Author : Sajida Niger Category : Romance
sake shafa fuskarta ya kuma furta " U'r a baby , my baby, Wifey" ya idasa yana dan sakin murmushi kadan yana kallonta
A hankali ya ci gaba da tofa mata Adu'a har ya yi ya gama ya mike ya fice ya rufe mata dakin
Ta baya tmya rufe ya duka ya tura masu ky din ciki sannan ya koma nasa bangaren cike da bege da jin rashi a cikin zuciyarsa, sai dai kamar yadda ya kudurta ba zai takurata ba, idan dai hakan shine burin Amina zai hakura, ko menene ai in sha Allah ya tabata Allah zai sanyaya masa, balema ba wani abu mai karfi da ya wuce tarin kaunar abinda ke cikinta!
Sosai suka raya daren nan, bayan Risala ta yi masa rantse rantsen cewa ba zata kuma bari wani ya ji abinda ya shiga tsakaninsu ba, ta bashi hakuri na wanda ya faru, sun karra tataunawa a kan furucinta na gidan Baba mai shanu sun ganewa junna
Ta sha wahala a yauma , ta sha wahala sosai, domin ya kwana biyu da abin shima, a dole ya barta daga karshe domin irin nishin da take fitarwa kar ta summe masa
Da kyar shima ya samu barcin bayan sun tsaftace jikinsu yana jin yadda mararsa bata sakar masa yadda yake so ba, ama ba halin sake koma mata dan shi ba makaho bane ya gane kwarai ta yi hakuri ta jure kuma ta gaji dole ya tausaya mata ya barta ta huta
___________________________________
Washe gari ta kama asabar, ranar da ya ware ta hutu ce tunda ya tare da matansa, ya kasance yana gida ne tunda safe har wata safiyar, sallah kawai ke fitar da shi sai ko idan ana wani abu mai mahimmanci irin zuwa taaziya, ko zuwa wajen daurin aure, ko zannen sunna, da zarar an gama yake dawowa gida dan ya ware ranar ne dama wa iyalinsa
Kusan karfe goma bayan an kai Biyu wajen aski ta fito a nutse ta nufi bangarensa ba tare da ta yiwa Firdausi salama ba, dama ko da ta tashi a cike ta tashi kamar yadda ta kwonta a kufule, kamar zata tashi sama dan haushi da take ji na kowa da kowa
A nutse ta tsaya bakin kofar tana dan bubugawa kamar yadda ya zame mata jiki, bata fadawa waje ba tare da ta nemi izini ba sannan ta yi salama a amsa mata
A karro na biyu ta sake yin salamar , sannan ta ji muryarsa, duda bata yi tunanin samunsa a falo ba, dama ta tsaya a falon ne da nufin idan ta yi salama uku ba'a amsa ba ta shiga ta haye sama ta same shi a samansa
A hankali ta tura ta shiga tana baza dubanta dan ya lalubo shi a cikin kwayar idannuwanta
A hankali ta karru da kujerar dake gabanta wace bata san ta kawo inda take ba sakamakon kallonsu da ta shagalta da yi dan mamaki dake ciciyar zuciyarta
"Be careful please, don't injured ur ur self " Ya fada yana dan son tashi da dan karfi daga zaunen da yake kan Risala na saman cinyoyinsa yana dan shafa hannayenta dake waje sanadiyar karamar rigar dake jikinta, idannuwansa kuwa tarr a cikin na Amina
A hankali ta dauke idannuwanta ta dan juyar da kanta tana gyara tsayuwarta dan kar ya karaso ya tabata
Shima dan dakatawa ya yi bayan ya tuna da Risala a samansa ya koma ya zauna yana lumshe idannuwansa hadi da lalubo hannunta a hankali ya jimke dan abinda zai rike hakan yake so dan samun kwarin gwuiwar fuskantarta
Yawu mai dacin gaske Amina ta hadiye ta sake juyowa tana dan kallonsa, a ranta tana ayana' Namiji kennan, buhun kaya, watau ga Maina kaya ko? Har ka hau ka jida mata aiki ka sauka ka rike yar shila?, Shine ina fama da ciye ciyen cikin da ka dura min babu ruwanka na rayu ko na mace kana nan ka labe a jikin yar yarinya kamar a karyata dan shegen kasusuwa a wuya ko? Ba damuwa ni ba makashiya bace, zan haife maka na dire maka dan walahi babu wanda zai sakani zawarci da malulun yaro, an jima baa zageni ba!'
