BACCIN SO

Author :  M Shakur Category :  Love

Chapter   29 / 51

84K to 87K   out of 151.6K words

na karama sai aka hada mahaifiyarta da yayan baban Amirah Yusuf kenan aure Allah yabasu Maryam Baffa yayi shiru shi kansa Marwan baitaba sanin mutumin ba shine mahaifin Amirah ba sai yau no wonder yanzu komi ke making sense, Baffa yace  dudda rabuwansu bai dade ba amman dai sun rabu, zancen danake maka bamuda sanin zancen auren nan sai jiya da safe daya kirani awaya kan yanaso nazo masallaci kaza danazo yace nadan jirasa bari agama dayrin auren nan yaganni nadaiji ana daura aure da Amirah, Baffa yayi shiru hakama duka yan dakin yace mahaifiyarta batasan komi akan zancen ba, Abba yasauke ijiyan zuciya, ahankali Baffa yace  dalilin dayakawo ni anan yau sabida nagana daku ne iyayen Marwan, sabida Yusuf ya sanar dane cewa ada yayan Marwan ne zai auri Amirah amman yafasa Dr ya aureta, daga mahaifiyarta hatta ni munada yar damuwa, na farko dai Amirah yarinya ce da bazan boye muku ba condition dinta ba yau ko jiyane yafara ba a a tun tana yar kankanuwa abin yafara, so ba lallai tama iya wani zamantakewan aure ba, and condition nata is not a good thing da on top of everything zatai rayuwa da wanda ba lallai yana kaunantaba!
Hakanan Marwan yaji kirjinsa yafara bugawa yana Jin wani tsoro har baiso Baffa yasake wani magana dan gani yake kaman za ace yasaketa kirjinsa bugawa yake kawai wlh wlh Sauda Mami ya lura, Baffa ahankali yace  munsan komi nufi ne Allah sannan bawai nazo danna kashe auren bane a a abinda Allah yahada shine zai raba ba niba! Wani boyayen ajiyan zuciya Marwan yasaki, Baffa yace  kawai inaso nasan cewa eh Marwan yasan wacece diyarmu sannan zai riketa amana, idan bazai iyaba amm& . Dasauri Abba yataresa yace  Hakan bazai taba faruwa ba!
Baffa yakallesa, ahankali Abba yace  ko bana duniya Marwan mutum ne dazan shedesa cewa bazai taba cutar da Amirah ba wallahi wallahi, zai riketa amana, and zai sama mata lafiya da izinin Allah wani sanyi Baffa yaji azuciyansa ganin yanda iyayen mutanen arziki ne, anatse Mami tace  zaka iya binkici kan wanene Marwan tundaga kan asibitin nan zuwa gida dako ina, Marwan mutum ne mai amana, tausayi, dakuma zuciya mai kyau murmushi Baffa yayi sai cikeda hikima irin na manya yace  Marwan! Saida gaban Marwan yafadi yanda Baffa yakirasa, dago kansa yayi ahankali suka hada idanu da Baffa dake kallonsa anatse yace  zaka rike Amirah amana Marwan? Lumshe idanu Marwan yayi saiya budesu ahankali, cikin murya mai dadi dakenan anytse ba garaje ciki yace  zan rike Ameenah amana Baffa namaka alkawari!

Wlh wani sanyi Baffa yaji sai yaji ya yarda da yaron sai yayi murmushi yace  Masha Allah ina addu a Allah ya albarkaci auren ku Ameen Ameen
Mami tadan kalli Marwan sai ta kalli Baffa tace  yaushe zamu iya zuwa daukan Amaryan mu dan dariyan manya Baffa yayi yace  eh toh ga mai gidan nan Hajiya ai sai abinda yace Marwan yasake sauke kansa dake kasa sosai cikeda kunya Baffa na kallonsa, Baffa yace  da so samune dai, Maryama zata tare gidan Mijin nata nan da sati biyu da yan kwanaki, to zanso ahada bikin ayisu idan Mijin nata ya yarda
Dasauri Mami tace  ai yama yarda muma kafin nan mun gama shiryawa gabaki daya Abba yace  kwarai kam, Allah yakaimu lokacin duk akace Ameen Ameen sai Baffa yatashi yace  to bari na koma Abba jiyayi yanason Baffa sosai yace  muje na taka maka tare suka fito suna zance na manya, harya rako Baffa wajen machine dinsa, Abba jiyayi yanason Baffa sosai saiya taba aljihunsa yaciro kudi duka dayake jikinsa wanda bundle na yan 100dollars ne yace ga wannan ayi tsaraba dasauri Baffa yace  ahhh bazamuyi hakaba Allah na amfana, nagode kwarai Allah yakara sauki damai jiki ya buga machine nasa yayi gaba Abba yabisa da kallo sai yayi murmushi


