ta, sai da Ummi tayi mata injection kana ta ɗaura mata drip Abbu yi yayi kamar bazai fita ba ganin kallon da Ummi ke masa yasa ya ɗan shafa kansa yace.
"Miss You dear, let's go"
Gaba yay ta bisa a baya kana ta jawo masu ƙofa,
Daman p.a tuni yay masu sallama ya tafi gida.
A hankali bakinsa ke motsawa yana tasbihi can ƙasa zuciyarsa, saboda zafin da zuciyarsa ke masa, cikin haɗaɗɗan parlonsa ya shiga komai na Parlon white ne.
Ya haɗu sosai har ba'a magana, kai tsaye wata corridor ya bi hadle ɗin ƙofar ya buɗe, wani irin lumshe idanunsa yay tare da sauke wani maraitaccen numfashi yaja tare da saukewa, saboda wani sassanyan ƙamshi daya daki hancinsa ya sashi lumshe idanun da bai niyya ba.
Tura kansa cikin bedroom yay bakinsa ɗauke da wata kamilalliyar sallama yana maida ƙofar ya rufe.
Derect bathroom ya nufa yana mai zare kayan jikinsa, a saman hanger ya saƙale tare da sakarwa kansa shower, a hankali yake sauke ajjiyar zuciya yana jin yadda ruwan yake dukan saman fresh skin ɗinsa.
Bayan yay wankan ya ɗaura alwala kana ta ɗauki wani long white towel ya dauraia wist ɗinsa, ko kansa bai tsane ba ya fito ruwa na sauka daga sumar kansa zuwa ƙwantaccen gashin ƙirjinsa.
Wani irin ɗaci bakinsa yake masa rabon da yaci abinci har ya manta wajan fridge ya nufa ya ɗauki Apple da cake ya fara ci bai wani ci da yawa ba ya ajjiye.
Wasu haɗaɗɗun nightwear slik Pajamas milk colour, a hankali ya miƙe tare da goya hannunsa a bayansa ya ɗan fara tafiya yana mai karanta addu'a yana bin duk kusurwa ɗakin da tofi bayan ya gama ya kwanta saman bed ɗin tare da jan duvet ya rufe jikinsa, gaba ɗaya ya ƙasa bacci tunda matarsa ta rasu wajan haihuwar Amani baya iya cikakken bacci ya saba da jikin mace sosai duk da auran kamar na dole ne bai so amma ya saba da jikin matarsa ainun.
A haka bacci ya ɗauke sa.
Misalin 4 na dare ta shiga buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi kanta na sarawa sosai, hannunta mai ɗauke da carnoner ta kala ɗan marai-raice fuska tayi kamar wata ƴar baby Wanda ya sanya manyan dimples ɗinsa bala'in lomawa.
A hankali kuma ta shiga bin bedroom ɗin da kallo sosai gabanta ya faɗi ganin bata dan ɗakin ba, jiki babu ƙauri ta miƙe tsaye tana Miƙewa gashinta ta sauka har wajan manyan ass ɗinta.
Da Mamaki tabi jikinta da kallo ganin wata Robe Nightgown silver wacce ta sauka iya laps ɗinta gaba ɗaya manyan gwayen ƙafafuwanta suna waje ga wani gashi da yay kwance lub a saman fatar ta.
Shanyayyun idanunta wanda kullum suke a Lumshe ta ƙara buɗe, jikinta babu ƙwari ta nufi ƙofar data gani, tana tafe ko'ina na jikinta moving yake kamar tarwaɗa.
A hankali ta buɗe ƙofar ta fita ita bama ta san dare bane sai da ta fito parlon daga duhu ga wani masifafan sanyi na Kaɗawa, da sauri ta matse jikinta waje guda ta shiga taune bakinta kamar wata ƴar turawa haka ta zama cikin nutsuwa take tafiya harta isa tsakiyar Parlo tana zuwa zata shige taji an sanya mata ƙafa baya tayi tare da hantsilawa zata faɗi wata kuma ƙyakkyawar Ajjiyar zuciya ta sauke jin ta faɗa saman ƙirjin mutum...
😂Abbu ya biyo dare jama'a
*TSINTACCIYA*
Na kuɗi ne kada ki siyi litaffi na idan kin san zaki fitar🤷🏾♀️.
