Author : MARYAM STAR Category : Horror
a kunnuwanta.
"Allah wadai da halinki Zulai bazan iya ci gaba da cakuɗaki da iyalina ba alhalin baƙin hali ne da ke, tun da nike a garinan kaf ban taɓa jin ko da a labari wani ko wa ta sun aikata irin abin kunyar da kika aikata ba, kamar yanda Me gari ya ce, ki tattara inaki ya naki kibar mana Ƙauyenmu bamu buƙatarki." Tsugunnawa tai a ƙasa tare da dafe kunnuwanda da tsananin ƙarfi ta saki ƙara ta na kiran "Mamman! a'a Mamman a'a a'a." sai kuma kuka me ƙarfi ya ƙwace ma ta irin wanda ke fitowa daga ƙasan zuciya.
Fadeel da jikinshi yai sanyi ya ja sanyayun ƙafafuwanshi ya zauna a kusa da ita ya shiga rarrashinta duk da shima ya na cikin damuwar, sam hankalin Zulai ba ya tare da ita dan baƙin cikin abin da iyayenta suka aikata ma ta agaban jama'a ya dameta, izuwa yanzu ta fara tunanin cewa ita ɗin ba ɗiyar Mamman ba ce.
Yayinda Zulai ke rizgar kuka babu tsaitsayawa wa ta dalleliyar mota ƙirar benz c class ta nufo inda suke a zazzaune, ƙiiiiii lafiyayyar motar ta taka burki yayinda aka ɓalle murfin motar da tsananin ƙarfi, wani dogon kyakkyawan matashi ne me cikar kamala ya fito daga bayan motar, fuskarshi a ɗaure tamau ya nufo inda Zulai da Fadeel ke zazzaune, zuwanshi bai yi wa ta-wata ba ya ɗago kafaɗar Fadeel ya miƙar da shi da ƙarfi sannan ya saka shi cikin jikinshi ya rungume shi tammm kamar zai bayar da shi cikin jikinshi.
Ƙanƙameshi shima Fadeel yai tare da sakin tagwayen ajiyar zuciya cikin farin ciki ya ce.
"Broth yaushe ka dawo? kuma ya akai ka san inda nike?."
Ɗago da Fadeel matashin yai tare da sakin tattausan murmushi sannan ya kama kunnen fadeel ya murɗa da ƙarfi tare da dungure ma shi kai sannan ya ce.
"Bana da isashen time zo muje kawai."
Yana faɗin hakan ya juya wajen Zulai da izuwa yanzu kukanta ya daina fita da sauti sai hawaye da ke zuba kamar an kunna fanfo.
YANZU LABARIN ZAI FARA DA ZAFI-ZAFIN KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA TA KAYA.
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
Chapter 7
بسم الله الرحمن الرحيم.
Kallon secons biyu yai ma ta sannan ya kauda kanshi tare da faɗin "Ta so muje".
Yai gaba abinshi ba tare da ya ankara da ba ta biyo bayanshi ba, sai da ya taimakawa Fadeel wanda izuwa yanzu ƙafafuwanshi sun gaza ɗaukarshi, dan har wani jiri-jiri ya ke gani, har ya shigar da Fadeel front sit shima ya zauna driver sit Zulai na inda ta ke babu ko alamar ta motsa bare ta tashi, cike da zafin zuciya matashin ya tada motar da niyyar ya tafiya zai yi ya barta anan, Fadeel ne ya dakatar da shi da faɗin.
"Sorry broth ita ɗin amanace a wajena ta sadaukar da komi nata saboda ta taimaka min, yanzu haka ta na cikin makamancitar matsalar da ka taɓa fuskanta a wajen Abba saboda ni, pls na damƙa amanarta a wajenka da ba dan ita ba da yanzu baka sameni a rayeba, sannan ita ɗin yanzu matar...."
Bai ƙarasa maganarshi ba yai baya luuuu alamar ya suma.
