Auren Katin Kasa Book 1 Complete Hausa Novel

Author :  Queenmerh Category :  Romance

Chapter   13 / 16

36K to 39K   out of 46.7K words

zai mashi wannan tambayar kuwa yayi preparing kanshi, kallonshi hammam yayi sannan yace ‘’katuna corn dog da muke saya tun a school kuwa?...corndog din jezz dai wanda kullum sai munci? amar yayi tambayar yana fuskantar hammam, girgida mashi kai hammam yayi sannan yace ‘’yes sudai, I had that sun dawo nan shiyasa nace bari muzo nan muci saboda tuna baya lokacin kana acicin ka’’…murmusawa amar yayi sannan suka fito daga cikin moton, ajere suke tafiya har suka isa gaban gate, amar wanda yake sanye cikin farar jellabiya irinta larabawa wanda suke kira da ‘kandura’ yayi rawani akanshi irin yanda larabawa sukeyi sai yayi kyau sosai, cute fuskanshi tayi dau, pinkish lips dinshi kuma kamar jini zai fita daga ciki tsabar yanda yayi pink, faffadan kirjinshi ya fito da kayan sosai, arms dinshi ya wani murde ta cikin rigar, amar saurayi ne mai jini ajika ga kyau ga naira ga tsayi gaint komai dai ya hada, hammam kuwa shima saurayi ne kyakyawa ajin farko saidai shi amotse yake, jikinshi ba kamar na amar ba da shi kallo daya zaka mashi kasan he is so attractive, shima yana sanye da irin kayan jikin amar sai ya fito a zallan balaraebnshi, ciki suka shiga,wuri ne mai shauqi, ko’ina ka gitta couples ne suna daukan pictures, daga gani wajen na masoya ne, ga flowers different types a ko’ina, tabe baki kawai amar yake saboda shi duk irin wannan baya gabanshi, baima damu da irin mutanen wajen ba, duk inda yaga masoya sai yace wasting time dinsu sukeyi kawai, shi aganin shi babu wani abu wai shi love, true love does’nt exit, shi ganin duk wanda suke soyayya sunayi ne don wani abun da suke nema na duniya wajen partners dinsu. Tafiya suka danyi mai tsayi sun wuwwuce slot na masu saida junks da yawa kafin suka iso wajen jezz corn dog, agaban slot din wajen suka tsaya, saiga amar yana murmushi daga gani wajen is special to him yanda yake murmushin ganin wajen har fararen hakwaran shi suna bayyana daga labbenshi, saida aka salami wasu couples tukunna aka zo kansu, tun kafin hammam yayi Magana yayi sauri cewa ‘’ two pack with special garlic dip topping’’..murmushi hammam yayi sannan ya dan kebe gefe yana yima Haifa message cewa ya iso,..karba masu amar yayi sannan ya karaso gaban hammam yace ‘’lets go’’ tafiya suka fara amar harya fara cin nashi yana lumshe ido saboda santi.

Haifa kuwa direct wajen inda take sayan wani special gelato ice cream suka tsaya, amra dai har yanxu jikinta a sanyaye, ganin taki sakeya yasa Haifa ta karba ice creams din sannan ta mika mata nata tace, ‘’amra ki jirani ina zuwa’’ sannan ta juya.. wani dan shop ta shiga, saigata ta fito da snake na roba nade a wuyanta, gaban amra ta tsaya tana kunshe dariya sannan tace ‘’babe kallo kiga’’ juyawan da amra zatayi me zata gani..maciji ajikinki haifan,, a hankali ta soma ja da baya,jikinta ya fara bari bakinta har karkarwa yake wajen furta ‘’maci…maciiji Haifa ki gudu,’’ Haifa kuwa me zatayi banda dariya, gaban

