ke masa dariya p.a yay kafin yace "Sorry sir" banza yay masa yana shigewa cikin gidan, juyawa p.a yay zuwa gida.
Lokaci daya shiga Afaf ce a Parlo da Aleema sai Akeela dake kwance saman duguwar sofa tana bacci gashinta duk ya rufe mata fuskarta, ga wani ƙaramin Teyana wide-leg trousers dake jikinta sai Applique logo detail t.shirt jikin nan nata sai glowing yake.
Wani series film suke kalla mai suna My perfect husband a zee world.
Da sauri Afaf tace "Wlcm Hero" harara ya watsa mata cikin sauri ta ɗauki remote tare da kashe kallon.
Ɗauke kai yay ya nufi upstairs, yana shigewa Akeela ta sauke ajjiyar zuciya yana dafe ƙirji dariya Aleema tayi tace "Laa! so you're pretending kenan ai kam zan faɗa masa" kwaɓe fuska tayi tana langwaɓar da kanta gefe alamar "No" ba tare da tace komai ba kuma.
Wanka yay ya sauya kaya zuwa Racing jersey da tracksuit trousers, a hankali yake sakkowa daga steps ɗin benen idanunsa a lumshe yunwa ya keji sosai sai baza ƙamshi yake yana tafiya kamar so, kai tsaye kitchen ya nufa domin samun mayen nasa Coffee da ice cream domin ya duba gaba ɗaya ya shanye ice cream part ɗinsa, yana shiga ya rufe ƙofar kitchen ɗin tare da jingina da jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa.
Tana tsaye a kitchen ɗin tana haɗa tea sai zabga madara take a mug ga kyawawan ƙafafuwan ta a waje ƙafarta sanye cikin wani slippers ga laft tummy ɗinta a lafe ya ƙara fidda shape ɗinta, a sanyaye take komai kamar bata so tana gamawa ta ɗauki mug ɗin tana juyawa idanunta ya sauka a kansa tsananin tsoro da gigicewar da tayi yasa gaba ɗaya ta saki mug ɗin cikin rashin Sa'a gaba ɗaya tea ɗin yay masa ka! Nan da nan fuskarsa tai ja idanunsa ya ƙanƙance ya wani haɗe fuska ta mau a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take tsaye....
*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616
*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.
*FITATTU HUƊU🔥*
BAƘAR FATA
AutaR ManyA
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
SULTAAN
Mss flower
gaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218
*SARAUTAR MARUBUTA*
*🌈TSINTACCIYA🌈*
FITATTU HUƊU🔥
Http://wa.me/+2348119237616
EPISODE9️⃣
Jikin Akeela na wani irin ɓari tayi baya tare da manne bayanta a jikin canter ɗin kitchen ɗin ta wani matse idanunta, laɓɓanta na wani irin Kaɗawa tana taune su gaba ɗaya ta jiƙasu da yawo, rawar da jikinta yake ya ƙaro.
A hankali Akeem yake takuwa zuwa inda take fuskarsa a haɗe tamau babu walwala sai ƙwantaccen sajansa dake ta sheƙi tsaye yay a gabanta yana ƙare mata kallo, ƙara matsawa yay kusa da ita very close to her har tana jin yadda Numfashinsa ke fita ga mayataccen ƙamshin turarensa dake dakar mata hanci.
Kamar zai matseta haka ya tsaya a gabanta kafin a hankali ya ɗaga ƙafarsa tare da sauke ta a saman ƙafarta ya wani irin murzawa.
Innalillahi wani irin azaba ta ratsa mata jiki har tana jin yadda ƙashin yatsunta yay ƙara baki ta buɗe zata kuka yay saurin sanya hannunsa tare fisgota jikinsa ya haɗata da Physique chest ɗinsa ya matse ta sosai cikin wata lallausar Muryar mai amsa kowa da sanya mutum zullumi da tarin fargaba yace.
"Shittt!!! Kul Kimin kuka" wani irin matse idanunta tayi wani kalan tsoran Akeem take kamar mutuwa haka take jin tsoransa komai nasa da banne look what he did to her amma yana cewa kada tayi kuka gashi still ƙara murje yatsun ƙafarta yake.
