_page 1 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 da sassafa take saukowa daga kan step ɗin benan, jikinta sanye da uniform ɗin boko, wanda su kai matuƙar yi mata kyau. farar rigace mai dogan hannu, sai black ɗin skert wanda ya fara daga ugu har zuwa ƙasa, sket ɗin bai ƙarasa har ƙasan kafafunta ba, amma da yake tasa farar safa hakan bai hana aga ƙafafun ta ba,. takalmin sau ciki ne shima black. hajab ɗin jikinta fari ne, ba wani babba bane sosai amma hakan bai hana ya rufe mata ƙirjin ta da suke cike fall ba masha Allah. hanun ta saƙale yake da ɓakar jakar wanda haka rubuta AYUSHA da larabci, a ƙasa kuma aka rubuta da hausa. matashiyar yarinyar ba zata wuce 17 year's ba, ba lefe tana da kyanta masha allah. tana da haske ba fau ba, amma kallo ɗaya za kai mata ka kirawota da farar fata. tana da jiki madedeci wanda ba zata kirata da ramamiya ba kuma ba zaka kirata da me ƙiba ba, amma zata fi shiga sawun masu jiki. tana da hanci ba lefi da madede cin baki, idanun ta suna da girma amma ba sosai ba, tana da tsayinta madede ci amma ba sosai ba, ba zaka kirata da gajeriya ba kuma baza ka kirata da mai tsayi ma, madedeciyace de. haƙoranta jere farare rass madedeta, ga tsakiyar haƙoranta da tsagu, wato wushirya. da matashiyar yarinyar taga sassafar ba zatai mata ba, gudu ta farayi domin ta samu damar saukowa daga kan step ɗin da wuri. mami!! mami!! mami!! abinda take faɗa kenan cikin ɗan ɗaga murya. ''haba MA'EESHAT sai kace wata yarinya kike min kalar wanan kiran, ina kicin ina faman haɗa breakfast, naji kina ta faman ƙwalamin kira kullum kina girma amma ba hankali koh?'' ''hmmm mami kiyi haƙuri sauri nake yi ne gani nake kafin na nemo ki a cikin gidan nan mun gama makara kuma kin san yau da wuri zamu shiga exams, kuma ga MEENAL zamu tsaya mu ɗauka, kin san meenal bata abu da jiki may be ma sai munsha jira, kin san jiya munsha karatu". "wlh kuwa shi yasa jiya mukai-mukai da ita ta kwana taƙi, kinga da ta ƙwana, da yanzu ba zaku sake westing ɗin tame ba kwai tafiyar ku zakuyi". "nima mami sai da nai fama da ita, amma tunda kikaga jiya duk daran datai, tace amai da ita gida tabbas da akwai abinda za tai kin san de meenal bata da kafiya". ''Allah Sarki baiwar Allah meenal ba, bade haƙuri ba, to maza kiyi sauri de ki wuce ku ɗaukota, bari na miƙo miki breakfast ɗin naki kici ko ki tafar muku da shi. zaro ido ma'eeshat tai sanan tace ''no mami yaushe naci abinci na tafi gaskiya bazan iya jira ba, ki bari nasiya wani abun muci'' daga haka ma'eeshat ta fuce da sauri, tana futa daga flour bata tsaya ko ina ba sai inda driver yayi parking ɗin mota yana jiran futowarta, a hanzarta ta ƙarasa ta buɗe ta shiga. ba ɓata lokaci driver ya ja motar ya fuce da sauri da yake Already mai gadi ya buɗe mai get ɗin dan sun san halin ma'eeshat bata san jira mafaɗaciyace ta ajin farko. driver yana fita daga area ɗin, bai nufi ko ina ba sai hanyar gidan su meenal sabida ko ma'eeshat bata gaya mai inda zasuje ba yasan inda zasu. haka suka cigaba da tafiya ba wanda kewa kowa magana, ma'eeshat da take kame a bayan motar haka ta buɗe jaka ta ɗauki littafin ta domin sake dubawa, sam bata san wannan exams ɗin tai wasa ko kaɗan sabida tasan itace ta ƙarshe da zasuyi a junior school in bataci ba ba wani waec ko neco da za tai, demotion kawai za'ai mata sabida hakane tsarin school ɗin su. lokacin da driver ya ƙaraso, gidan su meenal duk da ma'eeshat ta tafi duniyar karatu amma hakan bai hanata jin tsayuwar motar ba alamun an iso gidan su meenal. da sauri ta ajiye littafin hanun ta a hanzarce ta fara ƙoƙarin buɗe murfin motar domin fita. layin ba wani na masu kuɗi bane saboda geto area ne, ba za'a rasa masu rufin asiri ba de, amma talakawan sunfi yawa. wani madede cin gida ma'eeshat ta nufa a hanzarce. gidan bawani babba bane sosai, babu wani abin zamani a ƙofar gidan dan ko pent babu iya plaster ne kawai. ma'eeshat tana gaf da ƙarasawa kofar gidan ta hangi meenal ta futo fuskar nan tata cike da fara'a. irin uniform ɗin da yake jikin ma'eeshat irin sa ne a jikin meenal sak. bama uniform ɗin ba har takalmin da jakar iri ɗaya. "meenal baƙace ba fara ba, amma ba wai baƙa wulik ba, a'a kana ganin ta de kasan ba fara bace. baƙar fata ce amma ba baka wulik ba sai de ace mata bata da haske kawai ko a kirata da chocolate. fatar jikin ta mai kyauce dan har wani glowing take. tasha kwalli abinta idanun nan nata farare tass masu kyau, bata da wasu manyan ido, idanun ta madede tane, hancin ta ma haka. fuskarta de ba siririya ce tana da ɗan faɗi kaɗan, da yake itama tana da jiki ba lefi dan har taɗanfi ma'eeshat jiki. amma a zahirin gaskiya ba jiki ta fita ba kawai diri ne. goshin nan nata saje yayi lufff, ga kumatun nan nata sai lotsewa suke dimple ɗin ta yana bayyana, koya ta motsa bakin ta. cikin farin ciki suka rungume junan su kamar sun jima ba suga junan su ba. cikin kulawa ma'eeshat tace "I miss you my meenal" "miss you too ma'eeshat ɗita good morning dear". sakin junan su sukai sanan ma'eeshat tace "morning how was your night yesterday?" "very fine" meenal ta faɗa tana sake sakin murmushi. hanunta meenal ma'eeshat ta riƙe cikin kulawa tace "are you shower?" "Yes ma'eeshat im shower" "masha allah haka nake so maza muje mu shiga mota kin san fa muna da exam yau on this morning muyi sauri gani nake kamar mun makara" ma'eeshat ta ƙarasa magana tana jan hanun meenal. binta meenal take tana cewa "a'a ki bari mu tafi a hankula mana, tabb wallahi meenal bazan iya tafiyar nan taki ba rabani kamar an fasa miki ƙwaii''. haka ma'eeshat tai tajan meenal da sauri har suka, ƙarasa bakin mota, sanan suka buɗe suka shige, suna shiga ba ɓata lokaci driver yaja motar da sauri su kai gaba abun su. ••••••••••••••••••••••••••• Idan kaga wata akace dole kaga zahra, amintar da take tsakanin ma'eeshat da meenal mai ƙarfi ce sosai, zaka daɗe baka ga aminai wanda suke aminta da junan su ba irin ma'eeshat da meenal, duk da halin su ya babbanta kuwa. ma'eeshat ta kasance mace mai yawan faɗa bata da hakuri ko na second 1, ita kuma meenal ta kasance me haƙuri sam bata san faɗa bare hayaniya so silent ce shirunta ma yayi mata yawa, in kaga maganarta to tabbas tana tare da ma'eeshat ne amma in ba haka ba sai ta wani batace ƙala ba. Asalin mahaifin meenal malam shu'aibu ɗan garin maiduguri sana'a ce ta kawo shi garin kano,. tun kafin yayi aure yana da rufin asiri sosai. bayan yazo kano ya haɗu da mahaifiyar meenal balaraba ya aure ta, lokaci daze aure ta duk dangin sa basa son auran sun fuso ya auri wata yar uwarsa, sa'adatu a garin mai dugurin, duk da ya jima bai yi aure ba dan a lokacin da sukai aure da balaraba zeyi ahekara 35. malam shu'aibu daya ga 'yan uwan sa basu goyi bayan auran ba, hakan ne ya sake ƙarfafamai guwar ya cigaba da zama a garin kano ya cigaba da kasuwancin sa, baiyi tunanin komawa maiduguri ba. bayan malam shu'aibu da balaraba sunyi aure da shekara guda suka haifi meenal, taci sunan mahaifiyar malam shu'aibu da ta jima da rasuwa wato amina ake mata kara da meenal. iyayan meenal suna san ta fiye da tunani sabida tun tana yarinya bata da wani kuka har ta fara wayo bata ƙiwa. Bayan meenal ta girma takai a sata a makaranta, mahaifinta ya kai ta makaranta ya siyar mata duk abinda ya dace tayi karatu. to bayan meenal an sata a makaranta da one week aka sa ma'eeshat. duk da yarane amma allah ya haɗa junin su sosai da yake suna zama a sit ɗiya. barema ma'eeshat tana matuƙar ƙaunar meenal kullum in an futo break haka za kaga ma'eeshat ta ruƙo hanun ƙawarta meenal da yake meenal bata da wayo sosai. duk da kuwa shekarun ma'eeshat da meenal ɗaya ne amma ma'eeshat tafi meenal wayo sosai, koda wani ya daki meenal a school to in sha allahu sai ma'eeshat ta ramawa ƙawarta meenal, ko kallan banza bata bari ai mata. kullum ma'eeshat ta koma gida sai ta cika mami da abba da labarin ƙawarta meenal, tun suna ɗaukar abu wasa har suka fahimci meenal ta shiga ran ma'eeshat. hakan ne yasa mami da abba suka je makarantar takanas ta kano dan ganin meenal duk da kuwa 'yar ƙarama ce dan lokacin ma suna play group. da mami da abba sukaje school ganin meenal har address ɗin gidan su meenal suka ƙarɓa dan sometimes in week end tai sai ma'eeshat ta cika su abba da kuka sai an kai ta wajan meenal. itama ɓangaren meenal tana son ƙawarta ma'eeshat sosai dan komai tare take sawa baba ya siya mata ita da ma'eeshat, duk abinda aka siyo mata sai ta kaiwa ƙawarta ma'eeshat. sai da iyayan meenal da ma'eeshat suka san juna sosai sabida amintakar su. to haka amincin meenal da ma'eeshat ya cigaba da ƙulluwa, har suka kammala nursery 3 za su shiga primary 1. A lokacin da zasu ma'eeshat zasu shiga primary class, a lokacin akai rashin sa'a karayar arziki ta kama babban meenal malam shu'aibu ya zama talaka sosai. 'yan uwansa kuwa sai faman zagin maman meenal suke sunace mata me farar ƙafa. karayar arziki da ta samu baban meenal ne yasa meenal bata koma school ba. bayan an koma makaranta kullum in ma'eeshat taje school da kuka take dawowa gida sam bata yin karato wai ita sai an kira mata meenal, meenal bata zuwa makaranta. haka haka har akai one week da komawa school meenal bata dawo ba. hakan ne yasa abba da mami suka ɗauki ƙafa takanas ta kano suka je gidan su meenal. ko da abba da mami suka je gidan su meenal, a kulle sukaga gidan. dan a lokacin ma, su meenal sun tashi dan baban meenal ya sai da gidan ya ƙara hanun jari, can bayan layin su ya sai wani ƙaramin gida. haka mami da abba su kai ta tambaya har aka raka su inda su meenal suka koma., ko da suka je bayan an musu tarbar mutumci an gama gaisawa tambaya su kai sabida me meenal ta dena zuwa makaranta ƙwana biyu ko lafiya?. umman meenal kuwa tace musu canza mata school za ai sabida yanzu ba zasu iya biya mata makarantar ba tai musu tsada karayar arziki ta same su. a take a wajan abba yace ya ɗauki nauyin karatun meenal kuma zai bawa babanta jari sosai. to bayan baban meenal ya dawo gida yaji labarin hakan sam be amince ba, yace shi baya nema a wajan kowa sai Allah. ko da daddare da abban ma'eeshat ya dawo wajan baba meenal, domin neman amincewarsa, fafir malam shu'aibu yaƙi amincewa yace aa yabar shi. haka de aki ta ja'in ja, tsakanin abba da baba. sai da aka kai ruwa rana sanan baban meenal ya yarda abba ya ɗauki nauyin karatun meenal ta cigaba da zuwa makaranta amma shi yace baya bukatar ya ƙara mai wani jari. haka abba ya haƙura badan yaso ba,. baba yayiwa abban ma'eeshat godiya sosai, abba kuma yace ba komai ai duk yiwa kai ne kuma meenal ai ƴar ce a wajan sa, kuma yanzu ai an zama ɗaya. to amuntar meenal da ma'eeshat kullum ƙara ƙaruwa take suna girma suna ƙara shaƙuwa, duk wanda yasan meenal yasanta da ma'eeshat haka zalika duk wanda yasan ma'eeshat yasanta da meenal. ma'eeshat da meenal duk suna da ƙoƙari sosai, amma meenal tafi ma'eeshat hazaƙa kullum meenal ta ɗaya take zuwa, ita kuma ma'eeshat ta 3 ko ta 4 in ta dage sosai zata zo ta 2. wataran meenal zataje gidan su ma'eeshat ta wuni wataran ma'eeshat itama taje gidan su meenal ta wani, in su kai dare har kwana suke. tare mami take siyarwa ma'eeshat da meenal komai, komai nasu iri daya ne, kamar yarda suma iyayan meenal suke siyar musu komai iri ɗaya da ma'eeshat. baban meenal ya ɗauki san duniya ya ɗora akanta sabida ita kaɗai Allah ya bashi a duniya. shi yasa duk abinda meenal take so in de befi ƙarfin sa ba yana yi mata, duk da har lokacin rufin asirin sa be dawo ba amma basa rasa ci bare sha kuma yana kyautatawa ɗiyarsa meenal dede gwargwado, duk da kuwa yasan iyayan ma'eeshat sun ɗaukewa meenal komai, komai yi mata suke. ma'eeshat kuwa itace 'yar fari a gidansu, daga ita sai ƙananta maza uku, fadil aryan ayman, sai kuma 'yar autar su afnan. itama iyayanta suna santa ba lefi musamamman ma abbanta da yake ita ce first born a wajan sa. ma'eeshat ta, taso cikin gata sosai duk abinda take so tana samu da yake ba lefi mahaifin ta yana da arzikinsa. a yanzu de ma'eeshat da meenal suna sss 3 inda suke rubuta jarabawar second term wanda itace zata zama ta ƙarshe, duk da suna da ƙoƙari sun dage sosai wajan karatu sabida tsoran repeating dan inba kaci maki sosai ba dole ayima demotion, dan wanan karan ba wasa har wanda basa karatu karatu sukeyi. wanan shine takaitaccen labarin musabbabin amintakar da take tsakanin meenal da ma'eeshat. Wannan kenan. ••••••••••••••••••••••••• Sai juye-juye yake akan bed yafi one hours yanata juye-jiye, duk da ya saba da shiga irin wanan halin amma ji yake na wanan karan yafi na ko yaushe. hmmm gaskiya ya zama dole na taƙaita neman zaɓina, tabbas na yarda baka samun abunda kake so 100% har yau fa banga complete matar dana tsarawa kai na zan aura ba. duk a cikin zuciyarsa DOCTOR ASHMAL yake faɗin haka, ya daɗe yana saƙa da warwara kafin yayi ƙarfin halin miƙewa. "idanun sa gaba ɗaya sun janza kala sai wani gumi yakeyi, shima kansa doctor yasan abun, ya farayi masa worst. yana sauka daga kan bed ɗin, talamansa ya saka a nitse sanan ya wuce toilet, zuciya cike fall da tunanin halin da yake ciki kuma ina zai samu mata nan kusa ya aura. ya ɗauki Kimanin 10 minutes kafin ya futo daga toilet ugunsa ɗaure da farin towel,. wardrobe ɗinsa ya nufa direct,. a nitse ya buɗe ƙwabar, bayan ya buɗe kyakkyawan hannunsa ya kai ya zaro ɗaya daga cikin fararan towel a cikin jerin towels ɗin da suke rataye a cikin wardrobe ɗin. bayan ya ɗauka, ruwan wuyansa ya fara gogewa yana tafe yana gogewa har ya ƙarasa bakin merro ɗin bedroom ɗin. haka DOCTOR ASHMAL yabi yana goge ilahirin jikinsa cikin nutsuwa. bayan ya kammala goge jikinsa, sumar kansa ya fara gogewa wanda ta jiƙe jagab da ruwa. bayan ya gama goge sumar kan, mataji ya ɗauka ya fara taje lallausan gashin kansa wanda yake kwance luff akansa. wuyan nan nasa har wani ja yake sabida kwanciyar da yayi. abinka da fari, dama farar fata bata jurar wahala sai ta nuna. doctor ashmal fari ne tass, bakinsa kuwa jane raɗau kamar ya shafa red lips. hancinsa dogo ne samɓal, idanuwansa kuwa madede ta masu ɗaukar hankali, yana da tarin gashin gira da kuma gashin ido. yasha gyaran fuska masha allah. yana da tsayi amma ba can sosai ba, sanan bashi da jiki kuma ba ramame bane, kawai za a kira shi da madedeci. inde ke mace, ce in kika kalli doctor ashmal sai kin ƙara, masha allah dan yana da sanyin kyau sosai. bayan ya kammala taje sumar kan tasa maya-mayan suma ya fara shafawa a nitse, haka ya ringa shafa su kala-kala. bayan ya kammala, body cream da lotions ya fara shafawa a fatar jikin sa. sai da doctor ya shafe jikin sa tass sannan ya rufe lotions and creams body ɗin yabar bakin merro. ba ɓata lokaci ashmal ya shirya tsaff cikin baƙar shadda, dogayan kaya. wanda kayan su kai matuƙar ƙarɓar jikinsa, Masha allah ba ƙarya. bakin merro ya koma yasa agogonsa sanan ya shafawa lips ɗinsa mai ɗan kaɗan, bayan ya gama, feshe jikinsa yayi da turarukansa masu matuƙar ƙamshi da kwantar da hankaki, sanan ya joya kan bed sade domin ɗaukar wayarsa da key ɗin motarsa. lokacin da doctor ashmal ya ɗauki iphone 16 pro max ɗinsa kamar yarda yayi tunani haka ya gani wajan miss call 30. dr ashmal bai tsaya duba wanda yake kira ba sabida yasan ko ba'a gaya mai ba daga hospital ne. bayan ya zura wayarsa da key ɗin a aljiwu, farar lapcout ɗin sa ya ɗauka, ba tare da yasa ba ya riƙe ta a hannu, ya fara tafiya a nitse har ya fice daga room ɗin................... DOCTOR ASHMAL STORE and WRITING BY AMINA BAYERO my number 09162226240 mutanan arziki nawa karmu manta da like a ringa yimin voting ɗin emojis ko wana kala ne, sabida nasan kuna tare dani ni, inayi muku fatan alkhairi, ku cigaba da bibiya ta a cikin littafin doctor ashmal. kar ku manta kuma da share to another groups. please share. mu haɗu a next page gobe. _page 2 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 A hankali doctor ashmal ya kutsa kai ɗakin momy ya shiga baki ɗauke da sallama. zaune ya same ta akan gado yesmeen ƙanwarsa tana maƙale da momy tana ta faman zuba mata rigima, sai kace wata yarinya. sallamar da ashmal yayi ita tasa yesmeen da momy ɗaugowa har suna haɗa baki wajan amsa sallamar. nan da nan faskar yesmeen ta ƙaru da hannuri akan wanda yake kanta, cikin farin ciki tace “good morning yaya ashmal?”. doctor ashmal murmushi ya saki shima faska cike da annuri yace “morning too yesmeen” ya faɗa yana jan kumatunta, bayan doctor ashmal sun gama gaisawa da yesmeen mai da kallon sa yayi wajan momy tare da cewa “momy ina kwana” ya faɗa fuska cike da murmushi. fuska a sake itama momy ta amsa gaisuwar tare da cewa “fatan kai ma ka tashi lafiya”. “alhamdulillahi momy, bari na wuce hospital tun daran jiya suke kirana nasan patien suna can suna jira bari na wuce sai nadawo” doctor ashmal ya ƙarasa maganar yana miƙewa daga ɗan zama da yayi a gefan bed. tom shikenan doctor allah uban giji ya tsare hanya ya bada sa'a, ka kula sosai da marasa lafiya sosai dan allah”. “tom shikenan momy” Doctor ya faɗa yana fucewa daga room ɗin cikin murya mai nuna kulawa yace “bye my yesmeen ki kulamin da kanki sosai. banda tsokanarsu fadeel da muhseen bana so suna taɓa min ke”. da sauri yesmeen ta mike tabi bayan doctor ashmal da sauri tana turo baki. cikin murya mai nuna shagwaɓa take kiran sa da! yah!! yah!! yah!! da sauri doctor ashmal ya tsaya cak tare da tsayawa yana jiran ƙarasowar yesmeen, dan shi baya son yawan juyawa bayan in ya fara tafiya. yesmeen tana ƙarasowa ta riƙe hanun doctor ashmal cikin sanyi murya tace “yah I want to talk to you but I don't always get you free, I want to talk about something important”. yesmeen ta ƙarasa maganar tana matsa hanun yayan nata. kallon yesmeen doctor ashmal yayi, dan yasan halin yesmeen da rigima, ba wani important abu da zata faɗa masa, may be wani abun take so, ko kuma hirama zatace su zauna suyi, ko kuma tace! ya kai ta wani wajan shaƙatawa ko shipping. doctor ashmal gyaɗa kai yayi cikin kulawa yace “Don't worry, my beautiful sister, I promised you that we will talk to you later, but now I am in a hurry”. cikin yanayin farin ciki yesmeen tace “tom shikenan yaya Allah ya dawo da kai lafiya, ka kula da kan ka sosai” murmushi doctor ashmal ya saki tare da jan kumatun yesmeen a karo na biyu “Tom shikenan ƙanwata kema ki kula da kan ki sai na dawo”. "daga haka doctor ashmal ya cigaba da tafiya yesmeen kuma tana faman ɗaga mai hannu, sai bye bye take masa duk da baya ganin ta kuwa. doctor ashmal yana fita farfajiyar gidan nasu ya nufi parking space, cikin jerin motocin gidan ya nufi gaban wata kyakkyawar baƙar motarsa ya zira key, bayan ya shiga a hanzarce ya kunta. a hankali yaja motar har ya fita daga gidan ko da ya fita ma driven ɗinsa ya cigaba cikin nutsuwa har sai da ya hau kan titi sanan ya ƙara gudu motar shima ba sosai ba. *DOCTOR ASHMAL doctor ashmal mutum ne sananne, wanda yawan cin mutane in sukaji an ambaci sunansa to tabbas kuwa sun san shi. musamman ma garin kano,. doctor ashmal yana zuwa state state da dama sabida ya duba patien likita ne mai hazaƙa da basira wanda yasan aikinsa sosai, saka makwan ba a ƙasar nigeria yayi karatun likitancin saba, acan ƙasar us yayi. ko da doctor ashmal ya kammala karatun likitancin, ya zama ƙwararran likita ya samu gurbin aiki a ƙasashe da dama ciki kuwa har da U.S ɗin, amma sam doctor ashmal yaƙi amince yayi aiki a can. Dalilin dayasa doctor ashmal baiyi aikin likitancinsa a ƙasashan waje ba shine “hajiya hajara da alhaji sulaiman wato iyayan doctor ashmal. sam sun hana shi yin aiki a ko wace ƙasa sunce ya dawo nijeria kawai, ya cigaba da temakwan bayin allah, kar yaje ya bautawa wata ƙasar gwara ya dawo nigeria yayi aiki sabida suma, nigeria suna buƙatar ƙwararrun likitoci, gwara yazo ya zauna a nan kawai. iyayan doctor ashmal mutanan kirki ne sosai, dattawan arzikin ne sosai. duk da sun kasance masu arziki amma hakan baisa sun dena ganin darajar mutane ba, kosu dena mutunta su ba, mutanan kirki ne sosai ga san taimako, sam basa san wulaƙanta na ƙasa dasu, har so suke suga suna taimakon mutanan da basu da shi. Doctor ashmal shine babban ɗansu, bayan sun haife shi da shekara goma suka sake haifar tagwaye maza fadeel da muhseen bayan shekara shida da haifar su suka sake haifar last born ɗin su sumayya wanda ake mata kara da yesmeen. doctor ashmal mutumin kirki ne sosai kamar iyayansa, sam baya son hayaniya ko kaɗan some time yana yawan ɗaukar nauyin marasa lafiya magungunan su da kuɗin asibiti, musamman wanda basu da ƙarfi, ko talakawa liƙiss. yanzu doctor ashmal de yana nan yana shirye-shiryen buɗe asibiti na kansa. amma de a halin yanzu yafi zama a asibiti aminu kano, gaba ɗaya asibitin shine babban likita wanda ba'a ganinsa, sai abu ya gagari saurin likitocin, ko kuma wanda aka kasa gane meke damun sa. kullum burin iyayen doctor ashmal ya samu mata yayi aure sabida yanzu har ya kai 32 years beyi aure ba, kullum in su momy suka yiwa doctor ashmal zance aure, to yake cewa musu kawai. in kuma sukace yaushe zaiyi auran? sai yace sai allah ya kawo ta gari. bawai dan doctor ashmal baya son aure bana aa yana so aure sosai, dalilinsa naƙin yin auran shine “har yanzu bai samu irin macen da yake so ba. yasha haɗuwa da mata da dama wanda sukai dede da ra'a’yinsa amma sai yaji gaba ɗaya basu kwanta mai ba,. abun mamakin shine tunda doctor ashmal yake bai taɓa wata budurwa ko soyayyah ba har yanzu zuciyar sa a wanke take, yana nan yana jira yayi katari da sahibar sa. doctor ashmal yana so macen da ze aura ta kasance, mafaɗaciya sosai sabida shi yana da sanyi, yana son yaga mace mai surutu da faɗa tsiwa tana burge shi sosai. sanan yana so ya samu mace mai ɗan jiki baya son siririyar mace, breast ɗinta ya kasance manya amma ba can sosai ba, baya son farar mace shi a so samunsa ya samu mace mai duhu, amma bawai baƙa can sosai ba, kawai de mara hasken fata. wanan shine irin macen da doctor ashmal yake so. har gobe yana jiran yayi katari da irin wanan macen duk da yasan ba komai zai samu yarda yake so ba amma a ƙalla ya samu abinda yake so a tattare da ita ko 70 to 80% ne. wanan kenan. ••••••••••••••••••••••••••• a gajiye ma'eeshat da meenal suka futo daga school hannu riƙe da juna. suna futowa suka ƙarsa wajan driven su da yake zaune yana jiran futowarsu, suna ƙarasawa ba ɓata lokaci suka shige cikin motar a gajiye. wata nannauyar ajiyar zuciya ma'eeshat ta sauke tare da cewa driver “ƙara mana A.C mana” ta ƙarasa maganar tana ajiye jakarta a gefe. bayan ta ajiye jakarta ta cewa tai “ka wuce da mu gida kawai anjima in rana tai sanyi bayan mun wuta, ka kai mu gidan su meenal ɗin”. “Kai ma'eeshat duba kiga yarda lokaci guda kikayi wani zuru-zuru, dan kinyi exams fefa uku kawai, abinda ma yaune last, yanzu in kika shiga university kiyi yaya?”. da sauri ma'eeshat ta zaro ido har da wani dafa ƙirji “ni a university kuma meenal rufamin asiri wallahi bazan iya ba, ke kike ɗaukar zance da nake miki wasa, nifa da gaske candy to marriage zanyi ba ruwana da wani karatu”. “kai ma'eeshat sai ki ta wani cewa, aure-aure dududu nawa kike ba kifi 17 to 18 bafaa, haba gwara de kiyi karatunki, in yaso daga baya sai kiyi karatun sai yafi”. harara ma'eeshat ta watsawa meenal tare da cewa “to ni ina ruwana da shekarun nawa, yanzu de ai na isa aure, dan haka shi za ai min, ke ai bama ni kaɗai ba har ke zan sa abba ya haɗe ya aurar damu kinga in kinyi auran kuma, mijin ki me son karatun ne shikenan sai kije can kiyi, gwarama ki shirya tun wuri ki tantance samarin da suke sanki”. taɓe baki meenal tai tare da cewa “ni kin san gaba ɗaya ba aure nakeso ba, ke kika damu da aure ma'eeshat nide barni aure ba yanzu ba”. “kamar ya aure ba yanzu ba sai yaushe kenan, so kike duk sai kinbi kin zazzage jikin ki me kyau a yawan karatu, to wallahi ki shirya ki dena wulaƙanta samari kina ƙin kulasu, dubi yarda maza suke rushing a kanki, amma sam basu isheki kallo ba, nan ga WALEED corsen ɗina sai bibiyarki yake kinƙi, kullum sai yaya waleed ya isheni ta chat da kira akan nasa ki amince da shi, koya bugo miki waya bakya ɗagawa gaki ke ba gwanar hawa online ba. wallahi waleed yana son ki tsakani da allah meenal, duk yarda ake neman namiji, ya kai ɗa namiji ya cika ga kyau, nutsuwa, kamala, ga aji duk yana da shi, gashi ba lefi waleed yana da arzikinsa, amma duk kinbi kinƙi bawan allah nan, ko ni nan wani mai kalar halin waleed yazo yace yana sona wallahi zan amince masa ɗari bisa ɗari. ke bama iya waleed ba maza nawa ne suke binki, masu kuɗi marasa shi masu kyau da masu muni farare faƙaƙe, masu aure, da wanda auran ya mutu, kai gasu nan barkatai sai kin zaɓa amma kin tsaya wasa mene haka dan allah meenal?” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana kama hanun meenal da tai jigum tana sauraranta. “ba zaki gane bane ma'eeshat ni gaba ɗaya mazan ne basa wani burge ni a halin yanzu wl. gyaɗa kai ma'eeshat tai tare da cewa “zasu fara birge ki meenal dan baki fara soyayyah ba, amma kina fara soyayyah duk zaki dena jin hakan yanzu de dan allah roƙona ɗaya ki fara kula da waleed, kin sande shi so a hankali yake shiga wallahi kika bashi lokaci zakiji ya kwanta miki a rai”. shiru meenal tai ba tare da tace komai ba. “haba meenaluwa tawa dan allah ki amince farin cikina, wani siririn murmushin dole meenal ta saki tare da cewa “shikenan yarda kikace ma'eeshat”. “yauwa aminiyata ni kaɗai kuma 'yar uwata, nima yanzu ina saban kamu zakiji buɗa wallahi aure zanyi”. da sauri meenal ta juyo ta kalli ma'eeshat cikin mamaki tace “to shi abass ɗin naki fa, ina kika barshi?”. wata shu'umar dariya ma'eeshat ta saki, bayan tayi mai isarta tace “rabu da banza kawai ina rage tame da shi ne bama shi kaɗai ba gaba ɗaya boyfriends ɗina muna dating da sune amma har yanzu ban haɗu da wanda nakeji zan iya aure ba wallahi”. “kai ma'eeshat ba kyau fa yaudara”. ɗaga kafaɗa biyu ma'eeshat tai tare da cewa “oho canta matsewa 'yan iska, suma ai suna yaudarar wasu matan, sufa haka maza suke suna ganin fine girl, sai su maƙale mata kamar wasu tsofaffin mayu”. “hmmmm ma'eeshat kenan Allah uban giji ya shirya mun ke” meenal ta ƙarasa maganar tana murmushi. “ameen ƙawata Allah ya barmu tare”. to haka ma'eeshat da meenal su kai ta shan hirar su har suka ƙarasa gida. suna ƙarasawa gida suka shiga sukai wanka sannan suka canza kaya ma'eeshat de ƙarfin hali kawai takeyi amma ciwan kai ya takura mata. dama tunda suka fara exams ɗin nan take tafama da ciwan kai an kaita hospital duk magungunan da suka bata, tasha-tasha basayi mata aiki, kamar ma ƙara mata ciwan kan suke. da ma'eeshat ta gayawa mami da abba, abba cewa yayi zai kaita wani hospital ɗin a dubata, zaiyi mata booking ɗin ganin babba likita sabida kar ciwan kan yayi mata worst ko kuma kar’aje wata matsalarce. kafin ma'eeshat da meenal su kammala wanka mami tajera musu abincinsu da kayan sanyi. bayan sun futo saukowa ƙasa sikai sukaci abincinsu, sukayi nak, bayan sun gama ci meenal cewa tai zata koma gida. “haba meenal sai kace wanda ake korarki ko kuma kinzo baƙwan guri, nan fa gidan mune baki ɗaya, jiya ma haka kika takura bayan mun gama karatu da daddare kikace sai an mayar dake gida. dan allah ki bari sai anjima, yanzu mu kwanta mu huta kinsan mun gaji fa, kuma kinga ina ciwon kai, ki bari de in rana tai sanyi, kafin nan naji dede sai mu tafi tare”. gyaɗa kai meenal tai, tare da cewa “tom shikenan taso mu koma sama sannu”. da ƙyar ma'eeshat ta miƙe, meenal ta riƙe hanunta suka haye sama, domin zuwa bedroom ɗin ma'eeshat, suna shiga ba ɓata lokaci suka haye kan bad. kafin kace me tuni baccin gajiya ya kwashe su musamman, ma ma'eeshat, dan ma'eeshat harma tafi meenal gajiya, ga kuma ciwan kai. LA'ASAR misalin ƙarfe huɗu da 'yan mintina, mami ce tashigo domin tashinsu ma'eeshat da meenal suyi sallah. lokacin da mami ta tashesu, iya meenal ce kawai ta iya tashi amma ma'eeshat ina, bata iya ko ƙwaƙwaran motsi sabida matsanancin ciwan kan daya sake rufeta, kawai wani irin bacci takeji. cikin ƙanƙanin lokaci hankalin meenal duk yabi ya tashin dan sam bata so taga ma'eeshat bata da lafiya kamar yanda itama ma'eeshat ɗin bata so taga meenal bata da lafiya. amma ba yarda meenal ta iya dole haka ta wuce toilet jiki a sanyaya ta ɗauro alwala sannan tafuto tafara gabatar da sallah zuciya cike fall da damawa. bayan meenal ta idar, da sallah komawa tai wajan ma'eeshat tanata, faman jera mata sannu. da ma'eeshat taga hankalin meenal ya tashi, ƙoƙarin tashi tai, sanan ta wuce toilet itama tai alwala ta futo, sanan ta fara gabatar da sallah duk dan hankalin ƙawarta ya ƙwanta. bayan ma'eeshat ta idar da sallah, cikin ƙarfin halin tace bari na shirya meenal sai na raka ki gida koh?. da sauri meenal ta girgiza kai cikin muryar tausayawa tace “haba ma'eeshat keda bakida lafiya ki bari kawai, ki ƙwanta ki huta. girgizar kai ma'eeshat tai tare da cewa “a'a ki barni ai na ɗan fara jin sauƙi, tinda nai miki alƙawari ki bari muje mana”. “a'a ma'eeshat gaskiya kiyi zamanki, ko najema zamuyi waya hankalina baze ƙwanta ba, dan Allah ki zauna ki huta”. “tom shikenan meenal tinda kince haka amma ki ƙwantar da hankali ki zan samu sauƙi in sha Allah, bari dady ya dawo sai ya rakani hospital, kullum sai yace wani booking ɗin ganin babban likita yake min, shi wanan likitan waye haka da sai an gama ɓatawa mutane lokaci?” ma'eeshat ta ƙarasa magana tana jan tsaki. “hmmm lallai yayi ta gidana ai gwara ki nunamin kin samu lafiya kalar wanan tsaki haka?” meenal ta ƙarasa maganar tana sakin siririyar dariya. itama dariya ma'eeshat tayi tare da cewa “kullum fa nace zani ganin likita sai yace a'a wai booking akemin wanan wana kalar likita ne, sai kace wani me busawa mutane rai”. “kiyi haƙuri ki mai da wuƙar haka ma'eeshat, baride na tashi na baro umma bata jin daɗi ne, to ban sani ba ko ta watsake, da sai na zauna ma hankalina duk yayi gida, amma ina koma zamuyi waya, nasan ma gobe ba zakije school ba koh?”. “ina zani gaskiya hutawa zanyi kema kiyi hutawarki meenal kar wani muje an gama exams fa, ba abinda za'ai sai wasanni, ba zamu sake komawa makaranta ba sai ranar hutu, muje mu karɓo jarabawar mu”. murmushin meenal tai sanan tace “hmmm ma'eeshat tawa, Allah ya barmu tare, kede bakya son makaranta, tom shikenan de allah ya kaimu ranar hutu”. duk da ma'eeshat bata jin daɗi har bakin mota ta raka meenal haka suka rabu daƙyar. dama kullum in zasuyi sallama haka suke sam basa san rabuwa da junan su. night. wani irin azababban ciwan kai da zazzaɓi ma'eeshat takeji sai faman juyi take akan bed. " sallamar abba ce ta dakatar da ma'eeshat daga juye-juyen da take, a hankula ta buɗe idanuwan ta tare da amsa sallamar abba a hankula. abba ƙarasowa har bed ɗin ma'eeshat ya zauna daga gefe tare da cewa “taso nan ma'eeshat sannu”. da ƙyar ma'eeshat ta miƙe daga kwanciyar da tai tare da matsawa kusa da abba, ta kwanta a gefan hanunsa,. “abba kaina kamar zai fashe haka nakeji” ma'eeshat ta faɗi hakan cikin azabar ciwan kai. shafa bayanta abba yayi cikin kulawa tare da cewa “sannu ma'eeshat, in sha allahu gobe ni ko mamin ki, zamu kai ki asibiti kiga babban likita, nasa anyi miki booking ɗin ganinsa, nafiso a dubaki sosai sabida musan abinda yake damunki”. “haba abba gobe kuma, gobe da yaushe nifa kaina kamar zai fashe sai nai ta jira har gobe, shi wanan wana kalar likita ne da baza'a iya ganinsa a lokacin da akeso ba sai anyi booking?”. “sorry ma'eeshat ɗita, likitan ne ba'a ganinsa haka nan kai tsaye, sai anyi booking tun kafin lokacin da akeso a gan shi, amma gobe da asuba ma zaku fita sabida ku samu ganin likita da wuri, kina yin sallah asubayi karki koma zaku fita keda mamin ki”. “asuba fa kace abba, yaushe na tashi daga bacci, nayi breakfast nayi wanka?”. “kiyi haƙuri ma'eeshat ki daure, in ba kije da wuriba, ba zaki samu damar ganin doctor ɗin da wuri ba mutane da dama zaki gani, kuma kita jira bakuje da wuri ba kiyi haƙuri sannu”. “tom shikenan abba allah ya kaimu goben” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana rantse idanuwa................... DOCTOR ASHMAL STORE and WRITING BY AMINA BAYERO my number 09162226240 mutanan arziki nawa karmu manta da like a ringa yimin voting ɗin emojis ko wana kala ne, sabida nasan kuna tare dani ni, inayi muku fatan alkhairi, ku cigaba da bibiyata a cikin littafin doctor ashmal. kar ku manta kuma da share to another groups. please sharing. mu haɗu a next page gobe. _page 3 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 * MEENAL Lokacin da meenal ta koma gida a kicin ta samu umma tana faman rufe tukunya. da sauri meenal ta ƙarasa tana fadin “ah umma sannu da aiki ashe kin samu ƙwarin jikin naki ma, ai dama kin jirani na dawo na dafa abincin tunda na dare ne Koh?”. fuska a sake umma tace “ah mutanan makaranta sannu da dawowa ya kika baro su ma'eeshat ɗin, kinga ba girke nake bama, ɗazu baban kine ya kawo min raiɗore da zaiti nake tafarfasawa kona samu ƙarfin jikina, kin san yanzu lamarin sai ana haɗawa da magungunan gargajiya”. “oh allah sarki umma na baro su lafiya ma'eeshat ce, dai take ɗan ciwan kai”. “wayyo Allah sarki ɗiyata ma'eeshat wallahi yanzu haka ake ta fama”. “hmm ke dai bari ummata sannu ya jikin naki?”. “Ah jikina da sauƙi meenal dama kece kika ɗaga hankalin ki jiya, bama wata babba cuta ce take damuna ba, maza kije ga abincinki nan kici in kina jin yunwa” girgiza kai meenal tai sanan tace “a'a, Ni a ƙoshe nake bana jin yunwa sai zuwa anjima de, ai munci abinci, daga gidan su ma'eeshat nake fa, yanzu ba wani aikin da zan taya ki ne?”. “A'a meenal ki huta ba wani aiki a gidan nan, duk nayi komai da komai. miƙewa meenal tai hannu riƙe da ledar uniform ɗinta, da yake tayi wanka ta canza kaya tun a gidan su ma'eeshat. meenal bata tsaya ko ina ba sai bedroom ɗin ta. tana zuwa ta ajiye kayanta da jakar a ƙasa sanan ta haye kan madedecin gadonta ta fara ƙoƙarin ɗaukar wayarta wanda tunda ta shigo take faman jin ringing ɗinta. a hankali meenal ta miƙa hannu ta ɗauki i phone 14 pro max ɗinta wanda dadyn ma'eeshat ya siya musu tare. kafin ma, takai ga duba mai kiran, har wayar ta katse. sunan waleed ne kwai yake bayyana akan screen ɗin wayar yayi mata miss call wajan 10, kafin meenal ta ƙara wani ƙwaƙwaran motsi wani saban kira ya sake shigowa, again de waleed ɗin ne,. ba yarda meenal ta iya haka ta ɗauki wayar cikin sanyayiyar muryar tace “hello salama'alaikum”. wata nannauyar ajiyar zuciya waleed ya sauke tare da furta “alhamdulilahi, wa'allaikissalam, ina mai godewa Allah da yasa kika ɗauki wayar nan ko na samu sukuni a zuciyata, zuciyata kamar ta fashe haka nakeji”. shiru meenal tai ba tare da tace komai ba. “dan Allah kice wani abun mana bana son shirun nan naki, baki san halin da nake ciki bane, kullum kina rai na, amma ke nasan baki damu dani ba, dan allah meenal in wani laifin nai miki ki gayamin mana”. cikin siririyar murya tace “a'a ni ba abinda kai min” meenal ta faɗi hakan a taƙaice. “a’a meenal ki gayamin karki ɓoye min sabida tsanar da ki kai min tayi yawa” waleed ya ƙarasa maganar cikin murya mai ban tausayi. harga Allah waleed ya bawa meenal tausayi yau, sabida yayi kimanin shekara guda, yana bibiyarta tun bata da waya amma taƙi ta bashi dama bare fuska. “a'a ni ban tsane kaba taya zance na tsane ka kawai dan kace kana so na, sai na tsane ka kuma?”. wata nannauyar ajiyar zuciya waleed ya sauke tare da cewa “yauwa meenal ɗita, wallahi tunda nake baki taɓa gayamin maganar data sanyaya min rai ba irin yau nagode Allah yasa kiso ni kamar yarda nake son ki”. shiru meenal tai ba tare da tace komai ba, zuciya cike fall da tausayin waleed. “meenal ɗina dan Allah kimin alfarma mana, inna kiraki ki ringa, ɗagawa ko baza kice komai ba, ki saurare ni na ringa gaya miki son da nake miki, duk da nasan ko zan ƙwana ina wuni ina gaya miki bazan faɗa miki adadin son da nake miki ba, amma ko yaya ne in na gaya miki zuciyarta zata samu sanyi karta fashe”. shiru meenal tai dan tausayin waleed ya gama kashe ta a zaune. tunda meenal take bata taɓa tausayawa waleed akan irin san da yake mata ba ko na minti ɗaya ne sai yau. “haba meenal ɗina kinyi shiru dan Allah kiyi min magana”. a taƙaice meenal tace “tom zan ringa ɗagawa amma yanzu zanyi aiki sai anjima”. “tom shikenan meenal ɗina nagode sosai, dan Allah karki ƙi ɗaga wayata zan bugo miki anjima bayan sallah magriba, please my meenal, don't tell me that you don't trust me, feel sorry for me”. “to shikenan ba damuwa allah ya kai mu anjima” daga haka meenal ta katse wayar ba tare data sake jin komai daga gare shi ba, dan ita gaba ɗaya bata son yawan magana ma. •••••••••••••••••••••••• *MA'EESHAT Koda ma'eeshat ta tashi da asuba tayi sallah, komawa bacci tai. sabida mami ta shigo ta gaya mata ta koma bacci, ba sai ta shirya ba. sabida baban likita baze samu damar shigowa da wuri ba seda yamma za suje. Ai kuwa ma'eeshat taji daɗin zancen mami sosai sabida har ga Allah bason fitar sassafan nan kuma gashi gaba ɗaya bacci bai isheta ba. Dan haka hankali kwance ma'eeshat ta koma baccinta...... misalin ƙarfe biyu ma'eeshat da mami suka shirya tsaff domin zuwa hospital suga likita. ma'eeshat tayi kyau sosai duk da ba wata kwalliya tai a fuskarta ba kuwa, hodace sai lipstick da ƙwalli. jar abaya tasa har ƙasa mai haɗe da mayafinta, wanda tasha stone sai walwali take, abayar tayi matu karɓar jikin ma'eeshat. bayan sun gama shiryawa, mami ce taja su a motar suka fita, ba driver ba, sabida basu san ƙarfe nawa zasu dawo ba, kuma misalin ƙarfe biyar driven zai je ɗauko ƙanan ma'eeshat daga school. bama dan haka ba mami tana so ta ringa driven da kanta bata so driver ya ringa kai ta unguwa eny how. lokacin da su mami suka isa hospital ɗin, ma'eeshat tun daga ƙofar bakin get ɗin hospital ɗin ya burge ta sosai, anyi mai hawa-hawa wajan goma. hospital ɗin ya tsaru kamar ba a ƙasar 9j ba. bayan an buɗe musu get haka mami ta shiga cikin hospital ɗin tai parking. suna futowa mami ta kira dady ma'eeshat domin ya faɗa mata sunan likitan, yarda baza su sha wahalar neman office ɗin likitan ba. bayan dady ya faɗawa ammi sunan doctor ɗin, haka suka cigaba da tafiya suna tambaya har sai da suka hawo step na biyar sanan suka iso reception ɗin da zasu jira. yanayi da tsarin hospital ɗin ya sake burge ma'eeshat sosai, sabida komai a tsare yake, baka ganin patien barkatai a inda basu dace ba. Basu wani daɗe da zama ba ,mami tace ma'eeshat taso muje ina ganin wancan ne likitan, da abban ki yace mu same shi, yayi mana bayani dan shine yai miki booking ɗin ganin doctor ɗin. A sanyaye ma'eeshat tace “dan Allah mami kije idan kin tabbatar shine sai na taso ya raka mu, kinga yanzu nasha tafiya kai na har ya fara yimin ciwo”. “ok tom shikenan bari naje na duba, daga haka mami ta wuce wajan doctor ɗin”. ma'eeshat de tana daga nesa tana hango su mami da wanan doctor ɗin suna magana, amma ma'eeshat bazata iya sheda abinda suke cewa ba. to sai da mami ta ɗauki kimanin mintuna 5 suna magana da doctor ɗin, kafin ta dawo inda ma'eeshat take zauna tana jiran ta. bayan mami ta dawo cikin kulawa tace “yauwa ma'eeshat shine, duk yayi mun bayani, taso muje ya raka mu office ɗin”. a hankali ma'eeshat ta miƙe suka fara tafiya ita da mami,mami tana gaba ma'eeshat tana biye da ita, suna ƙarasawa likitan ya cigaba da tafiya har sai da ya kai su bakin office ɗin babban doctor ɗin, sannan yace musu su shiga. fuska a sake mami tai wa likitan godiya sanan ta murɗa handle ɗin kofar office ɗin, bayan mami ta buɗe kallon ma'eeshat tai tare da cewa “shiga muje Koh?”. ba musu ma'eeshat ta shiga baki ɗauke da sallama, itama mami tana biye da ita a bayan. amma abin mamaki shine! mami da ma'eeshat basu ga kowa a cikin lafiyayyan office ɗin ba, wanda yake faman zuba ƙamshi. ita kuwa ma'eeshat glass table ɗin office ɗin ta fara bi da ido, wanda aka jera shi cikin hikima yayi matuƙar burge ta. tsakiyar glass table ɗin wasu read and green ɗin flowers ne a cikin ma'ajiyin su, na baƙin glass. gefe kuma ball ɗin word ne a kai, ga kuma takardar date a gefe, date ɗin ranar ya futo ɓaro-ɓaro, haka ma'eeshat tai tabin tables ɗin da kallo tana ganin abubuwan da aka ƙawata shi da su da sauran files. sai da ma'eeshat ta gama kalle komai tasss sanan idan ta ya faɗa kan sunan mai office ɗin a kan glass table ɗin, da manyan baƙi taga an rubuta doctor ashmal. ƙofofi uku ne a cikin office ɗin wanda gaba ɗaya a kulle suke. ta cikin ɗaya daga cikin ƙofofin mami da ma'eeshat sukaga an buɗe ɗaya. Doctor ne ya futo yana ƙarasa, sa farar lapcote ɗin likitoci, a jikin sa. yana ganin su mami ya saki fuska tare da cewa “ah sannun ku da zuwa ga waje mana ku zauna, sai ku tsaya a tsaye kuma?”. itama mami fuska a sake tace “yauwa sannu da aiki doctor” “yauwa hajiya ga waje nan zaku iya zama, wace patien ɗin?”. nuna ma'eeshat mami tai tare da cewa “gata nan itace ma'eeshat baki iya gaisuwa ba ne?”. da ƙyar ma'eeshat ta iya buɗe baki tare da cewa “ina wuni?”. “ina wuni ga waje nan ki zauna ita kuma hajiya ta zauna a waccan kujerar” doctor ya faɗa yana nunawa mami wata lafiyayyiyar kujerar. cikin fara'a mami tace tom nagode sosai doctor, sanan ta nufi kujerar ta zauna abinta. ita de ma'eeshat in kunuwan ta suna ji dede, sai tajikamar doctor ɗin baya hausa da kyau, harshan sa ya juye da wani yaran wata ƙasar duk da kuwa yana kama da ɗan nigeria,. Ma’eeshat bataji daɗi ba da doctor yace mata ina kwana ba, bata so in ta gaishe da mutum, shima ya gai data tafi so ya amsa. ma'eeshat bayan takai nan da tunanin ta zama tai ba tare da tace komai ba. fuska a sake doctor ya fara yiwa ma'eeshat tambayoyi kamar haka! farko de file ya ɗauko ya buɗe tare da cewa “ya sunane ki?”. kawar da kai gefe ma'eeshat tai tare da cewa “a'isha”. “A'isha your full name?” doctor ɗin ya sake tambaya a taƙaice, fuska a sake. “a'isha aliyu abdul wahab” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana haɗe rai. bayan doctor ɗin ya rubuta sunan ta shekarar ta ya sake tambaya, “how old are you?”. a takaice ma'eeshat ta bashi amasa da “17?”. ɗan zaro ido doctor ɗin yayi tare da cewa “duk girman nan naki 17 kai ashe ma yarinya ce ba babba ba” ya ƙarasa maganar yana sakin wata siririyar dariya. ma'eeshat kuwa wani mugun haushin doctor ɗin ta sake ji ya lulluɓe ta, dan haka bata ce komai ba ta sake kawar da kai gefe. “me yake damun ki ?” doctor ɗin ya sake tambaya yana bin ma'eeshat da ido. “ciwan kai?” ma'eeshat ta faɗa tana watsawa doctor ɗin wani kallo dan gaba ɗaya haushi yake bata. bayan doctor ɗin ya rubuta kallon ta ya sake yi tare da cewa “sai kuma me?”. a daƙile ma'eeshat ta sake bashi amsa da cewa “yawan jiri”. tana rufe bakin ta, taji yace “nifa ba wasan yara nace kimin ba complete abinda yake damunki nake so ki gayamin”. shiru ma'eeshat tai tana mamaki yarda doctor ɗin nan yake raina mata hankali. A zuciyarta cewa tai “tabb lallai baka san wace ma'eeshat ba”.” ki gayamin nace sai kuma me?” doctor ɗin ya sake tambaya. a hankali ma'eeshat tace “shikenan” yarda tasan doctor ɗin baze iya taɓa jin abinda take cewa ba. sai da doctor ɗin ya ɗaga kai ya kalli mami ya tabbatar hankalinta baya kan su, sanan ya kalli ma'eeshat tare da rage murya yace “ke ki shiga hankali nifa ba cewa zanyi ina sonki ba ki dena jamin aji” likitan ya faɗa hakan cikin barƙwanci. ai kuwa ma'eeshat bata san sanda ta saki wata dariya ba, da sai da ta bayyana tsakanin tsagun da suke saman haƙoranta wato wushirya. ai kuwa adeɗe lokacin aka murɗa handle ɗin kofar office ɗin aka shigo. fuskarsa sanye take da mas, jikin sa sanye da kayan likitoci na tiyaya. da sauri yasa hannu ɗaya ya fara ƙoƙarin cire mas ɗin fuskar tare da sakin wani tattausan murmushi ai kuwa karaf su kai 4 eyes da ma'eeshat wanda ita take faman wangale baki tana dariya, saka maƙwan dariyar da doctor ya bata. wani irin yarr ma'eeshat taji, ta fara bin mutumin da ya shigo galala da ido. shi kuwa doctor ɗin daya shigo, ɗauke idon sa yayi daga cikin na ma'eeshat ɗin, sanan ya mai da kallon sa kan doctor ɗin, ya cigaba da shigowa sannu a hankali, yana nufar doctor ɗin da yake duba ma'eeshat. ma'eeshat kuwa kallon likitan da ya shigo ta cigaba da yi ko ƙiftawa bata yi. in ma’eeshat tana gani sosai, doctor ashmal taga an rubuta a gefan ƙirjin farar rigar tasa. doctor ashmal yana ƙarasawa ya miƙwa doctor hannu tare da cewa “ah doctor saukar yaushe dama jiki na ya bani ka ƙaraso kuma kana cikin hospital ɗin nan” doctor ashmal ya ƙarasa maganar yana jijiga hanun doctor ɗin. lumshe ido ma'eeshat tai ta buɗe dan jin maganar doctor ashmal ɗin tai kamar a cikin ƙwaƙwalwar ta yake maganar, sabida tsabar daɗi da sanyin muryar sa. “Ah babban likita kenan bana son daɗin baki fa, naso ina shigowa hospital ɗin nan, ina isowa office ɗinka, na saka a cikin ido na amma sai naga wayam, baka nan, dana tambaya sai akace tiyatar gaggawa ce ta taso, shine ka shiga, naso na biyo ka ɗakin tiyatar amma ban zo ba, sabida kar farin cikin ganina yasa ka mantawa patien almakashi a ciki a ɗinke, shi yasa nace bari na bari inka futo ma haɗu. shine kawai na shiga office ɗinka na shiga ciki na ɗaukilapcote nasa na fara ganawa da patien ɗin ka tinda kai babban likita ne ganin ka sai an sha wahala”. wata dariya doctor ashmal da doctor suka kwashe da ita, amma abinda ya sake burge ma'eeshat ɗin ganin yarda doctor ashmal yake dariyar tasa a nitse, ba kamar wancan doctor ɗin ba mai shegen surutu. “ashe de ba shine doctor ashmal ba, wanan ɗan kyakkyawan ne doctor ashmal ɗin, dama ni ina shigowa naga wanan likitan baiyi kama da sunan ba, ashe kuwa ba shi bane mai sunan” duk a cikin zuciyarta ma'eeshat take faɗin hakan. saki baki ma'eeshat tai saka maƙwan jin sun canza yare suna magana, duk da fatajin yaran amma tasan da yaran france suke magana. bayan sun gama maganganu su da yaran france dawowa su kai da maganar su da harshe hausa. ɗayar doctor ɗin ne mai shegen surutu ya kalli mami tare da cewa “hajiya gafa likitan ya shigo, dama ni zama nai a kujerar sa domin rage mai aiki, dan yauma na dawo daga ƙasar amma nima likita ne”. murmushin mami tai tare da cewa “tom ba damuwa”. cikin girmamawa doctor ashmal yace “hajiya ina wuni?”. “lafiya ƙalau doctor, ya fama da marasa lafiya” “Ah maras lafiya hajiya alhamdulilahi” doctor ashmal ya faɗi hakan yana sunkuyar da kai cikin ladabi. “masha allah, allah ya bada sa'a yasa a cigaba da temaƙwan al'umma a sa'a”. “Ameen muna godiya hajiya” doctor ashmal ya faɗa cikin jin daɗin addu'a da mami ɗin. ɗayan doctor ne ya cafe zance da cewa! “yauwa yanzu tinda ka shigo bari na baka waje ka cigaba da duba patien ɗin ka, dama wanan patien ɗin taka sai ku” doctor ya ƙarasa maganar cikin barƙwanci. itaa kuwa ma'eeshat sai faman sakin murmushi take kamar wata zautacciya, ai kuwa karaff suka sake haɗa ido da doctor ashmal a karo na biyu tana satar kallon sa................ mu haɗe gobe a next page. mutanan arziki dan Allah kar ku manta fa da like and share please. fallow my channel. _page 4 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 doctor ashmal ji yayi gaba ɗaya ya kasa janye idon sa daga na ma'eeshat, kamar yarda ma'eeshat ɗin itama ta kasa janye nata idanuwan. kawar da ido gefe doctor ashmal yayi, tare da cewa “ah ka cigaba da aikin ka kawai, nima yanzu futowa nayi, sabida nai sallah inayin sallah zan koma da akwai patient ɗin da zan sake yiwa tiyata, yau fa aiki yayi min yawa, amma tunda gashi Allah yayi kazo sai ka cigaba da temaka”. dariya doctor usman yayi tare da cewa “ah tom shikenan ba komai, babban likita kaje ka cigaba da farka cikin mutane kana temakwan su, ni kuma ina nan ina kan kujerar ka”. murmushi doctor ashmal yayi ba tare da yace komai ba ya kama hanyar shiga toilet domin ya wanke hanuwan sa, kuma yayi alwala. bayan doctor ashmal ya kammala wanke hanuwan nasa kuma yayi alwala. futowa yayi daga toilet ɗin sanan ya sake shigewa wata ƙofa domin sallah. ɓangaran ma'eeshat kuwa, haka ta ringa bin doctor ashmal da ido har ya shige ciki, dan ta tayi nisa a dogwan tunani, har ga Allah doctor ashmal yayi masifar tafiya da tunanin ta. yanayin kyansa da kuma yanda yake komai a nitse. muryar doctor usman ce ta dawo da ma'eeshat daga dogwan tunain da ta tafi. “yanzu de jinin ki zamu ɗauka domin ai miki scanning kinga sai a gano meke damun ki tunda kinƙi, faɗa”. nan da nan hankali ma'eeshat ya dawo jikin ta, dan ita bata son abinda zai haɗa ta da allura ko kaɗan. da sauri ma'eeshat ta girgiza kai tare da cewa “a'a ni gaskiya bana son allura ta shiga jiki na, zanyi maka bayani yarda zaka gane”. girgiza kai doctor usman yayi tare da cewa “no dole ai ɗibi jinin ki mana, in ba'a ɗiba ba taya za'a gane mai yake damun ki?”. kafin ma'eeshat ta kai da magana mami da take can gefe a kan kujera ta miƙe tare da cewa “ma'eeshat bari na sauka ƙasa zan ɗauko power bank nasa wayata a caji sabida ta kusan ɗaukewa yanzu zan dawo” daga haka mami ta fuce daga office ɗin. “yanzu fa ni da kai na zan ɗaukar miki jinin bama sai na turaki wajan scanning ba, ko dan darajar hajiya, dan naga tana da kirki sosai, kuma gashi ke naga kin fiya tsoro” doctor usman ya faɗi hakan tare da miƙewa tsaye. ta cikin ɗaya daga cikin ƙofofin, doctor usman ya shiga bai fi 3 minutes ba, ya dawo hannu riƙe da sirinji da sauran kayan ɗiban jini. ajiye kayan ɗibar jinin doctor usman yayi a kusa da ma'eeshat kan glass table ɗin, sanan ya ɗauko wata kujera ya zauna a gefan ma'eeshat ɗin tare da cewa “kawo hanun naki”. girgiza kai ma'eeshat tai tare da cewa “ni ai nace ma bana buƙata”. da sauri ma'eeshat ta miƙa hanun ta saka makwan ganin doctor usman yana ƙoƙarin kamo hanun ta, tana miƙowa yace “ko kefa ai ku yaran nan sai ana fama daku”. haka doctor usman yasa wata siririyar farar robar ɗiban jini ya ɗaurewa ma'eeshat hannu katamau, ai kuwa tun daga nan idon ma'eeshat ya fara raina fata sabida yarda taga doctor nan a ganin ta ba zeyi imani ba. ai ma'eeshat tana ganin doctor usman ya ɗauki sirinji tai saurin zame hanun ta. dariya doctor usman yayi tare da cewa “kai meye abin tsoro a cikin nan please ki mayar da hankali mana, cikin few minutes za’ayi a gama, amma in kina wanan abun zafi zaki ji sosai”. rarrashin duniya doctor usman yayiwa ma'eeshat akan ta kawo hanun ta taƙi kuma gashi mami bata nan bare ta riƙe ta. da doctor usman ya gaji da magiya da rarrashin ma'eeshat hanun ta ya ruƙe da ƙarfi ya fara ƙoƙarin tsira mata allura domin ɗibar jinin nata. ai kuwa ma'eeshat ƙwanstama iwu ta fara yi kamar wata yarinya. ai kuwa adede lokacin nan doctor ashmal ya buɗe ƙofar ya futo yana sawa hanun sa handglob, yana jin iwun ma'eeshat yayi turus tare da zuba mata kyawawan idanuwa cikin mamaki yana binta da wani irin kallo wanda shi kaɗai yasan fassarar sa. ai kuwa ma'eeshat tana haɗa ido da doctor ashmal ɗin ta kama bakin ta tai shiru tsit sabida kallon da doctor ashmal yake mata ya rikita ta, doctor usman yayi mamaki yarda yaga ma'eeshat tai shiru da bakin ta kuma ta dena ƙwatar hanunta, dan haka ba ɓata lokaci ya fara ɗibar jinin ta har ya kammala bata sake ko ƙwaƙwaran motsi ba sabida har lokacin doctor ashmal bai dena jifan ta da kallon nan ba mai kama da harara. ma'eeshat ta janye idon ta yafi sau biyar tana sake kallon doctor ashmal amma ko ƙifta idanuwan sa bayayi, doctor ashmal sai da yaga an gama ɗibar jinin ma'eeshat sanan ya janye idon sa daga kallon ta, ba tare da ya sake cewa komai ba ya fuce daga office ɗin. yana fita ma'eeshat ta sauke ajiyar zuciya, dan doctor ashmal ya rikita ta da wanan kallon da ita kan ta bata son mane fassarar sa ba. “ah wato ku yara naga alama bakusan wasa ba, duk wasan da nake miki kinƙi yarda na ɗibi jinin ki, wato kun fusan likitoci marasa sakin fuska kamar doctor koh, kunfi jin shakkarsu, mu kuwa raina mu kuke yi” doctor usman ya ƙarasa maganar yana sakin dariya. ma'eeshat kuwa a zuciyar ta cewa tai “tabb, waye zai wani ji shakkar ka ko kai masa kwarjini, kana sakin baki kana ɗan banza surutu, kana yashe baki kamar gonar audiga, kawai duk ka cika mutane da surutu, taya ma zaka haɗa kan ka da kyakyawan doctor ɗin nan wanda bashi da surutu ɗan I don't care gashi kyakyawan”. ma'eeshat tana kai nan da tunanin ta mami ta shigo office ɗin baki ɗauke da sallama. fuska a sake doctor usman ya amsa tare da cewa “hajiya sannu da dawowa har kin dawo?”. “eh wallahi na dawo har kun kammala gwajin?”. “eh an ɗibi jininta kuma an buɗe mata file, yanzu zan sa a auna mata jinin zaku iya jira nan da 1 hour zai fito”. “a'a anya doctor zamu iya jira kuwa, nabar yara a gida ne su kaɗai kuma basu da wayo, dama ita ce babbar tasu, to in ba matsala, gobe a dawo a ƙarɓa in ba damuwa”. “Ah to hajiya ba komai hakan yayi ma, amma aisha kece babba kike tsoran allura yanzu in a gaban ƙanin ki ne ai sai kiji kunya”, doctor usman ya faɗa yana kallon ma'eeshat. ma'eeshat kuwa ko ta kansa bata bi ba ta wuce wajan mami. “Ah ma'eeshat baki iya godiya bane?” mami ta faɗa tana watsa mata kallon bata kyauta ba. ala dole ma'eeshat tace “nagode doctor” sanan ta kama hanyar fita daga office ɗin. itama mami tayiwa doctor usman godiya sosai, sabida taga yana da kirki ga sakin fuska. ko da mami da ma'eeshat suka fita daga office ɗin suka fara tafiya, ma'eeshat sai baza ido take, ko za taga doctor ashmal amma ina. tunda ma'eeshat take a rayuwa bata ganin mutumin daya burge ta kamar doctor ashmal ba. “kai amma kuma kamar yana da girman kai anya zai yi mutunci ma kuwa?” ma'eeshat ta watsawa kanta tambayar. “to ko kuma irin mutanan nan ne masu kamun kai basa san hayaniya?”. ma'eeshat ta sake watsawa kanta tambayar a karo na biyu amma ba mai bata amsa. haka de mami da ma'eeshat suka cigaba da tafiya har suka ƙarasa inda su kai parking ɗin motar su suka shige, suna shiga ba ɓata lokaci mami ta tayar da motar ta, ba ɓata lokaci suka fuce daga hospital ɗin. MEENAL Bayan meenal tayi sallah isha'i Qur'ani ta buɗe ta fara maraji'a. sai da tayi maraji'ar izu biyu sannan ta rufe ta ajiye shi a ma'ajiyin sa. bayan ta ajiye wayarta ta ɗauka ta hau kan gado ta fara ƙoƙarin kiran ma'eeshat. aikuwa kafin ta kai da ƙarasa kiranta ma taga kiran ma'eeshat ɗin ya shigo, wani tattausan murmushi meenal ɗin ta saki tare da ɗaukan kiran tana karawa a kunne, tare da cewa “hello asslama'laikum ƴar halak kinga ina ta ƙoƙarin kiran ki kika bigo”. “hmm ke de bari meenal yakike dazu naga kin kira ni kuma bama gida munje hospital ne nabar wayar a gida”. “to ma'eeshat yau kuma da kan ki kikabar waya a gida duk sanki da waya”. dariya ma'eeshat tai sanan tace “hmmm a kafin mu fita wayar tawa tayi short down, shi yasa ban tafi da ita ba nasa ta a caji kinga kafin mu dawo tayi caji, ai kuwa ina dawowa na cigaba da ga shi”. “gaskiya ne ma'eeshat tawa, aljanar waya ya jikin naki meke damun ki?”. “hmmm ina fa sakamakon ya futo sai gobe jiki de alhamdulillahi, kai ai yau meenal nayi gam da ƙatar”. “ah bani nasha ta gida na wa kika kamo mana?”. “ke da kamowar nayi zaki ganni a haka ai na same shi na gama dace, kawai ganin sa nayi ba cewa yayi yana so na ba, abinda ko kallo ma ban ishe shi ba, ni de nai ta kiɗa na ina rawata”. “subhanallahi garin yaya kika bari hakan ta faru duk iya kisisinar ki, gaskiya de kin bani kunya, ma'eeshat da baki satowa bawan Allah zuciya ba”. “ke banza waya gaya miki, irin wa'annan suna jin wani kisisina, ai ko sau ɗaya ya kalle ki sabida tsabar ƙwar jini sa, ko ƙwaƙwaran motsi sai kin kasa meenal”. “kai ma'eeshat rabani da son kyawawan samarin nan naki, yanzu da zai ce yana son ki to bashi 3 months kin yaudare shi nafa san halinki ciki da bai”. da sauri ma'eeshat ta girgiza kai kamar meenal tana ganin ta sanan tace “ah haba de waya gaya miki irin mazan nan ake yaudara hmmm meenal kenan ba zaki gane ba”. “eh naji banni a rashin ganewar tawa” meenal ta faɗa tana sakin wata siririyar dariya. “yauwa meenal na manta ban gaya miki ba, yau da safe munyi waya da waleed kinga yarda yake farin ciki wai jiya kin bashi time kunyi hira”. wani ƙasaitacciyan murmushi meenal ta saki tare da cewa “wallahi kuwa ai jiya bayan na dawo gida ya kirani muka gaisa sanan yace bayan isha'i zai kirani, ai kuwa ile haka akai bayan isha'i ya kirani sai da muka kai goman dare muna waya ke tun ina jin haushi sama naƙi sakar mai jiki har na dena, na fara sakar mai baki muka fara hira”. cikin farin ciki ma'eeshat tace “ah alhamdulillahi naji daɗin wanan harka, ai waleed ya gasu wallahi tallahi ya cancanci ki bashi dama ku fara shan soyyayyah.” “kai ma'eeshat nifa bana son wani zance soyayya daga hira kuma sai soyayyah”. “hmmm meenal kenan ni zaki rainawa hankali, kince jiya kunyi wajan 2 hour kuna waya, sanan kice ba ruwan ki da soyayyah ni nasan ai baki fara son waleed ba, amma very soon zaku fara soyayyah sai kince ni na gaya miki wanan, da sai ki ta zama dutse zuciya a bushe, bakya soyayyah, dan allah ke jiya bakiji daɗin bacci ba, da ki kai waya da shi”. murmushi meenal tai dan tasan hakane jiya taji daɗin bacci, amma sai ta basar taja wani ƙaramin tsaki tare da cewa “ce miki akai ni ƴar iskace, dallah ki rabu dani da zancan waleed ɗin nan”. dariya ma'eeshat tai mai isarta sanan tace “tom shikenan in tai tsami maji. amma de gobe zaki zo koh?”. girgiza kai meenal tai tare da cewa “gaskiyar da ƙyar nazo goben nan”. “kai haba meenal kamar ya ba zaki zo ba dan allah kizo mana da akwai abinda nake so muyi, ko ni zan zo na ɗauke ki ne ma?”. “a'a haba de ke da baki da lafiya ai ba sai kinzo ba”. “Tom shikenan gobe de ki shirya, zan sa driver yazo ɗaukar ki dan allah kizo”. “tom shikenan ma'eeshat allah ya kai mu goben da rai da lafiya”. haka de ma'eeshat da meenal su kai shan hirar su sannan su kai sallama. meenal tana sallama da ma'eeshat ko 2 minutes ba tai ba kiran waleed ya shigo. miƙewa tai ta kashe fitilar bedroom ɗin sanan ta dawo ta ƙwanta ta ɗauki wayar baki ɗauke da sallama. to kamar jiya ma haka waleed da meenal suka sha hirar su. dan wayar yau tafi ta jiya daɗi ma, sabida waleed yasa meenal dariya yafi sau biyar, lokacin da zasuyi sallama ma sai da meenal taji kamar kar suyi sallama, sabida waleed ya iya maganganu masu sace zuciya, dan tunda meenal bata bashi lokaci ne da tuni ya daɗe da sace zuciyar ta........... washe gari. MA'EESHAT. Misalin ƙarfe goma na safe ma'eeshat tana ƙwance akan bed tana faman latsa waya, ta kunna data tana ig tana kallonta cikin Jin ɗadi. dama aikin ma'eeshat kenan some time in de tana gida tom bata wani aiki sai yawan danna waya, yawanci 247 tana online dan ko kashe wifi ma bata yi. tun mami da abba suna mata faɗa har sun gaji sun zuba mata ido. ma'eeshat tana kallon wani abin dariya, tana ta sheƙa dariyar ta taji ana knocking ɗin ƙofar ɗakin ta. cikin dariya tace “a buɗe yake, fa shigo”. mai makwan a shigo kamar yarda ma'eeshat tace “sai taji an cigaba da buga ƙofar dole ta ajiye wayarta ta sauka daga kan bedroom domin buɗe ƙofar. lokaci da ma'eeshat ta buɗe ƙofar ƙanwarta afnan ta gani tsaye wanda ba zata wuce shekara uku zuwa huɗu ba, kyakywa da ita kamar aljana sabida kyau. “Ah my afnan ashe kice gaskiya ki girma ki ƙarasa tsayi, har yanzu hanun naki baya kai handel ɗun ƙofar nan?” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana ɗaukar afnan ɗin a hannu. “aunty ma'eeshat wai abba yace kije yana kiran ki” afnan ta faɗa tana sosa idan ta. “to yau abba bai fita da wuri bane, kuma meya hanaki zuwa makaranta afnan yau duk zakizo ki ishe ni da surutu?”. dariyar su ta yara afnan tai sanan tace “dan kiji in gaya miki cewa mami nai bana da lafiya ba zani ba kuma lafiya ta ƙalau”. itama ma'eeshat dariya tai tare da cewa “baƙya son makaranta wlh afnan Allah ya shirye ki”. dariya afnan ta sake yi tana ɓoye fuskar ta a cikin ma'eeshat, ma'eeshat kuwa cewa tai “sauka muje wajan abban to”. “a'a nide kar ki sauke ni mu tafi a haka” “tom shikenan muje” daga haka ma'eeshat ta wuce hannu ɗauke da ƙanwar ta afnan. lokacin da ma'eeshat taje wajan abba sanar da ita yayi, a makarantar su anyi kira ance tazo sabida exams ɗin english ɗin wasu daga cikin ƴan class ɗinsu ta ɓata, kuma daga ciki kuwa harda tata. dan haka wajan ƙarfe 12 su zo za'a fara. gaba ɗaya ma'eeshat bataji daɗin hakan ba musamman da taji banda meenal zasu je tata bata ɓata ba sam bata son ƙara zuwa school ɗin. “tom shikenan abba sai anjiman zani”. mami ce ta tari nunfashi su da cewa “a'a kamarya anjima zaki yanzu kije ki shirya kisa uniform ɗinki, dama yanzu abban zai je hospital ya ƙarɓo awan jinin naki, to kinga in kun ƙarɓo ya sauke ki a school ɗin sabida yau driver na aike shi sosai, kuma nasan ba lallai ya dawo da wuri ba”. “eh hakane kuwa maza kije ki shirya” cewar abba. afnan da take gefe cewa tai “nima abba zan biku”. ba in da zakije wai ke mai wayo kinƙi zuwa makaranta sanan kice zakije hospital” mami ta faɗa tana ɗan hararar afnan ɗin. kuka afnan ta fara tare da tsalle wai wallahi sai ta bisu sai kace tasan inda zasu je. “yi shirin ki auta ki rabi da mamin ki zamu tafi tare dake, maza kije ki raka auntyn ki ma'eeshat ta shirya”. cikin farin ciki afnan tace “tom abba” sannan tabi bayan ma'eeshat wanda ta fara tafiya. suna shiga afnan ta ɗauki wayar ma'eeshat tare da cewa “autyki buɗe min nayi game”. ba yarda ma'eeshat ta iya haka ta buɗewa afnan wayarta ta, sanan ta fara shirya tana shiryawa cikin uniform, tana gama shiryawa ta kama hanun afnan suka fuce a hanzarce..... lokacin da su ma'eeshat da abba suka isa hospital ɗin, ma'eeshat ce take ta nunawa abba hanya har suka ƙarasa office ɗin doctor ashmal domin ƙarɓar awan jinin ma'eeshat ɗin. murɗa handel ɗin ƙofar office ɗin ma'eeshat tayi hanun ta riƙe da ƙanwar ta afnan ta shiga baki ɗauke da sallama, tana shiga idon ta ya sauka akan doctor ashmal yana danna laptop....... mu haɗe a next page gobe. kar ku manta da share mutanan arziki. kar ku manta da like. kar ku manta kuyi following ɗin channel ɗina. my number 09162226240 _page 5 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Gaba ɗaya wunin yau ya kasa gane mai yake damun sa, shi yasan da akwai abinda ya rasa amma ya gaza tina ko mene. shi de yana ji a jikin sa ya rasa wani abu mai mahimmanci gaske. aiki yake yi amma yanayi ne kawai ƙwaƙwalwar ta tafi wata duniyar hanun ne kawai akan laptop ɗin. yana cikin wanan halin yaji an buɗe handel ɗin office ɗin tare da sallama. cikin sanyayiyar murya ya amsa sallamar, ma'eeshat ɗin ba tare da ya ɗago kansa ba, shima abba sallama yayi, amma bai kai ga ƙarasa shiga office ɗin doctor ashmal ba yaji wayar sa ta fara ringing, lokacin da abba ya duba sunnan, kallon ma'eeshat yayi wanda ta tsaya hannu riƙe da afnan tana jiran shigowar sa “ma'eeshat gani nan zuwa bari na fita waya zanyi mai mahimmanci” abba ya faɗa yana komawa baya ma'eeshat bata ce komai ba, abba yayi fucewar sa. mamaki ya kusan kashe ma'eeshat ganin doctor ashmal bai ɗago ba bare ya kalle ta har lokacin bai tsaya da abinda yake ba, cikin zuciyarta tace “wanan ya cika girman kai aikin banza wallahi bazan sake yarfa kai na ba, ko kallan sa bazan ba”. ita kuwa afnan da gudu ta ƙarasa wajan doctor ashmal tare da cewa “ina wuni?” cikin muryar su ta yara, tana taɓa ƙafarsa. A nitse doctor ashmal ya ɗago ya sauke idon sa a kan afnan! wani tattausar murmushi ya saki tare da cewa “lafiya ƙalau an baby, ya sunan ki?” “sunana afnan”. “wow masha allah sunan ki da daɗi”. dariyar jin daɗi afnan tai tare da cewa “to kai yaya sunan ka?” murmushi shima doctor ashmal yayi sanan yace “sunana doctor” ya ƙara maganar yana riƙe hanun ta da ta ɗora akan ƙafafuwan sa. zaro ido afnan tai tare da cewa “kai doctor ne mai yiwa mutane allura”. wata siririyar dariya doctor yayi tare da cewa “eh, ko kema kina so ayi miki ne?”. “a'a ni bana so afnan ta ƙarasa maganar tana girgiza kai. “ah bakya so kuma afnan sabida me bakya son allura to?”. taɓe baki afnan tai tare da cewa “sabida, aunty na in za ayi mata tana tsoro, sai tace mami wallahi ni bana son allura, kuma in za’ayi mata har kuka take, tace min wai da zafi shi yasa bata so”. dariya ce ta kama doctor ashmal sosai da yaji abinda afnan tace. ita kuwa ma'eeshat da take gefe a tsaye mamaki ya kashe ta, yarda afnan ta saki baki tana magana da doctor ashmal, shi kuma yana biye mata. lokacin da ma'eeshat taji sautin dariyar doctor ashmal sai da ta dan ɗago ta saci kallon sa abin ya burge ta ganin yarda doctor ashmal yake dariyar sa a nitse haƙoran nan nasa farare tasss. bayan doctor ashmal ya tsagaita da dariyar, da yake! cewa yayi “To ni ai bazan miki mai zafi ba”. itama afnan dariya tai tare da cewa “to kai ka fara yiwa kan kan ka nagani in bakaji zafi ba sai kayi min”. “Ah wayo zaki yimin nima kenan?” dariya afnan tai sanan tace “eh mana, in kaji zafi zan gudu na barka”. “kai kai kai, haka kike da wayo, kuma gashi kin iya surutu, waya koya miki surutu”. dariya afnan tayi tare da cewa “aunty macica”. dariya doctor ashmal yayi sabida yasan ba dede ta faɗi sunan ba duk da bai gane sunan ba kuwa. bayan ya gama dariyar cewa yayi “a'a ai manya basa surutu sosai, ba aunty kice ta koya miki ba”. zaro ido afnan tai tare da cewa “lah! lah! lah! nide aunty na ta iya, kullum tana cika mu da surutu tai ta magana bata gajiya”. shima zaro ido doctor yayi tare da cewa “aunty taki haka take to kiyi shiru kar ki faɗa a gabanta, ta dake ki”. dariya afnan tai tare da tace “aunty macica wai zaki dake ni?”. da sauri doctor ashmal ya ɗago dan shi gaba ɗaya bai bada da wani mutum a cikin office ɗin ba, yayi tunanin an shigo an fita afnan kawai aka bari a ciki. lokacin da doctor ashmal ya ɗago ma'eeshat ya gani ta kawar da kai gefe kamar ma bata san mai suke ba. zuba mata ido doctor ashmal yayi yana tunanin kamar ya taɓa ganin ta. ji yake idanun sa sun gaza ɗaukewa daga kan ma'eeshat, lokaci guda yaji yana son tuna abunda ya manta yake ta ƙoƙarin tunawa yau ya kasa. kawar da kansa doctor ashmal yayi daga kallon ma'eeshat yana ta tunanin inda ya taɓa ganin ta. cikin sanyayiyar murya doctor ashmal yace “kicewa aunty ki wana doctor tazo nema?” doctor ashmal ɗin ya faɗa yana satar kallon ma'eeshat sabida yaji amsar da zata bada, duk da kuwa shi bai fiya kallon mutane, har sai suzo ya gama duba su bai kalle su ba. ma'eeshat taji sarai abinda doctor ashmal yace, dan haka lokaci ƙanƙani baƙin ciki ya sake rufe ta, wato, shi ɗan I don’t care ne a lallai sai ya nuna bai damu da zuwan ta ba. afnan tafiya wajan ma'eeshat tai da gudu tare da cewa “aunty kinji abinda yace”. cikin zafin rai ma'eeshat tace “kije kice mai file result ɗina nazo ƙarɓa da aka ɗibar min jini jiya”. Duk da kuwa a yarda ma'eeshat tai maganar babu ɗa'a a ciki, mai maƙwan hakan ya bawa doctor ashmal haushi sai ya bashi nishaɗi, dan shi yana so yaga ana faɗa kodan shi kansa da mutanan gidan su basu da faɗa ne oho. afnan dawowa tai tare da cewa “kaji me tace?”. girgiza kai doctor yayi tare da cewa “banji ba kice mata, ta maimaita”. afnan tana kusa da doctor ashmal tace “aunty macica kizo ki gaya bazan iya faɗa ba”. a zafafe ma'eeshat ta tawo wajan doctor ashmal. shi kuwa doctor ashmal gaba ɗaya ya kasa control ɗin kan sa wajan dena kallon ta sabida shi yana son yaga ana faɗa, ko anji haushi sosai, musamman ma mace,. ma'eeshat tana tafe jikinta yana wani girgijewa sabida tsabar jin haushi. ku yi hakuri nasan wanan page ɗin yayi ƙanƙanta sosai, so nake kwai na cika muku alƙawari na turo muku, kunsan bana posting ranar weekend. wanan ma na friday ne.😂😂😂😂 kuma darajar 'yan channel ɗina kuka ci da masuyi min reaction da bazanyi ba. kuje kuyi following ɗin channel ɗina. duk wanda yasan yana min like yaje yayi following ɗin channel ɗina sabida ina so na fifita wanda suke min reaction. mu haɗe gobe a dogwan page. _page 6 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 ma'eeshat tsayawa tai cakk saka makon jin sallamar Abban tah ya dawo. jiyo wa tai tare da cewa "Abba ina kaje ina tajiran ka” ma'eeshat ta faɗi hakan a shagwaɓe. “sorry ma'eeshat kira ne mai mahimmanci akai min amma ki kwantar da hankalin ki akan lokaci zamu ƙarasa school ɗin”,. “Toh abba ai tsoro nake kar a fara jarabawar nan kaga wannan itace damata karshe” Abba murmushi yayi tare da cewa “Ohh su ma'eeshat ana tsoron Repeating, in sha Allah zaki cinye baza ai miki ba”. Ai kuwa juyawar da ma'eeshat za tai kenan, adaidai lokacin data juya idonta ya sauka kan doctor ashmal yana sakin wani ƙayataccen murshmushi Harga Allah ma'eeshat tayi tunanin Ita yakewa dariya sabuda yaji Abban ta yayi zancen repeating, dan haka wani irin haushi taji ya sake rufe ta. amma a ɓangaren doctor ashmal shi Afnan ce take basa dariya sabuda hankalin sama baya kan su, duk da kuwa yana jin abinda suke cewa sarai. yana mamakin wai duk girman ma'eeshat batayi conday ba, dama shi tunda ya ganta yasan yarinya ce sosai. bayan doctor ashmal da abba sun gaisa cikin mutumci, abba bayani yayi masa akan zuwan da sukai ƙarbar awan jini. bayan doctor ashmal ya tambayi sunan tashi yayi ya nufi wata durowa domin ɗaukowa takardar, duk da kuwa hakan ba aikin sa bane, kawai de yayi ne sabida yaga mutumcin abba kuma yana son afnan, dan lokaci guda yaji ta shiga ransa. afnan kuwa ƙarasawa wajan ma'eeshat tai ta hau kan cinyar ta tana wasa da wayar hanun ta. harara ma'eeshat ta watsawa afnan tare da fuzge wayar tace "au da wayar tawa kika tawo kenan to bani a bata" ma’eeshat ra karasa maganar tana fizge wayar daga hannun afnan, cikin murya kuka afnan tace “ni ki bani abuna”. “tashi ki bani waje” ma'eeshat ta faɗa tana watasawa afnan harara. “wallahi in baki bani ba sai nacewa doctor yayi miki allura afnan ta faɗa tana nuna doctor ashmal”. da sauri ma'eeshat tace “shiiii! kar kice haka, muna fita zan baki kinga yanzu wayar ma a kashe take kin kashe sai na kunna” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin kunna wayar. ma'eeshat ta faɗi hakan ne kawai sabida afnan kar ta sake yarfata a gaba doctor ashmal. Afnan tana gani doctor ashmal ya bawa abba takarda result ɗin, ta koma da sauri tare da cewa “doctor bye sai mun dawo”. Murmushi doctor ashmal ya saki sanan ya ɗauki wata fara roba da take cike da sweet da chocolate kala-kala akan galass table ɗin, sanan ya kalli afnan cikin kulawa yace "zo ki ɗauka". “a'a ni de sai de a bani gaba ɗaya”. zaro ido abba yayi cikin dariya yace “ah afnan da wayo kin taɓa jin inda akai haka daga an miki kyauta sai kice sai an baki duka?”. Doctor ashmal kuwa cewa yayi "tom shikenan afnan zo ki ƙarɓa duka". ƙarasawa afnan tai tare dasa hannu biyu ta ƙarɓa, sanan tace “thank you”. har ta fara tafiya ta dawo ta miƙa mai tare da cewa “kai ma na baka ka ɗauki guda uku”. Wata siririyar dariya doctor ashmal ya sake yi, sanan yasa hannu ya ɗauki sweet ɗin guda uku kamar yarda afnan tace “thank you too afnan”. “Tom zan dawo gobe, kana da mutunci gaskiya” afanan tai maganar kamar wata babba sanan tai dariya ta wuce wajan abba. abba yaji daɗi sosai ganin yarda doctor ashmal ya sakarwa afnan fuska sosai harda bata alawa, ita kuwa ma'eeshat tana mamiki sosai saboda duk a ganin ta doctor ashmal ba shi da kirki kamar haka. bayan su abba sun fita daga office ɗin hannun afnan ma'eeshat ta riƙe suka cigaba da tafiya, suna tafiya ma'eeshat tana tunanin exam ɗin da zatai, dan ita har ga Allah ɓatan jarabawar nan ta english ya ɗaga mata hankali, dan ita yanzu ba zata ce ga karatun da tai ba duk da ya zube sabida tun farkwan exam ɗin sukayi english ɗin ba daga ƙarshe ba. suna shiga mota ma'eeshat ta ɗauki book ɗinta ta duƙufa da karatu. ita kuwa afnan alawarta tasha ta more bayan tasha ta more, ta ɗauki wayar ta cigaba da dannawa tana wasan ta. Abba yana tsayawa da tuƙi gaban ma'eeshat ya faɗi rass sabida tasan school akazo kuma gashi tunda suka fara tafiya take karutu, befi page uku ta karanta ba. A hankali ta ɗauki litattafan ta domin ƙoƙarin fita. lokacin da ta ɗago mamaki ne ya kama ma'eeshat ganin ta a layin su. “abba naga munzo gida kuma bayan a school zaka sauke ni, ko ka manta zanyi exam ne?”. “Oh ya haƙuri ma'eeshat na manta ban gaya miki ba, dazu dana fita nayi waya, ina gamawa aka sake bugomin daga school ɗin naku wai ba sai kunje ba anga exams ɗin, yanzu de ku sauka ku shiga sauri nake zani meeting. wata muguwar ajiyar zuciya ma'eeshat ta sauke tare da cewa "alhamdulillahi Allah na godema”. “Afnan dan gidan ku bani waya ta na koma online ah da na kasa danna waya hankali a tashe”. noƙe kafaɗa afnan tai tare da cewa " aa wallahi ni zan danna”. “dallah bani wayata mu tafi tun dazu kice na baki, ban ma san kin ɗauko kin futomin da ita ba, sanan wai kice a'a wallahi zan dake k. kuka afnan ta saki na shawaɓa tare da cewa “abba kaga aunty macica koh?”. “yi shiru autar abba naji ta, haba ma'eeshat ke da ƙanwar ki, ki rabu da ita mana ki bita a hankula ta gama wasan sai ta baki, maza kuje gida ki bata wayar mamin ku sai ki karɓi taki, kiyi haƙuri ki bar mata kar tai kuka”. “tom shikenan abba a dawo lafiya, tawo mu tafi” ma'eeshat ta faɗa tana buɗe murfin motar. “Tom ki ɗaukar min wanan” afnan ta faɗa tana nuna robar sweet ɗin da doctor ashmal ya bata. ma'eeshat bata ce komai ba tasa hannu ta ɗauka sabida yanzu afnan ta fara sa mata ciwan kai. Suna shiga cikin gida ma'eeshat taga gaba ɗaya gidan ba haske. cikin mamaki ta fara ƙwalawa mami kira kamar yarda ta saba in tana neman ta. futowa mami tayi daga kicin tare da cewa "kai ma'eeshat kin san de bana son irin wanan abun zaki ta kwaɗa min kira kamar wata sa'ar ki lafiya kike yimin wanan kiran?”. “ya haƙuri Mami, gani nayi gaba ɗaya gidan ba globs lafiya?”