Cikin kiɗimewa wanda yake kira da broth ya shiga girgiza shi tare da ambaton sunanshi amma ina babu alamun zai farko, hakan ya saka ya fito a birkice ya saɓi Zulai a kafaɗa ya saka ta gidan baya sannan da mugun gudu ya taka motar ya bata wuta ya wuce fitttttttt kamar tsuntsu.
ƘAUYEN YAGAWA
GIDANSU ZULAI.
Wacce ake kira da Mama ce ta cakumi wuyan rigar Mamman cikin matsanancin kuka ta ke faɗin.
"Na rantse da sittin ta Ubangiji baka isa ba Mamman ka yi tsuru-tsuru dan kuwa ruwa ya fika kauri, na rantse da tsarkin Allah sai ka dawo min da Zulai yau ba gobe ba ko kuma ka sawaƙemin kafice kabar min gidana tunda ba da kuɗin salele aka saye shi ba ko na Jummai, imbanda son zuciya irin naka sai ka biye wancan azzalumin me garin ku aikata san ranku, kun kori yarinya cikin dare kamar de wacce tai kisan kai, koda ace kisan kai tai aibata cancanci kora ba, ko dai ka je ka dawo da Zulai ko kuma ka sallameni yau ba sai gobe ba dan bazanbi wannan tsarin na ku ba, ace yarinya A DAREN AURENTA bala'u da masifu su rikito a kanta sai kace wacce ta zagi sama, yasin dubu sai ka sake ni Mamman." kuka ne ya ci ƙarfinta yayin wannan farar tsohuwar ta taso tinƙis-tinƙis daga inda ta ke zaune ta na sharar hawaye ta nufo wajen da Mama ke tsaye riƙe da kwalar Maman.
Ɓanɓare hannun Mama tai ta na faɗin "Rabu da ɗan banza Suwaiba, indai duniya ce gaka ga ta nan ta isheka wanda da riga harma da singileti da ɗan tofi, imbanda zamani ya lalace ina kai ina korar ɗan da aka baka amana dan an yarda da kai, ni dai ba zaka mai da ni tsohuwar banza ba zan tattare inawa-inawa inkama gabana dan ban san da wane ido zan kalli Audul maliki ba."
Wa ta irin zufar tashin hankali ce ta shiga tsatstsafowa Mamman sai yanzu ya gane kwaɓarshi ta yi ruwa, sam ya mance da mahaifin Zulai na nan tafe nan da wasu ƴan watanni, kuma wannan karo ba iya shi kaɗai ba har da mahaifiyarta za'a zo, kafin ya gama tunanin mafita ya sake jiyo salatin matan wajen, dubawar da zai yi sai yaga Mama zube a ƙasa anrufu a kanta, cike da kiɗimewa ya isa wajen da nufin ya taɓa ta, aiko Maradiyya ta zo da iya ƙarfinta ta bangajeshi yai gefe guda zube a ƙasa, kafin ya yunƙura da niyyar tashi ya ji ƙugunshi ya amsa da wa ta iriyar azaba, ya yinda Maradiyya ta saɓi Mama kamar ta ɗauki yarinya tai waje da ita ko mayafi babu, yayinda su Inno da sauran ƴan uwa suka rufa ma ta baya su na koke-koke.
KU KASANCE DA NI A CIKIN WANNAN LABARI MAI RIKITA-RIKITA SANNAN KUMA ME ƘAYATARWA DARE DA NISHAƊANTARWA HARMA DA FAƊAKARWA NAGODE 🙏🙏
TA KU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪.
Chapter 8
بسم الله الرحمن الرحيم
Isarsu asibitin babu ɓata lokaci likitan da ke aiki wanda shi kaɗai ne a asibitin babu kowa sai majinyata ya amshi Mama tare da bata taimakon gaugawa, cikin nasara aka samu ta farfaɗo ta na ta sambatu, allurar barci likitan yai ma ta, ganin ta samu barci ya saka likitan sallamar su, Iya badan ranta ya so ba hakanan tabi bayan sauran suka tafi amma sai faman mita take akan ita dai da ambarta wajen Suwaiba ta rarrasheta idan ta farko, rarrashinta suka yi gami da nuna ma ta idai akaiwa mutum wannan allurar sai ya kwana ya hantse ya na barci bai farka ba.
