Author : Binta Umar Abale Category : Romance
ko 07044417448*
5&6
Kansa ya girgiza ya kama hanyar fita yana sa'be babbar riga sai kace sabon limami.
Na yun'kura na tashi na fita zuciyata a 'kuntacce na shiga kicin domin lalubar abinda zan sa a bakina. Kicin din kace-kace babu gyara kudaje sai tashi suke yi ina kuma jin muryar Jummai mai yi mana wanke-wanken da shara a gurin Nafisa suna hira da dariya.
Raina ne ya 'baci ainun domin na san tabbas da Yaya Rabi'u ya lura da k'azantar kicin din a kaina zai sauke bala'i duk da ya san ba ni nake da alhakin hakan ba, zai ce ai ni ce babba amanar gidansa a hannuna take.
Kofar Nafisan na nufa na iske su a zaune durshen suna hira. Baffah da 'yan'uwansa suna zaune du'kun-du'kun da d'aud'a Nafisa ta yi wa Yaranta wanka tana shafa musu mai.
Babu fara a fuskata muka gaisa sama-sama, na ce." Jummai kin ga kicin kuwa 'kudaje sai bi sukeyi kwanuka duk sun bushe kina zaune kina hira ga sharar tsakargida da gate duk ba ki yi balle ki wanke band'ukuna, lokacin nan fa takaitacce ne, har yaushe ki ka kammala wannan aikin ki ka d'orawa Yara abincin rana, kuma kin riga kin san islamiyarsu ba su da wasa gaskiya Jummai ki canza idan ba haka ba zan sanar da maigidan halin da ake ciki domin wannan shine karo na uku."
Cikin ya'ke ta ce." Yi ha'kuri Uwar dakina bisimillahi bari na tashi na yi aikin da yake gabana.
Nafisa ta dakatar da ita babu fara'a a fuskarta ta ce." Wai Ummi girki ki ne ko nawa da za ki shigar mini hurumi?"
Jim na yi ina kallonta kafin na ce." Girki ki ne amma ba sai na yi miki 'karin bayani ba kin san komai.
Sunkuyar da kanta ta yi tare da cewa" Ni fa ki daina yi mini katsaladan ina ganin mutuncinki, ranar girkinki bana sa miki Ido saboda haka babu ruwanki Jummai dai ni na kira ta muna magana kuma ba ke ki ke biyanta albashi ba."
Murmushin takaici na yi na ce." Sai ki fad'awa Mijinki idan ya ce na zare hannuna daga kanku dama haka na fi bu'kata."
Ta bugi kirji tana fad'in." Ni fa ba Nadiya ba ce wallahi, kin san ni sarai idan ki ka yi mini ba zan saurara miki ba, ya kamata ki fahimci wannan, zaman aure ki ke yi, zaman aure nake yi, na lura kawaicin da nake yi miki ba kya gani amma idan ba rashin mutuncin ba ina ruwanki da shiga abinda bai shafe ki ba."
Tsaki na ja na kalli Baffah dake zaune yana had'awa 'kannansa jirgin Leda na ce." Ku ta shi Baffah mu je ayi wanka."
Da sauri ta ce." A banza dama ai babban burinki ki kore mu daga gidan, kin kori uwarsa kina kinibibi, ai wallahi Kulsumu tuntuni na dawo daga rakiyarki, ki juya mana miji sannan ki juya mu to ni wallahi ba ki isa ba, kin yi tsararo! Kuma zama daram a gidan Rabi'u."
Ban tanka mata ba saboda ganin yadda Yaran sukayi tsit! suna kallonmu, kawai na yi gaba ina fad'in" Baffah ku biyo bayana ayi wanka, ke kuma Jummai wata'kila shan ruwanki ne ya 'kare a gidan tunda gulma da munafurci ki ka zo yi."
