NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU Lamba ta 1 Ina godiya marar adadi a gareku masoyan rubutuna, Allah ya barmu tare, ya sadamu a aljannah maɗaukakiya. Shanono ma tace in miƙo mata godiya. Nagode da jimirin jira, na dawo da zafina. Shanono. Ina ji alƙali ya buga gudumarshi dam_dam. Aka miƙe a tare, tare da haɗin baki wajen cewa. "Kotuuu" Cikin ƙudurar ubangiji sai na nemi tsoro da fargabar da suke ɗawainiya da ruhina tun jiya na rasa. Fuskata na sake murtukewa, ina tsaye dam a kan ƙafafuna. A maimakon in sare, sai sabon ƙwarin guiwa ya ziyarceni. Kunto Salis nayi a baya na, tsabar ɓacin rai na miƙo ma Sabira. Ki kula dashi Sabira. Kui mana adda'a. Kwana ashirin a gidan yari , ba mutuwa bane. Wani darasin na rayuwa zamu mu je koyowa" Ban karashe maganata ba, ƴan sanda suka iso inda muke suka sanya mana saƙandami a hannayenmu. Yaya Use kuwa sai zare idanu take yi, halamu sun nuna tana cikin ɗimuwa sosai. Ni dai furtawa nake. Sabira ƴaƴana suna gidan Yaya Use, suma fama suke yi. Ki ajjiyesu a wajenki su koma karatu. Habiba Bala nagode." Inda Kaila yake na kalla, ba abun mamaki bane dan naga murmushi a shinfiɗe kan fuskar Kaila. A raina na furta. Zaku sha mamakin shanono muddin na fito." Ƙeyarmu aka kaɗo zuwa waje. Hajiyayye sai falli da zubar da maganganu kaifafa take yi ƴan uwanta suna kuma zugeta. Lauyanmu kuma sai kalma yake bamu, yana tausarmu akan komai zai daidaita. Ni bana so ma ya daidaitan a tunanina zaman gidan yari yafi zaman gidan Kaila daɗi da samuwar ƴanci. Yara kawai nake ji, amman da da kaina zan nemi takaddata dan ta fiye mun alkhairi. Damuwa da tagayyarar da yarana zasu yi ne kawai nake ji. A motar gidan yari aka jefamu, ina kallon idan Sabira da Habiba Bala, ina kallon Salis dake riƙe a hannunta. Kasa riƙe kansu su ka yi sai aikin kuka suke yi. Ni kuwa zuchiyata dan haushi tuni ta dake, ko halamar kuka bana ji. Muna ji muna gani aka fice damu. Yaya Use sai hauka da bige_bige take faman yi tana ambaton, ta mutu ta lalace. Ni dai sai Alhamdulillah kawai nake furtawa, bani da wata adda'a dana iya, sai godiya da nake ma Allah. Na yi imani tsananin son da Ubangijina yake yi munne yasa nake faɗawa kwatami iri_iri. Tun kafin in kai haka nake fuskantar ƙalubalen gidan aure kashi kashi. Jiya na kasance a cell, gashi yau zan kwana a kurkuku, oh ni shanono, wai ni Hajiyayye zata raɗa ma sharri, abun tambayar akan me take yin duk wannan abun, akan Kaila? A'a ba haka bane tunda tasan ko kallo ban ishi Kaila ba. To akan me take yi ne ku bani amsa in kun sani?. Kaina yayi zafi sosai. A haka muka iso gidan yarin. Gandirobobi suka tasa ƙeyarmu izuwa wani dogon falo. In da anan zaka faɗi sunanka da laifin da yasa aka kawo ka. Bayan duk mun faɗi sai aka ajjiyemu a ɗakin jiran shari'a wato ( waiting room? Duk wani wanda ba'a gama zartar mishi da hukunci ba, ana kotu ana gumurzu, to wannan ɗakin shine wajan zamansa. In an yanke maka zaman gidan yari, na wasu wa'adi, ko ɗaurin rai da rai irin na Su Hauwan Aminu diya ga marne ƴa ga Sada ( UNGULU DA KAN ZABO) to wannan wani abune da ban. Za'a shigar da mutum cikin yadi. Bayan an tasa ƙeyarmu zuwa cikin wannan ɗakin jira. Sai lokacin na saki kuka dana yi tozali da matan dake cikin ɗakin, harda waɗanda suka manyanta. Dama mata su na yin laifin da har ake kawosu gidan yari kenan. Iko sai Allah. Kwananmu na farko tamkar a cikin kabarina na kwana haka naji. Ashe akwai ɓirɓishin rahama da salama a cikin gidan Kaila. Duk lalacewar Kaila ya fi gidan yari gaskiya. Allah sarki yarana. Abincin gidan yari bala'i ne. Har maggi wasu suke barbaɗawa, suna da kuɗi a kanta, gandirobobi ke siyo musu. A kwana na biyu Sabira ce ta kawo mana abinci, amman bamu samu ganawa ba. Ta dai kawo mun aidigar mata, da ɗan dires sababbi guda takwas. Nonuwana sun suntuma sunyi tauri tamkar dutse, hakan ya haifarmun da zazzaɓi mai zafin gaske. A ranar ne Habiba Bala da lauyanmu su ka kawo mana ziyara, domin sake jin ta bakinmu. Halin da suka tarar dani ya kidimasu, da taimakonsu aka kaini ɗakin shan magani dake cikin gidan yarin aka harhado mun magunguna. "Shanono kiyi haƙuri. Muna kan bincike kuma akwai danshin nasara. Yaronki yana hannun Sabira tana bashi madarar yara. Makarantar islamiyyarku Sabira ta sanar musu wata tafiya ce ta taso miki, haka ma bokon an sanar musu. Yaranki suna cikin ƙoshin lafiya. Kaila ya je har gidan Sabira ya tasa ƙeyarsu ya mayar dasu gabanshi. Amman kiyi haƙuri gidansu ne ai. In ma kashesu zai bari Hajiyayye tayi ai sai ya bari. Yaya Use kema na je gidanki ni na sanar ma mijinki duk abinda ake ciki. Jiya yazo ba'a bashi damar ganinki bane." "To lokacin ku ya cika" Cewar wani gandiroba daya katse ma Habiba Bala hanzarinta. Haka dai rayuwar mu taci gaba da gudana a cikin gidan yarinnan. A cikin ƙanƙanin lokaci duk mun rame, bamu sake ganin kowa ba, basa bari a ganmu. Har Baffa da Inno suma sun zo bisa jagorancin Yaya Karime. Suna dai sanar mana sunayen masu kawo ziyarar amman ba'a basu damar ganinmu, in ba dai lauyanmu ba. A cikin sunayen banji sunan Kaila ko sau ɗaya ba. Sai da na kwana goma cib a gidan yarinnan banyi wanka ba. A cikin kwana na sha ɗaya ne na watsa ruwan sanyi, nayi wari har sai da bokan zamana suka ishemu da ƙorafi, gabana duk ya ɗaɗe, sabida ina jini, kuma baya samun ruwa, duk jinin biki ya bubbushemun, ya manne a gashin wajen, sai ciwo yake yi mun. Wuni nayi da zazzaɓi mai zafi a jikina a ranar. Bazan iya fasalta muku irin rayuwar gidan yari ba. Amman ko maƙiyina bazan so a kawo shi wannan wurin ba. Amman zaman gidan ya sake farkar dani, gami da zaburar da ni akan al'amuran rayuwa. Kwanci tashi asarar mai rai. Cikin hukuncin Allah yau yayi dai _dai da ranar laraba ashirin ga sabon wata. Wanda yayi dai_ dai da ranar da zamu yi zaman kotu na ƙarshe. A daren ranar ni da Yaya Use haɗe kai mu ka yi, mu kai ta kuka. Babban tashin hankalin mu shine ace dawo damu za'ayi wannan baƙin gidan. Cike da damuwa da taraddadi gari ya waye. Kaila: Tun bayan da Bilkisa ta dawo aiki ta ga yaran Tani a falo a takure suna kuka. Ɓarayinta ta ja su, ta basu abinci. Suna cikin ci kan baka kan ƙwarya, Kaila ya shigo, Bilkisa tayi tagumi tana kallonsu cike da tausayinsu, a zahirin gaskiya tana tausayin uwarsu sosai." "Su kuma waɗannan yaran me su ke yi a falonnan kalan su tsuttsula fitsari. Ku tashi ku fice ƴan iska" Jikinsu na rawa, Sani ya sasu a gaba suka fice daga ɗakin. Bilkisa ta kalli Kaila tace. "Wata rana na tabbatar yarana za ka yi ma wannan koran wulaƙancin. Tunda ai kana son Tani ne shi yasa tun farko ka aurota. Kuma duk ƙazantarta da kake kafa hujja dashi, gashi ɗanyan goyo ne da'ita. Sannan hausawa sun ce matar so ita ke yin konika. Kaila ni fa na gaji da aurenka. Na roƙeka dan Allah ka sake ni in koma garinmu" Zabura Kaila yayi, ya kafeta da idanunshi domin yasan suna da tasiri akan duk matanshi, ba ma su kaɗai ba akan duk macen daya zuba mata su, suna da tasirin kashe jiki. Saurin ɗauke kanta tayi. Shi kuma cikin sigar yaudara yace. "Tani na sota irin son da ban yi muku ba duk ku biyun. Amman shekararta uku a gidana naji duk duniya babu wacce na tsana sama da ita. Tantiriyar ƙazama ce. Bilkisa ki mun uziri ko mu'amular aure zanyi da Tani sai na sa tayi wanka fin sau uku, ki yarda dani, sai na toshe hancina nake iya kusantarta sabida irin warin dake fita a gabanta......" "Ya isa nace. Ka dena tona mata asiri haka. Akwai wani mataki daka ɗauka akan hakan ne, ka sani ko lalura ta gamu dashi, ko ka taɓa faɗa mata, ko asibiti ka kaitane, shin ko maganin gargajiya kake bata?" Zum yayi domun Bilkisa shirin ɗaureshi da jijiyoshinshi tayi. Yasan baiyi duk abinda ta lissafoba. Face cin zarafin Shanono da zaginta, da kiranta ƙazama ballazaga samodara. Hakanne yasa ya ja numfashi cikin kaurara murya irin ta cikar mazantaka yace. "Ɗanyan gwal. Kina ganin kamar bana yi ma Shanono adalci ne? A ƙarƙashin inuwar aurena fa take, kuma bana hanata abinci da yaranta. Sannan ai.. "Ya'isa yanzu ina taje naga yaran su kaɗai a babban falo, su da gidan ubansu amman duk sun takure?" "Tana firzin ita da yarta, alƙali yace a ɗauresu akan kashe yaron dake cikin Hajiyayye da suka yi. Zuwa ashirin ga sabon wata mai kamawa za'a sake zaman kotu" Cikin ɗaurewar kai tace. "Kotu akan Hajiyayyen, bayan ita ta cakali yar umman Sulaiman da faɗa, da cin zarafin iyaye? Ai ni banga ta yanda za'ayi su kashe mata ɗa a ciki ba. Domin babu wanda ya taɓa cikinta. Sannan ai ba da Umman Sulaiman akayi rikicin ba. Kai kuma wanne hukunci kake shirin ɗauka akan lamarin, Dady kuma yana ina?" "Dady yana hannun ƙawarta Sabira. Ɗanyan gwal wanne hukunci kuwa zan ɗauka. Ai kes na gaban alƙali sai abinda ya zartar" Tun daga wannan rana, Kaila bai sake samun kan Bilkisa ba sam. Ajjiyeshi tayi a kwandon shara, ta banza ajiyarsa hakkinshi ma da figi da yagi yake karɓa. Yaran Tani kuma ita ke kula dasu, ita take basu abinci. Ta ɓangaren Shamwila kuma sai tambaɗewa suke ita da Kaila. Tana ta yashe mishi aljihu. A cikin kwanakinnnan Kaila ya tafi Port Harcourt, ya buɗe ƙaton wajen gashin naman kaza harma da balango. Amadudu, da wani yaron aikinshi ne suka koma Port Harcourt ɗin suna kula da wajan. Sati biyu da kulle Tani Sabira da, Habiba Bala, da Yaya Karime su ka zo suka gyare ma Tani ɗakinta, aka zuba mata saitin kujeru, harda kafet na tsakiyar ɗaki. Wanda Sabira ta sai mata suka baje mata a uwar ɗakinta, doguwar kujerar da Sabira ma ta bata uwar ɗakin aka kai mata. Suka sa mata ƙarfen, da sababbin labule. Su Sani sai tsallen murna suke yi. Yara sunyi fes dasu har haske suka ƙara sabida kullum Bilkisa na sa Shamwila tai musu wanka, ta wanke musu kayan da suka cire. Yaya Karime ta saɓa Hauwa a baya da zasu tafi ta tafi da'ita dama tare suka zo. Hajiyayye tana babban falo sai ƙwafa take yi, tana mamakin yadda akayi Tani ta samu irin kujerun da taga an wuce dasu. Gogan kuma yana Port Harcourt ya koma ya ɗan riƙa ma su Amadudu aikin. Dan ba ƙaramin ciniki suke kwankwatsawa ba, kunsan mutanen kudu akwai su da son suya." Ɓangaren su Baffa kuwa. Bayan sun dawo suka ji abinda ya faru a bakin Baban yara mijin Yaya Use. Sun shiga tashin hankali marar misaltuwa. Su gani suke yi ma su Tani sun tafi kenan. Barin ma da Habiba Bala tai musu jagora zuwa firizin ɗin aka ƙi bari su gansu. Hankula ya kuma tashi. Yaya Karime ce tai ta aikin rarrashi. Nan kuma Baffa ya buɗe fitina da faɗan me ya kai Use gidan Tani salesalin ta turguɗe mata ɗan auren da suke lallaɓawa ta zauna. Sawunsu biyu wajan tukubar Kaila basa samunshi. Inno ce ta yi dubarar zuwa gidan iyayen Hajiyayye domin ta basu haƙuri. Su kai mata cin kashi da gori marar daɗin saurare. Haka ta fito, ba tai zuchiya ba ta je gidan Tani wajan Hajiyayye ta dinga bata baki. In kun tanka Hajiyayye ta tanka. Inno dole data gaji da zaman jiran amsar Hajiyayye ta fita jiki a mace, bayan ta shiga ta dubo yaran. *RANAR ZAMAN KOTU* A motar gidan yari aka shigo damu kotun. Da Inno da Baffa na soma yin tozali. Sai su Habiba Bala, Sabira, Yaya Karime, Baban Yara, da Hajara ƴar Yaya Use da take aure a can garin su Baban yara. Hawayene suka shiga suntiri a kumatuna. Yaya Use kuma ta saki kuka mai sauti. Gefe da gefen mu gandirobobine mata suke tsare damu. Cikin kotun muka shiga, Su Inno suka mara mana baya. Zama mu ka yi a wajan zama. Da Kaila na haɗa idanu yana cikin ƴan uwan Hajiyayye. Bilkisa tana ganina ta taso, ta dawo ɓarayin da su Inno suke. Hindatu ta kalleni ta watsar, naga kotun an cika sosai, har da ƴan kallo a wannan karon. Bayan shigowar alƙali da mintuna aka soma karanto ƙara. "A yau Ashirin ga sabon wata. Wannan kotu mai alfarma zata ci gaba da sauraren shari'ar Hajiyayye, da Tani,da Use." Alƙali yayi gyaran murya tare da cewa. "Laiyoyin ɓangare biyun in sun hallara zasu iya soma ba da shaidarsu" Zuruf lauyanmu ya riga lauyan su Hajiyayye tashi. "Na gode mai lord sunana Barister Suwiɗi, nine lauyan dake kare waɗanda ake ƙara. Ya mai girma mai shari'a. Ranar biyar ɗin babbar sallah data wuce. Malama Tani tana ɗakinta mijinta Kaila ya je ya sameta har ɗakinta. Ya ce ta ɗakko atampar da tasa ranar ukun sallah, tazo ta same shi a ɗakin kishiyarta. Haka Tani ta ɗakko kayan ta bi Kaila ɗakin Hajiyayye ta bashi. A gabanta ya ɗauki kayan ya miƙa ma Hajiyayye har yana tambayarta. Rigimar ta ƙare ko?" Alhalin ba Kaila bane ya sai ma Tani wannan kaya ba. Asalima rabon da Kaila yai ma Tani sutura shekara huɗu kenan. Ya kasance marar adalci, kuma azzalumi akan matarshi..." "Ina da ja ya mai shari'a lauya mai kare waɗanda ake ƙara yana shirin sauka daga kan doron abinda ya tara mu. Shari'ar Hajiyayye da su Use akeyi, ba wai tuhumar Kaila ba. Nagode my lord" Alƙali yace. "Ƙorafi ya karɓu. Dan haka barister Suwiɗi ka kiyaye" Barrister Suwiɗi yace. "Nagode my lord. Akan wannan kaya da aka kwace ma Tani ta hanyar fin ƙarfi shine. Yaya Use taje ta karɓo ma Tani kayanta. Wanda a ranar da abin zai faru kayan Hajiyayye ta saka, ta fito tsakar gida tana homa. Use ba da tashin hankali ta je ma Hajiyayye ba. Itace ta cakaleta, ta hanyar zagin iyayensu. Daga nan dambe ya ɓalle a tsakaninsu. Kuma ba Use bace ta kashe ma Hajiyayye yaron dake cikin ta ba. Yaron ya mutu tun kafin wannan faɗan." "Ina da ja ya mai shari'a. Wannan ƙirƙirarren labari kawai Barista Suwiɗi yake ba kotu." Lauyanmu yayi murmushi yace. "Ya mai girma mai shari'a iyakar abinda zance kenan. Kafin in soma gabatar da hujjojina. Nagode my lord " Zama Barister Suwiɗi yayi, yana share zufa. Ni a wannan karon ko gezau bana ji a zuchiyata. Kuma da zan samu dama a cikin kotunnan zan kashe Kaila uban kowa ya rasa. Muryar makirin lauyan su Hajiyayye ne ya dawo dani daga duniyar tunani. "Ina neman wannan kotu mai alfarma ta bani dama in gayyaci Hindu Facalar su Hajiyayye wacce a idanta faɗan ya wakana. Asalima da ita aka ɗauki Hajiyayye ranga_ranga zuwa asibitin matanmi." "Kotu tana neman Hindatu" Ƙur na ƙura mata idanu. Ta tawo sai harɗewa take yi, ta tsaya a cikin ɗan akwaku. Alƙali yace da'ita. "Gabatarma da kotu sunanki" "Sunana Hindatu Madaki." Lauya ya tsaya a gabanta yace. "Hindatu zan so ki bani labarin abinda ya faru a ranar talata, wanda yayi daidai da bakwai ga wata na bature, da misalin ƙarfe shida da minti goma na yamma" "Ni dai ina tsakar gida ina aikina. Sai naga Use akan Hajiyayyen tana cewa su je ciki su yi magana. To Hajiyayye dai ta nuna mata ba zasu shiga ciki ba. Shine Use ta rufe Hajiyayye da duka, Tani na tayata. Haka su ka zauna a cikinta Use na kokawar sai ta yi mata tsirara, dan harta yayyage mata rigar jikinta, daga ita sai gwado. A haka jini ya ɓalle mata. Ko da mu ka kaita asibiti likitoci suka ce tiyata za'ayi mata, sakamakon dukan cikinta da akayi yaro ya mutu mata. Iyakar abinda na sani kenan." Murmushi nayi kawai, Hindatu zata aika ai. Tunda ta taɓa kuzama Balarabana ruwan zafi tana rarrafe, ɗuwaiwanta sai da ya sale. Yaya Use kuma kuka ta rushe dashi. "Ko lauya me kare waɗanda ake tuhuma yana da tambaya da zai yi ma Hindatu" Cikin ƙarfin guiwa yace. "Ina da shi my lord " Ƙwaf_ƙwaf_ƙwaf ya isa bakin ɗan akwakun yace . "Malama Hindatu. Shin dama Tani ta saba rigima da Hajiyayye ne, ko wannan shine karo na farko?" Hindatu tayi tsiri, daga baya tace. "Basu taɓa yin faɗa ba gaskiya." "In na fahimceki zaman lafiya suke yi kenan, babu komai a tsakaninsu" "Ina da ja my lord. Lauya na son ɗaura ma Hindatu fargaba. Wannan shine tsaiwarta a kotu na farko, bata saba ba" Alƙali yace. "Ƙorafi bai karɓu ba, dole Hindatu ta amsa wannan tambayar. Barista Suwiɗi ci gaba da tambayarka" "Nagode my lord. Hindatu kotu na saurarenki" Hindatu ta nisa, kana tace. "Zaman doya da manja suke yi. Amman basa yin faɗa, Tani bata fiye shiga harkar Hajiyayye ba gaskiya" Kai ya gyaɗa yace. "Zaki iya tafiya" Sum_sum ta fito. Lauyanmu yace. "Ina neman alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da shaidata ta farko" Bayan rubuce_rubuce da alƙali yayi yace. "Kotu ta baka dama" "Ina son Bilkisa Ɗanyan gwal ta fito gaban kotu"" Bani kaɗai ba naga hatta Kaila, da Hajiyayye, dama Hindatu sai da su ka kaɗu. Ƙwas_ƙwas_ƙwas ƙwas take tafiya takalminta na fitar da sauti. Cikin ɗan akwakun ta shiga. Kaila sai zazzare mata idanu yake yi, ita kuwa tayi biris ." "Bilkisa kotu na son jin sunanki daga bakin ki" "Sunana Bilkisa Salis Sabo" "Ko zaki iya sanarma da kotu gaskiyar abinda kika sani?" Bilkisa ta gyara tsaiwarta tace. "A kan idanuna komai ya faru. Tun daga zuwan Yaya Use wajan Hajiyayye har fitar da'ita da akayi a gidan tana zubar da jini. Yaya Use bata je gun Hajiyayye da fitina ba, asalima Hajiyyen ce ta nemi ayi damben, dan ita tai ta zagin yaya Use. Sannan Yaya Use bata daki Hajiyayye a ciki ba, kuma bata zauneta ba. Hindatu ƙarya take yi ma kotu bata faɗi gaskiya ba. Sannan Tani ita ƙoƙarin raba faɗan ta dinga yi ita da Hindatu. Kuma ita ta fita tayi kururuwa jama'a suka shigo. Iyakar abinda na sani kenan." Alƙali bayan ya gama nazari yace. "Lauyan masu ƙara yana da abinda zai tambayi Bilkisa?" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe yace. "Bubu ya mai Shari'a. Amman ina roƙon wannan kotu mai alfarma da tai gaggawar yanke hukunci. Domin likitoci sun tabbatar da cewar buguwace tasa yaron Hajiyayye ya mutu." Alƙali yace. "Barista Suwiɗi kana da wata shaidar ko iyakarsu kenan" "Akwai my lord. Inason kotu ta bani dama in gabatar da shedata ta ƙarshe." "Kotu ta baka dama" Cewar alƙali. "Inason Dr Ruƙayya ta fito gaban kotu" Wata mata ce fara ta fito tana sanye da fararen kaya na likitanci. Lauyanmu yace. "Dr ki gabatar ma da kotu sunanki, da halaƙarki da wannan shari'ar" Tace. "Sunana Dr Ruƙayya. Kuma nice na ciro mataccen jaririn dake cikin Hajiyayye" Lauyanmu yace. "To ko zaki faɗa mana abinda ya kashe wannan yaron a ciki, kuma ai ku likitocine ina tunanin zaku iya sanin kwanan jaririn nawa da mutuwa ko?" "Tabbas kuwa. Jaririn a ƙalla zai kai kwana uku da mutuwa a ranar da aka ciroshi, bincikenmu ya nuna mana buguwace tasa jaririn mutuwa, dan har jikinshi ya soma yin yellow, da saɓulewa. Tabbacin kwananshi uku zuwa huɗu da mutuwa a cikin. Kuma Hajiyayye bata zuwa awon ciki balle likitoci su dinga duba lafiyar jaririn. Iyakar abinda zan iya cewa kenan." Murmushi ne ɗaure a kan fuskar iyayena,ƴan uwana, da Aminaina. Alƙali yace. "Kina nufin mutuwar yaron bata da alaƙa da dukan da su Use su ka yi mata, wanda yai sanadiyyar zuban jininta, sannan ance zanga_zanga aka kawota asibitin, kuma sabida laushin da tayi ne yasa akayi mata aiki. Shi aikin yana da halaƙa da dukan da su ka yi mata ne?" Dr Ruƙayya tace. "Tiyata bata da alaƙa da dukan da Hajiyayye tasha. Tana da alaƙane da mutuwar yaron a cikinta. Tunda yaron a mace yake, naƙudar za ta yi mata wani iri, ba kamar in yaro yana da ranshi ba. Wasu yaran ma basu cika fitowa ta hanyar mace tayi naƙuda ba in dai sun mace a ciki. Shi yasa muka zaɓi yi mata tiyata mu cire yaron, ba tare da ita uwar jaririn ta sha wahala ba. Wannan shine dalili" Alƙali yace "Dr Ruƙayya kin tabbatar gaskiyane duk abinda kika faɗa ma kotu? Kotu ba zata barki ba muddin tayi bincike ta gano kin mata ƙarya, ko shaci faɗi" Cikin ƙwarin guiwa Dr Ruƙayya tace. "Abinda nake faɗa gaskiya ne. Ko da wasa bazan yi ƙarya ba ko dan kare martabar aikina da asibitinmu MATANMI" "Lauyan masu ƙara yana da tambayar da zaima Dr Ruƙayya?" Alƙali ya jefo tambaya. Lauyansu Hajiyayye ya miƙe jiki ba laka yace. "Babu ya mai shari'a" Alƙali ya ba Dr Ruƙayya izinin tafiya. Raina fal farin ciki, ta wani ɓangaren fal takaici. Alƙali yace. "Akwai sauran hujjoji ko babu in yanke hukunci?" Kotu ta ɗau shiru halamar ba wani sauran hujjoji. Hajiyayye sai sauke kanta ƙasa tayi, suma ƴan uwanta su kai ɗib.........✍🏻 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lmhttps://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NA FAƊO DAGA BENE...... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 2. Alƙali kawai kowa yake jira domin jin hukuncin da zai zartar. "Wannan kotu mai Alfarma, bayan sauraren ƙara, da kuma yin nazari game da hujjojin da aka gabatar mata, da gamsuwarta akan lamarin. Kotu taci tarar Hajiyayye da Hindatu nera dubu ɗari biyar , wanda za'a ba Use da Tani, a bisa ɓata musu suna da su ka yi. Sannan za su yi zaman gidan kaso na kwana ashirin da aiki mai wuya a sakamakon cin zarafin Use, da Tani da su ka yi, su ka sa aka kullesu a gidan kaso ba tare da sun aikata laifin komai ba. Kotu ta wanke Tani, Use a bisa tuhumar kisan kai da ake musu. Dan haka Tani da Use zasu iya komawa cikin iyalinsu. Kotu zata karɓo musu kuɗinsu daga hannun Hajiyayye da Hindatu, tare da danƙa musu a hannunsu, Kuna da damar ɗaukaka ƙara matsawar hukuncin da aka yanke muku bai muku ba." Guduma alƙali ya buga duk muka miƙe. Hawayen godiya ga Allah nayi, tare da jero kirari ga Allah mamallakin raina. Su Hajiyayye ido ya raina fata, Kaila sai zazzare idanu yake yi, tsoro yake kar kotu ta yanke mishi nashi hukuncin shima. Tuni aka tasa ƙeyarsu zuwa waje. Kotu ta karaɗe da hayaniya da kukan ƴan uwan Hajiyayye. Hindu kuwa dama ita kaɗai tazo kotun, ba ƴan uwa take dashi a garin ba. Muna fitowa Baffa yace. "Allah ya soki Use Wallahi da ace yaronnan ya saki Tani da tsine miki zanyi kibi uwa duniya. Ke kuma Tani muddin na kuma jin wata fitina wallahi ranki in yai dubu sai ya ɓaci. Inno wuce mu tafi wajan bara. Use ta bi mijinta su tafi gida, Karime ta raka Tani gida." Baffa ga Habiba Bala kui mata godiya, ita da Sabira sun taimaka mana sosai. Habiba itace ta ɗauki Dauda yana hannunta" Da jin haka su ka washe baki su ka shiga runtuma godiya. Baffa yace. "Wayyo yarinya Allah ya saka miki da Alkhairi mun gode sosai" Habiba Bala tace. "Babu komai Baffa." Sallama su kai mana suna tafe suna faɗa, Yaya Use ma Baban yara ya tafi dasu gida. Ni dai wasai nake jin kaina. Motar firzin ta fice a guje dasu Hindatu, ƴan uwansu kuma suka nufi ofishin alƙali dan ganawa dashi. Barista Suwiɗi ma ya tafi ofishin yanzu. Habiba Bala, Sabira nagode muku. Allah ya barmu har gaban abada" Cikin zolaya Habiba Bala tace. "Wa zai gane mun idon shanono a cikin firzin. Kin haɗu da kuɗin cizo kuwa" Sabira ta tuntsure da dariya tace. "Kuɗin cizon gidan yari bazai bata tsoro ba. Tsohuwar katifarsu in kika ɗagata zaki ga kuɗin cizo yafi ɗari suna yawo fa" Murmushi nayi musu kawai, dole su zolayeni mana. Amman ni yanzu ai naji faɗansu, za su ga canji a zahiri. Ba ma su kaɗai ba, duk waɗanda suke tare dani zasu ga canji. Bilkisa ce ta ƙaraso muka gaisa, nayi mata godiya, su Sabira suka taya ni yi mata godiyar suma. Sallama tayi mana muna gani ta shige motarta ta figa ta bar Kaila da Baba Rammai a tsaye. Baba Rammai ta riƙe haɓarta. Bayan na karɓi Salis na je wajan Baba Rammai na gaisheta, wani harara ta watso mun. A tunaninta zanci gaba da tsaiwane har sai ta gama mulkinta. Sai kawai nima na yi ficewata na bi su Habiba Bala. Ko ta tafasa ko ta ƙone a shirye nake da kowa." A lifan Kaila ya Goya Baba Rammai suka fita. Barista ne ya fito yake shaida mana duk sanda kuɗin da aka yanke ma su Hajiyayye suka biya ta hannun lauyanmu zai zo. Nan muka ɗunguma sai gida. Da shigata yara suka tare ni da murna da ihu. Bilkisa ta tare mu da liyafar abinci mai garɗi, Ina shiga cikin ɗakina na fashe da kukan murna kamar wata ƙaramar yarinya. Naita musu godiya ina shi ma zuriyarsu da albarka. Wuni su ka yi cur. Habiba Bala ce ta soma tafiya. Kafin ta tafi sai da tai mun albishin zata riƙe mun Dauda, zata mayar dashi makaranta ta sashi a wajan sana'a kuma. Ta bani nera dubu tamanin a lokacin kuɗin ma da daraja. Wannan kuɗin ƴan ajinmu ne su ka haɗamun dan in ja jari. Wannan shine silar soma kasuwancina na sai da kayan miya. Cikin yardar ubangiji cikin ƙanƙanin lokaci aka sanni a kan sana'ata. Domin na faɗa muku filin sukuwa unguwace mai zurfi. Kuma duk tsukukun naci sa'a nice kaɗai mai siyar da kayan miya. Duk da dai mu muna ta can ciki ne, inda gidajen yaku bayi sukafi yawa. Unguwar ta hamshaƙan masu kuɗine sosai. Cikin ikon Allah komai yana tafiya dai_dai har na koma bakin karatuna. Ɗakina da jikina babu yabo babu fallasa, gaskiya na ɗauki shawarwarin masoyana, na gyara ba irin shanonon da kuka sani bace yanzu, mai shafe miya a kai, mai dangwalar yawu ta kama kuɗin cizo. Fita a cikin sabgar Kaila da kowa ma, da kuma dogaro da kai, da karatu, da cuɗanya cikin mata iri iri, yasa mun nutsuwa da kamewa, ni kaina in ance in yi abinda nayi a baya na ƙazanta bazan yi ba. Kwanansu Hajiyayye ashirin cib a gidan ɗan kande, wata rana da yamma sai gasu sun shigo bisa jagorancin ƴan uwa, duk ta rame ta yi duhu, tun daga ranar suke kiyayemun dukkansu. . Ni uban gayyar ma ban sake saka shi a idanuna ba. Sai wata ranar juma'a na fito ina sauri zani islamiyya. Da ɗan madaidaicin hijabina wanda ya wuce guiwa, sai doguwar rigata irin yadin hijabin. Harda ɗan niƙab ɗina na ɗaura. Ina fitowa muka haɗu da Kaila. Gabana ya faɗi, shi kuwa galala yake kallona, bai ce mun ba, nima ban ce mishi ba nasa kai na fice. A wajan Bilkisa nake jin wai sati biyu yake yi a Fatakwal, sati biyu a Jos. Ciniki ya kankama dan naga ya ɗebo gini harda ƴar motarshi ya siya yana murza kwalta gayu da kayan gayu yaci uban nada, lifan ɗin ya bar ma Amadudu. Tunda su Hajiyayye suka dawo ita da Hindatu babu wanda ya sake kallona daga cikinsu, balle ya takaleni da faɗa ko habaici, banyi wata ƙaxanta ba balle su tozartani. Amman fa kafin jikina ya saba da wanka kullum na ɗan ci wuya, da nayi wanka jikina zai shiga ƙaiƙayin jaraba, sabida rashin sabo da yi kullum, kitso kuwa duk sati in nayi sai nayi jinyar ciwon kai na kwana biyu sabida rashin sabo. Sai na yi kamar in watsar sai Sabira ta tallafeni, a haka har ya zame mun jiki, kullum zan yi wanka, yara zasu yi, zan gyara ɗakina in sa tsintsiyar ƙamshin viji, ko in kunna turaren kajiji wanda nake siya a wajan Mrs Bukhari. Tun Hajiyayye na mun kallon mamaki ni da yara har dai ta watsar. Da ina gaishe da Hajiyayye da Hindatu in mun haɗu, sai suke wani fuskewa, daga baya nima na watsar, su wuce in wuce. Kaila kuwa tun wannan dubu ukun da yaba Sani ya ajjiyemun ƙwandala bata sake shiga tsakanina dashi ba. Ni kuma na lashi takobin bazan tambayeshi ba. Rabon kwanane banaso, yaje can ya riƙe abarsa, bana zuwa, yaƙin na Bilkisa da Hajiyayye ne. Duk da ma na ga Bilkisa ta kanta take yi, cikinta ya fito titsitsi, Hajiyayye ma har ta sake amsar wani, ga Hindatu itama da ciki. Ni kuwa sai karatuna nake yi kawai, da sana'a. Barister Suwiɗi ya turo mana da kuɗinmu dubu ɗari biyu da hamsin _hamsin, wanda aka haɗa da ƙyar da siɗin goshi. Kuma dulmiyasu nayi a kasuwanci. Na soma ɗauko manja, mangyaɗa, maggi. Sani shi ke siyar mun da kaya in na tafi islamiya. Bayan wani lokaci: Kwanci tashi asarar mai rai, wai yau gamu a fagen zana jarabawar game sakandare, wanda yayi daidai da shigarmu S S 1 A islamiyya. Alhamdulillah na gama karatuna, amman fa harna kammala ban iya turanci ba. Ina dai jin komai, amman bana iya mayarwa, larabci kam mune gurayen aji Alhamdulillah, na fi mayar da hankali a fannin harshen larabcin. A wannan shekaru ukun abubbuwa da yawa sun faffaru, marasa daɗin faɗe, nayi rama, na komaɗe na zube sosai, ko bacci bana samu cikakke. Akwai raɗaɗi ace kana aure, wanda kake zamanshi ya saka a kwandon shara. A baya ana ganin ƙazantace tasa Kaila sani a gefe. A wannan ɗan shekarun na fahimci ko agwagwa zan zama dan wanka, in zama ɗawisu dan ado, Kaila bana gabanshi, bazan kasance a gabanshi ba. Wani irin raini ne mai ƙarfin gaske Kaila yake yi mini. Kuma yana tunanin ya wuce ajina yayi gaba ya barni a baya. Tunda yasa ƙafa ya shure baya. Haka naci gaba da kasancewa a gefe ni da Yarana. Da ni zasu yi wasa su yi dariya, nice uwar, nice