amra ta soma takowa ganin haka yasa amra tafiya ta baya da hanzari, tana cewa ‘haifa stop it, this is not a joke’ idon ta har yana neman kawo kwalla, jintayi dan tuntube don da baya take tafiyan yasa ta runtse ido tana karanto addu’a dayazo bakinta dukta tsorata jiran faduwa kawai take, jin ta tsam ajikin mutun ga wani sanyin kamshi dake tashi daga jikin shi yasata runtse idonta sosai, amar kuwa wanda yaji kamar daga sama an wullota jikinshi yasa shi qamewa awajen kamar gunki ya kasa motsawa kwata kwata, gashi babu damar tureta ajikin shi saboda hannunshi daya rike yake da corn dog dayan kuma wayanshi ne daya kara akunne yana waya da m-5, muryar m-5 ce ta dawo dashi daga dogon suman tsayen da yayi, rankwafo da kanshi yayi yana kallonta da yake tsayin nata bai wuce kirjinshi ba, har tsakiyan kanta yana hangowa, gaba daya ta sakar mashi jikinta, mazaunanta sun matse da gabanshi tsamm ass dinta ya manne da jikinshi yayi mashi ruf,gashi yanda kirjinta ke bugawa yana sama da kasa yasa jikin nata yin girgiza kadan, ahankali yasoma jin wani irin abu na tunkaro masa tun daga babban dan yatsan shi, da sauri ya jefar da corndog din a wajen sannan yadan tukudota gaba, idonshi yayi jaa kamar zaki, bakinshi nason furta abu amma ya kasa dakyar ya tattaro nutsuwarshi ganin mutane na kallonsu, hammam ne dake gefenshi yayi sauri karasowa gabanta yace ‘’mss are you okay?.. karasowa gabansu Haifa tayi wadda tuni ta cillar da snake din robar ganin amra ta gigice, ‘’hammam ta furta yayin data tunkaro su, ‘’babe daman munata  ji…’’ saurin katse ta hammam yayi da cewa ‘’hey babe what a pleasant surprise me kikeyi anan?.. ya kifta mata ido alamun tayi shiru.. murmusawa tayi sannan tace ‘’banyi tsammanin ganinku ba anan kaida best friend din naka, dama munzo yawo ne nida amra’’, ta karashe tana nuna amra dake tsaye kamar gunki agaban su… hamman ne ya dubi amra sannan yace ‘’ayya ashe itace sukayi dan clashing da best friend,’’ ko kallon inda suke amar baiyiba saima takawa daya soma yi, ganin yayi gaba yasa hammam cewa su zo su zagaya, amra kuwa binsu take amma har yanxu bata dawo daidai ba, gaban wani resting chairs da hut amar ya zauna, nan suma suka samu waje suka zauna, kujeru hudu ne a wajen kowannane su ya samu waje ya zauna banda amra wanda tunda sukayi clashing da amar ya yi mata wani kallo yasa jinin jikinta boiling, kame kame ta fara don Haifa ta zauna saitin hammam while extra kujeran na facing amar wanda ko ta kanta baibi ba yana ji da kanshi karshe ma waya ya fara dannawa, haka nan sadap sadap ta samu waje ta zauna duk atakure, sau daya ta dago ta kalleshi ta dauke kanta bata kuma gigin kallonshi ba.. zama sukayi na kusan 30minutes wanda duk hammam ne da Haifa suke hirar masoya abinsu, daga bisani kuma sukayi ordern large pizza da fresh orange juice, anatse su hammam suke cin abinsu su kadai inda yake bama Haifa abaki tana bashi, su kuwa su amar babu wanda ya kalli pizza, shi amar cin pizza dinne bai dameshi ba shiyasa ko kallon wajen baiyiba ita kuma amra cikinta ne ke kugi sbd duk atsorace take, tana tsoron yin laifi shiyasa ta kasa ko daukan daya taci sai dai juice din da take dan sipping, kallonsu hammam amar yayi sannan ya kawar da kai don duk abinda suke haushi yake bashi..mikewa yayi sannan yace ‘’ka

