ba halinshi bane,.dan haka sadiya kuyi
haquri kawai kubi abinda nace.,sadiya dai shiru
tayi Ahmad ne yai qoqarin cewa insha allahu
zamuyi yadda kikeso momy kuma babu Wanda
zaiji wannan maganar abakinmu dayardar Allah
munyi miki alqawari;momy tadan saki fuska tace
yauwa Ahmad allah yaimuku albarka yanxu
kiramin habibu nagaya masa muna asibiti.,kuma
inaso idan zaka tafi kuwuce tareda sadiya domin
su kwana da yaran nan.yakarba wayan yakira
yamiqa mata.,bugu 3 yayi taga an danna busy
bata damu ba tinda daman tasan baya daukar
kiranta saidai yakashe yakirata.,jim kdan kuwa
saiga kiran Habib tadau ka yagaisheta cikin
ladabi.ta amsa muryarta babu
annashuwa.,sannan tace habibu muna nan fa a
asibity salma ba lapia yanxu haka dai gatanan
sai abinda allah yaso,.what?momy meya sameta
wani asibity ne momy ina fatan dai tana nan da
ranta momy bani ita dan allah ko bata magana
ne gaba daya Habib yarikice momy tama rasa
amsar dazata bashi ajiyar zuciya kawai tayi
sannan tace muna horeb hospital ne saikazo
kawai takashe wayarta.,afurgice Habib ya nufi
daki fadeela tamiqe a tsorace tana fadin
sweetheart lapia kuwa?waye ba lapia.ko
sauraronta beyiba yaje yasaka farar jallabiyyarsa
yafito da sauri yana fadin asibity zanje yanxu
momy takirani take fadamun salma ba lapia
yanafadi yana qoqarin ficewa,.batayi mamaki ba
dan tasan yadda yakeson qanwar tashi aranta
taji haushi amma afili cewa tayi subhanallah
allah yabata lapia saika dawo kafin tarufe baki
shiyariga ma yayi waje,aranta kuwacewa tayi
allah yasa ta mutu inga qaryar iskanci.,taja
tsaki ciki ciki tajuyo ta rufe qofarta ta wuce
dyning ta zquna cike da haushi.,shiko gogan
naka tuni yafigi motarsa sai asibity,.a bangaren
su abban afnan kuwa Abba yakira yakira wayan
sadiya amma anqi dagawa tuni yafadama hjy
abinda ke faruwa sannan yace tai maza ta dauko
hijjabinta dan basuga tazama ba dan yaji ance
afnan dinshi ba lapia kome yasameshi
oho.,hankulansu duk atashe suka kama hanyan
asibity mu samman ma Abba da ko kadan
bayason yaji abinda zai cutar masa da
dansa.,suna isa saiga Habib ya iso nan suka
hadu a harabar asibityn daidai nan kuma Ahmad
da sadiya sun fito da nufin tafiya gida.,nan suka
hadu babu Wanda yatsaya wata gaisuwa Habib
yadubi Ahmad yace ina ne word din?!Ahmad yace
kuxo muje suka dunguma gaba daya suka nufi
inda salma take.,nan suka tadda doctor a tsaye
kan salma yana mata allura sannan ya cire ledan
ruwan daya qare yasa mata wani.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 9
==>Habib yai saurin qarasawa wajen jikinsa na
rawa yana fadin doctor ya jikin nata da sauqi
kuwa!?Dr yace yp zazzabine me zafi yanxu ya
rufeta nayi mata allurori yanxu yanada kyau
kubarta ta huta domin gaskiya taji jiki tana
buqatar Hutu bamason ana yawaita surutu
kubarta ta huta pls!Habib yace insha Allahu za a
kula amma Dr menene matsalar nata abinciken
da kukayi meyake damunta ne pls walh bata
saba ciwo irin wannan ba naga harda qarin jini
akai mata,.Dr yace eh abin ya danganta ne daga
irin mijin da kuka aura mata wata qila yafi
qarfinta kuma kaga qaramar yarinya CE gaskiya
kunyi mata auren wuri gashi kun
hadata da ba qauye marar tausayi yayi muku
kaca kaca da yarinya gsskia ina iya cewa harda
laifinku.,amma insha Allahu zata samu lapia
karku damu.yafada tare da bude qofa yai
ficewarsa inda yabar Habib atsaye yasaki baki
hannunsa na rawa bakinsa na motsi amma
yakasa magana gashi kuma yanada tambayoyi
domin shidai be fahimci zantuttukan likitannan
ba shin meyake nufi ne menene yasamu
salman!;momy kuwa da Ahmad da sadiya tinda
likira yafara zancen nan a furgice suke tsananin
tashin hankali yaqara ziyartar zukatansu kuttt.!!