Hannunsa guda ya ɗura akan waist ɗinta ya ƙara holding jikinta a nasa very tight. Ɗaya hannunsa kuma yana kan laɓɓansa daya nuna mata alamar tayi shiru ɗib tai shiru kamar ruwa ya cinyeta amma jikinta yana wani irin vibration, ga wani masifafan ƙamshin turarensa wanda yake sanyata jin bacci zuciyarta na wani irin bugu beating fast fast har Akeem na iya jin yadda ƙirjinta ke ɗagawa, ko da wasa ko baiyi tunanin kallon wajan ba domin babu haka a ransa..
Ƙara murje yatsun yay da sauri ta buɗe idanunta tare da buɗe baki tace "Auchhhiiii wayyooo Baffana" ta faɗa tana girgiza kanta tare da motsawa zata gudu daga jikinsa yadda kake tsoransa zaka ɗauka ma'aikatan ɗaukan rai ta gani.
Hannunsa dake saman lip's ɗinsa ya zame tare da sanya hannun ya tallafo haɓarta zuwa wajan fuskarsa fuskar nata yay so cute a hannunsa musamman eyes lashes ɗinta masu mugun tsayi da yawa.
Cikin wata husky kamar wanda akai forcing nasa dole yay maganar yace "kee!!" Da sauri ta buɗe idanunta tare da sauke Kallonta a gashin ƙirjinsa dake kwance fuska ya ƙara haɗewa kamar zai fashe yace "look at into my eyes witch" girgiza kanta tayi tana ƙoƙarin sakar masa kuka cikin wata ƙaramar tsawa yace "heeey!!" Muryarta na rawa tana ƙanƙanme jikinta waje guda tace "Am sorry but I can't do this" lumshe idanunsa yay sosai yana jin wani abu mai kama da mugunta na taso masa a hankali kuma ya buɗe idanunsa tare da sakar mata wata gigitacciyyar tsawa haɗi da faɗin "keee" Innalillahi tsawar da tayi mata yawa ne da kuma rashin sabo da tayi da ita haɗi da gigicewar da tayi yasa kawai ta faɗa jikinsa ta wani ƙanƙamesa tana sakin maraitaccen kuka haɗi da faɗin "am sorry ha....ban sakewa Hamma Akeemmm!!" Ta jaa! Sunan nashi ta rufe fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa gaba ɗaya jikinta rawa yake sosai.
Gaba ɗaya ta firgita da tsawar da yay mata domin tunda take a rayuwa babu wanda ya taɓa yi mata something like this to wama ta sani gaba ɗaya even friends Wannan bata dasu ita ɗaya take rayuwarta ita kam da zama a wajan mutum irin Akeem gwamma ta koma inda ta fito.
Sauke numfashi yay tare da jan wata iska zuwa cikin hancinsa, yadda Jikinta ke rawa yasa gaba ɗaya take neman yarda su a ƙasa, taƙi yarda ta buɗe idanunta balle ga kallesa sai tura fuskarta take cikin ƙirjinsa.
Wani irin taɓe baki yay kafin yay baya kaɗan tare da jingina da canter cikin wata kasalalliyyar murya can ƙasa yace "Uhm hold me tight kafin na ɓallaki" jin haka yasa ta ƙara tura hannunta in between his hammata tana ƙanƙamesa sosai kamar zata koma cikinsa, ganin yadda ta rungomesa irin rungumar nan ta neman tsira da rai rungumar da babu wanda ya taɓa yi masa ita sai Amani yasa ya wani shafa sumar kansa kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"Duk abinda nace kice You are" da sauri ta ɗaga masa tana ƙoƙarin zame Jikinta daga nasa yace "don't ever try" dole ta koma tare da kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke numfashi a wahalarce.
Gyara tsaiwarsa yay Muryar nan nashi kamar ana buda algaita yace "witch" bakinta na rawa tace "i am" tsaki yaja yana ƙara murje yatsun ƙafarta yace "pairy, mumu jakaness, emty head" wani runtse idanunta tayi sharrrr kuma hawaye suka zubo mata muryarta na rawa tana son fashewa da kuka tace "i am" shafa lafiyayyiyan gemunsa yay yace "aljanar ruwa, Kidnapper mai cin naman mutane ƴar yankan kai" kuka na kwance mata tace "i am" wani shu'umin Murmushi Yay Wanda ya jima bai irinsa ba kafin yace "Uhmm mai warin hammata" wani raunataccen kuka ta fashe da shi tama kasa magana hannunsa yasa ya zareta daga jikinsa harya juya sai kuma ya dawo ya ɗauki mug ya fara haɗa coffee ko inda take bai ƙara kalla ba, yanzu haka sai yay wanka domin shi da gaske warin take masa sbd rashin tsoran Allah irin na Abdul-hakeem Bukar Bello.
