sukaci abinci wanda aka tanada masu professional chefs da zasu dinga dafa masu harsu bar camp din.
HAIFA’s RES….
Kwance Haifa take akan katon gadonta cikin wani Turkish riga mai santsi ta shan iska, kunnenta maqale da airpod tana jin waka, hannu ta miqa gefen bedside dinta ta dauka glass of orange juice tana sipping, knocking dakinta akayi har sau uku, sannan aka shugo, wata farar mata sanye da abaya baka kanta babu mayafin sai gashinta dake asauke har gadon bayanta, fuskarta sak irin ta Haifa amma ita ta manyanta don Harda furfura ya futo mata, kana ganinta kaga mahaifiyar Haifa, takowa tayi har gaban gadon Haifa wanda yasha zanin gado da duvet mai kyau purple, wayan hannunta ta wafce, da sauri Haifa ta dago ashagwabe tace ‘’ummii.. aetini hatifi ummi (give me my phone ummi)’’ kallonta wadda ta kira da ummi tayi sannan tace ‘’limadha anat hakadha Haifa? Why are you like this haifa’’?.. maraice fuskatayi sannan tace ‘’ummi me nayi kuma, hutawa kawai nake yi’’ cikin larabci matar ta cigaba da mata Magana wanda yake nuni da fada take mata sosai, chan kuma tace ‘’your abuh is calling you’’ ..sannan ta ficewarta ba tare da ta bata wayanta ba,…tashi tayi sannan ta wuce hardakin abuh wato mahaifinta…fadar tsaruwar gidan su Haifa sai wanda ya gani, gidane da ake cema aljannar duniya, komai irin na larabawa,har cikin dakin abuh ta shiga bakinta dauke da sallama, kodata shiga yana zaune akasa gefen gadonshi yanacin kayan marmari,har gabanshi taje ta rusuna ta gaishesa,’’ dagowa yayi ya kalleta yace ‘’ Haifa menena matsalarki ne, da makaranta,? Kince bazakiyi karatu ah dubai ba na turaki London, shekaranki biyu achan
kikace bakyaso zaki dawo nan, nanma kin dawo na turaki the most popular and high skilled educated university yanxu kin maida abin shiririta, Haifa yau almost a year Kenan bana gane progress dinki sbd haka nayi deciding yanxu duk school din da naga dama zan kaiki sannan wallah daga farko zaki fara, idan baki tsaya kinyi abinda ya kaiki ba kuwa aurar dake zanyi kuma duk wanda yayi min shi zan bamawa, karkiyi tunanin don ke kadai Allah ya bani ko zan kyale ki, no bazan kyaleki ba, idan baki nemi ilimi ba me zakiyi, sbd haka get ready gobe zaki fara makaranta kuma ni zan kaiki da kaina, and mind you duk course din dana zaba maki dolenki kiyi shi’’ dagowa Haifa tayi idonta tap da hawaye tace ‘’abuu’’ daga mata hannu kawai yayi sannan ya nuna mata kofa, ahankali ta mike ta futa, shima kanshi ya daure ne yayi hakan sbd yana son diyar tashi sosai amma kuma bazai tsaya rayuwarta ta salwanta ba,
koda Haifa ta koma daki ta wayarta ta fara lalube ko ummi ta aje mata, hango wayar tayi kan dresser, da sauri taje har gaban dresser din ta dauka m ta fara laluben number hammam,
wajen sau biyar tana kira amma baya shiga, jefar da wayan tayi sannan ta kwanta rub da ciki ta saki kuka sosai, itafa karatu baya gabanta, aure takeso kuma auren wanda take so amma sanin al’adar gidansu cewa sai mutun yayi karatu ya fara aiki tukunna zaiyi aure yasa ta kasa fadi ma abuh, sai gashi yanxu kuma yana mata maganar zai aura mata duk wanda yake so, ya kasa gane ita auren takeso amma ga wanda ranta yakeso, shekarar su biyu da haduwa da hammam, wanda ya kasance shine mutun na farko data fara so.
