TSANTSAR BUTULCI Masifa Cikin Murmushi by BINTA UMAR ABBALE

Author :  BINTA UMAR ABBALE Category :  Romance

Chapter   3 / 6

6K to 9K   out of 17.9K words

yace" Baba mungode da wannan karamcin naka, Allah ya kara girma yaja kwana, da wannan nake Neman alfarma a barni in zauna nam domin in cigaba da kula da dukiyarnan ganin babu wani tsayyaye"

Alh Madu yace"Wannan shawarar taka tayi kyau nima sai da nayi tunanin haka, dama dole yanzu ka tsaya ka kula da "yan uwanka gami da mahaifiyar ka, na amunce da maganar ka, saboda haka duk wani Abu da kake bukata kazo la tunkareni kar kaji fargabar komai har yanzu kanan a matsayin Habibu a gurina"

Hajiya Laure taita godiya sauran "Yayanta suma sunayi.
Haka
Alh Madu ya tattara Iyalinsa suka tafi yana kewar Abokinsa Alh Auwalu





Karku manta da cewar wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[19/08, 12:34] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿10*





Wannan shine cikkaken tarihin Khamis.
Yanzu ma ya dawo daga Aba ne,a cewarsa yaje sarin takalma sai ya fake da yawonsa ya biya b'ukatarsa da mata, shi mace ko arniya ce mutukar tayi masa sai ya kwanta da ita, duk wannan mugayen halayen nasa abokinsa bai sani ba, saboda sunyi nesa da juna yanzu,sai dai idan d'aye ne ya kai wa d'aya ziyara, haka ma Alh Moddobo kullum cikin ganin girman Khamis yake gami da nagartarsa.




Sumayya ko tana sauka k'asa ta manta abunda ya faru tsakaninta da Khamis d'in ta cigaba da sabgoginta

Kwanan Khamis uku da zuwa Habibu yayi Waya yace"A tareshi a airport misalin sha biyu na rana, gida ya rud'e da murna, yara da manya,hattaa da samarin gidan murna suke da dawowarsa, banda Sumayya duk ta b'ata rai tayi kicin-kincin da fuska duk inda taje ta zauna taji ana zancan dawowarsa gida sai ta bar gurin,k'arashe ma da taga ba'a ta ita,sai ta shig'e k'uryan d'akin Hajiya Tabawa babarsu Suwaiba kenan tayi kwanciyarta.
Karkuce duk tsawon wannan kwana ki ukun Khamis be fasa tab'a jikin Sumayya ba,har indai yaga babu idanun jama'a a guri sai ya san yadda yayi ya tab'a wani b'angare na jikinta.


Umulkairi ce ta shigo da gudu d'akinsu ta buga tsalle ta haye gado, sai murna take,a fili take cewa"Yayan mu zai dawo, nasan tunda naci jarrabawa inada kyauta ta mussaman,wayyo dad'i kashe ni in huta"

Sumayya ta k'ulu iya k'uluwa,juya baya tayi taja tsaki gami da cewa"Aikin banza Aikin wofi kawai"

Umulkairi ta juyo tana kallonta cikin mamaki tace"Dama kina cikin d'akin nan"?

Banza Sumayya tayi mata, Umulkairi tace"Ni kike zagi ko Sumy,ai babu komai nagode Allah,watan cin ubanki ya kama,yaya ya dawo wallahi sai na fad'a masa irin rashin mutumcin da kikayi"


A fusace!Tace"Ki fad'a masa mana don. Allah in kin fad'a masa kar ya barni da raina,ko an fad'a miki tsoransa nakeji kamar yadda kuke tsoronsa, k'arya kike"
Sumayya ta k'arashe maganar cikin raini


