NI ZAN LADABI novel By Sajida Niger

Author :  Sajida Niger Category :  Romance

Chapter   31 / 45

90K to 93K   out of 134.9K words

zaune take a falonta, ta cire hijabin dake jikinta , sannan ta cire riga da zanninta ta ba TV baya da wayarta yar latse tana jiran kiran Baba da tace mata tana gidan rasuwa zata yi kiranta, ta ci kuka har ta gode Allah

An dauki lokaci kusan minti arba'in domin baba bata fito daga gidan rasuwar ba sai da yan rakiya suka dawo aka yi Adu'a sannnan ta fito ta sa aka saka mata kati a tata wayar itama ta samu guu ta zauna ta kwalawa Uwar biyu kira tana fadin" Na'am kina jina uman biyu?"

Amina ta gyara zamanta ta sake fashewa da sabon kuka har tana murza idannuwanta

A rikice Baba ta ce" Allah ka sadani da gannin manzo ba dan halayana ba, ke kuwa me ya faru haka ne? Me aka yi miki da zafi Amina kike kukan nan haka? Ina biyun me ya faru ne ke kike kuka?"

Amina ta shiga magana har tana shasheka ta ce" Wai sai kace saarshi, sai kace wata y'arsa ko wata kanwarsa? Ni ? Ni Baba?"

Baba kam bata gane komai ba, ama ko menene ta san ba zai wuce mutumen nata ba, dan haka ta ce" Me ya faru kina magana kina shan kwana"

Amina ta ce" Yanzu fisabililahi, ya rasa wai wa zai ce zai yiwa tsakani da fita sai Ni?, An fada masa ni matar kulle ce? Ko mijin da zan yi zaman dindindin da shi ai ba maganar kulle bale shi?, Tsakani da Allah da Annabi ace wai ni Amina ya cewa ba'a zuwa? Yo ko biyu yanzu da suka girma ai yar shawara ce bake ni gotai gotai da ni?,"

Sai yanzu Baba ta gane inda maganar ta nufa, dan haka ta ce" ke in ba rashin ta ido ba ki fita ki je ina kuma bayan ko lafiyyar kirki bakida ita? Ina zaki je yau kwana bakwai da tarewa?"

Amina ta ce" Kin ga, maganar jarabawar nan ne aka sake ba talakawa dama, to talakawa mana wa'inda nasu samu sun ajiye a kan lokaci ba, shine na so in yi gagawa in zo gidanki in amshi ajiyar na je na dauki takarduna a gida na je na gyara ma gyarawa na ajiye sannan na siyo kayan wainar Baba, shine wai ya wani ce wai ba'a zuwa, kuma kin ga har yanzu Asma'u fa bata zo ba, a jiya na ji yana cewa bai yarda da aikina ba in ba million ake bani ba, kin ga kar ya min abinda ba shikenan ba ina zaman zamana ya rabani da nemana ya sakeni in shiga uku, dan idan ya watsar min da customa ina zan saka kaina ga y'ayana?"

'bakinki ya sari danyen kashi, Allah ya kiyaye ya sakeki, shashasha!' shine abinda Baba ke ayanawa a ranta
A fili kuwa ta ce"


A hankali ya ce" Ko dai tanada wanda take so ne na tauyeta??????"

Sai kuma ya samu kansa da faduwar gaban jin abinda ya fada din, bai san dalili ba

A hankali ya juya a saman bed din yana lumshe idannuwansa hadi da sake neman barci

Da asuba sunna dawowa daga masalaci tare da yaren ya rakasu dakinsu domin yana son komawa nasa bangaren ya ja carbi har rana ta fito

Yana fitowa ya ringa jiyo kwaramniya kamar daga cikin kicin take fitowa
A nutse ya nufi kicin din da tunanin waye da duku dukun safiya yake kwaramniyar nan?

