AURE KO BOKO 3?

Author :  Category :  Love

Chapter   3 / 9

6K to 9K   out of 25.1K words

Halima tayi murmushi ta canza position din rikon wayar ta, daga dama zuwa hagu, a lokaci guda tana lullube Safeeyah da bargo, bata ce masa ita ta gayawa Zarah ba don bai san ta karanta rubuce-rubucen sa ba. Tace.
"Idan wannan shine alherin mu, Baban Safeeyah Allah ya tabbatar da shi, ya hada mu da dukkan alkhairin da ke cikin sa, ya dawo min da kai lafiya".
Hashim yayi kasa da murya cikin jin matsananciyar kewar matar sa, ya ce "i'm missing you, Sweetheart, anya zan iya kara wasu kwana bakwan a nan gaba ban zo na gan ki ba, na kuma ga apple of my eyes (Safeeyah)? This is too much for me to bear" Halima ta kara kankame wayar hannun ta, cikin tsananin shauki tace.
"Daurewa zaka yi Cheriè, suffer till you succeed. Nothing good comes easy…Halima is there for you forever"
"I so much love you Leemah....." ya fada a raunane.
"And Leemah loves you more!". Ta fada cikin karsashi.




ABUJA
Sai ga Hashim tsakiyar jiga-jigan ‘yan siyasar Najeriya a washegarin ranar Alhaji Datti na gabatar da shi. Sosai ya samu karbuwa a wajen dattijan, sabida kwarjini da kamalar da Allah ya zuba masa. Gami da kwalayen ilmin da ya tara a kananan shekarunsa. Duk da baza'a rasa wadanda zuwan nasa ta hannun Alhaji Datti bai musu dadi ba, don shine shugaban jam'iyya komai ya saka ta zauna. Musamman matasan cikin su. Masu shekaru tsararrakin na Hashim din.
Hashim kallon komai yake kamar a mafarki lokacin da Alhaji Datti ya zaunar da shi a gefensa, a kusa da shi ‘yan takarar gwamnoni ne na jihohin Najeriya wadanda ke karkashin NRC. Lokacin da Alhaji Datti ya tashi yin bayani a matsayin sa na shugaban jam’iyyar NRC bakidaya sai yace,
"Na raba gardamar da ake yi tsakanin mutum biyu, wadanda ke son karbar takarar gwamnatin Kano, wato Aliyu Sardauna da Inusa Zango, na maye gurbinsu da Hashim Ismael Yakasai, ya kawo hujjojinsa a kan cancantarsa da tsammanin da yake da shi na cewa zai fi su yawan mabiya tunda shi ba dan kowa ba ne, sannan matashi ne mai shekaru arba’in kuma haifaffen birnin Kano ne wanda ya zauna a cikin matasa daban-daban mazauna cikin gari (tsakiyar birni) yake kuma cikin irin rayuwar da suke yi.
Ya ci gaba da kawo musu manyan dalilansa da misalan sa na baiwa Hashim wannan takara har sai da dukkaninsu suka gamsu, cewa Alhaji yayi don cancanta ne ba don son kai da nuna fifiko na sanayya ba, banda Aliyu Sardauna da Inusa dake ganin son kai ne karara Alh. Datti yayi don Hashim yana dan uwansa. Amma in ba haka ba ta yaya su da aka yi fadi-tashin kafa jam'iyya dasu rana daya za'a hambare su a bawa bako matsayin su?
Dattijan kam sun gamsu da cewa Hashim din shi ya fi dacewa da tsayawa primary election idan lokaci ya zo.

Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba, cikin dan lokaci fastocin Hashim suka soma yaduwa a jihar Kano da kafafen yada labarai, wadanda komai daga aljihun Alhaji Datti dana jam'iyya yake fita, musamman da yake jam’iyyarsu ita ce jam’iyya mai farin jini a wurin talakawa. Sunansa ya soma fita a hankali a kafafen yada labarai. Matsayin dan takarar gwamanatin Jihar Kano karkashin Northern Region Congress party. Watanni uku da fara campaign ganin irin karbuwar sa yasa jam’iyyah ta ba shi gida da full security a unguwar Nassarawa GRA.

