Kauyen Yar Kadde Complete Hausa Novel

Author :  Safiyya Category :  Love

Chapter   10 / 14

27K to 30K   out of 39.4K words

amma ai da kun dawo tare ta barki ke d'aya kin dawo".

" Amma a mashin kika dawo ko?" tace ina gab da shiga d'akin.

"Uhum" nace kawai tare da sa kai.

Kallon d'akin na tsayayi kawai har kusan minti biyar sannan na fito, ganin bata tsakar gidan na saki ajiyan zuciya tare da falfalawa da gudu.

Ina fita na bud'e mota na fad'a cikin tare da sauke numfashi.

"Lafia?, ina 'kawar taki?" yace yana kallo na.

Ban sa ansa ba nace "muje kawai" bai wani matsa ba ya tada mota muka bar wurin.


Mun fara nisa sannan nace "Aisha fa ta tafi, kuma nasan ta shiga gidan mu nema na".

"Yayi, kinga mai himma kenan" turo baki nayi tare da cewa "naji ni ban da himma".

" A'a ni bance ba" banza dashi nayi shima bai matsa ba ya cigaba da tafiyan sa.


Yana parking na bud'e 'kofa zan fita, "ansa" yace .


Waigo wa nayi tare da kallon hannu sa, "ki ansa nace" hannu a dun'kule.

"Me zan ansa?" nace ina le'ka sa'kon hannu 'kara dam'kewa yayi tare da sa d'aya hannu sa ya janyoni tare da kar'be jaka ta yasa min tare da saki na.

Zanyi magana yace "oyo wuce kin makara, maza aji kar a ta'ba min lafia jikin ki" murmushi nayi tare da fita daga motan.

'Daga min hannu yayi nima haka nayi cikin makaranta.



Sauri ya tada motan yabar wurin bayan yaga shiga ta aji.


Ina shiga Aisha ta tsare ni da ido, murmushi nayi tare da cewa "lafia kallon malama?".

"Ina kikaje ne besty? naje gida mama tace kin dad'e da fita".

" Gidan doctor " nace murya 'kasa 'kasa, don malam ya shigo lokacin.

Zaro ido tayi tare da bud'e baki, murmushi nayi tare da cewa gab da kunnin ta "rufe bakin, kinsan wannan malamin mai rainin wayau ne, ki bari sai ya fita sai ki sake wani tambayan".


Aiko kamar wa wuya ta kasa magana rufe bakin tayi muka natsu aka fara darasi.



Yana fita Aisha ba ta barni na koda matsa ba ta jefomin tambayan.

"Mekikai a gidan doctor fisabilillahi da girman ki da 'kiman ki?" .

"Tashin sa a barci nayi, bayan haka na masa break fast".

San'kare wa tayi a wurin.


Niko dariya nayi, in banda abinki Aisha ina ruwan arne........




**********


Rayuwa tama su Joy dad'i soyayya kawai suke kamar ba gobe, suna tsananin 'kaunar junan su da kulawa da junan su
Sosai.

Amma fa Auwal bai sake sakacin barin 'kofar gidan sa a bud'e ba, don yana tsoron Allah yana tsoron Joy.

Duk da haka bai tsira ba, a hakan tana yawan ta'ba sa, ko son shige masa jiki.

Wani abu da ta tsiro shine zuwa asibiti duk bayan ta dawo daga makaranta, sai tazo tawani kanai naye shi.


Haka suke ta tafiya har wa yau, yanzu haka saura jibi Auwal zai koma garin sa, ya gama sabis d'in sa, ya rasa yadda zai sanar mata.

Ganin cewa suna ta faman jarabwa, don bai son ya tada mata da hankali ko kad'an.

A haka har kwana uku tayi ba tare da yasan yadda zai ya gaya mata ba.


Can Abuja su mami sun kasa sun tsare suna jiran dawo wa Auwal shiru har washe gari bashi ba labarin sa.

Sun kira wayar sa a kashe, shiko yayi hakan ne saboda bai san mai zaice masu ba.

Sati d'aya da gama wan sa saura kwana biyu su Joy su gama jarabawa, yana zaune a 'kofar gidan sa kawai sai hango motocin gidan su yayi guda biyu suna taho wa.

Farin cikin ganin 'yan gida da fargaba suka taru suka diran masa a lokaci d'aya.

Mi'kewa yayi daga farin kujeran da yake zaune, dai-dai nan sukai parking, nufar motan sister d'in sa yayi.

