TSANTSAR BUTULCI Masifa Cikin Murmushi by BINTA UMAR ABBALE

Author :  BINTA UMAR ABBALE Category :  Romance

Chapter   4 / 6

9K to 12K   out of 17.9K words

rabo a duniya da lahira, muyi wa kanmu kyakykyawan zato, mu giji fad'ar abunda ba,tayi ba, muce anyi, A kwai ranar tsayuwa ta ranar mahashar,ranar da kowa yake ta kansaUwa Uba Miji mata "yaya, K'awa Aboki kowa na takansa, mun sanyawa Harshenmu linzami_


*Allah kasa mu dace*



_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_




*🅿13*


Kafin Alh Madu ya ankara matar tayi kan titi da gudu, bata kallon gabanta bare bayanta, wato mota k'irar marsandi tazo tayi gaba da ita,abunda yake hannunta ya gangara bakin hanya.

Salati Alh Madu yayi ya nufi inda matar take kwance tana nishi cikin jini,me motar kuwa yayi nasa guri, Hajiya Zulai ta futo daga mota da sauri,bakinta d'auke da Kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un.

Kukan jariri taji da sauri ta nufi inda take jin kukan ta dauke jinjiri sabuwar haihuwa,bata tsaya dubawa mace ko namiji kawai ta nan nad'e shi,ganin babu ko wando a jikinsa, kusa da mijinta ta matsa tana nuna masa jaririn dake hannuta, shi hankalinsa na kan matar, gashi sai nishi take,tana k'okarin mutuwa babu mataimaki, da sauri ya mik'e yaje ya bud'e but d'in motarsa ya ciro tayar mota,yazo ya kwance wacce ta sace ya daura wacce ya d'auko, da kansa ya zo ya kinkimi matarnan cikin jini yaje ya sanyata a mota,Hajiya Zulai taje ta shiga tana rungume da jariri sabuwar haihuwa,gwanin tausayi sai kuka yake, cikin tausayi da tu'ajibi ya kunna motar suka bar gurin,sauri kawai yake ya isa abuja, domin ya kai matar asibiti a dubata ganin yadda jini yake ta zuba ta baki ta hancinta,ga kanta ta fashe duk jikinta ya kurje,da alama batasan inda kanta yake ba, wani babban asibiti suka isa, da sauri ya futo daga motar ya bude gidan baya inda take kwance rai a hannun Allah,ya ciccib'ota, fuskarta kawai ya kalla ya tabbatar da cewar rai yayi halinsa,amma domin ya kara tabbatarwa yasa ya shiga da ita asibitin, ma'aikaita sai kai kawo sukeyi, suna ganinshi, da sauri suka k'araso, suka karbeta daga hannusa, kai tsaye, Emagency aka nufa da ita.


Duk wasu aune-aune sunyi sun duba ta sosai matar Allah yayi mata rasuwa mintuna talatin da suka wuce,haka suka futo suka sanar da Alh Madu, dama ya san haka, innalillahi ya furta a fili yace"Allah ya jikanki wannan baiwar Allah, wannan abunda kika bari kuma Allah ya rayashi ya albarkaci rayuwarsa,nan Alh Madu ya sanar da hukumar asubitin abunda ya faru dashi,da matar kuma ya nuna yana bukatar taimakonsu kan yadda za'ayi rayuwar wannan jaririyar da tabari ta inganta, shawarwari sosai suka bashi, kan abunda ya nema, suka d'ora baby kan madara irin wacce ta dace da ita, a takaice dai, wasu daga cikin ma'aikatan asubitin dasu akai jana'izar matar da ba'asan daga wace duniya take, Alh Madu yayi musu godiya sosai kuma ya sakar musu kud'i yadda ya kamata, sannan suka kama hanya suka bar asubitin, kai tsaye gida suka koma,domin ji yayi bazai iya zuwa wani guri ba, da jaririyar yarinyar domin wani irin so da tausayinta yakeji a zuciyarsa,yana tausayawa rayuwarta,

***
Kaf ya tara matansa ya sanar musu halin da ake ciki,to suma dake sun san meye rayuwa sun tausawa rayuwar Sumayya, Alh Madu yace"Bayaso su tab'a nuna banbanci tsakanin Sumayya da yayansu, duk suka d'auki Wannan alk'awari, Masu hankali daga cikin yaran gidan sune suka fahimci abunda yake faruwa, amma sauran k'ananun yaran murna sukeyi wai Hajiya Zulai ta haihu,Rab'ia sai murna take, ta samu k'anwa.

