Duniya Biyu Mabanbanta Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  M Shakur Category :  Love

Chapter   23 / 48

66K to 69K   out of 142.7K words

Kasa saka jacket dinma Waleed yayi sabida ihun Arham dayake mai a kunne kaman zai fasamai dodon kunne yamaida jacket din yarike a hannu sanan ya kalli Arham yace "since you are too dumb to understand a simple question dana tambayeka then take it anyhow you wish to take it" yana gama maganan yadau wayanshi daga kan table zai juya yay kofan fita Arham yasha gabanshi yace "ni kakema gori"? cikeda mugun bacin rai da kulewa da maganar Waleed yace "nayi, kai duk abinda kaga dama" kaman amafarki Arham bai wata wata ba ya daurama Waleed wata lafiyayyen mari ata gefen ido dan marin har yadan taba idanunshi na side din dama jikake kau! Idan Waleed yace he was expecting a slap from Arham he is lying, jin saukan mari yayi kawai daga sama baisan lokacin daya saki wayanshi da jacket din dake hannunshi akasa ba suka fadi, wani irin fincikanshi Arham yayi ya bugada bango bayanshi yabada bam, Arham ya shakemai wuya, cikin kunfan baki da mugun tsana yace "sabida rashi da talauci yasa am working under you, yaro dakai u are just 28 inada 35yrs na girmeka da shekaru shidda zaka tsaya kana gayamin magana yanda kaso, daman hausawa sunce yaro da kudi babba yake dawowa, this can not work with me, yau saina koyama hankali, I will teach you a lesson, fight me back now, fight me back" har alokacin Waleed was shocked yama kasa yarda Arham dinshi ke fada dashi haka, ya shakeshi yana neman kashe shi idanunshi sunyi jajir jijiyoyin kanshi sun fito, fuakanshi tai jajir abunku da farin mutum, ahankali ya iya yataba hannun Arham dake wuyanshi muryanshi bata fita sosai yace "u.....are....hurt.....ing me blood.....am....am.....my....my.....breath" yay maganan about to die amman Arham baida alamun sakinshi saima kara shakeshi dayayi yace "I said fight me, fight me mana, I want you to fight me dan Allah inka isa, kai fada dani kaga yanda zan baka kashi, na farfashe maka wanan bakin dakake min gori dashi kan kasayama Mahaifiyata wanan shegen tsukukun gidan kaman gidan kiwon kyankyasai, da shegiyar akurkan motar nan, inda don Allah kakeyi da tikeken gida zaka saya mata irin naku mansion, mota mai numfashi bata manoma ba, yau saina nuna maka kudin ka bazai iya taimakonka a hannunna ba, I will deal with you yau Waleed, wlh saikai fada dani zan kyaleka na rantse maka" daidai lokacin akai knocking kofar office dinshi, sake shakeshi yayi to the extend this time idanunshi sun soma juyawa gashi yakimai komi dan he can't raise his hand on his friend or hurt him in anyway ba, da kyar hannunshi ya iya komawa baya dashi yatataba flower verse din dake kan table dinshi ya kabar dashi kasa yay kara akasa sabida wanda ke waje ke knocking kofarshi yaji ya shigo, jin karan flower verse yasa Mama Iyami tace "subhallahi karan menene wanan" ta murza handle din kofan kawai ta shigo ciki, ganin yanda Arham ya shake Waleed yasa da sauri tai kansu yace "Mr Arham innalillahi wa innailaihi raji'un, wats happening here? Meke faruwa haka? Kaida abokin ka, let him go, sakkashi kaga" ta shiga kokarin fincike hannun Arham daga wuyan Waleed, cikin fushi Arham yace "wlh bazan sakeshi ba saiyay fada dani, sainaga uban karfin dayike dashi dayake juyani yanda yakeso sabida yaga yanada kudi dan ubanshi" ganin yanda Arham ya harzuka Waleed na neman mutuwa a hannunshi yasa tafita daga office din da gudu ta kurma uban ihu. "jama'a kuzo kutaima keni, Dr Waleed Warbai and Mr Arham are fighting, please helppppp" ihunta gabaki daya yadauki gidan marayun, da gudu wasu staff din Waleed da yaran gidan marayun damasu shara, gardeners da waye da waye aka shigo office dinshi da gudu, Nura dawasu maza hudune suka fizge Arham, suka jashi baya Waleed kuma yay baya zai zube wasu ma'aikatan suka tareshi, da gudu Iyami tafashe da kuka tace "innalillahi is sir alive jama'a?" wani ma'aikaci ne mai suna Auwal yace "he's alive but sai ankaishi asibiti" da sauri suka fita dashi daga office din, Mama Iyami tajuya ta kalli Arham dake huci yana tsaye ya fizge kanshi daga rikon da akamai tace "Mr Arham meya hadaka fada da abokin ka eh, dan uwanka fa, blood naji kuna kiran junanku, Mr Arham meya hadaku dashi" cikin wani irin fushi Arham yace "kije ki tambaye shi mana, dayake shi ogan kine bazaki iyaba shine yabaki aiki, yana baki na abinci bazaki iya tambayanshi ba, amman dayake ni kin rainani dole kitasani agaba kina tambaya, matsiyatan mutane, masuyin boyi boyi dan abasu kudi, fatararru kawai" yay maganan fuuu yafita daga office din ma'aikatan kowa yabishi da kallo ana mamakin tome yahada su tsawon shekaru nawa ba'a tabajin kansu ba saiyau, motarshi ya shige yaja motar yawuce yabar orphanage din.







