Author : Category : Romance
haƙuri, kuma ba zan ƙara kiranta ba."
"Hakan shi yafi,"
Da ya shiga cikin bayin sai ya tura mata da tsaƙo kamar haka;
Ina ba ki haƙuri bisa laifin da na yi miki. Haƙiƙa na cutar dake, amma soyayyarmu ba za ta yiwu ba.In a roƙon ki yafiya don a yau zan bar Ƙasar nan ki yafe mini na ɓata miki lokacin da na yi. Sai dai ina son ki sani ina matuƙar ƙaunarki daga Muhammad na ki.
Sai ya tura hoto wanda daga baya ya goge.
Wayar ya ije cikin ƙunci sai kawai yaji hawaye na zubar masa a ƙunci.
"Da gaske ba zan auri Hilah ba za ta zamo mallakin wani? Innnalillahi wa inna ilaihir raju'un!" Ya furta a cikinn zuciyarsa.
Wankan ya yi, sannan ya shirya cikin tsadaddiyar shadda. Haƙiƙa ya yi kyau duk da ramar da ya yi bai hana shi kyawu ba.
Yana shiga cikin gidan, abokan wasa suka yo kanshi wanda ko murmushi ya kasa yi musu.
A mota Hilah da take tuƙi cikin rashin natsuwa ta waiwayo ta kalli Afrin ta ce,"Har yanzu gabana faɗuwa yake yi, ji na ke kamar a mafarki zamu haɗu, da mahaukacin masoyina. Ko ya ya haɗuwarmu zai kasance? Ina fatan wannan haɗuwar ya zama sanadin da zai jagoranci zamanmu a inuwa ɗaya."
"Amin," Afrin ta ce cikin zaƙuwa, domin ta ƙosa ta ganshi wanda ya sanya ta fara samun saɓani da ƙawarta.
Parking suka yi ta tsaya tare da fitowa. Ganin babu motarsa a inda suka yi za su haɗu ya sa ta jingina da motar ta ɗan bashi lokaci ƙila yana hanya.
Minti goma sha biyar bai iso ba, sai ta ɗaga waya don ta kira shi. Gabanta ya faɗi jin wayar a kashe, saboda ko da safe sun yi waya.
Datar wayarta ta kunna, tare da shiga Whatsapp don ta yi masa magana. A nan ta tsinci tsakonsa da sai da ta yi taga-taga za ta faɗi Afnan ta riƙe ta.
Hawaye shar! Suka wanke mata ƙuncinta. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta furta tare da dafe kanta da take jin juya na ibanta.
"Lafiya Hilah?"
"Don Allah ki riƙe ni kar in faɗi."
Da sauri ta kamata, ta buɗe murfin motar ta shigar da ita, ganin yadda take haƙi kamar wace ta yi gudun famfalaƙe.
"Wayyo Allahna!" Ta furta tare da rushewa da kuka.
"Lafiya, don Allah ki yi mini bayani."
"Mayaudari ne mahaukacin masoyi! Ya turo mini da tsaƙon, na manta da shi a rayuwata zai bar ƙasar."
Jikin Afrin ya yi sanyi, har ta kasa cewa komai, musamman yadda ta ga ta ruɗe matuƙa ta fita hayyacinta.
"Don Allah ki natsu, ni dama tuntuni zuciyata ba ta aminta da shi ba, saboda bai kamata ki mallaka masa zuciyarki ba tare da haɗuwa ta zahiri ba.!"
"Ya cuce ni ya sanya mini soyayyarshi ya guje ni ya zan yi?" Ta yi mata tambayar tare da kama hannunta.
Wayarta ta zaro ta danna numbar Huwais, da yake cikin taro, zuciyarsa a cinkushe tunanin halin da za ta shiga yake yi.
Ganin kiranta gabansa ya faɗi matuƙa. Ya kasa ɗaukar kiran har sai da ta yi masa yafi goma. Ganin ba za ta daina ba, ya kai hannu zai kashe sai ya ga rashin adalcin yin hakan.
"Ya Huwais, mahaukacin masoyi mayaudari ne, ya tura mini da tsaƙo na manta da shi ya bar ƙasar." Ta furta cikin tsananin kuka.
Rintse idanunsa ya yi, cikin wani yanayi yana jin babu daɗin yaudararta da ya yi, saboda shi da zaɓin da ya wuce haka.