Gannin ba kowa a kicin din ama fes fes yake sai cokula dake zube nan ga dukkan alamu an cirosu ne, ya nufi hanyar da ya fi jiyo kwaramniyar domin ya ga kofar bayace a bude, dan haka a nutse ya fice sai ya ja ya tsaya yana kallon ikon Allah

Amina ce ta sauka kasa ta duka sosai wajen itacen nan tana hurawa da bakinta domin wutar ta mutu ne kuma du abubuwan fifitar nan Amina ta fi gane hurawa da bakinta, ga wani daurin zani da ta yi a saman wata riga mai siririn hannu ruwan copee

Hular kanta ce ta fadi , ta dakata ta dauka tana lalubar birke ta daidaita ta shiga kunnawa tana fadin" Kayan aiki du na nasaru, yanzu ace wannan abin mai ruwa a ciki ne zai bada wuta? To wai kananzir ne a ciki ko ruwan nasaru ne?, Shi yasama ya kasa hasa wutar gashi zubi daya tak na yi tunda duku dukun duhun asubahi kar safiya ta waye Baba ya yi jiran wainarsa ina nan ina gantali da itace!"

A hankali ya jingina da jikin kofar ya harde hannayensa yana kallonta fuskarsa dauke da yannayin da shi kansa bai san ya kai cen ba

Murmushi yake yiwa dukkan motsinta, ya shagala da kallonta, komai take yi sai ya daukeshi daban, ya bashi fasara daban, ya nemi waje daban ya ajiyeshi mai matukar girma da son daukaka lamarin a bayane, ita batama san yana wajen ba domin hayakin nan da aikinta ya fi komai daukan hankalinta

Hayakin ne ya fara janyo hankalin ma'aikatan gidan masu kula da gidan, maza kennan, domin ko'ina shukoki ne, hayaki dai irin haka a gaskiya basa fatan gani domin ko shara ba konata ake yi a gidan ba bale ace hayakin shara ne, dole zasu duba su ga ta inda yake fitowa

"Aminu, ka ga ka bi ta cen ni bara na bi ta nan mu yi gagawa mu ga ta inda hayakin yake fitowa, ka ga wannan hayaki haka ai ba lafiya ba" usman ya fada yana sakin hanyar ya nufo dayar hanyar, shi kuma Aminun ya nufo hanyar da Amina take

Da dan sauri ABDUL ya fito ya ratsa ya wuceta ya nufo hanyar da ya tabata ta nan za'a bilo a tardo uman biyu ta bararaje tana buga tsugunon nan a haka ita ga mai tuyar waina

Sai da ya wuce ta lura da shi
Samun kanta ta yi da yin dogon wuya tana karra tabatarwa kanta shine, sai kuma ta koma ta dauki hijabinta ta saka ta dauko mafici tana fifita wutar , Allah ya taimaketa ta tashi ta ci gaba da suyarta hankali kwonce, kanshi kuwa ya gama gidan tuni, masu kaunar waina bakinsu ya gama rikicewa da hadiyar yawu

Kusan zubewa ya yi a kasa dan gaisar da uban gidansa
Yana dan dube dube ya ce" Sir dama hayaki ne muke ta gani shine muke neman wajen"

ABDUL ya gyada kansa a nutse ya ce" Ni na hasa shi"

Kai Aminu ya gyada ya mike yana mai yi masa fatan a yi sallar juma'a lafiya

ABDUL ya dan yi gyaran murya yana fadin" Ji mana Aminu?"

Aminu ya dawo ya sake dukawa
Abdul ya ce" Kana ji, du ranar juma'a zakunna gannin hayakin nan, Uman biyu ke tuya, bana son gannin kowa a nan wajen ka fahimta?"

Aminu ya amsa shi sosai sannan ya mike ya tafi

Ajiyar zuciya ya sauke ya koma wajen da take tuyar yana kallon an saka hijabi ashe

Karasawa ya yi wajen wani kyakyawan kwano mai rike zafi an rufe shi da wani farin tawul ya dan tsuguna ya bude yana ciro guda hadi da jujuyata sannan ya yi bismillah ya kai bakinsa ya gutsura yana taunawa a hankali, sai kuma ya saki jikinsa da taunawar domin ta masa dadi a bakin nasa

Amina dake kallonsa kasa kasa ta ce" Baka tsoron kar aje na yi bade baden magani a ciki na asiri?"

