BOKANYA

Author :  Mrs Sadauki Category :  Love

Chapter   6 / 7

15K to 18K   out of 18K words

a mota " Suby ƴar kuri ta na jin haka ta yi tsalle.



Aliyu na zaune a mota Hajiya ta umarce shi da ya kai Suby salon,ba don ya so ba ya ce "ok ta shigo mu tafi" Hajiya ta ce "Yauwa Auta sannan ka biya kuɗin gyaran,shiga ƴata" ta buɗe ma Suby gidan gaba ,har sai da suka bar layin kafin Hajiya ta koma ciki.






★Ciwon kan Anty Murja ya matsa sosai duk da ta sha magani amma ga banza, wannan ya saka ta kira Umma ta ce ta aiko mata maganin Hausa .
Mu na zaune ne suka yi wayar ko minti goma ba a yi ba Anty Murja ta tashi ta fita sai ga ta da ledar magani.
Wannan lamari ya ɗaure min kai sosai amma na ƙyale,ta na shan magani ai kuwa ta samu lafiya mu ka ci gaba da hidimar mu.



Da dare Aliyu ya shigo,yanayinsa kawai na duba na san da matsala.Na tashi na bi bayan shi,ina shigowa ya yi raf da ni.Na ɗan ja da baya na ce "Ali..." Ban ida ba ya haɗe bakinmu ya fara yi min kiss.
Can ya tsagaita ya ce "Bahijja gaya min sai yaushe za ki samu tsarki?" cikin mutuwar jiki na ce "nan da kwana 36" ya rumtse ido tare da ranƙwafowa saman jikina cikin cool voice ya ce "ba zan iya jurewa ba my Bahij Allah ji nake kamar zan mutu,ban taɓa tsintar kaina cikin irin wannan mugun feeling ɗin ba" mi jikina zai yi banda rawa? Tamkar na hau mazari haka na fara zanzana ƙafafuna ma sun fara gazawa,kuka,kuka fa Aliyu ke nan ga yi mini saboda ya na son kasancewa da ni amma ba hali.



Ya ƙara jawo ni ya manna a ƙirjinsa ya matse ni gam,a tare mu ka sauke ajiyar zuciya.Yadda yake fitar da huci kamar kumurcin zaki kawai ya isa ya ƙara jefa ni cikin cakwakwalin damuwa da tashin hankali.


Daga can falo kuwa ina jin Anty Murja na cewa "shirunsu ya yi yawa fa, Iyani ya kamata ki shiga ki dubo" "a'a ita da mijinta! Ai yanzu an bar irin wannan sakarcin,na san dai ba zai nemeta ta na jinin biƙi ba sai dai romence ku ke cewa ko mi" Anty Murja ta gagaɓe da dariya.
Kukan Baby na fara ji sama-sama,na yi niyya zamewa daga jikinsa da sauri ya sake riƙe ni.A hankali na ɗago kaina wanda ke ɓoye a ƙirjinsa,gabana ya yi mugun faɗuwa ganin yadda idonsa su ka yi ja.
Na lumshe ido ba tare da na shirya ba jin damshin yawunsa kan laɓana,sumba yake min cikin fitar hankali wacce ta kai mu da yin kwance kan bed.



Mun ɗauki lokaci a haka ya na rungume da ni kafin na fara jin saukar numfashinsa.Na ja ajiyar zuciya ina jin salama tunda har ya samu bacci,falo na fito inda Baby ke ta yin kuka Iyani na bata madara.
"Anty Murja ki na ganin Baby na kuka ko ki amshe ta" na faɗa ina turo baki,ba ta tanka ni ba ta ci gaba da latsa wayarta.
Ina ɗaukar ta na ji yanayinta ya sauya ba kamar jiya ba,sai ta dawo sak Babyn farko mai kama da Hajiya .Ba zan ɓoye maku ba har wani kallo na ga ta na yi min kamar ta na jin haushi na......