Washe gari tunda sassafe ummi ta tasheta, batayi wani musu ba ta tashi ta shirya cikin wata brown kaftan mai hula wadda ta amshi fuskarta sosai, wayarta kawai ta dauka da handbag sannan ta sauka kasa, anan tasha dan coffee sbd abuh dake jiranta amoto zai fara sauke ta kafin ya wuce office, tapiyar 20mins sukayi sannan suka iso gaban school din,ganin inda zasu shiga yasa ta juyawa ta kalla abuh,sannan tace ‘’abu wannan school din? Haba abu duk kawayena fa babu wanda ya yi irin school dinnan sai ni, wallahi idan kawayena sukasan nan nake zuwa ay saisu rainani, gaskia abu I can’t study in unisex, wannan school dinfa yana top 3 abu noo pleas’’ murmushi kawai abu yayi sannan yace ‘’haifa dear, this is my final decision, dole kibi umarnina ni mahaifinki,’’… jin kamar abu yana Magana da fada fada yasa tayi shuru kawai amma ranta baisoba, wannan ay sai a rainata,…..ni kuwa nace ohh Haifa yayan manya amra da tazo school dinnan ay kusan suman tsaye tayi sbd bata taba tsammanin zata iya dasa kafarta anan ba.
Already daman an gama yi mata komai direct har first lecture class dinta ya rakata sannan ya wuce office… kodata shiga kallon wajen take tafi karfin wajen, haka yasa ta zauna kawai har aka gama lecture din tana danna wayanta
bata dago ba, batama san wani course bane sukeyi balle kuma course din da zata karanta…..
kwanan su amar uku ah camp, kana ganinshi kasan yes training sukeyi har wani dan duhu yayi kuma nanda kwana biyu suna saka ran barin wajen sbd daman training din kwana biyar ne…
Amra kuwa an dage da karatu sosai, kullum itane farkon shiga class kuma karshen fita class ah kwanakin da tayi an kawo sabbin student har hudu wanda babu ruwanta da sha’anin kowa, ta maida hankalinta sosai tana karatu kuma tana waya dasu salima, inda suka shaida mata basuda wata matsala.
Haifa kuwa tana shan wahala ashe abu course ya zabo mata maidan wahala wanda bataso haka ba, tafison abinda yake da sauki sabd tayi ta gama kawai ta huta, ganin course din har shekara uku ne yasa hankalinta tashi sosai.
Yaune last day na training dinsu amar, duk ya qagu su wuce kawai saboda yana buqatar hutu sosai, sai wajen dare suka iso headquarters, koda suka iso kiran m-5 kawai yayi ya kawo moton shi su wuce gida, suna isa dakinshi kawai ya wuce direct yayi wanka ya shirya cikin pajamas dinshi farare, light abinci yaci sannan ya koma sama ya kwanta, ya kwaso gajiya sosai, remote ya jawo daga gefen bedside dinshi ya kunna tv sannan ya rage hasken dakinshi, dayake komai na gidan is smart ya sanya shi yin komai daga kwance, news ya sanya , daga gefe wayanshi ya fara vibrating (amma) ya furta ganin wayan na neman katsewa ya sa shi dauka da hanzari sannan ya kara ah kunnenshi, anatse ya fara jin muryarta mai kwantar mashi da hankali ‘’son how are you har yanxu fushi kake da AMMA ka ko?” shuru yayi sannan yace ‘’amma na ina wuni kuna lapiya kuwa?” murmushi tayi sannan tace ‘’lapiya lau son, dan allah kayi hakuri da abinda ya faru last time kaji yaushe zaka dawo?’’ shuru yayi sannan yace ‘’amma ba yanxu ba gaskia bazan iya zama ba ina kallon abinda wanchan mara tunanin yake ba, idan nayi yunkurin saita mashi hanya saikice ba haka ba’’…shuru tayi sannan tace ‘’I miss you son’’ sanin cewa daman ba son laifin aman take ba ya sashi kawar da maganar…saida suka danyi fira sama sama sannan sukayi sallama, miqa yayi gefenshi remote dinda ya aje bai sani ba ya danne ya chanza channel, anatse ya sauko ba tare da yako bi takan tv dinba, toilet ya wuce direct mintuna kadan ya fito, da alamu alwala yayi, dogowar da zaiyi karaf idosnhi ya fada kan tv, cikin yan second kawai jikinshi ya fara karkarwa tundaga kan yatsun kafarshi har zuwa tsakiyar kanshi yake jin vibration nan take idonshi yayi jaaawur, macece zir haihuwar uwarta kwance agado saurayinta yazo gefenta yana mata wani irin shafa ta yana kissing dinta ahankali sautin moarning dinsu ya fara cika dakin nashi kawarda da idonshi yayi daga kan tv din, da sauri ya karasa gaban gadonshi ya fara laluben remote din hankali atashe, hanunshi har karkarwa yakeyi sosai sbd abinda ya gani kuma da sautin dake tashi, da sauri ya kashe tv din idanunshi suna qaqqafewa, ganin
