Author : Ummu Affan Category : Romance
wataba a danginsa ko mutanan gari sai tilon 'yarsa abin sonsa ita kad'ai ya mallaka kuma yasan bayan ita bai k'ara haihuwa domin tuni aka masa abinda bazai k'ara haihuwa ba,don a tsarin dodonsu kowa haihuwa d'aya zaiyi,kuka yake sosai yana tausayin kansa a haka Hjy luba da Khairat suka iskesa,
Hjy luba ta fara tambaya "Alh lfy me ya faru kake kuka haka kamar k'aramin yaro?,
K'amk'ame Khairat yayi yanaci gaba da kuka,turesa take "Dad lfy meye hakan?,sakinta yayi yana share hawaye,yace"babu komai,kallonsa sukayi amma ganin baice masu komaiba sai suma suka sharesa,
................................................
"Haba Lameer meyasa zaka saka damuwa irin haka aranka kazama wani iri kamar ba Lameer jarumi me karsashi da jarumta ba,tabbas muma abin nan nadamunmu domin 6atan mutim bashi da dad'i 6atan mutum sai kace 6atan takalmi amma fa dolene kayi hakuri tunda iyayenku meye basayi kullum sai an sauke Qur'ani me girma ga addu'o'in da akasa,manyan malamai nayi ga wanda mukeyi insha Allahu an kusa ganin Zainab jikina na bani Ummi na kusa damu,
Umman Zainab ce ke wa Lameer wnn mgnr,numfashi yaza sai kuma ya mik'e baice komai ba,Ammi ta girgixa kai tace"Husaina dama kin barsa kullum cikin haka muke da yaron nan amma ko kulani baiyi,Umma taja numfashi kawai tare da tagumi,
Bayan sun iso kasuwar k'auyen yace"To wanne guri zai kaiki,kallomsa tayi tare dajan numfashi tace"uhmm uhmm,da sauri ya kalleta cike da rashin yarda yace"uhmm me?tasaki wani murmushin k'arya tace"naga banga shagon siyar da kayan kwalliya bane,yace"nima ba sanin k'auyen nan sosai nayi ba yanzu ya za'ayi,
Kalle kalle ta fara sai tace"to ko zaka fita kayi mana tambayane,yace"ok haka ne bari nayi tambaya ina zuwa kawai ya fice.........
Wallahi yau da kamar bazanyi ba,😏😏
Amma gashinan kunsan ance jiki da jini sai a sulo yaudai haka nakejin jikin nawa sai a hankali don Allah kusani a addu'a,
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to Fans
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
🅿️29↪️30
Tana ganin ya fice,itama ta sad'ad'a a hankali ta bud'e murfin motar ta fice da sauri,
Sauri-sauri take tafiya,ganin kamar yana binta tasaka gudu,yana dawowa yaga bata ciki gabansa ya buga,keiiii!ya furta a gigice,da sauri yabi bayanta,yana ta waige-waige amma kome kama da ita bai gani ba,cike da takaici ya koma gurin motarsa,
Ita kuwa Zainab babban titi ta koma duk motarda tagani sai ta fara d'aga hannu tana tsayarwa kamar wata mahaukaciya,haka motoci sukai ta wucewa sunk'i tsayawa,duk'ewa tayi a gurin tana kuka sosai don gani take boss ya kusan zuwa inda take,ji tayi ana danna mata wanu uban hune,a furgice ta d'ago zuciyarta na raya mata shi kenan tata ta k'are tunda boss ya isu..
