[4/25, 11:05 PM] #momyn twins#:            ❤XEEMAT___LOVE❤                    💅SARKI SAMEER...💅                (wasa farin girki)             *BOOK 2* *FREE PAGE*              Barkan mu da dawowa dafatan kowa yayi salla lafiya Allah ya karbi idabadin mu Kamar yanda nayi alqawari 25 April zan cigaba to gashi na cika Allah yasa yanda nagama book 1 lafiya Allah yabani ikon kammala wannan ma kuskuren da zanyi kuma Allah ya yafe mana baki daya Ameen🙏     Gargadi da jan kunne littafin sarki sameer na biyu na kudine nayi na Allah nayi na annabi a book 1 duk yawansa nagama batare da wani yabiyani ko sisin kwaboba amma yanzu zaku biyani dan haka dan Allah dan Annabi  duk wanda yasan be biya na biyu ba pls karka karantan littafi idan kinsan baki biyani hakkina ba, idan kika karanta kuma baki biya ke da Allah mahadu acan sannan kuma duk wanda yabiya yakaran ta kar yafitar min da littafi ga wanda be biyaba  pls kabarshi a inda ka karanta duk me buqata shima yabiya kudin dana saka ba mai yawa bane bare wani yace yayi masa tsada bazai iya biya ba saidai idan mutum baiga dama ba.... *Zakubiya dari biyu asaka ku a group normal group 200 spatial group 300 VIP group 500 iya kudinka iya sha'anin ka👌*ga account number nan👇👇 *yan Facebook* Wandan da suke da qaramar waya ko kuma wadanda sunfiso su ringa karantawa a Facebook din to zan bude muku wani group din a Facebook iya wadanda suka biya zan sakasu aciki  nan da kwana uku in sha Allah zan fara posting sai ku hanzarta biya kar abarku abaya , Ga duk wanda ya shirya biya 👇 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU OPAY BANK duk wanda yabiya  sai yaturon da shaidar biya ta number ta 08124226526 Yan facebook kuma sai kuturon ta account dina na Facebook ina amfani da Azeema dahiru Aminu(xeemat)                     🅿1&2 Bismillah...........✍ ________________*DADDA* da qyar nasamu wata qasan bishiya da ba wanda zai ganni anan nake kwana wajen kwana na biyu agurin ba ci ba sha damuwa babu wacce ban shiga ba ga Ameesha kullum cikin kuka take min dan 'yar madarar da nake batama ta kusa qarewa kadan kadan nake bata saboda idan ta qare bansan a inda zan samo mata wata ba daman ba ruwa take shaba ahaka mukayi rayuwa tsawon kwana biyu da wuni guda danaga de ina niyar halaka kaina sabida yunwar da nake ji ta gama kamani dan da qyar ma nake iya daga qafata nake tafiya idanuna kwa har rurrufewa suke yi saboda rashin bacci da yunwa haka nafito daga cikin dan dajin ga Ameesha  abayana sai kuka take min ahaka nazo bakin titi amma sai na dan rufe fuskata da gefen mayafina saboda kar aganeni......, saida nayi tafiya me dan nisa ina laliban inda zan samu tuwan sha amma bansamu ba ahaka naci gaba da tafiya saiga wani me adaidaita shine na tsaidashi nace dan Allah yataimaka min banda kudi yadan saukeni a police station amma yaki saida na tsaida wajen guda biyar kafin nasamu wani ga tausaya min ya dauke ni ina zuwa tunda ga waje da naga fanfo naje nasha ruwa na sauke Ameesha itama nabata sannan nadanji dama dama sai na shiga ciki ina zuwa nasamu wani dan sanda yayi min iso wajen ogansu nande nagaya musu halin da ake ciki shikam yace besan zance daman ai angaya min ko mu biya kokuma yayi zaman gidan prison duk magiya da nayi mishi da roqon sa amma be saurareni ba da na bukaci a fito min ma dashi inason magana dashi sai yace bazan samu damar ganin sa ba naci gaba da roqonsa daga qarshe ma sai kawai yasa azo a fita dani daga office dinsa wasu yansanda mata suka zo suka jani sukakai ni waje sai na riqe daya daga cikin su nace dan Allah tabashi hakuri ya barni inganshi ina son magana dashi amma sai tace min inyi hakuri hakan bazai yiyu ba har ta juya zata tafi sai kuma tajuyo murya qasa qasa tace baiwar Allah bari ingaya miki gaskiya danki baya cikin nan gurin amma bar garin nan dashi tun safiyar jiya hankalin yatashi nace mata ina aka kaishi tace gaskiya bata sani ba amma tana tunani ko kano aka kaishi dan tadanji qishi qishin din maganar amma bata da tabbas amma inje can in gwada tambaya ko yana can nace  mata ai bansan ko ina ba acikin kanon hasalima bantaba zuwa ba tace idan naje intambaya inana gidan yari sabon budewa za anuna min nayi mata godiya sannan ta tafi tabarni awajen sai nafara tunanin yanzu ta ina zan fara neman kudin da zan tafi kano amma na rasa mafita a gurin nayi zama na naqi tafiya saboda nasan sai nafi tsira daga wajen wadan can mutanen baza suganni ba anan jaka ta najawo nashiga bicikewa kamar na ajiye kudi aciki sai dai bansamu ko biyarba daman nasan hakan zata faru sai nasake zuge bayan zip din akwa abun da ban taba tunani ba kenan  sai kawai naci karo da ATM din malam da yaban lokacin da zan fita tashin hankali yama sa na manta da shi kwata kwata aikwa da sauri na miqe daga gurin na fita waje duddubawa nashiga yi ko zan samu inda ake cirar kudi amma ban samu ba akusa saida nayi nisa sannan na hango wani wajen me pos  ina zuwa na mika mishi sai nace ya duba min yagani nawa ne aciki yana dubawa sai yace min dubu tamanin da da bakwai ne aciki sai nace mishi kawai yacirar min sha bakwan yaban nasaka pin nabashi ya cirar min sannan na karba nabashi charges din dari biyar sannan natafi inda zan samu abinci nafara nema sannan nasiya naci na koshi dan saida nasai na dari biyar sannan naji na qoshi da naji kwarin jikina sai naje nayowa Ameesha siyayya  nata kayan harda kayan sakawa da duk de abun da nasan zata bukaqata kafin muje saida na kashe mata wajen dubu biyar sannan na nufi hanyar tasha inda zan hau motar kano bansha wata wahala ba nasamu na shiga kuma ina shiga motar ta tashi muka dau hanyar kano mundau lokaci muna tafiya sai wajen magrib muka qarasa muna isa cikin garin kano saiga wata baqar mota ta sha gabanmu inaganin haka gabana yafadi ina addu'ar Allah yasade ba yan fashi bane kar su kwace min kudade buga motar akai da da qarfi sai drivern ya bude yafita yana tambayar ko lafiya me suke so sai daya yace zamu dau wata mata ka bude mana ina jin hakan kuma najiyo muryar mutanen nanne nayi mamakin jin yanda suka biyo ni kota ya akayi suka san na taho waya ce musu ina hanyar kano da sauri nayi qasan kujera sannan nace wa matan gefena dan Allah sudan rufeni kar subari wadan can mutanen suganni ni suke nema kuma wallahi mugayene kasheni zasuyi sutaimakamin , suka ce to " ina jinsu drivern yace ya sunanta kuma meyasa kuke neman ta wani yace ina ruwanka ka bude mana kar muhada dakai driver ya bude musu yace gashinan dayane ya shiga ya lalleqa sai yafito yacewa sauran banganta bafa sai yace kade qara dubawa dole tana ciki tunda ta tabbatar mana da ta taho kuma taga motar da tashiga dan haka ka duba ko kuma kowa yafito daga cikin motar muduba idan mungama sa koma dan nasan tana ciki ba inda faje jin maganar da sukeyi ba qaramin faduwa gabana yayi ba shine yau tawa ta qare bani da wata hanyar guduwa ina cikin wannan tunanin sai wata mata tace kitashi ki shirya zan taimaka miki ki gudu kitsaya abayana ina fita zan fada kansu zan nannade mishi fuska da mayafi na ke kuma sai ki gudu kafin su ankare dake dannasan idan nayi haka zan ja hankalinsu gaba daya naji dadin taimakon da tace zata min dan haka sai natashi nagyarawa Ameesha goyo Allah yataimakeni ma tunda nabata madara tasha da maganin murar da nasiya mata saboda naji hancinta yafara toshewa tunda ta kwanta bacci kuma har lokacin bata farka ba, gyara mayafina nayi naqara rufe fuskata sai na cire ATM din dake cikin jakata da kudaden duk de abun da nasan me amfanine na cire nasaka acikin aljihun bujejen wandon da nasaka ta ciki saboda acikin motar zan bar jakar takalma nama aciki na barsu nade shirya gudu sosai mutane nata fita har akazo kanmu matar tace kimde shirya ko nace mata eh kamar ynada tafada kuwa hakan mukayi tana fita tayi kansa nikuma da farko banyi gudu ba sai nabi a hankaki na fita ba wanda ya lura dani har nafara gudu inajin su kuwa sauran sukayi kan matar sunayi mata magana wasu ma sun dauka itace matar da ake nema saidai bayi nisa ba naji wani daga cikin su kai ai kunganta can zata gudu ai dayan ma basubi takan matar ba gaba dayansu suka biyo bayana, inajin haka na kunce goyon bayana kawai na jefar da zanin a wajen nacigaba da gudu ni kaina bansan inda nake saka qafata ba kawai gudu nake suna bina abaya wata kwana nayi sai nasamu wani lungu na buya suna zuwa kuwa sukai ta nemana amma basu ganni ba sai suka wuce kawai sai da na bari sukayi nisa sannan ni kuma nafito sai na canza hanya nabi wani titi nacigaba da gudu bansan inda naked dosaba ina cikin wannan gudun ne wannan baiwar Allahn ta cece ni tafada tare da nuna Ammi da hannu (shine asalin haduwar ga da Ammi na farko anan suka san juna ) bayan na dan kwana biyu sai nayi tunanin gwara inbar gidan saboda zuwa lokacin nadena yarda da kowa tunda ko basu fadan ba dukkan alamu sun nuna yar sandar nan da tace intaho kano itace tagaya musu inda nake alhalin kuma itace tace intafi amma kuma daga baya ta ci amanata shiyasa nake ganin duk inda ma naje duk bakin su daya ba wanda zai taimakeni saboda Allah, bayan barina gidan bansan inda zan dosa ba sai kawai na nufi kasuwa sai na tambaya inda sabon prison din yake sai aka kwatan ta min amma da naje sai akace ba wanda aka kawo haka naqara dawowa jiki babu kwari har zuwa dare bansamu mafita ba ina tavgarari a bakin hanya aranar de a wani harabar masallaci muka kwana ina ta barci har mai ma sallacin yashigo bansani ba saida yatashi ni yace baiwar Allah lafiya kuwa kika kwanta anan adan takaice de nabashi labarin nace masa wasune suke bina zasu kasheni gashi sunkashe min mijina shiyasa na gudo nazo nan na kwanta kaji dalilin kwanan nawa agun shine ya taimaka min ya nuna gidan sa yace inje idan an idar da sallah zai shigo incewa mutanen gidan shi ya aikoni dana shiga ba kowa haka naita yin sallama amma ba wanda ya amsa sai kawai nasamu waje daga gefe na tsaya ina jiran shigowar sa ina gurin ba wanda ya fito har aka idar da sallar ya shigo yaganni awajen ya metasa na tsaya nace nayi sallama ba amsa ba yace to shikenan muje ciko yana tafiya ina binshi abaya muka shiga wani daki wata mata na salla saida ta idar sannan yace uwani ga bakuwa tazo tana ta sallama baku amsaba tace bakuwa kuma da asuba daga ina nande shima yayi mata bayani amma fuskarta ba walwala tace to barkan ta da zuwa ga guri ta zauna ta nuna bakin gado sai mutumin yace baiwar Allah ki ajiye yar sai kiyi salla kafin da gari ya qarasa wayewa ko nace masa to sannan na ajiye yarinyar ya nuna min inda bandaki yake naje yi alwala na fito bayan nayi idar na gaisar da matar amma sai naji ta masa min ciki ciki tunda ga nan nagane cewa matar bata son zamana dan haka nayi alkawarin gari nayin haske zanbar gidan zama nayi adakin saboda zuwa lokacin mutumin har ya fita daga dakin ina gurin har gari yayi haske ina shirin  fita kenan saigashi ya shigo dakin ganina a tsaye yace ina zani nace masa zan tafi ne yaca a'a ba inda zani idan na tafi ina zani bayan ba wanda nasani nace masa yayi hakuri yabarni intafi yace a'a saboda banason mitayin jayayya sai kawai nace masa to zan zauna zuwa gobe kafin insan yanda zanyi yace to haka na koma na zauna shiru kamar ni kadaice adakin danko inda nake ma matar bata sake kallaba kamar ma batasan da zamana acikin dakin ba, inda nayi sallah na kwanta agun dan bacci nake ji wanda nayi be ishe niba ina kwanciya kuwa bacci yadauke ni, kukan Ameesha ne yatasheni ina tashi naga tana tafaman kuka amma matar nan tana kallon ta bata dauke ta ba kuma bata tasheni ba haka natashi nadauke ta na rarrasheta nabata madara tasha saidaga baya na lura da kwanon abinci agefena saida nagama bata sannan nasamu tayi shiru nikuma daman yunwa nake ji dan haka kawai nahau cin abincin da nagama kawai sai ban kulata ba  nafitowata mutanen da nagani na shiga gaisarwa duk suka amsa amma suma mata daya ce naga fuskarta a sake dayar kuma ko amsawa ma batayi ba dayace tazo kusa dani ta karbi Ameesha dake hannu na tace kintashi ai malam yace muzo mu gaisa sai muka tarar kina bacci sai lokacin na danji dadi danaga ita ba irinsu bace dan haka kawai nima nasake da ita muka dan yi hira na lurama kamar adakinta yake ita take aikin dan haka na taya ta adan kan qanen lokaci muka saba da ita sauran kuma ba waccce na qara bi takanta tunda sun nuna basa sona nima sai nafita daga harkarsu sai da muka gama komai sai nace mata dan Allah taimako nake nema inason inkama gida dan madaidai ci ba me tsada ba sai inzauna tace bazan zauna anan ba nace mata eh nafison in zauna nikadai zama agidan wasu be kamace niba da girmana tace to shikenan bari zatayiwa malam magana idan yadawo sai aduba nace to shikenan shiru de inajira inga yadawo amma be dawoba sai dare yana dawowa kuwa tayi masa magana yace zaiyiwa wani abokin sa magana da yake harkar gidaje amma sai zuwa gobe anan muka bar maganar zuwa goben, Washe gari ma yace yama sa ana cigiya amma kamar na nawa nake so sai nace masa me sauke de yace kamar na dubu talatin ko ashirin ya isa tunda ni kadai ce nace masa eh ya isa ni koma bekai haka ba inaso duk tsufansa kuma dan nama fison tsohon gida me sauki sosai ko daki dayane ya isheni yace to ba matsala za asamu intakaice mukude saida mukai wajen wata ba asamu gida ba saida kyar akasamu shima ance sai andan yi masa gyara kuma ba anan bane awata unguwar ne nace ba matsala yanzu zuwa yaushe za agyara din yace inbada kamar nan da sati daya nace to alokacin nahada kudin da na ciro a pos da kuma wanda Ammi tabani nabashi dubu a shirin da biyar yakarba yaje yakai musu akallade sada nayi wajen wata daya da sati biyu sannan na tarkata yan kayan da na siya mana nabar musu gida dan banajin dadin zaman gidan kwata kwata agurin mutum daya nake samun sauqi duk tsawon lokacin da muka dauka dasu bawanda nasamu sauyi daga garesa kuma  hatta yaran gidan basu da kunya ba wanda yake girmamani ita kuma wacce muke mutuncin da ita bata da da ko daya shiyasa na matsu inbar gida, mu uku muka nufi unguwar dani da limamin da kuma abokinsa wanda zai kaimu gidan ranar da muka bar gidan tunkan mukarasa unguwar aka kira limamin awaya daya daga cikin matansa ce ta kira shi wai yadawo tare dani wasu mutane sunzo nemana ko mudawo ko mufadi inda muke duk ina jinsu sai nace masa yakashe wayar kawai karyace komai sai ya kashe wayar sai yatambayeni ya za ayi dayan abokin nashine da shima yasan komai sai yace kawai ai mafita dayace shine liman ya koma yace musu ya riga yakawoni gidan da yakama min inyaso sai ya kwatan ta masu gidan sai yace nikuma yanzu mutafi gidan sa kafin yasamo min wani gidan daban yanda bazasu iya sanin inda nake ba munji dadin shawarar sa dan haka muka yarda tun alokacin muka saukeshi ya juya mukuma muka nufi gidan wannan abokin nasa inda yake unguwar kurna banyan mun isa sai naga banbanci da wadan can mutanen gidan liman nan gidan mace daya ce sai 'yayan su mace da namiji suma duk yarane namijin nema me wayo amma macen bata da wayo hannu bibbiyu matar ta karbe ni ko jin wacece nima bata tsaya tambayar mijin nata ba kawai yace mata ga bakiwa nan kafin asamo mata gidan haya zata zauna anan saboda bata san kowa ba anan tace to ba komai ai sai muzauna sosai take kula dani duk danasan tama girmeni ko bada yawa ba amma yanda take kula dani tana bani girma kamar nice gaba da ita haka muka zauna da ita yatanta ma sai faman daukar Ameesha suke naji dadin zaman gidan sosai cikin kwanciyar hankali harnayi kwana biyu, bayan kwana uku aka samomin gida bamu da nisa da su badan taso ba muka bar gidan dan yaranta harda kuka macen ma cewa tayi sai ta bimu da kyar de suka bari muka tafi kudi naqara cirowa nasiyi duk wani abun amfani da nasan zan bukata da kayan sakawa da na daki komai de babu abun da bansiya ba dan zuwa lokacin ma kudin da na rage basu fi dubu goma ba dasu bayan 'yan kwanaki kuma sai nafara saro kaya inakaiwa wata makaran ta ina siyarwa saboda banason inzo in kashe kudin gaba daya shiya sa nafara juyasu ta hanyar kayayyakin yara haka naci gaba da rayuwata nikadai sai Ameesha amma wataran ina kaita gidan mutumin nan wajen 'yayan sa wataran kuma akawosu harma suka fara zuwa da kansu shakuwa ta shiga tsakanin su me qarfi har Ameesha tayi wayo sosai ta girma tama fara magana da tafiya ga tsiwa da take da ita lokacin da tayi shekara biyar sai nasakata makarantar su Azeema inda shakuwa taqara shiga tsakanin su duk inda kaga daya sai kaga dayar har takama ma wataran gida daya suke kwana ga halayen su yazo daya basaji a makaran kullum cikin kai qararsu kaf makarantar ba wanda besan Azeema da Ameesha ba kamar ya da kanwa wadanda suka fito ciki daya haka suke.................✍ *to anan nakawo qarshen Free Page na sarki sameer book 2 duk wanda yake son ya cigaba da karantawa yabiya ya karanta cikin kwanciyar hankali da salama 👌👌* [4/26, 8:13 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526,                          🅿3&4 Bismilah.......✍ _________________*DADDA*     "Alahamdulillah lokacin kasuwancina ya bunqasa inayin ciniki sosai ina cikin kwanciyar hankali na kwatsam saiga mutanen nan agidana sukazo suka qarayimin barazanar da suka saba yimin wai duk inda na ajiye dukiyoyin nan in fito dasu sannan in fada musu inda sameer yake da kuma matarsa nanma de nace musu matar ita da dan cikin ta sun mutu shikuma yana prison kuma bansan inda aka kaishi ba iyakacin abun da nasani kenan dukiya kuma itama bansan inda takeba na rokesu sugaya min inda mijin yake sukace inde inason mijina inbasu dukiyar da takaddun gidajen nace ni kuma kantaun bani mijna da kuma inda suka boye sameer amma sai suka kwashe min da dariya sukace ina haukane to baza suyi ko dayaba idan kuma nace zan cigaba da yi musu taurin kai to zasu kasheni sannan sukashe mijina yaron da naked magana ma akai zasu kasheshi ta yanda ba wanda zai amfana da dukiyar jin hakan yasa na dan tsorota amma ba nuna musuba saboda nasan barazana ce kawai sameer baya wajensu kuma baza su taba kasheni ba inde banbasu dukiyar ba dan haka kawai nace suje suyi duk abun da suka ga dama sunji haushin magana ta dan saida wani ma daga cikin su  ya makeni da duka sannan suka fita tunda ganan basu qara dawowa ba saida suka dau lokaci me tsawo sai wasu suka dawo amma ba wadan can bane wasune daban suma de maganace ta kawo su kuma amsar da na basu wancan lokacin ita naqara basu a wannan lokoacinma, nanma de saida suka masgeni kafin sutafi inda Allah yake taimaakkata duk sanda zasuzo Ameesha bata nan ko tana makaranta ko kuma tana gidan su Azeema shiyasa basu taba samun taba tunda daga wannan lokaci nadena jin tsoronsu kuma nace ba inda zan qara tashi intafi tunda de duk inda naje ma sai sun nemoni gwara kawai in tsaya a guri daya tunda na fuskanci ba iya kasheni zasuyi ba gwara kawai inyi zamana kuma duk wannnan tsawon lokacin da na dauka banfasa zuwa gidan yarin ba kusan kullum sai naje amma amsar daya ce ba akawo shiba wataran daga bakin gate ake korani ace bazan shigaba nafi wajen shekara biyar ina zuwa amma bantaba samun damar ganin saba, kuma nasan yana ciki saboda na koma garin mu har wajen sau biyu ina zuwa can intambaya ko yanan nan amma suka tabbatar da cewa su case din yabar hannun su sun turashi kano inje can inmemishi ba ruwansu dan su sunma manta dashi haka nadawo nan ma de kuma ba sa'a amma ban hakura ba banyi qasa agwaiwa ba naci gaba da zuwa, Allah cikin ikonsa  wata rana nayi dace ina zuwa sai wani tsoho da yake aiki agun daman duk sanda nazo inayawan ganin sa sai yakirani gefe bayan mungaisa shine yake tambayata dalilin da yasa nake zuwa kusan kullum yana ganina wanake nema nan take nayi mishi bayani da kwatanta masa kamanni sa yanda zai gane bayan nagama yimasa bayani sai ya jinjina kai yace ba matsala zai taimaka min akwai wani da suke mutunci dashi zai tambaye shi idan ankawo shi zai sanar dani inke gida zuwa gobe sai in dawo inji yanda sukayi naji dadin wannan rana nayi masa godiya na tafi gida yaude raina cike yake da farin ciki, kamar yanda mukayi dashi kuwa washe gari da sassafe na shirya bayan na ajiye Ameesha amakaranta sai na wuce in zuwa kuwa muka hadu dashi muka gaisa sannan natambayesa ya sukayi da mutumin yace baiwar Allah danki yana cikin nan amma fa gaskiya baza kisamu damar ganinsa ba saboda  tunda aka kawoshi aka sanar dasu kar subar kowa yagana dashi hasalima dakin da aka qulleshi shi kadaime aciki baya tare da kowa kuma ba wanda yake zuwa wajensa amma yasanar min akwai mutumin da yake zuwa yana ganin sa lokaci zuwa lokaci wanda shine yasa kar abar kowa yaganshi sai shi nide ina tunani akwai abun da suke qullawa akansa shiyasa suka hana kowa yagansa, kuka nafashe dashi ina roqon sa yanzu ba wani taimakon dazai iyayi min insamu ganinsa koda sau dayane yataimaka min sai yace wallahi bazai iyayin komai akai ba saboda ko bagaren da aka qullesa ma baza abarshi yaje ba saidai kawai inyi hakuri in koma gida inci gaba da addu'a Allah yakawo sauyi har zai tafi nayi saurin daka tar dashi sai nace ya suffan tamin kamannin mutumin kuma da mota yake zuwa ko aqafa yace wlh besani ba bema taba ganin saba sai nace dan Allah to kayi min wannan taimakon kasaka min ido akan mutumin duk ranar da yazo yatambayeni ko ina zargin wanine wanda nasani nace masa a'a da banyi niyar gaya masa ba amma sai kawai nagaya masa tunanin da nayi nace masa inaso inde be fini jikiba ko kuma banfishi ba inaso inyi shiga irin tashi inje inganda zaro ido yayi jin abun da nace sannan yace baiwar Allah wannan wane irin ganganci kikeso kiyi kinsan halin da zaki jefa kanki kuwa idan aka kamaki nace masa nide zan iya in sha Allah ba abun da zai faru dani yace gaskiya to shi bazai iyaba badashi bazan jefasa a wata masifar ba sosai nakama yimasa kuka ina roqonsa yataimaka min da yagade da gaske nake sai yace to inyi shiru zai taimake ni amma bata wannan hanyar ba injira duk yanda zaiyi yagano inda yake zaiyi inyaso sai ya samomin kayan ma aikatan gidan insaka hakan sai yafi akan inyishigar wancan mutumin da dole ma akamani tunda ba kamannin mu daya ba amma idan nai shigar ma aikata  ba lalle akamani ba saboda akwai ma aikata da yawa bakowa yasan kowa ba nace masa hakan ma yayi sai yace yanzu inbashi number wayata inyaso idan yagama shirya komai sai yakirani duk yanda ake ciki zai sanar dani da sauri na zaro salulata nabashi number sannan nayi masa godiya mukayi sallama, shiru shiru be kiraba harna cire rai da zai kirani sai ga kiransa amma sai yace in qara hakuri haryanzu besamu damar ganowa ba amma yana nan yana kokartawa nace masa ba damuwa Allah yabashi daman ganowa mukayi sallama atakaicede mufu tsawon wata shida be samu damaba saida kyar yagano yasanar dani aranar da yasanar dani naje da yamma nasame shi yabani kayan maza nashiga wani daki nasaka tare da rufe fuskata da face mask nasaka hula na dora wata qatuwar rigar sanyi akai nasaka takalmin maza wadan da duk shi yahada min su sai kwanon abincin da zan kai masa saboda damai kai abinci suka hada baji shima yataimaka min yabashi kayan sa yakawo min nasaka saida aka idar da sallar magrib sannan muka fito daga inda muka shiga haka na fito kamar namiji ba wanda zai ce macace addu'a nayi sosai gaba na na dukan uku uku haka nuka shiga ciki nida shi daman ya kwantan tamin inda zanbi dan haka muna zuwa shi sai ya tsaya daga baya yanda idan wani ya taho zaiyi sauri ya kirani awaya, a haka na doshi wajen nikadai ina ta jero addu'o'i ina tafiya  duk addu'ar da tazo bakina yi nake  har naje bakin wajen kuma Allah cikin ikon sa ba wanda na hadu dashi a hanya saboda wasuma basu dawo daga masallaci ba har naqarasa bakin gurin da yake ina tafiya naji hawaye na tahomin da narasa na meye na farin cikin zan ganshine ko na bakinciki kuka ne yaci karfina wanda nama kasa magana saida na tsaya agefe nayi me isata sannan na qarasa bakin dakunan dasuke ajere naje daidai kan inda yace zanga ansaka number 43 nanne dakin da yake ciki qaraswa nayi ina leqawa nagano sa a tsugunne ya kifa kansa akan cinyoyin sa naji dadin ganin sa ashede zan qara sakashi acikin idona kafin inbar duniya saida nagama qare masa kallo naga ya rame ya canza sosai shagala nayi da kallon sa dan harma na manta a  inda nake saida naja lokaci kafin indawo hayyacina dan bubbuga qofar nayi amma shiru be dago ba cigaba nayi da bubbugawar amma yaqi motsawa saida yajide baza adena ba sanna yace bazan ciba ka koma da abincinka saboda atunanin sa me kawo masa abincine banyi magana ba na qara buga qofar sai lokacin yadago lokaci guda muka hada ido dashi sai ya kawar da nasa gefe ahankali nace dan albarka juyowa yayi da mamaki qarara a fuskar sa sai kuma yamayar dan atunanin sa ko kunnuwan sane suka jiyo masa muryar wadda baya tunani zatazo qara kiran sa nayi nace dan albarka ko in komane baka son ganina yanzu kam saida yayi wata iriyar zabura da har saida yakusan bani dariya da gudu yazo wajen sai kuma ya tsaya yace bawan Allah kamar muryar mace naji anan ko ninake jin haka dan Allah bude idon nayi na kalle sa da kyau yacanza gaba daya ga gashi da ba gyarashi yake ba duk ya cika masa fuska inbaka sanshi bama sosai baza ka taba ganesaba gashi yayi duhu sosai ga wata uawar rama da yayi kana ganin sa kansan yana cikin mawuyacin hali, saida nagama qare masa kallo shima kuma ni yake kallo kana  nace masa  wai kana nufin baka gane niba nice ba nafada tare da dan bude fusakata kadan yanda zai ganni aikwa yana gani yayi suman tsaye yayi da qyar ya iya bude bakinsa yana in ina yace umm..um..ummin mu kice da gaske ko gizau din da nasaba yine kice min ba mafarki nake ba ummi ummin kece agabana ya akayi ki ka shigo daman kuna raye ina baba ina Ameesha duk suma suna raye basu cutar dakuba ummi taya akayi kika gano inda nake ina ne nan wane garin suka kawoni duk yabi ya kidime sai faman tambayoyi da yake jeromin sai da na bari yagama sannan nace dan albarka wacce tambayar zan fara baka yanzude duk ba wannan ba bani da lokaci kasande shigowa nan ba tadadin rai na shigoba kuma nanason azo a riske ni anan atakaicede yarka tana nan lafiyarta