Author : Binta Umar Abale Category : Romance
[12/10, 8:46 AM] Bintu: *BA A BORAN NAMIJI!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
Yabo da godiya su tabbata ga Ubangijin talikai. Tsira da aminci su kara tabbata ga shugaba Annabi Muhammadu S.A.W.
Wannan littafi ban yi shi don wani ko wata ba. Kama daga sunaye gari kamanceceniya. Idan an yi katari da hakan arashi ne. Ban yarda a yi amfani da labarin nan ta kowace irin siga ba, idan aka aikata hakan ba ni da masaniya Allah Ya saka mini.
*SADAUKARWA NE GA:*
*NANAH ABDUL*
*TUKWUCI NE GA:*
*SURAYYA DEE*
( Halin Yau)
*GODIYA TA MUSSAMAN GA:*
Momi Fatima Musa
Hajiya Babbah
Autar manya
Halima wada kura
Prof Asabe Kabir
Halimatu
Amarah
Basira Hamza
Usaina Ibrahim
Zainab Yola
Zainab
Fadima Sani
Hairi
Sakina Jumpum
Rauda Abubakar
Zainab Salisu Umar
Ummi Labaran
Maman Rahama
Ummu Ulfat
Rabbatul-Bait
Rajkumari
Maman Janan
Fatima Gwaram
Asiya Mu'azu.
*KANO STATE*
*UNGUWAR KURAWA*
*Shimfid'a*
1&2
"Kyauta kina ina? fito nan, wallahi yau a gaban kowa za'a yi ta ta k'are na gaji da wannan halin na ki".
Zuciyata ta harba tare da zullumin yau kuma mai aka shiryo mini ni Ummu Kulsumu"
Na fita ina hirji.
Gabadaya matan gidan suna tsaye sun yi cirko cirko tamkar zakaru.
Ya kausasa harshe yana cewa "Kyauta wana d'amkawa ragamar kulawa da sito din abinci?" Murya babu amo na ce ni ce amma me ya fa.....
Ya daga hannu a zafafe yana cewa " Sa aya kawai malama, ta ya ya za'a ce mini babu man gyad'a da indomi a gidan nan?"
Zuciyata ta buga da tsananin gaske. Domin ni kaina na ka'du da furucinsa. Idan lissafina daidai ne to
kuwa yau kwanaki goma kacal da bude jarkar mai 25 Lita. Taliyar yara kuwa yau kwanaki uku da ya shigo da katon biyu. Sau daya kacal na dafa domin kuwa su ban ga sun dafa ba ma. Amma ace yau babu. Lallai dole ya yi fad'a ban ga laifinsa ba a yanda rayuwar nan ta yi tsanani.
A sanyaye na ce "Allah ya huci zuciyarka Yaya amma wallahi ban san komai ba akan wannan sha'anin. Kuma Dole idan iyalai suka yi yawa sai an yi hak'uri saboda hidima tana k'aruwa za'a gyara In sha Allah"
Ya ja tsaki ya ce "Kina nufin dole na yi hakuri na zuba ido kina neman yi mini sanadin shiga ba'kin talauci?
Nawa ake siyar da kwalbar mai ne bare jarka? wato bak'in cikin da ake cewa kina yi ne yake neman fitowa muraran ko?"
Nan da nan zuciyata ta karye hawaye ya cika idona murya na rawa na ce "Yaya da bakinka kake jifana da yi maka bak'in ciki a cikin gidanka?"
Maimakon ya sassauta sai kuwa ya sake fusata ya ce "Ba iya bakina kad'ai nake magana ba, har da zuciyata. Domin mugunta da bak'in ciki ya sanya kike kwashe mini kayan abinci".
Kuka ya ke ce mini. Na kasa cewa uffan domin zuciyata ta yi nauyi ainun! To na kwashe kayan abinci na kai su ina?
Ya ja tsaki ya ce "Kukan ki ya k'are Kulsumu je ki dauko mini mukullin sito din hannun ki. Na yi iyakacin kokarina akan na baki girmanki amma abin ya faskara dan haka idan girkinki ya zo sai ki karba a hannun Nadiya."
Kafin na yi magana. Nafisa ta yi fit ta ce "Ai kuwa idan kana nufin ita zaka bawa mukullin sai dai a raba girki amma tabbas ban yarda da alwalarta ba bare ta ja mu jam'i."
