A DAREN AURENA

Author :  MARYAM STAR Category :  Horror

Chapter   2 / 5

3K to 6K   out of 13.8K words

ya ishi uwata Salame, wato dama labarin da ya karaɗe gari cewa kina can yawon iskanci A DAREN AURANKI, to wallahi uban kuturuma yai kaɗan yau sai munga ubanda ya tsaya maki a ƙauyen nan ƴar iskar yarinya mai halin ban...."

Bai idasa faɗin abin da zai faɗa ba Zulai ta taso da dukkan ƙarfinta tare da yin girgiza ta wancakalar da ɗan kwalin kanta ta barbaza gashinta ya zubo gaba da baya sannan ta fasa gigitacciyar ƙara tai kan Audu gwangwan da yai suman tsaye lokacin da yai tozali da juyayun idanuwanta, ɗaram Zulai ta maƙale akan Audu gwangwan da ya ke yana da jiki ma sha Allah, siraran hannuwanta ta ɗaga ta dinga tallare sontaleliyar ƙeyar Audu gwangwan wacce ta sha askin kwal da kobo sai sheƙi ta ke gami da walwali, cike da tsananin tashin hankali Audu gwangwan ya shiga kiciniyar yanda zai sauke Zulai daga jikinshi ya kasa, kyarma su mai gari da sauran mutanen wajen suka shiga yi jin yanda Zulai ke wani irin gurnani mai ban tsoro, sai da ta rantali kan Audu gwangwan san ranta sannan ta ƙyale shi ganin har ya fara kukan azaba, direwa tai daga kanshi ta nufi inda me gari ya ke tsaye ya na sallati gami da addu'o'in neman tsari daga sharrin shidanun aljannu, bai yi aune ba ya ji hannun Zulai akan gemunshi ta janyo da iya ƙarfimta, wani irin gigitaccen ihu mai gari ya saki jin yanda aka wani fizgi dogon gashin gemunshi, cike da azaba ya ke neman agajin mutanen da ke wajen amma babu wanda yai koda motsi bare akawo mai ɗauki, kuka mai gari ya saka kashirɓan tare da bawa Zulai haƙuri tare da yi ma ta alƙawurrra da yawa.

Ita ko Zulai yi tai kamar bata san abin da ke faruwa ba dan kuwa dama can ta na jin haushin mai gari da tawagarshi saboda yanda suka saka ma ta

TAKU HAR KULLUM

MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪

👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️

WRITE BY

MARYAM STAR ⭐⭐⭐

(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)

MARUBUCIYAR

DAFIN MACIJI🐍

AND

RAYUWAR SAMHAD🌹

Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

💙💙💙💙💙💙💙💙

A DAREN AURENA

PAID BOOK

💙💙💙💙💙💙💙💙

Chapter 4

بسم الله الرحمن الرحيم

Idanu suka hana ta rawar gaban hantsi ga wani bin diddiƙinta da suke saboda kawai wanda za ta aura ƴa na ɗan mai gari, sai da Zulai ta tabbatar da ta wajiga mai gari sosai dan shima sai da ya yi kuka sannan ta kyale shi, haka ta bi mutanen mai gari da su kaɗai suka rage a wajen dan kowa ya watse dan tsira da lafiyarshi, su ma fadawan duk sun tsure ganin yanda ake azabtar da mai gari, babu halin tserewa ne saboda muddin mutum ya gudu idan wani abu ya faru to fa ancire shi daga matsayinshi.

Zulai na sakin gemun mai gari tai baya-baya ta faɗa luuuuu a jikin wannan matashin tai ɗaiɗai abinta, a zuciya ta ke faɗin 'Wai dama wannan baturen haka jikinshi ke da laushin tsiya wallahi sai na mori wahala ta akan shi, sabo da shi ceto ranshi yau nai gwagwarmaya harda sadaukarwa sai da nai walahi, ina dalili gwara in ɓararraje in mure laushin wannan fatar.'

Yayinda a fili kuwa ta shiga yin murƙushe-murƙushe tare da sakin numfashi ta koma tai lakwas alamar ta dawo hayyacinta, mai gari tun da ta saki gemunshi ya tattare babbar rigarshi tare cire takalmanshi ya saita hanya ya kwasa a mugun guje, fadawanshi ma ganin oga ya tsere su ma suka rufa ma shi baya kamar ma su gudun tsere dan kuwa kowa fata ya ke ace ya wuce ɗan uwanshi, gudu suke bakin rai bakin fama ga rigunansu sai cika suke sa iska, babu inda suka ci birki sai a fadar mai gari, nan kowa ya zube ya na maida lumfashi, ko gama sauke numfashi basui ba suka hango zugar mutane da wa ta irin ƙura na tashi, da mugun gudu mutanen ke tafe wani azakwakwuri ya dage sai ɗaga murya ya ke yana faɗin.

