Author : Sajida Niger Category : Romance
Firdausi, karma ki saka damuwar wani a ranki ki kasa nutsuwa kin ji?"
Firdausi ta sauke numfashi yinwar fa na cinta, a sanyaye ta ce" Docter, dama wata sharaar ai sai a kiyama......., Luuuu luuuuuuuuuu
Nake gani kar aje nima mutuwar zan yi na shagalta da kurbar juss, shi yasa nake ta Adu'a a zuciyata......ka ga kuma biyu ba nawa bane ba fa, na uman biyu ne"
Tausayinta, madaukakin tausayinta, shi ya fi komai rinjayarsa,
Da dabaru irin na likitoci ya samu ta amshi juss din har ta yi masa sha na mamaki
Tana gama sha ta koma barci domin akoy allurorin barci a lamarin dole sai da hutu
Huci take yi na wanda ke daf da fashewa da kuka tana kallon Hindatu ta ce" Hindatu, halo turaran wutar ne? Nace maku juwa yake sakani Hindatu kin cika masa muski hawar mun kai yake yi Hindatu, wayo Allahna Hindatu". Sai kawai Amina ta fashe da kuka tana zama a kasa kamar wata yar baby
Ido Hindatun ta zarro tana yin waje da turaran ta hanyar kicin da gudu sannan ta dawo hankali tashe sai fadi take"Na shiga uku na lalace, Hajia,dan Allah ki yi hakuri ban san bakya sonsa ba HAJIA, dan Allah ki yi hakuri ki daina kukan na shiga ukuna"
Amina ta tuje hijabin, wani mahaukacin kyau da ta fara yi na daban fiye da gyaran amarcin da ta sha, da wani irin luf luf da gashinta ya karra yi sai wanda ya gani, tana tuje kafafuwanta ta ce" Ki daina ce min Hajia, ni ba HAJIA bace, hasalima filin jirgin kansa ban san a wace anguwa yake ba, kawai sai ki ringa min abinda raina baya so bayan ban maki komai ba?"
"Annabi Muhammadu Rasulullah salalahi alaihi wa ahlihi wa salam, na shiga uku ni Hindatu jikar Maryama, Hajia ki yafe mib baki daya rankatakaf laifin da na yi maki, ki kuma dauka kan ba za'a kuma ba, duka kaf abinda bakya so zan daina yi miki har karshen rayuwata a gidan nan kin ji Hajia?" Hindatu ta fada tana sake dukawa gaba daya hankalinta a tashe, ita tama manta tana sake maimaita Hajiar da aka hannata fada
Da haushi Amina ta mike tana jin juwar na daukanta, dan walahi juwa take ji sosai , gaba daya hadin turaran nan ya mata karfi shi yasa ita bata anfani da turaruka masu karfi, dan sunna cutar da ita ko cenma
Hijabinta ta amshe tana hararar Hindatu dan ganu take yi ai du laifinta ne, ta hannata ce mata HAJIA ta wani sake fada mata
Dakinta ta nufa tana fadin" Sai ki yi ai , ki yi ta cewa Hajiar Hindatu, nace ki kwana kina fada"......
