Author : Ummu Affan Category : Romance
QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Wannan page sadaukarwa ne ga Hussen Abu Sameer da Nuradden Shu'aib Light,Ina godiya sosai🙏
Masoyana ako da yaushe kuna raina ina yinku irin sosai d'in nan,Masu kirana nagode da soyayyar da kuke min masumin magana da pc kuma nagode sosai,NI DA YAYA LAMEER Fans ina godiya sosai da soyayyar da kuke nunamin nagode🙏
My bestyna Ummu Inteesar marubuciyar 'YAR GANTALI,Inayinki keda Maman khaleel marubuciyar KISHIYAR ZAMANI,i luv u wujiga-wujiga.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
🅿️9↪️10
Malam Halilu,wanda aka fi sani da Malam babba babban malamin addini ne,wanda ke zaune a garin Kaduna,tare da matarsa Gwoggo Abu,asalinsu 'yan jahar katsina ne a wani k'auye me suna,Dukke"dake k'aramar hukumar funtua,
Malam babba karatun addini ne ya kawoshi kaduna inda yazama babban malamin addini na ahlussunna,matarsa Gwoggo Abu duk 'yan gari d'aya ne,
Yara biyu suka haifa duk maza,Ibrahim ne babba sannan Ahmad,sunyi karatun addini sosai haka harna boko,don ba laifi mahaifinsu na k'ok'ari akansu,
Ibrahim babban d'an kasuwa ne wanda yanzun yayi kud'i sunansa ya shahara shi kuwa Ahmad Babban malami ne dake koyarwa a jami'ar kaduna,
Rana d'aya sukayi aure domin Allah ya d'aura musu k'aunar junansu,Hassana da Husaina suka aura,Ibrahim keda Hassana shi kuma Ahmad Husaina,
Babban gida suka gina nakece raini anan suka saka matansu,kuma suna tare da iyayensu,
Shekara guda da auran matar Ibrahim ta hauhu wato Hassana,ta sami d'a namiji zo kuga murna,gsky sunyi farin ciki da samun k'aruwar nan,nan akayi ta murna da farin ciki ranar suna yaro ya amsa _LAMEER_ Yaro kenan d'an gata gurin iyayensa da kakaninsa haka Ahmad da Hussaina suna k'aunar Lameer part d'insu yake wuni,
Tunda aka haifesa ba ak'ara haihuwa a gidanba,ita dai Hussaina ba lbr da yake suna da ilmin addini sai suka mik'a al amuransu gurin sarki Allah suka dage addu'a,
Shekarun Lameer goma amma ba wani lbr shima iyayensa basu kuma haihuwa ba tundaga kanshi,
Makaranta me tsada yake zuwa,tun yana yaro shi d'in mai hazak'a ne baison wasa da karatu,kyakkyawa dashi ga miskilanci da jan aji kamar wata mace ko a class bai cika mgn ba wasu suna masa kallon mai girman kai shidai haka Allah yayisa baison surutu,
Bayan kammala primary yaje secondry,yana SS3 aka haifi Zainab,wato Ummarsa Hussaina ta haihu kamar yarda yake kiranta,Anyi farin ciki da haihuwar nan bama kamar Lameer,tunda aka haifeta yana tare da ita,haka nan yaji Allah ya d'aura masa k'aunar yarinyar,
Ranar suna taci Zainab,sunan Gwoggo sai iyayen ke kiranta Ummi,Lameer yace Zainab Kaka da Malam babba suce Abulle,
Zainab kenan yarinya mai k'iriniya kamar ba haihuwar gari ba,haka Allah ya halicceta sakaryace ta k'arshe,gaba d'aya halayenta irin na k'auyawa ne kuma ita d'in haihuwar gari ce,
Kaka wato Gwoggo tana tsantsar k'aunar jikar tata musamman da taci sunanta,bayan kammala secondry d'in Yaya Lameer yaci gaba da karatunsa a Kaduna university,mahaifinsa a waje yaso yayi karatu amma yace bazai jeba sbd Zainab,
Wacce sukayi sabo sosai,be bari Umma tawa Zainab komai shi ke mata tundaga kan wanka shafa sa kaya tsifar kai komaidai shi ke bata,
Lokacin da Ta isa shiga makaranta akasata,sai tayi ta kuka ita bazata ba,Kaka tace tayi zamanta,sai ta had'u da yaran unguwa ayi ta shirme,
Lameer duk baisan da hakanba kasantuwar karatunsa da yayi masa zafi kunsan karatun likitoci akwai wahala,
