Waleed bai bada sanarwanta ba sabida karyazo koma waye yaso kasheta yadawo ya kasheta, kasa dena kuka tayi ahankali Ammi tace "kinsan waye keson kasheki, me kika tuna last na past life dinki"? Cikin wani irin muryan kuka tace "abinda natuna?" gyadamata kai Ammi tayi, shiru tayi kaman mai tunani sanan tace "ranan aurena da Ahmad komi yafaru" ba Waleed kadaiba kowa nadakin saida gabanshi ya Yanke yafadi, tacigaba. "Allah kadai yasan wani hali mijina yake ciki, kunce nayi morethan a year tareda ku anan, omg Ahmad, Aby da Amah must be super worried" tai maganan ahankali tana fashewa dawani irin kuka, Ammi bata hanata ba dan itama yanzu kukan takeso tama danta jin Widad nada miji wanan wani irin tashin hankali ne, takai kusan 5min tana kuka sanan tai shiru tace "sunana Widad Bint Othman Benjelloun, ni haifaffiyar yar Morroco ce, iyayena komi nawa daga chan ne, ina karatun mass com a Egypt ina shekarata na biyu agarin nema na iya wanan yaren nasaran dakukaji ina muku magana dashi, Mahaifiyata tarasu" taidan shiru tareda share hawayen dasuka zubomata sanan tace "cancer yakasheta, ni kadai mahaifina ya haifa step Mom dina Umm bata sona, ranan aurena bansan maiya faruba nadai farka naganni cikin wani jirgin awani daji......." nan tabasu duka labarin abinda yafaru sanan tace "yanzu I need to see Aby ku kaini wajenshi I need to tell him abinda Umm tamin karshima ta kasheshi sabida Umm is just after dukiyan Aby, please ku kaini gida yanzu" shiru Ammi tayisanan tanisa tace "Widad muba yan kasar morroco bane, koda yanzu zamuje garin dole muyi yan shirye shiryen takardun shiga kasar, bankuma son ki kira mahaifinki matarnan zata iyaji tayi wani mummunan abu in taji kina raye, gwara muje abazata saidai kawai ta ganmu, yanzu kiyi hakuri kibamu nanda kwana biyu zuwa uku muyi yan takardu sanan saimu dunguma mu maidake gidanku kinji" ahankali tace "to mijina fa shina kirashi Ahmad can keep secret inaso hankalinshi ya kwanta" wani irin tari Waleed ya shigayi da sauri Ammi ta tashi dagakan kujeran daga ita harsu Mom sukai kanshi, tari yake sosai Ammi batasan lokacin data saki salati ba. "Innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, kai Waleed sha ruwa" aka kai ruwan da Abdul yadauko bakinshi amman kaman bashi ake bamawa ba sumewa kayi yayi warwas ya sandare awajen, haukane kawai Ammi batayiba da sauri Mom tarike Ammi tace "Adda ki kwantar da hankalinki dan Allah" cikin wani irin yanayi na kaman wacce ta zare Ammi tace "wlh in Waleed yarasa yarinyar nan mutuwa zaiyi mutuwa zaiyi" kallon Abdul Mom tayi tace "daukeshi mukai mota" ta kalli Ammi tace "ke ki zauna da ita kinsan itamaba lfy gareta ba, ki kira Babanshi(Uncle) yazo asan me ake ciki, Asma'u zauna dasu kema" gyadamata kai tayi suka dauki Waleed itada Abdul sukafitada shi sai mota Widad na binsu da kallo tana zaune inda take dan ba gane hausar dasukeyi takeba, zama Ammi tayi ta kalli Asma'u tace "kawomin wayata Ma'u" wayar Ma'u takawo tabama Ammi kira daya Uncle yadauka Ammi ta shiga sanar dashi abinda ke faruwa, shi yamafi Ammi rudewa da sauri yace kwantar da hankalin ki gani nan zuwa, am leaving office yanzun nan duk jirgin danasamu binshi zanyi ya katse wayan ya tashi xumbur.
