shiko hannun ta dake nasa ji yayi kamar an watsa masa garwashin wuta.
"Na tsani 'kyauyen nan gaba d'aya" yace a zuciyar sa yana mai share hawaye dake shirin zubo masa.
Har sunyi nisa sai ya d'an saci kallon ta, gani yadda take yayi matu'kar firgita sa, ga wani malulun ba'kin ciki da ya rufesa.
Kamar wada akama dole yace yana mai zame hannun sa daga nata "don iskan a haka kike nufin zamu tafi da yagaggen riga? ko dama ai ba damuwar ki kayan mutunci sukayi ba, ansaba, hakan ya nuna baki tubaba, baki saduda ba. Hmmm" yaja ga garumin numfashi.
"Bazan iya tafiya dake a haka ba gaskiya, in anbinci kama kekika gayyace shi, kila bai miki yadda kike so bane shiyasa kike neman wani. Toni ba d'an iska bane, sanan ban mu'amala dasu, tir, fasi'kanci baiyi ba Sam, Allah tsare mu ya kare mu, amin".
Yace yana mai takawa abinsa.
"Ni nayi nan, Allah had'a ki da dai-dai ke sai aje can a 'karata , misssss".
Ya cigaba da tafiyan sa, kuka ta fashe dashi mai tsanani, ha'ki'ka yaci mata mutunci tace cikin zuciya, zuciya nata na mata 'kuna.
" Wato nufinsa ni karuwa ce ko? hmmm" tace tana cije le'ban ta.
"Ba komai ba laifin ka bane, kuma nagode da taimako" bai masan tanayi ba domin yayi nisa.
Tayi nisa cikin tunani sai ta tuna inda take aiko bata san sand ta mi'ke da gudu ba tama manta bazata iya tafiya ba, duk da taji a jikin ta, amma guma ta tsira da mutunci ta.
Tafiya take tana tattare yagaggen rigan ta tana rufe 'kirjin ta dashi.
A haka ta kawo har gida mutane nata kallon ta amma ko ajikin ta, hakan bai dame taba sam.
Tura 'kofar gidan su tayi ta shiga, wurgar da yagaggen rigan tayi ya rage daga ita sai d'an guntun siket d'in ta.
'Daura ruwan wanka tayi, domin a lokacin babu abinda take bu'kata da ya wuce hakan.
***
Auwal kwance a gadon sa yana ta rafka uban kuka kamar wani mace, kuka ya'ke bil ha'ki da gaskiya, yayi dana sanin ganin ba'kin abinda ya gani a idonsa.
Zuciyar na masa zafi mai tsanani, da ya rufe idanun sa abinne ke bayyana masa kamar yanzu ake a gaban sa.
Yana hango abun dake fizgan zuciyar sa gare ta a hannun wani yana sarrafasu yadda ya gadama.
Wani irin 'kara ya saki tare da ri'ke kansa.
"Duk ita ta janyo ta jama kanta, musulunci yayi, Allah ka 'kara mana imani" yace tare da dafe zuciyar sa.
"Kullum bata da shiga sai wanda zai hankali mutum gare ta, kai anya ba ita tanemai ba?" yace yana cije le'be.
Kiran sallah ya tayar dashi, mi'kewa yayi direct toilet ya shiga wankan yayi sa'an nan yasa white d'in jallabiyan sa ya fito bayan yayi alwallah domin tafiya masallaci.
Jin idanuwan sa sun masa nauyi yasa shi saka gilasa a fuskan shi, domin baiso a gane damuwar sa.
Yana rufo gidan sa, yaji motsin tafiya, bayan ya rufe ya juyo domin tafiya, sai yaga Joy tsaye kusa da gidan nasa, ta jingina da bangon gidan su Aisha, hannun ta rungume a 'kirjinta.
Idanu wan ta nakan sa tunda ya fito, d'auke kai yayi kamar bai ganta ba tare da had'e fuska ya fara tafiya.
"Nagode doctor" tace cikin za'kin murya, tsayawa yayi cak, tare da sauke 'boyeyyen numfashi.
Can kuma mai ya tuno kawai sai ya wuce fauuuuuuu.
Murmushi ta saki tare da lumshe idanuna ta, tana mai bin bayan sa da kallo.