Halima da Safiyyah suka tare yau a sabon gidansu karkashin rakiyar makwabtanta na arziki da Sa'adatu da Dr. Rabiah yayin da komai ke zuwar wa Halimah kamar a mafarki. Kamar ire-iren mafarkan data saba yi tana farkawa ta ga komai bai faru ba.
Ta rasa irin godiyar da za ta yi wa Zarah da ta maida mafarkin Hashim reality, tabbas Zarah ta cika masoyiya ta hakika.
Hashim ya zagayo da hannayensa zuwa kafadun Halima, yana sanye da wata lallausar shaddah light pink, 'yar ciki da wando kawai, ya aje babbar rigar bisa kujera. Halima ta sha ado da swiss lace ruwan zuma dinkin bou-bou, sai kamshin davidoff ke tashi a jikin ta. Falon ya kawatu da english furnitures farare kal komai a saukake, amma yana da matukar girma, ta yadda kujeru seti biyu ya dauka, kowacce kala daban da 'yar uwar ta. Suka hade goshin su wuri guda, dogon karan hancin su ma wuri guda yana zungurar na juna. Sai shakar numfashin juna suke, mai cakude da sanyin turaren jikin kowannen su.
"Cheriè, pls, in mafarki nake ka taimake ni in tashi" " Halima ba mafarki kike ba, gidan ki ne da jam'iyyah ta baki halak malak, ko mun fadi zabe ya riga ya zama naki".
Safeeyah na zaune akan leather tana ta lallatsa kujerar da hannun ta tana shafawa tace "Daddy, nan ina muka zo ne? Kujerar su akwai laushi" dariya suka yi su duka biyun suka isa gareta suka durkusa a gaban ta.
"Safeeyah this is your new humble abode. How i wish you can open your eyes and see its serenity?". Ya sumbaci kuncin ta. Safeeya tace "Daddy idona a bude yake amma bana ganin komai, sai duhu". Halimah kasa tsayawa tayi a wurin ta nufi dakin da ya zam nata tana share hawayen tausayin Safeeyah. Ta bar Hashim yana lallabata yana gaya mata watarana zata gani idan Allah ya nufa.
Saida ya kai Safeeyah dakin ta, yayi mata addu’a ya rufe ta da lallausar bargo, yarage mata wuta, sannan ya shafa kanta ya bar dakin.
Ya tadda Halima a tsaye jikin mudubin jikin bango tana karewa kanta kallo, cikin dan lokaci ta fara ciccikowa, ta fara tada komadar ta, kasusuwan da suka yi mata sarka a wuya sun ciko, ta fara komawa hayyacin ta, duk da yawon kamfen kauyuka da birane bai barin ta hutu sam, kuma tun daga wancan lokacin kawancensu ya farfado da Zarah, dari-darin da ta ke da Zarah duk ta bari. A hankali zuciyarta ta ke budewa daga tsukewar da ta riga tayi a baya, ta fahimci ashe dai tana bukatar 'yar uwa mace wadda zata dinga kaiwa matsalolin ta bayan Hashim, ta soma karbar canjin rayuwar da ya same su tana adopting din sa gradually da budaddiyar zuciya yanzu.
Tana wannan tunanin taji Hashim ya zagayeta cikin hannayensa, ya sumbaci dokin wuyan ta ta baya, tace "Hashim!" Yace "...Halimah-Leemah, me kika tanadar min a daren yau?" Ta juyo gabagadi ta fuskance shi, sannan ta maida masa sumbar da yayi mata, tace
"Duk abinda kake so, whatever…special Baban Safeeyah!".
****




Yawon kamfen da hada-hadar siyasa da ke sa ‘yan siyasa mancewa da iyalansu idan siyasa ta matso, wannan ba haka yake a wajen Hashim Ismael Yakasai ba, duk inda ya shiga, duk runtsin da yake ciki sai ya ware kansa ya kira iyalinsa ya ji muryar diyar sa Safiyyah ya tabbatar ba su da damuwa a kullum, sannan hankalinsa yake kwanciya.
Hatta miskiniya Safiyyah da ba ta da idanu ta san sun samu sauyin muhalli, sauyin abinci da sauyin atmosphere.

Zaben farko wato (primary election) na kara karatowa, abubuwa na kara yi wa su Hashim zafi, ta yadda zaman gida ya karranta gare shi. A daidai lokacin ne Halima ta bada kaimi wajen addu’ar nasara wa mijinta dare da rana yini da safiya addu'a take yi tana sadaqa, Dr. Rabi'ah gabadaya ta janye adawar data ke yi da Halima sai shishshige mata take, Halima bata taba canza mata fuska ba dai-dai da rana daya, sabida ko kare ne in dai daga dangin Hashim yake tana girmama shi balle Yayar sa uwa daya uba daya. Ta dauki abinda Dr. Rabi'ah tayi mata a matsayin ajizanci irin na dan adam, saidai bazata taba hada matsayin ta da na Sa'adatu ba a zuciyar ta;
Wanda ya soka a lokacin da duniya ta juya maka baya shine masoyin ka, ba wanda ya zo don ya rabi ni'imar da Allah yai maka ba.
Halima na tsananta addu'ah ne domin amsuwar Hashim Yakasai a Kano farat daya a wajen Kanawan Dabo, ya ja hankalin abokan hamayya kwarai da gaske a kansa, wadanda a baya ba su damu da shi ba, kasancewar sa bako a harkar siyasa. Amma yadda ya samu karbuwa farat daya ya gigita jam’iyyar adawa, musamman da aka buga primary election a tsakanin ‘yan jam’iyyarsu ya haye saman Inusa da Aliyu Sardauna da kaso mafi rinjayen magoya baya.
Wannan yasa jam'iyyar NRC (Northern Region Congress) ta kara baiwa Hashim tsaro a duk inda zai shiga haka a gidan sa dama iyalin sa.