Umulkairi ta fidda hannu ta tsinka mata mari a fusace!tace yayan namu shine yake miki k'arya lallai Sumy baki da Hankali"
Da hauka Sumayya tayi kan Umulkairi da duka,dama a fusace take,jin Umulkairin tana murna taci jarrabawa,ita bataci tasan dariya zasuyi mata suyi mata gwalo in yayi musu kyauta shiyasa ta fusata,takama Umulkairi da kokawa fad'a suke sosai,Umulkairi tafi Sumayya k'arfi kuma dama ta girme mata da shekaru hud'u,ita Sumayya mugun girman jiki ne da ita,gashi babu k'arfi, Umulkairi ta yar da ita k'asa, tana niyar gudu itama ta rik'e mata k'afa d'aya ta fad'i k'asa tayi saurin mik'ewa ta haye ruwan cikinta tana duka kamar wata "yar dambe, Umulkairi k'okarin kwatar kanta takeyi,Sumayya duk ta yakushe mata fuska,duk wasu dabaru na fad'a Sumayya ta sani, dak'ay Ummu ta cilar da Sumayya k'asa ta rugu da guda tana dariya,gami da haki!dad'i take shegiya sai kace mage duk ta ya kushe min fuska"
Da gudu Sumayya ta biyo bayanta tana zaginta tana kuka,gashi dai itace taci galaba kan Ummu d'in amma kuka take,Mamansu ta tare ta tana tambayarta abunda ya faru,,k'okarin funcikewa take daga hannun Maman tana son kaiwa Ummu duka,Mama tace"Ke Ummu me ya had'a ku ne, wallahi na tsani tsokanar da kuke mata"

Umulkairi tace"Wallahi Mama itace me tsokana haka kawai ta hau zagina tana zagin yayanmu"

Cikin mamaki Mama ta kalli Sumayya tace"Hakane maganar ko kuwa "

Shiru Sumayya tayi tana share hawaye.
Hakan ya tabbatar wa da Mama gaskiya ne, b'ata fuska tayi tace"Kul! kinji na fad'a miki idan zaki rashin kunyar ki, ki tsaya idan kike, dan baki da hankali Habibun kike zagi, kar in k'araji,kinji ko baki jiba"?
Kuka Sumayya ta fashe dashi,Mama ta shige d'aki abunta,Umulkairi ma tafiyarta tayi,ta cigaba da sabgoginta, Sumayya ko can saman babansu tayi tafiyarta ta kwanta tana kuka har bacci ya d'auketa.

*******
K'arfe goma sha biyu da rabi na ranar Habibu ya sauka a gida, "Yan uwansa duk sun baibaye shi suna gaisawa cike da farin ciki, yake amsa musu, d'aya bayan d'aya ya shiga d'akin iyayen nasa suka gaisa,ya fito yana kallon " yan uwan nasa mata kowacce na zaune sunyi shiru, kallon Rab'ia yayi yace"Ina Sumayya take"

Inda-inda ta farayi domin bata san inda take ba, Umulkairi tace"d'azu tana nan, inaji tana sama gurin Baba"

Habibu yace"Baba,yana waje can na baroshi yana hutawa a waje"
Hajiya Gaji tace"Tana sama tana bacci, d'azu da na hau na ganta,indai ba ta tashi ba"

Shiru sukayi, Khamis ya mik'e da sauri ya nufi hanyar futa, shima Habibu mik'ewa yayi ya kalli "yan uwan nasa yace" Ku bari inje inyi Wanka in huta tukkuna zan zauna da kowacce a cikinku"

Hajiya Gaji tasa dariya, tana fad'in lallai kuwa yau zamu sha kallo da dariya"


Ya k'okarin tafiya yace"Duk wacce batayi abun arzik'i ba a makaranta ai ta san sauran, babu duka babu zagi sai dai taga anayi"
Yana gama maganar ya futa daga falon d'akinsa ya nufa.

Khamis kuwa da yayi saurin mik'ewa ya nufi sama,kai tsaye d'akin Baba ya bud'e ya shiga . aikuwa Sumayya ya gani kwance kan kafet din dake shimfid'e a kasa tana bacci sosai, dake dogon Wanda ne a jikinta da k'aramar riga me dogon hannu, duk sai hallitun jikinta suka bayyana, jikinta ya shika bacci take sosai, kura mata ido yayi yana mata kallon k'urulla wata irin sha'awarta tana bijoro masa, zuciyarsa na ingizashi kan yaje yayi mata abunda ya saba,yanzu tunda bacci take,ko ya samu ya rage rad'ad'in sha'awar da yake ji, motsi yaji alamun za'a hau sama, yayi saurin dawowa hankalinsa,jin ana tab'a kofar d'akin yasa ya wayance da zuwa gaban tv ya tsuguna yana duba kasa-kasai.Habibu ne ya shigo d'akin, suka had'a ido dashi, yace"Kai dama nan ka shigo" Cikin wayancewa Khamis yace"Eh mana ina duba kasat ne, yau kallon hausa film nake sha'awa" Tab'e baki Habibu yayi yace"kallo baya isarka kai kam,ina fata ba'anan zakayi ba,kar ka tashi Sumayya daga bacci"