Bata bar kallon sa ba har dai ya kure mata.
Sa'an nan tayi gidan su Aisha.
Manager please
Share please
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³π³
(Ta'kai taccen labari)
*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*
*π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«*
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
LITTAFAN MARUBUCIYAN:-
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
A fuwan my fan's, bakuyi fushi bako? nama sani baza kuyi ba domin kun kasance masu ha'kuri dani, ina godiya sosai sosai.
Dedicated to my fan's, luv you guysπ₯°
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
π
Ώ1β£5β£to1β£6β£
Shiga gidan su Aisha tayi, maman Aishan ne zaune a kusa da murhu tana fiffita wuta, "sannu da gida mama" tace tana d'an du' kawa kad'an.
"Yauwa Joy" tace fuskan ta d'auke da murmushi, "mama Aisha ta dawo kuwa?" "a'a, amma yanzu zaki ganta don zataje islamiya anjima, okay" tace tana mai zama a kan turmi dake tsakar gidan.
Suna zaune shiru sai ga Aisha tayi sallama, ansa mata mama tayi. Ita dai Joy kallon ta kawai take.
"Besty yakike" cewar Aisha lokacin da ta'kariso gaban ta.
"Lafia" kawai tace da ita "zo muje ko?" Aisha tace, mi'kewa tayi sukayi d'akin Aishan.
Kwanciya kawai tayi a katifar Aisha daga shiga d'akin.
Kallon ta kawai tayi ta kyauda kai, domin tunda taga haka to miskilancin ne tsaba ya tashi.
Sai dai abin mamaki gani kawai tai lokacin da ta waigo tana ta faman murmushi.
Cire hijabin hada tayi tare da d'aukan na islamiya ta saka.
Zama tayi kusa da ita tare da cewa "besty zani islamiya, zanje na dawo nasha labari domin da alama dai wanan murmushi da ake saki zanji labari mai dad'i".
Ta'ba baki tayi tare da mi'kewa " sai ina kuma besty? inace zaki jirani na dawo ne?" "Uhu'um" tace da ita tare da riga ta barin d'akin.
Sometimes tana mamakin 'kawar nata, "wata irice ita gadai tanan".
Fito wa tayi lokacin har takai 'kofar gida, 'kofar gidan su ta tsaya tana kallon gidan Auwal.
Fitowan Aisha yasa ta kauda fuskan ta daga wurin ta maida kan Aishan.
" Besty sai na dawo ko?" d'aga mata kai kawai tayi, ita kuma ta wuce makaranta ta.
"Baki gajiya kedai, kullum makaranta, ina zan iya wannan wahala, ga wani abu biyabiya dashi".
Tace tana ta'be baki tare da barin kallon 'kawar tata.
Tsawon lokaci tana tsaye a wurin kafin tayi cikin gida.
Koma wanta da kad'an maman ta ta dawo, saukan ta a mashin Auwal ya fito daga gidan sa, da murmushi ya'ke yace "sannu da zuwa, yauwa yaron kirki" tace dashi "Joy ta dawo kuwa?".
Wani 'kululun ba'kin ciki ya tokare masa, amma ya daure yace " uhmm".
Shiga gida tayi shi kuma ya wuce inda zashi.
****
Watan Auwal shida a 'KAUYEN 'YAR KADDE, abubuwa da dama sun faru, daga ciki akwai yawan shige masa da Joy keyi, kamar idan ta gansa ta gaishe sa da dai sauran su, ta rasa maike damun ta dangane dashi, kuma sau goma zata masa magana bazai tanka taba, duk sanda ya ganta idan a hanya ne canza hanya yake, idan kuma ta tasame sane sai ya d'auke kai yayi kamar bai ganta ba.
******Auwal kwance yana waya da mami sai faman narke mata yake tana biye masa "mami don Allah ki ro'ki Dady ya yarda na dawo, wallahi mamina nayi missing d'in ki, ga 'kauyen ko dad'i babu, har yanzu ban saba dashi ba".
" Ga sister zata dawo nan da sati mai zuwa,".
"Ni Auwal bansan yadda zanyi ba, nayi nayi koni nazo na ganka ya'ki, bansan yadda zanyi ba nima inason naga boy d'ina" tace tana murmushi.