A fili kuwa , a dake ta ce" Wajenka na zo, ina son zamu yi magana"
Fuskarta da ta hade da cire kan da take ya saka shi shima a dan hade ya ce" Bismillah"
Juyowa ta sake yi gannin kadangaruwar tasa sai sake dago kai take kamar ta sha rana tana son innuwa kadan ko jin ƙishirwa, sannan ta sake kallonsa ta ga ita yake kallo da idannuwansa dake daf da kasheta dan kaifafan kallonsa sam ba risinawa a ciki
A hankali ta sake juyawa da nufin tafia, dan ta ga soyayar irin mai hawa kan nan ce tanada bukatar a basu waje
A hankali ya dubi Risala kasa kasa ya ce" Bab, dan bamu waje kadan kin ji?"
Sai da ta dan dago yana kallon idannuwansa ta mana masa kisss wanda tsaf a idannuwan Amina sannan ta mike taa nufi ciki firki firki tamkar zata karye biyu
Ita amina Al'ajabinema ke neman kasheta, oh yaren zamani jarabace cike da cikinsu, yanzi wannan yar ita kuma halin da ta saka kanta kennan a rayuwa? Jarabar maza? To Allah ya sanyaya
Zamansa ya gyara yana nuna mata wajen zama dan nesa da shi, a tsare ya ce" Bismillah"
Kujerar ta kalla, tana nesa da shi ainun, sannan ta kalli ta dan kusa da shi
Haka kawai sai ta ga harda rashin adalci a lamarinsa
Ama sai ta kyale shi ta barshi da halinsa ta je ta zauna a kujerar, itama ai gani take ta fi mata alkhairi fiye da kowace
A nutse ta ce" Dama, dama dangane da maganar makaranta ne, jiya twins ke ce min ashe ka cire su a wancen makarantar tasu, ni ban sani ba, kuma har ka saka su wata ta kudi duka ni ban sani ba, shine nace dama zan zo na ganka a kan hakan"
Sai da ta dire aya yana kallonta, shima a hankali ya ce" Eh an yi haka, ashe ban nemi izininki ba Amina, na cire su ne baki yarda ba?"
Idannuwanta ta dago cike da jin wani irin abu marar dadi, tana kallonsa a hankali ta ce" Aa ba haka nake nufi ba fa"
Gannin ya yi shiru ya sakata ci gaba da fadin" Dama na zo mu yi maganar ne, saboda na ji wace makarantar ce suka koma, saboda halin rayuwa idan bata yi mugun tsada ba, kuma na yi godiya"
Yanzunma jin shirun ya yi yawa a dole ta dago idannuwanta dake sade ta zuba masa ido
Sai ta ga ita yake kallo, ama ba da kallon nan na kamar zai cinyeta danya ba, kallo ne normal kawai wanda zaka yiwa irin wani wanda baka sani ba haka
Basarwa ya yi yana kauda kansa ya ce" Allah zai badaa yadda za'a yi in sha Allah"
Amsar tasa a dunkule, kuma yua ja ya tsaya, kamar ya gama maganar yake nufi
Ta dan jima tana cicira maganar, har dai ta rasa abin bilowa a kan maganar sai ta ce" Kuma, Kuma fido yau take ce min an ce ta shirya gobe ta fara zuwa, ta fara tafiya makaranta da kuma koyon girki da.........."