qalau malam kuma tun washe garin ranar da muka bar wajen ka nafita unguwa kafin indawo sukazo suka tafi dashi bansani ba ko sun kasheshi ko yana raye Allah masani ammade suna zuwa inda nake sunce kuma inde ban basu abun dasuke nema ba sai sun kasheshi amma basu san Ameesha na raye ba nace musu ta mutu tare da mahaifiyar ta shiyasa ma inajin take araye haryanzu kuma duk sanda zasuzo basa samunta agidan ni kuma bazasu kasheni ba sai nabasu takaddun ka da komai naka ni kuma na hanasu amma yanzu abun dasuka fi damuwa dashi shine su fara sanin inda kake saboda kasaka musu hannu nikuma nace musu suje can garin su nemeka idan 'yan can kuma suma da nasu shirin akanka shiyasa basu fada musuba inda kake saidai ni suke ta bibiya duk inda naje sai sunbini sun gano inda nake shiyasa ma tun ina guduwa har na dena saboda koma ina naje sai sun nemoni shiyasa na rabu dasu tunda na fahimci baza su kasheni ba, adan takaicede nabashi labarin komai harda kukansa jinyanda naked ta garari nikadai yace alokacin kuma na tambayesa wai ance wani mutum yana zuwa wajen sa shikadai ake bari yagansa waye mutumin shine yace shimade ba alkhairi bane yake kawosa  ba shima duk akan maganar ne aikosa akayi amma be bashi amsar komai ba yace kuma inde banbashi ba bazan taba barin gidan nan ba har abada ni kuma nace yayi duk abun dazaiyi amma bazaiji komai daga gare niba saboda nasan kona basu ba barina zasuyi ba gwara in hanasun ma gabadaya,nace masa yayi tunani awajen aikinsa ba wanda suka taba samun sabani ko yayi masa laifi da zaisa suyi masa wannan sharrin ko akwai wanda yake jin haushin shi yace min shidai bai taba fada da kowa ba inma akwai wanda yakejin haushin sa to besani ba ammade dole akwai hannu mutane da yawa akansa ba iya dauke wayar ne yasa akayi abun da akai ba saida sa hannun masanin bankin sannan kuma wadan can mutanen ma suma daban ba bakinsu dayaba nace masa hakane nande muka dan tattauna game da yanda zamu bullowa lamarin ta yanda zamu gano ko suwaye amma sai mun hada hujjoji sosai sannan zan shigar da qara awata kotun ko Allah zaisa adace mugano meye musababbin bibiyar tashi da akeyi me ya aikata ko me mahaifiyarsa ta aikata amma dole sai munsamu tsayyayen lauya me gaskiya in bahakaba yanda sukayi mana awacen qarar da akayi yanzu ma haka zasuyi zasu siye alakalanne gaba daya yanda baza ataba bamu gaskiya ba daga qarshe ma za a iya hadamu gabadaya a qulle mu saboda ba imanine da suba basu da tausayi akan abun da suke so kodan kar asirin su ya tonu zasu iya yin komai daga qarshe reshe ya juye da mujiya  shiyasa sai munbi komai a hankali  inda so samune na musamu lauya na kusa damu sosai yanda baze iya cutar muba, alokacinne kawai yazo min da wata shawara yace me zai hana insaka Ameesha makarantar privet yanda zata samu karatu me kyau ta shiga jami'a tayi karatu me zurfi inyaso sai ta karanci bangaren law wannan ce kawai hanya mafi sauki yanda zata tsaya musu amma in ba haka ba duniyar nan bata da tabbas mutane ba abun yarda bane yanzu kowa yafi bawa kudi mahimmanci anfidaukar kudi fiye da komai inde za abawa mutum kudi to zai iyayi maka komai zai dannai gaskiya ya dau rashin gaskiya yanzu rayuwar ta zama haka saidai fatan shiriya (Allah yasa mu cika da imani Allah ya kawar da kanmu akan abun duniya ameen) kiran da yashigo wayatane yasa mu katse hirar da muke ashe har lokaci yaja haka lalle mutumin nan ya taimakamin ina dagawa yace inyi sauri infito ga shinan za azo wajen da sauri mukayi sallama yace ingaishe masa da Ameesha sannan dan Allah kar intaba sanar da ita labarin komai har sai ta mallaki hankalin kanta, daga nan mukayi sallama badan musoba muka rabu ina daf da fitowa naji ance Rabi'u zo ka kamamin wannan tun dazu nake neman ka ina kashiga ne gabananen yafadi nakasa juyowa ina tunani ta inda zan fara yin magana kawai na qarajin wata murya ance laa ai da kabarshi ma kawo inkaima ka zan iya to to gashi shikenan ma ngd ai bangama jin maganar tasu ba nayi saurin barin wajen, lokacin da muka fito har anidar da sallar isha mutane sun fara shigowa muna shiga dakin nayi sauri nacire kayan na maida nawa nasaka nayi masa godiya sosai sannan na taho gida, tundaga wannan lokacin inde ina son ganin sa ina zuwa mutumin nan yana taimaka min kuma inajin dadin hakan dan nadena ma yawan damuwa hankalina kwance naci gaba da rayuwata kuma mutanan ma daga baya sai nadena ganin su kwata kwata suka dena zuwa, Abun mamaki da nakasa ganewa ranar da naje ina son ganin sa saikawai na nemi mutumin da yake taimaka min na rasa wayarsa ma ta dena shiga da na tambaya sai akace min yadena aiki agun baji dadin labarin ba shikenan  yanzu na dena ganin sa tundaga lokacin inde naje bana samun mafita tun ina zuwa ko zan samu wata hanyar da zanshiga bana samu har na hakura na fawwalawa Allah nadena zuwa, Bayan su Ameesha sun kammala makarantar su ta primary zasu shiga secondary sai nace ita tadena zuwa sai nasamu kudi saboda makarantar da tsada sosai kuma bana so nasakata ina biya afara zargina akan wayake bani kudin da nake biya mata shiyasa nace ta dakata kafin inyi tunani insamo mafita amma yarinya sai tasakamin kuka saboda tana mugun son karatu nayi nayi tayi hakuri akan banda kudi amma ita bata fahimtaba saboda bata cikakken hankali akwai yarinta akanta haka kullum sai tasakani agaba da kuka ita sai nasaka ta makaran ta gashi Azeema zata wuce ta tun ina kulata ina rarrashin ta har nadena, Wataran ina zaune kwatsam ta shigo da gudun tana ta faman sakin murmushi take har saida na tambaye ta lafiya tace albishirina nace mata goro tace ai tasamu aiki zata ringayin wanke wanke ana biyan ta kuma matar gidan tace ma zatana biya mata kudin makaran ta ko nawane raina yabaci dajin batunta sai nace ba inda zata aikatau tace meyasa nace kawai saboda ta kare mutuncin ta wasu basu da mutunci ko kadan gwara ta zauna batayi karatun ba inde sai tayi aiki a qarqashin wani to bazata taba karatun ba sosai tayi kuka da har saida ta kwana ta tashi bata dawo daidai ba ganin hakan yasa na shiga rarrashin ta na bata hakuri akan in sha Allah zan saka ta da kudina tabari sai na tara sai tafara zuwa tace to kawai amma bawai dan ta hakura ba tundaga ranar sai naga ta canza bata da walwala kullum tana cikin kunci ganin hakan yasa kawai na yanke shawarar gwara kawai inbarta tundade har zuwa lokacin bansamu kudin ba kuma bana son na taba wani abun daga abun mahaifinta gashi kuma yagayamin insaka ta makaranta tasamu ilimi sosai hakanne yasa kawai nasame ta nace nabarta taje tafara amma duk sanda nasamu kudi zata dena zuwa ranar naga murna kamar me tundaga nan tafara aiki a wani gida makotanmu kuma suna biya mata kudin makarantar da duk wani abu da ake bukata suna biya mata bata da matsalar a bangaren karatun ta saidai tana fuskan tar takura abangaren matar gidan da kuma yarinyar gidan basu da mutunci har dukan tama sunayi amma ita bata jin hakan burinta kawai karatun ta inde zasu biya mata bata damuwa da dukansu ko zagin da cin mutuncin ba irin wanda basa mata tun tana boye min har nafara fahimta kuma nayi nayi ta dena amma batajin magana saboda taurin kanta abun da sukayi mata na aarshene yasa nace baza ta qara zuwa ba shine kuma sanadin haduwar su da Aliyu saboda matar da ze aura agidan take yana zuwa gidan anan suka saba da Ameesha har takai ga yasan abun da take fuskanta agidan shiyasa yace inbashi zai dauke ta ta komo hannun sa ta dawo gidan su da zama ni kuma nace bazan basa ba saboda banyarda dashi ba a lokacin saida nagade da gaske yake har yaje ya taho da mahaifiyar sa kuma naga nasanta ta taba taimakona shiyasa kawai na amince dasu akan zamu bisu, Ranar da zamu tafi itace ranar da mutanan suka sake dawowa wajena akan sun gane yarinyar wajena yar sameer ce bansan wayaga ya musuba bansan ya akai suka gane ba nabasu hakuri akan su rabu da ita zan basu duk abun da sukeso amma basu ji hartakai ga sunyi mata abun da yayi sanadin kwanciyar ta a asibitin ku taqarasa fada tare da nuna su da yatsa sannan tace to kunde ji ko mu suwaye kuma mahaifin Ameesha yana raye mijina kuma bansani ba yana raye ko baya raye takaddu kuma da koman sa da ya mallaka har yanzu suna gurina basu samu damar karba ba kuma basu dena bibiyata ba nasan yanzu haka basu san Ameesha na raye ba sundauka ta mutu bansan me muka tsare musu ba haryanzu kuma bangane suwaye ba saidai tunda gaku kinji sai muhadu ku taimaka min mugano ko suwaye Amma sai munyi ahankali sai munbi kmai a sannu saboda ba qaramin shirine da suba kuma abun lurar ma ba mutum daya bane suma duk yan aikene a kwai wanda yake sakasu  amma gano ko waye ba qaramin aiki bane sai munshirya muma shiri ba dan qarami ba shiru tayi tana jiran jin amsarsu, Amma shiru falon ya dauka babu wanda yabiya budar baki yayi magana kowa da abun da yake sakawa da yanda zasu bollowa lamarin da tunanin suma gabadaya ya dauke basu san wane irin tunani zasuyi ba akan wannan lamarin da suke jinsa kamar almara kamar ta tsuniya shiru bakajin qarar komai sai kukan Ameesha da take jikin Ammi a kwance tana faman shashshekar kuka kamar ranta zai fita tunda aka fara bada labarin take kuka dan wasu magangnun ma sama sama take jinsu bakomai take fahimta ba dan tayi alaqawarin ko kowa be tsaya mata ba sai ta dauke fansa da kanta da hannun ta duk wanda da sa hannunsa aka kashe mata mahaifiya sannan ake azabatar da mahaifinta baza ta barsba da halin da aka jefa rayuwarta da ta sauran bayin Allah da basuji ba basu gani ba bazata taba yafe musu ba kuma saita dauki fansa akai da kanta wannan alqawari ta daukarwa kanta......... Finally yaude dadda tagama bada labari yanzu wasa zai fara da zafi zafi kowa sai ya gyara zama dan ganin yanda za afara wasan [4/27, 9:12 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿5&6 Bismilah.......✍ ____________*AZEEMA*         Ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi saurin sunnar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannun ta wani bafade ya daka mata tsawa da cewa ke zonan dan ubanki daga ina kike wacece ke jiki ma kyarma ta daga qafa da kyar amma sai taji takasa tafiya saida ya qara dakama ta wata tsawar bata san lokacin da ta qaraso gurin sa ba zubewa tayi a wajen sai kawai ta fashe da kuka shide sarki tare da wasu mutanen har sunyi gaba saura mutum biyu awajen, cikin kuka tace dan Allah kuyi hamuri ni marainiya ce iyayena duk sun mutu shine nazo nan ataimakamin daya yace to waya baki iznin shigowa ko ance miki nan gidan mabarata ne kai ta girgiza musu tare da cewa a'a ammade na tambaya na shigo me gadi ne yace inzo abani abinci yau kwana na biyu banci komai ba sai ruwa nake shi dan karku koreni ku taimaka min kumin rai bani da inda zan iya zuwa neman taimako da ya wuce nan wanine ya daga hannu zai kifa mata mari akayi saurin dakatar dashi tsayawa yayi tare da juyawa danganin me maganar duk dade daman yagane muryar Amma ce (maman 'yan biyu) itace ta qaraso wajen tace me nake gani haka wannan 'yar yarinyar zaka daka tafada tare da saka hannu ta dago da Azeema tsaye tace yarib me yake tafe dake nanmade cike da kuka tayi mata bayanin abun da yakawota bayan Amma nagama jin labarin nata sai tacewa muta nan suje kawai suka juya sukatafi itakuma sai tace to ya isa haka share hawayen ki zan taimaka miki kinzo inda ake taimako zo muje tafada tare da ruqon hannun ta suka fara tafiya, ran Azeema fari tas dan ji take kamar ta kama tsalle awajen saboda murna da kyar take iya riqe murmushin da yakeson kwace mata dadi be gama cika ta ba saida ta ganta acikin falon Amma anzaunar da ita akan kujera wani irin farin cike ne yasake lullubeta wanda duk son dannewar ta idan ka qura mata ido sai ka fahimci tana cikin farin ciki  bayan ta zaunar da ita sai takira wata jakadiya tace ga wannan yarinyar nan kije da ita dakinki tayi wanka kisa ma mata kayan da zata saka sannan kibata abinci taci ta qoshi sai ki kawo min ita zamuyi magana da sauri jakadiyar ta amsa da to tare da cewa Azeema tazo su tafi tashi tayi tabi bayan ta suka bi wata hanya suka bar falon, Amma zama tayi a falon tana jiransu ta tausayawa yarinyar  kuma hakan nan taji jinin ta ya hdu da na yarinyar yarinyar ta kwanta mata arai tana gurin bata tashiba har suka gama abun da zasuyi suka dawo falon, Jikin ta sanye da wani yadi me dan ado sun mata kyau saidai kuma sunyi mata yawa sosai kana ganin zakasan ba natabane kusa da Amma ta dawo ta zauna a qasan qafafun ta tace gani saida Amma tagama qare mata kallo sannan tace tashi ki zauna anan ki saki jikin ki kisa aranki kamar agindan ku kike kije ki kwanta zuwa dare zan nemeki domin in gabatar dake awajem wasu mutanan  sannan kema ina bukatar qarin bayani daga gare ki Azeema tace in Allah ya yarda nagode sosai Allah ya biyaki da gidan aljanna Allah yasaka da alkjairi bansan da wane baki zanyj amfani dashi wajen gode miki ba domin kimga ma yi min komai nadade ina yawo a bola ni kadai bani da kowa bansan kowa ba amma yanzu gashi lolaci daya nasamu gatan da ban taba thnani zan sameshi ba a rayuwata na dauka ahaka zan qare rayuwata har in mutu ashe akwai wannan ranan ashe zan samu wata uwar sai kawai ta fashe da kuka kamar gaske (lol😂) sosai Amma taji taqara bata tausayi kuma taji ta yarda da ita rarrashin ta ta shiga yi tace ya isa haka kishare hawayenki kidena tuna baya abun da ya wuce ya riga da ya wuce ba ason ana tuna abun da yariga ya wuce kinji ni kai ta daga mata sannan a hankali ta qara furta na gode, Amma ce tacewa jakadiyar ja hannun ta kuje ta kwanta ki qara kwantar mata da hankali har sai kinga tayi bacci jakadiya tace to kawai amma ita yarinyar ko kadan bata kwanta mata ba dan ba yanda zatayi ne amma da ko kallon inda take bazatayi ba wai ta rarrasheta za aga rarrashi kuwa hannun ta ta kamo suka tafi suna zuwa dakin ta saketa tace gashi nan inkinga dama ki fashe ma ba ruwana da kukan ki kitayi tana gama gadar haka ta gita daga dakin bata san maganar ta ba ko a kwalar rigarta tana ganin ta fitan ma sai kawai tafara tsallen murna har da dan taka rawa sannan ta fada kan katifar waccen matar da ta fahimci bata da mutunci zaman su bazauyiyu ba ta dadin rai amma ita ba itace agaban ta ba har ta kwanta sai kuma tayi sauri ta tashi ta shiga bandaki tasaka saqata sannan ta zaro wayar ta takira saleem aikwa bugu daya kamar jira yake yadaga kiran nata tare da cewa hello auta itamurya qasa qasa tace yayana ya kk har kaje gida yaca a'a na wuce aiki gashima nakasa aikin sai faman tunaninki nake kinshiga gidanne tace eh yay wlh kama dena tunani nasamu gurin zama nande ta kwashe komai ta bashi labari shima yaki dadin jin batasha wata wahala ba sannan yace keda me yakaiki kiran sunana da sarki ya sa ankoreki tace yaya wlh baza ka ganeba kuna kama sosai ne amma watakil ko dan nayi kewarka ne yasa naga kuna kamar yace ai hakanne ma a ina zakiga me kama dani agidan sarauta mu da ko digo bamu da alaqa da  sarauta bare ace ko jinine yasa kamar kawaide idon kine yake miki gizo tace eh nima abun da nayi tunani kenan gashi nakusa jawowa a min dukan tsiya a koroni Allah ya taimakeni ya kawo min baiwar Allah nan wallahi tana da mutunci sosai saleem yace to Allah yabaki sa'ar cin nasarar abun da kikaje nema Allah yasa yanda kika shiga lafiya Allah ya fito mana dake lafiya  tace Ameen sannan yace bari inkira mama ingaya mata kinsan iya rabuwar mu dake ta kirani yafi sau goma tanaso taji halin dakike ciki tace tode ka kaimata labari me dadi kace ta kwantar da hankalin ta amma fa naga masarautar da girma nasan kafin ma muhadu da baba zan dade kude kawai ku tayani da addu'a Allah yasa inyi nasara kuma Allah yasa kar asirina ya tonu, yace mata In sha Allah ma bawanda zai sani duk tsawon lokacin da zaki dauka har kije kidawo Amma auta makarantar kifa kinga baku dade da komawa ba za a wuce ki karatu da yawa gashi bamusan adadin kwanakin da zaki dauka ba bare inje can makarantar in fada musu ko kina ganin ba matsala saida ta dan numfasa sannan tace yaya kar ka damu da karatuna karatu zai jira ni duk sanda nayi niyar yi zanyi amma wannan damar ita kadaice mafita agaremu bamu da hanyar da ta fita idan muka bari ta kubuce mana shikenan kamar munrasa mahaifin mune har abada dan haka ka ajiye komai agefe batun karatuna ka kamanta dashi duk daren dadewa indai da raina da lafiyata zan yishi karkadamu da rashin yina yanzu kaji yayana, to shikenan auta Allah yataimakeki yabaki ikon cika abun dakikai niya zan gaya mata duk yanda mukai dake sai anjima karfa kibari akamaki da waya kinsan dole zargi ya shigo indai aka ganki da ita bare kuma aji kina waya shikenan ba wanda zai qara yarda dake, eh hakane kuma yanzuma  ai ina bandaki kuma dakin ba kowa sai anjima kar matar tadawo ta kamani nasan bazata rufan asiri ba dan na fahimce bata batason zamana tunda ta fara ganina anjima ma idan nasamu lokaci naga ni kadaice zan kiraka sai ka hadani da mama mugaisa yace to shikenan sai anjima sallama sukayi sannan ta fito daga bandakin gaban tane yafadi ganin matar nan adakin amma bisa ga dukkan alamau kamar bataji me tace ba bade tasani ba tunda taaga hankalin tama yana wani wajen daban kuma yanda take magana ba lalle bane ma aji taba guri tasamu ta zauna sai kuma ta kwanta tayi lamo kamar mejin bacci idon ta kwa a kenkeshe yake ba alamar baci acikin su kawai dai ta tafi duniyar tunani tana tunanin rayuwar da zata fuskan ya na wani lokaci yau gata acikin gidan sarauta a kwanace amatsayin wacce za ataimakawa wacce tayi qarya tashigo gidan sai kuma tafara tunanin yanzu idan asirin ta ya tonufa aka kamata ita makaryaciya ce wane hukunci zasuyi mata ita kadai dai sai tunane tunane take ahaka har bacci barawo ya salallabo ya suya sureta bata farka ba sai wajen qarge uku shima jakadiya ce ta tashe ta daga baccin saboda Amma ce tace tazo ta tasheta sannan ta kawo mata abinci amma da bazata tasheta ba tana farkawa taje tayo alwala tafara yin sallah sannan tazo taci abincinta hankali kwance taci ta qoshi tayi nak sannan ta ture abincin gefe tana so ta tambayi jakadiya zata iya fita amma tana jin tsoro kar ace daga zuwan ta bazata iya bari akirata ba shiyasa kawai ta hakura taci gaba da zama ita kadai shiru ba uhm bare uhm uhm dan zuwa lokacin ma matar har ta gita daga dakin ita kadai ta rage adakin,                 *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*       *AMEESHA* da gudu ta tashi daga kan Ammi ta koma wajen dadda tana zuwa ta rungume ta tare da fashewa da wani kukan cikin kuka tace dadda kiyi hakuri da irin abubuwan danayi miki ashe haka kisha wahala akan iyayena da kuma ni kaina rashin sani yasa har nake yi miki wasu abubuwan dan Allah ki yafe min duk abun da nayi miki bazan qaraba shafa bayanta tayi tare da cewa ya isa haka ni baki min komai ba hasalima ni yakamata in baki hakuri tunda duk ni ce silar dayasa har suka kusan kashe ki baniya yin komai ba akai a'a dadda karma kice haka duk wani qoqari kinyi akaina kuma kina kan yi hannu dadda tasa ta raba ta da jikin ta sannan ta share mata hawayen ta kana tace ya isa haka ki manta da komai yanzu nasamu in tayi in sha Allahu zaki ga mahaifin ki duk inda yake zamu nemo miki shi adaina yi miki gorin mahaifi ko kai ta daga mata tare da cewa dadda to yaushe zan ganshi wlh harna matsu inganshi ashede ina da uba ake cemin bani dashi aikwa yana dawowa gareni zanje innunawa aunty  Rasheeda da mom suganshi sudena zagina dadda tace kwarai kuwa shalelena daga lokacin ba wanda zai qara zaginki akan uba saboda naki ubanma yafi na wasu, ganin de alamaun sun mantama da zaman si agun yasa hajiya yin gyaran murya batare da tace komai ba dagowa sukayi gaba dayan su suna fuskan tar su Ameesha ce ta kalli bossay tace yaya bossay ai zaka kaini wajen aunty Rasheeda ingaya mata ina da mahaifi ko mahaifita kuma tarasu tun ina qarama tana qarasa maganar kuma sai jikin ta yaqara yin sanyi tunawa da yanzufa bata da uwa kenan ita marainiya ce kula da hakan da bossay yayi ne  yasa yayi saurin tashi daga inda yake yakoma kusa da ita yazauna tare da ruqo hannun ta sannan yace karki qara yin kuka yanzu bakiga  nan gurin gaba daya iyayen ki bane dukan su zasu daukeki kamar 'yar cikin su daga yanzu baza ki qara neman wani abu kirasa ba uwa sai wacce kika zabama gasunan ga kuma daddar ki akusa dake itama tamkar uwa take kula dake dan haka karki qarajin ba dadi agame da mahaifiyar ki kiyi mata addu'a kawai kinji meesha na kai ta daga masa tare da dan qaqaro murmushin yake da iyakacin sa kan labba ahakanli tana kallonsa tace thanks shima murmushin ya mayar mata zai qara magana kenan Ammi tayi sairin  katsesu da cewa yanzude komai ya kusan zuwa qarshe kamata yayi mu tattauna akan yanda za abullowa al'amarin ko bahaka ba hajiya, hajiya tace eh hakane gwara asan abunyi yanzu ku yakuke ganin za ayi duk kunyi shiru ba wanda yace komai  tafada tana kallon su shettima shiru sukayi sai daga bisani sannan shettima yace hajiya ni wlh bansan ma mezan ceba dan wlh kaina yagama daurewa gabadaya akan wannan lamarin tace yama kunce tunda kukazo kuka tambaya aka baku labari ai dole ku tsaya tsayin daka ganin komai ya daidaita tunda kune maza daman mace bazata iya ba dole saida namiji aciki tana kaiwa qarahen maganar ta maida kanta kan SAM da yayi zurfi cikin tunani dan hankalin sama gaba daya ba akansu yake ba saida hajiya ta tabashi tace to kai kuma fa me zakace akan wannan labarin ya kake ganin za ayi dan girgiza kansa yayi tare da maida hankalin sa gareta sannan yace tunanin da nakeyi kenan inason yin dogon nazari akan maganganun ta kubamu lokaci zamuyi shawara muga ta ina yakamata mufara Ammi tace to hakan ma yayi daman dole sai anyi dogon nazari akai hajiya tace hakane wlh abunne duk wani iri danni labarin ma ba komai na fahimta ba kafin ingama tantance wannan sai inji wani abun da yafi nabaya abunde sai ahankali , Sam ne yace kar kudamu kubar komai a hannun mu zamuyi komai  maida dubansa yayi ga dadda da itama hankalin ta na kansu sannan yace yauwa dada kike ko dady hararar sa tayi tace kaifa matsalata daki kenan naga alamar baza mushirya dakaiba ka rainani wlh to kairani da hadizatu na kawai kai tsaye da ka tsaya kana lalata min suna yanzu inbanda abu irin naka ina sunan dadda yayi kama da dada  ko dady kanade sane kawai daman dan kasani magana ne  shiyasa kafadi haka to ka kyauta banza yayi da ita be tanka mata ba saida yaji tayi shiru sannan yace what ever de ni banda lokacinki kinajina tambayoyi zan miki tace to inajinka dan ta fahimci kamar yana da miskilanci be fiya zama ana jayayyar magana dashi ba.........✍ ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿5&6 Bismilah.......