uban, nice ƙawar duka yarana. Ina sake godema Allah subhanahu wata'ala da ya bani damar tarbiyyantar da yarana, na jure ƙunci dominsu, ina fatan wata rana su maisheni wata aba, uwa irinta kwatance a gari. Bilkisa tana goyon ƴarta me Suna Fatima, Hajiyayye tana goyon Anas, Hindu tana goyon mai sunan Kaila. Ni kuma tuni na yaye Salis jira nake ya shekara huɗu in danƙarashi a makaranta. Yara kuma na cire su a makarantar gwammati, na mayar dasu ta kuɗi, nice cinsu, nice shansu, suturarsu, jigilar lafiyarsu. Sai in yi wata cur ban sa Kaila a idanuna ba, ko yazo gari baya nema na, ya fiye mun dan na mugun tsanarshi, ina zaune ne kawai sabida yarana, da kuma tsoron bakin Baffa. Amman ko iyakar hana Yaya Use zuwa gidana da Kaila yayi ai ya cutar dani. Yaya Use ta aurar da ƴan matan ta du biyun. Sanda za'ayi bikin satinmu guda a gidan ni da yaran Bilkisa ma ta zo mana kamu da mu ka yi a mufiz Garden." Haka na sake kammale karatun islamiyyata cikin farin ciki, tare da haɗa gagarumar walimar data samu baƙuncin masoyana, da ƴan makarantarmu ta kwana , da kuma makarantar matan aure dana kammala. Mata matan layinmu ma sun zazzo sosai, sabida an sanni sosai a unguwar, nayi fice ta fannin sana'ata, har niƙaƙƙen garin tuwo nake siyarwa, da albo, da dakakken yaji, wani zubin harda fulawa da shinkafar tuwo. Bayan na kammala karatuna, sai na mayar da hankali na a kan kasuwanci na. Duk abinda na samu akan su Inno da Yarana nake ƙararwa, Dauda kuwa yana Bauchi makarantar kwana yake yi, ya ma fi su Sani gata dan Habiba Bala ta mayar dashi tamkar ɗan data tsugunna ta haifa da cikinta, yaro yayi tsawo, yayi haske kamar ba shi ba. Ga taron ƴan makaranta duk babbar sallah sai mun gabatar dashi, duk in da zani kai tsaye nake zuwa, ba makwaɓi. Gidan Kailan ma naga duk ya wargaje, da halama matan nashi duk zaman haƙuri suke yi, naga Hajiyayye ta dawo rakiyarshi dan kullum a cikin yaji take. Sanda Bilkisa ta haihu ma da ta tafi wankan gida, sai da ta yi wata tara cur, auren dai kamar zai ƙare, daga baya kuma sai ta dawo ɗakinta. Alh Kaila girma nata kamashi, gashi Allah ya sa mishi Nasibi cikin harkar kasuwancin shi, ya sake buɗe gidan gashi a Abuja, ya gangara Bauchi. Kuɗi sosai sun zauna a wajanshi, naga ma ya bar ma Hajiyayye motarshi, ya sai wata sabuwa. Ranar naga falli a tsakar gida, ina tsugunne ina ba yara tumaturi ya bata keyn motar. Ta wani rungumeshi ta ɗafe jikinshi, shi kuwa yayi lib a jikinta. Kaina na kaɗa kawai nayi shigewata ciki, Hajiya Hajiyayye an samu duniya, cikin ƙanƙanin lokaci ta zama wata hamshaƙiya, sutura kuwa ita da Bilkisa wannan na wane wannan ne, dan a yanzu Hajiyayye ta kamo Bilkisa ado da kwalliya, dan har shagon koyon kwalliya Kaila ya sata, yanzu ana biyota har gida taima mutane make up. Ina ji tana faɗa ma Hindatu ta samu shago a wajajen Salisu Adamu, ta buɗe shagon kwalliya, da lalle. Shikenan gidan sai na zama mai gadi da jiran yara, na ɗan waye ɗin ma ban tsira ba, tsabtarnan ina kamantawa, duk da banayi ɗari bisa ɗari, amman a ganina bani da wani aibu da zai sa Kaila ya kasa jerani da matanshi. Ni dai nasan na fi Hajiyayye kyau na fita haske, duk da itama da kyanta, kuma fararce, bilkisa kuma duk ta fimu kyau ita kuma, wata rana haka kaila ya sasu gaba su ka tafi bikin abokinshi a Abuja, ni duk suka zube ma yaran, ko wacce ta wanke ƙafa tabi miji. Ko banyi niyyar kuka ba dole ina ware lokaci in yi kukana mai isata, ganin yarana da rayuwar Dauda ta tayi kyau ne kaɗai ke sanyaya mun raina. Kuma fa har gobe Baffa bai daina ja mun kunne da gargaɗin kar in yi sake aurena ya mutu a karo na biyar ba. Su fa abun faɗe kawai suke gudu iyayenmu, Inno ta riga tasan zaman haƙuri kawai nake yi, ƴan uwana duka sun san ni nake riƙe da kaina da yarana, kaila mafaka kawai ya bamu. Gasuwa ruhina yake yi sosai, har fatan mutuwa na dinga yi ma kaina, daga baya na tsiri wuni cur a uwar ɗaki a kwance. Kamar da wasa Habiba Bala tai mun tayin me zai hana na zana jam, in ci gaba da karatun jami'ata. Ai tana faɗin haka naji na gamsu ɗari bisa ɗari. Kamar wasa na zana jam tare da cike kos ɗin da zanyi nazari akai. An yi harna mance kwatsam na samu gurbin karatun jami'a a Jami'ar Bayero unibasiti dake jihar Kano, a fannin ilimin low. Murna babu irin wanda banyi ba, nan na kikkira su Yaya Use nake sanar dasu na samu gurbin karatun jami'a, Sabira ina kiranta ta nufo gidana. A lokacin tana karanta islamic studys a jami'ar Jos tana aji na biyu. "Na ta ya ki murna Tani. Oh rayuwa, yanzu dubeki yanda rayuwarki tayi kyau, yara sun dena amalala, babu ƙwarƙwata, babu kuɗin cizo, babu konika. Ɗakin ki tsab, gidanki sai ƙamshin turaren kajiji yake yi. Ga ilimi, ga sana'a masha Allah, na yi farin cikin maganar karatunnan. Amman Abban Sulaiman ya san zancan?" Tana faɗin haka raina ya ɓaci. Sai kuma jikina yayi mugun yin laushin. Sabira ba lallai bane Kaila ya hanani tafiya ba. Sabida ai bai damu dani ba, yasan zaman yarana nake yi, kuma naga matanshi duk suna fita aiki, sai nice zai hana zuwa karatu? kuma kinga karatunnan dana kammala, harna gama bai ce mun komai ba, idanu kawai ya zuba mun. Kuma yara bana jinsu, abinda yasa nace Haka. Zan iya sa Shamwila ta dinga kularmun dasu, ina biyanta a wata, duk Sati zan dinga shigowa, kamar juma'a da safe, lahadi in kama hanya. Ina buƙatar karatunne Sabira. So nake in gyara rayuwata da rayuwarsu Inno, bana ƙaunar barar nan da suke yi. Amman zan je anjima in samu Inno mu yi magana in ji me zata ce" Sabira tace. "Ki soma tuntuɓar Abban Sulaiman da batun tukunna. Amincewarshi ai itace amincewar su Inno. Amman Tani kar ki sake ya tauye miki hakkin ki, wannan damace wacce ba kowa take iya samu ba. Wa yayi tunanin zaki taka irin wannan matsayin a rayuwa? Jibeki fa masha Allah, har wani kashe ido kike yi tsabar fari." Dariya mu ka yi. Ta jima tana bani shawarwari daga ƙarshe ta koma gidanta, dama daga makatanta take. Ina zaune jigum har su Sani su ka shigo. Binsu nayi da idanu, jibi yanda suka girma, Sani da Sulaiman suna sakandare, Shafi'i yana ajin ƙarshe a firamare, Amina da balaraba suna aji biyar, Hauwa na tana firamare 2, Salis na Nosiri 2. Wallahi ban zaci zamu kai ba, daga ni har su ban tamman zamu zama haka ba. "Umma sannu da gidan. In ji Sani dan duk cikin yaran yafi ƙulaficina sosai. Kuma ya fisu tausayina ko dan shine Babba yasan abubbuwa da dama ne oho. Yauwa Yaya an dawo, ita kuma waccan cuno bakin me take yi?" Na tambayi Sani. Shafi'i ne yace. "Abba mu kai ma sannu, yana tsaye da Shamwila shine ya doketa sai da ta faɗi ƙasa" Raina ya sosu sosai. Kaila ya tsiro da sarar ko tsakar gida yarana suka fita muddin yana gari, to kwa jishi yana hantararsu yana koromun su. Na rasa gane wai tsanatace yasa yaran da suka fito daga tsatsonshi baya son ganin sun raɓeshi? Sai yaran Hajiyayye wanda a yanzu yaranta uku, da Yaron Bilkisa, ita bata kuma haihuwa ba tun daga Fatima. Family planning ma take yi, a babban falo suka sha rikici lokacin da ya gano tana shan ƙwayoyin hana haihuwa. Buɗar bakinta tace. "Ni bazan sake jiki inta haihuwar maka yara, daga baya ka barni da wahalarsu ba, ka samu a kwandon shara kamar yadda kasa umman Sulaiman ba" Maganar tayi mun zugi sosai a ruhi, ta soso mun wani gyambo da yafi shekara goma a ƙirjina, abinda Bilkisa ta faɗa gaskiya ne, ta farkar dani daga wani bacci, amman farkawar babu amfanin da zata yi mun, abinda ya faru ya riga da ya faru, sai dai kiyaye gaba. Bilkisa ba ƙaramin zubar ma da Kaila gwandon rashin mutunci take yi ba. Sawa take yi kanshi yayi jaji har ya batse. Kuma daga gidansu ma a kirashi anason jin ba'asin abinda yayi mata, ta kai ƙara wajan iyayenta ( yana daga cikin illolin talaka ya auri ƴar masu kuɗi, ko ya auri matar da take ganin ta wuce ajinshi, musamman in iyayenta sun san dan dukiyarsu ya auri ɗiyarsu). Zo Hauwa na, tawo" Tana zuwa ta saki kuka har tana shessheƙa kamar zata shiɗe mun. Raina ya sake ɓaci. Hannayena na ɗaura a bayanta na shiga rarrashinta. Ƴan uwan nata kuma suka shige ciki sake kayan makaranta. Da unifom ɗin da suka cire Sani ya fito a bokiti, da ɗan omonshi. Ya dubi Hauwa yace. "Hauwa zo ki cire kayanki, ki hado mun dana Salis in wanke mana tunda yau babu islamiyya. Da wata iriyar siga mai raunata zuchiya yayi maganar, gabana ya yanke ya faɗi, sai kawai nake tunanin ko dai mutuwa zanyi ne. Take zazzaɓi ya rufe ni sosai" Salis shima ya faɗo jikina sabida kishin yaga Hauwa a cinya. Duk na haɗe na rungumesu wani abu na mun motsi a zuchiyata...... Shanono tana gaisheku. Ku faɗi ra'ayinku, in Kaila ya hana Shanono tafiya jami'a wanne matakin a ganinku ya dace ta ɗauka?NA FADO DAGA BENE...... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 3 Sun jima a jikina kafin na sake yin ajjiyar zuchiya na ciresu a jikina Amina zo ki cire ma Auta kayanshi, ki kaima Yaya. Hauwa kema ki cire naki sai ku yi tsifa. Zaku je gidan Yabi ta wanke muku kai, tai muku sitirecin. Gobe kuma sai ku je ayi muku kitso. Ni gobe Bauchi zanje, zamu je ganin Yayanku Dauda a makaranta. Balaraba tayi carab tace. "Umma dan Allah zamu je, kinji ummanmu, munason muje muma mu ganshi." Take zuchiyata tayi na'am da in tafi da matan, mazan sa zauna a gida. Sani babu abinda bai iya dafawaba, har tuwo ina bar mishi yayi mana, in ina makaranta, ko kuma ina farar gada sarin kayan miya. To shikenan, ku yi sauri ku tsefe kan naku, kuje a wanke muku. Ayi muku kitson in muka dawo daga Bauchin." Nan ɗaki ya kacame da murna. Amina ta cire ma Auta da Hauwa kaya. Shafi'i ya tafi kaiwa, Sulaiman ya zaunar da Hauwa ya soma tsefe mata kanta, Amina da Balaraba kowacce tana tsefe nata. "Umma sai yaushe Baba zai sai miki mota, kece kaɗai ba ki da mota a gidannan?" Murmushi nayi mishi nace. In Allah ya hore maka sai ka sai mun ai Sulaiman ko? Su Inno kuma ka sai musu gidan da zasu zauna su dena yawon bara, da yawan bin gidan haya" "Umma ke ma zan sai miki ƙaton gida da ƙatuwar mota, direba ne ma zai dinga kai ki anguwa" Amina tace. "Uhm wa yaga Umma a bayan mota a hakince" Dariya mu ka yi dukkanmu, sai zuchiyata tayi wasai ina cikin yara muna nishaɗi. Sani na gama wankin sai ya zubo mana abinci a tire shinkafa da wake da latas na yi mana. Tare muka zauna mu ka ci abincin. Sai mu kai sallar azahar. Amina ta kama ƙannenta zuwa gidan wanke kai. Sani kuma ya kama ƙannenshi maza zuwa shagon aski. Ni kuma a maimakon in tashi in yi kaye_kaye. Sai na yi linkib a saman kujera na nutsa cikin tunani da fargabar abinda kaje kazo dangane da makomar karatuna, Allah ya sani inason karatu ko dan nima in sake samun canjin rayuwa. Gashi wannan zamanin da muke ciki maza sun fi son wayayyun mata masu ilimin arabi da boko, ƴan ƙwalisa. Kuma nima Bilkisa da su Habiba Bala sun sake kwaɗaitamun sha'awar aiki. Ina son in yi karatu mai zurfi in samu aiki mai kyau. Domin in tallafi ƴan uwana da iyayena. Ina fatan in zama haske kuma fitila a cikin dangina. Ada sunana yayi fice ta fannin ƙin zaman aure. A yanzu inason in zama jajirtacciyar ƴar gwagwarmayar ƙwato ma mata da zawarawa hakkinsu. Dan a Arewa ne zaka ga bazawara a cikin gidan ubanta Almarijin gidansu me ɗebo musu ruwa yana da kwanon abinci amman ita bata dashi. Akwai ƙarancin wayewar ilimin addini tattare da iyayenmu maza da mata. Domin a da iyayenmu ba su yi karatuba sai ɗaiɗaiku, hakan yasa suka fi fifita al'ada fiye da addini, face ɗaiɗaiku daga cikinsu. Inason in zama mudibi abun dubawar zawara da matan gida, wanda wahala da takaici ɗa namiji suka linkime rayukansu. Mata har yanzu a baya muke, duniya tana ta samun ci gaba, amman mazajenmu sun ki su tallafemu ko da da ilimine. Ya Allah kaga abinda na saka a gaba. Da abubbuwan da sukaita kawo min cikas cikin rayuwata, kama daga ranar da aka haifeni a ƙasan gada har izuwa yau da nake a matsayin uwar takwas. Allah kayi mun zaɓi abunda yake mafi alkairi " Washe gari da wuri muka shirya, yaran fes dasu gwanin sha'awa, ko wacce saye da hijabinta har ƙasa, dan yanzu Shanono malamace, nasan abu mai kyau da mara kyau. Nasan mahimmancin lulluɓe jiki, mace ta suturce kanta umarnin Allah ne, ba umarnin wanin Allah ba. Shi yasa nake son yin ƙoƙari in ɗaura yarana bisa tsanin ƙarfe wanda nake da yaƙinin sari bazai cishi ba. Kuma na tsaya tsaiwar daka akan karatunsu, musamman ɓangaren muhammadiyya. Ibini Abbas suke zuwa islamiyya Makarantar Amayar sheik khalid Aliyu Babansu Umaima da Abdulwahit, sirikin gidan Garba na Garba. Kuma tana daga cikin makarantun islamiyya manya a garin jos. makarantar tana kan titin SALISU ADAMU, KUSA DA NEW MARKET ƳAN TIFA. Har zamu fita daga ɗakin Sani yace. "Umma ba dan masu zuwa sayen kaya ba da nace kije damu. Kuma banason fa ciniki ya wuce ki ummanmu" Turus nayi a dokin ƙofar na kalli yaron. Ku tawo mu tafin kawai tunda dai a shirye kuke, dan dai yau ɗaya ai babu komai mu yi haƙuri da cinikin. Shima wan naku duk santa mu ka je mishi bistin sai ya ce me yasa ba'azo daku ba." Ɗakina na kulle ruf, na nufi ɓarayin Bilkisa, su kuma nace su fice zan biyo bayansu. Sallama nayi ma Bilkisa akan zanje Bauchi dubo wan su Sani. Ai kuwa a cikin irin biskit da cakulet da Kaila ke siya ma ƴar lelen ƴarta ta ciro katan na biskit ta zura a ƙatuwar farar laida, ta ciko hannu da cakulet ta watsa, ta kuma cikowa ta watsa. "Gashi ki kai mishi kice in ji mamanshi. Ba za'a bar mun dadi a gida ba Umman Sulaiman?" Dariya nayi nace. Angode sosai. Babanki sarkin rigima ba, yana hannun Sani nace su yi gaba." Sallama nayi mata na fito. Bayan yaran na dinga bi ina kallonsu, yanzu cikin ƙudurar ubangiji wadannan yaran duk ni nayi naƙudarsu nai silar wanzuwarsu? Wannan ma kaɗai arzikine, dan suturar da aure tai mun kenan, banda yara dana samu da sai in ce babu abinda na tsinta a zaman aure. Sani yana reƙe da bakko babba wanda na shaƙe ma Dauda da kayan makaranta. Irin su biskit, siga, madara, confilakes na awo, da garin rogo da dakakken ƙuli, sai man ƙuli dana cika mishi goro, da maggi dunƙule. Haka nake yi mishi gwargwadon ƙarfina ba dan Habiba Bala ta gaza ba, dan ta ɗaukema Dauda dukkannin raɗaɗi, yaron ma ya fi saninta fiye dani, dan ni babu sabo tsakaninmu, ni inai mishi kunyar ɗan fari, shi yana mun kunya irin ta gadon fulani. Motar kuɗin baya na biya dukka, sit ɗin mutum uku, sai mutum ɗaya a gaba Yaya Use ce, a tasha muka haɗu da'ita, a taƙaice mu kaɗai ne a motar. Muka zauna a sake babu laifi, yara sai hayaniya suke yi, murnace fal ransu. Haka mu ka ci hanya, cikin awa guda da rabi sai gamu cikin falon Habiba Bala. Murnarta a wannan rana bata misaltuba. Tayi mana liyafar ban girma. Kafin muka nufi F J C Bauchi. Yau ranace da iyaye ke kaima yaransu ziyara. Da iyaye da yaran a wannan ranar sukan shiga cikin farin ciki marar misaltuwa. Duk yaron da iyayenshi basu samu zarafin zuwa ba kuwa, haƙiƙa wannan yaro an ɓata mishi ranar, bazai kasance da walwalaba. Akan yi girke_girken abinci masu kyau, a tawo da taburma ko dadduma a zauna. Kuga ɗanku, ɗanku ya ganku, ku bashi provision ɗinshi, in yamma tayi kuma ku tafi. Muma hakane ta kasance, mun samu damar shiga cikin makarantar, sai dai fa babu masaka tsinke, sai yaro yayi da gaske zai iya gano ahalinshi. Amman abun mamaki sai ji nayi an riƙe mun hannuna. A zabure na juyo mu kai ido huɗu da yarona Dauda. Farin cikin maƙil a zuchiyata, bakin na washe mishi. Shima bakin ya washe mini. "Innata sannunku da zuwa. Mummy ina wuni?" Yace da Habiba Bala. Hannu ta miƙa mishi, sai ya sakeni ya kama hannun nata. Allah sarki Habiba Bala a gaskiya Habiba Bala mutum ce guda gar da ɓari. Waje muka samu muka shinfiɗa ƙatuwar dadduma, muka baje plate da kulilin abincinmu, daga gefe kuma ga siyayyar da mu ka tawo mishi dashi. Abokanshi sai zuwa gaishe da Iyayen Dauda Naroro Shanono suke yi. Da sunan Baffana yake amfani kamar yadda nima sunana yake Tani Naroro Shanono. Masu karatu ina fatan baku mance ba Narani yace in Dauda ya haɗa sunanshi da nashi bai yafe ba? In kun man ce Shanono bata mance ba. Ada Da sunana yake Amfani Dauda Tani Naroro Shanono. To malamansu ne suka cire mai Tanin, dan a lokacin da aka cire sunana a cikin sunanshi, sai da yayi ciwon da dole makaranta ta dawo dashi gida, aka kula da lafiyarshi. Sai da nai ta rarrashinshi kana ya kwantar da hankalinshi, tare da mun alƙawarin komai daren daɗewa sai ya amsa wannan sunan. A ɗan zamana da fahimtar da nayi ma Dauda, yarone haziƙi mai nacin tsiya akan abinda yasa a gaba. Hakanne yasa ya zama tamkar zakara a makaranta, yana ƙoƙari sosai. Kuma yana da ƙulafacina, ko ince yana da kishina ainun, shi da Sani abun nasu tamkar gasa haka yake tafiya, ko dan su manya ne oho. Yaya Use tace. "Dauda anata girma, har ka kamo uwar taka a tsayi" Dariya yayi ya sosa kanshi kawai. Habiba Bala tace "Shanono yaronnan murmushinku iri ɗaya wallahi. Kinga can wajan Shanono zaki iya tuno ranar da muka daku a wajan lokacin muna makaranta? Lokacin kina kan karagar ƙwarƙwata." Dariya mu kai ta yi, harda ƙyaƙyatawa na dubi Habiba Bala nace. Allah ya isa Habiba Bala. Sai kace wani sarauta wai karaga" Itama tana Dariya tace. "To ai dukan akan mun shafa ma Siniya Zainab Abola ƙwarƙwatane fa. Kin tuna tana bacci muka je har ɗakinsu muka saka mata akai. Khadija Bakari kuma ta tona mana asiri. Shi kuma Malam Tanu kuɗin cizo muka tara guda shida, Halima Bawa ta je ta bayanshi kamar zata wuce ta saka mishi a rigarshi. Kai rayuwa kenan, Allah kar yayi abinda ba zai wuce ba" Abinci yaya Use ta zuba ma kowa, anaci ana nishaɗi. Dauda na samu gurbin karatu a jami'ar Bayero unibasiti. Ka taya ni da adda'a zanje in karanta fannin shari'a, ya soma burgenine sanadiyyar shari'ar da muka gabza da Hajiyayye " Dauda yace. "Ina miki fatan Alkhairi Innata. Allah yasa ki zama barister me ƙwato ma talakawa hakkinsu. Ki share hawayen marasa gata irinmu." Ɗib wajan yayi, na kasa cewa ameen, sha'anin Dauda na tsoratar dani. Shi ba yawan shekaru ba, shi ba wayewa ba sai hikima da tsarin zance kamar Kaila ne ya haifeshi. Habiba Bala ce ta kawar da zancan ta hanyar cewa. "Ni kuwa Hajiyayye tana nan abunta iya rigima kenan, yanzu dai an mayar da kai wajan tarbiyan yara. Ai fa, rigimarta ta koma kan Bilkisa gasa sosai take yi da'ita. Suna nan suna fama." Yaya Use tace. "Kaila ya game ginin da kika ce yanayi kuwa a gidan?" Nace. "Ya gama, wannan gini yaci kuɗi sosai yafi ko wanne ɓarayi cin kuɗi. Da halama amarya zaiyi ya sakata a ciki. Muna nan daku zaku ji" Mun jima muna fira, yaran ma Dauda ya kwashesu sun ɗan zaga. "Shanono. Ni shawarar da zan baki itace kar ki bari Kaila ya tauyeki ta hanyar dakushe miki burinki. Kinsan irin zaman da kike yi a gidan Kaila, yanzu duk matanshi mota suke murzawa banda ke. Hajiyayye ya buɗe mata shago tana caskar kuɗinta. Bilkisa dama da aikinta ya kwasota. Kar ki sake ki biye mishi, kije ki yi karatunki ki game fes, ki samu aiki kema ki shiga daga cikin sahun mata masu daukar albashi. Kinga sai dai ki haɗa kai da Bilkisa ba dai Hajiyayye ba. Kune zaku fi ajin Kaila. Wannan kallon da yake miki na ƙazama mabaraciya, marar galihu duk sai kiga ya kau. Ke Kaila da kanshi zai kawo kanshi gareki a lokacin da zai ganki hasken ilimi na haskawa a rayuwarki kin zama lauya. Karatun lauya ai karatune na manya. Domin lauyoyi karatu baya isarku, kullum a cikin bincike kuke da sanin dabarun makamar aikinku. Na kuma ji daɗi da kika amshi tayina. Zan biya miki komai da komai, tun daga kan rijistiretion, har zuwa kama miki ɗaki, da ɗan abincinki da sauransu. Akwai ƙawata a bayaron take, ƙila ku zauna ɗaki ɗaya, in dai ita kaɗaice a ɗakin sai ku zauna tare." Maganganun Habiba Bala sai suka sake zaburar dani har nake ganin babu gudu babu ja da baya akan maganar karatuna. Sai da la'asar tayi muka kama hanyar gida. Kai tsaye ma tasha Habiba Bala ta kaimu. Ita ta biya kuɗin motar, banda alkhairi da tayi ma Yaya Use da yaran. Ita dai bata gajiya da tallafata, Allah sarki masoyiya Habiba. Gaga_gaga sautin garawar rayuwa, rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Na gama hidimar rijistiretion, Habiba Bala ta nema mun ɗakin ƙawarta dake wajan makaranta, zamu zauna tare, bazawarace itama mai aure uku. Inata shirin makaranta, nice harda dinke _ɗinke, shopping da duk abinda zan buƙata a makaranta na tanadarma kaina. Ana jibi zan tafi na je gida domin yin sallama da su Inno. Duk wannan budurin fa Kaila baisan me nake ciki ba, jiya da daddare ya diro garin, ya dai kirawo Sani ya bashi manja ya kawo mana, iyakacin kyautar kenan itanma Bilkisa ce ta dameshi da ƙorafi. Yara na tafiya makatanta na nufi gida, Baffa kam bai kwana a gidan ba, shi da Habu. Innon ma a bakin ƙofa muka haɗu. "Ince dai lafiya ko? Dan duk randa na ganki a sanyaye sai gabana ya faɗi. Menene ba dai auren bane ya ƙare ko Tani? Ki rufa mana asiri ki yi zaman aure Tani. Jibi yanda kika canja, da ganinki kina cikin sukuni, ga arzikin Kaila ko wanne daƙiƙa ƙara burunƙasa yake yi." Katseta nayi da faɗin. Ni aurena bai mutu ba. Sallama nazo yi miki zan tafi Kano ƙaro karatu?" Idanu ta zare tace. "Da yawun wa, ko da yawuna kike son kice zaki tafi ni Inno? Tani kina cikin nutsuwarki kuwa, to dawa zaki bar yaran, shi kaila yaya zaki yi da aurenshi dake kanki? Kin dawo da maitar son karatunnan, kinsa ƙafa kina son shure musabbabin abinda ya rabaki da Aurenki na Farko ko? To bari kiji babu wani karatu da zaki je ƙarowa, wanda kika samu ma ɗaga hannu ki gode ma Allah. Kar ki sake Baffa ya ji wannan labarin, dan tsine miki zaiyi tsab ki kasa yin albarka. Inno ni sai yaushe zaki kama hannuna ki sa mun albarka, ko ki zaunar dani kiji damuwata ne. Inno daga ke har Baffa kunsan Kaila mafaka kawai ya bani. Aurenshi sunane kawai, amman shekara sama da shida ban sake taka ƙafa zuwa turakarshi ba. Bai nemi yasan daliliba. A matsayina na mace mai jini a jika ban taɓa yin ƙorafin hakan ba. Yarana da gobensu kaɗai nake dubawa. Hajiyayye yanzu haka ma'aikata sama da biyar ne suke aiki a ƙarƙashinta take biyansu albashi duk wata. Ga mota tana ja, jan rayuwa take yanda taso. Bilkisa tana aikinta kuma bai hanata zaman aure ba. Yanzu haka jita_jita nake ji a gari wai Kaila na gina mata asibiti. Inno ni sai yaushe zan zama kamar kowa ne, kefa uwace ya kamata ki tallafeni raunine a jikina limlib. " Maganganuna sun shiga Inno sosai. Ajjiyar zuchiya ta sauke. "Hakane da duk abinda kika faɗa gaskiya ne. Tani Allah ya baki nasara, in mijinki ya amince miki, nima na amince, ina miki fatan nasara tare da samun dace. Wannan batun karma ki tari Baffanku dashi, ki je ni zan yi mishi bayani in an kwana biyu. Sannan yaran wa zai kula miki dasu?. Yarinyar Yaya Use Hasiya ita zata zauna dasu, da naso mai aikin gidanmu ta kula dasu. To dana tuntuɓeta da batun sai ta ƙi amincewa. Shine Yaya Use tace Hasiya zata kular mun dasu." "To shikenan Allah yasa a dace." Daga haka mu kai sallama da Inno. Indo na tuƙata a keken guragun dana siya mata. Gidan Yaya Karime na soma zuwa nayi mata sallama. Daga bisani na je gidan Yaya Use na tawo da Hasiya. Gidan Sabira ne gida na ƙarshe daga nan muka nufo gida. Sabira tayi mun alƙawarin zata dinga zuwa duba mun yaran, in da hali ma zata ɗauki Salis ya dawo hannunta. Da daddare na gama ninke kayana tsab na rufe sabon akwatina mai ruwan goro. Sani ya dubeni. "Umma ji nake kamar in kika fita a gidan kamar ba zaki dawo ba. Amman inason kiyi karatu umma" Murmushin ƙarfin hali nayi mishi nace. "Duk juma'a da izinin Allah zan dinga zuwa. Ina Jos ina Kano. Ga Hasiya nan ku dai ku bi umarninta duk abinda tace muku kuyi. Banda ɗakko rigima a cikin gida. A gidannan duk kaine babba ko wanne yaro an sameshi ne bayan wanzuwarka. Wata rana kaine jagora a cikin gidannan. Sabida haka ka kwatanta adalci a tsakankanin ƙannenka da baku fito ɗaki ɗaya ba." Muna cikin wannan maganar muka jiyo shigowar Kaila babban falo. Ina zuwa bari in je in ma mahaifinku Sallama." Mayafina na zara na fita babban falon. A cukume na iske Kaila a hannun Bilkisa tana rantsuwar sai ya saketa tare da faɗin. "Na fi ƙarfin ka haɗa ni kishi da mai aikina. Dan cin Amana wato soyayya kuke yi da Shamwilar shi yasa take yi min gani_gani. Yau bazan kwana a gidannan ba wallahi. Ɗan iska mai biye_biye, wanda ya kasa tsaida idanshi akan matanshi kaɗai, ni zaka kawo ma kayan faɗar kishiya, kishiyarma ƴar aikin gidanka dan lalacewa.........