MRS SADAUKI 💫✍🏻🫶🏻
[01/11 à 15:07] MRS SADAUKI 💫: *BOKANYA👽🌪️🌪️🌪️*
```gajeren labari```



*MRS SADAUKI 💫✍🏻*

SADAUKARWA ga *ASSOCIATION DES ÉCRIVAINS MADUBI*🇳🇪


FCWA☀️


Littafin kuɗi ban yarda ki karanta shi ba tare da kin biya kuɗin karatu ba,duk wacce ta karanta shi ta sani ina biyarta 200 ko gobe.Sannan da wacce ta fitar,da wadda ta gani a wani groupe ita ma ta tura kuma duk ina biyarku kuɗin iya adadin mutanen da suka karanta. Duk mai so 200 ne kacal ta turo da katin ta WhatsApp +22795045822



*PAID PAGE*



11

Shimfiɗe Baby na yi don ba zan juri kallon nan ba,ina nufar ɗaki don dubo Aliyu Baby ta canyara kuka.Bakina na ja na ce "wannan yarinya na kasa gane kan ki wlh,kamar wata hawainiya sai rikiɗa ta ke .Yanzu mine ne na kuka?" Na faɗa ina mai dawowa na ɗauke ta.

Iyani ta ce "ta saba da hannu ne shi yasa,ku iyaye in aka ce ku rinƙa ajiye yara sai ku ga an takura ku to ai ga irin ta nan.Bahijja tunda aka sako ku daga asibiti anya kin taɓa ajiye Baby?" Na turo baki ina gunguni kafin na wuce ɗaki.




Bawan Allah Aliyu sai bacci yake, ka na ganinsa za ka san na wahala ne.Da mamakina ita ma Baby shi take kallo har wani juya ido take gabanin ta maido da idon gare ni ta tsayar da su ƙyam cikin nawa .


Gabana ya yi wata irin muguwar faɗuwa,da sauri na nufi falo .Bisa kan ƙafafuwan Anty Murja na ajiyeta,kuka ta fara ta na wani motsa jiki kamar wacce aka ɗora kan garwashin wuta.


Anty Murja ta ce "mine ne wai ke damun yarinyar nan?" Na bata amsa da "ki duba cikin idonta ki gani" da sauri Baby ta rufe idon har wani matse su ta ke.Anty Murja ta kece da dariya ta ce "Bahijjar Ƴar nan taki da abun mamaki take dubi yadda ta ke jimƙe ido,ɗauko kwalli a saka mata" ko motsawa ban yi ba ina nan ina kallon Baby a gaban idona wani abu mai kamar haƙi kamar baƙin zare ya fita ta hancinta.


Kuka ta fara mai cike da rauni ta na buɗe idonta uwanda tuni sun yi jawur.Anty Murja ta yi mata addu'a kafin ta bani na ɗorata ga nono,sha ta fara har ta na ƙwarewa.Baiwar Allah ta ji yunwa sosai,a wannan ranar daidai wannan lokacin na ɗan fahimci wani abu amma wautar da na yi shine na bar ma kaina sani tare da ɗaukar aniyar sai na bi didigin Baby.






★A can ɓangaren Hajiya kuwa duk jikinta ƙaiƙayi yake yi mata,Karime da ke gefenta wacce Hajiyar duk ta bata lambarin komi ta ce "Hajiya da barin yaran nan ki ka yi suka yi zaman aurensu tunda dai shi Aliyun bai rage ki da komi ba,dubi yanzu wajen ki cutar da Bahijjar ga sakamakon da ki ka dawo da shi"


"Ki bari Karime bisa jikin ƴar iskar Antynta ta ɗora ruhina tsabar mugunta,amma zan rama nan da kwana uku komi zai je daidai kamar yadda mu ka tsara"
"Ki na ganin Aliyu zai yarda ya auri Suby?" Karime ta tambaya.
"Mi zai hana? In ma bai yi don Allah ba zai yi don tsiya,tun jiya na so ya kawar da budurcin Suby amma yaron nan mai taurin kai ya tafi gidan shi"
"Ni zan so su yi komi bayan aure kar mu je ayi biyu babu,ba ta ga Aliyun ga shi kuma ta rasa budurcinta" cewar Karime .
"Hum! Sai kace ba ki san ni ba? Ko ko kin manta ni ne? To ki tsaya ki ji auren Aliyu da Suby ki ƙaddara ma har an yi shi" Hajiya ta faɗa ta na susar bayanta.
"To Hajiya bari na je na kwanta sai da safe" Karime na gama faɗa ta bar Hajiya ita ɗaya.
Kamar jira suke abokanta suka bayyana cikin ɗakin, meeting suka fara kafin ɗaya daga cikin su ta baiwa Hajiya wani garin magani "ki karɓi wannan ki tabbatar kin sa ma Yayar Bahijja shi cikin kayanta na jiki da zarar kin yi haka doli za ta barin gidan" Hajiya ta karɓa ta na cewa "gobe zan koma gidan ai,ku na iya tafiya amma kar ku manta ranar biki ku zo na gayyace ku a suffar mutum za ku zo"