✍ ____________*AZEEMA*         Ganin duk sun zuba mata ido yasa tayi saurin sunnar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannun ta wani bafade ya daka mata tsawa da cewa ke zonan dan ubanki daga ina kike wacece ke jiki ma kyarma ta daga qafa da kyar amma sai taji takasa tafiya saida ya qara dakama ta wata tsawar bata san lokacin da ta qaraso gurin sa ba zubewa tayi a wajen sai kawai ta fashe da kuka shide sarki tare da wasu mutanen har sunyi gaba saura mutum biyu awajen, cikin kuka tace dan Allah kuyi hamuri ni marainiya ce iyayena duk sun mutu shine nazo nan ataimakamin daya yace to waya baki iznin shigowa ko ance miki nan gidan mabarata ne kai ta girgiza musu tare da cewa a'a ammade na tambaya na shigo me gadi ne yace inzo abani abinci yau kwana na biyu banci komai ba sai ruwa nake shi dan karku koreni ku taimaka min kumin rai bani da inda zan iya zuwa neman taimako da ya wuce nan wanine ya daga hannu zai kifa mata mari akayi saurin dakatar dashi tsayawa yayi tare da juyawa danganin me maganar duk dade daman yagane muryar Amma ce (maman 'yan biyu) itace ta qaraso wajen tace me nake gani haka wannan 'yar yarinyar zaka daka tafada tare da saka hannu ta dago da Azeema tsaye tace yarib me yake tafe dake nanmade cike da kuka tayi mata bayanin abun da yakawota bayan Amma nagama jin labarin nata sai tacewa muta nan suje kawai suka juya sukatafi itakuma sai tace to ya isa haka share hawayen ki zan taimaka miki kinzo inda ake taimako zo muje tafada tare da ruqon hannun ta suka fara tafiya, ran Azeema fari tas dan ji take kamar ta kama tsalle awajen saboda murna da kyar take iya riqe murmushin da yakeson kwace mata dadi be gama cika ta ba saida ta ganta acikin falon Amma anzaunar da ita akan kujera wani irin farin cike ne yasake lullubeta wanda duk son dannewar ta idan ka qura mata ido sai ka fahimci tana cikin farin ciki  bayan ta zaunar da ita sai takira wata jakadiya tace ga wannan yarinyar nan kije da ita dakinki tayi wanka kisa ma mata kayan da zata saka sannan kibata abinci taci ta qoshi sai ki kawo min ita zamuyi magana da sauri jakadiyar ta amsa da to tare da cewa Azeema tazo su tafi tashi tayi tabi bayan ta suka bi wata hanya suka bar falon, Amma zama tayi a falon tana jiransu ta tausayawa yarinyar  kuma hakan nan taji jinin ta ya hdu da na yarinyar yarinyar ta kwanta mata arai tana gurin bata tashiba har suka gama abun da zasuyi suka dawo falon, Jikin ta sanye da wani yadi me dan ado sun mata kyau saidai kuma sunyi mata yawa sosai kana ganin zakasan ba natabane kusa da Amma ta dawo ta zauna a qasan qafafun ta tace gani saida Amma tagama qare mata kallo sannan tace tashi ki zauna anan ki saki jikin ki kisa aranki kamar agindan ku kike kije ki kwanta zuwa dare zan nemeki domin in gabatar dake awajem wasu mutanan  sannan kema ina bukatar qarin bayani daga gare ki Azeema tace in Allah ya yarda nagode sosai Allah ya biyaki da gidan aljanna Allah yasaka da alkjairi bansan da wane baki zanyj amfani dashi wajen gode miki ba domin kimga ma yi min komai nadade ina yawo a bola ni kadai bani da kowa bansan kowa ba amma yanzu gashi lolaci daya nasamu gatan da ban taba thnani zan sameshi ba a rayuwata na dauka ahaka zan qare rayuwata har in mutu ashe akwai wannan ranan ashe zan samu wata uwar sai kawai ta fashe da kuka kamar gaske (lol😂) sosai Amma taji taqara bata tausayi kuma taji ta yarda da ita rarrashin ta ta shiga yi tace ya isa haka kishare hawayenki kidena tuna baya abun da ya wuce ya riga da ya wuce ba ason ana tuna abun da yariga ya wuce kinji ni kai ta daga mata sannan a hankali ta qara furta na gode, Amma ce tacewa jakadiyar ja hannun ta kuje ta kwanta ki qara kwantar mata da hankali har sai kinga tayi bacci jakadiya tace to kawai amma ita yarinyar ko kadan bata kwanta mata ba dan ba yanda zatayi ne amma da ko kallon inda take bazatayi ba wai ta rarrasheta za aga rarrashi kuwa hannun ta ta kamo suka tafi suna zuwa dakin ta saketa tace gashi nan inkinga dama ki fashe ma ba ruwana da kukan ki kitayi tana gama gadar haka ta gita daga dakin bata san maganar ta ba ko a kwalar rigarta tana ganin ta fitan ma sai kawai tafara tsallen murna har da dan taka rawa sannan ta fada kan katifar waccen matar da ta fahimci bata da mutunci zaman su bazauyiyu ba ta dadin rai amma ita ba itace agaban ta ba har ta kwanta sai kuma tayi sauri ta tashi ta shiga bandaki tasaka saqata sannan ta zaro wayar ta takira saleem aikwa bugu daya kamar jira yake yadaga kiran nata tare da cewa hello auta itamurya qasa qasa tace yayana ya kk har kaje gida yaca a'a na wuce aiki gashima nakasa aikin sai faman tunaninki nake kinshiga gidanne tace eh yay wlh kama dena tunani nasamu gurin zama nande ta kwashe komai ta bashi labari shima yaki dadin jin batasha wata wahala ba sannan yace keda me yakaiki kiran sunana da sarki ya sa ankoreki tace yaya wlh baza ka ganeba kuna kama sosai ne amma watakil ko dan nayi kewarka ne yasa naga kuna kamar yace ai hakanne ma a ina zakiga me kama dani agidan sarauta mu da ko digo bamu da alaqa da  sarauta bare ace ko jinine yasa kamar kawaide idon kine yake miki gizo tace eh nima abun da nayi tunani kenan gashi nakusa jawowa a min dukan tsiya a koroni Allah ya taimakeni ya kawo min baiwar Allah nan wallahi tana da mutunci sosai saleem yace to Allah yabaki sa'ar cin nasarar abun da kikaje nema Allah yasa yanda kika shiga lafiya Allah ya fito mana dake lafiya  tace Ameen sannan yace bari inkira mama ingaya mata kinsan iya rabuwar mu dake ta kirani yafi sau goma tanaso taji halin dakike ciki tace tode ka kaimata labari me dadi kace ta kwantar da hankalin ta amma fa naga masarautar da girma nasan kafin ma muhadu da baba zan dade kude kawai ku tayani da addu'a Allah yasa inyi nasara kuma Allah yasa kar asirina ya tonu, yace mata In sha Allah ma bawanda zai sani duk tsawon lokacin da zaki dauka har kije kidawo Amma auta makarantar kifa kinga baku dade da komawa ba za a wuce ki karatu da yawa gashi bamusan adadin kwanakin da zaki dauka ba bare inje can makarantar in fada musu ko kina ganin ba matsala saida ta dan numfasa sannan tace yaya kar ka damu da karatuna karatu zai jira ni duk sanda nayi niyar yi zanyi amma wannan damar ita kadaice mafita agaremu bamu da hanyar da ta fita idan muka bari ta kubuce mana shikenan kamar munrasa mahaifin mune har abada dan haka ka ajiye komai agefe batun karatuna ka kamanta dashi duk daren dadewa indai da raina da lafiyata zan yishi karkadamu da rashin yina yanzu kaji yayana, to shikenan auta Allah yataimakeki yabaki ikon cika abun dakikai niya zan gaya mata duk yanda mukai dake sai anjima karfa kibari akamaki da waya kinsan dole zargi ya shigo indai aka ganki da ita bare kuma aji kina waya shikenan ba wanda zai qara yarda dake, eh hakane kuma yanzuma  ai ina bandaki kuma dakin ba kowa sai anjima kar matar tadawo ta kamani nasan bazata rufan asiri ba dan na fahimce bata batason zamana tunda ta fara ganina anjima ma idan nasamu lokaci naga ni kadaice zan kiraka sai ka hadani da mama mugaisa yace to shikenan sai anjima sallama sukayi sannan ta fito daga bandakin gaban tane yafadi ganin matar nan adakin amma bisa ga dukkan alamau kamar bataji me tace ba bade tasani ba tunda taaga hankalin tama yana wani wajen daban kuma yanda take magana ba lalle bane ma aji taba guri tasamu ta zauna sai kuma ta kwanta tayi lamo kamar mejin bacci idon ta kwa a kenkeshe yake ba alamar baci acikin su kawai dai ta tafi duniyar tunani tana tunanin rayuwar da zata fuskan ya na wani lokaci yau gata acikin gidan sarauta a kwanace amatsayin wacce za ataimakawa wacce tayi qarya tashigo gidan sai kuma tafara tunanin yanzu idan asirin ta ya tonufa aka kamata ita makaryaciya ce wane hukunci zasuyi mata ita kadai dai sai tunane tunane take ahaka har bacci barawo ya salallabo ya suya sureta bata farka ba sai wajen qarge uku shima jakadiya ce ta tashe ta daga baccin saboda Amma ce tace tazo ta tasheta sannan ta kawo mata abinci amma da bazata tasheta ba tana farkawa taje tayo alwala tafara yin sallah sannan tazo taci abincinta hankali kwance taci ta qoshi tayi nak sannan ta ture abincin gefe tana so ta tambayi jakadiya zata iya fita amma tana jin tsoro kar ace daga zuwan ta bazata iya bari akirata ba shiyasa kawai ta hakura taci gaba da zama ita kadai shiru ba uhm bare uhm uhm dan zuwa lokacin ma matar har ta gita daga dakin ita kadai ta rage adakin,                 *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*       *AMEESHA* da gudu ta tashi daga kan Ammi ta koma wajen dadda tana zuwa ta rungume ta tare da fashewa da wani kukan cikin kuka tace dadda kiyi hakuri da irin abubuwan danayi miki ashe haka kisha wahala akan iyayena da kuma ni kaina rashin sani yasa har nake yi miki wasu abubuwan dan Allah ki yafe min duk abun da nayi miki bazan qaraba shafa bayanta tayi tare da cewa ya isa haka ni baki min komai ba hasalima ni yakamata in baki hakuri tunda duk ni ce silar dayasa har suka kusan kashe ki baniya yin komai ba akai a'a dadda karma kice haka duk wani qoqari kinyi akaina kuma kina kan yi hannu dadda tasa ta raba ta da jikin ta sannan ta share mata hawayen ta kana tace ya isa haka ki manta da komai yanzu nasamu in tayi in sha Allahu zaki ga mahaifin ki duk inda yake zamu nemo miki shi adaina yi miki gorin mahaifi ko kai ta daga mata tare da cewa dadda to yaushe zan ganshi wlh harna matsu inganshi ashede ina da uba ake cemin bani dashi aikwa yana dawowa gareni zanje innunawa aunty  Rasheeda da mom suganshi sudena zagina dadda tace kwarai kuwa shalelena daga lokacin ba wanda zai qara zaginki akan uba saboda naki ubanma yafi na wasu, ganin de alamaun sun mantama da zaman si agun yasa hajiya yin gyaran murya batare da tace komai ba dagowa sukayi gaba dayan su suna fuskan tar su Ameesha ce ta kalli bossay tace yaya bossay ai zaka kaini wajen aunty Rasheeda ingaya mata ina da mahaifi ko mahaifita kuma tarasu tun ina qarama tana qarasa maganar kuma sai jikin ta yaqara yin sanyi tunawa da yanzufa bata da uwa kenan ita marainiya ce kula da hakan da bossay yayi ne  yasa yayi saurin tashi daga inda yake yakoma kusa da ita yazauna tare da ruqo hannun ta sannan yace karki qara yin kuka yanzu bakiga  nan gurin gaba daya iyayen ki bane dukan su zasu daukeki kamar 'yar cikin su daga yanzu baza ki qara neman wani abu kirasa ba uwa sai wacce kika zabama gasunan ga kuma daddar ki akusa dake itama tamkar uwa take kula dake dan haka karki qarajin ba dadi agame da mahaifiyar ki kiyi mata addu'a kawai kinji meesha na kai ta daga masa tare da dan qaqaro murmushin yake da iyakacin sa kan labba ahakanli tana kallonsa tace thanks shima murmushin ya mayar mata zai qara magana kenan Ammi tayi sairin  katsesu da cewa yanzude komai ya kusan zuwa qarshe kamata yayi mu tattauna akan yanda za abullowa al'amarin ko bahaka ba hajiya, hajiya tace eh hakane gwara asan abunyi yanzu ku yakuke ganin za ayi duk kunyi shiru ba wanda yace komai  tafada tana kallon su shettima shiru sukayi sai daga bisani sannan shettima yace hajiya ni wlh bansan ma mezan ceba dan wlh kaina yagama daurewa gabadaya akan wannan lamarin tace yama kunce tunda kukazo kuka tambaya aka baku labari ai dole ku tsaya tsayin daka ganin komai ya daidaita tunda kune maza daman mace bazata iya ba dole saida namiji aciki tana kaiwa qarahen maganar ta maida kanta kan SAM da yayi zurfi cikin tunani dan hankalin sama gaba daya ba akansu yake ba saida hajiya ta tabashi tace to kai kuma fa me zakace akan wannan labarin ya kake ganin za ayi dan girgiza kansa yayi tare da maida hankalin sa gareta sannan yace tunanin da nakeyi kenan inason yin dogon nazari akan maganganun ta kubamu lokaci zamuyi shawara muga ta ina yakamata mufara Ammi tace to hakan ma yayi daman dole sai anyi dogon nazari akai hajiya tace hakane wlh abunne duk wani iri danni labarin ma ba komai na fahimta ba kafin ingama tantance wannan sai inji wani abun da yafi nabaya abunde sai ahankali , Sam ne yace kar kudamu kubar komai a hannun mu zamuyi komai  maida dubansa yayi ga dadda da itama hankalin ta na kansu sannan yace yauwa dada kike ko dady hararar sa tayi tace kaifa matsalata daki kenan naga alamar baza mushirya dakaiba ka rainani wlh to kairani da hadizatu na kawai kai tsaye da ka tsaya kana lalata min suna yanzu inbanda abu irin naka ina sunan dadda yayi kama da dada  ko dady kanade sane kawai daman dan kasani magana ne  shiyasa kafadi haka to ka kyauta banza yayi da ita be tanka mata ba saida yaji tayi shiru sannan yace what ever de ni banda lokacinki kinajina tambayoyi zan miki tace to inajinka dan ta fahimci kamar yana da miskilanci be fiya zama ana jayayyar magana dashi ba.........✍ [4/29, 10:18 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿5&6 Bismilah.......✍ *SAM*      "Tambayar dazan miki yanzu zaki iya gane fuskokin mutanen da suke zuwa wajen ki sannan kuma zaki iya kaimu zaki iya kaimu wajen da yake aiki acan garin da duk wani wanda kikasan yana mu'amala dashi tace eh to nasande wasu amma bansan wasuba jinjina kai yayi sannan yace good amma abangaren kasuwancinsa da yake zuwa kasuwa bashida wani wanda sukafi kusa dashi sosai da har zai iyasanin wani sirrin nashi da har tace babu sai kuma tayi saurin cewa na tuna da akwai wani mutum da yake kulama sa da shagon sa kuma gaskiya bantaba ganinsa ba yanade bamu labarin gaskiya sa da mutuncin sa kuma yace babban mutum ne dan ya girme sa ma bashida kowa yana neman taimako kuma yaga yana da zuciyar nema Kullum zama gansa akasuwar yana dako ko wani aiki idan yayi abiyasa yasiyi abinci shiyasa ya tausaya masa yake basa aiki yana biyansa daga baya kuma sai yazama me kular masa da shagon abunde danasani gane dashi kenan amma bansani ba watakil malam yasanshi nide bansan shiba kuma jinjina kai yasake yi sannan yace shikenan kishirya zamuje can garin gobe zamu fara bincike dadda ta dan gyara zama tace idan muka je tare idon su nakaina dole zasu canza shiri idan suka fahimci tare da wasu nake nide ga shawarata yanda nake gani sai yafi mana sauqi shine ni inkoma gidan dana baro inzauna nasan zasu dawo nema na sannan kuma ina da wayar wani daga cikin su ranar da sukazo na qarshe wani ya ajiyeta akan kayan mu nikuma sai na faki ido na turata qasan wani waje kuma da suka gama dukan Ameesha sai yamanata be neme taba nima namanta da ita saida ga baya naje na dauko yanzu haka tana gurina, shettima mane yace ai wannan ma kadai ya isa yasa akamasu da kinsan da wannan kikatsaya daukota kawai ai basai kinje gidan da zama ba kiyi zamanki anan ko mutum daya aka kama sai ankama gabadayan su yakarasa fada fusakarsa dauke da murmushi dan ayaji dadin abun da tace ta kawo musu hanya me sauke wajen binciken su , Sam ne yace a'a dole sai ta koma gidan da zama tahaka ne zaisa sugane ita kadaice wannan yarinyar ta mutu sannan kuma zasu koma wajen ta idan sukaji ankira daya daga cikin zasu dawo wajen ta mukuma zamu hadata da mai kula da ita duk ranar da yaga sunzo sai yayi gaggawar sanar damu sai azo akamasu inba haka ba to zasudawo cikin gidan nan da binciken su daga nan su gano yarinyar bata mutu ba dukan su na'am sukayi da baya ninsa hajiya tace wannan tunanine me kyau hakan ma yakamata ayi amma ina ne man wata alfarma ni abani yarinyar intafi da ita gidana ta yanda bazasu gano inda take ba ko ya kuka ce Bossay ne yafara cewa ai anan ma baza susan tana nan ba ni zan kula da ita kamar yanda nayi niyya tun farko dan haka dan Allah kuyi hakuri kubarmin ita banason tayi nisa dani shiru sukayi ba wanda yayi magana saida ga bisani Sam da yagama qare musu kallo daga shi har itadin da suke riqe da hannun juna janye idon sa yayi sannan yace a'a kabarta sutafi da ita hakan sai yafi kwanciyar hankali tunda kai kaga yanzu akawai wanda yasanka dan haka bakasan waye ba watakil ma yazo har cikin gidan taganta alhalin kuma baka san shibane kuma baza ka taba kawowa shine ba tunda yace nakusan kusan kane ina ganin tafiyar tata shiyafi dacewa, Ammi ta dora dacewa hakane kuma gwara ta koma din zaman ta anan da matsala bamusan waye zaizo ba tunda bama zargin kowa zai iya shigowar bamusan shibane kuma dole su hadu dan haka nima na goyi bayan hakan hajiya, shide bossay be kuma cewa komai ba dan wani iri yake ji aransa har ga Allah bayaso yaji ance za arabashi da ita har cikin ransa yake ji da ita bazai iya jurar rashinta akusa dashi ba dande Ammi tasa bakine kuma yasan in yaqara magana bazataji dadi ba za tace ya rainasu suna magana yana magana shiyasa kawai yayi shiru ransa duk babu dadi jikinsa duk yayi sanyi kamar ance anrabasa da ita baze qara ganinta ba har abada babu wanda be lura da yanda yanayin sa ya canza ba amma ba wanda yayi magana saboda sums ba yanda suka iya dole abi wannan hanyar itakadai ce mafita, Ameesha ce itama da ta fahimci halin da yake ciki sai taqara damke hannun sa tare da leqa fuskar sa amma sai ya kawar da fusakarsa gefe ahankali ta furta yaya banza yayi da ita be amsaba taqara kiransa sai yadan juyo yakalleta sannan yaqara sauke idon sa tare da fara qoqarin janye hannun sa daga riqon da tayi masa amma sai yaji taqara damkewa taqi saki fuska adan bace yace sakarni mana ganin hakan yasa bata qara cewa komai ba tasakeshi kawai, tashi yayi daga inda  yake kusa da ita sai ya koma inda ya taso ya zauna tare da sunkuyar da kansa dan shikadai yasan me yake ji amma bayaso atafi da ita yafiso koda yaushe su kasance tare amma kawai sunzo zasu rabasu shikenan watakil ma ta manta dashi shi abunma da yafi tsaya masa arai shine zamansu guri daya da shettima ga yaga shima yana kula da ita yana tsoron abun da kanje yadawo a tsakanin su idan suka saba sosai soyayya zata iya shiga tsakanin su shikenan shi yayi dakon banza duk tsawon lokacin da yadauka akanta yanaso tafara sonshi amma yanzu wani zai juyar mata da tunani ta manta dashi jiyayi wani qaton abu yazo ya tokare masa magogaro yunqurawa yayi zai tashi daga wajen da niyar barin falon gaba daya amma sai yaji an dalatar dashi Ammi ce da duk tana kallon abun da yakeyi tasa hannu ta dakatar dashi kallon ta yayi da ido tayi masa alamun kar yatashi zama yayi be tashin ba, Sam duk na lure dashi kuma duk yagane Inda ya dosa amma sai ya basar yace tare da dorawa da cewa yanzu dada ki dauko mana wayar sannan ahadawa wannan yarinyar kayan ta yanzu zamu wuce ina so muje mufara shirye shirye yana sane yafadi haka dan yaga halin da bossay zai shiga aikwa yana rufe baki bossay yace habade yanzu kubari a shiryata a tsanake mana daga nan zuwa sati daya basai ta komaba shima yana rufe baki sameer yace a'a yanzu zamu tafi meye amfanin bari har tsawon sati idan mutum in zaizo zai sanar dakaine ranar da zezo tun kafin ma su ankara da ita tunda yau tazo to yau zata bar sa bossay yace amma ya........Ammi ce ta daga masa hannu da cewa kai wai meyake damun kane ana magana kana cewa ga yanda za'ayi kafimu sanin yanda yakamata ne kai zama gayamana yanda zamuyi mu duk bamusan yanda yakamata ba to kashiga hankalin ka banason shirme I'm sorry yace kawai sannan ya tashi daga wajen ya wuce part din shi be kara tsayawa ko inaba sai akan gadon sa, bawanda ya hanasa tashi duk suka zuba ido suna kallon ikon Allah kowa da abun da yake tunani akan wannan lamarin da suka fahimci ya shiga dadda ce ta miqe taje ta dauko musu wayar takawo masa  Sam yakarba sannan yace kayan nata fa komawa tayi daman tunda sukazo bata bude suba suna ajiye dan haka zuwa tayi ta dauko musu ta kawo musu yana kawowa sam yamiqe yace mu tafi zan duba wayar anjima yanzu ina da uziri agida zamu qara tattaunawa zuwa gobe zan nemeku sannan wancan yaron ma agaya masa ina son ganin sa gobe dadda tace to shikenan Allah yakaimu amma ni yaushe zan koma gidan yace zan gaya miki yanzude ki zauna anan din tace to kutashi mutafi hajiyace ta mike sannan ta kalli Ameesha tace daughter mutafi ko miqewa tayi shettima ne yaje kusa da ita ya ruqo hannunta yace to mutafi dadda ce ta kalleta ganin gaba daya hankalin ta baya kansu inda tunanita yake daban dan ta fahimci ma batajin ma me akecewa tabata tayi tace shalelena ba magana ko sallama ma baza kimin ba haka zaki tafi kibarni sakin shettima tayi ta koma kusa da ita tare da rungumeta amma takasa cemata ko uffan kawai saikuma ga hawaye ya fara fitowa kan fuskarta rabata tayi da jikin ta sannan tasa hannu ta goge mata hawayen tace shikenan kije ai zan ringa zuwa muna gaisawa kinji ko ga waya kuma zamuna gaisawa Allah yayi miki albarka kije itama daddar kawai jurewa take yi amma hawayeni yake son zubo mata dan itama anata bangaren batason arabasun dande ba yanda zatayi  ne shiyasa ta amince da hakan amma badanson ranta ba, Shettima ne yaqara ruqo hannun ta suka yi hanyar waje sai hajiya abayan su sannan Sam abayansu har sunje bakin qofa zasu fita database da gaske tafiyar zasuyi kuma bossay be fito ba gashi basuyi sallama ba tasan kuma idan ta tafi bata neme saba batayi masa adalci ba tsayawa tayi cak da  tafiyar datakeyi suma dakatawa sukayi suna kallon ta shettima be ya kalleta yace ya akayi ne bata tanka masa ba  kawai sai ta kwace hannun ta daga riqon da yayi mata basu ankara ba kawai sukaga ta kwasa aguje duk tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah gun da taga bossay ya nufa nan ta nufa aguje tana zuwa ta tura qofar dakin tashiga kwance tagansa kan gado yayi ruf da ciki ya kifa kansa tsaya wa tayi tana bin bayan sa da kallo qarasawa tayi gaban gadon amma har lokacin be motsaba duk da yaji shigowar mutum, yayana ta kira sunan sa ahankali still de be motsaba duk da yana jinta kuma yagane itace, tsugun nawa tayi agabansa tasake kiran sunan sa  tace yaya wai me yake damunka ne zan tafi baka fito munyi sallama ba ko baka da lafiya ne banza yayi da ita be tanka mata ba, dan dukansa tayi  abaya dan atunanin ta ko bacci yake, dan motsawa yayi kadan sannan yace ni kirabu dani dan Allah kar ki takuran, taji haushin maganar da yace dan haka kawai sai ta juya zata fita hartayi taku daya zata bar wajen taji ya ruqo hannun ta dakatawa tayi da tafiyar tare da juyowa tana kallon sa shima kallon ta yake, zubawa juna ido sukayi kowa yakasa janyewa daga kallon dan uwansa jawota yafara yi zuwa kansa..........✍ Kuyi hakuri ba yawa da babu gwanda ba dadi [5/5, 10:10 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿7&8 Bismilah.......✍ *Ameesha & bossay*    "Suna kallon juna yanajanta ahankali zuwa jikin sa ahaka har ta fado jikin sa rungumeta yayi tsam ajikin sa zata kwace jikin daga garesa sai yarada mata akunne yace pls just a some minutes don't leave me yaqara rungumeta sosai kamar zai mayar da ita cikin jikin sa tunda taji hakan bata qara yunqurin tashi ba tunda yabukai hakan zata zauna ko wane lokaci zai dauka inde hakan zaisa ya kwantar da hankalin sa har suyi sallama kuma itama anata bangaren hakan sai yayi mata dadi saitaji batason su rabu din lamo tayi ajikin sa daga nan kuma bawanda yaqara magana acikin su shiru sukayi suna sauraron bugawar zuciyoyin junan su babu wanda yasake motsi kowa anasa bangaren da abun da yake kiyastawa aransa, hannun sa yasaka abayanta yafara shafawa ahankali yana dan bubbuga bayan ta kamar me son rarrashin ta taji dadin hakan kuwa ba zato ba tsammani yaji saukar numfashin ta alamu hartayi bacci shiru yayi yana sauraron ta dayan hannun sa yasaka yayi mata cover tare da lumshe idon sa shima saboda yanayin yayi masa dadi besan lokacin da bacci yadauke sa a, Acan falo kuwa kowa yatsaya yana jiran fitowar sa amma shiru shiru basu fito ba Ammi ce tace bari inkirasu kunga har yanzu shiru basu fito ba Sam ne da ransa yagama baci da bata masa lokacin da tayi ya dakatar da ita yace bari inje yana kaiwa nan ya nufi dakin da yaga sun nufa nan shima yanufa kwankwasa qofar yayi amma sai yaji shiru tura qofar kawai yayi ya shiga turus yayi ya tsaya ganin halin da suke ciki kawai ji yayi ransa yaqara baci buga qofar yayi amma sai yaga bawanda ya motsa acikin qarasa wa yayi bakin gadon yatsaya yana binsu da kallo yanda suka wani nannade waje guda watakon saboda tsabar rainin hankali su suna can suna jiran ta amma su sunanan riqe da juna harda ma bacci saboda sun raina mutane ransa in yayi dubu to ya baci gabadaya yama rasa me zaiyi musu ya huce buga fuskar gadon yayi da dan qarfi, ahankali bossay ya shiga bude idon sa yana budewa ya saukesu akan sameer dake kansu a tsaye shima nasa ran baci yayi akan me zaizo ya tsaya musu akai kuma yasan abun da yakawo sa zai rabasa ne da ita shiyasa yaji haushin zuwan nasa suna cikin kwanciyar hankali suna cikin baccin su me dadi zaizo ya katse musu, Sam ne ya katse masa tunanin sa da cewa malam katasheta zamu tafi kunzo kuna batawa mutane lokaci budar bakin bossay sai yace ina ruwanka da ita bakaga bacci take ba meyasa zan tasheta zaku iya tafiya idan ta tashi zan kawota dakaina anjima wani irin banzan kallo sam ya watsa masa sannan yace ka shiga hankalin ka kasan dawa kake magana anan bada sa'anka kakeba bana daukan raini zan iya yimaka duk abun danaga dama ba uban da ya isa yahanani katasheta nace baza ayi yanda kake sodin ba abun da muka shirya shi za ayi kaji nafada maka, be tanka masa ba ya yunqura ya janyeta daga jikinsa ya murgina ya kwantar da ita harda ja mata abun rufa, shikam sameer yana tsaye ya harde hannu wansa akan qirjinsa yana jiran yaga iya gudun ruwansa bayan yagama gyara mata kwanciyar sannan yajuyo garesa ido cikin ido yakallesa tare da nunasa da nunasa da yatsa sannan yace wai kai dan Allah me kake daukan kanka ne dan kana ganin ka agidan sarauta shine kake tunanin sai kataka kowa yanda kake so kowa sai yabika sai yayi abun da kakeso kana ganin idan kataba ni kataba banza to kayi duk abun da kaga dama wlh bazan tasheta ba sai sanda ta tashi nace kuje zan kawota amma kunqi ji sai kuyi ta zama nibansan meyasa kuka takurawa kanku akan sai kuntafi da ita ni banma yarda dakuba daman bakace zaka dauki fansar abun da tayi maka ba wayasani ma ko duk wayon ka cutar da itane shiyasa zaku wani ce abaku kutafi da ita ni sai yanzuma na tuna to wlh amma fasa bakun kuyi tafiyar ku babu inda zata tana nan awajena zamu zauna tare ba abun da zai faru dan Allah malam ka fitar min daga daki karka qara batamin rai yaqarasa maganar tare da jan tsaki yana gama tsakin yaji tas a fuskar sa ya kwashe shi da mari sannan ya ya murde hannun da yake nuna sa ranshi yabaci sosai da magan ganun da yafada masa idonsa har sun canza kala saboda tsabar yanda ransa ya baci, dafe kunmatunsa yayi shima cikin bacin rai yace ni kamara yace eh ko zaka ramane yace to wallahi baka mari banzaba hannu yadaga zai rama yayi saurin riqe hannun sa yace kar ka kuskura wai kai baka da hankali wane irin dakikine kai ni zaka mara yace baka da tarbiya wlh idan ka tabani wlh sai na karkarya ka anan yanzu ma kaci sa"a banda lokacin zaman kula ka saboda bakakai matsayin dazesa in tsaya ina ja in ja dakai ba ina da abunyi yana qarasawa ya jefar da hannun sa tare da nufar gadon ya tsugunna ya yaye mayafin rufar da sauri bossay yayi riqe hannun sa cikin sanyin murya dayaga fadan nasa ba inda zai kaisa sai yasauko kamar ba wanda yagama cika baki ba yace dan Allah kayi hakuri ka rabu da ita kar ka tashe ta Wani banzan kallo ya watsa masa da yasa shi dakatawa da abun da yake fada batare da yace masa komai ba baya yaja daga gurin sa ya koma can gefen gadon tare da sadda kansa qasa sannan yace pls ahankali batare da sautin yafito ba amma sarai yajishi sai kawai ya shareshi gaban gadon ya nufa tare da dan bubbuga gefen gadon amma yaga ko alamar motsima batayi ganin tana ta bata masa lokacine yasa shi yaye bargon yakai hannun zai kai mata duka kenan shettima da yake bakin qofa tun dazu yana kallon su ya shigo dakin da sauri ya qaraso gurin ya dakatar dashi yace haba yada haka tunda bacci take ai ba sai ka daketa ba bari in dauketa kawai mu tafi tun dazu mun bar su suna jira kaima kuma Dana shigo kabiye masa memakon kawai ka daukota awucen wajen da tuni munje gida inma bamuje ba mun kusa amma kuntsaya anan yana qarasa maganar ya tsugunna da niyar ya dauke ta amma hannun sa bekai ga taba ta yaji bossay yayi saurin riqe hannun shi rai abace dan shifa yanzu hakan nan yaji yana jin haushin shettiman dan ya lura kamar shima zai iyacewa yana sonta (tab kishi yafara rufewa bossay ido yanzu baya ganin kowa da girma dan kowama haushin shi yakeji musamman shi shettima ji yake kamar idan ta tafi shikenan ta tafi kenan kamar anrabashi da itane har abada, shiyasa yace masa kar kataba ta wlh daga zuwanka zaka wani ce zaka dauketa saboda abun da kake so kenan daman to kabari bari ni zan dauki abata dakaina na hutar dakai kuma wlh daman naga kana rawar qafa akan ta to bari kaji ko taje can dinma tunda agidan ku zata zauna to wlh wlh wlh inde kataba ban yafe ba ko hannun ta banyarda ka sake riqewa ba gaba dayan su da mamaki suke binsa da kallo tsaye shettima yayi yare da nade hannun sa yana kallon ikon Allah sai da yagama, sannan ya dubesa maganganun sa ba qaramin bata masa rai yayi ba betaba tunani haka yakeba saurin kai zuviyarsa nesa yayi saboda shi baya son cecekuce arayuwar sa bayason yawan fada shiyasa alokaci guda yayi saurin kai zuciyar sa nesa,(tab to gaskiya kai nadabanne masu sunan ka basu da shi kana musu zasu mayar kiris suke jira ataba su daman) qara dubansa da kyau sannan yace to naji amma awane gamon kare zaibi liman masallaci meye alaqarka da ita nide alabarin da naji banji ance kaine ubanta ba ko kuma mijin ta nasan su kadai ne zasu iya bani wannan umarnin baya gasu babu Wanda ya isa yakafa min wannan sharaden shima ido cikin ido yakalle sa yace ai kafadi amsar kaima me kace mijin ta ne kadai ya isa ya kafa maka sharadi ko to ni nine mijin ta yafada yana nuna qirjinsa tare da zazzaro ido shi abun ma dariya yaso bashi ganin yanda duk yabi ya tada hankalinsa sai wasu abubuwa yake dashi da begama fahimtar inda ya dosa ba, dan fuzzar da iska yayi daga bakin sa sanna ya kallesa yace Allah ko to yaushe aka daura bamusani ba ya bude baki zaiyi magana kenan sameer dake tsaye takaici yagama cikashi ya daga musu hannu...