. zama mami tai akan kujera tare da cewa “wearing ɗin gidan ne gaba ɗaya ya lalace, bayan kun fita. kuma munyi waya da abba masu gyara zasu zo su gyara kafin dare”. “to mami mun shiga uku yanzu muyi yaya, har sai dare za'a gyara kenan?”. “kamar ya mun shiga uku muyi yaya, ke har yanzu ma'eeshat baki san haƙuri ba koh, wallahi bamu shiga uku ba ya kamata ki san rayuwa wallahi ke yanzu ba zaki iya zama ba wuta ba kenan?”. “hmmm mami ba zaki gane ba, ba a.c ba charge, gashi power bank ɗinta tana wajan meenal, ga shi ke taki ba zama take da caji ba ko kina cikin gida sai ki ringa wani sa wayarki a power bank”. “kai ki jiye min 'yar ina ruwan ki in nasa wayar tawa a power bank ɗin in ina gida? ni da abuna lallaibma'eeshat baki da hankali”. Dariya ma'eeshat tai tare da fuzge wayar hanun afnan tana cewa “ke kuma dalla bani wayata, tun dazu nake fama ni da wayata, ai ga mamin ki nan ki ƙarɓi tata” daga haka ma'eeshat ta haye sama ta wuce bedroom ɗin ta. tana shiga ta cillah wayar kan bed, sanan ta cire uniform ɗin ta, ta saka rigar bacci domin shan isaka, ta buɗe window ɗin bedroom ɗin sanan ta zauna a kan bed. mamaki ne ya bayyana ƙuru-ƙuru akan fuskar ma'eeshat, ganin waya biyu akan bed ɗinta. “to yau meenal tazo ne?” ma'eeshat ta watsawa kanta tambar. hannu ma'eeshat tasa ta ɗauki wayar duka biyan, sake sakin baki ma'eeshat tayi, a fili tace “kuma ai duk farare ne, amma ai wayar meenal baƙace, ba fara ba”. ma'eeshat tama kasa gane waccece wayarta a ciki sabida tsabar tsanani kamar da wayoyin suke. I phone 14 pro max ɗin iri ɗaya ne sak. ita de ma'eeshat tasan a cikin wayoyin akwai tata amma ta kasa gane ɗayar ta wace, kuma taya akai aka kawo ta bedroom ɗin, dan tasan gaba ɗaya gidan babu mai irin wayarta, kuma gashi ƙannan ta maza basa nan bare ma tayi tunanin wani ne ya shigo da ita ya kawo ta cikin ɗakin. ma'eeshat kunna screen ɗin wayar tayi, domin tantance wacece ta tan a ciki. tana buɗewa taga pictures ɗin wata kyakkyawar mace akai. “To wacece wanan ko ita ce mai wayar?” ma'eeshat ta faɗa a zuciyarta. tsurawa hoton ido ma'eeshat tai dan sabida kallon sani takewa ta kan wayar, amma sam ta kasa tuna inda ta santa. kamar ance ma'eeshat taja wayar sama, ai kuwa tana ja taga ashe ba password, ai kuwa ina ma'eeshat zata shiga in ba gellary ba. ma'eeshat tana shiga gallery hanun ta ya faɗa kan wani pictures dan haka dannawa tai kawai abinta ta shiga, sai da gaban ma'eeshat ya faɗi rass sau uku ganin wanda suke cikin hoton. in idan ta yana gani dede kamar doctor ashmal take gani ya dafe wanan yarinyar da ta gani akan wayar wanda takewa kallon sani. “kenan wanan mutum yana da aure” ma'eeshat ta watsawa kanta tambayar hankali a tashe, haka nan taji hankali ta ya tashi da taga hoton doctor ashmal da wata. kamar ance ta sake garawa sai taga yarinyar a tsakiyar wasu tagwayan maza kyawawa. “to ya haka kuma naga matar tasa a tsakiyar kyawawan mazan nan”. ma'eeshat da ido tabi mazan nan da kallo, ai kuwa gani tai suna mugun yi mata kama da doctor ashmal. ajiyar zuciya ta saki, dan jikin ta ya bata ƙanwar doctor ashmal ce wanan ba matar sa ba, dan a hoton taga tayi yarinya sosai, dan ko ita ta girme ta, ashema yarinya ce, dama can bata kula ba sosai. Kuma yarinya tana kama da doctor ashmal ɗin itama, shi yasa ma farko da ma'eeshat ta ganta take mata kallon sani. “kenan wanan wayar doctor ashmal ce?” ma'eeshat ta raya hakan a zuciyar ta, to garin yaya akai tazo kan bed ɗina?” nan da nan ma'eeshat ta fara tunani,. ai kuwa sai ta tuna da lokacin da afnan ta bata wayar a office ɗin doctor ashmal, ashe ba tata bace ta ƙarba, kuma ma'eeshat ta tuna lokacin da suka futo daga gida har suka shiga mota sam bataga wayar a hanun afnan ba. “Oh hakane ashe ba wayata bace ba” ma'eeshat ta faɗi hakan a fili. “To yanzu ya za’ai a mayar da wayar nan kuwa?”. ma'eeshat tana kai nan a tunanin ta taji wayar ta fara ringing. da sauri ta kalli wayar, tana karanta sunan da akai save, gani tai ansa my number. aikuwa gaban ma'eeshat sake faɗuwa yayi rass rass rass har sau uku, a fili tace “na shiga uku shine wallahi” ta faɗa tana dafa ƙirji kamar taga abin tsoro. “yanzu ai sai yace min ɓarauniya ma, taya zan ɗauki wayarsa, kai afnan kin jawo min wallahi”. Har wayar ta katse ma'eeshat bata ɗauka ba tana wanan banzan tunanin nata. ai kuwa wani kiran ne ya sake shigowa bayan wancan ya tsinke. ƙoƙarin daidaita kanta ma'eeshat ta fara, sai da wayar ta kusan tsinkewa sanan ma'eeshat ta ɗauka tare da cewa "hello". Daga ɗayan ɓangaren shiru akai ba tare da ance komai ba, ma'eeshat gabanta yana faɗuwa tace “wake magana?”. Cikin muryarsa mai daɗi doctor ashmal yace “mai wayar ne”. Gaban ma'eeshat sake faɗuwa yayi tare da cewa "kayi haƙuri ban san wayar ka bace muka tawo da ita". mamaki ne ya kama doctor ashmal sosai, dan shi bema san wacece ba kuma taya aka ɗauki wayar tasa. “wake magana?” doctor ashmal ya faɗa a taƙaice. “Ma'eeshat ce” ma'eeshat ta faɗi hakan zuciya cike fall da tsoro sai kace wanda ta aikata babban laifi. “ma'eeshat kuma, sorry ni ban gane mai magana ba, kawai ki turomin address zan aiko a karɓar min wayar” daga haka doctor ashmal bai sake cewa komai ba, ya katse wayar. Ita kuwa ma'eeshat wani dogwan tsaki taja tare da cewa "aikin banza mai girman kai ni zaka rainawa hankali sai wani jan aji kake, kana cewa baka gane mai magana ba sabida tsabar rainin hankali, dama maza masu kyau haka suke da rainin hankali ga jan aji da girman kai, kai ka sani kar ka gane ɗin”. cikin ƙanƙanin lokaci ma'eeshat ta tura masa address ɗin gidan su, ta wayar tasa sanan ta buɗe gallery ta cigaba da kallon hotunan su doctor ashmal da kyawawan yan uwansa, tana yi tana yabawa. “kai gaskiya wanan ahalin kyawawa ne sosai, kalle su fa ga haske ga kyau har wani ja suke wallahi” ma'eeshat ta faɗi hakan a zuciyar ta. in de akazo hoton doctor ashmal da ƙanwar sa yesmeen sunyi a tare, sai ma'eeshat taji wani yarrr a zuciyarta duk da kuwa yar uwarsa ce, kuma ba wata babba bace. DOCTOR ASHMAL Bayan doctor ashmal ya katse wayar wani dogwan tunani ya tafi dan shi har ga Allah bai gane dawa su kai waya ba. Kuma shi yasan sunan ma'eeshat aisha shi yasa baiyi saurin gane ta ba. jin ƙarar shigowa message wayar sane ya dawo da shi daga tunanin daya tafi. Lokacin da doctor ashmal ya karanta address ɗin da ma'eeshat ta tura masa gani yayi hanyar tafiya gudan sune ɗoɗar dau d kuwa da ɗan nisa da gidan su, kuma yau kafin magriba ma ya koma gida, dan haka bari yayi kawai in zai koma gida ya tsaya ya karɓa. miƙewa doctor ashmal yayi, ya ɗauki i phone 17 pro max ɗin sa ya zira a aljiwu, sanan ya ɗauki lapcout ɗin sa, da jakar laptop ɗinsa ya fuce daga office ɗin sabida yau gaba ɗaya bashi da aiki a hospital ɗin nan wasu takadduma yazo ɗauka daga nan ya fara duba wani abu a laptop shi yasa su ma'eeshat da su kazo suka same shi, lokacin da suka shigoma yayi mamaki sosai sabida yasan shi ranar bashi da wani booking din patients.......... MA'EESHAT ɓangaran ma'eeshat kuwa kallonta tasha sosai a wayar doctor ashmal har sai da taga wayar tayi low sanan ta ajiye ta, kuma gashi wearing ɗin gidan nasu ya ɗauke bare tasa mai a caji. ƙasa ta sauka ta zuba abinci taci ta ƙoshi sanan ta dawo sama ta fara dailing ɗin number meenal. Meenal tana ɗagawa ko gaisawa basu gama yi ba, tace "meenal wai ba zaki zo bane?”. “zan zo mana ma'eeshat ki bari sai anjima mana”. “a'a wallahi ni ban yarda ba yanzu ki tawo kin san yau ina so ki ciremin aiki hoto zaki yimin mai kyau, wallahi Abbas ya takuramin wai sai na turo mai saban hoto na”. “tom shikenan ma'eeshat bari na gama wanke-wanke nai wanka sai na tawo, kin san nima ina so muyi magana dake akan waleed” “hmmmm ai na sani wallahi 'yar nan ai meenal tunda kika fara bawa waleed lokaci dole ko fara son shi nan kusa” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana sakin dariya. itama dariya maeenal ɗin tai sanan tace “kai ma'eeshat bana son haka sai nazo kawai”. “tom shikenan sai kinzo, ke ban baki labari ba, wai yau da safe aka bugowa abba daga school wai naje makaranta exams ɗin wasu ɗaliban ta ɓata ta english kuma har da tawa wai nazo na sake wata”. “innalillahi garin yaya?” meenal ta tambaya cike da mamaki. dariya ma'eeshat tai sanan tace "hmm ke ai daga ƙarshe ance an ganta harfa na shirya dady zai kai ni na gaya miki ciki na yaja ruwa dan kin san duk karatun da nai na manta kuwa Hmm. dariyar itama meenal tai mai isarta, sanan tace “kai ma'eeshat kiji tsoran Allah naga alama bakya son karatu, yanzu karatun da ki kai a exams har ya zube ai da wani video kika gani a ig ko a social media baza ki manta ba”. “hmmm kede bari wallahi ina zan manta maeenal ai ni na gaya miki aure nake so ba karatu ba ke kike ɗaukar zancan wasa”. “Au haka zaki ce ma, bari nazo zan gayawa mami wallahi”. “Au tun yaushe nake gayawa mami ai mamin ma ta sani ke de kiyi sauri kizo dan Allah”. “Tom shikenan ma'eeshat gani nan sai nazo” daga haka ma'eeshat da meenal su kai sallama. ma'eeshat haɗa wayarta tai da ta doctor ashmal ta ajiye a ƙarƙashin folanta sabida afnan. ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita........ kar ku manta da fallowing ɗin channel ɗina, saboda sai na fara posting a channel ɗina, mutanan arziki kuje kuyi following. kar ku manta da sharing to another groups. kar ku manta da like (reaction) mu haɗe a next page. https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game buƙatar comments ga link ɗin group ɗina yayi joining _page 7 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ma'eeshat ba ita ta tashi daga bacci ba sai wajan ƙarfe 3 na yamma, a lokacin ma maeenal ta daɗe da zuwa tana jiran ta. “Kai meenal shine kika zo ko ki tashe ni?” meenal da take kwance akan sofa murmushi tai sanan tace "kin tashi kenan to sannu, haba daga zuwa kuma sai na tashe ki kina bacci, barin ki nai ki wuta kawai kuma gashi baki da lafiya". mutseke ido ma'eeshat tai tare da yin miƙa sanan ta ɗaga ƙarƙashin fulo ta zaro wayoyin data ajiye, tare da cewa “meenal zo kiga guy ɗin da nake baki labari jiya nace miki ya haɗu” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana shiga cikin gallery a wayar doctor ashmal. Meƙewa meenal tai tare da cewa "ah masha allah kice har kun haɗe kenan”. taɓe baki ma'eeshat tai tare da cewa “wana kalar mun haɗe, baki ga wayoyin biyu bane ba, wanan ai wayar sa ce ba tawa ba”. zama meenal tai a gefan ma'eeshat ɗin tare da cewa “to garin yaya wayar tazo hanun ki kuma?”. washe baki ma'eeshat tai tare da miƙawa meenal wayar tana cewa. "dan Allah meenal ya kika ga guy ɗin nan, kamar ba bahaushe ba ko?”. karɓar wayar maeenal tai tare da zuba mata ido. meenal tana kallon hoton ta taɓe baki sanan tace "eh masha allah yana da kyansa, amma ma'eeshat akan namiji kike rawar jikin nan to wai ina ma kika samo wayar tasa, wanene shi wai?”. “Doctor Ashmal sunan shi, shine fa wanan babban likitan da nake ce miki wai sai anyi min booking ɗin ganin sa, to yau da safe muka koma karɓo gwajin da akan min nida abba da afnan, shine afnan ta ɗauko wayar, ni kuma ban lura ba har sai da muka dawo gida sanan na gane ba tawa bace”. “Ah kai afnan da abin dariya, yanzu to ya za ai a mayar mai da wayar?” meenal ta tambaya tana kafe ma'eeshat da kyawawan idanunwan ta. “Hmmm ai ya bugo, har na tura mai address yace zai aiko a ƙarɓa masa, kuma gashi wearing ɗin gida ya lalace bare nasa masa waya duk fa ni na ƙarar da caji da akwai wajan 60 percentage fa, amma yanzu dubi befi saura 12 percentage ba”. “Kai ma'eeshat kiji tsoran Allah shine kika fara yiwa bawan Allah bincike a wayar sa?”. dariya ma'eeshat tai tare da cewa “ke kuwa ba dole ba naga jinin larabawa ke kinga 'yan gidan nasu ma suma kyawawa kai wallahi mutumin nan ya haɗu” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana lumshe ido tare da kara hoton nasa a ƙirji. Fuzge wayar meenal tai tare da cewa cillata gefe tana cewa "ke de wallahi ma'eeshat ba de san maza ba, daga ganin bawan Allah kin bi kin ruɗe mutsuuuu”. “kai meenal wallahi ba zaki gane ba ke kawai dan baki ɗauki rayuwar ki da zafi bane shi yasa maza, basa burge ki. ke wai ya maganar waleed kuwa ƙwana biyu naga ya dena yimin magana amma da kullum roƙona yake akan na shawo mai kan ki”. meenal bata san sanda wani siririn murmushi ya ƙwace mata ba. ma'eeshat wani uban iwu ta ƙwada tare da dukan meenal ɗin tana cewa "shegiyar gari wato kina sumu-sumu da kai kice kun fara shan soyayyah ". maeenal bata ce komai ba kawai ta sake sakin wata dariyar. “Ke bana son iskanci dan Allah ki gayamin me yake faruwa?”. gyara zama meenal tai tare cewa “ke nifa ba abinda kike tunani bane ba wata soyayya da muke sha, kawai kwana biyu na bashi lokaci ne muna shan hirar mu da shi sosai, amma gaskiya yana da kirki sosai jiya fa da daddare ya turomin kati waya airtime na 20k data kuma 50GB. Zaro ido ma'eeshat tai tare da cewa "kai! kai! kai! kai! meenal irin wanan abun arziki haka, dama wallahi waleed bada ga nan ba, bashi da rowa, abinki da me shi yana da kuɗin sa babu laifi kuwa, da tunda kin bashi lokaci kun fara soyayyah ai da yanzu Allah ne yasa mai zai ringa kashe miki”. Girgiza kai meenal tai tare da cewa "a'a nifa ba ruwana, rufamin asiri da cin kuɗin maza nifa wallahi dama yayi shawara dani da bai turamin ba”. “Kai meenal ke dai ƴar ɓarar da samu ce, ni kinga turamin ko katin 5K ne na rage zafi”. Miƙawa ma'eeshat wayarta meenal tai tare da cewa ƙarɓi ki tura na 10k ma kinsan de ni bana yawan kiran mutane, kece kawaii muke waya ko kin bar katin ma ba amfani zanyi da shi ba”. Hannu ma'eeshat tasa ta ƙarɓi wayar meenal tare da cewa “ah kawo wallahi na tura ni kuwa nake waya, meenal tawa, dan Allah ki cigaba da sakar mai fuska yana sakar mana abun duniya. dan baki san yarda yaya waleed yake son ki bane, duk abinda kike so yayi miki yi miki zai yi, ke ko yanzu kika buɗe baki kika cewa yaya walee ya baki 500k wallahi sai ya baki, kinji ma na rantse”. Zaro ido meenal tai tare da dafa ƙirji tace "dubi ɗari biyar kuma ma'eeshat? ah rufamin asirin nayi me da su, ke nifa bazan taɓa iya roƙwan namiji kuɗin sa ba, ko ya bani ma bazan ƙarɓa ba, dan kiji in gaya miki”. Tsaki ma'eeshat taja tare da cewa "sai kije kiyiwa kan ki in ya baki karki ƙarba, ke baki san ihsanin masoya ba, wallahi ko million 5 yaya waleed zai fitar nasan ko ajin sa sabida shi baya jin fitar kuɗi Allah ya bashi in kinji ana yaro da kuɗi shine”. Girgiza kai meenal tai tare da cewa “kai ma'eeshat Allah ya shirye ki da son kuɗi, Allah ya baki miji na gari mai arziki, arzikin mai amfani” “yauwa ameen meenal mai kuɗi kuma mai kyau”. “Kai ma'eeshat Allah ya iya miki” meenal ta ƙarasa maganar tana girgiza kai. To haka ma'eeshat da meenal su kai ta hira har sai da aka fara kiraye kirayan sallah la'ara sanan suka miƙe su kai sallah. Bayan sun idar ma'eeshat toilet ta shiga tai wanka, bayan ta futo zama tai ta fara shafa kayan kwalliyar ta. ta ɗan yi de kwalliya ba mai yawa ba, sanan ta ɗauko abayar ta baƙa ta saka, tai yafa ɓakin mayafin abaya. Ma'eeshat ma'abociyar son abaya ce sosai, duk rabin kayanta abaya ce, kuma gashi in tasa tana matuƙar yi mata kyau abinka dame jiki. Bayan ma'eeshat ta shirya tsaff wayoyin su ta ɗauka harda ta doctor ashmal sabida kar a kirawo in ya aiko a ƙarɓar mai wayar kuma bata kusa da ita. daga haka ma'eeshat da meenal suka wace garden domin yin hoto. haka meenal da ma'eeshat su kai ta shan hotunan su kala-kala, waccan tayiwa wanan, wannan ta yiwa wanan, basu suka gama pictures ɗin ba sai wajan ƙarfe 5:30. Suna gamawa suka fara editing ɗin abin su hankali kwance gaba ɗaya hotunan a wayar meenal akayi su. “Kai meenal ji yarda kika yi kyau a hotanan dole na turawa waleed ko nima yayimin kyauta”. ringing ɗin wayar daya fara tashi ne ya dakatar da meenal daga maganar da zata yi. Wayar doctor ashmal ce ta da take gefe a ajiya ta fara ringing. da sauri ma'eeshat ta kai hannu, ai kuwa gaban tane ya faɗi rass ganin ansa my number. baki na rawa tace "Kinga meenal shine yake kira wallahi, may be ya aiko a ƙarɓar mai fa”. meenal kuwa ci gaba tai da editing ɗin hoton tare da cewa “to ki ɗaga mana kiji ko ya aiko”. Hannu na rawa ma'eeshat ta ɗaga wayar tare da karawa a kunne tana cewa "hello". “Gani nan nazo dede address ɗin da kika bani, ki aiko a kawo min wayar tawa”. Rass gaban ma'eeshat ya sake faɗuwa jin muryar doctor ashmal, amma dakewa tai tace "Please in ba damuwa ka shigo cikin layi sai ka miƙe, gida na ƙarshan layin daga hannun hagu ka tsaya ganin nan futowa sai na baka wayar, sabida yanzu ba wanda zan aiko kuma bazan iya futowa har titin nan ba yayi nisa”. Ma'eeshat tana ƙarasa faɗin haka Doctor Ashmal ya katse wayar. Wani gumi ne ya fara getowa ma'eeshat, Kallon meenal tai wanda ta duƙufa tana editing ɗin hototunam. ckin sanyayiyar muryar ma'eeshat tace "meenal kizo ki raka ni mana na kai mai kinga ya katse wayar Allah yasa ba haushi yaji ba, da kansa ma yazo”. Girgiza kai meenal tai tare da cewa “a'a kinga ki bari ba sai munje ba ki bawa baba mai gadi kawai ya miƙa masa wayar tunda su aryan basa nan. Wani kallon galala ma'eeshat ta watsawa meenal tare da cewa “tab Allah ya kiyaye yanzu so kike nai asarar ganin kyakyawan nan da kan sa fa yazo ba aikowa akai ba, ni kuma sai naƙi fita gaskiya bazan iya ba kawai ki tashi muje malama”. Meenal tana ƙoƙarin yin magana wayar doctor Ashmal ɗin ta fara ringing, a karo na biyu. Da sauri ma'eeshat ta ɗaga tare da cewa "hello". Amma ma'eeshat shiru taji ba amsa, da ma'eeshat taji shiru sake cewa tai “hello kana ji?”. amma de again shiru, sai ma ƙarar cajin wayar taji alamun wayar za tai short down. Da sauri ta katse kiran tare da cewa kinga meenal ba network kuma gashi wayar saura one percentage yanzu zata mutu wallahi kuma ban san ya zanyi ba. maeenal hankali kwance tace “to ki sauri ki kwafi number mana ko wayar ta mutu sai ku cigaba da communication da wayar ki”. “Eh kin kawo shawara” ma'eeshat ta faɗa tana shiga call, Tana shiga ta buɗe number tara da miƙawa meenal tana cewa yi sauri ki karanto min dan Allah kafin wayar ta ɗauke”. Kamar yarda ma'eeshat ta buƙata haka meenal ta fara karanto mata number da sauri ita kuma tana sawa, ai kuwa suna cikin ƙwafa wayar ta mutu. “Wayyo ma'eeshat wayar ta mutu, amma 4777 ne a ƙarshan number maza kisa, number special ce”. Yauwa maeenal ma'eeshat ta faɗa tana ƙoƙarin sawa, tana gama sawa ta danna call tare da karawa a kunne. Amma abin mamakin shine har wayar ta tsinke Doctor Ashmal bai ɗauka ba. Wani dogwan tsaki ma'eeshat taja tare da cewa “dama nasan zaka aikata sai girman kan tsiya wato bama zaka ɗauki number da baka sani ba” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana sake kiran doctor ashmal ɗin. A taƙaice de sai da ma'eeshat tai wa Doctor Ashmal kira uku be ɗauka ba. Tsaki ta sake ja sanan ta tura masa gajeren message kamar haka, "Wayar taka caji ya ɗauke shine nake kiran ka da wanan layin, in kazo zaka iya bugomin ta wanan layin". Ba a ɗauki 2 minutes ba Doctor Ashmal yayiwa ma'eeshat reply da " ina kofar gidan da kika ce". Ma'eeshat tana gama karantawa ta saki ajiyar zuciya tare da cewa “yauwa meenal yazo, taso ki rakani na kai ma, kinga kema kya ganshi a zahiri”. girgiza kai meenal tai, sanan tace " a'a gaskiya ni ba zani ba wallahi tabb”. Tsaki ma'eeshat taja sanan ta ɗauki wayar ta da ta Doctor Ashmal ɗin tace “to ni bari naje kar kije ɗin” daga haka ma'eeshat ta wace fuuuuuuuuuuu. Ko da ta fita ƙofar gidan nasu wata mota ta gani mai rai da nunfashi gaba kaɗan da gidan nasu. A cikin ranta ko ba'a gaya mata ba tace " wanan shine". Ɓangaren Doctor Ashmal kuwa zaune yake a cikin mota yana danna wayarsa kamar ance ya ɗago yana dagowa ya hange ta, a baya ta cikin mudubin motar. Sosai ya tsura mata ido yana kallon yarda take tafiya, duk da ba sauri take ba amma jikin ta yana ɗan rawa, sabida tana da jiki ba lefi. tunani Doctor Ashmal ya farayi, taya wayarsa taje hanun ta ita da ko ƙarasowa table ɗin ba tai ba bare ta zauna. sai yanzu yaji sunan ma'eeshat ya dawo mai lokacin da tace mai ma'eeshat ce, kuma ya tuna afnan tana ta cewa macica amma de ya kasa gane mai take nufi sai yanzu. Duk da doctor ashmal bai fiya kallon mutane ba amma haka nan yaji ya kasa janye idanunsa daga kallon ta harta kusa ƙarasowa, sai da yaga da gaske-gaske tana gabb da ƙarasowa ya sunkuyar da kansa ya cigaba da danna wayarsa. Ko da tazo galass ɗin motar a kulla yake kuma gashi baƙi ne baka ganin wanda yake ciki. Wani dogwan tsaki taja, tare da ɗaga wayarta domin kiran sa. Doctor ashmal kuwa yana kallon ta sarai tass, lokacin dayaga taja tsaki, burge shi tai sosai musamman ma dayaga lokaci guda tasha kunu. kiranta yana shigowa bai ɗauka ba, katsewa yayi sanan yasa hannu ya buɗe murfin motar. Ma'eeshat kuwa tana ganin ya buɗe murfin motar taja baya a zuciyarta tace “wallahi in be futo ba, ba zata bashi ba, sabida tsabar rainin hankali ko murfin motar ma bai gama buɗewa ba, ni yake so na ƙarasa buɗe mai kenan, to ai wanan ba office ɗin sa bane da zai zo yana shawa mutane ƙamshi” duk ma'eeshat a cikin zuciyarta take faɗin hakan. Doctor ashmal sai da yayi kimanin 5 minutes bai futo ba yana kallo yarda ma'eeshat take cika take wani batsewa shi kuwa sai murmushi yake ta saki shi kaɗai, dan abun ma dariya yake bashi. Doctor Ashmal ji yayi gaba ɗaya bai kyauta ba, da yake shi yasan darajar mutane Kuma yasan ya kamata shi har ga Allah ba da niya yaƙi futowa ba kwai yana so yaga ma'eeshat tayi faɗa ne in ya fita. Dan haka a hanzarce doctor ashmal ɗin ya cire bell ɗin motar sanan ya ɗauki wayar sa ya fita daga cikin motar ya rufo. Ma'eeshat tana ganin doctor ashmal ya futo tai saurin sakin fuskarta, daka jin haushi sanan ta fara takawa sannu a hankali har ta ƙarasa inda doctor ashmal ɗin yake....... my number 09162226240 kar mu manta da like (reaction) ayi following ɗin channel ɗina, mutanan arziki. kar ku manta da sharing. mu haɗe a next page. Game buƙatar karanta littafi doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya yayi fallowing ɗin channel domin samu. _page 8 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ma'eeshat tana ƙarasawa wajan doctor ashmal ta sunkuyar da kai tare da cewa "ina wuni"?. Fuska a sake Doctor Ashmal yace “ina wuni yakike?”. “Lafiya ƙalau Alhamdulillahi” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana sunkuyar da kai ƙasa. Doctor ashmal bai sake cewa komai ba yayi shiru yana kallon gefe. “Ga wayar taka afnan ce ta ɗauko, to nayi tunanin tawa ce, sai da nazo gida na gane ba tawa bace” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana miƙawa Doctor Ashmal wayar. A hankali doctor ashmal ya miƙa kyakyawan hanun sa tare da cewa “oh afanan ce ta ɗauko kenan tom shikenan ki gaishe da ita”. “Tom zata ji, amma kayi haƙuri, afnan ce tai ta yin wasa da wayar tana dannawa shi yasa cajin ta yayi short down”. Jinjina kai doctor yayi tare da kallon ma'eeshat ɗin yana cewa “ok ba damuwa, thank you kya gai damin da afanan bye” daga haka doctor ashmal bai sake cewa komai ba ya juya ya nufi motarsa. Ma'eeshat bin bayan sa tayi da ido tanajin kamar ta ruƙo shi karya tafi, duk sai taji ba daɗi da doctor ashmal ɗin bai sakar mata fuska sunyi hira da wasa ba, kamar yarda ya sakarwa ƙanwar ta afnan ɗazu. Ma'eeshat tana ganin doctor ashmal ya buɗe mota zai shiga tai saurin juyawa ta fara tafiya abinta, zuciya cike fall da kaɗaici. “Oh yanzu nasan ba zamu sake haɗuwa ba” ma'eeshat ta faɗi hakan a cikin zuciyarta. tun kafin ta shiga gida ma taga motar doctor Ashmal ta wuce. Ma'eeshat tana ƙarasawa ciki ta zauna kusa da meenal tare da cewa “har yanzu baki gama editing ɗin bane?”. “Eh ban gama ba amma na kusa har kin bashi wayar?”. “Eh na bashi har ya tafi, kai meenal wallahi mutumin nan babban yaro ne finemen, kin san I phone 17 pro max ce a hanun sa bayan 14 ɗin”. Jinjina kai meenal tai tare da cewa “masha allah kuma gashi ba a daɗe da lunching ɗin ta ba ko?”. “Ina fa aka daɗe da lunching ɗin ta dududu ba'a fi 3 months fa ba”. Jinjina kai meenal tai tare da cewa “gaskiya ne kema Allah ya baki” washe baki ma'eeshat tai tare da cewa “ameen meenal tawa ya bamu baki ɗaya ma”. To meenal ba ita tabar gidan su ma'eeshat ba sai da tayi sallah isha'i sanan driver ya mayar da ita. Bayan meenal ta koma gida zama tai suka sha hirar su da baba, kamar yarda suka saba. bayan su gama hirar tasu sallama su kai sanan meenal ta wuce bedroom ɗin ta, domin kwanciya, tana kwanciya kiran waleed yana shigowa. Murmushi meenal tai sanan ta ɗauki wayar, ta kara a kunne tare da cewa “asslama'laikum”. “Wa'alaikissalam gimbiya ta yau wace duniyar kika shiga tun wajan magriba nake kiran ki fa kin ƙi ɗaukar wayar, wajan 20 miss call nai miki, hankali na duk yabi ya tashi Allah yasa ba laifi nayi miki ba gimbiyar mata”. Girgiza kai meenal tai kamar waleed ɗin yana kallan ta, sanan tace "a'a ni ba abinda kai min, lokacin da ka kirawo ni bana kusa da wayar ne, muna tare da ma'eeshat, yau a wajan ta na wuni sai bayan isha'i na dawo gida, kuma ina shigowa nasa wayar tawa a caji, nabar ɗakin, sai yanzu na dawo ina shigowa kana kira”. Ajiyar zuciya waleed ya sauke tare da cewa "Alhamdulillahi da nayi tunanin wani abun nai miki, ya kika baro su mami da ma'eeshat fatan kowa lafiya?”. Jinjina kai meenal tai tare da cewa “eh kowa yana cikin ƙoshin lafiya”. “Masha Allah amma daga yau in zaki fita ki ringa gayamin kinji farin cikina”. “Ai kasan gidan su ma'eeshat ba baƙwan zuwa na bane, kuma shima kamar gidan mu ne, shi yasa ban sanar da kai ba”. Eh na sani meenal ɗina, Kin san bana son ki ringa fita wasu mazan suna kalle min ke ne, Bana son kowa ya kalle ki, sai ni kaɗai dan Allah meenal ki amince na zamo mijin ki wallahi kece farin cikina, ina son ki, bana son abinda ze raba ni dake ko na minti ɗaya ne meenal”. Shiru meenal tai ba tare da tace komai ba. “Meenal ɗina kiyi magana mana, bana so muna magana kinayin shiru dan Allah kice wani abun”. Ajiyar zuciya meenal ta sauke sanan tace “to ni me zance?”. “Kice komai ma meenal ɗina duk abinda kikace ina farin ciki da shi a gare ni”. Jinjina kai meenal tai tare da cewa t”om yakake?”. “Hmmm ina lafiya meenal damuta kawai kece, wallahi ina son ganin ki, gashi kuma ke ko tambayata bakya yi yaushe zan dawo na ganki”. Cikin sanyayiyar muryar meenal tace “tom yaushe zaka dawo kano?”. “Alhamdulillahi meenal ɗina ko yau kikace na dawo sai na dawo, na ƙagu naga kyakyawar fuskar nan taki mai cike da annuri”. “A'a ni ba ruwana duk sanda kake so zaka iya dawowa” meenal ta faɗi hakan tana gyara ƙwanciyarta. “haba meenal da bakin ki kike cewa haka, to bakya so na dawo kenan nifa in bake kike so na dawo ba bazan dawowa ba, sabida ke kaɗai ce farin cikina meenal, na rasa farin cikina a baya, Ada iyaye na sune farin cikina, amma sun rasu, shi yasa yanzu nake so na aure ki ko kya mayemin wani gurbin kewa da baƙin ciki, yanzu meenal bani da wani sauran farin ciki a rayuwa ta sai ke, dan Allah kar ki rabu dani, wallahi in kika rabu dani ban san inda zan sa kai na ba” waleed ya ƙarasa maganar muryarsa tana rawa. Cikin tausaya meenal tace “in sha Allah waleed ba zaka rasa ni a rayuwarka ba, in de nice zan dawo ma da farin cikin da ka rasa, to in sha Allah zaka same ni”. “Alhamdulillahi meenal da bakin ki kike faɗin hakan, wayyo Allah farin ciki zai kashe ni wayyo daɗi Allah na gode ma wallahi sai nayi azumi uku na farin ciki da godewa uban giji, meenal na yarda na rasa duk abinda na mallaka a rayuwa in de zan same ki I LOVE YOU meenal, kema kice kina so na, kinji?”. Shiru meenal tai dan ita kunyar cewa waleed tana son shi take. “haba meenal kice kina so na mana, dan Allah” waleed ya faɗa cikin muryar rarrashi. Girgiza kai meenal tai tare da cewa “a'a ni bazan iya ba gaskiya”. “Haba meenal zaki iya ki cemin kina sona kinji, ki rufe idon ki sai ki gayamin meenal kar zuciyata ta fashe”. Meenal runtse idon ta tai, tare dasa hannu biyu ta rufe idanun ta cikin tsananin jin kunya da wata siririyar murya tace "nima ina SON KA waleed". Daga haka meenal tai saurin katse wayar tana mai matuƙar jin kunya. Meenal tana cikin halin jin kunyar nan taji wayarta ta fara ringing. Duk da meenal bata duba ba tasan waleed ne yake mata kiran, tana dubawa kuwa taga shine yake mata kiran nan. Rufe fuska ta meenal tai da fullo ba tare da ta ɗauki wayar ba,. Sai da waleed yayi 5 miss call yana kira meenal bata ɗauka ba, tana kwance rufe da fuska tana jin kunyar da tacewa waleed tana son shi, shi kuma yana nan yana ta kira, haka de waleed ya gaji da kira ya haƙura. meenal kuwa, daran ranar da ƙyar ta iya bacci, tana rintse ido take hango waleed a idon ta duk da kuwa ba wani gama sanin kamarsa tai ba, a daran ranar taji son waleed ya turniƙe mata zuciya, gaba ɗaya tunaninsa takeyi, meenal ba ita tai bacci ba sai biyun dare zuciya cike fall da kewar da son masoyin ta waleed...... After one week Soyayyah mai ƙarfi ta shiga tsakani meenal da Waleed, duk da shi dama can waleed yana mutuwar son maeenal, to amma meenal data bashi dama ta fara son shi, sai son da yake mata ya ƙaru a zuciyarsa sosai. gaba ɗaya meenal bata jin daɗi in bataji muryar waleed ba, kamar yarda shima baya jin daɗi in bai ji tata ba a rana sai suyi waya sau 3 zuwa 4, shima a hakan dan meenal tana takawa waleed birki ne amma in za a biye ta waleed sai su wuni suna waya ma. Tun meenal tana ɓoyewa ma'eeshat ta fara son waleed, har ta dena ɓoye mata sabida kullum in suka zauna zancan waleed meenal takewa ma'eeshat. ma'eeshat kuwa taji daɗin hakan sosai, dan tana ganin dacewar waleed da meenal, tun ba yau ba. Tuni ma'eeshat ta manta da wani Doctor Ashmal ko mai kama da shi, tun daran ranar da yazo ya ƙarɓi wayarsa bata iya bacci ba sabida tunanin shi, amma gari yana wayewa ta manta da shi, ta cigaba da sabgarta, kamar ma ba'a halicci wani Doctor Ashmal ba haka ma'eeshat ta mance da shi. Exams ɗin meenal da ma'eeshat tayi kyau sosai dan gaba ɗaya sun cinye, yanzu nan da jibi zasu koma school, domin su cigaba da karatun su, in lokaci yayi, zasuyi jamb da su neco ɗin su, sanan suzo suyi shagalin candy. ••••••••••••••••••••••••••••• Kwance yake akan bed daga shi sai boxser da farar singlet, sai juyi yake goma ta haɗe mai da ashin, ga ciwan ciki da yake damun shi na rashin matar da zai yi ma'amala da ita, dama kusan kullum haka yake fama da ciwan ciki, in yazo kwanciya, tun yana iya daurewa har abin ya fara fin ƙarfinsa. ga kuma yawan tunani ta da yake yi a ƙwaƙwalwar sa. Yau kimanin 5 days kenan yana tunanin ta, tunda suka rabu yake tunanin ta, in ya rufe ido ita yake gani in yana aiki ita take faɗo mai gaba ɗaya ya shiga damuwa. tayi mugun burge shi yawanci abinda yake buƙata ga ƴar mace tana dashi, ko ta ina tayi mai, matsalar kawai tana da hasken fata. Doctor ashmal yana ta mamakin dalilin da yasa ta zauna mai a rai kamar haka, kuma gashi shi bai taɓa soyayya ba bare yasa rai ko ita ce ta kama shi. abun da zai tsayawa doctor ashmal a zuciya ba ƙarami bane sam baya tunanin abu kamar haka amma gashi yau har kimanin one week ta kasa fita daga ran sa. To wai me yake faruwa ne na kasa manta ta a zuciyata haka? Doctor ashmal ya watsawa kansa tambayar. “Anya baka fara son ta ba kuwa?” Ɗaya daga cikin zuciyar doctor ashmal ta tambaye shi. Da sauri doctor ashmal ya girgiza kai tare da cewa “no ni ba son ta nake ba, akan me zan kamu da santa, kawai burge ni take”. “Ka dena yaudarar kan ka, kana cutar da kan ka akan abinda kake so, to wai ita ta haramta gare ka ne, ko kuma tana da wani aibun da ba zaka iya soyyayyah da ita bane, da kake ta gudarwa kan ka faɗawa soyayyarta, ka dena yaudarar kan ka, ka bawa zuciyarka abinda take so”. Duk Zuciyar doctor ashmal ce take ta raya mata wanan. Ajiyar zuciya doctor ashmal ya sauke yana tunanin abinda zuciyarsa ta faɗa gaskiya ne, amma to taya zai sake haɗuwa da ita?. Take zuciyarsa ta sake bashi amsa da “A gidan su zaka ƙara haɗuwa da ita mana ba kasan gidan su ba?”. Da sauri doctor ashmal ya girgiza kai, yana tunanin impossible baze taɓa iya zuwa gidan su ba gaskiya, sabida shi duk harkar zubar da mutunci baya cikin ta, may be yanzu yaje gidan su kuma taƙi amincewa. Ai koda doctor ashmal yana da tabbacin in yaje gidan su ma’eeshat zata amince to ba zeje ba saboda ba ita ta gayyace shi wajan ta ba, yaje yace mata mai. To haka doctor ashmal yayi ta saƙa da warwara shida zuciyarsa kamar yarda yasa ba, tunda ya yaje gidan su ma'eeshat ya amshi wayarsa, ma'eeshat ta shiga ransa daram ta kasa fita, kullum cikin tunanin ta yake musamman ma in yazo bacci. Haka de doctor ashmal yayi ta saƙa da warwara yana jin shauƙin ma'eeshat har bacci yayi awan gaba da shi. kuyi haƙuri da wanan yau bazan iya typing mai tsayi ba sabida bana jin daɗi. My number 09162226240 kar ku manta da following channel ɗina ina muku fatan alheri mutanan arziki. mu haɗe a next page. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. _page 9 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 11:00am. A nitse yake sauke nunfashi yana matuƙar jin daɗin baccin da yake. yau weekend ta kasance ranar hutunsa, baze fita da wuri ba, shi yasa ya samu bacci mai daɗi, kuma gashi jiya da dadare sai wajan 2 ya iya bacci saboda ciwan ciki da tunanin ma'eeshat. Can cikin tsakiyar kan sa yaji ana knocking ɗin ƙofar bedroom ɗinsa. A nitse ya buɗe kyawawan idanuwan sa yayi shiru yana sauraran ƙarar knowing ɗin. Dole Doctor Ashmal ya miƙe daga kwanciyar da yayi, saboda yasan ba a fiya biga mai ƙofa bedroom da safe ba in yana bacci, sai da wani ƙwaƙwaran dalili,. Dan haka a hanzarce ya miƙe sanan ya zura jallabiyar sa idanuwa cike da baccci ya nufi ƙofar bedroom ɗin nasa, ya fara buɗewa. Yana buɗewa yesmeen ƙanwarsa ya gani tsaye a baki ƙofar. Ɗan saki fuska yayi ƙadan tare da cewa “my babe lafiya kika tashe ni daga bacci mai ya faru ne?”. “Yah good morning, dama momy ce tace nazo na gaya ma, tana ta kiran a waya baka ɗauka ba, tace kazo ka yiwa su muhseen magana tun dazu suke faɗa tayi musu magana sunƙi suji, yanzu ma sun fara dambe”. “What dambe kuma?” gyaɗa kai yesmeen tai alamun eh,. Hannun yesmeen doctor ashmal ya riƙe zuciya a harziƙe yace “tawo muje”. Doctor ashmal yana ƙarasawa babban falon gidan ya tarar muhseen da fadeel suna ta dambe wanan ya kai wa wanan naushi wanan ya kai wa wanan naushi, momy kuma tana daga gefan su sai magana take musu tana ƙoƙarin raba su. A zuciya doctor ashmal ya ƙarasa cikin fushi ya wanke fadeel da mari sanan ya juya ya wanke muhseen shima da mari, ai kuwa nan da nan suka rabu kowa yana wuci musamman ma fadeel. “Baku da hankali ne waii, ashe har yanzu baku girma ba mutanan banza kawai” momy ce da bakin ta take muku magana amma bakuji ba, sabida ku marasa hankali ne a cikin gida za kuzo kuna yi mana faɗa” cikin faɗa doctor ashmal yake maganar. Duk da doctor ashmal ba mutum ne mai faɗa ko saurin hannu ba, amma su fadeel sun kai shi maƙura yau wajan jin haushi, abinda yasa doctor yaji haushi har ya kai da marin su maganar da akace momy tai musu ba suji ba, dan shi a rayuwarsa ma ya tsani raini, bare ma ace momy ce take musu magana suka ƙi dai na faɗa. suma su muhseen sunyi mamakin ganin doctor ashmal yana faɗa kamar haka har da duka ma, saboda sun san shi ba ma'abocin faɗa bane kuma tunda suke bai taɓa dukan su ba sai yau. Fadeel a fusace ya kalli muhseen tare da cewa “wallahi sa'ar ka ɗaya an raba mu da yau sai jikin ka ya gaya ma”. Muhseen ne hassan shi kuma fadeel husaini, muhseen da fadeel suna da haɗin kai kuma suna shiri sosai amma in suka tashi faɗa sai ka rantse basu taɓa ganin juna ba. kyawawane na ajin farko sanan suna tsakanin kamar da ba mai gane ɗaya daga cikin su sai mutan gidan, ko abokan su ba kasafai suka cika gane su ba. fadeel yana da zafin rai sosai mafaɗaci ne, duk wani faɗa da za suyi tsakanin su da muhseen yawan ci shine da tsokana , sam bashi da haƙuri ko kaɗan. muhseen kuwa ba ruwansa kullum cikin fara'a yake abinsa gashi da sauƙin kai. Cikin tsawa doctor ashmal yace “short up your mouth stupid boy, ana yin magana kana magana, dama na daɗe da gane cewa kan ka yana rawa sai na saita ma shi, wai meye ya haɗa ku faɗa ma kake yiwa mutane shoutingl. A kunbure fadeel yace “duk shine ya jawo komai zuwa yayi zai yiwa abokina snatching ɗin budurwarsa” fadeel ya ƙarasa maganar yana gallawa muhseen harara. saura ƙiriss doctor ashmal ya fashe da dariya saboda fadeel ya bashi dariya, ita kuwa momy a gaban su ta fara dariya, ita da yesmeen da take gefan doctor ashmal ɗin riƙe da hanun sa sai dariya take tana yi tana toshe baki. Sake haɗe rai doctor yayi tare da kallon muhseen yace “kai mai ya haɗa da budurwar abokin nasa?”. “Wallahi doctor ƙarya yake ba wata budurwa abokin sa, wata class mate ɗin muce, shine take binmu mu koya mata karatu sabida taga ni da shi muna da ƙoƙari, farko shi ta fara cewa ya koya mata yayi mata wulaƙanci yaƙi, shine ni kuma na bata haƙuri nake koya mata. in akayi karatu bata gane ba sai tazo tace na koya mata, ko na sake yi mata bayini, to shine ƙwanaki ta ƙarɓi number ta wataran in na hau online sai tace na koya mata haka nake koya mata. to shine fa na gayawa muhseen har yanzu muna tare da ita ina koya mata karatu. Tun daga nan ya fara bibiyarta to bata sakar mai fuska saboda abinda yayi mata a baya. shine kuma wai ya dawo waje na yace min na bata haƙuri akan abinda yayi mata, ni kuma nace ba ruwana, karatu ne a tsakanin mu nake koya mata. to shine yake tajin haushi na wai soyayyah muke da ita, kuma shi gashi yayi nadama ya fara son ta. yanzu da safan nan ina fotowa daga toilet naga wayata a hanunsa wai ita ta kirawo, banma fa san mai tace mai ba shine ya kamani da dambe wai mayaudari na raba shi da masoyiyar sa”. Momy da yasmeen sake fashewa su kai da wata dariyar shi kuwa doctor ashmal shanye dariyar tasa yayi sosai tare da watsawa fadeel wani kallo yana cewa, "dama nasan kai ne da neman rigima sam baka san zaman lafiya, tunda kai kaƙi koya mata karatun ba sai kabar wanda zai koya mata ya koya mata ba, mene nayi musu binbini”. “Wallahi Doctor ƙarya yake maka, soyayya ce a tsakanin su ba wani karatu, da na ɗaga wayar fa ji nai tace, hello dear zaka shigo ne yau”. Jinjina kai doctor ashmal yayi zuciya cike da dariya yace “shikenan kuje kuyi, wato har tunanin soyayya kuke yanzu ko makaranta baku gama ba ko?. to ku shiga hankalin ku gaba ɗaya ku tafi ku bamu waje saura na sake jin kunyi faɗa zaku ga yarda zanyi da ku”. sumi-sumi fadeel da muhseen suka wuce suka bar wajan suna harara junan su ta gefan ido. duk da kuwa muhseen ne da gaskiya dan duk yanda ya faɗa haka zancan yake. bayan sun wuce doctor ashmal murmushi yayi tare da cewa “kai momy Allah ya shirya mana twins ɗin nan naki basa jin magana”. Yesmeen sake fashewa da dariya tai tare da cewa “wallahi yah, fadeel ne bashi da gaskiya duk abinda muhseen ya faɗa hakane sabida nima inaji suna faɗan akan haka tun ba yau ba”. Kumatun yesmeen doctor ashmal yaja, tare da cewa “oh, ni de babe ba ruwana in suka jiki, kiyi shiru kar suzo su takura min ke su ringa ƙoƙarin hucewa akan ki”. Dariya yesmeen tai sanan tace “tom yah, amma yaushe za kazo ka kai ni musha ice cream tare, jiya ma sai da su muhseen suka ce nazo su kai ni, nace a'a ni kai nake so, ka kai ni”. Zaro ido Doctor Ashmal yayi tare da cewa “no babe kar ki yarda, wanan yaran masu rawar kai ne zasu kai ki tabb ɗi jam, wallahi kibi a sannu duk sanda suka ɗauke ki a mota kafin kuje inda zaku sun gama ɗaga miki hankali, sun saki kinyi kuka da idanuwan ki, gudu za suyi tayi dake akab titi, wato har daɗi suke ji dan sun ƙarbo certificate ɗin su na driven school, shine suke cewa kizo su ɗanaki ko, to kar ki yarda babe na, ki bari ni da kai na, zan kai ki in na samu lokaci”. Jinjina kai yesmeen tai tare da cewa “tom shikenan yah ina son ka wallahi”. “hmmm nima ina sonki yesmeen tawa maza kije ki shirya ki tafi tahafiz kar ki makara a dake ki, kin san bana son a dakar min ke”. “Tom shikenan yah bye” daga haka yesmeen ta saki hanun doctor ta wuce bedroom domin shiryawa. Yesmeen yarinya ce kyakyawa mai diri, bata fi shekara 14yers ba, amma tana da girman jiki sosai dan in ka ganta sai kai tunanin za tai 16, amma ko na 1 hour ka zauna da ita zaka tabbatar yarinya ce shakaff, sabida kalamanta da rashin wayo. juyawa doctor ashmal yayi shima ya koma bedroom ɗin sa, ya kashe wayoyin sa baki ɗaya sanan ya koma wani saban baccin. Bashi ya tashi ba sai misalin ƙarfe 12:00 da rabi na rana, yana tashi ya shiga toilet yayi wanka, sanan ya futo ya taje sumar kan sa ya shafe jikin sa da maya mayan sa, sanan yasa wanda 3 qauter da baƙar t sheets ya fita fallo. Lokacin da ya fita ba kowa a fallon, amma ga abinci nan an shirya kala-kala, zama yayi a kan kujerar daining ɗin, sanan ya fara saving ɗin kan sa. Haka ya zauna ya ringa cin abinci yanaci tunanin ma'eeshat yana sake bijiro mai a zuciya. Bayan ya gama ci, bedroom ɗinsa ya koma ya ɗauro alwala sanan ya wuce masallaci domin sallah. Bayan ya dawo daga masallaci ji yayi gaba ɗaya jikinsa ya mutu, da yayi niyar fita ya shiga hospital ko guda ɗaya ne amma ya kasa, gaba ɗaya yana cikin damuwa, zuciyarsa ta azaftu da son ma'eeshat. Gashi kuma shi sai dambe yake da zuciyar tasa akan ta manta da ita ma'eeshat ɗin amma, ina abu kamar ƙara shi ake. Haka doctor ya kwanta yayi lamo kamar mara lafiya, yana ta tunanin mafita amma ya kasa gaba ɗaya komai ya tsaya masa cakk. To yau dai doctor ashmal wuni yayi a bedroom yana tunanin ma'eeshat, raban da ya zauna a bedroom ya daɗe har ya manta, sabida ko bashi da aiki in ya gama hutawa yana fita wani wajan, ko ya leƙa hospital. Amma sai gashi yau shine a bedroom ya kasa sukuni har wajan ƙarfe 7:30 na yamma dan har an fara kiraye-kirayan magriba. Ala dole Doctor Ashmal ya miƙe ya ɗaura alwala sanan ya fita ya gabatar da sallah isha'i. Yana dawowa yesmeen ta tare shi wai sai yazo sun je sunci abinci sunyi hira. Dr ashmal bashi da yarda zaiyi da yesmen, yasan ba zata yarda yace mata aa ba, dole haka ya biye mata, suka tafi suna cin abinci suna hira ko ta ɗebe mai kewa. Doctor ashmal yana matuƙar son ƙanwarsa yesmeen, sabida itace last bron ɗin su, kuma gashi tazo a mace, sanan ita kaɗai ce mace a cikin gidan nasu. Dama doctor ashmal yana son mace, mace tana burge shi ko saboda ƙannan sa duk ba mata bane, shi yasa yake bawa yesmeen kulawa duk abinda take so yana yi mata shi ko mene kuwa, kuma sam bayi yi mata faɗa ko tayi abun faɗan sai de ya lallashe ta yayi mata nasiha. Sai wajan ƙarfe 9:00 Doctor ashmal ya dawo bedroom ɗinsa, yana dawowa ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya futo gajeran wando kawai yasa ko arziki sa rigar bai samu ba yayi ƙwanciyar sa akan bed, sanan ya kunna wayoyin sa. Bayan wayoyin sun gama kamawa, babbar wayar ya fara ɗauka yana ɗauka yaga message ya shigo, dan haka direct wajan message ɗin ya nufa ya buɗe. Different message aka turomai wajan kala goma, dan haka kallon su ya fara yi yana tunanin wanne zai fara buɗewa sabodaa duk yasan de gama da aiki ne, suna da mahimmanci. Kamar ance doctor ya tafi ƙasan message haka ya yasa hanunsa ya gara messages ɗin wayar, ai kuwa cak wayar ta tsaya akan tsofaffin message. Wata duguwar ajiyar zuciya doctor ashmal ya saki lokacin da idon sa yayi masa tozali da number da ma'eeshat ta turomai gajeran saƙo lokacin da wayarsa ta ɗauke, da yaje gidan su. “Dama can ina da hanyar da zan haɗu da ita cikin sauƙi amma na manta kai” doctor ashmal ya faɗi hakan a zuciya sa yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Har ga Allah doctor ashmal ya manta da sunyi wani communication ɗin number shi da ma'eeshat, sai yanzu daya gani sanan ya tuna. Da sauri doctor ashmal yayi save ɗin number da litter m kawai, yama rasa ta ina zai fara kiran number, dan haka kawai tusa number a gaba da ido yayi yana kallonta kamar mai haddar number, shi kansa ya rasa ta ina zai fara kiran number.......... MA'EESHAT Sai wajan ƙarfe 5 na yamma ma’eeshat ta dawo gida, sabida tun wajan ƙarfe goma ta tafi gidan su meenal, sai da yamma driver yazo ya ɗauke ta ya dawo da ita gida. Tana dawowa gida wayarta ta saɓa ta hau online tana duduba messages ɗinta. gaba ɗaya ma'eeshat bataji daɗi ba saboda taga abbas bai mata reply ba, yau kimanin 3 days tana jiran sa, amma shiru. baya hawa online kuma in ta kira wayarsa a kashe. Ma'eeshat ta damu da abbas ne, sabida shi ko da yaush in ta hau online suna magana, 247 suna chat, shi yasa too days da baya hawa online ta damu tana ta tunanin ko lafiya, haka ma'eeshat tai ta danna wayar ta tana jiran kiran abbas. Sai da aka kirawo isha'i ta iya miƙewa dama batayin sallah, dan haka ƙasa ta sauka, ta wuce kicin za zubo abinci, taci, sai da ta gama cin abinci sanan ta dawo sama, tai wanka tasa kayan bacci. Haka ta cigaba da kallon ta a waya hankali ƙwance, wajan ƙarfe tara da rabi ma'eeshat taji ta fara jin bacci, duk da gobe babu school, ji tai ba zata iya ba gwara tai baccin ta kawai, dan haka kashe wifi ɗin wayarta tai, tana ƙoƙarin kashe wayar, taga wata baƙuwar number an kira ta da ita, wayar sai faman ringing take......... Gaskiya kuna yimin ƙauran like fisabillahi, sai na gama shan wahala na mu ku typing, amma like ya gagara, to kuwa zan tafi yaji, iya masu yimin like zan ringa turawa ta privet. kuma kar ku manta da fallowing ɗin channel ɗina. mu haɗe a next page. _page 10 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Da ido ma'eeshat ta bi number tana tunanin wanene? dan ita ba wani kasafai ta fiya ɗaukar number da ba suna ba. dan haka ji tai ba zata iya ɗaga wayar ba, zuba mata ido tai har tai ringing ɗinta ta katse. Ma'eeshat tana ƙoƙarin kashe wayarta ta tuna da Abbas, a fili tace “subhanahi ko to de shi ne yake kirana ma da wanan number?”. “Ai kuwa zai aikata in de abbas ne may be shine ma kika ƙi ɗauka” zuciyar ma'eeshat ta gaya mata haka. A fili ma'eeshat tace “tom bari na jira naga ko zai sake kira”. Sai da ma'eeshat tai 10 minutes tana jira a sake kira amma shiru, kawai ta yanke shawarar ta kira da kanta , dan tasan halin abbas in ya kirawo bata kusa, baya sake kira sai de in ta bushi iska wataran ta sake kira. “Kai gaskiya ban san ko lafiya ba yayi offline, yanzu in shine ya bugomin da wanan number ban sani ba fa, kai gaskiya gwara nabi shi” ma'eeshat ta ƙarasa zance tana ɗaukar wayar ta tah. Direct call ma'eeshat ta shiga sanan ta dannawa baƙuwar number kira tana gyara kwanciyar ta. ringing 4 ma'eeshat taji an ɗauki wayar. Shiru ma'eeshat tai tana sauraran number. abin mamaki shiru ma'eeshat itama taji anyi ba'ace komai ba kuma, bayan tana iya jin sautin numfashi mai wayar. Dan haka daurewa tai ta furta “hello ina ji?”. amma still shiru ma'eeshat ta sake ji ba magana, mamaki ya kama ta sosai ganin yarda taji an kira ta anƙi magana ita kuma tayi magana an mata shiru, kuma bayan tasan me wayar yana jin ta saboda tana jin alamun hakan. “Dan Allah waye haka ina ji ko wacece, koma wane yayi magana ina da abunyi fa” ma'eeshat ta faɗi hakan a ɗan tsawace. amma mai makwan magana sai jin sautin ajiyar zuciya taji kawaii. Cikin mamaki ma'eeshat tace “lallai ma, to ko wane ya bari duk sanda ya shirya ya kirani, in mutum yasan ba magana zaiyi ba to kada ya sake kira na dan gaskiya bazan ɗauki wanan rainin wayon ba, a kira mutum ai mai shiru, mutum yasan bashi da abin cewa ya kirawo ni, to ya bari in ya tanadi abin cewa sai ya kira ni, daga haka ma'eeshat ta katse wayarta tare da jan wani dogwan tsaki. Kashe wayar tayi gaba ɗaya, ta ajiye ta a gefe sanan ta shige cikin blanket ta kwanta tana jin takaicin kiran da akai mata ba magana, sabida ita ma'eeshat tana da zafi da saurin jin haushi sam bata son raini. Haka de ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita...... ••••••••••••••••••••••••• Ɓangaran doctor ashmal kuwa ma'eeshat tana kashe wayar ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tare da sakin wani siririn murmushi, sabida har ga Allah yayi matuƙar jin daɗi da yaji muryarta. Ji yayi zuciyarsa tai mai sanyi sosai, duk damuwar nan ta ragu sosai ba kamar da ba. Doctor ashmal ƙara danna call yayi domin ya kira ta amma yaji wayar a kashe,. Gyara kwanciya yayi yana ta tunanin sabida me ya kasa yi mata magana dan lokaci data ɗauki wayar ji yayi kamar an ruƙe masa baki. Gashi kuma sai wani burge shi take da take zazzaga masa faɗan nan, duk da kuwa yasan shi ya jawowa kan sa. To doctor sai da ya kai ƙarfe 12:30 na dare yana tunanin ma'eeshat kafin yayi bacci, zuciya fari ƙall yake baccin sa, ba damuwa kamar jiya, yana farin cikin jin muryar ma'eeshat ɗin. Washe gari. Doctor ashmal da wani tsananin son ma'eeshat ya farka, ji yake duk duniya ita yake son gani. dole haka yayi ƙarfin halin shiga toilet yayi wanka ya futo ya shirya a hanzarce. Be so fita hospital ba, amma jiya an mai message akan wani mara lafiya sosai, wanda aka kasa gane mai yake damun sa, dole sai yaje hospital ya duba shi. kaɗan daga baiwar da Allah yayiwa doctor ashmal kenan, duk rashin lafiyar mutum in aka kasa gane mai yake damun shi, doctor ashmal yana zuwa yake gane me yake damun sa, in de ba aikin asiri bane ko na aljanu, in sha allah yana ganin patien zai san mai yake damun sa. Haka doctor ashmal ya fita a hanzarce zuciyar sa cike fall da soyayyah da tunanin ma'eeshat. MEENAL “Meenal kwana biyu gaba ɗaya naga kin canza, kina yawan waya da mutane, sai ki shige ɗaki kita yin waya, kuma bayan da ba haka kike ba” umma da suke aikin tsinke zogale ita da meenal, ta watsawa meenal tambayar. Sunkuyar da kai ƙasa meenal tai tare da cewa “eh wanan ɗan uwan su ma'eeshat ɗin nan ne dana baki labari kwanaki, shine ma'eeshat tace dan Allah na ringa daga wayarsa in ya kirawo baya jin dadi, to bana son ma'eeshat ta roƙi alfarma ban mata ba shi yasa”. “A'a ai ba wani abun bane ba ma, in kuna magana tunda yanzu ai kin girma, matsala de shine yanayin tarbiyarsa, sannan kuma duk mutumin da yake san ki tsakani da allah ai ya kamata ace yazo ya samu iyayan ki kafin ku fara ma'amala Koh?”. Jin jina kai meenal tai tare da cewa "hakane umma, amma ni ina tunanin waleed zai kasance mutumin kirki tunda kinga ai nasan ma'eeshat ba zata haɗa ni da mutum da be dace ba, yayan ta ne, sannan mami ma da tasan bashi da hali ba zata bari yace yana so nah ba. sanan kinga baya garin nan a abuja yake aiki sai yayi wata biyar ma bai dawo ba, amma in sha allah yana dawowa zan gaya mai yazo ya samu baba”. “Gaskiya ne aminatuwa ya kamata kuwa, in mutumin kirki ne sai ayi a wuce gurin kin san de kyan 'yar mace ɗakin mijin ta, dan ni bana son wanan karatun”. “Kai umma aure kuma yanzu, a'a ni gaskiya bana so, ma'eeshat ce de mai wanan ra'ayin, ni karatu nake so”. “A'a ni kyma bana son wanan karatun me tsayi ko kinyi auran bana so, ki zauna a gidan mijin ki kawai ki mai biyayya, shifa karatun nan bashi da wani amfani in de ka samu miji na gari shikenan, karatun da ba zai taimake ki ba ranar ƙiyama, ai da na muhammadiya ne bazan damu ba, ko zaki mutu kina yi daɗi zanji, amma wanan karatun yanzu ai turawa ake bautawa kawai, abinda ba allah ne ya aiko mu muyi shi ba, iya karatun kore jahilci ai kin yi shi meenal”. “A'a umma yanzu karatu shine mutum wallahi, yanzu in nayi ilimi ai bazan dogara da mijina ba zan ringa taimaka muku, kuma misali ko mutuwa mijin yayi ai zan taimaki ƴaƴa nah”. Umma tana shirin yin wata maganar wayar meenal ta fara ringing. “to gashi ana kiran ki shine ko?”. Gyaɗa kai meenal tai tare da cewa “shine mana, matsala ta da shi yawan kira wallahi, amma mu cigaba anjima mayi wayar”. Girgiza kai umma tai tare da cewa “a'a gaskiya ya kamata ki ɗauka in mutum yana son ka ai ba'a wulakanta shi, yafi wanda yace baya yi da kai ai, maza ki tashi kije kuyi wayar, ni zan ƙarasa dama ai mun kusan gamawa”. miƙewa meenal tai tare da cewa "tom bari na ɗauka" dama tunda can meenal taiwa umma kara ne, amma tana son ɗaga wayar waleed ɗin dan yanzu har ta saba da nacin sa na kira, in bai kirata ma ba gaba ɗaya bata jin daɗi. Kafin meenal ta kai da ɗaukar wayar kiran har ya katse, amma yana katsewa wani ya shigo, sai data ƙarasa ɗakin ta zauna a kan gado sanan ta ɗauka tare da kafawa a kunne tana cewa “Assalama'alaika”. “Wa'alaikissalam babe nah, shine ina ta kiran ki baki dauka ba, so kike nai kuka ina kika shiga ne wai?. “hmmmm yanzu kai in ka kira ni ban ɗauka ba ai kasan uziri nake, haba yaya waleed sai kace zan gudu”. Dariya waleed yayi tare da cewa “to na sani ko guduwa zakiyi ki bar ɗan marayan allah?”. “Hmmm tom na gudu naje ina kai ma waleed ka cika rigima”. “Hmmm gimbiyata ba zaki gane bane, nifa in nayi one hour banji muryarki ba ji nake kamar zan mutu sabida tsabar damuwa”. Murmushi meenal tai tare da cewa “bama zaka mutu ba dama ina so muyi magana ka bugo akan gaɓa”. Da sauri waleed yace “tom ina jinki meenal maza-zama mai kike so nayi miki?”. “Dama ina so na gaya maka, kaga de bani nake da kai na ba kuma umma ta fara lura da yawan wayar da muke, dan haka ya kamata in ka dawo kazo ka samu baba, ka gaya mai abinda yake tafe da kai, kaga in ya baka izini sai munfi Jin daɗin fahimtar juna Koh?”. “Inalillahi meenal ɗina, dama har na kai wanan matsayin a wajan, da bakin ki, kike cewa nazo neman izini wajan baba, wayyo Allah daɗi kar ka kashe ni Allah na gode ma wallahi meenal kin gama yimin komai”. Murmushi meenal tai tare da cewa “kai ba fa cewa nai, kazo ka nemi aure na ba da kake wanan abun”. Dariyar jin daɗi waleed yayi tare da cewa “hmmm ba zaki gane ba wallahi, in de na samu baba ai mafarin auran kenan”. Meenal kuwa “hmmmm” kawai tace,. “Kai meenal ɗina nagode sosai da sosai Allah ya bar ƙauna, yaushe kike so na dawo?”. “A'a ni ba ruwa na duk sanda kake so ka dawo zaka iya”. “Tom shikenan jibi zan dawo in sha Allah”. Cikin mamaki meenal tace "da wuri haka kuma?". “Tabb to da a makare kike so nazo ai da zafi-zafi akan bigi ƙarfe, wallahi bazan tsaya wasa ba ai banga sauran zama ba, daga yau ma bazan sake daɗewa a nan ba, tunda na samu kin amshi soyayah to dole na ringa dawowa ina ganin ki naji daɗi a zuciya ta”. “Hmmm naji yanzu de ka rabu dani haka, zanje na cigaba da taya umma aiki anjima in na gama aikin sai muyi wayar”. “Ah maza-maza kije kar kibar umma da aiki, amma in kin gama ki kirawo ni pls”. “Tom shikenan zan kira”. “Hmmm meenal ɗina nasan halinki ba zaki kira ba kullum haka muke dake amma zan kintati lokaci in kin gama na kiraki da kai na, dan Allah ki gai da min da umma da kyau”. “Tom shikenan yaya waleed zata ji sai anjima”. Daga haka meenal da waleed su kai sallama zuciyoyin su cike da ƙaunar da kewar junan su....... DOCTOR ASHMAL Wunin yau gaba ɗaya jikin sa a sanyaye yake, yana duba mutane ne kawai amma shi kan sa yasan baya jin daɗin zuciyar sa yarda kasan anyi mai mutuwa haka yake ji. Sai da yayi sallah magriba ya samu ya futo daga hospital, direct ya shige motarsa sai gida. Yana isa gida ya shiga toilet yayi wanka, sanan ya ɗaura alwala yasa jallabiya ya nufi masallaci, bayan yayi sallar isha'i gida ya dawo, ya zauna akan daining su kayi dinner shi da mutan gidan harma dady. Suna yi suna tsokanan junan su suna wasa da rahama, amma doctor ashmal sam ya kasa, sa baki a hirar tasu, sabida shi tunanin sa da hankalin sa duk sun karkata wajan ma'eeshat. Suma su momy sun lura doctor ashmal ya canza baya mood mai daɗi, dan haka rabuwa su kai da shi kar su takura mai, duk da basu wani saba ganin sa a cikin wanan halin ba, amma sai su kai tunanin ko a hospital ne yaga abinda yasa jikin sa yayi sanyi ko wani abu makamancin haka de. Bayan doctor ashmal ya gama cin abinci miƙewa yayi yabar wajan, gaba ɗaya ya manta da mutane a wajan bare yayi musu sallama kamar yarda ya saba yi musu kullum, cikin farin ciki suke rabuwa. Yesmeen kamar za tai kuka tace “momy wai yau mai yake damun yah ashmal ne?”. Girgiza kai momy tai tare da cewa "a'a yesmeen ban sani ba may be de abunuwa ne, su kai mai yawa ki barshi ya huta zuwa gobe za kiga ya dawo dai-dai”. “Dady to kai kasan meke damun shi?” yesmeen ta faɗa tana kallon dady. fadeel da muhseen dariya suka kwashe harma da momy, shima kan sa dady sai daya dara. “Dady nayi tambaya kuma kuna yimin dariya sabida kunga yah ashmal baya nan ko?”. “hmmm auta kenan ai dole ai miki dariya, momy ma da take gida tace miki bata sani ba, bare ni da ba a gida na wuni ba, kuma kamar yarda momyn ki ta gaya miki may be busy ne yayi masa yawa, zuwa gobe zai dawo dede ki kwantar da hankali ki”.... Doctor ashmal yana komawa bedroom ya ƙure a.c sannan ya ɗauko wayarsa, ya lalubo number ma'eeshat ya fara kira. har sai da ta kusan tsinkewa ma'eeshat ta ɗaga ba tare da tace komai ba. shima kuwa doctor ashmal ɗin bai ce komai ba yayi shiru yana sauraran ta. Ma'eeshat da taji shirun yayi yawa wani dogwan tsaki taja tare da katse kiran. doctor ashmal kuwa kira ya sake yi, amma har ta katse no answer, dama yasan zaiyi wuya ma'eeshat ta sake ɗaga number. Gajeran message ya tura mata kamar haka" Please ki ɗaga mana ina so muyi magana ne”. Ɓangaran ma'eeshat kuwa, gani tai an turo mata message, amma tun daga saman wayarta karanta shi ba tare da ta shiga ba, shi yasa har lokacin bata gane doctor ashmal ɗin bane bare ma taga tsowan message ɗin daya taɓa shiga tsakanin su. Tana gama karanta message ɗin, wani kira ya shiga, ɗauka tai kamar yarda ya buƙata cikin faɗa-faɗa tace "wai wane wallahi in ba'ayi magana ba bazan sake ɗagawa ba”. Cikin siririyar murya ma'eeshat taji ance “nine”. Ma'eeshat har tsakiyar kan ta taji maganar tasa, tana son tuna inda tasan muryar ta kasa, amma dan haka ƙarawa tai da cewa "kai wa kuma?". ba tare da ɓata lokaci ba, ya sake bata amsa da "ni doctor ashmal............ wanan page ɗin friday ne, amma bana posting ranar weekend. Kar ku manta da yimin like (rejected) Ayi share and follow my channel. mu haɗe a next page. _page 11 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Gaban ma'eeshat faɗuwa yayi rass rass rass har sau uku. Sabida tsabar mamaki ko ƙwaƙwaran motsi ta kasa bare tai magana. Doctor ashmal kuwa cewa yayi "kina jin na?". Aro jarumta ma'eeshat tai tare da cewa “eh ina jin ka ina wuni?”. Murmushi doctor ashmal yayi tare da cewa "ina wuni”. Yamutsa fuska ma'eeshat tai tare da cewa “ina wuni kuma, ni kake gai dawa sai kace wata tsohuwa?”. Cikin mamaki doctor ashmal yace “oh sai tsofaffi ake gaidawa kenan?”. “Eh gaskiya de ni bana son a gaishe ni sai naji kamar an mai dani tsohuwa”. “Hmmm tom shikenan tunda bakya so na karɓi abata, yakike?”.murmusawa ma'eeshat tai tare da cewa “lafiya ƙalau ashe kai ne kake ta kira sai kayi shiru, kayi haƙuri kaga nayi tunanin wani ne har faɗa nai ban sani ba”. “No ba komai, Ya jikin naki kuwa fatan kin samu lafiya?”. “Ah jiki da sauƙi ma, dama rashin bacci da wuri ne, da banayi sabida exams, kuma yanzu nasha magani na warke sosai”. “Tom masha allah ya makaranta fatan de ba'a yi miki demotion ɗin da kike tsoro Ba Koh?”. Dariya ce ta ƙwacewa ma'eeshat tare da cewa “kai! kai! kai!, dama kana magana kenan”. “A'a ba sosai ba kawai ƙarfin hali nai sabida kar a kashe min wayar aƙi ɗauka”. “A'a taya za a kashewa manya irin ku waya, ai mu bamu kai ba, jarabawa ta alhamdulillahi tayi kyau sosai, ba za’ai min demotion ba na cinye”. “Ah masha allah haka ake so to Allah ya bada sa'a”. “Ameen doctor nagode sosai” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana sakin siririn murmushi. “Ok ba komai bari na barki haka kar na takura miki ki gai damin da afnan”. ma'eeshat har zata ce a'a bai ishe ta ba kar ya kashe amma sai taga kamar yarfi ne, dan haka murmushi ta sake yi tare da cewa “tom in sha allah zan gaya mata kuwa”. “Yauwa fatan next time in na sake kira za'a daga min waya?”. “sosai ma in sha allah duk sanda ka kirawo zan ɗauka”. “Yauwa nagode sai anjima” daga haka doctor ashmal bai sake cewa komai ba ya katse wayar. Ma'eeshat kuwa yana katse wayar ta fara birgima akan bed cikin farin ciki tace "wayyo daɗi zai kashe ni, wayyo Allah nah alhamdulillahi wai ni wanan kyakyawan mai aji ya kirawo oh Allah ya dubi zuciyarta Allah nagode ma wallahi yeeeeee”. Haka ma'eeshat ta kwanta tana ta burgima da murna tana sake godewa Allah bisa ni'imar da yayi mata. Jim ma'eeshat tai a fili tace “tom Allah de yasa so na yake yi, allah ka dubi zuciyata, Allah dan darajar annabi Muhammad s a w kasa yace yana so nah, Allah kana gani nima ina son shi tun sanda na fara ganin sa”. Haka de ma'eeshat tai ta sambatu tana addu'o'i a kan doctor ashmal ya furta mata kalmar so. ma'eeshat har Allah-allah take gobe tayi ta haɗu da aminiyar ta meenal ta bata labarin yarda doctor ashmal ya kirawo ta da kan sa. cikin wanan tunanin bacci yayi awan gaba da ma'eeshat ɗin.... Bangaran doctor ashmal kuwa yana ajiye wayar ya saki wata nannauyar ajiyar zuciya tare da cewa “alhamdulilahi, Allah nagode ma, wai dama ashe haka soyyayyah take. ƙiri-ƙiri na kasa sukuni sabida soyayyah ya ilahi, Allah de kasa ta amince dani”. Doctor ashmal ji yayi zuciyar sa tai masa wani sanyi sosai da sosai, gaba ɗaya farin ciki ya rufe shi ta ko ina, jikin sa har wani ƙwari ya sake yi lokaci guda yaji babu damuwar a zuciya sa. Daran yau de cikin farin ciki doctor ashmal ya kwanta bacci, haka yayi ta tunanin ma'eeshat har bacci yayi awan gaba da shi, shima. MEENAL Meenal tana shigowa motar ma'eeshat ta sakar mata murmushi tare da cewa “ke yau fa da labari”. itama meenal murmushi ta saki ta rufe murfin mota sanan tace "kai ma'eeshat ai kya bari mu gaisa daga shigowa sai labari kuma”. Dariya ma'eeshat tai sanan tace “hmmmmmm rabu da gaisuwar nan ke de kin san jiya da daddare mai ya faru kuwa?”. Girgiza kai meenal tai tare da cewa “a'a sai kin faɗa ina jin ki”. “Daran jiya” ma'eeshat ta faɗa tana dafe ƙirji tare da sakin wani kyakyawan murmushi. “kai ma'eeshat kin fiya jan aji mai akai a daran jiyan kuma?”. Gyara zama ma'eeshat tai tare da cewa “ina wanan doctor ɗin da ƙwanaki afnan ta ɗauko mai waya har yazo ya karɓa”. “Eh na tuna shi, wanan de ɗan kyakyawan Koh? “Shifa meenal, kin san jiya kirana yayi da daddare wai mu gaisa har da yimin ya jiki fatan naci exams”. “Ah masha allah garin yaya ya samu number ki?”. “Hmmm kin manta da wayar ta kusan ɗaukewa bake kika ce na ɗauko number sa ba har na kirawo shi bai ɗaga ba, daga ƙarshe kuma na tura mai message yayi min reply”. “eh na tuna tanan ya samu number ki ashe to alhamdulillahi allah ya temake ki dama kuwa kin ƙyasa sosai”. “Hmm wallahi kuwa meenal amma matsalar bai cemin yana so na ba fa wallahi”. Dariya meenal tai tare da cewa “kai ma'eeshat harda sauri haka komai a hankali akeyi, in sha allah zai ce yana son ki kar ki damu”. “Ameen meenal tawa nagode sosai nifa wallahi in yace yana sona har azumi zanyi sabida farin ciki in gaya miki”. “kai! kai! kai! gaskiya ma'eeshat kin kamu da yawa har azumi nawa zaki yi to?” meenal ta ƙarasa maganar tana tsare ma'eeshat da Ido. “Azumi 1 zanyi ba yawa” “oh to da sauƙi lallai ma'eeshat kin iya faɗawa soyayya wallahi”. “hmmm meenal kenan wallahi guy ɗin ne ya haɗu ba lefi duk abinda nake so a ɗa namiji yana da shi har ya wuce yarda nake tunani ma”. “To allah ya baki shi, wai kin san waleed gobe zai dawo kuwa?”. ɗan zaro ido ma'eeshat tai tare da cewa “haba de, masha allah wato kun kusan ku haɗu kenan”. murmushi meenal tai tare da cewa “eh zamu haɗu mana tunda sabida ni zai dawo ma”. “ah ai meenal ko baki faɗa ba nasan sabida ke zai dawo, in kika ce dawowar kan sa ne ai ƙaryata ki zanyi ma, to tunda ni kai na ban san zance ba, kuma kwanaki ya gayamin in de baki amince da soyayya sa ba baze dawo nan kusa ba”. “Kuma kin san, yace har baba zai zo ya gaisar in ya dawo?”. “Ah masha allah wallahi meenal lamarin nan yana tafiya yarda ya kamata, yanzu yana dawowa kawai ai sai asa muku ranar aure”. “Kai ma'eeshat ke baki da magana sai ta aure, ina de so baba yasan da zuwan sa, sabida kar muyi ta abu ba izini amma maganar aure ni de ba yanzu ba sai na gama karatu na”. “Wai sai ki ta cewa karatu karatu, wallahi yarda waleed yake son ki zai barki kiyi karatu ko kunyi aure kin san yana da sauƙin kai sosai ba ruwan sa”. “eh gaskiya in de ta wanan ɓangaran ne nasan bani da matsala da waleed yace min ma, ko da munyi aure zai barni na cigaba da karatu na”. “Yauwa ko ke fa, wallahi meenal gwara muyi auran nan yanzu de kin san duniya tazo ƙarshe”. “hmm ma'eeshat kenan tom shikenan Allah uban giji ya tabbatar mana da alkhairi”. “Ameen ya rabbi meenal”. To fah, yau ma'eeshat ta kasa tsaye ta kasa zaune tun ƙarfe bakwaii na dare har zuwa 11 na dare take jiran doctor ashmal ya kirawo ta amma shiru kake ji, gaba ɗaya jikin ma'eeshat yayi sanyi dole haka ta haƙura ta kwanta bacci abun ta. MEENAL To yau tunda meenal ta tashi cikin farin ciki take over, sabida yau masoyinta zai dawo waleed. Ji take kamar kar taje school saboda zumuɗi. gashi waleed yace mata a yau ɗin zai zo yana dawowa, tunda a jirgi zai dawo. Lokacin da aka taso daga school, meenal tacewa ma'eeshat tazo suje gidan su, sabida ko da waleed yazo ba zata iya sakin jiki sosai ba. ma'eeshat ta amince da hakan dan haka direct suka wuce gidan su meenal. Bayan sun isa sunyi wanka sunci abinci, ma'eeshat taya meenal shirye-shiryen tarbar waleed tai. ma'eeshat tana ta tsokanar meenal akan bakin ta yaƙi rufuwa saboda sahibin ta waleed zai dawo, suga juna. To misalin ƙarfe biyar meenal ta gama shiryawa taff tayi jigum tana jiran zuwan waleed da yake yace mata gashi nan zuwa, yana kan hanya. ma'eeshat ɗagowa tai ta kalli meenal tare da cewa "kai meenal gaba ɗaya kin kasa samun nutsuwa tun dazu sai duba waya kike yi, mai kike dubawa ne wai?”. “hmmm wallahi ma'eeshat ba zaki gane ba, wai kar naje ya kira ban ji ba”. Wata dariya ma'eeshat tai tare da cewa “baki saba bane wallahi shi yasa, gashi dama ba wata magana kuka saba yi ba mai tsayi ido da ido ba, sai de gaisawa Koh?”. “Eh gaskiya kam bamu wani taɓa magana mai tsayi ido da ido ba”. “Hmmm gashi kuma yau takanas zai zo wajan ki Koh, hmm inye lallai za'a sha soyayya hajiya meenal”. girgiza kai meenal tai tare da cewa “kai ma'eeshat ni bana son irin haka ai sai ki ta sawa ina jin kunyar wallahi”. Ma'eeshat tana ƙoƙarin magana ringing ɗin wayar meenal ya katse ta, kallon meenal tai wanda gaban ta ya faɗi rasss, sanan tace “shine yake kiran naki?”. Jiki na rawa meenal tace “shi ne wallahi”. Murmushin ma'eeshat tai tare da cewa "to meye haka maza ji ɗaga mana" jiki na rawa meenal ta ɗauka tare da karawa a kunne tana cewa “hello salama'alaikum”. Bayan meenal tai Jim, cewa tai “tom shikenan gani nan zuwa” daga haka ta katse wayar. “Ma'eeshat kinji wai har ya ƙaraso, masha allah gaskiya yaya waleed bade ƙwaƙwalwa ba har ya gane ƙwatance da nai masa?”. Murmushin ma'eeshat tai tare da cewa “eh yana da ganewa zaki ce, ƙwanakin baya fa sai da ya tuso ƙeyata yace sai na rako shi gidan ku, lokacin kin tsane shi, Ni kuma na rako shi, amma ban gaya miki ba”. “Kai Allah sarki kice ya daɗe da zuwa gidan, amma ya kama mutuncin sa da baya zuwa sai da muka dedeta”. “wallahi kuwa meenal da wani mayan ne ai da tuni ya ishe ki da zuwa, ki tashi ki je ku gaisa sai ki shigo da shi Koh?”. Girgiza kai meenal tai tare da cewa "kai haba ma'eeshat kin san de bazan iya zuwa ba dan Allah ki raka ni mana”. “To tashi muje, bari na ɗauko mana mayafai naki”: “A'a ni de gaskiya hijab zan sa jibi fa haka zai ganni, gani masha allah, komai sai ya futo fa in nasa hijab”. hararar meenal, ma'eeshat tai tare da cewa "ke dallah ki ɗauke mayafin kisa, shi hijab ɗin da kike cewa kika sa shi ai sai anfi ganin jikin naki, saboda kwanciya zai yi a jikin ki, wallahi kisa mayafin ki sai kin fi kyau ma”. “Tom bari na ɗauko mayafin amma de ni wallahi mayafin ne in nasa sai naji kamar ana ganin jiki na”. daga haka meenal ta ɗauko musu mayafai ita da ma'eeshat ɗin. meenal rufe jikin ta tai sosai kamar wata matar aure. Itama kuwa ma'eesha yafa nata tai yafan 'yan mata sanan suka jera suka fuce abun su, zuciyar meenal sai bugawa take bum! bum! bum!. Lokacin da suka fita wata tsaleliyar mota suka gani GLK, sai wani shining take, baƙa ce motar. Meenal tsayawa tai tare da cewa “ko na koma na ɗauko wayar sai muyi mai waya muce gamu nan mun futo ko?”. “Kai meenal kina da matsala sai wani tsoro kike ji jikin ki yana rawa, dan Allah ki nutsu mu ƙarasa ki sawa kan ki jarumta in de waleed ne yana hango mu zakiga ya fito, yana da sauƙin kai sosai”. ma'eesha ko gama rufa bakin ta ba tai ba sai ga waleed ya buɗe ƙofar yasha farar shadda sai ƙyalli take. “Ah hab bana gaya miki ba kinga har ya futo ma”. ai kuwa meenal suna haɗa ido da waleed gaban ta ya ƙara faɗuwa rass, da sauri ta sunkuyar da idon ta suka cigaba da tafiya ita da ma'eeshat, meenal tana jin kamar zata nitse. A haka de har suka ƙarasa, fuska cike da fara'a ma'eeshat tace “yaya waleed ina wuni?”. murmushi waleed yayi tare da cewa "ah lafiya ƙalau ma'eeshat, ya hanya fatan ka dawo lafiya?”. “alhamdulilahi yasu mami?” “kowa lafiya ƙalau yaya Waleed” “to masha Allah”. ita meenal fuska a sunkuye tace “ina wani?”. Idanuwa waleed ya zuba mata tare da cewa “lafiya ƙalau sanun ki” meenal ba tare da ta ɗago ba tace “yauwa ya hanya?”. “alhamdulilahi na dawo lafiya, to ki ɗago mana mu gaisa” waleed ya faɗa yana ƙurawa meenal ido cike da ƙauna. Murmushi meenal tai sanan ta fara wasa da zoben hanun ta,ba tare da ta ɗago ba. “Kai meenal ki ɗago mana sai wani sunkuyar da kai kike yi haba” ma'eeshat ta faɗa tana sakin murmushi. ɗagowa meenal tai tare da ɗan gallawa ma'eeshat ɗin harara. “Ah ido ya buɗe harda hararata dafa kasa futowa ki kai sai da na rako ki amma shine kike hararata, to bari na koma ciki na barki”. Da sauri meenal ta riƙe hanun ma’eeshat tare da cewa “a'a dan Allah ki tsaya mana”. shi kuwa waleed yabi ya tsare meenal da ido kamar zai cinye ta haka yake ji. “To wallahi ki ɗago in ba haka ba zanyi tafiya ta” ma'eeshat ta faɗa tana gyara tsayuwa, ba yarda meenal ta iya dole haka ta ɗago ta saci kallan Waleed, ai kuwa suka sake 4 eyes sai kallon ta yake kamar wani tsowan maye. Ba fari bane kuma ba baƙi bane amma yana da haske kaɗan, daga gani ma asalinsa fari ne kawai ya ɗan yi duwo ne. yana da ido masha allah ga dogwan hanji, ƙasunbar nan tasa sai ƙyalli take yi, ga tarin gashin jagira da gashin ido. Kallo ɗaya zaka yiwa waleed ka sheda huto ya ƙwanta a jikin sa, fatar nan tasa sai wani glowing take yi, yana da tsayi sanan yana da faɗi, kana ganin sa de zaka son cikakyan mutum ne, kuma duk macan da ta gan shi dole ya burge ta gashi da fara'a masha allah. Ma'eeshat ce tace “to ya kamata kazo mu shiga ciki tunda naga ita ba zata iya gaya maka ba, a ciki ma sai kunfi sakewa yanzu haka kunyar futowa wajan nan take ji”. “okay ba damuwa, amma bari na buɗe miki boot ki ɗauko mata trolly ɗin ciki”. gyaɗa kai ma'eeshat tai tare da cewa “to ba komai” daga haka waleed ya danna key, ai kuwa sai ga boot ɗin kyakywar motar ya buɗe, ba ɓata lokaci ma'eeshat ta zagaya ta ɗauko trolly ɗin da kyar ta iya futo da ita. Bayan haka suka rankaya suka shiga gida, ko da suka shiga gida ma'eeshat barin meenal da waleed tai a falo domin su samu damar zantawa, ita kuma ta wuce ɗakin meenal ita da trolley ɗin. To fah waleed ya kasa tsaye ya kasa zaune jiki sai rawa yake, yana ta kallon meenal yace mata wanan yace mata wanan, duk yabi ya cika ta da surutu, ita kuma meenal ta kasa sakewa daga eh sai a'a sai murmushi, tama ƙi ɗagowa tasa shi a idanuwan ta, sai sunkuyar da kan ta take ƙasa. Haka waleed yayi ta hira har time ɗin sallah magriba yayi, aka fara kiraye-kirayan sallah, meenal ta zuba masa ruwa a buta ya tafi, masallaci, bayan ya dawo, daga masallaci a lokan baban meenal ya dawo dan haka meenal waje ta basu domin su zanta da baban nata. ayi following ɗin channel ɗina sabida ku samu damar karanta posting da zarar na ɗora............. Karku manta da like (reacted) and sharing. Mu haɗe a next page. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. _page 12 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 To waleed da baba sun tattauna sosai, kuma baban meenal ya yaba, da nutsuwa da hankali waleed dan haka yace, ya bashi dama ya ringa zuwa wajan meenal su fahimci juna, kafin nan za’ayi binci ke, shima ya bincike su sanan a kawo kuɗi a tsayar da rana”. Daga haka baba yayi sallama da waleed, meenal da ma'eeshat suka futo suka raka waleed har bakin motar sanan su kai sallama, waleed ba dan yaso ba ji yake kamar kar ya rabu da meenal. waleed yana tafiya meenal da ma'eeshat suka shiga ciki, sanan suka fara ƙoƙarin buɗe trolly ɗin tsarabar da waleed ya kawo wa meenal. ma'eeshat ce take ƙoƙarin buɗe trolly ɗin ita kuma meenal tana daga gefe ta zubawa trolly ɗin ido tana farin ciki da karamcin waleed. Lokacin da ma'eeshat ta buɗe trolly ɗin saki baki su kai suna ƙarewa kayan ciki kallo. mayamayan shafawa ne sunyi kala ashirin, sanan ga wasu turarika da boday spr kala-kala,. wata madedeciyar a kwatin gift a cike suka fara ƙoƙarin buɗewa, suna buɗewa sukaga kyakyawar sarƙa da ɗan kunan ta da abun hannun ta, da zobe kuma, kai sarƙa iya sarƙa har kala uku. Cikin mamaki, ma'eeshat ta ɗauka tare da cewa “meenal kin san wanan wana kalar sarƙoƙi ne kuwa?”. Girgiza kai meenal tai sanan tace “a'a sai kin faɗa”. “wallahi tallahi gold ne?”