Ina jin hargowarta tana fad'in." Ba ki isa ba wallahi Jummai zama daram dam! sai ke ki fita ki bar mata gidan. " Takaici ya kama ni, dama ai mai hali ba zai fasa halinsa ba, lokacin muna biyu Nafisa ba irin cin mutuncin da ba ta yi mini ba, sai ta kai ni bango wani sa'in nake turmusheta na daki kayana Yaya Rabi'u yazo ya yi ta shari'a, ta kama hanya ta tafi gidansu wai ta yi ya ji saboda na doke ta, idan ya yi biko ta'ki ta dawo sai ya rabu da ita ya shiga sabgoginsa, da k'afafunta take dawowa saboda iyayenta ba su da karfi wasu daga cikin 'yan uwanta ma a k'arkashinsa suke cin abinci, kuma da yake Ubanta dattijo ne duk abinda zai shiga tsakaninmu ba ya goya mata baya, saboda sanin halinta sai dai ma ya ba ni ha'kuri ya tattaramu ya yi mana nasiha har mijin namu gabad'aya.
Ina ko'karin kunna wuta Jummai ta shigo tana soki burutsu duk a 'ko'karinta na kare kanta ta kar'bi ashanar da take hannuna tana gyara bakin buhun gawayi zata zuba a korfoti take fad'in na je na zauna yanzu za ta d'umama ruwa ta yi wa yaran wanka.
Kafin ma na yi magana Baffa ya yi caraf ya amshe Yana fad'in "Munafuka wallahi sai na fad'awa Babanmu maganar da na ji kuna yi akan Mama har kuna k'yalkyala dariya ai duk na ji abinda ku ke fad'a ke da Ummansu Walida."
Jummai ta diririce ta fara kame-kame. Yaron ya cigaba da za'kulo zance wanda ya d'aure mini kai mutu'ka wato dama amincin da yake tsakaninsu na gaibu ne suna yin hakan ne domin su kai ni kasa wai Nafisa yau ita take farinciki da fitar Nadiya har tana addu'ar Allah ya sa ta tafi kenan ba za ta dawo ba.
Na yi sauri na daka masa tsawa jin yana ko'karin zaginta saboda tana musantawa, Baffa ba k'yalle ba ne, ba shi da kunya uwarsa ma bai bari ba balle wani.
Na kalleta duk ta muzanta sai zare Ido take yi na ce " Jummai kin ba ni kunya wallahi, ai idan duniya da gaskiya ba za ki zauna a ci naman Nadiya dake ba idan an yi duba da irin hidimar da take yi miki a gidan nan cikinmu babu wadda take kwatantawa, ba gori zan yi miki ba daga gidansu Nadiya duk shekara kina da Zakkah ta bayar da sunanki, sannan da Azimi kina da buhun shinkafa da gero bayan wanda maigidanmu zai ba ki, da sallah kina da turmin atamfa da kudin d'inki duk daga gidansu Nadiya, idan ban mance ba kuwa Nadiya idan ta tashi bayar da kayanta dana Yara ke take had'awa d'auri guda ki d'auka ki kai garinku amma yau dake aka zauna ana cin dunduniyarta.
"Billahil-lazi 'karya yake mini Uwardakina kwarankwarsa dubu ban......Katse ta ya yi yana fad'in." Wallahi Ummi karya take yi Munafuka ce domin har ji na yi suna cewa wai kin wanke wandonki kin bawa Babanmu ya sha a ruwa kece ki ke sarrafa shi, sai umarnin da ki ka bashi."
Jummai ta yi tsuru-tsuru tana zare Ido.
Hakan ya tabbatar mini da gaskiyar maganar Baffah dama kuma yaron da wuya ya yi k'arya, kusan halinsu d'aya da ubansa rashin tsoro da kafiya da taurin zuciya!
Na kalleta tana sinne kai na ce." Jummai yi maza ki kunna wuta zan yi wa tufkar hanci.
Ido jawur ta ce." Dan zatin Allah ki rufa mini asiri kada ki sa a kore ni wallahi zan kiyaye gaba, zan kula da aikina.
Tausayi ta ba ni ganin yanda take shirin fashewa da kuka, tabbas idan na fad'awa Yaya Rabi'u abinda ya faru babu makawa sai ya sallameta 'karshe ya had'a mata da cin mutunci tunda na san hali.
Na ce." Jummai wannan ya zama na farko kuma ya zama na k'arshe kada ki kuskura ki sake ke'bewa da wata daga cikinmu ki yi gulma idan hakan ta sake faruwa a bakin aikinki."
"Zan kiyaye wallahi ba zan 'kara ba." Cikin nadama ta yi maganar. Na ce." Ki d'ora musu ruwan wanka idan kin sauke sai ki dafa mini indomi biyu.