Kalonta ya yi da dan mamakinta
Sai kuma ya yi murmushi yana idasa cinyewa ya ce" Uman biyu zan ci nima yau wainar, tai min dadi a bakina.....zaki bani?"

Samun kanta ta yi da sada kanta dan wollah sai ta ga kamar maganar da bata so ce ya yi mata, kawai sai maganarsa ta zai sha ta fado mata a rai jama'a,
Gaba daya tsigar jikinta sai da ta tashi, ta sake sada kanta tana dan bubuga tandar suyar dan gaba daya nema take ta rikice

Mikewa ya yi ya shige ciki ya dauko plate ya dawo ya sake budewa ya zuba kwaya hudu sannan ya koma gefe ya zauna yana kallonta tana tuyar kanta a gefe sam bata so su hada ido
Kunyarta na saka masa nishadi, bai san dalili ba

Koda ya gama cin sai da ya ga ya matse mata waje ya hanna mata motsi yadda take so sannan ya mike yana fadin" ki fa shirya karfe goma mu ajiyeki gidan Fido kafin mu wuce wajen baba"

Da sauri ta dago kanta tana kallonsa ta ce" Allah wai?"

Turus ya yi ya juyo, dan har ya kusan shigewa ya tsaya yana kallonta, to wai hala so take ya ja rantsuwa da ta tsatsareshi da ido, hm Amina kennan yanzu idan wani abin ne ta iya bude baki tace ita babace
Sharewa ya yi ya ce" Idan kika saka suturar dake lafe maki a jiki kuma sai dai mu yi tafiyarmu mu kadai"

Dariya hadi da farin ciki suka hade mata tana fadin" aa aa, in sha Allah bama zan saka ba, wayo Allahna dadi yau zan ga fidona"

Juyawa ya yi ya tafi dan ya koshi ainun so yake ya dan huta koda na awa daya ne kafin su fice gidan Baba su yi hirar safe sai su wuce masalaci tare

Da zumudi ta gama tuyar ta zubawa masu aiki , ta zubewa baba sauran ta rufe ruf ta dora miyar da yake ci da ita ta wuce dakinta

Tun a lokacin ta shiga shiryawa cike da zumudinta , yara kuwa sunna ji sunna gani barcin ya gagaresu domin kiri kiri mamansu ta hanna masu barci ta sakasu yin wanka ta ciro masu jalabiyoyi biyu iri daya da takalmansu ta koma falo tana ta aikin murmushi tana duba lokaci a wayarta

Karfe goma ta gota ya shigo da salama a bakinsa yana dan kallon falon da mutanen ciki

Zamanta ta gyara tana sake baza hijabin jikinta irin ya gani din nan bai matseta ba sannan tana washe bakinta da murmushin da sai ya rantse dai ba na Allah bane dan kawai yace zai fita da Uman biyu ne take washe masa baki har haka

Ratsawa ya yi ya shige dakin biyu, suka rakashi da kallo baki dayansu

Jim kadan ya dawo hannayensa rike da shadoji iri daya ya mimikawa kowane yana fadin" ku cenza kayan nan"

Amsa suka yi , kowane ya nufi inda zai labe ya cenza suturarsa,

Da kallo ya bisu ya juyo yana murmushi ya ce" Wai zuzuzu dinsu zasu boye miki"

Ido Amina ta zarro ta juya da dan sauri tana nufar wajen table dan dauko kwanonin wainar nan a zuciyarta tana ayana' Sam ba kunya a lamarin ABDUL'

Tana kawowa ta ajiye ya bi kwanonin da kallo ya gyada kansa ya ce" Kin san na kula yannayin tafiyarki ne yannayin nuna halitar jikinki, kawai ki daina tafiya da sauri sai bombom din su daina dancng......"