"Ni ma na zama mahaukaciya kamarsa, tun da na aminta da soyayyarsa." Ta ƙarasa faɗin hakan cikin kuka ganin ya ƙi cewa komai.
"Ki natsu Hilah, ki bawa Afrin motar ta tuƙa ki ku da... Ko kuma ki faɗa mini inda kuka na zo."
Wayar ta miƙa wa Afrin." Ki yi masa kwatance ba zan iya ba."
Afrin ta yi masa kwatance tare da kashe wayar, tana rarrashinta da take kuka kamar ranta zai fita. Wani irin ƙaunarsa take bijiro mata ganin ta rasa shi.
Duƙawa a gurin ta yi, ta saki kuka duk irin rarrashinta da take yi ta tashi taƙi.
Huwais kuwa cikin tashin hankali ya miƙe xai fice.
"Ina za ka ga baki kana da su?"
"Ka kula da su, ina zuwa Najib." Ya furta hakan ba tare da ya amsa kiran ya juya ba.
Yana isa guri ya buɗe motar ya fito. Tana ganinsa, ta fashe da kuka tare da miƙe wa ta isa gareshi ta faɗa jikinsa.
"Ba zan yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata ya yaudare ni."
Kama hannunta ya yi suka shiga motar bayan ya bawa Afrin umurnin ta tuƙa motar ta dawo gida.
Ganin irin kukan da take yi, ya yi matuƙar daga hankalinsa matuƙa. Yana tuƙi amma shi kansa ba shi da natsuwar da zai mayar da hankalinsa ga titi.
Kukan na ƙara mishi ƙunci a zuciyarshi sosai, musamman in ya tuna shi ne sanadin zubar hawayenta.
Gangarawa ya yi ƙasan titi ya sauka, tare da paking ɗin motar ya kifa kansa a sitiyarin
"Ya Huwais, ba zan taɓa yafe masa ba, domin ya cutar da zuciyata. In har ya san ba ya ƙaunata mai xai sanya ya shigo cikin rayuwata?" Kukanta ya ƙara tsananta bayan ta furta hakan.
Jiyowa ya yi yana kallonta, yadda ta ci uban kuka, abin ka da farin mutum fuskarta har ta canza ta ƙara haske.
"Hilah," Ya kira sunanta can ƙasar murya, wanda ya sa ta ɗago kanta da sauri tana kallonsa.
Girman idanunta da suka canza kala, ya sanya ya kasa rarrashinta da ya yi ninyar yi, wanda ganin hakan ya sanya ta ci gaba da kukan har da ƙara sauti.
"Please, don Allah ki daina kuka domin zuciyata na zafi." Ya furta cikin sanyin murya.
Jin ta rage sautin kukan, ya sanya shi buɗe motar ya fito. Ta inda take zaune ya zagaya ya buɗe motar.
A gabanta ya tsuguna yayin da ya yi narai-narai da fuskarsa.
"Kina son damuwa ya sanya na mutu kuma ki ga hawayena ko?" Ya yi mata tambayar cikin wata irin murya tare da saukowar tagwayen hawaye a fuskarsa.
Hankalinta ya tashi sosai! Da sauri ta share hawayenta tana kallonsa.
"Don Allaah kar ka yi kuka na daina."
Ajiyar zuciya ya yi lokacin da ya ji muryarta na faɗin haka.
"Ina jin rayuwata wani iri Hilah. Yau ake mini auren dole, kuma ƙanwata wacce na fi ƙauna tana cikin wani yanayi. Ban san da wani irin kalamai zan rarrashe ki ba, amma na yi miki alƙawarin nemo mahaukacin masoyi duk inda ya ke, tun da na fahimci ya riga ya sace zuciyarki."
A yadda ya yi maganar, ta kasa gane ko bai ji daɗin irin yadda ta nuna tashin hankalinta ba ne, ko kuma tsananin tausayin halin da take ciki, ya sanya shi shiga cikin yanayin.
"Ka yi haƙuri ka gafarce ni, na sanya mahaukacin masoyi a raina, amma halayensa da iya kalamansa suka sanya na mallaka masa zuciyata ba tare da dogon nazari ba, kuma Yayana, duk wanda zai shiga rayuwata, ba zan taɓa ba shi matsayinka ba."