Maman ne ya fito zai je wajen Me gari, isarshi kusa da fadar ya fara jiwo muryoyinsu na tashi cike da nushaɗi inda Me gari ke faɗin. "Wallahi Allah ni kaina na so yarinyarnan kuma na daɗe ina bibiyarta dan insamu dama irin haka amma ban samu ba, ganin irin wahalar da muka sha saboda ita yasanya na yanke hukuncin ko shi Audul ɗin bazan bari ya aureta ba haka kawai ya kawo ma ni annoba da jaraba cikin gida, shi kuma Mamman sakaran banza da bai da tunani ya na fama da kanshi kamar na kifi daga amfaɗi cewar amfasa auren yarinya shine ya hasala ya zuciya wai ta yi abin kunya ya kori ƴar banza, ni wallahi hakan yayimin daɗi sosai dan wallahi ba ƙaramin tsoro ta bani ba ko sanda aka taru anan ana maganar a ɗofane na zauna gudun ko ta kwana." Dariya fadawan suka sake kwashewa da ita cike da nishaɗi, dan sun daɗe basu yi fira me tsawo irin haka da me garin nasu ba, ko da yaushe fskarshi a ɗaure kuskure kaɗan mutum zai yi a sauke shi daga matsayinshi.
Cikin sauri Mamman ya sha kwana ya na jin zufar tashin hankali na yanko ma shi, tabbas ya yi kuskure ya tafka babban kuskure wan da bai san ta yanda zai fara gyaranshi ba, wani sashen na zuciyarshi kuma na sake tabbatar ma shi da ya yi daidai tunda ba hakanan ya kori Zulai ba sai da ya ɗaura ma ta aure.
BAYAN AWANNI UKU
03:00am
ABUJA NIGERIA
Da tsananin gudu ya isa babban asibitin da ke cikin Estate ɗin MUHAMMAD IMAM, kai tsaye ya danna kan motarshi cikin asibitin me wadatar haske kamar rana, mutane sai kaiwa da komowa suke saboda tsarin da aka bi wajen ginin asibitin ba zaka tantace dare da rana ba.
Kai tsaye norsing suka zo suka tura Fadeel a keken tura marasa lafiya sulai emergency room da shi, taimakon gaugawa aka fara bashi kafin zuwan Doctors waɗanɗa ke bawa wa su mutane da aka kawo sun yi accident taimakon gaugawa.
Babu jimawa su ka shawo kan matsalar sannan suka dawo kan Fadeel wanda numfashin shi ya tsaya cak bai da maraba da matacce, sun daɗe sosai akan shi kafin suka samu nasarar ceto numfashin shi ya dawo daidai sai de bai farfaɗo ba.
Doctor Hafeez ne ya nufo inda waiting chairs suke ya taradda FAHAD zaune ya saka hannayenshi cikin sumar kanshi yana caƙudawa duk ya birkice.
Dafa kafaɗarshi Dr. Hafeez yai wanda hakan ya saka shi ya dago birkitattun idanuwansa da suka rine saboda damuwa ya watsa su akan Dr. Hafeez wanda sai da yaɗan ja baya saboda kwarjinin da idanuwan abokin na shi, murmushi ya sakarwa Fahad tare da kauda kai daga kallonshi sannan ya ce.
"Haba manah Man bai kamata ka dinga shiga damuwa irin haka ba, indai Fadeel ne yanzu haka ya na cikin ƙoshin lafiya."
Haɗa ido suka sake yi da Fahad wanda ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe manyan kaifafan idanuwanshi ya na godiya ga Allah acikin zuvciyarshi.
Kamo hannushi Dr. yai tare da miƙar da shi ya nufi office ɗin shi da shi.