Tunda yace Ammi bata tare da mutumin abu dayane yazo ransa Alhaji Bashiru babban abokinsa matarsa tarasu 10months kenan yanzu baiyi aure ba, yaga Ammi she s so gently and homely zaiso itada alhaji Bashiru suyi aure, yaransa uku duka maza duk sunyi aure, shi kadaine agida sai Chefs dinsa maza dake masa girki bari zaimai maganan yaga.
EPISODE 4?? 8??



Komawa gida Baffa yayi wannan karan a falon Lami yasamesu gabaki daya, Amirah tayi lamo jikin Ammi tana danna wayan Ammi, yanda take bala in son waya tanason game idan tagama game saita shiga danne danne babu inda bata sani awaya ba tafara danna wayan Ammi kona Miemie sai takusan karan da chajin ko ka amshi shine zaka tsira, doguwan rigane ajikinta na atampa red wani kalan sheki takeyi bana wasa ba, tana glowing ga kamshin datakeyi da turarata da akeyi, karbe wayan hannunta Ammi tayi tace  baki iya gaisuwa ba ahankali ta tashi daga jikin Ammi takalli Baffa dake murmushi yana kallonsu murya yar karama tace  ina kwana Baffa yace  Amirori yaya an tashi ince anyi kari dai ? Ammi tace  wannan tafi karaman Salma neman abinci da sassafiyan Allah komawa jikin Ammi zatayi Ammi tace  jeki wajen Miemie tana daki kin tashi tayi Ammi tace  maza nace ahankali ta mike rikeda wayan Ammi tajuyo tana kallonta saita wuce tafita tashiga Dakinsu duk Ammi na kallonta kafin Ammi tajuyo takalli Baffa, dayayi murmushi na manya yace  Haleematu kinga dai bani kaunar halin Yusufa amman Allah yasani mijin daya aurama Amirah naga yaron kuma Allah ya dauramin kaunar sa da yarda dashi dan haka ni na yarda da auren nan dari bisa dari fatana Allah ya kyautata zamansu

Wani kallon Baffa Ammi keyi, Baffa kuma ya gyadamata kai cikeda gamsuwa yace  I know duka abinda kike tunani, kina tunanin Amirah batai girma da wayan dazatai rayuwa inda babu ke ba, now the question is yan kwanakin datayi a asibiti ai baki wajen ko? And she was fine, infact kalli improve Ada Amirah bazata taba barinki taje wani daki ke kina wani daki daban ba Lami tace  kwarai! Baffa yace  ki kwantar da hankalinki kibita da addu a karki rigima da mutumin chan Babansu ki barsa da halinsa, munyi concluding zasu tare rana daya da Miemie dan haka ki kama shirye shirye kinji Baffa yadan sauke murya yasan yanda takeson yarinyar Amirah saidai in baka zauna da itaba wlh saika sota, ahankali yace  is time for Amirah to grow up a inda baki haka rayuwa yake, this is her next step na rayuwa, ki daure ki koyar da ita the little you can in this period, kibarma Allah komi, Allah na ganin komi Haleema, and Allah bazai baki kunya for all hakurin dakikay1 ba, in sha Allah Dr Marwan will take care of Amirahn mu da kyau and zata warke tass tass kinji gyadama Baffa kai tayi ahankali saita lumshe idanu saiga hawaye wlh wlh tana ma Amirah wani so da batason tarabu da ita ko kadan batason tarabu da baby girl dinta, Baffa yace  laaaaaa Lami tai yar dariya tace  kukan tunanin rabuwa da yar diyarta take Baffa yace  tun yanzu, yau naga Maman Amarya mai kuka dan dariya sukayi, sai Ammi ta share fuskanta tass takalli Baffa da Lami tace  ragowan kudin dana rage zanja jari bari kawai muyi amfani dashi nama Amirah kayan daki ko Baffa yace  nima zan kara miki daga miliyan daya ta wajena dasauri Mami tace  ah ah Baffa kabarshi suka cigaba da hira.