Itama Widad din zazzabi ne yarufeta tadinga amai da kyar Ammi da Asma'u suka samu bacci ya Kwasheta bayan tasha magungunan ta, Mom takirasu tacema Ammi jikin Waleed da sauki dukdan hankalinta ya kwanta nanko har lokacin bai farfado ba.
Ahankali Waleed ke bude idanunshi dasukamai nauyi sama sama yaji ana kiran sunanshi "Waleed, Son, Son an you hear me" karasa bude idanunshi tass yayi ya saukesu kan Uncle dake zaune yana sanye da kayan wajen aiki, Waleed na ganinshi ya zabura zai tashi Uncle ya taimaka mai yazauna, Uncle yace "why will you kill yourself kan mace eh? Zuciyarka fa chak tsayawa tayi ta dena bugawa dasu Mom dinka basu kawoka asibiti dawuri ba daka mutu, listen boy ko yarinyar nan nada aure namaka alkawari saitadawo taka, sai inda karfina yakare wlh, ina mahaifinka inhar ban iya nabaka abinda kakeso ba after all you've went through Waleed in this life yaudaran mata da aboki me amfanina? Are you ready cus we are flying to morroco yau dinan da daddare" hannun Uncle yarike ahankali murya chan kasa kaman wani dan yaro yace "Uncle am scared, I've never been scared in my life like this, am afraid of losing the love of my life, banso muje morroco Uncle let's just go back to Nigeria zata hakura tazauna dani, in mukaje morroco shikenan narasata har abada wlh Uncle zan mutu, Dad I, I, I love Saheeba beyond much" sosai Uncle yaji jikinshi yamai sanyi, kamashi yayi ya sumbaci goshinshi yace "inhar ina tare dakai aduniyan nan don't ever be scared or afraid of anything, do you trust me Waleed?" gyadama Uncle kai yayi, ahankali Uncle yace "inhar you trust me then trust in me idan nace babu wanda ya isa yarabaka da matarka aduniyan nan kosu wayesu, let's so, duk su Mom nakadasu gida, stand up" daga Waleed din yayi yarikoshi suka fito dan already yariga yay clearing all bills sanan ya shigar dashi mota yaja motar har gida, lokacin yamma tayi, har dakinsu yakaishi yazauna yajirashi yay wanka sanan yafito mishi da kaya masu kyau ya saka ya feshe shi da turare sanan yajawo box dinshi yabude ganin marriage certificate dinsu aciki yasa hankalinshi ya kwanta ya shirya musu komi sanan yafito yasashi a kota dansu Mom na airport already, airport suka tafi private jet yamusu booking yana zuwa akai komi jirginsu yatashi sai satan kallon Widad yake da tunda yashigo jirgin daidai daso daya bata dago kanta ta kallai ba dudda taji anata gaisheahi ana mai yajiki, yanda gabanshi ke faduwa yasa Uncle yashafa kanshi yace "calm down, inhar yarinyar nan tasoka da yanzu ma zata soka it will only take time, what goes around comes around remember this" gyadama Uncle kai yayi haka uncle yadinga kwantar mai da hankali har jirginsu yasauka a airport din morroco karfe shidan safe.
Uncle yariga yay handling accommodation dinsu dan babban gida ya kama musu a casablanca yanaso su dira gidan as manyan mutane dan ba raini, ana kiramai sunan mahaifin Widad din yasanshi dan shi yana dealing da manyan mutane a business, gidan suka fara zuwa dudda saida Widad tadinga musu kukan bala'i amman duk aka shareta, abinci akaci itama taci, sanan kowa yashiga wanka akayo shiga ta alfarma, Waleed baiso ya shirya amman saida Uncle yasa ya shirya cikin wasu fitinannun native na gizna white, ance duk inda zaka represent your culture, hausawa suka taimaki yarsu, sanan hausawa suka auri yarsu dan haka a hausawan su zasu shiga gidan larabawan wanan ake kira da TWO DIFFERENT WORLD wato DUNIYA MABANBANTA wanda ayau zasu hadu, shima Uncle sky-blue shadda yasaka yakafa hula, yadaura rolex agogo kaman yanda Waleed ma ya daura, Abdul ma haka, Ammi da Mom sukai shiga ta lace da zinarai daya bala'in amsansu, itakuma Asma'u ta shirya cikin atampa riga da sket ma codivore dayay mata kyau, ita kanta Widad dataki tai gayu binsu kawai da kallo take bata taba ganin wanan irin shigan ba amman sun mata kyau sosai dan is obvious takasa dena kallonsu duka, motocin da Uncle yamusu haya na company gidan dasuka kamane jeeps guda uku bakake suka iso, fita duk sukayi suka shiga motar da Widad keciki ne agaba danta nuna hanya aka dauki hanyar Mansion din gidan Othman Benjelloun.
