AURE KO BOKO 3?

Author :  Category :  Love

Chapter   2 / 9

3K to 6K   out of 25.1K words

Ba za ta iya jure ganinta cikin wannan rayuwar ba. Duk da Halimah ta nuna ba taimako ta ke bukata ba, sannan ba ta ga nakasu cikin rayuwar da ta ke yi ba, zama lafiya ya fi zama dan Sarki a wurin Haleemah. Haka nan a karshen labarin da ta ba ta, ta nuna Hashim ya daina sha’awar aikin gwamnati ko wani aiki da ya shafi zaman ofisoshi, wanda shi ne iya taimakon da za ta iya yi musu.
Ga Halima babu takardu balle ita din ta sama mata aiki. Sai ta tuna Halima zata iya sake karbar takardunta online daga jami’ar National Autonomous University Mexico. Zata yi mata wannan kokarin sai dai Halima ta ce bata bukatar duk wani abu da ya fito daga gumin Daddynta. Karatun ta kuwa gumin Daddy ne. A yadda Halima ta ce, he only has passion for POLITICS. Itama ba gaya mata yayi ba, ta fahimci hakan ne daga irin rubuce-rubucen da yake yi akan shugabancin Najeriya. Wani tunani ne ya fado mata, nan da nan ta yi murmushi, don tana ganin ta samu mafita.

Waya ta dauka ta loda mata isassun kudi bayan fitar maigidanta aikin da ya kawo su Kano, sannan ta kira mahaifinta. Tsohon gwamnan jihar Bauchi Alhaji Datti Giade. Bayan sun gaisa Zarah ta ce.
“Daddy, za ka iya tuna Bestyna Halima Zubair Numan, wadda muka yi karatu a Mexico tare?”
Ya yi dan tunani kafin ya ce, “Ko ‘yar gidan Prof. Numan na NCC?”
“Ita fa Daddy, dogon zance ne, zaka iya sauraro na na minti talatin?”.
“Babu matsala, ina jinki Fatimatul-Zahra’u”.
Tiryan-tiryan Zarah ta koro masa labarin Halimah, tun daga haihuwar su da rayuwar su hannun Ubansu babu uwa babu dangi, rikicin aurenta da mahaifinta da hukuncin da ya yanke akan su, wahalhalun da suka sha a ryuwa, har zuwa kan gabar da suke kai a yanzu ita da mijinta Hashim.
Sosai ya yi mamaki, don bai taba jin sacrifice makamancin wannan ba, ya kuma tausaya wa Halima ba dan kadan ba.
Ya ce, "Dama har yanzu akwai ‘yan boko masu irin wannan gurbataccen tunanin irin Prof. Numan? Aure ai gaba yake da komai, kuma umarnin Ubangiji ne. Har ga Allah ba ta da hakkinsa, domin Ubangiji da Ya yi mana umarnin yin biyayya ga iyaye yayi togaciya kan ban da abin da ya saba umarninSa ne.
Ki kira min yaron, ya zo nan gida Bauchi ya same ni, ya taho da dukkan takardun sa".
Murna wajen Zarah ba a cewa komai. A take ta kira Halimah ta gaya mata. Ta ce, Hashim ya yi kokari gobe ya tafi Bauchi, ta bada lambar da zai kira idan ya isa tasha za a zo a dauke shi zuwa gidan su Zarah.
Halimah ta sha daga da Hashim kafin ya yarda zai je Bauchi wajen Baban Zarah. A cewarsa shi fa ba ya bukatar aiki, da zata je ta wani ce da kawarta ta samo masa aiki, abin da yake so ya san ba zai taba samu ba tunda ba shi da hanyar shigar sa. Bai san cewa Halimah na ganin rubuce-rubucensa ba, kuma ta shigar da zancen cikin labarin da ta bai wa Zarah.
Mahaifin Zarah kuma tsohon babban dan siyasa ne, wanda ya yi gwamnan Bauchi har sau biyu, ya yi sanata dinta ya yi minista. A halin yanzu shi ne shugaban jam'iyyar NRC, jam'iyya mai farin jinin da babu kamarta a Najeriya.
A yadda ya ji labarin Hashim daga bakin Zarah da 'determination' dinsa, sai ya ga kwarai yana bukatar irinsa matuka a siyasa, musamman a wannan lokaci da siyasa ke gabatowa. Ya gama tsara abubuwa da yawa a kan Hashim tun kafin ya zo, albarkacin Halimah da Zarah. Yana so yarinyar ta samu 'future' mai kyau albarkacin sadaukarwarta da gudun duniyarta.
Don ta kara jin tsoron Ubangiji ta san cewa wanda ya tsorace Shi ba zai tabe ba. Ta kara zage damtse wajen biyayyar aure, ta manta da rayuwarta ta baya.
Kudin motar zuwa Bauchin ma Halimah ce ta yi fafutukarsa da kyar da sudin ludayi daga cinikin kwan kajinta. Ya shirya a ranar asabar ya kama hanya, bayan Halima ta bi shi da addu'a da fatan alkhairi mai dumbin yawa.
*****
