kafafunshi suna neman gaza daukarshi yasashi zama dabas akan gado ahankali ya fara karanto addu’oi, chan kuma ya mike har yana harde kafa idonshi gam, dakin closet dinshi ya shiga har lokacin hannunshi kakkarwa yakeyi, da sauri ya bude wata locker, wasu kananun magani ya dauko kala biyu ya afka abakinsa sannan ya zame ya zauna awajen kusan minti sha biyar kafin abin ya soma lafa mashi, saida ya kwashe almost minti talatin kafin ya mike da kyar yana dan layi sannan ya wuce bathroom, kayan jikinshi ya sabule kallon gabanshi yayi da yake drippin sosai ta cikin shorts dinshi wanda ya jike sharkaf Kaman yayi wee wee, runtse idonshi kawai yayi ya tako wajen shower ya sakarma kanshi ruwa saida ya dade tukunna ya fito ya dawo ya chanza kaya ya koma bedroom, kwanciya yayi sannan ya kashe tv dinma baki daya, ya kwanta yana rufe kanshi cikin duvet dinshi, bacci yakesonyi amma ya kasa, duk kokarin da yakeyi yanayi sbd kaucewa shigarshi irin halinnan shiyasa dayaga mace yake kaucewa sbd lalurar shi idan har yayi sake to fa abinda yayi mashi saura zai kubce masa, rufe idonshi yayi da tunanin zuwa asibiti washe gari, dakyar bacci ya daukeshi.
Washe gari ta kasance Friday, yau lecture daya zasuyi wanda practical, ganin yau Friday ne yasa amra shiryawa cikin atampa Riga da skirt kayan sunyi mata kyau sosai, kodata isa school yau saita zama abar kallo har tana dana’sanin saka kayan, sukuwa yan skul mamakin suke ganin kayan jiki ta wani culture ne ita, cikin nutsuwa ta shiga class dinsu tana tunanin yauma itace ta fara zuwa, tana shiga ta ga wata kwance daga gefe,wuri ta samu ta zauna tana duba last practical da sukayi acikin littafin ta, jin sheshekar kuka yasa amra kallon inda budurwar take, shuru tayi chan dai ta mike ta tsaya gabanta tadan rankwafo tace ‘’hey is everything okay’’? jin Magana yasa Haifa dagowa ta kalleta sannan tace ‘’can you get me to clinic please’’ kallonta amra tayi sannan tace ‘’yes’’ lets go, rike hannun amra Haifa tayi sannan suka wuce har clinic, dubata doctor yayi sannan ya bata magani daman dan period pain ne, amra kuwa sanin zafin ciwon yasa ta zauna da Haifa Har abun ya lafa mata, har time din lecture dinsu ya wuce, sai wajen karfe 3 suka fito daga clinic, inda amra ta rakata har gaban motor data zo daukan Haifa, abuh kuwa ganin Haifa da wata wadda ta fita daban cikin irinsu yasa ya karaso har gaban su sannan ya fara Magana cikin larabci ‘’haifa bakida lafiya ne? meya sameki’’??? Magana ta maida mashi itama cikin larabcin ‘’abuh yau na wuni ne bana jin dadi amma naji sauki wannan ce ma ta taimaka min’’ kallon amra yayi sannan yace ‘’menene sunanki’’ kallonshi tayi sannan tace ‘’Aisha badaru amma ana kirana da amra’’ godiya sosai abu yayi mata sannan suka wuce, itama gida ta wuce direct bata tsaya ba…
Amar ne gaban doctor idonshi nakan waya yana danna wa, ahaka zaka dauka baya sauraron bayanin likitan, nan kuwa hankalin shi yana kanshi, dagowa yayi sannan yace ‘’I hope that little drip will not cause me so much’’ kallonshi likitan shima yayi sannan yace ‘’Mr amar I’m afraid that we’ll have issues with your health, for now ina kokarin inga komai ya tsaya sbd idan har dripping din
ya cigaba zai jawo maka asarar kwayayen da suka rage maka, which kasan cewa idan har babu su bazaka taba haihuwa ba, in most cases wasu nasu yana kaiwa to the point din da guda daya ne yake ragewa ajikinsu mai amfani, kuma risk ne babba idan yakai to the point dinan, so I will advice you to be more extra careful because oligospermia ba abu bane mai sauqi sannan zan baka medication da zaka dunga sha’’
Godiya kawai amar yayi mashi sannan ya fucewarshi.