✍🏻 Ina sake godiya a gareku masoyan ShanonoNA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 4 Ni kaina saida naji wani gingiringin. Da jin furucin Bilkisa. Kallon Kaila nayi ido a cikin ido, yana shaƙe a hannun Bilkisa, ba abun ya daketa kamar yadda ya saba mangareni ba, iyayenta su yo zuga domin jin dalili. Maganin biri karen maguzawa, nice ƙaramar katangar kaila mai daɗin tsallaka. Bilkisa tayi bigi bigi da wasu akwatuna da nake tunanin na dannar ƙirjine. Ana haka Hajiyayye ta fito da tulelen cikinta tana turawa. Da Bilkisa ta daka wani ihu, sai ga Hindatu a guje ta shigo. "Meke faruwa anan kuma? Baby kai kuma kana tsaye kana kallonta ta cukumeka? Cewar Hajiyayye tana magana tana farfari da idanu Dariya nayi kawai. Bilkisa tace. "Malama babu ruwanki. Kaila ka sake ni nace, ko in ƙone gidannan uban kowa ya ƙone" "Kaila, Gwanda ta ruɓe kenan, ikon Allah na kwance ya faɗi. Hajiyayye ta sake fesama Bilkisa magana. "Daka auro Shamwila ina cikin gidannan na gwammaci mutuwa ta ɗaukeni." Hajiyayye jin an ambaci Shamwila ta soma salati, cikin rishin kuka. "Kaila kaji kunya Wallahi, na jima ina zarginka yanda ka damu da Shamwila, baka da aiki bini _bini sai fita tsakar gida. Ashe zamewa kake kaje wajenta, Wallahi nima bazan zauna ba. Ke kuma ai duk ke kika jawo mana matsiyaciya, ke uwar son jiki, turakar miji ma sai an gyara miki, to gashi har mijin take garewa ashe, dan nayi imani da Allah Kaila ya gama da yarinyarnan tare yake yi mana rabon kwana ƙila ma kasonta ya fi ƙarfin namu" Tana ƙarashe faɗar hakan kaila ya fincike rigarshi a hannun Bilkisa. "Babu wacce na riƙe nace sai tayi zaman gidana. Akan Shamwila zan iya rabuwa da kowa nawa. Wallahi ko Rammai bata isa ta hanani auren Shamwila ba. Itace wayewarta tayi daidai duk cikinku babu wacce zata iya ɗaukeni kamar yadda Shamwila zata yi. Ku bani waje dallah, ƴan iska mahaukata." Gaga_gaga ya tawo zai bangajeni, ba shiri na kauce. Lallai sha'anin maza akan mata abun azimunne, banyi tunanin akwai macen da zata shiga rayuwar Kaila ta ture matsayina ba, kamar yadda Hajiyayye ta shigo ta ture matsayina itama tunaninta babu macen da zata ture ta. Cikin ikon Allah sai ga Bilkisa. Ni na ɗauka itace ƙurewar daraja a idanun Kaila, ashe ƴar aikinta ce cinyewar Kaila. Ni al'amin Kaila da matanshi baya gabana, ci gaban rayuwata da kafuwar yarana shine burina. Juyawa nayi da sauri na fita tsakar gidan. A bakin ƙofar ɗakin Shamwila na hango Kaila. Yana ganina yayi firgigit ya tawo, sai wani muzurai yake yi mini. Kaila inaso mu yi magana " "Dakata Shanono kar ki sake in ji ƙazamin bakin ki a cikin wannan maganar. Banga ubanda ya isa ya hanani wannan auren ba. Kin tawo faram_faram a tunaninki kina da darajane a wajena ko me? Zaman ƙaddara. Ni dai nayi nadamar auren bagidajiya kamarki, jibakki wai a hakan gani kike ke kin kile ko? Ya isheka haka, kullum aikin ka kenan nadamar aurena, yau turarka ta kaini bango Kaila. Shin me yasa kaketa riƙe ijiyar auren ƙaddara na tursasa maka ne, ko kana tunanin in bana zaune a gidanka mutuwa zanyi? Nice nake zaman aure na ƙaddara da kai Kaila. Kaila kaci amanar ƙauna ka zalunci alƙawari. Ka mance sanda kake a cikin gareji cikin ƙazantar baƙin mai? Duk taƙamarka da homarka dai Tani daka raina itace silar fito da sunanka, domin itace sila kuma matattakalar arzikinka, matattakalar samun nutsuwa da sauyi a cikin rayuwarka. Kai butulu ne Kaila. Ka zalunci baiwar da ta yarda da ........" Tas naji saukar mari zazzafa a kan kuncina. Da sauri na dafe kuncina na saki kuka mai motsa rai, dan yau na kai bango, bana gudun duk abinda zai je ya zo. Ya daɗe bai ma zo ba. Cikin kumfar baki yace. "Ke baki isa ki mun gori ba. A bazawara karuwa na aureki mai yawo kwararo_kwararo ƴan cirani da kanukawa suna hutawa dake, suna baki kuɗi. Tunda bara da tumasanci shi uwarki da ubanki suka koya miki. Rammai babu yadda bata yi dani ba dan kar in aureki amman na ƙeƙashe na aureki, na haɗa jini da tsiya, mitsitaciya....." Tas na zuba mishi mari, kafin ya fita a cikin mamaki na sake zuba mishi mari, wallahi sai da ya kifa. Bai san sanda ya danna ihu ba. A guje Hajiyayye da Hindatu suka fito, Bilkisa kuwa ko oho. Mamaki da tsorona ya hana Kaila iya furta kalma, sai ajjiyar zuchiya yake saukewa. Ni kuma a yanda nake ji banƙi in dira a wuyanshi in ta dukan ɗan kutumar uba ba. "Kije na sake ki sati biyu. Ki tattare kayanki ki bar mun gidana yau ba sai gobe ba. Aurena dake ya ƙare har abada, aje a auri miji na shida" Ji nayi kamar ya buga mun guduma a maɗigata. Bansan yanda zan musalta muku zafi da raɗaɗin dake cikin kalmar saki ba. Ji nayi kamar ya watsa mun ruwan dalma. Take na soma haɗiɗiyar zuchiya, musamman dana tuno ƳaƳana in na tafi na barsu rayuwarsu zata iya tarwatsewa ƙila fiye da yanda rayuwar Dauda ta kusan nakashewa. Gashi ina ji Bilkisa na faɗin ita tafiya gidansu ma zata yi, to Hajiyayye ce zata kular mun da yara in na tsallakesu. Hajiyayyen da bata ƙi mu mutu mu duka ba. Hajiyayye ce ta buga tsaki ta koma ciki, Hindatu kanta naga rauni a kan fuskarta. Ni kuwa ina ƙame kamar takadda a wajan. Bilkisa ce ta fito tiri_tiri da akwatuna manya. Ciccike da kaya tana jaye da hannun Fatima. A bayan motarta ta jefa Fatima, kafin ta shige motarta, Kaila ya isa a zabure yana ƙoƙarin hanata tafiya. Hmmm duk wannan abun da akeyi ashe Shamwila tana bayanmu a gaban idanunta komai yake wakana. Murmushi tayi mun irin na mugunta. In dai Kaila ne gata gashi, daya ci moriyarta zai watsar da'ita a kwandon shara, ayi dai mu gani. Bana ko gani na shiga ɗakina. Yaran sai wasansu suke yi Hasiya na musu tatsuniya. Zamewa nayi na yi ciki. A kan gado na faɗa na saki kuka mai ciwo. Kashedin Inno da Baffa ya dinga yawo a kaina, shikenan tawa ta ƙare, babu mai yarda dani, nasan Inno zata yi tunanin sabida batun karatunane Kaila ya sake yi. Ko Qur'ani zan haɗiye in dinga aman surori babu mai yarda dani. Ni ba Kaila nake so ba, yarana nake so, gobensu nake tunani, yaya zasu rayu babu ni tare dasu, kuma bacin ba mutuwa nayi ba? Gashi yarana dani kaɗai suka saba, a gabana Hajiyayye ta kusan hallaka mun Ɗa, haka ma Hindatu ta ƙona mun ɗiya ina gani, haka ina cikin gidan kaila ke ma yarana dukan shan gishiri, yau in na tsallake na tafi yaya makomar yarana?" "Shanono ke shanono. Ki tattare inaki inaki ki zo ki fice mun daga gidana, babu aure a tsakaninmu baki isa ki kwana mun a gida ba. Harni zaki sa hannu ki mara, ko da yake ai kun saba cukume maza, da ƴaƴan jagora da ƴan tasha bansan wa yafi dama_dama ba" Tun kaila na yi kamar wasa, sai abu ya rikiɗe zuwa zagin iyaye da cin zarafinsu. Hakan bai mishi ba sai gashi ya shigo uwar ɗakina a fusace. Da sauri na miƙe tsaye, hannuna riƙe da akwati da ƙatuwar ledar provision na makarantana. "Zo ki fice kuma kar ki kuma tako ƙafarki da sunan zuwa ganin yara. Gidanma siyarwa zanyi in bar garin, ba dan komai ba sai dan sabida fitina da nacin iyayenki, kar su zo suita mun magiya da suntiri. Zo ki fice maza umma ta gaida assha." Ji nake kamar in dira a wuyanshi, haka nake ji. Idanuna take suka kafe, hawaye ya dena zuba. Yarana kuwa ina jiyo sautikan kukansu. Raɓawa ta gefenshi nayi na fito falon. Ina ganinsu na karaya, da sauri Sani yazo ya rungumeni tsam. Idanu na runtse inaji kaina na tashi sama. "Baba dan Allah ka bar mana ummanmu. Kayi haƙuri." Yaran dukkansu suka tsugunna a gaban kaila suna kuka, abun mamaki harda Salis Auta. Kaila yayi tsam yana kallonsu, jikinshi naga halama ya mace mus, ruɗani ne tare dashi. Hasiya zo ki daukar mun kayana muje" Na faɗa a sanyaye zuchiyata na harbawa. Da sauri Hasiya ta zo ledar hannuna ta ɗaura a kanta, akwatin kuma ta ja ta fita. Nasa ƙafa ta ɗaya a waje ɗayar a ciki, sai naji Sani ya saki kuka mai sauti yace. "Baba mun shiga uku zata tafi, dan Allah ka ce ta dawo. Ina ɗaga ɗayar ƙafar naji Kaila ya ambaci sunana cikin muryar nadama. "Shanono......." Meye ra'ayinku akan Shanono, kuna ga ta tafi ta bar yaranta, ko ta ci gaba da zaman haƙuri? Kar ku mance da abinda ya faru da Dauda a sakamakon barinshi da tayi a gaban mahaifinshi. Nagode da haƙurin bin labarin, ina ganin saƙonninku masoya ina godiya marar iyaka. Sannan inason shaida muku sai Monday zan ci gaba da post, sakamakon rashin lafiya dake damuna, ina barar adda'ar masoya. GAWURTATTU UKU 👠👠👠 1 _KWAI A BAKA_ *(UMMU AFFAN)* 2 _ZULFA_ *(UMMU MAHEER MISS GREEN)* 3 _NA FAƊO DAGA BENE..._ _NA ZARCE RIJIYA_ *(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)* _Littafi ɗaya; 400_ _Littafi biyu; 800_ _Littafi uku; 1000_ Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 0037219728 Fatima Rabi'u Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻 2k kacal Sati biyu 3k ne Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama 10k kacal. Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 5 Tsigar jikina sai da ta tashi. Amma wallahi ko me zai faɗa mun bazan dawo ba. Gidansu Inno ɗinma ba zuwa zanyi ba, dan nasan Baffa ka iya illatani a banza, cikin dakiyar zuchiya nace. Saki ne dai ka sake ni, ƙila ka ɗauka mutuwa zanyi ko? Ga yaran ga gidanka duk na bar maka, komai daren daɗewa yarana zasu tako su zo har inda nake, na fita a rayuwarka har abada, ko da kaine namiji tilo daya rage a duniya."Fuu na fice da sauri ko waige bana yi, dan muddin dai na juya, kaifin idanun yarana bazai barni ƙwatar rayuwata da ƴancina na ɗiya mace ba. A baya ma dana zauna jahilci ne ya zaunar dani Kaila yaita gasa mun aya a hannuna. Amman a yanzu Alhamdulillah duk da ban sauke Qur'ani ba amman nayi nisa sosai, kuma na haddace hadisai da dama. A makaranta na san yaya Aure yake, da zaman Aure a musulunci, anan naji yanda Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama yayi rayuwar aure da matayenshi. Ni a al'adance kaɗai nasan aure, na kuma gane al'adu mun bari sun yi fintikau a cikin lammuran Malam bahaushe. Bance duka ba, domin akwai da dama masu aiki da ilimin muhammadiyya, da dama kuma Al'adunsu sune kan gaba akan komai bama auren ba. Dana fito a cikin gidan sai na ɗaga kai na kalli gidan, domin na barshi har abada, in yarana sun kawo ƙarfi zasu neme ni a duk inda nake, amman ni babu wanda zan sake waiwaya ya'isa haka kuma. Bana ko gani, jefa ƙafafuna kawai nake yi. Ina baya Hasiya tana gaba da kaya tiri tiri. Kai tsaye gidan Yaya Use muka nufa. Har sun rufe gidansu, Yaya Use ce tazo ta buɗe mana, dan Baban yara sana'arshi ta dare ne shima. "Lafiya Tani mutuwar Aure a karo na biyar ko?" E Yaya Use " Yanda taji muryata gadagau ne yasa ta bamu hanya muka shiga daga ciki. A ɗakinta muka keɓe, ko wanne gida da wuta a layin, amman su basu da'ita. "Tani yanzu akan karatun naki ne Kaila ya gwammaci ya sakeki, sai da ya gama kwararraɓa miki rayuwa, yaranshi dashi suka tsotse ƙuruciyarki. Shin kin mance da kashedin Inno da furucin Baffa ne? Ni da kin nemi shawarata da zance miki ki haƙuri dakaratun kiyi zaman aurenki, ko dan yaranki. A baya ke kinga illar barin yara a tsakar gida, yanda hakan ya shafi babban ɗanki, da ace bamu je garinnan ba da mutuwa Dauda zaiyi. Can kuwa yaran har da mata duk kika tsallake kika bari? Tani kiyi haƙuri, sannan kiyi tunani me kyau, kar ki zo ki aikata aikin dana sani akan rayuwar yaranki, kar ki fifita karatunki akan rayuwar yaranki. Kinga dai mu irin rayuwar da mu ka yi a gaban su Inno, rayuwar gantali da rashin zuchiya. Ki kwanta zuwa gobe da safe ƙila kin yanke hukuncin da kike gani yayi miki dai_dai. Gado ta hau ta yi baccinta. Ni kuwa a wajan na takure ina kukan baƙin ciki, haƙiƙa inason rayuwa da yarana sosai. Amman kaila ba namijin zama bane, kuma gashi da ruwan ido, da maitar mata. Allah ya gani inason karatuna, domin in taimaki ƴan uwana harda dangina. Iyayena suna buƙatar tallafi, haka zalika ƴan uwana. Meye banyi ma Kaila ba, ai nayi mishi riga da wando, ni na zame mishi matar rufin asiri, da dukiyata yake wadaƙa da ninƙaya, da dukiyar tawa ya wulaƙantani, da dukiyar tawa yaketa auren mata, da dukiyar tawa ɗakin da zamu zauna ni da yara sai da kishiyoyi suka gama zaɓe aka bani wanda ya rage. Bayan dani aka yi hidimar ginin da komai. Meye ban gani ba meye ba'ayi mini ba? Ba Kaila kaɗai ba duk inda naje da zummar zaman aure sai anyi mun korar wulaƙanci, shin auren dole ne? Ko ɗaya, in nace na gaji haka zan zauna in yi rayuwa ni kaɗai akwai wanda ya isa ya ƙalubalanceni ne? Babu shi ba'a yishi ba. Damuwa ta dameni a wannan baƙin daren haka na kwana cur a zaune, tsabar bugawar da kaina yayi bansan safiya tayi ba, har sai da hayaniyar yara ta shiga kara kaina a kunnuwana. Alwala na je na ɗauro kaina kamar zai tarwatse da ciwo, wani ƙududun abu ya riƙe mun maƙoshina, bai wuce ba, bai fito ba, sai nake jin ina jan munfashi da taurin gaske. Bayan na idar da sallah, Yaya Use ta zauna a gabana. "Me ake ciki, wanne hukunci kika yanke ma kanki. Mu je in mayar dake ɗakin ki asirinmu a rufe, ko kuwa kin haƙura da yaran naki?" Na haƙura dasu, bana ma ƙaunar sanyasu a idanuna. Yaya Use ni zan tafi in da rabo zamu gana wata rana. Ki roƙa mun gafara a wajan Baffa da Inno. Zan neme ku bayan wasu shekaru in rayuwata bata tsaya ba. Yara ko da nake tare dasu, dani da su Allah ke riƙe damu. Ko babu ni zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru, ana shawo sai yayi wannan caran. Duk suna zuwa sana'a ko basu samu ilimi ba, zasu samu aikin hannu na dogaro da kai. Dauda in ya samu Habiba zata kwatanta mishi taimakon ƴan uwanshi. Zan tafi ko dan in kwatantama matan da suke zaman aure domin yaransu, daga ƙarshe ciwon zuchiya ko hawan jini yayi ajalinsu, yaran da basa son bari kinga a ƙarshe dole sun barsu" Ƙanƙameni Yaya Use tayi tana kuka. "A'a Tani kar ki bar gaban iyaye da ƴan uwa. Kima Allah ki zauna anan gidan, zan barki ki ci gaba da karatunki." Fur naƙi, dole Yaya Use ta haƙura ta barni. Kai tsaye na nufi Bauchi wajan Habiba Bala. Ita ta kwantar mun da hankalina tasa nutsuwa ta saukar mun. Inna tuno yarana sai faɗuwar gaba, sai dai Alhamdulillah yanzu na iya addu'o'i da dama, duk wacce tazo bakina biyata nake yi. Nice harda wanka, da cin abinci. Amman dana rufe idanu yarana sai su shiga yi mun gizo a idanuna. Sai dai in share hawayen dake sunturi a idanuna kawai." Kaila: Jigum yayi a tsaye a tsakar ɗakin Shanono. Yana jiyo sautin kukan yaranta, ya kasa cewa komai, ya kasa fita a ɗakin ma. Zama yayi a kujera ya tusa yaran a gaba, tausayinsu na shigarshi. Sani na ganin haka ya kwashe ƙannenshi suka shige ɗaki abinsu harda rufo ƙofar ɗakin. Da idanu Kaila ya bi sani. Yafi awa ɗaya a ɗakin shanono yayi kurum ya rasa meke yi mai daɗi. Da ƙyar ya ja ƙafarshi ya fito babban falo. Hajiyayye ya tarar jaye da akwatuna ga uban ciki. Yana tsaye ta gama kwashe komatsen suturunta tsaf. Ta dure mishi yaranshi a gabanshi. "Gasu Shamwila ta haɗa ta kula dasu baki ɗaya. Nima banci ta zama ba, kaga sai kuci amarci da kyau babu mai saka muku idanu. Baice komai ba ta gama fitsararta ta fice, hannun yaran ya kama ya musu nuni da su shiga ɗakin Shanono. Shi kuma ya wuce turakarshi. Amman me Kaila sai ya kasa tsaye ya kasa zaune. Daya rufe idanu Shanono kawai yake gani. Take ƙwaƙwalwarshi ta shiga aikin tariyo mishi irin so da yardar da Shanono ta damƙa mishi, da irin gudun fishinshi da take yi. Kab duniya sai yanzu ya gane Shanono bata da tamka a cikin duniyarshi. Hawayene masu zafi suka gangaro mishi a kumatunshi. Gabaki ɗaya yayi laushi, har yake jin tamkar wani ɓari na cikin jikinshi ne ya mace. Kaila baisan awowi nawa ya kwashe a tsaye goye da hannayenshi ba. A tsayen Shamwila ta sameshi, tana shigowa ya ƙura mata idanu, bai yi aune ba ta zame doguwar rigar data sako, daga ita sai fatarta fara tas. A wannan dare sun gurje juna sosai ita da Kaila, dan a turakarshi ma ta kwana. Duk da wannan lamari Kaila bai bar tunanin Shanono ba. A gurguje bayan misalin bakwai na safe ya sake wanka. Ya je ya samu Hindatu ya bata kuɗi yace tai ma yaran abincin kari zai je ya dawo. Kai tsaye wajan barar Baffa yaje ya sameshi a bakin masallaci. "Kaila kaine da safe haka?" "Wallahi nine Baffa nayi tunanin kana wajan bara ne shi yasa ma nazo nan kai tsaye." Baffa yace. "Ai anan na kwana, Inno ma yanzu ta tafi masallacin ƴan taya wajan tata barar duk anan muka kwana. Ince dai lafiya ko?" Kaila yayi shiru, ya fahimci Shanono bata je gida ba, ko kuma su basu san tana gidan ba. Sadaka yaba Baffa a gurguje ya nufi gidansu Shanono. Wayam, kai tsaye ya nufi gidan Yaya Karime nan ma wayam. A gidan Yaya Use ya samu labarin a gidan ta kwana, amman ta tafi da safennan, kuma ba'asan inda ta nufa ba. Kaila gabaki ɗaya ya ruɗe sosai. Yana hanyar komawa gida mahaifin Ɗanyan gwal ya kirayi wayarshi akan yazo suna da zama dashi a Zaria. Yana shiga gida, ya shiga falon ya tarar da Salis sai kuka yake yi Sani da Amina na rarrashinshi. Sameera ma ɗiyar Hajiyayye hawaye take matsewa, gashi duk sun zubar da taliya a kan kafet, manja duk ya ɓata wajen. Wayarshi ce ta ci gaba da ruri. Mahaifin Hajiyayye ne, yana ɗauka yaji zancan irin na mahaifin Ɗanyan gwal ne. Take zazzaɓi ya rufe Kaila yama rasa inda zai dafa ya samu sassauci. Gidansu Hajiyayyen na soma zuwa, nan ya tarar da mahaifinta, da kishiyoyin mahaifiyarta, da Yaya Tabizaro, da Anas, sai Hajiyayye a zaune a gabansu kamar mai roƙon gafara, sai kuka take shirga. Kaila ya nemi waje ya zauna, a kan kujera, bai gaishe da kowa ba haka zalika bai nemi izinin zama a wajan kowa ba. Mahaifin Hajiyayye yace. "Kiyi ma mutane shiru, yau ga mutuniyar banza, bini bini sai ki kwaso kaya ki dawo gida ko kunya bakya ji, duk rufin asirin da kike ciki, kece da ƙaton shago harda motar hawa. Uwar me akeci a gidan da kike son dawowa? Wallahi daga yau sai yau muddin kika kuma fitowa daga ɗakin ki, sai kin sha mamakina mutuniyar banza, dukan da kika sha ba komai bane akan wanda zaki sha in kika dawo." Ya dawo wajan Kaila. "Na dawo gareka Kaila. Ka sake haƙuri da wannan sakarar yarinyar, shirme ne yake damunta kasan mata hankali bai ishesu ba. Amman in ta kuma zuwa kai kan ka sai ka tausaya ma halin da zata shiga. Ka ɗauki matarka ku tafi gida" Da sauri Hajiyayye tace. "Baba ƴar aikin kishiyata fa yake shirin aure, dukkansu matan gidan ko wacce ma ta kama gabanta, sai ni ce zan koma?" Ai ƙarshe a guje Hajiyayye ta fita har ƙofar gida, kakafab_kakafab Mahaifinta ya shiga dukanta ga ciki, Kaila da Anas ne sukai ta bashi haƙuri. Babu shiri Hajiyayye ta shige motar Kaila suka koma gida. Amman sai zazzageshi take yi suna tafe, shi kuwa ba ita bace a gabanshi tunani yake yi ya za'ayi ya ga Shanono? Shine abinda ke gabanshi. A ƙofar gida ya sauketa har ya juya ya kirayi sunanta. "Ki yi girki harda su Sani, a basu su ci su ƙoshi kar a sake a takura musu" Wani banzan kallo ta watsa mishi, ta ja dogon tsaki ta yi shigewarta ciki. Ya jima a ƙofar gidan ma, ya rasa ina zai dosa, Isa abokinshi ya nema suna tafe a hanyar Zaria ne yake sanar mishi abinda ke faruwa a gidan nashi. "Ka tabka babban kuskure wallahi Kaila. Ai rabuwa da uwar ƴaƴa tashin hankali ne, ballantana Tani da ta ɗago da darajarka kayi suna. Jibeka a yau, jibi motar da kake hawa, kaya okutenti kake sawa, kana da biranj kusan a garuruwa biyar yanzu. Ga gidan ka mallaka, ga tabkeken fili da kake ginin gidan sama. Kuma ka sani duk wannan ɗaukakar ka sameta ne silar Tani. Ni Isa bazan mance lokacin da Shanono take zuwa har garejinmu ta bamu kuɗin abinci ba. Lokuta da dama a bakin kwata take samun mu, rana da ƙishin ruwa na cinmu. Muna hangota muke ajjiyar zuchiya. Kaila Tani mutum ce harda ɓari, ka yaudareta ka cutar mata da rayuwarta ka ɓata mata lokaci a banza da wofi, da kasan sakinta zaka yi, da ka shina ka saketa tuni ai. Wallahil ƙudrat da zan ga Tani aureta zanyi in wanketa fes mu yi zaman mu" Wani mugun kallo Kaila ya watsa mishi, ba shiri ya haɗiye maganar, dan dama suɓutar bakine. Kaila idanuwanshi suka kaɗa su kai jawur, hawaye suka cika guraben idanun tab, daya tuno da soyayyar da Tani ta nuna mishi da irin sadaukarwar da tayi mishi, taƙi ɗan uwanta sabida shi. Yau ga abinda yayi mata a matsayin sakayya. Hawayene suka gangaro a kumatunshi, bai san sanda ya fashe da kuka ba. Ba shiri ya sauka daga titi, ya haɗe kanshi da sitiyari ya dinga rera kuka kamar majnun. Isa ne ya amshi tuƙin zuwa Zari'a, anan Zaria sun ga wulaƙanci sosai, dan mahaifin Bilkisa kafewa yayi akan sai Kaila ya sakar mishi ƴa. Isa sai haƙuri yake bayarwa. Tas mahaifin Bilkisa ya dinga zagin kwaɗayi da rashin ta'idon Kaila. Hakan duk bai isheshi ba yace su fice mai a gida sai ya sake nemanshi tukunna. Sun so ganin Fatima, ko uwar Fatiman amman basu samu damar hakan ba. Rana zafi inuwa ƙuna. Kaila duk in da yasan zai samu Shanono ya karaɗe, shine har gidan Habiba Bala, amman babu labari. Ko bacci baya iya samu ishasshe sam. Yaran Shanono kuwa wani irin ji dasu yake yi, dan kullum sai sun yi rikici da Hajiyayye a kansu, baya son ko ƙula ya taɓa yaran, wani irin so yake musu marar musaltuwa, har mamakin kanshi yake yi, Sani kuwa daya ga shigowar uban yake haɗe kan ƙannenshi su koma ɗaki sum_sum, hakan ba ƙaramin dafa Kaila yake yi ba. Daga ƙarshe da Hajiyayye ta ƙi kulawa dasu sai ya ɗaukar musu ƴar aiki mai kula mai dasu, yaci gaba da ɗaukar nauyin dake rataye a wuyanshi nasu. Yaran fur basa ƙaunar ganinshi. Dan ko dariya suke yi, yana shigowa zasu gimtse barin ma Sani da yake ji kamar ya kashe uban nasu, Kaila kuwa kullum a cikin siyo musu sabbin suturu yake ko zasu ji sanyi. Rayuwa kenan Allah me yin yanda yaso. Ana cikin wannan yanayi aka ɗaura auren Kaila da Shamwila an yi shagali ba ɗan kaɗan ba. Sai dai babu zumuɗin angwaye tattare da Kaila. Ranar da Amarya ta tare a sabon ɓarayinta ma, kulle kanshi yayi a turaka, ya kasa zaune ya kasa tsaye. Lamarin Shanono yana giirgizashi ainun..... GAWURTATTU UKU 👠👠👠 1 _KWAI A BAKA_ *(UMMU AFFAN)* 2 _ZULFA_ *(UMMU MAHEER MISS GREEN)* 3 _NA FAƊO DAGA BENE..._ _NA ZARCE RIJIYA_ *(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)* _Littafi ɗaya; 400_ _Littafi biyu; 800_ _Littafi uku; 1000_ Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 0037219728 Fatima Rabi'u Sunusi StanbicIBTC Bank Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 08104335144 Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻 08104335144 *GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻 08104335144 07068606171 08179523215 Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻 2k kacal Sati biyu 3k ne Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama 10k kacal. Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻..NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU Assalamu alaikum masoyana, ina mai godiya q gareku, jikina da sauƙi babu laifi. Amman kuimun afuwa kunsan sha'ani na ido sai ana yi ana lallaɓawa. Ba lallai bane in ringa posting kullum ba, kuimun afuwa, idon ya matsa mun sosai. LAMBA TA 6 Har zuwa wannan lokacin Bilkisa tana Zaria tace ita fa ba zata dawo ba. Bata ga kuma wanda zai sa ta dawo ba. Ya aiko mata takaddarta ta gaji da auren ita ba zata yi kishi da ƴar aikinta ba. Shi kuma Kaila yace taci ƙarya ta kwana da yinwa. Ya faɗa mata bazai sake karambanin sakin mace ba a rayuwarshi. Haka dai lamarin gidan Kaila al'mura suke ta gudana. Sani, da Sulaiman da Shafi'i ya turasu makarantar kwana a Kano MAI TAMA SULE SAYENS SCHOOL GAYA" su kuma matan suka ci gaba da karatu a gabanshi, kuma iya bakin ƙoƙarinshi yana kulawa dasu, dan mai aikin daya ɗaukar musu su kaɗai take yi ma Hidima. Amman har zuwa wannan lokacin basu sake dashi ba. Ko ziyara ya kaima su Sani a makaranta basa ko farin cikin ganinshi. Dariyarsu ma daya gani a wani ziyara da ya kai musu dan sunga Yaya Karime ne, sai su kai farin ciki, tare da kukan takaicin rashin Ummansu da babu ko ɗuriyarta, a wannan rana hankalin Kaila ya kuma tashi ainun. Sabira da Abban Mustapha suna kaima su Sani ziyara, haka ma Habiba Bala da Dauda suna zuwa dubasu. Sai dai fa Dauda da kuka kullum suke rabuwa da ƙannen nashi. Dauda an girma yanzu yana ATBU anan yake karatu ɓangaren ilimin injiniyanci. Kuma yana da shagon ɗinkin kayan maza ɗinkin zamani, duk sanda zasu je Gaya kai ma su Sani ziyara kayan provision cikin Ghana most go yake dire musu. Duk abinda ya samu tanadi yake ma ƴan uwan nashi, domin yana gani shi suke kallo a makwafin uwa da uba. Su Sani kuwa ko sun yi hutu basa ƙaunar zaman gidan mahaifinsu, sabida takura da hantarar da suke fuskanta a wajan Shamwila a hakanma ba ƙaramin taka mata birki Kaila yake yi ba, Su kansu su Amina cikin matsatsi suke, Hajiyayye kanta bata da damar shan ruwa cikin salama, mulkar kowa Shamwila take yi a cikin gidan. Sai abunda ta zana dashi ake aiki dole. Kaila ba mazauni bane, hatta kuɗin kayan abinci ya dawo hannun Shamwila, keyn store a hannunta yake amman banda kuɗin abincin su Sani, Hajiyayye sai ta jaye jikinta ta koma gefe tabi sahun Shanono ada, taci gaba da ɗaukar nauyin kanta dana yaranta. Motar da take hawa Shamwila ba tai sati ba a gidan tasa Kaila ya kwace motat. Hatta shagon da take gadara dashi, ba ko da yaushe Kaila ke barinta fita ba. Kuma duk munafurcin Shamwila ne. Hajiyayye dai tana zaune ne a gidan dan babu yanda zata yi, kuma ko ta koma gida mahaifinta bazai amsheta ba. Sannan al'ummar Hausawa ba zasu karɓeta hannu bibbiyu a matsayin bazawaraba. Wannan dalilin yasa dole take zaune, gashi sai kwatso yara take yi, kafin ta yaye ta haihu, sai ga Hajiyayye na fama da zarnin fitsari, da ƙiriniyar yara. Hidimar yara yasa ta zama kamar mahaukaciya kawai. Hindatu kuwa nata ido ne, dan ko ga maciji basa yi da Hajiyayye. Lokacin da Hajiyayye ludayinta yake kan dawo, babu irin wulaƙancin da ba tai ma Hindatu ba har goranta mata take yi, wai Amadudu yaƙi yin zuchiya shima ya gina musu nasu gidan. Tunda aka aureta a cin alfarma suke. Ranar dambe su kai a tsakar gidannan babu wanda ya raba su, sai da suka gaji suka bari. Tun wannan lokacin suka dena magana. Da duniya ta saki Hajiyayye taso su dawo halaƙa da Hindatu, ita kuma ta nuna mata babu wannan ƙofar. Ta ɓangaren su Inno kuwa, sai da akafi wata da sakin Shanono sannan ranar Inno ta tutsiye Yaya Use a wajan bara tace. "Use wato dake za'a haɗa baki a rufe mu bai_ bai ko? Ashe mitsiyaciyar yarinyar nan kashe auren nata tayi ta zaɓi karatun banza akan tai ma Baffa biyayya? Sani ya sanar dani wata guda kenan Tani bata gidan mijinta. Bama asan inda take ba. Shi kanshi Kailan ya yi sunturin nemanta bama asan inda ta tafi ba" Yaya Use tayi tsilli_tsilli, cikin rawar murya taso labarta ma Inno abunda ya faru. Nan ta hauta da zagi harda yi mata dundu a gadon bayanta. "Ai shikenan ta faru ta ƙare Tani ta kashe aurenta na biyar, ta watsar ta yara tabi uwa Duniya. Baffa kuma ya kwashe ma rayuwarta albarka, abinda na guda kenan. Ranar ko rintsawa na kasa yi wallahi, sabida irin tsinuwar da Baffa ya dinga narka ma Tani bazai bari taga Haske ba. Amman ai ita ta jama kanta, Allah ya kyauta, ni ban yi mata baki ba na yi mata uzuri, wata rana Tani zata neme mu." Dole haka Use ta ja bakinta ta tsuke ta bar su Inno akan tunaninsu. Dan tayi imani watarana zasu so ganin Tani, ko muryarta sai sun so ji. BAYAN WASU SHEKARU MASU DAMA. BARISTA SHANONO: Ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas kawai kake jin ƙaran takalmina mai tsini daga cikin kotu. Sanye nake cikin ɓaƙaƙen kaya irin na lauyoyi. Farar riga mai kwalace a jikina, sai baƙin sitiret skirt ɗina irin na ƴan gayu, kaina saye da ɗan ƙaramin hijabi gayu fari, sai hular lauyoyi dake kan nawa, kafaduna sagale da rigar shari'a wacce take iyakar cinyata. Takalmi da jakata fararene sol masu dan banzan tsada, ga takalmin da tsinin gaske, sai kwas_ƙwas kake ji duk inda na wuce, sai busa ƙamshin ni'imtacciyar Humra nake yi ta asalin matan Kanuri wanda nake siya a wajan Mrs Bukhari gidan ƙamshi Duk wanda ya shaƙi ƙamshina yasan turaren na manyan mata ne irinmu, shi yasa bana wasa da wannan haɗi na musamman, tsadarshi bata mun tsada sam, domin ƙamshinshi da riƙe fata da kaya ya kai a bata lambar yabo. ( Ga masu buƙata su tuntuɓeni) . Alhamdulillah ayau na kawo ƙarshen kes ɗin Dattijon da yaima yarinya ƴar kimanin shekara goma fyaɗe. Na tsaya tsaiwar daka cikin ƙwarewar aiki da sanin makamar bincike, har sai da nakai lauyan wannan Dattijo ƙasa. A yau kotu ta yanke mishi hukuncin zaman gidan kaso na wasu shekaru, tare da cin shi tarar kuɗaɗe masu yawa, wanda za aci gaba da kulawa da lafiyar yarinyar. Iska na fesar daga bakina, ina tafe ɗas_ɗas kamar ɗawisu har zuwa bakin titi domin taran abun hawa zuwa chamba. Hannu na sa ma mai ɗan sahun ya tsaya. Kabuga zaka kaini malam" Shiga nayi na zauna, idanuna da suke saye cikin farin tabarau mai mugun kyau, sai kallon titi nake yi, zuchiyata fal tunani da kewar yarana. Wayata na zaro, na kutsa cikin ma'ajjiyar hotuna, na shiga kallon yarana ɗaya bayan ɗaya. Take farin ciki ya kamani, na shiga murmushi idanuna cike tab da ruwan Hawaye. Wannan tunanin shine abincina tsawon wannan lokaci, ban taɓa dena tunaninsu ba, zuchiyata tana bugawane tare da sansu da kewarsu tsantsa. A dai_dai Kabuga na sauka, na biya mai ɗan sahu kuɗinshi na shiga cikin chamba. "Barister Shanono wanka, kina sauka a abun hawa Nafi'u ya gyara zama wai zai kashe ƙwarƙwatar idonshi. Murmushi nayi na manyan mata gogaggun da suka san jiya da yau. Bance dasu komai ba na kutsa cikin office ɗinmu, mai ɗauke da tebura huɗu na baristoci, mu biyu mata, biyu maza. Khadija mai hula ta ɗago ta kalleni tace. "Barister Shanono har kin kammala shari'ar taki, aina ɗauka zai ɗauke ki tsawon lokaci sosai." Sai da na zauna a kujerata na ajjiye farar designar jakata kana nace. "Ke dai bari Mai hula, na gaji tulus, gashi ƙarfe huɗun yamma ma ina da wata shari'ar, yanzu nazari ma zan ɗan kuma yi. Littattafan dana ce ki tawo mun dasu kin kawo mun kuwa?" Na tambayi Mai Hula cikin kafeta da idanu. Tace mun. "E na tawo miki dashi, yana mota bari Aisha in ta shigo zan bata key ta ɗakko miki. Ɗazu wasu mata suka shigar da ƙara, akan wai mijin ita ɗayar ta siya musu gida suna zaune, mahaifinta daya rasu ta harhaɗe kan gadonta ta bashi ya ja jari. Katsaham sai ya jijjigo aure kinji dalilin shigar da ƙaran." Idanu na lumshe ina nazari tare da ƙalubalantar mazan wannan zamani, da rashin amana yai ƙaranci ga dayawa a cikinsu. Kafin ince wani abun Oga Rashid ya turo office ɗinmu, ya doge a bakin ƙofar ya kalleni. "Barista Shanono " Sir ( Yallaɓai) Shine kaɗai abinda nace mishi cikin girmamawa. "Ki same ni a office zamu yi magana yanzu, dan ina da shari'a nan da awa guda" Yana kai aya ya rufe ƙofar. Numfashi na ja, cikin ƙarfin guiwa na miƙe na fita ƙwas_ƙwas zuwa office ɗin Barista Rashid. Office ɗin babbane sosai, ga kayan more rayuwa a ciki, dangin Tv, firji, dispensa, da doguwar kujera babba daga gefe, ga kafet malala a office ɗin. Waje ya nuna mini na zauna. "Akwai wata mata da ɗazu ta shigar da ƙaran mijinta, har na yankar musu sammaci ta tafi dashi. Inason ki jagoranci kes ɗin. Nan da kwana talatin za'ayi zaman farko." Takadda ya miƙo mun mai ɗauke da cikakken sunan matar, da number waya, harda adireshi. "In kin samu lokaci sai ki neme ta ki soma binciken daya dace. Abu na gaba ina yabawa da