Alh Madu shine ya zab'a mata suna Sumayya, Hajiya Zaliha ta cigaba da rainonta cikin kulawa,itama haka kawai take jin tausayin Sumayya ita kuma haka zata taso batare da tasan suwaye iyayenta,menene tushenta wannan abu na d'aga mata hankali.


*Wannan shine tarihin Sumayya*

Shida da rabi na yamma "yan makaranta suka fara dawowa, Alh Madu na zaune kan wata kujerar k'arfe wacce yake zama yana shan iska a k'ofar gidansa yana kallon hanya, da yara " yan makaranta, Sumayya na zaune kusa dashi da goro ba,a hannuta tana ci, ko kishin kanta batayi,ganin yadda yara suke ta wucewa ko wanne sanye da uniporm na makaranta, can ya hango iyalinsa sun tawo reras da su abun sha'awa, ya kalli Sumayya, a tausashe yace" Yanzu Sumayya bakya yiwa kanki fad'a ba, dubi "yan uwanki fa,suna zuwa makaranta ke kink'i kin tsaya wasa, ko kinaso in had'aki da Yayanku ne"?

Girgiza kai tayi,tana cigaba da cin gorobar ta,yace" To indai kina so mu shirya dake,kar in k'araji anyi rigima dake, gurin zuwa makaranta,lokaci na yi kiyi himma,kinji ko, in naga kina maida hankali ke zan fara kaiwa Umara"

Dariya take sosai ta rik'e hannusa cike da k'uruciya tace"Don Allah da gaske kake Babanmu"

Fuskarsa a sake yace"Kwarai kuwa ke dai ki maida hankalinki kan karatu ki gani"

Tace"Insha Allahu zanyi,amma zaka bani kud'in makaranta wanda yafi nasu Ummu da Rabi'a ko"?

"Ke zan bawa a hannuki ma,in zaku tafi, makarantar sai ki rarraba musu"
Jin abunda yace ne yasa tai ta murna da dariya.

Su Rab'ia duka k'araso tsugunawa sukai dukaninsu sukace"Babanmu Sannu da hutawa"

"Yawwa sannu ku, Rabi'a kun dawo"
Suka amsa da "Eh mun dawo Baba"?

Yace" Allah yayi muku albarka,to ku shiga gida"



Har sun wuce, Suwaiba ta dawo da baya,tana kallon Sumayya dake musu wani irin kallo,yace" Ke Sumayya malam Mubarak yace"Wallahi zaku gamu ne, yana lissafa iya adadin fashin da kikayi, sai ya zane miki jiki"


Cikin tsiwa Sumayya tace" Eh ai dama kune masu zugashi ya dake ni, gobe zanje,kuma Babanmu ne zai kaini sai inga ta inda zai dake ni"

Suwaiba tace"Oho miki dai!ke kika sani"

Sumayya ta mik'e da sauri jikinta na b'ari tace"Babu ruwanki dani,tunda dai ni kinga ban kulaki ba,ko"?

Alh Madu yace"Ke Suwaiba wuce gida,bana san tsokana" Suwaiba ta wuce gida,tana mamakin masifar Sumayya daga magana ta mik'e tana k'okarin kamata da kokawa"

Bayan tafiyar Suwaiba Sumayya ta koma ta zauna,tana zumb'ura baki tace"Babanmu gobe ka kaini makarantar da kaina idan ba haka ba,nasan muguntar Malam Mubarak wallahi"

Alh Madu Yace"Allah ya kaimu lafiya,ai dai kinyi min alk'warin baza ki k'ara fashi ba ko"?

D'aga kai tayi
Yace"Yawwa"

Suwaiba kuwa
Dai-dai soro na biyu suka had'u da Habibu shi da Khamis zasu futa,ta durk'usa har k'asa ta gaishe su, suka wuce,ita kuma ta mik'e ta shiga Gida.


Abun mamaki suna futa ya ga Sumayya na gwagwuyar goroba sai kace wata akuya,babu kamun kai,a tare da ita, still haryanzu,Wannan kayan ne na jikinta Wanda yace ta cire, wato bata ciresu ba,saboda tana ji da taurin kai,lallai dole yayi maganinta.

Tana ganinsu ta d'suke kanta,domin bata so su had'a ido da Habibu,shi kuwa Khamis sai wasa yake mata,ta sha kunu,tak'i kulasa

Shima bai kalli inda take zaune ba.

"Barka da yamma"
Yafad'a yana mik'awa mahaifin nasu hannu"
"Barka ka dai"
Alh Madu ya fad'a,Khamis ma gaisawa sukayi cikin mutumci, suka wuce majalisar su.