hjy da Abba suma dai sun kasa fahimtar
maganganun Dr dan duk yasasu a duhu.,amma
shidai Abba hankalinsa be kwanta ba dan kuwa
bega afnan ba.,babban burinsa kawai a nuna
masa dan autan nashi,.Habib ne ya katse kowa
daga saqe saqen zuci jiki a sanyaye yace momy
nifa ban gane maganar Dr ba wai meya faru da
salma!?.momy ta maida numfashi sannan tace
Habibu wannan ba maganar nan bane.,yqnzudai
yakamata kuje kuduba afnan din ko ta maida
dubanta gun Abba tace alhj kuje kuduba afnan
din ko,. Habib yai saurin cewa haba momy
kifada mana abinda ya sameta mana mu fita
daga cikin rudaninda Dr yajefamu yanxu ga
salma a kwance afnan din shikuma meya
sameshi??!yaqara sa bakin gadon yataba jikin
salma agigice yajuyo yana fadin momy kinji
jikinta kuwa,.dan allah meya sameta ne idonsa
duk sun ciko da qwalla.,ta dubesu gaba daya
tace alhj muje wajen afnan din inyaso mayi
maganar a waje kaga Dr yace kar a yawaita
surutu!,alhj kan daman ya qosa yaga afnan dan
haka shiya fara bude qofa hjy tabi bayanshi
dukansu zuciyarsu cike da saqe saqe,.momy ta
kalla habib sanna tace kataso muje cen zakaji
qaddarar data afko mana yau.,amma inaso
kazamo me yadda da qaddara kuma karka tashi
hankalinka domin haka allah yaso sannan itama
ta fice sadiya da Ahmad sukabi bayanta.,da
sauri yamiqe shima yabisu yna nanata
maganarda momyn nashi tai masa yanxu a
zuciyarsa!yasan lallai akwai wani Abu me
girma,.suna shiga suka cimma afnan
kwance sai rawar sanyi yake hatta gadon dayake
kwance girgizawa yake.,Abba yaqarasa a furgice
yana fadin afnan mega sameka ne haka!,dan
allah kuyi mana bayanin abinda yasamu yaran
nan.nan danan masu saurin kuka suka fara
musamman ma wa Inda suka San abinda
yafaru,.momy tai ajiyar zuciya sannan tace
tabbas abin kuka ne yasamemu kuma dole muyi
kuka bazan hanaku kuka ba,.taqara da
cewa an tsutsemu an tsutsi salma yau anci
mutuncin mu anci mana zarafi anje har gida
anyima salma fyade na rashin tausayi.!!ta fashe
da kuka
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 10
==>Dukkansu saida suka razana da jin
maganarda momy tayi.,Habib ne yameqe hankali
tashe yace what momy fyade fa kikace salma din
akaiwa fyade!;momy tace tabbas kuwa anyi mata
fyade na rashin tausayi.dan dalilin dayasa
kukaga afnan anan wajen kenan domin kuwa
sanda abin yafaru da ita afnan yaje gidan da
nufin yagaisheni yanata sallama yaji shiru gashi
kuma yaga qofa abude sai yace bari ya leqa
falon ko muna bacci ne aiko gana shiga yaga
salma cikin wani hali juyowanda zaiyi saidai yaji
an buga mai qarfe akanshi nan take shima ya
fadi qasa sumamme,.yakai wani lokaci sannan
yafarka jini sai binshi yace domin anfasa mishi
kai daqyar ya iya qoqarin daukar wayanshi shine
yakira sadiya yafada mata ita kuma tai maza
taxo da mota aka kwasosu sai asibity nanne ma
aka gane Ashe fyade akai mata.,innalillahi wa
inna ilaihirraju'un gaba daya suka sa salati
sadiya kuwa da Ahmad suna mamakin abinda
momy ta shirya amma babu yadda suka iya dole