Ya gama haɗa coffee ya nufi wajan ƙofa tafiyarsa ma kaɗai abar kallo ce har zai fita sai kuma ya tsaya cikin wata kakkauran murya yace "ki faɗawa wani kiga sai na bawa karnuka sun cinye namanki" yana faɗin hakan ya fita.
Zubewa tayi a wajan tana sakin wani sabon kukan gaba ɗaya taji ta fara tsanar zaman gidan saboda shi.
Yana fitowa idanunsa ya sauka akan Didi tana zaune saman kujera an ɗura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ganin ta washe baki "kaga irin albarka, kai dai kaji daɗin ka tausayinta kaɗai yasa a soka baka da ƙyashi ko kaɗan shiyasa nace babu wanda zan faɗawa zaka siyo min nama, ato kaf Duniyar nan wa kake dashi mai sonka da sanya maka albarka ai sani ɗin dana zame maka dole na haifi gantalallan Ubanka" banza yay mata yana zaman kan sofa a hankali yake sipping coffee ɗin a bakinsa, Ummi ta fito daga part ɗin Abbu yana biye dashi da alama alwala yay idanunsa ya juya ganin babu Mami yasa ya nufi part ɗin ta.
A can cikin bedroom ya sameta zaune ta zabga tagumi idanunta yay jajir a gefenta ya zauna yana Kallonta a hankali itama ta kallesa kafin kuma kuka ya kwance mata bakinsa ya buɗe yace "come here" da sauri ta ƙara jikinsa tana fashewa da kuka sosai, bai hanata ba sai da tayi mai isarta kafin yace "Mami nasan dole kiji zafi domin ke ɗin uwa ce, duk yadda zanji ciwon abin ba kamar ke ba, amma wallahi bana baccin kirki kullum da damuwa nake kwana, ya Adnan yake? Wanne hali yake ciki? Yana raye? Baya raye? No one's know, amma dukkan abinda ya samu bawa rubutacce ne daga Rabbil izzati mai kowa da komai, ko da ba'a ce ruwa ya faɗa ba Tabbas zamu nemesa mu rasa, amma har yanzu jikina yana bani Adnan yana raye koma zai dawo garemu in sha Allah, so kiyi hqr kiyi accepting Wannan destiny ɗin you're muslim a musulmi should trust ƙaddara good or bad ok!"
Kallonsa tayi kamar yadda yake kallonta kafin tace "Abbu ina jin babu daɗi ƙwarai rashin ɗa ba ƙaramin abu bane, kullum ina addu'ar Ubangiji ya kare min Adnan aduk inda yake,amma idan na kalli wannan Yarinyar zuciyata zafi take inside of kai punishing ɗinta akan dalilinta muka rasa Adnan amma ka ɗauke ta ka sanyata cikin yaranka me kake expecting idan wani abu ya samu ɗayan su?" Tunda ta fara magana yake kallonta kafin yace "jinina kike son na wulaƙanta Khadijertou? Ɗiyar yayana Baffa zan ci zarafi, ko bayan raina nasan Baffa zai kula da komai na iyali na mene yasa kike son ni naci zarafin tasa ƴar ƙwaya ɗaya tilo? Please bana so ki barni da masifar da take shirin kunno mini please" shiru tayi masa tana sauke ajjiyar zuciya, Miƙewa yay da ita kafin yasa hannu ya share mata hawayen cikin damuwa yace "Ni Ubane kuma mijine mai adalci, amma hakan ba zai sanya naƙi bin abinda zuciyata keso ke muradi ba" da rashin fahimta Mami tace "Me kake muradi Abbu" hancinta yaja yace "time zaizo Ohyyyah go and pray" "bana yi" zare ido yay yana faɗin "eyee baƙin ciki ido biyu Allah ya Bukar Bello ba'a ɗakin Mami yake ba dana shige" ya faɗa yana ficewa.
