ta qara tambayar ta knn,.
dafa ta momy umaima tayi tace
"nuree ne yayi mamakin miya kawo kunu ne a wajen....... nan ta fad'a mata tundaga sanda hannat ta fad'a kunu ne a qasa a wajen adan taqaice sannan ta dan yi shiru na yan mintina sannan tace"amman dai kada ki damu indai mahabeer nd bazai ce komi ba yasan tsautsayi kinji ko Ummu na???
cikin son 6oye halin da zuciyar ta take ciki ta kama gyada kai alamun amsawa,
dai dai nan dady mua'zzam yasake fitowa dan sauraran labaran sa na NTA. kamar yanda ya saba,, gaishesa ummu tayi ya amsa cikin kulawa ahankali ta zame zuwa kichen.
har ta gama wanke kayan hankalin ta bai gareta sam zullumin mizai biyo baya daga mugun mutumin nan kawai takeyi.
koda ta gama dakin annah ta shiga da sallama dan tayi raayin shiga wajen tsohuwar ne kobs komi tasamu sauqin abinda ke muntsininta a lokacin.
iskewa tayi annah har ma ta kwanta abinta hannun ta riqeda cazbi tana lazuminta.
Jin sallamar ne yasa annah tashi zaune bayan ta amsa cikeda faraa take cewa"ummu ce ashe zoki zauna to, kinkuwa kyauta kinzo taya tsohuwa fira,, cikin Murmushi ummu ta zauna qasan carpet din ta gaisheda annah ta amsa cikin kulawa.
"kinganni nan yau banjin 'yan fita falon shiyasa ban fita ba,,
Ansha ruwa lpia ko ummu?
"lpia lau annah"
tayi maganar tana mammatsa yatsun hannun ta cikeda d'ari d'ari.
haka annah taita janta da fira tun tana matsewa harta kai ga tasaki jikinta tana taya annah firar itama.
dady mua'zzam ne ya shigo shida momy umaimah nn dady mua'zzam yace "annah kuzo muje gidan Alhj Muhammad domin muyi musu barka da zuwa a maqotanmu kuma babban aboki a gareni.
Anna tace "hakanma yayi to bari na dauko mayafina sai muje ko,, har cikin ran ummu hani taji dadin tasu dan dama har yanzu ranta naga son ganin iyayen nata.
Kamo hannunta momy umaimah tayi tace "muje ummu ko?
dukkansu suka d'unguma sukayi suka fita maigadi na musu adawo lpia a haka har suka isa gidan dayake baffa ya fito waje lokacin mafarin knn suka samu qofar get din a bud'e.
Ya fito ne siyo ma maman ummu din kifi anan wajen titin dawowarsa knn suka hadu. baffa ya gaisheda su annah suka amsa dukkansu cikin faraa sannan suka wuce ciki shima ya shigo tareda rufe qofan ummu data tsaya har ya gama rufe qofan yayinda su momy umaimah suka wuce ciki ganin ta tsaya wajen baffan nata. ta gaishesa baffa ya amsa cikin jin dad'i har cikin dakin da bintey take suka shiga da gudu ummu ta qarasa wajen maman nata ta rungume ta tana Murmushi. nan sikai ta fira ummu tanata fad'a wa iyayen nata kirkin iyayen gidan nata su kuma suna qara qarfafa mata gwiwa akan taci gaba da musu biyayya kamar iyayenya sannan ya qare da cewa "banda sa ido ga abun wani ummu kinjini ko? , cewar baffan.
"insha Allah baffa"
Yawwa ummu na nasan daman baki hakan tunatarwa ce dai Allah dai shi yi miki albarka, musamu mi samu kudin aikin nan da zaiwa mamanki komayi mu koma gida cikin yardar AllAh "
"amin baffa."
Bintey tace "to kije kada kuma su nemiko,,baffa dake warware qumshim ledar kifin yace
"zokici kifin nan ummu dudda babu yawa kan ki tafi,, yasanta dasan kifi shiyasa.
tsoka day'a ta dauka sannan ta yi musu saida safe ta shiga can cikin gidan a falo ta samesu nan ta gaisheda alhj Muhammad da momy ni'ima sannan ta koma can gefen momy ni'ima ta zauna.
sun dan jima suna fira a tsakanin abokan sannan da suka tashi tafowa sukayo musu rakiya suma har bakin gate momy ni'ima tace
"hjia umaima imsha Allah gobe zan shigo ganin dan nawa,, to shiknn hajia ni'ima Allah shi kaimu lpia.
a haka suka bar gidan suka koma nasu.