Aliya da ita ce amarya ta ce "Ai kuwa dai ni ma ban yarda ba.
Kukana ya tsaya cak. A dalilin na fahimci dukkansu sun had'a kai ne dan su kai ni k'asa.
amma kuma da za'a shugabantar da wata a cikinsu ba ni ba, to zasu koma rikici da junansu.
Na yi k'asa da kaina.
Ina jin sauki da jarumta na ratsa ni. Wato duk da ni kad'aice ban haihu ba a gidan ba ni da ko kaza amma na dame su, na yi musu karantsaye a zukatansu.
Duk wadda ta kwaso makircinta a kaina zata sauke shi. Abin da yake d'aure mini kai shine; ba ga ni suka yi yana fifita ni ko yana tausaya mini ba. Asalima wani cin kashin suna yi mini ne dan sun ga yana yi mini kai tsaye babu d'ar.
Nafisa ce kawai take sassauta mini tare da mutuntanta ni itama kuma akwai dalilin hakan ba wai tana yi ne dan na kai ta yi mini ba. ta yi ne saboda yadda nake cire Ido akan yaranta mussaman hajjaju dukda yarinyar bata mutuntani na kan saya mata kayan ado da kwalliya ganin ta fara girma idan na fita duk abinda na gani na mata sai na sayo mata, wannan dalilin ne kadai ya sa take daga mini kafa, amma duk lokacin da ta so rashin mutuncinta mancewa take yi da komai Nafisa fitinnaniya ce sosai domin duk rabin rigimar da take faruwa a gidan itace take haddasawa dan dai kawai maigidan a tsaye yake shiyasa take shakkarsa.
Maganarsa ta katse mini tunanin. Domin a kausase ya ce "Nafisa ki yi duk abin da kike ganin zaki yi, ita zan bawa idan kuwa kin ga ba zaki bi hakan ba kina iya tafiya ai ba daure ki na yi ba."
Yana rufe baki ta fashe da kuka ta ce "Akan me zaka dinga nuna banbanci tunda ka bawa Kulsum ka ga bata yi maka yadda kake so ba, ai yanzu ni ce nake bin ta, ba sai ka ba ni ba, amma ka tsallake ni ka tafi kan wadda ta zo daga baya dan kawai ita kana jin tsoronta, saboda babanta maigidanka ne!.
Ya harzuka ainun ya ce "Ki tsarkake bakin ki Nafisa domin wallahi zaki koma gida, kin san na ce miki ba zan sake daukar iyashegen ki ba. Tabbas ba ki yi karya ba ubanta maigidana ne kamar yadda nake maigidan yayunki guda biyu."
Ta sake rushewa da kuka fiye da na farko.
Nadiya ta zabgata mata harara tana cije bakinta ta ce." Nafisa ki iya bakinki fa kada mu kwashi 'yan kallo a wurin nan, wace irin magance wannan ko ubana abokin wasanki ne?"
Ya daka musu tsawa Yana gyara zaman babbar rigar jikansa Ya ce." Ku ka kuskura ku kayi cacar baki a gabana ba zamu wanye lafiya ba." Sai kowacce ta yi shiru.
Ni dai Allah Allah nake yi ya sallame ni na koma dakina. Ko kad'an ban ji ciwon karbe mukullin rumbun abinci da ya yi a hannun ba. Asalima sauki zan samu tare da addu'ar y'ar manuniya ta nuna kanta.
Ya Kalli Aliya ya ce." Saboda Nafisa ta ce ba ta yarda ba ke ma ba ki yarda ba ko? To zan ga wanda zai rusa mini tsarin gidana a cikinku."
Ya ja tsaki ya wuce yana banbamin bacin rai. Wanda har cikin zuciyata nima na ji takaicin yadda aka kwashe kayan abincin. Ina matukar kaduwa da bak'ak'en taadodin da matan yau suke aikatawa da sunan kishi.
Ban da haka ka samu mijin da zai ajiye maka abinci ka diba babu fargabar awo amma sabida son sai an yi makirci da mugunta sai a kwashe dan kawai ana son a kai wata k'asa.
Sannan ban da abinsu ni da suke yiwa wannan makircin dan kawai suna kallon bani mukullin wata alfarma ce, bakina ne kad'ai, su kuwa fa?