✍ Kuyi hakuri da wannan dan Allah kuyi min uziri da rashin yin😎 Amma in sha Allah ko ba yawa zanyi qoqari zan ringayi kullum in sha Allah bazan qara tsallake rana ba [5/8, 9:05 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526 Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*                          🅿9&10 Bismilah.......✍ daga musu hannu yayi tare da daka musu tsawa yace enough!!!!!!! kurufewa mutane baki  kunzo kuna abu kamar qananun yara ranshi ba qaramin baci yayi ba musamman bossay jiyake kamar yakama sa yayi masa dan iskan duka haka yakeji kawai yana rabuwa dashine saboda yanzu ba yan dukanne akansa ba amma da tuni ya koya masa hankali dan ya fahimci beda hankali inma yana dashi yana bukatar qarin wani wani wawan tsaki yaja tare da banka musu harara irin kushiga taitayin ku nan, gabadayan su shiru sukayi ba wanda yakara yin magana acikin su, kallonsa ya maida kan Ameesha yaga ita har yanzu baccin ta take hankalinta kwance wani abu yaji yazo masa wuya ya tokaresa duk sai yaji haushin ta saboda  da duk ita tajawo wanann abun gashi ita tabata musu lokaci azuciye yayi kanta da nufun ya kaimata mugun dukan da zaisa ta farka har yakai hannu sai kuma yadakata ko me yatuna kuma oho saikawai ya yaye abun rufar gaba daya sannan yasa hannunsa duka biyu tare da dan rankwafawa kanta zai dauketa kenan kawai sai ta bude idon ta ahankali tana budesu ta saukesu akansa qara waro ido tayi ganin shi dab da ita shikuma duk da yaga ta bude idon amma be daga daga rankwafawar da yayi ba saima qara ynuqurin da yayi zai dauketan sai kawai ta matsa daga kusa dashi sannan tayi saurin ja baya tana hade rai hadi da turo dan mitsitsin bakin ta gaba ashe tun farkon shigowar sa ta farka daga bacci kawai likimo tayi amma duk abun da sukecewa tana jinsu tayi shiru saboda bata son tafiyar amma kalaman bossay ba qaramin tsaya mata arai yayi ba wai miji shi zai aureta abun dabata taba tunani daga garesa ba wai aure sai maimaitawa take aranta kenan daman tunfarko bossay sonta yake bata sani ba ko kuma yanzune yafara bata da wanda zai bata amsa ganin hakan yasakata murginawa dayan bangaren na gadon tare sa zura qafafunta qasa sannan ta miqe batare da ta kalli kowaba ko kuma tayiwa wani magana ba saboda duk haushinsu takeji gaba dayan su hakan nan taji harshi ma bossayn  haushinshi take ji duk datasan kowa ita yake jira amma sai ta wuce wajen qofa kawai ta bude ta fita daga dakin, Sukam kamar wadanda aka kafa agurin duk suna kasa motsawa kawai sunbita da idanu harta qarasa ficewa daga dakin ta bacema ganinsu sannan bossay yayi saurin bin bayan ta daga bisani ma shima shettima yabi bayan su shikam yana gun atsaye kamar gunki saboda tsabar mamakin da yagama kasheshi shi wannan yarinyar zatayiwa haka har yazo zai dauketa amma ta maida su 'yan iska ta tashi tayi ficewar ta karkada kai yayi tare da furta lalle sai na koya miki hankali kwafa yayi kawai sannan shima ya fice daga dakin yana zuwa yaga duk bama sa falon har sun fita daga ciki sunyi waje saboda tana fitowa bata tankawa kowa ba ta nufi waje taje wajen motar ta tsaya tana ciccin magani saikace wacce akayiwa wani abun sai cika take tana batsewa su hajiya kuma daman sun gaji da tsayiwa dan haka suma suna ganin ta fita ba wanda ya dakatar da ita sai ma binta da sukayi abaya sunsan de tunda tafito yanzu suma mazan zasu fito basu kai ga qarasawa wajen ba bossay yabiyo su yana kiran Ameesha amma ko kallon inda yake batayi ba saima juyar dakai da tayi da dan mamaki yaje binta da kallo meyasa ta juyar masa da kai kuma ya kira ta tayi masa shiru leka fuskarta yayi yace baby meesha ya akayi ne bakison tafiya ko kiyi hakiri anfi qarfinane nima bada son raina zaki tafi ba amma kar kidamu koda yaushe zan ringa zuwa inda kike kwanciya ce kawai zata ringa rabamu dake zuwa wani lokaci kuma zan daukeki gaba daya, Ammi ce ta doke masa qeya tace dalla malam rufewa mutane baki banason shashancin banza kadauketa kakai ta gidan uwarka meyasa kai baka jin maganane me kake so kazama dan hade rai yayi yace Ammi ba nan zan kawota ba gidana zankaita ana gama wannan bincikin idan komai ya daidaita za ku aura min ita muje can muyi rayuwar mu mukadai watakil ma mubar muku qasar gaba daya saidai muringakawo muku ziyara  ko baby meesha yafada yana kallon ta kawar dakai tayi batace masa komai ba, riqe baki Ammi tayi zatai magana kenan su sameer suka qaraso wajen yana zuwa kuma ya bude motar yashiga yasa suma sauran duk sukayi saurin shiga amma banda Ameesha da bossay ya riqawa hannu lokacin da take qoqarin shiga motar inda hajiya ta shige bayan motar itama kuma nan zata shiga kamarde ayanda sukazo kallonta yayi sannan ya matso daf da ita yanda bama kowa zai iya jin abin da zece ba sannan  yace ki kulamin da kanki nabaki amanar kanki gobe zanzo tunda safe kai kawai ta daga masa amma bata samu damar basa amsaba zaicigaba da magana Ammi ta daka masa tsawa tace wai kai wani irin yarone sai batawa mutane lokaci kake kasake ta ko kwa sai na saba maka anan gurin nibansan yaushe ka canza ba kazama haka to wallahi inbakai wasaba sai na hana ka zuwa wajen nata kaci gaba dayin abun da kakeyi karkafasa Ammi me nayi to ni banga wani abu da na aikaya ko nafada da baidace ba yafada cin qunan rai tare da sakin Ameesha ya juya yayi tafiyarsa batare da yaqara kallon ta ba kuma tunda yatafi be jiyo ba itama kuma sai takasa shiga motar ta tsaya tana bin bayansa da kallo saitaji duk ba dadi jitake kamar ta kirashi tace yadawo karyatafi amma ba halin yin hakan ba yanda ta iya dole ta hakura tayar da motar da shettima yayi ne yasa ta dawowa cikin hayyacin ta sannan ta shiga motar dadda dake tsaye takasa magana tama zama wani sakaka da ita jikinta duk ya mutu itama bata son tafiyar tata shiyasa ma takasa yimata magana saboda idan tayi zata qara karyar mata da zuciyar ta itakam Ameesha batama kalli inda take saboda gaba daya hankalin ta nakan bossay tana shiga Ammi ta rufe mata murfin motar sannan Ammi ta shiga yimusu Allah kiyaye hanya hajiyace kawai ta amsa mata sannan sukayi sallama yatayar da motar tare da janta baya sai lokacin Ameesha ta dagi kai suka hada ido da dadda jitayi zuciyarta wani iri ganin yanda dadda ta koma kamar zatayi kuka  suna hada ido dadda ta saukar da kanta qasa duk yanda taso dadda ta dago su hada ido amma hakan besamu ba har shettima ya juyar da kan mota suka nufi wajen gate suna zuwa gate man ya bude musu suka fita daga gidan saida su Ammi suka ga fitarsu sannan suka juya suka koma cikin gidan, su shettima suna hawa kan titi Ameesha ta saki wani marayan kuka sosai tasakar musu kuka acikin motar cikin bacin rai Sam yadaka mata tsawa da yasata san yin shiru hajiya ce face aa babana ya isa haka karkasake yimata  same kakeso taji ai dole tayi saboda kewansu gashi anrabata dasu zataje inda batasani ba bata saba zama acan ba kaga dole kwa saitaji ba dadi taqarasa fada tare da  qara jawo Ameesha jikin ta tana rarrashinta da bata baki ahakade akaci sa'a da kyar tayi shiru sai daman shashshekar kukan take tare da sauke ajiyan zuciya atare atare runda yayi shiru kuma motar sai ta dauki shiru ba wanda yakara magana ahaka suka cigaba da tafiya sunzo daidai wani super market hajiya tace wait.. kaga kutsata adan yimata siyayya ai tana rufe baki Sam yace hajiya da kinrabu da ita muje kawai zuwa gobe  sai ko shine sai ya kaita tace to shikenan nan ma shirunne ya biyo baya basu dau loqaci ba suka qarasa gidan bayan yayi horn me gadi ya bude musu sun shiga ya daidaita parking sannan suka firfito sam be fito ba yace wa shettima su wuce asibiti kawai basai sun shiga cikin gidan ba OK  yace masa bayan sungama fita hajiya da Ameesha har sunkai bakin qofama sannan shettima yace hajiya zamu wuce hospital sai mundawo ta dan juyo ta kallesa sannan tace to shikenan sai kundawo Allah ya kiyaye hanya sannan ya shiga cikin motar yaqara tayarwa suka bar gidan.......✍ *kuyi hakuri da wannan daga yaude angama yin typin kadan kadan nadawo gida daga tafiyar danayi in sha Allah zuwa gobe zanyi me yawa*       Assalamu alaikum, kutsaya ku karanta kar ku wuce yana da matuqar muhimmaci agareku. *ILIMI HASKEN RAYUWA* Ina matan aure harma da 'yan mata wadanda basu samu damar yin makarantar islamiya ba ko kuma wadan da sunyi amma yanayi rayuwa yasa sun manmanta da wasu abubuwan to ga dama tasamu akwai mata dayawa wadan da suke cikin wannan halin suna bukatar ilimi kuma wasu suna so amma basusan ta inda zasu fara ba wasu kuma hidimar gida da iyalai bazasu samu damar fita su nema ba, To amma fa kusani hakan ba hujja bace awajen Allah domin acikin wani hadisi ance azaba ta tabbata gawanda be nemi yasani ba kuma ko kasani ma idan baka aiki dashi nan ma azaba zata tabbata agaresa dan haka kutashi kunemi ilimi kar kuzauna da duhun kai ko girman kai ilimi ba ai masa girman kai kitsaya ki fadada iliminki musamman bangaren akdari mata dayawa suna da qarancin ilimi akai, Duba da hakan yasa muka kawo muku hanya mafi sauqi na online class kina zaune a cikin gidan adakin ki azaune ko akwance ma zaki samu duk wani ilimi da kikeso dai dai iyawarki, yar uwa awa nawa kike batawa akan wayarki batare da ki qaru da ita baki koyi komai ba aciki awa nawa kike batawa akan karatun littattafen novel da kalle kalle da basu da amfani, zamu bude group iya mata zamu kawo muku littattafan addini sannan kuma zamu ringa qarin alqur'ani me girma duk surar da baka iya ba za akoya maka duk daga inda kake so zaka koya zamu koya muku baki kodaga alifunne baka iyaba za a koya maka kuma da yardar Allah zaka iya, Ga abubuwan dazamu ringayi kamar haka👇 1_ALQUR'ANI 2,HADISI 3,AKDARI 4,ARABIYYA, 5,SIRATUL NABIYYI 6,NURANIYYA DA dai sauran su duk waddannan abubuwan zaku samesu agarabasa me sauki naira dari ukun ka ta baka ilimi kuma idan kabiya ka ta samu kenan baza ataba cemaka wata yayi ba biya kudi ko shekara nawa zakai saidai idan kai kagaji da nema kace ya isheka domin karin bayani sai ku tuntubemu ta wannan number 08124226526 Pls duk wanda ya karanta yatayamu da share dinsa zuwa group group domin inkai baka ra ayi watakil wani yana da ra,ayi akai kuma be ganiba plss share it [5/9, 11:32 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526 'Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*                          🅿11&12 Bismilah.......✍ Suna qarasawa asibitin kowa ya nufi nashi office din dan gabatar da abun da sukazo yi sam na shiga nasa office din ya wuce dakin sa kai tsaye saida yafara shiga bandakin ciki yayo wanka sanan yafito ya canza kayan da yake ajiyewa aciki sannan yadan bude frige yadakko fresh milk me sanyi ya sha yaji yadan samu nutsuwa sannan yaje wani guri kawai naga yadaga wani labile saiga qofa agurin budeta yayi ya shiga dakine haka dan qararrami ba anan yake ajiye duk wani mahimman abubuwansa dan ba kowa ma yasan da dakin ba gaban wani board dake jikin bango nan yake yadauki makar yafara rubuce rubce ajiki yana yi yana tunani saida yagama rubce duk wani suna da yaji dadda tafa in kuma bata fadi sunan ba to zai rubuta abun da yafaru da kuma abun da akeso agano agun saida ya gama rubuce shi tass da danni wani wani abunma bansan me yarubuta ba shikadai yasan yanda yayi lissafinsa inba ayi maka ma bayani ba cazakayi hauka ya rubuta agurin saida ya tabbatar komai yayi daidai yanda yakeso sannan yafito daga dakin yamaida qofar yarufe kan gadonsa yadawo ya kwanta fuskarsa tana kallon sama yana ta sake nazarin maganganun dadda yana musu dalla dalla sosai ya shiga kogin tunani kamar kuma wanda aka tsikara da allura haka ya tashi zunbur jikin sa yaqara gyarawa sannan yafito daga dakin wayarsa da yabri a office yadauka yakira shettima yace yazo su tafi yana fadar haka yayanke wayar sannan ya fito daga office din yana fitowa suka hadu da shettima tare suka qara fita suka shiga mota suka bar asibitin suna fitowa shettima ya kallesa yace ina mukayi yace gida dan haka direct masarauta suka nufa lokacin da sukaje anfara kiraye kirayen sallah sai kawai suka fara shiga masallaci sukayi sallah kafin suka shiga cikin gidan suna part din momma suka fara shiga suka gasheta sanna suka fito suka nufi part din fulani da sukaje basu sameta ba dan haka kawai sai suka wuce wajen Ammah........ ____________*AZEEMA* tana zaune adakin bata fita daga qarsjede bacci ne ya salallabo ya sureta bata farka ba sai wajen magriba shima jakadiya ce ta tasheta ta watsa mata wasu kaya sannan tace gashinan idan kinyi salla kizo tana nemanki tana kaiwa nan ta qara fita bata jira amsarta ba daukar jakar gana must go tayi ta bude sai taga kayan sawa ne da hijabai harda mayafai yawancin kayan ma duk dogayan rigunane irin na larabawan nan da mayafan su sai riga da sket shima kananu ne harda takalmi da jaka tana kalla tana ta faman sakin murmushi saboda ba qaramin dadin kayan taji ba kuma tun a ido sun matukar burgeta tasan zasuyi mata kyau tunda take daman bata saba saka kaya irin wadannan ba masu tsada da tagama dubawa sai ta tashi tsaye saboda murna harda tsalle tashiga yi adakin saida tagama tsalle tsallen sannan tasamu waje tazauna tame jin dadi aranta dan harta matsumu tagansu ajikinta, agurin tabar kayan ta shige bandaki ta cire kayan jikin ta tafara wanka sannan ta dauro alwala ta fito jikin ta daure da zanin wankan da ta shiga dashi kayan ta kuma yiwa dai dai sannan tafara gwadawa haka taitayi idan ta gwada wannan saita kalli wani taga kamar shi zai finata kyau sai tacire ta qara gwada wani ahaka jakadiyar ta qara shigowa dakin kallon ta ta shiga yi tundaga sama har qasa saida tagama qare mata kallo sannan ta girgiza kai batare da tace mata komai ta wuce bathroom din bata jima ba ta dawo cikin dakin fuskarta da danshin ruwa alamar de itama alwala tayo salaya ta shinfida ta tayar da sallah, shi go war jakadiyane yasata tsaida gwajegwajen da takeyi ta dauki daya kawai tasaka da hartasaka ta daidai yanda akeyi tayi rolling da mayafin sai kuma ta tuna ashefa bawai amatsayin wayayyirta zata zauna ba sai kawai tayi saurin kunce daurin datayi rigarma sai ta cireta gaba daya sai ta dau wata rigar marar ado sosai brown color sai dan wani ado da akayi aqarshen rigar da qarshen hannu sai wuyan ma duk akayi ado da coffee sai mayafin ta shima brown amma sai ta ajiye dan kwalin rigar ta dauki na wata rigar amma shi yellow ne itakanta saida tabawa kanta dariya ganin irin hadin ganbizar datayi kawai sai ta daura shi kamar dan kwali ta dauko red din hijabi ta sake daurawa akai kuma bekai mata har qasa ba kana kallonta zaka ga kalar rigar da kuma kalar dan kwalin da ta daura ga kuma jan hijabi sai ta fito das abinta kamar jakar kauye daga kanta tayi ta kalli wani dan tebur dayake cikin dakin an dan jere abubuwa akai qarasawa tayi tana zuwa kuwa taga wata hoda akai sai kwalli taso tasamu janbaki akai amma babu shi sai kawai hoda da kwalli kuma hodar ba mudubi ajiki bata damu daganin madubiba kawai ta hau shafa hodar ahaka tasan ta isa amma sai ta qara gogo wata ta qara dan barawa tanasane ta ringa shawafa har kan hijabin da kuma kan yellow dan kwalin data daura hmm abun ba acewa komai dan bazakace ga da hallitar datayi kamaba gaba daya ta canza kamanni kwalin ta zaro taqara ranbadawa akan idon ta harda yin jagira tajata atsaye kamar dogon yaro idan baka qura ido bama zakayi zaton bata raba girar ba saboda saura kadan ta hadesu bangama tsorata da itaba saida naga space din data bari na jagirar sai taja fashin goshi agurin(wannan abun da wasu sukeyi yanda ake zanen bille shima haka akeyinsa akan goshi wasuma tunda ga farkon gashin su ake jamusu shi har zuwa tsinin hancin su zakugansa an tsgawa mutum shi to itama irinshi tayi da kwalli), tana gama zanawa sai kawai ta dawo kan bakin ta nanma ta zana amma saboda ba kallon madubi take ba saikawai tazana ya kusan cike mata duka leban nasama da naqasa bayan tagama nan kuma sai kawai ta dawo kan kuma tunta taqara jan bille awajen dayan bangaren kumatun kuma sai taja abu guda biyu amma atsaye suke kuma ba wanda ya hade da wani guda dai dai ne saidai rashin kallon madubi yasa daya yafi daya tsawo taso tayi miyau miyau(uku uku nagefen baki da akeyi) amma tana tunanin bazata iyaba saboda zata iya cike fuskarta da baqi gaba daya shiyasa kawai tabarshi tanayi tanawa kanta dariya aciki ciki saboda kar jakadiya tajita tsayawa tayi tana tunani kuma me zata qara sakawa dazaisa de asan itafa yar qauye ce bata san komai ba bata da gata kuma ba kallon madubi take ba batasan tayi ba yanda kowa zai qara yarda da ita kuma bata yanda wani zai zargeta saboda shirmen dazata ringayi musu tsawar da jakadiyar ta daka matane yasata katse tunanin datake ubanwa yace kitaba min kayana waya baki izini tafada tana tunkaro inda take itakam takasa motsawa daga gurin bare tayi tunanin tashi duk dataji tahowarta kusa da ita bata gama tunanin ba taji matar tasa hannu ta tayar da ita tsaye tare da juyo da ita suna facing din juna hannu ta dafa zata kaiwa fuskarta mari amma sai ta dakata sakamakon tozali da tayi da fuskarta asukwane ta saketa tare da sakin dan qaramin ihu tana ja da baya baqaramin firgita tayi ba da ganin fuskarta ba gashi dama tubarkallah tana da idanu gasu farare tas kuma sai ta qara waro su akanta tana kallon ta da mamkin abun da yasata shiga wannan tashin hankalin harhaka batasan kuma zaro idon datakeyi matane yasa ta qara tsorata da itaba jakadiya na ja da baya itama tana qara binta hakan yasa jakadiya qara rudewa ganin tana qara tunkarota gashi bata bar zazzaro idanun da take ba kana kallon fuskar ta bayan haukan da tayi sai idanun zaka gani da kyar jakadiya ta iya budar baki tace dd...an...Allah kuyi ha....kurrrrrrri taqara da wata irin murya wace kanaji kasan mutum yagama tsotara tana fada ta kulle idon ta rufff harda dorawa da tafikan hannun ta wajen rufesu bakomai yasata hakan ba sai washe bakin da Azeema tayi mata fararen hakoranta suka bayyana sai tasake canza kamanni gaba daya ko farin sani kayiwa Azeema ayaude kallo daya baze sa ka ganetaba saidai idan tsayawa kayi sosai ka qura mata ido shima da kyar zaka iya ganeta bare kuma wanda ba wani sanin taba yayi sosai kana ganin ta zakace wannan ba halittar bil adam bace saidai jinsin jinnu(aljanu) abangaren Azeema kuwa sai da riyar taqe yi amma bata bari sauti ya fito ba dan ita saidaga baya ma tagane kwaliyar da tayine ya tsorata jakadiya shiyasa tana sane ta qara wangale mata haqora dan taqara firgita ta daman haushin ta tajeji saboda tun farkon ganinta ta nuna bata sonta ga abubuwan da take mata dan haka itama yanzu tasamu zata rama, jakadiya na kyarma jikin ta gaba daya sai faman karkarwa takeyi gashi sotake tafita daga dakin amma takasa daga qarfata daga gurin ganin hakan yasa Azeema qarasowa inda take daf da ita ta tsaya sai tasa hannu tacire hannun jakafiyar data rufe fuska dashi jakadiya najin anriqe hannun ta taqara damqe idonta tana so tayi magana amma bakin ta sai karkarwa yake takasa budeshi Azeema sai faman dariya take tanaso tayi mata magana amma tasan tana bude baki dariyar da take zata fito ahakan ma saura qiris dariyar ta kwace mata ta fito fili sai kawai tayi saurin sakar mata hannun tare da juya baya tan sa hannu tana kunshe dariyar ta aciki, jakadiya kam jin ansakar mata hannu yasata bude ido daya tana dan kyallowa aikwa tana kyallo bayan ta alamar ta juya baya yasata qarasa bude idon ta dan tabatarwa kanta abun da tagani datade ga da gaske ne ba kallon ta take ba sai kawai takwasa aguje ta bude qofa ta fita daga dakin tana gudu tana kiran nashiga uku wayyo Allah na tawa taqare yau nayi ido hudu da aljana tana cikin gudun tazo zata fita daga dakin kenan taji tayi karo da mutum qara rudewa tayi dan duk atunanin ta aljanar ce ta fito tasha gabanta wanu ihun tasaki tana neman hanyar fita taji andaka mata tsawa da cewa ke mahaukaciya inace baki da hankali daman wajen gudu ne da har zaki ture mutane saboda tsabar jahilace ke bakisan me yakamata ba nutsuwa tayi tare da zubewa awajen jikin ta na karkarwa tama kasa bashi hakuri hannu zai maketa yana cewa baki iyayuwa mutum laifiba kibashi hakuri kenan yakusa sauke mata lafiyayen mari kenan aka katseshi da cewa haba babana me yayi zafi haka ayi mata afuwa mana batasani ba kuma ka tsorata tane shiyasa takasa baka hakurin ranshi abace ya dago yana kallon papa da ya dakatar dashi da abun da yayi niya badanshi ba da baze dakata ba sai ya koya mata hankali papa na qarasowa gurin saiga Ammah ta qaraso falon tana cewa wai meke faruwane wa yataban na gaban goshin farin cikina tana fada tana gama qarasowa inda yake tare da ruqo hannun sa sai yanzuma idon ta ya sauka akan jakadiya dake durkushe agurin tana faman muzurai da idanu tare da hamdala aranta da Allah yakawo mata papa da ba abun da zai hanasa yayi mata dan isakan duka dan zuwa lokacin tsoron ganin aljana yabarta tsoron abun da zai matane akan gaba shine fargaban ta dan ba qaramin tsoranshi take ba hakannan ma inde yana gari bata son ko hada hanya suyi saboda dan qaramin abu zakai yahauka da masifa da duka bashida hakuri kwata kwata shiyasa ma mutane dayawa suke tsoron hada hanya dashi gudun matsala.... Ammah ce ta katseta da kiran sunan ta tace mari lafiya naganki anan me yafaru zatai magana kenan papa ya tareta da cewa bata saniba sukayi karo da shi shine zai kaimata duka na dakatar dashi shiyasa kika gansa haka itakuma takasa basa hakuri, saboda ta tsorata kinsan mutumin naki bashida hakuri yafada yana barin wajen ya koma kan kujera ya zauna yana kallon su, Ammah tace ayya Allah sarki mari meyasa baki duba hanaya ba lokaci da kike tafiya da har yasa kika biheshi wannan ai gangancine yakamata idan kina abun kirin ga kallon gaban ki tana fada mata ta maida duban ta kan Sam tace dan lele na kayi hakuri karkasa damuwa aranka manta da ita zata kiyaye nan gaba tafada tana qara ruqosa sanan tace zo muje kaci abin ci dan naga cikin ka yana neman abinci Allah yasama kaci na dare be tanka Mata ba tasan halinsa daman yanda ransa dinan yabaci bazai kula taba dan haka kawai sai taja hannun sa da niyar kaisa kan dinning shettima dake bayansu yayi gyaran murya hakanne yasata juyowa ta kallesa sannan tace daman tare kuke shine kayi shiru ai ban kula dakai ba wallahi shima ita yake kallo yace daman ina zaki ganni hankalin ki yana kansa ni ai komawa ma zanyi inda ake nemana tundade in mutum yazo nan yar wariya ake nuna mishi ido ake rufewa anuna ma basan da halittar sa agunba wannan san kan fa yayi yawa aringa ragewa inba haka ba kuma nidai baza aqara ganin qafata awajen nan ba tunda ba a son ganin mu sai mujanye jikin mu ko yafada yana qoqrin juyawa yabar wajen yana juyawa kuwa yaji saukar dundu abayan sa tare da talle masa qeya sannan ta jawo rigar sa tabaya amma ko gezau beyiba to basamude mutum sai qarfin tsiya yanzu ji yanda na daddage na jawo ka amma kaki motsawa to juyo ka qara gaya min abun dakake fada dannasan basu qare ba shiyasa nayi maka shiru ka qarasa ki juyowa yayi yana sakin murmushi ta can bangaren shima daman ba fita zaiyi ba yasan dole ta dakatar dashi dan sunsaba haka da it, gamin da yaqi juyowar yasata dan sassauta muraya tace kaifa kafiya matsala wallahi tuzuru kawai ina maka magana kayi qeqam sai kace tsohon soja da sauri ya jiyo yana kallon ta yace lallema tsohuwar nan ke har kina da bakin cewa wani tuzuru bayan ga qaton gardin tuzuru nan agaban ki kibari idan kika fara kawar dashi saiki cewa wani tuzuru koda yake ma wanna ai a tuzuran ma riqaqqe ne ya ruqa kamar dan yar kubewa kinsan kubewa ce idan ta riqe ko yankuwa ma batayi saidai a jefar dan bata da amfani to shima haka yake dan ko tsohuwar bazawara aka bata sadakar sa ma bazata karba ba saidai ko kinemo masa wata yar tsohuwara ahadata da Allah da kudade sannan tadan lallaba tayi maleji dashi dan sai tayi hakuri in kwa bahaka ba to saidai ya mutu ba aure, be ankara ba yaji saukar filo afuskar sa da qarfi zai dago kenan yaqara jin wani haka sameer da yabarsu agun tun dazu yakoma kusa da papa yazaun yana jinsu da bayi niyar tanka masa ba amma yaga abun nasa yayi yawa shiyasa ya dauki filulli kan yafara jifansa dashi saida yaga sun qare gaba daya sannan ya dakata, Ammah ce ta daga hannuta itama tana kaima sa duka ta ko ina tare da cewa bakin ka ya sari danyan kashi saodai kagani akan ka amma bade akansa ba nan da watanni ma zaka gansa da zankadediyar budurwa kai kuma saidai ka qare a tsohuwar bazawarar daman dasu ka dace ba budurwar da zata kulaka inda tana da hankali saidai ko in makauniya ce bata gani sai acuceta ahadata dakai amma me lafiyade cikakkiyar me hankali bazata yarda ta aure ka tana fada tana dukan sa a qirji, Shikam ko ajikinsa dukanta ko kadan bajinsa yake ba yana ta faman dariyar sa saida yaga dan kanta tagaji da dukan sa ta cire hannu tare da yin kwafa zata bar wajen yayi saurin ruqo hannun ta tare da kafeta da ido yana dan murmushi yace kema kinsan fade kike dan kinganni dan saurayi dani kinga kwa yanda 'yan mata suke rubibi akaina hmmm ba a magana zan kawo mikima kizaba min danni sunyi min yawa narasa wacce zan dauka aciki shima yagaya miki wace macen ce take sonshi duk wace ma yace yana so sai ta gudu tace bata son tsoho ita saurayi take so kamar ni fisge hannun ta tayi daga riqon da yayi mata tana galla masa harara sannan tajuya batare da tace masa komai ba saboda ya kaita qarahe bata da abun da zatace kuma tarama cin