa na ce." Wai Yaya Rabi'u don Allah menene haka? wannan fa ba mutuncinka ba ne, YA ZA A YI a gaban yara ka dinga tozartamu, wallahi zaka lalata musu tarbiyar baka sa ni ba."
Ba tare da ya ce mini komai ba ya ture ni ya je ya d'auki hularsa ya d'ora a kansa ya tsaya gaban mudubi yana daidaita zamanta.
Ashe ba ni kad'ai lamarin ya yi wa ciwo ba. Kawai sai na ga ta zabura! za ta nufe shi hawaye na zuba share-share a kumatunta.
Na ri'ke hannunta ina girgiza mata kai. Tana sheshshekar kuka ta ce ." Me yasa ba ki bari ya nakasta ni ba, ai duk abinda yake yi mana a gidan nan da sa hannunki, kin san ba girkin ki ba ne amma idan ya shiga d'akinki da asubah sai ki rike shi Allah ne kad'ai ya san abinda kuke aikatawa na shiga hakkinmu wallahil-azimin ban yafe ba."
Da mamaki mai yawa a tare da ni na ce." Nafi ki dinga kyautata zato na alheri tsayin shekarun da mukayi a tare ya kamata ace ki san halina, bana fatan ranar da zan ci amanar wani daga cikinku abinda ki ke zargi Bai ta'ba faruwa ba.
Ta cire hannunta daga nawa tana fad'in." Ai ga shi nan sai ki tambaye shi yaushe rabon da ya had'a shimfid'a da ni, yau kusan wata biyu kenan, Kuma na auna na lura duk ranar girkina yake shiga gurinki ya shud'e awanni bai fito ba, wallahi ba zan yarda ba sai manya sun shiga maganar nan."
Shiru na yi kawai ina kallonsa domin maganar ta girmi tunanina, lallai kishi ya rufewa Nafisa Ido da har ta yi subtar Baki gurin fad'in sirrin dake tsakaninta da mijinta. Na san dabi'arsa ce yin hakan, amma ni bana lamuntar son zuciyarsa duk da a wani 'kaulin Malamai sun yi inkarin cewa; Miji zai iya kwanciya da matarsa Koda ba ranar girkinta ba ne. To ni duk lokacin da ya bijiro mini da lamarin bana aminta gudun abinda zai je ya dawo, zahiri dai duk ranar da girki ya dawo hannuna baya daga mini 'kafa cikin kwanaki biyun nan ina jin jiki a hannunsa dan dai na saba da dabi'arsa ne tuntuni shiyasa ban fiye damuwa ba.
Maganarsa ce ta katse tunanin da nake yi. " Na 'ki na kwanta dake d'in, ai zuru na yi miki sakarya kawai babu abinda ki ka sa a gaba sai kishin jaraba. Ni ba soko ba ne, a gurin da na fi samun maslaha da nishad'i zan lalace, ki yi nazarin maganata."
Zuru mukayi muna kallonsa yana d'aura agogo a hannunsa babu abinda ya dame shi ya cigaba da cewa" Ita Aliya ai matar rufin asiri ce Dama ku ne kuke 'kokarin lalata mini ita, tana burgeni mutu'ka babu ruwanta da sakarci irin naku, kuma tana Jin maganata saboda haka ita da na auro a bayanku ta fiye mini ku sau dubu tunda zan kafa doka ta bi, kuma ba ta yi mini rashin kunya sakarkaru kawai."
Ya suri mukkulin motarsa ya kama hanyar fita 'kalau da shi sabuwar shaddar jikinsa tana ta motsi!
Tsabar takaici ban iya cewa komai ba na ja jiki na fita daga dakin guiwa a sanyaye, ba yau Yaya Rabi'u ya saba tsinka ni ba, amma zahiri cin mutuncin da ya yi mana a yanzu ya sosa mini zuciya, Rabi'u wani irin ba'aboren mutum ne da duk jarabar mutum ba zai gane ha'ki'kaninsa ba.