Ina masu neman turare exotic ones, masu mugayen dadi, masu kama daki, masu dadi, da armashi, long lasting turaren gargajiya gashi sanyi yazo, Awwaba Scent got you covered, kayanta akwai sauki, tana delivery ko'ina, me kuka jira ne wai? ππΌππΌππΌππΌ Just chat her up kuga abun mamaki ga number tanan https://wa.me/+2348034236800
[11/27, 9:56 PM] saleemah: π« _TWO DIFFERENT WORLD_ π«
βοΈ M SHAKUR
7οΈβ£0οΈβ£
Kasa koda motsi Widad tayi dagakan gadon, jitayi kaman yadauke duka mugun zazzabin dayake cinta tunda tazo gidan, babu abinda ke mata ciwo yanzu sai jikinta dataji yamata mugun tsami, hannu tasa ta share hawayen da suka zubomata yanzun shikenan she's this man's wife not Ahmad, jiba yanda yay having dinta in her father's house, takai kusan minti 20 kuka take akan gadon, da kyar ta lallaba ta tashi zaune, lallabawa tayi da rarrafe ta shiga bayi da ruwa mai zafin gaske tai wanka sanan taji wani irin karfi tadauro wani towel batare data kalli pink dinta daya daura dazuba tafito zanin gadon dasuka bata tacire takai bayi ta saka a washing machine tadawo tafito dawani ta shimfida ta tattare ko'ina da kyar ta iya tanemo wani simple gown tasaka sanan tadawo ta kwanta akan gadon, kamshin turaren shi datake mugun sone taji yana shiga hancinta juye juye ta shigayi kafin tagano daga filon daya daura kanshi ne takejin kamshin taja ta rungume tsamtsam ajikinta tana tunani, lumshe ido tayi tana ganin image dinta dashi suna dariya tana rungume shi duk a Nigeria, yatsine fuska tayi tacigaba da tunanin ahaka bacci yay awon gaba da ita, har dare yayi Aby dashi kanshi baya iya bacci in baizo yadubata ba yau kasa zuwa yayi hakama Amah haka kowa yay bacci ita takasa zuwa wajen su suma haka, washe gari ma haka tawuni adaki tana rungume da filon Waleed tana shakan kamshin shi deep down haka takeji kaman yazo yauma tasake ganinshi, tana zaune taji Ahmad yazo amman still takasa fita taganshi wasa wasa yau kwana uku kenan batabar dakin nanba.
Tana zaune yauma kaman kullum akai knocking kofar dakin, anatse yay magana yace "is Ahmad, I come to talk to you" hakanan taji gabanta yafadi, hakanan kuma taji ta tuna kashaidin da Waleed yamata kan Ahmad ranan nan, kasa magana tayi tai shiru kaman batajishi ba, jin an murza hannun kofa yasa ta tashi da sauri zatai bayi daidai Ahmad ya shigo dakin, murya chan kasa yace "Widad" chak ta tsaya batare data juyoba, ahankali yace "you don't have to go to the toilet ki boye dan kawai bakison ki ganni, today is the fourth day nake zuwa nai knocking kimin shiru kiki amsani I simply come to talk kidawo ki zauna akan gadon ki please" yanda taji muryanshi yay rauni yasa tajuyo ta kalleshi gyadamata kai yayi yanuna mata kan gadon, dawowa tayi ahankali ta zauna kan gadon shikuma yaja kujeran gaban madubin kwalliyanta yazauna agaban gadon yana facing dinta.