Nafisa da ita ce amaryar da ya fara yi mini yaranta hudu a yanzu. Babbar shekrarta sha hudu. Wacce sunan mahaifiyarsa ta ci muna kiranta Hajjaju. Sai mai biye mata sunan uwar Nafin ce Aisha sai muke kiranta da Walida. Tun kuma daga lokacin gwamnatin Nafi ta fara sanyi a wajensa a dalilin ba mata yake so a haifa masa ba. Ni ban haihu ba, sanadin haka ne k'arin auren. Ya samu haihuwar kuma sai kuma jinsin da ake haifa masa basu yafi so ba. Dan Adam da butulci da izgili yake. Ni da zan bada komai dana mallaka na haifi macen da na yi. A dalilin haka ya auro Nadiya wacce y'ar maigidansa ne.
Nadiya kyakkwar yarinya ce ta gaske.
Sannan tana zuwa ta haifo masa namijin da yake muradi. Shekararta bakwai yanzu a gidan yaranta hudu duk maza. Yayin da Nafisa ma ta sake haifar namiji Khalid a huzaifa yaranta hudu kenan biyu maza biyu mata Ga Nadiya da take da Baffa sunan mahaifinta, Sadik, Umar Usman. Wadannan dalilan ya sanya da wahala ya yiwa Nadiya wulakanci a gaban jama'a sai dai ko a dakinta tunda ta sha yin yaji ana dawo da ita. Amma dai yadda ake ga ni tafi mu kyallin goshin a wajensa. Y'ar babban gida kuma uwar mazaje reras.
Sai Amarya Aliya da take da yara biyu Aliyu da mai sunana Ummu Kulsum.
Tamkar kazar da k'wai ya fashewa haka na ja sayyadata zuwa dakina.
Na fadi tamkar wadda aka ingiza ni kan kujerar falon.
Tsawon lokaci na zama mutum mutumi. Ba abin da nake yi sai nazarin rayuwa. Wai menene riba ne idan mace ta sace kayan abinci sannan ta kitsawa miji da mutanan gidan watabce daban ba ita ba? A da na dauka sai tsofaffin mata ne suke irin wannan makircin ashe yaran mata ma sun iya shirya kaidi. Ko da yake ai ance kowacce mace da irin nata makircin. Hawaye ya balle mini a dalilin yadda kullum zaman gidan yake sake tsananta mini. Shi ya yi, matansa su yi, haka yaransa su yi mini. A yadda nake gani barin gidan shine yafi alheri a gare ni, tunda Wanda ya ajiye ni ba wani muhimmancina yake ga ni ba. Yana gigicewa ne idan ya kuntuka mini takaici na gudu gidanmu hankalinsa yana tashi ya dinga tura jama'a har sai an dawo da ni. Mafi yawa dangina da makusantana gani suke yi hak'urina ne ya yi karanci a dalilin ban samu haihuwa ba. Amma ai ko dakina aka shigo aka yadda yake a shirye da kayan alatu an san yana sona. Ni Kuma ni nasan me nake fuskanta a hannunsa. Ba abu mai wahala ba ne ya yi mini tijara akan y'aya'nsa tunda shi mutum ne mara kawaici da rashin ha'kuri. Yanzu duk rashin kunyar da Hajajju take yi mini da zan d'an bugeta sai kowa ya ji bare kuma ace Baffah ne shalele. Shi wannan da a ta'ba shi a gidan gwara an yi ya'ki, domin ko Uwarsa ce ta yi masa hukunci muddin Yana gidan suna kwasar 'yan kallo. Kuma nan da can ba ya aikuwa hatta na uwarsa ma baya zuwa shiyasa bana damuwa. Walida ce Allah ya had'a jinina da ita. Duk yadda uwarsu take hanasu zuwa wajena sai ta faki ido ta zo mini. Ni kuwa bana gajiya da mika mata komai nake da shi mussaman da yake Ina sana'ar kayan Kwalam da makulashe. Domin ina yin albushir na bayar akan sari, ina yin iloka a biyani lada, ina yin kuma ta siyarwa, sai dai ni da yawa nake yi sai azo a sara na bi karamar riba na karbi kudina take. Sannu a hankali na k'ara da tuwon madara da y'ar kullisuwa. Dan haka kullum bana rabuwa da kayan dad'i a dakina. A dalilin hakan sai na yi