Dingishin Kwado Book 2 Complete Hausa Novel

Author :  Salma Category :  Romance

Chapter   5 / 7

12K to 15K   out of 19.7K words

to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu"
Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ganin ya ruɗe yana ta wasu surutai yasa na s lalubo jarumta na yi ta masa nasihan da jan hankalin cewa tunda mutuwar Mami ta zame masa wa'azi ka da ya karaya, ya yi haƙuri ya cigaba da harkokinsa kowa iya kwanakinsa zai yi a duniya ya ɗauka ita Mami kwananta ne ya ƙare, da irin kalaman da na yi amfani kenan na lallashi Ansari ya bar kuka ya samu natsuwa.

"Allah ya jikan Mami da Baba ƙarami Allah ya sa sun huta."
Ya faɗa cikin karaya, na amsa mishi da Amin ina mai ɗauke hawayen da suka zubo mini da yatsun hannuna.
"Ya Sulaiman har yanzu ba labarin shi Ansari??
"Wallahi babu, na bincika duk in da ya kamata da wajen abokansa da suka yi karatu tare a Germany amsar duk iri ɗaya ce basu san in da yake ba sannan suma ba ya magana da su."
Ansari ya amsa mini cikin damuwa a muryansa.

"Shike nan. Idan yana raye Allah ya tsare shi a duk in da yake. Idan da rabon mu gana Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri."

Na faɗa ina jin kamar na fashe da kuka Ansari ya amsa da Amin mun daɗe muna tattaunawa kafin mu yi sallama bayan mun gama wayar na zauna a ɗaki ni kaɗai na ci kuka na ƙoshi sannan na faɗa bayi na wanke idanuwana, haka nake yi idan na tuna da yau ba Mami ba Baba ƙarami, sannan ba iyalan Baba Babba. Ga Ya Sulaiman ya yi nesa damu sai na ji ina kuka wanda banma san ina yi ba, ƙarfin zuciya ne da tasirin musulunci ke rike da ni amma matuƙa zuciyata da gangar jikina sun raunana, ƙarfin hali ne kawai da karɓar kaddara tunda rubutattaciya ce daga littafan kaddarar rayuwarmu, kuma cikar kowani musulmi karɓan kaddara mai kyau ko akasin ta.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi haka nan bawa yake zirga-zirgarsa na yau da kullum tunda akwai rai har da lafiya mun godewa Allah. Ba laifi ina samun ƙudi sosai tunda gidajen da na samu duk haya na saka, sannan ga sana'ata ta snack ta karɓu sosai da dukkan zuciyata da jikina nake yin aiki tuƙuri domin idan tuna maganar Ya Sulaiman ta ƙarshe a gare ni akan na zama jarumace na tsaya akan ƙafafuwana saboda ni uwa ce domin zama garkuwan ƴayana wata rana. Bana ko tsayawa jiran Baban Amrah domin ɗaukan laluranmu ta riga ta zame mini jiki komai ni nake yi, mantawa ma nake yi nauyin hakan na kan Baban Amrah ne, tun kuma da hakan ta faru ban sake komawa Funtua ba, saboda ko na je wajen wa zan je? Gida na can a kulle babu kowa shi yasa ko marmarin zuwa ban taɓa yi ba. Ansari da ya dawo ya zo kwanaki da ya shigo garin kan harkokinsa duk ya rame amma ba laifi tun da ya kwantar da hankalinsa ya fara ɗaukan dangana, ya sanar mini ya samu aikin amma an tura shi Maiduguri babban birnin jihar Borno. Jikina ya yi sanyi tare da zullimin yadda Ansari zai yi nisa Ga shi a lokacin garin Maiduguri na fama da ta'adin yan tada k'yar baya. Amma na daure na yi masa kyakkwar adduar alheri. Ya mini sallama akan gobe zai tafi. Tafiyar Ansari ya sake kassara ni don gani nake yi tamkar shima ya tafi kenan. Da k'yar na hak'ura na cire al'amarin a raina amma bansan me yasa nake ji a jikina ƴaƴana kad'ai suka rage mini. Shi yasa na rike aikina da sana'ata da muhimmanci don duk ƙokarina da wahalata sabo da su ne, domin na ingata musu rayuwa ko da wata rana bana tare da su.

*BAYAN WATA SHIDA*

Bayan watanni shida da tafiyar Ya Sulaiman, ba wanda ya sake jin labarinsa, yana raye ko ba ya raye ba wanda ya sani sai Ubangiji.
Ni dai addu'ata kullum shi ne idan yana raye ubangiji ya karkato da hankalinsa gida idan kuma ta Allah ta kasanance da shi Ubangiji ya haɗa mu a darussalam.

