HASKEN RUHI BOOK 1 BY Asmeetah writer

Author :  Asmeetah writer Category :  Horror

Chapter   7 / 45

18K to 21K   out of 133.7K words

Nasreen riƙo hannun Aasmeen tayi tana ƙoƙarin rarrashin ta...

Madam Nablah ce ta kalli yanda Abeesh yake sannan ta ce "sai kuma Nasreen da Abeesh..."

Nasreen da Abeesh duk ɗago kansu suka yi suna kallon juna daga bisani suka mayar da kallon su kan Madam Nablah,
ta cigaba da cewa "na daɗe da tsara hakan a raina cewa Abeesh da Nasreen zasu zamo ma'aurata, don haka ya kamata ku ƙara fahimtar juna, na riga da na yanke hukunci na, hukunci na kuma shine dai dai, Nasreen da Abeesh ku fara tsara rayuwar ku kafin lokacin bikin ku..."

Daga nan Madam Nablah ta miƙe tsaye tana faɗin,
"Ke kuma Tasleem zan ji dake daga baya..."

"Aasmeen idan kun kammala fahimtar juna ke da Shaprees ki kaishi order part na musamman yanda zai zauna sannan daga yau ke zaki na masa gyaran room ki kai masa abinci part ɗinsa, gyaran gado da wanke toilet room duk ke ce, kar ki kuskura naga kin yi masa ba dai dai ba, sannan bana son ganin house worker a part ɗin Shaprees domin shi ɗin naki ne, babu macen da ta fi cancanta taje part ɗinsa in ba ke ba,
Wannan shi ake ƙira da training kafin Aure..."

Kema Nasreen daga yau ke za ki na gyara part ɗin Abeesh ba ƴar aiki ba, idan naga ba kiyi abinda nace ba haƙiƙa zaki ga ɓacin raina, kina ji ba..."

Nasreen gaba ɗaya ta ɗauke wuta domin bata taɓa tunanin zata Auri Abeesh ba, bata taɓa jin soyayyar sa ta Aure a cikin zuciyar sa ba, sai kuma tunanin Ayub ya faɗo mata a rai...

A tsawace Madam Nablah ta ce "kina jin abinda nake cewa ko Nasreen?..."

A firgice Nasreen ta amsa mata..

Madam Nablah bata tsaya ta ji daga bakin Abeesh ba kawai tayi tafiyar ta, kai tsaye upstairs yanda room ɗin ta yake ta nufa...

Abeesh kallon ta kawai yake gaba ɗaya ya rasa abin cewa, yanda kasan an sa masa kwaɗo ya gagara yin magana,. Shima a fizge ya miƙe gudu-gudu sauri'sauri ya bar falon, domin haɗa shi da Nasreen da akayi ba ƙaramin nauyin ta yake ji ba, har kunyar haɗa ido yake da ita samm bai so wannan haɗin ba.....

Tasleem ganin irin rainawa ƴan uwanta wayo da akayi ne yasa ta tashi cikin takaici ta haura saman upstairs zata shige room ɗin su,
Nasreen tana kuka itama haka ta tashi ta haura upstairs room ɗin su...

Aasmeen itama kuka take da sauri ta miƙe tare da shirin barin falon Shapris ya dakatar da ita yana faɗin "Amaryata shin baza ki kaini wurin mazaunina bane?..."

Asmeen tsayawa tayi idonta akansa yanda suka yi jawur domin haɗin yazo mata a bazata, tsoro da fargaba duk ya ratsa ta bugu da ƙari bata san shi ba, bata taɓa ganinsa ba lokaci guda ace an bayar ta a shi, abun yana ƙona mata rai......



NEXT NEXT NEXT

New Book 2025.



*💋HASKEN RUHI💋*
(Spiritual Light)

A Fictional Story✍️

Writing and Organizing
Asma'u Muhammad Auwal

Which is best known as
*Asmeetah writer*

*WhatsApp 09065443871*

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


EP 9 to 10


Shapris miƙe wa ya yi tare da tako wa har yanda Asmeen take a tsaye, a gaban ta ya tsaya yana ƙare fuskar ta da kallo a yayin da ita kuma take kallon ƙasi ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya ɗago da haɓarta a hankali ta sauƙe kyakkyawan idanuwanta akan fuskar sa tana bin sa da kallo daga bisani ta kawar da kanta gefe tare da faɗin "mu je na kai ka part ɗin ka...."

Sauƙe numfashi ya yi tare da bin bayan ta suka bar falon, sai dai suka fita can compound na gidan kafin suka hau wani beni mai hawa uku acan aka tanadar masa da tsararren part site ɗin sa,
Su na shiga falon suka tarar an tsara komai, komai da komai na rayuwar duniya an zuba a falon, ba abinda zai nema ya rasa, falon kaɗai ma abun kallo ne,

Murya ciki-ciki Asmeen ta furta "inaso zan koma part ɗin mu..."