ƙoƙarinki, jajircewarki tana burgeni. Na tura miki frend request a shafinki na facebook, ance kina faɗakarwa sosai, amman baki aseptin ɗina ba, ko me yasa?" Ya ƙarashe zancen da zolaya. Basarwa nayi nace. Za'ayi aseptin Sir ( Yallaɓai), ban samu zarafin hawa bane kwana biyu sakamakon aiyuka da suka sha mun kai. Asabe kuma zan nemeta ni da ita mu tattauna kafin zuwan shiga kotun. Nagode akwai littattafan da zanyi nazarinsu yanzu Yallaɓai, zan iya komawa bakin aikina?" Dariya yayi mun yanata daddana komfutarshi. "Zaki iya komawa Barista Shanono" Da sauri na miƙe na fice. Office ɗinmu na koma, na samu waje na zauna. Aisha mai mana goge_goge tace. "Anty Shanono zanje siyo abinci akwai abinda kike son ci?" Ido na lumshe, sai lokacin na tuno ruwan shayi kawai na kurkurɓa da safe a gurguje shima. E Aisha, a siyo mun amada, da miyan ewedu da ganda" dubu ɗaya da ɗari biyar ne plate. Sai na zaro dubu biyu na bata. Ki riƙe canji, ko abinci kya siya kema" Tana godiya ta fita. Ban ɗakin cikin ofishinmu na shiga na ɗauro alwalar azahar. Daddumata na shinfiɗa, na buɗe durowata na ciro ƙaton hijabina na ta da kabbarar Sallah. Ina idarwa wayata ta shiga kuka Yaya Use ce take kirana. Sai da na yi addu'o'in da kullum su nake maimaitawa, yarana nake roƙama ni kam Alhamdulillah duk abinda nake buri na samu, harda wanda ma ban roƙo ba Allah ya dubabe ba dan cancanta ba ya bani. Kullum dai a cikin ƙara gode mishi nake a bisa ni'imar da yayi mun nake. Ina zaune a daddumar ina jan jarbi Aisha ta dawo daga aiken da akayi mata. Nawa ta ajjiye mun a gabana da ruwa leda ɗaya. Ta ajjiyema kowa abincinshi akan teburinshi. Haidar ne ya shigo da sauri, kot ɗin jikinshi ya zame, ya zauna akan kujerarshi yana faɗin. "Barister Shanono ina neman agajinki, wallahi wata shari'ace mai rikitarwa nasa a gaba ko runtsawa bana iyayi. Yau da mu ka yi zamannan sai nake ganin kamar abokin aikina zai yi galaba a kaina." Dariya kawai nayi mishi, na buɗe takeaway din gabana kafun nace. "Ba zai kai ka ƙasa ba muddin ɓangaren daka riƙe me ƙwarine, sannan kune kake tunanin masu gaskiya, ba murɗa_murɗa irin na yawancin ƴan uwanmu lauyoyi ba? Amman duk da ina da shari'a ƙarfe huɗu kuma zanyi nazari. Zan saurareka bari in samu in sa wani abun a cikina." Abincina nasa a gaba inaci a hankali, harna kammala tas. Na shiga kewaye na wanke bakina da hannayena tas da sabulun ƙamshi. Ina fitowa Khadija mai Hula na shigowa. Teburina na koma na zauna na buɗe ɗaya daga cikin littattafan da Mai Hula ta ajjiye mun. Nazari na yi na awa guda, kafin na rufe, na saurari Haidar kuma. Ƙarfe uku dot na miƙe. To da Alkhairi, daga kotu sai gida kuma. Sai gobenku" Sallama nayi musu na fice a nutse zuwa kotun da nake da shari'a. Ƙarfe huɗu muka shiga kotu, awa guda mu ka yi ana fafatawa kafin muka tashi, sai ƙarshen wata mai kamawa za'a sake sabon zama. Ban samu damar kiran Yaya Use ba har zuwa wannan lokacin. Key na zaro a jakata na buɗe ɗan madaidaicin gidanmu da muke Zaune ni da Rahama, wannan bazawara mai Aure uku da na zauna a ɗakinta lokacin ina karatu. Har zuwa yanzu tare muke zama, kowa in gari ya waye ya fita wajan aikinshi. Da sallama na shiga tsararren falon namu duk da nasan babu kowa. Gidan karamine sosai, falonmu 3sitter kawai muka saka ƙatuwa mai kyau. Sai kafet da muka malala a falon, sai kayan kallo, da dispenser, sai wajan cin abinci, sai primes da muka ƙawata falon dashi. Ko ina tas, to mu ba yara ba kuma mu ba mazauna ba ma. Ɗakina na tura na shiga dake hannun dama, na Rahama yana hannun hagu. Katiface sumbuƙa a ƙasa tasha lallausan farin zanin gado, da fululluka ƙananu har guda takwas, masu kala_kala. Daga gefen gadon durowar littattafainane shaƙe da manyan littattafai irin namu lauyoyi, sai teburi da kujerar karatuna, da laptop ɗina a kai. Daga kusa da inda wadrope yake kuma anan katakon sagale jakunnuna na suke, da abun jera takalma. Abunda zai baku sha'awa takalman duk yawansu kala biyu ne tak, fari, baƙi. Hakama jakunkunan suke, dan tsabar gaye ko wanne takalmi tare da jakarshi nake siyanshi, bana iya siyan wari da wari. Jakata da na shigo da'ita yanzu na sagale a inda sauran suke, takalmina ma na cire na mayar dashi gurbinshi. Na cire kayana tsab na yo wanka, su kuma kayan dana cire na dulmiyasu a ƙaramin injin wanki dake kewayena, na zuba ruwa da omo inji ya shiga aikinshi na wanki. Ni kuma na zura doguwar riga marar nauyi, na tada kabbarar sallar la'asar, na jima a kan sallayarnan ina roƙama yarana arzikin duniya dana lahira. Abu na gaba sai na kira Yaya Use a waya ringin biyu zuwa uku ta ɗauki wayata. "Tani barka da yamma. Ai tunda na kira naga baki ɗaga ba nasan aikine yayi miki yawa. Kuma kinga yanzu Sani ya bar gidannan, ka kawo mun cefane wallahi" Murmushi nayi na farin ciki nace. Masha Allah Yaya Use, wallahi aikine ya sha kaina kinga sai yanzu ma nayi sallar la'asar. Kuma a hakanma wani sabon aikin zan shiga fa. Ya iyalin, ya Baban yara?" Dariya tayi tace. "Lafiya duka muke, dama inaso in sanar miki gobe inason zan shigo kanon, wallahi Tani Jos taci wuta talauci da rashin aikin yi na neman durƙusar damu. To kinga dai Baban yara yama dena gashin balangon yanzu, babu jari. Ni jarukan da kikaita bani a kai duk muka ta'allaƙa dole aita cinyewa. Ni kunyar roƙonki kuɗi ma nake yi wallahi. Ga su Inno maganar barannan wallahi sunƙi denawa duk kuɗin da kike turowa kuma wallahi ina kai musu, in sai kayan abinci in jibge musu. Ke Inno siyar da kayan abincin ma take yi. Indo ce ɗazu ta kawo mun wani zance, amman ki bari in na shigo kanon ma tattauna" Ajjiyar zuchiya na sauke na dafe kaina, hawaye suka zubo mun. Wai me yasa mabarata su basa son dena barane, shin sun fi son ganin rayuwarsu a wulaƙance kenan ko yaya? Duk abinda na tara akan su Inno da yara nake ƙararwa, duk da basu san kuɗin daga gareni bane. Yaya Use ce kaɗai ta sani, sai Habiba Bala, da Sabira, ko Yaya Karime bata san cewar Yaya Use ta san inda nake ba. Kowa akan haka yake. Yarana ina jin labarin duk halin da suke ciki, na kuka in yi musu, na jin daɗi kuma in taya su farin ciki. To Yaya Use shikenan babu damuwa Allah ya kawoki lafiya. Ki aika yara wajan mai P O S ɗin bakin unguwarku su karɓo miki dubu ashirin zan tura mishi yanzu. Sai kiyi kuɗin mota, ki ɗan ajjiyema yara abinci. Bari in ɗan taɓa aikin, sai goben." Godiya Yaya Use ta dinga ragargazo mini. Ni kuma sai murmushi kawai nake yi mata. Alhamdulillah duk sanda na taimaki iyayena da ƴan uwana, da yarana sai inji farin ciki sosai, ko da kuwa ace ni bani da ko sisi a jikina. Dadduma na naɗe na adanata. Wayata da labtop ɗina na ɗauka na fito falo. Ruwan zafi na tara a kofi a dispenser, na zuba milo da madara, kana na zauna. Labtop ɗina na buɗe, a hankali.....NA FAƊO DAGA BENE... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU SAKON GAISUWA GA ƊAUKACIN MEMBERS NA GIDAN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. INA JINJINA MUKU. ƳAN V I P BAN BARKU A BAYA BA. LAMBA TA 7 Facebook na shiga kai tsaye zuwa shafin Ƴancinmu wanda ni ke jagorantar shafin. Ina amsa tambaoyin mata. A rana ina amsa tambayar mata mabanbanta sin goma. Saƙonnin tambaya a rana ina cin karo da fin ɗari. Kuma duk zancan matanmu na Arewa baya wuce akan, cin zarafin maza, Zawarci, A'a miji ya sakoni da yara, iyayena sun koreni nike biyan haya nake kula da yarana. Iri iren matsalolin kenan. Wannan matsalar ta jefa Arewa a cikin gararin zina, maɗigo, luwaɗi. Mace dan miji ya saketa sai iyaye su hanata saƙat, dole ta fita ta kama haya dan ta dinga ciyar da yaranta. Iyayenta suna da rai amman kowa wahalar yake gudu. Daga haka wasu suke afkawa karuwanci,maɗigo. Duk dan su rufa ma kansu asiri, kuma sun samu damar hakanne a sakamakon gazawar iyaye. Bazawara a ƙasar Hausa bata da daraja balle kima. Wannan dalilin ne fa ya jefa mata da ƙananun yara cikin garari. Hawaye na share a guraben idanuna. Na soma amsa tambayoyi kamar yadda na saba, tare da ba da shawarwari. Wacce naji matsalarta babbace sai in nemeta in bata izinin zuwa gidana ta same ni. Wasu da kaina nasa suka shigar da kes kotu, na tsaya musu Alhamdulillah sun samu nasara, sun dawo suna rayuwar cikin sassauci. Akwai wata baiwar Allah Fatima, da miji ya saketa da yara goma, ya koresu har yaran. Tana zuwa gida raɓe_raɓe da kuka mahaifinta yace sai dai ta kama haya shi bashi da in da zai ajjiyeta da bataliyar yaranta. Hmm jikokin nashi yake kira da bataliya, a madadin manya su shiga lamarin Fatima, sai suka bar Fatima na ta yawon haya, da yawan wanke wanke gidan masu kuɗi, dan ta ciyar da yaranta. Da Fatima taga muddin da wannan sana'a zata dogara to tabbas yaranta ba zasu samu karatuba. Fatima sai ta faɗa zina, motoci na zuwa ɗaukarta short time, ko kwanan gida. Sanadiyyar shiga rayuwar Fatima da nayi ne da taimakon Allah na cireta a wannan ƙangi. Muka doka mijin Fatima a kotu, alƙali ya nuna mishi kurenshi, yanzu mijin Fatima kullum yana kai mata cefanen da zata ciyar da yara, shike biyan kuɗin hayanta, shi ke biyan karatun yara. Fatima ita kuma na tallafeta ta koma makaranta. Da wannan nake kira ga mata, mu yi ilimi, mu kuma riƙe sana'a. In mace tayi ilimi tana da sana'a kuma tafi ƙarfin wulaƙancin kowa. Dan wannan rayuwar ta sauya hatta iyaye sun fi ji da yaron da yake da tagomashi a cikin ƴaƴansu. Murmushi nayi dana tuno da irin rayuwar ƙasƙanci da wulaƙancin da nayi a gidajen aurena na baya. Babu mijin da bai sa hannunshi ya jibgeni ba. Kowa da irin wahalar daya bani. Amman na kan yi farin ciki in na tuno da yarana ababen alfaharina, da irin tarbiyyar dana ɗaurasu a kai. Rahama ce ta shigo tana tsaki. Hawayena na share na dubeta. Yaya dai kika shigo babu ko sallama, sai tsaki?" Zama tayi a ƙasa ta yar da mayafi da jakarta a fusace tace. "Ke dai bari. Ni gani dangina suke yi kamar wasu maɗuɗun kuɗi na tara ne. Duk matsala in ta taso sai a kirani. Sun manta korar karen da su kai mun. Dan sun ga iyayena basa raye. Wallahi Shanono da gudu ba ko takalmi na fito daga ƙauyenmu." Kuka ta rushe dashi, nima hawayen nawa nake ƙoƙarin mayarwa, amman ina sai daya ɓalle. Mun fi minti biyar muna rera kuka babu mai rarrashin kowa. Da ƙyar na yi shiru, na tuntsure da dariya dan in rage mana raɗaɗi nace. Ya'isa haka Rahama. Mu dena kokarin tunowa da baya. Mu fuskanci abinda ke gabanmu. Mu gode ma Allah, matan cikin gida kuka, zawarawa kuka, ƴan matan ma fa a wannan zamanin kukan suke yi. Rahma mu gode ma Allah da yai mana ni'ima muke zaune ko wacce tana neman na kanta. Bama shashanci, bama zuwa inda za'a ganmu mutuncin yaranmu ya zube. Ki share hawayenki ki faɗa mun meye matsalar, nima ban daɗe da sauraren matsalolin iyayena daga bakin Yaya Use ba. Gobe ma tace akwai maganar da take son tazo mu tattauna." "Nagode Shanono. Ina jin daɗin zama dake sosai. Tun muna wajen makaranta lokacin muna karatu, zuwanki yasa hankalina ya sake kwanciya. Ada gani nake yi kamar ni kaɗai na taɓa aure uku. Sai da na ganki ke mai Aure biyar. Yaya Hamisu ne ya kirani wai ɗiyarshi zata yi aure, shi kuma bashi da kuɗin kayan ɗaki. Shine Kawunmu yace mishi ya sanar mun. Ke ki ji fa Shanono, ni sanda nake buƙatar taimako wa ya saurari kokena? Kullum su kenan a cikin faɗamun matsala. Dubu ɗari uku ne kacal a aljihuna, kaya duk na dunƙule na saro kaya, ƴan office ɗinmu sun kwashe bashi. Dazu ina tsaka da aiki. Raliya babbar ɗiyata ta aro waya a maƙota wai Amir ƙaninta bashi da lafiya kwana uku yana kwance Baban bai kaishi asibiti ba fa, sai ni na tura musu da kuɗin asibitinshi" Rarrashinta dai na dinga yi, dan na fahimci yau a hasale take, da ƙyar na shawo kanta. Bayan mun yi sallar magriba sai na doka wayar Asabe. "Assalamu alaikum wake magana?" Cewar Asabe, bayan na amsa mata sallamarta, sai na gabatar mata da kaina, tare da ɗaurawa da cewa. Misalin ƙarfe goman safe gobe ki same ni a office inaso zamu tattauna, domin mu san yanda zamu ɓulloma lamarin ko Asabe." "To Barista zaki ganni in sha Allah. Ai na ma san sunanki a facebook" murmushi nayi mata mu kai sallama. Rahama tana zaune sai lissafi da cike_ciken takaddu take. Aiki take a ma'aikatar shinkafa. Uwar lissafi, me ake lissafawa ne haka. Ga wayarki tana ta ƙara" Rahama ta ɗago tace. "Oganane Wallahi, nifa tunda yace yana sona sai na dena ma ganin girmanshi sam. Shanono ni fa tunda dai aure ba dole bane, ni kam na haƙura. Zan iya riƙe kaina in ci gaba da kulawa da rayuwata. Ina jin daɗin kasuwancina, da aikina sosai." Zancan Rahama hakane. Nima duk yanda mu ka kai da mutunci, muddin aka furta mun kalmar so, to zame jikina nake yi. Ni gani nake yi ma ai nafi ƙarfin wata soyayya a yanzu haka da girma na. Kula da rayuwar su Inno shine kawai a gabana." Bani na kwanta bacci ba sai wajajen ɗayan dare, ina kan labtop ina nazari. Washe gari kuma bakwai da rabi na fice. Yau saye nake da farar riga, da skirt na kanti, nayi zanzaro, saina ɗaura baƙar sut, da baƙin hijabi gayuna, farin takalmi da jaka. Sai ƙamshi nake busawa fatata ta wani murje tana sheƙi, gashina dake yana shan gyara, yayi wani irin tsawo sosai, sai yanzu kyauna ya sake bayyana, kasancewar bani da ƙiba kuma ni ba ramammiya bace sai shekaruna suka ɓuya. Kuma bana wasa da cin kayan itatuwa, domin Allah shine shaida banason in tsufa da wuri. Ƙarfe takwas dot ɗan sahuna ya saukeni a daidai chambar mu, isowar Mai Hula kenan itama. Tare muka ɗunguma ciki. Kowa ya kama aikinshi yana ta faman yi. Ƙarfe goma dot a chamba taima Asabe, mun samu keɓewa da'ita tayi mun duk bayanin da zan riƙa a kotu wajan ganin hakkinta ya fito. Shikenan Asabe, in ina da buƙatar jin wasu jawaban daga gareki zan sake nemanki. Sannan kar ki sake kulashi kuyi wata rigima tunda kinsan kotu zata kwato miki dukiyarki." Godiya sosai asabe tayi mun, ta kama hanya ta koma ɗakinta. Ni kuma na koma bakin aikina. Ban jima da zama ba Oga Rashid ya leƙo, ya daɗe yana kallona ta ƙasan idanunshi. Sarai ina ganinshi, na daɗe da sanin manufarshi. Ina kiyaye mai zubewar mutuncinshi, dan yana furta mun kaimar so, naga zai takura mun, to zan iya barin aiki in sake chamba. Meeting ya sanar mana muna dashi gobe misalin takwas da rabi na safe, ya mayar da ƙofar ya rufe. Karfe hudu na baro office zuwa gida. Ina shiga Sabira ta kirawo wayata. Ƙawata Sabira, kinsan tunaninki nake yi yanzu sai ga kiranki?" "Babu wani nan lauya zance dai irin naku na lauloyi. Gani a Kano ni da Baban Mustapha shine dai nace bari in ji in kina gida sai ya saukeni a gidanki." Baki na washe nace. Yanzu dawowata gidan kenan. Sai kun ƙaraso." Sallama mu ka yi. Na ajjiye wayar, a gurguje na watsa ruwa, na saka doguwar rigar atampa. Sai na shiga kitchen, ruwan shinkafa na ɗaura, muna da stew dinmu da Rahama tayi mana cike da naman kaji. Ruwan ko tafasa bai yi ba na jiyo muryar Sabira a tsakar gidan. Da sauri na fito na taryota muka shigo ciki. Sai dariya muke yi. "Shanono Allah ya yarda kinga yadda kika dawo kuwa? Babu mai cewa uwar takwas ce wannan. Rayuwa ta yi kyau. Naji daɗin ganinki Shanono" Zaunar da'ita nayi a kujera, rabonmu da juna shekara biyu kenan. Baban Mustapha duk sanda zai shigo Kano tana biyoshi tazo wajena, mu yi hirar zumunci, mu yi dariya da nishaɗi. Ruwa da lemo na kawo mata na dure a gabanta Sha lemo, kinsan Kano akwai zafi ba irin Jos ba. Malama ya ɗalibai?" Malama ce Sabira a Al bayan tana koyar da matan aure ilimin hadisi. Sai da ta shanye lemon kafin tace. "Ɗalibai munata fama dasu. Ya kotu ƙawata?" Muna ta fafatawa, Yaya Use ma tana hanya. Ƙila daga nan ta wuce Kaduna dubo yaran nata" Zama Sabira ta gyara, nasan magana take son yi, sai na bata hankalina" "Tani wai sai yaushe zaki bari yaranki su saki a idanunsu ne? Ni ina ganin lokaci yayi daya dace ace kin kaima yaranki ziyara. Ko dan hankalinsu ya kwanta. Kullum fa Sani a cikin tunaninki da ba Mustapha labarinki yake. Bana faɗa miki ajinsu ɗaya a jami'a ba. Yaran suna cikin raɗaɗin rashinki. Duk da fa uban na ƙoƙarinshi a kansu, ƙarfinshi kawai akafi. Su Amina har yanzu Shamwila bata sarara musu ba, damba sun girma kuma sune manya a gidan. Ni na kwana biyu ma ban kira wayarsu ba. Zan kira Amina anjima ki ji muryar su, hankalinki ya Kwanta. Ko su Inno a yanzu yana da kyau su san inda kike ai ko, ko dan halin mutuwa.?" Hakane Sabira. Akwai abunda nake jirane shi yasa kika ga banje dubo yara ba. Kuma inajin labarinsu a wajenku, duk da banso barinsu Jos ba dan nasan kuna yawan kai musu ziyara. Batun su Inno kuma kinga na sai musu ƙaramin gida anan garin, na zuba musu kayan katako, inaso nima in je in tawo dasu, amman tunanin yanda zan tunkari Baffa nake yi Sabira. Da ciwon rashin yaran nake kwana in tashi." Sabira ta dubeni tace. "Yanzu ba da bane. Nayi imana su kansu su inno zasu yi farin cikin ganinki a wannan yanayin. Ina kuma ga kice musu kin siya musu gida su biki ku tawo, kinsan da gudu Baffa zai yafe miki, girma ya kuma sakko mishi baki ganshi ba. Yarannan ki duba lamarinsu Shanono." Murmushi nayi na kawar da zancan ta hanyar tambayarta maƙotanmu na layinmu na da, dan bana ƙaunar abunda zai sa in dinga tuno Kaila" Dariya tayi mun. Misalin shiddan yamma sai ga Yaya Use ta shigo, Sani na biye da'ita. Idanu muka zuba ma juna ni da Sani. Hawaye yaron yake zubarwa sosai, ya kasa furta komai. Ji nake kamar in je in kamoshi in rarrashi abuna, amman sai naji ƙafata na rawa kamar wacce tayi ƙarya. "Sani ga Tani nan ka ganta. Na cika maka alƙawarinka. Tani Sani tun bayan fitanki gidansu yake cikin ƙunci da damuwa, ko walwala sam bayayi. Yarannan ya kamata ki bayyana kan ki su ganki Tani. Dama ance mai haƙuri bai iya fishi ba" Hannu na miƙo ma Sani, da gudu yazo inda nake maimakon ya rungumeni sai ya tsigunna a gabana ya kama mun ƙafafuwana ya sake sakin kuka. Sai na tuno ranar dana tafi na barsu a tsugunne a gaban Kaila suna bashi haƙuri akan karya barni in tafi. Hawayena na share cikin nuna dakiya nasa hannu na rikoshi, na ɗan tallafoshi zuwa kafaɗata, ina dukan bayanshi halamar rarrashi. Yi shiru Sani na. Ba gashi ka ganni ba? Ban gujeku dan bana sonku ba, na barku ne dan bani da yanda zanyi Sani" Yaya Use tace. "To ku zauna kukan dai ya isa haka Yaron Tani" Murmushi yayi kawai ya sauke kanshi ƙasa. Girman ɗan mutum babu wuya, jibi Sani yanda ya zama babba, da ganin suturarshi kasan ɗan masu kuɗine, ga sumar fulani lub_lub a kanshi. Sabira tace. "Yaya Use kin kyauta. Kinsan Allah maganar Sani nake yi mata yanzu muka jiyo sallamarku. To Alhamdulillah naji daɗi da kika tawo da Sani ya ga mahaifiyarshi, a ƙalla ya tsayar da zuchiyarshi yayi karatunshi." Abinci na zubo mana a tiran silver dukkanmu, muka gyara zama, kowa ya soma ci. Sani daya kalleni sai murmushi. Duk duniya babu abinda nake so sama da ƴaƴana, na ji daɗin ganin Sani cikin shigar kamala. Ya su Shafi'i da Sulaiman, da su Salis duka?" "Suna Kaduna Umma. Ni kaɗaine a jos nake karatu Sulaiman yana karatu a Bauchi, duk sati Yaya Dauda yana zuwa wajena a makatanta. Har Kaduna yake zuwa ya kaima su Amina kayan sawa" Farin ciki ya sake ziyartar zuchiyata, nayi dariyar da na jima banyi ma irinta ba. Ana cikin haka sai ga Rahama ta shigo. Sani ne kawai bata taɓa gani ido da ido ba. Amman ta sanshi a waya. Cikin sakin fuska ta marabcesu, dan Rahama akwai kirki sosai. Bayan mun idar da sallar isha ne Yaya Use ta jamu ɗakina ni da Sabira, mu ka bar Sani a falo yana kallo hankalinshi kwance. "To ni dai abunda ke tafe dani abu biyu ne Tani. Ki ma Allah ki bayyana kan ki yaranki su ganki, ko ba gaskiya ba Sabira? Nayi magana da Habiba Bala ashe bata ƙasar ma wai taje wani kos, ita ma tace in ta dawo zaku zauna ku tattauna. To Sani da kike gani yana da ƙulafaci da bin diddigi har sai da ya gano nasan inda kike. Da kuka yazo mun, babu shiri na kawo shi gashinnan. To Habiba Bala tace shi kanshi Dauda abun na taɓa mishi aikin shi Tani, dan ma shi yana da uwa madadinki. Ki yi haquri Tani." Suka hadu su kaita daddanneni har sai da na amince week end zan shiga Kadunan in ga yaran. Sannan suka ƙyaleni. "Magana ta biyu akan su Inno ne Tani. Saudiya fa suke son tafiya yawon bara Inno da su Indo da Habu. Wata almajirace tai musu hanya. Baffa yana kwance kwana biyu ba lafiya. Mun je ni da Karime mun yi ma Inno roƙon duniya kar ta tafi taƙi. Shikenan rayuwarsu su a yawon bara zata ƙare, baki ga Baffa yanda ya tsofe bane, ina laifin ma su koma shanono su zauna tunda suna da ɗaki acan. Banga amfanin wannan barar da suke yawon yinta ba. Tun muna yara ake abu ɗaya har zuwa girmanmu ni na rasa ina zan sa kaina Tani. Daga ni har Yaya Use hawaye muke zubarwa, iyayenmu a wannan bakar rayuwar ta yawon bara muka taso muka tsinci kanmu tare dasu, ta sanadiyyar bara babu abinda bamu yi ba, babu abunda bamu gani ba. Rayuwar mabarata da ƴan jagora cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Ina roƙon Allah ya kawo mana shugaban ƙasan da zai haramta bara a Najeriya baki ɗaya kowa ya huta. Sabira cike da tausaya mana mu duka tace. "Tani tun wuri ki je ki kwaso Inno da Baffa, su Indo su samu su shiga makaranta. Ko rayuwarsu zata yi haske. Nasan duk wannan aikin da kike ci tuƙuru sabida su Inno kike yi. Baffa jikinshi akwai rauni sosai." In sha Allah, jibi babu aiki a gabana zan kama hanyar Jos, kafinnan an gama yi mun plate number na sabuwar mota dana siya ban faɗa muku bane da naso sai an gama komai. Suma yaran zanje su ganni zukatanmu suyi sanyi" Yaya Use tace dani. "Amman Tani kina shan magungunan hawan jininki dai ko, sannan ki dinga kiyaye duk abinda zai tashi hankalinki. Oh Tani nayi miki murna da rayuwarki ta samu canji sosai." Mun daɗe sosai muna tattaunawa, ko da na leƙo falo Sani har yayi baccinshi akan doguwar kujera. Na jima a kanshi nayi tsaye ina jin wani irin san shi na motsa mun raina. Sani tun yana yaro daban yake shi a cikin yarana. Da Dauda ya shigo rayuwata saina kasa iya tantance wa yafi ƙulafacina a cikinsu. Allah sarki Allah yai musu albarka, da ɗaukacin yaran musulmai baki ɗaya. Rabuwa da yara kana da rai yafi duk wani abun misali zafi da ciwo. Ta sanadiyyar damuwar rashin yarana ne hawan jini ya kamani, domin har kasa barci nake yi, ko inta firgita. Komawa nayi ɗakin Rahama acan na kwanta. Yaya Use da Sabira suka kwana ɗakina. Washe gari tun wurwuri na shirya tsab, yau shigar baƙaƙen kaya nayi daga sama har ƙasa, ƙaramin hijabinane kaɗai fari, hannuna na dama sagale da jaka, na hagun kuma sagale da rigar lauyoyi. A kurguje na kurɓi shayin dake hannun Sani, nayi musu sallama na fice a guje. Harna fita na jiyo muryar Sani a bayana. "Umma" Da sauri na juyo na zuba mishi ido, shima ni yake kallo. "Umma kinyi kyau sosai, kin fi ko wacce mace a duniyarnan kyau. Allah ya tsare Barista Tani Shanono Naroro" Murmushi nayi tare da lumshe idanuna. Haƙiƙa nayi kewar yarana sosai. Sani nagode sosai, ina alfahari da samunku. In na dawo daga office zamu zauna ka ban labarin ƴan uwanka kaji ko? Sai na dawo" Sani bai gushe a tsaye ba har sai da Ɗan sahunmu ya ɓace mishi. Ina ganin hannunshi ta mudubin gaban ɗan sahu yana mun adabo ( by by).......✍🏻[17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FADO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 9 Motar mu ta tsaya a daidai ƙofar gidan dana siya ma su Baffa. Yaya Use tana riƙe gam da hannun Baffa suka fito a mota, Inno, da Yaya karime suma suka fito, sai nima na fito. Na buɗe gidan muka shiga. Inno sai washe bakinta take yi, na buɗe ƙofar falon nasu muka shiga baki ɗaya. Inno Baffa ku zauna ga kujerunan. Yaya Use kinga gidan yayi ko?" Sai da ta zaunar da Baffa tukunna tace. "Masha Allah Tubarkallah. Gida yayi kyau Tani Allah ya saka miki da aikhairi. Kamar yanda kiketa ƙoƙari a kanmu Tani Allah yasa ƴaƴanki su zame miki ni'ima a rayuwarki. Inno, Baffa wannan gidane da Tani ta daɗe tana yin asusu dan ganin ta siya musamman domin ku. Allah yau ya cika mata burinta gaku a gidan da Tani ta siya muku." Tana kaiwa nan ai sai dukkanmu kowa ya soma sharar ƙwalla, harda Baffa da Inno wanda mamaki, ko farin ciki suka hana su cewa uffan. Yaya Karime tace. "Gaskiya Tani kinyi namijij ƙoƙari sosai. Ji rayuwa kamar ba zata kai miki ba, amman ji beki yanzu kin zama tauraruwa a cikin dangi. Allah yai ma zuriya albarka.' Baffa ne ya amsa da cewa. "Tani Ubangiji Allah yai ma rayuwarki da rayuwar iyalanki albarka. Yau Tani kece kika ciremu a ƙangin da muka tsinci kanmu. Kinga uwarku gata saudiyya take son tafiya ta barni yawon bara. Dan taga ƙarfina ya ƙare. Ni da duk inda zani nake riƙe hannunta muje, amman ita tsallakewa zata yi ta barni. Yawon bara har kwatano munje, a can akai cikin Karime, lokacin Use na hannu." Inno ta doka mishi harara tace. "Ana zancen farin ciki zaka dagula mana zukata Baffa. Tani mun gode Allah yai miki albarka. Kiyi haƙuri da tsangwamarki, da ƙyamatarki da muka dingayi a baya, lokacin da gidan aure yaki yi miki dadi. Ɓatanki ya taɓa mu ainun, ni dai dashi nake kwana nake tashi. Da tafiya naga tanata tafiya na fidda rai da ganawarmu na zaci sai a darussalam" Babu komai Inno. Wannan abunda nayi muku shine kaɗai abinda zan iya muku hankalina ya kwanta. Bana ƙaunar ganinku a kwararo, cikin zafi, ruwa, da iska kuna bara. Lokaci yayi da zaku zauna ku nutsu waje guda ku bautama Allah yanda ya dace. Zan ɗaukar muku malama da zata dinga zuwa tana koyar daku addini har gida. Dan akwai gyara a alwalarku, sallarku, da karatun sallar kanshi. A irin wannan shekarun hutu kuke buƙata ba wata wahala ba. Inno babu maganar zuwa saudiyya bara." Dariya mu ka yi dukkanmu. "Sai abinda kika ce yarinyar kirki" Dariya muka sake kwashewa dashi. Muna cikin haka sai muka jiyo sallamar su Goggo Ige, su Goggo marka, Goggo mai riga, Da su kawu Junaidu. Da ƴan uwan Inno, su Goggo Azumi, da su Kawu Mati. Bus guda su ka yo. Ni na fita na sallami mai Bus ɗin. Kuma munyi dashi da yamma zai dawo ya mayar dasu. Yaya Use ce ta yi musu bayanin na siya ma su Inno gida ne. Kai Alhamdulillah Wallahi ranar an shi mun arbarka fiye da tunanin masu karatu. Ige tace. "Naroro bara ya ƙare. Muma in Shanono ta ɗau zafi sai mu zo mu huta anan." Inno tace. "Ke da ba miji ba Ige dama zamanmu mu ka yi na samu abokiyar taɗi ai ko?" Nan fa kowa ya ɗauka da cewa. "Kuma wallahi hakan yayi" Kawu mati yace. "Gaskiya Tani kinyi kokari sosai, Allah kaɗai yasan irin ladan da kika samu. Kinga su Yusuf kai tsaye sun san inda Baffa yake a matsayinshi na babba. Duk wata matsala za'a kawo mishi gabanshi. Allah yayi albarka. Su Inno yawo ya ƙare, har aka gama yawon bara banga wani abun da kuka tara ba. Mu kuma ana ce mana mabarata kuɗine dasu." Baffa cikin karfin murya irin na makafi yace. "Wata gigitacciyar sata akayi mana a wata anguwa a legas mai suna agege unguwace ta hausawa. A funfata sai da ɓarayinnan suka samu million biyar. Inno kuma million uku ne cib a lalitarta cikin leda, duk suka yashemu. Wadannan kuɗaɗe mun daɗe muna tarasu amman ɓarayinnan suka durƙusar damu" Baffa sai kuka shi da Inno. Duk lokacin da suka tuno da wannan satar to fa sai sun zubar da hawayensu, nima rana ce da bazan manta da'ita ba abadan. Ana cikin rarrashin su Inno wayata tayi kuka, Sani ne yake kira ƙila sun shigo Kano ne. Ina ɗagawa kuwa ya sanar dani shigowarsu Kano kenan. Da tambaya ana nuna musu hanya har suka iso ƙofar gida. Ina tsakiyar dangina yarana suka shigo da sallama. Cike tab idanuna yake da hawaye na kura musu idanuna. Amina da su Shafi'i sai murna da ihu. Hauwana da Salis ɗina kuwa basu gane ni ba sam. Dauda gefe ya koma ya fashe da kuka. Ya zama saurayi sosai harda ƙasumba ya ajjiye. Kyawun yarana ya fito sosai, kowa ya girma gasu cikin kyawun shiga da kamala. Bani kaɗai naji sha'awar wannan yara ba. Kab falon babu wanda bai yaba dasu ba. Dauda kuwa sukaita mamakin girmanshi ya zama babban mutum. Gefena duk suka zauna, na ɗaura Salis a kafata. Dauda