Annah da dady mua'zzam suka wuce room dinsu yayinda momy umaima tace "ummu wannan dakin da kike shine naki kinji ko?
gyada kai ummu tayi tace "to mah"
Yawwa ummu na to kije ki kwanciyar ki sai da safe ko?
"to momy Allah tashemu lpia"
"Ameen ummu.
a dakin kuwa ummu ta jima tana sake kallon tsaruwar sa da kyansa, ba wani abu bane mai tarkace a cikinsa ba iyaka gado ne mai lulube da tattausan beedshet akai, sai durowas da mirow harda dan qaramin deep freezar sai kuma can 6angaren toilet dake gefe.
kwanciyar ta tayi tareda lumshe idanun ta ciwon mahabeer ne kawai ke ranta a lokacin tasan sam baida kirki mutumin nan tarasa ya zata kaya tsakanin su inya warke, anya kuwa zai barta kamar yanda mah din tace kuwa???
qara gyara kwanciyar ta tayi tareda sake lumshe idanun ta tanata irin tunanin nata a haka barci yayi gaba da ita cikeda mafarkai ciki kuwa harda na mutimin nata.
tsawon sati 2 mahabeer yana Yana gida baije ko ina ba yana jinyar qafarsa yayinda ummu keyin kaffa kaffa dadud wata hanya da tasan zata hadasu,,yayinda kullum hannat tana manne da gidan,,
Kullum Ummu saita je ganin mamanta da baffanta in ta gama ayyukan ta,,,
yau ta kama juma'a ne ummu ta gama girkinta da momy umaima tace tayi mata jefin dan wake dan Yau jikin nata ya motsa batajin dadinsa sosai gashi dady mua'zzam bainan yaje dubai annah kuma tana dakin ta tana hutawa.
lokacin ta koma dakinta tayo wanka ta shirya cikin kayan da momy umaima ta bata jia wato wannan riga da wandon fakistan din sai rawa sukeyi kuwa a jikinta.
babu wani make up a fuskarta shiyasa fuskar tayi fiyau abinta gwanin sha'awa.
parking gashin ta tayi gefen kanta sannan ta dauki mayafin kayan ta nada sa akanta nan da nan ummu tasake fitowa da usulin kyanta babu wanda zaiga ummu bai ji buqatuwar cewa ta zama mallakin sa ba.
fitowa tayi tashiga kichen ta dauko abincin momy umaima ta nufi dakinta tayi sallama ta shiga ganin bata nan ne yasata tunanin kotana wajen annah mafarin knn ta juya ta koma dakin annah dun, anan tasamesu zaune suna fira, har cikin ran ummu taji dadin ganin yanda mah din tasamu lpia ba kamar d'azun ba.
zama tayi tana 'yar dariya dariya ta murna bayan ta gaida annah tace "mah gashi na gama danwaken da kikace"
"kai ummu nagode fa sosai naji dadin ganin dan waken nan yanzu yanda niketa jin kwadayin nan dan na zata ma sai dare zaki yi mana"
Murmushi ummu tayi tace "annah kin iya cin dan wake ma kuwa?
tayi maganar a tsokane dan itama yanzu ta saki jikinta ta mayar da annah kakarta,,,
"lalala ummu karkice zaki biyewa mahabeer na fa kuna tsokanar mun uwa"
cewar momy umaima tana dariya itama,, annah cikin raha tace "rabu dasu umaimatu,,zanyi maganin sune a gidan nan ay, hijira zanyi gobe in koma katsina sainaga wanda zasu tsokana,,fiddo fararen idanunta ummu tayi tareda ruqo hannayen annah cikin kalar murmushin ta tace
"wasa nike anna zanje na kawo miki kema naki yanzu ay, dariya momy umaima tayi ita da annah kawai har ransu qaunar yarinyar kullum take qara shigarsu,,
anna tace "aa ni bnjin yunwa ynzu nagama cin abinci"
Marairaicewa ummu tayi tace
"to amman in ajiye miki ko annah zakici anjima?
cikin Murmushi annah ta shafa kan ummu tace zanci ummu allah dai shi miki albarka yanda kike dad'ad'a mana kina samu farin ciki a kullum,,ameen cewar momy umaima dataketa saka danwakenta a baki tana ci harda lumshe idanun ta tosshin yasha yajin daddawa da magi d.s sai qamshi yake.