Daga Bbaya Baffa yafice yaje kasuwa Ammi tawuce tashiga dakinsu Amirah na tare da Miemie tana kwance jikin Miemie suna kallo da wayan Ammi a YouTube dan Ammi nada data Miemie data dinta yakare amman anjima Umar zai samata, bama suji shigowan Ammi ba, Ammi tace  ahh yayi kyau sharan kenan ko Miemie dasauri Miemie ta kalli Ammi Amirah ma haka saita taso daga jikin Miemie ahankali, Ammi tawuce bakin katifa ta zauna dasauri Amirah tazo wajenta Ammi zata mata magana kawai saita zauna ajikin Ammi tana kallon fuskanta sosai muryan nan chan ciki tace  Ammi tsareta da idanu Ammi tayi tace  menene kika haumin jiki kaman mage ? Yanda Ammi taga tana kallon kwayan idanunta yasa tagane Amirah harta gane tai kuka kafin abin yashiga ranta ya zauna ya tada mata da hankali saitai sauri tace  gashi yafadamin ido, idanuna sunyi wani iri ne? Gyadamata kai Amirah tayi itama Miemie na zuwa wajen dasaurin ta.
EPISODE 4?? 9??



Cikeda hikima da dabara irin na Uwa Ammi tace  huramin idanun Amirah Dasauri Amirah tadaura soft hannayenta akan fuskan Ammi saita hura mata iska a idanun, Ammi tai murmushi tace  iyye yammatana ta iya fa kinga gashin yafita Miemie, Miemie tai dariya, sai Ammi tasa hannunta takama na Miemie tazaunar da ita gefenta tace  zauna kiji
Zama Miemie tayi duk suka kalli Ammi, Ammi tai murmushi tace  mesa kika gayamin kinason Dr Marwan Amirah ? Wani kyalli idanun Amirah sukayi sabida Ammi tahanata maganan Dr Marwan tamata fada sosai ganin Ammi yau tamata tambayan akanshi wani sanyi taji saita kankame Ammi sosai Miemie tawani kwashe da dariya tace  Ammi wlh da gaske Amirah son Dr nan takeyi jibi yanda take farin ciki sabida kin tambayeta, ohh su Ya Amirah anga fine Dr Ammi takalli Amirah yanda take murna tana wani blushing kyawawan hakoranta na nunawa tace  ina jinki fadamin ahankali Ammi tai shiru tana kallon Ammi tana tuna duka abubuwan da Marwan yamata tace  Dr Marwan nama Amirah kirki kaman Ammi Miemie tace  wooooohhh! Ammi tai shiru harareta hakan yasa tai shiru Ammi ta kalli Miemie tace  mesa kikace haka Safan kafanta tanunama Ammi ahankali yace  yasama Amirah takalmi da safa, yaba Amirah chocolate, da abinci mai dadi, yahana Amirah kuka, Dr shima Ammi na ne Ammi
Tunda Amirah ke maganganun Ammi ke kallonta batajin there sa single soul in this world as innocent as Amirah ba, nobody can understand abinda Amirah tafadi inba a mother ba, in the moment when she was scared tai feeling alone ba Ammi ba Miemie gardawa sun dauketa mutum daya saved her with a kind hearted spirit yabata exact kulawa irin wanda Ammin ta ketaba sai for the first time sai Ammi taji zuciyanta ya natsu da auren it might be a good thing afterall, cike da hikama Ammi tace  na aura miki Dr Marwan ahankali Amirah dake wasa da yan flowers na gaban rigan Ammi ta tsaya ta kalli Ammi dasauri, Miemie ma haka, wani tsare Ammi Amirah tai da idanu kaman tasan menene aure, Ammi tace  an daura auren ku jiya a masallaci karfe biyu sadakin ki na hannun Babanku, kema yanzu matar aure ce kaman Miemie rana daya za a kaiku gidan mazajen ku wani mamaki ne yakashe Miemie, wani kalan bugawa zuciyan Amirah keyi, ahankali tace  Mama Lami matan Baffa ne, Maman Baby Matan Daddy ne, Miemie Matan Ya Umar ne, Amirah Matan Dr Marwan ne? Gyadamata kai Ammi tayi alamun eh, wani washe baki sai tawani kankame Ammi tahau kyalkyala dariya da karfi abinda basu tabaji Amirah tayi ba tawani kankame Ammi, Itama Miemie saitahau dariya tace  laaa Ammi wlh Ya Amirah batada kunya, wai dadi fa takeji an mata aure ko Ammi kawai girgixa kai tayi irin na manya tana kallon yaran nata dake dariyan rashin hankali kawai tunani take yanda zata rabu dasu tai rayuwa ita kadai, dakewa tayi tace  ku tsaya ban gama magana daku ba zonan Amirah
Ammi tadagata daga jikinta wani murmushi takeyi sai Ammi taja kujera ta ijiye gabanta tace  zauna anan zama tayi anatse, Ammi tace  kinason auren? Dasauri ta gyadama Ammi kai, Ammi tace  kinsan me akeyi a aure ? Dasauri tace  zanci abinci nima na haifo katoton jariri Miemie tawani kwashe da dariya Amirah ta kalleta sai itama ta kwashe da dariya dan she s extremely happy, Ammi ta kwadama Miemie duka tace  tashi ki fita wuce jeki daura sanwa mara kunya tashi Miemie tayi takalli Amirah tace  Amaryan Dr Marwan Amirah tasake washe baki.