"Na fahimta yadda kike ji, da kuma yadda soyayya take tasiri a zuƙatan masoya, ba tare da tsimi ko dubara ta masoya ba. Sam ban yi miki mummunan fahimta ba, saboda ni ma ina jin kwatankwacin ɗacin da kike ji."
Miƙewa ya yi, tare da sanya hannu sa ya riƙe murfin motar, sai kuma ya saki ya kama gefen hijabinta.
"Share hawayenki ƴar ƙanwata kin manta na gaya miki matuƙar ina raye ba za ki taba yin kuka ba?"
Ɗaga masa kanta ta yi tana murmushi tare da saukowar hawaye a fuskarta.
Gefen hijabinta da ya ɗauke hawayen da suke zuba, ya ƙara sanyawa ya ɗauke mata wasu da suka ƙara zubowa.
Rufe motar ya yi, bayan ya sakar mata murmushi, ya zagaya ya koma ta bangaren mai tuƙi ya shiga.
Bayan ya tada motar sai ya tsaya yana kallonta yadda ta ƙurawa titi idanu.
"Yayana, ina sonka." Ta furta daidai lokacin da ta juyo ta kalle shi.
Rintse idanunsa ya yi tare da jin wani irin tsau a ransa.
"Ba irin wannan soyayyar na ke so ba Hilah;wace za ki zamo murfin asirina kuma farincikin rayuwata uwar ƴaƴana."
Murmushin ya mayar mata sannan ya fara jan motar.
"Ni ma ina sonki ƙanwata."
A hanya suna tafe Hilah ranta a ɓace. A ranta tana jin in har ya ƙara kiranta, sai ta yi masa rashin mutunci, duk da cewar ba halinta ba ne.
"Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har."
Labarin ya zo da wani irin salo da nishadi, karku baru a ba ku labari. Ku biyo ni domin it’s just like a little introduction part, and guess what? You will really enjoy it. Believe me, my dear readers. Your happiness is my concern. Follow me on Facebook, Whatsapp, Wattpad, Arewaboo, and Bakandamiya. Ta ku, Jamila Lawal Zango (Jamsy).
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 008144072423
*RANAR WANKA...*
NA
JAMILA LAWAL ZANGO
"JAMCY"
☀️ *First Class Writers Asso* ☀️
Hame of Qualities And Trusted writer's of The Nation
*GARGAGAƊI*
Ban yarda kuma ban amince a juya mini labari ko ta wace siga ba, sannan ban bada lamuni a ɗora mini littafi a kowane kafar sadarwa ba sai da izinina a kiyaye⚠️
JAN HANKALI
Kirkirarran labari ne ban yi shi don wani ba, idan har ya yi daidai da labarin ki/ka to arashi ne.
SADAUKARWA
Kacokam labarin daga farkonsa har karshe sadaukarwa ne ga ƙawata sahibata Aysha Na Lado. Allah saka miki da alkairi ya raya zuri'a.
PAGE 16
BISMILLAHIR RAHMANINR RAHIM
"Mai ya sa zai guje ni bayan ya yi mini alƙawarin kasancewa a tare da shi? Shi kenan ya guje ni na rasa shi har abada?" Ya zan yi da soyayyarsa da ta shige mini zuciyata. Wayyo Allah ka dawo mini da shi a cikin rayuwata, domin shi ne irin mijin da nake masifar so." Haka ta rinƙa addu'a har ta fara jin sauki a cikin zuciyarta.
A maimakon ya kai ta gida, sai ta ga ya ɗauke hanya. Gurin shaƙatawa ya kai ta mai kyau, ya kashe motar ya fito tare da zagayowa inda take.
Hannu ya miƙa mata bayan ya buɗe motar.
"Ya Huwais, mai za mu yi nan, kar ka manta yau ne fa auren ka? Mutane na can na jiranka."
"Karki damu, farincikin ƙanwata kawai na ke so." Ya ce mata tare da kama hannunta da ta miƙa masa.
Cikin gurin suka isa, wanda wurin ya yi kyau matuƙar haduwa iya gaya! Hilah ta sha zuwa gurin, domin yana ɗaya daga cikin guraren shaƙatawa da take so, kuma ya ke yawan kawo su.
Siyayya ya fara yi mata har sai da ta riƙe masa hannu.
