AMALEEKH by Asmeetah writer

Author :  Category :  Love

Chapter   31 / 82

90K to 93K   out of 244.2K words

ta ji wani irin nishaɗi, zuciyarta cike da farin ciki, yayin da Maleekh ya rungume ta kaɗan, suna dariya tare. A cikin driving academy, sauran instructors da students sun jinjina mata saboda yadda ta koyi driving a cikin sati guda, kuma award ɗin ya ƙara mata kwarin gwiwa sosai...

Daga wannan rana, Amal ta zama cikakkiyar mai iya tuƙi ba tare da jin tsoro ko shakka ba, kuma soyayyar Maleekh da ita na karfi, suna cikin nishaɗi da jin daɗi, suna shirya tarurruka na driving sessions..


Bayan Amal ta samu cikakken kwarin gwiwa a Skyline Driving Academy, Maleekh ya yanke shawarar yau ita za ta tuƙa motarsu. Sun fita daga gidan da safe, rana tana haskakawa cikin annashuwa. Maleekh ya miƙe hannunsa a kan seat na passenger, yana kallon Amal da idanuwan cike da alfahari ya ce:

"Amal, yau ke za ki tuƙa mu, ba zan shiga driving ba. Ina son ganin yadda kika koya, zamu zagaya cikin gari har wajen gari shiyasa na fito da safe..."

Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, ta sa hannu a kan gear, ta kunna motar, sannan ta fara ja a hankali. Motar ta motsa cikin santsi, Maleekh yana kallonta yana murmushi:

"Wow… ki kalli wannan smooth driving! Ina alfahari da ke sosai."

Amal ta juya kanta kaɗan, tana dariya ta ce:

"To fa, Yaya Maleekh, yanzu ka tsaya a gefena kana son ganin kwarewa ta kenam."

Duk dariya suka yi tare da jan mota suka tafi a slow...

Sun fara zagaye Lugbe Road, suna hawa zuwa Jabi Lake Mall da Central Business District na Abuja. Amal tana tuƙi cikin hankali, tana canza gears ba tare da wata tsoro ba. Maleekh yana ta dariya, yana tsokanar ta:

"Ba zan taɓa mantawa da ranar da kika fara koyon driving ba… yanzu ga ki, kamar gogaggen driver..!"

Amal ta yi dariya tare da tsokanar shi da cewa:

"Eh! Kada kayi tunanin zan zauna haka kana driving ɗina. Domin na fi ka ƙwarewa yanzu."

Maleekh ya yi dariya, ya riƙe hannun ta kaɗan:

"Eh… wannan gaskiya ne. Ina ganin zan bari ki zama official driver ɗina."

Suka wuce Millennium Park... motarsu tana tafiya a hankali, suna jin iska mai sanyaya jiki. Amal ta yi parking na ɗan lokaci a gefen titi, suka fito daga motar, suna kallon shimfidar birnin Abuja daga saman titi, Maleekh yana kallon Amal cike da soyayya ya ce

"Amal, kina da kyau sosai a kowace rana, amma a yau, ganin ki kina tuƙi, na ga kin samu cikakken iko da komai… Ina matuƙar son ki."

Amal ta yi murmushi tana riƙe da hannun shi ta ce:

"Yau na ga soyayya cikin motsin mota da nishaɗin birni, Yaya Maleekh."..

Bayan sun gama hutawa..
Suka koma cikin motar, Amal ta ci gaba da driving zuwa Wuse Market da Garki, suna yawon shakatawa, suna hira da dariya a kan titi. Maleekh yana ta godewa Amal a zuciyarsa, yana ganin yadda ta koyi motar da kyau, yana jin ƙaunar ta ta ƙaru da kowace rana.

Daga karshe, suka dawo gida bayan zagaye birni, Maleekh yana jinjina kai cikin alfahari ya ce

"Na san yau kina jin daɗin driving sosai, kuma na ga kin cancanci duk girmamawa da kyaututtuka. Ina matuƙar alfahari da ke."

Amal ta yi murmushi mai cike da jin daɗi, zuciyarta na cike da farin ciki, tana jin cewa soyayya da Maleekh ta girma sosai yayin da suke cikin nishaɗi a kan titi.

Cikin begen juna suka yi sallama Maleekh ya koma gida, yanzu burinsa ya cika Amal ta iya mota yanzu sauran fara aiki a kamfaninsa....


_Bayan Sati, ranar Monday_ ..