Tsuru Hindatu ta yiwa kofar , sai kuma ta yi hanyar kicin har kamar zata kifa tana adu'ar Allah ya sa kar Hajia ta koreta, ita ta rasa me ta yi da zafi haka har Hajiar take kuka? Wayo duniya
Tana shiga dakinta ta yi bayi tana wurgar da abubuwan dake jikinta
Wanka ta sake yi dan zafi take ji du irin sanyi sanyin garin
Tana fitowa ta dauko yar yololuwar riga fara ta saka , sannan ta dauki hijabinta ta zurma ta fita falo
Wajen abincin ta bubude tana dubawa, gannin abubuwa irin na turawa sak ta rufe tana jan dan tsaki ta nufi kicin din da kanta ta dauko dadawa da tafarnuwa da dan kayan yaji mai kanshi sai magi ,
Friza ta bude ta babako kaza guda ta tsomata a ruwa ta zauna tana jira
Sai da kazar ta saki sannan ta yayankata ta cire bindin ta sakata cikin tukunya ta zuba dadawar nan da komai da komai sannan ta dora saman gaz ta sake hayewa tana dan balancing din kafafuwabta tana jira
Kanshin dadawar ya sakata hadiyyar yawu har kazar ta silalu sosai ruwan ya janye saura kadan, ta juye a kwano ta yi zamanta a cikin kicin din ta ringa dangwalar kazar nan da yajin dadawa tana ci, har wani lumshe ido take yi, a irin wannan lokacin babu abinda ya kai mata kazar nan dadi du duniya
Kwafa ta yi ta ce" Husaini harda kai a kin biyoni ko? To gashinan ina cin irin dahuwar da kake so ni kadai"
Tana gamawa ta kimtsa komai ta koma dakinta ta sake wanke bakinta taa kuma murza humurarta sannan ta hau saman gadon ta zauna tana zubawa waje daya ido
Samun kanta ta yi da yin kwafa kasa kasa ta ce" A me ka dauki kanka? Me kake tunani a kaina? Ko me kake tunani daidai nake da kai walahi!,ina nan gobe sai ka bani sakina malan!"
Ta jima tana fama da tunani da fadace fadace sannan ta koma saman gadon ta kwonta ta yi Adu'a ta yi shiru tana tunanin ta yaya zata iya yin barci a irin wannan lokacin , sam bata jin barcin walahi, gaba daya ranta a wani bace yake bata san dalili ba
Sai da karfe goma ta gota ya shigo dakin bayan ya kashe komai ya sadada a hankali saman gadon ya haye ta bayanta ya sanyo hannunsa a hankali wajen mararta yana dan shafawa
Matsawa ta yi tana son juyowa dan ta mike lokaci daya ta fashe da kuka
Da mamaki kasa kasa ya ce" Na shiga uku mai kuka ne shi kuma"
Tana kukan ta ce" Ka sakeni, ba dai nice abin wulakantawar ba ko?, Mema na maka a duniya da zafi ne wai? Haka kawai ka ringa sakani kuka , da me kake so na ji ne? Harda zaka yi magana kuma ka ki bani amsa a bayane , kuma ka min alamun zaka zabga min mari? Abdul yayarka ce fa ni idan ka mareni ina zaka kai abin kunya?, Ka sani sarai a duniya Hajia batada makiyi irina, bata so, ta taki Sa'a nima bana so, kaima baka so to ba shikenan ba? Babane zamu san yadda zamu bashi hakuri ya yafewa kowa idan yana so dan ya huce ya bani wani datijo mu je mu karata ko?"
A hankali ya sakata a jikinsa ya yi mata rumfa ya juyo da ita barin da yake ya sake riketa a jikinsa sosai yana jin yadda kanta ke sarawa ama rigima ta ki ta daina kukan
A hankali ya ce" To ki yi hakuri kin ji?"
" Na yi hakuri fa kace fa, cewa fa ka yi na yi hakuri? Bayan kana kallona na dawo baka biyoni ka bani hakurin ba, ni kawai ba'a yi min adalci a gidan nan" ta kuma fada tana dago udannuwanta tana kallonsa
Shima tsai ya yi yana kallonta, har ga Allah tausayinta da son fashewa da dariyar rigimarta ke dawainiya da shi
Ajiyar zuciya ya sauke a sanyaye ya ce" Ni kam ban san me yasa yanzu kike da kuka ba Uman biyu, Haba auntynmu wai menene na kukan a ciki? To maganar ba mun san da zamanta ba me ya sa za'a ringa maimaitata?, Kuma ni babar damuwata Baban ne, shi nake jira na yiwa wayo ta yadda zai yarda ya yafe mana ko? Ko baki damu da fushin Baba mai shanunki bane?"
Aminaa ta dan kikifta ido tana ta jan ajiyar zuciya, a zuciyarta tana aauna furucinsa
Ya dora da fadin" Ranar da na ce masa soma kike a rabu cewa ya yi da kuwa ba shi ba mu gaba dayanmu ko a lahira"
Gabanta sai da ya fadi ta dago tana kallonsa da alamun maganar ta tsoratata
Abdul ya ce" Ni kuma da na ga haka sai nake ta son samo hanyar da zan yi masa wayo, baki gani ba ko yanzu da yace maza mu tafi gidanmu na kamo hannunki a gabansa? So nake yi idan ya zo abin kawai ya dangana ya dauka haka Allah ya hukunta ba tare da ya yi mana fushi ba Ko Uman biyu?"