*****

ABUJA
GIDAN PROF. ZUBAIR NUMAN

Lokacin da ya shigo gida magriba ta kawo jiki, Prof. Har wannan lokacin haka nan yake zaune kwal shi kadai a tafkeken gida kamar tsohon maye, sai tarin arzikin da ya fi karfinsa kamar ya kashe shi, neman mata kam ya dade da dainawa tunda ya fahimci tsufa ya fara kama shi, kayan alatu na fita hankali har ya rasa yadda zai yi da su a gidansa saboda babu masu mora. Ga tsufa da ya fara cin karfinsa. Domin tenure din sa ta dade da karewa daga NCC. A yanzun shi retired ne daga aikin gwamnati. Zaune yake a gida baya aikin komai. Sai pansho da garatuti da yake karba. Baya zuwa ko'ina sai cin dukiyar da ya tarawa 'ya'yan sa shi kadai ransa.

A kujerar falon shan iskarsa ya zauna ya kwantar da kai a masangalin kujera yana lumshe idanunsa. Kwanannan ba tunanin da yake yi sai na Halima. Ta tsaya masa a rai har mafarkin ta yake cikin kyakkyawan yanayi. Wayarsa ya dauka a karo na sau ba adadi ya kira Hanan, wadda ke gidan mijin ta a garin Porthearcourt, ita kam Hanan har ta fara jin tausayin Daddyn nasu, a bisa damuwar sa akan son sanin inda Halima take, ta fara karaya, amma in ta tuno gargadin Halima sai ta kara sarewa.

"Idan kika fadawa Daddy kinsan inda nake Allah ya isa Hanan ban yafe miki ba".

Ta kuma tuno muguntar da shi Daddyn ya yiwa Haliman. Sai ta ga cewa Halima ta fi ta gaskiya, bata bukatar Daddy a halin yanzu cikin rayuwar ta. Bai ji kanta a lokacin da take neman jin kansa da gafarar sa ba!!!

“Yanzu Hanan ba za ki tausaya min ba? Duk soyayyar da na ba ku kin manta, ba za ki gaya min ina Halima ta ke ba sai ranar da na bar duniya ban ganta ba ko? Hanan ki tuna ko waye Daddynku, shi ne mahaifin ku mai sonku da kula da ku, wanda ya yi muku komai da uwa ke yi wa ‘ya’yanta. Na karbi kuskure na kun fi ni gaskiya, ba za ki afuwan ta min ki hada ni da ‘ya ta ba?”
Ya soma wani irin tari kuful-kuful, maganar ta sarke ta kasa fitowa, alamun rashin koshin lafiya ya bayyanar da kansa a tare da Farfesa.
Hanan couldn’t keep it, ta yi shiru tana hawaye. Ba za ta iya kirga wannan shi ne karo na goma sha nawa da Daddy ke rokonta ta hada shi da Halimah ba.
“Daddy sis Leemah ba ta cikin Abuja fa, nima nemanta nake yi ruwa a jallo. Amma insha Allahu zan kara zage damtse wajen neman ta, kuma zan gaya maka da zarar na samu labarin ta”.
Ta kashe wayar ba tare da ta jira cewarsa ba. Kada ya karya sauran lagon ta ta karya alkawarin data yiwa Leemah. Sannan a take ta kira Halimah, ta gaya mata komai kan damun ta da Daddy ke yi wajen neman ta.
Halimah wadda ke hakimce cikin luntsumemiyar kujerar leather ta falonta, ta yi murmushi ta kwantar da kwayan idon ta kasa tamkar Hanan na kallon ta, sanna tace da kanwar tata.
“Kyale Daddy kin ji Hanan, har yanzu bai fara nadama ba, kadaici ne ya ishe shi. Yake neman abokin taya zama, tunda kema kin tashi. So yake na koma mu ci gaba da zama ko? To ni da igiyar AURE za'a kai ni kabari na insha Allahu".