suyi shiru,.afnan dake kwance yana fama da
matsanancin zazzabi da ciwon kai.zuciyarsa ta
qara daukar zafi.tabbas shidai beji dadin yadda
momy ta rufa masa asiri ba,yazatai mishi
haka,wata qila data bayyana gaskiya hakan ze
iyasa ya mallaki salma amatsayin matarshi.ji
yayi kawai zuciyarsa tana qara masa quna da
zugi,shin kodai ya bayyana gaskia ne!?.,Habib
ne yataso jikinshi yana karkarwa yaqaraso
yazauna a bakin gadon da afnan yake.'ya dafa
qafarsa zuciyarsa kamar zata buga yana fadin
afnan ko kaga fuskar wanda yaima salma
wannan mugunta?pls idan kaganshi zaka iya
ganeshi!?nayi alqawari ko dan gidan uban waye
sainaga bayanshi tinda ya cutarmin da
salma!kuka ne ya kubuce masa tare da cewa na
shiga uku shikenan an lalatama sister na
rayuwa.innalillahi wa inna ilaihirraju'un",momy
ta dubi aljh tace dashi inaso sadiya taje ta taya
yara zama kafin mu koma gida yanxuma nace
tabi Ahmad su tafi,aljh yace ba matsala,ta dubi
Ahmad tace yakamata kutafi dan dare yayi sosai
anbar yara a gida,tashi kawai sukayi suka fice
ba tareda sun CE komai ba.,momy ta biyo
bayansu sukai sallama ta wuce wajen
salma,.Habib yasake maida dubansa kan afnan
yana qoqarin sake yimishi magana,.sai gani
sukayi yana wani miqewa yana nadewa jikinsa
yasake dafewa kamar wuta gaba daya sukayo
kanshi kar kuso kuga rudewa wajen Abba da
ummanshi.Habib ma yadan tsorata da ganin
yadda yakeyi.,dan haka da sauri ya miqe yace
Abba bari akira Dr.dasauri yafice sai gashi tare
da Dr umma dukta rude gani take kamar dan
nata mutuwa zeyi.harta fara kuka,Dr yayi masa
wata allura sannan yace su samu towel da ruwa
su dinga jiqawa suna goge mishi jikinshi
ahankali zazzabin ze sauka,.sannan akula kar
ana yawan surutu akanshi,.dan jininsa ya hau
saisun kula Dr ya fice,nanfa hankali yaqara
tashi!!,Habib ficewa yayi abinsa ya nufi gun
salma,yana zuwa yaga momy tana sallah
yazauna bakin gadon ya tallabo salma tanata
bacci saidai jikin nata har yanxu da zafi,.addu'a
yafarayi cikin ransa ya allah ka nunamin Wanda
ya keta haddin yar uwata.lallai an cutar mai da
yar lelenshi,umma ta idar race dashi yakamata
kaxo katafi gida ko,ya kalleta momy kije gida
kawai ki huta zan zauna da ita.,momy so nake
da zarar ta farka ta kwatantamun fuskar wannan
azzalumin;.momy ta girgiza kai tace habibullahi
abinda yafaru yariga yafaru,kaje gida abinka
nizan kwana da ita kuma Dr yace da wuya ida
zata farka yau,kuma kota farka ba lallai ne ta
iya wata
magana me tsawo ba.dan haka katashi kawai
kaje gida abinka.,,haka momy ta matsa masa
yatashi yatafi badon ransa yaso ba
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 11
==>Gari na wayewa sadiya ta kimtsa komai daya
kamata ta hada musu,.Ahmad yaxo yace idan
tashirya taxo suwuce shima zaije yaga yadda
suka kwana kafin ya wuce wajen aiki.sumayya
tasa kuka itama sai anje da ita taga
salma,.daqyar Ahmad ya lallabeta tareda
alqawarin anjima zai dawo ya kaisu idan anty
sadiya ta dawo sannan ta haqura,.suka kama