Abu kuwa yaji dadin haduwar Haifa da amra because yaga nutsuwa a tattare da amra, wanda nan take yayi naam da ita, Haifa kuwa tana wucewa daki hammam ya kirata sukasha hira sosai cikin so da kaunar juna.
Akwana atashi babu wuya yau har sunci first semester sunyi hutu,amra kam ta dage da karatu sosai sannan yanxu kadaici ya ragu sosai sbd tayi qawa yanxu kafin suyi hutu wato Haifa wadda kusan kullum sai sunyi waya, har aka dawo hutu suka cigaba da karatu, amra ta dage sosai tana neman ilimi, inda take taimaka wa Haifa sosai don taga batason karatu wanda hakan ba karamin dadi Abu din Haifa yakeji ba, yau ma suna fitowa daga lectures Haifa ta kalli amra tace ‘’babe muje musha ice cream mana treats on me pleas karkice no’’ kallonta amra tayi sannan tace ‘’okay but banason muyi dare’’ fita sukayi suka shiga motor Haifa wadda yanxu abu yadan sake mata har tana fita da motor sabanin lokacin data shugo sbd yana gudun karta dunga yawo taki karatu ganin yanxu kullum tana tare da kawarta yasa ya kyaleta, ice cream suka sha sannan Haifa ta sauketa agida itama ta wuce gida, kwana biyu batajin dadi sosai sbd idan ta kirasu salima saita dunga jin kamar basa cikin walwala.
***Auren Katin Kasa ***
(Unexpectedly falling)
Story and written by:
QueenMarh
Free page….
Chapter 33-34
ABUJA NIGERIA
MAITAMA
Wata matace da bazata wuce shekaru 40 ba, azaune kan wata luxurious kujera, tana sanye da lace red yasha dinkin stones kana ganinta kaga kudi ya zauna, jin karar saukar motoci yasa tadan mike, ba ayi ko minti biyu ba saiga wani babban mutun ya shigo da sallama, da fara’arta ta karaso har gabanshi sannan tace sannu da dawowa, kallonta yayi sannan yace ‘’yawwa’’ na sameku lpy, takawa
sukayi har sama wajen part dinshi, saidata taimaka mashi ya yi wanka sannan suka sauko kasa, dining direct suka wuce tayi serving dinshi abinci kala kala wanda tunda ta bude warmers din kamshi ya cike parlorn, abincin ya fara ci atsanake, jin takun tafiya yasa shi dagowa shida ita, wani saurayi ne yana sanye da kaftan brown hannunshi rike da waya kanshi yasha wani dan iskan aski na zamani, gefenshi wata chika ce da alamu daga daki suke ya fito rakata, saidaya rakata waje ya juyo ya shiga cikin sitting room, direct dining din ya wuce fuskarshi sakayau babu alamun jin kunya yace ‘’Amma mai kike dafa ne naji duk kin cika gidan da kamshi’’ ganin wanda ke gefen wadda ya kira da amma yasashi cewa ‘’ahh dad yaushe ka dawo daga US din ne’’ kallonshi yayi sannan yace Aman what is the meaning of that? Shi iskancin naka bai tsaya awaje ba har cikin gida? Ban hanaka yin komi ba amma ka daina kawo min any trash cikin gida,” sunkuyar dakai kawai yayi sannan ya kalli Amma yace ‘atura yar aiki ta kawo min part dina sannan ya fuce abinshi,’…. Allah ya shirya kawai amma ta furta sannan ta cigaba da abinda take…