Ashe Abida ta haihu ban sani ba, kuma ba na tunanin wani a cikinmu ya san da batun haihuwar nan, nima Ya Faruƙu ne ya k'ira ni kwana uku da haihuwar ya sanar da ni, sai na ji abin kamar a mafarki tambayar kaina na ke yi dama Abida na da ciki ne? Mamaki da al'ajabi suka sake mamaye ni da jin ikon Allah! Yafaɗa mini namiji ta haifa da uwar da abin da aka haifa duk suna lafiya.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Duk da C.S aka yi maa Abidan a dalilin ba zata iya haihuwa da kanta ba, ban sani ba, sam bansan Abida na da cikin Ya Sulaiman ba wato shi ya sa da rasuwar Mami na ganta wani iri ashe lokacin ma tana cikin laulayi ne? Allah sarki! Kwalla ta zubo mini a dalilin na Kara fahimtar ya'yan Baba Babba gabaɗayansu sun rufe ni daga ganin status dinsu koma share lambata suka yi oho! Ya Faruƙu da na ke ganin yana yiwa zumunci kara bana ganin status dinsa Sai dai ina masa zaton bai share lambata ba, amma na gode masa domin ba dan shi bazan ji labarin haihuwar ba. zumunci ya riga da ya lalace gyaruwarsa zai zama wani abu ne mai wahalan gaske.
Amma na dinga mamakin yadda Baba Babba bai fada mini ba don kuwa ni ban daina gaishe shi ba, a kai akai ina k'iransa a waya na masa gaisuwar juma'a tare da tambayar jikinsa da iyalinsa gabad'aya.


Ni na kira su Saddiqa na faɗa musu haihuwarAbida suna ta mamaki, Ya Hamida ce sai da ta dama ta ɗaga kirana da nafaɗa mata haihuwan Abida ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Ta baya ta rago kenan. Ta yi nasaran koran shi daga k'asar gabaɗaya, sai ta zama uba da uwar abin da ta haifa."
Daga haka ta kashe wayarta sai na sake kiranta.
A fusace ta ɗauka tana faɗin" Wai lafiya kike ta kirana Bilki?"
N tausasa harshe na a ce" ko za ta shirya mu je Abuja mu ga Abida da abin da ta haifa?"
Kawai haka na fad'a Ya Hamida ta fara zagina ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce ita kam ba in da za ta je idan ni zan je Allah ya raka taki gona tunda ban san kishin kaina da na y'anuwana ba.
"Ba haka ba ne Ya Hamida, kar ki manta ba saboda ba Abida za mu je ba. Saboda Ya Sulaiman ne."

Ko saurarena ba ta yi ba ta sake katse wayarta tana faɗin sai kuma na yi, tun da na ji haka sai na zare ta a ciki a raina na kudiri niyyar ni kaɗai ma ya isa zan je na duba ta saboda zumunci da kuma Ya Sulaiman. Na kira Ansari mun yi magana ya ce shi Wallahi nauyi yake ji da ya raka ni amma na fara zuwa shima daga baya zai je, ko dai bai je ba magana ma mai daɗi sadaka ne na ji daɗin mgana da shi. Baban Amrah na dawowa na tare shi da maganar haihuwar Abida.

"Wace ce kuma Abida?"
Ya tambaye ni yana kallona, bai wani ba ni mamaki ba sanin dama ba ya son duk wata magana da ta danganci Abida yake yi ba.
"Abida dai tawa da ka sani y'aruwata"
Na ba shi amsa a takaice kuma a dake.
Ya jinjina kai kafin ya ce" ikon Allah, dama tana da ciki ne?
Na amsa masa da ce wa "ni ma ban sani ba sai da ta haihu."
Tabe baki ya yi bai yi magana ba, ni kuma ganin haka saboda bana son mu sake wata mgana daga baya da sauri na ce" Ina so ka yi mini izini na je Abuja na duba su."
Ya ɗaure fuska kafin ya ce" Me yasa za ki je?"
"Saboda ya kamata!
Na amsa mishi kai tsaye, tuna Ya Sulaiman da na yi yasa kawai sai na fara hawaye ina faɗin" Baban Amra ka yi mini izini na tafi, zan je ganin abin da aka haifawa Yaya Sulaiman wanda ba mu san ko yana raye ba, ni ina ji a jikina wataƙila ba ya raye, domin idan yana raye ba zai kai wannan wattanin bai neme ni ba, k'ila ma a inda ya je ya haɗu da tsautsayi na ajali."
Na ƙarisa faɗa ina mai fashewa da kuka. Jikinsa ya yi sanyi ya taso zuwa gare ni ya rumgume ni yana lallashina.