hanya sai asibity,suna shiga sukaga momy tsaye
akan salma suka qarasa da sauri,wai Ashe taga
tana motsi da qafarta ne shine duk ta rude wai
ko farkawa zatayi,.nan suka gaisa momy tace
suje su duba afnan rai abace sukaje badon sunso
ba,shima dai baccin yaketayi kamar
matacce,suka gaisa da umma sama sama Ahmed
yai sallama ya wuce abinsa,.sadiya taje ta
kawoma momynta abinci.sukaci sannan tatashi
taje ta duba salma ta dawo.,fitarta keda wuya
saiga Habib yaxo ya nufi qanwar tashi yna
tambayar momy ta farka kuwa,tace tadai dan
motsa yau da safennan,inaga da alamun
sauqi,likita yace babu wata damuwa zata tashi
cikin ikon Allah.yace ya afnan dinfa.tace shima
ba laipi kaje kadubashi mana.momy tayi tayi
yace shidai agaisheshi koyaje tinda ba magana
zai masa ba ai ba anfani,.ranar dai daqyar momy
tamatsa masa yatafi office yana maqale da
qanwarsa ko zaiga farkawanta amma shiru
hakadai yadaure ya wuce.,duk wannan abin da
ake inna bata sani ba.,aiko rufayda ta fakaici
idon sumayya ta salale sai gidan inna, tana zuwa
ta tadd inna a Palo taruga aguje ta fada jikin
inna tana haki,,inna tace yau naga arziki yannan
karyani zakiyi,daga ina kike haka kamar an
jefoki kodai kinyo tsokana ne aka biyoki.,tace a
a inna gudowa nayi sumayya bata sani ba nasan
zata iya biyoni shiyasa naketa gudu nasan
zataina nemana na barta ita kaidai.inna tace oh
kudai Baku rabo da shiririta.to ai yanxu zakiga
tabiyoki., ta dago kai a a inna ai bata isaba
tinda momy batanan kuma Khalid yana bacci
bazata fito tabarshi ba.,inna tace ina Maman
taku taje bayan jiya tabar nan!?rufy tace ai
tinjiya damuka koma gida bamuga anty salma
muna shiga dakinta mukaga jini a towel dinta
Ashe an yankata ne da bamanan shine momy ta
fita itama taqi dawowa aunty ne ma tatayamu
kwana shine....ai tuni inna ta hankadeta daga
jikinta takai mata duka ban gane an yankata ba
dan ubanki wani irin magana ne wannan ni zaki
kawoma shashanci.,rufy ta zumbura baki tace to
shine zaki dukeni ni gidama zan tafi abuna"inna
ta ruqota yanxu ina salman take?! Taqara turo
baki toba nace miki an yankata ba;,gaban inna
ya yanke ya fadi lallaima yarinyannan da gaske
take ko kuwa,.dan haka taqara jefo mata
tambaya! to ina mamanku tace ai tin jiya bata
dawo ba!,inna tasa salati innalillahi wa inna
ilaihirraju'un. Inna tayo waje tna qwalawa husna
kira!husna husna ta nufi sashensu,.momyn husna
ne tace ke bakyaji inna na kiranki husna tace ni
walh momy kinsan kiran inna yanzu haka ba
wani abin azo aji bane.,saiga inna tashigo
agigice ta miqa mata waya tace kirawomin
abubakar yanxu rafida tazo take cemin wai an
yanka salma wai mamansu ma bata kwana a
gida ba.,safiya tace wani irin an ynkata
kuma.husna ta kwashe da dariya tace umma kinji
ko yanxu shirmen rufy zaki kama,.inna tace
atafaf sai ankira mata abubakar.,husna ta kira ta
miqa mata, yana dauka inna bata bari sun gaisa
ba tace bukar
meyafaru da salma ne?!shiru yayi yana tunanin
waye yafadama ina abindake faruwa.tace kayi