Da farin ciki ya bud'e 'kofar motan, ita ce hakin CE a bayan motan sai Akaram.

Ko bari ta fito baiyi ba yace "oyoyo sis, oyoyo my son".

Harara ta maka masa, tare da cewa " shiga mota muje" d'aure fuska yayi tare da cewa "kai Anty wani irin in shiga mota daga zuwan ki?".

" Auwal ban wasa da kai nace ka shiga mota mu tafi" bud'e d'ayan motan da akayi ne yasa shi waiga wa.

Ba kowa bane illah Dady da kan sa, sai yaya wato Wanda ya kawo sa.


Ga farin ciki ga far gaba, amma hakan ya matse yayi musu barka da zuwa.

"Son mai kake a garin nan bayan ka gama abinda ya kawo ka?" cewan Dady ba tare da ya ansa sanu da zuwan da yake masa ba.

Shiru shima Auwal yayi, ganin zai 'bata lokaci yasa Dady yace "shiga muje" rasa yadda zaiyi yayi tunda Dady da Kansa yace haka.

Kamar zai kuka yace "Dady kuje kawai gobe zan.........." bai 'Kari saba sakamakon wani matsiya cin harara da Dady yayi masa.

Bai dan dara ba yace "Dady bari na had'a kaya sai muje".


" Bama wani ka wuce muje" "akwai takadduna fa a cikin gidan".


" Jeka maza rakasa" yace da yayan nasa, bai so hakan ba amma haka yayi gaba yayan yabi bayan sa zuwa cikin gidan.

Tarka ta takkdun yayi kaf tare da abubuwan sa masu mahimmanci suka fito, amma kafin su fito ya faki idon yayan ya rubuta leta ya aje a kan kujera d'aki .



Suna fito wa saka kayan a bot d'in motan yayi tare da kallon gidan yana mai jin wani iri a cikin ransa, gashi Joy suna makaranta yau bai san yadda 'yar rigiman sa zatai ba.

"Dady bari na bawa gidan nan key d'in nazo".


" Ga wani can bashi ya kai musu kana 'bata min lokaci " waiga inda dadyn yai nunin yayi.


Aiko ganin Muhusin ne yasamu kwanciya hankali.


Matsawa kusa dashi yayi tare da cewa cikin 'kasa da murya yana mai tura masa abu a aljihu "'kani na, don Allah ga wannan wayan da kye d'in nan Joy na dawo wa kaba ta, kace nace don Allah tayi ha'kuri zan zo bayan kwana biyu".

" To yaya insha Allah zan gaya mata, yauwa 'kanina nagode" yace tare da juyawa wurin motan .




Shigan sa keda wuya suka bar wurin....................
.





To fah, wata sabuwa inji 'yan cacaπŸ€¨πŸ˜…






Comment & share pls
[11/5, 9:53 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*


*πŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπŸ’«*


*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



πŸ…Ώ3⃣5βƒ£βž‘3⃣6⃣

Tun shad'aya suka gama jarabawan su, tafe suke suna d'an fira har suka zo inda Auwal ya saba zama don jiran su, don basu ta'ba jiran saba kullum shike jiran su.

"Abin mamaki Aisha yau my heart bai zo da wuri ba" cewan Joy tana mai kafe wurin da ya saba parking da ido.

Aisha tace" Allah sa dai lafia, amin" nace ina maijin fad'uwan gaba na ya'karu fiye da yadda nakeji tun da na tashi a yau.

"Mu zauna daga nan mu jira shi besty" ba tare da nace komai ba na bita muka zauna a wata gindin bishiya.

Shiru muke zaune amma idanuna na hanya, muna zaune har na tsahon wasu lokaci babu doctor babu labarin sa.

Mune har 2:00pm babu shi, a lokacin kuwa zo kuga idanuwa na, idanuwa na fal da 'kwalla, gabana sai faman bugawa yake.

Nayi zurfi cikin tunani mai ya hanasa zuwa d'aukan mu, fatana dai ace yana cikin 'koshin lafia idan ba haka ba akwai matsala babba ma.

"Tashi mu tafi besty kinga rana tayi da uban yunwan da nakeji" cewar Aisha tare da mi'kewa tana kamo hannu na.

Dojewa nayi na'ki tashi, kallo na tayi tare da cewa cikin marai rai cewa "please ki tashi nasan wani babban uzuri ne ya tsayar dashi, don haka mu tafi kawai".