Saleem shine aminin Lameer wanda suka taso tun lokacin k'uruciya tare sukayi karatunsu,ba'abinda Saleem bai sani ba gami da gidansu Lameer shima Lameer d'in yasan komai na gidansu Saleem domin dukkansu kai tsaye suke shiga gidan iyayensu,shima Saleem Doctor ne,
Lameer yace"me kake cewa?,kallon aminin nasa yayi cike da tausayi yace"yanzu duk uban surutun nan da nayi cewa zakayi bakaji abinda nace ba,sosa kai Lameer yayi yace"uhmm wllh Saleem tunda abin nan yafaru nifa kallon mutane kawai nake mgn ma ba damuna tayi tunani duk yana gurin halinda k'anwata take ciki,
Saleem yace"ai hkr ya kamata kayi wnn ma wata jarabawarce ta Allah sai kayi hkr kaci jarabawa,yace"hakane,Saleem yace "daman Jos nace maka zani akan mgnta da Hannah iyayenmu sun matsa ita sukeson na aura,kasan d'iyar yayan Abbanmu ce zanje zance tunda a Jos suke da zama,Lameer yace"kamusu biyayya sai kaga al'amuranka na tafiya ta daidai bare Hannah batada wata makusa,bazan iyaba da na rakaka,
Saleem yace"na sani ni daman bance ka rakani ba bari na wuce don a yau insha Allahu nakeson dawowa,
Har bakin motarsa ya raka sa yamasa fatan alkhairi snn ya juya,girgiza kai Saleem yayi cike da tausayin aminin nasa snn ya ja motarsa ya wuce,
To akan hanyar dawowar Saleem daga Jos,tundaga nesa ya hango ta tana d'agawa moto hannu har zuwa lokacin da ta zube tana kuka,bai ta6a kawowa Zainab bace har ya wuce ya dawo don tabasa tausai besan meyasa tayi hakamba don hk ya dawo da niyyar temaka mata yasakar mata hun,
Shinefa ta d'ago agigice a tunaninta boss ne,ganin ba motar boss bace yasa ta taso da gudu ta bud'e tace don Allah bawan Allah ka temakamin Kaduna zani,
Jin kamar muryar zainab yasa yace"Ummi,a d'an gigice,da sauri ta d'ago ganin Saleem ta fashe da kuka tace"Yaya Saleem mubar gurin nan wllh xai biyomu,ai da sauri ya tada motar ya fuzgeta,
Suna tashi Boss ya zo gurin,sai dube dube yake ransa a jagule amma bai gantaba,yace"wllh zaki gane ne koda na barki Khairat tunda tayi niyyar kasheki to saita kasheki wawiyar yarinya,ai bai gama rufe baki ba,wata babbar mota dake ta aikin danna masa hune don ya tsaya bisa hanya tayi ciki da motarsa domin me babban motar yakasa sarrafa burkinsa,aikuwa motar boss tayi ta wuntsilele luwa a daji zuwa cen ta kama da mota,shi kansa me babban motar da sauran mutane biyun dake ciki da k'yar aka curosu d'aya cikinsu ya rasu,boss kuwa ai tuni ya gama k'onewa haka 'yan kwana-kwana suka ciroshi da kyar aka nufi asibiti dashi da sauran biyun waccen motar,suka hau kashe wutar,
Kuka kawai Zainab keyi hakan yasa Saleem bai iya cewa komai ba har suka isa Kaduna kai tsaye gidan malam babba ya nufa da ita tunda acen sukayi sallama da Lameer,
Ai tun kafin ya gama parking,ta fita a guje tana "yayah Lameer Ummana Babbana Abbuna Ammina Kakaaaaaa!,
Da sauri dukansu suka mik'e dukansu sukayi waje da sauri ai tana ganinsu ta ruk'umk'ume Ammi tana kuka,suma duka suka saka kuka,suka ciki suna tambayarta ta kasa bada amsa sai kuka,
Shi kuwa Saleem jin ana sallahr magrib shiga yayi masallacin k'ofar gidan,bayan sun fito ne ya yaga sun fito gaba d'aya tare da su Abbu Baba da Lameer,nan ya gaishesu,suka amsa cikin fara'a,
Lameer yace"kadawo kenan,yace"aikuwa,ya d'aura da cewa mushiga kaga abinda xaka gani yau har tukwici sai ka bani,
Da sauri ya kallesa tare da murmushin yak'e yace"aini yanxu ba abinda ke burgeni idan ba Zainab zaka dawomin da itaba,yace"kaidai abokina mushiga ka gani,haka suka shiga gidan suma su Abbu suna addu'ar Allah yasa suga alkhairi......