shiru ina sauraronka kafadamun abinda yafaru
da salma.kame kame yafara inna..walh..inna
wayace miki.tsawa taimasa taredacewa zaka
fadamun kosaika rainamin wayau kodai salman
ta mutu ne da gaske.,yace a a inna bata mutuba
walh suna asibity tamaji sauqi inna ki kwantar
da hankalinki. Kuka inna tasa da salati shikenan
Ashe gaskiyane an kashe salma ba ason
fadamunne magana yake mata amma kojinsa
batayi duk. ya birkice gashi akan hanya yake
zaitafi asibity ba shiri ya jiyo yayo gidan Inna.,
husna da mamanta sunyi tsarko tsarko suna
kallon inna cike da mamaki.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 12
==>Zama tayi dirshan tana tafa hannuwa tana
cewa kungani ko yrinyar nan nasan haka nan
kawai bazatazo ta fada wannan maganar a
banza ba. Nasan ba hakanan ba akwai wani
abinda ake boyemin.,husna tace inna wani Abu
yafaru da salman ne?!tace gashi kuwa abubakar
yacemin suna asibity to da wuya idan salma tana
Raye., hjy safiyya tahau salati tace inna barida
asake kiranshi aji!;sai sukaji sallama abubakar
ne yashigo da sauri yayogun inna yana fadin
inna bata mutu ba tashi muje nakaiki ki ganta
.,tamiqe da saurinta tayo waje yabiyota
abaya,.husna tafito a guje tana fadin Abba nima
zanje kujirani Abba wai salman batada lapia ne?!
yace wai waye yaxo yafadama inna ne,.husna
tace rufy CE taxo tace mata wai an yanka
salma., murmushi kawai yayi yace allah ya
shirya jeki dakko hijabinki mutafi.,dasauri taje
da dakko suka fice akabar hjy safiyya a gida.,ita
kuwa rufy tuni ta sulale tai gida abinta., basu
tsaya ko inaba sai asibity.,suna shiga momy
saida ta tsorata da ganin inna amma ta dake
tace inna waye fada miki muna nan?!tace ban
sani ba an bari saita mutu sannan agayamun
ko.tace yi haquri inna walh tin jiya hankalinmu
be natsu bane,. Inna taqarasa gun salma tana
fadin oh
ni zuwaira meya samarmin salma ne!alhj kam
juyawa yayi yanufi gun afnan yana shiga yaga
dakin ba kowa mamaki ya kamashi yawo waje
sai suka hadu da hjy tafito daga toilet tayo
alwala.,yace ina afnan din?!tace ai yana ciki
baka shiga bane yace yanxu nashiga banga
kowaba tace wani irin bakaga kowa ba muje
nabarshifa yana bacci,suka shiga tare hjy taga
wayem tasaka salati tace alhj ina yanufa ne?!
sukayo
waje arude tai hanyan word dinda salma take
yace dawo karkije tare mukaxo da inna yanxu
kinazuwa hankali zai qara tashi murasa yadda
zamuyi da ita,.tace saida nace
ma sadiya tazo tazauna dashi amma ashe bata
xoba,.yace yanxu taho muje inyaso daga baya
saimu kirasu awaya mugaya musu abinda ke
faruwa. Da sauri sukai mota suna tafe suna duba
hanya, nan bangaren salma kuwa motsawa
tafarayi gaba daya sukayo kanta suna
tsatstsaye.Salma kuwa jitake kamar awani
duniyar take jikinta duk inda tai qoqarin juyawa
saitaji wani masifar ciwo kamar anyi mata
shegen duka., momy ta zauna tana fadin salma
salma sannu kinji!"ahankali
abubuwa suka fara dawo mata tafara tuno
abubuwanda suka faru tsakaninta da yaya afnan.