Amina ta gyada kanta a hankali cike da tunanin maganar
Ta dago tana kallonsa ta ce" ABDUL kuma sai ya fita a harkar tamu?"
ABDUL ya gyada kansa ya ce" Sosaima, shi kam yana son hadin nan sosai bayan mu ba wani so muke yi ba"
A hankali ta ce" Hakane"
Abdul ya ce" Shi yasa nake so mu bi komai a hankali ta yadda zamu kai ga ci a hankali ko?, Kin ga akoy abubuwan da ya dace ace kin fara a matsayinki na ke, irin su fitar da taimakon gajiyayu, taimakawa marayu dai da sauransu ko?"
A hankali Amina ta ce" A matsayina na ni wa?"
ABDUL ya zubawa fuskarta ido, shinning din da bakinta ke yi idan tana kuka ya fi komai daukan hankalinsa
A hankali ya ce" Wai da a matsayinki na Matata ko?"
Fuskarsa har zuwa karshen karen hancinsa ta zubawa ido har sai da ya dan dage mata gira ta ankara ta dauke idannuwanta
A hankali ta ce" Kennan kafin mu rabun ka rabani da sana'ata?"
"Kece bakida hakuri, ba zan rabaki da nemanki ba, za'a fara yi maki gyaran baya ne a zuba maki kayan gyaran amaren.......gyaren nima ai na anfana da shi ko?" Ya idasa yana kane mata ido daya
Kunya ta sakata turo baki hadi da son juyawa
Riketa ya yi a yadda take kasa kasa ya ce" Amina, da gaske sai da na kusa summa fa......"
"Ya Allah" ta fada tana zuba masa ido
Murmushi ya yi ya dora da fadin" Takardunki na amsa a wajen Baba, zaki zana ko me kike so, ama........"
Da dan zumudi tana kallonsa ta ce" Ama me ABDUL?"
"Ama bana son maganar aiki Amina, bana son ki fita aiki ne, kin ga ai ga aikin nan a gida ko? Tunda na gida ne ni ba zan hannaki ba" ya fada yana sake kasheta da kallon da bata san me yasa bata sonsa ba
A ranta kuwa ayanawa take yi' Alhamdulilah, dama nima ai ba son sana'a a titi nake yi ba, kafin a rabu dai da sana'ata, kuma indai na zana jarabawar nan ai shikenan du wani tashin hankalinama ya ragu in sha Allah'
Da sauri ta saka hannunta tana damkar nasa jin ya shiga yin wani abin daban
Da matsananciyar kunya ta ce" Menene haka kuma?"
Fuska ya shagwabe ainun yana kallonta ya ce" Marata ke ciwo fa"
"To ni kuma me hadina da haka?" Ta fada muryarta na gargada, tsoro na fara kamata
Kasa kasa ya ce" Ba yi zan yi ba ai, kadan ne zan dan yi wani abin ko?"
"Ka ga babu wannan a tsakaninmu"
Amina ta fada idannuwanta na yin rauraurau
"Na sani aunty.........just wannan.....".........ya fada yana hafe bakinsa da nata a hankali ya shiga kising dinta
Ya dan saki kadan yana sake hade jikinsa da nata ya ce" Kadan ne zan dan taba......"