****






Hanan Zubair, ta fito daga dakin ta da gudu jin 'yar ta Yusra na callara kuka, sai ta hangeta tana mirginowa daga matattakalar dogon benen su har ta kai kasa... jini ya soma malala kamar an sunce famfo. Wata kara da Hanan ta saki ita tayi sanadiyyar fitowar Saleem a guje shima daga kitchen din falon, kafin Hanan ta idasa saukowa ta cimma 'yar, Saleem ya riga ta.
Ya girgizata ya girgizata amma babu alamun akwai sauran rai a jikin ta. Ta rasu!.
Hanan da mijin ta Saleem sun shiga wani mawuyacin hali, na rashin yarinyar, duk da ba ta hanyar halal suka sameta ba suna son ta kamar yadda iyaye ke son kowanne da. Babban tashin hankalin su ba'a fi kwana biyar ba kenan da yiwa Hanan check up a asibiti bayan wani zubar da jini da tayi ta yi mara yankewa, likita ta tabbatar musu Hanan bazata iya sake conceiving ba (daukar ciki). Mahaifar ta ta yi rauni.
Tun daga lokacin kuma Hajiyar Saleem ta bude masa wuta kan sai ya kara aure, tunda shegiyar ta mutu, kuma an ce bazata sake haifar na halali ba.
Da wa zata yi sharing wannan abubuwan alhinin da suka sameta tunda su ba su da uwa? Sai Haleemah kadai.
Watakila Halimah ta tausaya mata ta bata Safeeyah ma, ita kuma ta yi alkawarin yi mata kyakkyawan riko fiye dana diyar data haifa.
Saleem bai hanata zuwa Kano ba data ce masa zata je wajen Yayar ta Halimah. Duk abinda zai sa ta farin ciki a wannan dan tsukin shi yake yi. Washegari ya yankar mata tikitin jirgin Azman mai zuwa Kano daga Porthearcourt.
*****




Hanan ta sauka a Kano da yamma lis, daga nan ta dauki Adaidaita zuwa unguwar data san su Halima suke wato Yakasai. Bata gayawa Halima zata zo ba, surprise take son yi mata.
Saidai katon kwado ne yayi mata sallama. Wani dake tsaye daga gefe ya ce da ita. "Ai tunda aka tsayar da Hashim takarar gwamna suka tashi suka koma Nasarawa".
Hanan tace "no, ba wadannan ba dai, ko suna ne ya zo daya" yace "in dai Hashim mijin Halima mai kwan kaji ne to shi nake nufi".
A take Hanan ta fiddo waya ta kira Halimah. "Sis, gani a kofar gidan ku ana gaya min wai kun tashi" Halima tsabar farin ciki da zuwan Hanan kidimewa ta yi, tace da Hanan ta tsaya anan kofar gidan sun yanzu zata turo direba ya dauketa.

Hanan sai ta kara sakankancewa da al'amarin Ubangiji. Ba jimawa direban ya faka a gabanta ta shiga suka nufi Nasarawa.
Halima da Hanan suka wani irin rungume juna kafin Halimah ta saketa ta tambayi baby Yusra. Hanan ta nemi waje ta zauna tana share hawaye da gefen mayafin ta, lokacin ne Halima ta lura da tsananin ramar da Hanan din ta yi. Jikin ta yayi mugun sanyi, ta zauna gefen Hanan tana kara tambayar ta ina Yusra?
"Ta rasu!"
Hanan ta fada tana kifa kanta a kafadar Halimah. Tare da rushewa da kuka.
Tiryan-tiryan ta bata labarin yadda Yusra ta fado daga bene ko shurawa bata kara yi ba, da matsalar mahaifarta sannan da halin data ke ciki da mahaifiyar Saleem a yanzu.
Halima bata san yaushe ta fashe da kuka ba suka hada goshin su suna ta yi. Bazasu daina dakacen rashin rayuwa tare da mahaifiya ba. Wani tunani ya zo wa Halimah.
Hashim ya dade da yi mata alkawarin sada ta da dangin ta na uwa da uba, tana ganin babu lokaci mafi dacewa da hakan irin yanzu, ga ta ga Hanan in Salim ya amince su je tare.
"Lokaci yayi da zamu nemawa kanmu gata Hanan, mu tashi mu nemo dangin mu na uwa da uba, mu bar Daddy da halin sa shi kadai don bazai taba canzawa ba".
Hanan tace "wallahi ya canza Leemah, ya dade da

3 / 9