Murmushi Shaprees ya sau tare da faɗin "baza ki rakani ciki ba ne?..."

A ruɗe ta furta "ciki kuma?..."

Ya ce "eh! ko baza ki iya ba? sai na ƙira Mommyn ku a waya tazo ta shigar dani ciki..."

Aasmeen kamar zata yi kuka ta ce "Shikenam! four bedrooms ne a site ɗin nan, ka zaɓi a wannan kake son zama?..."

Sai da ya baza eyes sannan ya ce "aina bedrooms ɗin suke?..."

Idonta na kallon gefe ta furta "duk su na upstairs, 2 su na hawa na biyu, 2 a hawa na uku..."

Goya hannayensa ya yi akan ƙirji yana hura iskar bakin sa da alamun akwai abinda yake tsarawa a cikin ransa,
Ya ce "Ok mu je hawa na ukun, domin bana son zama a farko-farko, kinsan mijin ki matsoraci ne..."

Su na cikin wannan halin sai ga wasu security su biyu sun shigo da kayayyakin sa, daga nan ya sallame su, gyaran murya ya yi sannan ya ce "my Bride zaki iya taya ni ɗaukan jakakkunan nan?..."

Ba tare da ta furta komai ba tasa hannu ta ɗauki kaya biyu tabar masa sauran biyun ta haura saman upstairs,
Shima murmushi ya yi ya ɗauki sauran ya bi bayan ta....

Sai da suka hau saman upstairs ta uku sannan suka buɗe room ta ƙarshe suka shige, ga wantalelen gado da kujeru ata gefe guda har da plasman da ƙaramin frig, ta wani site guda dake cikin bedroom wardrobe ne da mirror and drowers, da kuma bathroom, su na shiga ta ajiye masa kayayyakin sa tayi saurin juyawa zata fice yayi saurin dakatar da ita, ba tare da ta juyo ba ta ce "na gama maka komai ai yanzu..."

Goya hannayen sa ya yi akan ƙirji tare da murtuƙe fuska kamar bai taɓa yin murmushi ba, zuciyar sa kawai take haurowa da zaran ya tuno da matar sa Sophia,
Cikin ɗaga murya ya furta "Keee!..."

Cike da mamaki Asmeen taji wannan kalma ya daki dodon kunnen ta, a firgice ta juyo tana kallon sa ganin ko shine domin taga yanayin sa kamar bazai iya cutar da mace ba...

Ya cigaba da cewa "Ke mallaki nane a yanzu, inada ikon da zan sa kiyi mun duk abinda nake so, saboda haka ki cire wannan jiji da kai naki ki fuskance ni da idon girmama wa...."

Asmeen lumshe idanuwanta tayi sai ga zafafan hawaye sun gangaro mata, murya a sanyaye take furta "ban kasance mai jiji da kai ba ya meri pati, ka mun afuwa domin fushin ka a gare ni tamkar wuta ne mai cin duk ilahirin jikina..."

Shapris cikin izzah ya furta "idan kuwa kina gudun ɓacin raina to kiyi duk abinda na umarce ki..."

Jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha Allahu Indai bai tsaba wa Ubangiji na ba..."

Ba tare da ya furta komai ba yasa hannu ya fara cire kayan jikin sa, Asmeen ganin haka yasa tayi saurin juya bayan ta jikinta har wani kakkarwa yake, ba ƙaramin tsorata tayi ba ganin ƙiran jikin sa,
Sai da ya kammala cire komai ya bar iya short pant a jikinsa sannan ya tako dab da Asmeen yasa hannu ya rungumeta ta baya yana faɗin
"Meri Bi-wi shin kina son kasance tare da ni?..."

Asmeen tsabar ta gama tsorata hatta muryar ta ma ƙakkafe wa yake, hawaye sun gagara tsayuwa, numfashin ta ne yake haurowa da ƙarfi-ƙarfi lokaci guda sai ji yayi ta faɗa jikin sa ba alamun motsi, ganin kamar a sume take yasa hankalin sa yayi matuƙar tashi, a ruɗe ya ɗago ta tare da kwantar da ita akan gado yana jijjiganta, ganin babu alamar zata farfaɗo yanzu yasa ya yi saurin zuwa wurin frig ya buɗe ya ɗauko ruwan sanyi sannan ya fara yayyafa mata, cikin ƙanƙanin lokaci ta farfaɗo a ruɗe tana furta sunan "Mom! Mom!! Mom!!!..."