A yinin ranar na yi ta zuba ido na ga ko Nafisa za ta tafi gidansu shiru ba ta fito ba sai hankalina ya kwanta cikin zuciyata nake yi mana addu'ar samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Nafisa ta fita da girki Aliya ta kar'ba a tsakanin kwanaki biyun wata hatsaniya ba ta tashi ba maigidan ma baya zama sosai a dalilin hidimomin da suke gabansa na harkar kasuwanci, idan ya shigo gurina da asuba a tsaitsaye muke gaisawa ya fita.
Ranar da girki ya dawo hannuna ya shigo muka gaisa ya mi'ko mini mukkulin sito na ce." Me zan yi dashi kuma?" Ya ce." Tsarin na canza a gidana duk wacce take da girki zan bata da hannuna idan ta fita na bawa 'yar'uwarta."
Ban ce komai ba nasa hannu na kar'ba. Ya kama hanyar fita yana gyara zaman agogon hannunsa yau kwalliya aka ca'ba da k'ananun kaya sai ya yi kyau sosai ya dawo matashi babu wanda zai ce ya ajiye 'yar shekara goma sha hud'u dalili yana da jiki mai kyau kuma yana kula da kansa. Na ce." Adawo lafiya." Ya amsa kafin ya sa kai ya fita daga d'akin.

Dama tsarin gidan namu wacce take da girki ita ke bawa maigidan karin kummalo da abincin dare. Jummai kuma tana kula da hidimar abinda yara za su ci da safe da rana da wanda za su tafi dashi makaranta.

Towon shinkafa na shirya yi mana da daddare. Na sa Jummai ta harhad'a mini komai. Ina idar da sallar la'asar na yi niyyar shiga kicin. Sai kira ya shigo wayata Maigidan ne, a nutse na gaishe shi ya amsa yana shan toka. Shiru na yi ina sauraransa Ya ce." Yanzu Yunusa zai kawo kaji inaso ayi farfesu dalili yau Nadiya za ta dawo sannan ki sa Jummai ta 'kara gyara gidan a kunna turaran wuta."
Na ji wani gundumemen abu ya yi kakagida a ma'kogwarona. Saboda Nadiya za ta dawo shine za a yi farfesu na mussaman sannan a tsabtace gida harda su turaran wuta! Lallai Lamarin Nadiya a gurin Rabi'u azimun ne."
"Kyauta ko ba kya ji ne?" Ya fad'a a kausashe! Na daure sosai ina danne zuciyata na ce." Bayan farfesu me kuma za a yi Yallabai?"
"Shi kad'ai na buk'ata." Na ce." To za a yi in sha Allahu." Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake magana ba.

'Kwalla ce ta cika kwarmin idona. Na nemi guri na zauna k'afafuna duk sun yi sanyi. Nadiya ta 'kwace mini Yayana hawayen da nake dannewa suka su'bce suka fara falfala gudu kumatuna. Nasa hannu na rufe fuskata ina ta Kiran sunan Allah kafin na samu sassaucin kishin da yake yun'kuro mini.
Na tashi da rashin kuzari na fita daidai lokacin da yaronsa Yunusa ya shigo hannunsa da buhu muka gaisa sama-sama ya ajiye buhun ya fita. Na kira Jummai domin ta taimaka mini, kaji ne manya guda takwas a gyare. Na ce ta markad'a mini kayan miya kafin na zo kansu.
Har na kammala aikina Nafisa da Aliya babu wacce ta fito kowace tana gurinta da yaranta. Na zubawa maigidan nasa da yawa su Baffah ma na di'bar musu, sauran kuma na bari a kicin din na san duk zulumar mace za su ci su bari, Jummai da ta taimaka mini itama na d'ibar mata rabonta.

Sai da na gabatar da sallar magariba tukkuna na yi wanka na samu kaya marasa nauyi nasa a jikina.
Bayan Isha'i wajan karfe takwas Nadiya da 'Yan uwanta suka dira a gidan. Baffah da 'Yan'uwansa duk suka fice daga gurina suna ihu Mamanmu ta dawo. Murmushi kawai na yi na gyara kwanciya ina ta nazarin rayuwar duniya.

Hayaniyarsu har gurina duk da cewa akwai tazara a tsakaninmu. Ni da Nafisa muna daf da juna Nadiya da Aliya suna kusa haka tsarin gidan yake 'bangaran maigidan kuma yana tsakiyarmu sai babban gate wanda yake d'auke da d'akunun ba'ki da masu gadi da gurin ajiye motaci, cikin gidan kuma akwai babban tsakargida da band'akuna uku d'akin Yara hud'u da kicin mai yalwa, tsarin gidan dama can na zaman mace hud'u ne da kuma gurin da yara za su sake.