Ta amsa da sauri ta fara ko'karin rura wuta.
Yaran na ja d'akina muka zauna ina ta kwakwkwafar Baffah akan maganar kada ya fad'awa Babansu ko Mamansa, da 'kyar na shawo kansa ya yi mini al'kawarin babu wanda zai fad'awa a cikinsu. Sai hankalina ya kwanta domin ina fargabar maganar ta fita wani rikicin ya 'balle wata'kila itama Nafisan yana iya kora ta gidansu muddin ya ji murna take da fitar Nadiya a yadda hankalinsa ya tashi da faruwar hakan bai 'ki gabad'aya mu fita mu bar masa gidansa ba muddin Nadiya tana ciki.
Da daddare muna tare da yaran a dakina muna karatu Ya shigo na yi sauri na yi masa sannu da zuwa ya amsa babu walwala yaran suka gaishe shi ya amsa ya nemi guri ya zauna kan kujera.
Baffah Ya ja 'yan'uwansa za su fita sai ya dakatar dasu suka koma su ka zauna, ni kuma ban so Hakan ba domin tunda na ga yanayin fuskarsa nasan abin babu dad'i, wata'kila duk dabarunsa sun 'kare akan lamarin sai kawai na ji hargaginsa Yana hura hanci yake Fad'in." Kyauta kin san Allah da Annabi sai kin gyara kwa'bar da ki ka yi idan ba haka ba zamu sa kafar wando d'aya dake. YA ZA A YI Littafin Binta Umar Abbale Ya za a yi ki yi sanadin fitar Uwar Yara ki zauna kina koya musu soki burutsu, ni kin bar ni da kame-kame! Ina galantoyi kina so ki sabauta mini rayuwar yarana, shi fa d'a dole sai uwarsa, ba zaki ta'ba burge ni ba idan wannan salon ki ka d'auka, ki kyale ni da matata ya fiye mini, yanzu ga shi juyin duniya Nadiya ta yi fushi ta'ki dawowa dole sai kin taka sayyadarki kin je gidansu kin bata ha'kuri da iyayenta. Ina dalili ni da na ajiye matayena ban mika hannu na dake su ba sai ke, to ba shakka zan sayi bulala na rataye duk ranar da hannunki ya kara gangancin dukan wata da cikinsu na rama musu ba zan lamunta ba."
Tunda ya fara maganar Bai tsahirta ba har sai da ya kai geji tukkuna ya ajiye Yana nishi kamar wani kumurci tsabar bala'i hular da take kansa ma ta karkace tsininta ya yi gefan kunansa, banta'ba ganin namiji da gumin hanci ba sai akan Yaya Rabi'u, idan Yana bala'i karan shancinsa dabaibayewa yake da gumi kamar an yayyafa ruwa.
Shiru na yi tak ban ce ba, domin ina iya yin magana ta 'baci dalili ya Kai ni ma'kura inda nake Jin ba zan iya jurewa ba, shiyasa nake ta nanata Kiran Allah a cikin raina saboda bana so mu yi b'ataciyya a gaban Yara. Allah ya kar'bi addu'ata kuwa Yana cigaba da nanata maganar Hajjaju ta shigo tana kumbure-kumbure daga Bakin kofa ta tsaya tana fad'in aiken da akayi mata.
Aikuwa ya buga mata tsawa da sauri ta zube a kasan gurin.
Ya ce." Don Ubanki waye sa'anki a gurin nan ? Za ki shigo babu gaisuwa ki tsaya kerera akan mutane zan yi maganinki da Uwartaki Gabad'aya.
Da rawar murya take ba shi ha'kuri tana gaishe shi, Bai amsa ba illah ta shi tsaye da ya yi, ta gaishe ni na amsa ban ko kalleta ba, domin na San gaisuwar dole ce ta yi mini dalilin Ubanta.
Ya nufi bakin kofar Yana fad'in." Ta shi daga gurin nan kafin na k'araso dan ball zan yi dake na karya ki."
Da sauri ta ta shi ta raku'be har ya wuce kana ta bi bayansa.