"Daina kuka, in sha Allahu Sulaiman yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya."
Ya furta hakan murya babu amo.
Na ɗago daga kan k'irjinsa ina faɗin" To idan yana raye yana ina. Me ya sa har tsawon wannan lokacin bai neme mu ba?
Na faɗa hawaye na sake kece mini! Shi ya share mini hawayen yana sake rumgume ni, a daran ya yi ta lallashina da kalamai sai ga shi na saki jikina tun ballanta ma da ya ce ya amince na je amma shi ba zai samu zuwa ba, za su je Zaria shi da Amrah su duba mai sunanta.
Na ce masa sai na tafi da Faruk da Farha. Ya ce to sai mu tafi gabaɗaya idan muka duba Maman Zaria ni da sauran yaran mu ƙarisa Abuja.
Da wannan shawaran muka tsaya washegari kasuwa na shiga na yo siyayyar kayan jarirai da su pampers kamar za a bude shago.
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ni kaina sai da na ga kayan sun yi yawa Abida kuma na siya mata super wax da leshi mai tsada da mayafinsu masu tsadar gaske, ko ba za ta amsa ba ni dai na sauke haƙƙi da nauyi a matsayina na uba tunda ina makwafin yaya Sulaiman ne, tunda ba inuwarsa a wajen kuma babu wanda zai maye gurbinsa sai ni shi ya sa ban ji na sare ba.
Da na koma gida shi kan shi Baban Amrah da ya ga yawan kayan sai da ya yi magana, ni kuma na sake ba shi amsa da fadin "Abida ce ta haihu sannan d'an Ya Sulaiman ne, komai zan yi musu ban biyasu girman ƙaunar da suka nuna mini ba".
Jin na faɗi haka yasa sai ya yi shuru bai yi mini sharhin nasa ba".




Washegari tun safe muka d'au hanya, azahar muna Zaria salla kawai muka yi sai abinci da muka ci, ya kai mu tasha muka shiga mota cikin sa'a gurbin mutum biyu ya rage dan haka muka biya wajen ni da yara. Nan da nan muka kama hanyar Abuja ni da su Faruk, muka bar Amra da Babanta a Zaria sai washegari za su koma Katsina. Ni kuma dama na ce masa zamu dan yi kwanaki, daɗin da na ji, jiya mun samu hutun mid semester.

Sai da muka sauka a garin Abuja sannan na kira wayar Ya Faruku na ci sa'a ya daga k'iran ya sha mamaki da na ce masa ga ni a Abuja, addreshin gidan Baba Babba zai ba ni. Ya shanye mamakinsa, ya turo mini adreshin, mai taxi ɗin da na tare na nuna masa ya ce ya san wajen tunda fitattaciyar anguwace ta masu hali.
Danƙareren gida Ya Asad ya saka iyayensa a ciki, har sai da na saki baki ina kallon gida.
Ba kowa a gidan daga Baba Babba sai Momi sai Abida, sai ma'aikata.
Kawai suka ganmu kwatsam kamar daga sama, tunda da na isa bakin gate din gidan Yaya Farouk na k'ira ya yiwa maigadin magana ya bude mana bayan ya kinkimi kayana.
Ya ce mu shigo zai dawo ya shigo mini da sauran kayan.

Momi ce a falo tare da Baba Babba.
Dukkansu bakinsu ya kasa rufuwa na murna da mamaki.
Momi ta miƙe tana faɗin" Lale marhaban Maigado ke ce tafe?"
Ina murmushin jin daɗi na ce" Ni ce Momi."
Su Farha suka nufe ta ta tarbesu cikin farinciki. Ni kuwa gaban Baba Babba na ƙarisa na rusuna ina gaishe shi.

"Barka da zuwa, lale da Bilkisu yayar Abida!
Nan da nan idanuwana suka kawo ruwa domin na tuna shekarun da suka shud'e a lokacin da muke hade, muke rayuwa cikin jin dadi da kaunar juna.
Kaina na kasa da rawar murya na ce " Sannu Baba mun same ku lafiya?"
Ya amsa da lafiya k'alau yana tambayata sauran yaran da sauran ƴan uwana duk na amsa mishi da muna nan lafiya.
'To Alhamdulillah sannu mai gado. Allah ya yiwa rayuwarki albarka.'
Na amsa da "Amin"
K'wallah na taruwa a kwarmin idanuwana farinciki da alhini sun kewaye ni kamar na fashe da kuka haka nake ji.
'Sai kika ji yar uwar taki ta haihu ko?'
Baba Babba ya katse mini tunani.
"Ban ji ba Baba. Sai shekaranjiya ne Ya Faruku ya kira ni ya faɗa mini."
Ya jinjina kai kafin ya ce" Da ya ke sai jiya aka sallamo ta daga asibiti wataƙila ba ta samu natsuwar kiran ki ba ne maigado "
Ina kallon Baba Babba a cikin zuciyata sai ayyana har yau Abida ce raunin Baba.
"Maigado har yanzu baku samu labarin Sulaiman ba?