A hankali Akeem ya miƙe kai tsaye suka nufi Masjid suna fita Akeela ta fito da sauri idanunta duk yay jaa sosai ga lip's ɗin nan yay wani pink yirrrrr dashi.
Didi ce ta tafka satali tace "Innahu sulaimanu wa Innahu Bismillahi Meye haka kamar wata munafuka kuma jama'a na shiga uku ke zonan" kwasa Akeela tayi da gudu tana nufar part ɗinsu dan Didi ta iya bala'i da surutan tsofa.
ABUJA
*Aso Rock Presidential Villa*
A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga cikin wani makeken bedroom kusan dai gidan Shugaban ƙasa wasting time ne tsayawa description nasa just imagine.
Tsayawa yay yana ƙare mata kallo kafin a hankali yace "Meema" shiru tayi kanta a ƙasa ta tura hannunta a tsakanin cinyoyinta sai sauke Ajjiyar zuciya take..
Wata macace zatai sa'ar Akeem shekarunta kusan 32 amma idan ka ganta zaka ɗauka bata shige 25 ko 26 ba tana da kyau sosai fara tass da ita gashinta ya sauka sosai..
Ganin yadda tai masa shiru yasa ya girgiza kai tare da faɗin "ohh Rabbi ka kawo min ɗauki" ya faɗa a hankali ya gyara zaman babbar rigar jikinsa babban mutum ne shekara wajan 65 to 67 fari ne kamar Balarabe wajanta ya ƙarasa yana zuwa ta ɗaga kanta a tsoro ce domin kullum cikin firgita take kwaɓe fuska tayi har zatai shiru sai kuma tace "Dad" gashinta ya tattare tsaf kafin ya sanya ribbon ya haɗe mata su yace "oyaa stand up" tashi tayi a hankali har yanzu idanunta a ƙasa yace "Your Mom told me har yanzu baki breakfast ba what exactly wrong with my darling eh?" Kwaɓe fuska tayi kafin tace "Dad how is he?" Dafe kai yay yace "Ya rabbi Wannan mutumin ba kuwa asiri yay maki ba Meema? Mun tsinci Mutum a hospital daga zuwa zaga marasa lafiya kince dole dole a ɗauke shi na ɗauke sa gashi can ana kula dashi amma dole sai an fita dashi waje" kamar zatai kuka tace "Dad why?" Shafa kanta yay yace "come with me" Kallon Mahaifin nata tayi PRESIDENT AHMED ADIL kenan.
Kama hannunta yay kai tsaye ratsawa yay ta haɗaɗɗan parlon yarinyar tasa kafin ya nufi wani corridor a nan zaka samu main Parlo iya kar haɗuwa ya haɗu wata mata ce zaune tana kallon Aljazeera zatai shekara 54 tana sanye da wata haɗaɗɗiyar shadda ko'ina na jikinta sheƙi yake ga wasu gold a hannunta murmushi tayi tace.
"Ok dake kaine ta kulaka ko yayi" Murmushi Dad yay mata kafin yace "Meema kullum jin kanta take wata ƴar baby look da aure tayi da wajan yara biyu uku har huɗu gareta" dariya Mom tayi tace "aifa" hannunta yaja yace "bari na karata wajan mutumin ɗan yanzu bazan ƙara barinta fita ba"
"Adawo Lfy Ur Excellency" fita yay kafin ya shiga Elevator kai tsaye kuma da shiga ya dannawa lift ɗin 1floor, tana kusa dashi sai Ajjiyar zuciya take saukewa a haka suka sauka jama'a kuzo kuga haukan securities sai ku ɗauka yaƙin duniya ake, da sauri aka buɗe masu ƙofar wata lafiyayyiyar mota, kai tsaye wani Aso Rock Clinic Gulps suka nufa motar guards na biye dasu.
Sun ɗan jima suna tafiya a cikin gidan kafin su ƙarasa gaba ɗaya guards ɗin sukai masu rumfa Meema dai sai ɓoyewa take domin tsoran mutane take sosai.