Zazzafar ajiyar zuciya na sauke na d'an sa ci kallon yaran domin lura da halin da suke ciki. Wasa suke yi Amma ga dukkan alamu Baffah duk ya nad'e abinda ya faru domin na ga sauyi a tattare da shi.
Na ce." Babbah anan zaku kwanta ne ko a dakinku?"
Kai ya girgiza tare da cewa" Zamu kwana a nan." Na ce." To maza ka je ka d'auko muku bargo sai ku rufa da shi tunda ana sanyi.
Da sauri ya amsa ya ta shi ya fita.
Duk yanda na so na danne ba'kincikin da yake cikin raina kasawa na yi, na kwana ina kuka da tunanin abubuwan da Yaya yake mini. Wai ni yake wa gorin haihuwa har Yana fad'in d'a sai uwarsa wannan kalma ta tsaya mini a raina mutu'ka idan na tuna kausasan lafuzansa sai hawaye masu azaba su goce mini. Yaya Yana da manta alheri, a tunani na ni da shi mun zama d'aya 'ya'yansa nawa ne wallahi har a cikin zuciyata haka nake ji ko da na haihu ba zan iya bambamta abinda ya Haifa da wata da Wanda na haifa ba, sai ga shi da bakinsa yake munana zato a kaina yana jifana da manyan kalamai duk akan Nadiya da iyalinta to ina tsammanin zai yi biyu babu domin na rantse da girman Allah muddin ni zan je masa bikon matarsa sai da ya sake ni, tunda shi mutum ne mara adalci idonsa ya rufe saboda Yana Jin tsoron bacin ran Ubanta a matsayinsa na Ubangidansa zai d'auki lefi ya d'ora mini ni kad'ai alhalin ya san taura biyu Bata taunuwa haka kawai ba zan Kai hannuna jikinta ba sai da dalili, zahiri sai dai ya zaba Ni ko Nadiya wannan shine hukuncin da na yanke.
Ina zaune a kan dadduma ina lazimi na ji maganarsa da Yara suna gaisawa.
Ya shigo d'akin babu sallama ya coge daga bakin kofa.
Zuciyata na danne na gaishe shi, Ya amsa Yana muzurai! sai na kawar da kaina daga barin kallonsa saboda yanda nake jin wani irin haushinsa.
"Ki tashi ki shirya gari Yana yin haske zan sauke ki a gidansu Nadiya domin ki bata ha'kuri da iyayenta, mahafinta mutumin kirki ne ba za ki yi mini kasassa'ba."
Uffan ban ce masa na ninke dadduma na kwanta a gado. Sai ya shigo d'akin sosai ya tsaya a kaina yana magana.
A nutse na tashi zaune na ce." Idan ka yarda idan na yi maka bikonta ni zan wuce gidan tsohona wannan shine hukuncin da na yanke." Yanda na yi maganar babu wasa shine ya sanyayyar masa da guiwa, ya zauna kusa da ni yana yi mini wani irin kallo.
Na ce." Ka za'ba Kulsumu ko Nadiya Yaya na gaji da zaman gidanka Allah ne sheda na yi abinda zan yi Allah ya saka mini tozarcin da ka ke yi mini." Kuka mai k'arfi ya k'wace mini.
Kamo ni ya yi yana so ya rungume na kama hannunsa na gartsa masa cizo! Ya ri'ke hannuwana duk biyun Yana girgiza kafad'ata. A raunane Ya ce." Kyauta Ya zan iya rayuwa babu ke! kin san dai abinda ki ka yi ba daidai ba ne, me ya sa za ki dinga dukan iyalina? ke waye ya yi miki haka? Kuma kin fi kowa sanin matsayin Uban Nadiya a gurina, me yasa a matsayinki na wakiliyata ki ka d'aura damarar wargaza mini kan gida, duk wata 'baraka daga gurinki take fitowa ya ba zan yi zargin ki ba."
Ina kuka na ce." Shiyasa kenan ka ke yi mini gorin haihuwa ko Yaya Rabi'u? Ni ban yi maka gori ba sai kai za ka yi mini, anya duniya da gaskiya Yaya, kullum rikici idan ya tashi a gidan nan baka bin ba'asi ni kake d'orawa lefi na gaji wallahi, dama ban ajiye komai ba ka sallame ni kawai ka zauna da masu cikin haihuwa, ba za ka had'a kai da matanka ku tarwasa mini zuciya ba." Kuka na ke yi mai cin rai. Na tashi da sauri na fara birkito da kayana da suke jere a cikin kwaba...