. Zaro ido meenal tai tare da dafe ƙirji, cikin furgici tace “gold kuma ma'eeshat na shiga uku”. “Wallahi shine ai kin san mami tana da su, ina ganin su, na gane gaba ɗaya saitin fashion ɗin nan gold ne”. “Inalillahi wallahi ma'eeshat bazan iya ba gaskiya ki ajiye masa kayan sa ni de bazan iya ƙarɓar gold ba Allah yana gani”. “Kai akan me meenal, Allah ya baki bakyau mai da hanun kyauta baya fa, wallahi ki ajiye abunki gaskiya waleed yayi ƙoƙarin kalar wanan tsaraba haka”. ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana ajiye sarƙoƙin a gefe. ɗayan gefan trolly ɗin kuwa an cika shi da saitin kayan zaƙi chocolate, sweet, biscuits, wafa, dade sauran kayan motsa baki kala-kala, tun su ma'eeshat suna iya duba kayan zakin nan har suka hakura sabida tsabar yawa. A cikin wata madedeciyar jaka, mai rubutun larabci, Quran ne sai addduma da carbi da kuma sauran hadisai da azkhar. gefe guda kuma ga 'yan sababbin kudi dari biyu-biyu har bandir biyar. jikin meenal gaba ɗaya yayi sanyi da irin tumulin kayan arziki data gani, bama ita kaɗai ba har umma ta ɗan tsorata da ganin kayan, shi kuwa baba yace a ajiye masa kayan, taci wanda zata iya ita da ma'eeshat amma sauran kar meenal tai amfani da su ta bari, sai Allah ya tabbatar in mijin ta ne sai tayi amfani da kayan a gidan sa. Daga ƙarshe de meenal tacewa ma'eeshat ta ɗibi abinda duk ranta yake so koma menene. ma'eeshat kuwa haka tace a'a ita de kayan zaƙi kawai zata iya ɗiba ragowar na meenal ne. meenal kuwa fafur tace a'a dole sai ta ɗibi sauran. ƙarshe de ma'eeshat ta ɗibi turarika biyu sai maya-mayan shafawa guda biyar sai su chocolate da kuma banɗir ɗin kuɗi guda ɗaya. meenal tayi-tayi ma'eeshat ta ƙara kayan amma tace ita haka ya ishe ta,. Ma'eeshat sai da suka gama cin abinci dare, sanan driver yazo ya ɗauki ma'eeshat ya kai ta gida. Lokacin da ma'eeshat taje gida ta bawa mami labarin kayan da waleed ya kawowa meenal cikin farin ciki. mami tayi farin ciki da hakan sosai kuma tana sake addu'a Allah ya tabbatar da auran meenal da waleed, saboda ita tana support ɗin soyayya tasu tana son suyi aure. Ma'eeshat zuciya cike da farin ciki ta koma bedroom ɗin ta tasa kayan bacci sanan ta kunna wayarta, ta haye kan gado. ma'eeshat tana kunna wifi kafin ma ta kai da shiga ig taji wayarta ta fara ringing. Lokacin da ma'eeshat taga number doctor ashmal, ajiyar zuciya ta sauke tare da furta alhamdulilahi. hannu na rawa ma'eeshat ta ɗauki wayar tare da cewa "hello assalama'alaika". Wa'allaikissalam doctor ashmal ya furta a nitse tare da cewa “ya kike?”. murmushi ma'eeshat tai sanan tace ina lafiya ƙalau doctor fatan kai ma kana cikin ƙoshin lafiya?”. “I'm very fine” doctor ashmal ya faɗa cikin daɗar muryar nan tasa mai ratsa jikin ɗan adam. masha allah abunda ma'eeshat ta iya faɗa kenan. Daga haka shiru ya ratsa wajan na wasu daƙiƙu, can doctor ashmal yace “am sorry kiyi haƙuri da kiran ki da nai, kuma gashi bani da abin cewa”. murmushi ma'eeshat tai sannan tace "ba komai ai ni sai na baka labari in kana so". “Uhmmm da gaske that is good solution, maza ki bani labari naji”. dariya ma'eeshat tai sanan tace “tom wanne kake so?”. “Ko wanne ma ina so, amma ya zamana kina yi kina yin faɗan nan naki”. “Kai har ka gane ina da faɗa kenan, kuma kaga ai nace maka ban san kai ka bugo wayar bane”. Murmushi doctor ashmal yayi tare da cewa “hmmm tun ba ranar ba na gane cewa kina da faɗa sosai, kuma ni faɗan naki ma yana burge ni”. “Kai! faɗan nawa ne yake burge ka, kai kuma gaka shiru-shiru baka son magana Koh?”. “eh ban iya yawan magana ba, yanzu ma dole ce tasa sabida kar a kashe min waya”. “Uhmm haba de kullum sai kace zan kashe ma waya, a'a bazan kashe ma ba, tunda yanzu na gane kai ne”. “Tom shikenan nagode sosai da bani lokacin ki da ki kai, amma please in ba damuwa ina so muyi magana da ke?”. Ɗan zaro ido ma'eeshat tai tare da cewa “ni?”. Jinjina kai doctor ashmal yayi kamar yana gaban ma'eeshat ɗin tare da cewa “eh mana ke”. Gyara kwanciya a hankali ma'eeshat tai tare da cewa “tom shikenan ba damuwa ina ji”. “Oh sorry ina ga ba yanzu ba, sabida yanzu haka ina motar ban isa gida ba, nayi tunanin in ban kira ki da wuri ba zaki yi bacci, jiya ma 12:00 na dare naso na kiraki, amma nasan a time ɗin kinyi bacci, aiki ne yake min yawa, but ki turomin number da kike whatsApp da ita zan faɗa miki a WhatsApp gobe sai ki duba in kin tashi”. Murmushi jin daɗi ma'eeshat tai sanan tace “okay ba damuwa, da wanan number nake Whatsapp ɗin”. “Tom shikenan in sha allah in na koma gida zan duba number sai na gaya miki” “Tom shikenan Allah ya kai ka lafiya ya tsare hanya” lumshe ido doctor yayi cikin jin daɗi yace “ameen ya rabbbi ayushat”. “No jus call me ma'eeshat” ma'eeshat ta faɗa tana fari da ido kamar doctor yana ganin ta. “ok next time a will call you ma'eeshat right?”. Ma'eeshat Jin zuciyarta tayi kamar an zuba mata ƙanƙara sabida tsabar daɗi, ji tayi duk duniya ba wanda ya iya faɗin sunan ta ma'eeshat kamar doctor, taso ta sake magana amma taji doctor ya kashe wayar sa kitt. Wani kyakywan murmushi ma'eeshat ta ringa saki tana addu'a Allah yasa taga alkhairi, a saƙon doctor. Daga haka bacci ya kwashe ma'eeshat zuciya cike fall da kewar doctor. Washe gari. Ko da ma'eeshat ta farka a makare ta tashi abun haushin shine ko sallah asubayi bata samu ba duk da kuwa ta saba samu. Dan haka da sauri ta shiga toilet tayi wanka da brush sanan ta ɗauro alwala ta futo sanan tafara gabatar da sallah. Ma'eeshat ko takan abinci bata bi ba, sabida ta makara kuma in ta tsaya cin abinci har sai a rufe get ɗin makarantar tasu ma, kuma gashi zasu biya su ɗauki meenal, dan haka a hanzarce ta shirya tasa kayan ta, sanan ta ɗauki jakarta ta fuce da sauri...... A gajiye ma'eeshat ta dawo daga school ga yunwa, dan haka ko uniform bata cire ba sai da ta cika, cikin ta taff da abinci sanan ta samu damar cire uniform. Tana cirewa ta ɗauko wayarta, ta shiga whatsApp domin hankali ta gaba ɗaya ya koma kan maganar da doctor ashmal yace zai faɗa mata, tun a makaranta take ta tunanin mai doctor ashmal zai ce mata, har Allah-allah take ta dawo gida ta duba message ɗin nasa. message sosai ne suka ringa tururuwar shigowa, dama ma'eeshat gata ita ba gwanar buɗe message ɗin muta ne bace, ma'eeshat sai dubawa take tana jiran taga message a number doctor ashmal ya shigo amma shiru. Tana cikin bincike taga saƙonni har uku sun shigo ta wata number, nan da nan jikin ta ya bata itace number doctor ashmal ɗin dan haka bata yi wata-wata ba, ta buɗe message ɗin. Bayan sallama next message ce mata yayi doctor ne, daga haka sai wani dogwan message na uku, wanda ma'eeshat ta fara karanta shi kamar haka! -Ayusha ina son na gaya miki abinda yake rai na, ni de ba yaro bane bazan tsaya ɓata lokaci na ba muna ta waya ba tare da na sanar dake mai yake tafe dani ba. Shi yasa na yanke shawarar kafin mu cigaba da waya na gaya miki dalilin da yasa nake kiran ki. komai kin san shi ana yin sa da dalili ne. Ayusha ina sonki, kuma so ba na wasa ba, ba irin na soyayya kawai ba, so na aure nake miki, ina fatan zaki amince da hakan. Amma bazan takura miki akan haka ba, zaki iya yanke wukunci duk abinda kike so, ina yi miki fatan alheri kuma sai naji daga gare ki, dan Allah ki zauna ki yanke shawara nan bada jimawa ba”. Wani uban tsalle ma'eeshat ta daka tare da cilla wayar a gefe tana furta “alhamdulilahi allah, wallahi nima ina son ka sosai, addu'a ta ta karɓu Allah maji roƙwan bayin sa. Yanzu kamar wanan kyakywan mai aji babban mutum yace yana sona, ai na gama morewa nafi ko wace mace dacewa wallahi, wayyo daɗi zai kashe ni wayyo Allah, Allah na gode ma, wallahi azumi biyu zanyi ma ba ɗaya ba”. Haka de ma'eeshat tabi tai ta sambatun jin daɗi tanayi tana godewa Allah, bayan ta gama jim tai tana tunanin wace kalar amsa zata bawa doctor ashmal, dan ita fa har ga allah tana son sa. kai amma fa ni mace ce, gaskiya ya kamata naja ajina fa, ai ita mace da jan aji aka santa, daga yace yana sonah kuma sai wani nace na amince. to amma de mai yakamata nayi?. “Bari de na rabu da message ɗin ba tare da na bashi reply ba, zuwa anjima sai nayi tunanin mai zance masa”. “A'a ma'eeshat kar fa yace kin masa rashin mutunci ma, kinga message ɗin kuma baki yi masa reply”. “A'a gaskiya ni bazan masa reply ba saboda ban san mai zance masa ba, ya kamata naja ajina gaskiya”. to haka de ma'eeshat tai ta shawara da zuciyarta daga ƙarshe de ta bigawa meenal waya, domin kiran meenal ta bata labarin farin ciki, da ya same ta. Ringing uku meenal ta ɗauka baki ɗauke da sallama,. “wa'allaikissalam ƙawata meenal wayyo daɗi kin san mai yake faruwa?”. meenal cikin zumuɗi tace “a'a ma'eeshat ina zan sani sai kin faɗa min”. Meenal albishirin ki?. cikin zumuɗi meenal tace “goro, dariya ma'eeshat tai sanan tace goron fari ko ja?”. “Ah wanan wana kalar jan raine ma'eeshat ai kin san de fari zance wa yake son jan abu kuma”. “hmm meenal doctor ashmal yace yana sona wallahi wayyo daɗi zai kashe ni meenal”. daga ɗayan ɓangaran meenal cikin farin ciki tace “haba ma'eeshat da gaske?”. “Eh mana meenal da gaske nake, ba dazu na baki labarin yace zamuyi wata magana a WhatsApp ba, ita ce yanzu na gama karantawa wayyo daɗi kashe ni, amma bari zan miki screenshot, na turo miki”. “Ah daɗi kar ya kashe ki ma'eeshat in daɗi ya kashe ki muyi yaya, gwara de ki bari mu kai ki gidan doctor kya mutu acan”. “Kai wayyo meenal na sake tuna miki wani abu ma, kin san kuma ma har da mai yace”. Cikin wani zumuɗin meenal tace “a'a ma'eeshat sai kin faɗa”. “Hmmm cewa yayi fa son aure yake min aure na zaiyi”. “ah masha allah kice da ƙarfin sa yazo ai mu to haka muke so, wallahi ma'eeshat na tayaki farin ciki ba kaɗan ba, Allah uban giji ya tabbatar muku da alkhairi”. “Ameen meenal nagode sosai kema Allah ya bar soyayyah ku da waleed” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana sharar hawayan farin ciki. “Ameen ma'eeshat lallai wai yau kece da kukan farin ciki, akan soyayyah lallai Allah yayi miki babban kamu”. “Hmmm kede bari ƙawata meenal ba zaki gane ba, Allah yana sona wallahi ya biyamin buƙatuna na alkhairi, ban taɓa tunanin doctor ashmal zai ce yana sona ba, ke ni ko bai aure ni ba, cewa yayi yana so nannan nawa da yayi wallahi ya biya ni” Dariya meenal tai tare da cewa, “a'a gwara de ayi auran, to yanzu mai kika ce mai kin amince ko yaya?”. “A'a kin san de ita mace ansan ta da jan aji to wallahi sai naja ajina tukunna”. Dariya meenal ta sake yi tare da cewa “kibi de a hankali kar a garin jan aji, ajin ya tsinke”. “ke rufamin asiri ai kaɗan zan ja ba dayawa ba, nima fa ina son kayana”. “Ah ai ko baki faɗa ba ma'eeshat nasan kina so”. To haka meenal da ma'eeshat suka sha hirar su sosai, sanan su kai sallama abun su, zuciyoyin su ce da farin ciki...... meenal tayi kukan farin ciki sosai da sosai kuma ta godewa waleed, har sai da yace mata dan Allah ta dena komai nasa nata ne. A halin yanzu duk duniya meenal ba wanda take so kamar waleed gaba ɗaya ta cirewa kan ta samun ko wana namiji sai waleed. DOCTOR Tunda ya turawa ma'eeshat saƙo bai samu sukuni a zuciyarsa ba, sai addu'a yake ta faman yi akan Allah yasa ma'eeshat ta amince da soyayyah sa, sabida shi a halin da yake in ma'eeshat tace bata amince ba wallahi bai san inda zai sa kan sa ba, sabida shi son ma'eeshat bada wasa ya shiga zuciyarsa ba. Burin doctor ashmal, ya samu ma'eeshat a matsayin mata ta amince da auran sa, duk da kuwa yasan yarinya ce sosai. Doctor ashmal yana ganin in ya auri ma'eeshat ɗin sai yafi samun nitsuwa, ko dan ya dena fama da ciwan ciki da yake, kuma ya samu keanciyar hankali da ishashiyar lafiyar da zai duba wasu. night. Sai wajan 11:00 dare doctor ya samu ya dawo gida, yana dawowa ya shiga wanka, sanan ya samu abinci yaci, sabida ya dawo da yunwa. gaban doctor ashmal sai faman faɗuwa yake akan kar ya buɗe whatsApp yaga ma'eeshat tace mai ba ta amince ba. dan haka ayyukan sa ya farayi a laptop, sai kimanin 12:00 ya kammala sanan ya ɗauko wayarsa ya buɗe zuciyarsa na dukan uku uku, sabida bai san wace amsa ma'eeshat ɗin zata bashi ba, a fili yace " Allah uban giji kasa naga alkhairi"............ kwan 2 baƙwa yimin like shi yasa jiya banyi posting ba, kuma in de zaku ringa yimin ƙauran like, ni kuma bazan gaji da fashi da yajin yi muku posting ba. Sanan ina muƙa dubun godiya da masuyi yi min like irin su, ummu sadeeq, humaira, ummi, hauwa, ummu salama babayo, aunty zee, dade sauran su. da kuma mutanan CHANNEL ɗina kuma ina yinku wallahi, ina alfahari daku, ba waii. Ayi following ɗin channel ɗina. A ringa yimin like (reacted) and sharing. Mu haɗe a next page _page 13 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 A nitse ya zubawa saƙwan da suke tururuwar shigawa ido yana faman ƙare musu kallo. Amma abunda ya bawa doctor ashmal mamaki har suka gama shigowa ba wani saƙon ma'eeshat ɗin. Message ɗin za suyi kimanin dubo goma, dan haka wayar ya ɗauka yayi surcharge ɗin sunan ma'eeshat ɗin, abun mamaki doctor gani yayi ta buɗe amma bata masa reply ba. Gaban doctor ashmal faɗuwa yayi rass, nan da nan damuwa ta luluɓe masa zuciya. “Innalillahi kar fa ace taƙi accept ɗina, to yanzu in ma'eeshat batai accepting ɗina ba ya zanyi kenan?”. Doctor ashmal ya watsawa kan sa tambayar. Doctor ashmal ji yayi kamar ya ɗaura hannuwan sa a kai ya zabga wani uban iwu, lokaci guda ya rasa mai yake mata daɗi kuma yaji duniyarta tsaya masa cak. Zuciya doctor ashmal nuna masa take kamar ma'eeshat bata amince ba. Doctor ashmal yana so ya sake tura mata wani message ɗin again, amma baze iya ba, saboda sam baya son takura, kuma baze so ya takurawa wasu ba. Doctor mutum ne mara naci kuma mai aji, baze taɓa zubar da mutuncinsa akan komai ba dan haka kawai haƙura yayi ya ajiye wayar. Kuma ya ɗauki alwashin baze sake bibiyar ma'eeshat ba in de bata bashi amsa message ɗin daya tura mata ta whatsApp ba shi a ganin sa kamar wulaƙanci ne, ko kuma takura mata zaiyi....... Doctor asmal ya shiga damuwa sosai a ƴan kwanakin nan, ko baccin kirki baya iya yi, ga yawan tunani da damuwa. dole yake iya aro jarumtarsa sanan yayi aiki domin tai makwan al'umma yau kimanin 3 days kenan yana jiran shigowar saƙon ma'eeshat amma shiru kake ji. Gaba ɗaya yabi ya canza ko wasa ya dena yi da yesmeen duk dan saboda ma'eeshat, kullum cikin tunanin ta yake, lokaci guda har ya faɗa yayi zuru-zuru abun tausayi, gashi shi dama bai taɓa faɗawa soyayyah bare yasan yarda take sai akan ma'eeshat, yasan meye soyayyar ma..... MA'EESHAT To itama ɓangaran ma'eeshat ɗin ta shiga damuwa sosai, tana ta faman jiran kiran doctor ashmal amma ji kake shiru har 3 days. Gaba ɗaya ta shiga damuwa ko a makarantar bata iya wani mai da hankali. Sai ma'eeshat ta shiga message ɗin doctor ashmal zata bashi amsa sai taji ba zata iya ba gwara ta bari ya sake nemanta da kan sa, dan ma'eeshat tai ta sake jan ajin ta. Ma'eeshat ta tafi dogwan tunani gaba ɗaya class ɗin sun fuce break, daga ita sai meenal da itama tana gefe tana sakin murmushi saboda tana tunawa da masoyin ta waleed wanda suke shan soyayyah, yayi yayi ya sake zuwa amma meenal tace a'a ya bari ita kunya take ji, sai zai koma sai yazo suyi sallama. Meenal bayan ta dawo daga duniyar tunanin data tafi, juyowa tai ta kalli ma'eeshat da itama ta tafi tata duniyar tunanin. Hannu meenal tasa ta zo zunguro ma'eeshat ɗin. Firgigit ma'eeshat ta dawo daga dogwan nazarin data tafi. “wai ma'eeshat mai yake damun ki jiya da yau gaba ɗaya naga, kin canza?”. “Hmmm meenal ban so na gaya miki ba wallahi bana so na ringa saki cikin damuwa”. “Haba ma'eeshat duk abinda ya same ki dole nima ya dame ni, ki gayamin mai yake damun ki?” meenal ta faɗa hankali a ɗan tashe. Ajiyar zuciya ma'eeshat tai sanan tace “meenal kin san matsalata ba zata wuce doctor ba”. “Yah ilahai, ni kuwa kinga nama sha'afa, ƙwana biyu bana tambayar ki ya kuka ƙare da shi ba, yanzu de mai ya faru?”. “Hmmmmmm meenal inaga de da gaske garin jan aji, ajina ya tsinke a wajan doctor”. zaro Ido meenal tai tare da dafa ƙirji tana cewa "subanallahi ma'eeshat mai ya faru kuma". Cikin murya mai nuna tsantsar damuwa ma'eeshat tace "wallahi meenal akan message ɗin nan ne, wanda nace miki bazan bashi reply ba sai naja masa aji, to har yau kimanin 4 days bai sake nema na ba, baya min waya bare massage kuma bai sake yimin magana ta whatsApp ba”. Ajiyar zuciya meenal ta sauke tare da cewa "kai har kin ɗaga min hankali na wallahi ma'eeshat. yanzu akan wanan kike ɗaga hankali ki, to ki maza ki ƙwantar da hankali ki in sha allah bai hakura da ke ba yana nan yana son ki. Ai in de da gaske doctor yake kin burge shi kuma son gaskiya yake miki baze taɓa hakura da ke ba akan ɗan wanan abun”. tarar nunfashi meenal ma'eeshat tai tare da cewa, "to meenal ba gashi ya dena nema na ba in ba haƙura yayi da ni ba, kuma da yana so nah, ai baze taɓa yimin hakan ba”. “A'a ma'eeshat kar kice haka, baki son mene so ba ne, ina tunanin kawai shi irin mutanan nan ne wanda suka san tsari basu da takura, ai ke da ganin sa ma kin san yana da nutsuwa, to kin san a rayuwa da akwai wanda suke da lissafi basa son tusa kai in da ba'a buƙatar su, inaga ya baki dama ne yana jira yaji ta bakin ki baya son takura miki”. “To yanzu meenal ya zanyi bayan nasa ya riga da yaga na buɗe message ɗin daya turomin kuma ban mai reply ba, yanzu kawai sai na koma nai mai reply ai abun ba aji kuma gani zaiyi na damu da share ni da yayi”. Murmushi meenal tai, sanan tace "kai ma'eeshat kin cika rigima tunda ba zaki iya haka ba bari na baki wata shawara”. “Yauwa meenal wallahi shi yasa nake ƙara ƙaunar ki, inajin ki bani shawarar nan”. “Shawarar da zan baki kawai ki kira shi, amma ringing ɗaya zatai sai ki katse, nasan dole zai biyo ki”. yamutsa fuska tai ma'eeshat sanan tace “haba shima wanan ɗin ai duk zubar da mutuncin ne, sai yace na damu da shi shi yasa na kirawo shi”. “A'a daɗi na dake bakyacin ribar zance, ba sai ki tambaye ni ya za a ƙare ba”. “tom shikenan naji ya za a ƙare?” ma'eeshat ta tambaya tana zubawa meenal idanuwan nan nata masu nuna tsantsar damuwa. “Yauwa bayan ya kirawo ki sai kice, on mistake kika kirawo shi baki san number sa kika kirawo ba yayi haƙur. To nasan daga nan zai tambaye ki akan message ɗin daya turo miki, to nide ba ruwana kika sake ja masa ajin nan naki”. rungume meenal ma'eeshat tayi cikin farin ciki tace “eh wallahi kin kawo shawara mai kyau ƙawata ƴar uwata, ina ƙaunar ki Allah ya barmu tare ina son ki”. Itama meenal cikin jin daɗi tace nima ina ƙaunar ki ma'eeshat, a halin yanzu kece sanadin farin ciki soyayyah ta, saboda ke kika takuramin akan na bawa waleed lokaci gashi har na fara son sa, kin min zaɓi na gari nagode ma'eeshat”. “Ba komai meenal ai ke 'yar uwa ce a waje na kuma aminiya duk abun da nai miki, kamar kai na nayiwa”. ma'eeshat ta faɗi hakan tana sakin meenal. Sanan ta ruƙo hanun ta tace “tashi mu fita break ni saboda tsabar tashin hankali ban san sanda aka fita break ɗin ba”. Dariya meenal tai sanan tace “kai ma'eeshat tawa, in kika fara zurfi a soyayyar doctor ban san yarda zaki zare ba kuwa”. “Ke ai nama yi zurfi yanzu ma, nifa ko a yau aka ce za'a ɗaura min aure da doctor a kai ni gidan sa wallahi zan yarda”....... Ma'eeshat bayan ta koma gida taci abinci kuma tai sallah misalin ƙarfe 3 ta ɗauki wayarta ta fara lalubo number doctor domin tayi yarda meenal ta bata shawara. Koda ma'eeshat ta lalubo number zuba mata ido tai kawai tama kasa dannawa. Tana ta tunanin taya zama ta fara kiran doctor ɗin, wani iri ta ringa ji kamar karta kirawo, amma ba yarda ta iya dole ta rufe ido gabanta yana faduwa ta fara kira. ringing ɗaya tai kamar yarda meenal ta bata shawara sanan ta katse wayar. zubawa wayar ido tai tana jiran shigowar kiran doctor din. Abu kamar wasa kusan 5 minutes ma'eeshat tana jira doctor ya bigo mata amma shiru kake Ji. nan da nan ma'eeshat ta shiga damuwa hankali ya sake tashi tana tunanin kar de ace doctor yayi fushi da ita gaba ɗaya ma. To ma'eeshat abu kamar wasa, har karfe biyar na yamma tana jiran shigowa kiran doctor ashmal amma shiru kake ji. gaba ɗaya ji tai duniyar tai mata zafi, tana addu'a allah yasa doctor ba haƙura yayi da ita ba...... DOCTOR ASHMAL. Agajiye ya futo daga ɗakin tiyata lokacin sai kiraye-kirayan sallah magriba ake. Dan haka yana wanke hanun sa ya ɗaura alwala ya tafi masallaci hospital ɗin domin gabatar da sallah. Yana idarwa ya koma office ɗin sa ya ɗibi wayoyinsa da mukullin motarsa, sanan ya futo a hanzarce dan yau ya gaji sosai baze iya kai ko isha'i a hospital ba. Yana shiga cikin lafiyayyar motarsa ya rufe murfin sanan ya saƙala belt,. a hankula ya kunna motar tasa, sanan ya ajiye wayoyin nasa a ma'ajin su na cikin motar. adede lokacin message ya shigo, dan haka wayar da kan ta ta buɗe ta kawo haske. Kamar ance doctor ya kalli wayar, ai kuwa gani yayi sunan ma'eeshat ya bayyana. A fili yace “kai kenan kira na tai?”. Da sauri doctor ashmal ya ɗauki wayar ya bude ya shiga cikin call. Doctor gani yayi tun wajan uku da ƴan minutes ma'eeshat tai masa kiran, doctor ji yayi wani farin ciki ya kama shi bai yi wata-wata ba ya dannawa ma'eeshat kira. Ɓangaran ma'eeshat tana kan dadduma tayi sallah magriba tayi jigum tana tunanin doctor ashmal taji wayarta tana ringing. a hankula ma'eeshat ta mike ta fara tafiya, dan tasa abbas ne yake kiran ta. Ma'eeshat tana ƙarasawa ta ɗauki wayar tare da zuba mata ido, tana ganin sunan doctor gaban ta yafaɗi rass, hannu na rawa ta ɗauka dan wayar tana gab da tsinkewa. “Assalama'alaika” ma'eeshat ta faɗa gaban ta yana faɗuwa rass. “Wa'allaikissalam 'yan mata ya kike?”. murmushi ma'eeshat tai tare da cewa “alhamdulilah”. “Masha allah kiyi haƙuri dazu kin kira ni bana kusa da wayar ina busy sosai sai yanzu na gani”. “Ah ba komai wallahi dazun ma mistake nai na kirawo ka bama kai zan kirawo ba, nanyi tunanin karan ya shigo ba”. Jim doctor ashmal yayi lokacin guda farin cikin da yake kan fuskarsa ya ɗauke. ma'eeshat kuwa da taji shirun yayi yawa cewa tai “hello?”. Doctor ashmal amsa ya bata da cewa "kenan ni ba za ki iya nema na ba sai kuskure to shikenan nagode”. “No ba haka nake nufi ba doctor” jinjina kai doctor yayi tare da cewa “tom yanzu de ina motar driving nake, zan koma gida, ina koma zamuyi waya.” “Tom shikenan Allah ya ya tsare hanya ya kai ka gida lafiya sai anjima take care” murmushi doctor yayi tare “thank you dear take care too” daga haka doctor ashmal ya katse wayar. Doctor ji yayi zuciyarsa tai masa sanyi kuma damuwar da take ciki akan ma'eeshat ɗin ta ɗan ragu kaɗan. Dan haka a hazarce yabar hospital ɗin ya kama hanyar gida. Sai da doctor ya tsaya a masallaci yayi Sallah isha'i sanan ya koma gida. yana komawa ya shiga toilet yayi wanka sanan ya futo suka ci abinci shi da yesmeen suna ci suna hirar su cike da kulawa, bayan ya gama sallama yayiwa yesmeen sanan ya wuce bedroom ɗinsa. Doctor ashmal sauri yake ya kirawo ma'eeshat sabida suyi magana, baya so ya tsaya westing ɗin time kuma ma'eeshat ta tafi bacci. yana ƙarasawa ya kashe globe ɗin bedroom ɗin nasa ya kunna na bacci, sanan ya haye kan bed ya shiga blanket. A lokacin ƙarfe tara da 'yan mintina, dan haka doctor yana ɗaukar wayar tasa bai yi wata-wata ba ya shiga call ya dannawa ma'eeshat kira. Ringing uku wayar tai sannan ma'eeshat tai picking baki ɗauke da sallama. Lumshe ido doctor yayi dan muryar ma'eeshat ɗin har ƙwaƙwalwar sa yaji ta, sanan ya amsa mata sallamar tare da cewa “kin ji ne sai yanzu ko fatan ban tashe ki daga bacci ba”. “A'a ban fara ba assignment nake yi ne shi yasa ban kwanta ba”. “oh sorry na katse miki assignment ko zan bari sai kin gama ne?”. “A'a na riga dana gama, ai assignment ɗin ba wani walaha sosai” ma'eeshat ta faɗa tana shigewa cikin blanket saboda sanyi da take ji. “Oh masha allah haka nake so naji kina cewa, ki ta mai da hankali a school”. murmushi ma'eeshat tai tare da cewa “tom shikenan in sha allah zan cigaba da mai da hankali”. “yauwa to ya makarantar?”. “Alhamdulilahi komai normal”. “Masha allah haka ake so” doctor ya faɗa yana sauke ajiyar zuciya. Daga haka shiru ne ya ratsa wajan, doctor yayi shiru ma'eeshat tayi shiru. Can dai doctor yayi gyaran murya tare da cewa "fatan dai kinga saƙon dana turo miki ta chat Koh?”. Jim ma'eesha tai kamar baza tai magana ba, sai daga ƙarshe de tace “eh nagani”. Jinjina kai doctor yayi sanan yace “masha allah to mai kika yanke akai kenan?”. Ajiyar zuciya ma'eeshat itama tai sanan tace "ka bari tukkuna sai nayi shawara”. “No ma'eesha bazan iya jure wanan shawarar taki ba, bana so na takura miki kuma bana so na takurawa rayuwar ki, sanan na ɓatawa kai na lokaci, duk lokacin da kika ɗuba baki min reply ba yaci ace kinyi shawara, in kuma kina da wanda kike so, karki damu ki gayamin zan fahimce ki”. doctor ashmal a nitse yake faɗin hakan. Shiru ma'eeshat tai ba tare da tace koamai ba. “yanzu de ina ji ki, yanzu nake so maganar nan ta ƙare just tell me do you accepting me or not ma'eeshat?”. shiru ma'eeshat ba ba tare da ta bawa doctor amsa ba. “yanzu fa ma'eeshat ba time ɗin wasa bane, ina sonki sosai tsakani da Allah nake son ki, bana so ki cigaba da wahalar min da zuciya ta, please in bakya so na ki gayamin, in sha allah ko ta halin yayane zan rabu dake bazan sake neman ki ba. Ni ba mutum bane mai naci, ban taba tunanin zan iya naci kamar haka ba, kin san shi so yana canza mutum, in na sake tambayar ki, ki kai min shiru ma'eeshat hakan ya nuna min baza ki amince dani ba kuma ban miki ba, ko kuma de kina da wanda kike so”. Ma'eeshat ji tayi gaban ta ya faɗi nan da nan gumi ya keto mata, dan tasan in bata amince da doctor yanzun nan ba to tabbas zata rasa shi kuwa na har abada. Muryar doctor ma'eeshat taji ta sake ratsa kunnuwanta, cikin raunaniyar murya doctor ya sake cewa "ma'eeshat kin amince da soyayyar da nake miki ki bani amsa?”. Baki na rawa ma'eeshat tace “eh doctor na amince da kai a matsayin masoyi na”. daga haka ma'eeshat ta katse wayar cikin tsananin jin kunya ta lulluɓe fuskar ta a cikin blanket, zuciya cike fall da farin ciki......... Ina godiya sosai masoyana masuyi min addu'a da bani da lafiya kuma yanzu na samu sauƙi ina godiya da addu'o'in ku gare ni, yanzu na samu sauƙi sosai in sha allah zan cigaba da yi muku posting. ƙwana biyu bani da lafiya ne shi yasa kuka jini shiru. A rigan yimin like (reacted) Karku manta da share da kuma fallowing ɗin channel ɗina dan samu posting da zarar na ɗora. My number 09162226240 _page 14 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ma'eeshat ji tai wayarta ta sake karadewa da ringing tana dubawa taga sunan doctor. wata kunya ce ta sake rufe ta, ji tai bazata iya ɗaga wayar ba saboda tsabar kunya da take ji. itama bata taɓa tunanin tana da kunya kamar haka ba sai yau. Doctor ashmal sai da yayiwa ma'eeshat kira 2 amma taƙi ɗauka daga ƙarshe de dole ya haƙura ya rabu da ita. Ma'eeshat kuwa zuciyarta cike fall da farin ciki ta kunna data ta hau online domin bawa meenal labari ta WhatsApp. saboda yanzu itama meenal ta fara chat ɗin dare tanan suke shan soyayya su, ita da waleed. Ba ɓata lokaci ma'eeshat ta lalubo chat ɗin su da meenal domin bata labari. voice ta danna tana bata labarin abunda ya faru tsakanin ta da doctor ashmal. Ma'eesha tana cikin voice note ɗin sai ga kiran doctor ashmal ya shigo, ya kirata voice call. murmushi ma'eeshat ta saki a file tace "oh ni ma'eeshat na ruɗa babban likitan nan wai, duk ajin ka haka” ta ƙarasa maganar tana sakin siririyar dariya. Har wayar ta kusan tsinkewa ma'eeshat taji ba zata iya jurewa ba, dan haka a hankali ta ɗaga wayar tare da karata a kunna tana miƙewa zaune. wata nannauyar ajiyar zuciya doctor ashmal ya sauke tare da cewa "yauwa ko ke fa, muna magana kuma kika katse min waya”. A hankali ma'eeshat ta lumshe ido ta buɗe sanan ta kashe murya ta fara cewa "tom ai or ready mun gama magana koh?". “Ah haba waya gaya miki?”. Gani nai ai na riga dana baka amsar da kake so kaji to me ya rage?”. “Naji muryar ki mana ma'eeshat muyi mag”na ban gaji da ke ba ina so muyi hira”. Shiru ma'eeshat tai ba tare da tace komai ba. “Ok ko bakya so muyi magana ne, ko kuma bacci kike so kiyi?”. A hankali ma'eeshat tace “a'a”. “in kina so ki kwanta ko bakya buƙatar muyi waya ki gayamin bana son na takura miki fa”. “A'a doctor ba komai ina sauraran ka” ma'eeshat ta faɗi hakan zuciya cike da ƙaunar doctor. Sauke ajiyar zuciya doctor ya sake yi, sanan yace "naji daɗi da kika amince dani a matsayin masoyin ki, kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin na faranta miki zan zama masoyi a gare ki wanda ba zaki taɓa ladamar zaɓan sa ba har abada”. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace "nagode sosai doctor in sha Allah nima zan faranta ma, kuma zan guji duk abinda baka so, yaushe zaka zo mu haɗu mu sake ganin juna”. Dariya doctor yayi mai sauti wanda har sai da ma'eeshat taji ta. bayan ya tsagaita cikin daɗaɗar muryarsa yace “duk sanda kike so.” Haɗe rai ma'eeshat tai kamar doctor yana ganin ta sanan tace “bana so kazo ɗin”. Ɗan zaro ido doctor yayi kamar ma'eeshat tana kallon sa, sanan ya ɗage girar sa yana cewa "subanallahi saboda mai kika ce kin fasa kuma?” “Eh bana so tunda abun dariya ya baka”. Murmushi doctor yayi mara sauti a zuciyarsa yace “oh ni ashmal na fara shan yarinta” a fili kuma cewa yayi “a'a ai ba'a haka ba sai ki tambaye ni dalilina nayin dariyar ba kafin ki yanke min wanan zazzafan hukuncin naki mai ɗaga hankali”. Taɓe baki ma'eeshat tai sanan tace “to ina jin ka, gayamin dalilinka in bai min ba kuma bazan janye maganar ba”. “sorry eeshat zama ki janye”. lumshe ido ma'eeshat tai har cikin zuciyarta taji daɗin sunan da doctor ya faɗa mata, eeshat, sai taji sunan ya ƙara mata daɗi da ya cire ma ɗin. Ɗayan ɓangaran doctor cewa yayi “ni abinda yasa kika ji nai dariya, nasan kinyi ƙanƙanta sosai taya za kice nazo wajan ki zance ai nasan ba zaka a barki a gidan ku ba ko kina zancan ne?”. Girgiza kai ma'eeshat tai tare da cewa “a'a ba'a bari na amma kai ma ai ba zance zaka zo muyi ba gaisawa nace fa muga juna”. “hmmm ma'eeshat kenan zan zo amma abba zan zo na fara gaidawa tukunna in ya ban izini sai na ringa zuwa wajanki”. “Tom shikenan Allah ya kawo ka”. “ameen eeshat ajin ki nawa a school?”. “saura 2 month fa muyi canday dan har mun fara shirye-shiryen zana jarabawar waec”. “Ah masha Allah kice eeshat ɗin tawa babba ce sosai, har kin kusan canday kenan” “doctor ya faɗi hakan cikin tsokana”. ita kuwa ma'eeshat daɗi taji, a fili tace “eh mana nibabbace”. Doctor dariyar sa ya danne sanan yace “ok wace school zaki fara zuwa in kinyi canday nasan ai ba za'ai miki aure yanzu ba” doctor ya faɗa cikin son jin gaskiya zance. yana so ya bigi cikin ma'eeshat saboda yaji za'a iya aura masa ita bayan tayi canday a gidan su. “A'a ni fa bana son zuwa school na de fisan auran” ma'eeshat ta bawa doctor amsa. dariya ce ta sake ƙwacewa doctor dan haka da sauri yasa wayar tasa a mute domin kar ma'eeshat taji dariyar da yake, a lokacin ya sake tabbatarwa tabbas ma'eeshat yarinya ce sosai kuma bata da wani wayo sai de tsiwa. Muryar ma'eeshat doctor yaji ta sake ratsa kunnan sa tana cewa "hello naji kayi shiru ko baka ji na ne?”. da sauri doctor ya cire wayar daga mute sanan yace “yauwa sai yanzu na fara jinki, da bana jin ki, kuma gashi na tambaye ki?”. Ma'eesha kuwa ko a jikinta ta sake maimaitawa doctor cewa "A'a nifa nace ma aure nake so ba school ba, kuma kaga abinda nake so shi abba da mami za suyi min”. Jinjina kai doctor yayi dan har zuciyar sa yaji daɗi hakan, saboda shi auran ma'eeshat yake so yayi gadan-gadan, baya son jira saboda a matse yake, in ma tana so sai tayi karatun a gidan sa, bayan ya aure ta. A fili kuwa cewa yayi “gaskiya de ya kamata ai miki abinda kike so eeshat ɗina”. ma'eeshat bawa doctor ashmal amsa tai da cewa “yauwa” ta faɗa cikin farin ciki. “Shekarar ki nawa to?” doctor ya watsawa ma'eeshat tambayar. Ma'eeshat kuwa ba tare da wani dogwan nazari ba tace “17 years amma bayan nayi canday zan cika 18”. Mamaki doctor yayi da jin shekarun ma'eeshat ɗin duk da kuwa dama baya mata wani kallon babba amma yayi tunanin zata ɗan fi haka. Kuma yayi farin cikin da shekarun nata basu da yawa saboda dama shi can baya son babba mace, wanda ko sunyi aure ba zata ji maganar sa ba, amma yanzu yasan zai ƙarasa rainon ma'eeshat ne zai ɗorata akan duk abinda yake so. A filo doctor kuma cewa yayi “lallai babba ce ke ai nayi tunanin baki kai haka ba”. dariyar jin daɗi ma'eeshat tai tare da cewa “kai a hakan duk girmana baka ga nafi shekarun nawa girma ba?”. “A'a ni ban gani ba nida bana ganin ki ma”. “A'a to ba ka ganni ba sau uku ma kuma har gidan mu kazo fa mu kai magana”. Girgiza kai doctor yayi tare da cewa “ai ni ban kalle ki sosai ba ban kula da girman ki ba” doctor ya faɗi hakan ta sigar tsokana da ɓoyewa ma'eeshat gaskiya zance. “Tom shikenan kafin kazo mu sake haɗuwa zan turoma hotana ka ganni sosai”. “tom shikenan eeshat yaushe kenan za'a turomin?”. “a'a kar ka damu muna gama wayar zan turama amma nima ka turamin naka”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “a'a ni ai bana hoto babba ne”. “A'a kawai baka son ka turomin ne, wanda na gani a wayar ka fa?”. cikin mamaki doctor yace “what a waya ta kuma yaushe kika gani?”. Zaro ido ma'eeshat tai tare da toshe baki da hannu dan shaff ta manta, ta saki baki tana tonawa kan ta asiri. ji tai doctor yace “eeshat ina jin ki yaushe ki ka gani?”. Girgiza kai ma'eeshat tai tare da cewa “ban gani ba wasa nake yi”. “No ki gayamin gaskiya” doctor ya faɗa hakan cikin son jin gaskiyar zancan. “A'a gaskiya fa na faɗa maka kaga bacci zanyi bari na turama hoton kasan gobe zani school kar na makara bye.” Kafin ma doctor yayi wata maganar ma'eeshat ta katse wayar. Murmushi doctor ya saki, a zuciyar sa yace “ma'eeshat kenan wai ni zaki yiwa wayo” dama doctor ashmal tun ranar daya ƙarɓo wayar sa bayan yayi mata caji, yana kunnawa ya gane an shiga gallery amma sai bai kawo komai ba yayi tunanin duk afnan ce ta shiga ashe ma'eeshat ɗin ce. Doctor ashmal yana cikin tunanin nan yaji ƙarar shigowar message ta chat ɗin su da ma'eeshat da yake yana cikin chat ɗin nasu, bai fita ba. Da sauri ya dawo daga tunanin da yake, sanan yasa hannu ya dauki wayar tasa domin dubawa. kamar yarda ma'eeshat tai wa doctor alƙawari haka ta tura masa hotunan nata har guda 4. Doctor kuwa a hankali ya fara buɗewa picturs ɗin, bayan ya gama buɗewa ɗaya bayan ɗaya ya fara bi yana kallo. ma'eesha tayiwa doctor kyau sosai a hotunan dan haka zuba mata ido yayi yana ƙare mata kallon ƙurillah zuciya cike da soyayar ta. Doctor ashmal ya daɗe yana kallon hoton ma'eeshat komai yayi masa na jikin ta, kamar yarda yake son ƴar mace, sai da doctor yaji ciwan cikin sa ya tashi, sanan ya haƙura da kallon hoton. Dama sha’awar doctor take tashi haka nan bare yayi tozali da kyakywar surar ma'eeshat gata da jiki masha allah dole hankalin doctor ya sake tashi. Haka doctor ashmal yayi ta fama da ciwo, zuciya cike fall da soyayyar ma'eeshat ɗin. Daran ranar de ciwo yayiwa doctor ashmal worst da ƙyar ya iya bacci....... Ita kuwa ma'eeshat daran ranar farin ciki kamar ya kashe ta, soyayyar doctor ta sake nunkuwa a zuciyar ta, ta daɗe tana tunanin doctor sanan bacci itama ya ɗauke ta. MEENAL To ɓangaran meenal itama tana nan tana shan soyayyar ta ita da waleed, dan yanzu waleed yayi zuwa na biyu ma wajan ta. Sanan yaso ya kawo kuɗin auran ta kafin ya koma abuja wajan aiki, amma baba yace a'a ya bari zuwa 2 moths in suyi canday sannan sai azo ayi maganar auran masu. Yau ta kassance ranar da waleed zai zo wajan meenal suyi sallama sabida washe gari da sassafe zai bi plane na safe ya koma abuja. Tun bayan sallah magriba meenal ta zauna a bakin madede cin merro ɗin ta tana ɗan kwalliya. duk da ba wata ƙwalliya tai ba amma tayi kyau sosai abunta, zuciyar nan tata cike da zumuɗin ganin waleed. Meenal tana gama shiryawa taji ringing ɗin wayarta, duk da meenal bata duba ba, jikin ta ya bata waleed ne ya iso, dan haka mayafinta ta ɗauko wadatacce ta rufe jikin ta ko ta ina sanan ta ɗauki wayar, tana dubawa kuwa kamar yarda zai tazon haka ta gani waleed ɗin ne. Kafin ta kai da ɗagawa ma wayar ta tsinke dan haka, takalmin ta tasa sanan ta leƙa ɗakin umma da baba ta sanar da su. bayan ta sanar da su ba ɓata lokaci ta kama hanyar fita daga gidan. Tana ƙarasawa soron gidan su kafin ma ta fita taji wayarta ta sake sabon wani ringing ɗin. Bayan ta ɗauka karawa tai a kunnan ta sanan tace "hello assalama'alaika". “Wa'allaikissalam babe gani na ƙaraso” murmushi meenal tai sanan tace “to nima gani na futo, daga haka ta katse wayar ta fara takawa a sannu”. A tsaye bakin mota meenal ta hangi waleed yasha blue black ɗin yadi, dogayan kaya, sai hula itama mai launin kayan nasa, duk da unguwar tasu ba haske tun daga nesa meenal taga agogwan waleed yana ƙyalli mai kashe ido. Meenal kuwa a zuciyarta ta raya tabbas agogon waleed ko ba'a faɗa ba tasan mai tsada ne sosai. tun daga nesa waleed yake bin meenal da ido kamar zai lashe ta, ita kuwa meenal kamar kullum sai wani sunkuyar da kai take. Tana ƙarasawa ta sake rausayar da kai cikin daddaɗar muryar nan tata mai sanyi tace “ina wuni”. Waleed daya shagala da kallon meenal murmushi yayi tare da cewa “lafiya ƙalau meenal tawa kinga yarda kika sake wani kyau abin ki”. Wasa meenal ta farayi da hanun ta sanan tace “hmm kullum ai kai baka gajiya da yabo na, shi yasa bazan gane nayi kyan ba ko kuwa”. Girgiza kai waleed yayi sanan tace "hmmm meenal ai ke mai kyau ce, dan haka a ko da yaushe kinayin kyau a kowana hali kuma a duk yarda kike". Jinjina kai meenal tai ba tare da ta dago kanta ba tace "tom shikenan nagode sosai". no meenal baƙya buƙatar godiya saboda yaban gwani ya zama dole, kin ga kuwa nima dole na yabi gwana ta Koh?. murmushi meenal tai ba tare da tace komai ba. “Yanzu dai kizo mu shiga cikin mota ki zauna bana son kina tsayuwa kuma gashi garin naji shi da ɗan sanyi Koh?”. Da sauri meenal ta girgiza kai sanan tace “a'a ka bari nan ɗin ma ya isa”. “Hmmm ai nasan zaki ce a'a tun kafin na faɗa amma ki daure mana please sallama fa zamuyi, yanzu in na tafi bazan dawo ba har sai lokacin candy ɗin ku yayi”. Ajiyar zuciya meenal ta sauke sanan tace "Tom shikenan Allah ya kai mu lokacin da rai da lafiya”. “Ameen ya rabbi babe dina dan Allah ki shiga ki zauna bana son mu ringa jayayya ban sanki da haka ba”. Ba yarda meenal ta iya dole haka ta zagaya, shi kuma waleed yana biye da ita ta baya yana ƙare mata kallo cike da ƙauna. bayan sun ƙarasa waleed shan gaban meenal yayi ya buɗe mata murfin motar na gaba sanan ta shiga, bayan ta shiga tace mai ya bar murfin motar a bude. Kamar yarda meenal tace haka waleed yayi bai musa ba, shima ya zagaya ya shiga mazaunin driver. bayan ya shiga A.C ya kashe sanan ya kunna futulun motar domin ya ringa kallon meenal. Tunda suka shiga ba wanda yacewa kowa ƙala meenal ta sunkuyar da kai, shi kuma waleed yana ƙare mata kallo. Meenal kuwa ta tsargu sosai dan haka a hankali ta dago dan jikin ta ya bata waleed kallon ta yake. Ai kuwa tana ɗagowa suka haɗa ido da waleed kamar yarda tai tunani yana ƙare mata kallo. meenal cikin sanyayiyar muryar nan ta ta mara ƙara tace, "dan Allah ka dena kallo na haka bana son ana kallo na sosai". Haba meenal ki barni na kalli kyakyawar halittar da Allah ya zuba, in ban kalle ki ba wa zan kalla kar ki manta fa gobe zanyi tafiya ki bari mana muyi sallama gimbiya ta......... Dan Allah ku daure a riga share. ku ringa like (reacted). Ayi fallowing channel domin samun posting da zarar na ɗora. My number 09162226240. _page 15 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Meenal ba tare da ta ɗago ba tacewa waleed "a hakan zamuyi sallamar kana ta kallo na kenan?". “To meenal aya zamuyi, tunda ba zaki iya magana ba sai na kalle ki naji daɗi, ke daga eh sai a'a fa kike cemin”. Murmushi meenal tai ba tare da tace komai ba. waleed kuwa sake zuba mata kyawawan idanuwa yayi tare da cewa “au ba zaki maganar ba kenan?”. “Hmmm ni bani da abin cewa” meenal ta faɗa tana wasa ya yatsun hannunta. “meenal kenan ba zaki gane yarda nake son ki bane, komai kika ce burge ni kike ko baki magana ba burgeni kike, in kinyi magana burgeni kike, ki kai murmushi kuwa ƙarasa son ki nake, dan Allah meenal karki rabu dani”. Da sauri meenal ta ɗago tare da cewa “kai haba waleed wanan wace kalar magana ce akan me zan rabu da kai”. “hmmm meenal kina da kyau da diri da ko wana ɗa namiji ya ganki dole ya so ki, to yanzu in na tafi kar wani ya ganki ya nane miki, kice shi zaki aura ba ni ba”. Girgiza kai meenal tai sanan tace "a'a ni ka dena cewa haka kasan ba zan taɓa yaudarar ka ba, sanan kuma bazan so wani ba bayan ka". “Alhamdulilahi meenal Allah ya mallaka min ke in sha allah zan ƙare rayuwata a mai nuna miki so da kulawa”. Murmushi meenal tai a zuciyar ta tace "Ameen". Cikin mamaki waleed yace “babe kice ameen mana ko bakya so”. cikin jin kunya meenal tace “ai na faɗa a zuciya”. girgiza kai waleed yayi sanan yace “no ni a fili nake so ki faɗa”. Sunkuyar da kai meenal tai sanan tace "a'a bazan iya ba, in kana so dole na faɗa kaji, to ka bari sai na koma gida". kai meenal kin cika kunya sosai kuma hakan yana burge ni dan nayi sa'ar mata wallahi”. Murmushi meenal tai ba tare da tace komai ba. To haka waleed ya ringa jan meenal da hira har ta ɗan saki jiki tana bashi amsa bade wani sosai ba. Sun jima sosai suna hira har sai da meenal tace zaka koma gida saboda kar ai mata faɗa sannan waleed ya yarda su kai sallama. Waleed kamar maye sam baya so ya rabu da meenal da ƙyar ya barta ta fita, ƙarshe ma sai da ya raka ta har ƙofar soran gidan su, nan ma bayan ya rako ta bai rabu da ita ba har sai da baba ya leƙo kiran ta sanan ya tafi, zuciyarsa cike fall da kewa da soyayyar meenal. DOCTOR To soyayyah gaggaruma ta shiga tsakanin doctor ashmal da ma'eeshat. Kullun doctor in bai ji muryar ma'eeshat ba baya samun sukuni, itama in bata ji tasa ba batajin daɗi. Yanzu ma'eeshat da wuri take bacci tana sallah magriba, shi kuma doctor in ya dawo gida wajan 12:00 sai ya bugo mata waya. To in doctor ya tashi ma'eeshat da yake ta dan yi bacci sai susha wayar su, har sai su kai 1 dare suna waya. sam doctor baya son wayar daran nan, sai yaji kamar hakan da yake bai dace ba, amma ba yarda zai iya hakan ya zamar masa jiki in ba suyi wayar ba baya iya bacci, shi yasa ma suka yanke shawarar ta ringa bacci da wuri kafin suyi wayar 12:00am saboda school. Shaƙuwa sosai doctor da ma'eeshat su kai, duk da de gaɓuwa ce ma'eeshat bata da wayo tana yawan yiwa doctor yarinta da kuma ƙwaɓa mai maga haka doctor yake haƙura ya lallaɓa ta. Yanzu shima doctor ya gane ma'eeshat ta fara son sa, dan haka yayi farin ciki sosai kuma yana nan yana shirin zuwa wajan dadyn ma'eeshat on expected ba tare da ma'eeshat ɗin ta sani ba, shi yasa doctor yayiwa ma'eeshat dabara har ta bashi number abba.... Yau weekend ta kasan ce doctor ba zai fita ko ina ba, gaba ɗaya yaran gidan basa nan twins tun tafi driving school ita kuma yesmeen ta tafi tafiz daga dady sai momy sai kuma doctor ashmal ɗin. Bayan doctor ya gama wanka ya shirya direct falo ya futa domin samu yayi breakfast. Lokacin da doctor ashmal ya fita daga bedroom ɗin sa yana shiga falon ya hangi dady shi kaɗai yana breakfast. Fuska a sake doctor ashmal ya ƙarasa inda dady yake tare da durƙusawa har ƙasa yana cewa “dady ina ƙwana?”. murmushi dady yayi tare da cewa “lpy ƙalau alhamdulilahi fatan ka tashi lafiya kai ma, ya gajiya asibiti kuma?”. Miƙewa doctor yayi sanan yace “gajiya tabi jiki alhamdulilahi dady” ya ƙarasa maganar yana jan kujerar draining ɗin yana zama. “Masha allah haka ake so a cigaba da tai maƙwan jama'a”. Murmushi doctor ashmal yayi sanan yace in sha allah Dady. Bayan doctor yayi saving ɗin kan sa, a hankula ya fara ci a nitse yana ci yana tunanin ma'eeshat. doctor yana tsaka da tunani yaji dady yace masa "yauwa dama ina taso muyi magana amma naga alama 2 days baka samun wani free sosai ko dawowa da wuri bakayi, shine nace bari na bari sai weekend mayi magan". Jinjina kai doctor yayi tare da ajiye spoon ɗin da yake hanun sa yana kallon Dady, cikin girmamawa yace “Tom shikenan dady ina jin ka”. Shima dady ajiye spoon ɗin hanun sa yayi sanan yayi gyaran murya kafin ya fara cewa "Doctor gaskiya zaman nan naka haka yayi yawa na gaji da ganin ka haka, wanan maganar tawa itace ta ƙarshe gare ka daga haka zan ɗauki mataki da kai na ni da momy gaskiya". cikin mamaki doctor yace "dady lafiya fatan ba wani laifi nayi ba". “Laifi mana kayi doctor yanzu ace har ka kai 32 to 33 years ba kai aure ba, kullum mu sai muyi ta zuba maka ido kenan, in munyima magana kace komai lokaci ne, tabas komai lokaci ne amma ai mutum in ya daura niya sai allah ya temake shi. Kai baka so kaga yaranka kenan, su taso kaga girman su, yanzu fa doctor kayi girma sosai dan da kayi auran wuri da tuni ka ajiye mana jikoki fiye da biyu ma, gaskiya mun gaji momyn ka kullum cikin damuwa take akan kai aure, in ma ka kasa zabar matar da kan ka mu zamu zaɓa maka wanda ta dace, mutum sai kace wnda aljana ta aura”. Murmushi doctor yayi tare da cewa "a'a dady aljana kuma"?. “Ƙwarai kuwa doctor to me kake nufi in ba aure akai maka da aljana ba?”. Dariya doctor yayi sanan yace “a'a dady bana nufin komai sai alkhairi, kamar de kullum komai lokaci ne, in lokaci na yazo zanyi”. “Wallahi doctor baka isa ba, gobe zan sa momy ta binciko ma can wata yarinya a ƙauye ka aura”. Zaro ido doctor yayi tare da girgiza kai yana cewa “a'a dady kasan ƴan ƙauyan nan basu wani cika wayewa ba bare su san ya kama ta”. “Eh in tazo gidan naka, sai ka koya mata ya kamatan ai tunda taimaƙwan ka ma za tai ta aura, kai fa yanzu na dena mamaki, dan naga alama aljanar ce ma ta aure ka”. Ajiyar zuciya doctor ya sauke sanan yace "a'a dady bama sai anyi haka ba, dama da akwai yarinyar da nake nema yanzu ina so ita zan aura, to bana so na gaya muku da wuri so nake sai mun gama dedetawa na samu baban ta munyi magana sai na gaya muku”. Nan da nan dady ya saki wani murmushin farin ciki saɓanin da daya haɗewa doctor rai, cikin farin ciki dady yace "ah to to haka nake son ji, ashe haka abun alkhairi ya faru ah masha allah". shima doctor ɗan murmusawa yayi, saboda tunawa da mosoyiyar sa ma'eeshat da yayi, sanan yace “in sha allah dady ade taya ni da addu'a Allah ya tabbatar da alkhairi”. “Gaskiya doctor ka bani mamaki sosai da badan nasan baka yimin ƙarya ba sai nace ban yarda ba, yau da bakin ka kace kana neman wata a matsayin mata aure kai Allah uban giji yayi maka albarka ya baka ita a matsayin matar aure”. “Ameen dady ina so ku taya ni addu'a kai da momy, kasanar da ita”. “tom shikenan doctor ai ko baka ce na gayawa momy zancan farin cikin nan ba zan gaya mata. amma dan Allah banda wasa na baka nan da 3 moths ka gama shirya komai ku fahimci juna dan bana so wata shekarar ta zagayo ba kayi aure ba”. “Tom dady in sha allah komai zai tafi yarda ake so”. Jinjina kai dady yayi sanan yace, “nasan kana da hankali sosai kuma kai babba ne, amma ina so na sake jan hankalika akan kasan yar gidan da zaka aura kake nema, ina son mace ƴar gidan manya mai tarbiya mai ilimin addini sosai”. Jinjina kai doctor yayi sanan yace “hmmm dady kar ka damu in sha allah itama tana da tarbiya sosai, dan gaskiya ba wata babba bace ma dan ko canday ba tai ba, nan da wata ɗaya zata yi candy, to so nake sai munyi aure in tana so sai ta cigaba da karatun nata”. Jinjina kai dady yayi sanan yace “ba komai ai wanan ba matsala bace, daka auri babba mara hankali mai halin banza gwara ka auri yarinyar, sai kama fi iya control ɗin ta, ni de fatana ta zama mai tarbiya”. To haka de doctor da dady suka cigaba da cin abinci suna hirar su hankali ƙwance. dady kuwa ya saki jikinsa sosai saboda yayi farin ciki da jin doctor ya samu wanda yake so...... Bayan doctor ya koma bedroom number abban ma'eeshat ya duba, ya tura masa matsakaicin saƙo mai ɗauke da sallama, gaisuwa, da kuma neman izinin ranar da ze zo suyi magana. Doctor bai fi 20 minutes da turawa abba message din ba, abba yayi masa reply da, ba damuwa zuwa anjima in yana da lokaci ma zai iya zuwa da yamma su gana. Doctor bai nunawa abban ma'eeshat son ta yake ba, kawai ya nuna masa shi doctor ɗin daya taɓa dubata ƙwanaki ne, kuma yana so su haɗu da dady dan suyi wata magana mai mahimmanci. Allah sarki abba harda turawa doctor address ɗin gidan, dan shi ya bada akan rashin lafiyar ma'eeshat za suyi magana. Doctor kuwa lokacin da yaga message ɗin yayi farin ciki sosai da ganin abban ma'eeshat ɗin ya amince yazo, kuma yana sake addu'a akan Allah ya bashi sa'a. Doctor ko sanar da ma'eeshat zuwansa baiyi ba, kuma sun daɗe suna chat, suna ta shan soyayyah su. Doctor misalin ƙarfe 5 na yamma ya gama shiryawa tsaff cikin ash color ɗin shadda bakajin komai sai tashin ƙamshin turare. Shaddar tayi matuƙar ƙarbar jikin sa, abinka da farar fata, ga hular nan tasa itama ash sai ƙyalli take. Zuciyar doctor cike da zullumi ya shiga motar sa, sanan ya fuce daga gidan nasu. Kafin doctor ya ƙarasa shiga layin su ma'eeshat parking ɗin motar sa yayi sanan ya fita ya shiga masallaci mafi kusa da shi da yake yana da alwala kuma lokacin an fara kiran sallah. Bayan doctor ya idar da sallah futowa yayi ya koma motar sa sanan ya shiga layin su ma'eeshat sai gashi a ƙofar gidan nasu. Wayar sa doctor ya ɗauka sanan ya fara kiran layin abba zuciyarsa cike da zullumi. Bayan wayar tayi ringing 4 abba ɗauka yayi baki ɗauke da sallama. cikin girmamawa doctor ya amsa sanan ya sanar da abba ya ƙaraso. Abba cewa yayi “tom bari ya aiko yaro yayi masa iso”. Sai da doctor ya ɗauki kimanin 10 minutes, yana zaune a mota yana chat da ma'eeshat. ita kam ma'eeshat bata san wainar da ake toya ba tana can harɗe a bedroom ɗin ta. sanan doctor ya hango wani yaro mai shigen kama da ma'eeshat ɗin ya futo wanda baze gaza 12 years ba. Har mota ya ƙaraso cikin giramamwa ya gai da doctor sanan ya sanar da shi abba yace ya rako shi ciki. ba musu doctor ya futo ya rufe motar ta, sanan suka fara jerawa shida yaron. Bayan sun shiga, sai da suka ɗanyi tafiya sosai da yake gidan da girma ba laifi sanan suka isa ƙofar wani katafaran sitroom. Tun daga nan yaron ya dakata sannan ya cewa doctor ya shiga abban nasu yana ciki. Doctor kuwa ba musu ya shiga baki ɗauke da sallama. A zaune ya hangi dady akan kujera afnan tana daga gefan sa tana danna wayar abba. Amma afnan tana ɗagowa ta hangi doctor da sauri ta ajiyewa abba wayar tasa sanan ta sauka daga kan kujera a guje ta nufi doctor ashmal tana masa oyoyo............... Kuna tunanin abba zai amince da doctor ashmal ya basa auran ma'eeshat ko kuwa de?. kar ku manta da like (reacted) and share. Ayi following ɗin channel ɗina saboda ina samu posting da zarar na dora. mu haɗe a next page. _page 16 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Lokacin da afnan ta ƙarasa wajan doctor a guje tana masa oyoyo, ko ƙaurin sa bata ƙarasa ba sai ƙafafuwan sa ta samu ta rungume. Fuska a sake doctor ya riƙe hanun afnan tare da cewa “oyoyo afnan sanun ki”. Sanan ya durƙusa har ƙasa yace “abba ina wuni” hanun sa riƙe dana afnan. Abba kuwa kana ganin fuskar sa kasan yayi farin ciki da zuwan doctor sosai, cikin sakin fuska yace “lafiya ƙalau doctor, sannu da zuwa ya hanya, ah tashi-tsahi haka, ga kujera nan ka zauna, mana”. Miƙewa doctor yayi kamar yarda abba ya umarce shi ya nufi lafiyayyiyar kujera mai face ɗin wanda abba yake zaune ya zauna. itama afnan miƙa masa hannu tai tare da cewa “nima kaga doctor ɗorani na zauna kusa da kai”. Murmushi doctor yayi tare da ɗaukan afnan yana zaunar da ita akan kujerar kusa da ita. Abba kuwa cikin jin daɗin yace “ah afnan kenan wato baki manta doctor ba ko, har kin gane shi”. Dariyar su ta yara afnan tai, sanan tace “eh na san shi mana abokina ne, ko doctor?” Afnan ta tambaye tana tsare doctor da Ido. Murmushi doctor yayi wanda har sai da fararran kyawawan haƙoran sa suka futo, sanan ya gyaɗa kai yana cewa “sosai ma afnan ni abokin ki ne ni”. Dariya abba yayi tare da cewa "eh lallai afnan an girma yanzu doctor ne abokin naki kenan”. gyaɗa kai afnan tai, sanan tace kuma gashi har sweet ma yake bani in naje wajan sa, nima zan bashi nawa alawar”. Murmushi doctor yayi sanan yace “tom afnan harda kyauta haka nagode sosai” afnan saukowa tai da sauri ta miƙe tare da cewa “na tafi naje na kawo maka” daga haka afnan ta miƙe ta fuce ta cikin wata ƙasaitacciyar kofar daga cikin sitroom ɗin. Daga abban har doctor ashmal murmushi su ke, saboda afnan ta basu nishadi ba laifi. Bayan afnan ta fita doctor da abba sake gaisawa su kai yi sosai, cikin ladabi da biyayyah. Bayan sun gama gaisawa sun ɗanyi hira akan marasa lafiya hospital, abba cewa yayi “doctor zai iya faɗan abunda yake tafe da shi kai tsaye”. Gyaran murya doctor yayi tare da gyara zama. Cikin nutsuwa ya fara yiwa abba bayani kamar haka "dama zuwa nayi in ba damuwa na roƙe ka alfarma abba akan ayusha”. Jinjina kai abba yayi alamun yana sauraron sa., doctor ashmal kuwa cigaba da magana yayi cikin nutsuwa. “Nayi tunanin kafin komai yayi nisa nazo na same ka na gaya maka saboda ka bani izini, ina so ka bani izini mu dedeta da ayushat kafin a nema min auran ta, naganta na yaba da tarbiyar ta da kuma hankali ta, tayi dede da irin matar da nake so. Tom shine nace bari nazo na sameka abba kafin na fara zuwa sai na nemi izini”. Jinjina kai abba yayi, sanan yace "ƙwarai kuwa doctor kayi ƙyan kai sosai, kuma nima na yaba da ƙyawawan halinka, duk da dama ana ganin ka anga babba mai nutsuwa da hankali. saboda yanzu gaskiya a zamanin nan ba ko wana saurayi ne zai fara zuwa wajan iyayan yarinya ba kafin ya fara neman ta, naji daɗi hakan sosai, kana da aure ne?”. abba ya watasawa doctor ashmal tambayar?. Murmushi doctor yayi tare da girgiza kai cikin ladabi da biyayyah yace " a'a abba bani da aure kuma ban taɓa yin aure ba yanzu ne de nake sa ran hakan, tunda komai lokaci ne". “Gaskiya ne doctor komai lokaci ne, dama na daɗe ina tunani, bazan bawa ma'eeshat yaro ta aura ba sai mai mata, saboda ta cika rawar kai da gaɓintar fari. kuma kasan yaran zamani basu da kirki, yanzu sai aita samu saɓani, in ta haɗu da mara haƙuri, amma yanzu kai naga ka dace da irin mijin da nake so, sobada kai babba ne kuma na yaba da tarbiyyar ka. Sai de wani hanzar ba guda ba, kasan ni uba ne a wajan ma'eeshat kuma ba tare nake zama da ita kullum ba. baze yu na gane ra'a yin ta ba, amma zan tambayi mahaifiyarta ta tambaye ta in de har tana son aure bayan tayi canday to sai ka fara zuwa ko dedeta har Allah yasa ku fahimci juna”. Jinjina kai doctor yayi tare da cewa "gaskiya ne abba duk abunda kace haka ya kamata ayi, amma ni bani da ra'ayin fara zuwa wajan ta hira har sai tayi canday saboda kaga kar na janye mata hankali, kuma gashi za tai jarabawar ƙarshe”. “Gaskiya ne doctor kayi gaskiya kam, shi yasa ake son masu hankali irin ku, dama ina tunanin sauran wata ɗaya ta kammala jarabawar dan inaga zuwa jibi zama su fara jarabawar. Bayan kuma nan sai canday. Amma yanzu bari de na bugawa ma'eeshat ɗin ta sauko ku gaisa, daga nan ko exchange ɗin number ƙwayi ku fara gaisawa kafin aga abunda Allah zaiyi”. Kafin doctor ma ya kai da magana abba ya ɗauki wayarsa ya fara lalubo number ma'eeshat ɗin. Ɓangaran doctor kuwa ba ƙaramin daɗin hakan yaji ba, saboda shi dama har ga Allah yana son ganin ma'eeshat amma ba hali kuma ko da wasa bai yi tunanin abba zai sakar mai fuska kamar haka ba har ya bashi damar ganawa da ma'eeshat ɗin. Doctor jin muryar abba yayi yace “hello daughter?”. Bayan Abba yayi jim kaɗan ƙarawa yayi da " ki sauko ki same ni a sitroom ɗin kasa, nayi baƙo zaku gaisa daga nan ki tawo masa da abun sanyi” daga haka abba ok yace kawai sanan ya katse wayar. Cikin sakin fuska abba yace “yauwa doctor gata nan zuwa”. murmushi doctor yayi cikin jin daɗi yace “okay shikenan abba ba damuwa angode”. Daga haka abba da doctor ashmal hira suka cigaba da yi har tsawan 15 minutes amma shiru kake jin ma'eeshat. Abba cikin mamaki ya kalli agogo tare da cewa “kai subhanallahi, kaga har 18 minutes amma ma'eeshat shiru, hmmm dama haka ƴan fari suke da shiririta, sai haƙuri bari na sake kiran ta”. Girgiza kai doctor yayi tare da cewa “no abba ba komai”. Abba yana kiran wayar ma'eeshat ringing uku tai suka ji ma'eeshat ta ƙwaɗa sallama, ta futo ta ɗayar ƙofar da afnan ta fuce. Katse wayar abba yayi tare da amsa sallama, shima haka doctor ya amsa sallamar ƙasa-ƙasa zuciyar sa cike fall da son ganin ta. Baƙin skirt ne a jikin ta na engalish wst, sai riga fara t shert mai dogwan hannu wanda taluluɓeta da babban mayafi dan bama a ganin rigar sai hanun ta, saboda mayafin ma na mami ne. A hankali ta shigo tana tafiya, hannun ta rike da tire mai ɗauke da leman ƙwali da kuma ruwa sai class cup guda biyu. Abba kallan ta yayi tare da cewa “ma'eeshat kenan ina kika tsaya, kina can kina danna waya ko”. murmushi ma'eeshat tai hannu rike da flat tace “kai abba amma a haka sai naga kamar ma nayi saurin zuwa”. Ma'eesha ta ƙarasa maganar tana tsugunawa ƙasa gefan ƙafar doctor ashmal ta ajiye tire ɗin tare da cewa “ina ƙwana” ta faɗa tana ɗagowa domin ganin wana abokin abba ne, saboda tunda ta shigo ko kallan sa ba tai ba, sai faman ƙamshin turare da yake tashi. Gaban ma'eeshat faɗuwa yayi rass, rass,rass har sau uku, sanan ta fara sosa idon ta dan tunani take doctor gizau yayi mata. Doctor ashmal kuwa, mazewa yayi ba tare daya ɗago ba yace mata “lafiya ƙalau” ya amsa a taƙaice yana danna wayarsa alamun bai ma wani saba da ita ba, dan tunda ta shigo bai kalle ta ba. Abba cewa yayi “ok ma'eeshat ki zauna zaku gaisa, doctor bari na baku waje kuyi magana” abba ya ƙarasa maganar yana miƙewa. ma'eeshat kuwa ji tai gaba ɗaya bakin ta ya kulle gam, sai doctor ne ya iya cewa “tom shikenan abba nagode sosai”. Daga haka abba bai sake cewa komai ba ya miƙe ya fuce. Abba yana futa doctor ya ɗago ido a hankali ya sauke akan ma'eeshat da take tsugune cikin tsananin mamaki. Murmushi doctor ashmal ya sakarwa ma'eeshat tare da cewa “ƴan mata na”. Rufe ido ma'eeshat tai ta buɗe tare da miƙewa tsaye tana cewa “wai da gaske doctor kai ne. Jinjina kai yayi fuska cike da murmushi yace “eh nine mana eeshat ko baki farin cikin ganina ba?”. Murmushi jin kunya ma'eeshat ta saki tare da sunkuyar da kai tana cewa “zuwa kuma on expected mai kacewa abba haka”. Doctor murmushi ya sake saki, duk da ba wani kayan azo a gan bane a jikin ma'eeshat tai masa mugun kyau musamman yanayin yarda ta yafe jikin ta da babban mayafi har kanta, ta rufe ko ina, duk da kuwa hakan bai hana ƙibarta futowa ba da kuma sauran surarta, musamman ƙirjin. “Eh so nake na baki mamaki, da banyi tunanin abba zai kirawo ki mu gaisa ba da sai de nazo na tafi kawai, maza kije ki zauna mana ki dena tsayuwa”. Girgiza kai ma'eeshat tai sanan tace “dube ni fa” ta karasa maganar tana kallon kan ta sama da ƙasa. a sace doctor ya kalle ta sanan yayi saurin kawai da kai tare da cewa “naƙi na kalle kin, mai jikin nake yayi da kike cewa a kalla, bana so ki ringa cewa a kalli jikin ki, a kalla me a jikin naki?” Turo baki ma'eeshat tai sanan tace “a kalli kayan jikina mana banyi ƙwalliya ba fa, kuma kawai sai kazo ka ganni haka, haba ka bari yanzu naje na shirya mai kwalliya”. “No bana son kiyi wata ƙwalli ko ki canza kaya kinyi kyau sosai ƴan mata nah, maza ki zauna muyi hira”. Ba yarda ma'eeshat ta iya, haka ta koma kujerar da bata da nisa da ta doctor daga hannun hagu ta zauna. Zuba mata ido doctor yayi cikin farin ciki yace “wai baki farin ciki da gani na ba ne?”. Washe baki ma'eeshat tai wanda hakan sai da ya bayyana wushirya ta sanan tace “inayi mana, nama rasa mai zance ganin abun nake kamar a mafarki bamu daɗe da gama chat ba”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “ba wani abun mamaki anan, haka ma zakiga na fara zuwa wajanki zance?” Dariya ma'eeshat tai sanan tace “yaushe zaka zo” ta ƙarasa maganar tana tsare shi da ido. Doctor kuwa kawar da ido yayi daga na ma'eeshat sanan yace “hmmm very soon”. Cikin shagwaɓa ma'eeshat tace "a'a ni gaskiya sai ka gayamin” ta ƙarasa maganar tana bibbiga ƙafafuwan ta biyu alamun shagwaɓa. Cikin mamaki da birgewa doctor ya zaro ido tare da cewakuka zaki yi?”. Girgiza kai ma'eeshat tai, kafin tace “a'a amma ni de gaskiya ka faɗa min” ta ƙarasa maganar again cikin shagwaɓa. Jinjina kai doctor yayi dan lamarin ma'eeshat ya wuce yarda yake tunani ya gane yarintace take cin ta, kuma hakan ba ƙaramin burge shi yake ba, dan haka cikin kulawa yace “sai kinyi canday tukunna”. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace “remind too days zamu fara zana exams, ka taya ni addu'a Allah ya bamu sa'a ni da ƙawata”. “tom shikenan eeshat zan miki addu'a sosai, kema ki cigaba da addu'a Allah yasa abba ya bani ke”. “To yanzu wai ni mai abban yace maka ne?”. Girgiza kai doctor yayi sanan yace “ba sai kinji ba sirri ne tsakanin mu, amma de kawai ki cigaba da addu'a kuma in an tambaye ki kina son aure dai ki gaya musu abinda kike so”. Gyaɗa kai ma'eeshat tai, sanan tace “tom shikenan in sha allah, ga ruwa nan kasha mana” ta faɗi hakan cike da kulawa. Girgiza kai doctor yayi ido cike da soyayya ma'eeshat yace “a'a alhamdulilah ni de kawai ke nake son gani”. “Ah haba de gaskiya ni ban yarda ba, barima na taso na zuba maka da kai na” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana miƙewa, doctor kuwa danna wayarsa ya farayi, saboda baya son ya cika kallan ma'eeshat ɗin in tana tafiya, saboda dalili da dama kuwa. Bayan ma'eeshat ta ƙaraso gaban doctor durƙusawa tai, sanan ta ɗauki cup ta fara ƙoƙarin buɗe jarkar lemo domin zuba masa. A hankali doctor yake satar kallon ma'eeshat ɗin. Har ga Allah ma'eeshat tana mugun rikita doctor ashmal, duk abinda yake buƙata ga ƴar mace ta tare har ta wuce haka, abinda ta rasa wanda doctor yake so shine ɓakar fata, a rayuwarsa doctor yana son mace mara haske chocolate color. Amma da doctor ashmal ya haɗu da ma'eeshat kawai sai ya haƙura da baƙar mace, dama ya ƙadarta a ran sa dole zai rasa wani abun akan macen da yake so ba lallai ya samu komai ɗari bisa ɗari ba. kuma shi a halin yanzu, son ma'eeshat ya gama kama shi ko ta ina. Shi yasa yanzu ko wace mace bata burge shi a duniya sai ma'eeshat son ta yake sosai burinsa ya farka ya ganta kusa da shi a matsayin matar sa ta sunnu. Kamar doctor ance ya ɗago yana ɗagowa su kai 4 eyes da ma'eeshat tana kallon sa. Kawar da kai doctor yayi ba tare da yace komai ba, yana mamakin wana kalar kallon ma'eeshat take masa haka. cikin mamaki itama ma'eeshat tace, “mai kake tunani haka magana nake maka fa”. shima doctor cikin mamaki yace “oh sorry banji abinda kika ce ba”. Gyaɗa kai ma'eeshat tai tare da cewa “shikenan kuma ya wuce” ta ƙarasa maganar tana miƙa masa glass cup ɗin hanun ta. Murmushi doctor yayi sanan yace “kin dage sai nasha kenan tom nagode” ya ƙarasa maganar yana ƙarbar cup ɗin. Daga haka ma'eeshat ta koma kan kujera suka cigaba da hira da doctor cikin soyayya da ƙauna. Ma'eeshat da doctor sun kai kimanin 30 minutes suna hira, dan har sai da afnan ta shigo hanun ta rike da ledar Sweet da kayan zaƙi wai ta kawowa doctor shima. Doctor kuwa yaji daɗin hakan sosai, amma sai yayiwa afnan dabara akan ta ajiye masa gobe zai dawo ya ƙarba, afnan ta yarda da hakan amma duk da haka sai da tace sai ya tafi da sweet biyu. Kuma ba yarda doctor ya iya dole haka ya ƙarba. Kallon wayarsa doctor yayi sanan ya miƙe tsaye yana cewa, har mun “kai 40 minutes muna hira daga gaisawa Koh?”. Murmushi ma'eeshat tai sannan tace “har zaka tafi haka da wuri, kaga ko lemon ma baka sha ba”. “Hmmm a hakan ne zan tafi da wuri haka fa abba yace kawai mu gaisa, yanzu de tafiya zanyi gaskiya”. “Tom shikenan bari na kirawo maka abban kuyi sallama Koh?”. girgiza kai doctor yayi sanan yace "a'a ki rabu da shi duk maganar da zamuyi mun gama, nasan yanzu da akwai abinda yake in kin koma kyayi mai sallama.” “Tom shikenan bari na raka ka” ma'eeshat ta faɗa itama tana miƙewa tsaye daga zaman da tai. Girgiza kai doctor yayi sanan yace “a'a kiyi zaman ki bana so ki wahalar da kan ki, ki koma cikin in na koma gida zamuyi waya”. Afnan ce ta tari nunfashi doctor da cewa “ni de zan raka ka, tunda kai abokina ne ba abokin auty macica ba”. Dariya ma'eeshat tai sanan tace “gaskiya ne afnan dole doctor ya rabu damu mu raka shi tunda a bokin ki ne”. Shima doctor murmushi yayi sanan yace “it is okay, na yarda kinci darajar afnan, shi yasa zan barki ki raka ni”. murmushi ma'eeshat tai sanan ta fara ƙoƙarin gyara mayafin ta. Doctor de da sauri ya kawar da kai gefe, sanan yaja hanun afnan yana cewa “bari mu fara gaba kyabiyo mu a baya” daga haka doctor da afnan suka fuce. ma'eeshat ji tai gaba ɗaya ta tsargu, ganin yarda doctor yake nesa-nesa da ita, tun dazu yaƙi ya amince ya kalli wani sa shi na jikin ta ko kaɗan sai fuskar ta kawai. Kuma ita har ga Allah bada niya tace ya kalli jikin ta ba, kuma bada niya tayi ƙokarin gyara mayafin ta ba, a iya haka ma'eeshat ta tabbatar doctor yana da tarbiya da kamun kai sosai, kuma yana iya babbance halak da haram. Bayan ma'eeshat ta gama gyara mayafin nata, fucewa tai tabi bayan su doctor, gani tai har sun ɗan yi mata tazara, dan haka a hankali ta fara tafiya itama. Sai da suka kusan fita gate sanan doctor ya dakata shi da afnan domin jiran ƙarasowar ma'eeshat duk da kuwa bashi da tabbacin ta biyu bayan su, saboda shi doctor bai cika son juya bayan sa ba. Ma'eesha tana ƙarasowa, tace “tom shikenan nasan haka zaka ce iya nan ya isa ko?”. murmushi doctor yayi tare da cewa “eh haka zance mana ƴan mata na”. Jinjina kai ma'eeshat tai tare da cewa “ok bye afnan zo mu koma Koh?”. Hanun doctor afnan ta saki tare da ɗaga masa hannu tana yi masa, bye bye sanan ta wuce wajan ma'eeshat. shima doctor bye yayi mata sanan suka sake sallama shi da ma'eeshat ɗin, bayan haka ya fuce zuciya cike da farin ciki. itama ma'eeshat ɗin hanun afnan ta kama suka juya domin komawa ciki........... Abinda yasa kukaga ina yi muku fashin posting saboda, baƙwa yawan like. Amma na kusan na tsame masu like na ringa yi musu posting ɗin su kullum. Bazan gaji da cewa kuyi mana like (reacted) and share. kuje kuyi following din channel ɗina. mu haɗe a text page. _page 17 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Suna ƙarasawa ciki ba inda ma'eeshat ta wuce sai bedroom ɗin mami. Baki ɗauke da sallama ma'eeshat ta shiga bedroom ɗin mami. Akan bed ta tarar da mami tana danna wayarta. Mami tana jin sallamar ma'eeshat ta ɗago tare da amsa mata sallamar. ma'eeshat tana ƙarasowa wajan mami ta zauna tana ta sakin murmushi. kallon ta mami tai cikin mamaki tace “iye ma'eeshat duk yarda akai haɗuwa da doctor tayi miki daɗi ko”. Dariya ma'eeshat tai, sanan tace “kai mami waya gaya miki”. “Yanzu abban ki ya futa ya bani labarin duk abinda ya faru, har kin dawo kenan?” mami ta faɗi hakan tana ajiye wayarta a gefe. “Hmmm mami na dawo, amma naji daɗin zuwan doctor wallahi, dama fa already na riga da na son doctor, mun kai kimanin 2 to 3 moths muna soyayya da shi, shine yanzu yazo wajan abba on expected, ni ban masan zai zo ba”. “Eyee lallai ma'eeshat wato har soyayya kika farayi ban sani ba kenan, hmmm kice banyi ɓatan kai ba, dana nacewa abba ya barki kawai ku fahimci junan ku ya ringa zuwa kuna zance, aure kike so ba karatu”. Dariya ma'eeshat tai cikin farin ciki tace “kai mami alhamdulilahi da gaske haka kika cewa abba na”. “To mai zance mai kuwa ma'eeshat ni de nasan aure kike so,tun ba yau ba kike cemin bazaki cigaba da karatu ba aure zakiyi”. “Eh haka nace kam mami, ni bana son wani karatu, amma in naje gidana sai nayi in mijina yana so”. “Hmmm ma'eeshat kenan yarinta tana cin ki, shifa aure ba wasa ake ba kuma ba danna waya ake ba, da kuma shagwaɓa, wallahi ki shiga hankaliki”. “mami kenan, nifa aure nake so ah to”. “Shikenan ba damuwa za'ai miki ai ba laifi doctor usman yana da kirki”. Zaro ido ma'eeshat tai sanan tace “wana doctor usman ɗin kuma mami?”. Wani kallo mami ta watsawa ma'eeshat tare da cewa “doctor usman ɗin da yazo yanzun nan”. girgiza kai ma'eeshat tai sanan yace “a'a mami baki gane wana doctor abba yayi miki bayani ba. Kin tuna farko da muka je hospital ɗin, ai ba asalin doctor ɗin muka gani ba, cewa akayi zamu ga wani madadin wanca, to ba sai daga baya ɗayan doctor ɗin ya shigo ba, wani fari haka mai kyau”. “Ok na gane shi ma'eeshat wai wanan doctor ɗin ne?”. “Eh shine lokacin da muka je ni da abba shi muka gani dama office ɗin sane ai”. “Lallai ma'eeshat kar fa ace haske kika bi da kyau, wallahi ki kiyayi kan ki, ni bana so ki kwaso mutum mai kyau ba kyan hali, gwara kin samu mara kyan gani, me kyan hali sai yafi miki kwanciyar hankali”. “A'a mami wallahi ba iya kyau nabi ba, shifa yana da tarbiya sosai, some time ma in na faɗi abinda bai dace ba har faɗa yake min, kuma gashi tunda muke bai taɓa gayamin maganar da bata dace ba. nifa duk samari na kullum cikin faɗa muke da su amma ban da shi, kona gaya mai abinda bai dace ba, baze nuna min bai ji daɗi ba”. “Masha allah haka ake so, shima abba yace ya yaba da tarbiyarsa, saboda yanayin maganar sa, kuma yace min babba ne koh?”. “to gashi nan de ni bana gane babba kema kin taɓa ganin sa, kamar haka yace min shekarar sa 30 dana tambaye shi. Amma gaskiya ni ban yarda ba, saboda banga ya fara tsufa ba”. Dariya mami tai sosai sanan tace “dadi na dake ma'eeshat hankali, in banda abinki mutum yayi shekara 30 sai tsufa kuma. ai wani tsufan tension ne na yara da mata, amma shi tunda bashi da mata taya zakiga ya tsufan sa? Kwai bai yi aure da wuri bane, kuma dama abban ki baya so ya baki yaro, daba haka yake cemin mai mata zai aura miki saboda saurayi baze ɗauki shashancin nan naki ba”. Zaro ido ma'eeshat tai tare da taɓe baki tana cewa “tabb Allah ya kiyaye da na auri mai mata, gwara na zauna ba auran har abada”. “Hmmmm lallai ma'eeshat wai ni taya ma kika samu number doctor ɗin haka har kuka saba?”. “kin tuna lokacin da afanan ta ɗauko wayarsa da mukaje hospital. To lokacin na samu number sa ni na ƙwafa ma na tura mai message da yake cajin wayar tasa ya ɗauke”. Jinjina kai mami tai, sanan tace “to Allah ya tabbatar da alkhairi, kinga ai sai a aurar daku ke da meenal in kin ƙara hankali, dan ko doctor ya turo shekar biyu za'a sa miki kafin nan de kin fara zuwa makaranta”. Tabe baki ma'eeshat tai sanan tace “kai haba mami har 2 years wallahi ni bazan yar ba, kuma ni nace miki bana son karatun nan” daga haka ma'eeshat ta tashi ta fuce. A fili mami tace “kai! ma'eeshat kenan ba hankali, wato ita gani take aure wasa ne?” mami ta tabbatar ma'eeshat bata gama sanin mene auran ba....... Cikin farin ciki ma'eeshat ta koma bedroom ɗinta, tana komawa ta lalubo wayarta ta bugawa meenal. bayan meenal ta ɗauka cikin farin ciki, ma'eeshat ta fara bata labarin zuwan da doctor ashmal yayi wajan abba on expected. Meenal ta taya ma'eeshat murna sosai, tana ta tsokanrta ta kusan zama amaryar doctor ashmal. Ma'eeshat ita kuwa daɗi take ji amma duk da hakan itama sai data tsokani meenal akan ta kusan zama amaryar waleed. Tofa meenal da ma'eeshat sun sha hirar su sosai da sosai. meenal tana ta yiwa ma'eeshat faɗa akan ta dage da karatun exams ta rage yawan waya da doctor saboda itama yanzu ta dena biyewa waleed da yawan chat ko waya, karatu take yi. Ma'eeshat ta ɗauko shawarar meenal ɗari bisa ɗari sanan kuma ta sanar da ita, tana karatun itama ba laifi. Bayan meenal da ma'eeshat sunyi sallama, ma'eeshat miƙewa tai, ta nufi toilet ta ɗauro alwala, bayan ta futo ta fara gabatar da sallah isha'i. Bayan ma'eeshat ta kammala, litattafanta ta ɗebo har guda uku ta zauna tana ta faman dubawa tana karantawa. Haka ma'eeshat ta ringa karatu baji ba gani, har wajan 11 dare. Da ta gaji ajiye litattafan nata tai sanan ta fuce daga bedroom. Ba jimawa ta dawo da plate, a hanun ta, wanda yake dauke da cincin sai lemon mai sanyi da cup. dawowa ma'eeshat tai ta zauna a gefe tana ta tunanin sahibin nata. Tana tunani tana bawa cikin ta hakkin sa, ana cikin haka kuwa wayarta ta fara ringing. Da sauri ma'eeshat tasa hannu ta janyo wayar. wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke sakamaƙwan ganin number doctor ashmal. Da sauri tasa hannu ta ɗaga wayar sanan tasa ta a hands free, ta ajiye a gefe ta cigaba da cin abin da take ci. “Assalama'alaika” doctor yayi sallamar cike da kulawa. “wa'allaikissalam fatan kaje gida lafiya ya hanya”. “Alhamdulilah eeshat naje gida lafiya ƙalau, ya na barki fatan na barki lafiya”. “Alhamdulilah ka barni cikin mamaki kawai”. “Hmmm wai ƴan matana har yanzu ba zaki dena cewa na baki mamakin nan ba, mamakin mai na baki haka?”. “zuwanka wajan abba mana ba tare da sanina ba”. “Oh yanzu dan zan zo wajan abba sai na sanar da ke kenan kai eeshat kin cika rigama”. “Eh to ai sai ka gayamin de ko, gaskiya next time in zaka dawo ka gayamin, in ba haka ba zanyi fushi da kai”. “It's okay my eeshat kar kiyi fushi dani, zan gaya miki in zan sake zuwa next”. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace “yauwa ko kai fa”. “Hmmm kema ko ke fa ƴan matana kin cika rigama sosai kamar yar baby”. “To ni ba baby bace a wajan ka?”. murmushi doctor yayi sanan yace “eh haka ne kinma fi baby, a wajan doctor” “Yauwa haka nake son ji”. “Tom babe gaskiya yau naji daɗin ganin ka sosai dama haka kike da kyau?” Murmushi ma'eeshat tai sanan tace “duk kyau na ai ban kai ka ba”. Cije lips doctor yayi sanan yace “ke daɗi na da ke kin cika yarinta, dama maza suna da wani kyau ne?”