Amal Starts Work at CashTalk

Yau da safe Amal ta fito daga gidan ta cikin sabuwar motarta, jeep mai kyau, wacce Maleekh ya bata, tana tuƙi kamar gogaggen driver. Hasken safe na yi mata kyalli, kowa a unguwar yana kallonta kamar tauraruwa. Yanzu itama ta shigo sahun masu kuɗi, dake unguwar da take duk masu kuɗi ne..

Tana zuwa CashTalk FM, gate security suka hango motarta. Sai da suka buɗe gate tare da gaishe ta cikin ladabi:

"Good morning, Madam Amal," ɗaya daga cikin masu tsaro yace, idanuwansu na cike da mamaki.

Duk ma’aikatan da suka hango Amal, sun tsaya cike da mamaki. Yarinyar da suka daɗe suna ganin a matsayin talaka matsiyaciya yanzu ta bayyana cikin ƙyakkyawan tsari da ƙwarewa:

Black glass yana rufe akan golden eyes ɗinta, yana ƙara mata sirri da kwarjini.

Tana sanye da Abaya mai milk color da stones a gaba, gyalen rigar ya ɗan yi masa highlights, yana bayyana kyan ta...

Handbag ɗinta da wayarta a hannunta guda.

Takalmanta mai tsini yana ƙara mata kwarjini a kowace mataki.


Kowanne ma’aikaci yana kallonta, zuciyoyinsu cike da sha’awa da mamaki. Mata da maza, duka suna mamakin wannan canji: daga ƙaramar matsiyaciya zuwa mataimakiyar babban attajiri.

Maleekh kuwa daga ofishinsa dake saman building stairs yana tsaye a glass office da ke zagaye da windows, yana kallonta yayin da yake shan coffee daga glass cup ɗinsa:

"Ahh… wannan ita ce nawa… babu shakka, ta cancanci duk wani yabo," ya ce cikin ransa, yana murmushi.

Amal tana motsi a hankali cikin compound ɗin kamfanin, tana lura da kowace matsala da takalmanta mai tudu zai iya janyo... tunani ta fara yi shin wata hanya zata bi don haura wa sama yanda Offince ɗin Maleekh yake... Tunani tayi gwara kawai ta shiga elevator ya kaita har sama ba tare da ta sha wahala ba..
Wani ma'aikacin saurayi ne ya nuna mata hanyar elevator, domin ta kauce wa stairs ɗin da zai kawo mata cikass da takalminta...

Tana shiga elevator, ta tsaya cikin kwarjini, zuciyarta cike da farin ciki da ɗan tsoro. Ta san wannan rana zata fara aiki a CashTalk, a matsayin mataimakiyar Maleekh, wanda hakan zai ƙara mata ƙwarewa da girmamawa a gaba...

Maleekh ya dan yi murmushi, zuciyarsa cike da alfahari yake faɗin

"Yau za ta fara aikinta… ina fatan zata ba da kyakkyawan hoto ga kamfanin."

Elevator ya tsaya a floor na 18 na ƙarshe ƙarshe... Amal ta fito cikin nutsuwa, tana shirya handbag ɗinta, tana duba ma’aikata da murmushi. Duk wanda ya hango wannan sabon fuskarta, sai zuciyarsa ta narke, domin Amal ba karamar kyakkyawa bace ta asali..

"Good morning, everyone," Amal ta ce cikin ladabi da nutsuwa, kowa ya miƙe ya amsa gaisuwa, suna kallonta cike da mamaki da yabon kwarjinta...

Kai tsaye Office ɗin Maleekh ta nufa, tana zuwa tayi knocking, daga ciki ya ce: "come in."

Ta shiga da Murmushin ta, bayan sun gaisa ta zauna akan kujerar dake facing ɗinsa..

Maleekh ya ɗan ɗaga kofi ɗinsa yana zuƙar juice, yana murmushi ya ce:

"Amal… I knew you would shine today," ya faɗi a ransa, cike da jin daɗin ganin yadda yarinyarsa ta girma cikin kwarjini...

A wannan lokacin yasa aka ƙira masa duk ma'aikacin dake aiki a wannan kamfani, za'a gudanar da meeting a office ɗin taro na musamman..

First Official Meeting at CashTalk FM

Kowa ya hallaru a babban ofishin CashTalk FM, babban ɗakin taro wanda yake na zamani, da dogon table a tsakiyar room, gefen table an jera kujeru masu yawa ga ma’aikata. Hawa hawan bene na wannan kamfani sun kai goma sha takwas, kuma babu wanda zai iya zuwa floor na sama sai da elevator ko escalator. Gida ne na kamfani mai girma a Abuja, wanda babu wanda bai san shi ba.