"Ina jin tsoro Hajiya kar asirinmu ya tonu "
"Matsalata da ke kenan,mugwar siffarki ki aje ta gida ko ba a koya miki yadda ake yi ba?"
"An koya min amma ban taɓa gwada wa ba saboda ina gudun a samu matsala"
"Mtsw ba ki ga lokacin da zan tafi neman auren Aliyu ba sai da na ajiye duk wata muguwar siffa ba? To ke ma kiyi haka"




★Washegari
Ina zaune gefen gado Aliyu ke shiryawa cikin wani farin yadi.Na dube shi a karo na ba adadi na ce "Aliyu jiya mine ne ka sha da ya saukar ma da mugun feeling?" Da mamaki ya dube ni ya ce "feeling ? Ni? Mi ki ka gani?" Shiru na yi ban ƙara cewa komi ba.


Ya na gama shiryawa ya zo inda nake a zaune ya yi min sumba kafin ya fita,addu'a na bisa da ita kafin na fito falo.
Ina shirin zama Hajiya ta shigo babu ko sallama sai ƙamshin turare ke tashi irin na ƴan bori .Gaisheta na yi,ta amsa ciki-ciki kafin ta ce ma Iyani" yau kuma ku biyu ne gidan?" "A'a Murja na toilet ta na wanka" ba ta sake cewa komi ba ta shiga ɗayan ɗakin,sam ban yi tunanin wani abu za ta yi ba kawai na barsa ƙila kayanta na riƙe da hannu za ta aje.



Ko minti biyar ba yi ba ta fito,kan kujera ta kwanta ta lumshe ido.
Cike da mugunta Hajiya ke kallon Bahijja da Iyani ta ƙasan ido,so take ta nuna masu kamar ta na bacci.
Murja ta fito daga wanka hankali a ɗan tashe kafin ta shiga ɗaki ta ɗauko jakar kayanta."Bahijja zan tafi na dawo" ta ce min ta na mai ficewa ba tare da ta ko tsaya ta ji amsa ta ba.




Fitar Anty Murja da kamar minti goma Hajiya ta fara nasarin bacci yayin da kuma Baby ta fara wani irin kuka kamar ranta zai fita.Duk ruɗewa na yi saboda ta ƙi shan madara,an yi mata wanka an cire kayan jikinta amma ta ƙi yin shiru.
"Ki bata ta sha ƙila za ta yi shiru" cewar Iyani,na karɓi Baby.Jikina tuni ya bani wannan Baby ta biyu ce amma na daure na ɗora mata abincinta,sha ta fara ta na kuka ƙasa-ƙasa kafin ta yi shiru.



Zut! Zut! Zuuuuuu haka nake ji kafin na farga ta tsotse duk madarar da ke ciki,kamar an yi min doli haka na maidata ga ɗayan mamar nan ne na ga ikon Rabbi.Tamkar ana jan raina haka na fara ji,ban san ta yaya ba naji na fizgo kalmar "ya rahamane!!" Ina mai cire mamar a bakinta,in ba idona suka gane min ba daidai ba tabbas jini na gani ya na ɗiga a mamadin madara.



Na sa hannu na laƙuto sai kuma ya koma fari ƙal kamar rufa ido, Baby na kalla wacce ta ke wani min fari da ido.
"Ban san mi ke damun ki ba,haka ban san mine ne tattare da ke ba amma haka kawai nake jin ke ba alkhairi ba ce a rayuwata.Zan bar shayar da ke daga yau tun da dai akwai madara,gobe zan sa Aliyu ya ƙaro miki wata"
Cikin sakwani biyu Baby ta canza wanda ya yi daidai da tashin Hajiya .
"Ban gane ba za ki ƙara shayar da ita ba? Gaya min dalili?" Shine tambayar da Hajiya ta yi min .Sosai na yi mamakin yadda aka yi mai bacci ya ji maganar da nayi duk da ƙasa-ƙasa na yi ta.




Wani murmushi na yi wanda ni kaina ban san na mine ne ba na ce "eh Hajiya saboda babu ruwan nono madara za ta rinƙa sha" ai kuwa Hajiya ta hau ni da masifa "sai in ke za ki sawo madarar amma ba dai Aliyu ba" "sai yunwa ta kashe ta kowa ya huta amma ba zan sake shayar da ita ba" kamar wacce ta sha wani abu haka na koma ranar har sai da Hajiya ta yi mamaki,a ƙarshe dai ta bar gidan bayan ta gaya min kalma " za ki gani"




Ko da Aliyu ya dawo bai tambaye ni Hajiya ba haka ni ma ban yi masa ba.Matsalata guda a yanzu shine ina Anty Murja ta shiga tunda na kirata wayarta ba ta shiga, Umma kuma ta ce har yanzu ba ta je can ba.