sameni a moto’’ ficewa yayi abinshi yana takun nan nashi cikin isa, ganin haka yasa amra sauke nauyayiyar ajiyar zuciya, aranta take ayyana badan mutane ba yanda taga wannan mutumin yayi dazu bazasu kwashe da sauki ba, fuskarshi take tariyowa akanta, yana da kyakyawar fuska saidai daga ganinshi baida sauki, kawar da zancen tayi alokacin Haifa ta kalleta sannan tace “bakici ne amra’’.. girgiza mata kai kawai tayi sannan ta dan kwatar da kanta jikin kujerar itama ta qagu su tafi kawai, saida suka dauki kusan awa daya kafin suka fito, har bakin motor hammam ya rakasu wanda duk akan idon amar dake zaune cikin motor kamar bai gansu ba, saida suka wuce sannan hammam ya shiga motor shima suka wuce gida, akan hanya hammam ya fara mashi Magana ‘’amar don’t tell me har yanxu kana fama da wannan oligospermia dinnan cos naga yanda kayi reacting lokacin da kawar Haifa ta….’’ Bai bari ya karasa ba yace ‘’hammam please lets not talk about it, not in a good mood now’’.. kyaleshi kawai hammam yayi wannan zurfin ciki na amar yana damunshi, wai ace mutun yana cuta amma bazai nema ma kanshi sauqi ba, sautin waka ne kawai ke tashi ah motorn su babu me cewa qala har suka isa gida.

 

Koda hammam ya saukeshi gida, wanka kawai yayi sannan yayi sallah yadan ci abinci yabi lafiyar gado, rufe idonshi yayi, ahankali event din dazu ya dinga tariyowa akanshi, da sauri ya kawar da abin sbd wani irin zafi da daci da yakeji aranshi.

Amra kuwa itama bayan Haifa ta sauketa sunyi sallama, daki kawai ta wuce tayi salla sannan ta kwanta, tunanin mutumin dazu take wanda taji Haifa na cewa shine best friend din saurayinta, ganin bacin rai a idonshi yasa ta jin babu dadi, duk ita ganin bacin ran nashi yayi ne sbd ta fada mashi ne wanda itama bataso hakan ba, da tunaninshi ta kwana aranta.

***Auren Katin Kasa ***

(Unexpectedly falling)

Story and written by:

QueenMarh

Free page….

Chapter 37-38

Washe gari da safe ta shirya domin zuwa motsa jiki, yauma kamar kullum ko’ina busy, black tight ne ajikinta sai riga mai girma sosai wadda ta rufe mata kwankwasonta har kasa, saida ta gama komai tukunna ta fara shirin futowa domin zuwa gida, jin sallama abayanta yasa ta tsaya, wani saurayi ne fari dan

gajere dashi don kusan ta fishi tsayi kadan balarabe ne, murmushi yayi mata sannan suka gaisa, gabatar da kanshi yayi ‘’sunana abdul-basit, kullum ina ganin ki ke kadai bakida company, shine nace bari mu gaisa,’’ ganinshi kamar kamilalle yasa amra maida mashi martini ‘’ hey nice to meet you I don’t need a company ay, I’m a grown up lady thank you’’, ganin she’s hard to get yasa basit saurin cewa, ‘’you look so calm daga yanda kike Magana na gane kina da kirki, zan iya zama abokin mai kirkinnan,?’’  ganin zai bata mata lokaci gashi dare yana yi yasata cewa ‘’yes goodnight’’ bata jira amsan shi ba kawai ta wuce ta fita,, murmushin gefen baki yayi sannan yace ‘’she’s hot’’ yana lashe lebensa.

 

Gida ta wuce kawai bayan ta tsaya ta saya abinci, ko data karasa wanka tayi don yau tayi exercise sosai jikinta yayi tsami, kuma tana ganin progress din ajikinta, sbd yanda ko ina ya fara zama snatch, duk wani excess fat ajikinta ya fara tafiya, abinci taci sannan ta kirasu salima, yau kwana biyu Kenan bata samunsu, kodata kira ishaq ya shaida mata suna cikin koshin lpy, hakan yasa hankalinta yadan kwanta, ta dukufa da karatu sosai batada wata sauran damu banda su salima.

Aranta tana tunanin dama da yanda za ayi ta kwasosu ta kawosu kusa da ita sbd bata jin dadin rashin zamansu ba tare ita ba.

 

Kwanaki karamar ruwa ja suke sosai inda amar ya fara shirinshi na last case din da zaiyi wanda yake saka ran idan har ya tafi daidai zai samu promotion saboda shekarunshi sun kusa 30years gashi Amma kullun saita dameshi akan ya dawo dukda taki fada mashi dalilinta nason dawowa amma bayajin zai dawo nan kusa.