"Kai jama'a" ta fada kasa kasa ta sake yin shiru, dan dai burinta ai su kaita inda zata je , bata so ta biye shi su yi wani fadan ya sake hanna mata fita

Cikin motar suka shige, biyu a gaba su biyu, ita da shi a baya a zaune, sai sasada kai take yi tana tunanin idan aka ganta a make a wannan shareriyar motar ai ta gama siyawa kanta zunde da yagalgala, bama irin wa'inda suka nuna mata soyaya ta kiya, ai har ance dama kudi take so ba wani datijo ita kuma du wanda ya fasarata haka ya cuceta Allah ne zai saka mata

A hankali yake jansu, sai da suka je anguwani uku sunna sauka da biyu da shi kadai da direba su shiga su fito sannan suka dauki hanyar gidan Fido tana kwatanta masa yana fadawa direban kamar wani wanda aka saka dole sai shi zai fadawa direban har suka iso kofar tsakuraren gidan Fido din direban na tuki a guje kamar zai tashi sama, ta kula da direban da ABDUL din du kamar yan daba Walahi

Ido ya zubawa kofar yana kallo, sai kuma ya dubeta ya ga tana washe baki ta kama kofar ta bale ta fita harda yi masu byby abinta ta tsalaka kwatar ta nufi soron kofar gidan

Basu tashi ba domin a tunaninsa zata dawo ta yi masa iso ne su gaisa da kanwar tata, haka kuma a tunaninsa ai biyu zasu sauka su gaisar da mahaifiyarsu, sai ya ga basu motsa daga inda suke zaune ba

Da kulla ya ce" Boys ku je mana"

Husaini ya juyo ya kalle shi, sai ya juya yana girgiza kansa ya ce" Dady ai bama shiga, idan muka shiga mijin Aunty ke dukanmu , itama ya doketa, yace maza basa shiga gidansa wai"

Daga Abdul din har direban a zabure suka kalle shi,
Abdul ya sake fuskantarsa da kyau ya ce" Husaini, ba nan ne gidan mamanku ba?"

Husaini ya kalli Hasan, Hasan ya kalle shi, Hasan ya juyo yana kallon ABDUL ya ce" Dady gidan kanwar mamanmu dai ko? Gidan aunty ne nan, mu mamanmu ba a gidanmu sabo bane kace gidanta cen ne gidanta ko?"

Sai yanzu ya tuna wa suke duba uwa a duniya

Sai ya ji haka kawai ya kasa bada umarnin su tafi
Haka kawai ya ji yana so Uman biyu ta fito su tafi gida kafarsa kafarta, bai san dalili ba sai ya ji gaba daya hankalinsa na kan gidan

A hankali ya bude bangaren da yake ya fito ya tsalaka wajen mazan dake zaune sun zubawa motar ido tsuru sunna kallo

Hannu ya basu suka ringa gaisawa da kula sosai sannan ya nemi waje ya zauna a kan bancin da aka marmatsa masa ana yi masa bismillah mana

Habu mai teburin ya ce" Malan bako ne ba? Sai na ga kamar gidan Mudi kuka sauka?"

ABDUL ya yi murmushi yana gyada kansa ya ce" Eh, na kawo madame ne ta ga kanwarta, inaga matar gidan itace kanwar tata"

Saley ya sauke ajiyar zuciya yana fadin" Alhamdulilah, dama yanzu muka gama maganar yarinyar, muna yi mata ADU'A, muna fatan Allah ya amsa, ace yarinya a kan gwuiwa yau kwana biyu tana fama ama ya ki a mikata asibiti? Yanzu da kai ya waye Allah na tuba ai ba'a haihuwar gida, mata na wahala ana kallonsu har sai sun lalace a yi watsi da su, ko idan abu ya zo a mace ko su su mace sai kaji ana fadin lokaci ya yi, eh Akoy maganar lokaci,wanda idan ya yi ba tsumi ba dabara, ko a ina kake ko a karkashin kulawar wa kake zaka tafi ne, ama kuma akoy mugun hali na wasu mazan,Allah na tuba wannan asibiti ta gwamnati da yan kudaden da zaka kashe basu taka kara sun karya ba kake yiwa macen bakin ciki?"