Maleekh ya tsaya a ƙarshen dogon table, kujerarsa tafi ta kowa girma, yana fuskantar dukkan ma’aikata da suka zauna a jerin kujeru a gefen table, ciki har da Amal. Ofishin yana cike da haske, tare da kyawawan kayan ofis da technology na zamani.

Maleekh ya ɗaga hannu, dukkan ma’aikata suka nutsu, suna sauraren shugaban su.

Maleekh ya fara magana:

"Good morning everyone, I hope you all had a productive week. Today, we are here not only to discuss our weekly operations but also to welcome a new member to our team."

Duk tafi suka fara yi..

Daga nan sai ya juya fuska zuwa ga Amal ya furta:

"Amal Abdulsamaad will be joining us as my Assistant. I trust she will bring fresh energy and perspective to CashTalk."..

Nan ma aka kaure da tafi..

Amal ta miƙe, tana murmushi, tana gaisawa da dukkan ma’aikata, ta ce:

"Good morning everyone. I’m very honored to be here. My name is Amal Abdulsamaad. Many of you may know me from my work as a journalist across different states, but today, I’m here to serve as Assistant to the CEO, Maleekh Abdul-Majeed, and I hope to contribute positively to the success of this company."

Duk ma’aikata suka fara tashi tsaye suna gabatar da kansu, suna nuna ladabi da professional attitude:

"I’m Ahmed, Head of Marketing."

"I’m Fatima, Finance Department."

"I’m Chike, IT Coordinator."

PA ɗinsa shima yana daga ciki ya miƙe tare da gabatar da kansa da cewa:

"I'm Ibrahim, The Manager."

Bayan kowa ya gabatar da kansa, Maleekh ya ɗaga hannu tare da faɗin:

"Thank you all. I’m proud of the team we’ve built here. CashTalk is not just a company; it’s a family. Every week we achieve milestones, but we also face challenges. Our goal is to continue expanding, innovate in broadcasting, and maintain our position as the leading media company in Abuja."

Ya ɗan ɗauki lokaci yana kallon dukkan ma’aikata, sannan ya ƙara:

"I encourage open communication, professionalism, and teamwork. Amal will be assisting me directly, so I expect everyone to support her as she transitions into this role."

Amal ta zauna bayan wannan jawabi, tana jin ɗan tsoro amma kuma cikin fargaba da excitement saboda wannan shine babban mataki a rayuwarta.

Duk wanda ya kalli Maleekh da Amal a wannan babban ofishin, ya gane cewa abu mai girma zai faru a CashTalk FM, kuma kowa yana ɗokin ganin irin canjin da Amal za ta kawo.

Meeting ɗin ya cigaba da tattaunawa akan projects, schedules, da objectives na kamfanin, dukkan ma’aikata suna nuna professional attitude, suna sha’awar sabuwar mataimakiya ta Maleekh.

Amal ta tsaya a bakin office ɗin Maleekh, tana kallon babban room ɗin, dukkan na’urorin zamani suna nan, computers, monitors, da smart boards. Ta ɗauki ajanda da pen a hannu, tana jin ɗan tsoro amma a lokaci guda cikin excitement.

Maleekh ya ce:

"Alright, Amal, yau zaki fara da tasks ɗin yau da safe. Zan nuna miki workflow ɗin kamfani, sannan zamu duba schedules, emails, da projects ɗin da muke yi."

Amal ta yi murmushi:
"Yes, Sir. I’m ready."

Maleekh ya ɗauki tablet ɗinsa ya fara nuna mata:

"CashTalk FM is structured in departments. Marketing, Finance, HR, IT, and Content Production. I expect you to assist me directly, manage appointments, and also liaise with department heads when needed."

Amal ta rubuta kowanne word a ajandanta.

Daga nan suka fara zagaye office, suna zuwa departments ɗin daban-daban:

Marketing: Amal ta gaisa da Ahmed, ya nuna mata ongoing campaigns.

Finance: Fatima ta yi mata briefing akan budget reports.

IT: Chike ya nuna mata dashboard na live broadcast da recordings.

Manager: Ibrahim ya gaisa da Amal, sannan ya bayyana mata aikinsa:

Yace shi ne ke da alhakin tsara ayyukan sassan daban-daban da tabbatar da cewa kowanne yana aiki bisa manufa.

Ya nuna mata yadda yake tracking progress ta weekly reports daga kowane department.