Abinci ta shiryama aman sannan ta kira yar aikin gidan lantana takai mashi,Alhaji kabiru kuwa daya lura matar tashi Maryam bataji dadin abinda aman yayi ba sai yayi kokarin tausasa ta har ya samu ya sakko suka wuce part dinshi biya buqatarshi sannan ya fuce daga gidan domin attending wani aiki,..sabon wanka Amma tayi sannan ta sauko kasa har kitchen domin bata cikin matan da suke bari yan aiki suyi masu girki, suna cikin aiki itada yar aikinta lantana suka jiyo sallama daga parlor, saidata aika lantana domin dubo ko wanene tukunna kafin ta fito daga kitchen din, da fara’arta ta karaso parlor sannnan tace ‘’malam labaran yauma anzo kwasar gaisuwar ne’’ dariya wanda aka kira da labaran yayi sannan yace ‘’barka da fitowa hajiya Allah ya kara daukaka’’..wuri ya samu ya zauna suka gaisa sannan daga bisani ya fara Magana ‘’hajiya bazan taba gajiya da yi maki godiya ba da dawainiya, hajiya kinyi min rufun asirin da alokacin nafi buqata, Allah ya albarkaci zuri’ar ki nagode sosai’’….murmusawa tayi sannan tace haba mlm labaran nayi nayi dakai kadaina min godiyar nan yau shekara kusan bakwai Kenan, ko gajiya baka yi, ai duk mai Imani ya ganka alokacin dana ganka dole ya taimaka maka, Allah dai ya rufa asiri, kana dai shan magungunan ka ko?’’ kansa akasa yace ‘’nagode sosai hajiya inasha, yanxu ina dan tuna wasu abubuwan,alqalami ne dai idon na gani saina dunga fargaba amma shima cikin ikon allah komai zaizo da sauki nagode sosai, Allah ya kara arziki nagode sosai’’ nunfasawa tayi sannan tace ‘’ya gidan gonar kuwa? Nasa aman ya sa asiyo taki akawo’’ ..kallonta ya danyi sannan yace ‘’toh inaga ya manta kuwa domin abinda ya kawoni kenan’’… shuru ta danyi daman tasan aman bazai yi ba..dukda ba wani nisa gidan gonar nata yake ba daga gidan.. sallama labaran yayi sannan ya fuce, kitchen din ta koma tana yaba halayya irin ta labaran, tunowa da ranar data fara ganinshi tayi lokacin suna kan hanyar dawowa daga Bauchi ita da aman, yawo yake duk cikin jini daga gani kasan accident yayi gashi baya iya cewa komai dalilin juyewa da kwakwalwarshi tayi (memory loss) haka ta dauko shi tundaga
Bauchi har Abuja wanda aman baiso haka ba, ita ta taimakeshi har ya fara iya Magana daganan ta bashi amanar gidan gonarta yana kula mata dashi.
Amar kuwa Yau kwana biyu rabonshi da baccin kirki bayayi, yana jira order daga manyanshi domin kamo mutanen da yake hari, yasha wahala yau kusan shekara guda da dawowan shi dubai babu abinda yake sai binciki, ganin kamar ogan su general officer bai maida hankali gurin target dinshi ba yasashi kawai shiri domin gudanar da qudurinshi dukda hakan zai iya saka aikinshi at risk kuma bai fadama kowaba banda amintaccen guard dinshi m-5,tafiya sukayi mai tsayi sosai shida m-5 sun tsallake safari dessert inda suka samu makafa, shikanshi yasan it’s risky saboda basuda yawa amma dukda haka yaci alwashin kawo karshen su kobai samu ya kasha su duka ba atleast zai samu ya kama wasu daga cikin mutanen su, boyewa sukayi bayan sun saita bindigunsu, daga gefe kuma m-5 ya rike da cobalt bomb, sun dauki wajen mintuna ashirin kafin motocin targets din suka fara wucewa kusan guda