"Amina, abinda ya Kawo ki kennan?" Ya fada yana katseta
Tsuru ta masa da ido
ABDUL ya ce" Idan shine kina iya tafia it's ok"
Sake zuba masa ido ta yi zuciyarta na kunna da tafarfasa, watau ta tafi ta basu waje su dora daga inda suka tsaya ko?
Rai bace ta mike ta juya zata yi tafiyarta tana dana sannin zuwa yi masa godiyar nan, farin cikin da ta tsinta a fuskar kanwarta ya sakata nufo dakinsa, sai gashi yana wulakantata
"Zaki fara awo gobe, dan ya kai wata daya da sati biyu , zaki je wajen Mansur ya hadaki da doctern da zara ringa maki awo in sha Allah" ya fada yana kallonta
Rai bace ta juyo ta ce" Awon me zan je?
A dake ya ce" Awon ajiyar dake tare da ke "
"Ni babu awon da zan je, kuma da kake fadin adadin lokacinsa wani ya fada maka ne?" Ta fada cike da neman a yita ta kare
ABDUL ya tabe bakinsa yana gyara zamansa ya ce" Anya wani ya isa ya fada min bayan ni kadai na diga abina?, Sai dai na fadi ranar da lokacin da tsayin lokacin da ya dauka, Allah dai ya fido shi lafiya"
Kukan da yake ta so ya ganin ne aka fashe da shi, ta nuna kanta, sannan ta nuna shi ta ce" ABDUL, ni kake wulakantawa ko? Ba damuwa Ai damarka ce, ka wulakantani son ranka, ni ga banza ko? Ai na laifi samu ka yi ABDUL, kuma babu inda zani!"
ABDUL yana kallon fuskarta da kukan da ba hawaye ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" Ai ba damuwa idan baki je ba ni sai na aunaki a gida,sai an jima Amina"
Tsuru ta masa kukanta na daukewa, jama'a ga mari ha tsinka jaka? Itace ke gannin haka a wajen ABDUL dan ya gama da ita?
A guje ta juya ta fice a dakinta tana sakin kukanta bilhaki
Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce" Ni fa kwata kwata ban fahimci inda kika dosa ba, me kike nufi ne?"
A hankali ABDUL ya ce" Hajia ki saka yarinyar a nonon mana kar ta mayar?"
Hajia ta ce" Ok, ina zuwa"
Ta sake gyara Amina da kyau ta ciro nonon duka biyu ta talaba hannunta ta nuna mata ta saka macen a hannun dama, sannan ta saka namijin a hannun hagu ta saka Fido talabe mata shi kafin ta iya da kanta tana fadin " sai kin jure fa, akoy zafi*
Amina ta gyada kanta tana rintse idannuwanta, domin namijin kamar jira yake ya yi raf da shi, macen cema ake ta koya mata a hankali a hankali
Karasawa ta yi tana kallon Risala ta ce" Ke tun jiya kina ina har mu na waje muka shigo muka raka yar uwarki haihuwa bakya wajen? Sannan har aka sakomu yau sai yanzu zaki zo?"
Risala ta sosa gaban goshinta da uwar makup din da ta sha tana inda inda ta ce" Hajia sai yanzu na ji ne"
Hajia ta gyada kanta tana yin kwafa ta dubi mahaifiyar Risala dake dan jujuyar da kai irin an takurawa y'arta fa ta ce" Hajia fahimtar da ni Hajia"
Maman Risala ta ce" Gani na yi yaushe kuma kuka shirya da yarinyar cen ne da har zaki dauki y'arta a hannunki kina koya mata shayarwa?"
Ido hajia ta zarro, wani irin mamaki na neman kasheta
Ta juya ta kalli wajen yan matan da kuma ABDUL da ya ciro waya ya koma ya gyara zamansa yana daukanta hotuna a dabarance yana murmushi
Hajia ta ce" Hajia kin kuwa san me kika ce? Na shirya da yarinya har na dauki danta? Ai ni dama ban yi fada da yarinya ba ra'ayina na fada na kuma ja mijina ya ja, a yanzu da na ga har karuwa ta samu kuma na sakar ko a kaina aka fara nuna kiyaya wa matar Da ne kuma daga baya a sota? Ko kina so ki fitar min da wata irin magana irin ta wadda baya gane abinda yake fada cewa ni Hajia Hauwau Alkali me ya hadani da daukan gudan jinnin ABDUL RA'UF Umar Faruk Aliyu?"