Nace muku banjin dad'i kuyi hak'uri da wnn,wad'anda sukamin addu'a na gode sosai ana mugun tare🤝😍
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
_Wad'anda sukemin addu'a nagode sosai ana mugun tare Alhamdulillah naji sauki nagode da addu'o'inku gare ni ana mugun tare_
🅿️31↪️32
Shiga sukayi ciki haka nan Lameer yaji gabansa na fad'uwa,da sallama suka shiga farlourn Kaka,
Duk hijabaine jikinsu da alama suma basu dad'e da idar da sallah ba,
Zainab kuwa na jikin Ammi har zuwa lokacin kuka take don gani take kamar boss zai sake zuwa ya tafi da ita,
Tajin sallamarsu ta mik'e da gudu ta ruga ta k'amk'ame Lameer,ai shi suman tsaye yayi bai ta6a tunanin Zainab d'insa zai gani ba,kasa magana yayi sai rik'eta sosai da yayi ajikinsa yana sauke ajiyar zuciya,
Abbu da Baba,kuwa Alhamdulillah kawai suke maimaitawa,Abbu ya d'aga hannu yace"godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai Allah kaine abin godiya mun gode maka,gaba d'aya gurin sukayi salatin Annabi,
Bayan duk sun zauna,Saleem ya musu bayanin komai yace"bayan na dawo Jos daidai k'auyen nan Fanbeguwa anan naganta tana tsaida mota ba motar da ta tsaya har na wuce sai tabani tausayi ban d'auka Zainab bace saida tashugo,
Kallonta sukai idanuwansu cike da alamar tambaya,cikin kuka ta sanar musu duk abinda ya faru har zuwa yau da ta gudu,
Ai wani mek'ewa da Lameer yayi kowa saida ya dubesa,idanuwan nan nasa tuni suka cenza launi zuciyar 'yan maza ta tashi cikin wata irin murya me had'e da kishi yace"maxa kitashi muje ki nunamin inda mutumin nan yake wllh yau sainaga bayansa,
Saleem ne ya kamashi ganin yadda yake fuzgar hannun Zainab yana"ki tashi muje nace,yace"haba abokina wnn duk ba naka bane tunda Allah ya ku6utar da ita daga hannunsa ai sai mugodewa Allah snn Allah zai mata sakayya ita da sauran mutanan da yacuta har yakashe don hakkin rai ai babba ne,
Baba yace"wnn haka yake karka damu d'ana Allah zaiyi ikonsa akansa,da k'yar ya zauna donji yake da zaiga mutumin nan zai iya kashesa sbd 6acin rai,
Kallon Zainab yayi yace"to ke bakiji yace wani yasashi ya d'aukekiba,shuru tayi tana tunani zuwa cen tace"eh naji dai yana yawan ambaton wata wai cewa tayi akasheni,gaba d'aya suka d'au salati yace"bai fad'i sunanta ba,tace"ko Khairat yace kome?,da sauri ya mik'e yace"Khairat ko daman na dad'e ina zargin dasa hannunta a 6atanki yau zata gane kuranta,
Da sauri ya fice,suna kiransa amma ina xuciyarsa ayi zafi,
......................................................
Acen gidan Alh Kamalu kuwa,rigima ake sosai domin an amshe Senator da aka basa daman ba mutane ne suka za6esa ba murd'iya ce,to asiri ya tuno don haka gwamna me adalci ya amshe anbawa wani ruk'on k'warya kafin ayi za6e,nan fa hankalinsa yatshi inda ake ta d'auki ba d'ai d'ai domin gidan Redio yaje yana ta zagin gwamna,
A hanyarsa ta dawowa dunduzun matasa suka taresa sukai masa tsinannan duka,snn suka kona motarsa,nan suka barsa kwance rai a hannun Allah,
Da k'yar wasu masu tawakkali suka kaisa asibiti,lokacin da aka sanar da Hjy luba da Khairat tsaki sukaja,sukace babu ruwansu aisaida sukace kar yaje snn yaje dama kashesa sukayi,
Cikin dare kuwa gidansu ya kama da wuta domin d'akin da dodonsa yake ya faraci,zuwacen gidan ma ya faraci,sosai suke ihu suna neman temako,kafin 'yan kwana-kwana suzo ai tuni sun galabaita,
Mutanan unguwa aka taru domin ihun da akeji a gidan yayi yawa,wani d'aki da aka bud'e anan akaga kawunan mutane da gangar jikin mutane,nanfa aka dunga tsine masa da Allah wadai,'yan jarida tuni suka hallara da 'yan gidajen tv kai abinfa ba kyan gani,