"Don Allah ka bar kashe kuɗinka Yayana, hidima ce a kanka. Ko ka manta yanzu kai mai iyali? Ba zan so Anty Wajnah ta sha wahala a gidan ɗan'uwana ba." Ta faɗa cikin sanyin murya tare da riƙe hannunsa.
Harararta ya yi, sai kuma ya ƙwace hannun ya ɗauki ƙaton biskit, wanda yasha cakulate ya saka a kwandon.
"Kar ki damu farincikin ƙanwata kawai na ke so. Sam ban damu da kuɗina su ƙare ba, matuƙar hakan zai sanya ki farinciki."
Murmushi ta yi tare da jan hannunsa suka fara tafiya.
"Haƙiƙa ka zamo ɗan'uwa mai kau da damuwar ƙanwansa. Fatana na samu miji mai irin kyawawan halinka da nagarta, wanda hakan yana da nasa ba da fara soyayyata da mahaukacin masoyi, saboda yana da kyawawaan ɗabi'u irin naka."
Ba tare da ya ce mata komai ba, ya fara tafiya, saboda in har bai bar gurin ba, zuciyarsa za ta iya fallasa abin da ke cikin zuciyarsa, saboda yabansa da ta yi.
Ganin haka ta fara tafiya da sauri har ta kamo shi.
Daga gurin da ake sayar da kayan maƙulashe gurin shaƙatawa ya kai ta.
Tana son ta yi masa maganar su koma gida, amma in ta buɗe bakinta sai ya tsareta da idanunsa, masu kama da an zuba zaiba sai ta kasa cewa komai.
Ganin an ɗauki lokaci suna gurin, kuma ga Najib sai kiran sa a waya yake yi, wanda daga ƙarshe ya kashe wayar ya yi gabakiɗaya.
Wayar Hilah ce ta yi ƙara alamun ana kira. Da sauri ta duba mai kiran. Kamar yadda ta ayyana Ummu ce. Ilai kuwa ita ce.
Da sauri ta kanga wayar a kunnenta."Kina ina tun rana ban ganki ba, kacaniyar biki ya ɗauke mini hankali, ban lura ba ki cikin gidan ba, sai yanzu da na zo ɗakinki?"
"Na raka ƙawayena ne Ummu." Ta shirga mata ƙaryar hakan, tana kallonsa da hankalinsa ya ɗauku gurin tuƙi kuma yana sauraren mai za ta ce.
"Ok, to ki yi sauri ki zo ina nemanki."
"To Ummu." Ta faɗa tare da ije wayar.
Waiwawo ta ya yi yana kallonta, daidai lokacin da take share sauran hawayen da yake maƙale a fuskarta.
"Ya kamata ki wanke fuskarki in da hali ki yi make up kar Ummu ta gane halin da ki ke ciki."
Babu musu ta buɗe jakarta, ta ɗauko kayan kwalliyar wanda ganin haka ya yi parkin tare da kashe motar.
Fita ta yi zuwa waje ta wanke fuskarta ta fito
A ƙofar gida ya ije motarsa ta shiga ciki shi kuma ya yi bangarensa.
Najib da yake zaune cikin tsananin ɓacin rai, da waya a hannunsa. Layinsa yake ta gwadawa amma a kashe.
"Ba ka da hankali ko Huwais? Shin ka san abin da ka aikata yau kuwa? Wannan wulaƙancin da ka yi mana, ko ni kaɗai ka yi wa da na san halin da kake ciki ba zan ji daɗi ba." Najib ke magana cikin tsananin ɓacin rai yana kallonsa da ya buɗe ƙofa ya shigo.
Shiru ya yi masa, ba tare da ya ce komai ba, ya ƙarasa kan kujera ya zauna jaɓar tare da sakin ajiyar zuciya ya dafe kansa.
"Ina magana ka yi shiru? Wallahi ji na ke kamar na rufe ka da duka, saboda takaicin abin da ka aikata. Just see the time, this isn't good."
Jajayen idanunsa ya watsa masa, tare da miƙewa bai ce masa komai ba zai wuce.
"Sam bana jin daɗin abin da kake mini da halin da ka sanya kanka. Ya kamata ka farka da ga mafarkin da kake yi. Toxarcin da kake yi wa yarinyar nan ya isa haka. Ta bani tausayi da ta kira ni tana kuka. Don Allah ka tausaya mata ka amshe ta a matsayin mata, domin aurenku an riga an ɗaura yanzu tana da haƙƙi mai girma a kanka."