Anatse yafara magana yace "Widad me and you have come a very very long way, tunba yauba kinsha fadi cewa no one understands you better than I do, kinsha fadi da bakinki cewan kafinma ki furta abu nakan fahimci abinda kikeso kafinma kifadi kintuna"? yaymaganan yana murmushi, gyadamai kai tayi ahankali, dan ajiyan zuciya yasauke yace "na zauna nai tunani mai tsawo, sanan na azumimci ranaku uku duk akanki ina rokon Allah should guide me to the right path which I believe shine abinda yayi dahar yasa nasami courage nazoma da iyayenki da maganan nan kafin ma nazo miki nan da ita" yasakeyin shiru sanan yace "after all this long journey Widad I come to understand wanan mugun son danake miki ba kowace irin so bace face so so kaman irin na wa da kanwarshi, I care about you Widad, I go for anything that will make you happy, bayan kin bace haukacewa ne kawai banyiba babu inda bamusa hoton ki ba, but for once in my life Widad nai tunani ba akaina dakanki kadai ba, for the first time in my life nai tunani akaina, akanki dakuma akan abinda kike dauke dashi acikin cikin ki" yasake yin shiru sanan yace "Widad da ace ni dinan dakike gani ba'a gidan mahaifina nataso ba bazan tabayin farin cikin dazanji irinshi agidan asalin mahaifina ba, kowani d'a dakika gani aduniyan nan burinshi shine yataso cikin so dakuma gatan iyayenshi, daga lokacin da mace ta dauki juna biyu a lokacin ne zata dena tunanin kanta kanta ita kadai, alokacin ne zatafara tunanin what's best for her and her child, our parents sacrifice alot for us, mata nawane ke zama da mazajan da basuso badan komiba saidan kawai yayansu ballema wanan da deep down kinasan ubanshi Widad, u just needs to find where wanan son uban nashi yake azuciyanki, kwanakin baya danazo naganku tare I saw how u looked at his father and I see nothing but pure love in your eyes" yay maganan ahankali kaman abin namai ciwo, yakai kusan 5min yay shiru sanan ya nisa yacigaba. "just to be sure nasamu natsuwa cewan kina hannun wayanda zasu kula dake yasa I made a research akan family mijinki nagano wayesu, your husband is a goodman a humanitarian, an activist, a Dr and many many more , yesterday I had a one on one chat da mijinki Widad I must admit cewa yaron nan na sonki and trust me idan nace TWO DIFFERENT WORLD means shit inhar Love din is real, komi dakika gani mukaddari ne da ace guy dinan ba mijinki bane da babu abinda zai kaiki Nigeria da bamu da yan uwa ko guda achan, kowani musulmi dolene yay imani da Allah dakuma rana ta karshe, sanan ya yarda da kaddara, koma meyafaru tsakanina dake kaddara ne, take me as your brother wanda kuma ya isa dake Widad ayau ina gayamiki cewa nida kaina without anyone forced me that na janye duk wata kalman soyayya dana taba fada miki ada, na janyeta nahakura, nadauke ki amatsayin sister na, and inhar kin daukeni amatsayin yayanki wanda yakuma isa dake abu daya zangaya miki shine kibi mijinki sauda kafa domin ko yana sonki sosai, go and build your marital home, go and build your family Widad I wish you all the best in this life kinji" yay murmushi yana hana kanshi kuka ganin yanda take kuka sosai, ahankali yace "tashi muje tun dazu Aby yakira family mijinki duk suna falo kibisu kutafi, sunce Qatar zaku koma bayan kungama vacation saiku koma Nigeria ko, don't cry let's go" bude kofa yayi yafita da ita, a falo tagansu duka sai kallonta suke banda Waleed da kanshi ke kasa yanada mugun kishi saisa baimason yadaura idanunshi akanta da Ahmad dasuke fitowa tare, tana zuwa tafada jikin Aby tana kuka sosai, hadasu Aby yayi yamusu wa'axi sosai mai ratsa jiki, sanan agaban kowa ya kwaso paper's na kamfamonin shi yasa tai signing dudda za'a dinga yimata managing, hana kowa tafiya Aby yayi yace sai yahada musu gagaruman liyafa wanda za'ayi gobe sanan zasubar garin, dakanshi yakaisu wani hadadden bangare agidan itakuma Amah ta tafi da Widad shashinta tun dare takira masu gyara, ranan yan aiki basuyi barci ba aka shiga decorating.