Turo baki yayi tare da cewa "mami niba boy bane gaskiya na girma" "da gaske my son? uhum".
"Amma mami na haka zanta zama sai na shekara sanan zan ganku?, eh son tunda haka Dadyn ku yake so".
" Haba sai kace mara gata, mara galihu? hab fisabilillahi kamata haba mami na, do something ".
" Hmmm, bari zan jaraba Allah sa adace, amin mami na, ko kuma kawai kisa 'yan gaban goshin sa agaba nasan suna cewa zaiyi na'am".
"To bari suzo muga" "yauwa mamina shiyasa nake tsananin 'kaunar ki, love you mum" yace tare da sakin masa kiss ta wayar.
Dariya tayi tare da kashe wayar, shiko wani farin cikin da yadad'e baiyyi ba yaji ya mamayeshi smiling kawai yake.
Tashi yayi daga kwancen tare da shiga toilet yayi wanka, T-shirt mai ratsin baki da fari yasaka da ba'kin wando, kayan sun matu'kar kar'ban sa.
Kallon kansa yayi a mirror shi kansa yasan ya had'u, smiling yayi tare da cewa "yaron mami ka had'u" tare da cewa yima kansa kiss ta mirror d'in.
Bayan ya kintsa ya fito domin le'ka asibiti lokacin la'asar ne sakaliya.
Yana rufe gida ya juyo yaga mutum a bayan sa, kauce wa yake ninyan yi ta tare, tace tana ya mitsa fuska "doctor cikina na ciwo ko zaka taimakamin please?".
Kansa na kallon gefe yace " nan ba asibiti bane, baya ga haka kije kinemi wani not me".
Kallon sa take ta 'kasan ido, "zaki iya bani hanya na wuce" yace fuskan sa kamar wanda bai ta'ba dariya ba.
"Kayi Kyau" tace a hankali tare da matsa masa a kan hanya.
Ya fara tafiya yaji kamar ana binsa a baya, bai waigo ba sai da yaje 'kofar asibiti sanan.
Ganin wace ke bayan sa ya had'e rai tare da shigewa.
Cigaba da bin nasa tayi har 'kofar office d'in sa, bud'e wa yayi tare da shiga, zai rufe ta turo jikin ta.
"Kibar wurin nan", " doctor nazo fa domin lafia tane, da gaske banda lafia ka yarda dani" ganin kallon da yake mata yasa tace haka.
Bud'e mata yayi ta shiga, zai duba ta kodon maman ta.
Zama yayi a kujeran sa, ita kuma tana nan tsaye, nuni yayi mata da hannu alaman ta zauna.
Zaman tayi sa'an nan yayi shiru yana jira daga gare ta.
Tasani sarai tagane nufin sa amma ta share sai ma 'kare masa kallo da take.
Gajiya yayi ya mi'ke domin zuwa duba marasa lafia, itako tana nan zaune ko motsawa batayi ba.
Fita yayi ya barta ba tare da yace da ita komai ba.
Kallon office d'in take lungu da sa'ko, ba wani babba bane tunda na 'kauye ne, amma da yake na d'an gata ne ba laifi yayi Kyau.
Tashi tayi taje kan 'karamin bed d'in marasa lafia da yake office d'in ta kwanta tana mai lumshe ido lokacin ne taji ciwon ya taso mata, don haka sai ta fara mur'kususu.
Dai-dai nan Auwal ya bud'e 'kofar, ganin bata a kujeran da take yasa shi ajiyan zuciya tare da cewa "mayya kawai ta tafi......." Bai 'karisa zancen saba yaji nishi .
Waigawa inda yake jiyowa yayi kwance ya ganta a gadon.
Tana mur'kususu, d'auke kansa yayi kamar bai ganta ba, abinda yazoyi yayi ko ya gama don haka sai ya tattara abinda yazo dashi domin koma wa gida.
Aje key d'in office d'in ya aje tare da ninyan fita yana cewa kamar mai ciwon baki "idan kin tashi sai ki rufe musu office d'in su".
Kuka mai had'e da ehu ta saki tare da cewa " wayyo doctor zan mutu kataimakeni please, mama tace nazo ka dubani".