Staff, ma'aikata, yaran gidan marayun aka fiffito aka taru awaje, daman ance bad news yafi yanda wuri nanda nan aka cika ko'ina, aka cika gaban clinic da saida Dr Kemi da Dr Ayo suka kira security gate biyu sukazo, akasa kowa yakoma various places dinsu, Baba Mani ne kawai da Mama Iyami aka bari suka shiga asibitin har zuwa dakin da aka kwantar dashi likitoci akanshi ba'a bari sun shiga ciki ba, fuskarshi tai mugun jan da saita baka tsoro, gefen idanunshi na dama ya kumbura dan hardan tsagewa yayi jini yadan fito, kasa daurewa Mama Iyami tayi ta fashe da kuka a rayuwa tanason Waleed, bata taba haihuwa ba, mijinta yarasu, an koreta gidan haya yazo batada inda take kwana, abakin titi takoma tana bara tana tara kudin datake samu danta kama haya, wata rana tana cikin baranta taga anyi parking, Waleed yafito kai tsaye yace mata mesa kike bara Mama, tace banda kowa, mijina yarasu, banda y'aya Allah baitaba bani haihuwa ba, ankoreni agidan haya, bara nake natara kudi nasami matsugunni, budan bakinshi bazaki kara baraba, sanan yajuya yay wajen motarshi yace zomuje, gabanta nafaduwa amman hakanan taji zuciyarta nacemata tabishi, motar ta shiga, yana zaune agefenta ga basket da alamun abinci ne aka dafamai agida, dauka yayi duka basket din yabata yace kici, budewa tayi ta shigaci kaman bata tabacin abinci, yakaita gidan marayun shi, yakaita asibitin shi yasa tai wanka, aka kawo mata kayan asibiti tasaka yadubata tsaf bata dawani ciwo sai maleria yay treating nata, sanan dakanshi yakaita girls hostel yabata daki na musamman dake dauke da komi sanan yace "aikinta kawai ta dinga kulamai da activities din yaran nan, she's in charge anan section din, zai dinga biyanta duk wata, sanan yasa akayo mata dinkunan kaya masu kyau aka kawo mata, tundaga ranan kulada ita yake to the extend har Ammi tasani tanada number ta, Ammi data ambata aranta yasa taciro wayarta ta shiga neman number Ammi tana kuka sosai, kaman wayan zata katse sanan Ammi ta dauki wayan, cikin kuka Mama Iyami tace "Allah yataimaki Hajiya amin afuwa hala ban kira alokacin daya kamata ba, amman dolece tasa nakira" takara wani irin rushewa da kuka dayasa gaban Ammi ya shiga dukan uku uku tama kasa magana tsabagen faduwan gaba dan tanada hawan jini, Mama Iyami cikin kuka tace "Hajiya kome kikeyi kibarshi kizo ba'asan ko karshen ne yazo ba, wayyo Allah na Hajiya" takara kecewa da kuka dayasa Ammi bakinta yafara motsi tana kokarin furta magana takasa dakyar tana wani irin nishi tace "k.....kar.....shen wane.... Iya.....mi"? Cikin wani irin mahaukacin kuka kaman wacce akama mutuwa Mama Iyami tace "karshen Dr Waleed Hajiya, Mr Arham yama Dr Waleed shegen duka, yanzu haka Dr Waleed baisan inda kanshi yakeba, likitocin mu gabaki daya na kanshi baisan inda kanshi yakeba ana kokarin ceto rayuwanshi, saisa nace kizo idan ma cikanwan ce yacika agaban ki, ai Mr Arham bai kyauta ba da kyar muka kwaci Dr Waleed a hannunshi Hajiya, dan Allah kizo yanzu koda karshen ce yayi ta a hannunki, wayyo Allah na Dr Waleed" tarushe dawani rikitaccen kuka tana katse wayan, majina shabe shabe.