Karku manta da cewar Wannan book din na kud'i naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nab.
08089965176
07084653262
[22/08, 14:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿14*





A na kiran sallahr magariba Alh Madu ya shiga gida domin d'aura al'wala, Sumayya na bayansa sai kace jela, Alwala ya d'aura ya futa zuwa masallaci, Ita Alwalar ta d'aura, ta shige d'akinsu babu wanda tayi wa magana a gidan.

Bayan ta idar da sallah ne ta kwanta kan dadduma bacci na neman d'auke ta.

Hajiya Zulai ta shigo d'akin, ganinta a kwance kan hanya tace"Ke ki tashi ki ci abunci sai ki kwanta, magariba nayi zaki hau bacci sai kace wata kaza"

M'ikewa zaune tayi, tana mutsika ido, Hajiya Zulai ta d'auki abunda zata d'auka ta futa,Sumayya ta mik'e tabi bayanta.


Habibu ne ya dawo gidan, yana rarraba ido neman Sumayya yake,da bai ganta ba, a tsakar gidan, sai ya nufi d'akin Hajiya Zulai sukayi kicib'us da ita, ta futo daga d'akin, Sumayya na bayanta.

Babu abunda yace Kawai ya kamo hannu Sumayya, ido ta bud'e jin an mata rik'on tsauri, Yayanmu ta gani yana janta, bud'e baki tayi zata kurma ihu ya rik'e bakin.



Hajiya Zulai tace"Wato da kaga Alh ya futa shine ka dawo domin kaci zali ko"


Shiru yayi yaja Hannun Sumayya tana turjewa ya kaita d'akin.

Girgiza kai Hajiya Zulai tayi kawai tai tafiyarta.

"Wayyo Hajiya ta"
Abunda Sumayya take fad'a kenan.

"Babanmu kazo ka taimake ni"

Tsawa! Ya buga mata, yace"Rufe min baki,ko in ci Ubanki"

Tsitt!! Sumayya tayi tana zare ido,ga d'akin da duhu Hajiya bata kuna fitila ba.
Zatinsa kawai, take gani a d'akin, cikin tsawa yace"Cire wannan kayan na jikin ki,kiyi shirin makaranta"


Jikinta na kyarma ta fara cire kayan jikinta,dake da duhu a d'akin ba sosai yaga jikinta ba,yana tsaye da fuska a murtuke

Ta bud'e sif d'in kayansu ta d'auko doguwar riga , ta zura da sauri ta d'ora hijabi a kai, yace"Wuce muje"
Simi-simi tayi gaba yana bayanta suka, Tsayuwa yayi tsakar gidan, yana kallonsu Rabi'a suna cin abunci Yace" Ke Suwaiba da kungama cin abunci, ku tafi makaranta tare,in ta gudo ko tayi barci, a makarantar ku fad'a min"

Suwaiba tace"To" fucewarsa yayi daga gidan,dama abunda ya dawo dashi kenan.

Hajiya Gaji ta zuba mata abunci ta zauna tana ci tana gyangyad'i domin baccin ya hau kanta sosai.

Kad'an taci ta cire hannuta, taje ta wanke, sai zumb'ura baki take.


Babansu yaji dad'i da yaganta cikin a yari zasu tafi makaranta, ya basu kud'i duk da cewa ta magariba ce, in sun dawo hanya suna tsayawa siyi siye-siye irin nasu gyad'a me gishiri da Aya me sukari.




Rab'ia na lure da Sumayya sai gyangyad'i take sam bata fuskanci, karatun da akai ba,haka aka tashi daga makaranta, Suwaiba ta rik'e mata hannu dan kar ta fad'i.

Har yanzu Alh Madu na zaune a inda yake, yanzu suna tare da wani mak'ocinsa suna hira.

Yaga ana rirrik'e Sumayya tun daga nesa,suka k'araso, inda yake, yace" Yaya kuke rik'eta ne"
Ummulkairi tace"Bacci takeyi a hanya"
Dariya Alh Madu yayi yace"Sumayya kenan, to maza ku shiga ciki kar ta fad'i"

Ciki suka shiga, Alh Madu suka cigaba da hira da mak'ocinsa.


Duk suna zaune tsakar Gida, suka shiga, Hajiya Zulai tace"Nasan za a rina dama,ai in bacci ya hau kanta, sai tayi ko a ina ne, Hajiya Tabawa tace" Ai kuwa dole ko zata dunga baccin a makaranta ta dunga zuwa sai ta saba"

Dariya suke wa Sumayya sosai.
K'asa ta kwanta,hijab d'in jikinta ma Rab'ia ce ta cire mata.