Sai wajejen tara da kwata tukkuna na daina Jin hayaniyarsu tabbacin sun gama abinda suke yi sun tafi, mamaki lamarin ya dinga ba ni, sai ka ce wata sabuwar amarya harda yin zuga! gurin dawo da ita.
Ashe mamakin da na ke yi lami ne domin lokacin da maigidan ya dawo kasa tsugun ya yi, ya kai ya kawo sai murmushi yake tauraruwarsa ta dawo. Ya shigo yana ta yi mini murmushi na babu gyara babu dalili, ni kuwa na sha kunu saboda yanda nake jin bala'in haushinsa kwata-kwata Rabi'u bashi da ta Ido ina tsammanin lokacin da akayi rabon kunya baya gurin.
"Kyauta ki kai mini abincina gurina sannan inaso zan yi magana daku."
"To." Abinda na ce kenan ban kara kallonsa ba. Ya shiga dakina ya yi minti biyu ya fito kafin ya sake maimaita mini maganar. Na sake cewa "To." Ban kalle shi ba, sai ya kama hanya ya fita, na bi shi da kallon takaici.

Lokacin da na shiga falon duk sun hallara ita tauraruwar tasa tana zaune kusa da shi ta ca'ba ado da wani lece wuya da hannu gold sai walwali take yi, ga lalle ja da ba'ki a hannu da kafa abinka da farar fata ta yi kyau kamar sabuwar amarya.
Na ajiye tiren hannuna a daddaumar da ya killace domin cin abinci.
Na samu guri na zauna ina d'an satar kallon Nafisa sai kace mahaukaciya Ido ya kod'e da wata koriyar atamfa ajikinta duk ta zazzage ko yari babu a kunnenta balle a kai ga maganar kwalliya ita ga wacce ta yi ta fad'a da miji sai hura hanci take yi. Ita kuma Aliya an sha k'ananun kaya riga da siket da kitson gaba sai da babu wata 'kira ta matantaka gaba da baya sai shukuran.
Da 'kyar na danne dariyar da take ko'karin 'kwace mini, na sunkuyar da kaina kasa ina nazarin yanayin zamantakewar gidan mata hud'u.

Gyaran murya ya yi kafin ya fara da Bismillah sannan ya kira sunayenmu duk muka amsa, sai ya d'ora Ido a kaina kafin Ya ce." Kulsumu ba zan ga ji da jadadda miki ba cewa; Ke din Wakiliyata ce a ko'ina. Ba wai don bana sonki na auri Nafisa ba, haka zalika ba don kun gaza ba na auro Nadiya Aliya k'addarata ce, kowacce da matsayinta a gurina. Kulsumu ke kin fi su sanin waye Rabi'u dalili auran kuruciya mukayi ni da ke, kuma ina sonki duniya ta sheda hakan kema kin tabbatar, ba wai na furta miki hakan ne domin ki yi fuffuka ba, yanda nake sonki haka nake son duk wacce na kawo gidana babu wacce ta fi wata a cikinku sai mai kyautata mini.
Kyauta ina gargadinki da babbar murya wannan ya zama na k'arshe kada sa'insa ya shiga tsakaninki da abokan zamanki ki mi'ka hannu da zummar duka, ba zan lamunta ba zan d'auki mataki a hukumance! domin babu wacce ki ka ajiye a cikinsu.
Ki ri'ke girmanki sannan ki kula mini da amanar gidana. wannan shine gargadina dake.
Ya numfasa kafin ya cigaba da cewa" Nafisa Nadiya Aliya ban amince ba ban kuma lamunta ba wata daga cikinku ta tozarta mini Kyauta, ita din wata baiwa ce ta mussaman wanda ni kad'ai na san hakan, kuma garkuwa ce a gare ni. Kada ku ga kun hayayyafa ku nemi wula'kanta mini ita ranku zai 'baci muddin na samu labarin faruwar haka. Itace babba a gidana Kuma mai wakiltata, duk da ba ta wani baku shekaru masu yawa ba, ya zama dole ku bata girmanta Wallahil-azimin duk wadda ta yi kuskuran cin zarafinta sai mun sa kafar wando d'aya. Saboda haka wannan shine dalilin zamana daku anan, ku zauna lafiya da junanku shine abinda nake buk'ata."