Gamsuwa da zancen ta nayi don haka sai na mi'ke, tare goyin mukayi muka nufo hanyan 'kauyen mu.

Tafiya muke amma gaba na na cigaba da fad'uwa, 'karuwan fad'uwan gaba na shine sanda muka zo muka cimma babu motan Auwal a inda ya saba ajeta, don sam bai zuwa da ita ko'ina da ya wuce kaimu makaranta.

Sai wasu lokutan da idan bai da wani abun anfani sai yaje cikin gari ya siyo. Kuma bai tafiya sam ba tare da ya sanar dani ba.

Barin Aisha nayi da sallaman mai mashin ni kuma na nufi 'kofar gidan sa, duk da na gansa a rufe.

Bubbuga gidan na farayi kamar mara kai, zuwa Aisha tayi tajani ina turjewa don jiki na ya bani ba lafia ba.

Da 'kar ta jani cikin gidan mu, mama ce zaune a tsakar gidan da alamu dai shan iska take, don zaune take da 'yar single a jiki ta sai faman fifita take.

Ko inda take ban kalla ba nayi hanyan d'aki, Aisha ce ta gaida ita tare da fita a gidan.

Ina shiga d'aki nayi wurgi da jakan makarantan, za gaye d'aki na farayi.

A haka mama ta shigo ta cimmini, kallo na tayi tare da cewa" lafia kuwa Joy? " kallon ta nayi tare da kauda kaina.

Gajiya da zaga d'akin nayi don haka na fad'a kan katifa tare da cewa" wayyo" da 'karfin gaske hawaye kuma suka fara ambaliya akan kyakkyawan fuska ta.

Da sauri mama tazo inda bake tare da d'ago ni tace" what happened Joy ".

" Mama ina doctor yaje yau bai gaya min ba?" Nace ba tare da naba ta ansan tambayan ta ba.

Wani irin kallo na tayi tare da cewa" lallai doctor nada aiki tunda zai auri matar da bazai ta'ba fita ba sai da sanin ta da kuma izinin ta" ta had'a da tsaki tare da tashi tabar d'akin.

Eyhu na sake saki ina cewa " wayyo doctor na ina kashiga ne zuciya ta zata fashe?" tare da rushewa da kuka.

Ranan babu zancen abinci, to yaya zakaci abinci ma bakaji yunwa ba? Toni ranan nama manta da wani abinci sam.


6:15pm Muhusin ya shigo gidan mu da uniform d'in islamiya a jikin sa.


Gai da mama yayi tare da cewa bayan ta ansa "Anty Joy na nan?"

"Eh tana nan shiga ciki" tace dashi, hanya d'akin yayi.


Ina kwance da uniform d'ina kuma har lokacin kuka nake ya shigo, naji motsi ban damu da sanin ko waye ba shiyasa ban waigo ba.


Ji nayi ance "Anty gashi inji yaya farin nan na kusa da gidan mu" ai da sauri na waigo hard murmushi na.

Nace ina kallon hannu sa "yana ina?" mi'ka min kye yayi tare da cewa" ya tafi gashi harda wayan nan yace na baki" yace yana bud'e jakan islamiyan tasa.

Gaba na ya fad'i na kalle sa tare da cewa" ina ya tafi?" Ina jujjuya kye d'in hannu na hawaye naji ya fara zubowa a fuska ta.

"Ban sani ba, wasu ne dai 'yan birni suka zo a motoci da yawa ya shiga suka tafi" .

Yace tare da mi'kamin wayar doctor, kar'ba nayi shi kuma ya fita.

Bin wayar nayi da ido ina jujjuya shi har na tsahon wasu lokuta.

Dana wayar nayi ta kawo haske, photo nane ya bai yana a fuskan wayan, ban san sanda akai photo ba amma yayi matu'kar kyau.

Tashi nayi da kye a hannu na nayi fito daga d'aki, nufan hanya fita nayi mama na kallo na batace dani komai ba.

Gidan nashi naje na bud'e, shiga nayi har ciki.

Tun daga yanyin yadda falon yake naji wani iri tsoro da fargaba.

Shiga bedroom d'in sa nayi, kaya ne na gansa a hargitse, kuka na saki tare da d'aura hannu aka.

"Wayyo doctor na, wayyo! Wayyo mai yasa zaka min haka?, mai yasa zaka tafi ka barni?"