"Annah mah zanje wajen su baffa in gaishesu,, cewar ummu hani tana mai miqewa tsaye,,
Momy umaima tace "to shiknn sai kin dawo annah ta qara da cewa "ki kuma gaishesu qwarai2"
tana fita ta koma dakinta ta zura plate shoes dinta ta tsaya gaban mirow tana kallon kanta Murmushi tayi tasan in su baffa suka ganta haka tasan zasuji dad'i sunsan cewa hankalin ta na kwance ba kamar sanda suka shiga damuwar nan ba lokacin da suke nemn mafaka.
dan siririn Murmushi tayi jin gyalenta ya dan zame daga baya sabida santsin gashin kan nata yasa tasa dogayen fararen yatsunta ta fiddo jelinayen gashin kanta guda 2 dogayen gaske baqi qirin dashi gashin sai shining yake.
ta gaban goshinta ta sakosu har saman q'irjinta suka hau suna yawo,,
maido da gyalen tayi ta yafa sa bisa kan nata sannan ta koma kichen ta d'auki kular abincin su baffa din tanufi waje.
dayake momy umaima tace in zatayi musu girki ta dinga girkawa dasu baffan nata dudda acan suma ana kai musun nasu in momy ni'ima tayi, hakan da momy umaima tace ba qaramin dad'i ummu taji ba, a rayuwa burinta shine taga komi ta samu ko taci to suma iyayen ta susamu hakan shine cikar farin cikinta.
daga nesa ta hangosa ta wajen swimming pool din wajen inda yar bukkar nan take yana zaune bisa kujera ya dora qafan sa guda biyun a bisa tebir din tsakiyan wajen,, hannunsa riqeda viju milk yana tsotsa ,,
batasan dai su waye kusa dashi zaune ba, ga alama dai abokansa ne mazan,,
rasa yanda zatayi ta wuce ta wajen tayi dan dole saita hanyar da suken ne zata fita.
ta jima tsaye a wajen datai taga lokaci na neman qure mata yasa kawai ta yanko tikitin shahada tayo hanyar wajen nasu,,tun daga nesa ya zuba mata idanunsa yau tsawon sati 2 knn rabon daya yarinyar dudda burin da yaci nason ganin nata akan qudurin nasa,,
tunani yake sonyi akan wane irin kalar hukunci ne waima ya kamata yayi mata danya huce haushin sa akanta amman kuma zuciyar sa taqi basa daman yin hakan ta hanyar shagaltuwa da yayi da bin yarinyar da kallo batareda ya ankara ba,,, ganin ta kusa isowane kusa dasu itama akayi sa'a ta dago idanunta nan da nan suka had'a idanu cikin sauri ya fara maido nutsuwarsa cikin jikinsa ya yamutsa fuskarsa cikin daure fuskarsa tamm tam saida ya danqaro mata wani zafaffen kallo wanda ya haddasa wa ummu wani iriyar faduwan gaba ba shiri shikuma yasake binta dawani banzan kallo na raini yana binta da wata hararar sannan ya janye idanunsa daga cikin nata yana sakin tsoki ya maida viju milk dinsa cikin saman lips dinsa yaci gaba da tsotsar abinsa.
mukhatar cikin rawar jiki da da kyarmar baki ya tabo bash da Masud da imran yace
"kai kutttttt,,, wowww gayu kun kalli kyakkyawar halittar dake tunkaromu kuwa a halin yanzu?,
anya ba aljana bace takeson budemin ido inyi *gamdakatar* da ita kuwa ba a yammacin nan?, dubn inda mukhtar din yake nuna musu ne sukayi suna bin wajen da idanuwa suma,,,,
babu wanda zuciyar sa bata girgiza ba da ganin yarinyar ba a cikinsu suma, nan da nan suka hau murtsuka idanusu suna tunanin anya kuwa ba Ubangiji Allah ne yasa yaci dasu da rabon yin mafarki daga day'a daga cikin matan hurul ayni ba kuwa?
