Author : Category : Love
AURE KO BOKO?
(Littafi Ga Matasa Maza da Mata)
3
SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
GABATARWA
Da sunan Allah mai Rahma mai jin kai.
Duba da halin da matasa ke shiga a kasarmu Nijeriya a yau, daga mazan har matan, akan rashin aikin yi ga wadanda suka samu damar yin ilmin zamani mai zurfi da matsalolin da hakan yake haifarwa, sannan da halin wasu daga cikin manyan 'yan bokon wannan zamani na baiwa boko fifiko akan addini, yasa na yanke shawarar rubuta littafin AURE KO BOKO? Ba don komai ba sai domin ya zamo hannun ka mai sanda ga irin wadannan 'yan boko da matasa masu zurfin ilmi marasa aikin yi. Tasirin furucin iyaye akan 'ya'yan su mai kyau ko maras kyau, hakika shi bakin iyaye kaifin sa da tasirin sa yafi na reza. Sannan 'ya'ya amana ne a hannun mu, kasancewar Ubangiji yayi musu umarnin su yi wa iyaye biyayya sai da yayi tagociya ga cewa banda akan umarnin Ubangiji.
Ina fatan wannan dan littafi ya zamo mai amfani ga al'umma, matasa maza da mata, ya zamo sadaqatul jariya ga iyaye na ya yafe min kurakuran da ke cikinsa.
- Sumayyah Abdulkadir (Takori)
3rd June, 2021.
GARGADI
Ban yarda a karanta wannan littafi a kowanne gidan radiyo ko kafafen yada labarai ba tare da izni na ba, ko copying dinsa a kafafen sada zumunta, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma daga Lauya na Barr. Sadiq Rufai Wali.
GODIYA
Ga dukkan members na Takori's online Forum, na gode da kaunar ku da goyon bayan ku.
FATAN ALKHAIRI
Ga duk makaranta littatafan TAKORI. Wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ina godiya da yabo da fatan alkhairin da kuke yi mun, Allah ya barmu tare cikin alherin sa, har zuwa ranar da muka daina numfashi.
TUNASARWA
Wannan littafi da labarin da ya kunsa duk Kirkirar marubuciyar shi ne. Sai a guji zargin cewa an yi ne don wani ko wata, ko wasu gungun jama’a, ko an dauki rayuwar wani. In ka ji wani abu da yayi kama da naka to arashi ne kawai aka samu.
-Takori
AURE KO BOKO 3
Direban motar wadda mace ce ta yi azamar dauke kan sitiyarin motarta, ta gwammace ta buga wa motar gabanta a kan dai ta kashe mai rai. A take mummunan accident din motocin ya ziyarci kunnen duk wani mahaluki da yake wajen. Motocin biyu sun kwankwatse sun yi raga-raga amma sumul matukiyar motar ta fito cikin shiga ta alfarma jikinta na rawa da karkarwa, don dai ta tabbatar ba ta gogi jikin Safiyyah ba ko kadan, wadda ta yi tuntube da dutse ta fadi a kasa, bakin ta ya fashe. Bata ko damu da damejin da dalleliyar motar ta kirar jiya-jiya tayi ba. Fatan ta da burin ta bai wuce ya zama bata yi sanadin ran wannan kankanuwar halittar Ubangijin ba.
Da gudu Halimah ta iso wurin, cikin wani yanayi na fita hayyaci, ta kwala kiran sunan “SAFEEYAH!” da iyakacin muryar ta, tare da daga ta a jikin ta tana girgiza ta cikin yanayi na madaukakin tashin hankali.
“Dauko ta mu karasa asibiti mafi kusa a duba ta sosai, don Allah”.
Matar ta fada cikin gigicewa. Muryarta da jikin ta na rawa. Guilty ya dabaibaye ta.
Halimah sai ta ji kamar ta san muryar, kamar ta sha jin muryar, a very familiar voice wadda duk inda ta ji ta zai yi wuya ba za ta kasa gane ta ba.
Da sauri ta juyo, cikin wani yanayi suka hada ido da matar. Gaba dayansu suka zaro idanu cikin mamaki da tu'ajjibi a lokaci guda suka hada baki wajen anbaton sunan juna.
“Zarah!”
“Haleemah- Leemah!!!”