sai kallona yake yi. In suka haɗa ido da Sani sai inga ya banka mishi harara. Rahama tayi ma masu abinci jaroranci suka shiga shigo da abinci. Masa nasa akayi, da jallof ɗin shinkafa wacce taji kayan lambu da tsokar nama, sai abun sha, da ruwa. A wannan rana zukata cike suke da farin ciki marar yankewa. Sai yamma lis mai Bus ɗin daya kawo su Kawu yazo ya kwashesu, bayan na bibbi kowa da dubu biyar biyar, na rakasu har bakin motar ni da Sani da Dauda da suka maƙale mun. "Tani tunda Dauda gashi a Kano, ki daure ki rakashi ya duba dangin mahaifinshi su ganshi shima. A daure ai komai ya wuce, kune a sama kin yi ma Narani tazara mai yawa. Yanzu kam aurenki ai sai wanda ya shirya. Murmushi nayi nace. "To Goggo Ige in na ɗan rarrage aiyukana zan je in sha Allah in rakashi ya gaishesu. Amman ba wannan zuwan ba, sabida jigilar asibitin Baffa ban je aiki ba, aiki ya tarumun a office " A haka muka rabu dasu kamar ba zamu rabu ba. Hannun yarana na ja muka koma ciki, ina zama yaran duk suka dawo kusa dani. Yaya Use kinga Salis, da Hauwa sun mance dani fa" Sulaiman yace. "Da Salis da Hauwa kullum sai sun yi kukanki Ummanmu. Gaskiya ummanmu muna sonki, duk munyi kewarki. Babanmu yace in mun zo mu gaisheki sosai." Amina tayi zaraf tace. "Ya ba da sako ma yace in baki hannu da hannu Umma. Umma mu fa ba zamu koma ba, dake zamu zauna" Ni dan tsantsar farin ciki ma duk wanda na kalla sai inji kamar nafi son shi. Su Baffa sai nan nan suke da su Sulaiman. Abun gwanin ban ƙawa. A gidan dai muka kwana baki ɗaya, washe gari kuma ya kasance asabar ne, in monday tayi sati na biyu rabona da wajan aiki, komai nawa ya tsaya cak. Da sassafe sai ga Rahama tazo ganin yara, Mai hula ma Rahama bata jima da shigowa ba sai gata. Kai wannan sammako haka, sai kace kun tashi dani a mafarkinku?" Da zolaya nake maganar. Mai Hula tace. "Ni tun daren jiya da kika faɗa mun yaranki sunzo ganinki, ba da ban mai gidan bazai barni in fito ba wallahi da a daren zaki ganni. Ga yara Tubarakalla, kyawawa dasu, ashe kina da samari manya ma, Shanono ke fa ba ta yau bace kyan jikine dake." Dariya nayi mata kawai. Kajita yarane fa tsayin dai kafane dasu. Rahama ta harareni tace. "Wadannan samarin da zasu iya ma mace ciki kike kira da yara Shanono? A gaisheki, gaskiya kin kyauta da kika dawo da iyayenki kusa dake, gida yayi kyau sosai." Yaya Use ce ta fito musu da abincin karyawar da nasa su Dauda suka fita suka siyo mana. "Shanono wannan itace Yaya Use ko, me yawan kiranki in kina office?" Dariya muka saka ni da Rahama. "Itace, ai Yaya Use akwaita da kiran waya." Itama Yaya Usen dariya tayi kawai ta koma ciki. Su Mai Hula suna tafiya muka fita cefane, ni da Yaya Use da Yaya Karime, da Sani da Dauda. Kayan masarufi muka siyo ma su Inno da duk abinda nasan zasu buƙata, hatta tukwane sababbi na sai musu dal. Bamu muka shigo ba sai bayan la'asar, a tsakar gida muka samu su Baffa da yaran. Amina na bashi magungunanshi, Sulaiman na rike da kofin kunun Baffa, dan da kunu yake iya haɗiyar maganin. Bayan mun yi sallah kuma muka shiga jera musu abinci da kayan aiki a kitchen, dan naga su Amina sun gyare gidan tas, ko ina fes. "Tani amman zamu koma Jos ɗebo kayanmu ko? Dan inada ajjiyar kuɗaɗe a cikin tsummokarai" Cewar Inno kenan, Yaya Karime tace. "Ni da Yaya Use zamu tattare muku duk abinda ya dace Inno, Yaya Use zata zo ta kawo muku kayanku, kuɗaɗenku ba za su yi ciwon kai ba" Da yamma na ɗebi yarana muka je gidana dan mu keɓe in basu lokaci sosai. Na shiga kitchen nayi musu girki mai daɗi, na shige tsakiyarsu muka ci tare muna suturu gwanin daɗi. Bayan sallar Isha muna zaune a falo ni da su Dauda yana bani labarin damuwar da suka shiga bayan rashina, da yanda ya kammala karatunshi, da garin da yaje bautar ƙasa, sai ga Amina da wata ƴar ƙaramar jakar kwali fara sol ta miƙo mun. "Umma ga saƙon da Baba yace a Baki, da muka je mishi sallama" Sani ya fisge jakar a hannun Amina yana mata muzurai, harda mikewa kamar zai daketa wai dan me yasa ta karɓo daya bata. Sai da Dauda yace ya zauna kana ya zauna. Ita kuwa duk ta firgita da Sani. Turarene a cikin jakar, da wata wasiƙa. Kekketa wasiƙar yayi, turaren ya sa a aljihun jallabiyarshi. "Sabida me kayi haka Sani, ba Baba bane ya aikota ba, daka sani ka ba Innata ta karanta ai" Ni kuma abinda Sani yayi shine daidai, dan koni dana karɓa kakketa takaddar zanyi shi kuma turaren in raɗashi da ƙasa. Meye zai fito daga hannun Kaila in ji ina sha'awar karɓa, babu shi." "Ni banaso ta karantane Yaya Dauda kar umma taxo taji tanason komawa ɗakinta. Ni kuma wallahi in dai ina numfashi ko mutuwa Baba zaiyi sai dai ya mutu akan ya sake mallakar Ummanmu. Nifa ina zaune dashine kawai dan bani da yanda zanyi, a yanzu banga wanda zai rabani da uwata ba. Me yasa dan ubanta da suka je mishi sallama ma ta sanar dashi inda zamu tawo?" Kawai sai ya fashe da kuka harda haɗiɗiyar zuchiya, ɗakina ya shige da gudu. Ƴan uwanshi suka bishi da idanu jikinsu a mace. Maganganun sani sun fama mun mikin dake ƙarƙashin zuchiyata. Hawayena na share na yi murmushi nace. Babu komai ai. Bayaso in koma hannun Babansu ne. Je ka rarrashi ɗan uwanka Dauda ka faɗa mishi babu abunda zai mayar dani hannun mahaifinsu" Da sauri Dauda ya bi bayan ɗan uwanshi, Amina jiki. Mace tace. "Umma dan Allah kiyi haƙuri bansan karɓo saƙon zai sa Yaya kuka ba. Umma muma bama so ki koma Allah, ko da ya bani saƙon yace in kawo miki ni na karɓane dan kar ya hana mu zuwa muganki. Murmishin ƙarfin hali nayi mata kawai nace. Baki da laifin komai. Ai ubanku ne, kuma aikoki yayi. Nan gaba dai in ya baki saƙo ki kawo mun, karma ki nuna mun. Koma meye saƙon kuyi amfani dashi, in takaddace ki yayyageta ki watsar, kinjini ko? Ku zo mu je mu kwanta ku mata. Ku kuma Sulaiman a falo zaku kwanta, Sani zai fito muku da fululluka." Ina yinƙurin tashi sai ga Dauda da Sani sun fito suna dariya kamar ba Sani bane yanzu yake kukan fitar rai. Murmushi nayi musu haƙiƙa haɗin kansu ya burgeni, gabaki ɗaya sun zamema kawunansu abokan juna, kuma na lura suna matuƙar girmama Dauda a matsayinshi na babban wa uba garemu baki ɗaya. Bamu muka kwanta ba sai wajajen ƙarfe biyun dare, ni da tani za'abi kwanan zaune ma zamu yi wallahi. Matan na kwashe muka shige ciki. Mazan kuma Rahama tace su kwanta a nata ɗakin, zata kwanta ita a falon tunda baƙine su. Su Amina nabi da idanu sunata sheƙar baccinsu, ko wacce da ɗan nono a ƙirjinta. Kamar jiya nake ganinsu a kwance a bayana a katifa, suna bacci cikin fitsari, mu wayi gari katifarmu na yararin fitsari. Dariyace ta kwace mun kawai, dana tuno irin ƙazantar dana dama. Babu abunda yafi bani wahala kamar sanda na kwana goma a firzin babu wanka, ga jinin biki daya mammane mun, na sha ɗan karen azaba. Dan sai da ruwan zafi bawo guda ya ƙare kafin wajen ya sake, amman saida ya kumbura ya zamemun ciwo gagarumi. Nifa bacci ɓarawone ya kwasheni harga Allah. Sai naji na kwaɗaitu da zama da yarana, zanso hakan ta kasance. Amman bari in yi ƙoƙarin siyan mana gida tukunna, sai in tattaro kan yarana mu yi zamanmu, domin sune sanyin rayuwata, dan banji daɗin yanda Salis da Hauwa suka mance dani ba, duk da daga baya sun sake, kamar suna son tunoni. Washe gari duk kuɗaɗen dana tara sai da na kashema iyalaina kab a ShopRite, kama daga kan suturu, takalma, kwalam da makulashe iri_iri. Daga ƙarshe muka ya da zango a gidansu Inno. Mun samu Yaya Use tana tuƙa musu tuwon semovita, harta kammala miyar ma. Sai da mu ka ci tuwon dare muka ɗau azamar tafiya. Yaya Use da Yaya Karime na sallamesu da kuɗin mota, jibi zasu koma Na ba Baffa da Inno ɗan na kashewa. Yara su kai musu sallama dan gobe zasu kama hanyar Kaduna. Bayan na idar da sallah, ina ninke daddamu Sani da Dauda suna falo, su Sulaiman kuma muna tare a ɗaki. Sai ga Amina da gudu da waya a kunnenta. "Umma, Babane yake son zaku gaisa dan Allah" Ita da wayar nabi da kallo. Bansan sanda na ɗauketa ta mari ba tsabar takaici. Na wuce na barta tana kuka, ɗakin Rahama na shige na kulle kaina dan baƙin ciki sai na sau kuka. Yaran hankalinsu ya tashi matuka barin ma Amina wacce take ta magiya a bakin ƙofar. Yayyenta sai hantararta suke yi. Da ƙyar na yarda Rahama ta buɗe ƙofar ɗakin duk suka shigo. Da kyau na dubeta, sai naji ta ban tausayi, amman hakan baisa na saki fuskaba. Daga yau kar wanda ya sake kiran sunan ubanshi a gabana, ni bazan rabaku da ubanku ba. Amman ban yarda wani ko wata ya sake dangantani dashi ba. Nan gaba kaɗan sai dai ya kira yaji muryarku, dan kwasheku zanyi nima a hannunshi, in gani ko zai hanani yin hakan ne, in buga shari'a dashi" Kowa sai ya shiga taitayinshi, dan ina maganar ne muryata na tsitssinkewa. Allah yayi dare gari ya waye. Yau yara suka shirya tsab suka kama hanyar garinsu, tare da mun alƙawarin da zaran anyi hutu duk zasu tawo muyi hutu tare. Sani kuwa shi da Dauda cemun su ka yi sunga hanya ai. A tsaye suka tafi suka barni cike da kewarsu mai tarin yawa. A gidan su Inno na wuni sai dare muka tawo tare da su Yaya karime, Ige ta kwaso kayanta ita da su Indo da Habu sun dawo gida. Washe Gari su Yaya Use suka kama hanyar Jos ni kuma na koma bakin aikina. Kullum muna waya da duk yarana, mukan daɗe akan waya suna mun labari ni kuma ina jin daɗi. Dana taso aiki gidansu inno nake zarcewa, sai ɗaiɗaikun ranaku da nake wucewa gida, musamman in inason inyi nazari. Gaga_gaga dai haka rayuwar tai ta shurawa, su Baffa basu da aiki sai batun aure, ni kuwa duk wani wanda zai nuna mun so jaye jikina nake yi. Waɗanda suka tunkareni kuwa da batun kai tsaye nake basu haƙuri. Ni a ganina soyayya bata dace dani ba, yanzu burina abu biyune. Buɗe gidauniya domin taimakon nakasassu da koya musu sana'a. Na biyu kuma dawo da yarana hannuna. Duk da anayin hutu Sani ya tarkato kansu yazo ya dure mun su ya koma. Yana gama jarabawa ya biyosu shima. Dauda kuwa duk juma'a a Kano take yi mishi, nayi faɗan harma na gaji. Habiba Bala tace in rabu dashi. Bayan shekara guda Alhamdulillah na samu wani gida kusa da maƙotan su Inno, katangarsu ma ɗaya. Me gidanne ya rasu shine yaranshi suka sa gidan a kasuwa. Kamar wasa Baffa yace in sayi gidan in ina da hali yaji Inno tana yabon kyawun gidan. Abu in ya tsaga rabonka ne sai ka sameshi. Ranar Dauda yazo daga Bauchi ya kawo mun ankon bikin Mamanshi Habiba Bala, sai yanzu Allah ya nufa zata sake yin wani auren. Komai lokacine. To tare dashi da Ige muka zaga ganin gidan da yamma. Akaima gida kuɗi million biyu, ni kuma a lokacin kuɗin dake asusuna bai shige million ɗaya ba. Dauda yace. "Inna in kina son gidan, sai in cika miki, ina da million ɗaya da rabi dana jima ina tarawa, dama gida naso in gina miki dashi." Allah mai iko, cikin kwana biyu muka tattaro kan kuɗi da shedu muka biya, aka sauya takaddu da sunana, akayi komai gida ya zama mallakina. Ragowar kuɗaɗen daya rage a hannuna kuma dasu na soma gyaran gidan a hankali. Cikin ƙudurar ubangiji a cikin sati biyu naci larfin gyaran gidan sosai ƙarewar kuɗine ya dakatar dani da gyaran. Bikin Habiba Bala yanata matsowa, yau sauran sati biyu. Duk wani shirye_shirye tare muke gabatarwa a waya komai da komai dai. Ana biki saura kwana Hudu Dauda ya tuƙa motata muka wuce Bauchi. Sani kuma munyi dashi zai tawo da su Amina daga Kaduna, Yaya Use su kuma sai ranar ɗaurin auren zasu tawo itada yaya Karime.Biki Habiba Bala ta shirya sosai na manyan mata. Ƴan uwanta da danginta cike da gidanta danƙam, anata harkar girma. Masu suyan naman sa nayi, masu suyan kaji nayi. Uwar ɗakinta na ƙule da akwatina. Anan na tarar da Sabira da likitoci ƙawayenta, ko wacce ka ganta babbace sosai. Sai kallon kayan akwati suke yi suna yabawa da kayan da aka danƙara mata babban abin da yafi mun daɗi shine Habiba Bala a Kano zata zauna, dan angon namu bakanone, zumuncinmu ya ƙara matsowa kusa.....✍🏻 [17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FAƊO DAGA BENE...... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 8 KAILA: Ta ɓangaren Kaila kuma. Bayan fitar shanono daga rayuwarshi sai Allah ya jarabceshi da ƙaunar buɗe idanu ya ga yaranta suna yawatawa yana kallonsu. Ya katange duk ƙofar da za'a ci zalin yaranshi. Tunda mai aikinsu ita yake ba ma kuɗin hidima dasu. Duk da Shamwila tana hana abubbuwa da yawa, amman ta kasa hana Kaila dena jawo yaran shanono a jiki. Musamman Salis da Hauwa tunda sune ƙanana, Kaila na matuƙar ji dasu. Sani kuwa baya ko son ganin mahaifinsu, shi kanshi kailan ya sani sarai. Da Sani ya soma girma ko sallama yayi sai gabanshi ya faɗi, tsoron yaron yake ji ko kunyarshi ya rasa ɗaya daga ciki, amman yana jin shakkar haɗe girar yaron. Shamwila ta takura musu ainun. Hajiyayye sai dai ido, dan Tani ta fita daraja da kima a idanun Kaila. Kullum a cikin yi mata gorin yawan tarin yara yake. Sai dai ta shige ɗaki tayi kukanta. Ko komawarsu Kaduna a ranar da zasu tafi Kaila yake sanar mata ta shirya zasu koma can gabaki ɗaya da zama. Ƴan uwanta ma sai daga baya suka zo suka dubata. Ita a BQ ma yace ta zauna da ƙazaman yaranta. Shamwila da su Amina a asalin cikin gida suke su kuma, duk da shanono bata gidan, fasali ɗaya ya ba yaranta suke ciki dana Shamwila, duk da Shamwila tayi ma Kaila tas akan hakan haƙuri kawai ya bata, sai ɗakin su Sani a tsakar gidan. Hatta makatantar da Kaila yasa su Amina ba irinta su Sameera suke zuwa ba. Hajiyayye dai ta yi na'am ta karɓi ƙaddararta dan tasan ta zalunci Tani a zaman da su ka yi a baya ƙaiƙayine ya koma kan masheƙiya. Da ba dan yaranta ba da tsallakewa zata yi ta bar gidan. Duk da in taje gidan ma ba daɗi bane. Dan yanzu shagon gwanjon ma mahaifinsu bashi dashi, sai tarin tulin yara cunkushe a gida ga mata huɗu reras. Iyayenta mata ma ko wacce yaranta ke ciyar da'ita. Waɗanda yaranta basu kawo ƙarfi ba kuma sai ta nemi abun yi. Kwatsam wata rana Hajiyayye na tsakar gida ta ji yiriri_yiriri an shige ma da Kaila Amarya, dariya tayi haɗi da shewa, tace. "Ai ko bunsuru ya shafa ma Kaila, sai dai su yi kunnen doki da Ayu." Daga zuwan amarya komai ya ɗauki saiti, dan ta saisaita ma kowa kai a gidan. Shamwila itama tana ji tana gani ta zama ƴar kallo. Amarya ta kafe gwamnatinta, shine har Hajiyayye ta samu iskar ƴanci ta ɗan soma shaƙa, ita da yaranta. Bilkisa fa tana Zaria mahaifinta ya siya mata gida, taci gaba da aikin asibiti a asibitin Shika. Duk randa Kaila yazo ya dubata ita da yaranta biyu miji. Duk randa ya tsallake ƙafa ya koma aboki, a haka Bilkisa ta ajjiye Kaila. Dan ba zaman soyayya take yi dashi ba, tuni ya gama fice mata a rai. Kullum a cikin yaɓa mishi gori take. Tunda ya auri Shamwila basu sake haɗuwa da Bilkisa ba, amarya ma daya auro Bilkisa bata santa ba. Harkokinta da kula da yaranta kawai ta saka a gaba, ta sake Haihuwar namiji. KAILA kuma a kullum da shanono yake kwana yake tashi, gurbinta yana nan a zuchiyarshi baya jin akwai macen da zata iya cike gurbin Shanono a zuchiyarshi, sanadiyyar tunanin Shanono har hawan jini sai da ya kama kaila. Duk wannan daular da yake ciki baya jin daɗinta sam, domin wacce ta zama silar arzikin ta fice a rayuwarshi. In ya tuno da butulcin da yayi mata, sai ya sake kyautatama yaranta. Ya saima Sani mota in yana gari shike kai ƙannenshi makaranta, sai dai in baya nan direba ya kaisu, tunda shi Kaila ba zama yake da'iman a Kaduna ba. Burin Kaila yayi tozali da shanono ya roƙi gafararta ko Allah zai sa ta yafe mishi ta kuma koma kan yaranta. Dan ji yake shanono kamar mahaɗin rayuwarshi ce. Yayi ma kanshi alƙawari zai yi amfani da iya kalaminshi, da yaudara, ya sake siyan zuchiyar shanono a karo na biyu. Ya yarda itace rayuwarshi, zai karɓeta ko da kashi take wanka kullum. SHANONO: Kafin in dawo daga aiki, Sabira da Abban Mustapha har sun kama hanyar Jos. Yaya Use da Sani kawai na tarar a gidan suna kallon tashar Arewa 24. Sani na jin sallamata ya taso ya karɓi ledar dake hannuna da jakata. Wash Allah sannunku da gida Yaya Use, kuna zaune shiru sai dai kallo. Yaya Use tace. "Ke dai bari kunne gashi ya saba da haya hayar yara, danma yanzu kowa ya girma ya kama gabanshi." Sani ya zauna a kusa dani yace. "Umma yau ni nayi mana girki a gidannan. Ni fa umma nan gidan zan dawo da zaran munyi hutun makaranta. Ni gaskiya bazan koma gidan Baba ba. Baba ya auro wata ƙaramar yarinya sai rashin kunya." Kul Sani" nayi saurin kwaɓa mishi. Kar ka zagi matar Babanku ban baku wannan tarbiyyar ba. Bazan hanaka in anyi hutu kana son zuwa wajena ka kwana biyu ba. Amman ba zaka bar gidanku ba duka, kaine fa uba a gidan, su Amina in baka nan suyi yaya kuma?" Yaya Use tace. "Gaskiya ne, kai suke kallo makwafin uwarku. Tunda a yanzu da kai suka fi shaƙuwa. Hauwa da Salis ma ba zasu gane Tani ba sai dai nan gaba. Tashi ka zubo mana abincin muci ni yunwa nake ji." Taliya Sani ya dafa mana mai romo irin wacce nake yi musu in baje mana a faranti muyi ta ci. Sai dai ita wannan banbancinsu shine taji haɗi ga kifi zuƙu zuƙu. Gaskiya Sani ya iya girki sosai, ni harma ya fini iya girki tunda mu ba iya girki mu ka yi ba. Inaci ina santi har na ƙoshi. Sai murmushi yake yi dan ya sake sani farin ciki. Bayan sallar magriba na samu zama da Sani mukaita tattauna zantuka yana bani labarin bayan rabuwa, da irin gashin da mahaifinsu yake amsa a hannun mace. Ai dama ni nasan jarabawar Kaila ta mata ce, duk wuyar da suke bashi bai dena ruwan idanu ba, gashi har yaranshi sun girma sun san a wanne irin layi mahaifinsu yake. "Umma tunda kika fita a cikin rayuwar Baba duk ya lalace, baki ganshi ba ya rame sosai. Wataran in ya sa su Balaraba a gaba kamar zai haɗiyesu, harfa ƙwalla yake fitarwa." Murmushi nayi kawai nace. Adda'ata ta karɓu, dama burina mahaifinku yasan mahimmancinku, da darajarku. Da yau na tawo daku ba lallai bane Babanku ya sake neman mu a rayuwa ba. Duk abinda ke faruwa a gidanku na sani Sani. Kuma nasan irin son da mahaifinku ya ɗaura a ranshi bayan tafiyata. Yanzu dai tunda kai ka biyo ni zanje in ga ƙannen naka." "A'a Umma ni fa wallahi Allah ba zaki je gidannan ba. In kin yarda Yaya Dauda zai kawomu dukkanmu mu zo mu ganki. Amman ban yarda ƙafarki ta taka gidanmu ba. Umma duk wulaƙancin da Baba yayi miki fa ban mance ko ɗaya ba. Umma kin tuna wani duka da yayi miki akan umman Samira ta muku sharri ke da Goggo Use, lokacin kin je Shanono kin tawo da Yaya Dauda a halin ciwo? Umma abun yana ɗamfare a raina har in koma ga mahaliccina bazan mance ba, kuma bazan daina ganin baikenshi ba" Kuka yaronnan ya fashe dashi, nima kukan nake yi, rungumata yayi tsam yana mun magiyar shi bazan je gidansu ba. Yaya Use a haka ta fito daga ɗakina ta same mu muna kuka mai raɗaɗi. Kaila ya cuceni yasa ma zukatanmu wani miki wanda dashi zamu koma. "Iko sai Allah. Sani, Tani to kuyi haƙuri kukan ya ƙare haka mana. Cikin rauni nace. Nima bana ƙaunar in buɗe idanuna in ga Kaila, dan kun tursasamunne shi yasa nace zanje, kuma nasan sabida yaranne. Sani yace bazani ba. Yaya Use bazan je ba, Dauda ya tuƙo mota ya kawo mun yara in gansu kawai. Kuma duk sanda su ka yi hutu zasu iya kawo mun ziyara." Da haka maganar ta mutu. Washe gari a sabuwar motata muka kama hanyar Jos. Sani sai tsiya yake yi mun wai yaushe harna iya mota haka. "Umma da ko titi falfalawa kike yi da gudu in zaki tsallaka." Dariya na kwashe dashi, Yaya Use dake gaban mota tai ma Sani daƙuwa tace. "Ungo naka, wato ka mayar da Tani kamar wata kakarka ko?" Cikin raha mu kai ta lula hanya. Dana gaji Sani ya amshe tuƙin, sai murja sitiyari yake yi da halamun ƙwarewa, bana ko gajiya da kallon Sani, gabaki ɗaya girma da kuɗin da kaila yake sakar musu yasa yaron ya goge, dake kuma ɗan jami'a ne sai naga yana da wayewa. Wai yau ni Shanono ƙazama bagidajiya, baƙauya ni da yaranane muka zama ƴan birni gogaggu? Duk macen da ta ganta a ƙasa itace ta kasa tsaiwa ta fuskanci matsalolinta. Duk da nasan akwai ƙaddarar da duk yanda bawa yaso fita, ubangiji baya bashi wannan hanyar, sabida yana cikin ƙaddararshi ta zaman duniya. Ko da muka shiga jos, sai na shiga zazzare idanuna ina ganin gari. Babu canji a garin ko na titin mota, ballantana sababbin gidaje. Babu wani ci gaba da Jos take samu, sakamakon yaƙe_yaƙe daya kassara jihar. Ƴan taya muka nufa wajan barar su Inno. Ina hango kwanar layin garejin su Kaila. Sai nake hango sanda nake zuwa ba Kaila kuɗin abincin rana, ko kuma zuwa ganinshi. Idanuna na runtse. "Inno bata nan wajan Tani. Muje babban masallaci Sani wajan barar su Baffa." Can ma muka je ba Baffa ba Inno. Kai tsaye muka zarce gida, muka tarar basa nan. "Tani inaga fa ba lafiya. Bari in kira Karime inji ko lafiya" Ni dai gabaki ɗaya na bi na tsure. Tana kiran Yaya Karime take sanar mana ai suna hanyar Shanono Baffa yana ta kukan shi a mayar dashi shanono ya rasu a cikin danginshi." Ba shiri muka nufi hanyar Kano muka sake niƙan hanya. Muna hanya Habiba Bala ta kirani da number ta na Najeriya. "Ƴar uwa abun wuya. Na dawo fa, yanzu na shiga Bauchi, Dauda nake jira ya kaini gida" Take faɗa mun. A gurguje na bata labarin ɗan abubbuwan da suka faru dai. Zamu yi waya duk yanda ake ciki. Da na shiga shanono zan wuce dashi asibitin Kano." "To shikenan ƙawata, ko in tawo ne?" Allah sarki Habiba Bala, masoyin mutum kenan. A'a Habiba Bala ki zauna kema ki huta. Sai na zo Bauchin" Sallama mu kai da juna na ajjiye wayar. Ba fa mu muka isa Shanono ba sai yamma sakaliya. Muna yin kwanar layin su Baffa muka hango kawu Yusuf da kawu Junaidu suna riƙe da Baffa za'a kaishi Asibiti ranga_ranga. Da gudu na fito na kamo Baffa tare da cewa. Subuhanallahi jikinne yayi tsanani haka Baffa?" Gabaki ɗaya mutanen wajen suka riƙe baki suna kallon yanda nayi kilin. Inno ta nunoni da yatsa. "Tani ashe zamu sake ganawa dake? Allah na gode maka" Hawayene suka zubo mun. Baffa sai nishi yake yi. A mota muka sashi, Inno da Kawu Yusuf suka shiga. Muka nufi Asibitin Murtala. A gigice muka shiga cikin asibitin sosai, dan Baffa baya ko numfashi. Saina tuno irin gigicewar da nayi a lokacin da muka shigo da Dauda cikin asibitin. Cikin gaggauwa aka ba Baffa gado. Ni kuma na je na yankar mishi kati, aka buɗe mishi fayil, sannan na dawo wajensu, duk fa inda na ɗaga ƙafata a wajen Sani ke saka tashi, yana biye dani kamar jela, jakata da wayata duk tana hannunshi. "Tani dama ashe zaki waiwaye mu, ince dai baki yi fishi damu ba? Ni nasan damuwa da tunanin halin da zaki riska a gida, da tsinuwar da Baffa yace zaiyi miki ne yasa kika gudu babu wanda ya sake jin ɗuriyarki. Tani sai na ganki a cikin sabon yanayi da kyawun shiga." Hawaye na share, hannuna ɗaya yana cikin na Sani. Inno ku yafe mini in nayi muku laifi. Wallahi ba dan fishi daku bane yasa na tsallake na barku ba. Fishi da zuchiya nayi akan Kaila kinji dalilin tafiyata." Kawu Yusuf yace. "Amman kinsa ƴan uwa a cikin taraddadi. Duk da muma mun yi kuskure cikinmu babu wanda ya kai cigiyar ɓatanki ko da gidan radiyo ne" Yaya Use da se yanzu ta yi magana tunda muka zo asibitin tace. "Inno duk wani kuɗi da kayan abinci, da sutura, zuwa sabuwar keke da aka sake miki. Duk Tani ke turowa nake yi muku. Ni nasan inda take kullum sai mun yi waya da'ita. Inno Tani yanzu mai shari'a ce a kotu, ta game karatunta da jimawa." Kuka Inno ta fashe dashi tana sambatu. "Tun tasowarki kike son karatu Tani. Allah mai iko ashe zaki zama wani abun ta dalilin karatu. Allah na gode maka da yasa kika bar gida kuma kika tsare kan ki. Allah yayi miki albarka." Da Ameen dukkanmu wajen muka amsa. Bamu muka samu damar ganin Baffa ba sai bayan isha, lokacin har mun yi Sallah na ba Sani keyn mota ya je siyo mana abinci. Muna shiga muka tarar da Baffa babu inda yake. Dr ya sanar mana ciwon siga da ciwon tsufa suke damunshi. Amman siga ta cinye mishi jiki sosai. Dan tun da na taso ban taɓa ganin Baffa ya je asibiti ba ko yasha ƙwayar bature ba. Ko ciwo yaji sai dai ya sa a dafa mishi ƴan saƙesaki yasha, ko sirace." Kwanan Baffa biyu a asibiti bai san inda kanshi yake ba. Har Habiba Bala tazo ta dubashi. Rahma kuma kullum ita ke sintirin kawo mana abinci, abokan aikina duk sun zo sun gaishe da Baffa. Sabira suna hanyar zuwa. Yau Baffa ya tashi jikin Alhamdulillah da sauƙi. Ƴan shanono sai sunturi suke faman yi. Duk wanda kuma ya ganni sai ya shiga mamaki. Da daddare muna komawa gida mu kwana, Kawu Yusuf ne yake jinyarshi. Ranar da Inno muka tafi da ita gida, tayi murna tayi farin ciki sosai. Da sassafe muke komawa asibiti. Sani kuwa da ƙyar na kaɗa shi ya koma bakin karatunshi. A cikin kwana na bakwai Baffa yayi ras dashi harma ya gane muryata. "Inno wannan muryar ai Tani ce. Tani dama zaki zo garemu?" Tsugunnawa nayi har ƙasa na riƙe hannun Baffa na dinga roƙonshi gafara akan ya yafe mun. Cikin sanyin murya tare da jan ajjiyar zuchiya yace. "Tashi Tani. Wallahi na yafe miki, Inno ki yafe mata kema kinji ko? Yaranki sun ganki kuwa Tani?" A'a Baffa Sani ne kawai ya ganni. Yaya Use ta labartama Baffa hidindimun da na dinga yi dasu ba tare da sun sani ba. Ai nan Baffa ya shiga kuka tare da ƙara shi mun albarka. Ko da aka sallami Baffa kai tsaye gidan dana sai musu muka wuce dukkanmu, ban ma kowa bayani ba, na dai ce su biyoni zamu tattauna in mun isa inda zan kaisu. Harda su Kawu Yusuf. Sauran ma zasu tawo daga Shanono, bisa jagorancin Ige Ƙanwar su Baffa, nayi mata kwatancen layin da gidan, dake tana yawan shigowa Kano , tace zata gane gidan ma in suka shigo layin, matanbayi baya ɓata. Na bada aikin abinci, da abun sha dan ƴar ƙwarya_ƙwaryar walima nake son haɗawa. Dauda da yaran ma suna hanyar zuwa bisa jagorancin Sani........