..........."uman biyu dan kadan ne nake son yi.....mmmmmmmm ......mmmmmmmmmm"
A hankali ya ringa tareta a jikinsa, du yadda ta so kaucewa ya juyota ya tarota a jikinsa, a hankali ya ringa ribamtarta, har ya zamto ta daina son kwace kanta ta ringa binsa da shanyayun idannuwanta da sukai mata wani irin nauyi
Irin yadda yake yi mata ya girmami tunaninta
Wani abin kamar ta kurma ihu ko zata ji sanyi sanyi, ama ta maze ta matse ta rike
Ba karamar dambe suka sha ba a lokacin da ya ringa lalubar wajen da ta sha dinki
Kiri kiri ta ce da shi tana iya barinsa da Allah tunda ya zo ne dan ya kasheta
Sai dai sunna wannan Hali ya sameta da wayo har bata san lokacin da ya kai harshensa wajen ba
Ihun kam a yanzu fitowa ya yi
Kar ku yi mata muguwar fasara, ihu ne na tsoro da mamakin dan Adam
Bata taba tunanin ana haka ba gaskiya,
Bata taba sannin ana yin haka ba
A haukace ta so dagoshi tana zarro idannuwa , sai dai bai bata damar hakan ba a lokacin da ya danna harshensa a wajen da bata iya ambata
Shidewa ta yi, ta yi summan wucin gadi idannuwanta a bude tana kallon sama
A gaskiya idan haka ne abin sai a yi
Du irin nauyi da take ji gaba daya komai ya barta ta ringa sake sakin jikinta ma kanninta (🧐)
A haka ya sake neman hanyar nan a karro na biyu bayan ya yi addu'ar saduwa da iyali
Du yadda ya bita a hankali, ya ringa bin wajen a hankali, du yadda wajen ya jike sai da ya tausaya mata
Domin shi da kansa ya san a jigace take, a wahalce take
Shi da kansa ya san a wannan fannin ita din daliba ce wace ke karamin aji
Da tausayawa ya rungumeta a jikinsa yana dan bubuga bayanta
Ba kuka take yi, ama jan numfashi take yi tamkar mai cutar huka
Jikinta du ya yi laushi ba wani karfi a tatare da ita
Gashin kanta yake kallo domin gaba dayanta ta shige jikinsa ya yi mata rumfa da fafadan jikinsa
A hankali ya karra shafa bayanta yana lumshe idannuwansa
Muryarta cen ciki ta budi bakinta da kyar ta ce" ABDUL ka yaganu ko?"
Idannuwansa ya bude yana kallonta, murmushi ya yi yana girgiza kansa ya ce" Aa fa, keda kika ce karra Abdul karra?"
Idannuwanta suka cika da kwallah ta sadda kanta tana fadin" Ka daina yi min shari mana, yanzu ina zan kai wannaj abin kunyar?"
Dariyarsa ya danne ya ce" To wama zai sani? Babu wanda zai sani ai bale har a miki wani kallon"
A zuciyarta ta ayana' Hakane kuma, ama da na shiga uku da kunyar jama'a '
Nanauyan barci ne ya yi awon gaba da ita, Barci mai tatare da gajiyar da ta sake kwasa da kukan da ta sha
Sai da ya ji jikinta ya sake Sosai sannan ya janye nasa jikin ya luluba mata zannin gadon yana kallonta
A hankali ya kai hannunsa wajen lebenta ya dan shafa yana kallon fuskar tata
A bayane kasa kasa sosai ya ce" Allah ya bani ikon gane cikinki, ta yadda zan tamkwasaki cikin ruwan sanyi......domin ba zan taba yi maki dole ba Amina'
Sai kuma ya yi murmushi yana kallon cikinta, abubuwan dake ransa da yawa a kan tunanin nan....uhum wata rigimar ko kansa zai iya dauka kuwa?, Yana da fargaba a cikin hakan.
______________________________________
Washe gari tunda safe aka kaita asibiti, Muhammat ne ya kaita , a cen ta tarar da Baba da biyu sun zo summa daga masalaci suka wuce
Fido ta farka daga barcin da ta sha ta dan taba hira jifa jifa da y'ar uwarta da Baba, Biyu kuwa tsakaninsu da ita ido ne, su basu wani shaku da ita ba, ita kuma sam bata jansu a jiki du irin masifar da Amina ke yi a kan hakan
...........SANNU a hankali , a kwana a tashi sai da Firdausi ta yi kwana hudu a asibiti sannan aka sake su
A ranar da zasu koma ita ta fito da ky din tsohon gidan da nufin idan sun je zata saka a je a siyowa fido dukkan abin bukata, sai ta ji Muhammat yace gida Oga yace a koma da su
Sunna zuwa gidan tare da su Baba ta samu kiransa a wayar falonta
Tana dagawa ya fada mata a bar Firdausi ta huta banda shan kai da hayaniya, a tabata ta ci wani abin......magana dai irin ta manya, tamkar wani baba a tsaren nan, sannan ya kashe
Dakin da Firdausi ke kallo kamar idannuwanta zasu fado ta juyo tana fadin" Baba wai nan dij kuwa nan dinnne dakina? Ko dai mun yi batan kai ne? Wannan daki haka ?"