Da wata irin azama suka kama suka kankame juna, Safeeyah na tsakiyar su, suna maimaita kiran sunan junansu. Kukan Safeeyah ne ya sa suka saki juna. Zarah ta sunkuya ta dauke ta tana fadin,
“Come on beauty, bude idon ki sosai ki ga Mamanki Zarah, ina fatan baki ji ciwo ba?”.
Ta maida dubanta ga Halimah tana kallonta sama da kasa cikin wani irin dumbin mamaki.
“Leemah, ke ce kuwa? Daga ina ki ke haka? Ina za ki je?”
Idanunta kamar za su fado waje. Murmushi Halimah ta yi, ta ce, “Maama na zan kai asibiti, ta wayi gari da kyanda, nan ne Murtala ba nisa, bari mu karasa maza”.
Zarah ta kama hannunta tana hawaye.
“I will NEVER let you go Haleemah, sai na ji daga inda ki ka fito, sai na ji labarin rayuwar ki. Sai naji abinda ya maida ke haka. This is not my Leemah! My beautiful, elegant Leemah. Ina Daddyn ki? Ina Hanan? Me kike yi a Kano? Wa kika sani a Kano? Leemah please tell me everything about you….”.
Zarah ta fada tana gwama numfashi, ganin cewa da gaske Halimah niyyar tafiya take yi ta bar ta a wurin.
Halimah ta san a baya ba ta boye wa Zarah komai, amma yanzu kam ba ta da abun fadi, don ba ta neman taimakon kowa. A gamshe ta ke da rahmar lafiya da wadatar zuci da sama da komai miji nagari, da Ubangiji ya yi mata.
Zarah kawai waya ta fiddo a jakar hannun ta, gabadaya hannu ta da jikin ta kyarma suke, ganin Halima ta ki ce mata komai sai kallo. Ba ta bi ta kan surutun mutane a kan accident din su ba, da mai motar da ta bugawa da ke ta kumfar baki da balbalin fada. Ta fadi dai-dai inda ta ke ta cikin wayar, ba jimawa sai ga mota (lemousine) a gabansu, tare da bakanike. Ta ba wa mutumin hakuri ta ce ga bakanike nan zai tafi da motocin a gyara musu, za ta biya komai.
Jikinta sai rawa yake don hankalinta duka yana kan Halimah. Tana gudun kada ta tsere ta bar ta. Don bata gama tabbatar da psychogical well being din ta ba.
Ta sanya Safiyya a motar, sannan ta ja hannun Halimah suka shiga, ta fada wa direban asibitin da zai kai su, wanda duk zaman Halimah a Kano ba ta ko taba jin sunansa ba.
Kwararren likita ba’indiye ne ya duba Safiyyah sosai, ya hada allurai ya yi mata, ya rubuta mata magunguna masu inganci ya ce yanzun nan a je a saya a bata ta sha a take.
Zarah ta karbi takardar ta ce su jira ta, ba jimawa ta dawo da ledar magungunan mai tambarin pharmacy din asibitin. Ta bude daya bayan daya cikin hila da dubara ta bai wa Safiyyah, da gani ta saba da baiwa kananan yara magani, sannan ta dauko ta a kafadarta, tana kankame da hannun Halimah suka koma mota, ta ce da direban ta ya kai su masaukin ta.
Suna tafe a hanya Zarah ke gaya mata, sun zo seminar lauyoyin Arewa anan Kano ne ita da maigidanta Barr. Zahraddeeni Alhassan, jiya suka zo, nan da jibi za su koma Bauchi. Direban ya shigar da motar gidan saukar baki na Ni’imah Guest Palace, Halimah hankalinta gabadaya ya yi kan Hashim. Duk da hilatar ta da hira mai dadi da Zarah ke yi. Ta dauko tsohuwar wayar ta nokia don ta kira shi ta gaya masa halin da suke ciki, ta tarar da babu ko sisi a ciki sai naira daya, don haka ta ce da Zarah ta maida ita gida, mijin ta bai san za su dade haka ba.
Zarah ta yi mata wani kallo, sannan ta girgiza kai ta ce,
“Ai in kin ga na maida ke ko, kuma na kyale ki kin koma inda kika fito ko, ko ma daga ina ki ka fito ke kika sani. Abinda nake so kawai ki gaya min labarin rayuwar ki dalla-dallah....in na ce dalla-dalla ina nufin daki-daki; tun daga rabuwar mu ranar graduating dinmu na masters degree a kasar Mexico zuwa yau da na tsince ki a Kano hajaran-majaran cikin yanayin da ban taba zato ba.