Hajiya Gaji tace"Ai saboda baccin da take da wuri shiyasa take riga kowa tashi da wuri, gashi abunci da na zuba mata ma kad'an taci"

Hajiya Zulai tace"Sai da safe kuma ta tashi da yunwa"

Haka suka cigaba da hirarsu cikin fahimtar juna har wajan goma na dare, daga bisani sukayi sallama da junansu ko wacce ta shiga d'akinta domin shirin kwanciya.




Karku manta da cewar wannan littafin na kud'i ne naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan.
08089965176
07084653262
[23/08, 13:00] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿15*




Washe gari da wurwuri Sumayya ta tashi daga bacci ,domin ko irin baccin nan na bayan sallah Asuba bata koma ba, shirin makaranta takeyi, cikin walwala,yau za'abata kud'inta a hannuta ta siyi abunda ta ke so, yau me alawar madara za tayi cini ki a gurinta, tsaf ta shirya, hatta da takalmi da safa ta saka, su Suwaiba sai dariya suke mata, tana kallonsu tai musu banza,domin tasan tayi musu wani abun, Yaya Habibu dukanta zai yi, ba tare da ya bi ba'asin waye me tsokana a cikinsu ba,amma dole sai ta gayawa Babansu domin yaja musu kunne babu ruwansu da ita.

Kai tsaye sama ta nufa gurin Babansu, tana taka matattakala ta uku, Habibu ya futo daga d'akinsa, yana sanye da riga da wando ga jere irin na "yan ball, wuyansa rataye da wani k'aramin towol, k'afarsa takalmi ne irin na " yan ball, da'alama motsa jiki zai futa.

Kallo guda yayi mata ya kauda kansa, ya fara saukowa.
Sai ta ja ta tsaya, tana jira ya sakko sai ta hau, hannunta ta zura a bakinta, as'usul ta fara cin farce kamar yanda ta saba in ta ganshi.

Wannan d'abi'a da take in ta ganshi yana mugun b'ata masa rai,yana zuwa dab da ita,yasa hannu ya buge hannuta dake bakinta, fuskarshi babu walwala,yace"Wallahi duk sanda kika k'ara ganina ki ka saka hannu a baki kina cin farce, sai na sa, d'an Yaya me yankan farce, ya cire miki farcen gaba d'aya, sai inga ta iskanci, shashasha kawai"


Wasu hawaye ne suke k'okarin zubo mata,taji haushin abunda yayi mata,k'okarin danne hawayen take tana son hanasu su zubo,bakinta na rawa tace"Yayanmu ina kwana" domin tasan wata masifar ce idan bata gaishe ba"

A banza ce ya amsa ya wucewarsa yana wata tafiya irin ta "yan kwallo.


Sai da ya futa, ta fara goge hawayen da ya ke ziraro mata,tana jin wata irin tsanar sa a zuciyarta, duk gidan babu wanda yake kyararta gami da hantararta sai shi,duk sauran " yan uwansa maza suna mata wasa ban dashi,Yaya Auwal har yawo yake tafiya da ita, a cewarsa,duk tafi sauran kyau ita ta shiga mutane ce.





Babansu na ganinta ya saki fuskarsa sosai, yace"Lallai yarinyata me jin magana ce, Allah yayi miki albarka"

Tsuguwa tayi kusa dashi tana gaida shi,ya amsa da fuska a sake.

Nazarin ta yake, yaga fuskarta babu walwala yace"Waye ya tab'a min ke da safiyar nan"?


Shiru tayi ta zumb'ura baki,domin babu halin tace"Yaya Habibu ne, tasan fad'a zai yi masa, shi kuma Yaya Habibu, zai iya dukanta a kan haka.


Girgiza kai yayi yace"Rabo dasu kinji ko,kinga je ki d'auko jakar alawa,cikin wancan kwalin, ki tafi da ita makarantar,ki bawa duk wanda kike so."


Da sauri ta mik'e taje ta bud'e kwalin da yake nuna mata,ta ciro jakar Alawa gudu,ta farke ta ciri biyu ta b'are, ta sa abakinta,tana tsotsa.


Dariya Alhaji Madu yasa yace"Uwar shan zak'i kenan, nasan dai babu komai a cikin ki,tunda safiya ce,yanzu kije ki karya tukkuna,sai ki sha alawar amma kar ki k'ara sha yanzu kar ta k'ulle miki ciki."