Baba ta yi yar dariya tana gyara mata ringeshenta ta ce" Naki ne ke kam yar nan, Ai Allah sai ya karra daukaki a kan cin zalin nan na mijinki, kin ga dai gidan yayarki ne duka wannan"
Murmushi ta ringa yi ta ce"
Asalamu alikum warahamatulah
Murmushi ta ringa yi tace "Baba, da gaske nan ɗin anan Auntyna take zaune? Yanzu wannan duk ni kaɗai?"
Murmushi Baba ta sakar mata tace "Ke kaɗai Firdausi, ai ina ga ma idan bai miki ba za'a iya canza miki."
Murmushi ta ƙara saki tana sauke numfashi a hankali, gyara tsayuwa Babar tayi tace "Bari na je na samo miki abinci, ina zuwa."
Da kallo ta bi Babar tana sake duban iya ƙofar ɗakin kawai, ba jimawa Baba ta dawo da abinci ta aje a gefenta ta taimaka mata ta zauna da kyau sannan ta zuba mata ta ci ta ƙoshi saboda Babar na sake nuna mata mahimmancin ƙoshin na ta a halin da take ciki, tana gamawa ta ɗauke kwanukan za ta fita tace "To yanzu ki kwanta ki huta, haka aka bani umarni."
Jinjina kai tayi da farin ciki tace "To Baba, nagode sosai."
Juyawa tayi ta fita ta sake rufo mata dakin ita kuma ta gyara ta kwanta tana lumshe idanu don neman bacci ido rufe.
_________________
Daga yanayin zaman nashi zaka san lallai yana girmama na sama da shi, ƙara gyara zama yayi yana murmushi yace "To shiyasa na ce bari na kiraka na ji, dan na ga shirun yayi yawa, ita tana zaune haka kuma ko sau ɗaya ban ga ka zo ko dubata ba."
Shiru yayi kanshi sadde ƙasa yana mamatsa tafukan hannayenshi da suka ɗauki sanyin acn mota daya fito daga ciki, kamar ba zaiyi magana ba saboda lokacin da ya ɗauka bai ce komai ba yana nazari kan lamarin na Risalah da mamanta, sam ya salewa lamarinta tunda ta masa wannan terere, a ganinshi sam bai cancanci ta masa haka ba, hakan ma da ta yi ba birgewa ba ce, ita ba ta fi ƴar uwarta sanin zafin jikinta ba, yadda ya je mata haka ya je wa ƴar uwarta, amma sai da ta sanar da duniya abunda ya faru, daga ƙarshe mamanta ta zo ta wani kwasheta suka bar gidan, to me zai musu? Ya dinga zaryar zuwa ganinta yana rawar jiki a kanta? Sam hakan baya daga cikin tsarinshi.
Ɗan siririn numfashi ya sauke kafin cikin nutsuwa yace "Abba ni ban san da zuwanta gida ba, ban ce a tafi da ita ba, shiyasa ma ban zo ba."
Kallo mai ɗauke da mamaki ya bishi da shi jin abinda ya ce, sai ya ji kunya na son rufeshi na abinda matar tasa ta aikata, sam bai ɗauka ta ɗauko Risala dan ra'ayinta bane, hakan yasa shi ɗan sadda kanshi yace" Ah to shikenan ai, ina ga tunda ta ji sauƙi ma zaka iya tafiya tare da ita ko?"
Shiru yayi na wasu daƙiƙu da tunanin shin ya tafi da itan ne? Samun gamsashiyar amincewa yasa shi jinjina kai alamar to amma bai ce komai ba, tahi yayi ya shiga ɗakin matar tashi inda anan Risala ta fi zamanta tunda ta zo gidan.
Yana shiga ya sameta zauna kan gado tana daddana waya fuskarta cike da damuwar