✍🏻 [17/10, 1:23 p.m.] +234 803 831 1474: NA FADO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 10 "Kaga Babbar kawar Amarya, maraba da zuwa." Inji Dr Nauwara kenan. Habiba Bala ta watso mun harara tace. "Dama zamanki ki ka yi a Kanon ai daya fi miki. Tun jiya nake jiranki, wasu abubbuwan kinsan dole sai dake zanyi. Wayarki na dinga kira a kashe, kuma nasan sabida ni kika kashe" Dariya ma ni ta bani wallahi. Ki haƙuri ƙawata, baga ni ba nazo. Kinsan aikin lauyoyi akwai wahala, kinsan da yaya ma ogana ya barni na ɗebi hutun kwanaki biyar ɗinnan ma? Hmmm da ƙyar ya amince. Sabira yau kika ƙaraso?" Sabira ta bani hannu muka tafa tace. "Ko awa guda banyi da shigowa ba ma. Kixo ki ga akwati dan nasan dai a waya kika gani" Hakanne kuwa video call Habiba Bala ta kirani, ta dinga ɗaga mun kayayyakin ina gani. Zama nayi na darje kallo gaskiya an kashe kuɗaɗe sosai a cikin akwatunan da akaima Habiba Bala. Mijinta babban ɗan kasuwane a kwari yake, shi yasa aka saka mata kaya kyawawa masu yawan gaske. Dan Alhazan cikin kwari in zasu auri mace suna ƙaryar sutura gaskiya. Daga nan muka shiga hada hadar shirye_shiryen duk abinda ya dace. Habiba Bala Dinna kaɗai zata yi mana a nan garin Bauchi sabida ƙawayenta da ƴan uwanta. Da an gama Dina kuma sai mu yi zugar kai amarya. To fa wanna dina ita ta cinye mana lokacin mu. Mun dai nemi masu yin abincin biki mun biya su kuɗin abinci mun basu time, haka masu snacks da zoɓo ma mun sallamesu. Ana gobe ɗaurin aure sai ga su Sani da yaran suma sun zo, wucewa mu ka yi shagon saloon da lalle. Muka sha gyaran gashi da jan ƙunshi mai kyau, damu da su Halima Bawa, ƙawayenmu na makaranta duk mun hallara, dan ana zumunci sosai babu laifi. Duk shirin bikin a group muka gudanar dashi tare da kowa da kowa. Abokan ango a daren alhamis suka shigo Bauchi, a hotel suka sauka. Mu duka hidima ta hana mu ganawa da ango da abokanshi. Washe gari da misalin ƙarfe goman safe aka ɗaura auren Habiba Bala da angonta Alh Nura bisa sadaki dubu hamsin. Muna ɗakin Habiba Bala, kowa na hidimarshi, ina sanye da angonmu na ƴan makaranta farin lace sol mai duwatsu da baƙin ɗankwali. Iya kyau ni kaina dana duba madubi sai da nace masha Allah. Amarya kuma tana cikin jan lace mai adon baƙi_baƙi a jiki. Anyi mata kwalliyar zamani ta fito kamar ma ba itaba, dan ire_iren kwalliyarnan sauya ma mutum kamanni suke yi. Ni shi yasa naƙi yarda ayimun fur. "Shanono ya kamata muje haka ko? Tun ɗazu Alh yake ta faman kiran wayata. Ki kira mun Dauda ya zo ya kaimu." Cewar Habiba Bala kenan. Waya na ɗaga na soma kiran layin Dauda. "Innata, ina waje ku nake ta jira, muna tare da Sani ma" To shikenan gamu nan fitowa muma" ƙit na kashe wayar nace. Sabira, Halima Bawa bari mu je mu dawo. Ba jimawa zamu yi ba. Sabira su Yaya Use suna hanya." Hannun Habiba Bala na kama muka ratso mata muka fice. Dauda na ganinmu ya buɗe murfin motar. Sani kuma ya sara mana, har da cewa. " Kaga manyan iyayenmu, alkhairin Allah yaci gaba da kai muku har gadon baccinku. Farare basui farin banza ba" Dariya dole Sani yasa muka tuntsure dashi. Dauda kuma yana gefe yana cin dariya. Motar muka shiga, Dauda ya ja mu zuwa hotel ɗin da Angwaye suka sauka. Tare da su Sani duka muka ɗunguma zuwa cikin hotel ɗin. A room 7 muka tsaya, Dauda ne ya ƙwanƙwasa ƙofar a hankali. Mu kuma muna daga gefe Habiba Bala na mun raɗa. "Baki ji yanda gabana yake faɗuwa ba Shanono, nifa ji nake yi dama banyi auren ba wallahi, yana kirana da yace an ɗaura, shikenan gabana ya shiga aikin bugawa, ku tayani adda'a ke da yaran" Haba ƙawata, in sha Allah auren karshe kika yi daga gidan Alh Nura sai kabarinki." Ƙaran buɗe kofar ne yasa muka zuba ma kofar idanu mu duka. Wani matashi muka gani a tsaye a kofar ɗakin, yana sanye da angon ƴan ɗaurin auren. Habiba Bala tace. "Alh Nura muke nema dan Allah " Murmushi yaron yayi yace. "Dady acan ɗakin suke, bari in muku iso" Shi ya shige gaba, muna tafe ƙwas_ƙwas_ƙwas har zuwa room 10. Shi da kanshi ya ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin wani dattijo yazo ya buɗe mana. "A'a Jega kaine tafe da iyayen naka? Bismillah Hajiya Habiba Bala ku shigo, Samari bismillah." Tare muka shiga cikin ɗakin hotel ɗin. Cike tab da abokan ango, suna saye da shaddaji mai ruwan sararin samaniya, da hulunansu masu ruwan baƙin blue, haka aikin gaban rigarma yake. Kujera dogowa da suka nuna mana muka zauna, ango ya rasa inda ma zai tsoma mu, ni kuma duk sai naji inata kunyar yara, sai satar kallonsu nake yi, Amman su naga hankalinsu ma akwance yake, sai gaisawa suke da abokan ango. "Hajiya Shanono barkanki, idanunki kenan na ɗauka ai aikinku na lauyoyi bazai baki damar halartar taron bikin mu ba." Cewar ango, dariya nayi mishi, shima da zolaya yayi zancan. In aikina zai iya zame mun katangar da zata hanani zuwa bikin Habiba Bala, da tuni na ajjiye aikin, dan Habiba Bala ta fi mun aikina muhimmanci. Guda da bari ce a wajena. Ango Allah ya sanya alkairi yasa gidan zamanta ne" Dariya yayi mun yace. "Ameen Ameen mungode da yabo Shanono." Uwar ɗakin cikin falon Alh Nura ya ja Habiba Bala. Ni kuma sai faman daddanna waya nake yi, wani saƙon neman shawara aka turomun, duk da tace mun. Malama ki ɓoye sunana. Amman na tausayama wannan baiwar Allah ainun. Copying nayi na tura cikin group ɗina, da shafina. Shine aketa tabka muhawara iri_iri. Inason karanta comments, wasu abun kayi dariyane, wasu kuma abun haushine sosai tattare da amsarsu. Wannan lamarin shi ya ɗebe mun hankalina har bansan lokaci ya ja ba, sai da wayar ɗaya daga cikin abokan ango ta doka kiran Sallah. Sai lokacin na duba agogon wayata ƙarfe ɗaya saura. Su Dauda na duba suma ni suke kallo, farfesun kaza suke sha hankalinsu kwance. Sani ne ya ɗebo farfesun a cokali ya nufo bakina dashi. Cikin farin ciki da jin daɗin yanda yaron yake kulawa dani na wangale mishi bakina ya sa mun farfesun. Dai dai fitowar Habiba Bala. Hakanne yasa na miƙe da sauri, tare da ango muka fice har gaban motarmu yai mana rakiya. Shine kika shanyani a zaune ko?" Cikin raɗa dan kar yara su jiyo mu nace. Ke daɗi miji ko?" Zungurata tayi tana nuna mun yara. Harararta nayi cikin wasa. Bayan mun koma gidane, na tarar da su Yaya Use sun ƙaraso, anata hada hadar rabon abinci dasu. Su Amina na gani sun cakare gaye sun yi kyau kamar ba ni na haifesu ba. Kayan jikinsu komai mai tsada ne sosai. Lallai kaila yayi kuɗi, har ya iya siyama yara tsadaddun kaya haka? A wajensu na tsaya Habiba Bala kuma ta shige ciki. Haka dai al'amuran biki su kaita gudana har zuwa dare. Da misalin ƙarfe takwas na dare muka fito tsab damu, a lokacin jama'ar biki sun daɗe da tafiya can hotel ɗin da za'a yi dinna. Su Sani sun sha jigilar kaiwa da dawowa ɗaukar mutane, motata tana hannun Dauda, Sani kuma da motarshi dama ya tawo Su Yaya Use duk sun tafi. Manyan ƙawayen Amaryane kaɗai muka rage mu huɗu, sauran ƙawayen suna can suma suna jiran isowarmu. Sanye muke da ankon wani material mai wawal_wawal ruwan gorone kalar kayan, sai muka ɗaura ɗankwali mai ruwan madara. Ƙatuwar sarƙar azurface a wuyana da kunnena, da tsintsiyar hannuna, har zuwa yatsuna uku da suke maƙale da zobunan azurfa suma. Takalmina da jakata masu ruwan madara na saka, takalmina yana da tsini sosai, sai ƙwas_ƙwas yake yi. Inata bige ƙamshin sihartacciyar humrarnan ta manyan mata wanda nake siya a hannun Mrs Bukhari gidan ƙamshi ƴar mutan Kanuri. A kusa da Habiba Bala nake, Sabira na kusa dani, sai Halima Bawa, sai Dr ƙawar Habiba Bala. A jere muka fito zuwa kofar gidan, motoci muka tarar guda uku a jere. Ta tsakiyar itace ta amarya da angonta kaɗai. Na gaban kuma su Halima Bawa suka shiga, har na isa bakin motar matuƙin motar yace. "Hajiya ki shiga waccar motar, wannan ta cika" Cikin takun hajiyoyin mata na isa motar ƙarshe, gaban motar na shiga da sallama ɗauke a bakina. "Ameen wa'alaikissalam Barista Tani Shanono Naroro, Ƙwararriyar lauya mai kare hakkin mata. Mamallakiyar Mu farka mata group, malama mai sauraron koken mata, mai burin buɗe gidauniya dominsu, Bazawara mai aure shida." Da ɗumbin tulin maɗaukakin mamaki na bi matuƙin motar da idanu. Wannan saurayin da muka kwankwasama ƙofa ne ɗazu a hotel wanda akaima laƙabi da JEGA Ƙur muka zuba ma juna idanu. Ni ina mamakin rashin ta'idonshine, dan banyi mamakin jin ya ambaci sunana da aikina, da kuma lambobin aurena ba, dan abune dana ɗaura a shafina na facebook, nasan labarina ya yaɗa inda ma banyi tunani ba, dan akwai wata hira da akayi dani bayan naci nasarar wata shati'a, to na ɗan ba da taƙaitaccen labarina, kuma na wallafa videon yana shafina. Shi kuma saina kasa gane irin fassarar da zanyi ma kallon da yake yi mun. Dan naga idanunshi kamar sun ɗan cika da ruwan hawaye, in ba dai nice ban gani dai_dai ba. Zare idanuna nayi daga kallon ƙudan da mu kai ma juna na kawar da kaina. Bin jerin motoci biyunnan yayi a baya, a madadin yayi gudu sai naga yana tafe a hankali. Ni dai bance dashi komai ba, ban kuma yarda mun sake yin ido hudu ba. "Na daɗe ina mafarkin saki a idona, na daɗe ina mafarkin gaki a cikin motata. Na daɗe ina mafarkin hotunanki. Abunda yafi komai burgeni shine, kinfi a hoto kyau, kinfi a video kunya. Yau babbar ranace a gareni mai ɗunbun tarihin gaske. Kar in cika ki da surutaina, da Farko Sunana Ahmad Jega, amman abokai da ma dangina da Jega suke kirana. Nine babban ɗa ga Alh Nura mijin ƙawarki, iyayena duk suna Kano da zama, ni kuma ina garin Kaduna da zama a cikin garin Jega, cikin tsotson mahaifiyata" Mamakin iya tsarin zancenshi nake yi. Gashi dai yaro, abun mamaki ya iya abubbuwa irin na manya, kuma akwai ƙwarin guiwa a tattare dashi. Lallai yaran yanzu akwaisu da rashin kunya. Nayi mamakin Jega yanda yake iya furta ra'ayinshi a kunnena. Yarone da bazai wuce shekara talatin ba, duk da dai yana da kamala, Amman dai yarone ƙarami. Da tunane_tunane fal kwanyata muka iso hotel ɗin da ake dinna. Yana gama parking na murɗa murfin motar da zummar ficewa ko zan shaƙi numfashi mai kyau. "Barista Shanono baki ce komai ba, yanzu a haka zaki barni kenan, duk dakon wannan ranar da nake yi a haka ashe zata same ni? Banyi zato ko tunanin haka daga wajan mace mai girman daraja da karamci kamarki ba. Ni fa na ɗauka masoyi duk ƙanƙantarshi, ko girmanshi abun a daki ƙirjine a nuna shi. Cikakkiyar soyayya ta gaskiya babu ruwanta da girman ma'abotanta, ko ƙanƙantarsu. Dan da tana la'akari da hakan. Da yara ƙanƙana basu isa saninta ba. Amman so bai ware kowa ba. Shanono ki ma ɗan jaririn da yake neman tallafin uwar goyanshi duban tausayi, zuchiyata jaririyar zuchiyace tarairaya take buƙata" Ƙur na zuba mishi idanu, cike da kallo mai ɗauke da fassarar baka da hankali. Na rasa me zance ma wannan yaron, na kuma kasa ɗauke idanuna a kanshi, shima ni ya zuba ma idanu. Na lura jikinshi har rawa yake yi kaɗan. Buɗe mun ƙofa in fita Samari." Iyakar abinda na furta kenan. Baice uffan ba ya zare sakatar data rufe motar. Na buɗe motar na fito abuna. Ido huɗu nayi da kaila yana tsaye suna gaisawa da wani dattijo. Yaci uban ado na kece raini, ga wata mata saye da lafaya a gefenshi a tsaye. Dinkin malum_malum na Ami green shaddace dakakkiyar gaske a jikin kaila, hular kanshi iri ɗaya da design ɗin dake gaban rigar tashi. Sai takalminshi mai rufaffen gaba irin na maza ƴan ƙwalisa. Idanunshi saye da farin tabarau mai ɗan girma, agogonshi da zabban hannayenshi kuma masu ruwan silver. Kunsan Kaila gwanine na iya wanka, duk da na yarda a jinin ƴan jos iya wanka yake. Kawar da kaina nayi, gabana ya tattake ya faɗi, daurewa nayi na soma tawowa ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas_ƙwas tsinin takalmina sai ba da sauti yake yi." Kaila: Mutuwar tsaye Kaila yayi ya ƙame kamar status. Tabarau ɗin dake manne a fuskarshi ya kawar, dan gani yake kamar tabarau ɗinne yake yi mishi gizo. "Ina wannan ba Shanono bace, gizo kawai Idanuna yake yi mun, shanono ba zata zama haka ba" Ya furta a zuchiyarshi tare da girgiza kai a zahiri. Salima Amarya ta dubi Kaila, ta dubi Hajiyar da yake ma wannan mayen kallon. Ta zo har wuya, take taji kamar tayi bindiga ta fashe dam. Kaila kuwa baisan ma me Amaryarshi Salima take ciki ba, kuma ita yai ma rakiya wajan bikin. Shanono tana gibtawa, ni'imtaccen sihirtaccen ƙamshinta mai kaɗa ruwan ƙwaƙwalwa ya sauka a salansar hancin Kaila. Baisan sanda idanuwanshi suka lumshe da kansu ba tsabar daɗin kamshin. Tunda yake bai taɓa jin makamancin ƙamshi irin wannan ba, wannan ya ya kasance na musamman ne. Da yaga turaren Shanono na shirin shagaltar dashi ya rasa kanshi, sai kawai ya tsinci kanshi da furta kalmar. "Shanonooooooooo" Shanono: Cak na tsaya da naji Kaila ya ambaci sunana. Ji nayi kamar ya watsa ma jikina ruwan dalma. Hawayen daya ciko Idanuna ne suka gangaro sirara. Ina jiyo takun tawowar kaila ta bayana. Ƙwab_ƙwab_ƙwab_ƙwab_ƙwab Hannu nasa na goge hawayen fuskata, na juyo. Da Jega muka haɗa idanu, yana tsaye a jikin motarshi ya harɗe hannu yana kallona. Sani da Dauda ne suka nufoni. Tare da Kaila suka iso inda nake a tare. Sani ya kalli Kaila ya kalleni. "Shiga ciki umma. Taro yayi taro a matsayinki na babbar ƙawar Amarya ke ake jira. Kowa jakarki ummana" Jakar hannuna Sani ya karɓa ya riƙo mun hannu muka juya mu ukun muka bar kaila a tsaye........✍🏻NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 11 A tsakiya suka tusani har sai da suka nema mun waje kusa da Yaya Use, kana suka juya Dauda hannunshi sagale a kafaɗun Sani, sunyi anko irin na abokan ango suma. Gabaki ɗaya sai na ji hankalina ya kasa kwanciya sam, jina nake kamar wata marar lafiya. Miki biyu ne suka haɗu suke neman kaini ƙasa. Na farko mikin da Jega ya fama mun a zuchiyata na ƙoƙarin shigar da kanshi zuchiyata, ko ince rayuwata yana ɗan yaro dashi. Ina daga cikin matan da suke ƙalubalantar manyan mata masu yin wuff da samari ƙanana sa'annin yaransu, wasu ma sa'annin jikokinsu. Ai da ace su Sani zasu san me Jega ke shirin yi musu na yi imani a wuyanshi Sani zai dira. Dan yaron zuchiya gareshi, ji dai yanda yayi fito na fito da ubanshi ma. Miki na biyu shine haɗuwata da Kaila, ya rarakemun babban ramin mikin daya tona mun a cikin rayuwata. Ko ɗar banji daɗin ganin Kaila ba, asalima da nasan zan haɗu da azal ɗin haɗuwa da Kaila, da Jega da ban yarda na tako garin Bauchi ba. Amman raina yayi fari fat dana iya gigita nutsuwa da tunanin Kaila, ai nasan Kaila akwai macewa akan mata masu aji. Na kuma yi farin ciki da abinda Sani yayi mishi, hakan ƙila ya zame mishi izna." "Tani Habiba Bala sai yafitoki take yi, hankalinki a ina yake ne?" Na jiyo sautin muryar Yaya Karime a kunnuwana. Kallon inda Amarya da ango suke nayi, naga ni Habiba Bala take kira. A hankali na miƙe jikina babu laka sam. Ina zuwa tsakiyar filin naci karo da Jega, da wani irin mayen kallo mai wuyar fassarawa ya bini. Harara na daddage na dalla mishi, shi kuma ya sakar mun murmushi" KAILA: Mutuwar tsaye yayi kawai. Ya bi Shanono da yaranta da kallo, yabi takun da shanono take yi cikin tsari da gogewa irin ta manyan mata, wayayyu waɗanda suka san ciwukan kansu. Murmushi ya saki. "Wacece wannan Apple da har ta ɗauke maka tunaninka ka mance kanka, a gabana kake ma mace mayen kallo haka, wai dama haka kake? To da kake kallonta sakin ɗaya daga cikin matanka zaka yi ka maye gurbi da ita ko yaya? Gashi naga har Sani ma ya santa, meke faruwane?" A jejjere take tuhumarshi tare da kafeshi da idanuwanta da suka koma jawur dan haushi. Shi kuma Kaila cikin rashin mallakar kai yace. "Gyatumar su Sani ce, uwar ƴaƴanace Shanono" Ya bata amsa tare da soma tafiya, ƙamshin shanono yananan daram a hanyar data wuce yana gauraye da iskar da Kaila yake shaƙa, sai lumshe idanu yake yi. Salima kuma mamakine ya cikata da ganin Shanono ita a tunaninta ba haka zata ga shanono ba, domin taji jita_jitar ance iyayenta mabaratane, amman dai bata da wani labari dangane da ƙazantar da aka dama. Jikin Salima yayi sanyi, dan da a tunaninta tafi ko wacce mace a idanun Kaila, ganin Shanono ya ture mata wannan tunanin kuma ta miƙa wuya cewar Shanono ta fita nesa ba kusa ba, kuma har wayewar da take taƙama dashi Shanono ta kere mata. Uwa uba yanda take fitar da wani irin fitnannan ƙamshi mai sa nutsuwar zuchiya, dan har zuwa lokacin hancinta cike yake da ƙamshin turaren da Shanono ta bar musu a matsayin abinda zai ta buga musu kawunansu. Da jan ƙafa Kaila da Salima suka shiga cikin holl ɗin, tare da samun wani teburi suka zauna. Ashe teburin dake kusa da su Sulaiman ne da su Amina. Sai ji Kaila yayi Balaraba tace. "Baba" Da sauri ya juya, ido huɗu yayi da Sani, yaga yaron na mishi wani irin kwarjini, da sauri ya ɗauke idanunshi akan nashi yana harararshi. Ya yafito Balaraba da hannunshi. Miƙewa tayi tazo kusa dashi. "Kina da number ummanki?" A kunne yake tambayarta, gyaɗa mishi kai tayi halamar e tana dashi. "To shikenan zan karɓi number a wajenki, amman kar ki sake ki faɗama kowa. Inaso in dawo muku da ummanku ne, kuma ku zauna a wajan mamanku" Sani idanunshi a kansu yake, yana ƙissima yanda zai ma Balaraba. Saketa yayi ta koma wajan zamanta, Salima ta harareshi, yayi tsam yana kallonta yama mance da shakkarta da yake ji yau sam. Juyawar da zai yi ya hango Shanono tana sakkowa daga inda Ango da Amarya suke, sai dariya take yi. Ganinshi yayi a tsaye kamar soja yana ƙarema takun Shanono kallo. Sai da Salima ta finciko hannunshi ta dangwarar dashi a kujera, ta nuna shi da ɗan yatsa. "Bari kaji nafi ƙarfin kai mun wulaƙanci wallahi, me akayi akayi ka? Namiji sai shegen kallon matan tsiya kamar wani bunsuru. Ji yanda kake kallonta ka mance da ni a zaune a gefenka. Ina zaka sata to in ta amince ma zata dawo kan yaranta?" Harara ya sakar mata. "Lallai Tanjirin. Baki san waye Shanono a cikin rayuwata bane. Baki san a yanda shanono ta tsinceni mu kai aurenmu na rufin asiri bane. Wanda nayi imani da kece zaki tsinceni a irin yanayin da shanono ta tsinceni ba zaki ma yarda ki saurareni ba. Kuma bance miki dan wani abun nake kallonta ba. So nake mu gaisa a matsayina na wanda mu kai rayuwa tare a baya, yaranmu bakwai tare da ita. Ai kuwa ta riga ta zama ni, na zama ita" Kallonshi ta yi ta sake mayawa. Kana Tace. "Zaka ga buyagin da zanyi maka wallahil azeem. Bari in je wajan su Yaya Hama, in ka ga dama sai kaxo ku gaisa" Sani: Balaraba na komawa yace mata. "Baba zai dawo mana da ummanmu ko? Nafi kowa farin cikin hakan" Ya faɗi hakanne domin ya nuna mata gaba yake da ita, dukan cikinta yayi. Abinka da yarinta nan ta hau ɓarin zance ta kwashe yanda su ka yi kab da Kaila ta faɗi ma yayyenta. Amina ta harareta tace. "Wawuya kinaso ummanmu ta dawo kenan Baba yaci gaba da dukanta yana zaginta a gabanmu ko?" Sani yayi carab yace. "Umma da fa ɗauke ku zata yi a hannun matan Babanmu, ta mayar daku Kano wajenta cikin sabon gidanta. Hankalinmu a kwance. In Umma taji labarin ke kika ba Baba number ta ya kirata. To a Kaduna zata barki wajan Umman Musa, mu kuma mu koma can. Duk sai Balaraba tabi ta ruɗe. Dauda ya harari Sani yace. "Wai me yasa kake yin duk wannan abunne? Ka ba Innata dama ta kwaci kanta a wajen Baba mana, ni ina ganin wannan faɗan nasu ne. Akwai gaɓar da zamu iya shigar mata ko ya kace?" Sani ɗan duniya dan yafi Dauda gogewa sosai yace.. "Ba za ka gane bane. Ai barinsu su yi doguwar magana ka iya rushe mun ƙudurina. Wallahi Allah in har sai Umma ta dawo hannun Baba misali zai ci gaba da numfashi. Tsaiwar numfashinshi yafi mun aikhairi ni. Umma taci wuya fa Yaya. Ta wulaƙanta ta ƙasƙanta sosai" Take hawaye ya soma gudu a kumatunshi, baya ƙaunar abinda zai tuno mishi da rayuwar ummanshi a hannun mahaifinsu. Shanono:. Anata sha'anin biki, kiɗe_kiɗe sai tashi suke yi, Amarya da ango suna zaune sai liƙi ake yi musu. Ƙawayenmu an haɗe kai seti_seti sai hira da shewa irin da duniya tai daɗinnan su ke yi. Ni kuma gabaƙi ɗaya maganganun Jega sai nuƙurƙusar ƙasan raina take yi. Ni ba'a taɓa rainani irin na yau ba. Ni yaro ƙarami haka zai nemi tsarani, ta ya yayi sake zuchiyarshi tayi wasa da tunaninshi? Yaro yarone ko da kuwa ɗan giwa ne. Ta wani bangaren in na tuno da irin ruɗewar da Kaila yayi a kaina sai inji wani farin ciki. Ko banza ina da abinda zan iya ma Kaila ƙwalele dashi, ƙwalele irin na har abadan kuwa. Dan kuwa nasan Kaila babu shi babu runtsawa a daren yau ɗinnan. Haka taro yaci gaba da gudana cikin farin ciki da nishaɗi. Anci ansha an goge wuya abun ba'a cewa komai. Mun yi rabon kasko da tureren wuta, harda ashana, wanda Sabira tai mana odarsu a wajan Mrs Bukhari gidan ƙamshi. Kowa ya samu, har sai da aka koma da rogowar kayan rabon, tsabaragen munyi komai a wadace sosai. Bayan taro ya tashi Sani shi da kanshi ya zo ya fito dani daga taron, ya sani a cikin motarshi, Kaila yana tsaye yana ƙare mana kallo, amaryarshi kuma tana gaisawa da ƙawayenta ne ko ƴan uwanta ne ohon mata dai. A gidan baya na zauna ina sauke ajjiyar zuchiya. Kaila ne ya kirayi Sani yace yaje. Su Amina kuma suka shiga motatata su da Yayansu Dauda. Bansan dai mai Kaila yake cema Sani ba, amman koma meye nasan yana da nasaba da abinda ya faru ɗazu, dan naga sai faɗa yake yi kamar zai daki Sanin. Ya dai gama borin kunyarshi Sani yazo muka bar wajen, ina ganin Kaila yanda yake bina da wani mayen kallo, naga har haɗiɗiyar yawu yake kamsr wani tsohon maye. Sani baice mun komai ba tunda ya shiga motar, sai gudu yake shararawa dani, ni kuma jin shi shiru sai hakan ya taɓani, ya saba da zolayata da kuma yi mun hira dan ya faranta mun. Bansan Sani kuka yake yi ba har sai da muka iso ƙofar gidan su Habiba Bala bayan na fito. Idanunshi sun kaɗa sun yi jawur dasu, hawaye sai zuba yake yi a kumatunshi. Take hankalina ya tashi ainun. Sani kukan me kake yi haka, me Kailan ya faɗa maka?" Na tambayeshi a jere, dai_dai shigowar motar su Dauda. Ka share hawayenka kar ka ɗaga ma ƴan uwanka hankali. Sani bazan taɓa iya bama Kaila dama ko wacce iri bace. Ba kaila kaɗai ba, ni ɗinnan da ka ganni babu batun aure sam a gabana, ina da tarin burika masu girma da nake son ganin na gabatar. Yanzu haka inason in ware office a cikin gidana na sauraren koken Zawarawa, da matan da suke shan wahala a gidan mazajensu. Dan haka kama dena damun kan ka kaji ko?" Murmushi yayi mun yace. "Nagode ummata ina alfahari da kasantuwata a matsayin ɗanki. Ina kishinki umma." Dariya mu ka yi dukkanmu. Dauda da ƙannenshi suka ƙaraso. "Wai Innata shi wannan yaron nunawa yake yi yafi kowa sonki ne? Nifa ban yarda ba wallahi duk bugun zuchiyata da sonki yake bugawa Innata. Sani naga yana shirin ture mun matsayina." Su Amina suma su ka ce ai suma basu yarda ba. Tuni yarana ababen alfaharina suka ɗebe mun damuwar dana shiga. Ina dariya nace. Dukkanku Umma tana sanku. Kune farin cikinta kuma, Dauda kai da Sani zaku je Jos gobe su Amina su harhaɗo kayansu, ku kawo mun su Kano. Zan ci gaba da riƙesu" Tsantsar murna da farin cikin da na gani a idanunsu bazai musaltuba sam. A guje su Amina da su Sulaiman suka shige cikin gidan. Dauda kuma ya ja Sani zuwa gidan abokinshi a maƙota, acan zasu kwana. Na juya zan shiga ciki kenan na ji an ambaci sunana. "Barista Shanono" Cak na tsaya ni ban shiga ba, ni kuma ban juyo ba" Kaila:. Tunda suka shiga ɗakin hotel Salima take huhhura hanci, ƙiris take jira kaila yayi mata magana ta sauke mishi kwandon ruwan masifa da bala'inta. Tunda ba raga mishi take yi ba. Tun a mota take sa ran soma bata haƙuri gami da rarrashinta amman abun mamakin bai ce da'ita komai ba har zuwa yanzu. Nutsuwarshi da tunaninshi ma baya tare dashi. Sakkowa tayi daga kan gado ta ja dogon tsaki ta shige banɗaki. Da idanu ya bita cike da karantar yanayinta. Ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi tare da lumshe idanunshi, ji yake yi tamkar yau ne ya soma shiga sabuwar soyayyar Shanono. Ko a mafarke_mafarken Shanono da ya saba yi baiyi tunanin ganin shanono a haka ba. Ta rikirkita mishi lissafi, ya rasa gane kanshi gami da kasa mallakar kai. Shanono ta zama babbar mai aji wacce ta wuce tunani da hasashe. Takunta, da ƙamshinta yau su suka fi komai ɗimautashi. Daren farkonshi da shanono yake hangowa, da irin alƙawarurrukan daya ɗaukar mata na mallaka mata kanshi, da bata farin cikin da zai mantar da'ita ƙuncin da take ciki. Tunaninshi ya dawo baya wata rana ya dawo daga gajeri jikinshi duk baƙin mai ya shigo ya iske shanono a zaune a bakin murhu tana girki, shi dai yasan bai kawo abinci ba, bai kuma ɗauki sisi ya bata da zai fita ba. Tana fama da tsohon cikin Sani da ƙyar take turawa. "Shanono ina kika samu kuɗi har kike yin girki?" Tambayar daya jefeta dashi kenan. Ita kuma Shanono bata bashi amsa ba, ta ɗakko tire ta zuba musu jallof ɗin taliya, suka shiga daga ciki, wayam yaga babu ko katifa a ɗakin sai ledar tsakar ɗaki, duk kayan ɗakin babu su babu dalilinsu. Kallon tuhuma yai ma Shanono wacce take miƙo mishi damin kuɗi. Tsakin da Salima ta doka ne yasa kaila ɗagowa da sauri ya dubeta. "Wai in tambayeka me kake nufi ne, sakin wata daga cikinmu zaka yi ka dawo da uwar ƴaƴanka koko Yaya, ya ma akayi har ka saketa yanzu kuma kake son yin zawarcinta?" Ta jero mishi tambayoyin cike da tsiwa har tana fitar da ƙwalla. Tsuru Kaila yayi yana kallonta, yana ji kamar son Shanono zai iya sanadinshi kafin wayewar gari. "Tanjirin ya kamata ki shiga taitayinki, ki kuma san waye a gabanki, dan na fuskanci kishi na shirin sanyaki a cikin uku. Kar ki ce zaki tsolma kanki cikin sha'anina da Shanono, zai fi miki tsayawa a iyakar matsayin da kike a wajena. Zancen dawo da Shanono, ko sakin wata mace kuma wannan duk a hannuna yake. Ke baki isa kin hanani abinda nayi ra'ayi ba" Ai Salima sai ta dira a wuyan Kaila, cikin ihu da tafi ta shiga yayyarfo mishi munanan maganganu marasa daɗin ji. Shi kuma yana zaune yana kallonta yama rasa me zai ce mata. Da dai yaga kuka take yi sosai, babu shiri ya shiga aikin rarrashinta, da ƙyar tayi bacci kanta na saman ƙirjin Kaila. Shi kuma sake dulmiya kanshi yayi a tunani. Yana son keɓewa da shanono domin su tattauna kafin ya bar garin Bauchi. Amman Sani na son hanashi rawar gaban hantsi, ya jima da sanin yaron kishin shi yayi yawa, kuma zai iya yin fito na fito dashi akan uwarshi. Shima kuma ganin Shanono yasa yana jin babu abunda zai iya gibtawa ya sake rabashi da farin cikinshi, koma waye, balle Sani ɗan cikinshi ƙaramin alhaki.........✍🏻[19/10, 8:54 a.