Wani irin baya Ammi tayi zata zube akasa daidai lokacin mai aikinta tafito daga kitchen dauke da katuwan kulan abinci, wani irin sakin kulan tayi akasa tai kan Ammi da gudu kafin Ammi ta zube ta tareta tareda ihu tace "Hajiyaaa!" duk masifar Ammi tana bala'in sonta dan tayi aiki a gidaje da dama bata tabayin aiki agidan dataji dadi irin na Ammi ba, ganin Ammi ta sume yasa ta kuma ihu. "Mai gadi, direba, duk wanda yake awaje ya shigo ku taimake ni, Hajiya ta suma" da gudu ma'aikatan gidan suka shigo, su mai gadi naganin Hajiya assume sukai kitchen suka fitoda ruwa agora yayyafa mata ruwa sukayi tawani irin sauke ajiyan zuciya tare da bude idanunta, ahankali take kallonsu one by one, kafin ahankali tace "ku kaini wurin Waleed gida a orphanage, dan Allah ku kaini wurin Waleed dina a orphanage".
[11/1, 11:47 PM] Re@lšŸ–¤ K@usy šŸ”: šŸ’« _TWO DIFFERENT WORLD_ šŸ’«





āœļø M SHAKUR





2ļøāƒ£9ļøāƒ£




FREE PAGE
Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji yana wani irin faduwa, ward din datake gabaki daya ta kalla babu kowa cikin ward din sai ita kadai dake kwance akan gadon an lullubeta da bargo sanan anmata parking gashinta gabaki daya anyi mata parking na ponytail, ihu dawani irin masifa dataji yana sauka akan kunnenta yasa ta yaye bargon jikinta ta tashi zaune dagakan gadon tana kalle kallen dakin, ihu da hayaniya da masifan da akeyi jitake kaman a brain dinta akeyi, sakkowa tayi dagakan gadon tazira pink slippers dinta dake wajen sanan tadau Teddy dinta ta kankameshi akirjinta ta shiga tafiya ahankali kaman ana kiranta, hannu tasa tabude kofar dakin datake tafito tana tafiya dogon jelar gashinta na lilo tana kankame da Teddy ta kaganta kaman kasace ta kagudu, tai bala'in kyau doguwan yarinya da ita, batada wani kiba tana sanye da gown din asibiti daya wuce guiwanta da kadan, batada wani cikan kirji sosai, kirjinta moderate yan daidai irin na yaran larabawan nan, kanta an mata parking an daure da ribbon gashin na lilo, tundaga nesa take hango su Ammi, Mama da Mom na hayaniya dayasa ta tsorata tasake kankame Teddy gam gam idanunta na kawo kwalla dan tsoro taji sun bata hakan yasa ta shiga waige waige tana neman Waleed, fitowa tayi daga corridor ta shiga tafiyanta kaman bana mutum ba a reception din su Mom ko kadan basu lurada itaba, tunawa da ranan Waleed yayi kofa da ita yafita da ita yasa tai wajen kofan da sauri tana cikin tafiya kaman ance ta kalli glass din kofar emergency ta hango Waleed kwance kan gado fuskarshi a kumbure yasa tai dakin da sauri, hannu tasa tabude kofan ta shiga duksu Ammi basu lurada itaba, maida kofar tayi tarufe, ganin ciwo ajikinshi yasa tawani irin saki Teddy ta akasa tai kanshi da sauri, hannayenta tadaura kan cikinshi tabude bakinta tana kokarin ma magana takasa sai kawai tasaki kuka sosai tahau jijjigashi, amman bai motsa ba, kai hannunta tayi ta daura kan gefen idanunshi daya kumbura suntum ta taba tana kuka sosai tanaso tai magana tama kasa, bama tasan sunanshi ba amman sotake yabude ya kalleta, girgiza shi tayi tace "ahhhh, Umm mm" kafadarshi mai lafiya ta bubbuga tana kuka da kyar bakinta ya iya furta. "you, youuuuuuu, yo.....u" tasaki kuka sosai kaman zata mutu saikuma tadaura kanta kan kirjinshi tahau kuka tana jijjigashi tace "youuuu" sosai take kuka, takai kusan 5min ahaka tana kuka tana jijjigashi sanan tadago kanta ahankali ta kalli fuskarshi saikuma tajuya ta kalli TV dakin dake aiki da babu kara ko kadan dan anyi muting television din, tashar AIT ke aiki suna wani series na Korean film.