Ya kuma gaya mata cewa duk lokacin da akwai matsala ko shawarwari, shi ne first point of contact kafin su kai wa CEO. Amma tinda ta bayyana a matsayin assistant of CEO yanzu ita za'ana sanar wa komai kafin ta kai wa CEO..

Daga ƙarshe ya nuna mata wani project board da yake amfani da shi wajen saka deadlines da monitoring...


Maleekh ya kalle ta cike da murmushi ya ɗora da cewa:

Assistant COE tana taimaka wa shugaban kai tsaye. Ita ce hannun damarsa wajen kula da abubuwa na yau da kullum, tana sauƙe masa nauyi da yin follow-up akan departments.

Manager kuma suya kula da departments (Marketing, Finance, IT, HR, da sauransu)...

Maleekh ya cigaba da sanar mata cewa:

Tana karɓar rahotanni daga Managers, ta tace su kafin su je wurin COE.

Tana iya jagorantar meeting idan COE baya nan.

Tana taimaka wajen tsara strategies da implementation, musamman idan COE ya fi kula da babban vision.

Ita ke sa ido akan discipline da compliance kafin rahoto ya kai ga babban boss.

Wato Manager → ya kula da department.
Assistant CEO → ta haɗa rahotanni daga Managers, ta tace, ta duba, sannan ta kai wa COE.
COE → ya yanke manyan hukunci da policies...

⚖️ Idan babu Assistant CEO, to duk Managers za su rinƙa damun CEO da ƙananan bayanai, hakan zai cika mun kai da workload.....

Maleekh yana lura da Amal, yanda take ta zabga murmushi, cikin dariya ya ce:

"You’re catching up fast, Amal. I knew you’d be able to handle this."

Amal ta yi murmushi sannan ta ce

"Thank you, Sir. I’ll do my best."

Bayan zagaye, suka koma office tare da hutawa a babban office na Maleekh, inda Amal zata fara handling emails, scheduling meetings, da drafting reports.

Yayin da take aiki, wasu ma’aikata suka zo suna tambayar ta:

"Amal, how are you finding your first day?"

Amal ta ce:
"It’s exciting! Everyone is so professional, and I feel welcomed."

Maleekh yana kallonta, yana murmushi ya ce

"Good. That’s exactly what I like to see. Confidence, poise, and professionalism."

Daga bisani, Maleekh ya ce:

"Amal, today is just an introduction. By tomorrow, I want you to handle your first mini project, liaise with HR, and prepare a short report for me."

Amal ta amsa da kwarin gwiwa:
"I’ll make sure it’s done, Sir."

Cikin wannan first day, Amal ta fara samun gaskiyar ƙwarewa akan aiki, tana ganin yadda take iya organizing schedules, communicating da manyan ma’aikata, da handling tasks efficiently.

Maleekh yana kallonta daga ɗaya gefe na office, yana jin alfahari da yadda take sarrafa aiki, sannan yana shirin ganin yadda zata ƙara bunkasa a CashTalk FM.

Meeting ɗin farko da Amal ta jagoranta (kodayake ƙaramin program ne) ya nuna cewa kowa ya fara yaba mata da kwarewarta, har ma da ma’aikatan da suka fara kallonta da mamaki.

By the end of the day, Amal ta gama dukkan tasks nata da kyau, Maleekh ya yi mata brief:

"Well done, Amal. I’m impressed. Keep this momentum, and soon you’ll be fully managing executive tasks on your own."

Amal ta yi murmushi, tana jin confidence da excitement: wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM.


An tashi daga aiki ƙarfe 6 na yamma, tun safe karfe 7 ake fara aiki. Amal ta ɗauki jakanta ta fita daga CashTalk FM cikin nishaɗi, tana jan motarta zuwa gida, zuciyarta cike da farin ciki da excitement; tana tunanin yadda ma’aikatan suka karɓe ta hannu bibbiyu, kuma yadda Maleekh yake lura da ita a office.

Da ta isa gida, ta tarar da Inna a falo tana shan tea. Amal ta sauri ta rungumi Inna tana faɗin

"Inna! Today was amazing! Kowa a office ya yaba da ni, da aiki na, har Maleekh ya nuna jin daɗinsa sosai."

Inna ta yi rawar hannu, ta girgiza jikinta, sannan ta ce cikin farin ciki:

"Allah! Ashe ya tabbata aikin, ya kamata kiyi farin ciki, yarinya ta. Ina ta tunanin yanda zaki je wurin aikin nan ki burge su duka."