A haka suka isa wani Dr ya tarɓesu bayan President Ahmad Adil ya zauna ya dubi Dr yace "Yaya jikin nasa?" Ajjiyar zuciya Dr yay kafin yace "To da sauƙi amma he's in critical condition sosai" gaban Meema ne ya faɗi da sauri ta riƙe Dad kafin Dr ya ɗura da faɗin "He lost his memory and fuskarsa ma ta lalace baki ɗaya.....
_Ki guji haƙƙin wani domin bala'i ne wallahi sosai fa, idan kina son this book ki siya akan 500 ko nrml grp 300 nidai bazan yafewa dukkan wanda zai karanta bai biya ba haka kukai min akan ABU MALEEK_
*TSINTACCIYA*
NRML GRP ₦300
VIP: 500 SAFE YAMMA POSTING
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616
*NOTE*
NRML GRP POSTING BA KULLUM BA🤷🏾♀️ IDAN ZAKI SAI BOOK ƊINA DOMIN KI FITAR NA YAFE NA FAƊA MAKU ZALLAR SOYAYYA NE A WANNAN BOOK ƊIN MAI TSAYAWA A ZUCIYA.
*FITATTU HUƊU🔥*
BAƘAR FATA
AutaR ManyA
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
SULTAAN
Mss flower
gaba ɗaya ₦800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 zaku tura Evedance of payment a nan 08142105218
*SARAUTAR MARUBUTA*
*🌈TSINTACCIYA🌈*
FITATTU HUƊU🔥
Http://wa.me/+2348119237616
EPISODE 1⃣0⃣
Kuka Meema ta sanya wanda ya ƙara tayar da hankalin President Ahmad Adil,cikin damuwa yace "he looses his memory? I understand,but problem ɗin fuskar fa? How long zai kasance cikin rashin sanin wane ne shi?" Kafin Dr yay magana Meema tace "i don't understand Dad,loosing memory kamar ya?" Cikin nutsuwa Dr ɗin ya kalleta kafin yace "everyone forgets things atimes,how often have you misplaced your car keys or forgotten the name of a person you just met,some degree of memory problems as well as a modest decline in other thinking skills,is a fairly common part of ageing,there's a difference,however between nrml changes in memory and memory loss associated with alzheimer's disease and related disorders,and some memory problems are result of treatable condition Madam Meema Ahmed Adil" shiru tayi idanunta yay rau rau zai kawo ruwa kafin a hankali tace "kenan bazai iya tuna waye shi ba? Balle ya tuna abinda ya faru dashi,more explanation please" farin glass ɗinsa ya ɗauka tare da sanyawa cikin nutsuwa yace da Meema "he looses his memory,he can't remember anything about his life,and normal age-related kin gane ba? Memory loose doesn't prevent you from living a full productive life for example,you might occasionally forget a person's name,but recall it later in the day,amma tunawa lokaci guda it's difficult,you might misplace your glasses sometimes,or maybe you need to make lists more often than in the past to remember appointment or tasks. These changes in memory are generally manageable and don't disrupt your ability to work,live independently or maintain a social life" Dr ya ƙare maganar yana sauke numfashi baya jin hausa ko kaɗan hakan yasa dukkan wani bayani da zai yi dole sai dai yay da yaran nasara Ingilishi kenan.
Kasa magana Meema tayi bata san mene yasa ba amma wani mugun jin tausayin mutumin take kafin a hankali tace "alright yanzu dole sai the same abinda ya faru da shi ya sake faruwa zai iya tuna waye shi?" Ta faɗa abinda Dr ɗin ya faɗa,jinjina kai yay kafin yace "sure" miƙewa President Ahmad Adil yay yana kama hannun Meema kafin yace "Dr ka shirya komai na tafiyar cikin week ɗin nan za'a fita dashi" ya faɗa yana jan Meema zuwa waje,kallonsa tayi tana kwaɓe fuska kafin tace "Dad" ba tare da ya kalleta ba yace "what again Meema?" Idanunta na kawo ruwa tace "Dad i want see him please! Please Dad" tsayawa yay yana kallonta kafin yace "Look Meema wannan ba age ɗin soyayya dashi bane,infact kin girme masa respect yourself ok?" Ƙasa tayi da idanunta tana jin ranta babu daɗi kafin tace "Dad ni fa ba?" Tsareta yay da idanu kafin yace "kefa mene? Uhm gayan naji" girgiza masa kai tayi kafin tace "nothing" kama hannunta yay