"Jama'a kowa yai ta kanshi yau gari ba lafiya, mata ko wace ta shige gida ta kulle yau garin nan babu lafiya."

Aifa su me gari jin haka ya saka su saurin tashi tare da bin ayarin wannan tawagar aka shiga tiƙar gudu da su, kafin kace mi kowane gida an garƴame shi babu wanda ke buɗe hatta masallatai duk an kulle su, haka wannan tawagar ta mutanen suka shiga tiƙar gudunsu babu gajiyawa, abin ka da mutan ƙauye dama ansaba aikin ƙarfi hakan ya saka basu gaji ba sai da suka tabbatar da sun fice daga ƙauye sun nausa cikin jeji sannan suka ankara suka zauna maida lumfashi.

A bangaren Zulai kuwa sai da tai kusan minti goma ta na morar daɗin jikin baturen matashinan sannan ta buɗe idanuwanta da suka canza launi, karaf idanunta suka karƙe dana wannan baturen dan kuwa ya ƙure ta ne da kaifafan fararen udanuwansa ya na kallonta, cike da basarwa kamar ba shine ke kallonta ba ya ce, "saukarmin a jiki".

Saurin direwa Zulai tai daga jikinshi zuciyarta na tsalle kamar me shirin buɗe ƙirjinta ta fito, idanuwanta ƙememe babu wa ta damuwa ta fara rantaɓo jawabi

TA KU HAR KULLUM

MARYAM STAR ⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪

👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️

WRITE BY

MARYAM STAR ⭐⭐⭐

(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)

MARUBUCIYAR

DAFIN MACIJI🐍

AND

RAYUWAR SAMHAD🌹

Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

💙💙💙💙💙💙💙💙

A DAREN AURENA

PAID BOOK

💙💙💙💙💙💙💙💙

FREE PAGE

Chapter 4

"Malam ya da haka, kasan irin kasadar da na ɗauka kuwa wajen ganin na taimaka ma ka, shine dan na ɗan hau jikinka shine zaka wani buɗe tsatstsaman bakinka ka...."

Ɗif ta yi jin yanda ya fizgota da ƙarfi ta faɗo jikinsa, cikin ƙaramin sauti mai cike da amo ya ce "Indai jikina ne zo ki kwanta ki yi birgima akai yanda ranki ke so babu mai hana ki, ni ɗan halak ne bazan mance alkairinki a gareni ba, ba dan kin taimakeni ba da yanzu bana cikin wannan duniyar ke ɗin ta musamman ce a wajena dole ne in baki dukkan abin da kike so damma dai ni ina tsoron mace mi aljannu musamman irinki mai rantalar ƙeyar maza."

"Wa ya ce maka ina da aljannu, Malam bari janyo min bala'i ni lafiyata ƙalau wallahi na yi abin da nai ne dan inyi maganin waɗanan shaiɗanun mutanen baka san halinsu ba ne tsaf zasu ƙullamin shari a garin nan fita ma ta gagari iyayena da ƴan uwana, kuma dama na daɗe ina jin haushi me gari da Audu gwangwan shi yasa nai masu laga-laga ƴan kwal uban." Zulai ta katse wannan matashin daga magnar da ya ke.

Wani tunani ne ya bijiro ma matashin, jinjina kai yai alamar na'am da zance zucin da ya ke hakan ya saka ya nutsu sosai sannan ya fuskanci Zulai ya fara magana a bisa umurnin zuciyarshi.

"Na ji maganganinki kuma na fahimce ki sosai, sannan kin burge ni da kika tsaya kika ɗaukarwa kanki mataki har hakan ya saka na ji ina sha'awar saka ki cikin rayuwar ɗan uwanah wanda ya ke fuskantar matsaloli masu sarƙaƙiya, idan za ki amince da ni zan saka ki aiki a kanshi sannan zan biya ki miliyoyin kuɗaɗe, na yi maki alƙawarin cika ma ki dukkanin burukan rayuwarki muddin za ki amince da buƙata ta ni sunana Fadeel ina zaune ne a garin ABUJA ɗan uwana na sunanshi FAHAD...."

Nan ya shiga zayyano zance tare da fatan samun amincewar Zulai dan ya hango maganin matsalolinsu a tare da ita.

Yayin da ya ke magana fuskarshi caɓa-caɓa da hawaye, haka Zulai ke zabura tare da nuna tashin hankali, wa ta maganar kuma idan yai sai kaga ta tashi ta na ɓurme-ɓurmen zaki, wa ta maganar kuma sai ta ciji yatsa ta jinjina kai, bai gama kai ƙarshen maganar ba Zulai ta tseshi da faɗin.