. “Eh suna da shi mana sosai”. Cikin mamki doctor yace to, in ban taɓa sani ba kuwa sai yau”. “Tab to in kai baka gani kyanka, ni ina gani kyan ka sosai da sosai”. “Hmmmm eeshat kenan Allah ya shiryamin ke?”. “Ameen doctor to ka bani labari”. “Hmmm my love labari sai ke maza ki bani nasha”. cikin jin daɗi ma'eeshat tace “tom shikenan zan baka labarin da zaka ji daɗin sa”. Tom haka ma'eeshat da doctor su ka sha hirar su sosai, sai da su ka kai kimanin 12 dare sanan doctor yace suje su ƙwanta haka. amma ƙiriƙiri ma'eeshat tace a'a ita bata gaji da shi ba ta ringa zabga masa shagwaɓa. Wanda hakan ba ƙaramin tayarwa da doctor hankali yayi ba, sai da tasa ciwan sa ya tashi, ba shiri. amma haka de ya lallaɓa ta da kyar ta yarda su kai sallama cike da ƙaunar junan su........ To jarabawar su ma'eeshat ta kankama sosai, dan meenal da ma'eeshat sun fara jarabawa. Gaba ɗaya ma'eeshat ta watasar da doctor saboda jarabawa, shima doctor ya ɗan ɗaga mata ƙafa saboda kar ya ɗauke mata hankali ta faɗi jarabawa. Sai bayan too day's yake kiranta shima ba wani jimawa suke ba, 30 minutes suke ko 1 hour. Ma'eeshat ta mai da hankali sosai tana karatu, ga addu'a da take ga sallah dare, ahakan Allah ya basu sa’a suji jarabawa ita da ƙawarta meenal. Itama ɓangaran meenal ɗin, tayi baya-baya da waleed duk da kuwa shi bai san haka ba, baya ɗaga mata ƙafa kullum sai sunyi waya. haka dole meenal take bashi lokaci, da yake duk karatun jarabarwar ma ta gama yi, sai de wanda ba za'a rasa ba. A rana sau ɗaya take ɗaga wayarsa, shi kuwa waleed sai ya kai 2 hours yana waya da meenal sam ya kasa ɗaga mata ƙafa, shi in bai ji muryar ta ba sosai sam baya jin daɗi ji yake kamar bashi da lafiya. To kwance tashi ba wuya wajan Allah, meenal da ma'eeshat sun kammala jarabawar su baki ɗaya bayan an ɗauki 2 moths. sunyi jab, waec,neco. yanzu saka maka makwan su kawai zasu duba su gani. Zaman gida ya kama su, suna nan suna shirye-shirye shan canday nan da sati 1. Soyayah tsakanin doctor da ma'eeshat ta sake dawowa sabuwa, kuma doctor yayi mata alƙawarin, ranar da sukai celebrate ɗin candy in sha Allah zai zo zance wajan ta. Ma'eeshat kuwa taji daɗi sosai, dan haka sai Allah-Allah take suyi, celebrate ɗin candy ɗin. ƙwana biyu basa zama, ita da meenal kasuwa suke zuwa da shopp saboda su, suyi siyayyar abubuwa da suke buƙata da kuma kayan da zasu sa ai musu picturs ɗin graduation. Musamman ma ma'eeshat ɗin tama fi meenal zagewa, dan ko meenal bata je ba, ita da kanta zata sa driver ya fita da ita ta suyo musu wani abubuwan. Ɓangaran waleed shima yana nan yana shirye-shiryen dawowa kano, saboda canday ɗin meenal. sanan yayiwa meenal alƙwari yana dawowa in sha Allah baze koma ba sai an sa musu ranar aure.......... Yau de gaskiya busy yayi min yawa shi yasa ban muku typing sosai ba, dan typing ɗin yau bai gama cika page ba, kuyi haƙuri da wanan. Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 18 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Yau ta kasance ranar canday ɗin su ma'eeshat. Zuciyar ma'eeshat cike fall take da farin ciki saboda tasan ko ba komai, doctor zai fara zuwa wajan ta zance. Itama meenal zuciyar cike fall take da farin cikin, saboda yau waleed zai biyo jirgin dare ya dawo, kuma tasan tabbas an kusan kawo kuɗin auran nata, saboda yace yana zuwa zai aiko manya ai maganar auran su. Makarantar su ma'eeshat ta cika sosai da iyaye malamai da kuma sauran ɗalibai. Ma'eeshat tasha yabo sosai wajan malamanta biyu. Ita kuwa meenal ba'a magana gaba ɗaya malaman school ɗin kowa sai da ya yebe ta ga san barka. Sanan har kyauta akai mata, ta gaba ɗaya makarantar tafi kowa hankali da nutsuwa a zangwan shekarar ƙarshe. kuma gashi taci kyauta zuwa first class a ajin su tunda aka sa meenal a school ɗin first class take zuwa, ba taɓa ɗaukar ta 2 ba kullum itace first class. Ita kuwa ma'eeshat kyauta ɗaya ta samu ta lashe, wato tazo ta uku. Shine kawai kyautar da ta lashe, saboda bata da haƙuri kuma ka shegen surutu a class kamar taci aku. Masha allah, yan uwa da abokan arziki sun hallaci candy ɗin su ma'eeshat sosai. Su ma'eeshat da meenal sun sha celebrate ɗin canday su da class mate ɗin su. Ansha picturs sosai da sosai. Sanan kuma an zane riguna da makoki kala-kala harda hijab, kowa yana yima ɗan uwan sa, sa hannun sa a kaya. Su meenal wuni ɗaya su kai suna abu guda, suna farin ciki sosai da wanan rana, masu kukan rabuwa da ƙawaye suna yi. Anci an sha, anyi picturs, anyi wasa, anyi tsalle tsalle, an zane bangwan school da rubutu, kai abubuwa da dama de akai, ranar sai da student maza da mata suka rikita school ɗin nan ta ko ina. Sai misalin ƙarfe biyar da rabi driver su ma'eeshat ya ƙaraso domin ɗaukar su. Haka suka rabu da ƙawayan su cike da kewa da ƙaunar juna. Direct driver gidan su ma'eeshat ya wuce da su. A gajiye suka shiga cikin gidan, bayan sun shiga ciki, mami tai musu san barka. bedroom ɗin ma'eeshat suka wuce., suna shiga meenal ta cire kayanta tai ta ɗauko towel ta ɗaura sanan ta shige cikin toilet domin yin wanka. Bayan ta futo itama ma'eeshat shiga tai domin wankan. A nitse meenal ta ƙarasa wardrobe ɗin ma'eeshat ta buɗe sanan ta fara lalubo kayan da za tasa. Wata blue ɗin abaya ta ɗauka mara nauyi bayan tasa, ta ɗauke kan ta da blue ɗin mayafin abayar sanan ta koma kan bed ta zauna. Bayan meenal ta duba wayarta dogwan message ta gani ya shiga mata na waleed. Ajiyar zuciya tai tana tunanin mene haka a cikin message ɗin. Dan haka karantawa ta farayi cikin nutsuwa. Koda meenal ta kammala karanta dogwan message ɗin murmushi ta saki saboda taji daɗin message ɗin Waleed. Congratulations yake mata kan canday ɗin da tai, sanan yana mata fatan suyi aure very soon, harda tsara musu rayuwar da za suyi. Godiya meenal tai mai sosai ta turamai, zuciya cike fall da kauna. Kafin meenal ta ajiye wayar kiran waleed ya shigo, tayi farin ciki sosai da ganin kiran nasa, dan haka kwanciya tai akan gado sanan ta ɗauki wayar baki dauke da sallama. Bayan ma'eeshat ta futo, itama wardrobe ta nufa ta ɗauko rigar tasa, sanan ta haukan gado tana bin meenal da ido wanda shauƙi da soyayah ya gama tafiya da ita, sai wani lumshe ido take kamar mai jin baccci tana magana a hankula. Murmushi ma'eeshat tai tana mamaki yarda meenal ta faɗa soyayya waleed cikin lokaci ƙanƙani, ita da ada ko burgeta soyayya bata yi. Lokacin da meenal ta ankare da ma'eeshat a wajan da sauri ta rufe fuska alamun jin kunya saboda tayi mugun tsarguwa da kallon da ma'eeshat take mata. Meenal ko sallama batayiwa waleed ba ta kashe wayar sanan ta sata a jirgi, saboda karma ya sake kira. “Ah kiji ƴar iska, shi yaya waleed ɗin da kike kashe mai murya kuna shan kalamai baki ji kunyarsa ba sai ni?” Ma'eeshat ta faɗi hakan tana gallawa meenal hararar wasa. Wani siririn murmushi meenal tai sanan tace "hmmm ai kece kin cika sa ido wallahi duk kin sa na wani tsargu da yawa". Murmushi ma'eeshat tai sannan tace "hmm ai meenal mamaki kika bani wai yau kece kike soyayya koh". Itama meenal murmushi sai sanan tace "hmmm ma'eeshat kenan ki dena mamaki kin san komai na allah ne, ai bama yanzu zaki mamaki ba sai allah ya kai mu lokacin bikin namu" meenal ta ƙarasa maganar tana sunkuyar da kai. Ɗan duka ma'eeshat ta kai wa meenal "iye lallai meenal matar waleed, yau da kan ki kike faɗar hakan, to Allah ya kai mu lokacin". Sunkuyar da kai meenal tai sanan tace “ameen” a hankali. Wayarta ma'eeshat ta janyo, bayan ta gama duba whatsApp gani tai gaba ɗaya ba message ɗin doctor, kuma gashi ko ɗan congratulations bai mata ba, yau gaba ɗaya bai mata magana ba bare ya kira ta, tunda safe, kuma bayan yasan yau ne candy ɗin nata. Wani siririn tsaki taja, sanan ta fara lalubo number doctor ɗin. bayan ma'eeshat ta gama lalubo number doctor ɗin, biga masa ta farayi zuciya a zafafe. Amma abun mamaki ba amsa, sai da ma'eeshat tai wa doctor kira har sau uku ta duka layin sa amma ina ba amasa. Gaba ɗaya jikin ma'eeshat yayi sanyi kuma farin cikin ta ya fara komawa ciki. Bayan ma'eeshat tai dogwan tunani, sai ta bada doctor aiki yayi masa yawa ne shi yasa, dan haka nan da nan hankali ta ya kwanta. "Hmmm ma'eeshat kin ga nifa gida zan wuce yanzu nan" meenal ta faɗa tana hamma. Cikin mamaki ma'eeshat tace “gida kuma meenal? kinga fa ana ƙoƙarin kiran sallah magriba, kuma gashi mun ƙwaso gajiya sosai kamar ma bacci kike ji?”. "Wallahi kuwa ma'eeshat na gaji da yawa bacci nake ji shi yasa nake so na tafi gida, tun kafin ma dare yayi". “Ah haba gaskiya ba in da zaki kina nan, to wai nan ma ba gidan ku bane, ki zauna mana kin san yaufa zamuyi hira dole mun mai da yarda akai”. "Ah haba ma'eeshat karfa kice na ƙwana gaskiya a'a" meenal ta faɗa tana girgiza kai. “A'a gaskiya meenal ba inda zaki wallahi yau a nan zaki ƙwana to menene, gobe ba sai ki tafi ba”. “A'a ma'eeshat yanzu nasan umma da baba suna nan suna jira na, kar suji shiru ban dawo ba”. Ki kwantar da hankalin ki, ki bari ni da kai na zan kirawo su na gaya musu”. To haka meenal da ma'eeshat su kai ta musu daga ƙarshe de dole sai haƙura meenal tai da tafiya gidan nasu, saboda ma'eeshat tafi meenal naci da ban baki, harma da kafiya, dan haka ba yarda ta iya. Daga haka kuma, kiran sallam magriba aka farayi, a tare meenal da ma'eeshat suke miƙe tsaye suka wuce toilet domin alwala. bayan sun gama ɗaura alwala sun fito, sallaya meenal ta shimfiɗa musu, sanan suka saka hijabai domin gabatar da sallah. Bayan sun idar ƙasa suka sauka domin cin abinci. suna cin abinci suna hira jefi-jefi, amma gaba ɗaya hankali ma'eeshat baya jikin ta, tunanin doctor ashmal kawai take yi. Bayan sun gama cin abinci komawa bedroom su kai, meenal sai jan ma'eeshat take da hira ita kuma ma'eeshat tai jigum, ana cikin haka wayar ma'eeshat ta fara ringing, da sauri ma'eeshat ta ɗauki wayar tare da duba sunan mai kira. Lokacin da ma'eeshat taga sunan doctor, sauke ajiye zuciya tai, lokaci guda farin ciki ya cika mata zuciya. amma da yake ma'eeshat tana ɗan fushi da doctor ajiye wayar tai a gefe, saboda ta rama abinda yai mata. Bayan wayar ta tsinke wani kiran ne ya sake shigowa. lokacin da ma'eeshat taga doctor ne yake sake kiran ta, tayi mamaki sosai saboda tasan doctor baya sake kiranta in bata ɗauka ba, sai bayan 30 minutes haka ko 20. Tunda ma'eeshat taga haka, tasan da akwai abu mai mahimmanci kuwa, dan haka ɗaukar wayar tai ta kara a kunne ba tare da tace komai ba. Daga can ɓangaran kuwa doctor ashmal sallama yayiwa ma'eeshat bayan yaji shirin yayi yawa. A daƙile ma'eeshat ta amsa sallamar kamar wanda akai wa dole, wai ita alallai fushi take da shi. Ma'eeshat jin sautin murmushi doctor tai yi, bayan ya ɗanyi jim, yace “hmmm eeshat wana laifi yau doctor yayi?”. Taɓe baki ma'eeshat tai kamar doctor yana kallan ta sanan tace "yafi kowa sanin abunda yayi ai". “Ah! Ah! Ah! kin taɓa jin inda mutum yasan abinda ba'a gaya masa ba”. “Eh sosai ma kuwa yana sani, musamman in shi yana da zurfin tunani da basira”. “To eeshat kin cika rigima, amma de yanzu kin san menene?”. Girgiza kai ma'eeshat tai sanan tace "a'a sai ka faɗa”. “gani a ƙofar gidan ku nazo zance wajan 'yan matana eeshat”. Zabura ma'eeshat tai tare da zaro ido tana dafe ƙirji, cikin tsananin mamaki tace “da gaske?”. Murmusawa doctor ya sake yi sanan yace “da gaske mana ko kina tantama ne?”. Cikin mamaki ma'eeshat tace "gaskiya kam ina koƙwanto, nafi tuanin wasa kake min kawai". “Ok shikenan tunda koƙwanto kike na koma ko zaki futo ki tabbatar da haka”. “Wayyo Allah na doctor wai da gaske kake?” shiru doctor yayi bai ce komai ba yana sauraran ma'eeshat. “Hmm tom shikenan ganinan futowa, give me 10 minutes only”. “Ok no problem” doctor yana gama faɗar hakan ya katse wayar. Ita kuwa ma'eeshat wani tsalle ta tafka tare da fara iwun daɗi. Meenal da tun dazu take kallan ta tana jira ta kammala wayar ta tambaye ta, cewa tai "kai ma'eeshat meye haka mai ya faru kuma?". A guje ma'eeshat ta rungume meenal tare da cewa "meenal ki taya ni farin ciki wai doctor ne yazo yace yanzu yana ƙofar gidan nan". “Ah da gaske masha allah inaga surprise ɗin ki kawai zai yi”. “Wallahi meenal surprise ɗina doctor yayi”. “Okay to kar yayi ta jiran ki maza ki tashi ki shirya mai kike jira?”. Sakin meenal ma'eeshat tai tare da cewa "yanzu ma kuwa meenal wayyo farin ciki zai kashe ni". Daga haka ma'eeshat ta nufi wardrobe ta fara binciko kaya jikin ta sai rawa yake. Dariyar meenal tai, sanan ta miƙe ta nufi wardrobe kusa da ma'eeshat, wanda har yanzu ta kasa zaro riga ɗaya a ciki. “Kai ma'eeshat ke da zakiyi sauri, kinga jeki ki ɗan gyara fuskar ki ko lipstick kisa da hoda, bari na duba miki kayan da zaki sa, dan kiyi sauri”. Jiki na rawa ma'eeshat tace “tom meenal na gode” sanan ta nufi merro domin yin kwalliya. A hanzarce ma'eeshat ta kammala gyara fuskarta ta, sanan ta fara shafa jel. Lokacin dta kammala, gani tai meenal har ta ɗauko mata kayan da zata sa. Doguwar rigar atamface, read ɗin atamfa mai ratsin baƙi da fari da kuma zanan ganye kore, an mata ɗinki doguwar riga rafa, wanda tasha stone ko ta ina sai wani walwali take. “Kai meenal nifa kin san nafi son sa abaya wallahi nafi jin daɗi”. Wani kallo galala meenal ta watsawa ma'eeshat tare da cewa "kullum ke sai ki tasa wata abaya har ta dena yi miki kyau, to wallahi sai kin sa wanan atamfar yarda kike da hasken fata kyau za tai miki, ke bakya so ki sace zuciyar doctor ne?”. Murmushi ma'eeshat tai tare da cewa "ina so mana, amma takuramin rigar za tai". “A'a ba wani takura, kisa mana, za tai miki kyau sosai bari ma na nemo miki mayafi black". “Tom shikenan” ma'eeshat ta faɗa tana ɗaukar rigar domin sawa. A hanzarce meenal ta nemowa ma'eeshat mayafin da zata sa, harma da takalmi. Meenal tana juyowa ta saki baki galala, ganin yarda rigar tai mugun karɓar jikin ma'eeshat ɗin, kamar drowning. “Wow dubi kiga yarda ki kai kyau ma'eeshat” meenal ta faɗa tana ƙarasowa. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace, "kinga maza kizo ki ɗauramin ɗaukwalin nan kin san de ba iyawa nai ba". Karɓar ɗankwalin tai meenal sanan ta buɗa shi ta fara ninkawa. Ita kuma ma'eeshat ta zauna akan kujerar merro, meenal ta fara ɗaura mata. Cikin ƙanƙanin lokaci meenal ta kammala yiwa ma'eeshat ɗauri mai v wanda yayi matuƙar yi mata kyau sosai da sosai. Da sauri ma'eeshat tasa sarƙa da ɗan kunne, bayan ta gama ta yafa ɗan mayafin ta. Tabarakallah masha allah, ko ɗan baƙin ciki ya kalli ma'eeshat sai ya ƙara kuma dole yace tayi kyau. itama kan ta ma'eeshat ta tabbata tayi kyau sosai da sosai, wanda raban da tayi irin sa har ta manta. Har ta kama hanya zata fita meenal ta biyo ta da turare, tana cewa " ki tsaya kin manta baki fesa turaran ba”. murmushi ma'eeshat tai sannan ta tsaya meenal ta fesa mata turaran sama-sama, daga haka ta fuce da sauri. Da sauri ma'eeshat take tafiya, tana gab da futa suka ci karo da Mami. cikin mamaki mami tace "kai ma'eeshat ina zakije haka kike sauri harda bige ni gashi kinci kwalliya”. Murmushi ma'eeshat tai, sanan tace “ya haƙuri mami sauri nake ban kula dake ba doctor ne yazo”. Cikin mamaki mamki tace "doctor ne yazo shine baki gayamin ba kike ƙoƙarin fita ma'eeshat?”. “Wallahi mami nima yanzu ya bugomin yace yana ƙofar gidan ban san da zuwan sa ba”. Jinjina kai mami tai, sanan tace “shikenan kije ki shigo da shi sitroom, sai kuyi magana, kin san ni bana son zancan waje”. “Tom mami” daga haka ma'eeshat bata sake cewa komai ba, ta wuce tabar mami tsaye da mamaki. da ido mami tabi ma'eeshat tana mamakin rawar kai irin tata, a fili tace "kai ma'eeshat Allah ya shirya min ke”. Ma'eeshat kuwa da sauri take tafi har sai da ta ƙaraso bakin gate tana gaf da fita sanan ta fara saita tafiyar ta. Ma'eeshat tana futa, ta hangi wata danƙareriyar baƙar mota gaba da gidan nasu kaɗan. haka nan jikin ta ya bata motar doctor ce dan haka gyara tafiyar ta tai, sanan ta nufi motar zuciya cike da farin ciki.......... Kwana biyu kunji ni shiru, busy ne yayi min yawa kuma bana jin daɗi. Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 19 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Da yake area da haske tun daga mudubi mota doctor ashmal ya hango ma'eeshat, sai faman ƙyalli take zubawa. Ai sai da komai na jikin doctor ya harba da yayi tozali da ma'eeshat. Sannu a hankali ma'eeshat take takawa, gabanta yana faɗuwa rass rass, tana mamakin wai yau ita zata ga doctor ashmal ɗin ta. haka ma'eeshat tai ta tafiya cikin rangwada har ta ƙarasa gefan bakin motar doctor. Doctor ashmal kuwa ma'eeshat tana ƙarasowa, ya buɗe murfin motar a hankali yasa ƙafa ya futo, sanan ya rufe motar. Sanye yake da brown ɗin shadda, dogayan kaya. Hular nan tasa sai faman ƙyalli take. doctor yayi matuƙar kyau sosai, kamar ba bahaushe ba. Yana juyowa su kai 4 eyes da ma'eeshat bai san sanda ya sakar mata wani tattausan murmushi mai rikita zuciya ba. Itama ma'eeshat sakar masa nata tai ba tare da ta ce komai ba. A hankali doctor yake sake matsowa wajan ma'eeshat ɗin ba tare da yace mata komai ba. Ma'eeshat kuwa rufe fuskarta tai cikin jin kuya tace “meye haka”. murmushi doctor yayi "hmmm eesha ta kinga yanda kika yi kyau kuwa, kamar na sace ki na gudu". Buɗe fuskar ta ma'eeshat tai sanan tace “tom nagode kai ma kayi kyau”. Zuba mata kyawawan idanuwan sa doctor yayi tare da saka sakar mata wani ƙasaitaccan murmushi. Sunkuyar da kai ma'eeshat tai dan bata san doctor da wanan kallon ba sai yau, shi bai cika kallon ta ba. “Congratulations for graduation my future wife” doctor ya faɗa cikin tsanin soyayya. “Thank you” ma'eeshat ta faɗa a hankali. “Naga kinyi shiru yau ba surutun kenan kamar yarda kullum kike cika min kunne a waya”. Ɗagowa ma'eeshat tai cikin mamaki tace “oh cika maka kunne nake kenan shikenan bazan sake baka labarin ba kuwa”. Ɗan zaro ido doctor yayi cikin siririyar muryarsa yace “oh ba haka nake nufi ba Ni”. “Tom shikenan yanzu kazo mu shiga ciki mu zauna mami tace ka shigo bata son mu tsaya a waje”. Murmusawa doctor yayi ba tare da cewa “tom” a taƙaice. Sanan yace mata “ina zuwa” daga haka ya zagaya gaban motar. ya buɗe sanan ya ciro wani madedecin box ɗin gift. Bayan ya ɗauko rufe motar yayi, sanan ya cigaba da tafiya a takaice har ya ƙaraso inda ma'eeshat ɗin take. Bayan ya ƙaraso fuska a sake ya miƙawa ma'eeshat ɗin. Hannu biyu ma'eeshat tasa ta ƙarfi box ɗin tare da cewa “hmm wanan gift ɗin graduation ɗin nawa ne?”. Jinjina kai doctor yayi alamun eh. “Thank you so much dear” ma'eeshat ta faɗa cikin farin ciki. Doctor bai ce komai ba kawai ya kawar da kai. “Tom kazo mu shiga ciki mana”. Jinjina kai doctor yayi sanan yace “tom mu tafi” daga haka doctor da ma'eeshat suka jera suna tafiya. gashi kuma baki gayamin ta nawa kika zo ba. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace “hmmmm nayi rashi sa'a duk karatu na ta uku fa nazo”. “Hmmm kinyi ƙoƙarin sosai ma hakan eeshat”. “A'a ni de banga wani ƙoƙari na ba, ni da nasa ran ɗaukar ta biyu ma”. Cikin mamaki doctor yace “to saboda me baki sa ran ɗaukar first class ba”. Girgiza kai ma'eeshat tai, sanan tace “ai first class na barwa meenal” Jinjina kai doctor yayi sanan yace “gaskiya ne kina son aminiyar nan taki da yawa”. “Kai sosai ma, amma ba wai dan saboda son da nake mata na bar mata first class ɗin ba”. jinjina kai doctor yayi tare da cewa “to saboda me, kika cire sa ran ɗauka first class ɗin?”. “Ai nasha gaya maka meenal gifted ce, duk class ɗin ta fimu ƙoƙari, kasan wani abu kuwa?”. Girgiza kai doctor yayi alamun a'a. “Kaf school ɗin nan tafi kowa nutsuwa da hankali, shi yasa yau ta ɗauki gift ɗin shekara, tafi gaba ɗaya student ɗin school ɗin hankali da nutsuwa”. Jinjina kai doctor yayi sanan yace "amma kuma ke saboda me baki ɗauka ba, ai sai hali ɗaya yazo ake abota”. Dariya ma'eeshat tai sanan tace “waye zai bani wata kyauta ma ni, har abada bazan taɓa iya haƙuri da kawai cin meenal ba, ni fa kusan kullum sai nayi faɗa da ƴan class ɗin mu to kaga taya ma zan ɗauki wata kyautar masu haƙuri da nutsuwa,. Itama tun muna play group ban taɓa ganin tayi faɗa da kowa ba, ko an tsokane ta bata cewa komai ni nake shige mata”. Ajiyar zuciya doctor ya sauke, sanan yace "hmmm eeshat ko baki ce ba zaki aikata fiye da hakan ma, dan naga kina da zafi sosai, kuma nayi mamakin yarda kuke aminta da ita har haka, kuma halin kowa daban". Dariya ma'eeshat tai tare da cewa “hmm kai de bari kawai, amma ina sake gaya maka meenal mace ce mai hankali da tunani duk mijin da ya aure ta a matsayin mata to ya wuta”. Murmushi doctor yayi tare da girgiza kai yace “kai ma'eeshat ke bakya yiwa kan ki shedar nan kenan, gaskiya kina yaban ƙawar nan taki over kullum fa sai kin min zancan ta, ni har gajiya nake”. “hmmmm doctor kenan ba zaka gane ba, amma yanzu nan zan kira maka ita ku gaisa gaskiya ma ya kamata kuka juna koh?”. “no bama sai munga juna ba kawai ki gai da ita”. “A'a sai fa kaga meenal, kana so ka aure ni kuma kace ba zaka ga meenla ba, meenal fa wani sa shi ce na rayuwa ta ina son ta sosai, yarda nake cika ka da labarin ta haka itama nake bata labarin ka, gaskiya ya kamata kuga juna”. “It's okay eeshat yarda kika ce haka za ai, tunda kina so sai mu gaisa, amma yanzu sai na jira tazo, ko gidan su ba nisa?”. “A'a tana fa gidan nan, yau tare zamu ƙwana da ita”. “Tom eeshat da kin barta ta huta ni a ganina bama sai mun gaisa ba”. “A'a gaskiya bazan ji daɗi ba ni wlh ina so kusan juna”. “Tom eeshat ya na iya dake, fatana de kema ki fita kyan hali nan gaba kinji kuma ki dena bani labarin ta haka, ni labarin ki nake son ji”. Wani murmushi ma'eeshat tai, a zuciyar ta tace “tabb ai har na mutu bazan iya halin meenal ba” amma a fili ce masa tai to. Haka de suna hira har suka ƙarasa cikin gidan, ma'eeshat ta kai doctor sitroom bayan ya zauna, tace masa “bari taje ta kira masa meenal ɗin”. Meenal tana kwance akan bed tana chat da waleed, taji ma'eeshat ta murɗa handel ɗin ta shigo rungume da ƙwalin gift. Ajiye wayar meenal tai cikin farin ciki tace “a'a har ya tafi kenan harda gift haka?”. Cikin jin daɗi ma'eeshat tace "a'a bai tafi ba, ke de bari harda gift wlh" ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana ajiye gift ɗin akan gado. "Ah Masha allah, ma'eeshat ta doctor fatan de ya yabar ƙwalliyar" meenal ta tambayi ma'eeshat tana kallon ta?. "kai sosai ma meenal bakiga yarda nai masa kyau ba sai kallo na yake, shi da bai ma cika kallo na. Amma yanzu Kinga tashi ki shirya na raka ki wajan sa ku gaisa, na gaya masa”. miƙewa meenal tai sanan tace “tom shikenan muje, na gaisa da surikina, bari nasa hijab”. Daga haka meenal ta ɗauki hijab har ƙasa ta saka. Cikin mamaki ma'eeshat tace "kai meenal wai yanzu haka zaki fita ji yarda kika wani zurma hijab kamar zaki je gaisuwar mutuwa ko hoda ba zaki shafa ba”. Taɓe baki meenal tai, sanan tace “gaskiya ni a haka zani, to saurayi na ne da zanyi wata ƙwalliya, ni in kika takura min sai na fasa zuwa ma". Hararar ma'eeshat meenal tai sanan tace “to hafiza ƴar ƙaƙida zo mu tafi”. Daga haka meenal da ma'eeshat suka jera abun su. bayan sun sauka ƙasa, kicin ma'eeshat taja meenal ta ɗebo kayan snacks a plate, sanan ta ɗebo ruwa da lemo mai sanyi shima ta sa su a plate. Ɗaya plate ɗin ma'eeshat ta riƙe ɗayan kuma meenal ta rike, sanan suka bi ta wata ƙofar da zata sada su da sitroom ɗin. Baki ɗauke da sallama ma'eeshat ta shiga sitroom ɗin, meenal tana biye da ita a bayan ta. Itama meenal a nitse tayi sallamar. A hankali doctor ya ɗago ya kalli ma'eeshat tare da amsa musu, sallamar. Murmushi ma'eeshat da doctor suka fara sakarwa juna, sannu a hankali ma'eeshat ta ƙarasa wajan doctor ta ajiye masa plate ɗin a gaban sa. ita kuwa meenal tun daga nesa ta tsuguna tare da cewa “ina wuni?”. Doctor ba tare daya ɗago ba fuska a sake yace “lafiya ƙalau, yana danna waya”. Ya mutsa fuska ma'eeshat tai tare da cewa “doctor meenal ce fa, ba zaka ɗago ka ganta ba”. A hankali doctor ya ɗago ya kalli ma'eeshat, bai yi niyar kallon meenal ba, amma ganin yarda ma'eeshat ta haɗe rai hakan ne ya sa shi mai da kallon ta kan meenal. Murmushi doctor ya ƙaƙalo tare da cewa “ya kike?”. Meenal sunkuyar da kai tai tana ɗcewa “alhamdulilah ya hanya?”. Mai da kallon sa doctor yayi kan ma'eeshat sanan yace “hanya alhamdulilah”. Meenal cewa tai “to masha allah, Allah ya temake”. kallon meenal doctor ya sake yi, sanan yace “Ameen”. dan har ga Allah ya yaba da hankali da tarbiyar meenal, kamar yarda ma'eeshat take gaya masa, duk da kuwa shi mace saliha bata birge shi yafi son mai surutu. Ma'eeshat ce ta cafe zance da cewa “tom, itama kai mata congratulations ɗin candy, kuma kaga itama likita take so ta zama kamar kai”. Murmushi doctor yayi sanan yace “masha allah hakan yana da kyau sosai, congratulations”. Jinjina kai meenal tai sanan tace “tom ngd sosai doctor, sai anjima” sanan ta miƙe tsaye. “Au har zaki tafi ai baku gama gaisawa ba?” ma'eeshat ta faɗa tana kallon meenal da ta miƙe tsaye. “eh mun gama gaisawa mana zan shiga ciki ne”. Kallon doctor ma'eeshat tai tana jiran taji me zai ce. doctor kuwa cewa yayi “yauwa eh mun gama gaisawa mana”. “Ok tom shikenan” ma'eeshat ta faɗa cikin farin ciki, itama kuma meenal ta fucewar ta. Sam meenal bata jin daɗi yarda ma'eeshat take tura, ta a wajan doctor ba, bayan taga shi daƙyar ma yake mata magana, shi yasa meenal sau ɗaya ta kalle shi daga haka bata sake kallon sa ba. Bayan maeenal ta fuce, ma'eeshat miƙewa tai ta ƙarasa inda meenal ta ajiye plate ɗin ta ɗauko ta kawo shi gaban doctor, sanan tace “uhmm kayi haƙuri fa doctor, meenal ɗin ce ta cika kunya shi yasa kaga tana wani ɗari-ɗari daga nesa”. Wani kallo galala doctor ya watasawa ma'eeshat yana mamaki, sai yaban halin ƙawarta take amma ita bata iya abunda take yi, shi har ta ishe shi da maganar meenal ɗin nan. Taɓe baki ma'eeshat tai cikin shagwaɓa tace “wai wanan wana kalar kallo kake min sai kace nai maka lefi, duk annurin fuskarka ya ɗauke”. Sauke nunfashi doctor yayi, tare da cewa “please ki mai da hankali muyi magana, ki dena zancan ƙawar nan taki ya isa haka”. Wani kallo galala ma'eeshat ta watsawa doctor, sanan tace “ban gane ba doctor mai meenal tai maka, kake cewa baka son zancan ta, nifa gaskiya in kana sona, to dole ƙawata ta burge ka da halinta, ni ko zan ƙwana ina maka zancan ta, ta cancanta ne, kuma ta wuce haka”. Murmushin dole doctor ya ƙaƙalo sanan yace “no ni ba haka nake nufi ba eeshat, akan me zance ƙawar ki batayi ba, ina so ne kawai yau muyi hira, amma na yaba ha halin ƙanwarki tana da kirki” doctor ya ƙarasa faɗar hakan kamar wanda akai wa dole. Murmushi jin daɗi ma'eeshat tai, sanan tace "yauwa yanzu naji zance na fahimce ka". “Tashi ki zauna akan kujera, nifa zance nazo yau dole muyi zance” doctor ya faɗi hakan cikin son ya basar da zancan meenal ɗin, saboda shi ya gaji da zancan. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace “tom” ta miƙe ta zauna akan kujerar da bata da nisa da doctor. Yanzu de ki gayamin wana course zaki cigaba da karanta. Girgiza kai ma'eeshat tai sanan tace “nifa kaga bana son karatu, nace maka aure nake so”. Murmushi doctor yayi yana mamakin rashin jin kunya irin ta ma'eeshat, kuma yanzu ya gane bama tasan mene auran ba kawai faɗa take. “Tom naji in kinyi auran gaskiya ya kamata ki daure ki cigaba da karatu kuma kema ina so ki karanci course ɗin doctor, ki zama babbar likita”. Murmushi ma'eeshat tai sannan tace” kamar kai kenan?”. “a'a kima wuce ni sosai, saboda nima ina so ki temaki al'umma kamar yarda nake”. “tom shikenan zan duba na gani ko zan iya”. kallon ma'eeshat doctor yayi cike da ƙauna da kuma mamakin yarinta irin ta ma'eeshat. To ma'eeshat da doctor sun sha hira sosai da sosai, kuma sun sha ƙauna da soyayyah, sai da suka ji kamar kar su rabu da juna, da ƙyar doctor ya lallaɓa ma'eeshat, sanan ta yarda suka rabu, kuma sai da ta raka shi har bakin gate, motar ma dan ya hana da har waje zata raka shi. A hanzarce ma'eeshat ta juya ta dawo daga rakiyar doctor tana allah-allah taje ta buɗe gift ɗin daya kawo mata. haka ma'eeshat ta ƙarasa gudu-gudu sauri-sauri, tana zuwa ƙofar bedroom ɗinta, ta murɗa handel, sannan ta afka baki ɗauke da sallama. Meenal tana zaune a gefan gado tana ta shan chat ɗin ta. Tana ganin ma'eeshat ta saki murmushi tare da cewa "haba tun dazu sai jiran ki nake sai yanzu, gaskiya soyayyah tai daɗi sosai”. “Hmmm kede bari meenal, dama haka zance yake da daɗi wayyo yarda kika san kar na rabu da doctor haka nake ji” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana cire ɗan kwali da mayafi ta ajiye su akan gado sanan ta ɗauko gift ɗin ta. “Eh zance yana da daɗi mana ma'eeshat musamman da wanda kake so”. “Hmmm wallahi meenal da daɗi kuwa, amma yanzu de maza mu buɗe gift ɗin nan na tsargu naga menene a ciki har ga Allah”. “Tom shikenan maza ki buɗe mu duba” da sauri ma'eeshat ta kwance igiyar da aka ɗaure gift ɗin sanan ta fara ƙoƙarin bude ƙwalin. Bayan ta buɗe idon ta kan wani farin ƙwali ya fara sauka. dan haka hannu na rawa ma'eeshat ta ɗauka, bayan ta gane ƙwalin mene wata uwar ƙarar farin ciki ma'eeshat ta saki kamar mahaukaciya. Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 20 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Miƙewa tsaye tai tana faman daka uban tsalle. Meenal itama cikin farin ciki ta tashi tsayan tare da cewa “kai haba meenal menene haka kuma, ki tsaya muga i phone nawa ce, daga ganin ƙwalin i phone sai iwu”. Cikin farin ciki baki na rawa ma'eeshat tace “wallahi meenal I phone 17 pro max ce. "What i phone 17 fa kikace ma'eeshat mu gani?". Hannu na rawa ma'eeshat ta miƙawa meenal ƙwalin wayar. "Lah wallahi kuwa i phone 17 pro max ce wow masha allah, kamar doctor yasan burin ki na riƙe iPhone 17 pro max masha allah". “wallahi meenal saboda farin ciki nunfashi da ƙyar nake yi, amma ƙwanaki de muna hira na taɓa gaya masa ina so wayar sosai, amma banyi tunanun sai suyamin yayi min surprised haka ba”. "Wow ma'eeshat abu kamar a mafarki wallahi na tayaki farin ciki sosai ma'eeshat, shikenan muma munyi i phone 17 ɗin nan mun wuce raini". Wata nanauyar ajiyar zuciya ma'eeshat ta saki, kafin kace ƙwabo hawayan farin ciki ya wanke mata fuska. Dafa kafaɗun ta meenal tai, tana rarrashin ta cikin tausasawa. "haba ma'eeshat, meye abun kuka yanzu a cikin nan, farin ciki fa za kiyi kuma ki godewa Allah, sanan ki godewa doctor daya cika miki burin ki”. Share hawayan ta ma'eeshat tai, sanan tace "hmm meenal kukan farin ciki nake yi, dama ashe da gaske ana kukan farin ciki a duniya, meenal ban taɓa sani ba sai yau”. Tom yi shiru de yanzu, ki zauna mu gama buɗe kayan nan mana”. Murmushi ma'eeshat tai sanan tace "tom shikenan meenal amma bari na fara buɗe wayar Koh?”. “A'a ma'eeshat me kike ci na baka na zuba, ki bari ki nunawa mami da abba mana, sai ki buɗe". "kin fini tunani ma meenal, ni na manta da hakan ma to, bari mu ƙarasa buɗewa”. Haka meenal da ma'eeshat suka zauna domin ƙarasa buɗe gift ɗin". Bayan i phone harda i watch, da kuma packed ɗin wayoyin wayoyin kala-kal, sanan kuma ga chocolate masu tsadar gaske dan ƙaramar cikin su ma za tai kimanin 10k. Bayan chocolates ɗin, har da wata doguwar takadar da aka buga mai ɗauke da hoton ma'eeshat ɗin, bayan congratulations ɗin graduation, sanan doctor ya sake jaddda da mata adadin soyayya da yake mata, duk cikin harshan engalish. Bayan wannan kuma, sai wani cup shima mai hoton ma'eeshat ɗin, bayan cup ɗin da akwai kuma wata ƙaramar box mai ɗauke da set ɗin zobuna masu ɗaukar hankali ɗan adam, sai wani walwali suke. Ma'eeshat de ta rasa mai za tai sabida tsananin farin ciki, dan haka tagumi kawai tai ta zubawa kayan ido, tana sake jin ƙaunar doctor tana shiga sassarar jikin ta ko ta ina. Bayan meenal sun gama duba kayan, haɗesu su kai sanan akai mai da su cikin box ɗin. meenal ce tacewa ma'eeshat ta tashi ta kai wa mami da abba su gani, sanan daga bisani ta buɗe ta fara amfani da kayan. Ba musu ma'eeshat ta miƙe hannu riƙe da ƙwalin sanan tace "taso ki raka ni na nuna musu" ba musu meenal ta miƙe suka jera da ma'eeshat zuciyoyin su cike da farin ciki. Mami suka fara nunawa kayan, tayi farin ciki amma ta ɗan tsorata da yarda taga doctor ashmal ya kashewa ma'eeshat wannan uban kuɗin kuma bayan manya masu kai da shiga lamarin ba, bare a tsayar da magana. bayan sun nanawa abba kuwa, shima yayi san barka sosai, sanan yace zai gayawa doctor a cikin satin nan a tsayar da magana manya su shiga, amma kafin nan ma'eeshat ta dakata da amfani da kayan har sai su doctor ashmal sun kawo kuɗin zance. kamar yarda abba ya faɗa, haka akai, a daran ranar ya bugawa doctor ashmal waya, akan ya bashi dama a cikin satin da suke ciki ya turo magabatan sa domin a tsayar da maganar auran su shi da ma'eeshat ɗin. Kai ranar doctor bai iya wani ishashan bacci ba saboda tsabar farin cikin busharar da abban ma'eeshat yayi masa. Kuma gashi yana sake farin ciki ganin yarda ya farantawa ma'eeshat ɗin dan shima har kukan farin cikin sai da tai masa. Ranar de itama ma'eeshat da ƙyar farin ciki ya barta tai bacci. Sai faman sambatu takewa meenal, itama meenal tana biye mata zuciyoyin su cike fall da farin ciki. Haka de har bacci yayi awan gaba da su. washe gari. Bayan ma'eeshat sun yi sallah asubayi komawa bacci su kai, basu suka tashi ba sai wajan ƙarfe goma na safe. bayan sun tashi wanka su kai sannan suka sauka kasa domin breakfast. Kafin su tashi har mami ta gama haɗa musu breakfast. Dan haka ci suka farayi suna ci suna hira. bakin ma'eeshat gaba ɗaya ya kasa rufuwa sai farin ciki take yi, ita ka ɗai ta san adadin farin ciki da take ji a cikin zuciyarta. Bayan sun kammala cin abinci, a gaggauce meenal ta fara shiryawa domin komawa gida. ita kuwa ma'eeshat sai cewa take “A'a ta bari sai rana ta fito”. meenal kuwa ta dage a'a yau da abinda take so tayi a gida kuma gashi yau waleed zai zo wajan ta. Ma'eeshat taso raka meenal, amma meenal tace ta barshi kawai, ta koma tai baccin ta, saboda itama tana komawa gidan bacci za tai. ma'eeshat tayi-tayi da meenal ta ɗauki duk abinda take so a gift ɗin da doctor ya kawo mata, amma meenal tace a'a. Tunda abba yace karta fara amfani da su yanzu, ta bari sai lokacin da ya ɗibar mata. daga haka har bakin mota ma'eeshat ta raka meenal zuciya cike fall da kewar junan su, suka rabu, abin gwanin ban sha'awa, driver ya jasu suka tafi. DOCTOR ASHMAL Yau yana da aiki sosai a hospital, amma saboda yana so yaga dady bai futa da wuri ba kuma bai kunna wayar sa ba. sai kimanin goma ya tashi ya shirya yayi wanka, sanan ya futa falo domin breakfast. A lokacin ba kowa akan table ɗin alamun kowa yayi breakfast. shima doctor cikin nutsuwa ya fara breakfast ɗin nasa, yana yi yana tunanin ma'eeshat. doctor yana cikin wanna halin momy ta ƙaraso wajan baki ɗauke da sallama. "Wa'allaikissalam momy ina ƙwana?". Fuska cike da murmushi momy tace "lafiya ƙalau doctor, yau naga baka futa da wuri ba, nace to lafiya?". “Ah ba komai momy zan fita ne amma ina so muyi magana ne da dady kafin na fita shi yasa na jira lokacin tashin sa yayi”. "Ai kam kaci sa'a de bai kai da futa ba, yana shiryawa de amma bari naje na gaya masa Koh?". “Tom shikenan momy kiyi masa magana”. daga haka momy bata sake cewa komai ba ta koma ciki domin kiran dady. Ba'a ɗauki wani dogwan lokaci ba, dady ya futo cikin shirnsa. cikin girmamawa doctor ya gai da shi, bayan sun gama wasan su na ɗa da uba komawa su kai gefe domin tattaunawa. "Yauwa doctor ina sauraran ka meke tafe da kai?". Gyara zama doctor yayi cikin ladabi da tausasa murya yace "amm! dama dady akan maganar yarintar nan ce da nace maka ina neman auran ta, da ƙwanaki na maka maganar ta". "Ah haka ne tabbas munyi haka, wanda nace kuje ku dede ta, yanzu ina aka ƙwana dama ina so na sake yi maka maganar very soon dan momyn ka ta damu da zancen sosai". "ƙwarai kuwa dady ita, amm yanzu finally de cikin ikon uban giji mun gama dedetawa kuma iyayan ta sun ce na turi a wanan satin domin a tsaiyar maga da ranar aure. Cikin farin ciki dady yace "ah masha allah alhamdulilahi bi ni'imatika, wannan labari yayi daɗi doctor, masha allah, in sha allah kamar yarda kace cikin wanan satin za’a tsayar da maganar auran ku nan kusa ma, bada jimawa ba". Wani farin ciki ne ya sake lulluɓe zuciyar doctor, amma sai ya basar yace "tom shikenan dady Allah ya nuna mana lokaci, amma wace rana akai za a saka domin tsai da zance?. "Ina tunanin friday ɗin nan mai zuwa in sha allah, za’a sa maka ranar aure doctor". Jin jina kai doctor yayi sanan yace "tom dady Allah ya kai mu ya tabbatar da alkhairi". “Ameen ya rabbi doctor ai zama bai kama ni ba bari na shiga nai wa momyn ka farin albishir". Daga haka dady ya tashi da sassarfa ya shige ciki. murmushi mai aji doctor ya saki, sanan ya miƙe zuciyarsa cike da farin ciki ya koma bedroom ɗin sa, a hanzarce ya shirya sanan ya ɗauki wayoyin sa da mukullin motar sa harma da laptop ɗin sa yayi gaba abin sa........ MEENAL Ta riga ta gama shiryawa tsaf cikin lace ɗin ta mai ɗumbi tsada da daraja tayi kyau sosai ɗaurin ɗan kwalinta ma yayi kyau, ya kwanta yayi biyayya. dama in de ɗaurin ɗanƙwali kake so, to tabbas in ka samu meenal an ƙare zance. Ta fesa turaranta mai sanyi ƙamshi, sanan ta ɗauko madedecin mayafin ta, ta yafa jikin ta da shi sosai. Haka de meenal ta cigaba da shiryawa ta gyara wanan ta canza wanan har wayarta ta fara ringing. A hankali ta tashi tsaye sanan ta ɗauki wayar ta kara a kunne. "hello meenal gani na ƙaraso ina ƙofar gida". "tom shikenan gani nan fitowa". Daga haka meenal ta kashe wayar ta ajiye. Sannan ta saka takalmin ta daya shiga da kayanta, ta shiga tai wa baba da umma sallama sanan ta fuce. A hankali meenal ta fara tafiya domin ƙarasawa bakin motar, tun kafin ta ƙarasa waleed ya buɗe mata gidan gaba, meenal batai musu wajan shiga ba saboda sanyi ake yi. Bayan ta zauna sallama tai masa, shi kuwa waleed da ya saki baki galala kallon ta ya farayi sanan ya amsa sallamar da ƙyar. “I miss you my love” murmushi meenal tai, sannan tace “miss you too”. “Komai ya kusan ƙarewa in sha allah, munyi magana da baba yace zai binci ke akai na, a cikin wanan satin, next week kuma in ya kammala bincike sai a tsayar da magana, month nawa kike so asa?” "one year nake so a saka". “what!” waleed ya faɗa yana zaro ido. cikin mamaki meenal tace "lafiya kuma ko yayi kaɗan ne?". "tabb kaɗan ko yawa ni da nake so asa mana 3 moths ma nifa wallahi a matse nake, burina kawai ki zama matata, ke kaɗai kika rage min farin ciki a rayuwata, mahaifi na da mahaifiyata sun rasu, bani da yaya bare ƙani sai ƴan uwa kawai, burina na aure ki mu tara zuri'a dake nayi farin ciki ni da ke”. Meenal ji tai kamar ta zubarwa da waleed hawaye saboda tsabar tausayi, cikin sanyayiyar murya meenal tace, "in sha allah waleed zan mayar maka da farin ciki da ka rasa, ko bai zama duka ba zan ɗauke maka kewa". "Yauwa meenal nagode sosai da sosai Allah ya saka da alkhairi Allah ya nuna mana lokacin da zamu zama mata da miji". “Ameen ya rabbi, ya hanya fatan ka sauka lafiya?”. “Lafiya ƙalau alhamdulilah my wife”. To haka waleed da meenal su kai ta sha hirar su cike da soyayyah da ƙaunar juna, sai da su kai 1 hour suna hirar su cike da soyayyah. ƙarshe de meenal tace “ita fa dare yayi gida zata shiga”. Waleed miƙa mata leda yayi guda biyu, ɗaya ƙarama ɗaya babba. Kallon sa meenal tai sanan tace "menene wanan?". “Ki bari in kika je gida sai ki buɗe ƙaramar ledar de ƙawarkice ma'eeshat tace na siya miki”. Hannu biyu meenal tasa ta ƙarba sanan tace “tom nagode, allah ya saka da alheri ya sake buɗi”. "Ameen ya rabbi matata, kin wuce haka a waje na, duk abinda na mallaka naki ne" waleed ya faɗa cikin farin ciki. daga haka su kai sallama meenal ta shige gida, shi kuma waleed ya tayar da motar sa ya wuce. meenal har zuci-zuci ta koma gida take domin taga mai waleed ya kawo mata. Tana komawa cikin gida direct ɗakinta ta wuce, sanan ta cire mayafinta. Bayan ta cire mayafinta kan bed ta koma ta zauna, sannan fara buɗe ƙaramar ledar saboda tana so taga mai ma'eeshat ɗin tasa waleed ya siya mata.......... Sorry mutanan arziki, yarda ku kayi missing ɗin littafin doctor ashmal, nima haka nake missing ɗin yi muku posting. Dan Allah dan annabi duk wanda ya karanta posting ɗin nan, ina neman addu'ar sa akan Allah ya biya mun buƙatuna na alkhairi ya yaye min abinda yake damuna, ya tabbatar min da alkhairi akan abinda nasa gaba. dan Allah ku sani cikin addu'a, ko a lokacin da kuka karanta ne kuyi min, addu'a ko kuce Ameen. Ina muku fatan alkhairi, kuma Allah ya biya muku buƙatun ku na alkhairi, in kuna da damuwa Allah ya yaye muku, ya samu cikin aljannah baki ɗaya, yasa mu cika da kyau da imani. Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 21 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ƙamewa meenal tai ƙam saka maƙwan ganin ƙwalin i phone 17 pro max, a fili ta furta “ya salam”. “innalillahi wai shi waleed baya gajiya da kashe min kuɗi ne, sai yayi ta kashe min kuɗi kamar ruwa” meenal ta faɗi hakan a zuciyar ta. “hmmm ma'eeshat mai yasa kika sa waleed nima ya siyamin I phone 17 pro max. A cikin zuciyarta meenal take faɗin hakan. Bama ta samu damar buɗe ledojin ba ta ɗauka takanas ta kano ta kai wa umma da baba. baba da umma sun tsora ta sosai musamman ma da suka ji adadin kudin wayar. Da baba yacewa meenal ta kirawo waleed yazo ya ƙarbi kayan da ya kawo mata, kuma daga yau kar ya sake kawo mata komai sai in sunyi aure ya siyar mata. Umma ce ta lallaɓa baba tace masa yayi haƙuri ba kyau mai da hanaun kyauta baya, amma zata iya ajiye duk abinda yake kawo mata in sunyi aure sai ta fara amfani da su. Sai ta gaya masa daga yau ya dakata da kawo mata kayan da yawa kamar haka, in su kai aure ya cigaba da siya mata. dole baba ya yarda badan ran sa yaso ba,. ita kuwa meenal komawa bedroom tai jiki a sanyaye, sanan ta bugawa waleed domin tai masa godiya. Washe gari kamar yarda baba ya faɗa da asubar fari bayan yayi sallah ya shirya tsaf domin tafiya burnin tarayya (Abuja) domin binciken waleed. waleed ya bawa baba address ɗinsa na wajan aiki da gidan da yake zama da duk de inda yake rayuwarsa acan abuja. Zo kaga murna wajan waleed, kamar yai take ɗaurin auran su shi da meenal. saboda Waleed yasan bashi da wani mummunan ɓoyayyan hallin da baba zai hana shi auran meenal, yasan shi me kyan hali ne ko ta ina. Itama meenal ɗin farin ciki take sosai, ranar baki yaƙi rufuwa har umma ta gane ta, sai tsokanar ta take yi. Meenal taji kunya umma sosai dan haka ba shiri ta shirya tsaf tace itafa wajan ƙawarta ma'eeshat za taje. After 2 week Yau ta kasance ranar friday, kuma yau baba zai dawo gida. Kuma yau ta kasance itace ranar da za'a sawa ma'eeshat rana ita da doctor ashmal. Misali ƙarfe 4 na yamma motocin magabatan doctor ashmal suka faka a layin su ma'eeshat. Ma'eeshat da take sama tana leƙe murna take sosai har da tsalle, meenal kuwa sai dariya take mata daga gefe tana cewa Allah ya shirya ta. Dama already abokai da ƙannan abba sun zo, kafin kace ƙwabo tuni an cika wajan da abubuwan ci da sha, abinci iriri kaji lemuka, snacks, dade sauran abubuwa. Bayan sun shigo cikin girmamawa aka hau gaisawa dangi doctor ashmal dana ma'eeshat. To masha Allah an tsayar da ranar auran ma'eeshat da doctor 8 moths shima hakan da ƙyar sai da akai ja in ja. saboda shi dadyn doctor yace nan da 6 moth, shi kuma abba yace yafi son asa one year, saboda yana so kafin nan ma'eeshat ta fara zuwa school, in akai auran kawai cigaba da karatunta za tai. Bayan de nan kawai sai dady yace to a ƙara 2 moths kawai ya zama 8 moths. abba ba yarda ya iya saboda yaga mutuncin mahaifin doctor sosai saboda datijjan arziki ne baze iya ja da shi ba bare sauran mutanan wajan dan haka dole abba ya amince. Bayan an tsai da magana aka bada kuɗin neman auran ma'eeshat 1 millon. Bayan nan abba yace ya kamata su zauna suci abinci tare domin su sake fahimtar juna kuma suyi hira. ba musu su dady suka zauna. Haka kowa ya zuba abinda yake so aka fara ci. Sunci sun ƙoshi sosai da sosai, sanan sunyi hira har sai da magriba ta kawo kai sannan su kai sallama domin tafiya. Bayan nan ma an bisu da kayan sa rana abubuwan arziki de sosai. su dady kuwa sunji daɗi sosai, da karamcin dangin su ma'eeshat. Hmmmm ma'eeshat ta kasa rufe baki saboda farin ciki, sai farin ciki take faman yi ta kusan auran doctor ashmal sai kace wanda ake mintsilar ta a gidan su. Itama meenal taji daɗi sosai da sosai, duk da itama tasa nan da 'yan ƙwanaki za'a sa mata rana ita da waleed. A ranar ma'eeshat ta farke wayarta i phone 17 domin fara amfani ni da ita. haka meenal ta zauna tana saita mata i cloud, saboda ma'eeshat bata iya. Ma'eeshat sai faman mita takewa meenal akan itama ta farke wayarta su fara amfani da ita tare. meenal ta yarda amma tace itama sai ranar da aka sa musu rana ita da waleed tukunna, ta fara amfani da ita. Bayan sallah magriba meenal tashi tai domin tafiya, saboda tasan a lokacin baba ya dawo daga abuja kuma tayi missing ɗin shi sosai. kamar kullum haka ma'eeshat ta raka meenal bakin mota zuciya cike da kewar juna……. DOCTOR Hmmmm tsayawa ma na gaya muku farin ciki da doctor ashmal ya shiga, na sa musu ranar auran su shi da ma'eeshat ɓata baki ne. Doctor yayi farin ciki sosai, duk da doctor bashi da yawan fara'a kuma ba'a gane me yake zuciyar sa, amma duk wanda yaga doctor yasan yana cikin matsanancin farin ciki. Ranar su da ma'eeshat sun sha soyayya yarda ba'a tsammani, sai da doctor ya kusan kashe ma'eeshat da mamaki dan bata taɓa tunanin haka ya iya soyayyah da magana ba sai yau, kusan ƙwana de su kai suna waya. MEENAL Driver yana sauke ta, da sauri ta futa ta kutsa kai cikin gidan su, zuciya cike fall da zumuɗi. Zaune meenal taga umma akan dadduma ga dukkan alamu sallah ta gamayi amma ta tafi dogwan tunani. sau uku meenal tana sallama amma umma bata ji ba, gaba ɗaya ta tafi duniyar tunani. Sai da meenal ta ƙarasa, ta tsugana ta dafa ta, sannan umma firgigit ta dawo daga dogwan tunanin da ta tafi. cikin mamaki meenal tace "lafiya ummata naga kin tafi dogwan tunanin nan haka, ke da kike hanani tunani amma yau ke kike yi?". "hmmm yau da gobe meenal mutum yana ɗan adam ai dole yayi tunani, kawai nace miki ba kyau yawan tunani yana haifar da cuta ko damuwa". Jinjina kai meenal tai tare da cewa "eh na gane". "Tun dazu nake zuba ido kince min zaki dawo da wuri wajan huɗu zuwa biyar, amma sai yanzu kika shigo, nai ta jiran ki wallahi". “Hmm ma'eeshat na tsaya taisawa sabuwar wayata shi yasa kika jini shiru". "Tom ba damuwa an sa ranar auran koh?" Eh an sa nan da wata taƙwas". Jinjina kai umma tai sanan tace "allah ya sanya alkhairi" "ameen umma wai naga gaba ɗaya kin canza kamar wani abun yana damin ki" meenal ta ƙarasa maganar tana riƙe hanun umma. Murmushi dole umma ta ƙaƙalo sanan tace “ba komai kawai bana jin daɗi ne". "Kode baba bai dawo bane?," meenal ta tambaya umma tana tsare ta da kyawawan idanuwan ta. "baban ki ya dawo meenal, ya fita masallaci ne amma yanzu zai dawo, har ya tawo miki da tsaraba iri-iri. Washe baki meenal tai "ah masha allah alhamdulilahi, me yace miki game da binciken da yayi akan waleed?". Jim umma tai sanan ta girgiza kai tace "a'a ni bamuyi wanan zance da shi ba cemin yayi sai kin dawo zai faɗa". "Wayyo Allah Sarki baba na, bani da kamarsa duk duniya wallahi ina son ku umma” meenal ta faɗa tana rungume umman". murmushi umma tai sanan ta shafa bayan meenal tana cewa, "mu ma muna son ki meenal, Allah yayi miki albarka, maza ki tashi kije ki huta kafin baban naki ya shigo". Sakin umma meenal tai sanan tace “to” daga haka ta wuce ta ɗakin ta, zuciyar ta cike da farin ciki. Bayan meenal ta koma bedroom, waya suka farayi da waleed sosai suke, hirar su har baba ya shigo. Sai wajan ƙarfe 10 sannan waleed ya rabu da meenal, shima saboda ita ta buƙaci hakan. Bayan sunyi sallama da waleed cikin farin ciki meenal ta nufi ɗakin su baba da umma. Tsayawa tai kamar yarda ta saba in suna ciki, ta fara sallama. Haka meenal tai ta sallama har sau uku amma shiru kake ji, meenal tunda taji shiru tasan sunyi bacci, dan haka juyawa tai ta koma bedroom ɗin, ta cigaba da chat ita da waleed. Washe gari. Meenal bayan tayi sallah asubayi bacci ta koma saboda bai ishe ta ba, wajan ƙarfe 11 ta tashi, sanan tai wanka tai brush, bayan ta futo ta shirya direct kicin ta nufa ta zuba abinci taci. meenal tayi mamakin da bataga umma a tsakar gida ba saboda kullum in ta tashi a tsakar gida ko a kicin take ganin maman ta. Bayan meenal ta kammala komai bedroom ɗin su baba ta sake komawa ta fara sallama, kamar yarda suka koya mata. bayan baba ya amsa sallama bata izinin shigowa yayi. Fuska cike da annuri meenal ta kutsa kai cikin bedroom ɗin, lokacin umma tana ƙwance akan gado kamar mai bacci, amma meenal bata gama tantance, baccin take ba ko kuwa. shi kuma baba yana zaune a kan sallaya yana jan carbi ga dukkan alamu sallar walaha ya kammala. Meenal bayan ta ƙarasa gefan baban tsugunawa tai har ƙasa sanan tace "baba ina ƙwana fatan ka tashi lafiya". Murmushi baba yayi sanan yace "lafiya ƙalau hajiya kema tafan kin tashi lafiya?". "Alhamdulilah baba ya hanya kuma fatan ka dawo lafiya?". “Hanya alhamdulilah aminatu na dawo cikin ƙoshin lafiya". Murmushi meenal tai sanan tace "masha allah baba, fatan de komai ya tafi yarda ake so koh?". Jim baba yayi kafin yace "meenal ina so na gaya miki ko wana bawa da jarrabawar sa kuma komai sai allah ya nufa akeyin sa, meenal nasan ke me haƙuri ce kuma mai tawakkali, kuma nasan kin sanya kamata koh?". Gyaɗa kai meenal tai sanan ta sake sunkuyar da kai ƙasa tana cewa "gaskiya ne baba". jinjina kai baba yayi sanan ga gyara zama, bayan yayi shiru na wasu lokuta yace "meenal a matsayina na mahaifin ki, ina umartar ki daga rana mai kamar ta yau na rabaki da waleed babu ke babu shi”. Kuyi haƙuri da wannan page ɗin yau bai gama cika ba. Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 22 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 A gigice meenal ta ɗago kai, baki na rawa tace “baba waleed fa kace?”. "ƙwarai meenal waleed nace miki, bana so wata ma'amala ta sake shiga tsakanin ki da shi". Cikin gigita meenal tace "inalillahi wa inna'ilaihirraji'un baba mai waleed ya aikata mai yayi dan allah?" "Nide aminatu, na gaya miki ki fita daga sabgar waleed sanan ki tarkata masa gaba ɗaya kayan daya baki, ki mai da masa abinsa". Cinkin tsananin kuka meenal tace “baba wai mai waleed yayi maka haka kake ƙoƙarin raba ni da shi ne?”. “aminatu ni fa baban ki ne bazan taɓa aikata abinda zai cutar da ke ba, kuma zan iya sanin abinda ke ba lallai ki sani ba, bai kamata kizo ki titsiye ni akan sai na gaya miki dalilin daya sa na rabaki da waleed ba, amma a taƙaice de kisan waleed ba mutumin KIRKI BANE, ba mijin auran ki bane”. Zaro ido meenal tai cikin tsananin ruɗu da kiɗimewa tace "baba wlh waleed mutum kirki ne, baba mai waleed ya aikata da zaka hanani auran sa haka? baba wallahi ko wana kalar hali ne da waleed naji na yarda na amince zan rayu da shi a hakan, baba waleed bashi da iyaye bashi da wani farin ciki sai ni baba dan allah kar kai haka waleed mutuwa zaiyi in be same ni ba”” “Ke aminatu dama haka kika koma? yaushe ki kai girman da zakiyi sa in sa dani, ina gaya miki kina gayamin, ke kika haifi kan ki ko mu muka haife ki, ni mahaifin kine kuma ya zama dole na zaɓa miki abinda ya dace dake, wanda ko bayan ran mu ni da mahaifiyar ki zaki samu farin ciki. Ke kaɗai muku haifa, ya zama dole mu gina miki rayuwar da zata amfane ki ko bama doran ƙasa. dan haka umar ni nake baki ba shawara ba, ki rabu da waleed na har abada”. Baba ya ƙarasa maganar cikin faɗa sosai, duk da kuwa bai taɓa yiwa ɗiyar tasa faɗa ba. Daga haka a fusace baba ya tashi ya fuce yabar gida. Ɗora hannu bibbiyu meenal tai a kan ta, ta saki wani gigitaccan kuka murya na rawa tace "na shiga uku inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un baba me kake ƙoƙarin aikata mana ni da waleed?". A hankali umma ta sauko daga kan bedroom ɗin jiki a sanyaye, ta ƙaraso kusa da meenal ɗin sanan ta tsuguna tana dafa kafaɗun ta bibbiyu, cikin tausayawa umma tace "meenal ki nutsu mana dan Allah ki dena wanan kukan kiyi haƙuri". “Dan Allah umma ki gayamin dalilin daya sa baba yake ƙoƙarin rabani da waleed, ki gayamin wana hali waleed yake da shi da baba ya kasa gayamin ko zan samu sukuni?". Jiki a sanyaye umma tace "wallahi meenal ban sani ba nima yarda yayi miki bayani haka jiya yayi min bayan ya dawo, wai waleed ba mijin aure bane. Sam yaƙi gayamin dalilin,. shi yasa jiya da kika dawo kika same ni cikin damuwa. tun jiya baban ki yayi ƙoƙarin gaya miki, da daddare bayan ya dawo, na hana shi hakan saboda kar ki kasa bacci muna jinki kina sallama mu kai shiru. Dan Allah meenal kar kisa komai a zuciyarki, ki zama mai tawakkali dama kina da shi ki ɗauki wannan a matsayin kaddarar rayuwarki kawai komai mai wucewa ne watarana sai labari”. "wallahi umma bazan iya ba damuwa kuwa na shige ta tun daga yau har ƙarshan rayuwata, in baku aura min waleed ba, ina son shi a haka ko wana irin hali ne da shi”. “Haba meenal ke kaɗai Allah ya bamu in kika shiga damuwa muma mun shiga dan Allah kar kisa wanan a ranki, in Allah yayi waleed mijin ki ne sai kiga Allah ya dedeta komai" umma ta ƙarasa maganar tana kuka. Itama meenal wani irin ihu da gunji kuka ta saki mai karya zuciyar mai sauraro "inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah in wani laifi nai maka ka jarrabi ni da wanan masifa allah na tuba ka yafe muni”. Cikin kuka mama tace, "auzubillahi meenal, baki da hankali ne wai, kar ki sake kiyi saƙo ko ki faɗi abinda zai futar da ke daga musulinci ki sauri ki tuba maza?". Cikin tsananin kuka meenal tace “allah na tuba, Allah ka dubi halin da nake ciki da maraicin waleed ka kawo mana sauƙi cikin wanan musibar”. Umma tayiwa meenal rarrashi duniya amma ina meenal taƙi tai shiru, daga ƙarshe ma meenal tashi tai ta koma bedroom ɗin ta, hankali a tashe ta ɗauki wayarta ta dannawa ma'eeshat kira. Sai da ta kusan tsinkawa sanan ma'eeshat ta ɗauka tare da sallama. Meenal ko damar amsa sallamar bata samu ba cikin kuka ta fara magana "ma'eeshat kina ina ne?". “Ina gida mana lafiya naji ki kina kuka mai ya faru?" "ma'eeshat wannan maganar bata waya bace dan Allah ki sauri yanzu kizo ina cikin tashin hankali da ban taɓa shigar irin sa ba a rayuwa". "Innalillahi meenal mai yake faruwa ki gayamin mana" ma'eeshat ta faɗa cikin tsanani tashin hankali". "Nace miki maganar nan bata waya bace kizo kiji abinda yake damuna kafin zuciyata ta buga na mutu na wuta da baƙin cikin nan". cikin wani saban tashin hankali ma'eeshat tace "inalillahi meenal gani nan zuwa bani 10 minutes" daga haka ma'eeshat ta gimtse wayar, ita kuwa meenal ci gaba da kukan ta tai. Tana cikin wanan halin taji wayarta ta fara ringing, ido jajiri meenal ta kalli wayar, ai kuwa sake fashewa tai da wani rikitaccan kuka ganin waleed ne yake kiran ta. “Allah sarki waleed bawan allah sai sake kiran meenal yakeyi amma ina meenal ta kasa ɗagawa ma. Meenal tana cikin wanan halin ba'a fi 25 minutes ba ma'eeshat ta rafka sallama hankali tashe ta shigo ɗakin meenal ɗin. Meenal tana ganin ma'eeshat ta sake rafka wani uban kuka mai cin rai". In hankali ma'eeshat yayi dubu ya tashi, dan haka da sauri ta ƙarasa wajan meenal ɗin". Cikin tashin hankali ta rungume ta tare da cewa "meenal meye haka yake faruwa inalillahi" meenal kuwa tana so tai magana amma ta kasa kuka sai cin ƙarfin ta yake. cikin tashin hankali da tausaya ma'eeshat ta sake rungume meenal tare da bibbiga bayanta alamun rarrashi. Cikin ƙwantar da murya ma'eeshat ta fara magana "haba meenal menene haka dan Allah ki kwantar da hankaliki, ki gayamin mai yake faruwa, wanan kukan bashi da wani amfani ki gayamin ko zan iya yi miki magani. Dan Allah kiyi haƙuri ki dena kukan nan wallahi nima hankali na a tashe yake da ƙyar nake iya maganar nan yi shiru meenal dan Allah ki dena kukan nan haka". Daga haka ma'eeshat ta saki meenal ta fara goge mata hawaye da hannun ta tana rarrashi. Har sai da meenal ta samu ta dena kuka, sai ajiyar zuciya take saukewa idon nan nata yayi luwu-luwu kuma yayi jajir abun tausayi. Cikin rarrashi ma'eeshat ta riƙo hanun meenal tana shafa shi murya a sanyaye tace "meenal ki dena kuka ki gayamin abinda yake damun ki ko zuciyata zata samu sukuni”. ma'eeshat ta ƙarasa magana idon ta yana zubar da zafafan hawaye. Haɗiye wani zazzafan yawu mai tsananin ɗaci meenal tai, sanan cikin rawar murya tace "ma'eeshat baba yace bazan auri waleed ba ya raba ni da shi har a bada” meenal ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani saban kuka. Cikin mamaki ma'eeshat tace “waleed kuma inalillahi saboda me, haba meenal kar kice haka nasan baba baze taɓa yin haka ba ko wasa yake miki ne, akan wana dalilin ma zai rabaki da Waleed?”. “Wallahi ma'eeshat yarda kika ji hakane ba wani wasa, ai kin san yaje abuja binciken waleed, shine yau da safe yake cewa na rabu da shi, da na tambaye shi dalili yace wai kawai bashi da kyan hali, kuma ba mijin aure bane”. "Innalillahi meenal yaya waleed kuma, gaskiya ban san yaya waleed da wani mummunan hali ba, maman shi fa yayar mami ce, kin san da nasan waleed yana da mummunan hali bazan taɓa bari ku fara soyayya ba har maganar aure ta shiga" ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye. "Wallahi ma'eeshat nima nasan haka, kuma ko za'a ƙwana ana cemin waleed bashi da hali bazan yarda ba, in de ba gani nai da ido na ba". Share waye ma'eeshat tai sanan tace “A'a meenal sanin halin mutum sai Allah ai baba bazewa waleed ƙaraya ba, tunda ba wanda yasan zahirin halin sa, kuma ba anan yake zaune ba, ba bin sa abujan muke ba”. “Haba ma'eeshat in de kika yiwa waleed wanan mummunar fahimta baki kyauta ba, ke fa ƴar uwar sace ta jini, ni da nake bare ma nai masa shedar arziki bare ke". "Hmmmm inalillahi wallahi meenal akwai damuwa mai tsanani ni bama ta ke nake ba waleed shine abun tausayi ba uwa ba uba gashi a rabaki da shi kin san kuwa tsananin son da yake miki, duk kunyar da waleed yakewa mami wallahi baya ji ta akan soyayyar ki. meenal waleed ya riga da ya mutu akan sanki, kuma gashi kun dace ni naso ace, naga ranar auran ku wanan masifa dame tai kama" ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka. itama cikin kuka meenal tace "wallahi na sani in bani a rayuwar waleed mutuwa zaiyi, nima bazan iya rayuwa babu shi ba ma'eeshat ina son waleed a rayuwata fiye da komai wallahi in na rasa waleed rayuwata ta ƙare har abada wayyo na shiga uku". Haka meenal da ma'eeshat suka haɗu suka ringa rusa uban iwu, kamar an musu mutuwa, sun jima suna kuka kafin umma ta shigo ta rarrashe su da ƙyar. Meenal kuwa duk sanda taga waleed ya kira sai ta sake fashewa da wani iwu mai cin rai, daga ƙarshe de kawai kashe wayar kawai tai. Ranar de ma'eeshat wuni tai tana rarrashi meenal kuma ta ɗan ƙwantar mata hankali akan zata je ta samu su mami da abba ko allah zai sa suyiwa baba magana ya amince, ade zo a sasanta. ƙarshe de ma'eeshat da taga meenal ta damu dole cewa tai zata ƙwana tare da ita zuwa gobe. Hirar duniya ma'eeshat takewa meenal saboda ta saki ranta amma ina, ko yaro yaga meenal yasan tana cikin tsananin damuwa a ranar kuwa, meenal bata iya bacci ba, saboda tasan waleed yana can hankalin sa a tashe yau bai ji muryar ta ba. Washe gari. Gaba ɗaya meenal ta kasa samun nutsuwa a rayuwarta, sai kuka take yi ta kasa ci ta kasa sha zancen ta waleed kawai, ma'eeshat har ta gaji da rarrashi dan haka ta yanke shawarar taje ta sanar da su abba abinda yake faruwa dan haka ba ɓata lokaci tai wa meenal sallama ta wuce gida. Hankali a tashe ma'eeshat ta koma gida bayan ta koma ba tai ƙasa a guiwa ba ta bawa mami labarin abinda ya faru hankali tashe. Ba shiri mami ta fara salati kafin kace kwabo hankali ta ya tashi. Mami taso ta bugawa waleed domin tabbatar da hakan amma ma'eeshat tace mami ta dakata, saboda in ta gayawa waleed hakalin sa tashi sai yi abu komai a sannu. Yarda kasan mami tai kuka sam ta kasa gane gaskiya lamarin, kuma tasan baban meenal baze faɗi abinda be bincika ba. Lokacin da abba ya dawo aka bashi labari, baiyi wani dogwan nazari ba ya amince da zancan baba, yace baze yu kuma ai auran meenal da waleed ba saboda shima ya ɗauki meenal matsayin ƴar, kamar yarda waleed yake ɗansa, dan haka baze shiga lamarin aka ayi aure waleed da meenal ba. Saboda baze sa baki akan abinda be dace ba, baba yayi dede, amma in ya samu lokaci zai je wajan baban domin yaji menene ɓoyayyin munanan halin waleed ɗin. Hmmm zo kaga tashin hankali wajan ma'eeshat, nan da nan ta fara kuka wiwi. MEENAL Kamar jiya yau ma bata iya wani cin abinci kirki ba, sai da umma ta takura mata tukunna, tayi wani zuru-zuru kamar mara lafiya, kana ganin meenal kasan tana cikin tsananin tashin hankali. shima baba da umma hankali su ya tashi ganin halin da meenal ta shiga, amma ba yarda suka iya dole sai rarrashin kawai. Yau ma meenal bata iya bacci ba tana can tana tunanin waleed hakan ma dan ta kashe wayar, ƙwana tai tana kuka. Washe gari. Hankali meenal ya sake tashi sosai bayan da su kai waya da ma'eeshat, ma'eeshat ta sanar da ita abinda abba yace, yana goyan bayan baba. Yau ma wuni tai tana kuka ta kasa komai. Da magriba meenal tana tsugune a bakin rariya tana ɗaura alwala domin sallar magriba. ɗagowa meenal tai, saboda jin sallamar wani yaro. Amsawa meenal tai tare da cewa "lafiya ko aiko ka akai wajan umma?. “A'a wai wani ne a waje yace wai yana sallama da meenal in ji waleed”. gaban meenal ne ya faɗi rasss, rasss, rasss, har sau uku dan saboda tsabar tashin hankali kasa cewa komai tai. Umma kuwa da take nesa cewa tai "kaje kace gatanan zuwa". Bayan yaran ya fita idon meenal cike da hawaye tace “umma ba baba ya hanani kula sa ba sabo da me kika ce haka dama kin bari an gaya masa bazan futo ba kawai". Meenal ta ƙarasa maganar tana zubar da zafafan hawaye, jiki a sanyaye umma tace "eh shi yasa yanzu nake so ki sauri ki futa, kice masa ya dakata da zuwa, nan da wasu ƴan lokaci, ki sauri kafin baban ki ya dawo". Jiki na rawa meenal ta amsa da to, ta shiga ɗaki da sauri ta ɗauko hijab ɗinta. Bayan tasa hijab ɗin jiki na rawa, meenal ta fita saboda itama ta matsu tasa idon ta cikin na waleed ɗin............ Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 23 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Jiki a sanyaye meenal ta fita, tun daga nesa ta fara ganin waleed ya faɗa duk yabi yayi wani zuru-zuru abin tausayi. tun kafin meenal ta ƙarasa waleed yake sakar mata wani tattausan murmushi. Meenal kuwa idon ta yayi jajir fuskar nan tata ta kumbura, tun daga nesa ƙwalla ta taru a idon meenal, saboda tsantsar tausayin waleed ɗin. Ko data ƙaraso gefan waleed ta tsaya ba tare da tace komai. "Meenal ɗina mai yake faruwa naga gaba ɗaya kamar bakyajin daɗi ko ɗan murmushi baki min ba bare sallama, har azo da gai suwa kuma". Ƙaƙalo murmushin dole meenal tai kamar yarda waleed ya buƙata. "Ina wuni?" meenal ta faɗa cikin tsananin ƙarfin hali,. "Lafiya ƙalau babe wai mai yake faruwa ne too days naga gaba ɗaya bana samun ki a waya ko na kirawo ki a kashe, kuma yanzu nazo naga gaba ɗaya bakyajin daɗi". Meenal bata san sanda wasu zafafan hawaye suka fara bin fuskarta ba. a gigice waleed yace "haba meenal mene haka, kinga yarda kika tada min hankali kuwa mai yake faruwa ko baki da lafiya ne?". Girgiza kai meenal tai hawaye ɗaya na bin ɗaya. "Dan Allah meenal ki dena kukan nan meye haka Please ki kwantar da hankaliki ki gayamin me yake faruwa ko wayar taki ce ta lalace na siya miki wata?". Meenal bata san sanda kukan tausayin waleed ya ƙwace mata ba, du du du yaushe ya siyar mata sabuwar wayar mai ɗumbin tsada wanda ko buɗe ta batayi ba, amma har ya fara tunanin wayar tace ta lalace. "Dan Allah meenal ki nutsu ki gayamin abinda yake damun ki wallahi bana so na ganki cikin mumunan hali". Hawayenta meenal ta share da hijab, sanan ta share majina murya na rawa tace " yaya waleed kayi haƙuri akan abinda zan gaya maka yanzu?". Baki na rawa waleed yace "ba komai meenal gayamin mai yake faruwa"?. cikin shasheƙar kuka tace, shekaran jiya bayan baba ya dawo daga abuja, baba yace min na rabu da kai wai kai ba mijin aure bane baka da kyan hali" meenal ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani matsanancin kuka. Zaro ido waleed yayi ya dafa ƙirjinsa cikin matsanancin tashin hankali baki na rawa yace "ni kuma meenal, anya kin san mai kike fada kuwa nine fa waleed ɗin ki". Cikin kuka meenal tace "wallahi waleed da gaske nake". A gigice waleed ya cire wular kansa, ya fara fifita da ita cikin tashin hankali ya fara ɓalle maɓallan rigarsa yana fifita da hula murya na rawa ya fara cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un allahumma ajirnifi musibati, meenal! meenal! meenal! wallahi ni mutumin kirki ne, meenal mai nayiwa baba wana laifi nai masa dan Allah zai raba ni da ke?”. Cikin kuka meenal tace "Waleed mutuwa zanyi in ba kai yanzu waleed haka zamu rabu, yanzu waleed ashe ba zamu auri juna ba yanzu waleed duk wani!!!! Adede haka waleed ya kai hanun sa bakin meenal ya toshe jiki na rawa yace “a'a meenal ki dena faɗin haka sai munyi aure wallahi". Da sauri meenal da waleed suka ɗago kai, saka makwan jin an bigewa waleed hannu daya toshewa meenal baki da ƙarfin gaskiya. Baba suka gani yana tsananin huce, cikin faɗa yace "Kee bana rabaki da wanan yaron ba, saboda baka da tarbiya rashin tarbiyar taka har ya kai nan kake sawa ƴar ta hannu a jiki kuma a waje?. To maza-maza kafin dare yayi maka ka tattara ya naka ya naka, kabar wajan nan, na rabaka da ɗiyata har abada mutumin banza kawai mai fuska biyu". Kuka meenal ta rushe dashi wanda har sai da ta dunrƙushe ƙasa a wajan. Shi kuwa waleed riƙe hanun baba yayi jiki na rawa yace "baba dan Allah kar kai min haka baba, dan Allah dan annabi ka saurare ni baba wallahi mutuwa zanyi in ban samu meenal ba, baba me nai maka haka in wani laifin nai maka ka gayamin na roƙe ka gafara, baba kayimin ko wana hukunci a duniya amma kar ka rabani da farin ciki na". Wani dogwan tsaki baba yaja tare da cewa " ni bazan iya haɗa zuri'a da kai ba, duk wani kayan da ka taɓa bata, yanzu ta shiga ta futo maka da su allah ya haɗa kowa da raban sa na alkhairi" daga haka baba ya wuce gida a fusace. Meenal miƙewa tai ido cike da hawaye tace “yaya waleed kayi haƙuri bani da zaɓi daya wuce bin umarnin baba, bari naje na kawo maka kayan ka". maeenal tana ƙoƙarin tafiya waleed ya sha gabanta tare da cewa “a'a meenal duk abinda na siyar miki na siyar miki ne saboda allah da kuma soyayyah da take tsakanin mu, har abada zan cigaba dayi miki hidima ba waiwaye”. Girgiza kai meenal tai, cikin kuka tace "waleed a'a ka bari na kawo maka kayanka baba umarni ya bamu fa ba shawara ba". waleed ido yayi jajir riga ta jiƙe da gumi ko ta ina, baki na rawa yace "a'a meenal bana buƙata na barmiki halak malak, in kika dawo min dasu zanji zafi sosai, fiye da wanda nake ciki. Meenal kar ki cire ran zamuyi aure ki cigaba da addu'a kawai, kuma duk abinda kike buƙata ki bugo ki gayamin ko menene in sha Allah zan miki, kuma ina neman wata alfarma a gare ki meenal". Ido jajir meenal ta ɗago tare da cewa "ina jinka waleed in sha Allah ko mene zanyi maka in de baifi ƙarfi na ba". "meenal babban tashin hankali na shine na kira ki waya baki ɗauka ba, dan Allah kiyimin wanan alfarmar mu cigaba da communication ta waya, kafin muga abinda allah zaiyi”. "A'a waleed baba bai taɓa fushi kamar haka ba tunda ya haife ni, yanzu in ya kamani ina waya baze ji daɗi ba, umma kuma za tai tunanin naƙiyi masa biyayya ne". Shikenan meenal na yarda da wanan amma, ki amince mu ringa magana ta chatting". Haɗeye yawu da ƙyar meenal tai tare da ɗaga kai alamun to. “Yauwa meenal nagode Allah yayi miki albarka a rayuwa, in sha Allah komai zai zo ƙarshe kiyi haƙuri, ba zamu rabu da juna ba, zanyi iya ƙoƙari na da dabara wajan munga mun auri juna kinji meenal ki dena kuka". Shima kansa waleed ɗin da kyar cikin ƙarfin hali yake iya magana amma yafi meenal shiga tashin hankali ma. “tom” meenal ta iya cewa kawai cikin tsananin kuka, waleed yana ƙoƙarin yin magana su kaga hangi baba ya futo a fusace, dan haka ba shiri meenal tayiwa waleed sallama ta kama hanyar gida tana rafsa iwu. Bayan baba da meenal sun shige gida, waleed motar sa ya shiga hankali tashe dan shi yama manta ya yarda wularsa mai dumbin tsada a wajan. Ko ta kanta bai biba ya tayar da motar ya fuce daga layin cikin tsananin gudu da tashin hankali mara musaltuwa............. Kuyi haƙuri mutane na iya abinda zaku iya samu kenan, saboda na tausayawa waleed da meenal Nima.🥹🥲 Ayi following ɗin channel na. kar ku manta da like (reacted) and share. my number 09162226240. mu haɗe a next page. _page 24 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Gudun da waleed yake yi allah ne ya kare shi, kuma Allah yayi yana da tsawan kwana a gaba, saboda shi yana tafiya ne kawai amma baya cikin hayyacin sa gaba ɗaya. Tunda waleed ya fuce a guje bai tsaya ko ina ba sai gidan su ma'eeshat. bai ma iya tsayawa ya dedeta parking ɗin motarsa ba yana zuwa ya kasheta. da ƙyar ma ya iya samun damar cire mukullin motar sanan ya fuce hankali a tsananin tashe. Ko da waleed ya shiga su ayman ya samu suna wasa a fallon, da ƙyar ya iya samun waje ya zauna a kujera sanan yace su shiga ciki su kirawo masa mami. Daga haka waleed ya kifa kai a guiwa hankali a tashe. Ko da mami ta ƙaraso sai da tayiwa waleed magana sau uku bai jitaba har sai da ta dafa sa sanan ya dawo cikin hayyacin sa. A firgice ya ɗago ido jajir ya kalli mami jijiyoyin kan sa sunyi ruɗu-ruɗu alamun yana cikin tashin hankali. Fuska cike da mamaki mami tace “waleed lafiya naga gaba ɗaya hankali ka duk yabi ya tashi mai yake faruwa ne?”