"E, Baba bamu samu labarinsa ba har yanzu."

Ya jinjina kai kafin ya ce" Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin aminci"
Na amsa da Amin kasa kasa sai falon ya yi shuru, tunda Momi ta ja yaran zuwa ciki, ta gefen ido nake k'arewa Baba Babba kallo ya warware sai dai bai mayar da jikinsa ba haka nan tsufa sosai a tare da shi alamun har lokacin zuciyarsa bata nutsu sosai ba.
Mamakin Baba Babba nake yi a kullum shin wanne dalilin ne ya sanya ya zubawa Abida ido ta zauna a gida har hakan ya taimaka wajen b'acewar Yaya Sulaiman?
Duk da dai nasan itace rauninsa, amma duk da haka ina mamakin yadda ya iya zuba ido Abida take zaune a gabansa, idan a lokacin ba shi da lafiya ai daga baya ya ji sauƙi ya kamata ya mayar da Abida d'akin mijinta tunda bai sake ta ba. Bai kuma yi laifin da za'a kashe masa aure ba.

"Maigado tashi ki shiga wajen y'aruwar ta ki, ku gaisa ki yi salla ki ci abinci ki huta."
[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Muryarsa ta katse mini tunanina, na amsa masa da to na tashi na shiga dama kayan da na zo da su tuni Momi ta shigar mini da su.
A bedroom ɗin farko na iske Momi da yara ta zuba musu abinci suna ta mata hira tana dariya.
Nan na fara shiga na duk'a har k'asa na sake gaishe ta.

"Lafiya lau Maigado, ya mutanen gidan ina me gidanki da amaryar Alhaji?"
Na amsa mata da duk suna lafiya, mun barta a Zaria tare da Babanta.
Na daɗe a wajenta muna hira itama sai da ta tambaye ni labarin Ya Sulaiman na ce mata ba wani labari cikin damuwa ta ce "Oh Allah ka bayyana wannan yaron alfarmar Annabi."
Na amsa mata da Amin.
"Za ki fara yin salla ne ko sai kin ƙarisa wajen y'aruwar ta ki?
Na ce bari na je can wajenta sai na yi, ita ta nuna mini dakin da Abida take ciki na shiga ciki na iske ta zaune a gefen gado tana shan tea ga Baby a cikin showel a gefenta yadda ta kalle ni na gane ba zan wani samu karbuwa daga gareta ba.

Ba ta yi mini mgana ba tun bayan da na yi sallama ta amsa mayafin jikina na yaye ina faɗin" Sannu "Abida."
Kai tsaye da muryata cikin dakewa ta ce" Yauwa Bilki"
Na kalle ta itama ta kalle ni, hawaye suka kawo mini amma ban bari sun zubo ba, itama ina ganin rauni a cikin idanuwanta sai dai ta yi saurin kauda kanta daga barin kallona.
Ganin haka yasa na ƙarisa wajen jariri na ɗauko shi zuwa jikina a gefen gadon na zauna, ina mai kallon yaron sai da na yi kabbara a cikin zuciyata yaron nan kamar ni ce na haife shi tsabar kammanina da ya debo, ni kuwa dama kaf ɗakinmu na fi kama da Ya Sulaiman hawayen da nake tarewa suka zubo har saman kumatun jaririn na saka hannu na share masa sai barci yake yi.

"Kai ma mu ka biyo?"

Na faɗa murya babu amo kamar shi da Farha a bayyane ba tantama, wannan jinin Ya Sulaiman ne! Da sauri na rungume jaririn ina mai fashewa da kuka har yana fidda sauti. Abida na gefe tana kallona amma ba ta yi mini magana ba sai da na sha kuka na k'oshi na share hawayena amma ina ƙankame da jaririn a hannuna zaman sama da mintina ashirin ba mu tanka ma juna ba sai ita Abidan ce da ta gaji da kanta ta kalle ni tana faɗin.
"Ina yaran ko ke kaɗai kika zo?"
Ina shirin bata amsa sai ga su Farha Momi ta kawo su Faruk ya nufi Abida yana ganinta, ta rike shi a jikinta tana faɗin" Yayanmu akwai ƙauna ashe baka manta da ni ba? Ta faɗa tana shafa kumatunsa shi kuma yana dariya.
Jaririn da yake hannuna ta nuna masa tana faɗin" Je ka kaga k'aninka? Kana son shi?
Da sauri ya ce" E Ammi ina son shi."
Don kaf yarana Ammi suke kiran Abida, wajena ya nufo yana faɗin na ba shi jaririn na ce ba zan ba shi ba Momi ta ce ya zauna sai na rike masa haka ko aka yi jikin shi har rawa yake yi.
"Mahmah da shi za mu tafi?
Ina shafa kan shi na ce"

5 / 7