Ammi na kallon ikon Allah saida Miemie tafita Ammi tace  ki natsu ko kinaso raina ya bac1? Dasauri ta girgizama Ammi kai tana wani kalan cute smile dake melting zuciyan mutum, Ammi tace  anayin abubuwa da yawa agidan miji, dagayau zan fara koya miki girki, da yanda ake gyara gida kinji gyadama Ammi kai tayi tace  Ammi anjima mijina zaizo? Tsayawa Ammi tayi turus tana jin nauyin yanda Amirah tace  mijina saita harareta tace  ban sani ba
Ammi tayi shiru tace  kin tuna wankan tsarki dana koyamiki kinayi duk idan kin gama period dinki? Dasauri ta gyadama Ammi kai, magana Ammi zatayi saita kasa maganan yamata nauyi ita zata koyama Amirah bangaren nan? Saita kasa tace  kome yafaru tsakaninki da mijinki karki fadama kowa kinji, sirri ne gyadama Ammi kai tayi, Ammi tace  muje kiga yanda Miemie ke daura abinci a wuta .
***


Tunda suka koma gida yasami all yayyinsa baimason surutun su dan harsun fara ango ango ya hade fuska yawuce dakinsa, bayi ya shiga yayi wanka da kyau yafito pajamas ya saka saiya fito yazo ya kwanta akan gado yayi shiru saiya lumshe idanu 3weeks is so long yafadi murya chan kasa saiya bude idanu dasauri maisa yafadi maganan? Deep down jiyake kaman yabude idanu yaga Amirah, da akace an daura musu aure dudda he s trying to fight d feeling saiyaji sonta yawani karu yakara doubling a zuciyansa.
EPISODE 5?? 0??




2WEEKS!
yau duka duka saura kwana 6 tarewa, bangaren Umar yagama gidansa tsaf dan ana maganan satin nan za aje ayi jere Ammi babu abinda batama Miemie ba masu kyau na gata kuma, ta zage gyara yaranta take ba kama hannun yaro, ga mai gyara su yan Maiduguri, kyan da Amirah da Miemie sukayi yabaci, Amirah jikinta kaman glass, cikinta ciwo yake sabida kayan matan da ake bata kaman yasoma ma jikinta yawa da kanta Ammi tafara ragewa cus taga kaman Amirah tamafi Miemie sensitive jiki and abu namata aiki ajiki sosai.