Yau ma Aliyu sai da na rage masa zafi mugun feeling yake fama da shi,ita kuma Baby kukan duniya ta yi shi amma na ƙi shayar da ita a doli ta sha madara.
Cikin juyayin sauyin rayuwa da kuma ɓatan Anty Murja aka yi zanen suna,ranar buki Umma ta zo sai na ga duk yanayin ta ya sauya.
Na yi niyyar tambayarta dalili amma ta ƙi bani fuskar haka,ana tsaka da buki ta ja ni gefe.


"Bahijja daga yau ina so ki koma wankan da ruwan kunnuwan magarya,sannan ki rinƙa karanta surorin ukun ƙarshe da ayatul ƙursiyu da kuma amanar rasulu ki na sha hakan zai warkar da ke da ciwon duk wani sihiri" Umma ta faɗa min tare da yi min nasiha mai ratsa jiki "duk tsanani kar ki mijin ki ya gundire ki,kar ki gaji balle ki ɗauki aniyar barinsa."
"To Umma in shaa Allah zan yi duk yadda ki ka ce.Shikenan anty Murja har yanzu ba ta dawo gida ba?" Na tambayi Umma.
Baki kawai ta ja ta sauke ajiyar zuciya kafin ta yi min sallama.


★Bayan buki

Yau kwana na arba'in har da kwana biyu a sama amma jinin biƙi bai da niyyar tsayawa,a kullum sake bulbulo min yake.Tun ina jin kunya har na yi ma Umma maganar,addu'a kawai ta ce na ci gaba da yi.Ɓangaren Baby kuma har yau ba ta sauya zane ba,duk da Aliyu ya yi nacin duniya amma fafur na ƙi shayar da ita.




"Bahijja ban san mi ki ka ɗauke ni ba, kin hana ma Ƴata abincinta haka ni ma kin ƙi karɓata a kullum sai ki ce jinin bai ɗauke ba.Wai ko zina ki ke so na fara yi?" Aliyu ke faɗar haka cikin ɗaga murya kamar zai dake ni.
"Ta ya zan shayar da yarinya da duk sati sai an canza mata robar feeding? So kake ta tattaune min mama? Ka na fa gani yarinya kamar ɗiyar aljannu gwangwanin madara bai yi mata kwana uku ta shanye shi" cikin masifa ya katse ni da "Ni kuma mi yasa har yanzu kin ƙi bani haƙina? Ko ko ni ma renon Aljannun ne tsoro ki ke ji na zazzage miki abu?"
Na ce "tunda *BOKANYA* ta yi ƙulle-ƙullenta ta yaya jinin zai tsaya? Ai wlh ko da na ga Hajiya ta na sa ma wannan ɗan banzan feeling ɗin na riga na gano nufin...." Ban ida kai ƙarshen kalmar ba Aliyu ya ɗauke ni da mari,yayin da Baby ta fara dariya har da ƙyarƙyatwa.



Wannan karon ba ni ba hatta Aliyu sai da ya firgita,a tare mu ka kalli inda Baby ke kwance kafin mu kalli juna.
Da sauri na ce "Aliyu ka ga abinda na ke gaya ma ko? Ina ce dai ka ji dariyar da jariri ƴar wata biyu ta yi?" Shiru ya yi ya na kallon Baby.



"Ki kwantar da hankalin ki Bahijjana,ko ma su uban waye suka shiga jikin ƴata za su fita a yau,ɗauko hijabin ki mu tafi" Aliyu ya faɗa ya na sungumar Baby.
A mota na tarar da shi kafin wuce,gidan wani malami ne mu ka je.
Albora shine sunan shi, Baby ya karɓa wacce ta rumtse ido,ya yi murmushi kafin ya saka ta cikin wasu ruwa a doli ta buɗe idon ta na kuka.



"Aljannu sun yi ma ƴar nan illa sun mayar da ita kamar wata shago su shiga su fita duk lokacin da suka ga dama" cewar malamin ya na mai yi mata karatu, Baby sai kuka take wanda ka na jinsa za ka gane babban mutum ne ba Jaririya ba.


"Ga wannan ruwan ku rinƙa yi mata wanka da su kullum,sannan ku shafa mata man zaitun" Malam Albora ya faɗa ya na mai miƙa ma Aliyu.
Mu na fitowa Aliyu ya ɗauki hanyar Kwalo,duk yadda na nuna rashin amincewa bai saurare ni ba.




Mu na isa mu ka tarar da wani tashin hankali,kaf iyalan gidan sai koke-koke suke.Hankali tashe Aliyu ya ce "mi ke faruwa?" Ya Yusuf ya bashi amsa da "Hajiya ce ta rasu"....
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter :

6 / 7