DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy

DIJAMAH 'YAR FULANI Ranar da Komai Ya Sauya by maman teddy
  • Author: Maman Teddy
  • Category: Romance
  • Compiler: None
  • Association: None
  • Book Series: None
  • Upload Date: 15 Wed 07, 2026
  • File Size: 226.83 KB
  • Total Views: 5
  • File Downloads: 2
  • Last Download: 2 days ago

Discover

  • ENGLISH DESCRIPTION

    Deep within the peaceful Fulani settlements, where cattle herding is a way of life, lives a cheerful and talkative young girl named Dijamah who has no idea that her entire life is built on a devastating secret.

    To her, the world is simple. Her mother, her friends, and the lively Lumo market are all she has ever known. But one unexpected encounter with a mysterious woman named Uwani changes everything. A single revelation is enough to shake the foundation of her existence.

    Why has her mother spent years hiding the truth about her father?

    Who is Alhaji Muhammad Maccido, the celebrated philanthropist admired by everyone, yet haunted by a painful past he cannot escape?

    Why was a mother separated from her newborn daughter just three days after giving birth?

    Who destroyed this family's happiness, and why has the truth remained buried for so many years?

    As Dijamah dreams of finally meeting her father, powerful people are determined to ensure that reunion never happens.

    The long-buried secrets are slowly resurfacing, and when the truth is finally revealed, no life will ever be the same again.

    DIJAMAH THE FULANI GIRL is an unforgettable story filled with love, family secrets, betrayal, jealousy, heartbreak, destiny, emotional twists, and an unforgettable search for the truth. Once you begin reading, you will not want to stop until every hidden mystery is uncovered.

    HAUSA DESCRIPTION

    A cikin dazuzzukan Fulani inda kiwon shanu da zaman lafiya suka kasance rayuwar yau da kullum, wata yarinya mai fara'a da yawan surutu mai suna Dijamah ta taso ba tare da sanin cewa rayuwarta cike take da babban sirri ba.

    A gare ta, duniya ta taƙaitu ne tsakanin Ummah, ƙawayenta, da kasuwar Lumo. Amma wata rana, haɗuwa da wata baƙuwa mai suna Uwani ta sauya komai. Kalma guda ta isa ta girgiza rayuwar Dijamah gaba ɗaya.

    Shin me yasa Ummah ta shafe shekaru tana ɓoye gaskiyar mahaifinta?

    Waye Alhaji Muhammad Maccido, mutumin da ake wa kirari a matsayin gwarzon alheri amma zuciyarsa ke ɗauke da raunin da bai taɓa warkewa ba?

    Me ya sa aka raba uwa da jaririyarta kwanaki uku bayan haihuwa?

    Wanene ya sace farin cikin wannan iyali, kuma me ya sa aka binne gaskiya tsawon shekaru?

    Yayin da Dijamah ke mafarkin haɗuwa da mahaifinta, akwai waɗanda za su yi komai don wannan haɗuwar kada ta taɓa faruwa.

    Sirrin da aka binne shekaru da suka gabata yana dawowa a hankali, kuma lokacin da gaskiya ta bayyana, rayuwar kowa za ta canza har abada.

    DIJAMAH 'YAR FULANI labari ne mai cike da soyayya, sirrin iyali, cin amana, kishi, hawaye, ƙaddara, da gwagwarmayar neman gaskiya. Labari ne da zai sa ka kasa ajiye wayarka har sai ka gano ƙarshen wannan babban sirri.