A wnn halin Lameer yazo,ganin abinda ke faruwa yasa jikinsa sanyi da Allah wadarai da halin Alh kamalu,
Su Khairat kuwa anji jiki,Hjy luba tuni ta amsa kiran Allah,khairat kuwa duk ta k'one ta cenza kamannin babu kyawun gani,abin da abin tausayi,
Haka Lameer ya koma gida yasanar da iyayensa nan suga dunga Allah wadai da wnn abu,
Alh Kamalu kuwa ai asibiti ihu ya dungayi yana fad'ar mugayen abunda yayi harda uwarsa da k'annansa da yabawa dodonsa da duk wasu da yakama,
Zuwa wani lokaci akaga cikinsa yayi girma sosai irin naban mamakin nan,uhmm kai abin fa babu kyawun gani da haka yarasu yana ihuuu,(Ya Allah kasa muyi kyakkyawar mutuwa kagara halayenmu ka hanamu aikata alfasha,don Allah yanzun ina amfanin bad'i ba rai Allah ya kyauta),
Alh kamalu dai an tafi cikin wani mayuwacin hali,ya Allah ka shirya masu hali irin nasa amin,
*************
Zainab kuwa tun bayan abinda ya faru,duk tadawo wani irin sanyi ta natsuwa kai bazakace ita bace,sosai yanzu ta mayar da hankali akan karatunta,
Babu wasa da shirme,ga girmama malamanta,
Akwana atashi babu wuya a gurin Allah,Shekaru hud'u kenan,a yau Zainab ta kammala jarabawarta ta SSCE ta kammala secondry,shekarunta sha takwas yanxu xuwa lokacin tayi girma sosai kyawunta yafito tazama cikakkiyar budurwa mai kyau da tsari ga natsuwa da kamala,
Kyakkyawar yarinya me manyan idanuwa ga hanci bak'inta mekyau da zubin hak'oranta farare tass,gashinta kuwa bak'i wuluk ga tsawo da yawa,
Idan tayi mirmushi kumatunta biyu sai sun lotsa kai da ka ganta saita burgeka,
Yaya Lameer ma an k'ara kyau,uhmm abin sai wanda ya gani cikakken namiji kenan da ko wacce mace zatayi alfahari ya zamo miji a gareta,sunyi kama sosai da Zainab d'imsa yanasonta so na hak'ik'a,gaskiya Yaya Lameer k'arshe ne wajen kyau da tsaruwa,
Tana zaune a farlourn Ammi ya shugo sanye yake da k'ananun kaya gaskiya yayi kyau,zuba masa ido tayi tunda yashugo aranta take aiyana kyau da had'uwa na yayan nata ji take inama ace shi,mijinta ne gaskiya tana k'aunar yayan nata,
Hura mata iska yayi cike da shagwa6a ta turo baki gaba yace"wnn irin kallo karfa ki cinyeni d'anye,tace"kai yaya Lameer kullum fa naga kyau kake k'arawa wllh,
Dariya yayi me k'ayatarwa yace"duk kyauna ai ban kai sarauniyar mata ba,yanzu,ma tad'i zani ko zaki raka nine,tuni ta zaro ido sai kuma ga yawaye sun taru mata tace"tad'i,kuma yaya,sai ta fashe da kuka tayi ciki da gudu murmushi yayi yabi bayanta da kallo aransa yace"dole in amshi matata hannun Ammi don yanzu ne lokacin da nafi buk'atarta,
Jikin Ammi ta fad'a tana kuka Ammi tace "lafiya me yafaru Ummi,cikin kuka tace"Ammi ba Yaya Lameer bane wai tad'i zashi don Allah kice kar yaje wajen wata,
Zaro ido tayi Tace"ehye,sai tasa dariya tace"ki kwantar da hankalinki Ummina kin kusan tarewa gidan,mijinki don yanzu haka shirye-shirye muke,tace"miji kuma wanne mijin?,nan Ammi tasanar mata duk abinda ya faru a baya na auransu da akayi da yayanta,
Ai tsalle ta buga ta rungume Ammi tace"kai amma naji dad'i Ammina gaskiya kun kyauta mana,da gudu ta fita cikin jin dad'in daman yaya Lameer mijinta ne lallai tafi,ko wacce mace sa'ar miji a duniya
(ni kuwa Ummu Affan nace a'a zee nimafa nafi ko wacce mace sa'ar miji😜😜)
Ammi murmushi tayi cike dajin dad'in Ummi ma tanason Lameer,Hussainarta takira tasanar mata wato Umman Zainab nan sukai ta dariya sukace yaran zamani kenan.......