fuskar da yakewa sameer qarasawa tayi wajen sameer itama ta zauna shima shettima man yana dariya yabiyo bayan ta inda ta zauna ya zauna kusa da ita yace yana satar kallon ta sannan yace madam nifa yunwa nake ji kitashi ki bamu abinci musamman ma tuzurin ki ba inda zaije abashi abinci sai wajen ki nikam banda matsala yanzu ina nan ma idan na dau waya nayi kira nace akawo min ana rawar jiki za akawo min har inda nake Allah sarki shikuma saida taimakonki sai kun hada masa da li'ilafi wannan baqin jinin yayi yawa yana fada ya dubi inda sameer yake azaune ya hade rai kamar anyi mishi albishir da wuta ganinsa yayi yana nannade hannun rigar sa yana shirin tashi daga gurin alamar de zaiyo kansa yana ganin hakan yayi saurin tashi ya koma kusa da papa yana buya agefen sa yace papana kayi masa magana kar yatabani inzo in karyashi dan inya tabani ba barin sa zanyiba saboda ni ba sa'an sa bane nafisa qarfi dariya papa yayi yace to ai shikenan tunda kafishi qarfi kuma yasani ai rabudashi kawai yazo sai ka koya masa hankali ko a'a papa ai banason kuzo kuce naci zalinsa ne shiyasa bana son indake shi papa yace mun yarda ba komai mu sai mu bar muku ma wajen kudan dan batu kaga daga yau baze qara tunkarar ka da fada ba to nide a'a Ammah to ke kisa baki tunda papa yaqi ji itama tace bazan ba din nima nagoyi bayan sa to shikenan zaku gani tunda duk kunqi yimasa magana yana kaiwa nan sai yatashi yayi saurin komawa kusa da sameer akunne yarada masa yi hakuri nifa bada kai nake ba da waccan tsohuwar nake ture sa yayi daga kusa dashi yace to ni ina ruwana ko kaji tunda kafara nace wani abun yace a'a to amma meya nade hannu riga yace ganin dama yafada yana hararar sa tare da kada kai shi kadai yasan ta inda zai rama wannan abun da yayi masa shiyake cewa tuzuru zai kamasa ne nan gaba yanzu beda lokacin sa, ganin kowa yayi shiru yasa Ammah tashi tace dan lelena rabuda shi bari inkawo maka abinci kai kadai shikuma yatafi wajen bazawarar tasa yaci tafada tana tafiya shettima ya bude baki kenan zaiyi magana sameer ya maka masa harara hakanne yasa shi yin shiru be tanka mata ba, har takai bakin qofar kitchen din sai ta tuna da mari jiyowa tayi taga har yanzu ashe tana gurin takasa tashi daga gurin kiran ta tayi tace mari wai wai har yanzu baki tashiba ki tashi daga nan ba abun da zai miki miqewa tayi jiki babu kwari har ta nufi qofar dakin ta sai kuma ta tuna da aljanar dazu sa sauri tayo baya Ammah da bata qarasa shiga kitchen din ba ta juyo tace ke lafiyar ki qalau kuwa meye hakan kikeyi sunkuyar da kai tayi tace Allah taimakike Allah ya qaraja da ranki yake uwar dakina Allah......dakatar da ita tayi tace fadi maganar ki kai tsaye qara sada kanta qasa tayi tace daman abun da zan gaya miki wannan yarinyar da tazo wacce take dakin ashe ba mutum bace aljana ce da sauri Ammah tadawo kusa da ita tace aljana kuma kamar ya bangane ba nufin ki ta gudu taya ma kikasan aljanace inkawo mutum kiringa cemin aljana cikin rawar murya tace wlh aljana ce ni na ganta da idona bayan nagantane na gudo shiyasa har nayi karo dashi ban kula ba gaban Amma na faduwa tace amma bata nuna ba tace yanzu hakan tana cikin dakin tace mata eh tana ciki juyowa tayi tana kallon su papa da suma sunzuba ido suna jin abun da suke cewa Ammah tace kai kunji me tace wai aljana a cikin gidan papa ya mike ts aye yace kamar ya aljana taya akai ta shigo kuma hartabari aka ganta daman aljanun haka suke Ammah ce tace yarinyar fa danake baka labari dazu wai itace aljanar gaba dayan su suka miqe tsaye papa yace to muje mugani ko watakilma shirmeni irin nata me sunan baba muje gaba dayansu tsayawa sukayi sukaqi tafiya saida yasake yi musu magana sannan sameer yadan shafa kansa yace papa aljana fa akace kuma sai kace muje idan tayi mana wani abun fa nide bazan jeba kuje ku gano papa baki yasaki yace tofa kai yanzu qato dakai kace wai tsoro kake ji ko kunya baka jiba to kaifa ko kaima tsoron kake ji yafada yana kallon shettima shimade ba kunya yace eh papa aljani ai ba abun wasa bane dade mutum akace to koma waye zamu iya dashi amma banda mutan boye papa kawai yanzu yanda za ayi mufita daga gidan gaba daya sai aje akirawo malami sai yazo ya duba yagani papa da mamaki yagama kashewa yace amma de kunban kunya wlh nibansan haka kukeba ashe duk matsorata na tara to wlh ba malamin da za akira kuma sai kunje idan aljanar ce inma wani abun zatayi muku ai da tun shigowarku zata yi muku kuwuce muta yafada yana turasa Ammah ma qarasowa tayi tace a'a bekamata kayi musu dole ba kabari kawai ayi yanda sukace aje akirawo malami hakan sai yafi duban ta papa yayi yace kinsan Allah na rantse kuma wlh sai munje kuma hardake dan haka kuwuce muje duk son bijerewar su amma papa yaqi ya dage akan sai sunje ba yansa suka iya haka sukayi hakuri suka tafi yasaka su agaba sai da sukaje daf da dakin sai kuma suka fara dawowa baya wannan yace wani yayi gaba wannan yace wani yayi gaba Ammah tace kunga kune maza kuyi gaba ni sai in zauna abaya shettima yace ai wlh kece agaba kinga ke kin tsufa daman kinkisa mutuwa mukuma kinga yanzu muke tasowa kinriga kin gama cin zamanin ki muma kibar muci namu tsohuwa kawai kiyi gaba yafada yana turata gaba dalla kadena turani daman angaya maka ita mutuwa zaba take duk da na tsufa sai kaga kai ka mutu kabarni yace eh na yarda amma de ai bata wannan hanyar ba da zamu mutu lokacin mu beyi ba papa ne yadaka musu tsawa yace banason shirme anan kuwuce yafada yana bude qofar dakin amma baigama budewa gaba daya ba sai yatsaya yace suzo su shige aikam kowa yaja burki daga inda yake shima kuma be shiga ba ashe shima aranshi yana danjin tsoron kawai dakewa yayi ganin sun tsaya yaqara yi musu magana wai baza ku wuce ba dan matsowa suka farayi ahankali Ammah ce agaba da shettima ya turota sai sai shi shima kuma sameer ne ya turosa sannan ya tsaya abayan su yana jiran yaga sungama shiga idan lafiya lau sai ya shiga idan kuma yaga sun dawo sai yajuya daga inda yake, Azeema dake dakin tana zaune take jin murya sama sama kamar aqofar dakin yasata tashi tayo wajen qofar dataji anturo tasa hannu taqara budewa tana budewa sukayi ido hudu da papa,papa naganin ta yaja baya da sauri amma be bar wajen ba ya tsaya itama Amma sai ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda tagane yarinyar ce dai kawai kwaliya tayi ta lalata fuskarta tun ganin da sukayi papa yadan ja da baya ai basu tsayabama bare susan me za ace har sunjuya sun nufi hanyar waje aguje har suna 'yar rige rige wajen bude qofar qofa kuwa kamar tasan halin da suke ciki sai taki buduwa tsayawa sukayi suna kokarin janta Ammah da ta juya bayan ta zatace su kwan tar da hankalin su sai taga wayam babu kowa awajen maida dubanta tayi ga Azeema tace fito waje kinga ki tsorata min 'ya'ya wannan wace irin kwalliyace kikayi jin hakan yasa papa ajiyar zuciya danshima yafara tunanin ko aljanar ce dan shi betaba ganin anyi kwaliya irin wannan ba matsawa yayi yace nima ai ta kusan tsoratani ina wadannan matsoratan sukayi je kikirasu suzo suga abun da suke gudarwa 'yar qaramar dariya Ammah tayi tace lalle kam bari inkirasu tana fitowa daga dan lungun dakin ta hangosu zasu fita, da qyar suka samu qofar ta budu ashe garin saurin su suka murda key din jiki basusan ta shiga luck ba suke ta faman janta ahaka suna murdawa ta budu zasu fita Ammah tayi saurin dakatar dasu tace ba aljana bace sai kudawo matsoratan banza kawai ni mace ma nafiku jarumta wallahi atare gaba dayan su suka juyo tare da sauke ajiyar zuciya sameer ne yace Ammah kunduba kuwa sosai kun tabbatar ba aljana bace tace musu wallahi ba ita bace jin harda rantsuwarta yasasu dawo wa cikin falon suka zauna suna sauke numfarfashi kamar wanda sukayi gudun tsere suna haka papa ya shigo falon tare da Azeema cikin falon kanta aqasa bata kalli kowa ba suka shigo dakin Ammah ce tace 'yata matso nan suganki kinga duk girman nan nasu tsoro ne dasu gaba dayan su yayyanki ne zo ku gaisa tafada tana jawo hannun ta kusa dasu dukan su zuba mata ido sukayi suna jiran ta dago suganta saida Ammah tace ki gaida su mana dago su ganki tana sane take so tadago suganta dan tasan dole su tsorata tunda ba saba ganin irin hakan sukayi ba itakuma daman tasan 'yan kauye suna irin haka shiyasa ma bata sha wahala ba ta ganeta ahankali Azeema ta shiga dago da fuskarta ai bata gama bude ido bama ta kalle su sam yayi zunbur zai gudu Ammah tayi saurin riqeshi tace kai wai wane irin matsoracine ancemaka mutumce kamar kai amma ka wani tashi zaka gudu shide shettima tunda yaga zanen girarta bejira yagama ganin ta ba duka ya rufe idon sa da tafin hannu wansa amma jin batun Ammah yasa yayi saurin bude idon sa yana budewa kwa baiyarda sun hada ido ba yaqara saka hannu ya rufe fuskarsa, dakatawa yayi da tafiya amma sai yakoma bayan papa yana buya a bayan sa tare da leqowa dan yaqara ganin ta da kyau dan shi beyarda ba aljana bace hakan da yayi kuma yayi daidai da dagowar Azeema aikam karaf idon su suka hade da na juna amugun zabure Azeema ta miqe tsaye dan qara tabbatar wa idon ta abun da tagani kode mafarkin da fasaba yine da qarfi ta furta aljani na wallahi na yarda aljani ne aljaniiiiiiii tafada tana qanqame Ammah datake kusa da ita tare da sakin wata uwar qara da saida ta karade duk falon tanayi kuma jikin ta yasaki gaba daya ta tafi luuu zata fadi Ammah tayi saurin tarota, Shettima da yarufe fuska jin muryar da yasani yasashi saurin bude fuskar sa dan ganin inda me muryar take duk da be gama tantance abun da kunnuwansa sukaji ye masa ba..........✍ Tofa yau akeyin ta ga Azeema ga shettima ko shettima idan ya kalli fuskarta zai gane ta gata kuma agidan su sam wanda akullum take mafarkin ganin sa yau gata ga shi ko yaza ayi zaman gashi kuma idan taganshi sumewa take kuma takawo kanta inda yake tode muje zuwa dan ganin yanda wasan nasu zai qare..... ************************************************** Assalamu alaikum, kutsaya ku karanta kar ku wuce yana da matuqar muhimmaci agareku. *ILIMI HASKEN RAYUWA* Ina matan aure harma da 'yan mata wadanda basu samu damar yin makarantar islamiya ba ko kuma wadan da sunyi amma yanayi rayuwa yasa sun manmanta da wasu abubuwan to ga dama tasamu akwai mata dayawa wadan da suke cikin wannan halin suna bukatar ilimi kuma wasu suna so amma basusan ta inda zasu fara ba wasu kuma hidimar gida da iyalai bazasu samu damar fita su nema ba, To amma fa kusani hakan ba hujja bace awajen Allah domin acikin wani hadisi ance azaba ta tabbata gawanda be nemi yasani ba kuma ko kasani ma idan baka aiki dashi nan ma azaba zata tabbata agaresa dan haka kutashi kunemi ilimi kar kuzauna da duhun kai ko girman kai ilimi ba ai masa girman kai kitsaya ki fadada iliminki musamman bangaren akdari mata dayawa suna da qarancin ilimi akai, Duba da hakan yasa muka kawo muku hanya mafi sauqi na online class kina zaune a cikin gidan adakin ki azaune ko akwance ma zaki samu duk wani ilimi da kikeso dai dai iyawarki, yar uwa awa nawa kike batawa akan wayarki batare da ki qaru da ita baki koyi komai ba aciki awa nawa kike batawa akan karatun littattafen novel da kalle kalle da basu da amfani, zamu bude group iya mata zamu kawo muku littattafan addini sannan kuma zamu ringa qarin alqur'ani me girma duk surar da baka iya ba za akoya maka duk daga inda kake so zaka koya zamu koya muku baki kodaga alifunne baka iyaba za a koya maka kuma da yardar Allah zaka iya, Ga abubuwan dazamu ringayi kamar haka👇 1_ALQUR'ANI 2,HADISI 3,AKDARI 4,ARABIYYA, 5,SIRATUL NABIYYI 6,NURANIYYA DA dai sauran su duk waddannan abubuwan zaku samesu agarabasa me sauki naira dari ukun ka ta baka ilimi kuma idan kabiya ka ta samu kenan baza ataba cemaka wata yayi ba biya kudi ko shekara nawa zakai saidai idan kai kagaji da nema kace ya isheka domin karin bayani sai ku tuntubemu ta wannan number 08124226526 Pls duk wanda ya karanta yatayamu da share dinsa zuwa group group domin inkai baka ra ayi watakil wani yana da ra,ayi akai kuma be ganiba plss share it [5/10, 10:32 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526 'Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*                          🅿13&14 Bismilah.......✍ *shettima* waige waige ya shiga yi ko zaiga me muryar amma bega kowa ba tunani yashiga yi tabbas ko awane yanayi ya tsinci kansa baze manta da wannan muryar ba tabbas muryar yarinyar nan ce yaji qanwar saleem wata ziciyar ce tace masa to ba a murya iri daya inde kana duniya ba abun da baza ka ganiba naban mamaki ba dangin iya bare na baba saikaga wani me kama dakai sak alhalin bama dangi daya kuke ba bare kuma murya hakan me sauki ne awajen uban giji tuna hakan dayayi ne yasashi saurin kawar da tunanin yamaida hankalin sa kan su amma da duk sunbi sunatada hankalin su anzubawa yarinya ruwa amma ko gezau batayi ba gaba dayansu daga Ammah har papa bawanda be tsorata da halin da yarinyar ta shiga ba lokaci daya komai tagani da yasata wannan furgitar lokaci daya papa ne ya kalli sameer yace daiketa mutafi hospital wani irin kallo yayiwa papa da besan ma yayi ba sannan yace papa kayi hakuri amma wlh bazan iya tabata ba danni har yanzu tsoron ta nake ji kuma kodama mutum ce bazan iya taba wannan qazamin jikin nata ba kalleta fa kalli shigar da tayi yafada yana yatsina fuska kamar wanda yaga kashi papa yariqe baki yana mamaki kodayake ba abun mamaki bane inda sabo yakamata yasaba da irin wannan halayen na sam da kaitsaye zaiyi maka magana kasa cewa komai yayi sai kawai ya maida dubansa ga shettima yace kai zo kaduba ta inma baza ka dauke ta kusan yanda zakuyi da ita tunda kune likitoci beyi masa musuba dan shide har zuciyar sa yaji yadena jin tsoron ta dan haka ya matso inda take tare da karbar ruwan hannu Ammah data tsaya akanta sai faman yayyafa mata take yana karba ya ajiye gefe yana so ya dora hannun sa akan qorjinta yadan danna mata ko zata kawo numfashi kuma yanajin nauyin su papa duk da aike ni bawai da wata manufa zaiyi hakan amma su agaresu zasu iyacewa wani abun tunda watakil basu taba gani anyi hakan agaban su ba sameer ne dayaga yatsaya yagane me yake shirin yi sai kawai yace Ammah to kubashi guri kunsande ba kowane marar lafiya ake duba akowane irin yanayi dan haka muna buqatar abamu guri, abashi guride cewar papa yana maka masa harara what ever de idan yayi ai kamar nayi ne kuma nima likitane ciwon likita na da likitane 😂 (anacewa ciwon 'ya mace na 'ya macene shikuma gana sa sabon salon) Ammah ce tadanyi murmushi sannan tace to da likita masu iya magana abaride mutum ya iya hausa kafin yayi karin maganar mutum yana ba haushe amma yamaida kansa besan komai ba papa ne ya katseta yace rabudashi ai inbeyi wasaba sai nahanasa komawa waccen qasar sai inga qarshen iyayi yafada yana sake hade fuska danshi ayaude sam ya bata masa rai kuma yabshi mamaki jan hannun Ammah yayi suka nufi daki dan basu wajen sameer kuwa shiru yayi be tanka musuba sai faman tabe baki da yake irin ko ajikina danshi bilhakki bega aibun maganar da yayi ba da har suke wannan cece kucen kallon shettima yayi yace to me kake jira baza kayi abun da yakamata ba sai ka kashe yar mutane wayasani ma ko kai ka tsorata ta da wannan gemun naka kamar bunsuraye ni sai yauma naqara kula dakyau da tace aljani sai naga kayi kama da aljannin kaga shikenan sai ku hadu aljana da aljani kaga gwara ma ka lallaba da ita bakasan wacce aljanarce zata qara zuwan maka ba dan ganin sun maida kai cikin su sunyi wuff dakai mijin aljana kayi sauri ka dubata karkayiwa kanka asara ni kaga tafiyata asha soyayyay lafiya kuma banda wuce gona da iri ajira afara daura aure tukunna karka jamata abun kunya acikin danginku yafada yana juyawa da niyar barin wajen kuma wallahi idan ka kalli fuskarsa baza kace shi yake zubar nan ba saboda fuskar nan tana nan yanda take ba annuri akanta , Mary dake labe tana sauraron su saura kadan dariya ta kwace mata sai tayi saurin barin wajen tana mamaki aranta daman wannan yana magana haka wlh tazata daga uhm sai uhm uhm sai kuma masifa ta zata iya abun da ya iya kenan ashe shima ba kanwar lasa bace tasan abun da akayi masa dazu yake ramawa lalle kam ya iya ramuwa tafasa tana sakin wani murmushi da ita kadai tasan ma'anar sa sannan taqara gaba abun ta barin falon ma tayi gaba daya tafita waje, saurin ruqosa shettima yayi yana fama hade rai yace meye hakan dan Allah nida nayi maka ai bada aljanu na hadaka ba kadena hadani da aljanu banaso da ace ni aljanine iya zamana da kai ai da tuni kagane ko kataba gani nayi wani abun da yayi maka kama da na me aljanu bare kuma aljani da kanasa ai da tuni babu kai ganzu aduniya kai bama kai kadai ba da tuni nagama da danginka gaba daya kuma......hannu sam yadaga masa tare da cewa kai ni banason surutun banza kayi abun da zakayi inbhaka ba kuma inyi tafiya ta inbarka da ita yafada yana kwace rigarsa da yariqe ya koma kan kujera yazauna tare da dora qafa daya kan daya yasaka hannun sa yatsa daya abaki yana dan ciza kadan yana tattara hankalin sa gabadaya akan su yana jiran yaga ta yanda zai fara taba yarinyar danshi koda kudi baze iya taba koda yatsanta bare kuma jikinta wai me kake jira Allah zanyi tafiyata jiki babu kwari shettima ya juya yana tunanin ta yanda zai fara dan shima sai yanzu yafara tsoron taba tan runtse ido yayi yakai hannu sa wajen qirjinta kamar wanda zai taba garwashin wuta haka yakai hannuwansa duka biyu saida yayi addu'a sannan ya tattaro  iya qarfinsa yadanna ta saida yayi wajen sau uku sannan ya ya bude idon sa ganin yayi har yanzu bata mawo numfashi ba ruwan yaqara diba ya yayyafa mata shi afuska duk samma karde ba wani canji yanzu de shide baze iya kaita asibiti ba bare asaka mata oxeging kuma hanya daya ce ta rage da ake jawowa mutum numfashin sa batare da anje asibiti ba kuma shide baya jin zai iya hada baki da ita besan daga inda take ba juyawa yayi yakalli sameer da shima su yake kallo dan marairai cewa yayi yace kaga fa har yanzu bata kawo numfashi ba kuma da ranta zuciyarta na bugawa ba mutuwa tayi ba ya kake ganin za ayi ko mukaita asibitin sai aduba ta acan hararar sa yayi yace wlh ba inda zamu kai zaka duba kasa bakin ka kajawo mata mana ba matar ka bace wani bazan kallo da ya watsa masa da yakusan saka sam murmushi amma sai yadake yaqiyi ya maze ya maida hankalin sa kan wayar sa papa ne yafito daga dakin fitwarsa tasa shettima bece masa komai ba sai ya dubi papa yace papa har yanzu bata dawo hayyacin ta ba da alama ta tsorata ne sosai da yasata doguwar suma saidai kuma....da sauri sam ya dakatar dashi yace papa wallahi so yake yakashe muku yarinya yasan yanda zai mata ta dawo amma yakiyi wai qazamace bazai iyaba kuma papa idan beyi mata ba zata iya rasa ranta gaba daya sboda doguwar suma tayi kuma daga nan zata iya wucewa lahira hankalin papa atashe yace haba yarona yanzu ko ahanya ka tsinci yarinyar nan ai baza kaso ta tarasa rantaba yakamata kayi gaggagwar ceton ranta saboda hakkine akanka daka zama likita duk wanda ya mutu ta sanadin rashin bashi kulawarka to kaimafa Allah baze barka ba katai maki rayuwar wannan baiwar Allahn kaga marainiya ce abar a tausayawa ce kar kabiye wani qazanta ko wani surutu kawai ka taimake ta dan Allah badan halulinta ba kodan mu saikaga kaima Allah ya taimake ka kaji yaron kirki maza dan Allah ni bari in koma yana kaiwa nan be jira abun da shettiman zaice ba kawai ya wuce yabarsa agun, sosai maganganun papa sukayi tasiri aransa ya cire komai yasa aiki zayi domin Allah badan kowa ba dan haka yanajin sam na tsokanar sa yayi banza dashi duba falon ya shiga yi can ya hango tissue kan dinning yaje yadauko yazo gabanta ya tsugunna sanna ya yago tissue din ya goge mata baqin kwalin da ta shafa akai saida yaga ya gogu sosai sannan ya ajiye tissue din tun awajen goge mata lebanta idan yazo gogewa bakinta yadan matsa sai haqoranta sai fito sai yaga kamar farin haqora yagani kawai sai yabude bakin nata dan tabatar da abun da yagani  ga mamakin sa sai yaga haqoranta farare tas ba alamar digon datti ajiki  jiyayi hankalin sa ya kwanta daman tunanin sa ko zai bude yaji wari ya fito kuma haqoran nata sunyi yellow amma sai yaga akasin haka wani qurawa bakin nata ido yayi sai yaga kamar yansan shi amma baze ce ga inda yasani ba kawai yayi mishi kama da bakin da yasani ne kawar da tunanin yayi ttare da miqewa tsaye sai kawai ya rufe ido yasa hannu  ya toshe mata hanci sannan yasa dayan hannun yadan buda bakin sai kawai ya dora nasa bakin akan nata yafara hura mata iska tare da jawo nata numfashin yayi wajen 3 minutes yana jawo mata numfashin kafin yaji ta sauke ajiyar zuciya qara qarfin hurawar yayi lokaci guda ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya alamunde numfashin nata yadawo jinkin ta sakin hancin nata yayi tare da dagowa zai cire bakinshi sai kawai yaji anriqe mishi lip din qasa da haqori zaro ido yayi saboda yaji zafin riqon da tayi masa sameer ne yadanyi gyaran murya da gefen idon sa yakkali inda yaji sam yayi gyaran muryar sai yagansa akansu daf dasu qara kan bakin sa yayi yaji still de bata saki ba dayan hannun sa yasa yadaketa agefen kafadar ta zafin da tajine yasata saurin dawowa hayyacin sa tare da sakar masa baki ita batama san me take ba lokaci daya ta bude idon ta tana budewa ta saukesu akan sa wanda shima jin ta sakesa yasa shi kallon fuskar ta zubawa juna ido sukayi kafin tayi saurin janye idon ta akansa gabanta na dukan uku uku fargaba da tashin hankali na rufar mata duk alokaci guda tunanin ta  yakasa yarda da abun datagani shin me yakawosa gidan darauta kuma me yakeyi akanta shikenan yanzu yagano ko ita wacece ta shiga ukun ta karde ace dan gidan ne shima inkwa hakan takasan ce gaske tana cikin matsala dan zai iya tona mata asiri tasan dole yacewa mutane yasanta yanzu yazatayi wacce mafita zata bi gashi kuma intace zatayi masa magana ta roqeshi kar yafada ya rufa mata asiri sannan tagaya masa gaskiyar abun da tazo yi wani zai iya ganewa gashima kuma suna cikin mutane taya zata fara tarar sa, ganin ta tafi duniyar tunani bata tare da wannan duniyar yasa shettima cewa sannu ya jikin bata kalle sa ba kawai ta daga masa kai tare da yunqurawa zata tashi yayi saurin dakatar da ita yace kar kitashi kwanta ki huta komawa tayi ta kwanta tare da rude idonta gudun kar yagane ta dan taga alamar duk yanda akayi be ganeta ba sakamakon kwalliyar datayi, miqewa yayi yana maida dubansa kan sam yana tasowa yaga sam yayi saurin maida wayarsa aljihu da kallon tuhuma yabisa dan yaga alamun rashin gaskiya ahakan da yayi sam ma kallon sa yayi tare da daga masa gira daya gace yane naga kawani tsatstsare ni da ido bafa itabace yafa da tare da satar kallon Azeema da ta rufe ido saurin kawar da idon sa yayi akanta danma angoge kwalliyar bakin sai batayi abun tsoro ba da yawa amma de duk da haka shide baze iya jurar kallon ta, shettima ne yace me kayi muga wayar yace daman nataba baka wayata mema zakayi da ita kana zargina ne shettima yace eh wlh banyarda da kaiba daukar mu kayi ko kafada yadaga tare da tabe baki yace akan wane dalili zanyi muku hoto yafada tare da komawa kan kujera ya hakimce tare da mazewa kamar bashi yayi maganar ba, ajiayar zuciya shettima ya sauke duk dade begama yarda dashi ba amma sai yaji hankain sa ya kwanta tare da kawar da maganar ma aransa har ya juya zai je ya kirawo su papa kawai sai yaji qarar wayar sa alamar sako ya shigo dakatawa yayi da tafiyar yasaka hannu aljihu tare da zaro wayar dan ganin message din da ya shigo masa private number yagani an turo masa da sako da sauri ya bude yana bidewa yaga anrubuto masa saqo da manyan baqi,        """KADUBA WHATSAPP DINKA YANZUNNAN ZAKA GA SAQO"" Hannun sa har karkarwa yake wajen budewa datar sa ya shiga WhatsApp yana shiga messages suka fara shigowa amma ga mamakin sa bega sabuwar number ba har yaja tsaki zai fita daga WhatsApp din sai yaga saqon my man ya shigo be dubaba yajuyo ya kalle sa sai yaga bama ya falon har ya fita daga ciki hakalin sa ya maida kan wayar sannan ya bude message din sameer dan ganin abun da yaturo masa saboda begane rubutun dayayi ba aqarshe yaga de 3  messages besan saura biyun me ya turo ba da haka yabude kanasa tsaye danshi har alokacin ransa bai kawo masa komai ba saida idon sa yasauka akan video da hoto guda daya amma basu gama budewa ba saboda ahaka ya saita wayar sa duk hoto ko video sai yayi downloading dinsa dakan sa shiyasa bega meye ba sai kawai ya dannan videon gabansa ne yafadi ganin sa kan yarinyar da yataimaka ashe tun lokacin da yake danna mata qirji kuma dake ta baya ya dauka sai ka rants wani abun yake aikatawa sai lokacin da ga tsugunna yana goge mata baki da likacin da ya bude mata baki dan ganin farare ne ko yellow ne dan iskancin daukar tasama kuna sai yasa stop agurin da yasa hannu ya toshe mata hanci be dauka dannan ba saikawai gurin da yasaka bakinsa cikin nata muraran kana gani zakace kissing dinta daga nan kuma sai gurin da suke kallon juna har qara zumin din fuskikin su yayi suka fito da kyau kana ganin kwalliyar fuskar ta nanma idan kaga kallon da sukewa juna zakayi zaton irin angana kiss dinnan anayiwa juna kallon love irin kowa nawa kowa kallon bangaji nan ba  muqarayi wani be isheniba fassarar kallon da sukewa juna kenan awayar 😂 Lol ganin yaqare yasashi fita daga videon yakoma ya bude hoton shikuma hoton lokacin dazata tashi yayi saurin kai hannun sa yace ta koma ta kwanta daidai inda yasa hannun sa ajikin ta daidai gurin ya daukesu jiyayi kamar ya fasa wayar dan ta qaici fasa zuwa inda yayi niyar zuwa yayi kawai ya juya tare da yin kwafa yabi bayansa yana ayyana irin rashin mutuncin da zaiyiwa sam idan yakamasa shiyasa ashe yabar falon to kwa yau zai nemosa duk ma inda ya shiga.. Azeema dake kwance jin shiru yasata dan bude ido tashi tayi zata zauna tana juyawa taga shettima a tsaye sai tayi saurin komawa ta kwanta saboda atunanin ta ko fita sukayi dataji shirun yayi yawa ashe yana nan to meyake atsaye kuma ina dayan dataji muryar sa agun shi ina yake tunda taji