Tuni tafara shure shure da qafa tana fadin yaya
dan Allah kayi haquri bazan sake ba yaya
kataimakeni nace baxan sake ba yaya.,kasakeni
tuni momy ta tallabota ta rufe mata baki tana
mata addu'oi inna tace oh wani yayan take kira
ne momydai batace komai ba saida taga salma
tadaina shure shure sannan tasake mata
baki!"ahankali salma tabude idonta taqara
lumshewa dan tarasa ina tace gashi hankalinta
be gama dawowa jikinta ba., ta sake cewa yaya!
yayana!kazo ka ceceni dan gani take kamar har
yanxu a hannun afnan take.,momy tace salma
bude idonki mana kiganmu ga inna tazo dubaki
ga antynki sadiya ga sisternki husna kubude
idonki kinji ba abinda zai sameki!"jin maganar
su kawai take sama!sama kamar wani almara!.
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 13
==>Tasake bude idonta tafara ganinsu dishi
dishi!.ta qara bude idonta sosai tana kalle kalle
dan batasan a ina take bama. Wajen yayi mata
wani kala ta kalli momynta tafara magana da
murya qasa qasa kamar haka"momy nan ina ne?!
momy tace asibity ne bakida lapia shine aka
kawoki,!tai shiru jim kadan tasake cewa momy
ina yaya Afnan!?momy tace yana nan
zuwa..zakici abinci?ta girgiza kai tafara kuka a
a momy dan allah kice masa karyaxo dan allah
momy walh kasheni zeyi.,momy tai saurin cewa
to kwantar da hankalinki zan gaya mishi dena
kuka kinji"inna ta bude baki tare da cewa kaji
wani shirme duk zafin ciwonne haka!inbada
zafin ciwo afnan dinne zai kasheki!ta kalli momy
tace Aisha anya kuwa yarinyar nan tana cikin
hankalinta? kijifa surutanda taketayi tinda ta
farka;momy tace inna zafin ciwo ne kawai zata
warware insha Allahu,.inna sai qara
shashshafata take itako tanata zare ido tana
kalle kalle sai lokacin ta kula da qarin ruwanda
ake mata.,sadiya da husna suka dubeta sukace
sannu ya jikin batace komaiba tafara qoqarin
tashi ta zaina nanfa taji qugunta yariqe gam ga
wani masifaffen ciwon jiki.,anty sqdiya tace ko
adagaki ne ta daga kai alamar eh., sadiyaa tazo
da sauri ta dagota ahankali,.amma Ina jitayi
bazata iya zama ba haka takoma ta kwanta;sai
hawaye suka fara gararowa afuskarta da sauri
anty sadiya tafara lallashinta tana goge mata ita
kuwa husna tsaye tayi tana kallon ikon allah
yadda taga salma lokaci guda ta rame manya
manyan idanunta sun qara bayyana fuskarta
yazama wani siriri lebenta ya bushe aranta tace
lallai wannan ciwo yabama sis dinta
wahala.,.alhaji abubakar kuwa haka suka dinga
Neman afnan ko zasu ganshi akan titi amma
babu shi babu labarinshi haka suka figi mota sai
gida.,suna shiga palo wazasu gani afnan ne
kwance ya daura hannuwansa akan qirjinsa ya
miqe qafa daya ya daga daya fuskarshi na kallon
sama!hawaye nata faman kwarara daga idonshi.,
sunyi tsarko tsarko suna kallonshi cikeda takaici
ta wani bangaren kuma sunyi hamdala da
ganinshi Abba yaqarasa yana fadin afnan
wannan wani irin rashin hankali ne zaka gudo
gida kazauna ciwo na cinka!hjy ta nemi waje
tazauna tare da cewa kaimadai kafada.,yaxo ya
kwanta ne yanata kuka kamar wani qaramin yaro
to dukanka akayi taja tsaki..mtsww tindazu
mukebin kwararo kwararo muna nemanka Ashe
kai gida ka nufo kabar yan iska acen KO., Abba
shikam harya karaya..yace haba kibarshi
hakanan mana bakya ganin halinda yake cikine.!