y'aya' da yawa. Ko na gidan basu zo ba, to kuwa na makwabta yini suke suna yi mini sintiri. Domin duk sadda zasu tafi islamiya sai sun shigo sun karbi alawar madara ko albishir. Hakan ta sake jawo mini iyayensu. Dan haka ban saka rashin haihuwa a raina ba domin na yi imani ba itace karshen niima ba. A duk sadda aka guma mini azanci ko bak'in ciki akan yara. Bana zama na yi kuka domin idan na tuna Nana Aisha sai ta zame mini madubin da take wanke dukkan kumburin da zuciyata ke yi. Na riga na yi imani da haihuwa dole ce, ko kuma ita ce cikar niima kad'ai da Annabi ya rokawa Aisha tunda gabadaya malamai basu samu sabanin akan itace ta yi rinjaye a zuciyarsa ba. Hakan bai zame mata nakasa ba, sai ya zame mata kususiya ce mai girma a wajenta. Ta rungumi k'addara ta yi rayuwa cikin walwala, ta yi ilimi ta kuma yad'a shi wanda har zuwa yau ana cin moriyarsa. Dama amfanin d'a ai ya cigaba da ayyukan alheri da kake yi da kuma yi maka addu'a bayan ka kwanta dama. Idan hakan bata samu ba, sai musulunci addinin adalci ya ce Idan ka yi sa'a ka yiwa kanka sadaka mai gudana ko baka nan ladan zai bika har zuwa sadda abin zai katse.
Bayan haka idan ka yiwa mutane adalci, ka kyautata musu, ka ja yara k'ananu da marayu a jikinka ka tallafa musu, Ubangiji kuwa ba zai barka ka koka idan tsufa ya zo maka a dalilin rashin y'aya'ba. Tabbas ne sai ya turo maka wadanda zasu yi maka abubuwan alfarma na kyautatawa tamkar y'aya'n da ka haifa ko ma fiye da hakan.
Wadannan nasiha da tunatarwar da mahaifina yake yawan yi mini ya sanya na cire bacin rai akan rashin haihuwa, na rungumi y'aya'n gidan da na makwbta da na yan'uwana nake yi musu iya abin da zan iya tare da fatan Ubangiji ya karba. Na kuma gamsu domin babu damuwa ko kad'an a raina, kullum kuma k'ara samun jama'a nake yi a kusa da kuma nesa.
Tunda ina da islamiyar yara da nake koyar musu a duk ranakun lahamis da juma'a a cikin gidan nake da kebebben waje dan gudanar da karatun kullum kuma makarantan cika take yi, tunda mafi yawa duk yaran da suke zuwa mini ne ma'ana ba makwabtaka. Ni kuma ina zuwa makarantar asabar da lahadi domin dai na cigaba da daukar ilimin addin da kuma yad'a shi a tsakanin al'umma.
Wani abin mamaki a gidan namu ni kad'ai ce bani da kowa sai Allah sai miji. Amma na damesu rufin asirin da nake ciki ya zama abin tattaunawa. Makarantar da nake koyar da yaran a cikin gidana tana matukar ci musu tuwo a k'warya. Hatta shi kansa mijin namu ya zama abin zargi a wajensu. Alhali shima sa'i sa'i sai ya yi barazanar zai dakatar da makarantar ana cika masa gida da hayaniya. Kawai ya ga abin ya girmama ne shiyasa ya yi mukus.
Babban abin da na rik'e kuwa addu'a ne, sannan ban tab'a ayyana na cutar da su ba. Amma mafi yawa kullum sai sun yi mini sanadin bacin rai. Misali zan aiki Hajjaju ta ki zuwa, karshe ta bige da yi mini kunkuni amma uwarta ba zata tsawatar ba, idan na hassala na tsawatar a tunanina taya tarbiya na yi sai ya zame mini kalubale. Dan haka sai na hak'ura da aikenta. Sai kuma sakayya ta shigo domin sai ta koma take yiwa uwarma babu yadda za'a yi ta sarrafata, uban kawai take shakka. A maimakon hakan ya zama izna ga sauran matan kowacce ta shiga a hankalinta. Ina sai suka sake nausawa jeji. Kowacce akan d'anta babu s'auki. Wata bata isa ta mori d'an wata ba.