muryar shi taji tanaso taganshi saboda yanda yake magana muryasa tayi mata dadi murya ahankali ba wani daga murya acikin ta kanaji zakasan me ita baqaramar nutsuwa ce dashi ba tun amuryarsa zaka gane hakan tana so taganshi amma tsoron shettima yagane ta yasa takasa bude idon ta ta kalleshi amma har cikin ranta ta qosa da ta gansa amma ba hali Allah yasa wataran yaqara dawowa taganshi, tanajin takun sa alamar ya juyo tayi saurin rufe idonta saida yagana fita daga falon sannan ta bude idon ta tare da tashi zaune zama tayi tana sauke ajiyar zuciya bi falon tayi da kallo sai yanzuma tafara tunani wai ya akayi ma ta ganta anan tunawa tayi lokacin da suka fito da papa har tazo zata gaida su to me yafaru da ita tasande Ammah tace ta gaida su yayintane hannu tasa abaki irin mutum yanason ya tuna wani abun tayi wajen minti 1 tana tunani sai kawai tayi zunbur ta miqe tsaye tana girgiza kai wlh shine shi naqara gani akaro na biyu arayuwa ta to amma meyasa inde nagansa bana qara ganin sa gashi idan nagansa rannan ance min na suma kenan yauma suman nayi to me hakan yake nufi inde ba aljani bane meyasa nake suma idan nagansa alhalin kaf duniyar nan banda wanda nake burin ingani inbashi ba banida burin da yarage min arayuwa irin inga gani gashi wake daya koda besoni ba duk danasan ma daman baze taba sona ba amma ni koda ganin sa ne ma kadai akabarni hakan ma zaimin dadi gashi kuma sai gizau yake min yana tsoratani hartakaini ga suma na shiga ukuna ni Azeema meke shirin faruwa dani kar aljanu subude min ido Allah na roqeka kaciren shi azuciya ta Allah kasa ba aljani bane idan kuma aljanine Allah kamin tsari dashi Allah kasa kar nasake ganin sa arayuwa ta mutum ne kamar ke taji anbata amsa daga bayan ta saurin juyawa tayi gabanta na faduwa Ammah ce ta qaraso inda take tana kallon ta ganin yanda  tashiga tashin hankali ne yasa amma cewa dukan su da kika gansu jikoki nane kuma duk anan suke nima nayi mamakin sumanki daman saboda nayi tunanin idan kika ganshi zaki iya suma saboda kyaunshi da kuma mamakin da kika shiga duk su suka haddasa miki doguwar suma, Jikin tane ya shiga karkarwa shikenan watakil taganota  Allah yasade bataji duk zancen datakeyi ba da kyar ta iya hadiye wani abu da yatokare mata makogaro sanna  ta bude baki daqyar zatayi magana kenan Ammah ta dakatar da ita tare da cewa kar kice komai kije daki ki goge kwalliyar nan sannan kisaka kaya complete mayi maganar daga baya  ina nan inajiran ki bata da zabin da ya wuce bin umarnin ta kamar wacce kwai yafashe ma aciki haka ta daga qafar ta datayi mata nauyi da kyar take janta jiki asanyaye gabanta na faduwa fat fat tabi ta gabanta batare da tace komai ba ta nufi dakin da tafito ranta fal da tunani kala kala ahaka taje dakin tana zuwa ta shige bandakin sai kawai ta fashe da kuka da ita kanta batasan dalilin yinsa ba sai da tayi me isarta sannan tayi shiru wayar ta ta dauko ta kira saleem taci sa'a kuwa bugu daya ya dauka tare da cewa salamu alaikum auta qanwata ta kaina Allah yasade kiran nan inji alkhari sunan shi takira tace "yaya" yana jin muryarta yagane ba lafiya ba cikin dan tashin hankali yashiga tambayarta lafiya cikin shashsheqar kuka tafara yimasa bayanin duk abun da yafaru amma bata gaya masa ganin sam ba saitace masa wannan mutumin da mukaje office dinshi abokin aikin sa wanda inde taje yake cewa ta zauna agunsa yace eh yagane sa nande tabashi labari banda ganin sam alabarin nata shima ya shiga tashin hankali sosai nande yarsa shawarar da zai bata saikawai de ya kwantar mata da hankali tare da cewa ba abun da zai faru amma kartasake ta fadi gaskiya kawai tace tasaba ganin sane amafarkin ta shiyasa yau da tagansa take tunanin ko aljani ne idan tafadi hakan za ayarda to tace masa tare da daga masa kai kamar yana gabanta sannan tace ya turo mata da number shi mutumin da to yace mata kawai be tambayeta dalili ba ya katse wayar ba jimawa ya turo mata dubawa tayi ta dauka tayi saving dinta sannan ta shiga tayi typing din message zata tura masa amma bata turaba sai kawai tabar wayar awajen in case koda lokacin turawar yayi sai ta tura masa ba tare da wani ya kula da ita zatasan yanda zatayi kar akamata  tunawa da anajiran ta yasa ta maida wayar gefe sannan tayi saurin daukar sabulu ta wanke fuskarta saida tayi wajen wanki hudu ta tabbatar da fuskar tafita sannan ta dauko wayarta tafito wasu kayan ta dauka tasaka amma bata fita da mayafin ba sai ta dauki wani hijabin da yayi kala da kayan ta saka ta fito das da ita farin ta da kyawunta suka bayyana tafito a Azeemar ta tada sannan tafito falon inda tabar Ammah ana ta dawo ta sameta tana zaune tana jiran ta tunda tafito Ammah take binta da kallo har ta qaraso ta zauna aqasa daga gefen qafar ta tare da sunkuyar da kai tana wasa da yatsun hannunta gaban ta na faduwa  tana jiran taji abun da zatace mata, Ammah ta bude baki zatayi magana kenan taji sallamar shettima hakan ya dakatar da ita daga abun da tayi niyar fada qarasowa yayi yana ta kunfar baki saboda suk inda yake sa ran zaiga sam yaje begansa ba shiyasa yaqara dawowa nan ya duba ko zai gansa ya bude baki zaiyiwa Ammah magana sai kawai yaji maganar ta makale sakamakon tozali da idonsa yayi masa da Azeema qarar message dinne ya katse masa tunanin da yake shirin fara yi Ammah dake binsa da kallo tanajiran taji me zaice tace ya akayi ne ina me sunan baban yake be bata amsa ba yazaro wayar sa daganin me kuma yaqara cemasa dan shi duk atunanin sa ko shine yaqara turo masa da wani abun yana dubawa yaga bakuwar number budewa yayi ransa na qara bace gefe kuma ga tunanin ganin Azeema dayayi yarasa ma wane tunani zaiyi fara karan ta sakom yayi kamar haka        *dan Allah dan annabi na roqeka kar ka nuna            kasanni zanyi maka bayani daga baya na                roqeka kayi min wannan alfarmar banzo            nan dan na cutar da wani plss and plsss            karkace komai akaina plsssssss* kurawa message din ido yayi bayan yagama karantawa tana satar kallon sa ta dauka ma baze taimake ta dan har tacire rai ma sai kawai taji yace Ammah daman nida wannan tuzurun naki ne yayi min wani babban laifi naje kuma na duba ya buya narasa inda yaje sai yanzu ya turo min wai inke waje insame shi yafada yana juyawa zai bar gurin tace baku gaisa da ita bafa gata ta wanke kwaliyar tayi hakane dan tanaso tagane acikin su waye yasa ta suma amma ganin yanzu ba ta suma ba yasa tagane amsarta watakon me sunan babane yasata ta suma zai fita kenan taqara tsayar dashi tace abincin naku fa kace masa yazo kuci kar ya kwanta ahaka dan nasan halinsa watakil shikenan baze dawo nan ba said da safe yace mata "to" kawai dan lokacin har yakai qofar fita budewa yayi ya fice daga falon nauyayyir ajiyar zuciya Azeema ta sauke aboye ganin ko kallon inda take ma beyiba ya fice hakan da yayi ba qaramin jin dadi tayi ba ranta taji ya kwanta tana murna aranta, Meyasa kikeson saka rayuwarki cikin hadari kina 'ya qaramar ki nawa aka baki kika saudakar da rayuwar ki WAYE YA TURO KI!!!!!!!!!!!!?? daram daram darammmmmm gabanta yafadi yana kidan disko tambayar da tazo mata abazata duk wani jini dake kwaranya ajikin ta ya dakata da aikin dayake wani irin diff taji kanta yayi kamar ma ba aduniyar take ba.............🙆 Tab kina ruwa takwara😭        [5/11, 8:41 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526 'Yan niger kuma suyi min magana ta number wayata*                          🅿15&16 Bismilah.......✍ Meyasa kikeson saka rayuwarki cikin hadari kina 'ya qaramar ki nawa aka baki kika saudakar da rayuwar ki WAYE YA TURO KI!!!!!!!!!!!!?? daram daram darammmmmm gabanta yafadi yana kidan disko tambayar da tazo mata abazata duk wani jini dake kwaranya ajikin ta ya dakata da aikin dayake wani irin diff taji kanta yayi kamar ma ba aduniyar take ba....... "Tambayarki nake Ammah tafada da dan daga murya hakanne yasata dawowa cikin hayyacin azabure ta daga ido tana kallon Ammah sai kuma jikinta gabadaya yadauki rawa bakinta harkarkarwa yake ganin yanda Ammah ta hade rai kamar ba itaba saima ta canza kamanni alokacin ta koma mata tamkar wata boss, idanuwan tane suka cicika da kwalla amma sai tayi saurin riqesu bata bari sun zuboba jitayi bakin ta yayi mata nauyi bata san ma me zata ce mata ba batasan ta inda zata fara yimata magana ba saboda ta qara tsorata da ganin yanayin Ammah, daurewa tayi saida tagama karanto addu'o'i acikin ranta duk wta addu'ar da tazo bakin ta yi take watama batasan me take cewa da qyar ta iya budar bakin ta dataji su tamkar andaure mata su ta ciki bakin ta na karkarwa kamar mejin sanyi tace ni ba wanda ya turo ni kamar yanda nagaya miki mahifana sun rasu sun barni wlh banzo gidan nan dan incutar da kowa ba kuma bada wata manufa nazo ba tun kan ta rufe bakin ya Ammah tace qarya kike ki fadan gaskiya tun muna shada juna tun a kallar fatar ki za agane baki kala da masu shan wahala ba qarya kike kice min baki da iyaye kina yawo a bola ai tun ganina dake tun farko nagane kalar zaren ba kalar yadin bane ina sane nabarki kika shigo dan in kamaki da hujja angaya miki bama abu da lissafi acikin masarauta zakizo ki rainawa mutane hankali bakisan bamu da yarda da mutane ba ni banma san ya akayi kika shigo ba waye yabarki saboda muna kafa kafa da rayuwar mu duniyar nan ba abun yarda bace musammama acikin gidan sarauta kowa zai iya zuwa dan ganin ga cutar da mu kawai abata mana family ko atarwatsa rayuwar wasu dan haka duk takun mutum muke lura dashi abun da yasa naqara tabbatarwa baki da gaskiya da kikaje ki kwaba wannan haukan a fuskarki alahalin watakil ma baki taba yi ba kawai danki wasa da hankalin mu kuma harda suman qarya ko kuma mamakin ganin sane wanda kike tunanin yasaki suman ko to kinfado hannun daidai dake yar qarama dake har kikasan kiyi min wayo yaushe kikazo duniyar yaushe aka haifeki tunda ta fara magana Azeema take faman kuka zuwa yanzu kam kukan yaci qarfin ta dan har bata san ma me Ammah take cewa ba jin kukan nata ya dameta yasata dakatawa da maganar da take kawai ta tsaya tana binta da idanu tana qara nazar tarta saida tagaji da kukan sannan ta dan dakata amma bata dena shashsheqar kukan ba cikin sanyin murya ta fara magana tace nasan nayi kuskure shigowa ta gidan nan kuma kinyi gaskiya bana kwanan bola kuma ina da uwa uba ne banda shi ki gafarce ni wannan qaryar danayi miki kuma nayine atunanina wannan ce hanyar kawai da zanbi incika burina amma kisani ni kwaliyar da nayi banayine dan in raina muku hankali ba kawai zaman dakinne ya isheni sai naga hoda da kwalli kuma ba mudubi shiyasa kawai na dauka nafara kwaliya dasu hasalima banga me nayi afuskar ba kuma daman niyata idan nayi sallar isha idan zanzo wajen ki sai inje bandaki in wanke kafin inzo wajenki amma banayi ba dan wata manufa wani irin banzan kallo Ammah take watsa mata me cike da fassariri iri iri hakan yasa Azeema dan daka tawa da maganar tare da shan jinin jikinta tana tunani ko kawai ta fadi gaskiya sai amfi yarda da ita tunawa kuma da cewa masarautar basu da imani koma tafada ba barinta za 'ayi ba kuma daga qarshema tazo tai biyu babu ita ahanata fita shima kuma aqara kwakwkwaron tsaro wajen riqeshi a masarautar ta yanda har abada bame fitar da su daga ciki ko kuma ma ace za ayanke musu hukuncin kisa tsoro yaqara nunnkuwa azuciyar ta shiyasa taji bazata taba fadan gaskiya ba koda me za ayi mata fatan tade Allah yasa ta yarda da bayanin da take mata, ganin ta tsatstsareta da idanu yasata katse tunanin da take sannan taci gaba dacewa suma kuma dakike cewa nayi na qarya hasalima bansan nayi ba saidai kuma nasan musabbabin abun da yajawo min suman shine tozali da nayi dashi mamaki ne yasani suman kamar yanda kike tunani tunda nataso arayuwata bantaba jin son wani mutum ba sai akansa tunda naje wani biki qawata naga hotonsa awayar amaryar naji nakamu da sonsa bata ma san nadau hotunan saba acikin wayarta ba tundaga lokacin nake mafarkin sa kuma zuciyata takasa samun nutsuwa har saida nahau Internet na nemosa sannan nayi tambaya akansa ahaka har nasamo address dinsa ashe dan gidan sarauta ne tundaga nan nafara tunanin ta yanda zan hadu dashi kuma ance min ba anan qasar yake zama ba saidai kawai yazo yadanyi kwanaki yatafi tunda naji haka nake son inshigo gidan nan ko Allah zaisa inganshi nayi duk yanda zanyi inga na shigo gidan nan amma nakasa samun hanyar da zan shigo wata qawata ce ta bani labarin masarautar akwai tsaro dan inde ba wanine yasanni ba baza ataba barina in shigo ba saidai ta hanya dayace idan naci sa'a zan iya samu inshigo nace tagaya min hanyar shine take cemin taji ance inde mutum yazo amatsayin almajiri yaneme da ataimaka masa da abinci to zai iya samu ace yaje ya karba amma saidai inje da sassafe kafin masu gidan su fara fitowa nikuma daga nan sai insan hanyar da zanbi wajen ganin na hadu dashi koda sau dayane arayuwata hakan zaisa naji dadi araina yanda muka tsara kwa hakan nabi har nasamu sa'a tambayar farko me gadi ya amince min da nashigo naje karba nikuma da na tafi inda ya kwatan tamin sai kawai nabi wata kwanar arashin sani nabi hanyar da sarki yake bi ananne dogaren suka kamani shine kikazo kika taimakeni kinji iya gaskiyar abun da nasan ya shigo dani gidannan amma ba yanda kike tunani bane banshigo dan na cutar da wani ba amma ki gafarce ni qaryar danayi miki kuma dan Allah karki tona min asiri ki rufamin asiri kar wanda yaji maganar nan na roqeki badan halina ba kuma kar ki koreni daga wajenki dan bansan yanda zanyi da rayuwata ba wallahi ina sonsa tana gadar haka kuma sai tayi saurin sada kanta qasa zuciyar ta na bugawa da fargabar abun da zataji daga gareta batasan da wata manufa zata dauki zancen taba zata yarda da itane ko kuma zatasa a hukuntata laifin qaryar da tayi ta shigo ciki shiru falon yadauka na dan mintina saboda Ammah ta tsaya tana nazarin maganganunta saida tayi wajen miti biyar batare da tace mata ko uffan ba sai daga bisani kawai tace mata tashi kije zan nemeki kawai abun da tace kenan ta tashi daga kan kujerar ta bar falon ta nufi dakin ta tana shiga ta fara zagaye dakin tare da saka hannun ta duka biyu tana zagaye zagaye tabbas azancen yarinyar nan kamar akwai gaskiya duba da yanda take kuka wiwi kuma naga alamar da gaske tanason sa to amma hakan bazaisa in yarda da itaba lokaci guda kuma abun da takeso duk son da gake masa bazai taba auren ta ba amma tunda har ta bukaci itako ganinsane zata ji dadi aranta to zan mata wannan alfarmar sannan bazan sanar da kowa ba qudurin ta agidan zan barta tacigaba da zama acikin har zuwa wani lokaci da na daukarwa kaina kuma zan qara sa ido akanta inde har da gaske take zan fahimata idan kuma nagano qarya take tofa zata kwashi kashin ta ahannu dan bazan raga mata ba turo qafar da akayine yasata dakatawa da tunanin zucin datake papane ya shigo da dan fara'arsa yaqaraso inda take yace kinga bakuwa afalon nan kuwa naganta de azaune ta gaida ni amma de ban tambayeta saboda naga bisa ga dukkan alamu zaman jiranki take yafada yana kallon ta danjin me zatace itama murmushin ta mayar masa dashi tace naganta yanzu nadawo daga wajenta ai ba bakuwa bace wannan yarinyar ce da da nake gaya maka baki asake yace yarinyar kuma kuma naga waccen fara ce fa ba baqa ba waccen yarinyar kuma da nagani ai baqace na tambayi yaron nan kuma na hadu dashi yace hartaji sauki tana daki tana bacci shiyasama kikaji bantambaye ki tana inaba kalloma Ammah tayi tana yar dariya tace tode wannan daka gani itace bawani bacci da tayi nasaka tade ta wanke fuskarta shiyasa kaga tayi haske kwaliyar datayi ne yasa tayi baqi amma itace de da mamaki yace kai amma kamar ba itaba to wadancan matsora tan sungantade ko tace a'a sun fita amma nasan wata kil suna hanyar dawowa ai shiyasa nasa ta wanke fusakarta dan sufi ganinta da kyau dan sudena tsoratan ta eh hakan kuma yayi ai ba wanda zaice itace yajikin nata kuma me yaje damunta Ammah tace kawai doguwar suma tayi ne amma bansan dalili ba zande tambayeta sonake sai ta qara samun nutsuwa yace to Allah ya kiyaye gaba Ameen tace sannan ta nufi toilet shikuma yakoma kan gado yadauki littafin da yasaba dubawa yafara dubawa, Azeema datayi zaune awajen tarasa wane irin tunani zatayi ita rashin maganar da batayi mata ba yafi tsaya mata arai taso tace mata wani abu amma tayi shiru batasan wane irin mataki zata dauka ba tana gurin har papa yaahigo saida taga ya wuce sannan ta miqe da kyar ta tafi daki zuciyar ta namata wani iri duk adagule take jinta duk dade a wani bangaren taji dadin ganin bata koreta ba kuma batayi mata fada ba to amma hakan bazaisa tayi sukuni ba har saitaji abun da zatace mata kafin ta saki jikin ta kayan jikin ta tacire ta shiga ta dauro alwala tazo tayi sallah aranar de bata jin zata iya cin wani abu kuma bazata sake fita ba dan haka tana idar da sallar tayi nafila tare da roqon Allah Allah yashige mata gaba akan abun da tazo yi Allah yasa tacika alqawarin da ta daukarwa kanta addu'a sosai tayi kafin ta cirehijab din tahau kan katifar dakin ta kwanta tareda nannadewa guri daya tana kwanciya taji shigowar mary ga mamakin ta saitaji mary nayi mata magana cikin lallami batare da daga murya ba tace kitashi kici abinci gashi nakawo miki dan Allah kiyi hakuri akan abubuwan da namiki bazan qaraba dan murmushi tayi aranta tace lalle ma matar nan haryanzu tsoron be bartaba kenan tashi tayi zaune tace ba komai komai ya wuce amma de nakoshi da abincin bacci nake ji kinga bandade da cin abinci ba (kunsa tade daman bawani abinci take ciba sosai saboda bata daci) duk yanda taso tace abincin nan amma taqi ci bayanda ta iya haka tafita da abincin dan mayarwa kitchen daman Ammah ce tace ta takurata taci kuma taqi ci dan haka kawai ta mayar dashi saidai kuma bata gayawa Ammah cewa bata ciba kawai taje taci abinta ta qoshi sannan ta dawo dakin lokacin da tadawo har Azeema tayi bacci tunanin tafara anya kuwa ta kwanta akusa da ita dan itafa har yanzu bata gama yarda ba aljana bace a tsorace take da ita dan lallabawa tayi ta leqa idon ta dan ta tabbatar tayi baccin ko batayi ganin de da gaske bacci take yasata daukan abun rufar kan katifar ta shinfida aqasa ta dauko filo daya tayi kwanciyar ta aqasa dan sai tafi jin dadin hakan sai tafi samun kwanciyar hankali, *shettima* yana fitowa zuciyar sa taf da tambayoyi kala kala me yakawo yarinyar nan dole yasan dalilin zuwan ta gidan da wuri badan dare ma yayi ba da ayau zaije gidan su yaji ko ansani agida amma yabarwa gobe ki beje gidan suba idan yaje asibiti zai tambayi yayan ta yaji da haka yaqarasa wajen motar sa kdaman yagaji da neman sam shiyasa kawai ya yanke shawarar sai gobe yasan dole zasu hadu bude motar yayi yatafi gida dan zuciyar sa da tunanin sa gabada suna kan ganin da yayiwa yarinyar nan da tunane tunaneta yaja motarsa yabar masarautar yatafi gida, Sam ya na ganin fitar sa yafito daga cikin wata mota yana bin motar sa da kallo aransa yace nasan da na tsaya da tuni kacika min kunnuwa da surutan banza kazo ma ka qara min ciwon kai inji da wanda yake damuna yana ayyana hakan yana tafiya har yakai bakin parta din Ammah sannan ya bude qofa yashiga saboda daman akwai maganar da yakeso suyi tun dazu amma waccen banzanr aljanar tazo ta bata masa lokaci da yaga be ganta a falo ba sai kawai yanufi dakin ta kai tsaye dan yanaso suyi sugama yaje ya kwanta dan bacci yakeji kwan kwasa qofar yayi aka bashi izinin shiga ya bude ya shiga abakin gado yazauna yana jiran Ammah ta idar da sallah suyi yatafi papa ne yace qaton banza kawai baka ga mutane ba kashigowa mutane guri ba sallama shiru yayi be kula masa ba papa yaci gaba da cewa au ga dan iska yana maka magana ko ciki ciki yace papa nayi fa saidai idan bakaji ba yafada yana hade rai saikace wanda akayiwa wani abun papa shiru yayi masa dan baya so yaci gaba da magana ransa yabaci saboda har yanzu haushinsa yakeji akan abun da yayi masa dazu shiyasa shirun sai yafi alkhairi dan zai iya gaya masa ba dadi shikuma daman ba hankali garesaba komai yazo bakinsa zai iya gaya masa shiyasa ya maida hankalin da kan littafin sa, Sam yana sane yayi masa haka shikuma anasa tunanin idan yabiye masa zai iyayimasa maganar yarinyar cen shiyasa ya hade masa rai dan karyasamu fuskar yi masa maganar kuma hakan da yayi sai yaga yaci nasara be kulasaba hakan ba qaramin dadi yayi masa ba Ammah ce da ta idar dasallah tayi masa magana dacewa ina abokin naka yace yatafi gida tace gida kuma ince yakira ka kuci abinci shine yakama hanya ya tafi to kwa zaidawo yasame ni kai taso muje yace Ammah nima na qoshi muje de waje ina son magana dake tace aikam baka isaba sai kaci inba hakaba kuma ba maganar da zanyi dakai daganan ma ka tashi kaitafiyar ka tafada tana juyar dakai gefe irin taji haushinan saida yagana binta da kallo aransa yace idan akace maka tsoho tofa sai ahankali burkitattune sai kabisu yanda sukeso ahankali ya bude baki yace naji muje inci tace karma kacidin yace Ammah....yafada cike dagajiyawa da surutun dasuke yace wai bani nace zan ciba kuma sai kin qara batamin lokaci yafada yana miqewa tare da nufar qofar wake itama miqewa tayi tabi bayansa tana mita mutum sai bakin hali shi yayi yanda yake so amma kai idan kayi masa sai yanuna maka yaji haushi tana mita tafita lokacin har yakusan fita daga falon tayi saurin dakatar dashi cak yatsaya dande yanaso suyi maganar ne amma da baze saurarera ba dan haka kawai sai yajuyo be kalli inda take ba kawai ya wuce kan dinning kaitsaye yana zama tazo ta zuba masa saida yadauke kai sannan yafara ci beci wani me yawa ba yace mata ya qoshi ganin fuskarsa ahade yasa bata takura masa akan sai ya qara dole ba ta rabu dashi sannan tace to ina sauraron ka gyara zama yayi yana fuskantar ta da kyau itama duka hankalin ta ta miqa garesa dan taga kamar magana me muhimmaci zamata tunda taga ya tukara kansa haryayi abun da baiyi niyaba dan badan maganar ba tunda yace bazaici ba da baze taba ci din ba ko mai zatayi masa ina sauraron ka taqara cemasa akaro na biyu........... *BOSSAY* ransa abace yakoma dakinsa rub da ciki yayi ya kifa kansa aqasa shikadai yasan radadin da zuciyarsa take masa akan wannan kwacen da sukayi masa wayar sace ta soma ruri banza yayi da ita har kiran ya katse wani yaqara shigowa be motsa daga inda yake ba saida yajide inba daga wa yayi ba baza adena kiraba ransa abace yadago daga kwanciyar dayayi tare da kai hannu yadauki wayar dake kan bed side drawer zaro ido yayi sakamakon ganin me kiran shifa gaba dayama yamanta da rayuwar ta yama mata da ita aduniyar nan gaba daya yana kallon number tata har be daga ba har tasake katsewa wani ne yasake shigowa yace mayya ai nasan bazaki dena ba ko zaki kira sai dari daga wa yayi tare da saka wayar a Hans free sannan yayi shiru yana jiran me zata fara cewa itama anata bangaren shirun tayi tana jiran yafara magana amma shiru ahankali tace hello baby uhm hum ykk jin muryarsa yasata sauke ajiyar zuciya sannan tace ba lafiya yace me yake damunki tace tambayata ma kake yanzu dan Allah kayi min adalci kenan idan bankiraka ba baza ka taba kirana ba ko kadena kirana ka dena zuwa gidan mu yanzu kusan 3 weeks rabona dakai tun lokacin dakazo gidan mu banfito ba kace zaka dawo haryau banganka tafada tana sakin wani marayen kuka shiru yayi yana sauraron ta saida tadena dan kanta sannan yace kingama tace a'a yace to cigaba yafada yana ajiye wayar gefe tareda kwanciya ya rufe idon sa yana sauraron tagana nata haukan shima ya nuna mata nasa tunda bata da hankali shifa arayuwar sa yatsani mutum marar zuciya da zubar da mutun cinsa kana jin taqara cewa tacikin wayar banza yayi mata be bata amsaba hakan be dameta ba ta dora da cewa tunda naga abun hakane nacewa dad dina kawai yayiwa mahaifinka magana asa ranar auren mu nan da wata daya dan naga alamar idan nayi wasa zan iya rasaka mamakin maganar ta yayi shi duk atunanin sa da yaji tace tunda abun hakane to nafasa auren amma sai yaji akasin haka wai nan da wata daya lalle yaqara yarda taci kai batasan kishin kanta ba sai ya fito mata amutum saida yabari takai aya sannan yace nikuma bazan yi aure nan da wata dayaba duk ma uban dakika gayawa kije kice ni banshirya ba kuma ba wanda ya isa yasa ni inyi abun da banyi niyaba inma zaki dena wannan maganar ki dena sannan kuma kibini ahankali inba hakaba kuma hmmm yafada yana cije baki kamar yana gabanta a zafafe ta fara magana yanzu nikake zagi abun yabar kaina ya koma kan ubana ince maka nagayawa dad dina shine zakace duk ma uban da nagayawa inje ince kai baka shirya ba to kasani zancen gama yariga da yagama auren mu nan da wata daya babu fashi sai ya tabbata saboda already sun gama magana da abban ka inkuma bakajin maganar iyayen ka sai kagayamin tsawa ya dakamata dakata ke harkin kai matsayin kigayamin magana son ranki to nikuma Aliyu nace nafasa auren ki ko ana dole kije ki nemi wani nima ina da wacce nake so yanzu banason ki ke nifa wlh ingaya miki gaskiyama hankaline baki dashi da baki gane banason ki har jakar kwakwalwarki take baki inasonki to daman zanbi umarnin mahaifiyata neshiyasa zan aure ki amma tunda kinzabi sanin ko waye ni gwara ingaya miki ni Aliyu bana sonki bana sonki bana sonki!!! Yanzu kuma na tsaneki kifita daga rayuwata kar kisake kirana sai kije kigayawa wanda yake daure miki gindin yin abun da kika ga dama kice wanda kikeso ya tsaneki bayason ganinki idan ya isa kuma yazo yasani insoki idan anaso dole banza ballagaza marar kamun kai be jira cewarta ba yayi katse kiran tare da wurgi da ita gefe yana faman huci kamar wanda yayi gudu tashi yayi yawuce bathroom yasakarwa kansa ruwa saboda yanda yake jin zuciyar sa nayi masa radadi,, *RASHEEDA* wani jakin ihu tasaki tare da durowa daga kan gadon da take har tana kifawa sannan tayi saurin tashi ta bude qofa tafita aguje tana kwadawa mom dinta kira mom mom nashiga uku na lalace wayyo Allah na wayyo Allah na nashiga uku duk da girman jikin ta jin kukan diyar tata hakan be hanata kwasowa aguje ba tayo inda taji kukan yar tata aguje ta fito daga kitchen tafara hawowa kan step din benan kicibus sukayi dan daura kadan mom ta gangaro qasa Allah ya taqaita wahala tayi saurin riqe qarfen benan tana haki dan ba qaramar wuya tace ba adan gudun nan da tayi ba saboda tsabar daukewar da numfashin ta yakeyi tama kasa yiwa yarta tata magana saidai kallon ta datake itakuma sai cewa take mom zan mutu wlh mutuwa zanyi nashiga uku tafada tana girgiza mom din tata mom kuceci rayuwata dan Allah wallah idan na rasashi mutuwa zanyi zan iya rasa rayuwata shine bugun nufashina kinji mom tafasa fuskar ta shabe shabe da hawaye lokaci guda duk ta fita a hayyacin ta tazama tamkar zararriya sai yanzu mom da taji numfashin ta yadan daidai ta cikin tashin hakalin tace ke kimin baya ni me yake faruwa waye kike magana akansa kinzo duk kindaga min hankali ni wallahi ma na dauka wani mugun abunne ya cijeki abanda ki me waye zai rabu dake mom bossay bossay ne yace yafasa aure na wai ya tsaneni mom kutaimakamin banason inrasa shi arayuwata jin abun da tace yasa itama tadanji wani iri saboda maganar tazo mata abazata kamo hannun ta tayi suka koma sama dakin ta tajata suka zauna abakin gado saidai suna zama kamar wadda ta zauna akan qaya haka ta miqe tsaye zata fita daga dakin aguje mom tayi daurin riqota tace ke wai baza ki nutsuba kinyi haukane kitsaya kiyim kwakwkwaron bayani bangane ba me ya hadaku yace yafasa auren ki watakil kinje kiyi masa haukan naki ko wlh mom ba abun da nayi masa hakan nan daman yadena kirana awaya kuma yadena zuwa gurina shine naked masa magana me gasa shine yadena sona baya sona harda zagina yaringayi yana cemin jaka mahaukaciya ballagaza marar kamun kai bani da hankali duk shi yake gaya miki wadannan maganganun cewar dad da shigowar sa kenan dakin yaji abun da take cewa aguje tanufi inda yake tare sa fadawa jikin shi tana sakin wani sabon kukan cikin kukan take cewa wlh dad duk shiyake gaya min wai danace ma kaje kayiwa babansa magana asaka ranar auren mu nan da wata daya shine yace wai koma uban waye yaje yafada inje ince be isa yasashi abun da bayaso ba sai abun da yayi niya kuma indai aure ne yafasa baze aure niba tafada tana rushewa da wani kukan sosai ran dady yabaci yace ya isa haka shine kuma keke tada hankalinki haka ai ko ubansane be isa yace anfasa auren nan ba bare kuma shi ki kwantar da hankalin ki kidena asarar hawayen ki aure kamar anyi shine angama aure dole ayi ko yana so ko baya so sai ya aureki kisa aranki yazama mijinki kuma ke kadai sai yanda kikaga damar juyashi ko wata be isa ya aura ba dake zai rayu mutuwa ce kawai zata rabaku yaqarasa fada yana rabata da jikin shi sannan yasa hannu ya goge mata hawayen ta yace yanzu abun da nake so da ke shine kar kisake damun kanki akan batun auren ku sannan kar kisake kiqara kiran shi kirabu dashi zanyi maganin sa itade mom tana zaune tana kallon su batace komai ba amma itama aranta tana kiyasta abubuwan da zatayi akan wannan cin mutum cin da yayi wa yarta tilo daya aduniya zai gane kurensa sosai dad ya rarrashi rashida har saida yaga ta kwantar da hankalin ta sannan ta koma dakin ta wayar da ta jefar ta dauka tana binta da kallo tare da sakin shu'umin murmushi tana jinjina kai.........