Ruwa ya tsiyaya mai masu sanyi ya bashi ya sha, sai da ya tabbatar da ya ɗan nutsu sannan ya fara bashi bayanai cikin tausasa harshe gami da nasiha da nuna ma shi dukkan abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, sanan babu wanda ya ke gujewa ƙaddararshi, ko wace cuta ta na da magani sai de wa ta cutar takan jima a jikin mutum ba tare da ansamu maganinta ba.
Cike da ƙosawa Fahad ya nemi Dr. da ya faɗa ma shi abin da ke damun Fadeel ɗin, Dr. Hafeez bai ja da nisa ba ya faɗa ma shi abin da ya nemi tsaida numfashinshi na tsawon lokaci, sai da ya ɗau lokaci yana ƙoƙarin buɗe baki yai magana amma abin ya gagara saboda tsananin tashin hankali ganin yanda ya shiga halin ruɗu da ɗimauta ya saka Dr. Hafeen fara kwantar ma shi da hankali ta hanyar yi ma shi alƙawari akan zai tsaya tsayin daka wajen ganin ya bawa Fadeel dukkan kulawar da yake buƙata.
Zafafan hawaye ne suka shiga gangarowa daga idanuwan Fahad wanda hakan ya saka Dr.Hafeez cikin ɗimauta dan tun tasowarsu su na yara bai taɓa ganin abin da ya gigita abokin nashi har ya saka shi hawaye ba sai yau, rungume shi yai suka shiga yin hawayen a tare babu me rarrashin wani dan sosai Dr.Hafeez ke tausayawa halin da Fadeel ke ciki, ko a emergency room sai da yai kuka ganin galin da ƙanin abokin nashi ke ciki.
Sun kai kusan mintuna goma a haka babu me rarrashin ɗan uwanshi kafin daga bisani Fahad yai jarumtar shanye kukanshi ya kuma rarrashi abokin na shi tare da faɗin.
"Tabbas na shiga tashin hankali da tsananin kaɗuwa jin cewa ɗan uwana mafi soyuwa a gare ni na ɗauke da wannan mumunar lalurar amma ban taɓa sa ni ba, ina jin haushin kaina da nakasa tsayawa wajen kulawa da ɗan uwana wanda ke girmama dukkan abin da ya shafi rayuwata, kaico da wannan rayuwar."
Haka yai ta faɗin maganganu kamar zarare yayinda Doctor yai shiru tare da bashi damar amayar da abin da ke damunshi, sai da yaga abin na shi bana ƙare ba ne sannan ya shiga rarsashinshi tare da nusar da shi ƙaddarar Fadeel ce a haka kuma Allah yasan dalilin ɓoye abin ba tare da kowa ya sa ni ba sai yanzu da lalurar tai nisa.
TAUFA WA TA SABUWA KUMA, TO KO MI KE DAMUN FADEEL ƊIN WANDA ANƘI FAƊI😳 NI TSORONA MA KAR ACE A GARINSU ZULAI YA KWASO CUTAR, KOMI KENAN DAI KU KASANCE TARE DA NI DAN JIN YA DA ZATA KAYA, DOMIN KUWA INA ME TABBATAR MUKU DA AKWAI ZAZZAFAR CAKWAKIYA NAN GABA KAƊAN.