Daidai wata yarinya tashigo dakin wani namiji mara lafiya tana kuka tana zuwa kawai ta duka ta daura bakinta kan nashi sai saurayin ya farka, tana ganin haka da sauri tana kuka ta kallai, kafin ahankali tana kuka sosai takai fuskarta saitin nashi tana kallon fuskarshi yana mata wani irin kwarjini ta kafe pink lips dinshi da ido kafin ahankali ta saukar da bakinta kan nashi, tasaka all his lips inside her tiny mouth tai shiru tana kallon idanunshi ita adole tana jira yabude ido shima kaman na film hawaye na zuba daga idanunshi.

Kaman acikin mafarki yaji saukar wani tattausan lips kan nashi, bude bakinshi kadan yayi yay grabbing those soft tender lips yashiga kissing dinsu kaman zai cinye bakin, yatura tongue dinshi cikin bakinta yana lasowa kasa daurewa yayi yamika hannunshi trying to grab something yaji yakama mutum, ahankali yashiga bude idanunshi dasukamai nauyi kaman banashi ba, dishi dishi yake gani saikuma idanun suka washe tarr, ido da ido yayi da Widad da bakinta ke cikin nashi har lokacin bai dena kissing dinta ba idanunta sunyi jajir tsabagen kuka tana kallon idanunshi kuri kaman wata mayya, wani irin sakin lips dinta yayi da sauri yacire lafiyayyen hannunshi daga bayanta yaja jikinshi yakoma baya da sauri yana kokarin tashi zaune yana kallonta still, mikewa tayi itama tsaye takai hannunta kan idanunta tana share hawayen daya kasa dena zubowa sanan ta taho da sauri tazauna kan gadon tafada jikinshi ta rungume ta hanyar daura kanta kan kirjinshi tana kuka sosai, rasama mezai mata yayi hakan yasa yakai hannunshi mai lafiya yadaura akan bayanta yadan bubbuga alamun tai shiru sanan yatureta daga jikinshi ta tashi, hannunta ahankali takai ta daura kan wuyanshi dayaji ciwo tana turo baki kafin ahankali bama tasan tayaya maganan yafito daga bakinta ba tace "so....ry" gyadamata kai yayi cikeda dauriya, sanan ya tsareta da idanu, saikuma yace "who thought you how to do that"? Yanuna mata bakinshi, juyawa tayi kaman wata yar yarinya ta nunamai TV da yatsan ta hakan yasa ya kalli TV, Korean film yaga anayi yasan tunda ta nunamai wajen yasan anan tagani, shiru yayi yana kallonta, muryan Ammin shi dayaji yasa ya kalli kofa da sauri, faduwa gabanshi yayi, hakan yasa ya kalleta, dagata yayi tamike tsaye, anatse sabida tagane cikin harshen turenci yace "inaso kidauki Teddy ki ki koma dakinki kinji Saheeba, anjima kadan zanzo wajenki, now be a good girl and listen to me and go" makemai kafada tayi tafashe da kuka, girgiza mata kai yayi kaman zaiyi kuka yace "please Saheeba kitafi, yanzun nan zanzo kinji" sake makemai kafada tayi tana kuka, ahankali yasanya hannunshi ya jawota jikinshi rungumeta yayi tareda bubbuga bayanta a kunnenta yamata whispering yace "listen to me, please Pretty go, I don't want Ammi to see you here, please pretty go" yay maganan tareda dagota ahankali, fuskarshi ta kalla ya gyadamata kai hakan yasa ta sauka ahankali daga kan gadon, daukar Teddy dinta tayi sanan tajuyo ta kallai shima kallonta yake kaman yau yafara ganinta, ahankali tasa hannu tabude kofar dakin tafita tamaido kofar tarufe yana kallonta, ta glass din kofar yacigaba da kallonta ahankali take tafiya ta kankame Teddy ta, tai corridor dazai sadata da ward din da aka kwantar da ita. Ajiyan zuciya ya sauke tareda lumshe ido yadaura hannunshi kan fuskarshi kafin yasauke hannun kan bakinshi yay shiru yana tunanin what just happened.