✍ (kema kinzo kin taka sahun barawo bake kika kar zoman ba amma yanzu ya dora miki alhakin yin kisan yasau ke fushinsa akanki mutum daman baso yake ba kuma akazo masa da magana yana cikin fushi kinga kwa ko wane irin hukun ci zai iya zartarwa nikama bazance komai ba akai kar nima ya dawo kaina dan naga alamar Ameesha na neman tasa shi yafara dukan mutane saboda idon sa yafara rufewa koma ince ya rufe) [5/14, 6:34 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿17&18 Bismilah.......✍ *shettima* cike da tunanni iri iri a ransa yaqarasa gida horn yayi ne gadi ya wangale masa gate shikuma ya danna hancin motar ya shiga ciki parking lot ya nufa bayan yagama daidaita parking ya fito yanufi cikin gidan yana shiga yaga babu kowa afalon yana qoqarin nufar dakin hajiyar sa sai gata tana saukowa daga upstairs tana ganin sa ta fadada fara'ar fuskarta tana sakin murmushi ganin tilon danta tanajin tausayin sa kodan rasa mahaifin sa dayayi shiyasa akullum sonshi yake qara nunkuwa cikin ranta ganin tana murmushi shima yasahi kawar da duk wani tunani da yazo dashi ya ajiye shi gefe da murmushin shima tunkan taqaraso yaqarasa inda take tare da yin hugging din ta sannan yace hajiya what happened ne naga kina ta smiling wani taqara saki tace ba dole inyi smiling ba nasamu 'ya mace wlh bakaji yanda naked jin dadi ba tunda muka dawo kasan me nayi mamakin yarinyar nan yanda ta saki jikin ta dani kai kace daman munsan juna sosai tare ma muka shiga kitchen mukayi girki nayi mamakin yanda naga ta iya abubuwa wani yau girkin kanwarka zakaci wani rin murmushi yake ta faman saki tunda tafara bashi labarin yake jin wani dadi na ziyartarsa cike da zumudin ganin ta yace hajiya tana ina hajiya tace ai har ta kwanta tayi bacci kasan jikin ta ba wani lafiya ne dashi ba shiyasa da tan tayani nace tayi wanka ta kwanta bayan taci abinci tundazu fa ta kwanta yace gaskiya banji dadin kwanciyar ta ba naso nadawo naganta kafin na kwanta dan hararar wasa hajiya tayi masa tace to meye abun damuwa aciki bayan muna tare inbaka ganta yanzu ba ai zaka ganta gobe ganin ta har sai kagaji ai tana rufe baki yace wlh hajiya bazan gaji da ganin taba nifa badan badan bama daki daya zamuna kwana idan natashi kuma mutafi aiki tare mu dawo tare baki hajiya tasaki tana kallon sa sannan tace nikuma sai abarni nikadai daman kwa bazan taba yarda ba nifa yarinyar nan koda komai ya daidaita zan roqesu subarta tace gaba da zama awajena har zuwa lokacin bikin ta shine kawai zai rabani da ita in sha Allah nasan bazasu hanani ba yace to Allah yasa ai hajiya ko tayi auren ma kuna tare ba inda zata tace dake shi mijin yace maka zai yarda yadawo nan da zama inama kataba jin inda a kai haka yace ai dolen sama ya zauna yana da inda yafi kusa dake ai ba inda zasu kuna tare dasu daga ita har mijin yana gama fada yace bari indan watsa ruwa inzo inci abinci baby sai yanzu ta dan fahimci zancen sa murmushi kawai tayi bata ce masa komai ba itama ta wuce kitchen abincin masa ta hado masa bata kai dinning ba kawai sai ta ajiye masa akan center capet din dan daddare befiya cin abinci akan dinning ba yafiso ya zauna aqasa yayi balance yanda zaifi cinsa da yawa yaci ya qoshi saboda baya wasa da cikin sa akwai cin abinci bare kuma idan ya kwaso yunwa ba a magana sai yaci abincin kusan mutum biyu shikadai tana gama jere masa ta zauna awajen tana jiran fitowar sa...... Sam & Ammah Saida yadan qara gyara zama tare da miqa duka hankalinsa gare ta sannan yace Ammah wata tambaya zan miki ko Allah zaisa kin sani tace ina jinka yace yanzu idan akace na kusan kusanka wa ake nufi kenan saida ta dan numfasa sannan tayi murmushi tace yanzu wannan har wata tambayace kaima ai zaka iya bawa kanka amsa yace Ammah da nasani ai bazan tambayeki ba tace to idan akace na kusan kusanka kamar ace mahaifiyar ai kaga itace ta kusa dakai to ba ita sai ace hasanarta ko kuma mahaifanta kaga su sune nakusan ta ita kuma itace ta kusanka kagane dan jimm yayi yace eh nagane to amma idan akace kuma zaku hada alaqar jin fa kinga kamar ba mahaifiya ake nufi ba tunda ita daman already jininku daya ba wata alaka da zaka hada da ita tace eh hakane tode wannan tambayar taka bandan fahimcekaba kaimin bayani dalla dalla dan har kaqara rikitani gyara zama yayi ya fuskance ta da kyau sannan yace yanzu alal musali ace bansan kiba ke kuma kin sani sai kikazo wajena fuskarki a rufe amma da ace kin bude zan iya sanin ki tunda nasanki abaya saidai rufe fuskar da kikayi yasa bangane kiba sai kawai kika zomin da wata bukatar ki wacce kike tunanin bazan iya ba amma sai kikace zaki bani kudi makude atake alokacin kika turamin kudade nikuma tsoro yasa nace miki na amince sai kike cewa idan banyi ba kinsanni farin sani kinsa gidan mu idan na kuskure tofa duka family na sai sunshiga wani hali hakan yasa nace na amince amma kifara gaya min ko wacece ke sai kicewa ai nima nasanki kece ta kusan kusana wanda zamu hada alakar jin nan da 'yan wani watanni kuma kika gargadeni akan kar inzafafa tunanj wajen gano ko wace saboda shima zaizame min matsala gwara kawai inyi aikin da kikasani idan ina son kwanciyar hankali sai nazo zancire miki abun da kika rufe fuskar sanadin hakan danyi kuma bangama ganin kiba kuma banqara sanin inda kaina yake ba sai agadon asbiti to kinji yanda abun yake kin gane yanzu tace eh na fahimceka sosai amma wanna amsar taka kabari ba yau ba sai nayi nazari sosai dan marairaicewa yayi yace plss Ammah ki gayamin yanzu kawai abune emergency nasan zaki iya mekika fahimta acikin wannan maganar bakajin hausane abun da na fahimta dinne ai nace kabari idan nayi nazari zan gaya maka shiru tayi na dan wani lokaci sannan tace kafin ma ingaya maka kaiwaye yayi maka wannan tambayar ko a ina kaji labari dan shafa kansa yayi tare da dan cizan lower lip dinshi sannan yace Ammah wannan ba abun da yashafeki bane kawai amsa ake nema daga gareki idan komai ya tafi yanda akeso zakiji komai ta danji haushin maganrsa amma sai ta danne bata bari bacin ran yafito ba tace masa ok kawai sannan ta miqe tsaye tace sai kaji daga garene shima da sauri ya miqe tare da qarasawa gare ta yace dan Ammah na daga nan zuwa gobe ki taimaka kigama nazarin kigaya min kai kawai ta daga masa alamar to daga nan ta nufi dakinta shi kuma ya fita daga falon tare da nufar sashen Fulani inda zai kwanta saboda yaga dare yayi atunanin sa kowa ya kwanta shiyasa ma be tsaya wani yin nocking ba kawai yatura qofa yashiga kai tsaye hajiya sarah inason ganinki agidana tun lokacin da kika tafi ka barni cikin duhu haryanzu nakasa fahimtar inda maganar ki ta dosa tun alokacin nake taqara trying number ki amma bata shiga me yafaru ne abun da yaji fulani nacewa kenan itama jin kamar motsin mutum yasa ta dagowa daga kan kujerar da take idanunta suka sauka akansa bata jira amsar da za abata ba kawai ta datsi wayar tare da miqewa gabanta na dan dukan uku uku tana tunanin Allah yasade baiji abun da take cewa ba wata zuciyar tace to meyema idan yaji ai ba gane abun da take cewa zaiyiba tuna hakan yasata sakin murmushi tare da qarasowa kusa dashi tace tunyaushe kashigo daman kai naked jira shiyasa na zauna anan tunda naga alamar kwana biyun nan baka son zuwa inda naked be tanka Mata ba saima wani kallo me cike da ma'anoni da ya wtmatsamata da yasa saida takawar da idonta daga garesa bece mata komai ba ya raba ta gefenta ya wuce sashen sa yabarta agun atsaye tana takaicin kallon da yayi mata da kuma kin kulatan da yayi kamar wacce aka dasa agun haka ta tsaya tana tunani kala kala saida ta dau wajen minti uku agun batare da tayi wani kwakwaran motsi ba sannan ta girgiza kai tayi gaba tare da cewa dani kake zancen zan saita maka zama acikin gidan nan baka san halina bane labari na kake ji cike da takaicin wulakancin da yayi mata naqin kulatan dayayi ta nufi dakin ta da tunanin abun da zatayi masa acikin ranta, shikam anasa bangaren bema san tanayi ba dan dagaske bai fahimce me take cewa ba saboda tsakanin su da yar tazara shiyasa kawaide yaji tana magana amma baya tantance abun da take fada abun da yabashi haushi da har yagane duk yanda akai abun da take fada bana alkhairi bane dana alkhairi ne ai bazatayi saurin katse kiran ba daga ganin sa dalilin da yasa yaqi kulata kenan yayi wucewar sa daman yanzu ba wani dasawa suke ba tunda yagane take taken ta ya fit a harkarta gaba daya, yana qarasawa dakin sa ya hau cire kayan jikin sa ya fada bathroom be dau lokaci ba yafito jikin sa daure da towel sai guda daya kuma da ya nannade gashin kansa dashi guri yasamu ya zauna gaban dressing mirror sannan ya kunce towel din kansa ya qara goggogewa sannan ya dauki lotion ya shafe jikinsa tareda turaruka nide tsaye nayi ina kallon ikon Allah sai kace amarya zata gurin me gida anaso aburge shi haka shima yake tafaman shafe shafe da murtsike murtsike yadau wannan ya shafa ya ajiye yadau wancan harda shafa wani abu akan lips din shi da nidai yau nafara ganin sa a hannun sa tunda akahaifeni aduniya ban taba gani ba saida yagama tsaf sannan ya mike yaje gaban slyzing drawer bayan ya bude ta yadauko wasu kaya marasa nauyi yasaka sannan yaje yadauko fresh milk a fridge din dak in ya dan sha kadan sannan ya mayar sannan ya haye kan tamfatsetsen gadon sa tare da jan lausassan blanket dinshi ya rufe duka jikin shi dashi amma banda fuska lumshe kyawawan idanunsa yayi ko addu'ar bacci beyiba yayi kwanciyar sa some times daman bata dameshiba abunde dana lura dashi kamar yana da dan qarancin yawan ibada ahaka yayi kwanciyar cikin qanqanan lokaci bacci yayi awan gaba dashi asuba tagari, Washe gari Yana tashi bayan yayi sallar asuba ya koma ya kwanta be tashiba sai wajen qarfe 11:am sannan ya farka shima saida shettima ya tasheshi awaya sannan ya tashi yana tashi ya shiga yayo wanka yazo yaqara kwalkwale jikin sa kamar yanda yasaba sannan yasaka kaya tare da qara feshe jikinsa da turaruka yafito sai faman zuba qamshi yake idan yazo waje kafinma ya qaraso gurin turaran sa zai rigashi zuwa saboda ba kadan yake sawa ba gasu kuma masu tsada da dadin qamshi fitowa yayi cikin takunsa na isa da qasaita da mulki da izza duk wanda yayi karo dashi yaga yanda yake takunsa kai kasan bada ganan ba shidin na dabanne koman sa na dabanne ya sha bambam da sauran samari(nide nace da sauran tuzuraide )yana qarasowa falon fulani yasame ta ita da papa azaune akan kujera qarasawa yayi ya gaida su gaba dayansu fuskarsa ba yabo ba fallasa duk dade ba wani sakinta yayi sosai ba amma de da sauki akan yanda yakeyi da ita koda yaushe cikin sakin fuska duk suma suka amsa masa har papa na tsokanar sa da matsoraci dan zuwa yanzu ya sauko daga haushin nashi da yake ji fulani ce tace haba de yaron nawa ne matsoraci kana ganin mutum dirare ga kwanji kace masa matsoraci wannan ai sai ya iya yaqi da mutane sama da dari uku ma batare da yagaji ba papa yace a ina din to kwa kallon kitse kikewa nama wannan ba abun da yaya iya jiya mace fa yaringa tsoro abun mamaki wai harda guduwa qato dashi abun ma abun haushi hade rai yayi ciki ciki yace papa ai wannan ba mutum bace aljanace nikam bana son ko ahanya inyi gamo da ita bare kuma har inje inda take Allah ya kiyaye bada ni ba wlh da ace cewa akayi ga wani nan yazo zai cutar daku to anan zaka gane ina da tsoro ko bani da shi amma bawai kahadani da aljana ba kuma kace bazan tsorata ba wannan ai wajibine kaima nasan kawai basarwa kake amma naga tsoro a idon ka kawai na yi maka shirune dukan wasa papa ya kawo masa shi kuma ya guje yace daga fadar gaskiya Allah ko na rantse bazata cini ba papa kaima ka tsorata dakiya de kawai kafimu papa yana dan murmusawa irin na manya yace yaron kai wai yaushe zaka koyi riqe magana duk maganar da tazo bakin ka baka tsoron fadar ta yace ai saboda ba wanda naked jin tsoro kaf fadin duniyar nan shiyasa bana shakkar kowa caraf fulani tace har uwarka da ubanka kenan marar kunya ko kunyar fadar hakama bakaji ba agaban mu ko bani da daraja agunka ai shi uban ubankane ka daraja shi tunda ni daman tunda nagama cin kashi da fitsarin ka na dauke ka tamkar da awajena amma da wuyanka ya isa yanka ka balaga shikenan nazama marar amfani awajen ka sai kawayi garima kafi qarfin kazo inda nake ka gaida ni saidai in munhadu ahanya hayar ma wataran bana samun damar gaisuwar saidai kayi min kallon banza ka wuce to ko uwarka bata isa tayi min abun da kake min ba kuma zanyi maganin ka jiyama Allah ne ya taimake ka amma da sai na kwashe fuskar ka da maruka marar mutun ci kawai wanda besan darajar nagaba dashi ba ni wallahi ka isheni zama kayi ka tattara inaka inaka kabarmana gida bama son ganinka ka ishemu tana rufe baki yace basai kizo ki fitar dani ba tunda agidan zakariyya nake zaune kutumar uban nan nikake kirawa sunan mahaifi ni ni sameer tafada cike da hayagaga kamar zata rufe shi da duka saboda yakira sunan mahaifinta, lalle sameer yanzu abun har yakai ga haka to kwa zaka gane kuren ka sai na koya maka hankali wallahi ina daga maka qafa amma ba ka gani to wallahi zamu saka qafar wando daya dakai, Saida yabita da kallon sama da qasa tare da kawar da idon sa gefe yana sake hade rai sannan yace musaka rabima kuma dakike nakira sunan mahaifinki kinji nazageshi ko nafadi wata mummunar magana akansa sunan sa kawai nakira zakariyya kuma daman dan afada aka rada masa da ba aso aringa fada da kawai sai asaka masa sunan da kike kiransa dashi kinga muma sai muringa fada amma tunda akasaka masa zakariyya dole muma mace zakariyya kema kuma yanzu kikace min sameer sameer kuma sunan baban papa ne kema kenan sai yace zaiyi fada saboda kin fadin sunan babansa ko uba yafi ubane, kana tayo gadan gadan zata rufe shi da duka papa dake zaune yana kallon su daman in sunayi baya saka musu baki saboda fulani ta hanasa amma da yaga abun nasu yana neman wuce gona da iri yasashi saurin tare fulani yace haba da girmanki dan Allah karki biye masa tundade kinsan halin sa muma hakuri muke dashi wani kallo ta watsa masa da yasashi matsawa daga tare tan da yayi yaja gefe tare da jan bakinsa yayi shiru aransa ya ayyana wlh ko yaron nan zaiyi mata dukan tsiya baze dakatar dashiba tunda ita ta bukaci hakan miqewa sam yayi tsaye tare da kafeta da ido yana jiran yaji me zatayi masa da kwa tagayawa aya zakinta idan ta kuskura hannuta yataba shi ganin yanda ya hade rai kamar kumurci yasa ta dan dakata daga niyar abun da tazo tayi masa sai kawai ta nuna sa da yatsa tace kai ka saurare ni nan bawajen wasan rijiya bane inkana cin qasa to ka kiyayi ta shuri saboda bata da dadi baka san ko wacece ba ko dan Allah fa to ke wace gashide naganki agabana kuma kamar kowa nake ganin ki nade san sunanki maryam zakariyya yar gidan talakawa sannan kuma me fuska biyu wacce bata abu dan Allah saidan cikon wani burin nata da sawa azabatar da mutane daga ke har wancan jankin dan naki kallon ku nake ke zancewa in kina cin qasa to kikiyayi ta shuri kici gaba da abun da kukeyi kar nake kallon ku kuma kibini ahankali dan daf nake da tona miki asiri acikin masarautar nan dan gakkin da ka raina shi yake tsokane maka ido kina ganin kin raineni kamar kin haifeni amma kuma baki isa kimin wata barazana dazaisa inji tsoron ki dan atafin hannuna kike kada kiga ba anan nake zaune ba amma duk wani takun ki ba wanda ba agayamin ina son in fara tanadar kwakwarar huja ahannu na kafin zaman masarauta ya gagare ki dan namiki alkawarin sai anyi miki korar wulakan ci a masarautar nan dai nasakinyi regretting din abun da kika aikata dan haka muzuba dani dake shige kafasa sai ki canza taku ni kuma zan gano kiyi koqarin hanani binciken danakeyi inzaki nasara yaqarasa fada tare da watsa mata wani banzan kallo me cike da gargadi sannan be tsaya sauraron ta ba ya wuce abunsa ko inda papa yake kallaba yafita daga falon ransa abace kana ganinsa kasan ba lafiya ba yana fita yanufi part din momma dinsa...... dabaya da baya fulani tafara ja da baya saboda tsabar firgita da rikice da ya risketa alokaci guda ga wani uban gumi da yagama wanketa daman ance marar gaskiya ko aruwa gumi yakeyi saura kadan ta fadi qasa tayi saurin dafe kujera hannun ta duk karkarwa yake jitayi qafafunta sun mata nauyi sun kasa daukar ta da sauri ta lalibi kujera ta zauna hadi da dafe kanta da taji kamar yana juya mata papa dake tsaye yana mamakin yanayi da ta shiga danshi duk atunanin sa kawai sam yafada ne dan ya tura mata bakin ciki amma sai yaga kuma kamar ta shiga tashin hankali da jin maganganun nasa qarasa wa yayi agabanta zai ruqo hannun ta tayi saurin daga masa hannu tare da yimasa tsawa bace min daga gani banason maganar banzau bayan kana jinsa yagama cin mutun cina amma ka kasa yimasa komai papa murya narawa yace kiyi hakuri kada ranki yabaci nasan da wasa yake miki kuma ai ke kikace kar na...bata bari ya qarasaba ta qara doka masa wata ysawar kafita nace bana son ganin ka anan tafada tana huce tare da nuna masa qofar fita da yatsanta ko motsi beyi ba bare tasa ran zai fita bakaji ba nace kafita tafada qarfi da har saida falon ya amsa.......✍ Kwana biyu kunjini shiru bana danji dadi ne wlh ina fama da ciwon kai amma yanzu Alahamdulillah da sauqi, [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿19&20 Bismilah.......✍         papa murya narawa yace kiyi hakuri kada ranki yabaci nasan da wasa yake miki kuma ai ke kikace kar na...bata bari ya qarasaba ta qara doka masa wata ysawar kafita nace bana son ganin ka anan tafada tana huce tare da nuna masa qofar fita da yatsanta ko motsi beyi ba bare tasa ran zai fita bakaji ba nace kafita tafada qarfi da har saida falon ya amsa...... Miqewa yayi jiki babu kwari sum sum sum kamar wani munafiki haka ya tashi ya fice daga falon da tunanin ganin wannan lamarin da yabasa mamaki  ganin yanada matar sata shiga tashin hankali abun da baitaba gani ba kenan yasan tsayayyiyar macece ita baka taba gani alamun tsoro atattare da ita kuma bata karaya awajen magana amma yau wandata raina tayi jika dashi ma yazo ya gaya mata maganar da har damuwa ta bayyana a fuskarta  qarara takasa boye shi kuma bata tanka wa sam ba har yagama ya fice yabata waje amma kuma yanzu zatazo ta sauke akansa amma bari yasa aje akira masa sam yatambaye shi shin abunda yake fada gaskiya ne ko kuma qarya yake dan ya tura mata haushine kawai yasa shi yi mata hakan da tunani ka fal cikinsa har yaqara sa part din Ammah tunda daman adakin ta ya kwana yazone su gaisa da fulani sai kuma wannan abun yafaru aka rabu bata dadin raiba yana qarasawa yatarar Ammahn bata falo sai kawai yayi zamansa akankujera yana qara tunano magan ganun sam da shi kwata kwata yakasa gane inda suka dosabe dadeda zaman ba sai ga Ammah ta fito fuskarta dauke da murmushi ta qarasota zaunakusa dashi tace har kadawo kenan da wuri haka yace eh wlh dakegurin maryama nafara shiga daga nan kuma nayo nan kallonsa ta danyi sannan tace a'a to bakaje fada ba kenan yace eh fasawa nayi zanje anjima tace to shikenan Allah yakaimu jimawar yace Ameen yauwa dan kiramin me sunan baba awayarki naga har ya fita dan bansameshi a part din may arm a ba naga harya fita kitashi inji yatafi wajen aikine ko kuma yana cikin nan baikai ga fita ba tunkan yagama rufe baki ta amsa masa da to sannan ta dauki wayar tana cewa nima daman ina neman sa bari in kirasa taqarasa maganar tare da dannawa number sa kira bugu biyu ya daga yanadagawa ua gaida ita bayan ta amsa take sanar dashi cewa yazo papa nakiran sa ok kawai yace daga nan suka katse wayar ta maida duban ta ga papa tace yace gashinan zuwa yace to daga nan suka ci gaba da hirar su ko kadan be bata labarin abun da yafaru ba kawai wata hirar suka cigaba dayi... *FULANI* bayan fitar papa hannu ta dora akai tashiga rarraba idanu cike da tashin hankali da bata taba tsintar kanta aciki ba a fili tafara cewa na shiga uku me yaron nan yake nufi da duk wani takuna ana gaya masa waye munafikin da yake akusa dani yazama dole incanza taku agidan nan to taya ma akayi nayi sake har wannan dan qaramin alhakin yasan me nake aikatawa acikin gidan nan kalamansa ba qaramin tayar mata da hankali yayi ba dan rabon da tashiga irin wannan tashin hankalin har ta manta shiru tayi nadan lokaci sai kuma can tayi zunbur ta miqe tsaye tafara zagayawa a falon tare da saka hannuwan ta duka abaya tana zagaye tayi can tayi nan abun duniya duk yabi ya isheta tama rasa tunanin da zatayi kamar wannan yaron har yakai girman da zai zo yana gaya mata magana son ransa lalle dole tayi maganin sa inyasan wata ai besan wata ba sai ta nuna mishi shidan qaramin kwaro sai ta juyar masa da tunanin sa yanda baya zato sai ta koya masa hankali fiye da tunanin sa sai ta gasa masa aya atafin hannun sa haka tai ta faman surutai ita kadai da ayyana abubuwa iri iri da zatayiwa sam kala kala daga yau zai gane shayi ruwa ne daqarfi tace qarya kake wallahi nafi qarfinka kai ka isa kasani shiga damuwa yaushe kazo duniya to wallahi qaryane koma waye yasaka sai nakoya muku hankali sai na nuna muku kuskuren shiga gonata ba atakani in kyale sai nasaku kunyi nadama sa min ido da kukayi cikin rayuwata taqarasa fada tana fitar da wata iska me zafi daga bakin ta tare da cije baki tana karkada kai kujerar ta koma ta zauna tare da dauko wayar ta takira wata number ana dagawa ta tashi daga falon ta nufi dakinta ranta amugun bace dasauri sauri take tafiya kamar zata tashi sama tana zuwa bakin qofar ta turata da qarfi kamar zata ballata tana shiga tabugo qofar da qarfin gaske...... Sam Ransa fess yake jinsa dan yasan ko banza de yasanya mata tsoron sa aranta duk dade yasan bata da gaskiya amma de babu abun da yasani akanta kawai de yayi mata hakane dan yagano abun da yake zargi kuma zarginsa ya kusa zama gaskiya yanzu tunda yagano logonta yanzu zai qara saka mata ido har Allah yasa yagano komai da wannan tunanin yaqara sa shoga falon Ammah da sallama abakin sa momma ce ta amsa masa sannan yaqarasa shiga cikin falon ya samu kujera ya zauna yana facing dinsu sannan ya shiga gaida momma din ta amsa masa fuskarta asake tana qara duban dan nata da kyau abun alfaharin ta Amra dake kan cinyar momma tana buga game awaya batasan wanda ya shigo ba tade ji anyi magana amma bata tantance muryar waye ba saboda hankalinta kacokan yana kan game din datakeyi shiyasa takasa dagowa taga ko waye shima kuma hankalin sa nakanta yana kallonta ganin har yanzu hankalin ta nakan game yasashi ce ke me yahana ki zuwa makaranta yafada da dan daga murya saura kadan tasaki wayar hannun ta Allah ya taimaketa tayi saurin tare ta tare da mikewa zaune tana muzurai da idanuwa sannan tashiga kame kame tana marairaice murya tace bani da lafiya fa yau kwanana biyu a kwance wani kallo ya watsamata da yasata yin shiru bata gama fadar abun da tayi niya ba shiru tayi tana turo baki tana qara matsawa kusa da momma qasa qasa tace momma kice masa banda