"Ya isa haka Fadil barni hakanan kar zuciyata ta buga inmutu a banza saboda baƙin cikin wannan labari na ka, ai tsaya ka ji zuwana birnin tarayya dole ne, dole inshiga cikin ahalinku dan inhidda maragurbi sannan inci uban munahwukai da ƴan iskan masheranta, amma wani hanzari ba gudu ba, yauɗin shine daren aurena bazan iya tsallake wannan ranar me daraja ba, kuma bazan iya barinka ka tafi kabarni anan ba yanzu minene abinyi?."

A ɓangaren su me gari kuwa, su na can cikin daji a zazzaune kowa da abin da ya dame shi, ga ƙishirwa ta addabesu ga shi sun kasa gane hanyar gida bare su dawo, wasu daga ciki har sumfara kuka saboda gabatowar kiran magrib, ya yinda me gari yai tsuru-tsuru kamar tarko ya kama kura a tarko, zuwa can Audu gwangwan ya buɗe baki yai tambayar da ta saka kowa kallon ɗan uwanshi dan jin mi zai ce.

"Wai dan Allah jama'a minene ya yo bi ake kwasar wannan gudun haka?."

Babu wanda bai faɗa tunanin akan abin da ya faru ba, zuwa can wannan jibgegen matashin da ya kware baki ya dinga shela akan kowa yai takanshi ya zabura ya ce.

"Wallahi Allah me gari za ku tambaya dan shi da fadawanshi muka gani sun zage sai tiƙa gudu su ke shine muma muka buyo sahu dan tsira da rayuwarmu."

Kasaƙe me gari yai zufar wahala na yanko ma shi, idan tunaninshi ya bashi daidai lokacin da Aljannun Zulai suka tashi ne aka gansu su na gudun ceton rai, kafin ya ce wani abu ya jiyo muryar Sarkin aska na faɗin.

"Wallahi Zulai ce ƴar gidan Mamman Aljanunta suka tashi shine ta...."

Saurin daɗe bakinshi Audu gwangwan yai tare da girgiza mai kai alamar kar ya faɗi, ajiyar zuciya me gari ya

TAKU HAR KULLUM

MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU💪

👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️

WRITE BY

MARYAM STAR ⭐⭐⭐

(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)

MARUBUCIYAR

DAFIN MACIJI🐍

AND

RAYUWAR SAMHAD🌹

Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

بسم الله الرحمن الرحيم

Chapter 5

Sauke jin Sarkin aska bai idasa faɗin abin da zai faɗa ba, ƙiri kowa yaiwa Me gari su na son jin ƙarshen jawabin sai de shi da Audu gwangwan sun hana hakan faruwa.

Sai da duhuwar magrib ta fara sannan Bala mafarauci ya ce ya gane hanyar komawa gida, cike da murna suke bin bayanshi har suka fito saga dajin suka kamo hanyar cikin ƙauyensu, a gajiye tuɓus suka iso kowa ka gani a harmutse saboda azabar wahalar tafiyar ƙasa da kuma uban gudun da suka tiƙa.

Bayan kowa ya je gida yai wanka tare da cin abinci da sallah Ma gari ya aika aime shela akan ya na son kowa ya zo fada akwai muhimmiyar magana, da ya ke kowa a ƙage ya ke akan san jin abin da ya faru hakan ya saka kafin Me gari ya fito fada ta cika taf da mutane, ba mazanba ba matan ba har da yara matasa kowa ya zo, a gefe guda kuwa waɗannan matan da sukai faɗa ne tare da folisawa har da Auwalu da yai jage-jage da zawo, duk sun jeme sun fita a hayyacinsu kamar wasu korarri, mutane sai kallonsu ake ana mamakin abin da ya same su musamman da aka san sune sukazo tafiya da Zulai, babu jimawa sosai Mai gari ya fito tsaf da shi sai de idanuwanshi sun zurma ciki sunyi zuru-zuru, bayan ya zauna aka gaggaisa ya fara rantaɓo jawabi.

"Wato dalilinda ya sa na tara ku anan shine, ina son kawo sauye-sauye da dama yayinda nike so in karrama wasu daga cikin fadawana saboda sadaukarwar da sukaimin a yau da wani iftila'i ya aukomin, sun tsaya tsayin daka wajen ceto rayiwata shi ya saka nima zan saka ma su da alkairi in nuna farin ciki da jin daɗin abin da sukai man, da farko dai ina so kowa ya maido hankalinshi akan waɗannan jami'an tsaron da kuma Auwalu ƙeya, idan kunyi duba da idon basira zaku ga sam basa cikin hayyacinsu, Auduwa ne ya tsintosu a hanyar barin gari sun zage sai ɓarza uban kuka suke su na share ciyayi da yatsun hannuwansu, shine yai da su akan su hwaɗi ma shi abin ke hwaruwa amma ƙememe sukai banza da shi sai kuka suke su na shara, da Auduwa yaga abin ya isheshi shi ne yayo waya ya sanar da sauran fadawan da suke zaune anan fada suka je suka ɗauko su kungansu sannan zube kamar ƴan banza kowa a cikinsu sai nishi ya ke."