BAUCHI
Hashim ya sauka a Bauchi lafiya da yamma lis, a matukar gajiye da takure da zaman bus, ya kira lambar da aka ba shi, mutumin ya gaya masa daidai inda zai tsaya ya ce zai iso nan da minti goma sha biyar.
Wata 'discussion contineous' ce ta yi parking a gaban Hashim. Mutumin ya fito ya ba shi hannu tare da karbar jakar hannunsa ya bude masa kofa ya shiga ya rufe, sannan ya zagaya mazauninsa ya tada motar.
Har suka zo unguwar 'Fati Mu'azu Links' inda gidan su Zarah yake suna hira shi da mutumin wanda ya ce sunansa Marzuq, shi ne babban yaron Alh. Datti Giade, wato mahaifin Zarah. Bangaren saukar bakin gidan su Zarah ya nufa da shi, ya bude masa daki ya ba shi mukullin, ya ce ya huta zuwa gobe ne zai gana da His Excellency, za a kawo masa abinci yanzu.
Hashim yana yin sallah, kafin yayi komai Halimah ya kira ya gaya mata saukarsa lafiya, ta hada shi da Safiyyah suka sha hirar su. Da kyar suka yi sallama cike da kewa da kaunar juna kamar kar su rabu, sannan ne ya ci abincin da aka kawo masa. Yayi wanka ya canza kayan jikin sa.
Da daddare ma kafin ya kwanta sai da ya sake kiran su. Washegari da safe bayan ya yi wanka ya kimtsa, Marzuq ya zo tafiya da shi wajen Alh. Datti.

Cikin nutsuwar sa ta halitta Hashim ya yi sallama a tankareren falon, Alhaji Datti ya amsa a mutunce, tare da cewa,
"Shigo ka zauna nan kusa da ni Mallam Hashimu".
Cikin matsanancin ladabi Hashim ya gaishe shi. Ga mamakin Hashim sai ya ji ya ce da shi.
“Yaya Halimatu da Safeeyyah? Ina fatan ka kira su bayan isowar ka?”
Kansa a kasa ya amsa da cewa, yanzu ma kafin ya shigo nan sai da ya kira su, sun tashi lafiya dukkan su.
Alhaji Datti ya fara jan sa da hira, cikin sakewa da hila irin ta manya, har sai da Hashim ya fara sakin jiki da shi ya daina nuku-nuku, labarin siyasar Najeriya yake ta bashi da mulkin soja dana farar hula na tun kafin a haife shi. Yana comparing dinsa da wanda ake ciki a yanzu. Yace "ratar dake a tsakanin siyasar da data yanzu mai tsananin fadi da girma ce Hashim, yanzu majority ana siyasa ne kawai don a yi kudi dare daya, yayin da shuwagabannin baya mulki suke don gina al'ummar su selflessly'. Shi Hashim yadda Alhajin ya sakar masa fuska da zuciya kamar ya dade da sanin sa har mamaki yake bashi. Duk zurfin ciki irin na Hashim dole ya saki jikin sa suka fara hira sosai da baban Zarah. Sai da Alhaji Datti ya tabbatar ya kama kurwar Hashim sannan ya sallameshi. Yace gobe da safe zasu gana sosai.
Washegari din kuma bai samu ganin sa ba sai azahar. Hashim na shigowa falon yace "koma ka dauro alwala mu yi jam'in sallahr azahar" Hashim yace "ai da alwala ta" "to kai zaka yi mana limanci, bisimillah".
Da suka idar da sallahr kuma Alhaji Datti yace "ban ci komai ba Hashim mu fara cin abinci ko?"
Tare suka ci abinci bisa ledar cin abinci wadda aka shimfida aka jera abinci nau'i-nau'i. Da suka kammala yace ya raka shi unguwa, Hashim ya fara tunanin Alhaji Datti bai kira shi don komai bane sai don ya zame masa abokin hira.
Tare suka tafi ofis din Alhajin, ya taimaka masa kan wasu ayyukan sa, sannan suka dawo gida.
Suna sauka a mota yace Hashim ya wuce masaukin sa sai Allah ya kaimu gobe.
Haka yayi ta jan Hashim a jikin sa kamar dan cikin sa, kulawar yau daban data gobe, don ya lura in ba da hakan ba bazai samu ya yarda da taimakon da yake son yi masa ba. Ya farfado da matacciyar zuciyar sa akan nasarar rayuwa. He already assumed shi bai zo duniya da sa'a ba. Ya riga ya karbi rayuwar sa a yadda take, baya bukatar wani sauyi a cikin ta.
Hashim na so ya koma gida amma kullum Baban Zarah cewa yake sai gobe zamu tattauna.