Dawo wa yayi tare da cewa idon sa na kallon gefe "meke damun ki?" "tunjiya da dare nan kemin ciwo, ina kenan?" yace ba tare da yajuyo ya kalle ta ba.
"Nan" tace, shi kuma yace cikin gajiya da 'kufula "shi wurin baida suna ne?" shiru tayi tana mai cigaba da kukan ta.
Haushi yaji zai fita, itako ta dage iya 'karfin ta tasaki ehu mai 'karfi.
Toshe kunnin sa yayi tare da kallon da azafafe ya nufo ta.
Kamar zai bugeta yace "wallahi kika sake min 'kara a kunni sai naci....." sai kuma yayi shiru.
"Ina kemiki ciwo? yace yana hararan ta.
Maimakon ta bashi ansa sai ta cigaba da kukan ta.
" Tashi kibarmin office yanzun nan kafin ranki ya 'baci" yace yana matsowa kusa da ita.
Bai aune ba kawai yaji ta kama masa hannun, da mamaki da ba'kin ciki yake kallon ta.
Bai gama mamaki na yaji hannun sa a lallausan jikin ta.
A han maran ta ta d'aura hannun nasa.
Cikin kuka tace "nan ne kemin ciwo" fisge hannun sa yayi cikin masifa yace yana tofar da yamu.
"Banza 'kazamiya, amgaya miki kowa 'kazami ne irin ki? ko ance miki ni Auwal irin karnikan kine 'kazamai Wanda basu san inda yake musu ciwo ba irin ki".
"Zan miki gargad'i da babban murya ni Auwal nafi 'karfin ki, nafi 'karfin 'kazan taccen jikin ki, kuma ki fita harka ta, idan ba haka ba ki kuka da kanki".
" Banza kawai, Auwal ba jaki bane, kisani koda ni mazinaci ne irinki to bancin sauran wasu, kina mace mai aji da kima da daraja amma kinzubar dasu, koba abun abun mamaki bane arna zasuyi fiye da hakan".
Ya sake tofar da yamu idanun sa ya rufe yayi ta surfa mata ba'ka'ken maganganu.
Koda ya gama bai damu da kukan da take da juye-juyen da take ba.
Yabar office d'in tare da sanar da mai gadin wurin idan ta tafi ya rufe masa office d'in ya'kara gaba.
Tafiya yake yana ganin dishi-dishi domin abinda yafaru yana ganin sa a idanuwan sa kamar yanzu ake.
Kuma ya tabbatar da zarginsa 'yar iskance ita......
Tofah fan's kunji fan
Kubiyoni domin jin yadda zata kaya, amma hakan bazai samu ba sai naga comments.
Comment & share pls
'Yar Aliyu ceβπ»
[11/5, 9:50 PM] Safeeya Aliyu: π³π³π³π³π³π³π³π³
*'KAUYEN 'YAR KADDE*
π³π³π³π³π³π³π³
Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili
π«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπ«
*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*
*LITTAFAN MARUBUCIYAN:-*
*MASAUKIN SO*
*SHI NAKE JIRA*
*BA JINSIN MU BACE*
*HAMDIYA DA HAMNA*
*Dedicated to my family*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
π
Ώ1β£7β£to1β£8β£
"Dole na cire ki a raina, kota halin 'ka'ka kuwa, zuciya baki min adalci ba, taya zaki sa naso wacce bata dace dani ba? yes bata dace dani ba, bata cancan ceni ba. Ni mai tsaftane ita 'ka zama, ya Allah fitar da ita a zuciya ta". yace yana mai rintse ido, lokacin yana kwancen a bed d'in sa, babu abinda yake tunani sai ita, tunani halin da ya baro ta kawai yake.
***Ta d'au tsawon lokaci a wanann yana yin, tana cikin damuwa mai tsananin, abu uku ke damun ta. Na farko 'kama da Auwal ya kira ta hakan yayi mata zafi sosai, ta gane cewa yana zargin ta da aika ta fasi'kanci, abinda bai sani ba, zina abune da take matu'kar 'kama, hakan da ya matu'kar tsaya mata a rai.
Na biyu ciwon maran dake damun ta, ba'kin ciki yasa ya rage mata kaso hamsin na ciwon.