NRML GRP: ₦300
VIP: ₦500 POSTING SAFE+YAMMA
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK, PLEASE MASU VIP IDAN DA HALI A TURAN TA BANK NA AKWAI P.O.S MA A GARI. EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616
*FITATTU HUƊU*
BAƘAR FATA
Autar manya
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
SULTAAN
Mss flower
Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu sulaiman fidelity bank, masu tura kati kuyi magan ta nan 08167888934, za ku tura Evedance of payment ta nan 08142105218 ƴan uwa na Niger ga number ku +22796515805
*SARAUTAR MARUBUTA*
*🌈TSINTACCIYA🌈*
FITATTU HUƊU🔥
Http://wa.me/+2348119237616
EPISODE6️⃣
Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda ya sanyata saurin janye shanyayyun idanunta tare mai dasu ta rufe,
Wani irin harbawa Zuciyarta keyi tana jin wani matsananci tsoro na shigarta, gata dai male male a jikin mutum amma ta kasa wani ƙwaƙƙwarar motsi bare tayi tunanin zame jikinta.
Yana zaune saman kujera 1 seater yana sanye cikin wani tattausan wando 3gauter sai farar singlet wacce ta kama jikinsa sosai ta fito da 6pack na jikinsa idanunsa a lumshe yana sauke numfashi, yayinda gudun da zuciyarsa ya ƙaro fiye da baya,
Idanunsa dake a Lumshe ya buɗe a hankali ɗan taune bakinsa yay jin yadda take masa sukur sukur a jiki kamar wata macijiya.
Hannunsa ya miƙa ta gefen lafaffan cikinta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya cup of coffee ɗin sa ya ɗauka, gently kuma yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar.
A hankali yake spending coffee ɗin a bakinsa ya ɗauki wajan 10minute kafin ya shanye coffee ɗin domin daman ƙa'ida ne sai ya sha Wannan coffee ɗin na Subhi da cikin dare kamar wani buzu ko labarabe.
Ajjiye cup ɗin yay cikin nutsuwa kuma ya sanya tafin hannunsa duk biyun tare da zurasu ta tsakiyar hammatar ta caraf ya ɗaga ta tsaye yana yatsuna fuskarsa.
Tsaye Akeela tayi kanta a ƙasa, kunya duk ya kamata through ba taga fuskar wanda ta zauna a cinyarsa ba, amma dadɗan ƙamshin parfume ɗinsa ya sanya tasan cewa shi ɗin daban yake ko a cikin maza.
Musamman yadda taji Physique chest ɗinsa dake cike da ƙwantaccen gashi lub! lub!!..
A razane ta sauke ajjiyar zuciya tare ƙanƙame Jikinta waje guda, naman jikinta ya wani irin rawa da ɓari dalilin saukar wani masifafan ruwan sanyi da taji tun daga tsakiyar kanta har ƙasan ƙafafuwanta, da alama ma ruwan daga cikin fridge aka ɗauko shi.
Idanunta da sukai wani irin juyewa suka ja ta buɗe da niyyar ganin wanda ya zuba mata ruwan.
Amma kamar walƙiya tuni Akeem ya haura upstairs babu mai cewa Shine yay punishing ɗin ta da wannan ruwan sanyin domin babu wani sign daya bari a wajan.
Abinka da mai ciwon ciki wanda jininta yake double SS tuni jininta yay wani daskarewa, tare da tsaya mata waje guda, a hankali kuma wata ƙwaya ta tsaya a tsakiyar jijiyar ƙafarta tare da lanƙwashewa kamar laushe.
Cikin ƙaramin lokaci ƙafarta ta fara wani irin matsanancin ciwo kamar ana sanya gatari ana datsa ɓargo da ƙashin ƙafarta haka ta keji.
Tsananin azabar da yay mata yawa ne yasa ko kuka ta kasa sai wani irin fitinannan numfashi da take gumi na yanko mata.
A hankali ta sulale tare zubewa a saman carpet ɗin parlon cikin wani irin wahalallan sabon yanayi ta kwanta tare da ɗura ƙafarta a saman kujera ta shiga jujjuya kanta tana sakin wani gigitaccen kuka iya zuci mai bala'in cin rai.
Gashi babu Folic acid da paludrine a kusa da ita bare tasha ko taji sauƙin abin.
Dukkan hannunta ta sanya a ƙafarta ta riƙe gam "ɗib! ɗib!! ɗib!!" Haka jijiyoyin ƙafarta suke harbawa alamar ciwo yayi ciwo a hankali kuma ciwo ya fara yawo a jikinta daga ƙafa zuwa kwankwasonta bata samu bacci ba sai wajan kiran sallar farko na Subhi.