****

"Cheriè, sai yaushe zaka dawo ne?"
"Ba ke kika jawomin ba Halima tunda nazo babu wata kwakkwarar magana sai hira da debe masa kewa da taya shi yawo a mota, anyway, he's a nice father. Kuma ina jin dadin zama da shi sosai saboda yawqn ibadarsa. Amma na kusa runtse ido in ce masa zan tafi wajen Halimah ta".
Halima tayi dariya tace "ka daure baban Safeeyaah, haka kawai bazai kira ka don kuyi ta hira ba, mu kam dai kada ka damu damu lafiya sumul muke. Ga Sa'adatu ma jiya ta zo mana wuni mun sha hira, ta kawo ma Safeeyah kuli-kuli mai suga tana ta ci tun jiya". Da haka Halima ta kalallame shi ya yarda zai cigaba da zama har Alhajin ya sallame shi.

Ilai kuwa washegari Baban Zarah ya kira shi, yau kuma kai tsaye cewa yayi, yana so ya fara ba shi tarihin iyayen sa da na rayuwar sa gabadaya. Domin shi dai ya riga ya samu Da (yana nufin Hashim din). Hashim yayi murmushin nan nasa mai ratsa zuciyar Halima, sai ya samu kansa da kasa musanta bukatar Alhaji Datti Giade, wani abu da bai taba tattaunawa da kowa ba a duniya bayan Halimah.
Ya sunkuyar da kai ya gaya masa komai a kan mahaifinsa wanda Ba-Kano ne gaba da baya dan Yakasai, da kuma Innarsa, wadda ita Basudaniya ce. Aurota yayi ya zo da ita Najeriya.
Yadda ya yi dukkan karatunsa da taimakon mahaifiyar sa, bayan rasuwar mahaifin su, samun aikinsa da NCC da taimakon Halimah. Bayan ta kade shi da mota. Zuwan su Holland da yadda soyayya ta kullu tsakanin su. Sallamar su da Prof. ya yi bayan auren su, amma ya dan sakaya wasu daga wahalhalun da suka sha a rayuwa ko wadda suke ciki a halin yanzu. A wurin sa fadin halin kunci daka ke ciki ga wani bayan mahaliccin ka, tamkar rashin godiyar Ubangiji ne.

Cikin mutuwar jiki Alhaji Datti ya ce ya ba shi takardun sa ya duba, ya ciro su daga jakar goyonsa ya ba shi cikin ladabi.
Ba abin da ke fita bakin Alhaji Datti sai, “Excellent… Mimtaaz… jamilan Jiddan!”.