Mata! mata muna da muguntar da take cin kanmu da kanmu Allah ya shiryemu kawai.
Ana cikin haka aka fara auren kanwarsa wacce da ga ita sai autansu.
Shine ya yi komai. Kuma ni ya damkawa ragamar siyayya da gudanar da komai. Dama kuma tun farko ya fara yi mini hakan akan y'aya'nsa, da abu ya k'i na ce ya d'ora ko wacce uwa akan d'anta ni ya bar ni Ubangiji ma da yake sona fiye da kowa hakan ya bar ni, ban kuma d'auki hakan a matsayin tawaya ba. Alhamdulillah da dukkan jarabawa.
Kullum ba ni da sukuni ina tafe tsakanin gidansu da nawa gidan da kuma kasuwa. Zuwa yanzu na fara samun sassauci da ahalinsa tunda halin kowa ya bayyana a tsakaninmu da abokan zamana. Da ace zan biya sharrin zuciya da na shaidan da ko kulasu bazan yi ba. Tunda ba abin da ban ga ni ba a shekarun baya.
A fili na furta wnada Ubangiji ya masa baiwar hak'uri da hadiye da bacin rai ya tara masa dukkan alherin duniya.
Fahimtar da na yi hak'uri ne yasa na cigaba, shine yasa ban zama yadda ake son na zama wato na tozarta na zama Allah sarki. Sai na dimanci addu'ar Fasbir sabaran Jamila. Nake yawaita kula'uzai da li'ilafi, domin na gamsu dafa'i ne daga dukkan wani kaidin mai kaidi.
Ta gidan kanwarsa ta uku na biya muka tafi kasuwar tare. Muna tafe muna hira tana jaddada mini abin da yake cikinta nawa ne ko ta mutu. Tunda na fad'a mata na ki karban y'aya'n yan'uwana ne saboda yadda gidan namu yake cike da rikitarikita da rashin tsarin tarbiya a wajen matan gidan. Dan haka bazan yarda na dauko d'a ayi ta tashin hankali da musgunawaa gare ni tare da gori mai ciwo ba. Ta kuwa ce "ai idan ni na baki babu mai tsinin bakin da zai tayar miki da hankali.
Ni a k'asan raina ma ba so nake yi ba. Bana damuwa tunda na riga na roki Ubangiji kada ya jarrabe ni da butulce nasa dan ban haihu ba. Na gode masa da ya sanya ni cikin bayinsa musulmai, ya ba ni lafiya, ya kuma bude mini k'ofofin alherin da zan yi ta neman lahira, da kuma yiwa mutane ihisanin da zan zama ni din ta kowa ce.
"Alhamdulillah" bana gajiya da furta hakan.
Kafin mu kammala siyayyar tuni na yi dinkunan da zan yi hidimar biki tare da bayar da gudunmawata mai kauri. Addu'a kan addu'a na sha a wajen mahaifiyarsu wadda suke kira da Inno
Amaryar kuwa da tun tana k'arama y'ar dakina ce, kayan gyara takanas na sanya Surayya HALIN YAU ta hada mata. Saiwowin sanyin da take siyarwa kyaunsu aziman ne. Bayan haka na shaida sauran kayan ma babu algus. Daga ni sai ita muka yi abinmu ba'a sani ba. Saiwowin dahuwar kaza kuwa da yake mutum biyu zasu yi amfani tare na siya na dafa mana kazar nima na sabuntawa d'an sababin nawa😅. *08032773332.*
A yanzu tauraruwata ce take haskawa a wajenta. Har wanda bai sanni ba, zai yi zaton bansan bak'in ciki ko musgunawar uwar miji ba. Amma da yake kowa ya yi hak'uri za'a yi da shi, sannu a hankali ta gane nice mai rangwamen tsiya a cikin surukanta gabadaya.
Tun ranar jere na fahimci Nadiya na nemana da sababi mai girma, material din da an sanya na Umm Nihla mazauniyar Malaysia ya yi matukar mintsinin ta. Ni kuma ban ga abin damuwa ba da ta tambaye ni sai na bata contact din kai tsaye ta zabi kalar da take so kafatalin kishiyoyina ba wadda take da takamarta,