tace to mu kuma ai soyayi yajefamu atashin
hankalinda yafi haka.yanxu daya fadi ahanya
mota ta takeshi aimu yabari da baqin ciki., Abba
ya dafa kan afnan yace my son me kakema kuka
ko jikinne!?nan yaji jikin Afnan zafi kamar
garwashi. Yace kinji jikinshi kuwa tashi mu
koma asibity,.shigo dake kwance duk maganar
da suke be tankaba saida yaji ance yatashi
akoma asibity.,da Sauri yatashi ya zauna yana
cewa Abba dan allah kabarni walh naji sauqi
baxan koma ba,.Abba da umma sukace atafaf
saiya tashi sun koma bazasu zauna suna kallo
ciwo yakasheshi ba; fashewa yayi da kuka kamar
wani qaramin yaro walh Abba idan kuka mayar
dani mutuwa zanyi ni bazan koma ba,duk sai
sukaji ya kashe musu jiki. Alhaji yace abarshi
tinda bayaso zaije ya karbo masa magungunan
sallama nan hjy ta kira momyn salma take fada
mata afnan ya gudo gida,. Salma kuwa tananan
tana masu kuka ita akira mata yaya Habib da
yaya Ahmad suzo su kaita gida.,bashiri momy
tasa aka kirashi! saigashi yaxo kamar Wanda
yahawo jirgin sama.yana aikinshi a office daman
hanklinshi yana wajenta saikuma yaji kira"momy
dai tarasa yazatayi kar ahaifa danda ba ido!yaxo
dasauri ya dagota murya a shagwabe tace wash
yaya bayana ciwo da cikina yaya harda kaina
ciwo yake'.saiga hawaye sun sake kwararowa:
hankalinshi yatashi yace sorry sisterna waye
yatabamin kene!;pls zaki iya gane fuskarsa dia
kidaina kuka saina daukar miki fansa!;gayamin
kinji zaki iya ganeshi?,!kuka ta sakar masa tare
da cewa ba yaya bane.....
===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 14
==>momy tai saurin cewa aina gayama yayan
naki karyaxo ba shikenan ba/Habib yai shiru
daga bisani yace momy wani yayan take
magana?tace uhm walh tinda tatashi taketa
shirme nima narasa mezan mata ma;salma kuwa
kallon maman nata kawai takeyi wai itace za ace
tana shirme/kodai basu San abinda yaya afnan
yai mata bane!;to amma idan basu saniba
meyasa tagansu a asibity?kodai daman sun tafi
sun barta ne dan yazo yai mata wannan Abu?!
duk acikin zuciyarta take wannan tunanin"ya
Habib ne ya katseta da cewa..qanwata kin
ganeni kuwa?ta daga mishi kai alamar eh"ya na
shirin jefo mata wata tambayar nan yakula
Ashefa inna tana dakin kuma ya tabbata batasan
halinda ake cikiba dan yasan baza a gaya mata
wannan mummunan labarin ba!shiru kawai yayi
ya dubi inna yace ke tsohuwa meran qarfe meya
kawoki nan?'ta turo baki tace abinda ya kawoka/
ai natsayane naga iyakar gudun
ruwanka tinda kashigo ko kallona