Akwai wata budurwa da suke karatu tare,tana mugun sonsa duk wata hanya da tasan zatabi saida tabi har Lameer ya fara kulata,KHAIRAT tana matuk'ar k'aunar Lameer kaiba ma itaba 'yan mata da yawa na kai masa hali Amma shi,baya kulasu,
Haka suke binsa kamarme,duk mkrntr Khairat kawai yake kulawa itama don tazomai a mutuniyar arziki ne da sunan karatu kawai zata dunga koya gurinsa,
Zainab bata son karatu sai yawo gidajen k'awaye abin na damun Babanta yasami yayansa sukai mgnr gurin Gwoggo sukaje suka sanar mata nan ta fara bala'in abar yarinya ta sakata ta wala,
Haka sukaci gaba da hakuri da halin Zainab yau taje gobe bata je ba,
Lkcn da Lameer ya gano abinda ke faruwa nan ya fara takurata,suyi fad'a wataran su shirya,
Yadawo da kansa yake kaita skul ganin hakan sai sam bata mayar da hankali tayi abinda ya dace,
Lameer yana matuk'ar k'aunar Zainab da kansa yasanar da Kakansu Malam babba nan take yace ko bayan ransa abawa Lameer auran Zainab,duk abinda Zainab zatayi Lameer baya ganin laifinta ta fannin mkrnt ne kawai suke samun matsala,
Dukkan mai rai mamaci ne Allah ya amshi rayuwar malam babba sunyi kukan rashi sosai,haka mutane domin malam babba mutumin arziki ne yasami yabo saidai fatan Allah ya kyautata makwanci,Gwoggo tayi kukan rashin miji adali,da haka akayi zaman makoki,
Lameer bayan kammala karatunsa,Abbu ya gina masa babban asibiti aka zuba ma'aikata,shi dakansa yasawa asibitinsa suna LAMZAH wato Lameer da Zainab,
Muje zuwa
Karfa kudamu nasan kun k'osa kuji taya akayi wnn auran nasu karda ku damu zakuji😉😂
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
🅿️11↪️12
Saboda rashin k'ok'arinta yasa aka dungawa Zainab rufitin,sam ko sunanta bata iya rubutawa,hankalin Lameer ya tashi ya dawo da kansa yake mata lessin a gida,ya fadage koya mata amma ta kasa domin haka Allah ya halicceta ita bamai gane karatu bace,
Wataran ya bugeta kai har yadawo suka dena shiri,don baisan rashin mayar da hankalin da batayi,
Da k'yar aka samu aka yarda har ta zana jarabawar fita Primary ganin irin takurar da Lameer kewa Zainab akan karatu yasa ta had'a yaranta ta kalli Alh Ibrahim tace"inaso ku tara mutane ku d'aurawa Lameer da Zainab aure don nagaji da wannan takurar da yakewa jikata,
Muryarshi akaji kamar daga sama dawowarsa asibiti kenan zai shugo yaji maganar da Kaka take,yace"wllh da ma hakan yafi aini nasan yadda zan sata gaba sai tayi ilmi ba abinda zai zaunar damu gidan nan balle kice na rabu da ita,
Iyayensa ruk'e baki sukayi,Abbu yace"Lameer rashin kunyarka har takai nan uwar tamu kake fad'awa haka,Kaka tc"rabu da shak'iyin ai shiyasa nace amasa aure ko ya rage,
Murmushi yayi yace"Abbu afuwan nifa ba rashin kunya nayi ba,Baba yayi mrmsh yace"Yaya kawai amasu auran nan hakan zaifi,girgiza kai yayi yace"shekarun Ummi goma fa taya za'a musu aure yarda yake rawar jikin nan ai sai ya illa yarinya,
Ai gaba d'aya Abbu kunya ya basa da sauri yayi k'asa da kansa ya rasa da wacce zaiyi wani abu Zainab haba shima Abbu da wani zance,
Kaka tc"kaga ni banson jin wata mgn auran nan sai anyisa inaso da raina naga auransu kuma mucika wasiyyar Malam,
Haka suka amsa don yadda sukejin mgnr Gwoggon tasu basason 6acin ranta,sad'af-sad'af Lameer ya fice cike da jin kunyar abinda Abbu yace,yaji frn cikin zai auri k'anwar tasa aransa yasa zai kula da ita sosai sai iyayensu sunyi frn cikin had'in da sukayi,