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 12 SHANONO:. Shiru banji halamar taku ba, kuma banji halamar motsin rai ba. Da sauri na juyo nayi tozali da JEGA a tsaye ya harɗe hannayenshi a ƙirjinshi yana ƙaremun kallo. Wani tuƙuƙin bakin cikine ya turniƙe mun zuchiya. Wai me yaronnan yake nufi da nine, so yake in je in sameshi, ko kuma dai me yake nufi?" Kaina nake yima tambayar, kamar yasan me nace a cikin zuchiyata sai ya soma tattakowa a hankali har zuwa dab dani. Ina jin tururin numfashinshi, wanda ya cakuɗe da ƙamshin turarenshi mai suna cool brize. Da sauri na matsa, jin motsin kamar za'a fito ne yasa na yi hanyar waje, dan bana fatan a ganni tsaye da JEGA. Biyo bayana yayi muka dawo bakin get. Jega ina fatan lafiya dai ko?" "Lafiya lau laifine dan masoyi ya zo wajan masoyiyarshi? Ni a tunanina babu laifi a ciki. Ba da wasa nazo ba wallahi, kuma ba yaudara bace ta kawo ni wajenki ba. Asalima nasan taƙaitaccen tarihinki da lambobin aurenki. Wannan dalilin shi ya kawo ni wajenki, ki yarda dani ba cutarki nazo yi ba, ina miki zalla marar algus a cikinshi" Ido kawai na kafa mishi, ni mamaki yaron yake bani, baya ko jin kunya, kuma na fuskanci da gasken gaske yake yi. Shi yasa na nutsu zan yi mishi bayani da kyau yanda zai fahimta, na tabbatar yarinta ke ɗibarshi. JEGA kai yarone matashi mai jini a jika. Bazawara mai yara takwas bata dace da kai ba sam, bazawararma mai aure biyar. Yarana manya ne, zasu iya yin fito na fito da kai, abun bazai yi maka kyau ba. Ina da halaƙar mutunci kyakkyawa tsakanina da mahaifinka. Mahaifiyarka kishiyar Aminiyata ce, mahaifinka mijin aminiyata ne. Taya zaka zo mun da wannan lamarin a matsayinka na yaro ƙarami. JEGA baka da budurwane?" Na tambayeshi ina mai tsattsareshi da ido. "Ina da mata dai ba budurwa ba. Ina da yarana biyu mace da Namiji. Kinga magidancine ni ba yaro yanda kike tunani ba. Batun mahaifiyata, da mahaifina da kike kawowa kuma. Ni banga wata matsala ba dan na tunkaresu kai tsaye da wannan maganar ba. Nine fa nace inaso, kuma zan iya. Ko tunani kike bazan iya bi dake yanda ya dace bane uhm?" Duk wata tsiga ta jikina sai da suka tashi, gashin jikina su kai tsaye, a sakamakon furucin da JEGA ya feso mun. Kunyace ta lulluɓeni, kamar yanda shima kunyar ta dabaibayeshi har yana runtse idanu. Wajen ya ɗauki shiru na wasu lokuta kafin yayi ƙarfin halin cewa. "Kiyi haƙuri da furucina, ke kike ingizani in kika kirani da yaro, ni ba yaro bane, zan iya sawa ki mance da tunaninki. Kije ki kwanta dare yayi, sai nazo taɗi in sha Allah, Allah yasa kiyi mafarkin munyi aure harda tagomashin fita yawon buɗe idanu. Ƙila shi zai kasance na farko a rayuwarki, dan ban tamman ƴan ƙauyan da kika aura a baya sun san yawon buɗe ido ba" Yana kaiwa nan ya fice. Hawaye masu zafi suka zubo mun a kan kumatuna. Zawarci babu daɗi, yanzu in banda Zawarci taya JEGA zai zo wajena a matsayin mai neman aurena, har yana furta kalaman sakin layi. Lallai Bazawara kina ganin rayuwa, Allah sarki zawarawan Arewa shanono ta yi kuka da kukanku. Na fi minti goma a tsaye ina tubka da warwara, kafin na shiga ciki na samu jama'ar biki. Wasu na zube a falo anata sheƙar bacci. Ɗakin Habiba Bala kuwa sai hira ke tashi harma da shewa. Babu walwala na shiga ɗakin da sallama. Banɗaki nayi saurin shigewa dan ma kar Habiba Bala ta ganni a cikin damuwa ta damu kanta itama. Ga Sabira ma muna haɗa ido zata gane me nake ciki. Wanka nayo na dole, na fito ɗaure da tawul da kayan dana cire a hannuna. Sukuku nake komai, amman da yake cikin hira suke, babu wanda ya kula dani ma. Ina sa kayan bacci na nemi waje a ƙasa nayi kwanciyata. Ido kawai na rufe zuchiyata na suya, tun inajin tashin muryoyin masu hira, da masu waye_waye har naji shiru, halamun sun yi bacci kenan. Idanuna na buɗe sunyi jawur sun kuma kumbura, hawaye sai tsiyaya suke ta gefen Idanuna. Silin na ƙurama idanu ina tunanin irin yanda maza suka ƙware wajen yaudara, ni babu irin yaudarar da ban gani ba, babu daɗin bakin da maza ba sui mun ba, maƙaryata masu son kansu da yawa. Ji yaro ƙarami suna zaman zamanshi da ƴar matarshi da yaranshi, yana neman ya jajiɓo ma iyalanshi wani al'amari. Yanzu in mahaifiyarshi ta Sani dan Allah me zata ɗauka, goɗai_goɗai dani sai in auri yaron mijin ƙawata abu ba ko fasali" bansan iya daɗewar da nayi ina karanta wasiƙar jaki ba. Ni dai bansan baccin awa nawa na samu ba. "Shanono tashi lokacin Sallah yayi, da wuri zamu wuce, kuma a gidansu Mama za'a ɗaukeni kinsan" Cewar Habiba Bala kenan. A hankali na buɗe idanuna da suka kumbura su kai suntum. Habiba Bala ta kalleni tace" "Kuka kika raba dare kina faman yi kenan ko? To me ya same ki Shanono, ni ai nayi tunanin kukanki ya ƙare tunda Allah ya cicciɓeki kina kan babban matsayi mai daraja. Jibi yaranki fa gwanin sha'awa, nifa nawa yaran bani da sabo dasu sam mahaifinsu ya daƙile hakan. To wacce damuwace zata dameki?" Shiru nayi mata kawai, bana iya ɓoye ma Habiba Bala komai. Amman lamarin JEGA na zaɓi in ɓoye mata shi. Sai nace mata. Bari in yi salla in zo zaki ji dalilin kukan nawa." Sai da na shirya tsab cikin ado da kwalliya da suka zame mun jiki, na bi jama'a muka gaggaisa. A wajen su Yaya karime na zauna, Sabira da su Amina ma acan na tarar dasu. Na shiga cikinsu muka karya baki ɗaya. "To Tani mu kam yau zamu gudu. Sai kuma mun zo Kano ganin Amarya. Shikenan Aminiya ta dawo kusa dake ko?" Dariya nayi ma Yaya Use nace. Hakane kam ai ina farin cikin hakan. Dauda ma ya samu canjin wajen aiki, shima Kanon zai koma Habiba Bala tace dashi zata tafi." Yaya Karime tace. "Gaskiya Habiba Bala na ƙaunarmu da yawa, yanzu da wannan tiƙeƙen saurayin zata tafi gidan auren? Iko sai Allah, batun shagon ɗinkinshi kuma fa?" Nace musu. E zasu koma da aikin nasu Kano da yaran shagon duka, in da zasu dinga kwana bazai gagaraba. Kano akwai arziki a cikinta, ko ɗinkin kaɗai zai iya isarsu ma. Yaran kuma nace suje dasu su kwaso kayansu a kai mun su Kano, zanci gaba da kulawa da yarana. Shi kuma yaci gaba da kulawa da sauran yaran nashi da matanshi." Sabira tace. "Kuma kina ganin hakan bazai zama wata matsala ba? Tani ke da muke miki fatan Aure shine zaki ɗebi yara ki mayar dasu hannunki, ki yi haquri ki bar yarannan a gidan ubansu, tunda kinga ga Dauda zai koma kusa dake. Ai uban yana ƙoƙarinshi a kansu" Wallahi Sabira ku baza ku gane bane. Sabida tare da yaranku kuke yin rayuwarku hankalinku kwance, baku san raɗaɗi da zafin ranuwa da yara bane. Sanadiyyar yarannan na kamu da lalurar hawan jini, sabida tunaninsu da nake yi babu dare babu rana. A halin yanzu bazan iya zama suna wata uwa duniya nima ina wata uwa duniya ba. Ku barni dan Allah kar ku hanani" Jikkunansu yayi sanyi sosai da sosai. Yaya Use tace. "Allah yasa hakan shine mafi alkairi Tani. Shikenan bamu isa mun rabaki da yaranki ba, yara tarbiyyarsu a hannun mahaifiyarsu yafi ai" Da haka zancan ya mutu dai, su Yaya Use suna yin wanka su ka hau azamar komawa Jos. Ko da su ka je yima Habiba Bala sallama sai da ta basu kuɗi, bayan cincin dasu alkaki data basu hilimi guda. Ƙin karɓa su ka yi fur. Tafiyarsu Yaya Use da kaɗan kuma sai ga su Sani sun shigo da shirinsu na tafiya Kaduna. A motar Sani suka ɗura ƙannen nasu suka tafi, Dauda kuma ya miƙo mun Key ɗin motata. Mu kuma. Da su Sabira muka kama hanyar gidansu Habiba Bala, wanda ta gyara musu ya dawo kamar ma ba shi bane. Sha ɗayan rana muka kama hanyar Kano. Gaga_gaga awanmu huɗu cib a hanya kafin muka shiga garin Kano ta dabo tumbin giwa. Kai tsaye zuwa Hotoro. Wani tabkeken gidan sama babba muka shiga, family house ne babba, ga motocinan jejjere. Ga canopys an kakkafa a tsakar gidan, da kayan kiɗa jibge a gefe guda. Da dukkan halamu wani sabon bidirin za'ayi a gidan ma. Muna fitowa dangin ango da dangin uwar gidan sukai mana tarbar arziki. Angwaye kuma suka wuce nasu ɓangaren daban. Da jagorancin Dangin Alh Nura muka samu damar ɗanewa sama ɓarayin Amarya wanda ya sha gyara matuƙa gaya. Babu wani hayaniyar kaya a ɓarayin. Ni babban abida yafi tafiya dani wata durowa na hango a kusa da Tv cike da turarukan wuta da humra, kwalaben ma abun kallone, dan ƴan Dubai ne ba ma ƴan ƙasata Najeriya ba. Abin mamaki sai naga sticer a jikin durowar mai ɗauke da tambari da sunan Mrs Bukhari gidan ƙamshi. Lallai matarnan ta shahara, wato har durowa suke zuwa su kafe ma amarya a ɗaki, aikin ki yana kyau Mrs Bukhari. Ciki muka shige kowa na ta faɗin masha Allah_ masha Allah. Bayan mun zauna mun huta kuma sai aka gabatar mana mana da abinci. Ɗaya daga cikin matan da suka shigo mana da abincin tace. "Hajiya tace mu sanar muku akwai biki data shirya na tarbar Amarya. Misalin ƙarfe huɗu za'a yi a cikin harabar gidannan." To shikenan Allah ya nuna mana lokacin, kuma a isar mana da godiya, kafin muzo da kanmu." Na ari bakin kowa da kowa na bata amsa. Bayan mun cicci abinci, an yi ramuwar sallah, sai muka soma yin wanka domin soma shiri. Mai Hula na kira a waya na mata kwatancen inda muke nace ta turo mun ƙanwarta mai make up tazo tai ma Amarya. Duk da bamu zo da shirin yin taro ba, ya kamata Amarya a kalleta a kuma, tunda ita uwar gidan bamu san irin shigar da zata yi, bamu da masaniya akan shirinta. Habiba Bala da Sabira na ja wani ɗaki daban. Habiba kina da wasu kaya da zaki yi amfani dasu na kece raini, ko kuma muje mu siyo miki ɗinkakku? Ko ba Gaskiya ba Sabira, uwar gidan bamu san shirin ta ba ko ya kuka gani?" Habiba Bala tace. "Ina da laces, da material, da atampa ɗinkin dubai irin mai stone dubu ɗinnan. Sannan ina da lafaya mai stone, da bakin lace. Mu je ku gani." Komawa mu ka yi uwar ɗakin Habiba Bala ta nuna mana. Atampar Aura ce, kuma ɗinkin ya dace da atampar sosai, gashi stone sai walwalin kashe idanu suke yi. To inaga abinda zamu siyo takalmi da ƴar jaka ne ko, sai ashoke na ɗaurawa akai. Sabira muje, lafin a gama make up ɗin mun dawo da izinin Allah." Sallama mu ka yi musu muka fito. A falon ƙasa muka haɗu da JEGA riƙe da hannun wata ƴar yarinya mai gashi. Yana ganina ya sakar mun murmushi. Ni ko na ɗauke kaina kamar ban ma sanshi ba. Bamu muka shigo gidan ba sai wajajen ƙarfe huɗu da rabi na yamma. Har zuwa wannan lokacin ba'a soma taron ba, an dai soma shirya kujeru da tebura. Masu kiɗa ma sun soma harhaɗa kawunansu. Kiɗanma kamar irin giɗan duma ne. Unguji suka kira daga Kaduna za'a saki duma. Na lura uwar gida ta shirya ma wannan biki tsab. Muna shiga muka tarar da Amarya an gama yi mata make up ta fito shar da'ita. Ɗaurin ashoke akayi mata, ta fito sai sheƙi take yi. Ta sa ɗankunne da sarƙa, da zobe da awarwaro na gwal seti ne guda mai kyau sosai. Sha'anin bikinnan ba'a soma ba sai da mu kai sallar magriba, kafin muka soma jiyo sautin kiɗan duma. Uwar gida Hajiya Kilishi da kanta ta shigo ɓarayin Amarya bisa jagorancin aminiyarta. Tako ci uwa da uban ado, ko iyakar gwai data damɓara a wuyanta abun a kalla ne. Lashi jikinta wanda akaima ɗinkin bubu kuɗin shi zai ɗara dubu ɗari biyu. Dake ba mai ƙiba bace, sai girma bai nuna a fuskarta ba, babu wanda zai ce ita ta haifi JEGA, dan da kaɗan ta wuce tsararmu, a idona dai nasan ba zata wuce shekarun Yaya Karime ba. Hannun Habiba Bala ta riƙe tana fara'a muka fita zuwa tsakar gidan. Kafin mu fita wajen ya karaɗe da guɗa ga hasken fitulo tamkar rana. Ina gefen hannun hagun Hajiya Kilishi. Har muka isa inda aka tanadar domin Amarya da danginta. Hidima gagaruma akayi a wannan dare, Unguji ya gwangwajemu da kiɗan duma, mun sa amarya a tsakiya mu ka ɗan rausaya ba mai yawa ba. Muna cikin filin rawar ne Hajiya Kilishi ta yafito wata kyakkyawar budurwa, tana isowa ta kama hannunta tace da Habiba. "Amarya ga matar Babban Ɗanki Jega Khadija sunanta. Itace surukata ta farko. Sai na tsinci kaina da ƙarema Khadija kallo da kyau. Baka ce kyakkyawar gaske, gata da fararen idanu da cikar gashin gira. Ɗagowar da nayi na hango JEGA a can gefe yana yi mana video da camara a hannunshi. Numfashi na ja..........✍🏻 [19/10, 5:04 p.m.] DEAR BADI'AT IBRAHIM: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 13 Ba shiri na zame daga cikin filin na je kusa da Sabira na zauna nima na zama ƴar kallo. Duk inda Khadija ta wulga idona a kanta. Har zuwa wajen JEGA da tayi ina kallonta. Oh maza kenan, jibi matarshi kyakkyawa amman ya kasa runtse idanunshi da kallona. Dududu yaranshi biyu, amman yana neman ƙarin aure da Bazawara mai yara takwas Aure biyar. Wayata ce naga tana wuta Sani ne yake kirana a waya. Sai na nufi bayan gidan can inda babu kiɗan sosai na ɗaga wayar. "Umma gamu mun shigo Kano, muna cikin gidansu Inno ma." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Alhamdulillah, barkan ku da isowa lafiya. Zan dawo gida zuwa anjima in sha Allah. Akwai event ne da akeyi bazan iya tahowa ba tare da an gama ba. Amman dai zan dawo da zaran an kammala, kaji ko?" "To Umma Allah ya dawo mana dake lafiya ummanmu." Murmushi nayi mishi nace. Ameen yaron Ummanshi." Mu kai sallama na sauke wayar a kunnena. Juyowar da zanyi naga JEGA yayi tsaye a bayana ya shagaltu da kallona. Sauke kaina ƙasa nayi bance komai ba. Domin al'amarin nashi ya soma isata hakanan. Ina jin kaifin idanunshi yana yawo a jikina. Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace. "Wallahi Allah ba yaudararki zanyi ba. Aurenki nake son yi dan mu raya sunnar ma'aiki Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama. Ban shiga rayuwarki domin in cutar ko in tozarta shekarunki ba. Kar ki mance nima fa ɗane ai bazan so a tozarta mun uwa ba, taya zan tozartaki Barista? Sama da shekara guda na jarabtu da sonki mai zafin gaske. Na soma saninki ne ta dalilin yanar gizo, na kasance mai bibiyar rubuce_rubucenki da kike yi akan harkar abinda ya shafi hakkin mata. Dana nan na gane ke ƴar gwagwarmaya ce. Barista in fa baki bani dama mun fahimci juna ba, to magana ta gaskiya zan tunkari Umma Habiba da batun neman aurenki, kuma ina sa ran zata shige mun gaba har zuwa wajan mahaifina." Da sauri na ɗago muka haɗa idanu waje guda, sai naga JEGA ya saka fuskar tausayi sosai. Ni ba yarinya bace, na san so, na san yanda zafin so yake sosai. Tabbas Jega yana sona ainun, ina iya karanta zuchiyarshi a fuskarshi. Matsalar itace Shanono ba Aure zata yi ba, baya gabanta, a ma ture batun yarinta a gefe. Shirin wuceshi nake yi, JEGA yayi ƙarfin halin riƙe mun hannuna. Naji wani zum, kallon dana watso mai ne yasa babu shiri ya saki hannuna. In ka sake tunanin furta mun kalmar so zanyi maganinka Samari. Kar ka sake tare mun hanya na faɗa ma kenan, sakarai kawai yara kun tusa Kallon indiya a gaba, soyayya na son ta ɓata muku tunaninku" Ina kaiwa ƙarshe na ja tsaki na barshi a tsaye ya kasa ko motsawa. Ni ko dan haushi ina fitowa na haura sama ta ɗakko jakata na sulale na nufo gida abuna. Ina shiga gidan na tarar da wata sabuwar dirama. Kaila ya kira a waya yana zazzaga ma yara ruwan faɗa. Zare wayar a hannun Amina nayi na kanga a kunnena. Nice na ce a ɗakko mun su. Ko yaranka ne kai kaɗai ka yi yinƙurin naƙudarsu ne? Yara dai sun dawo hannuna shine magana, kuma ina da ikon karɓar yarana, in baka yarda ba mu haɗu a kotu Allah ya ba mai rabo sa'a" Ban bashi zarafin cewa komai ba, na datse wayar. Inno dake tsaye ita da Ige tace. "Iko sai Allah. Tani ai da kin bar mishi yaranshi ko dan gudun fitina yazo yana tayar mana da hankali a banza" Baffa daya fito daga ɗaki yace. "A'a Inno mu bar yarinya tayi abinda ya dace. A baya mun tauye mata hakkinta. Kada mu sake yanzu ma mu tauye mata wani hakki. Tani Allah ya taya ki riƙon yaran. Su mazan sai mu zauna dasu anan, matan dai kwa zauna tare kafin ki ƙarashe gyaran gidan naki, Allah yayi miki albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke na farin ciki. Kaila kuma in dai yace hankali zai ɗaga mun to kotu zamu je alƙali yai mana iyaka dashi, shine maganar gaskiya. Tare da yaran duka muka ɗunguma gidana dake manne dana su Inno. So nake in yi gyara sosai a haɗe gidanma ya sake yin faɗi, in mishi gyara mai kyau. Sabida in dangi sun zo su samu damar hutawa. Su Sani ana falo an baje kolin hira da dariya. Ni kuma hankalina da tunanina baya ma jikina. Shin ko Habiba Bala zan sanarma batun JeGa ne ko ba komai ta sanar ma mahaifinshi dan a ja mar kunne. Kar in zo in yi mishi abunda sam bazai ji daɗi ba." Kaila:. Ko da suka kwana a Bauchi da sassafe ya shiga kiran wayar Amina dan ta kwatanta mishi gidan da Shanono take. Amman Amina fur taƙi ɗaukar wayarshi. Ya kira Sulaiman kiran duniya shima bai ɗauka ba. Take zazzaɓi ya lulluɓeshi mai zafi. Dan a cikin tunanin shanono ya kwana. Sai biyun rana suka bar garin Bauchi. Sun ɗanyi tsaye_tsaye a hanya, gaishe_gaishen ƴan uwan Salima. basu suka shiga gida ba sai wajajen taran dare. Yana dawowa Hajiyayye ta tarbeshi. "Barka da dawowa Kaila. Salima an dawo?" Hararar Hajiyayye tayi ta yi shigewarta ciki. Hajiyayye ta kalli kanta da koɗaɗɗen zanin dake ɗaure a jikinta tayi murmushi tace. "Salima kenan. Da kinsan sha'anin maza da baki ɗauki duniya da zafi haka ba. Ballema da kikai dace da samun irin su Kaila " A fusace yace da ita. "Me kike nufi Hajiyayye?" "Ina nufin kai azzalumine Kaila. Ni kam gidanmu zan tafi, zan bar maka yaranka ka kula dasu. Sannan ina mai maka albishir, Shanono ta kwashe yaranta sun koma hannunta. Sun zo sun kwashe komai da yake mallakinsu sun ma matan gida sallama. Dan haka nima banci ta zama ba, bazan zauna zaman ƴaƴa ya sa in rasa rayuwata ba. Jibi yanda ka mayar damu bola ni da Shamwila, ka mayar damu ababen tausayi. Duk da dai mu muka jama kanmu. Mu mata in namiji ya fifitamu, mu kuma sai mui amfani da wannan damar ta hanyar cusgunama mata ƴan uwanmu. Babu da irin makirci, da bita da ƙullin da banyi ma Umman Sulaiman ba. Dan kawai ka fifitani samanta. Kuna zaman zamanku na mutunci na shigo rayuwarku, sanadiyyata wulaƙanci da tozarci wannena bata gani ba? Nima kuma ai naga iyakata tun zamanin Bilkisa. Shamwila tazo ta rama ma umman Sulaiman duk abinda nayi mata harda riba. Salima itama tazo ta rama mun abinda Shamwila tai mun. Haka gidanka da rayuwarka zata ci gaba Kaila muddin baka gyara ba wallahi" Kuka ta fashe mishi dashi mai tsuma zuchiya, shi kuma yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi. Duk jijiyoyin jikinshi sun ɗaɗɗaure. Hajiyayye taci gaba da cewa. "Sani da ƙannenshi basa ƙaunar buɗe idanu su ganka a cikin gidannan. Yaron bai sake walwalaba har sai da yaji labarin mahaifiyarshi. Ga Samira can bata son ma in dangantata da kai. Haka suma kakeso su taso ko? To ni na gaji ka sakeni ko in kai ƙararka kotu bazan iyaba Kaila ya isa haka, ai nayi ibada." Tana kaiwa nan ta wuce fuu zata nufi BQ inda take rayuwa. Sai kallonta yake yi yanda ta zama ƙazama kamar ba Hajiyayye gwanar kwalliya ba. Ita kanta Shamwila ta fice a hayyacinta kamar bama ita bace. Sai yau ne Kaila ya gane ashe shi yake lalata matanshi na gida, sai yaga sun tsufa, shi kuma sai ya fice ya sake nemo wata. Yanzu ya gane rashin kula da mace shike sawa ta lalace ta fice a hayyacinta. Take nadama gami da dana sani ta saukar mishi. Bazai yi gigin rabuwa da Hajiyayye ba, domin duk da tayi abubbuwa, amman daga baya ya zalunceta. In ma akwai wacce ta dace ta bar gidan to Shamwila ce ya dace ya saki. Lokaci yayi daya dace ya haɗe kan yaranshi da matanshi waje guda." Wayarshi ya zaro ya kira Sani yana mishi sababi akan me zasu bar gida ba tare da an sanarma kowa ba, kuma wani babba bai zo ya mishi magana ba. Ana cikin haka ya jiyo muryar Shanono tana bashi bayani. Ƙwaƙwalwarshi kusan juyewa tayi dan mamaki wai yau shi Shanono take sanarma su haɗu a kotu. A sanyaye ya zare wayar a kunnenshi, ya nufi ɗakin Hajiyayye ya sameta sai harhaɗa kaya take yi. Carab ya cabki boron kayan nata. Ta juyo suka haɗa idanu, hawaye suka ci gaba da tsiyaya a kumatunta. "Hajiyayye ki yi haquri kar ki tafi ko ina. Zan gyara duk abinda na ɓata da kaina. Kuma zan tattare kan yarana in kula dasu yanda ya dace, in koya musu zumunci da son junansu. Kiyi haƙuri na san na zalunceki ki yafe mun ki zauna a ɗakin ki. Gobe zan tafi Kano in dawo da su Amina. Zan gyara miki waje a cikin gida in da zaki zauna. Shamwila kuma zan sallameta ta kama gabanta, domin bana ko ƙaunar in buɗe idanu in ganta a gefena. Bazan iya ci gaba da zama da'ita ina mai cike da zarginta ba" Hajiyayye tace. "Zargi wanne iri, ashe nima cike kake da zargina duk tsawon shekarunnan? Tunda dai na yi kuskuren baka jikina tun a waje." Kai ya girgiza yace. "Ko ɗaya wallahi. Ai ke nayi imani bayan ni babu wanda ya sanki. Domin ni na yage tantaninki. Itako Shamwila muna bara muna karuwa ce, babu hotel ɗin ba bata sanshi ba a cikin garinnan. Idonane ya rufe shi yasa har na aureta. Dan haka zan rabu da'ita in je in dawo da Umman Fatima daga Zaria ta dawo kuci gaba da zama. Tunda na auri Shamwila ta juya mun baya, har yau da nake gabanki Ɗanyan gwal fishi take yi dani shekara nawa." Haka dai Kaila ya rarrashi Hajiyayye tare da yi mata alkawarin komai zai daidaita, dama shi ya ɓata, zai kuma gyara. Fitowarshi ke da wuya ya nufi ɗakin Shamwila da zummar sallamarta. Sai yaji tana waya tana faɗin. "To shikenan zan zo zuwa anjima ka turo mun lambar ɗakin naka " Ganin Kaila a tsaye a kanta ne yasa ta saki wayar ta faɗi. Sai ta sau kuka kawai. Shima wasu hawayene suka shiga yi mishi zarya a kumatunshi. Tunani ya sureshi. Ita dama zina yaɗuwa take yi ta kewaye zuriya. Tunda shima ya aikata zinar nan da yaran wasu, shima gashi ana neman danne mishi tashi matar. "Kaicona da son zuchiya yasa na kasa iya faɗama kaina gaskiya na bi son zuchiya na auri marar tarbiya. Shamwila bazan dakeki ba, bazan zageki ba, abinda na shuka ne nake girba. Kije na sakeki saki uku, kar ki sake in dawo in sameki. Yarana sun raba gardama domin da yayyensu suke kama. Dan haka ki miƙa mun su wajen Hajiyayye " Juyawa yayi ya haye sama ya kulle kanshi sai tunanika ne suke dawo mishi. Kaila ya shiga tashin hankali mai yawan gaske a wannan dare. Sallar isha a ɗaki ya yi ta. Bai ci komai ba tun karin kumallon safe. Ga zazzaɓi kau a jikinshi. Wayarshi ya ɗaga ya kira Alh Isa. "Kaila ya kana gari kenan?" Ya ambayeshi. Cike da kasala yace. "Isa kai mun rakiya gobe zuwa Kano gidan Shanono, ta kwashe mun yara inason in dawo dasu ne. Yaran su nake buɗe ido in gani in ji sanyi Isa." Ajjiyar zuchiya isa ya sauke yace. "Tanin dama an san inda take ashe Kaila?" "Ba'a jima da jin labarin nata ba. Dan kwanakin baya can yaran suka zo mun da labarinta. Har ma suka tattare suka je mata ziyara, da akai hutu ma suka je mata. To yaune tasa Sani yazo ya kwashe mata kayan yaran dama suna tare da'ita a Bauchi sun je biki. To wai har ni Shanono take cema yara sun koma hannunta, in ina ganin kuma mu haɗu a kotu ne to" Da Alh Isa ya lura a cikin damuwa Kaila yake, sai ya rarrasheshi akan gobe da safe zai zo ya ɗaukeshi su tafi Kanon, a haka suka rabu. Kwana Kaila yayi yana juyi a kan gado ya rasa me ke yi mishi daɗi. Wannan dare yayi mishi nisa sosai da ƙyar garin ya waye. Alwala ya ɗaura ya fito zashi masallaci yaci karo da Salima. Harararshi tayi ta ja tsaki ta yi shigewarta ɓarayinta. Kai ya girgiza kawai ya wuce abinshi. Yana dawowa daga masallaci yayi wanka ya kece ado na daukar hankali matuƙa gaya, burinshi ya burge Shanono, yana fatan ta sanadiyyar yara ƙila auren nasu ya dawo, kuma yanzu ga gurbi ya nema mata na zama, duk ba da niyya yayi hakan ba. Ɓarayin Salima ya shiga, ko sallamarshi ta kasa amsawa. "Zan tafi Kano, daga can zan shiga Zaria. Inaso ke da Hajiyayye ku gyara wancan shashen Umman su Fatima zata dawo kuci gaba da zama. Itama Hajiyayye zata dawo ɗayan shashen?" Buɗar bakin Salima tace. "Ita kuma Shanono turakarka zaka bata ko, tunda ka saki Shamwila ka koreta dan uwar ƴaƴanka ta samu gurbi" Murmushi yayi mata yace. "Dukka gidannan gurbin Shanono ne, dani da dukiyata duk mallakin yaran Shanono ne, kinga kuwa a tafin hannunta nake. Ko bata dawo gidana ba, ai tafi ƙarfinki sai dai ki kalleta." Ficewarshi yayi. Yaje su ka gaisa da Hajiyayye ya jaddada mata abinda yace ma Salima, na game da komawarta ciki, da kuma gyaran ɓarayin Bilkisa. Godiya tayi mishi tare da yi mishi adda'ar dawowa lafiya. Fita yayi daga BQ ɗin ya samu Alh Isa a cikin mota, suma sun jima da dawowa Kaduna da iyalanshi. Sai da suka kama hanyar Kano Kaila ya samu salama." Barrister Shanono:. Tun sassafe na shirya tsab cikin shigar aiki, yau ina da sabuwar shari'a mai zafin gaske. Sani ne ya dafa mana tea ya soya mana wainar ƙwai. A gurguje naci, nai musu sallama na fita. Sai da na shiga gidan su Inno muka gaisa kafin na nufi chamba. Ina shiga na tarar ana shirye_shiryen meeting. Misalin ƙarfe takwas na safe duk muka hallara a meeting holl, duk muka doka wayoyinmu a silent dan gudun kar a kira ana tsakiyar tattaunawa. Oga Rashid ya soma magana. "Am maƙasudin wannan taron, na taraku ne domin mu tattauna akan wasu matsaloli da suka shigo mana wannan Chamba. Tun farko dana buɗe Chambata, na buɗetane domin in tallafi ƙananun baristoci da suka gama karatunsu na low suna yawon neman aiki. Gaskiya dokin ƙarfe na kafata ne domin gaskiya da gaskiya. A cikin baristocin da ni nake dasu, an samu waɗanda ake haɗa baki dasu ana murɗe ma masu hakki hakkinsu, akan abun duniyar da bai taka kara ya karyaba. Ni tsohon lauyane nasan yanda harkar take, nasan yanda ake mana tayin kudi, nasan yanda ake mana barazana da ranmu. Akwai wara shari'a dana gabatar shekaru talatin baya, wallahi sanadiyyar wannan shari'ar har makaranta akabi mai ɗakina aka saceta, tun duniyarma na kwance. Akace in ban ƙaryata duk hujjojin dana kafa ba wallahi sai sun kasheta. A lokacin na shiga tsaka mai wuyar fita, gashi ɓangaren dana riƙa rauni garesu ni suka riƙe a matsayin sandar jagoransu. Da dabara dai aka sako mun matata, nai musu alƙawarin zan ƙaryata kaina. Bayan sun sakota aka gama shari'ar ba tare da na yi abinda su suke so ba. Amman har biyoni su kai a titi suka harbeni a hannu. Banda motoci, ko gida da za'aima tayinsu. In muka ce zamu ruɗu da irin wannan tayin wallahi zamu cutar da kanmu ne. Sannan kun rage ƙwazo da himma akan aiyukanku. Barista Shanono, da Barister mai Hula ne suka fi kowa mayar da hankali akan aiyukansu. Kuma in suka nace ma kes sai sun yi nasara. Sannan suna da hanyayo da salon bincike sosai, ina bibiyar aiyukan kowa. Wannan shine maƙasudin taron namu. Kuma akwai sammaci da muka yanka ma mutum 6, zan rarraba muku aikin in sha Allah. In da me magana sai yayi" Mun fi awa uku muna abu ɗaya, daga bisani ya Sallamemu taron ya watse. Da zan fita Oga Rashid yace in na rarrage ayyukana in zo in sameshi zamu yi magana. Ina zama a teburina wayata ta shiga haske dake a silent take. Sabuwar number na gani. Ɗagawa nayi na kara a kunnena. Sai naji muryar mijin Habiba Bala. "Barista shine jiya kika gudu ko sallama babu ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke da naji muryar tashi washar da'ita. Na yi tunanin Jega ya kira mun ruwane. Ango da kanshi, barka da safiya ya kwanan Amaryar?" Da dariya yace. "Gata ita tace in kirawoki ma" Miƙa mata wayar Yayi. "Shine kika gudu ko Shanono dan wulaƙanci, su Sabira sai nemanki suke yi." Yi hakuri kira na samu na gaggawa ƙawata kuma nasan in dai nace miki zan tafi ba lallai ki amince ba. Ya kin tashi lafiya?" Dariya kawai tayi mun tace. "Zaki zo ne in kin baro office akwai labari fa" Nima dariyar na mayar mata nace. To zan yi kokarin hakan. Yaranki fa sun dawo hannuna, jiya ma Kaila ya kira ta inda yake shiga ba tanan yake shiga ba. In nazo ma zaɓa musu makarantar da kika ga ta dace dasu, sai nazo, Sabira sun koma ne?" "Tun yaushe, taje ma gida ta dubo su Inno. Tasan kin tara aiki a office ne shi yasa ma bata bi ta kanki ba, sun kusa shiga Jos ma ai yanzu" Sallama nayi mata, ina sauke wayar kiran Sani ya shigo. Sani ya akayi?" "Umma su Babane suka zo, suna cikin gidan su Inno, Baffa ne yace in kira ki, in ba wani abun kike yi ki zo yanzu." Gabana ya yanke ya faɗi ras a sanyaye nace. To ganinan zuwa yanzu Sani. Har zan kashe wayar yace. "Umman kin mun alƙawarin ba zaki koma hannun Babanmu ba, kar ki manta da wannan. Ni bazan taɓa yarda ki koma mishi ba umma" murmushi nayi dan in kwantar mishi da hankali. Babu ma wannan zancan Sani, kaji ko kasha kuruminka ganinan zuwa" Wayar na kashe Mai Hula ta kalleni tace. "Wata matsalarce?" E yarane nasa aka kwaso mun suka dawo hannuna, shine Babansu ya biyo sahu. Baffa ne yace yanason ganina. Bari in je sai na dawo" Fita nayi zuwa ofishin Oga Rashid. Kwankwasawa nayi ya bani izinin shiga. Ƙwas_ƙwas_kwas na shiga, kujera ya nuna mini yana murmushi. Nagode sosai Sir. "Ai ya zame mun wajibi in baki waje zama ni fa na gayyaceki" Katseshi nayi. Dama a gidane mahaifina yake nemana akwai abun da ya taso ne, shine nake neman izininka" Da mamaki ya kalleni yace. "Dama tare kike da mahaifanki a garinnan?" A'a dawowa dai su ka yi, da Bama tare sir" Murmushi yayi yace. "Allah sarki, to a gurguje nima bari in yi amfani da wannan damar domin in fallasa miki asirin zuchiyata, tunda kin ƙi ki fahimci inda na dosa sam. Kaina nayi sauri na sunkuyar gabana ya shiga harbawa Fat_fat_fat......... Team Kaila # Team JEGA # Team Oga Rashid # Ku futo. A ganinku wa ya fi cancanta Shanono ta miƙa ma zuchiyarta a karo na shida ?.....NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 14 "Barista na jima sosai ina rainon jaririn sonki a zuchiyata har yayi girman da nake kasa mallakar kaina. A mafiya yawan lokuta, zagaye da nake yi zuwa ofishoshin ma'aikata, ina yine domin in ganki in ji sanyi. Ina sonki Shanono, Allah yasa babu wanda ya rigani, dan ni tun ina matashi bana iya haɗa soyayyar mata biyu. In kuma naje wajen mace na ganta tana kula wani saurayin to jaye jikina nake yi. Dan ni in inaso ban iya so ba, haka in abu ya fitar mun akai ma haka nake. Da fatan zaki bani lokaci in zo in sameki a gida mu ƙarashe maganar?" Ni dai tunda ya soma jawabi gabana ke aikin bugawa, abun wani iri nake jinshi, duk da nasan Oga Rashid ya jima yana tattalin sona, amman ni fa ba auren da zanyi magana ta gaskiya" Nagode Sir, inaso ka bani lokaci zanyi nazari akai" Da murmushi ya dubeni yana wani numshe idanu yace. "Zuwa yaushe kenan? Kar ki sakani cikin zulumin tare da taraddadin me zai fito bakin ki. Domin rashin amincewarki zai iya jefa ni cikin wani hali mawuyaci. Na daɗe ina rainon sanki, yayi girman da rasaki zai iya kassara kuzarina" Ruɗani na shiga mai girman gaske, nama rasa bakin magana, bance komai ba har ya sake magana. "Zuwa yaushe zan jira amsar taki Barista, ba zaki tausaya mun zuwa ko gobe bane in zo gida in sameki mu tattauna ba? Ai mun wannan alfarmar, ban taɓa neman alfarmarki ba, yau ɗaya na roƙa aimun dan Allah " Ɗaureni da jijiyoyin jikina yayi tamau, Oga Rashid tabbas mutumin kirki ne, lokacin da nazo neman aiki, ma'aikata sun cika Chambarshi, amman da yaga macece ni mai rauni, a hakan ya nema mun ofishin da zan zauna, ya ɗaukeni aiki. Tunda dai ya nemi alfarma ya kamata in mishi. Amman bazai iya samun soyayya ba, dan in na faɗa mishi ina sonshi na zalunceshi, na zalunci kaina. Babu wani wanda daɗin bakinshi zai sa in iya sonshi sam an riga da an sha ni na warke. To shikenan Sir Allah ya kaimu gobe." Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya miƙo mun wayarshi. "Saka mun number wayarki da hatimin amincewa in kira wayar a ko da yaushe." Karɓar wayar nayi nasa mishi number, kana nace. Baka samu hatimin amincewa da kira ko yaushe ba. Kira in ya wuce taran dare wayata ma bata kunne, domin kullum ina zama in yi karatu domin nazari" "To shikenan sai yanda kikace ai. Muje in taka miki" Nayi nayi dashi ya barshi, amman fur yaƙi, sai da ya kaini har bakin mota. "Kina da shari'a yaune?" E inada ita, a kotun bayan gidan sarki, ƙarfe huɗu zamu yi zaman. Ƙila daga gida can zan wuce" Murmushi yayi kawai baice mun komai ba, naja motata na tafi na barshi a wajen. Ina tuƙi sambatun Oga Rashid suna yawo a kaina. Wayata ce tayi ruri, da sauri na duba ko Sani ne. Amman sai naga sabuwar number. Ɗagawa nayi na saka a kunnena. "Amincin Allah ya tabbata a gareki Amaryar Jega da fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya, yaya gajiyar biki?" Saida kaina ya sara mun, ƙit na kashe wayar ma baki ɗayanta, hawaye ya soma zuba a idona. Mahaukaciya ma suke shirin mayar dani na lura, soyayya dai_ soyayya dai a aureka daka kwana biyu kashi ya fika daraja. Ina bazan iya bama kowa damar shiga rayuwata ba sam." Da wannan surutan na isa gida. Ina shiga gidan na hango takalman maza biyu a ƙofar ɗakinmu. Yaran duk suna tsakar gida, Sani na ganina ya kamo hannayena muka shiga ciki tare. Idanu muka haɗa da Kaila. Ya zuba mun idanu yana kallona. Nima shi nake kallo, ina hango murmushin muguntar da yayi mun sanda zamu je zaman firzin. Ige ce tace. "Shigo Tani. Kai kuma Sani shikata ka koma ka jira waje." Kallon Sani nayi nace. Ka jirani, ku tafi can gidan bazan daɗe ba kaji Sani na?" Jayayya yaso ni na hanashi, yana hawaye ya fita, ni kuma na shiga na nemi waje na zauna. Sai ƙaremun kallo Kaila yake yi. Ban yi yinƙurin gaishe da kowa ba, Baffa yace. "Tani, Kaila ne yazo tafiya da yara. Yace shi bai yarda yaranshi su zauna a hannunki ba. Yanason haɗe kan iyalanshi waje guda. Dan haka ke me kikace, tunda kema yarannan naki ne?" Baffa yara dai sun dawo hannuna kenan. Ba yardarshi nake nema ba, asalima shi yasa ban nemi amincewarshi ba. Ina da damar da zan iya riƙe yarana. Ko kotu muka je mu kai shari'a alƙali zai bani yarana." Carab Kaila yace. "Bazan iya rabuwa da yaran bane Baffa, sune makwafinta a Idanuna. Dan haka zan tafi da yarana" Wallahil azeem baka isa ka taɓa mun yaraba. Yara sunzo kenan zama daram tare da ni uwarsu, kaila ka fice a cikin idanuna in rufe. Ba wannan shanonon daka sani bace a baya, ƙaramar katangarka mai daɗin tsallaka. Yaran ƴar jagora, mabarata, maƙasƙanta su kake son su zame ma sanyi a idanunka? Baka isa ba wallahi." Baffa yace. "kinci gidanku nace" "A'a Naroro Tani tana da gaskiya fa, a baya ma dokin zuchiyane yasa harta iya biye ma zuchiya ta bar yaranta. Ai tsakanin ɗa da uwa sai Allah. Ni ina ganin kai Kaila kayi haƙuri kawai yara dai kasan inda suke, a hannun gyatumarsu, duk sanda kake son ganinsu babu mai hanaka zuwa ka gansu. Zancan tashin hankali ma bai taso ba." Cewar Goggo Ige. Basshi Ige in yaji bazai barmun su ba, ai sai mu shiga kotu. Kaga hakkinsu na baya da ka kasa saukewa, ayi maka list ka biya. Sannan alƙali ya karɓarmun dukiyata daga hannunka ka koma matsiyaci yanda kake a baya" Na kakkafeshi da Idanuna da suka kaɗa su kai jawur, wallahi ji nake kamar in dira a wuyanshi. Ganin irin fusatar da nayi ne yasa Kaila saurin janyewa. "To shikenan Shanono, ni bazan yarda mu tsaya a gaban kotu dake akan yaraba. Amman ina roƙonki da girman Allah ki koma ɗakinki mu mayar da aurenmu, Isa bakace komai ba fa har yanzu" Murmushin mugunta nayi ina binsu da idanu kawai. Isa ya soma jawabinshi. "To hakane maganarka. Maganar tsaiwa a kotu bama ta taso ba. Mu alfarmar da muke nema a wajenku Baffa, umman Sulaiman ki yi ma Allah ki dawo ɗakin ki ko dan sabida yaranki. An riga da an haɗu tunda yara bakwai sun haɗa. Komawarki shi zai samar ma da yaran daraja. Su Amina sun riga sun kawo girma ba daidai bane ace kina matsayin bazawara yaran a hannunki zasu zauna ba. Da uba ake ado, darajarsu gidan mahaifinsu. Ni shawarata Umman Sulaiman ki daure ki sake ba Kaila dama ta barkatai. Nasan yana da tulin tarin laifuffuka da dama awajenki. Ni na san komai, babu kuma irin rikicin da ni da shi bamu yi ba akan irin zaman da yayi dake a baya. Wallahi Tani daga ranar da kika fita cikin rayuwar Kaila daga ranar ya shiga taitayinshi, ya gane matsayinki. Hidima kam kinyi da Kaila sai dai muce Allah ya baki lada." Falon ya ɗauki shiru. Ni kuma sai kokawa nake da hawayen da suke shirin zubo mun. Sam bana fatan Kaila yaga hawaye a fuskata. Kuma in mutuwa yake yana dawowa banga wani mutum a duniya da zai sa in koma aure da Kaila ba" Baffa yace. "Malam Isa zancanka babu son zuchiya a ciki. Amman mu bamu da ikon tursasa Tani ta koma ma tsohon mijinta, face in tana son komen. Wannan ya rage ga Kaila ya nemi yarjewar Tani. In ta aminta shikenan, in bata aminta ba shikenan. Amman Tani naji kina maganar dukiyarki, kuɗaɗenki ne a hannunshi ko ya abun yake?" Inno da bata ce komai ba tace. "Kar ka shiga wannan layin Baffa. Tunda har ya yarda yara su zauna a hannun uwarsu ai mun fita. Batun kome kuma sai in ta amince. Ige mu basu waje." Sandar Baffa Inno ta riƙe suka fita, ɗakin ya rage sai mu uku. An rasa me cewa komai. "Shanono wallahi da gaske nake son ki dawo ɗakinki ba yaudara bace. Isa shine shaidata tun ranar da kika tafi nayi nadamar fitarki a rayuwata. Kullum a cikin tunaninki nake tsawon wannan shekaru da suka shuɗe. Da zaki yi mun rai sai mu koma......" Irin kallon dana watsa ma Kaila ne yasa ya shiga in_ina ta dole. Ƙare musu kallo nayi tas cikin nutsuwa na miƙe tsaye, ya ƙara kafeni da idanu kamar zai cinyeni. Murmushi na sakar mishi na girgiza kai. Sai da na kai bakin ƙofa kana nace. Ku sauka lafiya" Nayi ficewata ina ji suna haɗa baki wajen kiran sunana. Ina fitowa Sani na shigowa cikin gidan. Da ganin idanshi yaci kuka ya gode Allah. Tausayinshi ya kamani, Sani yana burgeni yanda yake tsananin ƙaunata. Hannunshi na kama muka bar gidan zuwa nawa gidan. Yaran na samu sai hira da shewa suke yi Dauda na zaune yana waya, sai wani kashe idanu yake yi. Suna ganin shigowarmu duk suka yo kaina. Zama nayi na ɓoye damuwata na shige cikinsu muka ɗan taɓa hira. Ige ce tayi sallama ta shigo. "Tani yaran su zo Babansu zai musu sallama" Umarnin fita na basu, Sani kuwa har ya fita ya dawo. "Umma yaya kukayi ba dai tafiya dasu zai yi ba ko?" Dariya nayi na ɗan kai mishi dukan wasa. Shima dariya ya saka. "To Habiba Bala in ka dawo sai in baka labari ai" Dauda ya fashe da Dariya shima jin na ambaci uwarshi. Sai lokacin naga Sani ya sau ajjiyar zuchiya. Suna fita na kalli Dauda nace. Ka shirya week end zan kai ka gidan mahaifinka ku gaisa. Mu shiga mu yi zumunci da yara duka." "To Innata Allah ya nuna mana" Ameen. Dawa kake waya dan na fahimci kamar macece ko?" Kai ya shiga sosawa yana dariya ƙasa_ƙasa. Murmushi nayi wai Dauda har ansan soyayya. Toh na fahimta budurwace kayo kenan ko? To yayi ai. A ina take yarinyar, meye matakin karatunta?" Yarinyace shekararnan zata gama sakandare. Kuma tace Babansu sai yayi musu aure suke jami'a. A Bauchi take" Kai na gyaɗa nace. Gyatumarka tasan kana da budurwa ko bata sani ba to?" "Bata Sani ba Innata. Da naso sai mun fahimci juna ne" La hakan kuskurene, in ka je ka sanar mata dan tasan ka girma. Sai yaushe zaka soma zuwa aiki, da batun shago kuma fa?" Zama ya gyara yace. "Monday zan soma zuwa wajen aiki. Shagon kuma Ummata tace zata sa Abba ya nema mun inda yafi fuskar jama'a haka" Kai na gyaɗa. To Allah yasa mu dace." Kiran sallar azahar ne ya sa na miƙe zuwa cikin ɗakina. Shi kuma Dauda ya fita dan zuwa masallaci. Na daɗe a bayan gida ina kukan da in ba yinshi nayi ba zuchiyata ba zata samu sassauci ba. Sai da na ƙoshi kana na ɗauro alwala na fito. Ina idar da Sallah na kunna wayata. Saƙonni uku suka shigo a Jere. Biyu na Jega ne, ɗayan na Oga Rashid ne. Kuma dukka zafafan kalaman soyayyane, kowa na ƙoƙarin kafe tashi gwamnatin. Ido na lumshe ina hangosu dukka biyu a idanuna. Sallamar Dauda ne yasa na fito "Innata Su Sani fa basa gidan Inno. Kuma ban haɗu dasu a masallaci ba" Dam gabana ya yanke ya faɗi na shiga doka kiran wayar Sani har wani dashi_dishi nake gani....✍🏻NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA BOOK 2 HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 15 Sai da wayar ta kusan tsinkewa Sani ya ɗaga. Kuna ina Yayanku yace bakwa gidansu Inno?* Dariya Sani ya fashe dashi. "Umma muna sahad store Baba zai ma su Amina siyayya. Ni banso binsu ba ma, ina tsoron kar ya gudu dasune shi yasa na bisu" Wawuyar Ajjiyar zuchiya na sauke. To shikenan sai kun dawo. Ni fita ma zanyi yanzu zan koma aiki. Sai ku zauna gidan Inno" Sallama mu ka yi na ajjiye wayar. Na koma ciki, wanka na sabunta na sake kaya na fito. Tare da Dauda muka fito, ya kulle gidan ni kuma na shige mota na bar anguwar dan bana ƙaunar abinda zai sa ma mu haɗu da su Kaila. Kirane ya shigo wayata, na duba number da kyau, number da maras kunyan yaronnan ya kirani dashi ɗazu ne. Banza nayi da wayar, ina tunanin to ni me zance ma Oga Rashid gobe in yazo wajena. Da wannan tunanin na ƙarasa gidan Habiba Bala, me gadi ya wangale mun get na shiga. Fitowa nayi ina tafe gabana na faɗuwa. A falon ƙasa na tarar da Hajiya kilishi, da Khadija matar JeGa, da wasu mata dai haka. Da fara'a na gaishesu. Suma suka amsa mun cike da fara'a a fuskarsu. Bayan mun gama gaisawa sai na haura sama zuwa ɗakin Habiba Bala. Tana zaune a kujera tana kallo tayi ado shar da'ita fuskarta har wani annuri ta sake fitarwa. Amarya ba kya laifi. Irin wannan kyau haka Habiba Bala zaki kasheni" Dariya mu ka yi ta bani hannu muka tafa tabb. Waje na samu na zauna. Ince dai Angon ya fita dai ko?" "A'a da muna zaune ma muna kallo, to Babban yaronshi ne zasu wuce JeGa da iyalinshi. Shine ya buƙaci yana son su tattauna wata mihimmiyar magana to ya garin?" Tana faɗar haka cikina ya murɗa. Shikenan yaro na shirin tona mun asiri in kasa fita daga gidan dan tsananin kunya. "Ya dai ƙawata lafiya kike kuwa?" Na ji Habiba Bala na tambayata. Hmm lafiya ba lafiya ba, ina cikin tsaka mai wuyar fita Habiba Bala, da farko dai. Kaila na cikin garin Kano, Ko ince miki yana sahad store wai yaje yima yara siyayya. Da yazo tafiya da yaranshine, da dai yaga a tsaye nake kamar nonon maza shine ya janye. Ni ai naso ya kafe, dan sha'awar rikicin nake yi ƙawata." Dariya ta saka tace. "Kuma har ya iya fuskantarki akan shi yazo tafiya da yaran? Lallai Kaila bashi da kunya. Yaran da ada tsakaninsu dashi zagi da hantarane, sai yanzune yake son kasancewa tare dasu. Lallai ya kyauta. Hmmm kuma ma har suna batun in koma ɗakina sabida yara, shi da abokinshi yana ta faman kwatanta mun Kaila yayi nadamar sakina, ke soki burutsun zance dai. Da yaji inason fasa mishi taya ne fa ya haƙura. Ni duk bama wannan ba Habiba wallahi a cikin matsala nake wani al'amarine yake shirin faruwa a cikin gidannan naku. Habiba Bala koma ince miki asirina ya kusan tonuwa, bansan irin kunyar da zanji ba in abunnan ya fasu, ban san ya uwargidanki zata fassara lamarin ba" Shiru nayi duk na daburce. "Uwargidana kuma Shanono, wai meke shirin faruwa da kike son ɓoyemun ne? Shanono ashe kina mun ɓoye_ɓoyen sirrinki kenan ni ban sani ba ashe? Yawu na haɗiye nace. Ba ɓoye miki nake yi ba. Bagatatan abun ya riskeni, da na ɗauki maganar a matsayin shirme da bankaura irin na yara. A yanzu kawata dole in bayyana miki abunda ke faruwa, ko dan mu haɗu mu yi mafita " Kai na sauke na kasa cewa komai. Habiba Bala kuma kafeni da ido tayi tana sauraren me zai fito daga bakina. Muna cikin wannan zama na kurame, muka jiyo sallamar Alh Nura daga bakin ƙofa. Gabana ya tattake ya faɗi, ji nayi tamkar ƙasa ta tsage in faɗa ciki, sabida tsabar yanda na muzanta, jina nake kamar tsirara." "Alh ka shigo, har su Jegan sun kama hanya kenan?" Ajjiyar zuchiya me mugun nauyi ya fesar kafin yace. "Tafiyar zata iya kaiwa gobe dai. Barista barka da zuwa. Habiba sameni a ɗaki mu yi magana zamu fita ne da JEGA" In bude baki in amsa Alh Nura na kasa, bani da kalma ko guda a bakina. Lallai Jega ya zubar mun da mutuncina, ji irin gaisuwar yau da Alh Nura yai mun. Kamar ba shi bane ɗazu suka kirani a waya cikin fara'a ba. Wannan yaro ya ɓarar mun da gari. Bani ba sake zuwa gidan Habiba Bala har gaba da abada. Ita kanta a sanyaye tace. "Ƙawata ina zuwa bari in dawo" Bayanta na bi da kallo, tana shigewa nima nasa kai na fice. Tafiya nake kamar munafuka, inata leƙo, tsorona Allah tsorona kar in haɗu da kishiyar Habiba Bala a hanya. Itama ƙila labarin ya isa kunnenta. Cikin sa'a kuwa na fita har tsakar gida ban haɗu da kowa ba. A wajen ajjiye motoci naci karo da JEGA yana jingine a jikin motata. Kallo na kare mai da halamun yana cikin tashin hankali mai girman gaske, idanunshi yayi jawur. Kur ya ƙura mun idanunshi ya kasa ce mun komai, nima ban tankaba na shige motata kawai. Abun mamaki har na soma tafiya JEGA bai ce komai ba, bai kuma dena bina da idanu ba. Kallon da yake mun yana bani kunya ainun a shekaruna. Wani tunanin ne yazo kaina. JEGA gobe da yamma ka kirani zan baka adireshin inda zamu haɗu inason mu tattauna kafin ka koma garinku. Sannan kar ka bari damuwa ta damu rayuwarka, ka cutar da jikinka da iyalanka. Duk abinda mahaifinka yayi maka kai ka jama kan ka. Mai taurin kai zai iya fuskantar halin matsi fiye da wannan " Har zan wuce yayi saurin zuwa daidai windona. "Barista masoyi ba maƙiyi bane. JEGA masoyin gaskiya ne, mai ɗauke da burin kawo miki sauye_sauye a cikin rayuwarki. Duk da dama nasan bazan sameki a cikin sauƙi ba. Amman yafi kyau iyayena da iyalaina su san da zamanki a cikin rayuwata. Zuwa yanzu nayi imani kowa na cikin gidannan yasan meye sirrin zuchiyata. Allah ya kaimu gobe zan kiraki, in babu damuwa mu haɗu a munjibir da misalin 5zuwa 6 na yamma. Nagode da wannan gaiyatar da ki kai mun. Duk da na tabbatar shirin yaƙata kike yi. Amman ni ba matsoraci bane in dai a kan ki ne. Dady kanshi ai ko babu komai yasan ya haifi jarumi. Kawar matarshi nake so, kuma zan aura da yardar Allah sai na ɗura miki cikin yan biyu" Yana kaiwa ƙarshen maganarshi ya juya ya shigewarshi cikin gida. Kuri nayi na bi takunshi da kallo. Kyakkyawane irin kyawu na matasanmu na Arewa, yana da tsayi, da cikar zati da kamala. Shi ba mai ƙiba ba, kuma ba siririba. Fatarshi kuma wankan tarwaɗane, sumar kanshi bata da yawa, kuma ba mai sulɓi bace, yana da ƙasumba, da cikar gemu irin na mahaifinshi sak. Wannan gemu ya ƙara mishi zati, da kamala, ya kuma boye ɗanyantakar dake fuskarshi, dan in a fisge ka kalleshi ba za'aimai kallon yaro ba. Muryarshi tana da kauri sosai, irin na cikar mazantaka, domin karamar murya ga maza ba abun burgewa bane sam. JEGA dai yana da madaidaicin kyau a taƙaice zamu ce, bashi da wani aibu na zahiri, sai kusakurai da ba'a rasawa a rayuwar ɗan Adam. Ɗan kasuwane shi, kuma yayi digri a fannin kasuwanci domin gadar mahaifin nashi. Ƙaton uba uban shagon kayan atampopi da lesuka yake dashi a garin na JeGa. Kusan kab Jega babu shagon da yakai na Jega yawan kaya, da yawan kostoma. Daidai gwargwado yana zaune da matarshi da su kai auren soyayya lafiya, yana kuma iyakar ƙoƙarinshi wajen bawa diyoyinshi tarbiyyar islama. Amman yana da yawan Fishi, da zafin kishi akan abunda yake so. Sannan yana da ƙulafaci, gami da naci akan duk abinda ya saka a gabanshi. Yana da ƙanne biyu rak duk mata suna aure, ɗayar na Aure a jihar Borno, ɗayar kuma tana cikin garin Kano. Wannan shine takaitaccen tarihin JeGa." KAILA: Bayan sun dawo da yara gida da uba uban kaya cike da both. Yaso ya sake samun damar keɓewa da Shanono amman sai su kai rashin sa'a bata nan. A cikin gidan su Inno aka jibge kayayyakin. Su buhun shinkafane, katon_katon na su taliya, macroni, couscous, omo, sabulun wanki, sabulun wanka, suturu, kayan kwalliya. Babu dai tarkacen da bai siyo ba, dan yace baya buƙatar Shanono tasa ko ƙwandala a sha'anin ciyar da yaranshi, tufatar dasu, neman lafiyarsu, iliminsu. Shi zai tsaya musu akan komai , duk abinda ya taso a kirashi a faɗa mishi. Dubu ɗari biyu yaba Inno a ajjiyema Shanono na dangane da karatun yaranshi. In ma basu isa ba zai ƙaro ko nawa ake buƙata. Sannan su yara matan yace zai sa Amadudu mijin Hindatu ya kawo musu mota sabida su dinga zuwa makaranta, tunda Sani shima karatunshi yake yi. Yayi ma Sanin alkawarin zai yi mishi cuku_cukun ya samu tranpa daga jami'ar Jos zuwa Bayero unibasiti. Bayan sun gama sai suka nufi hanyar Zaria. Kaila na jingine da jikin kujerar mata, yayi zurfi cikin tunanin shanono, Allah ne ya jarabceshi da wata iriyar azababbiyar soyayyar Shanono, ya rasa ma inda zai tsulma kanshi ko zaiji sanyi. "Isa bazan iya haƙuri da Shanono ba maganar gaskiya. Baka ji ƙirjina yanda yake yi mun ba akan sonta. Allah ne ya jarabceni da soyayyar shanono a karo na biyu. Abinda ban yi tsammani ba, gashi naga ta ɗauki zafi fiye da tunanin me tunani Isa" Harararshi Isa yayi, ya girgiza kanshi kawai. "Kaila kenan, in banda abunka ai dole ma ka jarabtu akan Tani. Ni fa duk irin abinda nai ta guje maka kenan tun a baya. Kasa ƙafa ka shure. Ya Tani ba zata ɗau zafi ba, cin mutunci wannene ya rage baka yi mata shi ba? Ni kaga bazan sake rakoka Kano wajen Shanono ba. Zariar ma ina ajjiyeka a gidan Bilkisa zan dawo Kaduna abuna, babu ruwana da shiga sabgarka da iyalanka. Ka dawo a motar haya Kadunan " Ya ja baki ya tsuke. Kaila ma bai ce uffan ba, haka su kaita yawo a saman kwalta har Allah ya kaisu Zaria lafiya. A Samaru ya ajjiye Kaila ƙofar gidan Bilkisa. "To Isa sai na dawo. Kwana ɗaya zanyi ma mu tattaro mu dawo" "Wai in taƙi fa yaya zaku yi kaila?" Murmushi yayi na takaici dan son Tani sai muƙarƙusarshi yake. "Ni ke aurenta, in dai da gaske tana sona, dole ta biyoni nike da ikon ajjiyeta a duk inda nake so. Kai dai saina dawo zanzo har gida. Ka gaishe da iyalan" wucewa Kaila yayi zuwa cikin gidan. Isa kuma ya ja motarshi ya bar wajen. Ya ko taki sa'a Bilkisa tana gida yau night take dashi a wajen aiki. Tana falo ita da yara Kaila ya shigo da sallama babu kuzari a jikinshi. Zazzaɓine sosai a jikin nashi, bakinshi har ɗaci yake yi. "Kaine a tafe da yamma haka, yau an tuno damu kenan? Hmmmm Kaila kenan, ga waje zauna" Ta nuna mishi kujera ya zauna. Yaran ya kira suka zo inda suke yana kallonsu. Gabaki ɗaya basu saba dashi ba sam. Shi kam dai yaima rayuwarshi, dana iyalanshi giɓi. Amman ya ɗaura ɗamarar zama adalin miji mai son haɗe kan mata da yaranshi. Ruwa Bilkisa ta kawo mishi da abinci ta ajjiye mishi a gabanshi. "Bari in watsa ruwa tukunna, in yi sallar la'asar. In kina da maganin zazzaɓi ki kawo mun in ɗan haɗiya" Miƙewa yayi ya shige ciki ya watsa ruwa ya fito. Jallabiyya ya zura a jikinshi, ya rama sallah. Yana zaune jugum Bilkisa ta shigo da tiran abincin a hannunta. Magani ta ɓalla ta bashi ya watsa yabi da ruwa" "Meke damunka ne na ganka sukuku haka, kuma ba'a mota kazo bane?" "Isa ne ya saukeni ya wuce da motar Kaduna. Daga Kano nake wajen Shanono, yara sun koma hannunta " Kallon tuhuma ta cike shi dashi. "Umman Sulaiman dama an san inda take, har yara sun koma hannunta? Kai amman na mata farin ciki wallahi." Kallonta yayi kawai, abincin ya ɗan taɓa kafin yace mata. "Allah ya ƙaddari na saki Shamwila, zamanmu ya ƙare da'ita. Ina mai baki haƙuri a bisa ƙuntata miki da nayi na auri mai aikinki. Ada na kasance namiji makwaɗaici, mai kuma son mace ƴar ado da kwalliya gani da ruwan ido. Amman a yanzu in sha Allah daku zan ƙare rayuwata. Bilkisa kiyi haƙuri ki yafe mun duk kusakuran dana aikata miki." Kallonshi Bilkisa tayi da kyau tace. "To batun yafiya na yafe maka. Batun ƙarewar aurenka da'ita wannan ba abu bane daya shafeni. Allah ya yafe mu baki ɗaya. Kaima kasan mai kuskurene, duk wani abu daya ɓullo a cikin gidanka kai ka bashi damar faruwa. Amman tunda ka gane kuskurenka ai shikenan." "Nagode sosai. Ina roƙonki ki biyoni mu koma Kaduna da zama, domin inason in haɗe kawunanmu mu zama tsintsiya guda. Yarana inason su shaƙu dani, su kuma shaƙu da ƴan uwansu. Kiyi haƙuri karki ce a'a Bilkisa. A taimaka ayi hakan zaifi alkhairi, dama sabida Shamwila ne kika ce ba zaki zauna ba. To yanzu bata gidan." "Aikina da gidana in yi Yaya dasu?" Ta jefo mishi tambaya. "Aiki zan sama miki wani a Kaduna. Gidan ko haya sai ki saka. In kuma kinason in siya in caske miki kuɗinki zan siya, ni nasa hayar" A taƙaice dai Kaila yaci galabar shawo kan Bilkisa, dan Allah ya yi shi da iya tsara mace, da sarrafa harshe wajen lallashinta. ta amince zata dawo Kaduna. Amman sai ta samu aiki a Kaduna kafin ta baro Zaria, sannan gidanta da take ciki ya siya ya bata kuɗinta a haka suka rabu. Shanono:. Kai tsaye kotu na nufa, nayi shari'ar dake gabana, amman na kasa gabatar da sheduna dukka, na roƙi alfarma a zama na gaba zan gabatar dasu. Alƙali ya ɗage lokacin zaman zuwa wani lokacin. A girguje na shige motata na bar cikin kotun. Habiba Bala sai kiran wayata take ta faman yi. Fur naƙi ɗaga wayarta domin bansan me zance mata ba. Ina kuma tsoron ita me zata ce mun, daga ƙarshe ma wayar na kashe gabaki ɗaya. Ina shiga gidansu Inno na tarar da tulin kayan abinci kamar za'a buɗe shago. Yara suka taryoni da murnarsu, Sani da Dauda basa nan sun fita. Ige ce tai mun bayanin kayan da kuɗi da Kaila ya bayar na batun karatun yara. Karɓar kuɗin nayi kawai na shige cikin gida. Haka nadinga yin komai sukuku babu kuzari a jikina. Ga faɗuwar gaba da naita fama dashi. Tunani yaimun yawa, na rasa abinda ke mun daɗi sam. A daren wannan rana saina tsinci kaina da kasa bacci sam. Haka na wayi gari idanuna sunyi zuru_zuru. Takwas dai_dai na shiga office. Amman na kasa yin aikin kirki, sai in yi shiru ina tunani, haka naita faman yi. Ko Oga Rashid sai da yasa akai mishi kirana yake tambayata meke damuna. Nace mishi babu komai bana jin daɗine kawai. "Muje in kai ki asibiti, ya zaki zauna da ciwo har kizo office kuma a haka, no muje asibiti daga nan sai in kai ki gida" Bani da zaɓi ni kaina nafi sha'awar in tafi gidan in ɗan kwanta, ga jiri da ciwon kai ya tasarmun, halamu Bp na ya hau. A motata muka tafi, shi ke tuƙawa ina zaune a ɓangaren me zaman banza, idona a lumshe. Wani asibitin kuɗi ya kaini suka dubani, gwajin farko suka faɗamun jinina ne ya hau ina buƙatar hutu, da dena yawanta tunani. Magunguna suka bani muka fito. Oga Rashid da kwatance ya kaini har ƙofar gida.. Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi " "Babu komai. Dan Allah ki sha magungunanki ki kwanta kiyi bacci. Sannan in nazo da daddare kya bani labarin meye musabbabin wannan tashin hawan jinin. Allah yasa ba kalaman dana furta miki na asirin zuchiyata bane ya jefaki cikin wannan yanayin ba. In kuwa shine a shirye nake da in janye kalamina, muddin zaki zauna lafiya. Hakan yafi mun daidai, ki shiga gida " Godiya na kuma yi mishi, muka fito tare. Keyn motar ya miƙo mun, tare da yi mun sallama ya wuce. Ni kuma na buɗe gidana na shiga, ina jiyo surutun su Sani da su Inno. Ina shiga na wuce ciki na sha magani na kwanta. Amman na kasa bacci na kuma kasa dena tunani. Yanzu shikenan JeGa ya zubar mun da mutumcina a idan iyayenshi, ƙila har a idanun Habiba Bala ma. Dan nayi imani wannan lamarin bazai taɓa yi ma Habiba Bala daɗi ba. Domin ita kanta hakan ka iya sawa ta fuskanci matsaloli a gidan auren nata. Wasu ma tunani zasu yi baki muka haɗa da Habiba Bala dukiyar gidan muke son handamewa. Wadannan abubbuwan su nake tunawa in ji hankalina yayi ƙololuwar tashi. Kiran sallar azahar ne yasa na tashi nayo alwala na gabatar da salla. Ina idarwa na koma gado na kwanta. Ba'a jima da idar da salla a masallaci ba. Na jiyo muryar Sani da Dauda a Falo suna kiran sunana. Izinin shigowa na basu. "Umma lafiya kika dawo kika kwanta. Umma baki da lafiyane ko Babane? Dariya nayi nace. Baba kuma, me Babanku zaiyi mun Sani? Aikine babu da yawa a office shi yasa na dawo. Amman da yamma akwai inda zani." Zama yayi a bakin gadon yace. "Umma inason gobe zan koma makaranta. Baba yace zai yi ƙoƙari in samu tranpa karatuna ya dawo Kano. Kinga shikenan sai mu dinga tafiya shagon ɗinki da Yaya nima in koya. Nifa Umma kuɗi nake so inyi sabida ke kawai. In siya miki motoci, da gidaje, duk azumi ki je kiyi umara, in buɗe miki gidauniya. Kinga umma ai banci ta zama ba. Duk wata wahala umma sai ta rikiɗe ta koma arziki da izinin Allah. Waɗanda suka wulaƙantaki sai sunci arzikin abinda kika haifa." Wannan kalami na Sani ya sani farin ciki da samun kuzari sosai. Gaskiya Sani shi ɗin na dabanne a cikin yarana. Nagode Sani. Allah yai ma albarka ya baku abinda kuke nema, ya cika muku burukanku da Alkhairi. Nagode sosai. Ina su Sulaiman suke ne?" Dauda yace. "Suna can suna koyama su Indo karatun boko. Yanzu suka dawo makaranta. Su Amina kuma basu da aiki sai zaulayar Baffa. Muma muna son mu shiga gidan Umma ne mu gaisheta. Ɗazu ma ta kira da safe tana son yin magana dake, to lokacin kin tafi wajen aiki" Duk walwalar da nake ciki sai na nemeta na rasa, gashi ban isa ince kar suje ba zasu tuhumeni. Dole haka sukai mun sallama suka tafi. Misalin ƙarfe biyar da rabi na gama kintsawa tsab na fito. Sai da na kama hanyar Munjibir kana na buɗe wayata. Kamar ko jira yake yi sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ɗagawa nayi na kara a kunnena. "Hello ranki shi daɗe ina cikin Munjibir kamar yadda mu kai alƙawari. Ina fatan baki mance ba ko?" Numfashi naja. Ina hanya nima" "To shikenan Allah ya tsare miki hanya ya kawo mun ke lafiya" Ameen" Na datse wayata na ci gaba da bin santsi har zuwa Munjibir. A wajen da aka tanada dan ajjiye motoci na ajjiye motata na suri jakata na fito. Takawa nake yi a hankali, ina ɗan ware idanuna ko zan hangoshi. Ga ƴan mata da samari wasu a zaune a kujeru farare, wasu a zaune a kafet, wasu ma a tsaye suke,yayin da wasu suke tafiya irina. Yanayin garin babu rana yayi lub, sai iska sassanya da take busowa gwanin ban sha'awa. JEGA na hango cikin shigar manyan maza. Baƙar shadda ce a jikinshi ɗinkin malum_malum, hularshi da takalminshi duk baƙaƙene, agogo da tabarau ɗin idanunshi kuma masu ruwan zaiba ya saka, kalar surrfanin dake jikin kayan nashi kenan. A gaskiya yayi kyau sosai, ƙasumbarshi tasha gyara Masha Allah. Tun daga nesa yake ƙaremun kallo, tare da yi mun murmushi har na iso inda yake a tsaye. "Kinyi kyau marar musaltuwa. Ke ɗin kyakkyawace, uwa uba gaki da aji, da sanin daraja,, da kimar kai. Kar in cikaki da rashin kunya muje ga kafet na tanadar mana." Bayanshi nabi har zuwa kan kafet ɗin. Waje na samu na zauna muna fuskantar juna. JEGA bari in baka asalin cikakken tarihin rayuwata tun daga farkon soma sanin kaina izuwa yau da nake gabanka a matsayin Barista. Wannan itace kaɗai hanyar da zai sa ka haƙura da neman aurena kabar zuchiyata ta samu salama. Rayuwata a cike take fal da tarin ƙalubale, da jarabawa wani kan wani. Labarina ya samo asaline daga cikin ƙaramar hukumar shanono dake nan jihar kano. Cikakken labarin rayuwar shanono da irin jarabawar data samu a gidajen aurenta zai zo muku a ciki book 3 da izinin Allah wanda ni kaina bansan yaushe book 3 ɗin zan soma sakar muku shi ba. Na ɗan samu matsalar ciwon idanu, kuma an ɗaurani a kan magani, da izinin Allah da zaran komai ya daidaita zaku jini da book 3. Ananne Shanono zata feɗe mana biri har wutsiya. Shin ya halaƙar Jega da Shanono zata kasance, kuna ganin JEGA zai iya samun zuchiyar shanono kuwa? Ko dai shanono gidan tsohon mijinta Kaila zata koma ne? Ga Oga Rashid shima fa yana mutuwar son shanono da zafinshi yazo. Duk zamu ji yadda zata kaya da izinin Allah. Ki faɗi ra'ayinki dangane da littafinnan. Kai tsaye wanne irin darasi ke kika koya a cikin littafin? Ina jiran amsarki. Masu karantawa a batu, kuma ina yinku sosai. Nagode da ƙauna. MRS BUKHARI taku ce a ko da yaushe. Sai mun haɗu a book 3