. A gigice bakin waleed na rawa yana futar da wucin zafi yace "mami za'a raba ni da meenal shikenan rayuwata ta ƙare". Zama mami tai a gefan waleed ɗin jiki a sanyaya tace "waleed ka nutsu mana dan Allah, ka ga yarda ka ɗaga hankalin ka kamar wanda ka zauce, koma mene kai ka jazawa kan ka ai wana ɓoyayyan hali kake da shi da baba ya raba da meenal". Ido jajir waleed ya ɗago cikin tsananin mamaki yace "mami kema kin yarda ina da wani ɓoyayyan mummunan hali kenan, haba mami kin ga nai miki kama da mutumin banza ne wallahi mami ban san dalilin da yasa baban meenal yace min bani da kyan hali ba, wallahi ban san me ya binciko a kai na haka ba". Waleed ya ƙarasa maganar yana haɗe malolon baƙin ciki wanda ya tsaya masa cak a wuyan sa. "Waleed kasan de ni a yanzu matsayin mahaifiya ce gare ka, ko yaya rahma tana nan, zan iya yima maganin damuwarka ba tare da ta shiga lamarin ba, bare ma bata nan Allah ya jiƙanta da rahma”. Da ƙyar waleed ya iya buɗe baki ya amsa da Ameen. bayan waleed ya amsa mami ci gaba da magana tai "waleed in ka ɗauke ni matsayin mahaifiyar to ka faɗa min mai kake aikatawa da baba ya kasa baka auran meenal, nasan baba mutumin arziki ne baze hanaka auran meenal haka kawai ba". Murya a dashe waleed yace "mami dan Allah dan annabi kada ki sake yimin tambayar nan, wai mami baki yarda dani ba kema, mami wana hali zanyi a ɓoye bayan wanda kuka sanni da shi, mami da ina da wani halin ai bazan bawa baba address ɗin in da nake zaune ba a abuja, mami kema zaki, iya yimin sheda ko a wana hali, ko ina nan ko bana nan, zaki iya yimin shedar halina, dan Allah mami ki tausayi min ke da abba kusa baki nasan baba zai amince". Waleed ya ƙarasa maganar kamar ya fasa ihu. mami ta fara jin ƙamshin gaskiya a maganar waleed amma duk da haka wata zuciyar tana sa mata shakku, saboda tasan halin yaran zamani. "Waleed ka nutsu ka dena tayar da hankali ka, karfa ka manta ka rasa mahaifiyaka kuma ka rasa mahaifi, to ba wanda zaka rasa a duniyar nan ko wani abun ya faru da kai, kaji zafi kamar rashin iyayanka, tunda ka rasa su ka hakura to tabbas zaka iya rasa komai a rayuwar nan ka dangana”. A zabure waleed ya kalli mami, cikin mamaki yace "mami yanzu kema kina nufin na rabu da meenal kenan mami kar kice haka dan Allah wallahi mutuwa zanyi, mami so fa ba wasa bane innalillahi". hannun waleed mami ta rike tare da cewa "kai waleed nutsu mana, ni bana goyan bayan a rabaka da meenal, kuma ba haka nace kun rabu ba har abada, zanyi iya ƙokari na wajan ganin komai ya dawo kamar da, in sha allah zakuyi aure da meenal amma waleed bana so ka ringa zauta kan, ka kamar haka". "Mami dole na zauce meenal itace kaɗai ta rage min farin ciki ina son ta wallahi mami, dan Allah mami a taimaka a bani meenal, kiyiwa abba magana shima yasa baki a maganar nan". "Wallahi waleed tun ranar da naji zancan nan nacewa, abba ya shiga lamarin baba yana ganin mutunci sa, amma yace a'a shi baya so ya ringa shiga irin lamarin nan in mahaifi ya zartar da wukunci, amma yanzu waleed ka dage da addu'a nasan baka wasa da sallah in sha allah komai zai zo da sauƙi. "Mami wallahi in ban samu meenal ba komai zan iya aikatawa a duniya nan kar kuga laifina". "Auzubillahi Waleed bana so ka ringa irin zantutukan nan da basu dace ba in sha Allah ba zaka aikata komai ba sai alkhairi kuma zaka auri meenal alfarmar annabi, in de matar kace". To haka waleed yai ta sammatu da roƙan mami, mami tana ta rarrashin sa da ƙwantar mai da hankali, ita kuwa ma'eeshat da taga yaya waleed a wanan halin har kuka sai da tai saboda tsabar tausayin sa da kuma aminiyarta meenal. Mami ta hana waleed tafiya saboda taga kamar baya cikin hayyacin sa, sai da taga ya dawo cikin nutsuwar sa sannan ta bar shi ya tafi. Amma ɓangaran waleed shi kaɗai yasan mai yake ji a cikin zuciyarsa. MEENAL Bayan ta koma gida wani saban page ɗin kukan ta buɗe, tayi kuka kamar ranta ya fita haka baba da umma su kai ta bata haƙuri, amma ina kamar ma ƙara zuga ta suke. Dole daga ƙarshe haka ta tashi, cikin baƙin cikin da damuwa meenal ta gabatar da sallam magriba da isha'i tana sake rokwan allah, da mika masa kukan ta. Sunan waleed kawai meenal take iya kira in tai sujjada. Daran ranar dole meenal ta buɗe wayarta, ta hau online domin tayiwa waleed magana ko ransa zai yi sanyi. amma abin mamaki har wajan 2 hours waleed bai hau online ba shi da kullum yake active, nan ma meenal ta sake tabbatarwa waleed yana cikin damuwa. Dole meenal ta turawa waleed gajeren saƙo akan ya hau online su gai sa, tana jiran sa. Meenal tana turawa waleed soƙo kamar wanda yake jira sai gashi ya hau online. Bashi da wata magana da yake iya gayawa meenal sai inalillahi zai mutu in bai aure ta ba, dan allah ta bawa baba haƙuri. da ƙyar de meenal ta ɗan ƙwantar masa da hankali ta ringa jansa da hira tana nuna masa komai zai zo ƙarshe sanan hankali waleed ya ɗan kwanta kaɗa. Meenal bata wani saki jiki da waleed ba, basu fi 1 hours suna magana ba tai masa sallama. nan ma hankali waleed ya sake tashi, sai da meenal ta nuna mai bawai dan an rabu su bane, bacci take ji sannan ya yarda, su kai sallama. WALEED Yau kimanin 3 days da faruwar haka. waleed ya rasa mai yake masa daɗi kuma ya rasa mafita. gashi yanzu meenal gaba ɗaya bata bashi time kamar da, basa hira mai daɗi kullum cikin kuka take masa da maganar rabuwarsu. Duk wani tunanin waleed ya kulle. lokaci guda waleed yayi zuru-zuru ya rame, kamar wanda yayi cuta, ya zama abun tausayi. gashi soyayya meenal sai sake huruwa take a zuciyar sa, kuma gashi ba wani a kusa da shi da zai bashi shawara data dace, domin ya samu auran meenal. Kullum waleed cikin sallah dare da roƙa allah yake, Allah ya aiko masa da mafita. Daga ƙarshe de wani tunani mai kyau ne, ya faɗowa waleed wanda yana tunanin in yayi shi zai iya samu mafita da wuya ma ya kasa samun mafita. Waleed ya yanke shawarar yaje saudiya ya dafa ka'aba ya roƙi Allah sanan ya wuce madina ya kaiwa annabi kukan sa. Ai kuwa haka aki ba shiri waleed ya fara shirye-shiryen tafiya domin aiwatar da ƙudrinsa. Zo kaga farin ciki wajan meenal, saboda tasan wahala ta yanke in sha allah waleed yaje yayi musu addu'a komai zai zo ƙarshe. Meenal ko umma bata gayawa ba, ma'eeshat kawai ta gayawa su biyu suka san da tafiyar waleed kuma suna masa addu'a Allah ya bada sa'a. To waleed ya gama shirye-shiryen sa cikin 'yan ƙwanaki ƙalilan, ranar da ya cika saki ɗaya da samun labarin rabuwarsa da meenal, ranar jirgin su waleed ya tashi domin tafiya saudiya. Oh ni amina bayero nima ina cikin farin ciki da tafiyar waleed, kuma sai de nace malam waleed Allah ya bada sa'a. Ku yi haƙuri da wan nan yau ma baku samu full page ɗin ba. Ya Allah kasa wanan sabuwar shekarar da muka shiga mun shige ta a sa'a. Allah ka haɗamu da alkhairi cikin ta ka kore mana sharrin ta. Allah ka gyara mana ƙasar mu nigeria, kai mana maganin azzaluman shuwagaban ni da manyan ƙasa, in kuma masu shiryuwa ne Allah ka shirya mana su. Allah kasa nigeria ta fita daga cikin fatara, talauci, yunwa, musiba. Ya Allah duk ƴan iskan da suke janyo mana masifa a ƙasa da masu shirka Allah ka shirya su, in kuma ba zasu shiryu ba Allah kai mana maganin su. Allah ka yaye mana ƴan garkuwa da mutane, wanda suka addabi al'ummar musulmi. Allah ka tsare mana iyayan mu, 'yayan mu, mazajan mu, yayyan mu, ƙannan da kuma dukiyoyin mu, da mu kan mu daga faɗawa masifa. Allah wand basu da miji ka haɗa su da mazaje na gari wanda suke da shi ka basu zaman lafiya, wanda basa jin daɗin auran ka, kasa su fara ji ka yaye musu damuwa. Ya Allah kasa wannan shekarar ta zama farin cikin a rayuwar 'yan nigeria gaba ɗaya, kasa muji daɗin kasar mu fiye da ko wace ƙasa ka bamu zaman lafiya, da adalci, ALBARKACIN annabi Muhammad s a w. Happy new year mutanan arziki nah, Allah ka amsa addu'o'in mu ka yafe mana zunubai. AMEEN YA RABBI. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game buƙatar comments ga link ɗin group yayi joining. 👇🏼👇🏼👇🏼 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 25 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 MA'EESHAT Da sallama ma'eeshat ta shiga bedroom ɗin abba domin amsa kiran da yake mata. Bayan abba ya amsa sallamar ma'eeshat ɗin, ko damar gaida shi ba tai ba, ta zauna kusa da shi. "Hmmm ma'eeshat har yau de kin ƙi kiyi hankali ko kina abu kamar ba babba ba, wai a haka kuma aure za’ai miki ko?". Murmushi ma'eeshat tai sanan tace "to abba laifin mai nayi, kar de kace an fasa auran". Murmushi abba yayi tare da girgiza kai. itama ma'eeshat wata ƙaramar dariya ta saki, tare da cewa "abban mu kenan allah ya bar mana kai". "ameen ma'eeshat, dama wata magana nake so na gaya miki, maza ki bani hankali ki nan" abba ya ƙarasa maganar yana gyara zama. gyara zama ma'eeshat itama tai "tom abba ina ji". "Yauwa jiya na nema miki admissions ke da meenal, ya kamata ku cigaba da karatu ku. "Innalillahi abba nifa nace maka bana son karatun nan baki ɗaya, dan Allah ka barni na wuta". "Gidan ku ma'eeshat, rayuwar yanzu fa sai da karatu, gaskiya ki daure ki fara karatu ko yayane kafin ai miki aure". A'a abba gaskiya ni de bana so sai dai meenal ɗin". Haɗe rai abba yayi, sanan yace "tom shikenan kuma daga yau kar naji kin sake yimin zancen auran, sai ki ta zaman gidan". "Haba abba saboda me za'a fasa auran kuma? shima naga ai duk zaman gidan ne” ma'eeshat ta faɗa tana narai-narai da ido kamar za tai kuka. "Eh na fasa auran, in de kina son aure dole ki daure ki fara zuwa makaranta, in kuma ba zaki school ba sai de ki haƙura da karatun". Yamutsa fuska ma'eeshat tai tace “tom shikenan naji zan fara zuwa school ɗin". “Yauwa ko ke fa daughter yanzu naji zance" abba ya ƙarasa magana yana sakin fuska. Miƙewa ma'eeshat tai ba tare da tace komai ba ta fuce tabar ɗakin rai a ɓace. Jinjina kai abba yayi a fili yace "Allah ya shirye ki ma'eeshat". Ma'eeshat tana komawa bedroom ta ɗauki wayarta ta lalubo number doctor ashmal ta buga masa waya rai ba daɗi. sai da ta kusan tsinkawa sanan doctor ashmal ya ɗauka "hello cute" cikin murya mai nuna gajiya doctor yayi maganar. Cikin shagaɓa ma'eeshat tace "doctor". Har tsakiyar ƙwaƙwalwa doctor ashmal yaji muryar ma'eeshat ɗin nan da nan ya dawo daga hayyacin sa yaji jikin sa ya ɗan fara yi masa ƙwari. na'am eeshat ɗin doctor mai ya faru". "Abba ne mana" ma'eeshat ta faɗi haka tana ƙoƙarin kuka. “Cool down beb don't carry tell me what's going on”. “It was my abba who said I should go back to school and continue my university studies, and I don't want to continue studying like this”. Ajiyar zuciya doctor ya sauke sannan ya fara magana cikin kwantar da murya "haba ayushatu nah akan wannan kike ɗaga hankali ki haka, wannan ai ba abin ɗaga hankali bane kar ki sake kiyi kuka kinga yanzu kin fara girma Is that right?”. "yes, that's right" "good Now do you know what I want you to do?" gyara zama ma'eeshat tai tare da girgiza kai tana cewa “a'a”. "kefa yanzu kinga kin girma kin zama babba gashi za ai miki aure kuma zaki haifa mana yara ki basu tarbiya ko?". Murmushi ma'eeshat tai tare da ɗaga kai tana cewa"eh haka ne". Tom kiyi haƙuri ki koma school ai manya basa ƙin zuwa makaranta kinji beb". Kukan shagwaɓa ma'eeshat ta saki sosai, cikin kukan tace "yanzu kai ma haka zaka ce kenan haba doctor". "Shiiiiii bana son ki ringa musu dani fa, yanzu in baki je school ba bayan munyi aure taya zaki ringa koyawa yaran mu karatu?". "Zan koya musu dede nawa in kuma na kasa sai ka tayani mu koya musu koh?". " no eeshat maybe time ɗin da zaki koya musu ma ina wajan aiki please kiyiwa abba biyayya kije school, in munyi aure shikenan sai ki dena zuwa in ma bakya so". "Yeee are you really?" ma'eeshat ta faɗa cikin farin ciki. Murmushin cin nasara akan ma'eeshat doctor yayi, kawai ya faɗa mata hakan ne dan ya lallaɓa ta, amma ba har cikin zuciyarsa ya faɗa ba, a file cewa yayi "eh mana da gaske amma ina so ki ɗauki karatun ɗin likitanci. "oh kamar kai kenan nina na zama doctor?. "eh hakan yana da kyau saboda yanzu likitoci mata sunyi ƙaranci". "tom shikenan doctor yarda kace" “good my only one I love you" "I love you too" ma'eeshat ta faɗi hakan cikin nishaɗi. “ok yanzu de ina busy saboda ina hospital but when I get home we'll call you back”. "okay take care my" "take care too bye". Daga haka ma'eeshat da doctor su kai sallama. bayan sun gama sallama, meenal ma'eeshat ta kirawo domin su gaisa kuma ta sake bata haƙuri da kwantar mata hankali akan abinda ya faru na waleed. Ma'eeshat taji daɗin waya da meenal, saboda taji ta ɗan fara sakin ranta, kuma har ɗan hirama su kai da ma'eeshat ɗin sosai, har ma'eeshat take bawa meenal labarin abba ya samo musu admissions ɗin cigaba da karatu. meenal kuwa taji daɗin hakan sosai saboda dama ita can tana son ta cigaba da karatu. Amma da ta tuna tashin hankalin da take ciki ita da waleed sai taji, gaba ɗaya ta dena farin ciki ma. haka de su kai sallama da juna zuciyar meenal ba daɗi. Tunda waleed yayi tafiya ko ishashan lokaci baya samu na magana da meenal, kullum jam'in sallah a masallacin maka baya wuce shi, dashi ake ko wace sallah akan lokaci, ko ta asuba baya bari ta wuce shi, kusan kullum waleed wuni yake a masallaci, yayi addu'a a bakin ka'aba, ya dafata. Gaba ɗaya zuciyarsa ta samu nutsuwa ba kamar da ba. Musamman ma daya ziyarci madina sai yaji gaba ɗaya damuwar zuciyarsa babu, son meenal ya ƙaru ninkin banin ki a zuciyarsa. Lokacin da yaje kabarin annabi kuwa yayi addu'a sai yaji hankalin sa ya kwanta kamar ma ya samu meenal ya gama. Masha allah. After 2 weeks. DADY Da sauri dady ya fito cikin shirinsa na manya fararan kaya. kana ganin sa ko ba'a gaya maka ba zaka san sauri yake yi. idon dady sanye yake da baƙin glass. Bayan ya fito daga ciki, zaune ya tarar da iyalan sa a babban falon suna ta hira sama-sama, amma banda doctor a ciki da yake shi bama ya gidan yana hospital. yesmeen tana kwance a jikin momy sai wani zuba shagwaɓa take too days ta wani sake girma ta cika tai fam kamar ta fashe. Muhseen da fadeel kuwa suna daga zaune a gefe suna buga wasan ludo, da yake yanzu an ɗanyi musu wutun school. cikin mamaki momy ta kalli dady tare da cewa "a'a dady naga ka futo bayan kuma kace ba zaka fita ba, idon ka yana maka ciwo ina zuwa?". Momy ta faɗi hakan tana zubawa dady ido. "Wallahi kinga yanzu wani meeting ya taso mai, mahimmanci, kuma ina so na isa wuri nan da 30 minutes za'a fara muhseen ko fadeel kuje kuyiwa driver magana, yanzu zan futo ya kai ni, dan gaskiya bazan iya driving da kai na ba, ido na ciwo yake sosai". "Ya ilahi kuma gashi tun safe na aiki driver ya kai ladidi kasuwa domin tayimana cefanen gida, gaba ɗaya naman gidan da kayan miya sun ƙare". Mommy ta faɗa, tana shafa kan yesmeen. “To yanzu ya za ai kenan kuma gashi nace miki meeting ɗin yana da amfani sosai ko haka de zan lallaɓa nai driven ɗin da kai na amma ciwan idon ne kamar baze bari ba". "Dady ka bari mana ni da muhseen mu kai ka, ka manta mun iya driving kuma fa har takaddar shedar tuƙi an bamu ai mun iya" fadeel ya faɗi halan yana tsare dady da ido”. Cikin mamki daddy ya girgiza kai tare da cewa "Wa ni fadeel a'a bana son tuƙin ku na yaran zamani sai kuyi ta sharar gudu a hanya, kullum sai nayiwa doctor faɗa to shi naga ya rage ma gwara shi yana da hankali ma ba laifi dan yayi gudu ku fa?". Fadeel ɗan taɓa ƙafar muhseen yayi ta ƙasa alamun shima yasa baki. "Ah haba dady abinda tare da kai zamuyi tafiyar ai yarda kace ayi haka za ai mana, ba zamuyi gudu ba". "To gwara-gwara ma kai muhseen ɗin kana da nutsuwa ba kamar fadeel ba amma duk da hakan ba zan yarda da driving ɗin ku ba". "Ai dady nima ranar nan sun kai ni unguwa yanzu ba laifi sunyi hankali suna driving a hankali" momy ta faɗa tana murmushi. "hmmm momy ina jin tsoron rawar kan twins ɗin nan naki shi yasa kikaga har yanzu naƙi basu mukullin motocin dana siya musu, sai sun sake hankali" dady ya ƙarasa maganar yana dariya. “Kai dady in sha allah komai zai tafi normal tunda sauri kake ka jarrabasu mana” momy ta faɗa, tana sake sakin murmushi "Tom shikenan ku taso mu tafi kai fadeel zo ka riƙe min jakar nan". Ba musu fadeel ya nufi dady ya ƙarɓi jakar, sai wani daɗi suke ji shida muhseen zasuyi driving........ In baƙwa gigita ni da like bazan ringa muku typing mai tsayi ba, kuma zan cigaba da fashin posting ba. Ayi following channel dan samu posting da wuri. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game buƙatar comments ga link ɗin group yayi joining. 👇🏼👇🏼👇🏼 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 26 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Bayan sun isa bakin mota key dady ya miƙawa muhseen amma kafin muhseen ya kai hannu tuni fadeel ya amsa, girgiza kai dady yayi tare da cewa "kai fadeel ka fiya rawar kai ni muhseen nace yayi driving ɗin tunda ya fika nutsuwa kai a dawowa ka tuƙamu". "A'a dady ka bari na kai munde ni da muhseen ɗin ai duk ɗayane ko ba haka ba muhseen?. Gyaɗa kai muhseen yayi yana cewa “eh gaskiya ne dady" da yake shi muhseen ba ruwan sa yafi fadeel haƙuri da nutsuwa ma. Jinjina kai dady yayi sanan yace "tom shikenan muje de tunda kun haɗe mun kai, kuyi maza ku shiga saboda kar a ɓata lokaci sauri nake”. Bayan sun shiga, ba ɓata lokaci fadeel yayi horn mai gadi ya buɗe suka fuce abun su. A nitse fadeel ya hau kan titi ya fara tafiya, sai wani safiya yake slow duk dan kar dady yace masa ya fiya rawar kai, kuma yana so ya nunawa dady ƙwarewar su akan driving. "Ah masha allah abu yayi kyau haka nake so ai ku ringa driving cikin nutsuwa bana so kuna gudun nan, hakan ba yafi ba" Dady ya faɗi hakan cikin jin daɗi. Muhseen cafe zance yayi da "ai dama dady mun gaya maka cikin nutsuwa muke tuƙi yanzu fa mun sake hankali, ba twins ɗin da kasa ni bane da marasa jin magana”. Murmushi fadeel yayi tare da cewa "ai dady yanzu mun canza mun girma kuma" ya faɗi hakan yana ƙunshe dariyar sa a ciki. “Eh haka nake so yarda kuke da saurin girman nan hankalin ku ma ya ƙaru, jibe ku fa kamar kun kai 25 to 26, very soon zaku kamo doctor a girma,. To dady haka yayi ta hira da twins cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Har sunyi rabi dady yaji wayoyin sa suna ta faman ringing. Bayan ya duba gani yayi wanda zasu yi meeting ɗin ne suke kiran sa, dan haka ɗauka yayi sannan ya sheda musu yana hanya zuwa nan da 10 minutes ma ya ƙaraso. Bayan dady ya kashe wayar ɗagowa yayi ya kalli fadeel tare da cewa "fadeel maza ka ɗan ƙara sauri kaga kowa yazo ni ake jira”. Ai kuwa fadeel kamar jira yake ya kwashi motar nan a guje, bai ma kula da wanda yake tsallakowa titin ba. Muhseen ne yace “kai fadeel mene haka ka rage gudu mana bakaga wancan mutumin yana ƙoƙarin tsallakowa ba” amma kafin fadeel ya kai da rage gudu yaji dady yayi masa magana cikin tsawa yace “kai fadeel ka kula mana tsaya-tsaya”. hakan ba ƙaramin gigita fadeel yayi ba, dan gaba ɗaya ya kasa taka birkin motar sai ji kake ƙiiiiiiiiii. Sosai fadeel ya bige bawan Allah nan saboda tsabar buguwa sai da yayi gefe ya bigi har jakin baban gidan titin da ƙarfin gaske sosai bawan allah ya bigu. "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un". Abinda dady yake iya furtawa kenan hankali a tashe. Suma su muhseen hankalin su ya tashi sosai da sosai, musamman ma fadeel da ya bige mutum. Nan da nan mutane suka fara taruwa motoci suka tsaya cak a titi. Hankali tashe dady ya buɗe ƙofa ya fita, saboda mutane har sun fara zagaye motar a fusace. Shima muhseen buɗe ƙofa yayi ya fice, fadeel ma hannu na rawa ya buɗe ya fara ƙoƙarin fita hankali a tsananin tashe. Mutane sai hayaniya suke masu masifa da zagi suna tayi, shide dady direct wajan bawan allah nan da yake kwance ya wuce. Hankali su dady ya sake tashi sosai da sosai ganin yarda jini yake ta zuba ta kan bawan allah sai nunfashi yake saukewa da ƙyar. Baki na rawa dady yace “haba dan Allah yanzu fa ba lokacin zagi bane ko hayaniya, ya kamata akai bawan allah nan hospital mafi kusa in yaso daga nan sai azo a mai da zance”. A fusace wani mutum yace “haba alaji gaskiya lamarin nan ba adalci aciki kawai saboda kunga ku masu kuɗi ne sai kuyi ta cutar talaka, kuyi ta ɗaurewa yaran ku gindi suna cutar al'umma”. Murmushi yaƙe dady ya saki tare da cewa “dan Allah mutane Allah ya wuci zuciyar ku”. “Wallahi ba da sani aka buge bawan allah nan ba, kuma kasan ba zan sa a kaɗe rai da gangan ba, yaran yanzu ne da rawar kai, kuma kunsan lamari na kaddara dan Allah azo a ceci rayuwar mutum nan mu kai shi hospital mafi kusa”. "Tabbas alhaji gaskiya ya faɗa kuna ganin alaji kun san mutumin kirki ne dan in wani ne bama zai tsaya ba bare yayi mana tattausan lafazi yanzu de abinda alhaji yace za ai, ga wani hospital mai kyau gaba damu kaɗan ai sauri a kai shi" Wani magidanci ya faɗi hakan cikin mutuntawa. Nan da nan mutane suka amince da hakan dan haka ba ai wata-wata ba aka sa bawan allah nan a mota shi da wasu mutum biyu a wajan dady da kan sa ya tuka motar suka wuce hospital hankali tashe. Lokaci da suka je hospital ɗin cewa su kai ba zasu karbe shi ba sai da ɗan sanda, haka su dady su kai ta magiya amma sam hospital suka ki yarda. daga karshe de dady bugawa doctor ashmal yayi ya bashi labarin abinda yake faruwa. Hankali tashe doctor ashmal yake tambaya wane hospital ne, dady ya gaya masa. doctor ashmal cewa yayi yana zuwa sanan ya katse wayar. bayan wajan 3 minutes ya bugo ya cewa dady "yayi magana daga sama yanzu za'a karbi mara lafiyar a duba shi. Ai kuwa haka akai kafin kace me tunu likitoci sun zagaye bawan allah sun shiga da shi ciki domin duba shi. Hankali su dady tashe suka zauna a reception domin jira. Dady sai addu'a yake Allah ya tashi kafaɗun bawan allah, dan baya so rai ya rataya akan su, musamman ma fadeel. To bayan likitoci sun gama duba mutumun bacci ya tafi, su kuma su dady suka tsaya kafin bawan Allah ya farfaɗo a nemi iyalan sa. Abu kamar wasa har 4 bawan allah nan bai farfaɗo ba sai bacci yake likitoci sunyi iya ƙoƙarin su akan ya farfaɗo amma ina abu yaci tura, kuma gashi yana nunfashi amma ya tafi dogwan bacci. Hankali su dady kuwa ba ƙaramin tashi ya sake yi ba. Dole de a hospital ɗin ma cewa su kai sai de in babban likita yazo sai ya duba shi. doctor ashmal jin yarda hankali su dady ya tashi hakan ne yasa ya katse aikin sa ba shiri ya tawo hospital ɗin. Lokacin da doctor ashmal yazo ba ɓata lokaci ya hau kan bawan allah nan ya fara duba shi. Cikin ƙanƙanin lokaci bawan allah nan ya farfaɗo amma baya cikin hayyacin sa. haka doctor ya sake masa allura, da zata temaka masa ya dawo normal, sanan bacci ya kwashe shi. Bayan bacci ya ɗauke shi doctor ashmal ya cewa dady yazo ya mai da su gida su huta anjima sai ya dawo. Cikin mamaki dady yace "ina fa wani huto sun bige rai ai babu huto sai ya dawo dede ya warke". "Haba dady ka kwantar da hankali in sha allah komai zai tafi normal yarda ake so, kuma dady ai ba kai ka bige shiba ba lafin ka bane, duk da suma su fadeel ɗin tsaustasyi amma dady in baka manta ba nasha gaya muku kar wanda ya yarda su fadeel suyi driving ɗin shi a mota hakan yana da hatsari”. "Doctor kasan tsautsayi baya wuce rana, wannan abun tsautsayi ne, kuma tabbas nima nasan nayi ganganci bawa fadeel driving, tun farko sai da nace muhseen ya tuƙamu amma fadeel ya dage dole na haƙura". "Dady ai kai ma kasan halin fadeel akan me zai dage maka sai yayi driving baka sa shi ba ka amince, wai garin ya kai ma kace ya kai ka unguwa bayan ga driver?". “Yau na tashi da ciwan ido ne, kuma meeting ɗin gaggawa ya taso min. Gashi momy tun safe ta aiki driver da mai aiki kasuwa, kuma ni bazan iya driving ba, shine da nayiwa momy complain suna zaune a wajan suka ce zasu kai ni, farko de ban yarda ba, amma da momy tasa baki sai na yarda, kaji yarda akai wannan tsautsayi ya faru". “Tom shikenan dady ka daure mu tafi gida mana, zuwa anjima sai ka dawo, kaga an samu ƙaramar waya a aljiwun sa, zuwa anjima in ya farka ya dawo hayyacin sa, sai a tambaye shi wa za'a bugawa wani nasa a sanar da shi. In sha allah daga nan har ya warke komai za a ringa yi masa, kuma ina fatan nan ba da jimawa ba zai tashi, tunda ba wasu mugayan raunika ya samu ba, targaɗe ne sai kuma fashewar kai da buguwa kuma" To haka doctor ashmal yayi ta bawa dady baki, da kyar ya yarda ya amince suka tashi domin tafiya gida. Doctor yace a ajiye motar da su dady suka futo da ita a hospital shi zai mayar da su gidan, anjima a aiko driver yazo ya ɗauka. MEENAL Misalin ƙarfe 4 na yamma. tana daga kwance tana chat da waleed, yana ta bata labari akan yarda yake musu addu'a. kuma yana kwantar mata da hankali da cewa za suyi aure itama ta cigaba da addu'a komai lokaci ne. Sallamar da umma tai ne tasa meenal saurin ajiye wayar a gefe yarda kasan umma ta kamata tana waya da waleed ɗin. Cikin rashin gaskiya meenal ta amsa sallamar umman. Kallon meenal umma tai sosai kafin tace "hmmm meenal kenan, koya baki da gaskiya ina ganewa tunda baki cika ɓoyemin abu ba, ko da waleed ɗin kuke waya ne?”. Girgiza kai meenal tai alamun a'a. "Hmm meenal ba zaki iya ɓoyemin gaskiya ba, amma shikenan kide bi a hankali ki kasance mai biyayya ga mahaifin ki yanzu, in mahaifin ki yasan kuna tare ai baze ji daɗi ba, meenal kiyi ƙoƙari ki yakice waleed daga zuciyar ki, shine kwanciyar hankali ki a wajan baban ki”. Rantse ido meenal tai zuciya cike da tsantsar baƙin ciki tace "kiyi haƙuri umma in sha allah zan dena wallahi na kasa riƙe zuciya ta ne, kin san ina son waleed ne kuma yana bani tausayi shi yasa". "Haka ne meenal nai miki uzuri allah ya cire miki son sa acikin zuciyar ki". Sunkuyar da kai gefe meenal tai dan ita ganin ta ba zata iya cewa ameen ba. “Kinga tun dazu da safe da babanki ya fita bai dawo ba kuma kinga cemin yayi zuwa azahar ya dawo gida ma”. “To kuma gashi de baba bai saba haka ba amma ki buga masa mana kiji yana ina" meenal ta faɗa tana kashe data wayarta. "na buga masa amma wayar a kashe tun dazu nake biga masa ai". "ai baba baya kashe waya kuwa maybe cajin wayar ne ya ɗauke". "Gaskiya ne meenal ba mamaki to Allah yasa lafiya" "Ameen umma bare ma nasan lafiya, ai lafiya ce take ɓuya ƙila daga nan wani wajan ya biya, amma in sha allah kafin magriba ma zakiga ya shigo". To daga haka de meenal da umma suka cigaba da hira har aka fara kiran sallah magriba. Tashi su kai ita da umma suka ɗaura alwala sanan suka fara gabatar da sallah. Harde meenal da umma suka idar da sallah shiru. A lokacin de hankali umma ya ɗan fara tashi, ita kuma meenal tana ta bata baki tana nuna mata lafiya ƙalau ne. Abu kamar wasa de har su umma su kai sallah isha'i baba bai shigo ba, kuma umma da meenal sai sake buga number sa suke amma a kashe, a lokacin de itama meenal hankalin nata ya fara tashi. Har ƙarfe 8:30pm baba bai shigo ba lokacin kuwa meenal da umma sunyi tsuru-tsuru suna jiran ikon Allah. Ana cikin haka umma taji wayarta ta fara ringing, da sauri meenal tace "umma duba ko shine yake kira". Da sauri umma ta ɗauki wayar hannu na rawa, bayan ta duba kallon meenal tai tare da girgiza kai tana cewa "ba number sa bace, amma bari na ɗauka". Daga haka umma ta ɗauki wayar baki cike da sallama. Mu haɗe a next page. _page 27 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Jim umma tai na wasu lokacin kafin tace "eh matar sace lafiya de ko?" Ta faɗa hankali a tashe, itama meenal zaro ido tai tare da ƙurawa umma Ido. “Innalillahi mai ya faru da shi kuma?” umma ta faɗa hankali a tashe. meenal ji tai gabanta ya faɗi rass a fili itama tace "inalillahi" Hankali meenal sake tashi yayi da ta tsinkayi muryar umma tana cewa "asibiti kuma innalillahi wannan asibitin mai ya faru?. Zuciyar meenal fara bigawa tai da ƙarfi fat fat fat, ji take kamar ta ƙwace wayar hanun ummanta saboda tsabar tashin hankali. umma cikin tsananin tashin hankali ta sake cewa "innalillahi tom gani nan zuwa" daga haka ta kashe wayar hankali tashe. Baki na rawa meenal tace "umma lafiya naji kina zance hospital". Umma kamar tai kuka tace "meenal tashi zama bai kama mu ba, wani bawan Allah ne yanzu ya bugo yake gayamin baban ki yana hospital a kwance, ya ɗan samu matsala". "Baba kuma mai ya faru da baban nawa umma?" "wallahi meenal bai gayamin ba yace dai in nazo za ai min bayani, yanzu ki tashi mu tafi ko zaki iya zama ke kaɗai?. Ido cike da hawayan tashin hankali meenal tace, "a'a umma bazan iya ba gaskiya mu tafi tare kawai". Jiki na rawa umma ta shiga ɗaki domin ɗauko mukullin gidan. Itama meenal hankalin tashe ta miƙe dama basu cire hijab ɗin jikin su ba da suka gama sallah. takalmi meenal ta zura sannan tai hanyar waje sai kace wanda tasan hospital ɗin. Itama umma hankali tashe ta ɗauko mukullin gidan da kuɗin motar sanan ta fita ta samu meenal a waje hankali ta tashe. A hanzarce suka rufo gidan sannan suka kama hanyar tafiya jikin su duk a sanyaye. Lokacin da suka isa hospital ɗin dady har get ya aiki ladidi mai aikin gidan su domin ta shigo da su. da yake sun dawo hospital ɗin shi da momy. hankali momy itama yayi matuƙar tashi da taji labarin abinda su fadeel suka aikata duk tabi ta gigice. Ladidi tana gaba su umma da meenal suna binta baya, gaban su sai faɗuwa yake. haka suka cigaba da tafiya har ladidi ta kai su meenal reception ɗin da dady da momy suke zaune suna jiran su. Bayan sun shiga baki ɗauke da sallama, momy da dady har rige-rigen amsa musu sallama suke yi. Momy tana zauna sanye da zumbulele hijab hanunta riƙe da carbi. Duk da momy tana cikin damuwa sosai hakan bai hanata sakarwa su umma fuska ba cikin girmamawa tace suzo su zauna a kujerar da take zaune da yake kujerar tana da ɗan tsayi. Bayan sun zauna gaisawa suka farayi ko wannen su zuciyar sa cike da fargaba. Su meenal da umma suna fargabar halin da zasu samu baba, su kuma su momy suna fargabar yarda su umma zasu ƙarɓi lamarin. Bayan an gama gaisawa dady zama ya gyara sannan ya fara bayani kamar haka. Kuyi haƙuri sakamakon ruɗanin da muka saka ku ciki, da farko de muna masu baku haƙuri akan kaddarar da ta faɗa, duk da kuwa ko wana bawa baya wuce ƙaddarar sa. Tuni umma da meenal suka fara gumi da rawar jiki saboda yarda suka ji dady ya fara maganar. shi kuwa dady cigaba da maganar yayi da "Yau da safe muna tafiya ni da yarana biyu, cikin akasi yazo tsallaka titi, shi kuma yaran nawa bai kulaba ya bige shi, duk da de abin da tsautsayi a ciki amma harda rawar kai yaron gaskiya". "Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un" umma da meenal har suna haɗa baki wajan faɗar hakan. "Yanzu alhaji ya ake ciki ne ya mutu ne?" umma ta watsawa dady tambayar tana zaro ido, itama meenal tambayar da take so tayi kenan umma ta riga ta. “A'a hajiya ki kwantar da hankali dan Allah, mijin ki yana nan a raye kawai de ya ɗan samu buguwa ne, kansa ya fashe kuma yaji ciwo a ƙafa”. Wata nannauyar ajiyar zuciya meenal ta sauke, meenal tana saukewa umma itama ta sauketa. Hankali su ya ɗan kwanta da sukaji baba yana raye amma sam basuji daɗi mummunan labarin da suka samu ba. momy magana ta farayi kamar haka "Dan Allah hajiya kuyi haƙuri muna roƙan gafarar ku madadin ɗan namu, dama shi tsautsayi baya wuce ranarsa, kuma in sha allah har ya samu lafiya zami cigaba da kula da shi komai da komai har abinci zamu ɗauko nauyi". Momy ta faɗa tana kallon umma fuska cike da damuwa. Jiki a sanyaye umma tace “ba komai Hajiya kamar yarda kika faɗa ƙaddara ce kuma ai yaron baze bige shi da gangan ba, mude fatan mu Allah ya bashi lafiya" umma ta faɗi hakan murya na rawa. Meenal kuwa tuni hawaye sun fara gangaro mata shaɓe-shaɓe, dama tayi namijin ƙokari data kai har lokacin kafin tai kuka saboda tun suna gida taso ta fara kukan kawai daurewa take. cikin tausayawa momy ta dafa kafadar meenal, sannan ta fara rarrashin ta "kiyi hakuri yar nan in sha allah zai samu sauki baban ki ne Koh?. Cikin hawaye meenal ta gyada kai alamun eh. "ayya kiyi hakuri addu'a zaki masa allah ya bashi lafiya kinji?". to meenal ta iya cewa da kyar hawaye na sake shararowa ta idanuwan ta. Ƴar ta ki dena kuka kinji kiyi haƙuri haka, in sha allah baban ki zai samu lafiya, momy ta faɗa tana gogewa meenal hawaye da hijab ɗin meenal ɗin. Bayan momy ta gama rarrashin meenal tai shiru ta dena kuka, umma cewa tai "yanzu in ba damuwa zamu iya ganin sa?. Jinjina kai dady yayi tare da cewa "eh sosai ma, ai ba damuwa amma sai de bacci yake yi, zaku iya ganin sa kafin ya farka". "Tom shikenan alhaji in ba damuwa a rakamu" "tom shikenan ku tashe mu shiga" dady ya faɗa yana miƙewa. Suma umma da meenal harma da momy miƙewa su kai domin zuwa wajan baban, haka suka jeru dady yana tafe suna biye da shi, a baya. Bayan sun isa a hankula dady ya buɗe ƙofar ya shiga sannan su umma suka bi bayan sa. Kwance suka tarar da baba a kan gadon hospital ɗin, hanunsa yasha allurori hagu da dama. ɗayan hanun ana ƙara masa ruwa ɗayan kuma ana ƙarasa masa jini. Kan baba yana naɗe da bandeji da ɗayar ƙafarsa sai wani sauke wahalallan nunfashi yake yi kana ganin sa kasan baya cikin hayyacin sa. Umma tsayawa tai a gefan baba na hagu ita kuma meenal ta tsaya a gefan sa na dama, sun zuba masa ido sosai suna mugun tausaya masa, itama umma sai da taji kamar ta zubar da hawayan saboda tsabar tausayi. Basu fi 5 minutes ba likitoci biyu suka shigo, suka roƙi alfarmar su dady akan su fita, saboda mara lafiya amma zuwa goma wanda zai kwana da shi sai ya shigo, mutum ɗaya ake buƙata ya kwanta da shi. Ba musu su dady suka fita kamar yarda likita ya buƙata, suka koma reception da zama. Umma ta zabga uban tagumi saboda tsabar damuwa, itama meenal jigum tai tana tunanin baban nata. Dady fita yayi ya aiki ladidi da driver domin su siyo sababbin bedsheets da blanket, da kuma kayan shayi dade sauran abinda mara lafiya da mai jinya zasu buƙata domin ƙwanan hospital. Momy kollon meenal tai fuska cike da fara'a ta riƙo hanunta tare da cewa “ƴata baki faɗa min sunan ki ba?”. Itama meenal murmushin dole ta ƙwaƙwalo sanan ta sunkuyar da kai cikin sanyayiyar murya tace "sunana amina amma meenal ake cemin". "ah masha allah ashe ƴar tawa babban suna ne da ita sanun ki aminatu". Murmushi dole meenal ta sake yi tare da sunkuyar da kai ƙasa. "sanu aminatu izunki nawa a islamiyya?". momy ta watsawa meenal tambayar "nayi sauka yanzu bana zuwa islamiyya". “Ah masha allah kice ƴar tawa Hafiza ce ai haka ake so, amma ya kamata ki koma makaranta islamiyya ki cigaba da tulawa da sauran hadisai in ba haka ba harda zubewa za tai". Gyaɗa kai meenal tai sannan tace "in sha allah, amma de yawan ci ma ina bita a gida saboda gudu zubewar haddar". "Masha Allah ashe haka ƴar tawa take da hazaƙa, yanzu a boko kuma ajinki nawa ko kin kammal ne?". Jinjina kai meenal tai kafin tace "eh nayi canday amma ina sa ran zan cigaba da zuwa makaranta nan bada jimawa ba". "Masha Allah wana course zaki karanta?" cikin ƙosawa meenal tace "likita nake son na zama in sha allah". "Ah masha allah, allah ya yarda ai hakan yana da kyau aminatu ko dan taimakawa bayan allah, amma kina da yayye Koh?”. Girgiza kai meenal tai sannan tace "a'a bani da yayye bani da ƙanne ni kaɗai ce a gidan mu aka haifa". “Wayyo Allah Sarki amina kice ke kaɗai ce, Allah ya raya ki ƴata ya cika miki burinki ki zama babbar likita, ya baki miji na gari". "ameen hajiya Nagode" meenal ta faɗi hakan da ƙyar saboda momy ta tuna mata da waleed". "yanzu ina zaki zauna ai ba zaki koma gida ke ɗaya ba, tunda maman ki a hospital zata ƙwana, ko zaki bimu gida ne?. Girgiza kai meenal tai sanan tace "zani gidan su ƙawata ma'eeshat na ƙwana". "Ah muma ai gidan mu kamar gidan kune ƴarta kawai zaki bimu ne mu ƙwana acan kinji?". sunkuyar da kai meenal ƙasa tai ba tare da tace komai, ba dan bata jin zata iya bin matar nan gidan ta. Bayan su ladidi da driver sun dawo lokacin ƙarfe goma na dare. Dady cewa yayi ya kamata su tafi, tunda yanzu ne lokacin da likitoci suka basu domin tafiya gida. miƙewa momy tai tare da roƙo hanun meenal tana cewa “tawo mu tafi amina". Girgiza kai meenal tai sannan tace “a'a hajiya kawai kuyi tafiyar ku, ko ku saukeni a gidan da zan ƙwana”. “ah gaskiya kizo mu tafi gida ba wani sai kinje gidan su ƙawarki ba, gobe kinga da sassafe in za'a kawo abinci sai ki dawo kiga baban naki". "Momy in bata so mu sauke ta a gida mana kar taga kamar mun takura mata” dady ya faɗa yana kallon momy. "a'a dady gidan nasu fa ba kowa ita kaɗai ce aka haifa". "ayyah gaskiya kam ya kamata kizo mu tafi dake zuwa gobe" dady ya faɗa cikin tausayawa. Kafin meenal tai magana, umma cewa tai "meenal mene haka ba an hanaki musu da manya ba maza ki bisu mana ku tafi". Sun kuyar da kai meenal tai tare da cewa "kuyi haƙuri zan biku". Cikin birgewa da tarbiyar meenal momy tace "yauwa umma mun gode sai da safe zaki iya komawa ciki ki kwanta a gadon mai jinya domin kula da shi". "tom shikenan hajiya mun gode sosai" daga haka umma da su momy su kai sallama. Tunda suka shiga area ma meenal ta saki baki saboda yarda ta ringa ganin katafaran gida je kamar ba a ƙasar nan take ba. Cikin wani hamshaƙin gida taga an nufa da ita ana zubga uban horn. kafin kace me tuni mai gadi ya buɗe musu get. Wani uban gaske meenal taga ya dallare ta na musamman suna shiga cikin gidan yarda kasan rana ce, saboda tsabar globes masu tsananin haske. ko da suka fita daga motar sai da suka sha tafiya kafin su nufi ciki, iya farfajiyar gidan ma abun kallo ce kafin a shiga. Lokacin da suka shiga daskarewa meenal tai saboda tsabar tsaruwar gidan. fuska a sake momy tace “sannu amina, shigo mu ƙarasa ciki”. haka meenal ta ringa bin momy a baya a baya tana kallon gidan cikin mamaki, saboda ita tunda aka haife ta bata taɓa shiga gida mai kyan wanan ba. Bayan sun hau sama sun shiga wani lungu wani bedroom momy ta nufa ta murɗa handel ɗin ƙofar ta shiga itama meenal tana biye da ita. da gudu yesmeen ta taso wanda take game a waya, rungume momy yesmeen tai cikin farin ciki. Itama momy rungume ta tai tare da cewa “oyoyo auta ta”. meenal bin yesmeen da ido tai, ganin yarda Allah ya zuba halitta ga kyau ga haske, fatar ta har wani ja take yi yarda kasan balarabiya sai ka rantse bata iya hausaba in ba magana tai a gaban ka ba. Haka meenal ta saki baki tai ta bin momy da yesmeen da ido. "Baki ga baƙuwa ba" momy ta tambayi yesmeen tana yi mata murmushi. Kallon meenal yesmeen tai sanan tai murmushi tace “sannu da zuwa ya kike?” ta faɗa tana lumshe ido. Meenal ji tai wata kwanciyar hankali ta saukar mata ganin yarda yesmeen take magana a nitse, itama cikin sakin fuska tace "sanun ki de". Momy murmushi tai tare da cewa “bari nasa ladidi ta kawo miki abinci zan shiga daga ciki ne, yesmeen ga abokiyar zama nan zaku kwana tare, ki kula da ita sosai ki bata duk abinda take buƙata ki nuna mata toilet in tana da buƙata". "yeee da gaske momy tare zamu kwana gaskiya nayi farin ciki dama na gaji da kwana ni da teddys wallahi". murmushi momy tai tare da cewa “eh da gaske good night, meenla sai da safe" daga haka momy ta fuce. Yesmeen kallon meenal tai, ta sakar mata murmushi tare da cewa “aunty meenal sannu”. murmushi meenal tai tare da cewa "yauwa na gode". A zuciyar ta tana mamakin yarda yesmeen take bata respect, duk da itama ta kusan kamo ta a girman ma. Yesmeen komawa tai bed ta gyara bedsheets ta kwace teddies ɗin kan bed ɗin nata, sannan ta dawo wajan meenal ta riƙe hanunta, cikin sakin fuska da daɗin murya tace “aunty meenal tawo ki zauna” ba musu meenal tabi yesmeen, yesmeen na riƙe da hanun ta........ Mu haɗe a next page. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. _page 28 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Bayan yesmeen ta ƙarasa bakin bed sakin hanun meenal tai tare da cewa “yauwa aunty meenal ki zauna”. meenal ba musu ta zauna a kan bed ɗin, meenal tana zaunawa taji wani irin laushi da ni'ima. Bayan meenal ta zauna itama yesmeen zaunawa tai kusa da ita. "me kike buƙata na kawo miki aunty?” "a'a bana buƙatar komai nagode sosai" meenal ta bawa yesmeen amsa fuska a sake. "Tom in zaki shiga toilet gashi nan ko da za kiyi alwala" yesmeen ta faɗa tana nunawa meenal toilet ɗin da hannu. "tom nagode yesmeen nayi sallah isha'i, sai de in anjima zan shiga ko da asuba" "tom shikenan aunty meenal amma ki cire hijab ɗin mana ki huta". Meenal bataji daɗi da yesmeen tace ta cire hijab ɗin ta ba, dan ita ba ko ina ta cika son cire hijab ba, amma ba yarda ta iya dole ta bawa yesmeen amsa da “to". Sannan ta cire ta ajiye shi gefe. Yesmeen miƙewa tai tare da cewa "bari na shiga toilet" "tom yesmeen sai kin futo" meenal ta faɗa tana bin yesmeen da ido. Meenal tana mamakin yarda yesmeen take kiranta da aunty saboda kaɗan ne ya rage yesmeen bata kamo meenal a tsayi ba. Ɓangaran girman jiki ma sun kusan suyi kai ɗaya, amma sai de meenal ta nunawa yesmeen diri ko ta ina. saboda ita yesmeen girman jiki ne da ita. Meenal tana kai haka da tunanin taji ana knocking ɗin ƙofar bedroom ɗin. Meenal batayi wani tunanin ɗaukar hijab ba ta miƙe domin buɗe ƙofar saboda bata san ta ɓatawa mai knocking ɗin lokaci. Koya meenal tai tafiya jikin ta rawa yake ko ta ina da yake rigar jikin ta ba wata mai kauri bace sosai ta zaman gida ce. meenal tana ƙarasawa ta buɗe ƙofar, ladidi ta gani tsaye hannun ta riƙe da madede cin ture mai ɗauke da nau'in abinci kala-kala. ƙasa kuma plate ɗin water da lemo mai sanyi da kuma cup ta ajiye. Murmushi meenal taiwa ladidi tare da cewa "sannu da aiki ko zan iya taimaka miki?". Itama murmushi ladidin tai tare da cewa, "a'a basai kin wahalar da kan ki ba ke da kike baƙuwa" "ba komai ki bari na taimaka miki mana" meenal ta faɗa tana miƙa hanunta tana ƙoƙarin ƙarbar ture ɗin. Ba yarda ladidi ta iya dole ta miƙawa meenal ture ɗin abincin sanan ta sunkuya ta ɗauki na ƙasan. sosai ladidi ta zubawa meenal ido tana kallonta ta baya. dan iya tunanin ladidi gani take meenal iya cikar ƙirji ne da ita ashe harda hips da ɗuwawuka. "Wai masha allah, Allah ya zuba halitta" ladidi mai aiki ta faɗi hakan a zuciyarta. mamaki ladidi mai aiki take kawai ganin yarda jikin meenal yake rawa ko ta ina in tana tafiya, da sauri ladidi ta kawar da idon ta ganin meenal tana ƙoƙarin juyowa. Adede lokacin yesmeen ta futo daga toilet. "gashi nan hajiya ce tace a kawo miki" ladidi ta faɗa tana kallon meenal wanda take ta sunkuyar da kai saboda jin kunyar ladidi, ganin yarda take maka wani irin kallo sai kace mayya. "Tom shikenan nagode" meenal ta faɗa a taƙaice, daga haka ladidi ta fuce daga bedroom ɗin. yesmeen ƙarasowa tai tare da tsugunawa wajan plate ɗin abinci. "to aunty meenal bari nai saving ɗin ki" "a'a yesmeen ki bari bana jin yunwa ba yanzu ba". "kai aunty meenal dan Allah ki bari na zuba miki ko kaɗan ne" yesmeen ta faɗa tana tsare meenal da kyawawan idanuwanta. meenal tana mamakin yarda yesmeen ta riƙe sunan ta haka, meenal gani tai yesmeen tana mata kwarjini ga kyau da take mata kuma tana mugun birge ta, dan haka bata san sanda ta bata amsa da "tom shikenan yesmeen zuba kaɗan amma". "yauwa aunty meenal, kin san wani abu kuwa?" yesmeen ta faɗa tana zubawa meenal abinci. girgiza kai meenal tai tare da cewa "a'a sai kin faɗa yesmeen". murmushi yesmeen tai tare da cewa “wallahi kina burge ni sosai aunty meenal". Cike da mamaki meenal tace “birgewa kuma yesmeen to Nagode". "Eh mana saboda kina da kyau kin haɗu gashi ina son irin fatarki mai duhu haka, ni baƙar fata tana birge ni wallahi wataran sai naji dama ni baƙa ce". wata siririyar dariyace ta ƙwacewa meenal, a zuciyarta tana mamakin yesmeen. meenal gani take yesmeen gata fara ga kyau amma tana tunanin kalar fatar ta "kai Allah mai iko". Yesmeen tana ƙoƙarin magana taji horn ɗin motar, da yake bedroom ɗin ta, a setting parking space ɗin gidan yake, da sauri yesmeen ta ƙarasa zubawa meenal abinci sanan ta mike tsaye. "Aunty meenal ina zuwa, bari naje nayiwa yayana oyoyo, yau naci sa'a ya dawo da wuri kafin nai bacci". gyaɗa kai meenal tai kafin tace “tom shikenan sai kin dawo" daga haka yesmeen ta fuce daga bedroom ɗin a guje. kai gaskiya mutan gidan nan suna da kirki sosai ga tarbiya kuma ga kyau, dan tunda MEENAL taga momy da dady suna da kyau kuma itama yesmeen kamar ita tai kanta meenal ta tabbata sauran yaran gidan ma haka suke da kyau. Abinda meenal ta raya kenan a zuciyarta. Meenal ji tai dama ta ɗauko wayarta ko dan ta faɗawa ma'eeshat da waleed abinda yake faruwa da baba. bayan wasu lokutan ma'eeshat saukowa ƙasa tai domin cin abinci. duk da a ƙoshe takeyi, amma zataci ne kawai saboda yesmeen da kuma momy suna so taci. haka meenal ta fara ƙoƙarin cin abinci zuciyarta ba daɗi, saboda tunanin babanta da take yi. Meenal da ƙyar ta iya tusa abinci kaɗan a bakin ta, bai fi 5 spoon taci ba, ta ajiye abincin ta rufe sannan ta zuba lemo mai sanyi ta fara sha. meenal tunda ta ɗaga cup ɗin bata sauke ba sai da ta shanye shi tass, sabuda tsabar damuwar da take ciki. Meenal ji tai bayan tasha lemon nan mai sanyi wata nutsuwa ta saukar mata ko ta ina, sai sauke nunfashi take a hankali. Bayan nan miƙewa tai ta koma kan bed ta zauna sannan ta tafi duniyar tunanin halin da baba ya shiga. Yesmeen ta ɗauki kimanin 30 minutes kafin ta dawo. baki ɗauke da sallama ta murɗa handel ɗin ta shigo, kana ganin ta kasan tana cikin farin ciki. da sauri ta ƙaraso wajan meenal ta zauna wanda ta daɗe da tafiya duniyar tunani. meenal tana cikin tunanin taji an zauna kusa da ita firgigit ta dawo daga dogwan tunanin da ta tafi. "sannu har kin dawo" meenal ta tambayi yesmeen tana sauke ajiyar zuciya "eh na dawo hakan ma shi yace nazo na kwanta saboda school". "Oh Allah sarki s s s nawa kike a school?" meenal ta tambayi yesmeen tana kallon ta. Dariya yesmeen tai sanan tace "ina ban kai ba ai ina j s s 3". Ɗan zaro ido meenal tai cikin mamaki tace "j s s 3 kuma yesmeen duk giraman nan naki?". Dariya yesmeen tai kafin tace "eh wlh aunty meenal kin ganni saurin girma ne dani kawai 15 nake saura 2 moths na cika 16, amma de dady yace ina sss 2 zan zana jarabawa kawai nai canday". "Masha allah, gaskiya kam kina da saurin girma da nayi tunanin ma sa'a ta ce ke". kai a'a aunty meenal shekarar ki nawa?" yesmeen ta faɗa tana tsare meenal da ido". "18 but ban ƙarasa shiga 18 ɗin ba saura 2 weeks na shiga, ita kuma friend ɗina saura 1 week ma". "Hmmm gaskiya kam ke babbace aunty meenal" yesmeen ta faɗa cikin shagwaɓa. murmushi meenal tai sanan tace ki kwantar da hankali ki kema zaki zama babbar ai dan de nan da shekara biyu ma. "hmmm yanzu de bari mu kwanta dare yayi Koh?". gyaɗa kai meenal tai alamun eh. tashi yesmeen tai ta canza light ɗin bedroom ɗin ya koma blue. bayan nan ta buɗe wardrobe ta ɗauko blanket biyu ta miƙawa meenal guda sanan ta ajiye guda inda zata kwanta. Meenal ce ta fara kwanciya daga farko sanan yesmeen ta ƙwanta daga ƙarshe, haka yesmeen tai ta jan meenal da hira, meenal duk da bata son yawan magana haka ta daure tana ta biyewa yesmeen, haka har bacci ya kwashe yesmeen ɗin. Ita kam meenal fafir bacci yaƙi ɗauke ta, saboda tsabar damuwa da halin da mahaifinta yake ciki, sannan kuma ga zance lamarin waleed. haka de meenal tai ta juyi akan bed ɗin yesmeen, ba ita tai bacci ba sai biyu da rabi na dare. Asuba. Kiraye-kirayan sallah da ake ne ya tayar da meenal daga bacci da yake ita bata wasa da sallah. meenal tana miƙewa ta sauka daga bedroom ɗin a hankali sannan ta kunna globes ɗin bedroom ɗin masu haske. Bayan nan dawowa tai ta fara ƙoƙarin tashin yesmeen amma ina yesmeen ta kasa tashi sai mungagi takewa meenal. tashin duniya meenal ta yiwa yesmeen amma yesmeen ta kasa tashi, daga ƙarshe de meenal rabuwa tai da yesmeen ta shiga toilet. Bayan ta gama kama ruwa alwala ta ɗaura sanan ta futo ta zura hijab ɗin ta, ta shimfiɗa daddumar da ta gani a akan sofa. Bayan haka meenal kan dadduma ta hau ta fara gabar da sallah, a sujaddar ƙarshe meenal ta daɗe tana yiwa baba addu'a sannan kuma tana rokon Allah akan auran su da waleed. Meenal bayan ta idar ta gama lazumi komawa tai kan gado gefan yesmeen ta cigaba da tashin ta. ana cikin haka meenal taji an murɗa handel ɗin bedroom ɗin an shigo baki ɗauke da sallama. Momy ce ta shigo, amsawa meenal tai sannan ta tsuguna har ƙasa tana gai da momy. Lafiya ƙalau ɗiyata aminatu, maza tashi ki zauna meenal" momy ta faɗa tana dafe kafaɗun meenal. kamar yarda momy tace haka meenal ta koma ta zauna kan bed ɗin. "Har yanzu yesmeen bata tashi tai sallah ba koh" "eh tun dazu nake tashinta amma naga bata tashi ba" meenal ta faɗa hakan tana sake kallon yesmeen ɗin da take sauke nunfashi ta a hankali". Murmushi momy tai kafin tace "yesmeen ce fa, haka take da ƙyar take iya tashi saboda tana da nauyin bacci" momy ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tashin yesmeen ɗin. Abinka da uwa cikin mintina ƙalilan momy ta tashi yesmeen ɗin, nan fa meenal taga shagwaɓa iri-iri wajan yesmeen karshe de sai momy ce ma ta ruƙe hannun ta suka nufi toilet ɗin domin yesmeen tai alwala. Bayan sun futo daga toilet ɗin momy ce ta sawa yesmeen hijab sanan yesmeen ta fara gabatar da sallah. Kallon meenal momy tai sanan tace “ki shiga toilet kiyi wanka, kafin ki futo zan ajiye miki kayan da zaki sa akan bed”. Meenal ba musu ta miƙe sanan ta wuce toilet. bayan meenal ta haɗa ruwna zafin, wanka ta farayi a gaggauce. Cikin 10 minutes meenal ta kammala wanka sanan ta maida kayan jikinta ta futo. Lokacin da meenal ta futo, har momy ta fita daga bedroom ɗin ita kuma yesmeen tuni ta koma kan bed ta cigaba da baccin ta. amma kamar yarda momy ta faɗa ta barwa meenal rigar da zatasa akan bed. Sabuda abayace dan ko takaddar ta ba'a cire ba, rigar yesmeen ce aka siya mata, kuma tai mata yawa dan bata taɓa sata ba ma. bayan abaya da mayafin ta harda wani sabon pant. meenal kayan ta ɗiba ta sake komawa toilet, ta wanke pant ɗin da ta cire sanan tasa kayan, bayan ta gama shiryawa ta futo. Masha allah abayar tayi matuƙar yiwa meenal kyau. Bayan meenal ta futo, sai ga momy ta dawo ta kawo mata ruwan tea mai kauri da bread da kuma biscuits harma da dankalin hausawa. bayan momy ta fita meenal ba ɓata lokaci ta fara ci tana ci tana mamakin mutunci irin na momy, bayan meenal ta ta ƙoshi, rufe ragowar tai sannan ta komawa gefe ta zauna. Musalin ƙarfe shida momy ta shigo cikin shirinta, sannan ta tashi yesmeen tace mata tai wanka ta shirya domin zuwa school, amma yau ba driver ne zai kai ta ba, in yayan ta zai fita ya sauke ta, saboda driver yanzu zai kai su hospital. Yesmeen bataji daɗi ba da taji meenal yanzu zata taf, haka ta fita ta raka su har babban falon gidan, tana musu bye-bye, bayan sun fuce sa nan ta dawo ta koma bedroom ɗin ta ta shiga wanka. Tun da duku-duku su momy suka isa hospital ɗin tare da manyan kulolin abinci da filas ɗin shayi. lokacin da suka shiga zaune suka samu umma akan sallaya tana ta addu'a'i. cikin fara'a umma suka fara gaisawa da momy. sannan momy ta tambaya umma ya jikin baban?, umma tace jiki da sauƙi dan daran jiya yama farka da daddaren, momy da meenal sunji daɗin hakan sosai da sosai, musamman ma de meenal. Misalin ƙarfe 08:00 meenal ta bugawa ma'eeshat waya a wayar umma, bayan ma'eeshat ta ɗauka sun gama gaisawa, cikin damuwa meenal ta sanarwa da ma'eeshat abinda ya faru jiya da baba. Hankali ma'eeshat ya tashi sosai ba shiri ta kashe wayar domin taje ta sanarwa mami, dama shi abba yayi tafiya bama ya nan, bare shima ta gaya masa, dan haka mami ma'eeshat ta labirtawa hankali tashe. Wajan ƙarfe 10:00 baba ya sake farkawa, lokacin de jiki yayi kyau dan har abinci ya iya ci amma sam de gaba ɗaya baya magana ya kasa cewa komai sai de ya ringa bin kowa da ido, nan ma hankali meenal ya sake tashi sosai dan har sai da tai wani kukan. Likitoci da suka duba baba, allura su kai masa harda ta bacci. ai kuwa cikin ƙanƙanin lokaci baba ya koma bacci. misalin ƙarfe 11:00 momy tacewa umma ya kamata ta koma gida itama tai wanka ta huta zuwa anjima sai ta dawo. Umma farko de tace a'a amma da taga momy ta dage sai kawai ta amince, saboda itama tana so tai wanka, kuma gashi daran jiya bata rintsa ba. meenal ma har tana bawa umma saƙo akan ta taho mata da wayar ta a ɗakinta, tana kan gado. Dama da yake itama momy zata koma gida ta ɗora girkin da za'a kawo hospital da rana, ɗaukar umma su kai a mota domin su sauke ta a gida. meenal kuma aka barta ita da ladidi a hospital wajan baba. Misalin ƙarfe 12:00 meenal suna shan hira da ladidi, wayar umma da take hanun meenal ta fara ringing. bayan meenal ta duba gani tai ma'eeshat ce dan haka baki ɗauke da sallama ta ɗaga wayar. ma'eeshat sanar da ita tai suna cikin hospital ɗin sun zo ita da mami a wana ɗaki aka ƙwantar da su?............. _page 29 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Meenal gani tai ƙwatance baze mata ba gwara ma ta fita ta shigo da su, dan haka cewa ma'eeshat tai bari ta futo tazo ta ɗauke su. Bayan meenal ta kashe wayar da sauri ta futo domin taro su mami. Tun daga nesa meenal tana hango ma'eeshat da mami ta fara yashe musu baki sanan ta ƙarasa da sauri. tana ƙarasawa ta faɗa jikin ma'eeshat suka rungume junan su. Bayan sun saki junan su russunawa meenal tai tare da cewa "mami ina ƙwana?" "lafiya ƙalau meenal ya mai jiki?" "jiki alhamdulilah mami" "masha allah, allah ya ƙara masa lafiya ya tashi kafaɗun sa" ameen mami". Daga haka meenal taja mami da ma'eeshat su kai ciki. lokacin da mami da ma'eeshat suka shiga ciki, hankali su yayi matuƙar tashi ganin yarda jikin baban yayi. Amma bayan sunji labarin mutumci da family ɗin yaro da ya bige baba suke da shi da kulawar da suke basu sai hankali ya ƙwanta kuma suka sake dangana abun da tsautsayi ne kawai. Su mami sunyi kimanin awa ɗaya da rabi, sanan momy ta aiko da abinci kala-kala na alfarma hospital ɗin tacewa driver da ya kawo saƙon anjima zata zo, yanzu tana ɗan wani abun ne. Meenal tasha mamaki irin abincin da su momy suka kawo dan har yayi yawa a ganin ta. Bayan rabin awa da tafiyar driver sai ga umma ta ƙaraso. Kamar yarda meenal ta bawa umma saƙo, kuwa umma ta tawo mata da wayarta ta. Umma tayi farin cikin ganin su mami sosai da sosai, cikin ƴan ƙanƙanin lokaci hira ta ɓarke tsakanin umma da mami, itama meenal tana daga gefe ita da ma'eeshat suna hirar su. Ma'eeshat tana cigaba da bawa meenal labari yarda doctor ashmal yake son ta yake nuna mata kulawa ɗari bisa ɗari. Meenal kuwa jugum tai tana ta sake tunanin yarda baba ya rabata da nata masoyin, kuma tana addu'ar allah yasa komai ya dedeta. Bayan sun gama hirar sunyi sallah la'asar zama su kai suka ci abinci gaba ɗayan su harma da ladidi mai aiki. Lokacin da suka kammala cin abinci baba farkawa yayi, amma de kamar dazu baya magana sai de yabi kowa da ido. Haka de umma ta bawa baba abinci kamar yarda likitoci suka ce sanan ta bashi magani aka sake yi masa wasu sababbin allurai. Likitocin da suka ga hankali su umma ya tashi sunce in sha allah zuwa gobe baba zai fara magana in allurorin sun sake shi, kuma anjima babban likita zai zo ya sake duba shi. hakan ne yasa hankali su umma ya sake ƙwanciya,. ganin magriba ta fara kawo kai hakan ne yasa umma tacewa ma'eeshat su tafi gida saboda abba baya nan, kuma gashi sun bar afnan a gida ita da ƴan uwanta maza, kar ta gaji ta fara musu kuka. Har bakin mota meenal ta rakasu ita da ladidi sanan su kai sallama cike da ƙaunar juna meenal ji take kamar kar tai sallama da ma'eeshat. Mami da momy sunyi saɓani sosai, saboda motar mami tana fita driver su momy ya kutso kai hospital din. meenal da ladidi bayan sun koma, suna zama ko 2 minutes basu yi ba suka ji sallamar momy ta shigo, ita da auta yesmeen, hannu yesmeen riƙe da basket ɗin abinci. Yesmeen ajiye basket ɗin tai sanan tazo ta rungume meenal cikin tsananin farin ciki. Itama meenal rungume yesmeen tai tare da cewa oyoyo, bayan sun saki juna yesmeen cewa tai "aunty meenal ina wuni?". “Lafiya ƙalau yesmeen yakike ya makarantar" "alhamdulilah aunty meenal" "masha allah". Bayan umma da momy sun gama gaisawa cikin sakin fuska momy tace "tun dazu naso zuwa amma yesmeen ta sakamin rigima wai sai na jirata ta dawo daga school mun tafi tare, saboda tana so taga aunty ta meenal. "Allah sarki ai gwara da kika zo da itan" cewar umma, ita kuwa meenal sai sakin murmushi take dan taji daɗin ganin Yesmeen ɗin. Bayan magriba shima dady ya shigo hospital ɗin domin duba jikin baba, kuma ya sake ƙwantarwa da umma hankali sosai da sosai, sanan ya wuce gida. su kuma su momy sun kai kimanin ƙarfe goma na dare kafin su fara shirin tafiya. Lokacin da zasu koma kamar jiya harda meenal suka sake tafiya suka bar umma. meenal bataji daɗin hakan ba sai da ta raya a zuciyarta, dama ɗazu tabi su ma'eeshat gida kawai, dan ita bata son zuwa gidan su momy saboda ba wani sanin su tai ba. Bayan sun isa kamar jiya meenal bedroom ɗin yesmeen suka wuce, yau meenal ta ɗan saki jiki saboda ta saba da yesmeen jiya, kuma bugu da ƙari gashi yau tazo da wayarta ko ba komai tasan zasuyi magana da waleed. Kamar yarda meenal tai tunani, haka taga dm ɗin waleed rututu, bayan ta hau online taga yayi mata magana wajan 20, duk yabi yayi mugun ɗaga hankalin sa bawan allah. nan da nan meenal ba ɓata lokaci, ta fara bashi replay kuma take gaya masa abinda ya samu baba shi yasa ya jita shiru. Ma'eeshat Sai bayan magriba su ma'eeshat suka koma gida ita da umma, suna komawa ma'eeshat ta wuce bedroom ɗin ta. direct toilet ma'eeshat ta shiga tai wanka, sannan ta ɗauro alwala ta futo. A hanzarce ma'eeshat ta shimfiɗa sallaya ta fara gabatar da salla magriba. tana idarwa taji an fara kiraye-kirayan ta isha'i, dan haka miƙewa tai ta gabatar. bayan ta gama addu'o'in ta tai sosai, harda meenal da waleed take sawa kullum tunda abin ya faru. Ma'eeshat tana shafa addu'ar ta miƙe ta koma kan bed ta ƙwanta cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awan gaba da ma'eeshat. Dama ma'eeshat kullum da wuri take bacci saboda suna wayar dare da doctor in de doctor ya dawo bai ji muryar ma'eeshat ba sam baya iya bacci. Misalin ƙarfe 12:00 wayar ma'eeshat ta fara ringing, da sauri ma'eeshat ta buɗe idanuwan ta, dan tasan doctor ne yake kiran ta. watsake idanuwa ma'eeshat tai sanan ta ɗauki wayar baki ɗauke da sallama. Bayan doctor ya amsa ba ɓata lokaci suka fara hira kamar kullum, dan yau ma sai da suka kai har 2:30 suna hira gashi ma'eeshat sai zubawa doctor shagwaba take wanda hakan ba karamin daga masa hankali yake ba. daga karshe ba shiri ya kashe wayar saboda zazzafar sha'awar da ma'eeshat ta tayar masa. soyayyar ma'eeshat ta kama doctor yarda bai taɓa zata ba shi gani yake lokacin auran da aka sa musu yayi tsawo kamar ma tafiya...... Meenal Kiran sallah asubar fari momy ta shigo bedroom ɗin yesmeen ta tashi meenal da yesmeen suka shiga toilet suka ɗaura alwala, bayan sun futo suka gabatar da sallah,. bayan sun idar da sallah yesmeen komawa baccinta tai. Ita kuwa meenal toilet ta nufa tai wanka, kamar jiya kafin ma ta futo har momy ta sake ɗauko mata kayan yesmeen, dan haka meenal tana futowa kwasar kayan tai ta koma toilet tasa kayanta. dan meenal gani take ba zata iya sa kayan ba in bata shiga toilet ba, kamar wani zai shigo ya ganta. Bayan meenal ta gama breakfast ɗinta tass, ladidi ce ta shigo suka fara hira kafin momy ta gama shiryawa. Bayan momy ta gama shiryawa, ladidi har wajan mota ta raka su meenal saboda yau bada ladidi za'a ba. momy da meenal suna shiga ba ɓata lokaci driver ya fuce daga gidan domin zuwa hospital. Lokacin da su meenal suka isa hospital baba ya farka kuma cikin ikon Allah ya fara magana harshen sa ya dawo. Lokacin da baba yaga meenal yayi murna sosai da sosai ya riƙe ta gam ya rungume ta daga zaune kamar wanda za'a ƙwace masa ita. Itama meenal tayi murna sosai, bama ita kaɗai ba har momy taji daɗin hakan, kuma baba da meenal sunyi mugun burgeta ganin yarda suke farin ciki da ganin junan su. Meenal ta sake farin ciki sosai ganin baba da kan sa ya rike cup ɗin tea yayi breakfast. Wajan ƙarfe 11:00 na safe baba ya koma bacci bayan yasha magungunan sa. Itama momy da taga jikin baba yayi kyau cewa tai bari ta wuce gida domin dafa abincin rana amma anjima zata dawo, daga nan kamar jiya suka ɗauki umma domin su sauke umma a gida, ta huta ta ɗanyi bacci. Meenal ita ɗaya aka bari wajan baba, kuma bayan haka likitoci suka ce mata ta fita ta bawa baba waje domin ya huta kuma babban likita ya kusan ƙarasowa. Meenal da taji haka fucewa tai daga sashin baki ɗaya ta koma wajan wasu flowers masu kyau a hospital ɗin suka fara shan chat ɗin soyayya ita da waleed, saboda meenal yau ta nutsu ganin baban nata ya dawo normal. Har doctor ashmal ya shugo hospital ɗin meenal bata sani ba, ita de taji daga nesa-nesa wai ana cewa babban likita zai shigo. Bayan doctor ya shigo sai da aka tashi baba ya duba shi sosai su kai yi maganganu ya tambayi baba yanzu ya yake jin jikin nasa. Doctor ashmal ya jima kan baba saboda tun jiya dady yake masa magana akan dole yazo ya duba jikin baba ya gani ko akwai wata matsalar. Amma doctor ashmal bayan ya duba baba yaga jikin sa da sauƙi ba wata matsalar. Ya bawa likitocin shawara da dama yarda zasu kula da baba, sannan ya ja musu kunne akan su kula da jikin baba sosai kar suyi wasa, saboda shima kamar baba yake wajansa. Likitocin sun amsa umarni da doctor ya basu, kuma sun ce in sha Allah zasu kula. Doctor ashmal yayi hakan ne saboda yarda yaga momy da dady sun damu sosai akan jikin baba, kuma gashi twins ma hankali su ya tashi, musamman ma fadeel da ya aikata lefin. Daga haka doctor ya bar hospital ɗin bai sake duba kowa ba saboda yana da marasa lafiya sosai da suke san ganin sa. Sai wajan la'ar meenal ta miƙe ta ɗaura alwala sanan ta koma cikin hospital ɗin ta gabatar da sallah. meenal bata wani jima da idar da sallah ba momy ta aiko ladidi ita da driver domin ta kawo abinci rana. ladidi tace momy bata ɗan jin daɗi amma zuwa anjima zata dawo. Sai wajan ƙarfe uku sanan meenal da ladidi suka zuba abinci suka fara ci, suna ci suna hira. Bayan sun kammala ci baba ya tashi meenal zuba masa tai shima sanan ta kai masa ya faraci. daga nan kuma meenal da ladidin sukayi sallah la'asar. Masalin ƙarfe 5:30 na yamma baba yana ƙwance akan gado hospital ita kuma meenal tana dage gefe tana danna wayarta. "Aminatu" meenal har tsakiyar kanta taji baba ya faɗi sunan ta. Ajiye wayar meenal tai a cinyar ta sanan ta koma gefan kan baba ta zauna tare da cewa "baba lafiya ko wani abun kake so?" "a'a bana buƙatar komai meenal Allah yayi miki albarka" "ameen baba na" "amma ina so muyi wata magana da ke ne?" "Tom baba ina jin ka" meenal ta faɗa tana tsare baba da ido. “meenal kinga kece kaɗai wanda Allah ya bani na haifa a matsayin ƴa a duniya, kuma ina sonki har cikin rai na duk duniya bani da kamar ki ke da mahaifiyar ki dan haka ina so.........” shiru baba yayi da maganar sakamakon jin sallama. Meenal tana ɗago ido taga dady ne ya shigo fuska nan tasa ɗauke da fara'a. Har ƙasa meenal ta tsuguna ta gai da baba. "lafiya ƙalau sannu ki tashi ya mai jiki?". dady ya tambayi meenal. kafin ma meenal tai magana baba yace "jiki alhamdulilah" duk da kuwa bai san wane ba. Meenal a taƙaice tayiwa baba bayanin wanene dady,. Nan da nan dady ya hau bawa baba haƙuri bisa abinda ya faru, shi kuwa baba yace ba komai ya yafewa fadeel duniya da lahira ai ƙaddara ce. dady yaji daɗin hakan kuma ba laifi sun ɗanyi hira da dadyn. Da baba yaga dady kamar ba yanzu zai tafi ba kuma baba yana son yin magana da meenal, cigaba da magana baba yayi da cewa "aminatu kina jina koh?". Jinjina kai meenal tai tare da cewa"eh baba ina sauraran ka". “Meenal tunda na haife ki duk abinda kike so ina ƙoƙarin yi miki, ina so na faranta miki kuma burinki shine nawa, duk abinda kike so ina maraba da shi banda ƴan ƙwanakin nan da muka samu matsala hakane ko?". Sunkuyar da kai meenal tai sanan ta bawa baba amsa da cewa "eh hakane baba". gyara kwanciya baba yayi sanan ya ruƙo hanun meenal yana cewa "meenal dan Allah dan annabi kimin wanan alfarmar akan waleed". Shiru meenal tai ba tare da tace komai ba sai ma wani yawu da ta haɗiye mai kauri. baba kuwa cigaba da magana yayi kamar haka "nasan kina son waleed kuma ni bazan so na rabaki da abinda kike so ba ko a mafarki ba, amma meenal bani da yarda zanyi, waleed bashi da kyan hali meenal, naso na zaɓa miki mijin da ya dace dake nan kusa-kusa amma gashi rashin lafiya ta kamani, dan Allah meenal ki rabu da waleed, waleed ba mijin aure bane ko kin aure shi ba zaki taɓa samun kwanciyar hankali ba”. “bana so ko bayan idona ki cigaba da ma'amala da shi. Bana son ki auri waleed meenal wanan shine alfarmar da nake so kimin, waleed ba mutumin kirki bane, kuma ke nasan me daraja ce bana so na bawa waleed ke a matsayin miji ba mutum na gari bane kuma be cancanta da ke ba". Wani gigitaccan kuka meenal ta fashe da shi tare da cewa "baba ina son waleed sosai shima yana sona, baba in na rabu da waleed zai shiga wani hali dan Allah dan annabi baba ina roƙanka da ka gayamin mene halin waleed kafin na rabu da shi ɗin, in sha allah in ka gayamin halin nasa in de naji yayi muni zanyi maka biyayya na rabu da shi" meenal ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka mai cin rai, wanda duk wani ɗan adam in yaji tabbas zai sosa masa rai............. mu haɗe a next page. _page 30 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 "Shikenan meenal ki dena kuka in kina kuka zaki ɗagamin hankali zan gayamiki dalilin da yasa na rabaki da waleed duk da kuwa banyi niyar faɗa miki ba amma naga kin takura kuma kin ɗaga hankalin ki". Baba ya ƙarasa maganar tari yana sarƙe masa, da sauri dady da yake gefe ya miƙe tare da cewa "kuyi haƙuri zan sa muku baki akan maganar ku duk da bada ni kuke ba". "Haba aminatu ke da nake ganin kamar kina da hankali kar ki bani kunya mana, idan so hauka ne haƙuri magani ne ai, duk abinda iyaye suka hana ƴayan su wallahi abun ba shi da kyau, kuma abinda babba ya hango yaro baze hango ba, kuma bugu da ƙari iyaye biyayyah dole ce gare su,.Yarda kike da tarbiya kuma babanki yake yaban ki ai be kamata ki matsa masa akan dalilin sa na yanke wukunci akan ki ba, please amina kiyi haƙuri kiyiwa mahaifinki uzuri baki ga halin da yake ciki bane ko bakya tausaya masa?. Fuska cike da hawaye meenal tace "ina tausaya masa dan Allah baba kayi haƙuri bazan sake ba". Baba da yake ƙwance wanda ya gama tari girgiza kai yayi tare da sake matsa hannun meenal da yake cikin hanun sa yana cewa! "Ba komai amina baki yimin komai ba, nide fatana kimin biyayyah Allah yayi miki albarka, ya albarkaci rayuwar ki ya baki miji na gari tare da zuri'a ɗayyiba wanda ko ranar gobe ƙiyama za muyi alfahari da su". "Ameen babana nagode" Meenal cikin shasheƙar kuka ta faɗi hakan, hannu baba yasa ya fara ƙoƙarin sharewa meenal hawaye tare da cewa "ki dena kuma amina bana son gani kina zubar da hawayan ki, dan Allah ki dena kuka". Tom shikenan baba na dena meenal ta ƙarasa maganar tana goge hawayan fuskarta da mayafi. "Nagode sosai bawan allah da kake ɗora ɗiyata turba ta gari". baba ya faɗa yana kallon dady da yake gefan su tsaye. "Ba komai ai nima amina kamar ɗiya take a waje na, amina maza kije wajan ladidi ki zauna kinji kibar baba ya hutu". Ba yarda meenal ta iya haka ta miƙe tsaye domin ta fiya kamar yarda dady ya buƙata, kallon baba meenal tai sakamakon yarda ya rike mata hannu gam yaƙi saki. "Meenal tsayawa tai na kimanin 5 minutes saboda baba ya riƙe hanunta, kuma ita ba zata iya cewa ya saki ba yana binta da wani kallo wanda ita kanta bata san na menene ba. ƙarshe de baba sakin hanun meenal yayi ita kuma meenal ta fara tafiya jiki a sanyaye haka baba yayi ta bin meenal da ido har ta fuce daga cikin ɗakin. Bayan meenal ta fita, baba da dady hira suka farayi sama-sama har aka kirawo sallah magriba dady ya fita yaje yayi sallah magriba sannan ya dawo. jinin baba da dady ya haɗu sosai dan haka sun sha hira baba ya gaya masa magaggauna sosai wanda har su ka kai ƙarfe 9:00 dare suna hira. Lokacin momy da umma sun jima da dawowa hospital ɗin ma, har lokacin dady da baba suna nan suna hira, kai har sai da likitoci suka shigo suka bawa baba magani sanan suka masa allura bacci yayi awan gaba da shi. Bayan dady sunyi sallama da baba ko minti ɗaya bai ƙarasa yabar hospital ɗin yana ta tunanin zantutukan da su kai da baban meenal. lokacin da momy tacewa meenal tazo su tafi gida kamar yarda suka saba sai da meenal ta koma wajan baba, amma sai taga har ya koma bacci dan haka ba yarda ta iya haka tabi momy da ladidi suka tafi zuciyarta cike fall da baƙin ciki. Haka suka ƙarasa gidan jikin meenal a saluɓe, yau de momy tace ta zauna a falo su ɗanyi hira ita da yesmeen harma da ladidi. haka aka kawowa meenal abinci kala-kala suna ta janta da hira, itade meenal daga eh sai a'a kawai take cewa saboda damuwar da take ciki. Har tsakiyar kanta meenal taji anyi sallama amma ta kasa ɗagowa saboda ta tafi duniyar tunanin sahibinta waleed. Ji tai su momy sun fara amsa sallamar, ita kuma yesmeen da take gefan ta a zaune a guje ta ta miƙe ta nufi yayan nata tana masa oyoyo. Bayan ya ƙaraso yana gai da momy, meenal taso gai da shi amma ta kasa ɗagowa, saboda taji ladidi tana gai da shi. da kyar meenal ta iya ɗagowa tare da cewa "ina wuni" ta faɗa tana kallon sa. Lokacin da yaji baƙuwar murya tana gai da shi ɗagowa yayi dan shi tunda ya shigo bai kula da ita ba bare ma yasan da zamanta. doctor yana ɗagowa yayi sukai 4 eyes shi da meenal. kallo ɗaya su kai suka janye idanuwan su, saboda kowa ya sheda kowa. bayan doctor ashmal ya amsa miƙewa yayi ya tafi yana tunanin mai ya kawo wanan yarinyar gidan su kar fa aje itace fadeel ya bige mahaifinta, ya janyo masa baƙin jini wajan ma'eeshat, dan yasan ma'eeshat tana ji da wannan yarinyar. Abinda yasa doctor kallo ɗaya yayi ya sheda meenal saboda yawanci, ma'eeshat tana yawan ɗora status ɗin ta shi wataran yana buɗewa ma yana fara ganin hoton meenal yake dena fita daga status ɗin, yanzu yayi kimanin 2 moths ma baya buɗe status ɗin ma'eeshat saboda meenal. Kuma bugu da ƙara doctor yana da memory mai kyau ko da ace ma'eeshat bata yawan ɗora meenal a status, lokacin da suka haɗu da meenal da ya kalle ta sosai ba abinda zai hana ya gane ta, sai de ya shiga tattamar ina ya santa. “Kai subhanallahi kar de ace doctor ne ya kaɗemin babana?” meenal ta raya hakan a zuciyarta. can kuma wata zuciyar tace mata “a'a shi ai wanca kamar fadeel taji ana cewa shi kuma wannan sunan shi ashmal. Yanzu a taƙaice de ɗan gidan su doctor ne ya bigemin babana a mota. haba no wonder shi yasa nake ta ganin yesmeen kamar na santa, ashe da doctor take kama” duk a cikin zuciyarta meenal take raya wanan abun. Itama meenal ta gane doctor ne ba wai dan kallon da ta taɓa yi masa a zahiri bane yasa ta gane shi, a'a kawai saboda tana yawan ganin picturs ɗin sa wayar ma'eeshat, sometimes ma ma'eeshat ce take saka meenal a gaba wai sai taga hoton doctor, duk da ba shi yake turo mata ba, in yazo zance sai ma'eeshat tai tai masa picturs da video tun yana gajiya har ya zuba mata ido. Firgigit meenal ta dawo daga dogwan tunanin data tafi, sakamaƙwan ladidi ta zungureta da hannu. Momy murmushi tai tare da cewa "yau de meenal naga kamar bata son magana tun da muka tawo a hanya naga tana wanan tunanin maza yesmeen tashi ki kai ta ɗaki ta wuta ta ƙwanta". Murmushi dole meenal tai tare da sunkuyar da kai ƙasa kawai. "Gaskiya de kam hajiya meenal yau da yamman nan naga bata son magana" ladidi ta faɗa tana washe baki. yesmeen hannun meenal taja tare da cewa taso mu tafi aunty na, ba yarda meenal ta iya haka tabi bayan yesmeen suka wuce ciki. Bayan sun shiga bedroom ɗin meenal hijab ɗinta ta cire ta ajiye shi sanan ta zauna a gefan gado. Hawa online meenal tai, tacewa ma'eeshat “dan Allah gobe tazo hospital dan da akwai labari” meenal tana son gobe ta bawa ma'eeshat labarin ashe wai gidan su doctor ashmal ɗin ta tazo take ƙwana. Bayan ta gama turawa ma'eeshat message dawowa kan waleed tai wanda ya zubo mata message rututu, ko tsayawa karantawa ma ba tai ba, tace masa bata jin daɗi zata ƙwanta, saboda tasan yanzu in bata masa reply ba ko bai ganta a online hankalin sa tashe zai yi. daga haka meenal tasa wayarta ta a jirgi sanan ta ajiye ta a gefan gado. Yau meenal saboda damuwa bata ma tsaya yesmeen tai mata tayin kwanciya ba hayewa kan bed tai sanan ta shige cikin blanket tana ta tunanin taya zata fara rabuwa da waleed a rayuwarta. Itama yesmeen da taga meenal ta ƙwanta kuma yau de da gaskiya bata cikin mood ɗin da zasuyi hira, miƙewa tai ta kashe globes sanan ta kunna mara hasken ta dawo itama tabi lafiyar gado ta ƙwanta abinta, ba jimawa bacci ya kwashe ta ita da meenal ɗin. Washe gari. Asubar fari meenal ta farka daga baccin a firgican gaske. sakamako mafarkin da tai, ita de meenal tasan tayi wani mummunar mafarki mai cike da tashin hankali amma ta rasa mafarkin menene dan harma ta manta, duk da kuwa tana cikin mafarkin ta farka. Irin mafarkin nan ne da kake amma kana tashi ko kafin ka tashi harka manta. duk da a.c da take bedroom ɗin hakan bai hana meenal yin gumi ba. Jigum meenal tai tana tunani wana mafarki tai. Meenal yin duniya ta kasa tuno mafarkin da tai, dan haka miƙewa tai ta wuce toilet domin alwala. Meenal bayan ta ɗauro alwala dawowa tai ta tashi yesmeen, domin itama tai sallah. Bayan yesmeen ta shiga toilet ita kuma meenal dadduma ta shimfiɗa sannan ta zumbula hijab ɗinta ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar komawa tai kan kujera ta fara karanta azkhar ɗinta. ita kuma yesmeen ta hau kan daddumar ta fara gabatar da sallah. Bayan yesmeen ta idar da sallah ƙwabar kayanta ta buɗe tare da ɗebowa meenal kayan da zata sa. Kamar kullum abayar ce de wanda ta ɗanyiwa yesmeen yawa, itama sabuwar ce bata taɓa sata ba, dan yesmeen tana da kaya da yawa wanda bata taɓa sakawa ba na maji gaba. da yake mutan gidan suna ji da ita, kuma gata ita kaɗaice mace tilo. Bayan yesmeen ta ɗauki kayan meenal ta kaiwa har inda take zaune. hannu biyu meenal tasa ta ƙarɓa fuskar meenal cike da murmushin dole tace “nagode sosai yesmeen” daga haka meenal ta wuce toilet da kayan. Kafin meenal ta futo daga wanka har an kawo mata breakfast. bayan ta fito zama tai ita da yesmeen suka faraci, saboda yesmeen tana so tace abinci ita da mutum bata son ci ita ɗaya. yesmeen sai janta take da hira, itade meenal tana biye masa bisa dole. Meenal bata ci wani abincin kirkiba ta miƙe saboda gaba ɗaya bata son cin abinci. Meenal tana miƙewa taji an murɗa handel ɗin ƙofar. juyawa tai dan mai shugowa duk da kuwa tana tunanin momy ce zata shigo. Amma ga mamakin meenal sai taga ladidi ce ta shigo cikin zambalelan hijab. murmushi meenal tai tare da cewa "auty ladidi ina wuni?". Amma da mamakin meenal sai taga ladidi tace “lafiya lau” ba tare da tai mata murmushi ba hasalima fuskar ladidi ba annuri, ba kamar yarda take ba kullum in taga meenal tai ta washe mata baki ba. Meenal ji tai jkin ta yayi sanyi dan haka bata sake cewa komai ba. "hajiya tace in kin gama cin abinci zaki iya saukowa mu tafi". "yanzu kuma?" meenal ta faɗa cikin mamaki. Ladidi bata amsa tai da "eh yanzu tace". meenal cewa tai to kawai tana mamaki, a ganinta abinda yanzu garin bai gama wayewa ba da duku-duku kuma haka. Ita de tasan kullum sai gari ya ɗanyi haske suke tafiya. ladidi daga haka bata sake cewa komai ba ta fuce daga bedroom ɗin. meenal wayarta ta ɗauko ta cireta daga jirgi sannan ta zura jijab ɗinta. Yesmeen itama mayafinta ta ɗauka fuska cike da murmushi tace “aunty meenal bari muje na raka ki”. Har bakin mota yesmeen ta raka meenal tana yi mata bye wai sai sun dawo dan Allah yau kar su daɗe, meenal bin da yesmeen tai da to kawai sanan ta shiga cikin motar. Bayan ta shiga fuska a sake tace “momy ina ƙwana?” momy itama fuska babu annuri ta amsawa meenal da "lafiya ƙalau aminatu sannu". Mamaki ya kama meenal a karo na biyu ganin itama momy yau ba sakin fuskar nan ko de dan abinda tai jiya ne taƙi sakin jiki suyi hira?. Meenal tana cikin tunanin nan taji driver yaja mota sun fuce daga gidan. shiru ya ratsa wajan ko ta ina, meenal tai jigum ba tare da tace komai ba, dan har ga allah ta tsargu sosai da sosai. tasan da dane suna shigowa mota ko momy bata yi mata magana ba ladidi zata fara janta da hira. Meenal shiru tai ta su sunkuyar da kai tana addu'a a ranta Allah yasa ba wani laifin tayiwa su momy ba. meenal tana cikin wanan halin taji wayarta da take vibration ta fara ringing. MY ONE AND ONLY sunan da ya bayyana kenan da manyan baƙi kan scaring ɗin wayar. Wato ma'eeshat ce take kira, jiki a sanyaya meenal ta ɗaga wayar tare da karawa a kunne tana cewa “hello ma'eeshat”. Da kyar ma'eeshat ta saita muryarta cikin gunjin kuka tace “wai meenal kun tawo ne?”