PAID BOOK
#500via 7084653262....Binta Umar Opey bank ko 0542382124...Binta Umar gtbank. A tura sheda 07084653262. Masu tambayar wannan karon babu Vip ne . Zan yi amma a talgram kawai za mu kammala littafin cikin kwana goma ko 'kasa da haka da ikon Allah. Wad'anda suke bukata kuma suna yin talgram din sai su yi mini magana domin jin abinda za su biya. 'Yan Nijar kuma dala d'ari katin airtel sai ku yi magana da momina kai tsaye babbar macace don Allah a kula.
*+227 88 13 77 40*
*GARKUWAR MATA*
*BINTA ABBALE*
[12/13, 9:16 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*ADVERT* *HTTPS://INCENSEREPuBLIC.NG*
*KANO NAJERIA*
*GIDAN 'KAMSHI DA FITA KUNYA.💯💃*
*Ina masoyan kayan kamshi Ina manyan mata? mata 'yan kwalisa? wannan sanyi fah sai da turare trust me kina bukatar turaren wutan Incense republic muna da turaren wutar daki,turaren jiki,turaren kabbasa da kabbasa spray ba a iya turarukan wuta kadai muka tsaya bah muna da humrori asalin humra mai kamshin manyan Hajiyoyi irin asalin kamshin yan Maiduguri ba tsami gaye bah 😄 Ga kuma kullacha maii Tashin kai 💥wadda zaki ji dadinta a wannan yanayi na sanyi.Sannan muna da oil perfumes da zaki iya shafawa ko a jiki ko a kaya kuma wani abin burgewar a cikin oil perfumes dinmu akwai wanda har maza za su iya amfani dashi. Hajiya za ki iya sayawa mijinki ko kuma saurayin ki saboda kara dankon soyayya ♥️💃*
Turaren wuta
Humra
Kullacha
Kabbasa spray
Turaren Kabbasa
Turaren wanka
Room Freshner
Oils masu kamshi
Souvenirs package mai dauke da Turaren wuta,Humra,Kaskon turare wuta da Lalle da sticker
*Domin neman karin bayani sai a tuntubi wannan lambobin*
Wa.me/2348137369317
0813 736 9317 ko 0904 482 2052.
Na yi nisa sosai a arewa.
*Binta Umar Abbale.* https://www.arewabooks.com/chapter?id=67482a18ca3a075ba0996752
7&8
Ya dabaibayeni ta baya. Na fara turjewa ina buge hannuwansa. Yana nishi yake fad'in." Kyauta ki ka fita daga gidan nan, Allah sai ranki ya 'baci wai ya kuke so na yi da rayuwata ne? Me yasa ko wane namiji yake zaune lafiya da iyalinsa, amma ni kun mayar da ni gaula kullum cikin fargaba da zullumin kaidinku."
Na kalle shi hawayena na zuba na ce." Kai ka saya duk abinda yake faruwa a gidanka ba ka da adalci, dan haka ni na yi abinda zan yi a zamana da kai Allah ne sheda ban cuceka ba."
Kafin ya ce wani abu kira ya shigo wayarsa ya fito da ita daga gaban aljihunsa ya rike tsintsiyar hannuna katamau! Ya sa wayar a kunnansa.
Nafisa ce cikin hayaniya ta fara yi masa sababi! maganganuta duk a kaina ne tana furzar da su da tsantsar kishina da yake cikin k'okon ranta.
Na d'auka zai biye mata sai naga ya kashe a jirkice ya kalle ni ." Kyauta kada ki fita daga gidan nan idan kina so mu wanye lafiya." Da sauri na ce." Idan ba na so kuma fa?"
Tashin hankali muraran! Ya bayyana a cikin idonsa. Duk ranar da ya tu'ke ni na yi masa tutsu! irin wannan ya kan ransa nutsuwarsa komai nasa Yana tsayawa cak!
Na ja tsaki na juya ko tausayi bai ba ni ba domin duk abinda yake yana sane ya mayar da ni karkatacciyar kuka duk jarabarsa idan da tashi a kaina zai sauke.
Maganar da yake a waya ita