Ammi babu abinda bata koya mata ba, gyaran gida, gyaran daki, girki, da yanda ake handling su gas, Ammi tayi iya kokarinta takoya mata intimacy takasa wani nauyi takeji, tagayama Lami tadan koya mata wani abu amman ina daga ita har Lami abu daya suke, sun kasa, gawani kamshi da Amirah keyi an gasa an huda jikinta da turaren shuwa Arab na Maiduguri, Amirah kullum saitayi maganan Dr Yaushe zaiso amman shiru babu wanda yasani, shirye shirye suke ba kama hannun yara, Umar yakawo ma Miemie dubu dari uku na dinkunan ta an kawo akwatinta yau wlh wlh yayi kokari, gobe da safe za aje mata jere zai aiko da mota.


Bangaren su Mami suma shirye shirye suke bana wasa ba Abba ya ijiye kudi na ban mamaki hat chanza penti na gidan akeyi suma biki suke shiryawa meanwhile Mami tagama hada akwatin Amirah, Abba da kansa yakira su interior design ana sa komi agidan dayaba Marwan is like 2 houses tsakanin su, shida Mami suka yanke shawaran sAbida condition na Amirah plus Marwan na zuwa aiki gwara suma kusa dasu, kiri kiri Marwan yaki participating in anything, dudda azuciyansa yafi kowa duba calendar da date yawani irin ko_a but kagansa he looks so uninterested saisa Abba ya tsaya tsayin daka kan lamarin gidan da interiors din.


Yau wuraren 9 manya manyan kawayen Mami guda biyu sukazo sai kannenta su Yaya Ammah aka tafi kai akwatina Abba yayi magana da Baffa so ansan da zuwansu an basu address.
Ammi tasa Miemie ta tafi da Amirah gidan makotansu dasuke shiri da Lami sosai, Ammi tasa wata lace mai kyau tayafa mayafi mai kyau, wlh Ammi is a very very beautiful woman saitaci gayu ka kalleta saika kara kallonta, Sunyi girki, an soya kaji dan Baffa na kiwo, akai fankasau da waina, da alale na gwangwani dasu cincin da danbun nama makota duk sun shigo, wuraren 2 suka iso akai parking, su Ya Ammah suka shigo da farin cikinsu ana ayiririiii suna ina Maman Yarmu Lami na washe baki tanuna Ammi dake murmushi cikeda natsuwa wani irin rungume Ammi sukayi har Ammi saida tafarajin kunya, nan da nan aka shigo da akwatunan, anan tsakar g1da aka bubbude ana ayiriri, kafin afara kawo abinci, yanda sukaci abinci ko saida Ammi tai mamaki alalen tasss na kare waina da sinasir har take away sukayi suna tambayan waya dafa Lami tace  Maman diyarku ta dafa sun dade sai wajajen four suka tafi suka basu tukuicin 200k suka karba suna godiya sosai duk saida sukai take away na abubuwan da aka musu suka tafi suja murna yau sai Ammi takarajin ta natsu ganin sunada kirki Amirah ta bazata wahala ba.



Marwan na sama yaji sun dawo anata hira ana bada labarin abinci babu wanda yayi maganan Amirah har wani gyara kunne yake da laptop jikinsa amman babu wanda yayi maganan Amirah, Farida ne tace  Yaya bakuga matan Ya Marwan dinba? Wani ijiyan zuciya Marwan yasauke dasauri jin finally an tambayi Amirah, dariya Ya Fadila tayi tace  ai ba a ganin Amarya sai rannan biki wani irin Marwan yaji sai kawai yatashi yawuce yashiga dakinsa karaf a idanun Mami tai wani murmushi batace komiba.


Around 10 na dare Mami tai knocking gaban kofansa ahankali yace  come in bude kofa tayi ta shiga tana kallonsa yana zaune gaban system yana aiki, Mami ta maida kofan tarufe tace  an baka 2months wajen aiki fa Marwan why are you still working ? Batare daya kalli Mami ba yace  just small abu nakeyi? Mami tace  okay tana wycewa closet nasa tace  wai bazaka

29 / 51