Biki sosai akayi aka gayyaci 'yan uwa da abokanan arziki,Inda ranar wata asabar dumban jama'a suka shaida auran _Lameer Ibrahim Halilu_ da amaryarsa _Zainab Ahmad Halilu_ anyi biki sosai inda Zainab batasan komai ba itadai sai murna take ana bikin Yaya Lameer d'inta,
Bayan bikin basu tare ba domin saida Abbu ya gama gidin da ya musu part biyu babban gida na nunawa tsara,saidai shima Lameer yana gininsa had'ad'd'e saidai Abbu cewa yayi bazasu tare yanzuba sai Zainab ta mallaki hankalin kanta inda yace su tare nan gidansa da yamusu,
Lameer baiji komai ba haka suka tare inda aka shiryawa Zainab part d'inta sak na amare,saika rantse wata k'ayuwar mata ce za'a kawo,
Khairat ta kalli Lameer wacce ke zaune kujerar dake fuskantarsa a office nasa,mrmsh tayi tace"bazan 6oye maka ba Lameer na dad'e ina k'aunarka ganin lkcn karatu muke yasa nak'i sanar maka,
Shima mrmshn yayi yace"Khairat kenan kuma gashi kin makaro dumin a satin nan aka d'auramin aure,da sauri ta mik'e "aure kuma Lameer waka aura?,"wacce nakeso,ya bata amsa,
Ckn fusata tc"yayi kyau amma inason kasani ni Khairat ban ta6a neman abu na rasaba kuma kaima banajin zan rasaka ta halin k'ak'a sai na aureka,
Wani shu'umin mrmsh yai yace"Inaso daga kaina ki gane ba komai mutum ke nema yasamu ba,muzuba mugani,
Wani kallo ta masa kafin ta fita a matuk'ar fusata,
Da farko Part d'in su Ammi Zainab take kwana,daga baya kuma ta dawo gurin Lameer domin idan Ammi tasa ta kawo masa abinci sai ya rik'eta da hira har tayi barci don saurin barci gareta,tun Ammi na zuwa ta tafi da ita har ta gaji da wnn abu na 'ya'yan zamani😜,
Amma sosai suka sa masu ido don kar ya illata yarinya shekara goma meta isa,da sukaga rawar kan nasa yayi yawa Abbu da Ammi suka zaunar dashi akan karya kuskura wani abu ya had'asa da Zainab,shi wllh kunyama suka basa yace"wai Abbu me yasa kuke tada hankali haka ni ba abunda zan mata,nan dai sukaja kunnansa(ni kuwa nace kai Abbu shida matarsa😉loll)
Haka shuk'uwa me yawa taci gaba da wakana tsakaninsu,inda dakansa yake mata lessin,harta fara gane wasu abubuwan snn ya kaita junior secondry school,
To ko'acen ba wani maida hnkl take ba,sai shegen surutu da k'awaye,malamai har kawowa Lameer k'ara suke akan tsokanar mutane da take a skul har malamai bata 'yaleba,
Yayi mata fad'an har nasiha da rarrashi amma Zainab bataji,
Khairat ce gaban iyayenta tana zuba shagwa6a ckn kuka tace"dad an mum idan har baku yi yarda kukayi na auri Lameer ba wllh guduwa zanyi,nan takefa hankalinsu ya tashi suka fara lallashinta Dad yc"ki kwantar da hnklnki 'yata shiko d'an gidan uban waye sai ya aureki,Mum tace"duk yarda zanyi zan samo miki farin cikinki 'yata ba wani abu a duniya da zakiso ya gagaremu ki kwantar da hnklnki...
Tofa fans kunji wata sabuwa wai inji 'yan chacha,muje zuwa😂
Wanna littafin ya koma na kud'i duk wacce ko wanda hakan baiwa dad'i ba ina bai basu hak'uri wasu ke jawa wasu ga duk wanda/wacce ke son saya zata iya Transfer ta wannan acc d'in,Talatu Amadu Zaria 30719716460 First bank,ko katin layin MTN ta wnn number 08104335144 akan 200 kachal 👌
Kar ku mance duk wacce ta turo ta sanarmin ta wannan number dake sama👆ta fatan wanda yaji haushi zaiyi hak'uri🙏
Ummu Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
GAJERAN LABARI
Story and written
By
Fateemah Sununi Rabee'u
(Ummu Affan)
________________________
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com
MARUBUCIYAR ✍🏽✍🏽
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
And now👇
NI DA YAYA LAMEER!