Khamis yace"Banan zanyi ba, yanzu zan shigo muci abunci ai"

Futa Habibu yayi daga d'akin, Khamis ya mik'e shima yana waiwayen Sumayya, har ya futa yana cizon ya tsa.







Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne, naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan.
08089965176
07084653262
[20/08, 16:54] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

e: ⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿11*



Habibu na shiga d'akinsa yayi shirin yin wanka, wani katon towol ya d'aura a jikinsa ya shiga toilet ya wanke jikinsa tas ya futo ya tsaya gaban dressing miroow yana taje sumarsa ya sanya mata mayu ka, dake yanayin zafi bai shafa mai ba, turare kawai ya fesa a jikinsa, ya sanya wasu Jesi kaya irin na "yan ball kayan sun masa kyau sosai, da yake yana bala'in son kwallon k'afa shiyasa yake yawan sanya kayansu, yana son " yan k'ungiyar arsenal in kaji ana musu dashi akan ball sai ka rik'e baki,kallo in ba na ball ba babu wanda yake tsayawa yana mayar da hankali a kansa,sai dai ko labarai.


Khamis ya bishi da kallo lokacin da yake k'okarin zama kusa dashi,yace"Shikkenan an dawo fagen fama, za'a cigaba da fafatawa ko" Habibu yasa dariya gami da bashi hannu suka tafa yace" To me za'a fasa, ai yau sai na futa majalisa na buwaye su"

Khamis yace"Kamar ka sani kuwa d'azu da safe da naje, Lurwanu yake tambayar ka"
Habibu yace"Gani nadawo ai,zamu had'u da juna"

Hira suka cigaba da yi irin ta abokain da suka yarda da junansu, sukaci suka sha suka k'oshi, Habibu ya mik'e kan doguwar kujera yana lumshe ido,bacci na fuzgarsa kad'an shi kuma Khamis kaset d'in da ya d'auko ya sa a DVD ya fara gani,yana cin dariyar d'an Rabilu musa d'an ibro, cikin kaset d'inshi na *Ka kiyayi me nema* ganin film d'in dan Ibro ne yasa Habibu mik'ewa zaune yayi yana dariya duk rashin son kallo irin nasa, indai film din Ibro ne, yana kalla,dan yaci dariya.



Giftawar Sumayya ya gani tana kokarin sauka kasa sai faman sosa soshe take, saura kadan ta fadi saboda idanunta a rufe suke rike karfen barandan tayi ta bude idonta kadan tana kallon hanya,

Ransa ne ya b'aci ganin irin kayan da suke jikinta riga da wando ne duk sun matse ta sun futo mata da shatin jikinta gashinan, shi kuwa Khamis kallonta yake kamar tsohon maye, Tsaki yaja ya had'e fuska tamau ya kira sunanta a kausashe! Gabanta ya fad'i jin muryar Yayarmu sai tayi bude idon nata gaba d'aya tana kokarin sauka kasa da sauri,


Da k'arfi yace '' Sumayya mutukar kika sauka kasa baki kiran da nake miki ba sai na b'ata miki rai!



Tsayawa tayi tana sosa kai kamar mara gaskiya ta koma da baya simi simi hannuta ta sa abaki tana cin farce taje ta tsuguna gabansa, baki na rawa tace'' Yayanmu ina wuni an dawo lafiya''?