"Baka min adalci ba" nace tare da fad'a wa katifan sa ina mai cigaba da kuka na.


Haka na kasance a gidan nan har dare kuma baci basha sai kuka kawai. Bani na bar gidan nan ba sai 9:00pm.

Koda na shiga gida banyi takan mama ba na kwanta kawai ina mai cigaba da kuka na.

Da fitana mama ta biyo bayana, ganin inda na shiga yasa tai zargin wani abu.

Gidan su Aisha ta shiga bayan na shige gidan doctor, bayan sun gaisa da maman Aisha sai ta nemi Muhusin, tambayan sa tayi yayi mata bayani ita kuma tabar gidan.

Shiyasa bata ko nemeni ba, ganin kukan ya'kici ya'ki 'karewa yasa ta matso cikin tausayawa ta kamoni tare da lallashi na.

Ta d'au lokaci mai tsayi tana lallashina, da'kar na dai na kuka.

Baccin ranan ban samu yin saba sam.




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°


Auwal lafia suka kai gida, baiyi magana da kowa ba har da mami. Fushi sosai yake da kowa na gidan.

Duk wani gata da tarairaya da mami da uwar gayan suke sam bai burgesa, bai sa ya saki jiki ba.

Abinci sai anyi da gaske yake ci, kullum yana cikin d'aki, bashi da abinso dake saka shi nishad'i da jin dad'i wanda in har yana cikin yanayin zaka ga yana dariya ko murmushi, shine tunani masoyiyan sa.

Hakan da ya mai da kansa yasa damuwa mai tsanani a zukatan iyayen sa da 'yan uwan sa, musamman mami da Anty RAHAMA.

A haka har akai sati biyu, a sati biyun nan ko yayi muguwan rama kai kace wanda yayi ciwon shekara.

Kuma a yaune yasha alwashin koma wa 'KAUYEN 'YAR KADDE tun da nanne farin ciki sa yake.

Shirya wansa yayi ba tare da ya sanarwa kowa na gidan ba.

Bayan ya gama shirya kansa cikin 'kananun kaya wando na'ki da jan riga mai rane jah da fari sai wani zane na 'baki kad'an wanda yayi matu'kar 'karawa rigan kyau.


Kayan sun matu'kar kar'ba sa.


Fita yayi daga d'akin sa yayo main palon gidan. Da yake yau Saturday ne kowa na gida, zaune ya gansu duka, mami, RAHAMA, Dady har da yayyun sa maza.

Gai dasu duka yayi a cikin ciki ba tare da ya kallesu ba, ansawa duka sukayi idon su na kansa.

Sunji dad'in adon da yayi a tunani su ya kwantar da hankalin sane basu san ko kad'an ba hakan bane, domin kwanciya hankali sa shine yayi arab da za'bin ransa.

Gani sukayi ya nufi hanya barin palon, duk cikin su sun kasa masa magana.

RAHAMA ne kamar mai tsoro ta kira sunan sa, tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba.

Tashi tayi tare da zuwa inda yake.

Dafa kafad'an sa tayi tare da cewa" ina zakaje habibi?" Banza da ita yayi tare da zare hannu ta daga kafad'an sa ya bar wurin.

Wurin ajiye motocin gidan ya nufa, 'barayin da motocin sa suke ya nufa.


Rufe suke ruf d'aga wa yayi d'aya bayan d'aya, gani yayi duka sunyi kura.

Cike da masifa yake 'kwala ma mai wankin motocin kira.

Da gudu ya nufo sa, ma'kaitan kaf sunji kiran nan har 'kwa'kwalwan su.

Hatta su mami sai da suka fito suga dalilin uban wannan kiran.

Abinda bai ta'bayi ba fuska babu walwala yana zuwa ya dur'kusa tare da cewa" gani yalla'bai" .


Ya bashi wani irin mari tare da cewa cikin masifa "wani irin iskanci ne zaka barmin motoci da 'kira eyeh?"

Yace yana 'kara masa wani, cike da girmamawa yace" yalla'bai go kwana hud'u baya sai da na wanke".

"Sai akace maka kuma jiya ko yau karka wanke ko?"

"Maza wanke min wancan jan yanzu na baka minti biyar kuma ya fita, idan ba haka ba yau sai kabar gidan nan" yace tare da tsaki ya juya.