A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen part ɗinsa, yana sanye da Embrodiery Islamic jallabiya white colour, wacce ta kasance mai santsi da taushi tana da half hand daga gaban ƙirjin kuma a ɗan tsage take..
A hankali yake tafiya kamar bai so cikin nutsuwa bakinsa ke motsawa alamar tasbihi yake ga Ubangiji.
Hannunsa a goyo da bayansa yana taka ƙafafuwansa dake sanye cikin Mon mule slippers masu kyau..
A tsakiyar parlon ya tsaya idanunsa a rufe babu jimawa Abbu ya fito daga part ɗinsa shima sanye da jallabiya milk irinta Akeem.
Babu wanda yay magana a haka suka jera zuwa masallacin dake cikin estate ɗin nasu.
Rutse idanunsa yay da tuni su uku ne suke tafiya amma waccan shigiyar Yarinyar mai siffa da aljanun ruwa taja masa a rasa mafi muni a rayuwarsa.
Bayan an idar ya zauna zaman azkar ƙarfe 6 dai-dai suka fito daga cikin masjid ɗin zuwa gida.
Kai tsaye Akeem kitchen ya nufa yana zuwa ya samu Ummi a ciki sanye da ƙaton hijab har ƙasa, kallonsa tayi tana Murmushi, a sanyaye murya can ƙasa yace.
"Sabahul khair Ummina"
Mug ɗin hannunta dake cike da coffee ta ajjiye a hankali ta ƙarasu wajansa yana ganinta ya ɗan zube a ƙasan gwiwoyinsa tare da zame wular kansa, hannunta ta ɗura a saman sumar kansa kafin tace.
”Sabahul khair Hero”
Murmushi Yay irin Murmushin nan da idan ba ita ba ko Abbu babu mai ganinsa sai Md Adnan.
Addu'a ta shiga yi masa kafin gently ya miƙe, ganin yadda take kallonsa yasa ya ɗan kwaɓe fuska yana lumshe idanunsa cikin narkakkiyar murya yace.
“Ummi”
Hannu tasa ta ja dugun hancinsa tace "Allah ya kyauta maka, ƴarka tayi taɓara kai ma kayi"
Shi dai bai ce komai ba, maimakon ya fita daga kitchen ɗin sai yay zamansa akan kujera yay hakanne kuma saboda bai son fita yaga Akeela.
Fita Ummi tayi sam bata kula da Akeela ba kai tsaye part ɗinta ta shige.
Abbu da ya tsaya da Bala driver yana bashi hqr ne ya shigo cikin parlon kai tsaye kuma idanunsa ya sauka akan Akeela wacce take baccin wahala a saman carpet..
Da sauri ya nufi inda take yana faɗin.
"Ya Salam Babyna bacci a Parlo a ƙasan carpet why?"
Ya faɗa yana tsugunawa tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗauke ta zuwa jikinsa, Ajjiyar zuciya ya sauke yana ƙara kallon fuskarsa wacce tai jajirr idanunta ya kumbura sosai.
Cikin tausayinta da kuma masifafan sonta dake ƙara zautar da Abbu a hankali ya manna bakinsa a saman goshinta tare da sumbatar wajan karaf a idanun Akeem taɓe baki yay da kuma sauri ya juya tare da komawa kitchen ɗin.
"Sorry nine ko, sorry Babyn Abbu muje na goyaki kiyi bacci sosai, i promise to you cewa ba zaki kuma kuka ba, I'll be your side kinji Babyn Abbu na" ya faɗa yana ƙara shafa fuskarta tare dayin part ɗin yaransa da ita.
http://wa.me/+2348119237616
*_wannan book ɗin na kuɗi ne biya 500 a saki a vip ko kuma 300 a nrml grp_*
Abbu na shigewa Akeem ya fito fuska kamar hadari babu walwala baki ɗaya, kai tsaye wani room ya shiga yana shiga ya kunna hasken ciki, ɗakin karatu ne yana shiga wajan kujera yaje ya zauna tare da lumshe idanunsa yana sauke numfashi.
Not too long da zamansa a buɗe ƙofar a hankali aka shigo, Amani ce ƙyakkyawar Yarinya mai fuskar Akeem.
Washe bakinta tayi da gudu ta nufi wajan Akeem tana faɗin "Hero na" ware gajiyayyun idanunsa yay tare da mai da idanunsa kan Amani kallon da yay mata yasa ta tsaya tare da juyawa da sauri ta fita tana dawowa tace "Salamu Alaika" wani fitinan Murmushi Yay mata yana jin wani sanyi a ransa yace "Wasalamu alaiki Amani Abdul-hakeem Bukar Bello" ya faɗa yana lumshe idanunsa tare da ware mata hannayensa cikin jin daɗi ta faɗa jikin Mahaifin nata tace.