. Cikin mamaki meenal tace "mun tawo mana, yau da wuri kukazo hospital ɗin kenan lafiya naji kina kuka mai yake faruwa ne?" meenal tana faɗar hakan taji wayar kit ma'eeshat ta tsinke ta. mamaki ya kama meenal sosai dan haka bin number ma'eeshat tai ta kira, sai da meenal ta kira har sau uku amma ma'eeshat bata ɗauka ba. Ƙarshe de meenal haƙura tai, tai jigum tana tunanin mai ya samu ma'eeshat take kuka, dan daga jin muryarta tana cikin tashin hankali, dan tasan in ba abune yayi abu ba ma'eeshat bata irin kukan nan, ko de faɗa su kai da doctor ne, to haka meenal tai ta tunani ita ɗaya ba mai bata amsa. Gaba ɗaya meenal ta tafi wata duniyar, ƙwaƙwalwarta ta rabu sosai, ga lamarin waleed gashi tana so ta tuno mafarkin da tai, kuma gashi taji sahibarta ma'eeshat tana kukan tashin hankali. meenal ta shagala da tafiya duniyar tunani, sai da taji motar ta tsaya cak da tafiya ta dawo hayyacin ta. Lokacin da meenal ta ɗawo mamaki ne ya kamata sosai ganinta a unguwar su maimakon hospital, amma meenal batace komai ba ta buɗe murfin mota ta fara ƙoƙarin fita dan bata kawo komai a ranta ba. Lokacin da meenal ta fita mamaki ne ya kusan kashe ta ganin ƙofar gidan su ya cika da maza maƙil, harma da mata tsuraru suna shiga cikin gidan. Yawancin mutanan da carbi a hanunsu “to inalillahi gobara mu kai a gidan namu ko gine ne ya faɗo” meenal ta faɗi hakan a zuciyarta cikin tashin hankali. To ni kuwa amina bayero nace mai yake faruwa kuwa? to ku biyo ni a text page dan jin ya zata kaya bye. Mu haɗu a next page Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi following. _page 31 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Haka meenal ta cigaba da takawa cikin tashin hankali tana tunanin allah yasa ba wani abun ne ya samu umman ta ba. ƙafafuwa meenal sun mata nauyi da kyar take iya ci gaba da takawa ladidi da momy suna biye da ita a baya. Meenal tana zuwa ƙofar gidan taji baki ɗaya ta kasa tafiya jikinta duk ya mutu. momy ce ta riƙe hannun meenal na dama ladidi ta riƙe na hagu. suka fara jan meenal a hankula, meenal tana biye da su. Lokacin da suka ƙarasa tsakar gidan meenal ganin mutum tai shimfiɗe a tsakar gida an rufe shi da bedsheet. meenal gaba ɗaya kanta ya ɗauke tunanin ta ya ɗauke tama rasa waye ƙwance a tsakar gidan. haka ta runga bin wanda yake ƙwance da ido ita de meenal tasan umma bata da wannan tsayin haka. Mutuwar tsaye meenal tai ganin yatsun baban ta sun futo ba'a rufe ba. “Baba kuma mai ya dawo da baba ko an salla moshi daga hospital ne?” meenal ta faɗi hakan a zuciyarta dan ita tama manta ana mutuwa a duniya. Dafe kafaɗun meenal momy tai tare da cewa " ƴar ta meenal sai dai kiyi haƙuri, baban ya rigamu gidan gaskiya". Tun daga haka meenal bata sake jin komai ba, sai faɗuwa ƙasa tayi samamiya. nan da nan mutane suka fara salatin wanda haka yasa har wanda suke cikin ɗaki suka futo, daga ciki kuwa harda momy da ma'eeshat. Da kyar aka samu aka cinciɓi meenal aka shigar da ita ɗaki, aka fara yayyafa mata ruwa. Ma'eeshat kuwa sai faman kuka take tana jijiga meenal ɗin, meenal tana farfaɗowa ta saki iwu mai cin rai, haka momy da mami su kai ta lallashin meenal, suna ja mata aya da wa'azi ita kuwa meenal ina bama tasan suna yi ba. Daga haka rufe gidan akai dady da abba da kuma wani maƙocin baba aminin sa suka haɗu su kai masa wanka gawa suka saka masa ninkafani. suka gama shirya shi tsaff aka fesa mata turare. Bayan sun gama shirya shi, cewa akai umma da meenal harma da ƴan uwan sa na maiduguri da suka bugo sammako suka zo, domin su samu jana'iza da wuri, su futo suyiwa baba addu'a. Da ƙyar aka lallaɓa meenal tai shiru sanan ta iya futowa domin sallama da baba tai masa addu'a. Bayan ta iso tsugunawa tai gefan kan baba ta, hawaye suna gangarowa daga idanuwan ta, wasu nabin wasu. Itama umma da take dga gefe hawayan take yi, tana yi tana yiwa baba addu'a. Dafe baba meenal tai tana masa addu'a'i kala-kala tun tana sanin wace kalar addu'a take masa har ta rasa wace addu'a take masa kawai tanayu ne, saboda tsabar ruɗu. Hankali meenal bai sake tashi ba sai da 8:00 tayi akace za'a fita da baba domin yi masa sallah akai shi maƙwancinsa na gaskiya. da ƙyar aka ja meenal ta miƙe daga kan gawar baba amma tana miƙewa sai ta sake faɗuwa ƙasa sumamiya Amma duk da hakan ba ai sanya wajan kinkimar gawar baba a makara domin futa da ita ba. Itama kanta umma da take gefe sai da ta zube ƙasa sumammiya, saboda tasan tayi babban rashi a rayuwarta. Allahu Akbar Allah kenan baya barin wani dan wasu suji daɗi. Bayan umma da meenal sun farfaɗo kuka suka cigaba da yi musamman ma meenal wanda baki ɗaya ta fita daga hayyacin ta, bata ji bata gani, duk haƙuri da rarrashin da ake bata gaba ɗaya bata sauraran jama'a kukanta take kawai iya son ranta. Meenal ba ita tai shiru ba sai da aka fara kiraye-kirayan sallah azahar sannan ta tsagaita da kukan nata. Ta miƙe da ƙyar take tafiya saboda tsabar juwa, ƙarshema meenal kasa tafiya tai sai da ma'eeshat ta riƙeta tukunna. Haka de suna tafiya meenal tana tangal tangal kamar wata ƴar koyo, da ƙyar ma'eeshat ta temakawa meenal tai alwala sanan ta maidota ɗaki, itama ta ɗaura tata suka gabatar da sallah. Gida ya cika sosai da ƴan zaman majoki, dady ya siya kayan abinci yimuli guda domin dafawa ƴan gaisuwa. duk abinda ake biƙata ya aika an suyo an kawo tun daga kan kayan miya magi ice daɗe sauran abubuwan buƙata. Ɓangaran meenal tuni zazzaɓi mai zafi ya rufe ta da ciwan kai mai tsananin gaske, ga tashin hankali mutuwar baba ga kuma hayaniyar mutane, dama ita meenal bata cika san hayaniya ba ko shiga cikin jama'a. Tayi kukan tayi kukan har ta gaji tai shiru, fuskar nan tata ta kumbura suntum ido yayi jajir. Bayan zazzaɓi ga ciwan kai da mura da suka rufeta lokaci guda, abun de gwanin ban tausayi. Duk da ma'eeshat tana cikin tashin hankali hakan bai hanata ganin momy tana mata kama da doctor ba, amma bata kawo komai a ranta ba sai take ganin kawai dan itama tana da hasken fatane. Kuma haka nan ma'eeshat taji momy tana burgeta sosai da sosai, sai bunta da ido take tana satar kallon ta. Ƙarshe de dole ma'eeshat ta yarda matar nan tana kama da doctor ashmal ɗinta, amma ko kaɗan batai tunanin momy tama haɗa dangi da doctor ba. Magriba tana kawo kai momy da ladidi su kai wa su umma da meenal sallama domin tafiya gida. Meenal kuwa da ƙyar ta iya yi musu agai da gida, saboda ciwon da ya rufeta lokaci guda baya barinta tayi ko ƙwaƙwaran motsi. Misalin ƙarfe goma kowa ya watse gida ya rage daga umma sai meenal da ma'eeshat, sai kuma ragowar ƴan uwan baba da suka zo daga nesa. Meenal haushin su take ji kamarta kashe su, kamar ba gidan mutuwa suka zo ba. Tun dazu sai hira suke da shewa, kuma suna ta bankawa cikin su abinci suna ci suna tusa. Ƙarshe de meenal da taji ba zata jure ba tashi tai daga falon ta koma bedroom ɗin ta, ba jimawa ma'eeshat ta biyo bayan ta. Meenal tayi jigum ta ƙwanta akan gado hawaye na gangaro mata ta gefan ido. Ma'eeshat da ta shigo, ƙarasowa gefan meenal tai ta zauna, tare da dafata tana cewa "Kiyi haƙuri mana meenal ki dena kukan nan haka yanzu baba addu'a yake buƙata daga gare ki ba kuka ba, ko shi yaga kina kuka baze ji daɗi ba". Da ƙyar meenal ta iya samu ta miƙe zaune tana share hawayen ta ba tare da tacewa ma'eeshat komai ba, tana sake tuna sallamar da su kai da babanta ta ƙarshe a hospital, ashe shi yasan rasuwa zai yi shi yasa ya riƙe mata hannu yaƙi cikawa. Wasu zafafan hawaye ne suka sake gangarowa meenal bayan ta tuna da alfarmar da baba ya nema akan waleed a wajan ta. Ai kuwa kamar ma'eeshat ta shiga zuciyar meenal, meenal sai ji tai ma'eeshat tace "meenal wai kin gayawa wlaeed rasuwar baba kuwa?". Share majina meenal tai tare da girgiza kai alamun a'a. "Gaskiya ya kamata ki sanar da shi bama iya shi kaɗai ba ki sanar da sauran ƙawayanki da wanda kuke ma'amalar arziki dasu". Murya a shage meenal tace "hmmm ma'eeshat a halin yanzu bazan wani iya danna waya ba, bakiji yarda nake ji a zuciyarta ba, ga kuma zazzaɓi da ciwan kan nan da suka rufe ni, idona ma daƙyar nake buɗewa, koya na motsa shi zafi nake ji, hasalima ban san inda na jefa wayar tawa ba. "Eh dazu ni na ɗauketa na ajiye miki ita saboda jama'a bari na ɗauko ni sai na gayawa waleed ɗin, sanan na ɗora a status, ko dan baba ya sake samun addu'o'i mutane". Ma'eeshat ta faɗa tana ɗaga gefan gadon meenal domin ɗauko wayar. bayan ma'eeshat ta ɗauko wayar tana buɗe screen ɗin wayar taga miss call rututu har 20. Dama tasan posword ɗin dan haka buɗewa tai ta shiga call. ma'eeshat tana ganin number da bata ƙasar nan ba, tasan waleed ne. yayi mata kira wajan 12, sauran kuma kiran ƙawayan meenal ne. Wanda ma'eeshat ta tabbatar labarin mutuwa sukaji suka bugo domin yi musu gaisuwa, dan ita meenal ba mai yawan kule-kulen ƙawaye bace. Ma'eeshat bayan ta kunna data direct WhatsApp ɗin meenal ta nufa, wanda message suke ta shigowa. Musamman ma na waleed sun shigo yafi sau 30. “Kai meenal wannan wana kalar so waleed yake miki anya ba haukacewa yayi ba jifa yarda yake turo miki message kamar wanda ku kai shekara ba kuyi magana ba”. Meenal tana jin haka hawaye suka cigaba da ƙwaranyo mata zuciyarta tana sake bugawa, tana sake jin so da tausayin waleed sun mayeye mata zuciya. Ma'eeshat kuwa bayan message sun gama shugowa status ta nufa, ta fara rubutu kamar haka! "inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa mahaifina rasuwa jiya da daddare, yau akai jana'iza da safe ƙarfe 8:00 ina mai barar addu'a a gare ku". Bayan ma'eeshat ta gama rubuta hakan, ɗorawa tai a status sanan ta kashe data, tana ƙoƙarin ajiye wayar taji kira ya shig. number da ta kirawo dazu ce mara suna, wanda ma'eeshat take tunanin waleed ne ita ce take kira, dan number ba bata ƙasar 9ja bace. Ma'eeshat haskawa meenal wayar tai tare da cewa "meenal wanan number waleed ne yake kira da ita Koh?". Meenal da ƙyar ta iya kallon number, ko da ta gani sai da gabanta ya faɗi da ƙarfin gaske, kafin ta ɗagawa ma'eeshat kai alamun eh. Bayan ma'eeshat ta ɗauka ƙarawa tai a kunne tare da sallama. Ma'eeshat tayi mamakin yarda taji waleed ya sauke ajiyar zuciya kamar wanda akai masa bushara da an bashi auran meenal. Bayan waleed ya amsa sallamar ma'eeshat ɗorawa yayi da "ma'eeshat ina mai wayar bata wayar". "A'a yaya waleed taya ka gane nice na ɗauki wayar". ma'eeshat ta faɗi hakan cike da mamaki, "Haba ma'eeshat in banda a binki ko a mafarki naji muryar meenal dole na gane, nasan wanan ba murya meenal bace, kuma nasan ba wanda zata iya ɗagawa meenal waya sama da ke, shi yasa na gane kece". Jinjina kai ma'eeshat tai tare da cewa "eh hakane, yanzu de ba zaka samu damar waya da meenal ba, Allah yayiwa baban meenal rasuwa jiya da daddare kuma yanzu meenal bama ta cikin hayyacin ta da zaku iya waya". "Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un amma shine baku sanar dani ba sai yanzu?". "To ya za ai yaya waleed, kasan de yarda mutuwa take, kowa ya shiga cikin jimami shi yasa" "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah ya jiƙan baba da rahma yasa ya huta". "Ameen yaya Waleed" "yanzu ya jikin meenal ɗin?" waleed ya tambaya cikin damuwa. "hmmm gata nan de jiki sai godeyar Allah kasan de meenal ba zata taɓa dawowa normal ba a hankali yanzu har sai mutuwar baba ta fara sakin ta". "Hakane ma'eeshat amma dan Allah ki zauna tare da ita ki ringa rarrashin ta, ki bata haƙuri ki dena barin tana shiga damuwa sosai kinji?" "tom shikenan yaya waleed in sha allah zanyi iya kacin ƙoƙari na". "Yauwa ma'eeshat nagode kicewa meenal ina yi mata ya haƙuri, kafin muyi waya kuma na dawo nai mata gaisuwa". "tom shikenan yaya waleed sai an jima". daga haka waleed da ma'eeshat su kai sallama tare da kashe wayar. Waleed yana ajiye wayar ya sauke ajiyar zuciya, har ga Allah bai ji daɗin mutuwar baba ba, amma yayi farin ciki da wanan damar da tazo masa ta auran meenal. A fili waleed ya ɗaga hannu tare da cewa "Allah na gode maka, tabbas nasan Allah kana tare da mai gaskiya, Allah kana ganin banji na gani ba baba ya hanani auran meenal yace ina da wasu munanan halaiyar alhalin ni nasan bani da wani ɓoyayyan hali. Tabbas yau na sake yarda da cewa raban aure ko na haiwuwa yana kisa, may be ma Allah ya ɗauki rayuwar baba ne saboda auran mu da meenal tabbatacce ne, duk da ban so ayi auran da haka ba, amma Allah kai ka tsara komai kuma kai ne mai yarda kaso.Tabbas Allah mai tsausayin bawan sane kuma ko wana bawa in ya roƙi Allah zai cika masa burinsa, Allah na gode maka, Allah ka tabbatar da aure na da meenal nan bada jimawa ba, alhamdulilah bi ni'imatika"............. Mu haɗe a next page. _page 32 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Daran ranar dai meeenal juyi ta ringa yi akan bed ta kasa bacci, ma'eeshat kuwa sai faman rarrashin meenal take, karshe de ma'eeshat bacci ne ya kwashe ta ita kuwa meenal yarda taga dare haka taga rana, ɓangaran umma ma, itama bata iya bacci ba haka ta kwana tana tunanin baba. Bayan meenal ta idar da sallah asuba komawa tai ta kwanta kan gado domin tai bacci amma ina ta kasa, gashi tana jin baccin amma bacci yaƙi zuwa, dole haka ta haƙura ta tashi ta dasa wani saban kukan. Da sassafe dady da momy suka zo, suma su mami da abba sun zo, dan ana idar da sallah asuba suka tawo domin su samu sadakar 1. Bayan an kammala yiwa baba addu'a da sadaka, dady da Abba gaisawa su kai saboda sun gane juna. Tun jiya ma dady yake son su ɗan keɓe da abba domin, yasan ya yake a wajan baban meenal. to amma ruɗin mutuwa, gaisawa su kai basu samu damar zantawa ba sai yau. Bayan sun gama gaisawa dady ne yake tambayar abba ya suke da baba. Abba yacewa dady baba aminin sane ya zama kamar ɗan uwan sa na jini ma, haka zalika yaran su ma aminan juna ne, aisha da amina. Jinjina kai dady yayi tare da cewa “masha allah, Allah yayi masa rahma”. dady shima bai ɓoyewa abba abinda ya faru ba, ya bayyanawa abba gaskiyar zance akan yaron sune ƙanin doctor ya bige shi cikin rashin sani. Abba yayi mamakin hakan sosai, to amma sai ya sake ƙwantarwa da dady hankali, da cewa ƙaddara ce kuma da ajali. Haka abba yayi ta ƙwantarwa da dady hankali saboda yaga hankali dady ya tashi sosai, ko ace ma hankali sai yana tashen har lokacin..... Yau ma gidan mutuwa ya cika sosai da ƴan gaisuwa fiye da jiyama. Mutane ne suke zuwa ko ta ina da yake, baba yana da mutane ba laifi. kuma ga sauran ƴan uwa na nesa da ƴan makarantar su meenal. Yau ma meenal wuni tai da ciwan kai tun shekaran jiya rabanta da taci abinci, tun wanda taci a gidan su momy bata sake ci ba, saboda tasan ba zata iya ciba ma yau azumi ta ɗauka, ta mayar da shi na ramuwa. Da magriba ma tayi ansha ruwa, bayan meenal tai sallah kasa cin abinci tai saboda tsananin damuwa, da ƙyar mami de ta tursasawa meenal taci abinci, shima ba wani mai yawa ba sannan tasha ruwa. Sai wajan ƙarfe 11:00pm meenal ta samu salama da yake mutane sun ragu sosai kuma an gama share-share da wanke-wanke, sai taji kunnan ta yayi mata sakayau, saboda bata san yawan hayaniyar nan. Meenal ji tai gaba ɗaya bata jin daɗin cikin ta dan yau 2 days raban da tai wanka. Duk da fankar da take kaɗawa amma tana ɗan jin zafi-zafi, dan haka miƙewa tai ta ɗauki towel ta shiga toilet domin wanka. Ita kuwa ma'eeshat tana daga gefe tana danna wayar meenal tana ta karɓar gaisuwa a online madadin meenal ɗin. Tana yi tana tunawa da sahibin ta doctor ashmal, da yake yau kimanin 2 days basu yi magana ba,. tun da aka gaya musu mutuwar baba da zasu tawo ta manta ma da wayarta ta a bedroom ɗin ta. Amma yau de tacewa ummi ta ɗauko mata wayarta gobe in zata zo, saboda ma'eeshat ba zata iya jure rashin jin muryar doctor ba, ko kuma rashin chat, gaba ɗaya ta shiga damuwa. Bayan meenal ta futo daga toilet ɗaure da towel a ƙirji direct wardrobe ɗin kayanta ta nufa, ta ciro wata doguwar riga mara nauyi sosai, bayan ta ɗauko rufe dorowar tai, sanan ta buɗe ɗayar ta ɗauko bra da pant sanan ta rufe ƙwabar. Sai da meenal ta bawa ma'eeshat baya sanan ta iya saka kayanta, ta yarda bayanta da duwawukanta kawai ma'eeshat zata iya gani. duk da kuwa ma'eeshat ɗin hankali ta baya kanta, amma meenal ta cika jin kunya ne. Dan da ma'eeshat ce zata sa kayan to tass, a gaban meenal taza iya sawa ba tare da ta bata baya ba,. Sau nawa ma ma'eeshat tana saka kaya gaban meenal sai dai meenal ɗin ta ɗauke ido, tai tai wa ma'eeshat faɗa, tana cewa bata da kunya. itama ma'eeshat ɗin ta ɗauki meenal kamar ƴar uwa, jinta take kamar twins shi yasa zata iya komai gabanta. In ba gaban mamin ta ba ko meenal ɗin ba gaban wanda zata iya buɗe tsiraicin nata. itama meenal bawai dan bata yarda da ma'eeshat bane take kin cire kaya ko sawa a gabanta a'a kawai tsabar tsananin kunya ce, amma wataran in tana sauri shirin tafiya makaranta, tana iya canza kayan gabanta ma. Meenal bayan ta gama shiryawa kusa da ma'eeshat ta dawo ta zauna jiki a sanyaye. ma'eeshat tana ƙoƙarin magana sai ga kira ya shigo, wayar meenal ɗin da take hannun ma'eeshat. ma'eeshat da take danna wayar ɗagowa tai tare da kallon meenal tana cewa “yaya waleed ne yake kira”. Kawar da kai gefe meenal tai tare da cewa "dan Allah ki rabu da shi, ni ba wata waya da zan iya yi da shi". gyaɗa kai ma'eeshat tai sannan ta ajiye wayar tana cewa "tom shikenan yarda kika ce ya jikin naki?". "Lumshe jajayan idanuwa meenal tai, kafin tace da sauƙi". ma'eeshat sake tambayar meenal tai da "ko na kawo miki maganin ciwan kai da ruwan ki sha?". meenal tana ƙoƙarin magana wayarta ta fara saban wani ringing". Wani siririn tsaki meenal taja, dan tasan ko ba'a gaya mata ba waleed ne. ita kuma ma'eeshat bin meenal da ido tai gaba ɗaya bata so tai mata dole akan ta ɗauki wayar waleed. "wallahi ma'eeshat na gaji da nacin waleed, ko bai san halin da nake ciki ba ne ya barni na huta mana". Dafa kafaɗun meenal ma'eeshat tai kafin tace "kiyi haƙuri ma'eeshat, waleed ɗin ne gaba ɗaya ya haukace, wani irin mahaukacin so yake miki wanda baya iya control ɗin kan sa, dan Allah ki ɗaga naji muryar ki ko na 20 second ne, may be hankalin sa ya ƙwanta". Taɓe baki meenal tai ba tare da tace komai ba har wayar ta katse. Bayan wayar ta katse wani kiran ne ya sake shigowa, again waleed ɗin ne. hannu ma'eeshat tasa ta ɗauki kiran, tana ɗauka ta karawa meenal a kunne. Da ƙyar meenal ta iya amsawa waleed sallamar da yayi murya a dashe. wata wawuyar ajiyar zuciya waleed ya saki wanda ta yau ma tafi ta ko wace rana. Murya na rawa yace "meenal ɗina ya kike fatan kina lafiya ya ƙarin hakurin baba?". Murya a sanyaye meenal ta bawa waleed amsa da "alhamdulilah" "to Allah yajiƙan baba yayi masa rahma yasa ya huta, Allah yasa annabi yasan da zuwan baba" "ameen ya rabbi nagode sosai waleed" "meye na godiya meenal, nima ai baba na ne ko". Haɗiye yawu meenal tai kafin tace "haka ne" "tom dan Allah meenal ɗina kiyi tawakkali naji muryarki ta nunamin kina cikin tsananin damuwa sosai, Allah ne ya bamu baba kuma ya fimu san sa, shi yasa ya ɗauki kayan sa, yanzu tsakanin ki da baba addu'a ce, kiyi haƙuri ki daure duk da mutuwar iyaye tana da zafi to amma dole sai anyi haƙuri". "Wasu zafafan hawayan tausayin waleed da tsausayin kanta ne zuka zubowa meenal, a zuciyarta tace oh Allah sarki shi waleed bashi da uwa bashi da uba yake bata haƙurin rashin da tai, ai shine abun tausayin ma, kuma gashi ana so a raba ta da shi, ko tace an raba ta da shi ma. Muryar waleed meenal ta sake tsinka yana cewa, "kinji meenal ɗina dan Allah ki dena yawan kuka da damuwa" meenal saisaita muryarta tai yarda waleed ba zai gane tana kuka ba ko maganar da yayi gaya mata ta tsinka mata zuciya ba. "Tom shikenan waleed nagode sosai da shawararka kuma in sha allah zanyi amfani da ita, yanzu ina so nai bacci ne bye". "tom shikenan meenal ɗina bye i love you for ever”. daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta ɗan ture wayar da ma'eeshat ta riƙe ta kara mata a kunne. Katse wayar ma'eeshat tai, bayan ta katse kallon meenal tai tare da cewa "yauwa ko ke fa na kawo miki maganin ciwan kan kisha koh?". gyaɗa kai meenal tai alamun eh, ma'eeshat kuwa miƙewa tai domin kawowa meenal maganin. Ma'eeshat magugguna uku ta kawowa meenal, dana ciwan kai sai ciwan jiki, da kuma wanda zai sata tai bacci, tare kuma da ruwan jarka. Bayan ma'eeshat ta buɗewa meenal ruwan, miƙa mata tai sannan ta fara ɓallo mata magungunan tana bata, ita kuma meenal tana sha. Bayan meenal ta gama sha, ma'eeshat cewa tai ta tashi daga kan gadon domin ta gyara bedsheet ɗin saboda duk ya yamutse. Ma'eeshat bayan ta gyara bed ɗin pillow ta sakawa meenal ɗin sannan ta kamo hannunta ta ƙwantar da ita kan gado ta lulluɓa mata blanket. Bayan haka ta koma ta kashe musu hasken ɗakin kamar yarda meenal ta buƙata, sannan ta kunna futula caji mara haske. daga haka itama ma'eeshat ta ƙwanta akan gadon. Shiru ne ya ziyarci wajan kafin meenal tai ƙarfin halin cewa “ma'eeshat kinyi ƙoƙarin naga baki zo da wayarki ba, nasan kina nan kina tunanin doctor ɗin ki Koh?”. Murmushi ma'eeshat tai sannan tace “uhmm ke de bari meenal to ya za ai mutuwa ba wasa ba, amma saboda tsabar tunanin sa ni gani nake wata mata suna yimin kama, da na ɗauka shige suke amma sai kullum nake ganin kamar su tana ƙaruwa sosai”. cikin mamaki meenal tace “wata mata" dan ita tama manta da babin momy maman doctor ce. "Wata mai haske haka wanda naji kina ce mata momy, wata mai kirki haka". Cikin dashashiyar murya meenal ta katse ma'eeshat da cewa "sadaƙallahul azim, yi shirun ki momy ko, ai kam maman doctor ashmal ce in gaya miki ita ta haife shi, shine babban ɗanta ma". Da sauri ma'eeshat ta tashi daga ƙwanciyar da tai tare da cewa "kai haba da gaske, ke waye ya gaya miki?" meenal gyara ƙwanciya tai tare, da cewa “ina ta zuci-zuci na same ki na baki labari, sai kuma mutuwar baba ta riske mu". "Allah ya jiƙan baba, ma'eeshat ta faɗa jikin jimami". "Ameen ma'eeshat, kin san gidan da nake ƙwana wajan momy, gidan su ne fa, ni ban taɓa sani ba sai daran ƙarshe naga doctor ya shigo, wata ƙanwar sa yesmeen ta tafi ta rungume shi tana masa oyoyo, to naji ana ta gai da shi, nima bayan na gai da shi kamar ance in ɗaga kai na kawai naga doctor ki, wai ashe ƙanin sa ne ma ya bige baba a mota". cikin ruɗu ma'eeshat ta zaro ido tare da dafa ƙirji tana cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, dan Allah ƙanin doctor ne ya bige baba?". "Eh ma'eeshat shine amma ya za'ai ƙaddara ce kawai". shiru ma'eeshat tai murna ta koma ciki da taji abinda ƙanin doctor ɗin ya aikata. jiki a sanyaye ma'eeshat tace “amma shine baki taɓa gayamin ba sai yanzu”. "Ai nima nace miki ban san ƙanin sa bane sai daran da baba zai rasu, kuma nayi niyar, washe gari in muka haɗu na baki labari, sai baba ya rasu, nima dududu ban fi ƙwana biyu da sani ba". "jiki a sanyaya ma'eeshat ta ƙwanta tare da cewa eh hakane kam". To daga haka ba jimawa bacci gajiya, wahala, damuwa, ya kwashe meenal, ma'eeshat tayi farin cikin hakan sosai ganin meenal ta samu bacci itama ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita...... DOCTOR ASHMAL Gaba ɗaya doctor yana cikin tsananin damuwa 2. na farko rasuwar baba, yana tunanin in ma'eeshat ta samu labari ƙaninsa ne ya bige baban ƙawarta kar tace ta dena son sa, dan yasan halin yarintarta da kuma yarda take matuƙar ji da ƙawar nan tata. Na biyu kuma too days ya dena samun ma'eeshat a waya ga rashin jin muryarta. hakan ba ƙaramin tayarwa da doctor hankali yayi ba, doctor bai taɓa tunanin haka yake mugun son ma'eeshat ba sai yau. kuma bai taɓa ganin tasiri da shaƙura da su kai ba sai a lokacin. kuma a lokacin doctor ya gane amfanin wayar da yake da ma'eeshat a rayuwarsa. gaba ɗaya ko hospital yaje baya iya wani aikin kirki yake dawo gida, raban da doctor yaga abinda yake hana shi sukuni ko kuma yake yawan tunanin sa har ya manta a rayuwar sa, kamar yarda yake jin ma'eeshat. Shi doctor ba wani mutum ne da ya cika sa damuwa da tunanin bane akan sa, tun asalin rayuwarsa ma, kafin a samu abinda yake damun sa za'a jima, amma yau sai gashi ta sanadiyyar so da tunanin ma'eeshat ya kasa aikata komai............ mu haɗe a next page. _page 33 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Washe gari. Yau ma anyiwa baba sadakar uku da sassafe, kamar kullum momy tazo ana karɓar gaisuwa da ita. sannan momy sun haɗu da mami da yake sun samu labarin wajan mazajan su, an gaisa sosai cikin sakin fuska da raha. Momy tayi farin cikin ganin surukar ta ma'eeshat sai wani kaffa-kaffa take da ita, tana nunawa ladidi ita, harma da yesmeen da yake yau da ita kazo, tana cewa tazo taga matar da yayanta zai aura. Da yake yesmeen tana kusa da meenal saboda sun ɗan fi sabawa. yesmeen itama taji daɗin ganin ma'eeshat sosai ta gai da ita tana ta sakar mata murmushi. momy ma sosai ta sakarwa ma'eeshat fuska sai kace ba gidan mutuwa ba sai wani jan ta take a jiki. Duk da ma'eeshat bata wani cika jin kunya ba amma sai da taji kunyar momy sosai. mami taji daɗi haɗuwa da momy, musamman yarda taga momy nada kirki sosai sai jan ma'eeshat ɗin take a jiki. A zuciyar mami tana cewa tabbas ɗiyar ta ma'eeshat tayi sa'ar suruka. Ma'eeshat ji tai gaba ɗaya ta fara jin kunyar momy, kuma gashi ba dama ta ɗago kai sai sun haɗa ido da momy tana ta faman sakar mata murmushi, ma'eeshat sai mamakin irin mutuncin matar take yi, yarda kasan ta goya ta sai kace kanta aka fara suruka. Wajan sha biyu ma'eeshat ta ƙarbi wayar mami ta bigawa driver kan yazo ya ɗauke ta gidan su meenal, ya mayar da ita gida. ma'eeshat ji tai ba zata iya zama ba, sabida mami bata ɗauko mata wayar ba wai ta manta, kuma gashi ita ba zata iya jure rashin yin magana doctor ba. Kuma tana so taje gida ta huta da hayaniya ga kuma kunyar surukarta, momyn doctor da take ji. Bayan ma'eeshat tayi sallah la'asar, lokacin driver yazo ɗaukan ta, sallama tayiwa meenal, tace mata zuwa azahar zata dawo tana so taje gida. sai da ma'eeshat taga momy ta tayar da sallah sannan ta yiwa ladidi da yesmeen sallama, tace musu in momy ta idar ko zata neme ta, sai sucewa mata ta tafi gida ba zata jima ba zata dawo, daga haka ma'eeshat ta sulale abinta. Ma'eeshat tana futa daga gidan su meenal ba ɓata lokaci ta shiga mota driver ya tayar suka bar gidan. suna tafe ma'eeshat tana tunanin momy. A zuciyarta tana cewa dama haka ahalin doctor suka da mutunci, ashe duk mutunci doctor ashmal ko ƙafar momyn sa bai kama ba. Ko da yake shi doctor bashi da sakin fuskar kamarta su momy da sa yesmeen, shi in baku saba ba ma kafin kaga murmushin sa ma za ka jima. Itama ma'eeshat sai da suka jima da doctor yake iya yin dariya gabanta, hakan ma ba kullum ba wataran har yazo ya tafi baze mata dariya ba sai de murmushi kawai. Bayan su ma'eeshat sun ƙarasa gifa, driver yana parking ma'eeshat ta futa da sauri. Baki ɗauke da sallama ma'eeshat ta shiga babban falon gida. sabuwar ƴar aikin su ce zaune ita da afnan suna kallo a tv. Afnan tana ganin ma'eeshat ta taso a guje ta rungume ta cikin farin ciki. Itama meenal rungume afnan ɗin tai tare da ɗaukar ta, bayan sun gama wasa da dariyar su, ma'eeshat sauke afnan tai sanan ta wuce bedroom ɗin ta. Tana shiga bedroom ɗin ta kayan meenal ta cire daga jikin ta, sannan ta nufi toilet a hanzarce domin wanka. bayan ta futo ƙirji ɗaure da towel riga mara nauyi ta ɗauka tasa a jikin ta. bayan tasa kashe AC ɗin bedroom ɗin nata tai, sanan ta buɗe tagogin saboda ita iskar Allah take son sha ba AC ba. Daga haka ma'eeshat ƙaramar dorowar gefan gado ta buɗe ta ɗauko wayarta sannan ta kunna ta, ta dawo kan gadon ta zauna. Wayar ma'eeshat tana gama kawowa cireta tai daga security, sanan ta shiga call domin kiran sahibin ta doctor……… Gaba ɗaya yau ya kasa komai a hospital, jiya ya ɗanyi ƙarfin halin duba wasu marasa lafiya, amma yau ya kasa, dan haka bayan yayi sallah azahar office ya koma ya ɗauki laptop ɗin sa da wayoyin sa, sanman ya fice daga hospital ɗin. Doctor yana shiga mota ya ajiye wayoyin sa da laptop ɗin sa a kan kujerar gaba, sannan ya ɗan ƙwantar da kujerar motar domin ya samu ya ƙwanta dan gani yake baze iya driver yanzu ba saboda damuwa. Lumshe idanuwan sa yayi, kamar mai bacci yana tunanin ma'eeshat, saboda me wayarta take a kashe, kuma babban tashin hankali doctor ma'eeshat bata neman sa ko ta wace wayar dan yasan ta haddace number sa. Doctor ya ɗauki kimanin 30 minutes a haka dan har bacci ya fara ɗaukar sa sama-sama, kawai yaji wayarsa ta fara ringing. Ji yayi kamar kar ya buɗe idanuwan sa, har wayar ta kusan katsewa ya ɗan buɗe idanuwan sa, sannan ya juyar da kan sa gefe daga ƙwance dan yaga me kiran. Tuni idanuwan doctor suka washe damuwa bacci suka fuce a lokacin, saka maƙwan ganin ma'eeshat tana kiran sa. da sauri doctor ya kai hannu, amma kafin ma ya ɗauki wayar kiran ya katse. doctor yana ɗaukar wayar ya fara ƙoƙarin bin ma'eeshat ɗin. Amma kafin ma doctor ashmal ya kai da bin ma'eeshat ɗin, itama ta sake kiran shi. sai da doctor ya ɗan ja aji kaɗan kafin ya ɗauki kiran, duk da kuwa damuwa da ma'eeshat ɗin da yayi amma abin a jinin sa yake, komai a nitse yake. Doctor bai kara wayar a kunne ba a handsfree ya saka ta sanan ya rufe ido kamar dazu, kafin ya rangaɗawa ma'eeshat sallama cikin dadaɗar muryarsa. Bayan ma'eeshat ta amsa sallamar ƙarawa tai da cewa "ai nayi tunanin ba zaka ɗauki wayar tawa ba". "no me zai hana na ɗauki wayarki kuwa?". gyara zama ma'eeshat tai kafin tace "aiki mana, nasan ko aiki yayi ma yawa". Murmushi doctor yayi a zuciyarsa cewa yayi “hmmm lallai baki san halin da na shiga bane rashin ki” amma a fili cewa yayi "a'a ko ina aiki in de naga kiran ki zan ɗauka mana sai nace miki aiki nake a lokacin, bayan na gama kuma sai muyi wayar". "Tom yanzu de fatan ba aikin na katse maka ba Koh?" "a'a kin kirawo a dede bana aikin komai sai aikin tunanin ki". "hmmm banga alama ba ai nayi tunanin baka damu dani ba". Murmushi yaƙe doctor yayi, saboda shi ba mutum bane wanda zai iya tsayawa yana faɗar adadin damuwar da ya shiga akan abu, a ganin shi hakan ba tsari bane, amma da zai iya gayawa ma'eeshat damuwa da ya shiga akan ta, daya bata labari. Amma a fili cewa yayi "hmmm rigima ko na damu dake mana sosai eshata, ina kika shiga kika manta da ni haka ko laifi nai miki". "Kai ma kasan bazan manta da kai ba, baban meenal aminiya ce ya rasu kaga kuma kamar babana ne dole na shiga damuwa". Dama doctor yasan abinda zata faɗa kenan kawai ya tambaye ne "innalillahi Allah ya jiƙansa da rahma yasa ya huta, zan zo nai miki gaisuwa har gida". "Ameen kai kenan baka sani ba sai yanzu, ai nayi tunanin zaka sani tunda ance ƙanin kane ya bige shi har ya ƙwanta gadon hospital kafin ya rasu". "Eh na sani, kuma har jana'iza naje, kuma ina fatan zaki karɓi hakan matsayin kaddara". "eh in sha allah na ɗauki kaddara" ma'eeshat ta faɗi hakan cikin murya mai nuna damuwa. ajiyar zuciya doctor ya saki tare da cewa “masha allah haka ake son bawa ya kasance me ɗauakr kaddara Allah ya jaddada rahma gare shi". "Ameen kasan mene?" Girgiza kai doctor yayi kamar yana gaban ma'eeshat ɗin tare da cewa "a'a sai kin faɗa". "tun da naje zaman makoki nake ganin wata mata mai kama da kai". "uhmmm" doctor ya faɗa alamun yana sauraran ma'eeshat ɗin. ma'eeshat cigaba da magana tai kamar haka "kullum sai naga kamar ku tana ƙaruwa, shine jiya da daddare na faɗawa meenal sai take cemin maman ka ce". Numfashi doctor ya sauke kafin yace "momy nah kike cewa wata mata Koh?". "sorry nifa dan ka gane labarin nace maka haka amma na deba". "yauwa in zaki sake kiranta next kice mata momy kinji?" "tom shikenan na cigana da baka labarin?". "Uhmmm inaji?" "Yauwa shine yau da safe bayan tazo, bakaga yarda ta ringa ji da ni ba kamar ƴar baby, gaskiya momy tana da kirki sosai". wani siririn murmushi doctor yayi kafin yace "tom ƴar gidan momy farkon tambayar da zan miki shine ya akai momy ta gane surukar ta?". "Eh dadyn ka ne da abbana suka haɗu a gidan rasuwar, shine suma suka haɗa momy da mami" wata siririyar dariya doctor yayi tare da cewa "hmmm lallai wanan kin iya ƙwaɓa labari, kuma gashi na gane sosai". "murmushi ma'eeshat tai ba tare da tace komai ba". "Next question kina jina?" doctor ya tambayi ma'eeshat, jinjina kai ma'eeshat tai kafin tace “eh ina jinka”. "taya akai ƙawarki tasan momy mamana ce?" "uhmm tace min daran da baba zai rasu bayan sun zo gidan ku da momy ta ganka ka dawo gidan, shine yasa, ta gane momy maman ka ce". Jinjina kai doctor yayi a zuciyarsa yana mamakin har taya akai meenal ta gane shi haka, amma ba mamaki yawan ganin hoton sa ne wayar ma'eeshat shi yasa ta gane shi. "Tom shikenan yaushe zan zo nai miki gaisuwa?" doctor ya tambaye meenal yana buɗe idanuwan sa. "zama ka iya zuwa yanzu in kana da time, saboda zuwa anjima zan koma gida su meenal, yanzu ma dawowa nai saboda na ɗauki wayarta, kuma na ɗan huta, da hayaniyar mutane". "Tom shikenan gani nan zuwa" doctor ya faɗa cikin zumuɗi, saboda yana fala'in son ganin ma'eeshat ɗin, dama tunda suka fara soyayyah bai taɓa ganin ta da rana ba ga kewar ta da yake yi. "Tom shikenan sai kazo" ma'eeshat ta faɗa daga haka ta katse wayar,. Bayan sunyi sallama doctor ajiye wayar yayi sanan ya gyara kujerar sa ya tayar da motar sa. Lokaci guda doctor ya dawo dai-dai, yaji gaba ɗaya damuwarsa ta tafi, har wani ƙwari yaji jikin sa ya ƙara. Daga haka ba ɓata lokaci doctor ya fuce daga hospital ya kama hanyar gidan su masoyiyar ma'eeshat............... Kuyi haƙuri da wannan bazan iya cika muku page ba yau. mu haɗe a next page _page 34 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ma'eeshat tana katse wayar ta sauka ƙasa ta zuba abinci taci a hanzarce sanan ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta futo. ma'eeshat tana futowa ta nufi bakin merro ta zauna ta fara tsane fuskarta. Bayan ta goge fuskarta tas hoda ta shafa sama-sama sannan ta hau gyara jagirar ta wanda ta hargitse, duk da kuwa bata da wani yawan arziki. bayan ma'eeshat ta taje girarta ta, brown ɗin jagira ta ɗauka ta ɗan ƙara tura jagirarta ta sama-sama. Nan da nan jagirar ta futo raɗau tayi kyau sosai, bayan ta kammala. black liner ta jagira ta ɗauko tai zagaye bakin ta, shima sama-sama sanan ta shafa lipstick. wow masha allah nan da nan bakin ma'eeshat ya dawo cass cass abinta. Bayan ta kammala ƙwalli ta ɗauko tasa a idonta yarda baze zazzago ba, sannan ta fara gyara gashin kanta tana sa jel. Ai kuwa gashin ya ƙwanta luf musamman ma sajan nata tayi kyau abinta ta futo rass. Daga haka ma'eeshat ta miƙe ta buɗe drowar ta ɗauko jar abayarta mai ratsin baƙi a gaban rigar da, kuma hanunta, tai matuƙar kyau abayar tasha stone ko ta ina sai walwali take yi. Buɗe rigar tai sannan ta cire kayan jkinta ta fara ƙoƙarin sawa. Tana sawa a zuciyarta tana cewa oh karfa ya gaji da ganina da abaya kusan kullum abaya. haka de ma'eeshat ta cigaba da saka abaya. bayan ta kammala rebom ɗin ta ɗauko ta ɗparking ɗin kanta har guda biyu. Daga haka ta ɗauki hula wanda ta ɗan kama kanta tasa daga baya-baya, yarda bata rufe mata sajen ta ba. Bayan ta kammala ta ɗauko black ɗin mayafi na abayar, shima mai ratsin ja ta fara ƙoƙarin sawa. Kafin ma'eeshat ta kai da yafa mayafin Jin wayarta tai ta fara ringing, da sauri ma'eeshat ta nufi wayar a fili tace "ko yazo ne?". Tana ƙarasawa ta ɗauki wayar a hanzarce, sanan ta ɗaga. Bayan doctor yayiwa ma'eeshat sallama ta amsa cewa yayi "gani nan na ƙaraso". murmushi ma'eeshat tai kamar tana gaban doctor sannan tace "tom gani nan futowa". ma'eeshat da sauri ta ɗauko takalmin ta baƙi tasa, bayan tasa plat ɗin takalmi, merro ta nufa ta saka ɗan kunne ta tare da abin hannu, sanana tai rolling ɗin kanta da mayafin a bayar. tabarakallah masha allah ma'eeshat tayi matukar kyau sosai kamar ka sace ta. Daga haka ma'eeshat wayarta tasa a caji, sannan tasa ta kalmin ta plat, ta fuce daga bedroom ɗin a hanzarce. Ma'eeshat tana futa daga gidan ta fara canza tafiyarta cikin salo mai jan hankali, tana tafiya cikin rangwaɗa. Ɓan garan doctor kuwa, yana daga zaune a motar kamar ance ya ɗago yana ɗagowa ya hangi ma'eeshat tana tafiya ɗai-ɗai abinta. wata nannauyar ajiyar zuciya doctor ya sauke tare da sake tsurawa ma'eeshat ido sosai. Doctor yana ganin ma'eeshat tana gab da ƙarasowa ya dakata da kallon ta tare da buɗe murfin motar, amma ba tare da ya futo ba. har wani Allah-allah doctor yake ma'eeshat ta ƙaraso saboda yarda yake zumuɗin ganin sa. Ma'eeshat tana ƙarasowa bakin ƙofar ta tsaya cak ba tare da ta sake wani motsi ba. doctor yasan halin abarsa da rigima, dan haka dole ya futo fuska a sake. doctor ya kasa magana saboda yarda yaga ma'eeshat tai masa wani irin kyau na musamman, har ga Allah shigarta tana mugun burge shi. Ma'eeshat da taji shirun yayi yawa a hankali ta ɗago kai ta kalli doctor, ai kuwa caraf suka haɗa ido, wani kyakyawan murmushi mai kashe zuciya doctor ya sakar mata sannan ya ɗauke idon sa a na ma'eeshat ɗin dan shi bai yarda da haɗa idon nan ba yanzu hankalin sa zai tashi. Sai da doctor yayi ƙarfin hali ya saita kansa sannan yace "ki shigo ciki motar mana sai yafi naga wajan kamar akwai rana Koh?". Girgiza kai ma'eeshat tai kafin tace, "kai da nake ƙoƙarin nace maka ka shigo cikin gida". "A'a sauri nake yi ne kin san gaisuwa nazo yi miki ai ba daɗewa zanyi ba, nan da few minutes zan tafi". jinjina kai ma'eeshat tai, har zuciyarta bata ji daɗi ba da doctor yace mata ba daɗewa zai yi ba, dan haka rai ba daɗi ma'eeshat tace "to tunda ba jimawa za kai ba ai shigowa bata kamani ba zamu iya gama gaisuwar anan". "Hmmm eshata kin cika rigima fa, ki shigo ai tsayuwar nan ba za tai ba". "fuska ba yabo ba fallasa ma'eeshat tace "tom shikenan naji" daga haka ta fara tafiya a hankali domin zagayawa, doctor yaso ya raka ma'eeshat ta zagaya, amma yasan rikicewa zai yi ya kasa control ɗin kan sa shi yasa ma bai soma ba.komawa cikin motarsa yayi sannan ya buɗewa ma'eeshat murfin motar. tana zuwa ta shigo a nitse, bayan ta zauna magana ta farayi kamar haka. "sannu da zuwa ya hanya?". Wani madanni doctor ya danna a gaban motar, wanda hakan yasa murfin ƙofar ɓarin ma'eeshat da kansa ya rufo, sannan ya amsa mata da "lafiya ƙalau my future wife yakike?". "Nima ina lafiya ƙalau amma dama baka rufe ƙofar ba mu da ba jimawa zamuyi ba kawai ka buɗe min". "Ai eshat ta bana so rana ta taɓa min ke, amma ai ba complete na rufe ƙofofin ba bakiga nabar ta ɓangare na a kunne ba". "satar kallon sa ma'eeshat tai kafin tace “uhm haka ne, to kai baka tsoran ranar?". Murmushi doctor yayi sannan ya kawai da kansa yana cewa "kar ki damuwa ba komai, ya kuma ƙarin haƙuri Allah ya jiƙansa da rahman allah yasa ya huta". “haƙuri da godiya ameen ya rabbi" ma'eeshat ta ƙarasa maganar cikin jimami. doctor canza zance yayi da cewa "kinyi kyau sosai eshat ta". murmushi ma'eeshat ta saki tare da cewa "da gaske?". jinjina kai doctor yayi tare da cewa "sure". Cikin farin ciki ma'eeshat tace"thank you". "tom yar gidan momy kar ki samu damuwa". doctor ya ƙarasa maganar yana danna wayarsa, dan baze iya jure ganin ma'eeshat ba, tayi mai kyau sosai, baya so ya ringa yi mata kallon da ya zarce ƙa'ida, dan komai zai iya faruwa. Ma'eeshat tana jin haka ta saki murmushi tare da cewa "gaskiya momy tana da kirki sosai, nayi dacan suruka". murmushi sosai doctor yayi wanda har ana iya jin sautin dariya yana futowa sama-sama a murmushin nasa, saboda ma'eeshat ta bashi dariya sosai. Itama ma'eeshat ɗin dariya tai, saboda har ga Allah yarda doctor yayi murmushi da gajeriyar dariya yayi matuƙar burgeta sosai kuwa. haka ma'eeshat tai ta gayawa doctor mutuncin momy kamar bai san momy ba, in kaga yarda ma'eeshat take yaba momy sai kace mamanta ce bata doctor ba. shi kuwa doctor sai murmusawa yake, saboda labarin ma'eeshat ɗin nishaɗi yake bashi da dariya. to doctor da ma'eeshat sun jima sosai suna hira shi da yazo da niyar tafiya da wuri, har sai da aka fara kiran sallah la'asar sannan yayi mata sallama suka rabu cike da kewar juna. ma'eeshat tana komawa gida tai sallah la'asar bayan ta idar ta cire kayan, tasa marasa nauyi. sanan ta wuce toilet ta wanke fuskarta tas ta dawo ta ƙwanta ba jimawa bacci yayi awan gaba da ita. sai gab da magriba ma'eeshat ta farka daga bacci. tana tashi ta shiga kicin ta zuba abinci taci. bayan taci ta ƙoshi koma bedroom ɗinta tai ta ɗaura alwala ta mayar da abayarta da sannan ta ɗauko dogan hijab tasa har ƙasa, ana kiran sallah magriba ta gabatar da sallah ta. Bayan ta idar, ƙaramar jakarta ta ɗauka tasa wayarta da cajarta a ciki sannan ta rataya jakarta ta, ta fita. Tana futa farfajiyar gidan shima driver bai dade da idar da sallah ba, dan haka ba ɓata lokaci ya ɗauki ma'eeshat ɗin kamar yarda tace domin mayar da ita gidan su meenal.......... kuyi haƙuri too days bana muku posting. busy ne yayi min yawa kuyi haƙuri da wannan. mu haɗe a next page. _page 35 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Lokacin da ma'eeshat ta koma gidan su meenal anata kiraye-kirayan sallah magriba. itama ɗaura alwalar tai sannan ta shiga ciki ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar su momy cewa su kai zasu tafi, ma'eeshat tace musu a gai da gida Allah ya tsare shanye. Amma momy tace sam bata yarda ba sai ma'eeshat ta rakata har bakin motar. ma'eeshat ba yarda ta iya haka ta miƙe cikin jin kunyar su momy ta raka su, ko da suka isa bakin motar ma sai da momy ta tsaya tai tajan ma'eeshat da hira har sai da garin ya fara duhusannan ta rabu da ita suka tafi. Har ga Allah ma'eeshat taji daɗi haɗuwarta da momyn doctor ba kaɗan ba, kuma har cikin zuciyarta taji tana ƙaunarta saboda kyawun halinta ga fara'a. Haka ma'eeshat ta koma ciki fuska cike da walwala. Itama mami ana kiran sallah isha'i bayan ta gabatar da sallah ta wuce gida. haka-haka de mutane su kai ta watsewa har sai da kowa ya tafi sannan sauran masu ƙwana a gidan suka fara share-share da wanke-wanke. Kimanin 11 an gama komai gida yayi shiru kowa ya ƙwanta. meenal miƙewa tai ta wuce toilet domin tai wanka, bayan tayi wanka tana futowa ba jimawa bacci ya ƙwashe ta. Ita kuma ma'eeshat da taga haka kawai sai ta ɗauki wayarta ta hau online domin chat da doctor. Washegari. Kamar kullum yau ma da sassafe akai wa baba sadakar uku, da sauran addu'o'i. Mutane suna ta zuwa gaisuwa sosai, dan yau ma kamar anfi jiya cika. Ɓan garan ma'eeshat kuwa tuni ta saki jiki da su momy da ladidi suna ta hira, dama ita ma'eeshat bata da wahalar sabo. lokacin guda momy taji ma'eeshat ta shiga ranta ta ƙwanta saboda tana da sakin fuska sosai kamar de ita. To haka de su meenal su kai ta karɓar gaisuwa har magriba ta kawo kai. Su momy suna idar da sallah magriba su kaiwa umma da meenal sallama sannan suka kama hanyar tafiya gida. Daran yau de meenal dole ta saurari waleed saboda kiran da yake mata yayi yawa. Bayan ta ɗaga sun gaisa ya ƙara yi mata ya haƙuri sanar da ita yayi ya dawo, kuma gobe zai zo yayi mata gaisuwa. Meenal da ba zata amince ba, amma kawai sai tace masa “to Allah ya kai mu goben” daga haka bata sake yarda sunyi wata hirar ba ta katse waya. A dede lokacin ma'eeshat ta futo daga wanka a hanzarce saboda yarda taji wayarta tana ringing. Da mamaki meenal sai taga ma'eeshat ta ɗaga wayar ta zauna akan gado daga ita sai ɗaurin ƙirji, kuma meenal ko ba'a gaya mata ba tasan doctor ne yake kiran ta, tunda time ɗin 12 saura. Daga haka meenal ta shiga toilet ta ɗaura alwala tazo tai sallar lafila tayiwa baban ta addu'a sosai dan sai wajan 1 dare saura ta idar. Har lokacin kuwa ma'eeshat tana zaune suna shan waya da doctor, kuma tana nan da ɗaurin ƙirjinta, dan ruwan wanka jikin tama tuni ya bushe. Meenal de bata ce komai ba ta hau kan gado ta shige cikin bargo tana tunanin baba da kuma rashin nata masoyin. nan da nan hawaye suka shiga ƙwaranyowa meenal, haka de har bacci ya ɗauke meenal amma ma'eeshat basu kammala wayar ba ita da doctor. Washe gari. Yau gida yayi shiru da yake kowa ya tafi gida ya rage daga umma sai meenal da ma'eeshat. Lokacin mutuwa ta dawowa umma da meenal sabuwa. haka suka shige ɗaki su kai ta kuka abun su gwanin ban tausayi. Ma'eeshat da ta gaji da rarrashin su itama taya su kukan ta farayi. sunci kuka sun godewa uban giji, daga ƙarshe de dola suka haƙuara su kai jigum abun tausayi. Meenal lokaci guda tayi wani zuru-zuru, ko abinci bata iya ci. yauma umma ce ta takura mata ta ɗan tsakura kaɗan saboda ita meenal gaba ɗaya bama tajin yunwa ko kaɗan, saboda mugun tashin hankali da take ciki. Misalin ƙarfe 4 da ƴan mintina, wayar meenal da take hannun ma'eeshat ta fara ringing, ma'eeshat kallon meenal tai tace meenal "waleed ne yake kira fa". murya a dashe meenal tace " ɗauki kiji me ze ce". Baki cike da sallama ma'eeshat ta ɗauki wayar. Bayan sun gama gaisawa waleed cewa yayi ta sanar da meenal yana ƙofar gida yana jiranta. ma'eeshat bayan ta katse wayar kallon meenal tai tare da cewa "kinji wai yazo yana waje yana jiran ki". "murya a dashe meenal ta sake bawa meenal amsa da "kije ki shigo da shi fallo kawa, daga nan sai yayiwa umma gaisuwar itama". miƙewa ma'eeshat tai tana cewa “tom, bari na zuba miki ruwa alwala naga kamar jikin ki da zazzaɓi". "A'a ba sai kin zuba ba, dama tun jiya nake jin alamun zanyi period, kinga yanzu naji kamar yazo, amma kije kafin ki shigo da shi na ƙimtsa". "To kema garin yaya ƙwanakin period ɗin mu ya haɗe mu da muke bawa juna tazarar one week?". "Kai ma'eeshat kin fiya bin ƙwaƙwafi, ta ina zaki tambaye ni ina na sani laifi ne in ƙwanakin sun haɗe, in kin ƙwantar da hankali ki zasu rabe". "a'a anya kuwa zasu rabe kina 4 days ni kuma 5, kinga ya kama rana ɗaya zamuyi tsarki kenan, to taya ƙwanakin zai rabu?". Miƙewa meenal tai tare da cewa "ma'eeshat yi sauri ki buɗe wardrobe ki ɗaukomin pad da wani pant ɗin, bana so ya ɓatamin jiki kuma in na tsuguna zan ɗauko zai iya ɓatani. Ma'eeshat tana kammala sa hijab ɗin ta nufi ƙwabar meenal tare da tsugunawa, ba ɓata lokaci da ɗauko pad ɗiya tare da pant kamar yarda meenal ta buƙata sannan ta dawo ta miƙawa meenal. Runtse ido meenal tai saboda ciwan marar da take ji. cikin tausayawa ma’eeshat tace “sannu, bari na buɗe na sa miki” daga haka ma'eeshat ba ɓata lokaci ta buɗewa meenal pad ɗin tare da manna mata shi cikin pant ɗin. karɓa meenal tai tare da cewa, "nagode sosai ma'eeshat" daga haka ma'eeshat ta fuce da sauri. ma'eeshat tana futa meenal ta ɗage doguwar rigarta ta cire pant ɗin ta wanda ya ɗan fara jiƙewa da jini, sannan tasa wanda yake ɗauke da pad ɗin da ma'eeshat ta manna mata. Daga haka ta nufi bakin merro ta duba sosai ta bayanta domin taga ko jinin ya ɓata mata riga ta baya. Meenal gani tai jinin bai taɓa ta ba ko ƙadan dan haka sauke ajiyar zuciyar tai sannan ta wuce toilet ɗin ɗakin nata. Tana shiga ta zuba ruwa da omo a botiki sannan ta fara wanke pant ɗin a hanzarce, bayan ta kamalla shanya shi tai, sannan ta fuce, tana futowa ta tarar da ma'eeshat ta shigo. "kin shigo da shi?" meenal taiwa ma'eeshat tambayar, kana binta da ido, gyaɗa kai ma'eeshat tai alamun eh. Zura hijab meenal tai sannan ta kama hanya ita da ma'eeshat suka futa. sai da meenal ta fara shiga ɗakin umma ta sanar da ita sannan suka wuce fallon wajan waleed ɗin. Baki ɗauke da sallama meenal ta kutsa kai fallon ma'eeshat tana biye da ita a baya. ƙamshin turaran waleed ne ya daki hancin meenal, wanda hakan yasa meenal lumshe ido sannan ta mai da kallon ta kan sa. Shima waleed a dede lokacin ya ɗago ido yana amsa sallamar su meenal ɗin. karaf su kai 4 eyes shi da meenal a tare gaban meenal da waleed ya faɗi rass, rass,rass, har sau uku cikin ƙanƙanin lokaci meenal taji shauƙin waleed ya kamata sosai, duk da kuwa bata da ishashiyar lafiyar da zataji shauƙin namiji a halin yanzu. Lumshe ido meenal tai sannan ta zauna ƙasa ba tare da tace komai ba,. ma'eeshat kuwa bama ta kai da zama ba, ko me ta tuna oho ta fuce daga fallon da sauri tana cewa "meenal ina zuwa". Meenal tana ɗagowa suka sake haɗa ido da waleed ɗin, amma wanana karan meenal ji tai ta kasa janye idanunta. haka suka cigaba da kallon-kallon juna, meenal tana so ta janye idon ta amma ta kasa wani irin shauƙi da nutsuwa take samu a tattare da waleed da suka haɗa idonun su. Shima ɓangaran waleed ɗin wata nutsuwa yake samu harda ajiyar zuciya yake saukewa. can de meenal tai ƙarfin halin janye idanuwan ta tare da cewa "ina wuni"?. murmushi waleed yayi sannan shima yace "ina wuni meenal ɗita". "lafiya alhamdulilahi yakake ya hanya fatan ka sauka lafiya". "lafiya alhamdulilahi ya ƙarin haƙurin mu kuma allah ya jiƙan baba da rahma". gyara zama meenal tai tare da cewa "haƙuri da godiya ameen ameen nagode". "Ba godiya tsakanin mu meenal nima ai babana ne Allah yasa can tafi masa nan ɗin" meenal sake amsawa tai da"Ameen ya rabbi". daga haka meenal miƙewa tai tare da cewa “bari na kira maka umma kai mata gaisuwa ko?". jinjina kai waleed yayi tare da cewa “tom shikenan babu damuwa”. waleed yana rufe baki sai ga ma'eeshat ta dawo, cikin mamaki ma'eeshat tace "ah har kun gama gaisawar ne?" "eh umma zanje na kirawo yayi mata gaisuwa". "To ki zaman ki ni bari naje na kirawo ta” daga haka ma'eeshat ta juya ta sake futa. meenal zama tai ba tare da ta sake cewa komai ba, shi kuwa waleed ya zuba mata ido kamar wani tsowan maye. Ba'a wani jima ba sai ga ma'eeshat da umma sun shigo, waleed har ƙasa ya tsuguna ya gai da umma tare da yi mata gaisuwar baba, cikin sakin fuska umma ta amsa tare da yiwa waleed godiya, daga haka ba jimawa umma ta tashi ta koma ciki. Shima waleed ɗin miƙewa yayi duk da kuwa be so tafiya ba, amma yaga meenal bata wani bashi fuska ba kuma, yaga har time ɗin mutuwar bata sake ta ba, ba zasu samu damar ganawa sosai ba. haka waleed yayiwa meenal sallama, jiki a sanyaya ya fuce abin sa. DADY Zuciya cike da damuwa dady ya nufi bedroom ɗin mommy, yana zuwa ya murɗa handel ɗin ƙofar ya shige baki ɗauke da sallama. momy kuwa bama ta san dady ya shigo ba dan tana zaune ta rafka ukan tagumi, ta tafi duniyar tunani. Dady ƙarasawa gefan momy yayi ya zauna tare da ɗan dafata, firgigit momy ta dawo cikin hayyacin ta. ƙaƙalo murmushin dole tai tare da cewa "ah yaushe ka shigo, ka bani tsoro haka ake shigowa ba sallama". Hmmm in banda abinka momyn dtoctor ina zakiji sallama ta kin tafi dogwan nazarin nan?". "hmmm wallahi dady ina cikin damuwa" momy ta ƙarasa maganar tana sauke ajiyar zuciya. Cikin mamaki dady yace "subhanallahi mai yake damun ki?" cikin damuwa momy tace "kai ma Dady kasan ai baze wuce magana akan iftila'in daya faɗa mana ba fadeel ya bige bawan allah nan har ya rasu". "Allah sarki nima abinda yake damuna kenan, shi yasama na taso ƙafa da ƙafa muyi magana". gyara zama momy tai tare da mai da hankali ta kan dady tana cewa "tom shikenan dady ina ji". Tunda fadeel ya aikata wannan abun gaba ɗaya bamu da ƙwanciyar hankali, musamman ma fadeel da muhseen ko ishashan abinci basa ci, bakiga fadeel ba ya zama abun tausayi ba?". gyaɗa kai momy tai tare da cewa “eh wallahi dady na gani". "Kuma ni babban abinda yake ɗagamin hankali yarda ahalin bawan allah nan suka zama marayu musamman ma ɗiyarsa aminatu, kin san daran da zai rasu mun dade muna magana ashe wasiya yake barmin ataƙaice ni ban gane ba". Cikin mamaki momy tace “haba mai yace maka haka? "hmmm munyi magana da shi da dama sosai da sosai, amma ni gaskiya yanzu na yanke shawarar zamu haɗa meenal aure da fadeel, saboda gujewa hatsarin wani saurayin da yake bibiyar ta, daran da zai rasu naji mahaifin ta yana ce mata ta rabu da saurayin nan nata, ko bayan ransa bai yarda ta aure shi ba saboda bashi da kyan hali, kuma bayan haka da bakin sa yace min ya bani amanar ɗiyar sa ko bayan ransa dan Allah kar na bari ta auri yaron, a zaɓa mata miji na gari". Momy wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace "kai gaskiya de bai cancanta a aurawa Amina fadeel ba saboda fadeel yana da rawar kai kuma ko ta aure shi zata cigaba da ganin taban sa a matsayin shi ya kashe mata mahaifi". Jinjina kai dady yayi kafin yace "tabbas haka ne, amam kin san in bamu ɗauki matakin nan ba, wancan saurayin da yake bibiyar yarinyar zai zo ya aure ta". "tom mai zai hana a bata muhseen kawai madadin fadeel tunda shi yafi fadeel nutsuwa" momy ta faɗa tana tsare dady da ido. Dady yayi farin ciki da shawarar momy kuma ya karɓeta hannu biyu-biyu. amma sun yanke shawarar zasu aurawa meenal fadeel in mahaifiyarta ta amince, daga nan meenal tai ta dawo gidan, ta zauna wajan momy ta cigaba da karatu na tsawan 3 years kafin nan muhseen ya sake wayo ya kammala nasa karatun. Amma momy ta shawarci dady da, a bari sai bayan sadakar 7 in sun samu dangana sai ajewa mahaifiyar meenal da zance. Haka de momy da dady su kai ta tattauna yarda lamarin zai kasance....... mu haɗe a next page _page 36 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Barkan mu da dawowa rubutun littafin DOCTOR ASHMAL, wanda muka tafi hutun azumi, muna fatan Allah uban giji ya karɓi ibadun mu. Ameen.......... Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa ɗaya daga cikin members ɗin gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma ɗaya daga cikin admin din group ɗin mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jiƙan Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata maƙwanci yasa ta huta, wallahi munyi babban rashi.😭😭😭😭😭😭 Yanzu zamu cigaba. To kwance tashi ba wuya a wajan allah yau har anyi sadakar bakwan baba. dare tanayi kowa ya riga ya watse gida ya rage daga umma sai meenal da kuma ma'eeshat. Washe gari da safe ma bayan sun karya ma'eeshat taiwa meenal sallama driver yazo ya ɗauke ta domin komawa gida. Gida ya rage daga umma sai meenal ya Allah. Lokacin guda mutuwar baba ta dawowa meenal da umma sabuwa a rai, gaba ɗaya sun kasa sukuni. ko abinci rana basu iya ci ba suna cikin jimami,. umma da meenal basu ƙarasa shiga cikin jimami da tashin hankali ba sai da dare yayi. Lokacin ne mutuwar ta dawo musu sabuwa kamar yau akayi ta. haka suka sha kukan su suka gode Allah sai umma ce tai ƙarfin halin danne kukan ta, sannan ta rarrashin meenal, suka kwanta bacci a bedroom ɗin meenal. duk da wayar meenal a silent take tana gani waleed yana ta faman kiranta, taso ɗauka amma umma tana kusa da ita dan haka kifa wayar tai ta share shi sannan ta rufe ido kamar mai bacci. to umma da meenal sam sun kasa bacci idon su ya soye bacci ya ƙaurace musu. 2:00 am ( na dare) umma tacewa meenal gwara su tashi suyi sallah dare, tunda sun kasa bacci suyiwa baba addu'a. haka meenal ta miƙe suka ɗauro alwala ita da umma sannan suka fara gabatar da sallah su. Baba yasha addu'a wajan umma da meenal, umma da meenal basu suka kwanta ba sai bayan da su kayi sallah asuba, bayan sun idar sun kammala azkhar, komawa su kai suka kwanta ba jimawa bacci ya kwashe su. Umma da meenal basu suka tashi daga bacci ba sai 1:00pm na (rana) lokacin har an fara kiraye-kirayan sallah azahar. Miƙewa su kai domin sallah, ita de meenal sai da ta fara watsa ruwan a jikin ta da yake ita mai jin zafi ce sannan ta ta ɗaura alwala ta fara gabatar da sallah. Basu daɗe da idar da sallah ba suna ƙoƙarin ɗora abinci suka ji an fara ƙwanƙwasa ƙofar gida, kallon umma meenal tai sannan ta mike tana cewa "umma bari naje na buɗe koh?". "Tom jeki ki duba" daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta fuce abinda. Meenal tana buɗe kofa ladidi me aikin momy ta gani tsaye fuska a sake. itama meenal ƙaƙalo murmushi dole tai sannan ta matsa mata cikin farin cikin ganin ta tace "aunty ladidi sannu da zuwa shigo mana". Shigowa ladidi tai sannan tace "yauwa hajiya meenal sannun ki de ya kuke fatan na same ku lafiya?" "alhamdulilahi aunty ladidi ina wuni" "lafiya ƙalau alhamdulilahi kin ganni da tsakar rana ko wallahi momy da dady ne suka aiko mu ni da driver amma bari nai masa magana ya shigo da saƙon, sai in shiga ciki mu gaisa d umma". Ladidi bata jira meenal ta bata amsa ba ta wuce waje, bata wani jima ba ta dawo, suka shige ciki ita da meenal ɗin. kamar yarda meenal ta bar ummanta haka ta dawo ta same ta a zauna kan dadduma tana jan carbi. Amma sallamar ladidi umma tai, nan da nan umma ta faɗaɗa fuskarta da murmushi sannan tace "ah ladidi sannu da zuwa ga waje zo ki zauna ya hanya?" zama ladidi tai kafin ta fara cewa “hanya alhamdulilahi umma ya kuke fatan na same ku lafiya ya ƙarin haƙurin baba kuma?" gyara zama umma tai cikin dauriya tace "alhamdulilah ladidi haƙuri sai ma'aiki" "tom umma Allah ya sake jaddada rahma gare shi". "Amen ya rabbi, meenal kije ki kawo mata ruwa mana ba kiga yarda ake rana ba" da sauri meenal ta miƙe ta fuce ita kuma ladidi cewa tai "nagode sosai umma". Ba jimawa meenal ta kawowa ladidi ruwan pure water guda biyu a plate, sannan ta ajiye a gaban ladidi. "ya wajan su momy fatan kowa lafiya" umma ta tambaya tana gyara zama. "Ah lafiya ƙalau alhamdulilahi, yanzu dady da momy ne suka aiko mu ni da driver mu kawo muku saƙo" ladidi tana kai nan da zan can su umma suka ji sallamar driver, daga nan kuma su kaji alamar sauke abu. Haka su kai tajin shigowar drive da futa da alamun sauke kaya amma ba zasu sheda menene ba. Ladidi bayan ta kammala shan ruwan meenal ta kalla tare da cewa "momy tace tana gai dake da kyau yaushe zaki zo wajan ta ki ƙwana yesmeen ma kullum zan can ki take". Murmushi meenal tai ta sunkuyar da kai ƙasa ba tare da tace komai ba. to driver ya ɗauki kimanin 20 minutes kafin ya gama shigo da kayan nan, sannan yayiwa ladidi waya yana cewa "ta futo su tafi ya kammala". Miƙewa ladidi tai hannu riƙe da wayarta tace to umma zamu tafi ya kammala. miƙewa umma tai tare da cewa "tom bari mu taka miki" daga haka itama meenal miƙewa tai domin rakiya. Suna fita umma da meenal suka daskare da mamaki saka maƙwan ganin uban himulin kayan arzikin da aka shigo musu da shi. kayan abinci ne kala-kala, manyan buhun shinkafa yar gomnati uku, sannan ga buhun shinkafar tuwo shima uku, ga na basmati shima uku. Ga taliya katan biyar macaroni katan biyar kuskus ma haka, gefe guda buhun flower biyu da buhun suga ɗaya, ga kuma doya baje wajan ashirin da dankalin turawa kwando-kwando har kwando shida. sannan ga kwalin magi kala-kala, da jarkokin mai, jad da fari manya ɓanya, ga ruwan jarka da lemukan roba katan-katan egg kirat 10 ga kuma kayan miya shima ƙwando ɗaya, da sauran nau'in kayan abinci. da sauri ladidi ta buɗe jakarta tare da zaro rafa ta sababbin ƴan dubu-dubu, miƙawa umma tai tare da cewa "kuma ga wannan sun ce a ringa cefane, in kuna da wata matsalar ta kuɗi ko wani abun dan Allah ku tuntuɓe ta. Jiki a sanyaye umma ta girgiza kai tare da cewa "a'a ladidi wannan kayan abincin ma da suka kawo da yawa ai zamu shekara muna amfani da shi wallahi ko iya shi ya isa ba sai an ƙaro wani abun ba dan Allah a barshi haka nan”. Girgiza kai ladidi tai tare da ƙarasowa wajan umma tana cewa "a'a umma kinga nima ƴar aike ce, in baki karɓa ba laifi na momy za ta gani dan Allah ki karɓa tunda aiko ni akai wallahi ba komai, dan in baki karɓa ba ma momy da dady ba zasu ji daɗi ba". ladidi ta ƙarasa maganar tana sawa umma kuɗin a hannuwan ta bibiyu. hannu na ruwa umma ta karɓa baki na rawa tace “mungode sosai ladidi dan Allah ki sanar da mutanan arzikin nan mun gode sosai duniya da lahira Allah ya saka da alkhairi, meenal maza ki ɗauko wayarki ta baki number hajiya mu biga muyi mata godiya". Da sauri itama meenal jiki na rawa ta nufi ɗaki domin ɗauko wayarta ba jimawa ta futo hannu riƙe da waya. nan da nan saratu ta hau karantowa meenal number momy, meenal tana sawa. Bayan ta kammala sawa har bakin ƙofa meenal da umma suka raka saratu umma tana faman sake bawa saratu saƙon godiya. Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa ɗaya daga cikin members ɗin gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma ɗaya daga cikin admin din group ɗin mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jiƙan Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata maƙwanci yasa ta kin huta, wallahi munyi babban rashi.😭😭😭😭😭😭 Pls duk sanda kuka karanta book ɗin nan kuyi mata addu’a. Bayan ladidi ta futa rufo gidan meenal tai sannan ta juyo ta kalli umma wanda gaba ɗaya mamaki ya gama malale fusakr ta. Baki na rawa umma tace "meenal kinga abun arziki koh?" itama meenal cikin mamaki ta bawa umma amsa da “eh umma na gani gaskiya mutanan nan suna da kirki sosai Allah ya saka musu da alkhairi". "Ameen ya rabbi meenal, yanzu de bari mu ƙwashe kayan mu kai su ciki saboda rana daga nan sai ki bugawa hajiyar in mata godiya". to meenal tace daga haka umma da meenal suka ƙarasa ciki bayan sun ajiye kuɗin suka hau ƙwashe kayan. FADEEl. Har lokacin hankali fadeel bai ƙwanta ba duk ya rame ya zama abun tausayi. momy da dady harma da sauran mutan gidan duk sun tausaya masa, ganin lokaci guda yarda ya zama abun tausayi. Haka momy da dady suka dawo rarrashin fadeel suna nuna masa kaddara ce tunda bada sani yayi ba amma, ya ringa istigfari. sannan daday ya shawarci momy akan ya kamata fadeel ya fara azumin kaffara na alhakin kisan kai da yayi bisa rashin sani. momy ta goyi bayan dady, sannan kuma ta bashi shawara akan ya tura shi saudiya, sai yayi azimin acan sai yafi masa sauƙi kuma yafi samun nutsuwa yana yi yana ibada acan. Dady yayi na'am da zancan momy sannan kuma yace sabida fadeel yaji daɗin hankali sa ya dawo cikin jikin sa, ya kamata a tura shi, shida ɗan uwan sa muhseen saboda ɗebe kewa. Ai kuwa haka akai cikin one week dady ya kammala komai visa su ta futo shi da muhseen, dama already sun gama shirya tafiyar dan haka tashi su kai zuwa saudiya…….. Ɓan garan Doctor da ma'eeshat kuwa soyayya su sai ƙara zafi take suna sake son junan su, kullum sake shaƙuwa suke sun zama ƴan soyayya sosai, musamman ma doctor kamar ya cinye ma'eeshat baya bari yaga tana cikin ɓacin rai itama ma'eeshat ɗin tana kiyaye nata. Ma'eeshat har ta fara shirya-shiryan komawa school da yake takaddun ci gaba da karatun su ita da meenal ya futo amma sai abba yace ita ma'eeshat ta fara zuwa, ita kuma meenal sai mutuwa ta sake ta in anyi arba'in haka sai ta fara zuwa itama. MEENAL Yau kimanin too weeks da mutuwar baba. meenal tana kwance a ɗaki bayan sallah la'asar tana ta tunani iri-iri na rayuwa, taji wayarta da take gefe ta fara ringing. meenal ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ɗauki wayarta ta. Wanda meenal tai tunani shi ɗin de yake kira wato waleed, tunda baba ya rasu basu wani samu damar yin magana sosai ba gaisuwa ce kawai take haɗa su. gyara kwanciya meenal tai, kafin ta ɗauki wayar a nitse sabida har ga Allah taji daɗin kiranta da yayi dan tana cikin tsananin kewar sa. Bayan meenal ta amsa sallamar da waleed yayi mata cikin mutunta juna suka fara jin lafiyar junan su. Waleed sai ƙoƙarin jan meenal yake da hira meenal tana kaucewa sai de ta bi shi da eh da to. Tun meenal tana iya dannewa har ta fara biyewa waleed suna hirar soyayya dan gaba ɗaya in taga waleed ya bugo mata mantawa take an yi mata wani tsakani da shi ma. Meenal sun ɗauki 30 minutes suna waya ita da waleed yana mugun sata a nishaɗi da farin ciki, dan raban da ta shiga irin farin cikin da yake sata yanzu tun kafin baba ya rasu soyayya suke sha haiƙan abun su, waleed shima daɗi yake ji sosai yarda yaji meenal ta bashi fuska, farin ciki yake kamar an masa bushara da gidan aljannah. Meenal da waleed suna cikin wannan yanayin na mosaya umma ta shigo ɗakin meenal baki ɗauke da sallama. tsayawa cak umma tai tana kollon meenal, raban da taga ɗiyarta cikin farin ciki kamar haka har ta mance. Ko ba'a gayawa umma ba, umma tasan meenal da waleed take waya. umma gyaran murya tai tare da sake sallama, a taƙaice de sai da umma tai sallama sau uku amma ina meenal bata sani ba ta tafi duniyar masoya. Ƙarasawa umma tai kusa da meenal sannan ta fara taɓata, firgigit meenal ta ɗago, tana ganin umma a tsaye tai saurin katse wayar tare da kashe ta baki ɗaya cikin birkicewa da rashin gaskiya meenal tace "umma yaushe kika shigo". Fuskar umma ta canza ba walwala, zama tai kusa da meenal cikin rashin sakin fuska tace "dama ina zaki san na shigo tunda kina waya da masoyin ki". meenal ba tace komai ba ta sunkuyar da kai ta fara wasa da wayarta. Kallan meenal umma tai kafin tace "meenal gaba ɗaya kin canza min, kin koma wata meenal ɗin ta daban ba wanda na sani ba, ada ko yaya muka gaya miki magana kin kiyayeta har abada amma ban da yanzu, meenal karfa ki manta mahaifinki ya rabaki da yaran nan amma kin ƙi? Yanzu mahaifin ki yana ƙarƙashin ƙasa, ko baki masa biyayya yana raye ba, ya kamata ki masa biyayya yanzu tunda ya rasu". lokaci guda hawaye suka fara shararowa meenal, saboda tasan gaskiya umma take gaya mata kuma ga wasiyar da mahaifinta ya bar mata game da waleed tana faɗo mata. Ita har ga Allah ma ta sha'afa sabida son waleed ya rufe mata ido. hannun meenal umma ta riƙe tare da cewa "kiyi haƙuri meenal, kiyiwa mahaifin biyayya, baki san mai ya gani dan gane da waleed ɗin nan ba in sha allah, allah zai kawo miki miji na gari wanda ya fishi komai. Wallahi meenal da ina da halin da zan baki auran waleed da na baki sabida kiyi farin ciki, bazan iya hanaki abinda kike so ba, to amma bani da hali kuma mahaifin ki sai da ya roƙe ni akan ko bayan ran sa kar na bari ki auri waleed, kuma ya gaya min dalilin da yasa ya hanaki auran waleed, tabbas kuma dalilin babba ne ya cancanci a hanaki auran sa. Da sauri meenal ta ɗago ido sharɓe da hawaye ta cewa umma "dan Allah umma ki gayamin dalilin da yasa kuka hanani auran waleed kuka rabani da shi, na amince zan rabu da shi na har abada amma dan Allah ki gaya min dalilin". Meenal tana rufe baki, suka ji ana buga ƙofar gida, alamun anyi baƙi. kallon meenal umma tai tare da cewa "kiyi haƙuri ki dena kukan nan zamu zauna muyi magana, dan Allah kar kisa damuwa a ranki aminatu, bari naje na duba waye yake bugawa, ƙila ma'eeshat ce maza kije ki wanke fuskar ki". Daga haka umma bata sake cewa komai ba ta wuce tai hanyar fita,. kamar yarda umma tacewa meenal, haka meenal ta miƙe ta nufi toilet ta wanke fuskar sosai sannan ta dawo ta zauna tana sauke ajiyar zuciya. Ɓan garan umma kuwa, tana buɗe ƙofa ta tarar da momy tsaye bakin ƙofa. fuska cike da farin cikin umma tace “ah maraba lalele hajiya ashe kece tafe shigo mana”. murmushi momy tai tare da cewa “eh wallahi tare muke da dady zamu iya shigowa”. “Ah sosai ma, kije ki masa iso sai ku shigo hajiya”. fuska cike da fara'a hajiya tace to sannan ta koma domin kiran dady, umma kuwa tana tsaye tana jiran su da yake dama tasa hijab a jikin ta kafin ta futo............. Inalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Allah yayiwa ɗaya daga cikin members ɗin gidan nan rasuwa, tana bibiyar litattafan mu kuma ɗaya daga cikin admin din group ɗin mu na doctor ashmal, dan Allah dan annabi muna barar addu'a a gare ku Allah ya jiƙan Hafsah (oum farhan) da rahma, ya kyautata maƙwanci yasa ta huta, wallahi munyi babban rashi.😭😭😭😭😭😭 Mu haɗe a next page. _page 37 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Bayan su dady sun ƙaraso fuska sake umma ta musu jagora suka shiga cikin sitroom. Cikin giramawa momy da dady suka fara gaisawa da umma. Fuska sake dady yace "wai ina ɗiyata ne?" momy itama cafe zancen tai da cewa "nima tun dazu nake son tambaya amma ka rigani. "ah bari na kira muku ita ku gaisa" umma ta ƙarasa maganar tana miƙewa. Daga haka umma ta fuce daga sitroom ɗin ta koma bedroom ɗin meenal. umma zauna taga meenal gefan gado tayi jigum abinta, kamar mai tunani. Ƙarasawa umma tai gab da ita ba tare da ta zauna ba ta fara mata magana "meenal". Ɗagowa meenal tai tare da cewa "na am" “ki taso muje momy da mijinta ne suka zo, suna cigiyarki kije ki gaida su”. Haka nan meenal taji gabanta ya faɗi rass, amma sai tai ƙarfin halin cewa "tom" sannan ta miƙe abinta. Hijab ɗin ta na sallah meenal ta zumbula har ƙasa sannan ta nufi bayan umma, tana tafe salo-salo kamar wanda bata son tafiyar. Baki ɗauke da sallama meenal ta shiga cikin sitroom ɗin. Har ƙasa ta tsuguna ta gai da momy da dady. Fuska a sake momy da dady suka amsa, musamman momy ma sai washe mata baki take yi tana cewa tazo ta zauna kusa da ita. Meenal kuwa bata ce komai ba murmushi kawai ta saki abinta tare da sunkuya da kai. " meenal kenan sarkin kunya, kin mai damu surukan ki na ƙarfi da yaji, ji wani yarda kike sunkuyar da kai". Momy ta faɗa tana sakin dariya, itama meenal siririyar dariya ta saki. "Tom yaushe zaki zo gidana ki sake ƙwana yesmeen sai cigiyarki take, da, da itama zamu zo amma tana school". Murya ƙasa-ƙasa meenal tace "momy zan zo ne" "ah ni ban yarda da zuwan ki ba, kawai kizo mu koma tare yau". meenal bata ce komai ba sai sakin murmushi kawai, murmushin da yake sa dimple ɗin kumatun ta rige-rigen motsawa. Bayan momy ta gama zaulayar meenal da wasa, ɗorawa tai da cewa "tom shikenan de meenal tunda kin ƙi magana, maza kije ki haɗa kayan naki, ki bamu waje muyi magana da umma, in na gama zan miki magana kizo mu tafi kawai". Momy ta faɗa cikin sigar zaulaya, murmushi meenal tai tare da miƙewa, a dede lokacin umma ta shigo hannu riƙe da plate mai ɗauke da ruwan jarka da lemuka, sannan ta ƙaraso ta ajiye a gaban su momy. "Sannu da ƙoƙari mun gode" dady ne ya faɗi hakan yana gyara zama. momy kuwa ruwan ta ɗauko ta buɗe ta fara tsiyayawa a cup duk da bata jin ƙishi amma haka nan take son shan ruwan saboda bata so umma ta wahala, kuma basu sha ba". Momy bayan ta ɗan sha ruwan kaɗan ajiye cup tai sannan tace, “yauwa maman amina in ba damuwa muna son magana dake". umma da take zauna jinjina kai tai tare da mai da hankali tace "tom ina sauraran ku hajiya". Kallon dady momy tai tare da cewa "za kai mata bayanin ko ni zan fara?". "a'a ba damuwa ki farayi mata bayanin kawai". momy baya ni ta farayi kamar haka "Dama maman meenal wata magana ce take tafe damu game da aminatu". Gyaɗa kai umma tai alamaun tana sauraro. “Kafin baban amina ya rasu, sunyi magana da dady sosai, sannan dady ya fahimci mahaifin meenal baya son saurayin da suke tare, sabida dady ya shedamin cewa a gaban sa yake cewa amina ko bayan ran sa kar ta auri saurayin da suke tare, kuma bayan haka ma baban amina ya sake jaddadawa dady hakan” momy ta ƙarasa maganar tana tsare umma da ido. Jinjina kai umma tai kafin tace "ƙwarai hakane hajiya, nima ya barmin wassiya da ko bayan ran sa baya son meenal ta auri waleed kuma gashi ita yarinyar tana son yaran sosai, gaba ɗaya ta kasa rabuwa da shi, duk ta shiga damuwa sosai". "Subhanallahi wai menene dalilin baba na hana amina auran yaran nan, inaga in dalilin bai wucewa shari'ar muslinci ba, za'a duba kawai sai a gyara ko menene ayi auran in kuma, ya wuce dole ta hakura, tunda kince ta shiga damuwa sosai". Dady ne ya faɗi hakan cikin jimami. umma gyara zama tai da cewa "to ana gab da turo kuɗin auran su ne shine baban meenal yaje bincike nan ne ya gano wai bashi da tarbiyya shaye-shaye yake da kuma bin mata, a can abujan in da yake aiki, shine dalilin da yasa baban meenal ya dakatar da auran, saboda yace meenal ita kaɗai allah ya bashi baze so yaga ya aura mata mutum mara tarbiya kamar waleed ba, saboda yana so ya bata miji na gari wanda zata samu kwanciyar hankali ta haifi ƴaƴaye masu tarbiyya. Jinjina kai dady yayi kafin yace "eh gaskiya ne malam yayi gaskiya dole haka zata haƙura da shi gaskiya wannan ba mutumun aure bane". "Hakane amma ni da dady mun yanke shawarar zamu haɗa amina aure da ɗan wajan mu muhseen in ba damuwa". "Eh mun jima da yanke shawarar amma sai muka ce bari a share zaman makoki, sai muzo mu same ki da zance" dady ya faɗa yana gyara zama. momy ɗorawa tai da "amina ta shiga rai na sosai sabida yarinya ce mai hankali, bana so tai maraici sosai, kuma ina tunanin in anyi mata auran hankalin ta zai kwanta, kuma zata dena tunanin wancan saurayin nata". A zahirin gaske umma tayi mamaki da jin maganar su momy da dady sosai, dan batai tunanin ko da wasa za suyiwa meenal tayin auran ɗan su ba. momy da taga umma tayi shiru cigaba da magana tai kamar haka "Amma fa ba zamu matsa miki ko mu matsawa amina a kan haka ba, kawai shawara ce sai kin amince hakan zai faru, in baki amince ba shikenan, zamu cigaba da zumunci mu kawai” momy ta ƙarasa maganar tana sakin murmushi. Itama umma murmushi ta ƙwaƙulo sannan tace "a'a hajiya rashin maganar tawa, bashi yake nuna rashin amincewa ta ba, nayi mamaki ne sosai ta yarda kuka yiwa meenal tayin auran yaran ku, ba tare da shakkar wani abun ba". "Cikin mamaki momy tace "shakka kuma haba umman amina ki dena faɗar haka, ai na yarda da tarbiyar gidan nan 100% kuma amina mace ce da ko wana iyaye za su so ɗan su ya aure ta". "Hakane hajiya naji daɗi sosai kuma nayi farin ciki da jin wannan, saboda nima nasan duk yaran da ya futo daga gidan ku, ya futo ne daga babban gidan mutunci, tarbiya, da kuma sanin yakamata, ni de ta bangarena, na amince sai dai kuma ita amina, amma in sha Allah itama zata amince". "Alhamdulilahi kar ki damu ai ni bana jin ƴata amina zata amince in sha allah, komai zai zo dede". momy taso ta sanar da umma in anyi aure meenal a wajanta zata zauna ta cigaba da karatu kafin suma su muhseen ɗin su kammala nasu, amma sai taga hakan bai dace ba, umma zata fahimci lamarin a bai-bai gwara in lokaci yayi a sanar da umma". Daga haka momy da dady miƙewa su kai domin shirin tafiya, dady ne ya fara fita ita kuma momy tace sai tayi sallama da meenal dan haka har bedroom ɗin meenal momy taje. Ko da momy taje kwance ta samu meenal tana bacci dan haka bama ta tashe ta ba, kuma ta hana umma tashin ta. Daga haka umma har ƙofar gida ta raka momy, momy kuma ta sake jajjadawa umma duk abinda suke buƙata dan Allah ta tuntuɓe ta a waya ta sanar da ita. Su momy suna tafiya umma ta kullo ƙofa sannan ta nufi kicin ta fara ƙoƙarin ɗora musu abinci. umma aiki girki take amma gaba ɗaya hankali ta baya kan girkin yana kan maganar da su momy suka zo mata da shi...... Sai da aka fara kiran sallah la'asar meenal ta farka daga baccin da ta tafi. tana miƙewa ta ɗaura alwala sannan ta fara gabatar da sallah. Bayan ta idar kicin ta shiga ta zubo abinci, sannan ta zauna ta fara cin abinci, ci take amma ita kaɗai tasan damuwa da take ciki na rabata da waleed da akayi, har ga allah tana yiwa waleed son da ita kanta bata son adadinsa ba. Umma kallon meenal tai, ta fahimci cin abincin take kawai amma hankalinta yana can wata duniyar. "meenal in kin gama ina so muyi magana dake". Sai da gaban meenal ya faɗi rass, da taji umma tace haka, amma sai ta dake tace"tom umma". Nan da nan meenal ta mai da hankali ta cigaba da cin abincin dan a iya tunanin ta maganar waleed umma za tai mata, maganar da suka farayi ɗazu ita zasu ƙarasa. Bayan meenal ta kammala cin abinci mikewa tai ta kai plate ɗin kicin sannan ta dawo ko ruwa bata sha ba ta zauna kusa da umma tana cewa "umma na gama ina jin ki". "Eh na gani amma ya kamata ki sha ruwa kafin mu fara maganar, kyaci abinci baki sha ruwa ba kuma". Daga haka meenal bata sake cewa komai ba ta nufi bakin randa ta ɗebo ruwa tasha sai da ta ƙoshi sannan ta ajiye cup ɗin ta dawo wajan umma. Bayan ta zauna, itama umma gyara zama tai kafin ta fara cewa "meenal nasan za kiji maganar da baki zaɓa zata ba bare tunani, dazu momy da alhaji akan maganar ki su kazo gidan nan". Da sauri meenal ta ɗago cikin mamaki tace "maganata kuma umma?" "eh ki godewa Allah da yasa kike da farin jinin da kika shiga ran su lokaci guda har suke bibiyar lamarin ki". "Umma ban gane abinda kike nufi ba wallahi". "Eh zaki gane ai bayani zan miki yarda zaki gane, meenal momy da alhaji suna so su aura miki ɗan su, shi yasa suka zo suka sanar dani, sannan suka ce a sanar da ke kema in mun amince amma". Meenal jin maganar tai ta dakar mata kwakwalwa on expect, cikin mamaki tace "umma ɗan su kuma wana ɗan nasu, haba umma sai kace an ce musu bani da masoya ne, da zasu fara ƙoƙarin haɗa ni da ɗan wajan su". Umma tayi mamaki sosai da jin maganar meenal haka gatsau sabida meenal bata cika, fadar magana a tsaitsaye ba, musamman ma in maganar daga bakin manya ta fito. Girgiza kai umma tai kafin tace "a'a meenal bace musu akai baki da masu san ki ba, kawai gani su kai ya kamata tunda mahaifin ki yacewa alhaji ko bayan ran sa kar ki auri waleed shine su kai miki miji". "hmmmmm umma ni zan rabu da waleed ko nace nama rabu da shi amma, bana son ɗan su bazan iya auran saba ko wanene gaskiya, duk da kuwa suna da kirki da mutunci ga sanin darajar ɗan adam, amma ni gaskiya bama naso ba sai an kai maganar nan da nisa ba". Cikin mamaki umma tace "meenal ni kik cewa haka, meenal hankali ki ɗaya kuwa, meenal nima farko ban amince da zancan ba, amma daga ƙarshe sai naga in mu kai musu hakan ba zasu ji daɗi ba, kuma ya kamata tun wuri a aurar dake meenal, sabida ke ba irin matan da suke karatu me tsayi bane, ba tare da aure ba, ni na fahimci ke mace ce mai san aure tun ba yanzu ba, meenal baki da wani zaɓin daya wuce ki amince ki auri yaran su momy". Murya na rawa meenal tace "haba umma ni wallahi gaba ɗaya aure bai taɓa birge ni nan kusa ba, umma dan Allah kar kimin dole wallahi bana so” meenal ta faɗa hawaye na ƙwararo mata. "Meenal ai mace bada baki take faɗa taka son aure ba, ɗabi'un ta ne suke nuna hakan, kuma gashi ke macace mai gaba-gaban jiki komai naki masha allah bai ci ace kin cigaba da karatu babu aure ba, ko wana kalar maza hari za su ta kawo miki, na gari da na banza". Kuka sosai meenal ta fashe da shi sannan ta tashi ta shige ɗaki. sai da jikin umma yayi sanyi sosai ganin halin da meenal ta shiga sabida ita tunda ta haifi meenal bata taɓa tashi ta bata waje ba in suna magana sai yau. Umma tana kai haka da tunanin taji ƙarar bugu, ana buga gidan. Jiki a sanyaye umma ta miƙe ta ɗauki hijab ɗin ta da yake gefe ta saka, sannan ta tafi buɗe gidan zuciyar ta cike da tunani kala-kala. Umma tana buɗewa ma'eeshat ta gani tsaye bakin ƙofa, ƙaƙalo murmushi dole umma tai kafin tace "ah ma'eeshat kece tafe kenan sannu da zuwa". "eh wallahi umma ina wuni, kinga ni da driver nazo dady ne ya aiko shi, shine nace muzo tare saboda ina son zuwa". "lafiya ƙalau ma'eeshat Allah sarki to kice ya shigo, umma tana rufe bakin ta taga driver ya fara sauke kayan abinci a ƙofar gida. Ita kuma ma'eeshat ce masa tai in ya gama futo da su daga boot ya shigo da su ciki, daga haka ta shige ciki wajan meenal. Sosai hankali ma'eeshat ya tashi ganin yarda meenal take ta sharara hawaye, hankali tashe ma'eeshat ta ƙarasa kusa da ita tare da riƙe hannun ta tace "rabin rai kukan me kike yi ne haka, wallahi jiki na ya bani kina cikin damuwa tun daga yanayin yarda kike min reply a chat da kuma in na bugo nasan kina damuwa, haba rabin rai ki gayamin me yake damun ki ya isa kibar kukan nan haka please".daga haka ma'eeshat ta fara sharewa meenal hawaye da hannun ta. bayan ta gama tsare ta tai da ido tare da cewa “maza ki gayamin mai yake damun ki kar nima kisa nayi kukan”. Shaƙar hanci meenal tai sannan ta fara magana murya a dashe "ma'eeshat kema kan ki kin san ina matuƙar son waleed sosai koh?" gyaɗa kai ma'eeshat tai alamun eh. “An rabani da waleed ina cikin damuwa madadin damuwar ta ragu kullum ƙaruwa take, sannan yanzu ana so a bani wani wanda bana so". Cikin mamaki ma'eeshat tace "kai wa za a baki kuma meenal kimin bayani yarda zan gane mana". Nan da nan meenal ta zayyane labarin da umma ta bata na zuwan su momy da abinda suka ce, ta bawa ma'eeshat labarin komai........ Mu haɗe a next page. _page 38 ~DOCTOR ASHMAL ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ajiyar zuciya ma'eeshat ta sauke sanan ta gyara zama tare da dafa meenal tana cewa "meenal abinda nakeso na fada miki ko wana bawa akwai kaddarar sa a rayuwa, kuma dole ya dage domin yaga ya cinye ta". Cigaba da magana ma'eeshat tai da cewa "kuma meenal naga hakan ai ba laifi bane, sannin kan ki ne baba baya son auran ki da waleed har ya kwanta ƙasa, yanzu kinga ai ba hali ki aure shi, tunda ke yanzu kin san ba maganar auran ki da waleed to me zai hana ki bawa ƙanin doctor dama". Ido jajiir meenal ta ɗago ta kalli ma'eeshat cikin mamaki tace "Haba ma'eeshat ke da kan ki kike cewa haka ban taɓa tunanin zaki goyawa abinda bana so baya ba, wallahi ma'eeshat bana son wannan haɗin na tsani a rayuwa a haɗa mutum da wanda ba shi ya gan shi yace yana sona ba, Ke ni na haƙura da auran waleed ɗin amma wallahi bana son na auri brother ɗin doctor" meenal ta ƙarasa maganar a raunane tana fashewa da kuwa". Cikin nauyin zuciya ma'eeshat ta ɗago tare da jan gauran nunfashi tana riƙe hannun ma'eeshat ɗin. Murya a sanyaye ma'eeshat tace "tom meenal naji amma dan Allah wana dalili ne yasa ba zaki auri ƙanin doctor ɗin ba? baki yarda da tarbiyar gidan su ba ko kuma nasabar sa ce bata yi miki ba, ko kuwa shi kan sa yaron ne bai miki ba?". Share hawaye meenal tai da hannayan ta baki na rawa tace "ma'eeshat ni ban ma taɓa ganin yaron ba and kuma sanin kan ki ne su momy su suke da nasaba ko da ban san wanda take min tayi ba, bani da shakka yana da tarbiya amma ma'eeshat, ni bana son na auri mijin da bashi ya ganni yace yana so ba, bana so a haɗa ni da miji wlh gwara mutum ya ganka yace yana sona sabida gudun gori ma". "Gaskiya kika faɗa meenal amma, in sha allah nasan jinin momy baze taɓa miki gori ba, wannan ba halin su doctor bane suna da sauƙin kai sosai duk da kuwa wani yaron zaka haife shi baka haifi halin sa ba, amma ina kyautatawa yaran momy zato, kuma ai babban abin tsoran shine ke kiga namiji kice kana so, Duk da kuwa ba haramun bane, nana khadija ma ita ta fara ganin annabi muhammad s.a.w tace tana so, amma yanzu zamanin ya lalace bama zaki taɓa haɗa samarin yanzu da koyi da halin manzan Allah ba saboda shi na daman ne, kuma samarin yanzu yawan cin su basu da kirki sai sun goranta maka. Tom shi yasa matan yanzu suke gudun suga namiji suce suna so, wannan zub da mutuncin da ake cewa shine! namiji yazo yana goranta miki yana ci miki mutunci shine abinda ake gudar miki, kuma ya kasance kece sanadin cin mutuncin. Amma tunda bake kika ce kina son shi ba shikenan, maman shi ce ta kawo miki tayin sa, kuma mutuncin su momy zaki duba da karamcin su, bawai dan wani abun ba please meenal ki amince". Ido shaɓe-shaɓe da kuka meenal tace “wallahi ma'eeshat ba zaki gane abinda nake ji a zuciya ta ba bana ji zan iya amincewa". Cikin muryar lallashi ma'eeshat tace "sorry meenal kar kice haka dan Allah ki amince da wannan zancan zanfi kowa jin daɗin zancan nan kinga zumuncin mu ma zai ƙaru ace yau ni da ke mun auri miji yaya da ƙani". To haka de ma'eeshat tai ta rarrashin meenal da kalamai masu kwantar da hankali har zuciyar meenal tai sanyi kuma ta fara jin zata iya amincewa ko dan ta farantawa mahaifiyarta, tunda taga itama tana son abin, kuma ta farantawa ƙawarta ma'eeshat da momy. Cikin muryar rarashi ma'eeshat ta sake ruƙo hannun meenal duka biyun tare da cewa "to yanzu ya kenan kin amince?" Cikin dashashiyar murya meenal tace “yanzu bama wannan ba, gaba ɗaga hankali na ya tashi saboda ɗazu da umma ta sanar da ni zancen momyn, ba kiga yarda nai mata ba wallahi". Meenal ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye. "subhanallahi mai kikai mata?" "nayi mata abinda ban taɓa yi ba lokacin da ta sanar da ni, kuma naga kamar tana son abin, tana faɗa ina faɗa sannan ƙarshe na tashi na barta a wajan ba tare da mun gama maganar ba" meenal ta ƙarasa maganar kuka yana ƙwace mata. rungumota meenal ma'eeshat tai jikin ta tare da cewa "is okay cool down meenal, ki dena kukan nan haka komai ya wuce, dama ɗan adam watarana yana yin ba dede ba yanzu za kije ki tsuguna har ƙasa ki bawa umma haƙuri sannan ki sanar da ita kin amince hakan zai sa taji sanyi sosai kuma ta manta da abinda ki kai mata". Kallon ma'eeshat meenal tai almun tana nazarin shawarar data bata. "Meenal, don't think too long and just agree". "Tom ma'eeshat bari naje" meenal ta tashi jiki a sanyaye, duk da kuwa ta amince ne amma ba har zuciyarta ba. Zauna meenal taga umma ta rafka tagumi a gefan gado. jiki a sanyaye na rawa meenal ta ƙarasa wajan umman ta tare da zubewa kan guiwowin ta biyu baki na rawa tace "umma dan Allah kiyi haƙuri akan abinda nai miki dazun, nasan nayi kuskure sharrin sheɗan ne kuma na amince da maganar momy zan auri yaran nata". Meenal ta ƙarasa maganar baki na rawa tana fashewa da matsanancin kuka mai cin rai. Bibiga bayan meenal umma tai farayi alamun rarrashi, ko ba'a gayawa umma ba, umma tasan wannan aikin ma'eeshat ce, saboda meenal tana jin shawarar ma'eeshat, Ma'eeshat tana juyawa meenal ra'a yi sosai a lokaci guda,. Kuma umma taji daɗin hakan sosai da ma'eeshat ta shawo mata kan meenal har ta amince. Meenal taji shiru sai uwar ajiyar zuciya take saukewa. Umma magana ta farayi cikin sassauta murya take cewa "ba komai meenal komai ya wuce Allah uban giji yayi miki albarka kinji meenal, naji daɗi da kika amince nagode, in sha allah sai kin samu farin cikin da baki taɓa tunani ba a gidan auran ki"....... To ma'eeshat sai da ta tabbatar meenal ta samu nutsuwa sosai, dan har sai da tasa ta saki jiki su kai hira sosai sannan hankalin ma'eeshat ya kwanta. ko da doctor ya bugowa ma'eeshat, ma'eeshat taso tambayar shi zancan meenal da muhseen amma sai tai tunani doctor bai cika son mutum ya shiga maganar da bata shafe shi ba, dan haka shiru tai da bakin ta. Tom meenal sai bayan sallah magriba ta fara ƙoƙarin tafiya gida. da driver yazo ɗaukar ma'eeshat meenal har bakin ƙofa ta rakata, ma'eeshat ta dage meenal ta bita gidan su amma meenal taƙi amincewa tom dole haka ma'eeshat ta haƙura ta tafi. After one week. Tom komai na makarantar ma'eeshat ya gama kammala, yau ya rage saura one week ta fara zuwa makarantar. Ma'eeshat har ga Allah bata son zuwa school ɗin nan kawai dan abban ya matsa mata ne, doctor kuma sai rarrashin abarsa yake yana sake ƙarfafa mata guiwa shi yasa za taje. Ma'eeshat tana kammala sallah la'asar kishingiɗa tai a kan dadduma dumin duba wasu littattafai, dan yanzu ma'eeshat ta fara karatu sosai saboda school ɗin da zata koma ba wasa za tai ba karatu za tai, bata so taji kunya wajan mijinta doctor. Ringing wayarta da take kan bed ta fara, ma'eeshat gyara zama tai dan bata da niyar ɗaukar wayar sabida tasan ba mai mahimmanci bane doctor baya kiranta war haka in de ba weekend ba. Amma daga ƙarshe sai tai tunani meenal ce dan haka da sauri ta ƙarasa, tana zuwa ga mamakin ta taga doctor ne, wayar tana gab da tsinkewa ma'eeshat tai sauri tasa hannu ta ɗauka, tare da sata a handsfree sannan ta zauna akan bed ɗin tana cewa "hello". "Assalama'alaikum" doctor ya faɗa daga can ɓangaran" "wa'alaikassalam dee yau an tuna dani kenan naga kiranka war haka". murmushi mai sauti doctor ya sauke tare da cewa "eeshat ta kin cika rigima ni ai kullum cikin tunanin ki nake, wai dan bana kiran ki a lokacin bashi ne yake nuna bana tunawa da ke ba, aiki nake". "Tom dee naji daɗi kiran nan da kai min, ya aiki?". lafiya alhamdulilahi, yau na futo da wuri ne sabida ina buƙatar hutu zani gida, shine nace bari na kiraki naji muryarki ko na samu ƙwarin jikin komawa gida". "Hmmm dee nah ina son ka sosai na rantse maka". "hmmm eeshata nima ina son ki, ke ta musamman ce a wajena, kina bani farin ciki na musamman kuma ina ji dake eeshata fatan de kina karatu sosai kamar yarda nake tuna miki kullum". Cikin shagwaɓa ma'eeshat tace "eh ina yi mana sosai, yanzu ma gashi ina tayi, gaba ɗaya naji brain ɗin tawa ma ta toshe yanzu bana ji zan ci gaba da iya karatun nan fa yanzu gaskiya sai zuwa gobe". Cikin rarrashi doctor ya cewa ma'eeshat "sorry dear na, ki huta kar ki takura kan ki, ko nazo ne na ganki ko zaki samu nutsuwa?". Cikin farin ciki ma'eeshat tace "eh please kazo dan Allah ina son ganin ka maybe in na gan ka ma naji na dawo normal". "hmmm nima kamar yarda zan dawo normal na ganki ba, amma bari naje gida na shirya zuwa anjima kafin magrib zan zo, kin san bana son zuwan dare, gwara nazo da haske na ganki sosai" cikin shagawaɓa ma'eeshat tace “to ko kazo ai ba kallon na kake ba sosai ɗin". Wata siririyar dariya doctor ya saki sannan yace "ina kallon ki sosai mana". "uhmmm to ai ni bana gani" ma'eeshat ta faɗa tana turo baki kamar tana kallon sa. "zaki gani ne tom" "yaushe zan gani?" ma'eeshat ta tambayi doctor tana sakin murmushi. "Yau in nazo har sai kin tsargu zan ta kallan ki ba kiftawa. "Tom shikenan allah ya kawo ka lafiya my Love" "ameen tawan" daga haka doctor da ma'eeshat su kai sallama. Suna sallama doctor ya tayar da motar ya fita daga babban hospital ɗin. Doctor yana tafe yana tunanin rigima irin ta ma'eeshat wato ita so take ya ringa kallon ta, shima yana son hakan amma in de doctor ya cika kallan mace sosai, yana da matsala ciwan sa tashi zai yi. Bayan doctor yaje gida ko hutawa bai yi ba yayi wanka, sannan ya ci abinci, bayan yaci abinci shiryawa yayi cikin milk ɗin shadda, kana kallan sa dole ka ƙara yayi matuƙar kyau sosai. Bayan doctor ya gama shiryawa ya fesa turare yasa hula da agogo, wayarsa ya ɗauka ya turawa ma'eeshat message kamar haka "eeshata na gama shiryawa yanzu zan futo daga gida na taho". daga haka ya zura wayoyin sa a aljihu sannan ya ɗauki key ɗin motar sa yayi gaba abinsa. Ma'eeshat tana ganin message ɗin doctor jiki na rawa ta shiga toile tai wanda sannan ta fara shiryawa a hanzarce. Tayi matuƙar kyau sosai, abaya tasa baƙa sannan ta yafa mayafinta, ta kame akan bed tana jiran doctor har takalmi tasa.... Ma'eeshat tayi kimanin 1 minutes tana kallon doctor wanda bai ma san da zuwanta ba hankali sa ya karkata kan laptop ɗin da take gaban sa a kan ciyarsa. da yake yau mota mai farin glass doctor ya ɗauko ba mai baƙi ba. Kamar ance doctor ya ɗago, yana ɗagowa ya hangi kamar an tsaya bakin motar daga gefe. a hankali doctor ya juya gefe bayan ya ɗago, ai kuwa ma'eeshat ya gani tsaye tana sakar mata kyakyawan murmushi. Shima nasa murmushin ya sake sannan ya buɗe mata ƙofar motar a hanzarce. Ma'eeshat bayan ta shigo gyara zama tai sosai sannan ta rufo murfin motar tare da cewa "wai kai saboda me baka son shigowa cikin gida ne?". Ma'eeshat jin shirun doctor ba amsa hakan ne yasa ta ɗago domin ganin me yake yi bai bata amsar tambayar da tai masa. Sai da gaban ma'eeshat ya ɗan fadi rass saka makwan ganin doctor ya zuba mata ido yana kallo ko ƙiftawa babu, abinda bai taɓa yi mata kenan ba. Kawar da kai ma'eeshat tai sannan tace "wannan kallon bai yi yawa ba kuwa". Doctor ba tare da ya dena kallon ma'eeshat ba ya bata amsa da "ke kika buƙata kuma, hakan yana da fa'ida ashe gaskiya ke me kyauce sosai". ɗagowa ma'eeshat tai tana cewa "ai ban kai ka kyau ba ko" "dama maza suna da kyau ne" doctor ya tambaya yana sake tsare ma'eeshat da ido. Lokaci kuda ma'eeshat ta dabarbarce saboda kallon da doctor yake mata ya ishe ta haka gani tai yana mata kwarjini sosai, baki na rawa tace "pls doctor ka dena min kallon nan haka ya isa na gode". "hmmm me akai ai kallon ki yanzu na fara eeshat" cikin ruɗu ma'eeshat tace “to ni gaskiya ka buɗe min ƙofa na koma gida". "hmmm da kin san ba zaki iya jure kallon ba kike cewa bana yi ai yau zan sha kallo har sai idona ya bushe tukkuna". Lokaci guda ma'eeshat ta haɗe rai sannan ta fara cije leɓe. Doctor kawar da ido gefe yayi tare da cewa “I'm sorry na dena". dama can fuskarta kawai yake kallo ba wani abun ba. murmushin ma'eeshat tai tare da cewa "yauwa ko kai fa". "hmmmm ai yau nasha yarinta eeshat kin cika rigima fa". to doctor da ma'eeshat sun sha soyayya sosai da sosai, kamar kar su rabu,. sai da aka fara kiran sallah sannan su kai sallama cike da ƙaunar juna doctor ya wuce masallaci. Washe gari. MEENAL Yau ta kasance ɗaya daga cikin ranar baƙin ciki a rayuwar meenal wanda ba zata taɓa mantawa da ita ba a cikin jerin baƙaƙyan ranakun da suka zo mata, na tashin hankali. daga mutuwar baba sai rabuwar ta da waleed sai kuma wannan rana. Saka maƙwan yau aka kawo kuɗin zance meenal akai mata engagement ita da muhseen ɗan gidan momy. kuma an sa mata 3 moths ne ba wani dogon lokacin ba. Abban ma'eeshat ne ya ƙarbi kuɗin auran meenal sabida yace shi yake da alhakin aurar da ita koda baba yana da rai.............. mu haɗe a next page _page 39 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Kwana biyu gaba ɗaya meenal ta shiga matsanancin tashin hankali, gaba ɗaya ta faɗa kana ganinta za kasan tana cikin matsananciyar damuwa. ga mutuwar baba bata sake ta ba, ga rabuwa da waleed sannan gashi an mata engagement da dan gidan mommy wanda bata san shi ba bata taɓa ganinsa ba ma. Abun haushin ma da ɗaga hankalin bama shi yace yana son ta ba, auran haɗi za a musu, kuma har ga allah ita meenal bata so saboda a halin yanzu ma wata muguwar kaunar waleed ce take damun meenal daran duniya bata iya bacci. Tun meenal tana iya hakuri ta dena chat da waleed tai blocking ɗin shi harta hakuri taci gaba da kula shi a ɓoye ba tare da sanin umma ba. Yanzu meenal ta lura da cewa in ta rabu da waleed matsala za ta shiga ga ciwon zuciya yana ƙoƙarin ya kamata dan haka tuni ta sake sakarwa waleed jiki a karo na biyu suna ta shan soyayya su. Amma bata nuna masa anyi engagement ɗin ta ba saboda meenal tasan waleed zai shiga mawuyacin hali, kawai tana nuna masa, su cigaba da addu'a kuma zata shawo kan umman ta akan auran su, in sha allah umma zata amince, suyi auren su. Waleed yaji dain hakan sosai saboda, lokacin da meenal ta juya masa baya har rashi lafiya yayi duk yabi ya haukace ya furgice, kamar mara hankali. Yanzu waleed ya gama gane in ba meenal a tare da shi tsaff zai iya mutuwa sabuda mugun son da yake mata sosai. Allah sarki waleed bawan allah ga maraici ga soyayya, gashi ba shi da wanda zai kai wa kukan sa ya share mai sai de allah, ba uwa ba uba ba ɗan uwu ko ƴar uwa wanda suke uwa ɗaya uba ɗaya. hakan ne yasa meenal take mugun tausaya masa. Ɓangaran umma kuwa itama abun yana bata mamaki ace wai za'a haɗa auran meenal da ɗan gidan mommy amma baya zuwa ya ganta, duk da de mommy ta kawo uzirin baya ƙasar, amma ya kamata ai ace yana bugo mata. Umma ta fara jin tsoron kar aje yaron mommy baya son haɗin nan kuma bayan aure azo a samu matsala, kuma gashi itama meenal ɗin bata son abun. haka umma take ta irin wannan tunanin, amma daga ƙarshe dai sai ta kwantar da hankali ta kuma ta cigaba da addu'a akan lamarin. kullum sai umma ta tashi tai addu'a da daddare akan in wannan auran meenal ɗin da za ai ba alkhairi bane allah kar ka tabbatar in kuma alkhairi ne allah ya tabbatar,. itama ɓangaran meenal ɗin haka, in umma ta tashe ta sallah dare addu'a take akan allah ya mallaka mata waleed ko wana hali ne da shi zata iya zama, duk da tasan da wuya waleed ɗin ta yana da wani ɓoyayyan hali mara kyau,. Ma'eeshat. Ɓangaran ma'eeshat kuwa ta fara zuwa school masha Allah, duk da de ba wani mai da hankali take a school ɗin ba saboda hankalinta yana kan doctor soyayya doctor kawai tasa a gaba, duk da kuwa shi doctor ɗin yana iya bakin ƙoƙarinsa wajan ganin ma'eeshat tana mai da hankali a karatun. saboda yanzu doctor ya rage bugowa ma'eeshat wayar dare, sai ya tabbatar daran da za suyi waya washe gari basu da lactures,. kuma ba waya suke kamar da sosai ba in sun daɗe suna waya suyi 30 to 40 minutes suna waya, saɓanin da da sai suyi 2 to 3 hours suna waya. ma'eeshat har allah-allah take meenal ta gama warewa su fara zuwa school ɗin nan tare saboda bata jin daɗin karatun ko kaɗan, tasan da meenal tana nan ita zata ringa takura mata kan ta mayar da hankali wajan karatu. tunda yanzu doctor yasa ma'eeshat ta canza course ta koma medicine kamar yarda meenal take so, dan haka koda meenal ta fara course ɗaya zasu karanta. Yau ta kasance ranar weekend ma'eeshat basu da school dan haka bayan ta gama baccin ta sosai ta huta, tana tashi taci abinci ta ƙoshi, sannan tai wanka ta shirya, daga haka tayiwa mami sallama tace mata ta tafi gidan su meenal. tana futa driver ya ɗauke ta ya wuce da ita gidan su meenal. Bayan ma'eeshat ta ƙwanƙwasa umma ce ta buɗe mata sai da suka gama gaisawa ma'eeshat take tambayar umma meenal, umma tace meenal tana ciki tana bacci,. Daga haka ma'eeshat ta shiga ciki kamar yarda umma ta faɗa haka taga meenal kwance tana bacci tasa riga iya guiwa kan ta ba dan kwali duk gashin kanta ya baje ya rufe mata fusa. Ma'eeshat bata tashi meenal ba ajiye jakarta tai sannan ta cire mayafin ta, ta fuce daga bedroom ɗin meenal. daga haka ta wuce kicin ta fara taya umma girki, ma'eeshat tayi farin ciki sosai ganin umma tana dafa dambun shinkafa, saboda ma'eeshat tana bala'in son dumbu a rayuwarta. cikin farin ciki ma'eeshat tace "lah! umma kice yau favorite ɗina kike girkawa". itama umma murmurshi tai tare da cewa “eh wallahi kinga kamar nasan yau zaki zo, kinga na dafa a sa'a ai" "eh wlh umma gaskiya naji daɗi sosai dama na jima banci ba", "aikuwa yau za kici ya ishe ki kuwa". to haka umma da ma'eeshat suna girki suna hira abun su. umma tana gayawa ma'eeshat irin halin damuwa da meenal take ciki. ma'eeshat kuwa cewa umma tai, ya kamata meenal ta koma school in suna tafiya school tare, tunda meenal tana son makaranta maybe zata dawo normal in tasa karatu a gaba zata manta da komai, saboda meenal ma'abociyar son karatu ce sosai. Umma ba tayi wani dogwan nazari ba ta amince saboda ita har ga allah ta gaji da ganin yarinyarta meenal cikin wannan halin, saboda duk wani rarrashin duniya da ban baki tayiwa meenal, duk da kuwa meenal ɗin tana nunawa umma ba komai, komai ya wuce amma, umma ta fahimci meenal tana cikin damuwa, kuma in ta tambayeta sai tace ba komai. Bayan umma da ma'eeshat sun gama yin dambun shinkafa, umma cewa tai "yauwa aishatu tunda ya sauka sai ki zuba kici yarda kike so". murmurshi jin daɗi ma'eeshat tai kafin tace "a a umma ki bari sai meenal ta tashi sai mu ci tare da ita, saboda in muna ci tare da ita sai dumbun ya fiyemin daɗi". "Tom shikenan, bari naje na ƙarasa wanke-wanke can". da sauri ma'eeshat ta ruƙo hannu umma tare da cewa "haba umma ki bari ni zanyi kafin meenal ɗin ta tashi" "aa ki barshi aishatu kinga rigar jikin ki me dogon hannu ce nasan halinki sai kin ɓata jikin ki da ruwan wanke-wanke". dariya ma'eeshat tai tare da cewa tom bari naje na canza wata mara dogon hannun, dan allah umma ki bari nayi Ina so". Daga haka ma'eeshat bata bari taji amsa umma ba ta wuce bedroom ɗin meenal domin canzo wata rigar. ma'eeshat tana son tayi wanke-wanke saboda a gidan su bata saba yin wanke-wanke ba ƴar aiki ce take yi, kafin ma ta tashi daga bacci, in kuma an tara na rana tana can sabgar gabanta ko school bare ma tayi". in wataran ƴar aikin su bata jin daɗi kuma akace sa'a ma'eeshat tana gida in mami tacewa ma'eeshat tai wanke-wanke har daɗi take ji. bayan ma'eeshat ta buɗe ƙwabar kayan meenal ta bacci, daga sama taga wata riga iya guiwa mai siririn hannu. irin ta jikin meenal ɗin ce sak, kalace kawai ta babbanta, zaro rigar ma'eeshat tai da sauri sannan ta rufe kwabar a hankali saboda bata so ƙarar ta tashi meenal daga bacci. Daga haka ma'eeshat ta cire kayan jikinta tasa rigar, ko tsayawa kwashe kayan nata ba tai ba in da ta cire haka ta mai da, ta fuce, saboda taje tai wanke-wanke. ma'eeshat tana isa wajan kwaninka ta tsuguna ta fara haɗa kunfa, saboda umma ta tarar mata ruwan wanke-wanke ma a fomfo ba ɓata lokaci ma'eeshat ta fara wanke-wanke. Duk da kwanikan basu da wani yawan arziki sai da ma'eeshat ta ɗauki muntuna da yawa tana wanke-wanke kafin ta gama, sannan ta koma kicin taje ta kife su. bayan ta futo ta ɗauki tsintsiya ta fara sharce wajan wanke-wanke. "manya gari saukar yaushe". muryar meenal ma'eeshat taji tana mata magana ta bata. Da sauri ma'eeshat ta juyo tare da cewa “har kin tashi kenan ai ni na daɗe da zuwa kiji in gaya miki".ma'eeshat ta ƙarasa magana tana sakin murmurshi kamar yarda meenal ɗin take saki. "Amma shine baki tashe ni ba" meenal ta faɗa tana bin ma'eeshat da ido. girgiza kai ma'eeshat tai tare da cewa "aa meye na tashin ki kina bacci, yanzu ba gashi kin tashi ba". Takalmi meenal ta saka tare da cewa "amma da kin tashe ni bari nayi alwala, saboda yanzu za kiji an fara kiran sallah la'sar". daga haka ma'eeshat da meenal suka ɗaura alwala bayan sun koma suka shige bedroom ɗin meenal. "ma'eeshat nasha gaya miki in kika cire kaya ki dena ajiye su ƙasa ba kyau". meenal ta ƙarasa maganar tana duƙusawa ƙasa tana ɗauke rigar ma'eeshat ɗin". Bayan meenal ta ɗauke durowa ta buɗe ta ɗebo musu hijaban sallah. meenal tana juyowa cikin mamaki tace "haba ma'eeshat wannan kalar kallon da kike min, nasan akwai zance mene?". "ƙwarai kuwa meenal akwai, kinga yarda kika waɗa ido yayi zuru-zuru me yake damunki?” ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana yiwa meenal kallon tuhuma". Ajiyar zuciya meenal ta sauke tare da cewa "ma'eeshat kenan ke har sai na gaya miki damuwata ai kin san damuwata uku ce mutuwar baba, waleed, da kuma engagement ɗin da aki min na dole wanda ban so ba" ma'eeshat tana ƙoƙarin magana suka ji an tayar da sallah, dan haka ba wanda ya sake cewa komai a cikin su, meenal ta shinfiɗa musu dadduma suka fara gabatar da sallah. Bayan sun idar sun kammala addu'o'i da lazimi, miƙewa ma'eeshat tai. kallon ta meenal tai tare da cewa "ina zuwa kuma?". "abinci zan zuba mana yau umma ta dafa mana favorite ɗina tun dazun yawuna yake tsinkewa ina so naci amma nace sai kin tashi daga bacci zan ci to yanzu gaskiya na gaji da haƙuri". ma'eeshat ta ƙarasa maganar tana fucewa daga ɗakin. Meenal murmurshi tai ba tare da tace komai ba sannan ta janyo wayarta ta fara dannawa. Ba a ɗauki muntuna masu yawa ba ma'eeshat ta dawo bedroom ɗin hannu riƙe da madedecin ture wanda ta cika shi da dambu dam har wani tsiri yake. bayan ta ajiye ta sake fita ta ɗauko tasar soyayye mai tare da robar yaji. Bayan nan bata zauna ba sai da taje ta ɗauko musu leman kwali da ruwan jarka tare da 2 cups. ajiye wayar meenal tai a gefe tare da sake faɗaɗa fuskarta da murmurshi tana cewa "hmmm rabin rai sannun ki da aiki, yanzu wannan duk uban abinci zamu iya cinyewa kuwa?". murmurshi ma'eeshat tai tare da sauke ajiyar zuciya tana gyara zama, sannan ta ɗago ta zubawa meenla kallon kan ki ake ji. sorry kwana biyu kun jini shiru-shiru ko, wlh na tafi hutun da ba shiri ne but yanzu in sha allah na dawo... Aringa yimin reaction kuma ga link kuyi following ɗin channel ɗina, dan samu posting da zarar na ɗora. Game bukatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link din channel yayi fallowing. https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d _page 40 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Daga haka ma'eeshat ta ɗauki spoon ta fara cin dumbun ta, tana kai lomar farko baki, taji daɗi har kwanyar kanta, ai ma'eeshat bata san sanda ta ajiye spoon ɗin, ba ta cigaba da ci da hannu, saboda gani take sai tafi gamsuwa. meenal murmurshi ta saki tare da ɗaukar spoon ɗin ta fara ci a nitse. Ma'eeshat sai da taji cikinta ya fara ɗauka sannan tace "meenal ki dena sa damuwa a ranki karki ɗaurawa kan ki ciwan zuciya fa". ajiye spoon ɗin hannnu ta meenal tai cikin damuwa tace "ma'eeshat na gaji da rayuwar nan gwara ciwan zuciya ya kamani zuciyar tawa ta buga kowa ya huta". "A uzubillah meenal kin san me kike faɗa kuwa". ma'eeshat ta faɗi haka cikin tashin hankali tana tsare meenal da ido. "hmmm ma'eeshat ba zaki gane ba wallahi duniyar nan ta ishe ni, na rasa mahaifina kuma anaso a rabani da wanda nake so, sannan za’a auramin wanda ban san shi ba ban taɓa ganin sa ba". "A'a meenal ki dena faɗin hakan wallahi muna son ki bamu gaji dake ba, in sha allah mutuwa ba yanzu ba, ki dena damuwa ki barwa allah komai zai share miki hawaye nima ina nan ina tayaki da addu'a, komai zai dedeta. kuma Bama ke ɗaya ba nima ina so nasan wanda zaki aura amma doctor ko da wasa bai taɓa yimin maganar ba, kuma gashi doctor baya son mutum ya ringa shiga abinda bai shafe shi ba, shi yasa nake shakkar tambayar sa, baya gayamin komai da ya shafi gidan su. Banƙi ba de yana yimin zance ƙanwarsa yesmeen dan naga yana ƙaunarta". "ma'eeshat ni ba wai sanin wanda ake so a aura min bane damuwata ko labarin sa, damuwata fa akan bashi yace yana so na ba kuma bai taɓa ganina na ba" meenal ta ƙarasa maganar tana zubar da zafafan hawaye". dan allah meenal ki dena kukan nan kamar yarda na gaya miki addu'a itace mafita kawai, maza ki share hawayan ki dan Allah". kamar yarda ma'eeshat ta roƙi meenal haka meenal ta fara share hawayan ta. "dan allah meenal ki dena yawan kuka, watarana sai labari, kin san de babban tashin hankali na bai wuce ace na ganki kina kuka ba ko?". murya na rawa meenal tace "hakane ma'eeshat kiyi hakuri na dena". "Yauwa rabin rai na kin san menene kuwa?" ma'eeshat ta tambayi meenal tana binta da ido. "a'a ma'eeshat sai kin faɗa". "shawarar da zan baki shine kizo mu koma school tunda an gama yi mana registration tare, abba ne yace wai a bari mutuwar baba ta sake ki, kuma yanzu kinga in kin koma school zaki cigaba da karatu, in busy karatu yayi miki yawa komai mantawa zaki yi da shi dan allah kizo mu ringa tafiya tare". "Hakane ma'eeshat nima ina son zuwa school ɗin nan amma umma ce naga kamar bata so". "in de umma ce matsalar, tom albishir ki" kallon ma'eeshat meenal tai cikin mamaki tace "goro" "yanzu umma ta amince, mu ringa zuwa makaranta". "what! are you shower?" meenal ta faɗi hakan fuska ɗauke da mamaki da kuma ɓoyayyan farin ciki. "eh mana da gaske umma ta amince, yau munyi maganar da ita bayan nazo". cikin farin ciki meenal tace "alhamdulillah ma'eeshat nayi farin ciki sosai wallahi, nasan yanzu de damuwata zata ragu". "sosai ma meenal zakiji daɗin school ɗin sosai, ko mutane kike gani suna zurga-zurga ai zakiji daɗi". "Tom yanzu yaushe zan fara zuwa?". meenal ta tambayi ma'eeshat tana kallon ta. "Monday zaki fara zuwa in sha allah". ma'eeshat ta faɗi hakan ciki farin ciki, dan ma'eeshat tafi meenal jin daɗin komawar meenal makaranta, gaba ɗaya bata jin daɗin school ɗin. Haka meenal da ma'eeshat suka cigaba da cin abinci suna hirar su gwanin sha'awa. itama meenal yau taji daɗin zuwan ma'eeshat ɗin, dan raban da meenal ta saki jiki taci abinci sosai kuma tai hira kamar haka, harta manta. ma'eeshat ta sa meenal cikinfarin ciki sosai, sunci abinci sosai sun ƙoshi kuma sun sha hira harda dariya. Ma'eeshat ba ita ta fara ƙoƙarin tafiya gida ba sai da tayi sallah isha'i, ji take kamar karta tafi gida ta ƙwana a gidan su meenal, amma bata sanar da mami zata kwana ba. ko da ma'eeshat zata tafi har waje meenal ta raka ta. ma'eeshat tace zata bigo mata waya ta sanar da ita yarda su kai da abba wajan komawarta school. Bayan ma'eeshat ta shiga mota driver yaja, meenal komawa tai cikin gida. gaba ɗaya meenal ji tai tana cikin farin ciki yau, a cikin baƙin cikinta kaso 100% 60 ya ragu. itama umma ta lura da hakan sabida sai da suka zauna suka sha hira abun su, wanda suka jima basuyi hakan ba. Sai wajan goma dare meenal tai sallama da umma, bayan sunyi sallama bedroom ɗinta ta wuce, ta shiga toilet tai wanka sannan tasa kayan baccin ta. tana gama shirin bacci kamar wanda waleed yake jira ya kirawo ta. meenal cikin farin ciki ta shige blanket ɗin ta mai kauri sannan ta saita muryarta ƙasa-ƙasa yarda ba mai jin abinda take cewa, saboda umma. Daga haka meenal da waleed suka hau shan hirar su ta soyayya. shima kan sa yau waleed ya gane meenal tana cikin farin ciki, ko da ya tambayeta meenal bata ɓoye masa ba ta gaya masa school zata koma. shima waleed yayi farin ciki har zuciyarsa, sabida yasan ko ba komai wataran zai iya ziyarta in taje school su haɗu. Har yau waleed bai san anyiwa meenal engagement ba, ko da wasa. ko wajan su mami da abba ma bai ji zance ba bare ma'eeshat kuma. Mami da abba sun yanke shawarar, kar waleed yasan zancan, nan kusa sabida zai iya shiga wani hali, dan sun lura ba ƙaramin so yakewa meenal ɗin ba. Ma'eeshat Bayan ma'eeshat ta koma gida, direct wajan abba ta nufa dan taga alamun yana gida. knocking ma'eeshat take baki ƙofa, ma'eeshat da taji shiru hakan ya tabbatar mata yana can ciki bedroom ɗin, dan haka tura kai tai tunda tasan mami bata ciki ta barota a ƙasa, dan da abba yana tare da mami in taji shiru sai dai ta juya, kamar yarda aka basu tarbiyya. bayan ma'eeshat ta shiga fallon sai da tai sake knocking bedroom ɗin abba haɗi da sallama kafin abba ya bata umarnin shigowa. zaune ta samu abba kan bed ya baje takaddu idon sa ɗauke da glass ɗin ƙarin gani. kusa da shi ma'eeshat ta zauna tare da cewa "abba na sannu da aiki". "yauwa ma'eeshatu na sannun ki, dana dawo na tambaye ki aka cemin kin tafi gidan su meenal" "eh dady ina can too days ban ganta bane shi yasa naje yau, tunda ita har yanzu naga bata fara fita ba, tun rasuwa baba" "Allah sarki baban amina, allah ya jiƙansa ya jaddada rahma gare shi" "ameen abba". "To ya kika baro su ita da umman ta fatan komai lafiya koh" "ah abba duk suna lafiya". "masha allah ya makaranta fatan de kina karatu dayawa koh". murmurshi ma'eeshat tai kafin tace "alhamdulillah abbana ina karatu da yawa sosai da sosai". "Masha allah haka ake so allah ya temaka a cigaba da mai da hankali sosai" ameen in sha allah". daga haka ma'eeshat ta gyara zama tare da cewa “abba dama akan maganar zuwa makarantar meenal ne, gaskiya ya kamata yanzu ta fara zuwa, saboda karatu yana wuce ta". jinjina kai abba yayi kafin yace "hakane ma'eeshat amma ya kamata ace anyi ko 3 moths ne kafin ta fara zuwa, baban ta ne ya rasu fa". "Abba zuwa makarantar meenal ne zai sa ta dawo normal gaba ɗaya yanzu ta canza tana cikin damuwa, meenal tana son karatu, tana komawa school hankalin zai koma kan karatu damuwar da take shiga zata ragu". "Hmmm gaskiya ne ai sai a hankula zata watstsake dama mutuwa haka take da cin rai bare ma, mutuwar iyaye, to yanzu ita meenal ɗin tana son ta fara zuwa yanzu, zata amince kuwa" abba ya tambaya yana kallon ma'eeshat. "eh mana yanzu ma da izinin ta nazo na gaya maka, har umman duk sun amince". "masha allah haka ake so allah ya bada ilimi mai amfani, ranar monday sai ta fara zuwa in sha allah". cikin jin daɗi ma'eeshat tace "tom shikenan abba Allah ya kai mu" "ameen aishatu allah yayi miki albarka" "Ameen abbana wallahi ina son ka sosai" ma'eeshat ta faɗi hakan tana rungume abban ta gefe. “i love you too my special daughter”. Daga haka ma'eeshat ta tashi tare da cewa "okay abba good night bye". bayan ma'eeshat da abba sunyi sallama ma'eeshat fucewa tai ta kama hanyar bedroom ɗin ta zuciya cike da farin ciki. tana komawa ta ɗauki wayarta ta buɗe WhatsApp domin duba saƙon doctor. kamar yarda ma'eeshat tai tunani doctor ya turo mata message. bayan ta bashi amsa reply yayi mata da cewa "okay sannun ki da dawowa in kin huta zamuyi waya nima yau da wuri na dawo gida na gaji". "Wani murmurshi ma'eeshat tai naji daɗi tare da masa reply da cewa "a'a ba abinda nake na gama komai kwanciya zanyi yanzu, kawai ka bugo musha soyayya mu". Ma'eeshat tana turawa doctor reply ya saki murmurshi sannan ya danno mata kira ta WhatsApp call. sai da ma'eeshat ta kashe globe ɗin bedroom ɗin ta canza zuwa green, sannan ta ɗauki wayar tana ɗauka, ta ƙwanta tare da shigawa ciki blanket ɗinta da yake yau ana ɗan sanyi sosai a garin tun bayan sallah isha'i. daga haka de ma'eeshat da doctor suka faɗa kogin zumar masoya. soyayya suke mai tsafta ba ruwan su da faɗar abinda bai dace ba, ko ma'eeshat ta faɗi wani abun wanda bai kamata ba a matsayin ta na yarinya sai doctor ya ɗan gwaɓeta cikin kulawa da soyayya ya hane ta. Doctor yasan kan sa yana kare mutuncin sa sosai, koda suna waya feeling ɗin shi ya tashi yayi masa ƙarfi sallama yake mata ya katse wayar sabida baya so, in ya fita hayyacin sa a samu matsala. Momy and daddy Ɓangaran momy da dady, babu wanda suka sanar gaba ɗaya gidan akan engagement ɗin da akayiwa muhseen da meenal. su kaɗai suka san abun so, ko doctor basu gayawa ba, haka momy da dady suke ta fama ɓoye abun kamar wani sirri. Kamar yarda doctor be sani ba shima kan sa muhseen ɗin bai san an masa Engagement ɗin ba. Momy da dady sun bawa kan su ƙarfin guiwa akan komai zai tafi normal, in lokaci yayi kowa ya sani, amma ba yanzu ba, saboda basa so wani ya kawo musu cikas akan abinda soke so suyi. sabida suna ganin ko ba komai sun ceci rayuwar meenal daga auran waleed, dan su momy kallan mutumin banza sukewa waleed. Ga shi momy tana son meenal har cikin ranta, shi yasa take so nan da 'yan few months, a ɗaurawa muhseen da meenal aure, saboda meenal ta dawo wajan ta da zama. dan momy da daddy suna kan bakan su na, ko anyi aure ba za'a bawa muhseen meenal ba, sai ya sake hankali ita kuma meenal tayi karatu ko de bata gama ba ya kasan lce karatun ta yayi zurfi........ Kar ku manta ku ringa yimin reaction kuma ayi following channel ɗina saboda a can zan cigaba da posting yanzu. mu haɗe a next page bye. Game bukatar littafin doctor ashmal tun daga farko har inda aka tsaya ga link din channel yayi fallowing. https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d _page 41 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Yau ta kasance ranar monday tun asuba da meenal ta tashi daga bacci, bata koma ba, take ta faman shiri sabida zuwa school. Ta dan taya umma aikace aikace gida da yake da wutar nepa. Bayan sun kammala meenal ta hau feraye dankalin turawa sabida shi take sha'awar ci yau. Bayan ta kammala ferayewa ruwan zafi ta zuba a botiki ta nufi toilet din bedroom ɗin ta, ta kai ruwan sannan ta dawo bedroom ta fara cira kayan ta. bayan meenal ta cire kayan ta towel ta ɗaura sannan ta kama hanya zuwa toilet. Bata ma kai da ƙarasa shiga toilet ɗin ba, taji wayarta ta fara ringing. Murmurshi meenal tai ta juyo ta koma domin ɗaukar wayarta, dan ko bata gayawa meenal ba tasan ma'eeshat ce take kiranta da sanyin safiyar nan dan ba wanda zai aikata hakan sai ita sabida ko waleed baya kiran ta da sanyi asubayi kamar haka, dan a lokacin garin bai gama washewa ba. Meenal tana ɗauka wayar kamar yarda tai tunani ma'eeshat ɗin ce dan haka, wayarta ɗauka tare da sallama "Assalamu alaikum" "wa'alaikissalam meenal fatan de kin tashi daga bacci kin fara shiri ko?" ma'eeshat ta faɗa cikin zumuɗi. murmurshi meenal ta saki tare da cewa "na tashi mana ma'eeshat ai ke kin san bana letti sai kace ke" "Hmmm hakane na manta ai ke baki da westing time, in gari ya waye wajan 7:30 zamu zo ni da Abba saboda ya raka ki school yanzu wanka zanyi nima". "nima wanka zanyi towel ne ajikina ina ƙoƙari shiga toilet kika bugomin waya bye". ma'eeshat cikin farin ciki itama tace "okay bye see you litter". Daga haka meenal ta katse waya ta shiga toilet tayi wanka. bayan ta fito mai ta shafa a jikinta sannan tasa pants da bra, daga haka ta saka riga mara nauyi ta koma kicin ta fara soya dankali. bayan ta kammala soyawa ruwan shayi ta ɗaura sannan ta fara yanka albassa da zata soya kwai. Bayan ta sauke ruwan zafi ta fara soya kwai. kamar yarda suka saba haka ta soya umma uku ita uku, dama haka suka saba meenal sai da taji kamar tai kuka sabida ta soya harda baba sai da ta gama soyawa sannan ta dawo hayyacin ta dan ita ta sha'afa, saboda inde tazo soyawa haka take soyawa lokacin da baba yana raye. Daga haka meenal ta juye egg ɗin sannan ta kai musu ɗaki. Lokaci da meenal ta shiga bedroom ɗin umma ta sameta, ta koma bacci dan haka rabuwa tai da ita in ta farka taci nata. meenal tea ta haɗa san nan tai saving kanta a plate ta zauna tana ci tana tuna soyayya da suke sha ita da waleed tana sakin murmurshi abinta. Haka meenal har taci ta ƙoshi sosai sabida ta cinye duk abinda ta zuba kuma ba komai ne yasa ta hakan ba, face tunanin waleed. bayan meenal ta kammalaci cup ɗin data bata da plate and spoons ta kwashe ta nufi wajan wanke-wanke ta wanke su sabida gaba ɗaya meenal bata so umma ta ringa wahala, da aikace-aikace. Bayan meenal ta kammala wankewa kicin ta koma ta kife su sannan ta koma bedroom ɗinta ta ɗebo kayanta ta saka. Meenal har ta ɗauko mayafi da zata sa, ta mai da shi saboda taji yarda garin yayi sanyi yau dan haka hijab ɗinta, ta ɗauko domin taga sai yafi mata, kuma gashi ita ba gwanar son shiga dandazon mutane ba duk tsarguwa za tai gwara ma ta bari ta saba da school ɗin. Kamar yarda ma'eeshat tace haka kuwa akai misalin ƙarfe 07:30 Abba da ma'eeshat suka zo domin ɗaukarta. sallama meenal tai wa umma. umma kuwa tayiwa meenal addu'o'i da fatan samun nasara, bama ita kaɗai ba harda ƙawarta ma'eeshat, sannan meenal ta futo. Bayan ta shiga motar gai da Abba tai cikin ladabi bayan sun gama gaisawa cikin fara'a da sakin fuska Abba ya cigaba da driving abin sa. ma'eeshat kuwa sai farin ciki take tana faman jan meenal da surutu cikin farin ciki. saboda yau ma’eeshat wani mugun farin ciki take ji masoyiyarta zata fara zuwa school. Bayan su ƙarasa school, directed office suka nufa Abba yayi bayani game da meenal, dama already anyi mata registration, dan haka yan abubuwan da suka kamata aka ƙarasa mata sanan akace taje ta zauna a aji tare da ma'eeshat itama daga yau ta zama ɗalibar makarantar. Daga haka ma'eeshat taja meenal suka wuce aji. bayan sun shiga basu daɗe da zuwa ba lactures ɗin su ya shigo aka fara yi musu karatu. meenal taji daɗin karatun sosai bai mata wahala ba duk abinda aka tambaya tana bada amsa sosai duk da kuwa bada ita aka fara topic ɗin ba har sai da ta burge malamin nasu da sauran ƴan aji da dama. Ma'eeshat ce ta dan taɓo meenal a hankali. meenal sake matsowa tai sabida ajin yayi stit. A hankali ma'eeshat ta farayiwa meenal rada da cewa "kai meenal wlh lactura ɗin nan ya faɗa sosai, kinga wani kallo da yake miki na kulawa, wlh wannan kallon soyayya". Yamutsa fuska meenal tai tare da girgizar kai tana cewa "ke rabani mana kin san school ɗin nan malami da dalibai basa soyayya, ko ba haka kika cemin ba?". "eh haka ne tsarin school ɗin, amma kam ya zurma ba laifi, kin san ke haka kike da farin jini kamar me" Meenal tana kokarin yin magana suka haɗa ido da malamin da mamakin ta sai gani tai ya kashe ta da wani irin kallo me ban mamaki, wanda shi ka ɗai yasan me yake nufi". murmurshi ma'eeshat ta saki tare da cewa "u see". a hankali ma'eeshat ta furta hakan, Meenal tana ƙokarin yin magana suka sake haɗa ido da malamin da mamakin ta sai gani tai ya kashe ta da wani irin kallo me ban mamaki, wanda shi kaɗai yasan me yake nufi. murmurshi ma'eeshat ta saki tare da cewa "u see". a hankali ma'eeshat ta furta hakan. sai da malamin ya ɗauke ido daga kan meenal, meenal ta bawa ma'eeshat amsa na "yes I see". Daga time ɗin meenal taji haushin malamin yayi mugun kamata, dan ko yayi tambaya bata bada amsa kawar da kai take yi kawai….. Tafe ma'eeshat da meenal suke, sun futo daga makarantar su zasu ƙarasa in da ake sai da snaks domin su sai dougnot and meat f da kuma lemo. Meenal ce ta sake riƙe hannun ma'eeshat tare da cewa "ma'eeshat tun da muka futo daga school, ba jimawa naji motar da take bayan mu, anya bamu take ba” “conform nima abinda na gani kenan amma ina taso in juya na kasa, bana so in yarfa kai na ne wlh” meenal cewa tai “gaskiya kam, kar mu juya kawai mu cigaba da tafiya”. Meenal tana rufe bakin ta, sukaji ƙarar an kashe motar, alamun me motar zai futo. Cigaba da tafiya sukayi ko wannen su cike da zullumi, waye haka. Su ma’eeshat basu tsinke da lamarin ba sai da suka ji ana bun su ta baya. Amma hakan suka cigaba da tafiyar su cikin rashin nuna damuwa. “Assalama’alaikum” abinda su meenal sukaji, mutumun ya faɗa. Dakatawa su kai da tafiyar, sannan ma’eeshat ta, amsa, tare da juyawa. Ita kuwa meenal a zuciyarta ta amsa sallamar. “In ba damuwa zan iya magana da ƙawarki” mutumin ya tambayi ma’eeshat yana kallon meenal ɗin. Murmushi ma’eeshta tare da cewa “okay ba damuwa bari nai mata magana” daga haka ma’eeshat ta sake matswa kusa da meenal tare da cewa meenal ke yakewa magana fa”. Yamutsa fuska meenal tai tare da cewa “haba ma’eeshat me zanyi masa to, bayan kin san halin da nake ciki yanzu bana buƙatar wani saurayi ni”. “Please meenal ba’a haka kawai ki saurare shi, saboda ya barmu, in kuma ba haka ba bun mu zai tayi”. “Tom ma’eeshat amma daga nan, na rabu da shi ba wani time da zan bashi bare na saurare shi”. “Eh mana hakan ma yayi” duk a hankula ma’eeshat da meenal suke maga yarda mutumin ba zai ji su ba”. Meenal tana juyowa sai da gaban ta ya ɗan fadi rass saka makwan ganin mutumin. Masha Allah yarda kasan ba bahaushe ba haka yake kyakyawa da shi, fari ne tasss masha Allah. Dole duk wanda ya kalli mutum sai ya ƙara sabida kya. Meenal kawar da kai tai ba tare da tace komai ba. Fuska cike da murmushi yace “yan mata sannu fa, na tare ki a hanya ba daɗi ko zaki zo mu shiga mota ne?”. Sake haɗe rai meenal tai tare da cewa “aa ni sauri muke inajinka na haka minti 2”. Murmushi kyakyawan mutumin yayi sannan “yace ni sunana khaleed, amma kinga magana a titi ba za tai ba kawai ki bani number ki sai na kirawo ki ko nazo har gida mu tattauna”. Yarda ma mutumin yake magana kasan gentle man ne sosai yana da nutsuwa kuma ga ilimi. Girgiza kai meenal tai tare da cewa “gaskiya ba zaka samu number ta ba, kawai in baka da abin faɗa zamu iya tafiya” shiru mutumin yayi yana bin meenal da kallon. Ma’eeshat ce ta ɗan zunguri meenal tare da cewa “haba meenal mene haka”. Haɗe rai meenal tai sosai kamar ba ita ba. Shi kuwa mutumin mai da kallan sa yayi kan ma’eeshat tare da cewa “ please ki bani number ta in ba damuwa nayi maganar da ita ta waya naga kamar bata san, tsayuwar mu haka, kuma kinga hakan ba dadi”. Jinjina kai ma’eeshat tai tare da cewa “gaskiya ne bari na baka”. Hannu na ruwa mutumin ya zaro tsadadiyar I phone ɗin sa, ya miƙawa ma’eeshat. Ba musu ma’eeshat ta karba ta fara sa masa number meenal da yake ta haddace. Bayan ta gama sa mai miƙa masa wayar tayi tare da janyo hannun meenal har sun fara shirin tafiya, mutumin yace “afuwa pls sunan ta fa”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “meenal” murmushi sosai khaleed yayi tare da cewa “wow nice name aminatu okay goodbye” daga haka guy ɗin bai sake cewa komai ba, ya juya ya tafi. Suma su ma’eeshat ɗin basuyi ƙasa a guiwa ba suka bar wajan. Bayan sun cigaba da tafiya, cikin damuwa meenal tace “haba ma’eeshat yanzu sabida me kika bashi number na yanzu fa kin san halin da nace ciki, anyimin engagement da ƙanin doctor, bayan kin San yarda nake mutuwar son waleed, kuma yanzu sai ki ƙaramin da wannan guy ɗin ki bari naji da wa’annan”. Sauke ajiyar zuciya ma’eeshat tai tare da cewa, “please meenal ki dena wannan maganar ki cigaba da addu’a kawai mafita zata zo miki. Ni banga laifin guy ɗin nan ba, ji shi fa kyau iya kyau kamar doctor na gashi fari kai wallahi kun dace, wannan wane waleed a kyau ma, hmm wallahi kawai ki kwantar da kai ku fahimci juna, yanzu sai kiga maybe shine mijin naki ma”. Shiru meenal tai zuciya tana suya ba tare da tace komai ba. Daga haka suka cigaba da tafiya ma’eeshat tana ta yaban gayan nan……….. Bayan an tashi daga school sai da driver ya fara sauke meenal a gida sannan ya wuce da ma’eeshat gida. Ma’eeshat tana komawa gida tai wanka sannan taci abinci ta kwanta tana tunanin doctor. Bayan ma’eeshat ta gama tunanin doctor, tunani ta farayi Taya zata temakawa meenal ta samu farin ciki a so. Ma’eeshat ta ɗauki alwashin za tai iya ƙoƙarinta wajan ta shawo kan meenal ta fara son khaleed ko hankalin meenal zai kwanta dan ta lura sun dace, kuma daga gani kuɗi sunyiwa khaleed ɗin biyayya, ga kyau ga ilimi. Da wannan tunanin bacci ya ɗauke ma’eeshat…….. Too days kun jini shiru abubuwa ne su kai min yawa shi yasa na tafi hutu, but yanzu na dawo in sha allah zan cigaba da yi muku posting. Kuma karku manta kuyi following ɗin channel dina, kuma karku manta da reaction hakan ne yake tabbatar mu kuna biye dani ngd. _page 42 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 DOCTOR A cikin yan kwanakin nan gaba ɗaya doctor ya shiga cikin damuwa. Ƙarfin hali kawai yake sabida yana cikin matsanancin yanayin da yake bukatar aure. Wato sexual desire (sha’awa) ga wani irin son ma’eeshat da yake damunsa. Doctor yana iya ƙoƙarin ta hakan ya danne ciwan da yake damun sa, amma abin yaci tura. Doctor ya yanke shawarar bayan ma’eeshat ta dan kwana biyu tana zuwa school, dole a matso musu da auran su very soon sabida bazai iya jira ba. Gaba ɗaya yanzu doctor ya canza sosai, sabida matsalar da take damun sa. Too days har yesmeen ta kasa ganewa doctor gaba ɗaya ya dena sakin jiki da ita bare su zauna suyi hira. Tana zuwa wajansa yake ce mata taje tayi karatu. Sabida doctor bai da nutsuwar da zasu yi wasa da dariya da yesmeen bare hira. Ciikin yan kwanakin nan ma wataran doctor baya iya zuwa hospital sabida damuwar sexual desire ɗin da yake ciki, wannan karan abin yayi worst, ba kamar ada ba. Doctor yana ta tunanin kar hakan ya zame masa illa sabida a yanzu ya girma sosai da sosai tunda har yayi shekara 31 to 32. Yau ta kassance ranar friday doctor tun sallah asuba bai koma bacci ba kamar yarda ya saba. Da wuri ya shirya sabida yau yana so ya shiga babban hospital sabida duba wasu marasa lafiya. Bayan doctor ya gama shiryawa hospital ya nufa domin duba marasa lafiya. Bayan ya gansu bai wani sha wahalar gane mai yake damun su ba. Da yake doctor yana da baiwar nan sosai, koda mutum yaje hospital goma basu gane mai yake damun su ba, in sha Allah doctor ashmal yana zuwa zai gane mai yake damun su. Sometimes ma doctor yana ganin marasa lafiya ko be tambaye su ba, take iya gane damuwar su, saboda allah ya bawa doctor baiwar hakan sosai. Shi yasa Nigeria take alfahari da doctor ashmal dan babban likita ne sosai. Bayan doctor ya gama duba su, ya tabbatar da abinda yake damun su, bai wani jima ba yabar hospital ɗin, sabida yaji ciwan sa ya ɗan fara tashi. Dama yau kimanin one week doctor yake fama da ciwan ciki da ciwan mara, kawai karfin hali yake. Wajan 11:30am doctor ya koma gida. Bayan ya koma kwanciya yayi domin ya huta, amma gaba daya hutun ya gagara saboda ciwo ya tsananta. Dole doctor ya tashi ya fara laluban inda ya ajiye magani. Da yake doctor ya kwana biyu da zuwa da maganin amma yana iya ƙoƙarin sa ganini bai sha ba sabida yasan yawan shan maganin rage sha’awa yakan iya zama cutarwa, a jikin dan adam. Doctor bai sha wahalara ba ya ɗauko maganin da yake yasan inda ya ajiye. Bayan ya ɗauko tsiyayi ruwa yayi a cup ya dawo ya zauna bakin gado. Tablets ne maganin dan haka ɓallo su yayi har guda 3 sabida doctor yasan lamarinsa yayi worst a hakan ma bai sha yarda ya kamata ba kawai yana gujewa karya Saba da shan maganin ne. Sabida wannan shine karo na farko a rayuwar sa da zai sha maganin sha’awa yana iya daurewar sa amma wannan karan abun yayi mai karfi. (Antidepressants) sunan maganin da doctor ya sha kenan. Bayan doctor ya shanye duka ukun, ajiye cup ɗi yayi akan karamar drawer sannan ya kwanta akan bed yana mai da nunfashi. Daga haka doctor ya rufe ido kamar mai bacci. Ahankula doctor yaji ya fara samun nutsuwa sabida maganin ya fara masa aiki dan ciwan sai raguwa yake a hankula a hankula. Wajan 12:30 doctor ya samu nutsuwa sosai sabida ciwan ya ragu sosai nesa ba kusa ba, saura abinda ba za’a rasa ba. Dan haka miƙewa doctor yayi ya shiga toilet yayi wanka abin sa. Bayan ya futo a hanzarce ya shirya cikin tsadadiyar shaddarsa ya fesa turare tare da sa agogo da hula. Bayan ya kammala tsadaddan takalmin sa mai kyau ya saka sannan ya ɗauki lallausar daddumar sa. Doctor bai bi takan wayarsa ba bare mukullum mota saboda masallacin Jumma’a zai je. Kuma basu da wani nisa da masallacin sosai yana so yayi tafiyar ƙafa saboda samun lada. Bayan doctor ya fita bai tarar da kowa a fallon ba dan haka wucewa yayi ya fuce daga gidan. Haka doctor ya karasa masallaci bayan yayi sallah ya ɗauko dawowa gida. Lokacin da doctor ya ƙarasa gida zauna ya tarar da yesmeen a falo ta rafka tagumi kamar wata sabuwar marainiya. Tana jin sallamar doctor ta ɗago tare da amsawa sannan ta sunkuyar da kai ba tare da ta sake cewa komai ba. Cikin sakin fuska doctor ya ƙaraso tare da zama kusa da yesmeen ɗin yana jan kumatunta da hannunsa cikin kulawa yace “yesmeen yau ba zaki min oyoyo ba?”. Riƙe hannun doctor yesmeen tai tare da cewa “to ba kai ne kullum ka dena hira dani ba, kuma su ya muhseen basa nan, kullum sai de na zauna ni ɗaya, gashi momy busy yayi mata yawa, dady baya nan ladidi tana aiki, yanzu dawa zanyi hira. “Oh am sorry my yesmeen too days Nima nayi busy ne, amma bazan ƙara ba in sha Allah zan ringa baki time muna hira shikenan”. Murmushi Jin daɗi yesmeen tai tare da cewa “eh shikenan, pls doctor bana so naga kana canza min wallahi bana jin daɗi har raina”. “In sha Allah bazan ƙara ba yesmeen ɗina maza jeki kiyi saving ɗin mu muci abinci tare”. Ba musu yesmeen ta tashi ta wuce draining ta zubo musu abinci ita da yayan nata doctor. A plate ɗaya ta zuba musu, kamar yarda suka sabaci wasu lokutan. Sannan ta ɗauko musu spoon 2 ta dawo suka zauna a kasa. Suna ci suna hira, cikin kulawa da soyayyar yan uwantaka. Son Yesmeen yana sake ratsa zuciyar doctor, ji yake kamar shi ya haifeta, kuma yana sake jin farin ciki da yarda yaga yesmeen tana jin daɗi hirar tasu. Ko da suka gama cin abinci Sai da Doctor da yesmeen suka daɗe suna wasa da dariya sosai suka sha hirar su sannan doctor ya tashi ya koma bedroom ɗinsa. Yana komawa ya rage kayan jikin sa, sannan ya koma kan bed ya janyo wayarsa. Direct ma’eeshat ya fara ƙokarin kira da yake yau tace masa da wuri zasu dawo daga school kafin ma a shiga sallah Jumma’a. Ringing uku ma’eeshat ta ɗauka kamar mai jira kiran doctor ɗin. Cikin daddar murya tace “hello dee” murmushi jin daɗi doctor yayi sabida yaji muryar masoyayiyar sa tare da cewa “assalma’alaiki eshat, bana hanaki cewa hello ba kafin kiyi sallama, sallama zaki farayi kafin hello”. Murmushi ma’eeshat tai kamar tana ganin doctor tare da cewa “am sorry na dena”. “Kullum haka kike cewa amma kin kasa denawa Allah ya shirya min ke”. “Ameen dee” daga haka shiru ya ziyarci wajan na wasu daƙiƙu kafin yace “eeshata” gyara zama ma’eeshat tai kafin tace “na’am doctor” “kin san menene?” “Aa sai ka fada” “ba kina sona ba?”. Jinjina kai ma’eeshat tai kamar tana ganin doctor tare da sakin murmushi tana cewa “eh mana”. “Yauwa yar albarka, Nima Ina son ki” murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “nagode”. “To ya school?” Zuciya cike da tunani ma’eeshat tace “alhamdulillahi” sabida tasan doctor yana da maganar da zai faɗa mata ba wannan ba tunda ya fara tambayarsa tana son sa. Maganar doctor ce ta katse ma’eeshat daga tunanin da take ƙoƙarin tafiya, cikin lallausar murya ya sake cewa “eeshata”. “Na am doctor na”. Ajiyar zuciya doctor ya sauke sannan yace “gaskiya eeshata ya kamata a rage lokacin auran nan namu yayi tsayi fa sosai”. Cikin mamaki ma’eeshat tace “sabida me?”. Rintse ido doctor yayi da, da hali yau sai ya faɗawa ma’eeshat dalili, amma baya so su fara irin wannan zance, a ganin doctor hakan bai dace ba, kuma gashi ma’eeshat tana da karanci shekaru ba lallai tayiwa abun kyakyawan zato ba. Zata iya tunanin sabida hakan zai aure ta, kuma in ba mai san hakan bace zata tsorata, amma da babbace sosai mai hankali maybe ya iya faɗa mata. Maganar ma’eeshat ce ta dawo doctor daga tunanin da ya tafi inda ta sake maimaita tambayar “bee sabida me, naji kayi shiru”. Murmushi dole doctor yayi tare da cewa “sabida Ina sanki mana eeshata kullum Ina tunanin ki kuma, kinga in munyi aure kullum zan ringa ganin ki safe da dare muna hirar mu ba sai a waya ba koh?”. Murmushi jin daɗi ma’eeshat tai tare da cewa “eh kuma hakane, Nima kullum zan ringa ganin ka, kana nunamin soyayya da kulawa” “yauwa eeshata, to kinga shi yasa nace miki lokacin auran nan yayi tsayi a rage shi ko zuwa nan da 3 months ne”. Murmushi jin daɗi da farin ciki ma’eeshat ta saki a hankula yanda doctor bazai ji ba sannan tace “yanzu doctor tayaya bayan kasan abba da dady sun sa lokaci”. Girgiza kai doctor yayi tare da cewa “karki damu, ni zan samu dady da maganar sai yazo wajan abba su sake tattaunawa ko, sai a rage lokacin”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “tom shikenan bee hakan yayi yanzu yaushe dadyn zai zo?”. “Aa ina tunanin nan da one moth ko 3 week kafin nan kin ɗan kwana biyu school sai na gayawa dady, because dady nan da gobe zuwa jibi zaiyi tafiya zuwa wata kasar, sai ya dawo”. Cikin jin daɗi ma’eeshat tace “eh hakan yayi Allah ya dawo da shi lafiya” “ameen my future wife, shi yasa kullum nake sake kaunar ki saboda kina son abinda nake so koh”. Gyaɗa kai ma’eeshat tai tare da cewa “Nima kullum ina sake kaunarka doctor na sosai da sosai”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “good girl Allah yayi miki albarka fatan kina mai da hankali wajan karatu bkya wasa?”. Jinjina kai ma’eeshat tai tare da cewa “eh ina yi sosai, da yake itama meenal ta fara zuwa school yanzu tana temaka min sosai, in ma ban gane ba tana sake yimin bayani, kuma ina jin daɗin karatu tare da ita nafi samu nutsuwa”. “Jinjina kai doctor yayi shima sanan yace “okay ki dage da karatu sosai eeshata banda wasa”. Daga haka doctor da ma’eeshat suka cigaba da soyayyar su me stafta kamar su haɗiyd junan dan yau sun jima suna waya sosai da sosai………… MEENAL meenal tana zaune tana buɗe litattafanta makaranta domin karatu taji wayarta ta fara ringing. Lokacin data duba new number ta gani, dan haka bata ɗaga ba ta cigaba da karatun ta abinta. Again kiran ya sake shigowa meenal har taki ɗagawa, kuma sai tayi tunanin ko waleed ne ya canza number da yake 2 days yana kiran ta kuma bata samun damar dagawa sabida tana school ko kuma tana tare da umma”. Dan haka hannu tasa ta ɗauka tare da cewa “assallama’alaikum” “wa’alaikissalam”. Shiru meenal tai sabida ita ba muryar waleed taji ba. Daga can bangaran magana aka farayi da cewa “nasan zaki mamaki waye yake kiran, fatan ban takura miki ko na katse miki wani abun da kike mai mahimmanci ba”. Lumshe ido meenal tai sabida har ga Allah taji daɗin muryar mutum koma wanene, sabida yarda yake maganar sa a nitse. “Am kina jina kuwa?” Mutum ya tambaya cikin kokwanto. Cikin takaicewa meenal tace “eh ina jinka” ajiyar zuciya ya suke tare da cewa “yauwa pls zaki bani ko 6 minutes ne muyi magana yanzu in ba abinda kike?” “Eh ina jinka” “good thank you, farko de sunana khaleed, in ba zaki manta ba Wanda muka haɗu harda friend ɗin ki 3 to 4 days da suka wuce kin gane koh?”………… _page 43 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Yamusta fuska meenal tai tare da cewa “eh na gane” “yauwa da farko de sunana khaleed kamar yanda na faɗa miki a baya, ni ɗan Kano ne but ina aiki a abuja, yanzu ma hutu ne ya kawo ni, amma gaskiya nafi zama a kano”. Shiru meenal tai tana sauraran maganar sa, shi kuma cigaba da magana yayi da cewa “ina zaune a nasarawa g.r.a right kin san unguwar ko?”. “Uhmm na sani” meenal ta bawa khaleed amsa a takaice. “Okay masha Allah, ya kamata in muka samu time nazo mu haɗu, because ina so muyi magana important”. Jim meenal tai na wani lokacin kafin tace “aa ba sai kazo ba ko menene zaka iya faɗa a waya ina jinka?”. Jim shima khaleed yayi kafin yace “pls, ni zan iya jira har ki samu time nazo har gida, sabida maganar da zamuyi mai mahimmanci ce, to kinga zata fi in mun haɗu, ki daure ki samar mana ko short time ne haka, in sha Allah duk abinda nake zan katse shi, nazo mu tattauna”. Ajiyar zuciya meenal tai cikin zullumi tace “okay zan duba na gani”. “Yauwa aminatu ngd sosai da kika bani lokacin ki” “ba damuwa nima nagode”. “Okay Bari na barki haka kar inje wani abun na katse miki, in sha Allah zuwa gobe ko jibi zan sake kira in kin samu lokaci”. Shafa book ɗin gabanta meenal tai tare da cewa “okay Allah ya kaimu” “bye take care” daga haka khaleed ya katse wayar zuciya cike da farin ciki da shauƙi. A hankula meenal ta ajiye wayar zuciya cike da zullumi. Har ga Allah khaleed yayi mutuwar burgeta sosai, a rayuwar meenal tana son namiji mai nutsuwa ba mai takurawa rayuwar mace ba. Meenal ko ba’a gaya mata ba tasan khaleed yana da kamun kai ga nutsuwa, yanayin yarda yake magana ma zai shedawa mutum haka. Saboda tunda ya karɓi number ta wajan ma’eeshat bai kira ba sai after 4 days. Kuma yanzuma yace mata sai nan da 1 to 2 days zai sake kira. Kuma abinda ya sake burge meenal da khaleed yarda yace mata in ta samu lokaci zasu haɗu ba kamar sauran maza da suke takura mata akan zai ta so su ba. Meenal gyara zama tai a zuciyarta tace “hmmmm gaskiya khaleed sai ka jira, ka birge ni amma ni ban fiya san farin namiji ba, bama wannnan ce matsalata ba, ni da nake cikin matsala biyu ga mugun son waleed, sannan ga engagement ɗin da akai min wanda ya zamar min barazana a rayuwa, a gaskiya baka da sauran gurbi a zuciya ta”. Meenal haka tace ayyana a ranta amma wata zuciya take ce mata, engagement ba aure bane kuma addu’a tana iya canza komai, karta cire rai da lamarin uban giji. Lokaci guda meenal taji ta samu karfin guiwa da zata iya kula khaleed. Meenal ba mai san kula maza bace amma haka nan, taji khaleed ya kwanta mata a zuciya ta ko ina, duk da kuwa har lokacin, meenal tana san waleed, kullum ƙaruwa yake sake yi. To daga haka meenal ta mai da hankalita kan litattafin ta, ta duba abinda bata gane ba ta sake karantawa tana reach a wayarta. Sai da meenal ta gama duba littattafan karatu ta, tasha karatun ta, sannan ta miƙe ta fuce. Kicin ta shiga ta zuba abinci sannan ta dawo ɗakinta taci. Tana kammalaci taji an fara kiran sallah magriba, dan haka ba ɓata lokaci ta miƙe ta ɗauro alwala sannan ta dawo ta fara gabatar da sallah. After 3 weeks Meenal da ma’eeshat suna mai da hankali wajan karatu, mussaman meenal ma, sabida ita ma’eeshat tasa soyayyar doctor a gaban ta fiye da karatu da komai ma. Meenal kuwa ta saba da school sosai gaba ɗaya yanzu ta mai da hankali ta kan karatu ta samu sauƙi sosai ba kamar daba, da kullum tana cikin ƙunci da kuka ba. Kuma ba laifi meenal ta ɗan bawa khaleed time suna waya. Da temakawan ma’eeshat, ma’eeshat ce take sake ƙarfafawa meenal guiwa akan soyayyar khaleed. Ba laifin yanzu sun dan fahimci junan su cikin one moth, amma tinda khaleed ya fahimci meenal bata so yazo wajanta ya dena mata zancan zuwa, dan bai fi sau 2 ma ya taɓa mata maganar ba. Khaleed yayi tunanin ya bari su sake sabawa da meenal zai su haɗun. Ɓangaran waleed kuwa tashin hankalin duniya ya ɗora a kan sa na rashin haɗuwar su da meenal. Meenal waleed tausayi yake bata sosai, sabida ta lura kullum sake haukacewa yake akan son ta. Hakane ne yasa meenal ta amince da zuwan waleed school ɗin su, su haɗu ko ya samu kwanciyar hankali, in ya ganta, kamar yarda ya buƙata, zuwa school ɗin nasu………. DOCTOR Tunanin ma’eeshat ne ya ƙaru a zuciyar doctor ganin ya kusan ƙarasowa school ɗinsu, yake ta hanyar zai wuce. Murmushi yayi sannan ya ɗauki wayarsa ya bugawa ma’eeshat tare da ajiye wayar a mazaunin ta na mota. Sai da ta kusan tsinkewa sannan ma’eeshat ta ɗauka baki ɗauke da sallama. Ajiyar zuciyar doctor yayi tare da amsa sallamar sannan yace “meeshata how far?” Cikin sanyayiyar murya ma’eeshat ta bawa doctor amsa da “fine” cike da mammaki doctor yace “eeshata naji muryanki ya canza ko school ɗin ne?”. Doctor ya faɗi hakan yana rage gudun driving ɗin sa. ɗaga kai ma’eeshat tai kamar doctor yana ganin ta tace “Uhmm doctor bana jin daɗin school yau, gaba ɗaya yau na kasa ganewa karatun”. Cike da kulawa doctor yace “why ko baki jin daɗin jikin kine?” “Aa too days da suka wuce na takura an mai damu gida da wuri da yake bana jin daɗi mun rasa lecture 1, yanzu gashi an shigo saban topic har an bada assignment kuma bamu gane ba, meenal ma tayi iya ƙoƙarin, amma bata gane complete ba, kadan ta iya fahimta”. “Oh cool down my eeshata, wannan ba abin daga hankali bane ki min snap ɗin shi ki turomin ta WhatsApp zan duba miki”. Cikin farin ciki ma’eeshat tace “kai gaskiya naji daɗi sosai zaka temakamin nan da one hour kai min solving”. “Oh har nan da one hour za a shiga lectures ɗin?” “Eh nan da awa ɗaya da rabi za’a shiga”. “Oh da time sosai ko nazo ne ma yanzu kina class?”. “Aa yanzu mun futo sai nan da one hour 30 minutes zamu koma”. “Okay to bari nazo kawai sai na koya miki yarda zaki fi ganewa koh?” Murmushi sosai naji daɗi ma’eeshat tai tare da cewa “no nasa kana aiki yanzu, kuma kafin ka futo ka zo school ɗin namu ai zai ja time tinda da nisa kawai ka koyamin ta online ɗin”. “Hmmmm ai yanzun nan ina kusa da school ɗin ku, tanan zan wuce, kawai ki futo kafin ki futoma na ƙaraso”. Iwun daɗi ma’eeshat ta saki tare da cewa “really” amsa doctor ya bata da “yes, I’m really but come outside so you can confirm”. Mikewa ma’eeshat tai tare da cewa “okay I’m coming” daga haka ta kashe wayarta a hanzarce ta ɗauki jakar su, da wayarta da yake a jaka ɗaya suke sa littattafan su ita da meenal.  Kuma meenal tayi wajan 20 minutes da fita sabida waleed yazo, har sai da meenal tace ma’eeshat ta rakata amma ma’eeshat tace aa kawai taje. Daga haka a hanzarce ma’eeshat ta kama hanyar fita daga makarantar. Ma’eeshat tayi tafiya sosai da yake kafin ka fita daga school ɗin da ɗan nisa. tana zuwa get din makarantar ta bugawa doctor tare da tambayarsa yana daga ina. Doctor ba bata lokaci yayiwa ma’eeshat bayani. Ma’eeshat tana fita ta hango motar doctor da yake tasan wasu daga cikin motocin sa ba laifi. Doctor yana katse wayar kamar ance ya juya yana juyawa gefe yaga murfin mota a buɗe. Kallo ɗaya doctor yayi mata ya gane wace duk da kuwa bai gama ganin complete ɗin fuskarta ba. Da yake doctor yana da ganewa sosai. Ta sunkuyar da kai ƙasa shi kuwa waleed sai kallan ta yake kamar maye, jikin sa sai wani rawa yake kamar mara gaskiya, yana mata magana. Doctor bai wani ƙare musu kallo ba kallo ɗaya yayi musu ya kawar da kai bai sake ba, daga nan kuma ya hango ma’eeshat tana nufo sa, sai wani farin ciki ya sake lulube sa. Gaban ma’eeshat ya fadi sosai lokacin da ta hangi motar doctor kusa data waleed. “Innalillahi yanzu in doctor yaga meenal tare da waleed fa, bayan anyiwa meenal engagement da ƙanin sa fa, mai zai yi tunani?”. Cikin zuciyarta ma’eeshat ta faɗii hakan, a fili cikin tashin hankali meenal tace “ya allah yasa doctor kar yaga waleed tare da meenal, Allah ka ɗauke idon doctor daga kan su”. Ma’eeshat tana ƙarasawa, bakin motar doctor ta buɗe gaba ta shiga tare da rufo ƙofar duk dan kar doctor ya kula da waleed da meenal. Duk da meenal ɗin da waleed sunga ma’eeshat amma sai ma’eeshat tai kamar bata san su ba. Ɓangar meenal itama hankalinta ya dan tashi ba laifi da taga ma’eeshat ta buɗe mota ta shiga. Ko ba’a gayawa meenal ba tasan doctor ne yazo wajan ma’eeshat. Dan meenal tasan ma’eeshat ba zata taɓa zuwa wajan wani bayan doctor ba. Fuska cike da murmushi ma’eeshat tacewa doctor “ina wuni”. Kallonta doctor yayi sosai sannan ya kawar da kai yana cewa “lafiya kalau, amma wuni bata shigo ba, but ni bari na gyara ina kwana meeshata?”. Dariya ma’eeshat tai kafin tace “kai doctor kana son cina gyara koh”. “Uhmm to ai matar tawa ce bata iya magana sosai ba, yar baby ce zai ana koya mata”. Cikin shagwaɓa ma’eeshat tace “aa ni wallahi ba yar baby bace, babbace ni za ka cewa yarinya”. Dariya doctor ya ɗan yi mai sauti, sabida hakan da ma’eeshat tayi, tayi ƙololurar birge doctor. Bayan ya tsagaita cewa yayi “Uhmm ke yarinyace mana, amma muna aure kin zama babba” cikin jin daɗi ma’eeshat tace “yauwa amma har yanzu ni babbace ka dena yimin kallan yarinya”. “Aa naƙi, a cikin satin nan dady zai dawo, yana dawowa, zan same shi muyi maganar rage kwanakin auran mu koh”. Ɗaga kai ma’eeshat tai cikin jin kunya tare dasa hannu biyu ta rufe fuskarta. Wani shauƙi doctor yaji ya fara taso mai lokaci guda. Dan haka mazewa yayi ya kawar da zance da cewa “oh kunya kikeji kamar yau za a kai ki gadan ki, maza ki buɗe fuskar ki ki nunamin question ɗin na duba”. Ba musu ma’eeshat ta buɗe fuskarta tare da bude jakarta ta ɗauko handout ɗin ta bude topic din sannan ta mikawa doctor. Hannu doctor ya miƙa tare karba, bayan ya karba ya zuba masa ido. Doctor ko layi biyu bai gama dubawa ya gane topic ɗin. Ɗagowa doctor yayi tare da ajiye book ɗin yana cewa “Let me explain it to you so you can understand the topic”. da sauri ma’eeshat ta girgiza kai tare da cewa “kabar explained ɗin, a halin yanzu kawai ina so ka duba min assignment ɗin sai ka koyamin yanzu nayi”. “Okay bani pepar na rubuta miki amsar, sai ki kwafa ko zan iya, rubaga miki a cikim a book ɗin?”. Gyaɗa kai ma’eeshat tai tare da cewa “eh kayi a cikin book ɗin kawai”. “Okay zuwa anjima zan zo gida da daddare na sake yi miki bayani sosai, sabida bawai assignment ɗi nake so kici ba, aa ina so ki gane topic ɗin sosai”. “Tom shikenan hakan yayi” daga haka doctor ya zira hannun sa a aljiwun gaba ya zaro biro sannan yace ina assignment ɗin?” “Ka buɗe next page yana gaba”. Ma’eeshat ta faɗa tana gyara zama. Bayan doctor ya buɗo assignment ɗin a tsakiyar su ya ajige littafin sannan ya fara dubawa. Wajan 7 question ne amma har an amsa 2 saura biyar. Ɗagowa doctor yayi tare da cewa “naga kuma har a solving na 2 questions a ciki?”. Kallo assignment ɗin ma’eeshat tai tare da cewa “bai yi dede ba koh, meenal ce ta fara gwadawa, kuma end sai tace tana ganin kamar ba dede take ba karta ciagaba”. Cikin mamaki doctor yace “complete Wanda ta amsa is true but littafin ki ne ko nasa?”. “Nawa ne wannan, dama sai ta gama mun sai tayi nata, sabida taga na fita damuwa da assignment ɗin”. Mai da kai doctor yayi ya cigaba da assignment ɗin daga inda meenal ta tsaya tare da cewa “pls meeshata ki ringa mai da hankali sosai, ina so naga kina assignment da kan ki, right bawai a ringa miki ba, in ma baki gane ba, sai ta koya miki, in ta koya miki sai kiyi da kan ki bawai tai miki ba”. “Amma doctor da ni da meenal duk ɗaya ne ba laifin in tayimin ka manta amince dake tsakanina da ita”. Girgiza kai doctor yayi tare da cewa “sorry ni ba haka nake nufi ba, kawai ina so kema ki ringa karatu ne sosai da kan ki, bada brain ɗin wasu ba” “okay in sha Allah zan gyara”. Ma’eeshat tana rufe baki doctor ya ɗago tare da miƙa mata book ɗin. Cikin mamaki ma’eeshat tace “har ka gama?”. Gyaɗa kai doctor yayi alamin “eh”. “Cikin 1 to 2 minutes fa, Anya dede kayimin?” Ma’eeshat ta tambaya tana dubawa. Murmushi doctor ya sake yi tare da cewa “ki duba in kikaga nayi badede ba sai ki nunamin in gyara miki”…………….. _page 44 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “aa bama sai na duba ba, na yarda da kai, amma Naga saurin ne kamar yayi yawa”. Sosai doctor ya sake zubawa ma’eeshat ido cike da kauna yace “tom yanzu de ki koma school zuwa anjima zan zo har gida”. Cikin shagwaɓa ma’eeshat tace “Aa korata kake nifa ban gaji da kai ba”. Wani shauƙi doctor ya sake ci ya rufe ko ina na jikin sa har zuwa zuciyar shi sannan yace “aa nima ban gaji da ganin ki ba eesha ta, amma kinga school ne nan karatu kike bai kamata nazo mu zauna muta hira, ba daɗi fa saurayi ya rinaga biyo budurwa sa har school ko wani waje in taje. Bai kamata ba, ya kamata ya ringa zuwa gidan su, anan zasu ringa haɗuwa ba ko wana waje ba, nima kawai so ne ya rufemin ido kuma ina so na koya miki topic ɗin ki gane, shi yasa nazo, amma daga yau ba lallai na sake zuwa school ɗin nan wajan ki ba in ba aure mu kai ba”. Ɗan haɗe rai ma’eeshat tai tare da cewa “to me kuma ya kawo wannan zancan doctor?”