 

Tsaye yake cikin shirinsa na kakin sojoji inda ko ina na jikinshi sanye yake da bullet proof, anatse ya sauko kasa inda ya samu Pablo yana shirya abinci a dining, coffee kawai ya dan sha sannan ya wuce motorn shi, futowa harabar gidan yayi inda m-5 da wasu guards dinshi suma sanye da uniform suke duk suka sara mashi, bayan motor ya zauna sannan kowannen su ya je mazauninshi suka fice daga penthouse din, aguje suke tafiya kamar zasuje yaki, koda suka isa head quarter anan suka tarar da general atsaye da manya manyan karfafan officers, kowannensu ashirye da bindigu kaca kaca ajikin su, futowa yayi daga motor tare da sarama general sannan ya qame a gaggauce general din ya fara Magana ‘’ senior officer amar yunus TAURA of rank 1, this is an order you are to take the lead of this operation successfully with your men’’ atare duka suka ce ‘’yesss sir sannan suka fara shiga motocin yaqi, koda ya shiga motor waya ya dauka kawai ya kira Amma bayan sun gaisa yace mata ‘’Amma na I need your prayer zan tafi wani operation yanxu’’… addua sosai ta shiga zabgo masa cikin kamilar voice dinta sannan sukayi sallama.. ahankali ya lumshe idonshi sannan ya fara karanto adduo’I domin kariya da samun nasara,.. operation sukayi nakusan sati guda, inda sunsha wahala sosai kuma an kashe wasu daga cikin

mutanenshi wasu kuwa sun raunata amma cikin ikon allah sunyi nasara don babu wanda suka ragamawa acikin wanda suka kaima farmaki, lokacin da suka kira headquarters ba karamin dadi kowa yaji ba game da wannan successful aikin da sukayi, wanda har shugaban kasar yaji dadi sosai sannan yayi masu alqawarin kyaututtuka da dama, aciki kuwa harda waenda za a masu promotion, ajigace suka dawo koda ya dawo direct apartment dinshi yasa aka kaishi domin ya huta, babban building ne wanda yake kunshe da apartment din mutane da yawa, ciki ya wuce kawai yah hau 7th floor daidai house number 53 ya manna smart keys dinshi ya bude kofan, gida ne mai kyau sosai bashida wani girma daidai mutu daya harma da karin mutun daya, tundaga sitting room ya fara rage komai nashi, parlor ne maidan girma sai L shape kujera babba sai katuwar tv da dan center table mai dauke da glass flower asamanshi, gefe kuwa wani jibegen flower vase ce mai kyau jikin curtains dark gray masu kyan gaske da tsayi, daki kawai ya wuce direct, shima ba laifi akwai girma gadone babba sai side lamp masu kyau ako wane gefen gadon sai yar couch acahn gefe, bai tsaya komai ba ya fada toilet, shima toilet din babu laifi akwai girma amma baikai ko kwatan na penthouse dinshi ba, sabule kayan jikinshi yayi ya soma wanka, saida ya dirje jikinshi sosai kamar zai chanza fata tukunna ya dauro alwala ya fito, sallah kawai yayi kafin ya bi lafiyar gado bayan ya kashe duk wayoyinshi da aketa faman kira tunda suka dawo.

Yasha bacci sai wajen takwas na dare ya tashi, yayi sallah sannan yasa m-5 ya karbo mashi abinci daga gida wajen Pablo. Within 30mins saiga m-5 ya kawo mashi sannan ya juya ya tafi….

 

Amra kuwa yau kai ya gama daukan zafi sosai, last paper suka gama na 400 lvl first semester, ta wahala sosai sbd ba ayi masu da sauqi ba, ta wani bangaren kuma dadi takeji domin yanxu hutun karatun yazo mata sbd zasu fara housemanship, dama qa’idar school dince sai sunyi 400lvl tukunna saisuje housemanship bayan sun gama na yan watanni saisu dawo school suyi last semester ba kamar wasu school dinba da saikayi graduation zakayi housemanship wannan Kenan…