ji sukayi gaba day'a jikinsu yai musu sanyi a lokacin musamman mukhatar uban zalama lokacin daya tabbatar da cewa Lallaikm wannan mutum ce bil'adama abin hakitta.
cikin qunar rai mahabeer yasa hannu ya daki table din gabansu hatta sauran milk din da cups dake akai saida suka rigizazo qasa suka watse,,
da sauri suka maido hankalin su jikinsu shikuwa sai masifa yake tsattsaga musu da cewa "haba miye haka kukeyi dan Allah kuma mukhtar?? Kun wani kun sanyawa yarinyar mutane idanu dud salon dai kujanyo mana raini kuma? Yayi maganar ransa a matuqar 6ace wanda shi kansa baisan yaya hakan ta kasance ba,,
dai dai lokacin ta ida giftawa ta wuce ta gefensu cikin d'ari d'arin da takeyi gameda mahabeer din,,
saida ta wuce ne harta qulewa sannan suka maido hankalin su jikinsu lokaci day'a.
sauke ajiyar zuciya mukhtar yayi yace
"kamm bala'encan.. waiii zillaziya... duban mahabeer yayi yace
"gifted daga wane duniya gidan nan naku ya samo mun mata ya kawomun har gida dan Allah fada mun gifted??
bash yace "kaji dan iska namamajo kakai maryam din ina?? saura kwana 3 fa a daura muku aure,,?
"to dan yana saura kwana 3 in aureta ban iya fasawa ne kukega akan wannan zazzafar? kai kokuma in auresu duka ai addini ya yardar mun🤷🏽♂ ko? "
Wlh kunji ma na rantse zan iya barin auren maryam Dan wannan zata ishi mutum komi basai ya qara wata ba, yayi maganar yana sake zuqo hayaqin tabarsa.
Bash yace ''kaji dan iska kanata surutai ma kasani ko matar aure ce,,??
Mukhatar yace "ohhhshet..!!! daina mun fatar hakan dakuwa ba cutu wlh kajini da dan iska mugun bakinka ya koma maka to"
dammm!!!!!,,,,,, mahabeer yaji gaban sa ya amsa da maganar da yaji bash yace wai may be itan matar aure ce.
girgiza kai yakeyi samun kansa yayi a fili yana furta kalmar "noooooo mukhtar noo mukhtar,,, dukansu da kallo suka bisa shikuwa hannunsa yake kallo ganin yanda jini ke dan diga sakamakon cups din daya doka d'azun da hannun nasa harta kaiga ya yanke dan shi saima lokacin ya ankara da yankewar tasa. runtse idanuwan sa yayi gaam yayinda ya ciro farin hankicerf dinsa daga aljihun sa yafara qoqarin daure wajen dan jinin ya tsaya.....
*Xexen Fasaha*
[10/11, 2:47 PM] Xainab Documen: 🌊🌊🌊
*MAHABEER*!!!
🌊🌊🌊
Story and writing
by
Xayyneb 💤💤
🌊🌊🌊🌊🌊
Fasaha online writers f. o. w.
🌊🌊🌊🌊🌊
🅿2⃣9⃣
🌊🌊🌊
*A* hankali jinin ya fara tsayawa cak daga zubowar da yakeyi daga tafin hannun nasa.
Bash ne ya ida daure masa hannun da hankicerf din sannan yace
"garin yaya haka kuma gifted daga magana kuma?
idanunsa mahabeer ya dago ya duresa bisa na mukhtar ya banka masa wata harara,,, dariya mukhtar ya kwashe da ita sannan yace"gifted kaifa kana mana yabin wlh,, ya bani na tambayeka ba amman kanamun hararar haka? Ka harari bash d'in mana nikega ai zaifi ko? ,,,
Masu'd yace "plzzz mu dawo kan batun waccen fine babyn din guys koko ba haka ba,,, imran yace "Wlh kuwa friends kamar kasan abinda nike shirin fad'a knn ka rigani furtawa"
Mukhtar cikin zuqar tabarsa da yake sakeyi daga kishin giden da yake kan kujerar yace
"miye had'inku da da ita da kuka nacewa vatunta haka? Bakuka nayi shiru ba ne ni? Ina jiran gifted ya dawo dai dai ne daga yankan da yasha na dora masa tambayar ta daga inda na dora,,, bash yace "dalla mutane kuyi mana a hankali mana bakuganin irin jinin da ya gama zubarwa ne eye?