Shiru falon babu wadda ta yi magana. Sai na daure zuciyata a hankali na ce ." In sha Allahu zamu kiyaye Allah ya Kori shed'an a tsakaninmu." Shi kad'ai ya amsa da Amin.
Kafin ya ba mu umarnin tafiya.
Na koma wurina da tunani mai yawa a tare da ni. da kyar na ci abinci na yi shirin kwanciya domin ban yi tsammanin zuwa d'akinsa ba dalilin dawowar Nadiya a shari'ance ita za ta kwana tare da shi duk da cewa; Ni na yi girki sai kuma ga shi ya shigo Yana fad'in." Kyauta na ce Ya za a yi ne gashi ke ki kayi girki kuma Nadiya ta dawo ai bai kyautu mu yi mata haka ba ko?"
Ina bubbuge zanin gadona na ce." Gaskiya bai kyautu ba, kawai ka kwana a d'akinta ni ban damu ba. Ai tunda ta dawo an yi me wuyar."
Jim ya yi yana kallona kafin Ya ce." Anya kyauta ko dai akwai wani 'kulli a cikin zuciyarki ne ."
Na kalle shi ina jin kamar na farfasa masa hanci na ce." Wai ni Yaya Rabi'u yaushe za ka daina zargina ne? wane irin 'kulli kuma bayan yanzu na ji kana yabona a gabansu. Kuma fa shari'a ce ta ce hakan, ka je kawai ka yi kwanakinka idan basu isheka ba na baka kyautar nawa."
Murmushi ya yi mai sauti kafin ya tunkaro ni, Yana so ya rungume ni. Na yi saurin gocewa band'aki na bude na shiga ina jan tsaki.
Sai da na tabbatar ya fita daga d'akin tukkuna na fito. Na kwanta ina tunano abinda ya shud'e a shekarun baya..........


PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank. A tura sheda 07084653262. Masu tambayar wannan karon babu Vip ne . Zan yi amma a talgram kawai za mu kammala littafin cikin kwana goma ko 'kasa da haka da ikon Allah. Wad'anda suke bukata kuma suna yin talgram din sai su yi mini magana domin jin abinda za su biya. 'Yan Nijar kuma dala d'ari katin airtel sai ku yi magana da momina kai tsaye babbar macace don Allah a kula.
*+227 88 13 77 40*

*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE.*
[12/14, 11:04 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!*
*NA*
*BINTA ABBALE ABBALE πŸ’*
*M.W.A.*

Na yi nisa sosai a arewa.
*Binta Umar Abbale*
https://www.arewabooks.com/chapter?id=67482a18ca3a075ba0996752



52U/HARVERT NETWORKING BUSINESS.
*ALHERI NEπŸ’ƒπŸ’―*

Ina masu sha'awar shiga shahararren kasuwancin nan wato 52U basu da hali? Ga dama ta samu SZARIA tazo maku da sabon tsari domin taimaka ma marasa 'karfi, wato TEAM WORK. da kud'in ki 'kalilin zaki samu abunda zaki taimaki kanki da 'ya'yanki, tsarkakken kasuwanci ne mai ingancin da babu asara a cikinsa sai riba mai gwa'bi. 'Yar uwa maza ki shiga gruop dinmu ga link nan a kasa, domin mu gudu tare mu tsira tare.
Domin 'karin bayani ku tutubi wanan number 08037930727
https://chat.whatsapp.com/CSQ94ZeYnPJ26ppXhBnRII


9&10.
Sunana Ummu Kulsum Adamu Kyauta. Na samu inkiyar Kyauta ne a wajen mahaifiyata. Saboda maza biyu da na rako. Kafin nan kuwa sai da ta yi b'ari uku kafin cikina ya tsaya mata. Akwai tazara mai yawa tsakanina da yayana da na biyo wato Yaya Ibrahim.
Ina son sunan nawa na kyauta. Shiyasa ma na saka shi a cikin sunana a makaranta. A makarantar kuwa mafi yawa sun dauka inkiyar Babana ne ko ta kakana. Dan haka suke fad'in Ummu Kyauta, wasu ma kyauta kawai suke fad'a har malamai. Shi

4 / 9