Atare suka fito daga examination hall itada Haifa wadda itama kana ganinta kasan an sha wahala, direct café suka wuce suna dan taba hirar last paper da sukayi, saida suka ci burger da banana smoothie sannan suka miqe, atare suka wuce motorn Haifa wadda babanta ya saya mata recently Bugatti la voiture noire baqa,.. koda suka kama hanyan gidan babu abinda suke magna akai sai housemanship din da zasuyi…kallon amra Haifa tayi sannan tace ‘’amra wani hospital ne ah first choice dinki naga sun saka sabon asibitin nan na army’s ah farko’’… aikuwa shina saka fa as first choice dina” a cewar amra,,, kallonta Haifa tayi sannan tace nima shina saka fa, amma meysa kika saka ke?’ murmushi amra tayi sannan ta ce ‘’its because of my little brother, yana burin

shiga army, koda na fada mashi cewa ah cikin headquater din armys zanyi yaji dadi sosai sbd tun muna qananu zakiji yana cema abban mu shifa soja ne kuma zai kare abba da oumm dinmu’’ wasu siraren hawaye ne suka zuboma amra, Haifa dake kallonta da gefen ido tace ‘’baki taba cemin komi game da iyayenki ba amra please ki fada min ‘… shuru amra tayi chan kuma ta share hawayen nata sannan tace ‘’banida iyaye duk sun rasu ni yar riko ce wajen uncle dina tun bayan rasuwar iyayena ta dalilin hatsarin moto’’ jin haka yasa Haifa gangarawa gefe tayi parking sannan ta dube ta ‘’I’m so sorry amra shiyasa bakya maganrsu, inata mamaki ashe sun rasu, allah yayi masu rahama ameen, amma idan bazaki damu ba inason nasan tarihinki amra.. ahankali amra ta soma Magana ‘’kamar yanda kika sani sunana aisha amma ana cemin amra dalili kuwa sunan maman mahaifiyata ne, mun taso mu uku ne wajen mahaifinmu wanda ke son mu sosai nida kanne na, haka uncle dinmu yayan mahaifinmu shima yana sonmu sosai,ranar da bazan taba mantawa ba shine ranar da iyayenmu suka bar duniya, ranar munzo hutu gidan uncle Mustapha wato dady nidasu salima, lokacin su abba sun tafi umra, ranar da zasu dawo aranar Allah ya karbi ransu akan hanyar su ta dawowa gidan uncle daga airport domin dauko mu, lokacin uncle ya fita shida salim kanin mu, muna zaune nida salima da yaran gidan muna wasa uncle ya turo motor a daukemu, bayan mun isa asibiti emergency ward aka kaimu, gaban wani daki muna shiga mukaga uncle zaune yana kuka salim kuma kwance rai ah hannun allah sakamakon buqawa da zuciyarshi tayi, anan ake shaida mana iyayenmu sun rasu sakamakon hadarin mota kuma motorn su ya qone qurmus don ko gawarsu ba’a samu ba sai toka,nan take salima ta sume,mun shiga damuwa, sosai salim kam saida ya dauke watanni goma yana comer dalilin jin rasuwar iyayenmu wanda dady ne ya fada mana hakan, kullum muna tare da kaninmu school ne kawai ke rabamu har Allah ya farfado mana dashi saidai abin mamaki tundaga wayonshi har zuwa lokacin ya manta da komai, nan uncle ya kwashemu ya maidamu gida, bayan yan watanni mun samu kulawa daga bisani kuma muka fara ganin chanji, munyi rayuwar walaha sosai Haifa kamar ba mutane ba, har Allah ya tsallakar dani, shiyasa yanxu banida burin daya wuce na kawo kanne na kusa dani sbd hankalina ya kwanta nima bana burin komawa wannan gidan, har kusan raping dina yayana yayi wato wahab babban dan daddy’’ tana kaiwa karshe ta fashe da kuka sosai… ba karamin tausayi ta bama Haifa ba sai taji yanxu duk duniya babu wanda take ji a jininta kamar amra kuma tasha alwashin zata kula da ita har tsawon rayuwar ta kuma zata dunga taimaka mata.

Gida suka wuce direct inda Haifa tadan debe mata kewa sannan ta dawo gida itama.

 

Kwanan

13 / 16