Gyad'a kai tayi, tace"Babanmu bani kud'in to" Wata durowa ya bud'e ya ciro gudar dari biyu,yace"Gashi ke ki d'auki naira Hamsin, d'ari da Hamsin d'in kuma sai su raba, sauran "yan uwan naki"


Wannan magana da yayi, itace ta tuno mata da bashin, da take bin Rabi'a shaf! ta manta, Lallai kuwa yau zata bata kud'inta wallahi ko ta tona mata asiri,tunda itama dariya suke mata.


Karb'ar kud'in tayi daga hannunsa ta mik'e tana godiya,shi kuma ya nai musu fatan dawowa lafiya, har ta bud'e k'ofar d'akin zata futa, sai ta tsaya, tana kallonsa tace"Babanmu "Za'ai min dukan fashi fa,kace zaka kaini da kanka,ka basu hak'uri"


Girgiza kai yayi yace"Kije kawai, jiya na tura Yayanku Habibu yayi magana da malaman makarantar"

Dariya tayi cike da farin ciki ta futa daga d'akin.


Tana sauka k'asa ta zura jakar alawar da kud'in a jakarta, ta nufi kicin domin d'auko kayan karin kumallon ta.


Wani irin kunun gyad'a ne fari tas dashi ya sha madara,sosai sai k'osai jazur dashi,yaji attaruhu da albasa,ta zauna babbar rumfarsu ta fara shan abunta.


Sauri-Sauri ta kammala karyawa ganin duk sun shirya, ita kad'ai kawai suke jira.

Sallama sukaiwa iyayen nasu suka tafi, Suwaiba zata hau sama domin karb'o kud'in makaranta, Sumayya tace"Ke Suwaiba ga kud'in nan"

"Au! Ashe kin karb'o"
Suwaiba ta fad'a.


D'aga kai Sumayya tayi suka futa.







Karku manta da cewar wannan littafin na kud'ine naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[23/08, 16:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿16*




Sai da aka futo break, Sumayya ta fasa d'ari biyun ta d'auki naira hamsin d'inta,ta tafi ajin su Rabi'a, tana shiga ajin nasu,ta rik'e k'ugu ta tsaya tana neman inda suke da ido. Wata k'awarsu ce ta hangota, ta tab'o Suwaiba da hannunta "Suwaiba ga wannan k'anwar taku nan"

Suwaiba ta hango Sumayya, bakin k'ofar ajinsu tana harare-harare, tasan halin tsokanar Rabi'a zata iya tsokanar wata cikin ajin ko tayi mata rashin kunya,kuma gashi duk ba sa'ointa ba ne, Mik'ewa tayi ta nufi inda take.

Zumb'ura baki Sumayya tayi tana mik'a mata kud'in tana fad'in "Ga kud'inku nan, na d'auki cikon d'ari ta, wacce nake bin Rabi'a"


Suwaiba ta karb'i naira Hamsin a hannuta tana juyawa cikin mamaki tace"Bafa na san neman rigima ke Sumayya,ai ba Rabi'a ce kad'ai me kud'in ba, da zakije kice kin d'auki kud'in ki"

Sumayya na k'okarin futa daga ajin tace"Oho muku ni dai na d'auka, ai sai da na fad'a miki kece shaida,kina kallo bata bani kud'in ba, saboda na manta,to yanzu na tuna, kuma na d'auka"

Sakin baki Suwaiba tayi kawai tana bin ta da kallo har ta futa daga ajin nasu, Malamin Hausa ne ya shigo, tayi saurin koma wa ta zauna.


Bayan ya futa suka futa break, Suwaiba ta fad'awa Rabi'a abunda Sumayya tayi musu, haushi ne ya kama Rabi'a a fusace ta nufi ajinsu Sumayya.

Tana zaune tsakiyar k'awayenta,suna hira irin tasu ta k'wailaye sai dariya sukeyi, Sumayya tace"Ke ikilima naji fa ranan Yaya Rabi'a na cewa wai da dad'i abunda kike fad'a, kuma ba iskanci ba ne"


Ikilima tace"Meye ba iskanci ba? Sumayya ta mak'e murya tace"Tsotsar bakin juna,tsakanin mace da namiji"

Ikilima tace"Wallahi iskanci ne kuma k'azanta ce, haka kawai sai in tsaya namiji na tsotsar bakina,tab d'ijam"
Suka kwashe da dariya har da tafawa, Abashiyya tace"Wallahi naji

4 / 6