Nanfa wajen ya kaure da salati da sallallamin jama'a gami da jajanta abin da ya faru kunsan mutanen ƙauye da kara da karamci.

Mai gari ne ya sake katse surutun mutanen wajen da faɗin.

👰‍♀️A DAREN AUREN 👰‍♀️

WRITE BY

MARYAM STAR ⭐⭐⭐

(ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU WRITERS 💪)

MARUBUCIYAR

DAFIN MACIJI🐍

AND

RAYUWAR SAMHAD🌹

Follow the MARYAM STAR⭐⭐⭐ ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU HAUSA NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

*(J.W.A)*

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️

"Jajirtattu mu ne ƙarfi a zuciya, hikima a magana, jajircewa a aiki. Ba mu ja da baya, ba mu faɗuwa. Mu ne tarihi da ake ginawa!" 💪🔥✨

🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚

















(🦚✊DEDICATION IS OUR STRONG✊🦚)

💙💙💙💙💙💙💙💙💙

A DAREN AURENA

PAID BOOK

💙💙💙💙💙💙💙💙💙

Chapter 6

بسم الله الرحمن الرحيم

Babban lamarinda ya faru ɗazu a garinnan shine ita dai wannan yarinya wadda za'a ɗora ma ta arme da yaron wajena gobe idan Allah ya kaimu ita ce ke ɗauke da lalurar iskokai wanda basu bayyana ba sai yau da yake daren armenta, babban abin tashin hankalin bai wuce yanda iskokan suka maida kan yarinyar madaddalarsu ba, kanta cike ya ke taf da iskokai dan ko wajen aje tunani basu bar ma ta ba, zancen da nike muku ɗazu a asibiti ba ƙaramin ɗauki ba daɗi mukai ni da Audu gwangwan ba da kyar muka shawo kanta ta hanyar tuhe ta da addu'o'i, bayan sun bar jikinta shine suka fito fili da makaman yaƙinsu wai zasu gwabza da mu, da yake kunsan na yi gaɗon yaƙi a wajen kakan kakan kakana Zubairu sadauki shine na tsaya cike da jarumta muka fara fafatawa, abinka da sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi nan da nan suka cimu da yaƙi shi yasa mukai ta kanmu muka tsere."

Wa ta irin kabbara gami da hayaniya ce ta kaure a wajen, yayinda kowa ke yabawa da jarumtar me gari da kuma gasgata labarinshi, su kansu fadawan ƙaryar da Me gari ya karkace ya shafto ta yi masu daɗi dan kuwa babban abin kunya ne ace sun kasa ceton Me garinsu a hannun Zulai.

Yayinda aka shiga tattaunawa akan hukuncin da za'a yankewa Zulai a fadar Me gari ita ta na can a asibiti su na tattaunawa akan yanda za'a tabar garin ba tare da anzargi wani abu ba, dan jin labarin da Fadeel ya bata ya harzuƙa zuciyarta matuƙa inda fushinta ya bayyana muraratan sanan tai alwashin ɗaukar fansa akan yanda ake cutar da rayuwarsu shi da ɗan uwanshi.

Zulai ba ta ankare da dare yayi ba sai bayan da suka cimma matsaya sannan ta tashi da niyyar tafiya gida nan ne ta ga duhu ya mamaye wajen asibitin sannan babu kowa a ciki sai majinyata waɗanda suka jiggata basu iya ko tashi bare su gudu, Fadeel da sam ba wani ƙarfin kirki a jikinshi ne ya taso suka fice a tare.

BAYAN AWANNI UKU

Zulaice tafe a gaba hannuwanta riƙe da fitila mai tsananin haske, fuskarta a cunkushe babu walwala ko kaɗan yayin da Fadeel ke biye da ita a baya jikinshi a kasalacen ga alamun gajiya sun tabbata ɓaro-ɓaro a fuskarshi, tafiya suke ba ummm babu umumm kowa da tunanin da ya addabi zuciyarshi.

Sai da sukai tafiyar awanni biyu cir sannan suka fita daga ƙauyen YAGAWA suka isa babban titi wanda ya ke tsit babu kowa, haka suka yanki wannan titi su na bawa ƙafafuwansu hawala ta hanyar tafiya babu tsayawa hutawa, yayin da suke tafiya a ƙafa Zulai sam tunaninta baya tare da ita abin da ya faru ne tsaye cak a ranta musamman kaifafan maganganun da Maman ya faɗa ma ta, shuuuuuu maganarshi ta gifta

2 / 5