WhatsAPP no 08104335144
Diditated to ATK
Special gift to Anty Hauwa
Fans kuyi hak'ur da abinda ya faru,Wannan littafi ya koma na kud'i ga duk wacce/wanda zai iya saya zaya turo 200 kachal ta wnn acc Talatu Amadu Zaria 30719716460 First Bank ko katin layin MTN ta wnn number 08104335144 karku mance kuturo min alama idan kuntura duk ta wnn number👆domin nasaka ku sabon group d'in wnn book idan ma baki karanta ba zan turo miki tundaga farko,
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
🅿️13↪️14
Tashi tayi a juciye kamar ba iyayenta ba ta nufi bedroom nata,su kuwa duk sukabi suka damu,Dad ya kalli Mum yace"wai Hjy wanne yaro ne take mgn,numfashi taja tace"wani yaro ne dasukayi karatu tare tun lokacin take sanar mini nayi zaton yadda take kyakkyawar nan shi dakansa zaice yana sonta amma tunda ta furta masa ya watsa mata k'asa a ido zaisha mamaki bai san wacece Hjy Sa'a ba jina yake,
Cikin fushi Dad yace"uban waye ubansa a k'asar nan da har zai 6atawa 'yata rai wllh tallahi na rantse sai naci mutim cinsa sai ya gane ya ta6o d'iyar Alh Kamalu yasan waye ni kuwa a garin nan da k'asar nan to wllh ya ta6owa kansa,
Tashi yayi kamar zai tashi sama ya sa6a malin malin d'insa yayi gaba bedroom d'in Khairat ya nufa,
Zaune ya isketa tana kumburi idanuwan nan nata k'ek'ashe,kwalaben syrup me zube da alama su tasha don rage zafi,idanuwanta jawul sosai,
Zama yayi tare da kamo hannuwanta,da sauri ta fuzge tace"ba abunda zakamin na saurareka idan ba soyayyar Lameer zaka samomin ba,
Cikin sanyin murya kamar shine d'iyar ita uban yace"kiyi hakuri 'yata wllh nayi alkawari saikin auri wnn yaron badai kina sonsa ba gyad'a kai nayi alamar eh,
Yace"to ni mahaifinki Alh Kamalu nayi alkawari ko ta halin k'ak'a saikin auresa baisan waye niba,
Mik'ewa yayi waje yana banbami,ita kuwa nan take barci ya kwasheta sbd shaye-shayen da tayi,
***************
6angarensu Lameer yana k'ok'ari sosai ganin Zainab ta sami karatu amma a banza,
Suna skul zazzaune akan kujerun mkrnt,wani malaminsu mai d'aukarsu darasin English ya shugo,bayansu gaishesa kowa ya koma gurin zamansa,sai kawai Zainab ta tun tsire da dariya,malamin ya tambayeta"meke damunki,
Sake sakin dariya tayi tace"chafd'ijan to ai kaine kabani dariya malam tab lallai,ta sake sakin dry,
Ran malamin ya 6aci yace"fito nan yau zaki gane kuranki wllh,ko d'ar babu taxo gabansa tace"gani,kuma bata dena dryr ba,
Yace"baki da hankali ne,tace"da hankalina wllh kawai dai hhhhhhhh,sai ta kuma nunasa tana dariya,
Sosai malamin ya k'ule yace"ko kifad'amin abinda ke baki dry ajikina ko yanzun in zaneki,harararsa tayi tace"chaf wllh da anyi 'yar zane zane Yayana bazai barka ba,kai ni jad'ai na isheka,tasake sa dariya tana nunasa,
Hakan nan malamin yaji tsoro yakamasa aransa yace"anya kuwa yarinyar nan bata da aljanu,yace"fad'i abinda ke baki dry,cikin shashanci irin nata tc"yo naga kayi wata irin shigane kamar wani Bakano(😜Lol )
Taci gaba dacewa"kai kullum baka iya gayuba sai kawani shugo kana jijidakai kamar wani had'ad'd'e nidai Yaya Lameer ba haka yake ba,
Aiji yayi kamar ya maketa sbd takaici,jan hannunta yayi har waje ya wanchakar yace"shashashar banza wllh yau sai jikinki ya fad'a miki bugun tsiya zamu had'u da sauran malamai mu muki,
Dariya tayi tare da masa gwalo😜d'aga bulala zaiyi yadaketa ai tuni tawani chukukuye bulalar ta fara tsalle tsalle,nan fa ta burkice masa da sauri yayi baya cike da tsoro tace"wllh idan kasanar aka dakeni a mkrntr nan da daddare sai nazo maka a fatarwa,shuru yayi yana kallonta,murmushin mugunta tayi aranta tana cewa k'azami kawai nasan maganinka,