Da sauri yayarta ta ce" Hajia, du fa ba cen ta nufa ba, ai ita bata san kin sauko daga kiyayar da kike yiwa matar jikan naki ba shi yasa ta yi mamaki har ta furta, kin san ita batada munafurci ko cem, takan fadi abinda take tunani komai muninsa ne sai dai ka yi hakuri idan ya maka ciwo"
Hajia ta gyada kanta ta ce" Hakane, ba mamaki, halaya ne ai na mahaukata, gashi ita kuma cikin kyakyawar shiga"
"Hajia nice kike zagi da mahaukaciya kuma yau?, Hajia nice mahaukaciya? Walahi ni ba mahaukaciya bace, ai ba karya aka yi maki ba, da baki nuna mata kiyayar ba ai da ba zan zo na fada ba, ko kin ga na maki kage a nan ne? Maman risala da itama ta harzuka ta fada har tana cire hannun yar uwarta dake mayar da ita baya dan bata so ko kadan Maman risalar ta zubar da mutuncinta a idannuwan sirikinta, duda aikin gama ya gama sunne basu sani ba, a hausa ai ba'a haka, bahaushe da kunya da kara aka sanshi ba shirme ba
Rai bace ta ce" Dan Allah adda ki daina turani haba dan Allah, ita komai ya tashi sai ta wani nemi ta wulakanta mutane , ai nima ba yar talaka bace bale a zageni da arziki, ita yarinyar da kika tsana din ai dan yar mai datin hula ce, ko karya aka yi? Kema da bakinki kin ce jikanki ba zai zauna da mai tuyar waina tana bi kwararo kwararo da ƴaƴan shegu a hannunta ba, shine yanzu zaki wani hade kai da ita a cutar min ya? Ba zai yiwu ba tunda aka fara haka Risalar ba zata ga da kyau a wajenki ba, Risala kuwa yar gata ce gaba da baya ba zan bari a wulakanta min yata ina ji ina gani ba, koda banida da shi ba zan yarda abinda kika yiwa wancen ki yiwa yata ba walahi!, Ke risala wuce mu tagi gida wuce min!" Sama sama take maganar danma du wanda bai ji ba ya ji, gaba daya zagin da ta juyewa su Amina da wulakanci tasss kowa ya ji haka kuma sirikinta dake murmushi gaba daya murmushin ya dauke a fatar bakinsa
A nutse ya mike cikin shigar dakakiyar shadarsa ya karaso yana kallonsu
Aa hankali ya ce" am, ku yi hakuri ku koma waje, yanzu ta fito daga asibiti hayaniyar nan ba zata haifar mata da abin alkhairi ba................"
Maman Risala ta tabe baki, bata sake wata muguwar maganar ba dan ko HAJIAR gaba daya bakinta a mace tana kallonsu ne
Maman Risala ta sake lekowa ta ce" Ke wai ba da ke nake ba dan kutumar ubanki?"
Risala ta juyo ifannuwanta sun cika da kwallah ta fara taku daya biyu ta tsinkayi muryarsa a dakensa ya ce" Idan kika fita daga get din gidana a yau ba tare da izinina ba na yanke igiyoyin aurena dake kanki"
A haukace ta ci birki tana juyowa ta kalle shi idannuwanta na firfitowa waje
Haka mahaifiyarta da yar uwarta, haka hajia ta juyo tana kallonsa zuciyarta na karra tsintsinkewa
Bakinta na rawa ta ringa nuna kanta, da shi tana son furta wani abin ama ta rasa mene
Mahaifiyarta ta sake shaka ta saka hannunta ta fardota tana fadin" Sai me, ai mai kyai baya tsawa , wuce mu je Alhamdulilah ba ciki bs goyo bale abin duniya ya isheni, menene a auren da ya wuce cusa bakin ciki da kaskantar da mutun da darajarsa da komai? Wuce mu je zaki samu sama da shi a komai, ai ba shi bane autan maza a duniya!"