Mukhtar yace "hannu ke bada amsa koko bare kace hannun nasa da ya gama zubar jinin zai fama sa eye?
mahabeer gaba day'a ji yake surutun nasu na hawan masa kai dan haka cikin zafin zuciya yace "dan Allah ya isa haka,, dubiyana dai kukazo yi ko?
ya dubi su mukhtar din inka dauke bash dake gefensa wnda dama shi yasan baya cikin wnda mahabeer din kewa wannan tambayar,, dan da mukhtar din da Masud da imran dud halin su day'a na mugun son matan tsiya jarababbune na gasken gaske indai akan fannin mata ne ecpecially kyawawa ma.
masud yace "korar mu xakayi ne?
Imran yace ''ga alama dai kam hakan yake nufi,,,.
Mukatar yace "bari kaji gifted billahil axeem bazan bar wajen nan ba saika Fadamun wacece wannan yarinyar wacce ta gittamu ynxu ta wuce,,ya qara da cewa club zanje hakan na tsara amman zuwa na nan wajen ka da kuma arba da wannan lafiyayyar babyn da nayi ya rusa mun dud wani budget nawa Wlh, dan haka rufin asirinka indai kanason mu barka ka sarara shine kawai kai mana bayanin ta mlm"
Bash yace
''tirrr da kai mukhtar,, wlh kai dai mugun mayen mata ne dan air kawai, badai ka laso wajen dadin ba"
"kamace mun komi ni bazan da muba in dai zan samu amsata tofa hakan yayi"
cewar mukhtar din da yake sa cover shoes din qafarsa yana murje bindin sigarin da ya gama zuqarta ya yar a qasan wajen.
"plxxx gifted fada musu kawai ka wuce wajen kasan mayun mata ne su"
hade girar sama data qasa mahabeer din yayi tareda cewa"qyalesu bash barcin suna 'yan iska miye abin wani firgici da ganin yarinyar? da wani birgewa ga wasu matan hausawan marassa kamun kai???? balle ma ita wannan da tazo mana a matsayin 'yar aikin momy na s cikin gida face,,, tana aiki ana biyanta salary shine kukewa qwaqqafin tanbayr dai ko?
toga amsar nan kun samu saiku tashi ku qara gaba haka nan ko 'yan culub?
basu mukhtar da yafadawa cewa yarinyar 'yar aiki ce a gidan hatta bash saida yayi matuqar al'ajabi na mamakin ganin wannan kyakkyawar yarinyar wai house girl??????
wacce kamarta dai hakan ya kamata ace tana gidan wani dan shahararren dan kasuwan kokuma mai mulki ko sarauta tana aure amman gata available a matsayin 'yar aiki a gidan babban atrajirin dan kasuwa mua'zzam saraki tana bauta??????
"ta666 ikon Allah knn"
Cewar bash d'in yana mai sauke ajiyar zuciya.
Mukhatar kuwa baki ya saki shidasu Masud sai da qyar mukhtar ya bude baki yace "kutttt,,, anya kuwa???? to indai haka ne daga wace qasar taxo ne? dan da gani chief baby din nan ba zubin nan bane dagani zafinta zaiyi yawa Wlh ta hadu ta ko'ina k...
miqewa tsaye mahabeer yayi tareda jan wani kalar mugun tsoki yabar wajen bayan ya miqawa bash hannu sunyi hannu yayi shigewarsa cikin gida,, ya tsani irin firarrakun nan
da mukhtar keyi marassa kan gado haka,,,
dole su mukhtar sukabar gidan suma zuciyoyinsu amman cike suke da hasko zuqeqiyar babyn nan kuwa....
bash kuwa bayan mahabeer yabi zuwa cikin gidan shima.....
Ummu hani kuwa saida su baffa suka matsa mata