Jikina na ba ni ko dai kurciya aka yi miki ki ka baro mahaifin ki da 'yar uwar ki?”
Sai ta baiwa Halima bazawarar dariya, "kurciyar lafiya ana zaune kalau? Waye makiyina har haka? Kin sanni ko abokin fada bani da. In kina so in sauka daga motar nan, sai kin ba ni aron wayar ki na yi magana da Baban Safeeyyah, yana can yana jiran mu, in muka dade hankalin sa zai tashi”.
Ba musu Zarah ta ba ta dalleliyar iphone din ta, tana mamakin kauna da damuwar ta ga mijin ta har haka, canjin rayuwa bai sa Halima ta manta yadda ake operating babbar waya ba, ta karba jiki na rawa ta sa lambar Hashim a ciki, wadda ta ke haddace kamar karatun sallah a cikin kanta. Hashim ya amsa very politely da husky voice dinsa.
"Assalamu alaykum, Hashim Yakasai ke magana".
“Cheriè, ni ce Halimah, I met an old adorable friend of mine, Zarah Datti, da nake yawan ba ka labari, wadda ta koya min karatun sallah da karatun Alqur’ani a Mexico. Ta tafi da mu masaukinta a wata unguwa da ban sani ba, ta ce, lallai sai mun yi magana za ta dawo da mu gida”.
“A ina ne masaukin nata? Sabida zan zo in taho da ku da kaina nan da one hour”.
Ta daga kai tana karanto sign board ta ce, “Na ga an rubuta Ni’imah Guest Palace”.
Ya ce, “Alright. Ba matsala, ku gaisa kafin na iso”.
Zarah dai tana ta kallon ta, tana maganar ta da Hashim cikin tarin nutsuwa kamar yadda ta santa tun a can baya, fatar bakin ta a hankali take motsawa, ta kara sanyaya muryarta, ta zuba ladabi mai ban sha'awa da soyayya mai tattare da kauna a cikin ta, tana mamakin soyayya da yardar da ke tsakanin ta da mijin nata haka. Za ta so ta gan shi, ko don ganin me ya taka haka da ya tafiyar da zuciya da ruhin Halimah-Leemah a kansa har haka!.
Dakin da suka sauka ma anan Ni’imah V.I.P room ne, mijin Zarah bai dawo ba tukunna. Abincin da aka ajiye a rurrufe bisa dining ta fara bubbude musu sai tiriri yake yana tashin hadadden kamshi, ta ce su fara ci, suna ci tana baiwa Maama-Safeeyah a baki. Tana mamakin me ya sa yarinyar ta ki bude idon ta har yanzu? Gashi da alamun ba bacci take ba tunda kuwa abinci ma take ci. Amma dai Allah bai nufe ta da tambayar Halimah ba, hankalin ta ya fi daukuwa ga son jin labarin Haliman.
Sai da suka gama suka yi sallah, sannan Zarah ta kara rokon Halimah ta gaya mata labarinta. Tana rokon ta da girman Allah kada ta cire ko harafi daya daga ciki da sunan yi masa kwaskwarima ko sakaya mata wani abu a cikin sa. Ta tuna aminci da yardar dake tsakanin su?
Halimah ta yarda Zarah mai kaunar ta ce ba tun yau ba, mai son ta da alkhairi ce da tsira a duniya da lahira, don haka ta bude baki cikin nutsuwa ta gaya mata komai, tun daga ranar da ta kade Hashim a ma’aikatar NCC, yadda suka fada a soyayyar juna a kasar Holland, badakalar auren su, zamansu na dan lokaci a Abuja, rayuwarsu ta birnin Kano, zuwan Hanan da wayar su ta karshe da ita. Har kawo rabuwarsu ta yau da mijin ta Hashim da zummar zuwa kai Maama asibiti.
A lokacin Halimah ta lura Zarah Datti kuka ta ke yi, kuka ta ke tukuru da ran ta da zuciyar ta, hawaye da majina wani na korar wani. Ba tare da ta damu ko kadan da ta share su ba.
(Manzon Allah SAW ya ce ku ji tausayin mai arzikin da ya talauce).