Janyo hannun yar take yi , yar na tirjewa
Da karfi ta sake juyo da ita dan ta fuskanci kamar bata jinta, sai dai abinda y'ar ta yi ya sakata zuba mata ido, domin hannunta ne ta janye a hankali hawaye na zubowa yana neman bata kwaliyar da idan biya ne zasu yi a yi mata zasu iya kwararar dubu hamsin
A hankali ta ce" Risa, mu tafi mana kar rana ta yi zafi ta taba maki fata kin ji?"
A hankali Risala ta langwabar da kanta tana kallon Mamanta
ABDUL kuwa ya kama hannun Hajia da ta zama tamkar gunki ya shige ciki da ita, direct dakin Fido domin ya kula tana da bukatar dan kadaicewa ko yayane
A hankali Maman Risala, dan kar su Amina su jiyota ta ce " Me kike nufi da dakatawa a nan bayan kina gannin wulakancin da ake mana , ni uwarki da ke din kanki?"
Risala ta fashe da kukan da take rikewa ta kasa yin magana
Mamanta ta zarro idannuwanta tana nuna kanta ta ce" Risa, risa namiji zaki zaba a kaina?"
Da sauri ta girgiza kanta tana kallon mamanta ta ce" Aa mama, ba maganar na zabeshi bane mama, mama a shekara ashirin da takwas na same shi, na so shi, ya so ni, mun yi aure, yanzu na kai ashirin da tara a duniya, idan har ba zanen kadara ta fitar da ni ba zaki so na dawo na sake maki wani zaman? Mama banida matsala da shi, ban rasa komai ba, kema kin san a aurena zuwa yanzu na tara abinda ban tara ba kafin auren nawa......., Mama kakarsa ce, itace mamansa, itace duniyarsa, idan tana fada s kansa bana gannin laifinta, kamar kece da mu fa.........
, Mama, babar matsalarma ina son shi, mama ina son mijina, idan na biki muka tafi na dawo ina neman saka kanmu a uku baki dayanmu fa? Dan na tabata wata rana sai na tarda ABDUL, idan yau ya koreni, gobe ya koreni, jibi ya koreni, wata rana ina iya samun galaba a kansa, ina iya sakashi a uku, uwa uba na saka kaina...Mama ribar me zaki ci?....."
Dau mahaifiyarta ta dauketa da wani mahaukacin Mari tna nunata da yatsarta ta ce" Ni zaki watsawa kasa a ido a kan Kato?"
Risala da ta duke tana kuka tana girgiza kai, yayar mahaifiyarta na rike mahaifiyar tata har suka janyeta suka fita da ita a falon Amina sannan ta mike da gudu itama ta fita ta nufi bangarenta tana cire abubuwan kwaliyar da aka bata lokaci ana mata dan ta yi kira ta sanar kishiyarta ta haihu , mahaifiyarta ta zabo mata leshen dake da kyau da tsafa aka caka mata dauri, ama abin ya kare a haka? Yanzu yau ita da mahaifiyarta ne wannan abu ya faru? Ina zata shiga da ranta? Shin ABDUL da mamanta wane zata zaba? Idan ta yarda ta zabi Abdul din ya wulakantata da gaske fa? Shin yaya zata yi da rayuwarta?
Wayarta ta dauka ta ringa kiran mahaifinta, sai dai ya fada mata yana cikin aiki, da zarar ya zauna zasu yi magana, a dole ta kashe ta ci gaba da kukanta, domin an saba mata tana samun damuwa takan yi kiran mamanta ne ta zo inda take, ama a yau da maman nata ne damuwar a dole ta rasa inda zata saka kanta
____________________&__
A