Audu ya ce" Kai fa saley kanada matsala, aishi wannan mutumen bama maganar kudin bane inaga, wannan bakin hali nasa sam bai masa rana ba, wai sai ace maza sunnada kishi basa so namiji ya bude masu mace ya amshi haihuwarta, ni fa nan da ka ganni da innar baban gida ta jigata gwara namijin ya amshi haihuwar tata, to Allah na tuba lafiyarta ai ta fi min komai a duniya"

Saley ya amshe da fadin" Kai kace, bale yanzu fa mata ke amsar haihuwar nan,mata ilimi suke yi sun amshe abin fa, maza kuwa su duba maza yan uwansu, dama in ba mai laluwai a hannu ba ina kai namiji kato ina karatun feraye matar wani? In ba so kake yi ka ringa shiga hurumin da ba naka ba"

"Ku dai kun shiga uku da bakinku walahi, kun ga sai maganar nan kuke tunda safe matayenku sun zigo ku kun zubawa kofarsa ido kun kasa aikata komai sai saka da warwara kuke yi, inace yanzu na gama maganar mu kai kara wajen mai gari a fitar da yarinyar cen a kaita asibiti kuka nuna aa aa wannan ba huruminku bane, sai da mutun ya zauna zaku saki baki kunna cakalkalarsa, idanfa dan uwansa ne?" Mubashir ya fada da dan fada fada, domin tunda safiyar juma'ar nan ta waye suke kan maganar nan, ama da Mudin ya fito siyan garin kwakin ashirin hannu hannu suka ringa bashi sunna gaisawa shi kuwa yana wani cire kai kamar wani tsiya, wai shi baya shiga hurumin yan anguwa baya son tsegumi, wani tsegumin kuma, na nawa? Shi kulun kamar zai hadiyi zuciya dan bacin rai

Audu ya kama baki yana yar dariya da jan hakorinsa a bakinsa ya ce" Karan uwan nana kaya, gacin uwanan kayasa, ai da mun shiga uku, to ama ai da wahala a dangin Mudi a samu mai fara'ar wanann, Elhaji ko ba haka ba?"

ABDUL da komai suke fada ke karra dan tunzura jinnin jikinsa , da kara fahimtar wa kanwar matarsa ke aure, da son shiga gidan kai tsaye ke karra shigarsa ya rafka tagumi yana kallonsu har suka dasa Aya ya mike ya yi masu salama ya tsalako ya shiga kai kawo yana duban kofar yana tunanin ba zai iya motsawa ba sai ya ji daga bakin Uman biyu


A cikin gidan fido

Rungume Amina take da Firdausi tana magana hankalinta tashe tana fadin" Tun yaushe kike yashe a tsakar gidan nan haka Fido? Ina makotanki? Fido ina Mudi yake?"

Firdausi dake numfashi da kyar tana sake rike hannun yayarta muryarta cen ciki ta ce" Aunty, wayo Allahna Aunty mutuwa zan yi, Aunty mutuwa zan yi , bana iyawa na gajiya Aunty, dan Allah ki yafe min zan tafi nima na barki da nauyi a kanki Auntyna"

A zabure Amina ta mika hannunta jikin kofar dakin ta shiga bugawa da wani irin karfi tana fadin" Kai Mudi? Mudi? Mudi? Ga takalmanka nan kana jina ga takalmanka nan ka fito Mudi kana jina?"

Wani wawan tsaki ya ja ya taso daga kwoncen da yake yana son yin barci, domin daren nan kwana ta yi tana hailala da kiran Allah shi du ya zatama ba zata waye ba a irin yadda take haukan nan, ta saka makota sai binsa da kallo suke matayensu yan saka ido sun kai masu gulmar gidansa ko? To baki daya daidai yake da uban kowa, inda ubanda ya isa dan Allah ya fito ya fitar da Firdausi daga gidan nan ya gani! Iskancin banza iskancin wofi yanzu yayarta ta zo shine zata wani langwabe ita ga kwalba sarkin shari ko? To ya fisu iya iskanci, wa suke da shi da ya tsaya masu a duniya? Wai wani Amina ta yi aure ta auri mai kudi, ai ko kudin ta aura yana nan a yadda yake zata dawo ne zaman

31 / 45