Cikin fusata ya wani darara mata wani irin mahaukacin tsawa yana zazzaro idanu waje, bata san lokacin da ta haɗiye kukan ba ga yanda idanuwanta suka yi jawur tsabar firgici da tashin hankalin da ta shiga,
Jawo ƙafafuwan ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado sannan ya ɗora ƙafarsa akan gadon dab da ita ya matso da fuskar sa kusa da nata yana mata kallon ƙurilla sannan ya ce "zan cigaba da dasa miki tsorona a cikin zukatan ki, sannan zan toshe duk wata kafar da zai sa ki raina ni Meri Bi-wi..."

Asmeen gaba ɗaya ta gagara gane manufarsa, zuciyar ta cike yake da tambayoyi, girgiza kai ta yi idonta akan sa ta ce "nasan akwai dalilin da yasa ka shiga jikin mahaifiyar mu, shin meye manufar ka akan mu har aka mallaka maka ni, shin cutar da ni zakayi ko kuma so kake kayi rayuwar aure dani tsakani da Allah?..."

Kafin ta lumshe ido bata ankara ba taji wasu zafafan mari har sau biyu akan kyakkyawar fuskar ta, a ruɗe ta kama fuskar ta cikin tsoro da firgici tana sakin ihu domin ba ƙaramin mari ya yi mata ba, har sai da ta fara ganin farfatsin wuta...

Cikin tsawatar wa ya ce "zan zubar miki haƙwara idan baki mun shiru ba, har ke zaki mun maganar cutar wa? cutar wa ya wuce wanda uwar ku ta mun..."

Tana kuka ta ce "tin kafin Aure?..."

"ko zaki janye ne?..."
Tana hawaye ta ce "idan ka cigaba da cutar dani zan janye..."

Murmushi yasau tare da faɗin "okay fine! ki janye sai na Auri mahaifiyarki ita ai zata iya zaman Aure dani tinda ba haramun bane, yanzu zan je na sanar mata cewa kin janye...."

Cikin kuka ta furta "Nooo! Dan Allah kayi haƙuri Meri pati, zan cigaba da zama da kai a duk halin da na tsinci kaina, wannan kalmar da ka furta ya mun muni, gwara ka ɗauki wuƙa kaita yankan naman jikina hakan zai fi..."

Sauƙe ƙafarsa yayi daga kan gadon ya nufi hanyar toilet yana faɗin "zan shiga wanka, ki shiga kitchen ki girka mun abinda zan ci..."

Cikin girmamawa ta ce "godiya nake Meri pati..."

Ta miƙe tare da ficewa daga room ɗin tana ƙoƙarin goge hawayen fuskar ta....



Nasreen da Tasleem ne suke zaune a bakin gado sun jeru kamar masu karɓan gaisuwa, a hankali Nasreen take motsa lips ɗin ta tana yiwa Tasleem nasiha akan ƙin bin umarnin mahaifiyarsu,

"Tasleem kin san uwa uwace koda ita ɗin mahaukaciya ce balle mun samu uwa jajirtacciya kuma mai kula akan ƴaƴanta, tana matuƙar ƙaunar mu meyasa baza mu bi umarnin ta ba? meyasa baza mu mata biyayya a matsayinta na uwa ba? mu kaɗai ta haifa ƴan uku babu namiji a saman mu da ƙasan mu, mai yasa baza mu zamo mata jajirtattun jaruman triplets ba...."

Tasleem lumshe ido tayi tare da faɗin "please it's okay! shin a yanzu bama mata biyayya ne ko bama bin umarnin ta?..."

Nasreen ta ce "bakya tsoron ta sannan bakya bin umarnin ta..."

Tasleem murmushi ta sau idonta na kallon gefe guda ta ce "meyasa kika yi wannan tunani akaina ?..."

Nasreen ta ce "abinda ya faru yau ke da Mommy, a gaban baƙon ta kika rufe ido kamar ba mahaifiyar ki ba, kina sa'in sa da ita akan abinda bai kai ya kawo ba, just ki durƙusa ki gaishe da baƙon ta shine problem haba Tasleem, ana sara ana duba bakin Gatari mana, mata mai mutunci mai daraja mai kima a idon kowa amma ta kasa samun wannan darajar da mutunci a idonki, I think ko wani kika ga yana cin mutuncin mahaifiyar ki sai yanda ƙarfin ki ya ƙare balle ke da kan ki..."

Wani irin tsawa Tasleem ta dararawa Nasreen har sai da Nasreen ta toshe kunnuwanta, haka Tasleem ta miƙe tsaye tana faɗin "ke kin kasa fahimtata shin waye zai fahimci halin da nake ciki? waye zan gaya wa damuwata? duk babu domin kuma bakin ku ɗaya da mahaifiyata wacce ta kasa bamu lokacin ta, muhawara, shawara, damuwa duk mun kasa sanar mata saboda tsoron da ta dasa wa zuciyoyin mu, gani take idan ta zauna da mu tasan matsalolin mu zata cutu ne, har yau mommy bata

7 / 45