Dole malamin ya rabu da ita don yaga shak'i yancinta yakai intaha,
Da yamma wajen shidda ya Lameer yazo d'aukarta da yake mkrntr boko da islamiyya ce,tun a moto take dry tana rik'e ciki,mrmsh yayi yace"kai Zainab me yabaki dry hk,
Nan ta zak'e tana bashi lbr ta k'arashe dacewa"shi kullum malamin nan hk yake shugowa yayi ta wani iyayi shi ba kyauba wllh Yaya Lameer ko kwatarka bai kai ba,
D'aure fuska yayi har suuka kai gida,ganin hk duk jikinta yayi sanyi ta bisa tana cewa "yaya Lameer ya'akayi ne,
Zauna wa yayi kan kujera tare da tafe kansa,jikinsa ta fad'a tace"Yayanah kayi hkr bansan zan 6ata maka raiba,yace"haba Zainab malaminki fa kikawa hk wnn wanne irin abu ne,
Tace"don Allah to kayi hkr bazan sake ba,ja mata kumatu yayi,ya mik'e binsa tayi "Yayanah bakayi dariya bafa,d'agata sama yayi ya juya,ta k'amk'amesa gaba daya sukayi dry,
Bayan tayi wanka suka nufi part d'in Ammi cin abinci,
Jikinsa ta zauna tace "nidai Yaya Lameer a baki zaka bani,yace"baki da damuwa,nan ya zubo musu suka dawo kan carpet sunaci da chokali guda idan yabata tabasa,
Ammi ce ta fito,harara ta bankamasa shidai mrmsh yayi,haka rayuwa taci gaba da tafiya har Zainab tashiga JSS2 ikon Allah ya kaita ba k'ok'arinta ba shi Yaya Lameer cewa yayi abarta JSS1 Malaman sukace tunda dai sunanta yafito abarta taci gaba,
Wannan kenan,cigaba,
Wajen shidda na yamma Lameer ya gama aikinsa ya tattara kayansa cikin jakar office d'insa,
Fitowa yayi yana karkad'a key d'in motarsa cikin takun k'asaita irin tasa,
Zai bud'e mota kenan yaji mgn daga bayansa,bai juyo ba saida ta k'araso,Khairat ce wani mugun kallo ya mata'murmushi tayi"my Lameer an tashi kenan,
Yace"Khairat meye matsalarki da nine?nace kinada xuwa hospital d'in nan meyasa bakiji,
Uhmmm taja numfashi tare da shek'ewa dariya irin ta 'yan duniyar nan tace"Lameer kenan bazan ta6a dena bibiyarka ba har sai ranar da kazama nawa ni d'aya,Kallon tsana ya mata yace"magana dake sai yabani ciwon kai,
Shigewa motarsa yayi ya mata key,da sauri ta shiga tata tabi bayansa,mkrntrsu Zainab ya nufa bayan ya d'auko ta suka fito,kallonsa tayi"Yaya Lameer yau kajima saida aka gama d'aukar k'awayena kazo,yace"sorry my wife inata sauri nazo,
Bakin mkrntr Khairat tayi parking tazo gurin me gadi tace"waccar motar da tafita me motar gurin wa yazo?yace"ai yazo d'aukar k'anwarsa ne,
Komawa mota tayi tare dayin mrmsh tace"tabbas Lameer matarsa yaxo d'auka,ni kuma zan baka mamaki daga gobe karasata har abada......
Shin ya abun nan zai kasance?
Lameer da gaske zai rasa Zainab ko yaya?
Batun rashin son karatu na Zainab shin haka zatayi ta zama ba ilmi koya?
Zainab zatacenza hali koya?
Idan taji Yayah Lameer d'inta mijinta ne yazata kasance?
Khairat kuwa fa?
Wai wacece ma ita suwaye iyayenta
Shin komai ne kakeso arayuwarka kake samu?
Iyayenta zasu samo mata soyayyar Lameer koya?
Meye makomar soyayyar Lameer da Zainab?akwaifa kalo gaba,
Duk wnn amsoshin sai kun biyo Ummu Affan akan 200 kachal 👌
Anan na kawo k'arshen Free page,ga duk wacce ko wanda ke buk'atar saya za'iy transfer ta wnn acc,Talatu Amadu Zaria 30719716460 First bank,ko katin layin MTN ta wnn number 08104335144
snn ku turomin shaida idan kuntura duk ta wnn number dake sama👆ni kuma sai insaku sabun group,sai najiku,
Inayinku irin sosai d'in nan masoyana zan k'aramuku yawan page,sai mun had'e😂✍️
UMMU Affan✍️✍️✍️
❤❤❤❤
🧡🧡🧡💓
*NI DA YAYA LAMEER*
❤❤❤❤