'"Please, I need my space." Ya ce tare da yin hanyar ɗakinsa yana tangaɗi kamar wanda ya sha giya.
Najib takaici da ya ibe shi gabansa ya sha.
"I will inform Ummu, Huwais. Bana son ka kai ni iya wuya, domin zan sanar mata da duk abin da ke faruwa. Haka kawai ka sanya wa kanka damuwa da Hilah, don Allah kaɗai ya san halin da take ciki.".
"Then go ahead." Ya ba shi amsa tare da kaucewa, zai shige ɗakin duk da cewa ya ji tsoron abin da ya faɗi.
Tsaki ya yi, tare da kaucewa ya ba shi hanya ya shige ɗakin ya rufo ƙofar garam
Sharaf! Ya faɗa gado yana mai da numfashi, yayin da cikin zuciyarsa Allah kawai ya san halin da yake ciki.
"Ya kamata ka miƙe ka shirya ka san dinner ɗin nan ya kamata a fara da wuri."
Tsaki ya yi tare da janyo wayarsa yana kiran numbar Hilah ba tare da ya tanka masa ba.
"Hello, ƙanwata." Ya furta cikin sanyin murya.
"Na'am Yayana," Ta bashi amsa tare da saukar da zafafen hawaye a ƙuncinta.
"Har yanzu kuka kike yi ko?" Ya yi mata tambayar kamar yana ganin hawayen.
"A'a, kawai ina jin zuciyata kamar za ta fashe in har na tuna da cutar da zuciyata da ya yi."
"Ba na yi miki alƙawarin nemo miki shi ba, ko kina tunanin ba zan iya share miki hawayenki ba?"
"Ina jin babu daɗi ne, amma na san kai Yaya ne da ya cike ko wane gurbi."
"To shikenan, ki daina kuka ki ci abinci ki kwanta."
"To, amma sai dai bana jin zan iya cin komai. Yaya Huwais, yau rana ce mafi daraja. Ranar da kake yin aure ya kamata ace na fi kowa farinciki, amma sai na tsinci kaina akasin haka. Ina maka murnan samun abokiyar rayuwa, Allah ya ba ku...."
"Ina fatan Ummu, ba ta yi miki faɗa ba?" Ya katse ta yana faɗin haka don ba ya son maganar.
"Eh, saboda yau tana cikin farinciki matuƙa, saboda kallonta ka yi kawai za ka tabbatar da hakan."
"To ki ci abinci kisha magani ki kwanta, ko na zo na baki? Na san ba kya son magani."
Dariya ta yi." Kai haba! Gidan a cike yake Yaya, zan sha da kaina."
"Ok, to ki kular mini da kanki. Ni ma wanka zan yi na samu na kwanta."
"Yaya, dinner ɗin fa..."
Katse wayar ya yi jin tambayar da za ta yi masa.
"Wallahi inda uban kuturu ya yi kaɗan kenan." Cewar Najib cikin tsananin ɓacin rai.
"Tun da aka fara shirye-shiryen bikin ka ban huta ba Huwais! Wannan ko ni zan ƙara aure iyakan wahalar da zan yi kenan. In ba ka tausaya mini ba, ka tausaya wa matata da ke fama da laulayi. Ƴan matan amaryar kamar za su yaga ni, suna tambayata inda na ɓoye ango. Yanzu kuma sai ka ce ba za ka je dinner ba?"
Jin ya yi shiru yana kallon wayarsa wanda ya tabbatar hoton Hilah yake kallo, ya sanya shi fara duba contacts a wayarsa yana ƙoƙarin nemo numbar Ummu.
"Ba zan ɗora wa kaina wahala ba. Kai da aure ni da shiga damuwa. Ummu zan kira na sanar mata da wulaƙancin da kake yi a wataƙila ta sanya ka kaje."
"Bana son wulaƙanci Ummun za ka kaiwa ƙarata?"
"To ya kake son na yi Huwais? Kai ma ka san iya rufa maka asiri ai na yi."
"Bana jin zan iya halatar dinner ɗin. Xuciyata xafi take yi na yaudararta da na yi. Halin da ta shiga yau na ji babu daɗi da tsanar kaina."
"I