*******





Within 30min IGP yayi deploying police zuwa address da Ammi ta tura mai. Knocking Gate din gidansu Arham one of the police men yayi, fitowa daga daki maigadi yayi yaleko, ganin police ne yasa yace "bayin Allah wakuke nema"? Wani daga cikinsu ne yace "Goodday please we are looking for Mr Arham" mai gadi da tuni jikinshi yahau bari ganin yan sanda yasa yace " yes gidan nan ne gidan Mr Arham" daya daga cikinsu policeman dinne yace "is he in"? Ware ido mai gadin yayi dan baigane turencin ba hakan yasa daya daga cikinsu yace "yana nan? Da sauri yace "yes.....eh,yana nan, yanzun nanma ya shigo gidan" "kaimu wurin shi" da sauri yajuya yay gaba suna biyedashi abaya har flat dinsu yabude kofa yashiga suma haka, a palour suka sameshi ya daura kafa daya kan daya yayi resting head dinshi a kam one seater kujeran dayake zaune akai hannunshi rikeda chilled maltina, jin mutane akanshi yasa yadago yana kallonshi, babban su ne yace "good-day Mr Arham we are here to invite you to our office for some questioning" yana gama maganan yafito mishi da ID card dinshi ya nunamai, bin ID card din yayi da kallo sanan yatabe baki yamaida kanshi kan kujeran yana girgiza kafa, kara maimaita mishi maganar sukayi but no response still saima maltina shi daya cigaba dasha, mai gadi ne saya gama tsurewa yace "Alhaji dakai fa suke" dago kanshi yayi ya musu wani irin kallon banza yace "what questioning"? Cije lips policeman din yayi yace "when you reach our office you will find out" "and where is your office located at"?

Shiru police din yanasa baicemai komiba dakin ya tsit, maigadi dake shirin sakin fitsari yace "Alhaji kabisu kar su maka wani mara kyau, kagan sunata binka ahankali tun dazun, kawa Allah kamike kabisu" y
policeman dinne ya juya ya kalli wasu manyan officers guda biyu da sauri sukai heading directing to kujerar da Arham yake zaune. "Sir you are under arrest" fisgoshi daya daga cikinsu yayi ya tayar dashi tsaye Arham bayyi wata wata ba ya dauke policeman din da mari mai kyau, bai ijiye hannun kasa ba yaji saukan mari to ko'ina akan fuskarshi dayaji yaji kwakwalar warshi tajuya abaibai.


ā¤ā¤ā¤
[11/1, 11:48 PM] Re@lšŸ–¤ K@usy šŸ”: šŸ’« _TWO DIFFERENT WORLD_ šŸ’«





āœļø M SHAKUR





3ļøāƒ£0ļøāƒ£






Kamar jira suke suka haushi da duka kaman an aikosu suna bugamishi gindin bindiga all over his body, jin duka tako'ina yasa Sadiya tafito daga ciki dagudu tana ganin Arham ya sanda ke duka tahau ihu,

23 / 48