Mu had'e gobe don jin k'arshen labarin
Taku a kullum meson faranta muku,
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sunusi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to Fans
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
🅿️33↪️34
Sosai Ammi ke gyaran d'iyar tata,duk wani abu da yadace tana mata,
Tun lokacin da Zainab taji cewa yaya Lameer mijinta ne,suka dawo wasan 6uya don bata bari su had'u,wata irin kunyarsa takeji sosai,
Shi kuwa d'an anacin,kullum yana cikin gidan inda yadawo daga aiki,sai ta shige d'akin Ammi idan xai bita Ammi ta hana,tace"waiku yaran yanxu meyasa ne baku da kunya,
Sai yasosa keya kawai ya fita aransa yana cewa amma Ammi ai kinsan nayi k'ok'ari shekarun kusan bakwai ina renon matata aikuwa a jinjina mini,
Sosai aka shirya taron tarewa,inda akayi hidima sosai ta 'ya'yan gata,
Daman tuni Lameer ya gama gininsa anjerawa Zainab komai gidan ya had'u iya had'uwa ya tsaru,
Inda a ranar tarewar aka kaita d'akin mijinta kuma Yayanta _LAMEER_
Fad'ar farin cikin da Lameer yake ciki 6ata baki ne,shidai yasan yana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa,yarasa wanne irin sone yakewa k'anwar tasa,
Sosai iyayensu suka had'asu suka masu fad'a nasu xauna lfy sudai sunsan tamkar hanta da jini suke,Zainab bataji komai ba don tasan yayanta zai rik'eta amana hakan yasa ko kukan nan da amare keyi idan za'a kaisu ita batayi ba,
Wata abokiyar wasansu tace"kai Ummi ko kuka babu,tace"to mezanwa kuka nidaza'akai gidan yayana abin sona,nasan zanyi kewar su Ammi amma nasan danace yakaini zai kaini,dariya tasaka tace"ni gaskiya banta6a ganin amarya irinkiba kona k'aryarnan bazakiyiba,murgud'a baki tayi tace"to bazan ba,
Haka aka kaita gidanta,Wajen takwas na dare kowa ya watse itama tashi tayi ta d'auro alwala taxo tayi isha'i tayi shafa'i da wuturi,tana addu'a taji motsin shugowarsa,da sallama,addu'a ta shafa tayi saurin komawa kan gado ta rufe fuska,
Shi abinma dariya yabasa yayi murmushi snn ya ajiye ledar dake hannunsa ya zauna bakin gadon yace"amarya kinsha k'amshi,sake sadda kai k'asa tayi cike da kunya,
Yace baza'a bud'emin fuskar in ganiba ko saina biya,tace"a'a,tare da d'aga mayafinta kanta na k'asa,tafin hannunsa yasa ya d'ago fuskarta yace"Zainab kalleni,d'ago kwayar idanuwanta tayi,suna had'a ido ta sake k'asa da idanuwanta sbd kwarjininsa dayacika mata ido,
Yace"ki kalleni nace,da kyar ta iya kallonsa suka xubawa juna ido,yace"me kika gani cikin idona,turo baki gaba tayi cike da shagwa6a tace"ni banga komai ba,
Jawota yayi jikinsa yana sakin ajiyar zuciya yace"bakiga tsantsar sonki da k'aunarki ba acikin idanuwana,
Tace"nima ai ina k'aunarka yayanah,ajiyar zuciya yayi yace"Zainab tun ranar da aka haifeki nake kaunarki ke bugun numfashi nace ina sonki ina kaunarki Zainab don Allah nima kisoni,
Tace"inasonka yayanah a tun lokacinda na mallaki hankalin kaina nakejinka cikin jini da tsokata,
Murmushi yayi yace"tunda naga kin idar da sallah yanxu kina da alwala kitashi muyi sallah don nuna godiyarmu ga sarki Allah da ya nuna mana wnn babbar ranar,ba musu ta tashi,shima alwala ya d'auro yazo yajasu sallah raka'a biyu,bayan sun idar ya rik'e goshinta ya dunga kwararo mata addu'o'i,daga bisani ya jawo ledar da yashugo da ita,
Fulat ya d'auko da kofina ya dawo ya zuye musu kazar snn ya yago tsoka yace"bud'e bakinki,mak'e kafad'a tayi alamar a'a,ya janyota jikinsa yace wllh kici,ko namiki d'ure,
Turo baki tayi cike da shagwa6a,da sauri kuwa ya chafke bakin yana aika mata wani hut kiss,zaro ido tayi cike da tsoro😳,
Ganin haka yasaki bakin nata,wata irin kunya