"Azunnu annaka bikhair?"
Shafa bayanta yay tare da sumbatar goshinta yace.
"Lafiya lou and you"
Murmushi tayi tana sumbatar goshinsa tace "Ana bikhair"
Lumshe idanunsa yay yana ƙara rungome ta a jikinsa yana jin wani so da ƙaunar Yarinyar nasa na shiga zuciyarsa, zameta yay a jikinsa yace "sit" Zama tayi tana kallonsa sosai kamar bazai magana ba sai kuma yace "biya haddarki" a hankali tai rufe idanunta kamar yadda taga yanayi kafin ta fara karanta masa inda yay mata, tana cin karatun ne Afaf da Aleema suka shigo sanye da manyan hijabai, nan da nan walwalar fuskarsa ya ɗauke zubewa sukai bakinsu na rawa suka fara gaida shi.
Suna tsaye ko Kallon su bai ba yaci gaba dayiwa Amani karatu.
Bayan ya gama ya kallesu har zai magana sai kuma ya fasa.
Hadda suka bashi kana ya ɗura masu da karatu.
Suna cikin karatun ne Aka buɗe ƙofar Abbu ne ya shigo cikin tashin hankali ganin hakan yasa duk yaran nasa suka kallesa a kiɗime yace.
"Dr Saboda Allah ba danni ba kazo ka duba Yarinyar nan she's in critical condition ciwonta ya tashi bana son yay worse da yawa"
Shiru Akeem yay tare da ƙara haɗe fuska ganin hakan yasa Abbu faɗin "saboda Allah, saboda matsayina na mahaifi please Abdul-hakeem Bukar Bello" Miƙewa tsaye yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu yabi bayansa, Akeem kam ji yake kamar ya zunduma hannu aka yay ihu dan baƙin ciki.
A bakin ƙofar ya tsaya Murya a can ciki yace "Kaje Abbu I'll check her" yana faɗin hakan ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga tare da rufewa girgiza kai kawai Abbu yay ya juya.
Tana kwance saman bed ɗin sai juyi take domin a yanzu bata iya tantance inda yake mata ciwo a sanadin ruwan da Akeem ya sheƙa mata..
Hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa cike kuma da tsanarta ya ƙarasa inda take tsaye yana jin kansa na wani irine sara masa zuciyarsa na harbawa sosai.
Ganin bata hayyacinta gaba ɗaya yasa gently ya zaune a gefen gadon tare da sanya hannunsa ya wani irin fincikar ƙafarta wata razananiyyar ƙara ta saka jikinta na kyarma da sauri ta tashi zaune tana cije bakinta tare da yarfar da hannayenta Jikinta sai ɓari Yake gaba ɗaya rigar jikinta ya zame gashinta ya hargitsa sosai..
A karo na farko ya ƙara Kallonta kafin ya daka mata wata gigitacciyyar tsawa ƙarfin tsawar da kuma rashin sabon jinta ga halin ciwo da kuma matsanancin tsoron daya shigi Akeela yasa gaba ɗaya tai wani irin juyi tare da faɗawa jikinsa ta wani irin cusa fuskarta a tsakiyar ƙirjinsa jikinta duk rawa yake domin dam bata saba da kind of this abubuwan ba.
Tsaki Akeem yaja yana taune bakinsa kafin a hankali yasa hannunsa yay cilli da ita daga jikinsa, kanta ya daki frame ɗin gadon wani irin runtse idanunta tayi azaba biyu ta haɗe mata.
Bayan ya fita daga bedroom ɗin ne Akeela ta fashe da wani irin kuka, gashi ita magana sam bata tsarinta bai dame ta ba, wani irin zafi da ciwo ta keji a ranta, wanne irin mutum ta haɗu da shine? Me tayi masa da har zai dinga cin mutuncin ta har haka? She don't even know him balle tai wani abu na rashin dai-dai amma yana nuna ko ina kula infact ma shine yaja mata wannan masifar na tashin ciwon nata.
A yanzu ba ciwon ke sanyata kuka ba, domin idan da ana sabawa da zafi da kuma raɗaɗin ciwo da yaci ace ta saba dashi, amma a kullum idan ya tashi a sabo ta kejinsa, ciwon sikila ya wuce tunanin dukkan mai tunani ko mai haihuwa ba lallai taji azabar da suke ji ba.