Na uku tsananin 'kaunar sa da bata san tanayi ba sai yau, gashi Auwal yayi mata nisa, kalman sa kawai yasa ta gane tsananin kiyayyar da yake mata.
" Ina son ka, wallahi ina son ka, ina tsananin 'kaunar ka, 'kaunar ka shine ajalina zan rayu da son ka duk da nasan baza ka ta'ba sona ba".
Tace tana mai fashe wa da kuka mai tsanani, a daddafe ta bar office d'in nasa, idan nun ta nata zubar 'kwallah.
A haka taje gida bata damu da kallon da mutane kema taba sam.
Tana shiga ta tadda uwar ta a tsakar gida, ganin yana yin da 'yar tata ta shigo yasa ta isa gare ta da sauri ta taro ta.
Tare da tambaya ta abinda ke damun ta, shiru tayi mata tana mai cije le'be.
Tambaya duniya nan uwar ta mata amma ta share ta, ganin haka uwar ta fita harkan ta duk da yanayin da 'yar tata ke ciki na damun ta.
Kwanciya tayi tana mai tsine ma isah domin shi ya janyo mata tsana da 'kiyayyar da Auwal yake mata.
β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’β’Yau kimanin kwana hud'u kenan Auwal ya'ki fita ko waje komai a gida yake yin sa, duk yayi wani iri saboda damuwa dake d'awainiya dashi.
Ta kai ta kawo har da Kuka, kwancen yake yana tunani da ya zame masa abinci domin abincin ko damuwa dashi baiyi.
"Na sani ina sonki, so mai tsananin ma kuwa amma sai dai ya kasheni da dai na auri sauran wani, na tsaneki ban sanki daga yau" yace yana maiji zafi a zuciyar sa, domin tuno cewa ita sauran wanine ya hadda sa masa damuwa fiye da nada.
Wanda har tsanan ta wani sashi na zuciyar sa yake.
'Karar wayar sa ce ta dawo dashi daga halin da yake ciki.
Kallon wayar yayi na wani lokaci kafin ya d'ako, ganin mai kiran sa yasa shi peaking tare da sakin murmushi da ya kwana biyu baiyi ba.
Kafin tai magana ya riga ta da cewa "sweetheart" yana jan numfashi.
Dariya tayi tare da cewa "na'am sweet bros, yakake d'an 'kanina?" shiru yayi kamar mai tunani.
"My Auwal kanajina kuwa?" shiru ba ansa ta sake cewa "kana lafia kuwa my bros? talk to me please " tace cikin tashin hankali.
Sanin halin ta yasa shi
'bata rai tare da cewa "sister ba 'kalau nake ba sam".
" Oh my god!!! what happen?, sister my heart" sai kuma yayi shiru.
"Mai ya same ta?, ciwo take sister, kaje a duba ka mana".
" Na'ki gida kawai nake son dawo wa, mai yasa?" tace dashi, "'kauyen babu dad'i, ina son na dawo kafin ki dawo, don Allah ki ro'ki Dady na dawo".
" I miss you sister nd mamina, Auwal kenan Dady fa ya kafe ya nace yace sai ka gama sannan zaka dawo, kuma ma idan nazo dole nazo na ganka".
"Kad'an mafa ya rage maka, sister baza ki gane ba Wallahi ni gida nake so".
"Yanzu ya kake son ayi?, ki ro'ke sa nasan zai amince na dawo kinji tawa".
Shiru tayi ya sake cewa " pleaseeeee" .
"Naji, amma kamin al'kawari zaka koma duk lokacin da aka bu'kaci hakan".
" Na amince" nan dai sukai sallama.
°°°°°
Kwana hud'un nan Joy ta kasance cikin tsananin damuwa, damuwa ba d'an kad'an ba.
Tana son ganin sa, tana son jin murya sa, amma ta yaya? tunda ya'ki fita daga gidan.
"Inason ganin sa, bazan iya barci ba yau idan ban gansa ba" tace cikin damuwa.
Mi'kewa tayi tare da shirya wa, yau anyi abin arzi'ki, domin shigan dogon riga mai roba d'in nan tayi.
Yayi mata Kyau matu'kar gaya, har dasu rolling.
Da yake yau Sunday akwai church madam Gloria ta dad'e da tafiya.
Ta fashe