TAKU HAR KULLUM
MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪
👰♀️A DAREN AUREN 👰♀️
WRITE BY
MARYAM STAR ⭐⭐⭐
(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)
MARUBUCIYAR
DAFIN MACIJI🐍
AND
RAYUWAR SAMHAD🌹
Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)
💙💙💙💙💙💙💙💙
A DAREN AURENA 👰
PAID BOOK
💙💙💙💙💙💙💙💙
MUN KUSA KAMMALA FREE PAGE INSHA ALLAH, ZAMU TSAYA A PAGE 12
Chapter 9
بسم الله الرحمن الرحيم
Ajiyar zuciya Fahad ya sauke alamun maganganun Dr. sun shige shi, zama sukai anan wajen har akai kiran sallar farko, a tare suka miƙe suka nufi masallacin da ke cikin asibitin bayan sunyi alwala, nafila suka gabatar tare da zaman tazbihi har akai sallar asubahi, bayan an idasa ne suka fito a tare fuskar Fahad ta yi wani irin jah abinka da farin mutum ga kuma rashin barci, ga damuwar halin da ɗan uwanshi ke ciki, sai da suka zo giftawa da wajen da motarshi ta ke a parke ne ya ji gabanshi yai mummunan dokawa, zuciyarshi ta shiga bugu da tsananin ƙarfi, Dr. Hafeez har yayi nisa sai ya lura da Fahad baya tare da har zai tafi ya barshi sai kuma ya juyo ganin ya buɗe mota yai saurin isa kusa da shi dan dakatar da shi.
Turus ya tsaya a bayan Fahad ya na leƙo da kanshi ya na kallon farar yarinyar da ke barci zaune a cikin motar har zai yi magana sai kuma yai shiru ya na kallon yanda Fahad ya juyo a slow ya na kallonshi.
"Please Hafeez ka taimaka ka dubamin yarinyar nan ita ɗin amanace a wajen Fadeel shine ya damƙamin ita jiya, na manta da na kulle ta amota wallahi saboda ni ne nai tuƙin jiya cikin dare, yanzu banda isashen lokaci ina so inje in kwanta dan zuwa anjima zan yi tada jirgi dole ina buƙatar nutsuwa."
"Subahanallahi! kasan kana da aiki a yau shine ka saka kanka a damuwa jiyama fa bana tunanin ko gyangyaɗi ka yi bare barci, gaskiya Captein ka dinga kulawa sosai, yanzu bara inkira a shiga da ita ciki zan duba ta kafin gari ya waye, kai kuma bara in kira driver ya maidaka gida tun da ba'a yarda ku dinga tuƙin mota ba musamman da safe."
Norse guda biyu ya kirawo suka zo da wheel chair suka shiga da Zulai cikin asibitin, sallama sukai da juna Captain Fahad ya shiga mota yana jiran zuwan driver, shi kuma Dr. Hafeez ya shiga ciki don ƙarasa sauran ayyukanshi.
Bayan driver ya zo ne ya tuƙa Captain Fahad ya kaishi har can cikin MUHAMMAD IMAM ESTATE, estate ɗin babbane sosai dan daga asibitin zuwa ainahin cikin gidajen estate ɗin dole sai a mota, a bakin wani tangamemen gida me ɗaukar hankali wanda a saman makeken get ɗin gidan aka rubuta da manyan rubutu SHURAIM MUHAMMAD IMAM da yanayin ɗaukar ido saboda yanda aka tsara rubutun, manya garadan ƙarfafa jaruman sodoji ne a tsaye suke ƙyam babu alamun wargi a tare da su, driver da ke tuƙa Captain Fahad ne ya zuge glashin motar tare da nuna wani id card sannan aka buɗe ma shi tangamemen get ɗin ya harba kan lafiyayyar motar.
Ƙaton gida ne sosai wanda aka ƙawata shi da flawres haɗi da glasis ma su ɗaukar ido, ta ko ina a cikin gidan ma'aikata ne ke shawagi cikin mabanbantan uniforms, a tangamemen parking lot driver yai parking motar tare da futowa ya buɗewa Captain ƙofar motar cike da girmamawa.
Cikin yanayinshi na izza da jinkai ya sauko daga motar hannayenshi zube a aljihun wandon suit ɗin da ke jikinshi, cike da jarumta da sadaukantaka ya fara tako har ya isa jikin wa ta kyakkyawar kofa ta glashi fari da ruwan gorld, wasu madannai ya daddana nan cikin ƙanƙanin lokaci ƙofar ta shiga buɗe kanta, danna kanshi yai cikin ƙawataccen makeken main Parlour, babu kowa sai ma'aikatan da ke ta faman kaiwa da komowa kowa na aikinshi cike da taka