Ya dubi Hashim da murmushi ya ce, “Ashe tare da Dr. Of Philosophy nake zaune ni ban sani ba? Dr. of Telecommunication Engineering. Dr. Hashim kana son aiki a jami’ar Bayero? Ko Igbinedeon University? Ko Northwest University ta Kano, ko kuwa ba ka son aikin jami’a ka fada min duk wani industry da ka ke son yin aiki da shi a Najeriya?”
Hashim ya sadda kai yana murmushi cike da kaunar karimin dattijon, bafullatanin Giade, ya ce, a ha kali muryar sa ke fita inda ya ce.
“Babu ko daya, bana sha’awar aiki ranka ya dade! All the aspirations on it has gone”.
Alhaji Datti ya yi murmushi domin ya tsammaci jin hakan dama, ya ce, “Kana son international business kenan?”
Nan ma Hashim ya ce, “lala!”.
Alhajin so yake ya fada masa da bakinsa ga abin da yake so, yake da buri akai, shi ya sa yake ta zagayewa. Amma Hashim ya ki fada sabida zurfin cikin sa. Yana son ya kara tabbatar da wannan determination din daga bakinsa kamar yadda ya ji daga bakin Zarah, kada ya zamo cewa ya yi pushing ra’ayinsa ga shiga siyasa, wanda wannan ba shi ne abin da yake so ba. Don haka ya ce,
"To Hashim gaya min, me ka ke so to earn a living, tunda magidanci dai mai iyali bai zama ba tare da neman na kansa ba, kula da iyali abu ne mai matukar wuya, wanda dole sai da kwakkwarar sana’a mutum zai iya shi cikin sauki’.
Hashim ya kara yin kasa da kai. A karo na farko ya ji yana son fadin wannan burin nasa a fatar baki, ba don yana da hope na cewa zai same shi ba, wanda bai taba bayyanawa kowa ba sai alkalamin sa da littafin sa. Ko Halima bai taba bude baki ya gaya mata ba, ya dauki abun ne a matsayin mafarki (dream), which will never born alive. Wanda ba zai taba zama reality ba.

“Ni burina kawai siyasa ce ranka ya dade, ina son shugabanci kuma ba ni da hanyar shigar sa ko samun sa. Babban mission dina na son shiga siyasa shi ne; inganta rayuwar matasa marasa aikin yi, kawar da rashin aikin yi (unemployment) wanda ke maida su marasa amfani, marasa imani, kawo sauyi a kan yadda ake mulkar talaka da zama shugaba mai fada da cikawa ba irin shuwagabannin da ke ci yanzu ba. I want to curve POLITICAL DICHOTOMY.
Ka ga kuwa buri na zai tabbata a mafarki ne kawai daga nan har gaban abada, tunda ba ni da wata hanyar kaiwa gare shi”.

Wani tattausan murmushi ya subucewa Alhaji Datti, ya dubi Hashim da ke duke a gaban sa da manyan idanun sa irin na manyan shuwagannin da suka sha gwagwarmaya a rayuwar siyasa suke kuma da experience na su waye masu leadership motivation ko a kwayar ido. Jin sa yake a ran sa kamar 'yar da ya haifa, Zarah. A sati guda kacal da yayi tare da shi ya gama lakantar duk abinda yake son laqanta akan sa. Wato duk wasu (leadership qualities) ya mallake su har da kari.
“Ka zo gidan siyasa Da na, kuma ka shige ta ka gama. Irin ka muke nema ruwa a jallo masu patriotism, sannan masu jini a jika da dimbin ilmi a kananan shekaru, wadanda za su gaje mu tunda mu mun kusa ja baya.
Welcome to the NRC (Northern Region Congress party). Gobe za mu wuce Abuja tare in gabatar da kai ga shuwagabannin jam’iyyah. Insha Allahu Hashimu ka shigo da kafar dama, domin akwai rikici da ake yi tsakanin mutum biyu da za mu ba wa takara, zan raba gardama da kai duk su hakura domin kuwa ka fi su cancanta ta kowane bangare, welcome on board!".
****




















Hashim ya koma masaukin sa a daren ranar yana jin komai dake faruwa kamar a mafarki. Ya kasa hadiye wannan magana a ransa ba tare da yayi sharing din ta ga Halimar sa ba. Ya dauki waya ya kira Halimah wadda ke yiwa Safeeya shirin barci a lokacin.
"Cheriè, baka kwanta ba?"
Sassanyar muryar Halima ta tambaya.
"Ina zan kwanta Sweetheart, ban ji lallausar muryar ki mai tada tsigar jiki na ba? Baki yimin goodnight kiss ba? Bamu yi sallama mun gaida juna ba? Rabona da ke tun safiyar yau. Ga rayuwa na kokarin canzawa incredibly! Kin san wani abu?
Daddy yace gobe zamu tafi Abuja ya sanya ni a jam'iyyar su, jam'iyyar NRC dai da kika sani, he sounds kamar dama can ya san buri na kenan a yadda yake magana".

2 / 9