Harara ya banka mata. Batare da ya amsa mata gaisuwar taba yace, '' Dan ubanki ban hanaku sa kananun kaya ba? wato kece me kunan k'ashi ko'' Yafad'a yana murd'e mata kunne. Khamsi ya b'ata fuska yace'' Wanan cin zali ne kawai ka kama yarinya kana murd'e mata kunne duk abunda tayi k'uruciya ce in ta girma zata daina''



Babu abunda yace wa Khamis d'in ya cigaba da murde mata kunne. Yace '' Kika sake na sauko na same ki da wannan kayan a jikinki sai na zane ki wallahi kin san zan iya ko''

D'aga kai tayi cike da tsoro idanunsa ta kalla ta gansu jazur tasan bashi da imani dukanta zaiya. rank'washi ya buga mata a ka cikin tsawa yace'' Tashi ki bani guri munafuka kawai. Zan zo ai in tambayi duk abubuwan da kikayi da banan''

Da sauri ta mike daga kusa dashi ta ruga a guje, tana sauka matattakalar farko ta kurma ihu! sosai da gudu ta afka d'akin Hajiya Tabawa tana kuka kamar wacce a kaiwa dukan tsiya




Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira d'ari ga me bukata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[20/08, 21:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________






_*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_



*🅿12*





Hajiya Tabawa na tsaka da ninke kayanta na sawa taji ihun Sumayya, girgiza kai tayi kawai ta cigaba da nin ke kayanta tana fad'in, '' Ke kam Sumayya naga ranar da zaki daina shagwaba wallahi.ke kenan kuke-kuke bakya gajiya'


Cikin kuka Sumayya tace' Hajiya yayanmu ne ya rank'washe ni akaina kin san kuma babanmu ya hana a tab'amin kai saboda ciwon kan da nakeyi wallahi yanzu ma kaina ya fara ciwo'
Ta karashe maganar cike da shagwaba da sangarta.


Tab'e baki Hajia tayi tace'Wannan ciwon kan naki ai na sangarta ne,haka kawai sai kice baza ai miki kitso ba in aka tab'a kan ko yaya ne sai kice kanki na ciwo sai kace wata mai iska'

Kuka Sumayya take sosai cikin zuciyarta tana wa Habibu Allah ya isa domin babu hali ta zageshi gaban Hajia tasan halinta tana da zafi zata iya kai mata duka.


Babansu ne ya shigo gidan yana sanye da wani yadi fari tas anyi masa d'inkin babbar riga kanshi da hula dara irin ta mutan da, hannushi rike da carbi fari tas dashi, tunda soran farko yake jiyo kukan shalelensa dan haka da sauri ya k'arasa shiga cikin gidan da sallama a bakinsa.


Hajia Gaji na zaune kujera tana gyara kayan miya ta amsa masa.



'Alh Sannu da shigowa' Hajia Gaji tafad'a tana gyara zamanta


Amsawa yayi yace'Kukan me Sumayya take ne, tun daga soro nake jin kukanta.

Hajia Gaji tace' Yanzun nan ta sauko daga sama, bacci take tun d'azu amma inajin ita da Habibu ne, ai gwara da ya taso ta taci abunci ta tafi makaranta duk "yan uwanta sun tafi tun d'azu"


Alh. yace"Shikkenan sarkin cinzali ya dawo zai tasa min yarinya a gaba da duka kamar wanda ya samu jaka, bari zai shigo y same ni ai"


Hajia Gaji shiru tayi kawai tana d'an murmushi tasan halin fad'an mijinsu a kan Sumayya kwata-kwata baya son jin kukanta.


D'akin Hajia Tabawa ya nufa inda yake jiyo kukan Sumayya.

D'aga labule yayi ya shiga dakin cikin fad'a yace"Kina ji yarinyar nan tana kuka kinyi burus da ita ko"


Hajia Tabawa tace"Nayi -nayi tayi shiru taki yi alh kasan kukan Sumayya babu mai rarrashinta sai kai"


Da sauri Sumayya ta mike daga kan gadon taje ta rike hannun baban nasu tana fada masa irin cinzalin da Habibu yayi mata harda sharri ciki


Hannuta ya rik'e suka futa daka dakin. Sama suka nufa suna tafe yana rarrashinta kamar k'wai
Yace "Ki share hawaye ki zan samu Habibu in ja masa kunne kan kar ya k'ara dukanki"