Kamar d'azu suna kallon sa ya wuce ta gefen su baikoyiwa wani daga cikin su magana ba.

Da mamaki RAHAMA tace idanun ta cike da ruwan hawaye "Dady don Allah muje mu bashi ha'kuri muji meye damuwar sa, idan ma zaman 'KAUYEN yake so sai mu barshi ya koma idan yaso muyi masa ginin zamani a can. Sai ya rin'ka zuwa duk sati gida yana dubamu komu murin'ka zuwa".

Tunda ta fara maganan yake hararan ta har ta idda maganan ta.

Yau da badon 'yar gaban goshi bace tai maganan nan ai da tasha mari.

" Baki da hankali ko RAHAMA? ni kike so naje na bawa d'ana ha'kuri to bai zai ta'ba yuwu wa ba, don bashine ya haifeni ba, don ko uban sa.........."

Sai kuma yayi shiru "to bari kiji babu wata 'KAUYEN da zai koma, nd kwanan nan zai fara zuwa asibitin sa, don an gama komai bikin bud'e wa za'a sai ya fara aiki kinji ko?" Daga nan yayi tsaki tare da barin wurin.

"Kema dai inajin mahaukaciya ce ke, wai da bakin ki kike cewa Auwal ya koma 'KAUYEN da zama. Hmmm to bari kiji ko zuwansa sabis saboda ya rage wasu abubuwa da basu dace ba shiyasa muka dage kai da 'kafa ya tafi".

" Don sam bamu soba ke har Dady kan sa, saboda yayi hankali ne kawai muka kai sa" cewan babban wansu.

Kuka ta fashe dashi tare kallon mami da tai shiru .

Matsawa inda take tayi ta rungume ta tare da cewa" mami yanzu ya zanyi ya zanyi my brother ya dawo kamar da?" shiru tayi domin ita kanta abin na damun ta sosai.


Suna tsaye su biyu domin sauran sun bar wurin sai gashi ya fito.

Wuce su yake sonyi mami tace cikin matsawa da d'aure fuska.

"Ina zaka?" tsayawa yayi shiru ba tare da yace komai ba.

Tsawa da bata ta'ba masa ba shine tayi masa "dakai fa nake kayi shiru".

Fukan nan a had'e yace" nasarawa zani " daga haka yayi shiru.


"'KAUYEN nan zaka ko?" Shiru yayi ba tare da ya bata ansa ba.


"Wai shin Auwal meye kakeso? Meye kake nema a 'KAUYEN nan?" Still bai bata ansa ba.




"To tunda baka da ansan tambaya ta koma ciki" wani iri juyo wa yayi cikin tashin hankali yake kallon mamin.


Zaiyi magana tace" daga yau na sake jin sunan 'KAUYEN nan a bakin ka bare kace zaka sai na.............................










Comment nd share


Luv you all my fan'sπŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
[11/5, 9:54 PM] Safeeya Aliyu: 🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳

*'KAUYEN 'YAR KADDE*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳




*Story & written by: Safiyya Aliyu Wakili*





*πŸ’«DA BAZAR MU WRITER'S ASSπŸ’«*


*We are here to make you happy, smile, educate and realized that we are best among all........ DA BAZAR MU MUKE TUN'KAHO*


*My ❀, my kaka, my HafsatuwaπŸ˜‰, my Hafnan is back.πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒina masoya ku fito, ga shahararriyan Marubuciyan nan da ta saba nishad'an tar daku, wato Marubuciyan, SHI SO 'DAYA NE, FATALWAN MIJIN NA da kuma HIBBATULLAHI. ta dawo muku da wani shahararran littafin ta mai suna KAICON SO! Masoya ku hanzar to kar kubari a baku labari Hafsat Mustafah (Hafnan) ta shirya tsaf domin nishad'an tar daku, wa'azantarwa da ilimantarwa. Da abaka labari gumma ka bayar, saboda haka masoya ku fito 'kwai da 'kwar'kwata domin wanke idanuwan Ku, karrrrrrr kubari.....................*



*you will never brave, if you don't get hurt. You will never learn, if you don't make mistakes. You will never be successful, if you don't encounter failure..................Good morningπŸ˜‰πŸ™πŸ»



*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



πŸ…Ώ3⃣7βƒ£βž‘3⃣8⃣

"Wayyo Allah na, wayyo mami na. Wallahi mutuwa zanyi, mami in............" Sai kuma yayi

10 / 14