Kifa kanta tayi a tsakiyar cinyoyinta tana wani irin kuka mai cin zuciya.
Akeem na fita derect wani side ya shiga ashe ƙaramin clinic ne, wata injection ya haɗa guda biyu fuskar nan nashi babu walwala sam.
A haka ya gama haɗawa ya fito yana fitowa ya tsaya idanunsa akan Didi wacce ta ciko plate da farfesun naman cow head.
tsareta yay da idanu domin mamakin naman data kwasa yake amma fuskarsa sam bata bayyana yanayinsa ba, harara ta maka masa tace "to ba sai dai kaci kanka ba, ai dai lalura ce bata shige kan kuwa, jiya jiyan na dakta ya gama gayawa Bukari naci nama na ƙoshi, to wallahi nidai li'ilafi ƙurash kaci kanka nama na kurr aniya bil aniya ato"
Girgiza kai kawai yay tare da nufar part ɗin su Aleema.
"Ɗan banza fuska kamar karas in sha Allah sai Ubanka yay maka auran dole, masifa sai cin yaro take shi kenan shan lemun tsami"
_(shan lemon tsami baya rage sha'awa sai ma amfani da yake wajan inganta Mani, more impormation kiyi attending class ɗin we are all Women wanda zan gabatar da grp na Vip ɗin Tsintacciya 500 kacal)_
Parlo ta koma lokacin Abbu ya fito cikin wata dakakkiyar shampoo dark blue anyi masa ɗinkin jamper da babbar riga.
Ya haɗu sai ƙamshi yake zubawa, Didi na ganinsa ta fashe da kuka tana faɗin.
"Sai a gaya min cewa bani na haifi Bukari na kawosa duniya ba, da za'a dinga yi min gori a gidan ɗan dana haifa"
Kallonta yay yana zama dai-dai nan Mami ta fito cikin wata milk ɗin valisco sai ƙamshi take zama Abbu yay yace "Gori kuma Didi?"
Bakin zani ta cire ta face majina tace "A'a to ba dole nace gori ba gashi nan Audil yana cemin kura bani da aiki sai cin nama, kuma dai ai naga lalura ce ko ba gaskiya ba? Babu ruwana fisabilillahi nidai na basshi da Allah bance ka faɗa masa masifar sa ta ƙare masa akai wallahi"
Akeem a hankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga tana cure waje guda lokacin su Aleema sun gama shiryawa tuni Drive ya tafi kaisu makaranta su da Amani.
A ɗan fakaice ya kalleta dugun gashinta wanda yake zube har saman bed ɗin ya kalla taɓe baki yay aransa yana faɗin "har ƴan ƙauye sun iya ƙarin gashi mtwss"
Gently ya ƙarasa inda take zaune tana sauke ajjiyar zuciya har yanzu jikinta ɓari yake.
Baya jin zai ɓata lokacin da wajan yiwa Wannan stupid gal ɗin magana yay mata wata iriyar muguwar tsana wacce bai taɓa yiwa kuwa ba.
Yana daga tsaye ya ajjiye injection ɗin a gefensa cikin wani ɓacin rai ya sanya hannunsa tare fisgota daga kan gadon har sai da ƙashin ta yay ƙara.
Cije bakinta tayi bata son yin wani motsi saboda ciwon da jikinta yake mata, Nightgown ɗin tabi jikinta ta wani manne dukkan Jikinta ana gani ga fure fresh skin ɗinta sai glowing take.
Hannunsa ya miƙa dai-dai lokacin daya ɗauko allurar ta buɗe shanyayyun idanunsa wani irin zare ido tayi domin ba'a taɓa yi mata allura ba wata mugun jin tsoran allura take.
A sanyaye a hankali kuma ta shiga girgiza kanta har lokacin kuma bata kalli fuskarsa ba, jikinta na rawa ta ɗaga ƙafarta zata gudu da wani saurin ya sanya hannunsa ya fisgota ta zuwa jikinsa....
Free pages sun kusa kammala🤗 kada ki siyi littafi na idan kin san zaki fitar banwa kuwa dole ba please.
*TSINTACCIYA*
NRML GRP: ₦300
VIP :500 SAFE YAMMA POSTING.
0116886423 SULAIMAN NA'IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616
*🔥FITATTU HUƊU🔥*
BAƘAR FATA
Autar manya
SULTAN
mss flower
DATTIJON ARZIƘI
Real ladingo
Gaba ɗaya 800
Via 6850917335 Na'ima Shu'aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218
*AUTHOR NOTE*
_muhimman pages da romantic page suna cikin paid Page's kawai