Da safe wuraren 9, designers Aby yatura side din su Ammi, aka dauki measurement din kowa sanan aka kawoma kowannensu Morrocan dress, wuraren 11 aka fara ceremony din, aka fitoda Widad da Waleed yakasa daina kallonta, dauke kai tayi daga kallonshi ita adole fushi take dashi ta ballamai harara sanan tashiga cikin masu rawan larabawa, Waleed was blown away dayaga tana rawa, subhanallah bura'uba baitaba ganin yarinyar data iya rawa irinta ba, she looks so happy adorable and charming suna hada ido zata ballamai harara, haka har wuraren 4 Aby yasa aka shirya musu tsaraba dan Uncle yasanar dasu cewa jirginsu 6 ne, Aby da Amah har Airport suka rakasu, aiko Widad tasha kuka kafin tarabu dasu.
Nigeria
Asibiti
Case din Arham saida akai documenting nashi ababbban littafin da'ake recording incidence na bura, kwanan shi bakwai chur aka sallame shi daga asibitin bayan yayi clearing duka bill din dayacimai kudi sosai, bai wani damuba tunda yasamu andike fess yana iya fitsari, gabaki daya, adaidaita yatare for the first time tun bayan yaje gaisuwan Mama bayan tarasu saiyau kawai yaji yanaso yaje gidan mahaifiyar shi, keke yatare ya shiga yana tafiya yana dingishi har zuwa gidan, gani yayi an kulle gate din da makulli baida key hakan yasa yadau dutse ya balle key din ya shiga cikin gidan yana kallon ko'ina ga motar Mama da Waleed yasaimata apake a kasan tent, ahankali yake tafiya har zuwa gaban flat dinsu balla key shima yayi sanan yabude kofar, chak ya tsaya abakin kofa yana kallon falon yaga kanan zaiga Mama akan kujeran dayake yawan dawowa daga aiki yaganta, ahankali ya shiga cikin dakin zama yayi akan kujeran dayay kura sosai baima damuba yana kallon kujeran da Mama kezama kai yana ganin kaman ita ya kegani zaune tana kallonshi, yakai kusan 5min ahaka saiga hawaye ahankali ya zilalo mai murya chan kasa yace "Mama dan Allah kiyafemin, nasan sabida kin rasu da fushina a zuciyan ki saisa komi yafara juyamin up side down" shiru yayi yasa hannu ya share hawayen da suka zubomai murya chan kasa yace "Mama wani yakusan yankemin gaba, Mama Alhakin kine kona Waleed suke bina"? Ya tambayi kanshi kafin ahankali yace "Mama I feel so empty, na kwacema Waleed gidan marayun shi, yanzu haka baida gidan marayu, na kwacemai mata ta haifamin yaro ba mijinta ba yanzu tana dauke dana biyu, Mama inada katon gidan marayu, inada mota lambo kaman ta Waleed Tawa baka, Mama inada yara kananu masu danyen jini harsu takwas danake amfani dasu dukdan nafi Waleed jin dadin duniya suma sunada yet Mama am still not full am not satisfy, nothing seems to satisfy me, Mama pl......" bai karasa magana yaji anyi knocking kofar falon tareda shigowa duka at a spot, polisawa yagani guda biyar hade da government officials, babban cikinsu ne dake sanye da suit yay murmushi yace "good Day Mr Arham, yau kwana uku kenan muna nemanka aduk inda mukasan zamu sameka but bamu sameka ba sai yanzun nan informant din damuka ijiye awanan anguwan suka sanar damu sunga shigowanka anguwan ka shiga gida" wani irin gyada musu kai yayi gabanshi nafaduwa, mutumin yace "office dinka yakama da wuta an nemeka an rasa har saida aka