Shiru tayi tabar kukan suka haura sama, har yanzu d'akin Habibu a bud'e yake yana hango hawowar babansu da Sumayya ya mik'e zaune sosai yana me k'ara daure fuskarsa saboda yasan yanzu zai tuhume shi kan me yasa ya daki Sumayya, aikuwa dai-dai k'ofar d'akinsa ya tsaya yana ya mutse fuskarsa ya kalli Habibu da b'acin rai a fuskarsa yace" Kar ka kara dukan ta har ka koma inda ka futo.shikkenan kazo gida bata da kwanciyar hankali sai duka da kyara me ta tsare maka ne"?


Gyaran murya yayi yana d'an sunkuyar da kai yace" Alh wannan yarinyar bata da tarbiya duba fa ka gani irin tufafin dake jikinta, tuntuni na hanasu sakawa sauran sun daina ita tak'i jin magana, saboda tana samun d'aurin gindi a gurin ka, tarbiyarta tana iya lalacewa"



Cikin fad'a Alh. yace"kafi ni ido ne, da har zakace min in dubi tufafin dake jikinta yarinyar guda nawa take da gar kake min wannan zancan, na fad'a maka kar ka kara dukanta"


Habibu ransa ya b'aci jin abunda mahaifin nasu yake cewa kan Sumayya wannan na nuna cewar gata zai yi sanadiyar lalacewar ta, wanda yana ganin haka ba gata bane abunda yake nunawa yarinyar tunda amanar Allah ce ita, Ubangiji yace " yayanku amanarku ne kuma amana ta ne,zan tambaye ku ranar lahira to balle kuma Sumayya da take marainiyya wacce bata san uwarta da ubanta ba bata san kowa nata ba a sali ma batasan wacece ita ba ita dai kawai ta so cikin gata da kulawa gami da soyayyar iyaye biyu wato Alh MADU da HAJIYA Zulai matarsa ta uku kenan.



_*Wai shin wacece Sumayya?*_

SHEKARU GOMA SHA BIYU DA SUKA WUCE.

ALH. Madu ne tare da matarsa Hajiya Zulai suna tafiya cikin mota hanyarsu ta zuwa abuja shekaru goma sha biyu da suka wuce.
Akwai wani kamfani da k'warori suke bude a abuja ake har kar taklma a wancan lokacin. suka nemi sa hannun ALh MADU saboda shaharasa a duniya ta fannin kasuwanci ko wane iri ne, babu wani b'ata lokaci ya amunce musu ya zuba dukiyarsa aka fara aiki sosai ake samun albarka, ba sosai yake zuwa ba sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa.

Kwatsam!ranan ya shirya tare da matarsa suka nufi abuja cikin motarsa kirar toyota wanda a lokacin sai wane da wane.

Dake futar asuba sukai shiyasa suka yi sauri sun wuce kaduna kad'an dai-dai wani k'aramin gari motarsu ta tsaya taya tayi faci. Alh Madu ya futo da sauri yana dubawa lokacin shida da kwata na safe gari ya soma yin haske. d' agowar da zaiyi kawai ya hangi wata ba fulatana ta yanko daga wani daji da gudu jikinta sanye da kayan sak'i irin nasu hannuta nan nad'e da wani abu ta rungume sai gudu take.








Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira dari biyu ne ga me bukata ga numbar nan
08089965176
07084653262
[21/08, 17:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

⚱⚱⚱⚱
_*TSANTSAR BUTULCI*_
⚱⚱⚱⚱


_*NA*_
_BINTA UMAR ABBALE_
*®BINTUBATULA👄*


_*MARUBUCIAR*_

```NANA KHADIJA```
```YARO DA KUDI```
```GIMBIYA BALARABA```
```LOODING......```
_*TSANTSAR BUTULCI*_




_*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_
____________________
_*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_
_______________________




_Mu fad'i alkairi ko muyi shiru,mu kiyayi aibata wani ko cin zarafin wani,ba tare da hakkinsa ba, mu kintsa harshen mu,domin yana iya kaimu ya baro mu guji k'yashi da hassada ga jununmu, domin mu samu

3 / 6