. Murmushi doctor yayi tare da girgiza kai cike da kulawa yace “aa eeshat na, kawai abinda ya dace nake gaya miki kamar ko da yaushe, daga sanda iyayan mutum suka tura shi makaranta to sun bashi amanar kan sa ne. Bawai suna nufin ya ringa zuwa duk inda yake so ba ko su ringa haɗuwa da wani saurayin, aa kawai makarantar nan suke sa ran yaje yayi karatu, akan haka abba da mami suke bari ki futo, kinji dear na”. Gyaɗa kai ma’eeshat tai tare da cewa “eh naji” kuma kin gane abinda nake nufi?” Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “eh na gane”. “Good yar albarka, allah yayi miki albarka eeshata” cikin dan jin kunya ma’eeshat ta sunkuyar da Kai tare da cewa “ameen doctor”. “Tom yanzu me kike so, kina bukatar ki siya wani abun na baki kuɗi?” doctor ya ƙarasa maganar yana ciro sababbin kudi yan dubu-dubu bandir guda, mai yawan gaske a gefan mota. Girgiza kai ma’eeshat tai tare da cewa “aa muna da kuɗi daga bana buƙata”. Mika mata kuɗin doctor yayi tare da cewa “gashi ki ɗauki ko nawa kike so yar baby”. Dariya ma’eeshat tai tare da cewa “aa ni ai sai dai a bani duka kuɗin”. “Oh duka kike so basu miki yawa ba kuwa?” Doctor ya faɗi hakan cike zaulaya. Da yake kuɗin za suyi kimanin 500k, daga banki doctor yaje ya ciro sabida yana bawa mabuƙata sadaka yawanci in ya shiga hospital. Yakan raba musu 20 20k ko 30 30k. “Aa basu min yawa ba, sunyi min kaɗan ma”. “Ah to zan je na samu abba nace masa ade na baki kuɗi da yawa haka, sabida ke baby ce sosai ba a bawa yara kuɗi fa”. Haɗe rai ma’eeshat tai tare da cewa “ba nace kar ka sake cemin yarinya ba?”. Dariya doctor yayi tare da cewa “allah ya wuce sarauniyar zuciyar doctor ashmal na dena”. Itama dariya ma’eeshat tai tare da cewa “tom na haƙur” “tom gashi tunda kince duka kuɗin za’a baki” doctor ya ƙarasa magabar yana ajiye kuɗin a gefan ma’eeshat. “Hmmm to wasa nake maka “im very show bani da bukatar kuɗi, kuma ko ina da buƙata ma kuɗin nan sunyi min yawa sosai”. “Tom shikenan amma gashi ki ɗauka, ko bakya karbar kuɗin mijinki ne?” Murmushi ma’eeshat tai tare da sa yatsun ta biyu akan damin kuɗin ta zari 1k a cike, cikin soyayya tace “mata tana godiya miji ya bata kuɗi”. Cikin so da ƙauna doctor yace “yauwa matar kirki damu me kike so na siyo miki, na kawo miki anjima?” “Hmmmm wannan mijin yana shagwaba matar sa sosai to matar bata son komai sai, soyayya da zumuɗin ganin mijinta anjima, fatan matar allah ya kawo mata mijinta lafiya bye sai kazo”. Daga haka ma’eeshat ta buɗe murfin mota domin fita. Doctor sabida tsabar soyayya da birgewa ji yayi kamar ya janyo ma’eeshat jikin sa yayi hugging ɗinta amma ba hali. Dan haka kawaii binta yayi da ido harta fuce yama kasa cewa komai kamar wanda aka rufewa baki. Ma’eeshat bayan ta fita rufe kofar tayi tare da tsayawa bakin murfin motar tana ɗagawa doctor hannu tana masa bye-bye, duk da kuwa ba ganin doctor ɗin take ba da yake glass ɗin motar baki ne wato black tinted. Doctor kuwa zuge glass ɗin yayi ya sakarwa ma’eeshat murmushi cike da kauna tare da dago mata hannu shima alamun byee. Sun dan jima suna kallon junan su cikin da murmushi da ƙauna, kafin ma’eeshat tai ƙarfin hali ta juya ta fara tafiya. Shima daga haka doctor ya zuge glass ɗin motar sa ya fara tafiya a motar sa, bayan ya hau kan titi gudu yasa cikin ƙwarewa da yake ana jiran sa kuma lokaci ya ja. Doctor yana cikin tafiya kamar ance ya juya gefe gaban kujerar, da ma’eeshat ta zauna. Yana juyawa ya hangi 1k ɗin da ma’eeshat ta zara a cikin bundle of money ɗin ashe bata tafi da ita ba a nan ta ajiye. Girgiza kai doctor yayi a fili yace “allah ka amince na mallake ta matsayin matata ta har abada wlh ina sonta”….. Lokacin da ma’eeshat taji alamun tafiyar motar doctor, bata juyo ba ta cigaba da tafiya kamar gaske. Sai da ta tabbatar motar doctor ta ɓace daga wajan sannan ta sake juyowa, ta nufi inda motar waleed take. Bayan ta ƙarasa daga tsaye ta dan russina tare da cewa “ya waleed ina kwana?”. Murmushi dole waleed yayi tare da cewa “lafiya ƙalau ma’eeshat ya school din?” “Wlh alhamdulillahi yaya waleed”. “Masha Allah ya angon naki ko shine yazo, amma shine baki haɗamu mun gaisa ba?”. Murmushi jin kunya ma’eeshat tai tare da cewa “shine yazo kuma na sha’afa amma kar ka damu kai da kake yayan amarya har gida zan zo ki gaisa”. Jinjina kai waleed yayi fuska sake yace “tom shikenan aishatu Allah ya kai mu”. Daga haka kuma ma’eeshat ta ja hannun meenal da take gaban motar waleed tare da cewa “to ni de gaskiya zan katse muku wannan soyayyar, meenal taso mu tafi”. Dan hararar ta waleed yayi tare da cewa “oh shine dalilin da ya kawo ki kenan”. Wata siririyar dariya ma’eeshat tai tare da cewa “aa mun kusan shiga lecture ne, amma bada niya nayi muku hakan ba”. “Hmmm shikenan ya na iya, amma ki dan bamu waje muyi sallama?”. “Okay ba damuwa bari na baku waje ayi sallamar soyayyah amma kar a daɗe pls” ma’eeshat ta faɗi hakan tare da sakin dariyar tsokana. Daga haka tabar wajan, ta koma can bayan motar waleed ɗin ta jingina tana tunanin magaganin da suke, ita da masoyinta doctor. Bayan ma’eeshat ta tafi tabar wajan, kallon meenal waleed yayi tare da cewa “yanzu sai yaushe dan Allah ki bari gobe nazo na sake ganinki”. Dan haɗe rai meenal tai tare da cewa “aa gaskiya ban yarda ba, nazo makaranta sai na ringa futowa ka bari bayan kwana biyu”. Jiki na rawa waleed yace “okay shikenan ba damuwa pls ki saki ranki naji Allah ya kai mu kwana biyun”. “Ameen” meenal tai faɗa a takaice. Waleed cikin marairaice murya yace! “Dan Allah meenal ki ringa ɗaukar wayata, in kina ɗaukar wayata inajin daɗi a zuciyata, amma in ina ta kiran ki bakya ɗauka sai naji kamar in mutu”. Cikin tausayawa meenal ta kalli waleed, duk yabi ya rame kana ganin sa za ka sheda yana cikin damuwa kamar mai jinya wanda bai dade da tashi daga rashin lafiya ba. “Kasan yanzu ina zuwa makarantar ne, karatu yayi min yawa, kuma gashi kasan sai ina taka tsam-tsam da umma, karta gane har yanzu muna tare. Yanzu number ka ma ba save na barta gudun dai kar umma ta fahimci muna tare, amma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin kullum munyi waya in, na samu free da kai na zan kiraka”. Cikin nauyin zuciya da karaya waleed yace “shikenan meenal nagode sosai pls ki ƙoƙarta, wallahi na rantse miki da Allah ina mutuwar sanki wanda ni kai na ban san adadin san da nake miki ba. Wani lokacin ma sai naji kamar na haƙura na rabu dake Saboda maganar iyayan ki amma na kasa meenal”. Waleed ya karasa maganar fuska cike da ƙwalla. Itama meenal ji take kamar ta zubarwa da waleed hawaye amma ta sai ta daure tana cewa “yanzu mene na kuka kuma, ka cigaba da addu’a kamar yarda nake yi, Allah yana sane damu in sha Allah komai zai zo karshe, zamuyi farin ciki nan gaba”. Ajiyar zuciya waleed yayi tare da cewa “hakane ne meenal ba abinda yafi karfin addua, kuma kullum ita nake yi, dan bazan iya bacci ba bana iyawa, Allah ya kawo maka ƙarshan lamarin nan”. “Ameen” to haka meenal tai ta lallaɓa waleed daga ƙarshe su Kai sallama da yake sunbar ma’eeshat a waje tana jiran su. Haka waleed yayi ta bin meenal da kallo har suka shiga cikin school ita da ma’eeshat. Bayan sun Kama hanyar tafiya meenal ce tace “ma’eeshat ina jin zuciya ta kamar ta buga duk sanda naga waleed a mawuyacin hali sanadiyar soyayya ta, sai naji kamar na aure shi ba tare da sanin kowa ba, kai ina jin a halin yanzu kamar na bawa waleed kai na, mu hutawa junan mu”. “Auzubillahi, meenal da bakin ki kike fadar hakan ke da kika tsani, aikata zunubi bare ƙazamin zunubi irin wannan, wannan fa zina kike tunanin kuyi ke da waleed”. Ido cike da hawaye meenal tace “to ma’eeshat ya zanyi Allah yana gani ni da waleed muna son junan mu amma gashi ana kokarin tauye mu. Ni fa na yarda ko mene halin waleed zan iya auran sa haka nan, wallahi waleed yana cikin matsanan ciyar damuwa, wanda ba mai fahimtar hakan sai ni dade da tashi shi, kinga ina tunanin in na bashi kai na, dole ƙarshe za’a haƙura a aura mana junan mu”. meenal ta karasa maganar tana zubar da zafafan hawaye. Cikin tausayawa ma’eeshat tace “kiyi haƙuri meenal in sha allah komai zai zo karshe”. “Nima ban San yarda zanyi ki mallaki waleed ba, ban san yarda zan tai maka miki ba, amma nasan allah zai temake ki, yana sane da komai. Amma meenal koda wasa kar ki sake gangancin tunanin aikata Abu makamancin zina ke fa mace ce mai daraja tarbi ga riƙo da haddini, me ya hadaki sa mumuna zunubi kamar zina? Kuma koda kin bashi kan ki, in kunyi aure wataran zai ringa kallanki da abin baze ga darajar ki ba. In sha Allah meenal har ki mutu ko da wasa ba zaki aikata wannan mumunan abun ba. Bi izzininlahi, mijin ki wanda aka muku auran sunna zaki bawa mutunci ki da darajar ki ta ‘ya mace, in sha allah ba zaki zubar da darajar ki a waje ba, ko da wasa. Nifa nan da kika ganni duk son da nake wa namiji ke ko doctor da nake mutuwar so bazan iya bashi kai na ba, in de ba aure mu kai ba wallahi be isa ba, bare ma nasan shima baze yi gigi ko gangancin hakan ba. Kema nasan zafin kaddara ce ta saki faɗin hakan dan wannan ba halin ki bane, ko na wasa ma……….. Kuyi followin channel na doctor ashmal dan samu sababan posting da zarar a ɗora. Mu haɗe a next page. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 45 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ido na zubar da hawaye meenal tace “hakane ma’eeshat amma ni ada ina tunanin in na bawa waleed kai na shikenan, dole za’a mana aure nasan ba namijin da zai iya aurata a hakan in de ba shi ba”. Girgiza kai ma’eeshat tai tare da cewa! “aa meenal bana so ki sake wata magana makamarciyar haka, kimin alkawari koda wasa ba zaki sake tunanin nan ba, wallahi meenal in de kika kuskura, kika aikata kuskure makamancin haka ko irin wannan bazan taɓ yafe miki ba har abada, duk da kuwa nasan wannan ba halinki bane sheɗan ne yake so ya shige ki, koda wasa nasan b zaki aikata abu makamanci haka ba, Sai de in fita kika kai daga hayyacin ki dan allah meenal kar ki bari imaninki ya fita daga gareki, ki fawwalawa Allah kinji?”. Meenal da tuni zuciyarta ta karye da magaganun ma’eeshat ido cike da hawaye tace! “In sha Allah ma’eeshat bazan taɓa aikata hakan ba, allah na tuba bazan bari sheɗan yayi galaba akaina ba in sha Allah zan cigaba da tsare mutunci na har abada, bazan sake Tunanin aikata mumunan abu makamancin zina ba”. Meenal ta ƙarasa maganar tana zubar daga zafafan hawaye. “Haba meenal ki dena kukan nan haka, komai zai zo ƙarshe kinji yar uwata?”. Gyaɗa kai meenal tai alamun to. Haka de ma’eeshat tai ta rarrashin meenal harta saki ranta. Bayan an tashi daga makaranta, driver yazo ya mayar da su gida, meenal ya fara saukewa a gannan kamar kullum, sannan ya wace da ma’eeshat……… To kwanci tashi ba wuya a wajan allah yau kimanin wata uku kenan da fara zuwa makarantar meenal. Meenal ta mai da hankali sosai tana karatu lokacin dasu momy suka samu labarin meenal ta fara karatu sunji daɗin haka sosai kuma momy tana kawowa umma da meenal ziyara ranar da ba school. Meenal yanzu son waleed da sauki hankalin ya fara karkata kan khaleed duk da kuwa har yanzu basu yaɓa haduwa ba kawai chat suke da waya. Amma duk alaƙar da take tsakanin khaleed da meenal umma bata sani ba ko kadan. Yanzu meenal da ma’eeshat sun fara shirya-shirya haɗuwa da khaleed. In mami ta fita sai meenal taje gidan su ma’eeshat ta haɗu da khaleed. Duk wannan shawarar ma’eeshat ce, da yake meenal, ta bawa ma’eeshat labarin khaleed ya takura mata sai sun haɗu, yanzu de suna nan suna faman shirya-shiryan haɗuwar khaleed da meenal a cikin satin nan. Amma de har yau meenal bata dena son waleed a zuciyarta ba, duk da tana ƙoƙarin cire san sa a zuciyarta ta kasa, Kawai de yanzu yana baya-baya da shi ne. Shima waleed ya dan dagawa meenal kafa sabuda tayi karatu sosai, duk da kuwa san meenal kullum karuwa yake a zuciyar waleed bai taɓa raguwa ko na minti daya ba. Muhseen dan fadeel Ɓangaran muhseen da fadeel kuwa har sun dawo daga saudiya, sun sake kyau matuƙa, kuma ba lefi sun sake nutsuwa har dady ya fara tunanin ko zai maida su can su cigaba da karatu su, sabida yaga sunfi nutsuwa sosai, bayan sun dawo daga makaranta sai muhseen ya tare shi da meenal ɗin, in an ɗaura musu aure. Ɓangaran doctor kuwa ya samu dady da magana akan auransa da ma’eeshat a matso da shi kusa. Dady ya amince amma yace ya bari karatun ma’eeshat ɗin ya dan ƙara nisa, sai ya samu abba da maganar, sabida yaga alama, abban ma’eeshat ɗin yana son karatun nata yayi nisa kafin auran……. Wannan kenan Yau ta kasance ranar Friday, kuma tun da wuri su meenal suka dawo, bayan sallah jumma’a. Misalin ƙarfe 2 suka dawo gida, ma’eeshat tacewa driver ya sauke su gaba ɗaya a gidan su meenal, da daddare ko gobe sai yazo ya ɗauketa. Ma’eeshat sai murna take sabida tun jiya tacewa meenal ta faɗawa umma dan allah yau tai musu dambu. Lokacin da suka shiga umma harta gama dambu tare da zoɓo me sanyi gaske. Nan da nan yawun ma’eeshat ya fara tsinkewa. Da ƙyar ma’eeshat ta yarda ta shiga toilet ta watsa ruwa. Dan da farko cewa tai itafa aa sai taci, za tai wanka. Meenal kuwa tace mata gwara su fara watsa ruwan daga bisani sai suci abinci, in yaso suna cin abinci kawaii kwanciya bacci za suyi su huta. Bayan ma’eeshat ta futo daga toilet itama meenal shiga tai, ta fara wanka bayan ta gama ta futo ƙirji ɗaure da towel. Lokacin da meenal ta futo daga toilet ɗin bata samu ma’eeshat a bedroom ɗin ba. Dan haka a hanzarce meenal ta saka bra da pants sannan ta saka doguwar riga wacce da kaɗan ta wuce guiwa me siririn hannu ta shan iska, daga haka ta fuce daga ɗakin. Tana nufar kicin ɗin, nan ta tarar da ma’eeshat ta ciko musu ture da dambu shinkafa wanda yaji zogale. Murmushi meenal tai tare da cewa “kai ma’eeshat kifa acici ce ta ajin farko, akan dambu duk wannan uban dambun”. Dariya ma’eeshat tai tare da cewa “ni gani nake yayi kadan ma, ko ni kaɗai zan iya cinye shi tasss”. “ to bari na barki kici sai na zuba wanda zan iya cinyewa”. “Aa muci tare sai nafi jin daɗi, in ban ƙoshi ba ai zan ƙara”. Ma’eeshat ta faɗa tana sake haɗiye yawu, kamar wata sabuwar mayya. Meenal girgiza kai tai ba tare da tace komai ba, daga haka ta ɗauki juk ɗin zoɓo wanda yasha kayan ƙamshi, da ƙanƙara sai turirin sanyi yake, daga haka tabi bayan ma’eeshat ɗin. Haka ma’eeshat da meenal suka koma ɗakin meenal, suka zauna, sannan suka fara cin abincin su. suna ci suna hira jefi-jefi, ba kowace hira suke ba face hirar khaleed. Haka suka ta hirar su har sukaci suka ƙoshi. Meenal de sai da ta tashi ta barwa ma’eeshat abinci sabida ta rigata ƙoshi. Itama ma’eeshat da ƙyar ta ƙarasa cin abinci sabida ƙoshin da tai. Bayan sun gamaci tashi ma’eeshat tai ta ƙwashe plate ɗin ta kai kicin. Bayan ta futo ta samu umma tana share tsakar gida, kafin ma’eeshat ta kai da cewa umma ta kawo tsintsiyar ta taya ta sharar, suka fara jin bugun ƙofa. “Umma bari naje na duba waye” cewar ma’eeshat. “Aa ma’eeshat meye haka, ji fa rigar jikin ki, me siririn hannu ba mayafi ba hijabi, zo ki ƙarasa sharar ni bari naje na duba” da yake kusan iri ɗaya ita da meenal suka saka riga, yawan ci meenal su take sawa, tana da irin rigunan da yake ita ba ma’abociyar san zafi bace. Kuma gashi gidan nasu ba mutane, itama haka ma’eeshat take kusan kullum ko a gida bata sa wasu manya kaya wataran daga ita sai singlet da gajeran wando take zama a bedroom ɗinta, haka mami take ta fama da yiwa ma’eeshat faɗa. Daga haka umma ta kama hanyar fita daga gidan domin, ganin waye yake bugu. Umma tana buɗewa ta saki fuska saka makwan ganin momy tsaya bakin ƙofa cikin sakin fuska umma tace “ashe Kice tafe, sannu da zuwa hajiya” umma ta ƙarasa maganar tana matsawa momy hanyar domin shigowa. Itama momy cikin farin ciki tace “wallahi kam kin ganni da tsakar rana tafe koh, zuwa nan nawa na yau mai mahimmanci ne”. Daga haka momy ta shigo ciki, umma rufe ƙofar tai tare da cewa “ah masha allah, allah yasa muji alkhairi bari mu shiga daga ciki. Daga haka umma da momy suka fara tafiya domin shiga ciki. Suna tafe umma tace “Kinga kuwa kinzo a sa’a dan surukarki ma’eeshat tana nan, yau gaki ga ‘yayanki biyu”. “Cikin farin ciki momy tace “ah masha allah Kice matar doctor tana nan yau, gaskiya naji daɗi dama na jima ban ganta ba”………… -Kar ku manya da reaction Kuma ayi following ɗin channel doctor ashmal dan samun posting da zarar a ɗora. Kuma ina yiwa masoyana masu following ɗin channel na doctor ashmal albumshir da cewa, zan fara gabatar musu da takaitaccan labari me daɗi bayan na doctor ashmal ko every weekend ne in bamu da posting, pls ku cigaba da yimin reaction na emojis dan nasan kuna tare dani bye. Mu haɗe a next page Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 46 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Ma’eeshat tana gama kwashe shara taji sallamar momy. Ma’eeshat bata gane murya momy ba, dan haka amsawa tai, tare da mikewa domin take nubi Dustbin domin zubarwa. Gaba ɗaya hankalin ma’eeshat baya kan momy dan haka, bama ta kalle ta ba kawai tace “ina wuni”. Kafin ma momy ta kai da ƙarasa amsawa ma’eeshat ta wuce wajan zubar da shara. Murmushi momy da umma su kai kafin umma tace “hmmm da dukkan alamu de surukar taki bata gane ki ba”. Murmuri momy tai tare da cewa “ina ai naga ko kallona ba tai ba, bare ta gane ni, hankalin nata baya nan”. Umma ce ta kalli ma’eeshat da ta dawo tare da cewa “ma’eeshat baki gane baƙuwar tamu bane?”. Fuska sake ma’eeshat ta ɗago tare da zubawa momy ido, kallo ɗaya ma’eeshat taiwa momy ta gane cewa, maman doctor ta ne. Ɗan tsorata ma’eeshat tai tare da zaro ido tana cewa “momy dama kece?”. “Uhmm nice, naga surukata ba dan kwali, kema baƙya san sa ɗan kwali ne?”. Ma’eeshat kallon jikinta tai, lokaci guda taji kunya ta rufeta, ga rigar da take jikinta kuma gashi ba ɗan kwali a kanta, duk da de kan nata ba kitso a tsafe yake tayi parking. Cikin jin kunya ma’eeshat ta rufe fuskarta tare da juyawa da sauri tana cewa “bari naje na ɗauko ɗan kwalin nawa”. Daga haka ma’eeshat ta ƙwasa a guje cikin jin kunya. Dariya umma tai a zuciyarta tana jinjina yarinta irin ta ma’eeshat “uhm lallai doctor raino zaiyi”. Momy ta faɗi hakan a zuciyarta tana sakin murmushi, zuciya cike da son surukarta ma’eeshat ɗin. Daga haka umma kallanta tai tare da cewa “mu shiga ciki koh, sai a kira miki yar taki meenal dan nasan wajanta kike zuwa ba waje na ba”. Murmushi momy tai tare da cewa “muje amma de yau ba takanas nazo wajanta ba, da akwai mahimiyar maganar da nazo muyi, dan da alhaji zamu zo to, shine fita ta taso masa bakatatan, dan haka yace kawai nazo daga baya yazo”. Bayan sun shiga palour, zama momy tai umma kuwa miƙewa tai tare da cewa “bari na kira miki meenal ku gaisa” daga haka umma ta fuce, bayan ta fita ta wuce bedroom ɗin meenal ta cewa meenal da ma’eeshat suje su gaisa da momy, bayan nan ta wuce kicin. Ta kwasowa momy ruwa jarka da lemo masu sanyi da marasa sanyi, bayan ta kai mata har abinci ta zuba mata a flask ta kai mata. Bayan umma ta gama kai mata ta mike dan ta ɗauko spoon da plate meenal da ma’eeshat suka shiga baki ɗauke da sallama. Momy cikin sakin fuska ta kalli su meenal ɗin. Ma’eeshat ta canza kayan jikinta zuwa atanfa da mayafi, ita kuma meenal ta zumbulo hijab har ɗasa yana ja kamar wata mai takaba, gaba ɗaya fuskarta babu annuri. Amma da taga momy ƙakalo murmushi dole tai tare da tsugunawa har ƙasa tana gai da momy. Fuska a sake momy ta amsa musu gaisuwar tasu ita da ma’eeshat. Daga haka tace “sannuku yaran kirki maza kuzu kusa dani ku zauna”. Ma’eeshat ƙarasawa, tai kan kujerar kusa da momy ta zauna, kamar yanda momy ta buƙaa. ita kuma meenal gefan ƙafar momy ta zauna a ƙasa. “Aa maza ki tashi bakiga yarda yar uwarki aisha tai ba, kema a kusa dani zaki zauna ba’a ƙasa ba” momy ta ƙarasa maganar tana ruƙo ma’eeshat da take kusa da ita, tana kwantar da ita a jiki. Meenal da ƙyar ta iya miƙewa ta zauna kusa da momy duk tabi ta tsargu, dan ita harga Allah tana jin kunyar momy sosai. Meenal nesa da momy ta zauna ta ɗayan ɓangaran, sai wani ɗari ɗari take. Hannu momy tasa ta ɗan ruƙo meenal tare da cewa “Ki matso mana aminatu, sai kace wata abar tsoranki ya kike hakane?”. Murmushi meenal tai ba tare da tace komai ba “Yauwa aisha haka nake so, ki saki jiki dani sosai kinji”. Momy ta ƙarasa maganar tana shafa kan ma’eeshat wanda ta kwantar da kan nata jikin momy. Cikin farin ciki da ƙaunar doctor ma’eeshat tace “ in sha Allah momy, ina yesmeen take?”. Murmushi momy tai tare da cewa “yesmeen tana school, amma ya kamata wataran tazo ta gai da ki”. “Aa momy ni sai nazo har gida ma ai”. “Aa ke da kike auntyta, ai ke yakamata tazo ta gaisar har gida”. Murmushi ma’eeshat tai ba tare da cewa komai ba. Momy lokaci guda ta fahimci wani abu tare dameenal da kuma ma’eeshat. Ta fahimci ma’eeshat tafi meenal saurin sabo da faranfaran. Ita kuma meenal tafi ma’eeshat shiru-shiru da jin kunyar mutane. Ruƙo su momy tai baki ɗayan su ta rungume su sannan tace “allah ya muku albarka ʼyayana, ya nuna min lokacin da zan kai ku ɗakunan ku”. Meenal sake sunkuyar da kai tai zuciya cike tatakaici. Sabuda bata so ama fara mata zancan wani aure in bada waleed ba, tun kafin ma meenal ta fara ganin muhseen ɗan gidan momy taji tayi mugun tsanarsa. Muryar momy ce ta katse meenal daga tunani da ta tafi inda take cewa “maza kuce ameen”. Ma’eeshat ce ta fara cewa ameen, cikin jin kunya haɗi da sunkuyar da kai. Ita kuwa meenal sake sunkuyar da kai tai batare da tace komai ba tana wasa da yan yatsunta. Murmushi momy tai tare da zubawa meenal ido tana cewa “aishatu tace ameen saura Amina”. Murya a sanyaye meenal tace “ai na faɗa a zuciyata”. Murmushi momy tai tare da cewa “aa nifa banyarda da wayan nan ba a fili nake so ki faɗa”. Ajiyar zuciya a hankula meenal ta sauƙe tare da cewa “ameen” cikin murya ƙasa-ƙasa. “Masha Allah, allah yayi muku albarka” nan ma ma’eeshat da meenal sake amsawa su kai da ameen. Daga haka umma ta dawo falo tare da ajiye cokula da plate ɗin data ɗauko a hanunta ta zauna a gefe, fuska a sake tace “ah kuna nan kina gaisawa da yaran naki?”. Murmushi momy tai tare da cewa “eh ai har mun gama gaisawa dasu, yan albarka ku tashi kuje in muka gama magana da umma sai ku dawo mu cigaba da hirar tamu ko?” A kusan tare meenal da ma’eeshat suka miƙe tare da cewa “tom sai anjima”. Daga haka suka fuce abinsu. Bayan sun futa shirune ya ziyarci wajan kafin momy tace “dama maganar auran meenal da muhseen ne ta kawo ni”. Umma Sai da taji gabanta ya ɗan faɗi kaɗan kafin tace “tom hajiya inaji”. Momy gyara zama tai kafin ta cigaba da magana da cewa “tom nida dady munga lokaci yana ta matsowa Kuma ɓangaran ku naga kamar kun sha’afa da lamarin yanzu fa saura 2 weeks lokaci yayi”. Wani gauran nunfashi umma taja kafin tace “hmmm hajiya ai kin san lokutan yanzu gudu suke yi, har lokaci ya matso ikon allah”. “Wallahi kam duniya gudu take umman amina”. Umma cikin danne damuwa tace “to allah yasa mu dace”. “Ameen umman amina, yanzu ya kike ganin za’ai” momy ta tambaya tana zubawa umma ido. Umma kuwa Jim tai na wasu daƙiƙu kafin tace “aa ni ai bani da abin cewa duk yarda kuka yanke dedene, tunda kuma iyayan meenal ne ai”. Jinjina kai momy tai tare da cewa “ƙwarai kuwa amina ʼyace a wajanmu, amma yanzu ni da dady mun yanke za’a ɗaura auran kamar yarda aka sa a baya, in lokacin yazo”. Umma cikin mamaki tace “nan da sati biyu kenan”. Murmushi momy tai tare da cewa “ah umman amina mamaki kike ne?”. “Eh mana dole nayi mamaki hajiya aure yazo bakatatan ba shiri”. Murmushi umma ta sakeyi tare da cewa “uhm gaskiya de nima inaga de ya kamata a ƙara ko one moth ne a kai”. Umma girgiza kai tai tare da cewa “aa ai wata ɗaya ma yayi wuri”. Momy tarar nunfashin umma tayi da cewa! “Aa beyi wuri ba, ki ƙwantar da hankaliki umma amina, auren kawai za’a ɗaura, amina wajena zata dawo da zama, ba yanzu za’a tare ba. Dan yanzu mijinta ma saudiya zai tafi ya ƙarasa karatu, sai ya dawo sai yasamu aiki daga nan sai su tare”. Umma har zuciyarta bataji daɗin hakan ba, a zuciyarta tana mamaki wannan wana kalar aure ne haka, amarya ba zata tare ba sai a gidan uwar miji, ita a barta da yarta mana su zauna har mijin ya dawo daga saudiya in ya gama karatun sai a tare, ita wannan kawai fin ƙarfi ne da kwacan yar za’ai mata. Momy ce ta dawo da umma daga dogon tunani da ta tafi da cewa “umman amina naji kinyi shiru ko baki amince da hakan ba?”. Ƙaƙalo murmushi dole umma tai tare da cewa “aa ai nace miki meenal yar kuce duk yarda ki kai dede ne”. Jinjina kai umma tai tare da cewa “shikenan nan da 2 weeks za’a kawo lefan amina, bayan an kawo lefe da one moth za’a ɗaura mata aure da muhseen in sha allah, hakan yayi koh?” “Umma da ƙyar ta daure ta iya cewa “allah ya kai mu, amma inaga abban ma’eeshat za’a samu tunda yanzu shine wakilin meenal kuma uba, duk yarda su kai da alhaji shikenan, sai su ƙarasa tsayar da magana”. Momy amshe zancan tai da cewa “eh hakane in sha allah yau da daddare ko gobe dady zai je wjanasa sai su kara tattaunawa………. My number 09162226240 Ina muƙa dubun godiya ga masoyana masu bibiyar littafin doctor ashmal, musamman ma masu following channel allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci ya saka muku da mafificin alkhairi. Mu haɗe a next page. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 47 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Dakewa umma tai, sannan ta jinjina kai tana cewa “tom shikenan hajiya allah yasa muji alkhairi” “Ameen ya rabbi” momy ta faɗa zuciya cike da farin ciki. Ajiyar zuciya umma tai cikin danne damuwarta tace “hajiya ga dumbu nan, kona zuba miki”. Fuska cike da nuna farin ciki momy tace “ah masha Allah kice dambu muka samu, bari zan zuba da kaina umman amina, kinsa ina son dambu, bana jin yunwa amma saboda ƙaunar da nakewa dambu zanci shi yanzu” momy ta ƙarasa maganar tana saukowa daga kan kujera. Dariya umma tai tare da cewa “Uhmm wallahi kin san ai dambu yana da farin jini ne, sabida abincin gargajiya ne”. Adede lokacin da momy take bude flasks ɗin dambun tace “eh gaskiya kam yana da farin jini barema na daɗe banci ba, har ina tunanin zan sa ladidi tayimin gobe ko jibi”. To haka umma da momy su kai ta hirar su jefi-jefi, har momy ta gama zuba dambun ta fara ci. Da umma taga momy ta fara cin dambu miƙewa tai tare da cewa momy bari taje ta dawo, duk sabida umma ta bawa momy waje ta iya cin abinci. Momy kuwa a hankula ta fara cin dambu zuciyarta cike da farin cikin lamarin auran muhseen da amina, sai kace shine yaronta na fari ko iri. wanda ya daɗe bai yi aure ba, kamar de doctor, dan yanda momy take farin cikin auran nan ko auran doctor batai farin cikin kamar haka ba. Duk sabida tausayin maraicin da momy takewa meenal, shi yasa take son haɗin. Momy ta ɗauki alwashin sai tasa meenal farin cikin sosai a rayuwarta, sai ta manta tayi rashin mahaifi. To haka momy tai tacin abinci tana tunani kala-kala. Harga allah momy taji daɗin dambun nan sosai nesa ba kusa ba, raban da taci dambu me daɗin irin na umma harta manta ma ita. Momy sai da ta cinye wanda ta zuba dukansa, dan badaban cikin momy ya cika ba sai ta ƙara cin dambun shinkafar. Bayan momy ta kammalaci ruwa ta tsiyaya a cup ta farasha. Momy tana cikin shan ruwan dady ya bugo mata waya. Sai da momy ta kammala shan ruwan sannan ta ɗauki wayar baki ɗauke da sallama. Daga can bangaran dady amsa sallamar yayi, bayan ya amsa sallamar momy cewa tai “dady ya aiki”. Hankali kwance dady yace “aiki alhamdulillahi, dama kinga bugo miki nai, naji ya ku kai da maman amina, ta amince ko yaya, gaba ɗaya hankalina yana kan maganar”. Murmushi jin daɗi momy tai tare da cewa “ alhamdulillahi maman amina ta amince amma kuma tace In ka samu time sai ka haɗu da abban aisha, ku ƙarasa maganar sabida shine wakili kuma uban wajan amina, in shima ya amince shikenan ba damuwa”. Cikin jin daɗi dady yace “masha Allah ba damuwa in sha allah kamar yarda ta buƙata zamu sanar da abban aisha, yau ma zanje mu haɗu, in na tashi daga office”. To daga haka momy da dady suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har sai da momy taga umna ta dawo sannan su kai sallama da dady. Bayan momy ta katse wayar kallan umma tai tare da cewa “ina ta jiranki shiru, nace wataƙila kin faɗa wani aikin”. “Eh har kin kammala kenan, wallahi kam kin san aikin gidan ne baya ƙarewa”. “Wallahi kam baya ƙarewa, tun dazuma na kammala, yanzu nake ƙoƙarin tashi na tafi ma” momy ta ƙarasa maganar tana zura wayarta a jaka. “Ah yanzu zaki tafi ai da kin bari sai anjima kun sake gaisawa da yayan naki”. “Wallahi kam dan ina son nayi hira da surukan nawa, amma kin san lokutan yanzu gudu suke yi, yanzu za kiga an fara kiran salla magriba ga driver na jirana a waje, amma a sake kiramin ʼyayan nawa muyi sallama da su”. Mikewa umma tayi tare da cewa “hakane lokutan gudu sukeyi wlh, amma bari na kira miki su kuyi sallama” daga haka umma ta fuce daga palour. Amma bata jima da futa ba sai ga su meenal da ma’eeshat sun dawo wajan momy. Mikewa momy tai cikin sakin fuska tace “Yauwa ƴayana yan albarka zan tafi kuzo ku raka ni hanya”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “to momy har zaki tafi da wuri haka dama kin bari sai bayan magriba ai”. Dariya momy tai tare da cewa “aa bayan magriba kuma aishatu, ai yesmeen kuka za tai tayi, in ta dawo bata ganni ba”. Dariya ma’eeshat tai tare da cewa “haba momy kuka kuma, sai kace yarinya ko yar baby”. “Ah ai yesmeen tafi ƴar baby rigima aishatu, ko da yake yarinyarce itama 13 to 14 take fa, girman jiki ne kawai”. “Ah momy 13 to 14 fa, da ni nayi tunani in bata girme ni ba za muyi sa’anni”. “Ah ina aishatu ai kin girmeta nesa ba kusa ba, girman jiki ne kawai duk da bansan age ɗin ki ba, ke da amina waye babba ne?”. Momy ta tambaya tana kallon amina wanda take faman sunkuyar da kai, kamar sabuwar amarya”. Cikin jin daɗi ma’eeshat tace “momy ai duk sa’anni ne nida ma’eeshat 17 muke, tazarar mu 2 weeks ne fa”. “Ah masha allah, Kice duk age ɗinku ɗaya to allah yayi muku albarka yarin kirki”. Sai a lokacin meenal ta buɗe baki tace ameen a hankula, har suna haɗa baki ita da ma’eeshat wajan cewa “ameen”. Daga haka momy cewa tai “aishatu ɗauko ruwa ko lemon mu tafarwa da driver nasan yana can yana jira, maybe yana jin ƙishirwa”. Ba musu ma’eeshat ta durƙusa ta ɗauki lemo da ruwa masu sanyi” daga haka ta miƙawa meenal lemon ƙwali ita kuma ta riƙe bottle ɗin ruwan. Daga haka momy da umma su kayi sallama, ita kuma ma’eeshat da meenal suka bi bayan momy domin rakata bakin mota kamar yarda momy ta buƙata. Umma har bakin ƙofa ta raka momy sannan ta juya ta koma gida. Meenal da ma’eeshat haka suke tafiya biye da momy har suka ƙarasa bakin motar. Koda suka karasa, ma’eeshat ce ta karɓi lemon hannun meenal sanan ta miƙawa driver momy. Driver kuwa ba musu ya karɓa hadi da cewa “Yauwa nagode”. Bayan haka momy ta shiga bayan mota bayan ta, shi ta sake yiwa su meenal addu’o’i, tare dayi musu sallama, suka wuce gidan, ita kuma driver yaja motar su kabar wajan. Suna cikin tafiya ma’eeshat ta kalli meenal tare da cewa “meenal ya kikaga momy doctor tana da kirki koh?”. Gyaɗa kai meenal tai tare da cewa, sosai ma, mutunci ba kaɗan ba ai mutuniyar arzikice sosai”. “Wallahi kam ke de bari shima haka doctor yake, yana da kirki sosai ya kwaso halin momy, kuma ina da taabbaci in sha allah haka ƙanin Doctor yake da kirki mijin da zaki aura”. Meenal haɗe rai tai tare da taɓe fuska tana cewa “kai ma’eeshat nifa bana son wannan auran fa, kima dena haɗani da auran wannan, in sha allah waleed zan aura in kuma bashi ba na auri khaleefa”. Jim ma’eeshat tai kafin tace “tom shikenan meenal allah ya zaɓa miki abinda yafi alkhairi” a takaice meenal tace “ameen”. Bayan sun koma ciki direct falo suka nufa suka zauna. Itama umma tana zaune tayi jigum. meenal tana gani fuskar umma, tasan da akwai abinda yake damun umma amma sai tayi shiru, ba tare data tambayeta ba. Meenal zuciya cike da tunani ta cire hijab ɗin jikinta. Umma kuwa gyara zama tai tare da cewa “meenal kin san me yake faruwa?” Gaban meenal ne ya dan faɗi rasss, duk da bata san mai umma zata ce ba. dakewar meenal sannan ta kalli ma’eeshat wanda ta zubawa umma ido kamar sunanta umma ta kira. Meenal daurwa tai tare da cewa “aa umma sai kin fada”. Ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa “akan maganar auran ki da yaron momy muhseen ne”. Meenal a fili tace “Innalillahi maganar aurena kuma me tace umma?”. Cikin danne damuwa umma tace “mene kuma na Innalillahi meenal?”. Shiru meenal tai ba tare da tace komai ba. Ma’eeshat kuma tsomo baki tai da cewa “umma ki mana bayani me yake faruwa?”. Umma kallon meenal ta sakeyi tare da cewa “momy tace nan da sati biyu za’a kawo lefan auran meenal, kuma bayan an kawo wata ɗaya za’a saka lokacin ɗaura aure……….. Mu hade a next page dan jin yarda zata kaya. Game buƙatar littafin doctor ashmal daga farko har inda aka tsaya, yayimin magana ta private 09162226240 in sha Allah zan tura masa, in yayi following ɗin channel bai samu ba bye… Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 48 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Wani yawun tashin hankali me zafi da ɗaci meenal ta haɗiye, baki na rawa tace “umma me kikace kin amince kuma?”. “Hmmm meenal bani da abin cewa, amma in baki manta ba haka aka sa lokacin auranki lokacin da akai engagement a hakan ma an ƙara wata ɗaya ai”. Cikin rashin annurin fuska meenal ta sake cewa “aa umma ni so nake naji kin amince ko aa”. Jim umma tai na wasu dakiƙu kafin tace “eh meenal na amince amma nace su samu abban ma’eeshat su ƙarasa zancan”. “Innalillahi’wainna’ilhai’hirraji’un umma kin amince fa kikace” meenal ta ƙarasa maganar tana fashewa da wani gigitaccan kuka mai ban tausayi. Cikin dauriya umma tace “meenal ya kike so nayi ne, tun farko fa kin san da zancan nan har kin amince”. Cikin kuka meenal tace “amma wallahi umma ba’a san raina na amince ba”. “Meenal nima ban san yarda zanyi ba gaskiya, bazan iya cewa hajiya aa ba mutanan arziki ne sosai, kuma hasalima ba ɗan mafiya za’a aura miki ba ko ɗan iska kode wani mara kyan hali da zaki ɗaga hankalin ki ba! Ko kuma kina da wanda kike so ne bayan waleed, kuma sani kan kine, baban ki kafin ya rasu ya bani wasiya ya baki kuma ya bawa alhaji, akan kar a sake a aura miki waleed, hakan ne ma yasa alhaji da hajiya suka miƙe tsaye wajan ganin sun aura miki ɗan su”. Meenal kuwa sake fashewa tai fa kuka sosai, wanda kowa yana iya jin sautin kukan nata. Ma’eeshat kuwa rafka tagumi tai zuciya cike da tausayawa ƙawarta ma’eeshat dan harga allah bata so taga ma’eeshat cikin damuwa. Umma kuwa cigaba da magana tayi da cewa “meenal ina da yaƙini akan, ba zaki taɓa ladama ba, in de kika bi zaɓin iyayanki. Meenal kullum bana bacci tun kafin ki kai haka nake roko allah ya haɗaki da miji na gari, tabbas na sheda kuma ina kyautata zaton allah baze, taɓa zaɓa miki wanda bai dace ba. Kuma har yanzu akwai lokaci, tunda ba’a daura miki auran ba, koda yaushe ƙaddara zata iya canzawa, ki cigaba da addu’a kawai allah ya futo miki da mafita, ta alkhairi, meenal karki ɗorawa kan ki ciwan zuciya ki miƙawa allah lamarinki kamar yarda nai”. Umma ta ƙarasa maganar kamar za tai kuka. Daga haka umma miƙewa tai ta fuce tabar ɗakin, zuciya cike da tausayawa meenal. Sai da meenal tayi kukan baƙin ciki mai isarta sosai sannan ma’eeshat ta fara rarrashinta. Daga haka zazzaɓi mai zafi gaske da ciwan kai suka luluɓe meenal. Hankalin ma’eeshat ya sake tashi ainun ganin yarda lokaci guda meenal ta zube ta kwanta, duk da kuwa ba yau ma’eeshat ta saba ganin haka a tattare da meenal ba. Dama haka meenal take, in de ta shiga cikin tashin hankali, lokaci guda cuta take rufe ta, saboda meenal bata iya riƙe damuwa a ranta ba. Ma’eeshat ta fara tunanin kota sanar da doctor halin da ake cike ne akan meenal bata san auran da za ai mata da kanin sa muhseen, ko zai iya sanarda su momy. Haka ma’eeshat ta fara tunanin nan, duk da tana tsoron tunkarar doctor da irin maganar nan amma, ta yanke shawarar sai ta sanar da shi ko allah zai sa, a samu mafita, dan ma’eeshat ba zata iya jure ganin yar uwarta meenal cikin tashin hankali ba…….. Dady Kamar yarda dady ya sanar da momy haka kuwa akai bayan ya taso daga office direct gidan su ma’eeshat ya nufa domin haɗuwa da abban ma’eeshat. Da yake ya buga masa yace in yana gida zai zo suyi mahimmiyar magana, in ya futo daga office. Dady yaga tarbar alfarma sosai wajan abba yarda kasan ya goya shi abayansa, ga girke-girke kala-kala yasa ai masa. Dady kuwa yaji daɗin ganin yarda abba yake karrama shi kuma yake bashi respect a matsayinsa na gaba da shi. To bayan abba da dadyn sun gaisa sun ɗanyi hirar su ta rayuwa kafin dady ya fara magana kamar haka. “To ka ganni bakatatan ko, zuwa basa rana, wallahi abun ne yana da mahimmanci, shine nake so mu haɗu muntattauna”. Murmushi abba yayi cikin girmamawa yace “ah haba ba komai alhaji, ai duk lokacin da kake son mu haɗu zamu iya haduwa, in ta kama, ma ni zanzo har gida na same ka, ba sai kasha wahalaba”. Jinjina kai dady yayi tare da cewa “aa mene abun wahala dan nazo, daga office ma na tawo nan badaga gida ba wlh, dama magana ce akan auran yaron wajena muhseen da kuma yarka amina” jinjina kai abba yayi tare da cewa “okay masha allah na’am”. Dady cigaba da magana yayi da cewa “kasan Lokacin da aka kawo kuɗin sarana ansa wata uku” jinina kai abba yayi tare da cewa “hakane ranka yadade” dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa “to yanzu lokaci ya matso ya zamana a kwanakin da mukasa bai fi 2 week ba. Hakan ne yasa nida mai ɗakina muka yanke shawarar ɗaura auran kamar yarda akasa bamu ɗaga ba” abba jinjina kai yayi cikin gamsuwa alamun yana fahimtar zancan. Dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa “hakan ne yasa mai ɗakina taje ta samu mahaifiyar yarinyar! Kuma ta sanar da ita, akan shawarar da muka yanke, sannan kuma ta tambayeta akan ra’ayinta, kuma ba ɓata lokaci mahaifiyar yarinyar ta amince da hakan, amma tace kafin a aiwatar da komai, ni da kai mu zauna, mu sake tattaunawa akan maganar, tunda a yanzu kai ne a matsayin uba kuma wakili a wajan yarinyar”. Daga haka dady yayi jim, kafin ya cigaba da maganar abba yace “ ah masha Allah, alhamdulillahi hakan yayi kyau sosai, kuma ina farin ciki da wannan abu, amma kuma baka ganin kamar ansa lokacin auran da wuri haka, saboda su mata kasan su da shagali, ga taro kala-kala dan haka ya kamata a zauna a tsara komai”. “Eh hakane, amma ai a halin yanzu ɗaura auran kawai za’ai daga baya in zasu tare, duk shagalin da yakamata sai ayi in sha Allah”. Cikin mamaki abba yace “okay dama ba tarewa za tai ba, in an ɗaura auran sai nan da yaushe kenan?”. Jinjina kai dady yayi tare da cewa “hakane ba ana ɗaura auran, zasu tare ba, sabida mijin nata ma nan da one week zai koma saudiya ya ƙarasa karatunsa, sai nan da one years zasu dawo in sha allah sai su tare”. Abba gyara zama yayi tare da cewa “hakan yayi kyau ranka ya daɗe, amma wani hanzarri ba gudu ba sai nake ganin kamar, hakan za’a ƙwari yaran namu, ayi aure ba’a tare ba kuma, ko za’a bari sai ya ƙarasa karatu sai ayi bikin gaba ɗaya su tare, musamman ita amina sai tai ta zama da aure kuma a gidan su hakan kamar ba daɗi”. Jinjina kai dady yayi tare da cewa “gaskiya ne zancanka, kuma duba da hakan ne ma yasa, me ɗakina tace, in anyi auran za’a kawo mata amina wajanta, su cigaba da zama da ita tana cigaba da karatun nata, har lokaci yayi”. Jinjina kai abba yayi tare da cewa “gaskiya ne inaga haka sai yafi, in de kana ganin ba wata matsala, amina zata zauna lafiya kuma ta sake a can shikenan ba damuwa” cikin sakin fuska dady yace “in sha Allah hakan ba matsala, saboda ma, mahaifiyar yaran, tana ƙaunar amina hakan ne yasa ma tace zasu zauna tare”. Abba ya gamsu da zance dady amma da aso samun sane, ana auran a tare sai yafi. Dady kuwa kamar ya shiga zuciyar abba yace “amma dalilin da yasa kaga muna so ayi auran nan kusa, kamar mun dage shine “akan wannan yaron ne waleed wanda mahaifin yarinyar baya so ta aura! Kasan yaran yanzu, in suna soyayya basa so su rabu, in zasu rabu ko aka raba su, ba abinda baza su iya aikatawa ba, shi yasa muke so, ayiwa tufkar hanci, tunda har mahaifin amina yabada wasiya akan, ko bayan ransa kar’a aurawa amina yaro, to kaga yanzu in aka bar yarinya haka, zaune ba aure zasu cigaba da soyaya ne! Kuma allah ne kaɗai yasan abinda zai iya faruwa, amma yanzu in aka ɗaura mata aure nasan a matsayinta na mai nutsuwa da ilimin addini dole zata nisanta kanta da shi, kuma ta manta da shi”. Cikin gamsuwa da jin daɗin jawabin dady, abba yace!. “Gaskiya ne ranka ya daɗe kunyi tunani me kyau, allah ya temaka ya bada zaman lafiya, allah yasa anyi a sa’a, kuma yasa hakan ne yafi alkhairi”. Duk da abba yasan waleed kamar ɗa yake a wajansa, ɗan uwan ma’eeshat ne kuma ɗan matar sa mami ne, tunda dan yayar mami ne, amma in de ta tabbata bashi da ƙyan hali baze so haɗa su aure da meenal ba. sabuda meenal yana sonta kamar yarda yake son ma’eeshat. Maganar dady ce ta dawo da abba daga gajeran tunanin daya tafi in da yake cewa “Sai kuma maganar ɗanka kuma surikinka doctor, yana so akan nazo na sameka tun ƙwanakin baya, akan a rage kwanakin auran su da aisha, kuma gashi bamu haɗu ba, sai yanzu yau, dady ya ƙarasa maganar yana dariyar su ta manya…………… Please mutanan amana ku ringa sharing, kuma ku ringa react, kwana biyu, bakwa gigitani da like gaskiya, musamman mutanan arzikina ƴan channel ɗina kunyi sanyi, pls karki bani kunya mana, ko so kuke ƴan group suji kan mu.😂😂😂 Inayiwa masoyan doctor ashmal baki ɗanku, fatan alkhairi allah yabar ƙauna. Mu haɗe a next page bye 👋🏽. Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 49 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 To nataƙaicewa masu karatun littafin doctor ashmal zance dady bai bar gidan su ma’eeshat ba sai da dady da abba suka rage lokacin auran ma’eeshat da doctor ashmal suka mai da shi wata 4 madadin da, da yake wajan saura 7 to 8 moth. Bayan an ɗaurawa meenal aura da 3 moth itama ma’eeshat za’a ɗaura mata aure da doctor tare. Ma’eeshat Bayan ma’eeshat ta dawo gida rai ba daɗi ta wuce ɗakinta tai wanka sannan ta canza kaya. Zama tai akan bed tana tunani iri-iri, tunani take ta ina zata fara sanar da doctor wannan maganar ta meenal, akan meenal bata son dan uwan sa muhseen. Ma’eeshat tana ɗan jin tsoran haka amma in ta tuna meenal tana cikin damuwa sai taji zata iya. Adede lokacin mami ta shigo ta tarar da ma’eeshat a zaune tayi jigum. Sallamar mami ce ta dawo da ma’eeshat daga dogon tunanin data tafi. Bayan ma’eeshat ta amsa sallamar mami ƙarasowa tai kusa da ita ta zauna, tare da cewa “ma’eeshat lafiya naganki kinyi jigum?”. Murmushi dole ma’eeshat ta ƙaƙalo tare da cewa “hmmm mami kedai bari, wai zancan auran meenal ne da ƙanin doctor kuma kin san ita bata so, gashi yanzu wai nan da!!” Mami ce ta katse zance da cewa “aa ma’eeshat yi shirinki naji komai yanzu dady doctor yabar gidan nan”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “haba mami me ya kawo shi?”. “Zancan auran meenal da ƙanin doctor ne, kuma nan da one moth za’a ɗaura auran, sai ta cigaba da zama gidan su doctor har mijin ya gama karatun sa, sai su tare”. Jiki a sanyaye ma’eeshat tace “eh Momi wlh nima haka naji amma harga allah bana son auran nan wlh itama meenal bata so”. “Aa ma’eeshat ki dena faɗin hakan, a matsayin ki na yar uwa kuma ƙawa aminiyar meenal da addu’a zaki ringa tayata Kawai akan allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi”. Gyaɗa kai ma’eeshat tai tare da cewa “ameen”. Mami ƙara cewa tai “kuma dady doctor da abba sun rage lokacin auran ku, ke da doctor, nan da 4 months za ai bikin naku”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “ mami da gaske?” Cikin tsananin farin ciki ma’eeshat ta faɗin hakan. Ɗan hararta umma tai tare da cewa “to da ƙarya zan miki?”. Ma’eeshat Tana ƙoƙarin magana tajinwayarta ta fara ringing, kallo wayar tai domin ganin wane yake kıra. Ma’eeshat tana ganin sunan ta sauke ajiyar zuciya saboda tun dazu kiran nasa take jira. Kallon mami tai tare da cewa doctor ya kirani bari na ɗauka” jinjina kai mami tai tare da cewa “okay sai da safe gobe, maƙarasa maganar” daga haka umma ta miƙe domin fita daga ɗakin. Ma’eeshat kuwa hannu na rawa ta ɗauki wayar baki ciki da sallama. Bayan sun gama gaisawa cikin mamaki doctor yace “eeshata naga muryarki ta canza kamar wani abun yana damunki?”. Girgiza kai ma’eeshat tai tare da cewa “aa dear ba komai” jinjina kai doctor yayi tare da cewa “okay yayi kyau ya school ɗin?”. “Alhamdulillahi” doctor sake cewa yayi “okay ana karatu da kyau de ko?” Jinjina kai ma’eeshat tai tare da cewa sosai ma” “Yauwa eeshata haka nake so, kıta mai da hankali kinji”. “Jinjina kai ma’eeshat tai tare da cewa in sha allah”. Daga haka shiru ya ziyarci wajan na wasu lokutan kafin ma’eeshat tace “kasan menene?” Kamar ma’eeshat tana gaban doctor, doctor ya girgiza kai tare da cewa “aa sai kin faɗa”. Shiru ma’eeshat kafin tace “dama Uhmm ina so na gayama wani abu ne”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “eeshata ina jinki ki gayamin mana, sai wani noƙe-noƙe kike”. Ajiyar zuciya ma’eeshat ta sauke tare da cewa “akan zance auran su meenal ne”. Doctor gajeran tunani ya tafi akan zanca auran data faɗa. Ma’eeshat kuwa cigaba da magaa tai da cewa “doctor nasan zaka fahimce ni meenal ta shiga cikin damuwa sosai, saboda zancan auran nan, kuma su momy basu fahimci hakan ba”. Doctor kuwa tuni ya tafi duniyar tunani dan shi be ma san inda maganar ma’eeshat ɗin ta dosa ba. To shide yasan meenal ƙawar ma’eeshat ce, shine abinda ya iya ganewa kawai, sai kuma zancan meenal bata san aure, shi hasalima bai san za’a yiwa meenal aure ba, ma’eeshat bata taba bashi labarin za’ai bikinta ƙawaeta meenal ba, sannan yana tunanin saboda me sunan momy ya futo cikin maganar nan. Ataƙaice de doctor bai masan da zancan auran meenal da ƙaninsa muhseen ba, koda wasa bai taɓa jin maganar wajan su momy da dady ba, shi yasa maganar ma’eeshat ta raba masa hankali gida biyu. Ma’eeshat ƙara magana tai da cewa “doctor naji kayi shiru kana jina”. Cikin mamaki doctor yace “inajinka amma, maganar takice gaba ɗaya, ban gane inda ta dosa ba, yaushe kuma za ai auran ƙawar taki baki gayamin ba, kuma menene haɗin auran ƙawarki da momy, gaba ɗaya na kasa ganewa fa”. Jim ma’eeshat tai nan ta fara tunanin Anya doctor yasan da zancan auran meenal da muhseen kuwa? “Kai gaskiya doctor bai San da zancan auran meenal da muhseen ba, Innalillahi zance na saki baki zan ɓallo ruwa, na tona asiri, ƙilama su momy ɓoyewa doctor zancan suke yi”. Duk a cikin zuciyarta ma’eeshat take faɗin wannan zancan. Ma’eeshat tana cikin tunanin nan taji muryar doctor yana cewa “naji kinyi shiru ki yimin bayani, na kasa gane maganrki, ki yimin bayani yarda zan gane mana eeshata”. Gaban ma’eeshat sake faɗuwa yayi rasss tana tunanin, shikenan ta shiga uku zata tona asiri ashe doctor bai sani ba. Amma sai tai ta maza ta ƙaƙalo murmushi cikin yanayin kawar da zancan tace “kasan menene kuwa?” Cikin mamaki doctor yace “aa ma’eeshat inajinki, ki faɗamin mana”. Murmushi ta sake ƙaƙalowa tare da cewa “kasan menene kuwa” shima doctor cikin zumuɗi fuska cike da murmushi yace “no sai kin faɗa”. “Albishirin ka” cikin mamaki doctor yace “goro” ma’eeshat murmushi dole sai tare da cewa “fari ko baƙi”. Wata siririyar dariya doctor ya saki tare da cewa “an gaishe ki eeshata, bama ja da fari ba, baki da fari ko, to wa yake son bakin in banda abinda na zaɓi farin”. “Tom shikenan dole ka bani tukuccin albishir ɗina fa” ma’eeshat ta faɗi haka zuciya cike da jimamin ɓaranɓaramar da tai. Sosai ma zan miki tukuci babba in de albishir ɗin me kyau ne. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “dama haka zance yau dady yazo gidan mu wajan abba” doctor cewa yayi “uhm” alamun yana sauraranta, ma’eeshat kuwa cigaba da maga tayi da cewa! “Kuma an rage lokacin bikin mu an mai da shi 4 moths” wani ɗan murmushi doctor ya saki wanda bai kai har zuciya ba, sabida ko kadan baiyi tunanin ma’eeshat da gaske take ba yayi tunanin wasa take. Cikin rashin gamsuwa doctor yace “aa eeshata naƙi wannan wasan naki”. Ɗan yamutsa fuska ma’eeshat tai tare da cewa “haba doctor kasan bazan maka irin wasan nan ba, kuma harda abba da dady a ciki wallahi am serious nima yanzu mami take faɗamin fa”. Lokaci guda doctor yaji farin ciki ya luluɓe shi sosai. Da ƙyar ya iya control ɗin kansa tare da furta “alhamdulillahi allah nagode ma, gaskiya eeshata naji daɗi sosai da sosai, dama kullum inatason a rage mana lokacin auran nan namu, gaskiya kam naji daɗi sosai”. Murmushi ma’eeshat tai tare da cewa “to meye naji daɗin?”. Murmushi sosai doctor yayi mai cike da tarun fassarori tare da cewa “uhmmmm” daga haka bai ce komai ba yayi shiru yana ta sakin murmushi mara sauti wanda ma’eeshat bata isa taji shi ba, daga shi sai shi”. To daga haka hira ta tsinke tsakanin doctor da ma’eeshat, ma’eeshat sai da ta wayantar da zance sosai, shi kuma doctor farin ciki ma ya hana shi sake tambayar ma’eeshat akan zancan data fara masa, na auran meenal. Kuma saboda farin ciki doctor sai da ya ƙudurta a zuciyarsa sai yayi azumi uku na godewa uban giji, saboda matso da auran nan nasu da akai, shi da ma’eeshat nan kusa-kusa. MEENAL To ɓangaran meenal kuwa tana nan cikin ɓakin ciki, kullum umma rarrashin ta takeyi. Meenal ta kashe wayarta gaba ɗaya, saboda bata san takura, daga waleed har khaleed duk ta watsar da su gefe tana fuskartar damuwar da take ciki. Kullum umma cikin rarrashi da ban baki take, bama iya umma ba harda ma’eeshat. Meenal kullum cikin tunani da damuwa take, ko taje school ɗin ma hankalin ta atashe yake bata iya gane komai sai tunani. To ana cikin haka sati ya zagayo, kuma kamar yarda su momy sukace nan da one week za’a kawo lefan meenal haka kuwa akayi, rabar friday aka kawo lefan meenal gidan su ma’eeshat, su dady ne suka kawo da sauran magabata. Ɓangaran meenal kuwa bama ta san, za’a kawo lefe ba, tama sha’afa, dan ita har lokacin tana ganin lamarin kamar wasa-wasa. saboda haka ma, ba wanda ya gaya mata, ma’eeshat tasan ranar za’a kawo lefan meenal gidan su. amma bata faɗa ba mata ba, saboda, tasan meemal zata shiga cikin tashin hankali. Kuma ma’eeshat bata san taga meenal cikin damuwa. Dan haka su mami ne suka gama shirya-shiryan su aka karbi lefan a gidan. Mu haɗe a next page bye…… Game buƙatar littafin doctor ashmal tun daga farko har zuwa inda aka tsaya ga link ɗin channel yayi fallowing. 👇👇👇👇👇 https://whatsapp.com/channel/0029VavMxrsKbYMKEPbyoR0d Game ɓuƙatar cigaba da karanta littafin doctor ashmal da comment, akan littafin bayan ya karanta, dama wasu sauran sababbin littattafan novel ga link din WhatsApp group yayi joining 👇👇👇👇👇 https://chat.whatsapp.com/K5evfhIkkVw9kD7pYCLKKc _page 50 ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Tsayawa gayawa masu karatun littafin doctor ashmal tsaruwar lefan meenal ɓata page ne. Saboda lefe yayi lefe iya lefe, sai da aka kawowa meenal akwati set 4 wato akwati 48 banda sauran basket. Ita kanta ma’eeshat sai da taji inama ita aka kawowa lefan meenal ɗin. Bayan masu kawo lefan meenal sun tafi, ba jimawa mami tasa motocin gidan suka kwashi lefan, zuwa gidan su meenal. Dan mami da ma’eeshat ma basu buɗe kayan ba, mami tace abari, in ankai gidan su meenal sai a buɗe su gani a can. Bayan kuma an gama gani sai a rufe a dawo da shi gidan su ma’eeshat ɗin a ajiye mata har Lokacin da zata tare a gidan ta. Haka motoci suka rankaya har zuwa kofar gidan su meenal. Bayan an ƙarasa mami da ma’eeshat suka fara biga ƙofar gidan umma tana buɗewa, drivers ɗin suka fara shiga da lefan ciki. Time ɗin kuwa meenal tana ɗaki tana baccin wahala da tunani wanda ya kwasheta ba jimawa. Bayan an gama shigo da lefan, mami cewa tai ba za’a buɗe ba, sai an taso meenal, an buɗe kayan nata a gabanta. Umma kuwa ba musu ta miƙe domin kirawo meenal kamar yarda umma ta buƙata. Ita kuwa ma’eeshat batai gigin tashin meenal ba, zaman ta tai a gefan mami, saboda tasan mennal ba zatai farin ciki da hakan ba. Lokacin da aka taso meenal tana futowa tsakar gida tayi turus, saboda ganin iyayan akwatina kota, wanda ta kasa irgasu cikin kallo ɗaya. Gaba ɗaya lissafin kan meenal ya kwance, tama manta da wani lefanta da za’a kawo a kwanakin nan, ta tafi tunanin wannan uban kayan na wane. Muryar mami meenal taji tana cewa “yarta meenal, maza ki ƙaraso muga kayan naki, yar albarka masha allah, duk da bamu buɗe kayan ba, amma mun tabbata kinyi goshi allah ya sanya alkhairi yar albarka maza ki karaso a buɗe a gaban ki”. Mami ta ƙarasa maganar fuska cike da murmushi. Mamaki ne ya bayyana a fuskar meenal cikin mamaki meenal tace “mami naji kina cewa kayana kuma, wannan kayan daga ina”?. Murmushi mami tai tare da cewa “eh mana kayan ki ne na lefe”. Cikin mamaki meenal tace “lefe na kuma mami, dama umma da gaske wai bikin nan za ayi ne?”. Murmushi mami tai tare da miƙewa ta janyo hannun meenal tana cewa “maza ɗiyata yar albarka taho muje, karki furta komai, bana son kice komai in de ba godewa Allah ba”. Meenal kuwa haka ta ringa bin mami jiki a sanyaye, saboda ita harga Allah bata san wannan auran da za’ai dan ganin abun yake kamar mafarki. Tafiya meenal take ammma bata san inda take sa ƙafarta ba sabida tsananin tashin hankali. A zuciyarta cewa take “shikenan kuma da gaske rabani za’ai da waleed ɗina, wayyo waleed marayan Allah ashe de lokacin rabuwarmu yayi, Allah me nai maka astagfurullahi Allah na tuba ka yafemin zunubai na”. Duk cikin zuciyarta meenal take magagganun nan ba’a fili ba. To bayan meenal ta zauna haka tacigaba sa sambatu a zuciyarta mami da umma kuwa sai buɗe kaya suke kai harma da ma’eeshat ba’a barta a baya ba, kaya sunyi kyau sai dai san barka. To haka akai tabi ana buɗe kayan lefan meenal, har sai da su umma da mami suka gaji da buɗewa. ma’eeshat, ta cigaba da buɗe musu kayanta, har itama ta gaji. Sai da suka ɗauki wajan 3 hours suna buɗe kayan nan sannan suka kammala gani. Wasu abubuwan ma ba futo dasu ake ba. Meenal kuwa jigum tai tama rasa abin cewa, ɓakin ciki ne kawaiii yake sasakarta, a zuciyarta ta raya da ita watace da shikenan, ko iya lefan nan ta gani zuciyarta zata wuce taji tana son auran amma banda ita, dan ita tana ɗora ido akan kayan, taji tayi mugun tsanar su, dan ko kallo batayi. Haka su umma da mami suka gani, suna ta yiwa juna allah ya sanya alkhairi umma tana yiwa mami, mami tana yiwa umma. Daga haka mami da ma’eeshat sukaiwa umma sallama. Ma’eeshat taso ta zauna amma tunda taga halin da meenal take ciki, tasan ko ta zauna tayar mata da hankali zatai, kuma bata da kalaman bata haƙuri, shi yasama tabi mami suka wuce gida. Bayan umma ta tafi raka su ma’eeshat, da ƙyar meenal ta iya jan matattun ƙafaduwanta tabar wajan sabida tsananin tashin hankali, gaba ɗaya ji tai tama kasa kuka, tanaso tayi kukan amma ta kasa, saboda wani malolan baƙin cikine kawaii ya tsaya mata a zuciyarta, ji take kamar ta kurma uban iwu saboda tsabar baƙin ciki. Meenal tama rasa abinyi, ajiyar zuciya kawaii take saukewa, ji tai gaba ɗaya zaman da takeyi, jikinta yayi mata nauyi ba zata iyaba, dan haka sulalewa tai ta kwanta a kan bed wanwar kamar wata matacciya….. Momy Ɓangaran momy da daddy kuwa sai farin ciki suke abun su, duk gidan ba wanda yasan abinda yake faruwa daga momy sai daddy. suna ta shirya yarda lamari zai kasance, duk da ba wani taro za suyi ba, kawai ranar daurin aure za suyi taro su, dinner, kamu party, da sauran taro, da wasu shagalillika, sai za’a tare za’a yisu. Bangaran muhseen ango da ɗan uwansa fadeel kuwa, tuni sun cigaba da karatun su a saudiya har sun saba da zaman can ma, jikin su yayi fasss sun ƙara wani ƙasaitaccan kyau abunsu, hankalin su ya keanta sosai, musamman fadeel wanda ya samu nutsuwa sosai, fiye da dama……. Doctor kuwa bai san wainar da ake toyawa ba, na auran muhseen da meenal har yanzu, dan daya sani ma, ba mamaki yabawa su daddy shawara akan a haƙura da auran nan, saboda doctor yasan abinda ya dace sosai. Kuma momy da daddy suna jin maganarsa saboda yarda suka yaba da hankalin ɗan nasu da nutsuwa. Kuma bare ma doctor yaji ma’eeshat tana ce masa meenal bata san auran, tuni zai fara tunanin maganar da ma’eeshat ta gaya masa dangane da meenal bata son auran, nan da nan zai fahimci, inda maganar ta dosa, yana gayawa su momy za’a fasa auran amma sai de kashh bai san, wainar da ake toyawa ba. Doctor yana nan yan ta shirya-shiryan biki sa da masoyiyarsa ma’eeshat, kwana biyu sai wani farin ciki yake yi, kowa ya gansa yasan yana cikin farin ciki, kuma ba komai ne yakesa doctor farin cikin nan ba face, rage kwanakin auran nan nasu da ma’eeshat da kai aka mai da shi 3 month. Doctor wani irin mugun so yakewa ma’eeshat wanda shi kansa ma bai san yawan son da yake mata ba. Kuma bai taɓa tunanin zaiyiwa wata yar mace irin son nan ba koda wasa, shi har mamaki yakeyi, akan mugun son da yake mata, kullum cikin tunaninta yake, lokaci zuwa lokaci sai de doctor yayi ta sakin murmushi, kuma ba komai ne yake jawo hakan ba face so da kaunar ma’eeshat…….. MEENAL To ʼyan uwa da abokan arzikhi de suna ta zuwa ganin lefan meenal. Kowa in yaga lefan nan sai ya tofa, musamman ‘yan uwan baban meenal baƙin ciki ƙarara suke nunawa harda cewa wai ɗan mafiya zata aura. Wasu kuma suna munafurci wai aure bazeyi ƙarko ba. Kai harma da maƙota baƙin ciki sukewa meenal sosai kamar su mutu. Shi yasa umma da taga haka, aka rufe lefan aka mai da shi gidan su ma’eeshat, saboda gudan ɓarayi, dan tasan halin ʼyan layi da baƙin ciki, tsaff zasu iya aikowa a hauro gida da daddare a sace kayan. To bangaran meenal kuwa, tuni ta fita daga sabgar zancan auran nan, ta sawa zuciyarta tawakkali kuma duk daran duniya tun sanda aka kawo lefan nan, sai meenal ta tashi sallah dare ta gayawa allah halin da take ciki, shi yasa hankalinta ya kwanta. Kuma meenal har ranta tasan, baza’a taba auran nan ba haka nan jikinta yake bata, shi yasa ta kwantar da hankalin, kuma tayi offline gaba daya. Koda waleed ya tambayi ma’eeshat lafiya kwana biyu yaji meenal shiru, meenal tacewa ma’eeshat tai ta faɗawa waleed, karatune ya ɗauki zafi, kuma wayarta ma samu matsala. Kamar yarda mernal ta gawa ma’eeshat, haka ma’eeshat ta gayawa waleed. Waleed da yaji hakan, har sabuwar waya, ya siyarwa meenal mai tsadar gaske da sim ya kaiwa ma’eeshat ta bata, amma ina meenal tace karta kuskura ta karɓa, itade kawai ya barshi bata so, in kuma ya dage zasu samu matsala, haka dole waleed ya hakura sai da suna gaisa da meenal jefi-jefi ta wayar ma’eeshat. To yanzu de meenal hankalinta ya kwanta, sosai ta mayarda hankalinta kan karatu kamar ba itace tace tayar da hankalita da ba. Umma kuwa sai magunguna kyaran jiki take bawa meenal, duk da kuwa ba tarewa za tai ba, meenal de haka take karba ba dan ranta yaso ba. To kwanci tashi ba wuya wajan allah yau ya kasance saura one week a ɗaurawa meenal aure. Meenal kuwa bama tasan anayi ba, dan ta mai da zancan wasa, ma’eeshat kuwa tasan komai kawai kallan meenal takeyi. An riga da an bugo invitation ɗin daurin aure, daddy da abba sai rabawa suke yi, itama an kawowa umma, amma umma bata bari meenal tagani ba, kuma ta aika an kaiwa duk wanda ya kamata a gayyata a ɗaurin auran. Duk da ba wani taro umma za tai ba, kawai yini zatai, kamar yarda momy tace ayi. fatanta umma de allah yasa auran yayi ƙarko ya basu zaman lafiya, in a sun tare. After 6 days. Tun misalin ƙarfe 11:00pm Ma’eeshat taje tsaye bakin window ta fara waya da doctor. A yanzu waya ta ɗauki daɗi na soyayya, inda idon ma’eeshat yakea rufe tana mugun jin daɗin wayar da takeyi da doctor, kamar ance ta buɗe ido fa ta kalli ƙatsa, ƙwatsam, taga mota tana shigowa cikin gidan su. Mamaki ya bayyana a kan fuskar ma’eeshat sosai saboda ganin baƙuwar motar da bata gani bace a gidan ta bayyana. Ba komai ne yasa ma’eeshat mamaki ba face ganin, mota da tsakar dare kuma alamun baƙi ne, dan a halin yanzu karfe 11:30pm zuwa 12:00pm ne. Har zuciyata ma’eeshat da bada waleed ne a cikin motar nan. gaban ma’eeshat ne ya yanke ya faɗi rass,rass, rass, har sau uku. a fili ma’eeshat tace “Innalillahi” tabbas ma’eeshat tasan waleed ne, kuma tasan tabbas in waleed ne yazo gidan da matsala ba ƙarama ba, saboda gobe ɗaurin auran meenal. A zuciyarta ma’eeshat ta fara tunanin, anya ba labari waleed ya samu ba, dama zancan duniya baya ɓuya ai. Ma’eeshat tasan waleed ne yake iya shigowa koda yaushe gidan ba tare da me gadi ya dakatar da shi ba. Amma bai ma taɓa zuwa gidan da daddare kamar haka ba, gaba ɗaya ma’eeshat ta gama bayarwa waleed ne yazo, gidan dan tasan basa baƙi da tsakar dare haka. dukda de bata taɓa ganin waleed da motar nan ba, amma tasan dama something tana gani sa da mabbanta motoci, kala-kala kamar mai sai da mota, dan waleed yana da tarun motoci sosai, kullum cikin siyan mota yake. Muryar doctor ce takatse ma’eeshat daga tunanin data tafi “ Bakomai yake cewa ba face “eeshata lafiya kuwa?” Ma’eeshat data ɗagawa da kallon motar da take ƙokari parking, vewa tai “lafiya dear na, mai ka gani?” Cikin mamaki doctor yace “eeshata lafiyar ki kuwa? Muna magana naji kinje Innalillahi, kuma na jima Ina tayi miki magana naji shiru, yanzu kuma Kice min ba komai” ma’eeshat tana kokarin yin magana idon ya sauka akan mai futowa daga motar data zo gidan nasu yanzu…… Za kuga na canza yanayin typing ɗin book ɗin, kamar yarda na fara rubutawa a farko fatan hakan zai muku daɗin karantawa. Mu haɗe a last page, kar ku sake a baku labari dan anan ma littafin zai fara bye.👋🏽 -last page ~STORY AND WRITING BY AMINA BAYERO ~Typing📲 Da mamaki ma’eeshat sai taga kuma ba waleed bane, in idonta ya gani da kyau sai take ganin kamar daddyn doctor ne. Inda ya buɗe murfin bayan motar ya futo, ga dukkan alamu de driver ne yake tuka shi. Gauran nunfashi ma’eeshat taja tare da cigaba da kallon me yake wakana,. Kamar daga sama taga abban ta ya ƙaraso wajan dady sun gaisa cikin fara’a sannan taga abba yaja dady sun shige ciki. sai da suka ɓace mata da gani hankalinta ya dawo kan wayar. Sai a lokacin ma ta sake ankarewa wai ashe da doctor take magana. Ajiyar zuciya ma’eeshat taja, sannan ta sake cewa “hello” shima ta dayan ɓangaran ajiyar zuciya doctor ya sauke tare da cewa “har kin gama shirun kenan me yake faruwa ne”. Murmushi dole ma’eeshat ta ƙaƙalo tare da cewa “kaga afnan ce take wasa ita kaɗai a daran nan, shine take bani mamki kasan ba kyau wasa da daddare kuma ita ɗaya, please ka bani 5 minutes naje na lallaɓata tai bacci, sai mucigaba da wayar koh?”. “Murmushi doctor yayi tare da cewa “tom ki mata a hankula kuma kice, ina gaida ta na baki 10 minutes ma, sai kin dawo bye”. Ma’eeshat okay ta iya cewa kawai sannan ta kashe wayarta tare da ajiyewa, ta fuce daga bedroom ɗin nata. Direct bedroom ɗin umma ta nufa, tana zuwa ta murɗa handel ta shiga baki ɗauke da sallama. Zaune taga umma a gefan gado tana Danna waya, amma Jin sallamar ma’eeshat ne yasa ta ɗago tare da amsa sallamar. Daga haka ma’eeshat ta shigo ta zauna. Cikin mamaki umma tace “ma’eeshat lafiya naga, kin shigo mun a daran nan?”. “Mami lafiya lau, dama abin ne yaban mamaki naga baban doctor yazo cikin daran nan, shine nace bari nazo na tambaye ki ko lafiya”. Wani kallo mami ta watsawa ma’eeshat tare da cewa “kai ma’eeshat allah ya shirya ki, to ke mene damuwarki ta ina kikaga ma yazo?”. “Haba mami yaza kice haka, ta windor na gano shi mana”. Girgiza kai mami tai tare da cewa “hmm ma’eeshat allah ya shirya ki, to nima wallahi ban sani me ya kawo shi ba, Kinga muna kwance da abbanki ya bugowa masa yace, in ba damuwa yana so, yazo suyi muhimmiyar magana a daran nan sabida maganar, ba zatayu a waya ba, gwara su haɗu de. To shine abba yace masa yazo badamuwa allah ya kawo shi lafiya, to shine kikaga yazo”. Jinjina kai ma’eeshat tai tare da cewa “to allah yasa muji alkhairi” mami cewa tai “ameen” Daga haka ma’eeshat ta miƙe tayiwa mami sallama. Ma’eeshat tana tafe tana tunanin mai ya kawo dadyn doctor cikin daran nan gidan su. Tabbas tasan doctor bai san da zuwan dadyn saba, da zai gaya mata. Kuma har yanzu ma’eeshat tana mamaki akan doctor bai taɓa mata maganar auran meenal da kaninsa ba, kuma gashi gobe ɗaurin aure ma. To haka ma’eeshat tai, ta saƙa da warwara, harta dawo bedroom ɗinta. Dama bata kashe data ba, ta dauƙi waya ta dannawa doctor kira. Bata jima tana ringing ba doctor ya ɗauki waya. Nan da nan ma’eeshat ta saki jiki suka cigaba da shan soyayyah su ita da Doctor, amma koda wasa bata gayawa doctor zuwan dadyn sa gidan su ba. To a haka de ma’eeshat har su kai sallama da Doctor bacci ya kwasheta bata ji tafiyar dadyn doctor ba. Bama tasan sanda ya tafi ba. WASHE GARI Yau ta kasance ranar da za’a ɗaura auran meenal da muhseen ne. Dan haka tun safiyar fari su dady da momy suka fara shiri. Dady yana shirin tafiya ɗaurin aure da tarbar baƙi. momy kuwa ta ɗebo masu girki kala-kala, saboda jama’a. Tun 3 dare aka fara ƙoƙari ɗora girki kala-kala na alfarma wanda za’a raba wajan ɗaurin aure, da kuma wanda za’a bawa mutane in suka zo wuni. Abunci yayi Abunci, nama kaji, da raguna, shanu, kamar suyi magana. ba’a kuma batun mai da kayan miya da sauran kayan kamshi komai yaji nasha-nasha, abinka da bikin masu da shi. Bangaran doctor kuwa ko oho, dan bai masan abinda ake ba, da yake yana ɓangaran sa a lafe, yau da wuri ya shigo gida, duk da kuwa yaga kayan abinci a jibge a farfajiyar gidan, sannan kuma yaga anyi yanka sosai kawai sai ya bada sadaka za’ai da abincin, da yake yasan gidan su ana yawan sadaka sosai, koma bada azumi ba, musamman ma friday kullum sai anyi. To da safe ma da yake weekend ne yana gida yana baccin sa abun sa. Kuma abun mamakin shine! duk yarda su dady suka kai da gayyatar mutane, basu sanar da doctor zancan auran muhseen ba bare ma a bashi invitation har ya gayyaci wasu a matsayin sa na yayan ango. Ni kuwa amina bayero sai nake tunanin kamar momy da dady basa so doctor yasan zancan auran, gundun ma, kar ya soma karya musu da guiwa har ya bada shawarar, akan a dakatar da auran su meenal da muhseen ɗin, ya fara gabatar musu da, wani ƙudurun. MEENAL Meenal kuwa ta zubawa sarautar allah ido musamman ma, yarda taga ana ta shirya-shiryan ɗaurin aure, tun daran jiya, momy tasa aka jibgo abinci da kayan miya harma da uban naman girki biki da itace. Kuma Gashi yau yan uwa da suka dara zuwa ɗaurin aure, sun fara ɗora itace da asuba za suyi girki. Shi yasa meenal ta zubawa sarautar allah ido. Amma meenal har lokacin jikinta yana bata ba za’a taɓa ɗaura mata aure nan yau ba, haka nan meenal har lokacin jikinta yana bata ba za’a taɓa ɗaura mata aure nan yau ba, haka nan jikinta yake bata har yanzu guiwarta bata sare ba. Shi yasa ma meenal tana idar da sallah asuba ta ƙule ɗaki ta koma baccin ta me daɗi, tana ganin duk su umma shirin banza sukeyi. Ɓangaran umma kuwa, tuna ta saki jiki tana ta shirya-shiryan biki, an ɗora manyan tukwane ana girki me rai da lafiya.zuciyar umma kall da farin ciki, zata aurar da ɗiyarta, ɗaya tilo. Haka nan umma taji tana farin ciki da auran, saɓa nin da da take cikin damuwa. Saboda umma tasan tunda har lamarin ya kawo har yanzu, allah bai canza ba, kuma duk addu’ar da suke, tp tabbas tasan lamarin da alkhairi a ciki. Dan umma ta yarda da allah, akan baze taɓa, zaɓawa meenal abinda ba alkhairi ba gare ta, shi yasa da taga lamarin bai canzu ba, tasan hakan alkhairi ne kawai. Ma’eeshat Ba ita ta tashi daga bacci ba sai 11:30 na safe. Tana tashi ta miƙe ko addu’ar tashi daga bacci ba tai ba, alhamdulillahi ta iya cewa sannan taja wayarta ta hau online. Murmushi ma’eeshat ta saki, murmushi sosai, ba komai ne ya sata murmushi ba face ganin kamar yarda tacewa ƙaninta mai bunta yayi mata video ɗaurin auran muhseen da meenal ya tura mata ta WhatsApp, sai gashi ya turo mata, da yake da shi aka tafi ɗaurin auran. Har ma yayi wajan 30 minutes da turo mata. Murmushi ma’eeshat ta sake saki duk da tasan meenal kawarta bata san auran amma haka nan taji tana farin ciki da auran nan da aka ɗaura, saboda ko ba komai yau allah ya jika mata burinta tunda ya nuna mata auran meenal aminiyarta kamar yarda take fata. Daga haka ma’eeshat ba ɓata lokaci, ta fara buɗe videos ɗin da ƙanin nata ya turo mata. Bayan ya gama buɗewa na farkwan ta ta buɗe.Mutane ne zauna da dama a katafaran masallacin, duk da mutanan sunyi yawa hakan bai hana ma’eeshat gane abban taba da kumadaddyn doctor, da yake suna daga gaba-gaba. Dede wajan da aka fara ɗaura auran nan video ya fara inda ake cewa an ɗauka auran AHMAD ABDULKADEER USMAN da AMINA SHU’AIBU UMAR akan sadaki naira dubu ɗari biyar. Nan da nan waje ya karaɗe da kabbara mutane suna ta faman cewa sun sheda. Jim ma’eeshat tai ta tafi gajeran tunani fuska cike da murmushin farin ciki, tana so ta tuna wani abu dangane da, ɗaurin auran amma ta kasa. Daga haka ma’eeshat ta tafi status domin dorawa. Kafin ma’eeshat ta kai da ɗora status ɗin gabanta ne ya fadi rass, saka makwan ta ankare da wani abu. “Ahmad! Ahmad!” A fili ma’eeshat ta fadi hakan, amma sai tai saurin girgiza kai domin gazgata tunanin nata. Daga haka wayarta ta janyo tana mai dogon nazari game da sunan ahmad ɗin. Doctor ma’eeshat ta dannawa kira, sai data kusan katsewa sannan doctor ya dauka cikin muryar bacci yace “hello eeshata”. Ajiyar zuciya ma’eeshat ta sauke sannan tace “doctor baka tashi daga bacci bane, am sorry na tashe ka koh”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “no ba komai, kin tashe ni a lokacin daya dace ma, nagode sosai dear na”. Murmushi ma’eeshat tai kafin tace “hmm tom shikenan dama ina so na tambaye kane in ba damuwa pls?” Jinjina kai doctor yayi tare da tashi zaune yana cewa “okay my future wife ina jinki”. “Dan Allah wai ya sunan ka?”. Murmushi doctor yayi tare da cewa “to yau yarintar kike ji kenan, to sunana ma’eeshat da dadi koh?”. Dan kwaɓe fuska ma’eeshat tai cikin shagwaɓa tace “aa serious nake tambayar ka, yanzu ba time ɗin wasa bane”. Jinjina kai doctor yayi tare da cewa “Allah ya wuci zuciyar gimbiyar tawa, sunana ashmal”. Jinjina kai tai tare da cewa “full name ɗinka nake so”. “To ana kirana da ashmal ɗin ko office ɗina haka ake samun, but full name ɗina real name ɗina shine “Ahmad abdulkadir usman”. Wata mummunar faɗuwar gaban ma’eeshat yayi, amma sai ya dake saboda bata son ta amince da abinda zuciyarta, take faɗa mata, ko amafarki tasan hakan baze faru ba. Dakewa ta sakeyi tare da cewa “okay, pls sunan ka ɗaya da kaninka?” Cikin manaki doctor yace “kanina kuma eeshat me ya kawo zancan kanina wanne kenan?”. Jim ma’eeshat tai kafin tace “something de haka muhseen koh”. Jiniina kai doctor yayi cikin mamaki yace “shi kuma sunan sa Abdullahi” cikin tsananin karyewar zuciya ma’eeshat tace “okay su kuma sauran fa, duk ba sunan ku yake iri ɗaya?”. Doctor yana shan mamaki da tambayar ma’eeshat ɗin amma sai ya dake yana cewa “ ai su biyu ne twins muhseen da fadeel, shikenan”. “Tom na gane twins kenan, shi kuma ɗayan fadeel ɗin yasunan shi na Gaskiya” a takaice doctor yace “shi kuma sunan shi abdulrrahman”. Wani yawu mai ɗacin gaske ma’eeshat ta gaɗiye duk da kuwa har time d ɗin bata yarda da abinda take zargi ba, dan tasan hakan baze taɓa faruwa ba kuwa. Da sauri ma’eeshat tace “okay zamuyi waya anjima bye” daga haka ta katse wayar. Lokaci guda gumi yace rufe ma’eeshat wani ƙolulu me ɗacin gaske ya tsaya mata a wuya taji nunfashita yana ƙoƙarin ɗaukewa, duk da kuwa har lokaci bata taɓa yarda da abinda take zargi ba. Jiki na rawa ma’eeshat ma miƙe kamar ta faɗi, tana tashi ta fuce, sannan ta nufi bedroom ɗin mami. Tana zuwa bakin bedroom ɗin da sassarfa, tasa Hannu ta buɗe Handel ɗin a hankula adede time ɗin muryar mami ta daki kunnan ma’eeshat tana cewa “yanzu abba kana nufi da doctor ashmal aka ɗaurawa meenal aure bada ƙanin sa muhseen ba”. Nunfashin ma’eeshat tsayawa yayi cak tana jiran jin amsar abba, dan basu ankare da zuwan taba. Abba kuwa cewa yayi “ƙwarai mami da doctor aka ɗaurawa amina aure”. Cikin damuwa mami tace “Innalillahi yanzu ma’eeshat ɗin fa?” Kafin abba ya bawa mami amsa suka ji ƙarar faɗuwar abu temmmmm. Da sauri abba da mami suka juyo domin ganin me yake faruwa. Ma’eeshat suka gani ta yanke jiki ta faɗi ƙasa wanwar. Da sauri abba da mami suka fara yar rige-rige zuwa wajan, ma’eeshat ɗin suna zuwa, suka ganta kwance ba nunfashi, jini yana zubowa ta hanci da baki, yasalm……………. Shin kuna tunanin ma’eeshat zata tashi ko ta rigamu gidan gaskiya?. Wana dalili ne yasa, aka ɗaurawa doctor da meenal aure, ba tare da sun sani ba? Ya meenal za tai in taji zancan auran ta da doctor?. Kuna tunanin doctor zai amince da zancan auran nan kuwa?. Yaya amintar da take tsakanin meenal da ma’eeshat kuwa?. Da wana ido meenal da ma’eeshat zasu kalli junan su da maganar nan, har su samarwa kan su mafita?”. Kuna tunani umma, zata amince da zancan nan kuwa?. Ina uban gayya Oga waleed, ya kuke tunani zai ɗauki zancan nan, waleed bawan Allah za’a kwashe da lfy kuwa hmmmmmm!?. Duk ku biyo ni a part 2 ɗan jin yarda lamarin zai kasance, kar ku bari a baku labari. Alhamdulillahi Anan na kawo karshan littafin doctor ashmal book 1. Zan tafi hutun taƙaitaccan lokaci, kafin na dawo na cigaba da rubutu. Ina muku fatan alkhairi sai mun haɗu a book 2 Game buƙatar book 2 yayi min magana ta wannan number 09162226240 ra WhatsApp Byee.