Amal ta yi dariya tare da faɗin:

"Yes Inna! Duk suna kallona da mamaki, sun yaba min sosai. Amma Maleekh… Inna, Maleekh yana kallona ne har a office da yanda nake gudanar da aiki, yana lura da ni sosai."

Inna ta rungume ta da dariya:

"Ai yarinya, ki more wannan lokacin, ki nuna kwarewa sosai."


Maleekh ma ya koma gida cikin annashuwa da farin ciki...
Abu ɗaya ne yake ɗaga masa hankali da zaran ya koma gida shine..
Kullum batun mahaifiyarsa Ammy akan Auren Farha ne, damuwarta Maleekh ya amince da Auren Farha in yana son farin cikinta..
Shi kuwa ya dage akan baya sonta, baya kaunarta....ƙalubalen dake damunsa kenam..

Bayan ya koma gida, ya wuce part ɗinsa..zama yayi
yana kallon wayarsa, yana rubuta wasu notes game da projects na Amal da CashTalk, amma a zuciyarsa har yanzu akwai damuwa akan Farha da mahaifiyarsa...

Maleekh ya ɗaga kai ya yi murmushi sannan ya furta

"Amal… yanzu ke ce zaki cike min office da farin ciki. Kullum ina son ganin irin wannan ƙwarewa a tattare da ke."

A gefe guda, Amal tana gida tana ta shaƙe da labaran aikin nata, tana jin confidence da motivation, wannan shine farkon babban tafiyarta a CashTalk FM, kuma ranar Monday ya kasance mai cike da nishaɗi da farin ciki ga dukkan su biyu.

🌹🌹🌹

Ammy ce ta fara knocking a ƙofar Maleekh jin dawowarsa..
Ba jumawa yazo ya buɗe mata, ta shigo tana yatsine ta zauna cikin izzah sannan tace da Maleekh shima ya zauna..
Ya zauna yana fuskantar Ammy yasan batun ta baya wuce akan Farha...

Ammy ta ce cikin tsanani..

"Ya batun maganar mu akan auren?.."

Maleekh ya ce
"Auren wa Ammy?.."

"Ammy ta ce
"Kar ka raina mun wayo mana, ka manta maganar mu akan Farha ne?.."

Maleekh ya ce "Na riga da na sanar mik, kullum batun ki ɗaya kuma nima amsar da nake baki ɗaya ne Ammy, bana sonta taya zan aure ta?.."

Ammy tana harararsa ta ce

"Maleekh! Ka saurara da kyau. Ka fahimci cewa dole ne ka auri Farha, idan har kana son ganin farin cikina. Bazan zauna lafiya ba har sai ka yarda da wannan!"

Maleekh ya ɗaga kai, fuskar sa tana nuna ƙwarin guiwa da natsuwa, cikin murya mai ƙarfi ya ce:

"Ammy… na fahimci damuwarki, kuma ina son farin cikinki sosai. Amma ki saurara da kyau: bazan taɓa auran Farha ba, ko mata sun ƙare a duniya. Ko zata mutu… ba zan yi hakan ba."

Ammy ta wurga masa wani kallo ta taja numfashi mai ƙarfi, tana ƙoƙarin ɗaukar hankali daga fushin da take ciki ta ce

"Maleekh! Kai kasan me kike yi ne kuwa? Kai ba yaro bane, amma kana wasa da rayuwata! Ni ina son ganin Farha a gidanka. Kuma dole sai ka aure ta!"

Maleekh ya yi murmushi mai sanyi, ya matsa kusa da ita, amma bai bari ya nuna fushi ba ya ce:

"Ammy… Ina sonki. Amma ba zan auri matar da ba na ƙauna ba.… Farha bata da wani wuri a rayuwata. Ki fahimta cewa ni ba mutum ne mai yin wasa da soyayya ba."

Ammy ta ɗaga kai tana ƙoƙarin faɗar wani abu..kafin ta furta Maleekh ya ɗaga hannunsa da sauri ya toshe mata baki yana girgiza kai, cikin raunin murya kamar zaiyi kuka ya ce

"Ki yi haƙuri, mahaifiyata… Wannan shine gaskiya, kuma ba zan taɓa boye miki ba. Ina sonki, amma na san inda zuciyata take."

Ammy ta yi shiru, idonta cike da hawaye, amma zuciyarta ta fahimci cewa Maleekh yana da nufinsa. Duk da haka, fushinta da damuwa basu sauƙa ba gaba ɗaya.


Ammy kiyi haƙuri da abin da zance..

"Ni yanzu zan huta. Amma ki

31 / 82