Shiru ya ratsa a tsakanin su, bayan Halimah ta kai Ayah. Zarah taci kukanta ma'ishi ta koshi, sannan tasa habar zanin ta tana share fuska, ta dau tissue ta fyace hanci. Tsanar Prof. Numan ta wani irin darsu a ranta. Bata taba ganin mugun uba mai selfish interest irin sa ba. Sannan ta ce.
“Halimah ban hada sani da Allah ba, amma na tabbata bautar aure zai kai ki aljannah, sadaukarwar ki za ta baki ceton Annabi, gudun duniyar ki zai tsallakar da ke SIRADI, sannan yardar mijin ki za ta ba ki duk abin da Allah ya tanadar wa matan kwarai a ranar gobe. Allah ya sa ni a damshin ki Halimah!”.
Halimah ta yi murmushi, her beautiful serene smiles, mai narka zuciyar mai kallon ta, daidai lokacin da wayar Hashim ta shigo wayar Zarah, tana dagawa taji muryar sa very soft, a takaice ya ce.
“Ina downstairs, su fito mu tafi in kun gama”. Ya kashe wayar.
Zarah ta tsura mata ido, ganin yadda tayi maza ta mike futuk! Kamar wadda aka tsikara za ta dauki Safiyyah dake cinyar Zarahn.
“Amma me ya sa ki ka ce Hanan kada ta gaya wa Daddy inda ki ke, bayan ya gane kuskuren sa?”
Halima ta yi wani maqalallen murmushi na gefen baki, “Saboda na sanshi, na san ko waye Daddy na farin sani. He is not giving up easily, ban yarda ya yi nadama haka da wurwuri ba. Ita ma Hanan din kan ba yadda zai yi da abin kunyar da ta kwaso masa ne, beside bana bukatar komai daga gare shi sai albarkar sa, kuma yace bazai bani ba”.
Ta dauki ‘yar ta ta nufi hanyar kofa.
“To ba ni lambar wayar ki mana Leemah? Ko haka za mu sake rabuwa without each other's contact, kamar yadda ki ka watsar da ni a baya?”
Halimah ta ji kunya, hakika Zarah ba kashin yadawa ba ce a rayuwarta, amma a halin yanzu ba ta son yin alaka da kowa, ba don komi ba sai don ta fi son ta tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ta, kada alaka da irin su Zarah ya dinga tuna mata da rayuwarta ta baya. Ya raunata imanin ta da yadda Ubangiji yake so ya ganta.
Zarah ba ta tsaya sauraronta ba ta karbi wayar hannunta ta sanya lambarta a ciki ta kira, an yi sa’a da ragowar naira daya a wayar Halimah, don haka kiran ya shiga, ta yi saving mata sunanta da Besty, sunan da ta ke kiranta da shi a baya. Har downstairs Zarah ta rako su tana rike da ledar magungunan Safeeyah.
Nan suka tadda Hashim a reception, yana tsaye ya tokare kafarsa daya a jikin bango, sanye yake da jamfa da wando na farin yadi mara nauyi, looking smart and gentle sabida yadda tsafta ta kama jikinsa. Sumar nan baka sidik ta kwanta luf a kansa. Da sauri Halimah ta isa gare shi tana ba shi hakurin tsayar da shi da suka yi.
Zarah ta karaso tana murmushi ta mika masa ledar maganin.
“I’m so sorry Baban Safiyyah, na dauke su na barka kai kadai. Na dade ban hadu da besty ba, so an zauna ana tattauna bayan saduwa”.
Hashim ya yi dan murmushi, ya ce, “babu damuwa madam, mun gode. Za mu wuce, sai gani na biyu”.
Zarah ta ce, “ga driver yana jiranku zai maida ku gida sai ya dawo”.
Hashim ya ce, “Kuma na tsaida mai adaidaita da ya kawo ni. Ki yi hakuri, next time insha Allah”.
Da haka suka wuce suna daga wa juna hannu ita da Halimah. Suka bar Zarah standstill tsaye a wajen harde da hannaye a kirji. Tana ta mamakin wannan al’amari na kawarta. Akan karan-kanta ita bazata iya sadaukarwar da Halimah tayi ba. Sabida tsoron cin amana da halin butulci irin na maza. Sai dai kam ta yaba da zabin nata, ilmi da kwarjini a gun Hashim abin ba’a magana.
A tsayin daren bakidaya Zarah ta kwana ne tana tunanin hanyar da za ta bi ta taimaki rayuwar Bestynta Haleemah.