lafiya bayan bezo ya dubani ba amma zaizo yana wani zare min ido ni wallahi ma na matsu yatafi harar wasa momma tayi mata sannan itama qasa qasan da murya tace au hakama kikace to bari ingaya masa da sauri tace rufamin asiri momma so kike yakarya miki ni tace asuwa yaza ayi inso a karyamin auta ta momma sauri nake in kuma intafi to nazo kuma kintsaya kina biyewa wannan sakarar yarinyar muryar sam takatse musu zancen da sukeyi qasa qasa dagowa momma tayi tana kallon sa sannan tace to inbazaka iya jiraba ai qofa abude take mutum dai bakin halin jaraba maganar momma ba qaramin sosa mishi rai tayi ba amma ba yanda zaiyi tunda itace dole yayi hakuri da ita miqewa yayi yace fine kawai yadaga qafa zai tafi tace wallahi idan kabar gurin nan sai na mugun saba maka har inkira kazo kuma shine zakatafi saboda gaka isashe da mai ko to bismillah jeka cak yaja ya tsaya shi be tafiba shi be zauna ba jin gakan yasa Amra tashi daga gurin ta tafi dakin su saboda duk rashin mutun cinta da rashin kunyar ta inde za ayiwa mutum nagaba dasu fada ko kuma za ayi wata maganar da bai kamata suji ba to zasu tashi subar wajen wanna tarbiyar momma ce ita ta dora su akai dan hakan yanzuma jin zata fara yimasa fada yasata tashi tabat wajen kuma daman da biyu ta tashi tasan ko ta zauna ma daga qarshe zai iya sauke fushin sa akanta shiyasa tayi saurin guduwa, ahankali yadawo ya zauna awajen da yatashi yayi shiru tare da qara murtuke fuska ya hadeta waje daya kamar an ajiye kunu yakwana haka fuskarsa ta koma bata damu da ganin fuskarsa hakaba saboda inda sabo tasaba ganin ta ahaka dan haka tayi shiru tana binsa da kallo tare da yimasa addu'ar Allah ya shiryeshi yadena wannan dabi'un da kwata kwata bata qaunar taga yanayi duk datasan abune me wahala yadena saida tagama jan lokaci batare da tace masa komai ba shima kuma ko dagowa ya kalleta ba beyiba kawai yazauna tare da cusa lip dinsa abaki yana ciciza da qarfi daman da wani fushin ya fito gashi kuma yazo itama taqara masa wani, dan numfasawa tayi sannan tace ya maganar da nayi maka tun kwanakin baya kamaida ni yar iska baka cemin komai ba tunda ban isa da kaiba bakai matsayin da zakace min ga yanda kukayi ba ko to ni nayi maka tunda ni nadamu shiru yayi na dan wani lokaci sannan ya budi bakin sa da kyar yace wacce maganar kuma namanta riqe baki tayi tana kallonsa da mamakin ranin hankalin sa dan zata iya rantsewa batare da rantsuwa tacita ba yana sane yasan wacce maganar kawai rainin hankali ne irin nasa cike da bacin rai tace kamanta to tashi kabarmin waje kar nasake ganin qafarka anan duk lokacin da ka tuna kazo tashi kabace min dagani ba kunya ba tsoron Allah kwa ya miqe ya tafi har yakai bakin qofa sai kuma ya tsaya tare da juyowa yana kallon ta ganin ta dauke kai daga gare sa yadan shafo gemun fuskar sa sannan yace tun lokacin nagaya miki kuma mun gama magana dake kaf matan garin nan ba wacce takai matsayin in kulatama bare in aure qarewa ma ni bana ra ayin aure yanzu saboda ba mace da ta isa ince inasonta nibanma ga abun so a mace ba da harkuke naniqamin wata kucaka wacce ake neman kai da ita ni koda zanyima ai bata irin wadanda zan kula bare kuma har takai in hada guri da ita amatsayin mata bazan iyaba kucewa iyayen nata suje su nema mata wani irin ta amma baniba dan ni ba class dinta bane ni wlh nama tsane ta da kinsan yanda na tsaneta da baku qara yimin maganarta ba, yana gama fadar haka yasa kai yafice daga falon, tagumi momma tayi tana tunanin maganganunsa sosai yabata mata rai itade batasan yanda zatayi da wanna yaron ba dan yafi qarfin ta zaman waje da yayi yasa gabadaya ba tsoron fadar duk kalmar da tazo bakin sa wajen wata bakwai kenan da tayi masa maganar tun awaya amma sai yayi mata banza yace shi ba yanzu zaiyi aure ba ta rabu dashi ta zuba masa ido daga baya taqara yi masa maganar akwai yar kawarta da ta nuna tana sonsa kuma iyayen tama suka goyi bayan hakan amma da yake shi be gaji mutun ci ba shine ya bijire ba a isa ayi masa magana ba sai yabarka da magana kuma ko ajikin sa yaqara gaba batasan yanda zatayi dashi ba wallahi kullum halayen sa gaba suke basa raguwa ko kadan tana cikin tunani kawai taji saukar ruwa akan fuskar ta ashe hawayen takaici take batasan ma da zuwansuba sai zubarsu da taji hannu takai zata goge taji wani hannun daban akan fuskarta an shiga share mata su dagowa tayi dan ganin me share mata dan tunanin tama yafi bata ko Amra ce saboda itakadai ce idan taga ta shiga damuwa take kwantar mata da hankali shiyasa duk tafi ji da ita saboda itama tana jin tausayin ta amma ga mamakin ta sai idanunta suka sauka akan wanda bata taba tsammani ba sam ne tsaye agaban ta ya zuba mata ido cire hannun sa tayi daga kan fuskarta tana harararsa tare da nuna sa da yatsa tace don't touch me again if not I will slap ur face tafada tare da mikewa daga gurin memakon ya bata hakuri ma a'a kawai sai yadage kafadar sa irin I don't care it's ur fault is not my fault sannan yadau wayarsa da yabari daman yazo dauka yana dauka kuma shima yayi ficewar sa yana fita drivern sa yazo ya bude masa qofa yabar masarau tar ma gaba daya yama manta da ance papa na nemansa, *CIKIN MASARAUTA* "shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......✍🏿 [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿21&22 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ CIKIN MASARAUTA*    "shela akafara yi cewa ance duk wani ma aikaci kama daga manya da yara tsoho da yaro mace da na miji cewa uwar masarauta na neman kowa da kowa ya hallata a babban fili taro ba arage kowa ba har yaran masarauta zasu iya fitowa hakade me shela yake ta zagayawa yana fadar haka saida ya karade kaf masarautar yana fada kowa kuma yaji inda masu harama suka fara shirin fitowa danjin abun da zai wakana wasu kuma danjin gulma suke fitowa wasu kuma suna tsoro da fargabar fitowa  kar wani abun suka aikata da za ayanke musu hukun ci agaban mutane saboda wataran baka san me kayi ba za ataraku ayimaka hukun ci agaban mutane shiyasa kowa de da abun da yake sakawa aransa.......     dan danan gurin yafara cika da mutane kowa inka gani inma bezo ba to yana shirin zuwa wajen adan qanqanen lokaci gurin ya cika kowa ya hallara agun dai dai kune kawai basu qaraso ba, Mery dake kitchen tana so tayi sauri taqarasa aikin da takeyi tafita kar abarta abaya Ammah ce taqaraso cikin kitchen din zata dauki abu ganin yanda mary ke sauri tace ke lafiyar ki qalau kuwa inazaki haka naga sai faman sauri kike sada kanta qasa tayi cike da ladabi tace Allah yataimakeki uwargidan sarki ai anyi shela ne ana bukatar kowa ya hallara a babban fili shiyasa nake sauri taqarasa tare da qara sunkuyar da kanta jinjina kai Ammah tayi sannan tace to kibari idan kin dawo kya qarasa kar kijawa kanki laifi kamar ta zuba ruwa aqasa tasha saboda dadi shiyasa take jin dadin aiki a qarqashin ta matar tana da sauqin kai bata da jiji dakai yanda take mu'amala da bayinta da wasu mutanen sai ka rantse ba agidan sarauta take ba bare kuma matar sarki nomal take daukan kowa ganin take daidai suke da ita, godiya tayi mata sannan tafita cikin sauri ta qarasa dakinta tana tura qofa sukayi karo da Azeema hakuri ta bata sannan ta cire kayan jikin ta ta canza wasu duk acikin sauri takeyi tana gamawa tabude qofar zata fita Azeema tayi saurin tsaodata da tambayarta ina zataje taga tana sauri cike da qaguwa tace mata ananeman ma'aikata cikin masarautar nan za ayi sanarwa ko kuma za ayiwa wani hukunci bakinta haryana karkawar sauri wajen cewa nima zan iya zuwa ko sai iya ku karkada mata kai tayi alamar sannan tace inkinso zaki iya zuwa mana amma de kibi ahankali tunda ke bakuwace kar kije kiyi wani kuskuren da zaisa a hukuntaki dan any mistake game over zaki iya jefa kanki cikin wani halin tana gama fada tayi gaba tace kisame ni awaje banaso inzama qarshen zuwa da sauri Azeema tace to muje ai ba abun da zanyi tare da jawo hijab dinta dake jikin wardrobe ta ruqoshi ahannu saida tafito taqarasa sakawa tana Allah Allah kar ta hadu da Ammah saboda tunjiya da tace tatafi bata qara fitowa ba dan haka bata qara ganin taba daman batason su hadun shiyasa taqi fitowa  Allah cikin ikonsa kwa basu haduba har suka fice daga part din suka nufi gurin tundaga nesa suke hango mutane a zazzaune wasu kuma a tsugunne kale kale Azeema ta shiga yaude gata tama yawo acikin masarauta tunda ta fito take addu'ar Allah yasa taga mahaifin ta cike da farin ciki aranta suka qarasa gurin suma suka samu waje suka zauna kamar yanda kowa ya zauna, bayan zuwan su ma wasu suna ta qara fitowa inda Azeema take baza idanu lungu da sako duk wanda ya taho sai ta bishi da kallo amma Allah besa ta ganshi ba tunani tafara to kode baya gidan wancan mutumin qarya yake musu to amma akan me zaiyi musu qarya bama qarya bane wata zuciyar tata tabata amsa shiru tayi tana qara nazarin abun, sunkai wajen minti goma agurin kafin daga bisani sarki yataho tare da muqarrabansa suna mara masa baya wasu kuma agabansa dukde ankare sa yanda ba kowa zai gansa ba suna tafiya suna yi masa kirari gyara kintsi da kyau gyara kintsi da kyau takawarka lafiya sarkin sarakai Allah ya kare gabanka da bayanka kafi qarfin makiya saidai kai kaga bayansu bade suga bayanka ba dan sarki jikan sarki uba ga sarki nan gaba kuma kaka ga sarki gaba sarauta baya sarauta muliki ajinin jikin ka yake babu me ja dakai duk wanda yace zai gwada saidai a haifi wani bade shiba sarki me adalci acikin masarautar adalai aikin ku na kyau komai kukayi daidai ne bakwa kuskure tsarin ku nadaban ne Allah yaqara maka lafiya da nisan kwana yabaka tsawon rai me inganci hakade suke tafaman zabga masa kirari har suka qarasa inda yasaba zama suka nufa duk wani wanda yake awajen saida ya miqe gaba dayan su suka miqe tsaye saboda sarki zai zauna dole sukuma sukasance a tsaye yafara zama tukunna su zauna, suna qarasawa fadawansa suka baza masa babbar riga tare da juya masa baya dan yasamu damar zama (kunsan ba a ganin zaman sarki) bayan yazauna mutane duk suka gurfane agabansa ana diban gaisuwa kowa da kallar gaisuwar da yake saida suka kai wajen minti biyar ana gaisawa sannan kowa ya koma wajen sa ya zauna ana kuma jiran isowar uwar masarauta basufi minti biyuba  itama ta taho tare sa mabiyan ta guda uku daya agefen hagunta da damanta dayar kuma abayan ta haka take tafiya cikin isa da izza da takama da tinqahon ita ta isa kana ganinta kasan zallar mulki ke yawo ajikin ta tun akan takun ta zaka fahimci hakan yanda take takawa daidai kamar bata son taka qasar gimbiya maryama fulani uwar masarauta meji da kanta kenan itadin fa ta bance a masarauta haka take tafiya har suka qaraso wajen fadawan sarki ne suka fara yi mata kirari da gimbiya gimbiya matar sarki uwar sarki kuma kakar sarki Allah yaja da ranki Allah ya kawar da idon maqiya akanki Allah yakara girma da daukaka tafiyar kide ahankali uwar gida agun sarki mahaifiya ga abun alfaharin mu sarki me adalci  kowa nakine komai nakine kiyi yanda kikeso acikin masarauta masarauta takice kece uwa agunta kece gatan masaurata saboda jajircewar kine ba ataba samun matsala ba komai yake tafiya daidai da bake da bamu tunda dake muma muna nan duk inda kike nan muke Allah yaqara muku lafiya ke da sarkin mu abun alfaharin mu Kowa yace zaiyi dake shi zaiga daidai duk wanda yayi ba daidai ba dole yaga ba daidai ba duk wanda yayi da kyau shizaiga da kyau, saiwani cika take tana batsewa tare da zama tana dora qafa daya kan daya tare da kafe dukan ilahirin muatanen dasuke gurin da kallo ganin ta zauna yasa gurin ya kidime da hayaniya kowa nafadar albarkacin bakin sa wajen gaida ita hannu ta daga batare da tace komai ba kowa nagurin yayi diff shiru gurin yayi kamar babu kowa kamar wadanda ruwa yacinye yatafi dasu haka sukayi shiru tare da sada kansu qasa kowa na fargabar abun da zasuji daga gare ta babu wanda yadago saima qara danna kai qasa suke kamar zasuyi sujjada, acikin rashin sani Azeema ta dago dan ganin matar da tazo tana tunani ita kuma wace tunda ba sosai take jin kirarin da akeyi ba bare tayi tunani ko mahaifiyar sarki ce hakan ta dago tana qare mata kallo caraf kwa fulani ta kamata tana kallon saurin dauke kallon ta tayi daga gare ta ganin irin kallon da ta watsa mata tsayawa fulami tayi tana qare mata kallo da tunani kuma wannan daga ina saboda kaf ma'aikatan babu wanda bata sani koda sabon zuwane tasanshi idan kuma wanine zaiyi bako to nan ma sai yasanar da ita kuma idan bakon yazo anje ta ganshi kafin yazauna amma itade batasan wannan fuskar ba amma yanzu ba lokacin tambayar ta bane zata bari idan an watse zata sa akorawota taji daga gidan uban da take dan haka kawai tayi saurin ajiye tunanin agefe tare da sawa ayi mata hukuncin dagowar da tayi alhalin kowa kansa na qasa amma ita tafi kowa tafi qarfin ta sunkuwayar da kan, bazato ba tsammani kawai taji saukar bulala agadon bayan ta ba shiri kwa ta hau susa bayanta saura qiris tasaki kuka dan ba qaramin shigarta tayi taji zafi sosai kawaide dan tana da dauriya ne amma da sai tayi kuka wata aka qara mata akaro nabiyu wanda bata tunanin zata iya jurewa dan haka tasaki kukan ta amma bata bari ya fito ba kawaide hawayene suka shiga wanke mata fuska cike da takaici ta dago tana duban me dukan nata sannan tace kayi hakuri dan Allah wani kallo ya watsama ta me kama dana tsana yanaso ya gargadeta akan abun da tayi saidai fulani bata bashi daman ba tace kawai ya hukun tata abun da tace masa kenan shiyasa ya daketa kawai yaja bakinsa yayi shiru tare da barin wajen ya koma can inda yake ya cigaba da tsayiyuwa tunda ga lokacin Azeema bata sake gigin dago kanta ba ta sunkuyar dashi kamar yanda kowa yayi. *Bossay* cikin shirinsa tsaf yafara saukowa daga matattakalar benen yana ta faman sauri yana gama fitowa kwa sukayi karo da Ammi tsayawa yayi itama ta tsaya tana binsa da kallo kana tace kai kuma fa ina zuwa daman wajen ka zanzo abban ku ya kirani yace yana hanya gobe zuwa jibi zai dawo cike da murna yace Allah yakawosa lafiya muna jiran dawowar sa yafa yana shirin barin wajen ta qara dakatar dashi tace ai bakasan me zai dawo dashi dinba wutar da ka kunnowa kanka kasan yanda zakayi ka kasheta dan yace tunda har shi zaka mayar qaramin mutum to ka shirya yana da wowa za afara shirye shiryen bikin ku yace insanar dakai aure ba fashi ko mutuwa kayi sai andaura da gawarka dafe qirji yayi yana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nashiga uku Ammi dan Allah da gaske kike tace daman nataba yimaka wasa irin wannan wai mema kayiwa yariyar da har yakai haka kaga fadan da yakira yake min yace duk ni nake sangartaka kana abun da kaga dama dan haka yagama yanke hukunci inshirya yana dawowa za afara shirye shirye duk yanda naso inganar dashi duk dade bansan me yafaru tsakanin kuba amma naso inkareka da roqan alfarmar yabari adan qara lokaci ayi komai a tsanake yace shi sam besan zance ba yanda yace dole haka za ayi dan haka sai kafara shiri tun wuri danni kaina bani da abun fa zan kuma cemasa ya yarda ya hakura, Ammi wlh ni banasonta kice masa banason ta karya min haka wlh ko na aureta bazata taba jin dadin rayuwarta ba gwarama kar ayi auren naan dan wallahi banasonta nifa nama tsaneta gabadaya dan nadade da cire batun auren ta araina kuma nagaya mata amma dayake ita mayyace shine zata bullo min ta wani wajen to muzuba dani da ita bade aure ba zata ga aure dai tayi danasnin aurena wlh a'a Aliyu kar nakuma jin kafadi haka kanaso ubanhiji yayi fushi dakai tundade kai kafara cewa kanasonta kuma har anriga da ankai kudi kaga baka da bakin cewa bakaso dole kayi hakiru ka karbeta hannu biyu kabi umarnin mahaifinka sai kaga daidai nima bason hadin nan naku nakeso ba kawaidai dan ba yanda zanyi kawai kaima kayi hakuri wallahi Ammi bazan iyaba zuciyata yanzu ba ita take so ba tace to komade menene yanzu zacen gama yagama sai kabari idan ka aure tan sai ka qara wanda kake so daga baya kasande magaifinka baze taba canza maganar saba kamar yayi kuka haka yake ji saboda tsabar takaicin da yake ciki yama kasa qaratanka mata kawai yayi gaba zai fita yaje daidai qofa zai fita dadda da fitowarta daga daki taji zancen da suke saida tabari yakai qofa sannan tace mutum sai munafurci yanaso yana kaiwa kasuwa da wayace kace kanson ta da baka sonta ai da baka bari har akai kudiba dan haka aure ba fashi ko anfasa nidakain zan dauramaka kinibabai kawai wallahi yaran zamanin nan baku da ta ido ko kulata beyiba yayi ficewar sa ita kuma taci gaba da surutanta akansa kamar yanajin ta Ammi ce tace dadda gaskiya de dande bakisan yarinyar nan ba amma da ko ke dakanki sai kince kar ga aureta bata da tarbiya ga rashin sanin kanta bata da kamun kai ko kadan nasan wallahi ya aurera zata bashi wuya shiyasa nima banaso ayi aure nan gashi kuma wai nan da sati daya zuwa biyu dadda tace to meye aciki wanann abu dan sulula kawai dauka zaki ki sulalawa mutane waya ki sanar dasu nibanga abun wuriba anan yaro ya girma har yakusab wuce aure amma yaqiyi ni wallahi yama yimin daidai da ya yanke masa wannan hukun cin amma itama yarinyar zataci qaniyarta bari ta shigo hannu nida kaina zan bata kashi in koyamata hankali sai ta nutsu duk haukan dake damun ta zansa ta saukeshi kedai bari ayi auren kikagani shima zai dena fadar bayason ta watakil sun samu sabanine shiyasa zuciya take dibansa amma da zaran anyi auren to anyi me wuyar kar ki wani tada hankalinki akan wannan dan qaramin abun daga qarshe ma kizo kiji kunya idan kika gansu suna soyewa dan haka kiyi shiru da maganar zakiga abun mamaki nafada miki dan murmushi Ammi tasaki sannan tace to dadda shikenan Allah yazaba masa mafi alkhairi agare sa idan kuma ba alkhairi bane Allah yakawo masa mafi alkhairi ya musanja masa da alkahairi Ameen dadda tace daga nan de suka ci gaba da tattaunawa akan lamarin bikin da yazo musu barka tatan lokaci guda..........✍ Malejjj [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿21&22 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ *FULANI*    "saida ta gama shan qamshinta da yi musu kallon wulakanci sannan ta budi baki da kyara tafara magana, "kowa shiru yayi yana sauraronta" shekara da shekaru masarautar nan tana zaman lafiya amma yanzu da alama munafukai sunyi yawa ana daukar zancen masarauta anakaiwa wani lokacin to daga yanzu zamu qarfafa sa ido akan kowa zamu kwarara bincike ganin mungano wanda yake mana zagon qasa yana daukar zancen wani ana kaiwa waje, daga rana irin ta yau mutum yasani duk wanda aka kama dahaka to hukuncin kisane zai tabbata akansa ko da alamar rashin gaskiya aka kama mutum da ita to yasani masarauta baza ta kyaleshi ba kuma hukuncin mu baibar kowa ba kama daga kan mace ko namiji ba ruwan mu da girmanka ko qanqantarka duk tsufanka baka fi qarfin mu ba hukunci dayane gaba dayan ku dan haka sai akiyaye......          "dan dakatawa tayi tare da jan numfashi sannan taci gaba. Sannan abu nagaba shine daga yanzu za ayi canjin aiki kowa zaibar akin da yake acanza masa da wani hakane zai qara bamu damar gano me yi mana sa ido....dan haka yanzu nan za afara ba tare da bata lokaci ba, nan ta umarci dogare da fadawan sarki da sufara kiran mutane daya bayan daya aka ringa kiran su suna fitowa za atambayesu abun da sukeyi da kuma inda suke aikin idan suka fada sai ace to daga yanzu ga inda zaka koma haka aka ringayi har aka kai qarshe duk wadan da aka kira suna gefe, gaban Azeema ne yafara dukan uku uku gani ita kadai tsulum aguri guda ba a kirata ba saboda ba asan sunan taba gashi mutane duk sunbi sun zuba mata ido suna kallon ta saboda kaf gurin in kacire mary babu wanda yasan da zaman ta agidan dan me gadin ma da yabarta ta shigo zuwa yanzu ya manta da fuskarta bazai iya gane taba, duk sai take jinta atakure gashi ba ace mata ta tashi ba kuma tanaso ta tashi amma tana tsoron jawa kanta wani laifin sai da nasani fitowa take dama bata fito ba haka take ji gashi kuma wanda ta fito saboda shi bata gansa ba, babu wanda yabi takanta har aka gama warwarewa. wanine yaje kusa da fulani murya qasa qasa da ni kaina bansan me yace ba bayan yagama kitsa mata ya matsa gefe ya koma inda yabaro, girgiza kai fulani tayi cike da qara tamke fuska sannan tace ina sarkin dorina matsowa yayi jikin sa na bari yace Allah qara miki lafiya Allah.......    zai fara yimata kirari ta dakatar dashi cike da bacin rai tace aje afito min da Hamza da kuma wannan mutumin da suke tare har yanzu basu rabuba kenan aje afito min dasu yau za akoya musu hankali tunda basu dashi tafada tana ta faman hura hanci da gudu sarkin dorina ya tafi wajen da yasan suna can, bayan tafiyar sa fulani tasa aka kirama ta A Azeema jiki asanyaye ta tashi tazo kusa da ita tare da durqusawa kamar yanda ta ga anayi saida fulani tagama qare mata kallo kamar me son gano wani abun sannan daga bisani tace daga ina kike da iznin wa kika shigo gidan nan batare da sani naba tafada tana qara zuba mata idanu , itade Azeema tashiga tashin hankali batasan wane abu zatace dan jitayi jikin ta gaba daya ya hau bari kar taje ta fadi wani abu da zaisa agano qarya take gashi kuma  ko sunan wacce take zaune awajen tama bata sani ba bare tace ga gurin wace ta tazo, tana cikin tunanin abun da zatace kamar daga sama taji ance maryama bakuwatace jiya tazo gaba dayan su suka juya suna kallon Ammah da ta qaraso wajen daman tasan za arina shiyasa tunda ta duba dakin taga batanan tunanin ta yabata watakil tace zata bi mary shiyasa ma hankalin ta yakasa kwanciya ta taho gurin da sauri gudun kar wata matsala ta faru ilai kuwa tana tunkaro wajen taji abun da fulani kecewa kuma bisa ga dukkan alamu bakuwar tata take tuhuma shiyasa tayi saurin katse ta ta bata amsa, gaban fulani ta qaraso suna fuskan tar juna sannan tace ayi min afuwa ban sanar dake tun jiyaba daman bari nayi sai daddare sai inzo da kaina ma insanar dake, kallonta fulani tayi sannan tace bakuwa daga ina nidai nasan ban taba ganinta a dangin kuba bare kice min yar uwarkice tafada tana qara maida hankalinta tana jiran taji amsar da zata bata, dan murmushi tayi sannan tace ayya ai ba yar uwata bace daman kawaide wata qawata ce da muke mutun ci da ita shine tace min in taimaka inne mawa yar me aikinta aiki anan saboda ita bata da halin da zata riqe uwar ta riqe yar ga dan qaramin yaro agaban ta idan kuma tace yarinyar tabar mata gida to batasan inda zataba gashi kuma suna buqatar taimako dan me gidan ta ya rasu sannan kuma dangin ta bamasu hali bane name taimaka mata shiyasa tayi min magana nace mata ba matsala ta kawota baza arasa ba to kinji dalilin da yakawota gidab  kamar me nazarin wani abu haka ta tsaya tana kallon su suduka kafin da ga bisani tace to shikenan amma akiyaye nan gaba kafin wani ya kwana acikin masarautar nan yakamata ace ansan da zaman sa bawai kawai inganta ba Ammah tace in sha Allah za akiyaye yanzu gata nan idan da aikin da za abata sai abata in kuma babu sai inzauna da ita ashena tana taimakawa mary da aikace aikacen shiru tayi tana buqatar jin abun da zatace, itama fulanin shiru tayi kamar bazatayi magana ba sai kuma can tace a'a da akwai daman yanzu ancanzawa kowa me aiki kema wacce take miki da ba it zata ci gaba da yimiki yanzu ba, dan murmushi Ammah tayi duk da bahaka taso ba aranta amma afili sai ta nuna halin ko inkula fuskarta asake sai kawai tace to ai shikenan duk yanda kikayi ai daidaine ni zan wuce idan angama sai tazo ta kwashi kayanta ta fada tana juyawa tare da barin wajen, da wani irin kallo fulani ta bita tana hararar ta dan haka kawai bata yarda da ita aranta tace basai in kin qara ganin ta ba zata zauna dani zan saka ido akanta inma qarya kike zan ganoki nan bada jimawa ba, tana gama tunanin ta maida subanta ga Azeema sannan tace wannan amaida ta party dina anan zatana aiki daga nan kuma tace kowa yakama gaban sa kai tsaye kar wanda ya nufi inda yabaro yanu fi inda aka canza masa duk wani abu da yake buqata acan zata sa aje a amso masa daga baya amma bata yarda wani yake inda yabari ba, haka aka ga ma yanke hukuci zama yatashi kenan amma ko A sarki bece ba sunan yana gun azaune amatsayin sarki saboda inde tana gurin bashi da bakin magana dole yayi shiru sai abun da tace dan koda wani abun yayi masa ba daidai ba to beda ikon tanka mata dande kawai kar ace masarautar ba sarki shine amfanin sa amma baya ga haka bashi da wani amfani aciki komai a hannuta yake sai yanda tace akeyi.... Kamar yanda tace hakan kwa akayi kowa ya nufi inda aka canza masa tare da raka ko wannen su saboda ba kowane yasan ko inaba aciki shiyasa tasaka akayi wa wasu jagora zuwa inda basu sani ba, gurin yazamana babu kowa duk sun watse daga ita sai sarki sai muqarrabansu da zasu mara musu baya idan sun tashi tafiya saida taga kowa yatafi akan idonta sannan suma suka miqe dan barin wajen. suna shirin tafiya kenan saiga su sarkin dorina tare da Hamza da baba suna qarasowa wajen dakatawa sukayi da tafiyar suna kallon su dan ita har tama manta dasu sakamakon maganar yarinyar nan da sukayi shine ya kawar mata da hankalinta akansu tama manta dasu gaba daya, suna zuwa gabansu suka zube agabanta baba na gaida ita amma banda hamza ko motsa bakin sa beyi ba bare tasa ran zai gaida ta, wani abune yazo mata wuya ya tsaya mata cikin hargagi da masifa kamar zata rufesa da duka tace kai gaka isasshe damai ko waikai dan gidan ubanwaye da uban me kake takama naga take taken yayi yawa agidan nan kullum rashin mutun cinka qaruwa yake naga alamar baka jin duka ko uban me ya hanaku fitowa saboda ba a isa daku ba hardaki tsofe tsofe dakai baka gudun abun da zai tabaka to kasani ko kadan baza kaban tausanyi da zansa a horaka ba cikin rawar murya baba yace wallahi banji ba lokacin da aka sanar ina bacci sai yanzu da akasa akiramu aka tasheni amma bada gangan nayi hakan ba kimin afuwa agafarce ni bada son raina hakan ta faruba yafada yana sunkuyar da kansa qasa, banza tayi masa sannan ta mayar da dubanta ga hamza da duk abun zancen datake masa ya nuna kamar ma badashi take ba ko kallon inda take beyiba, dubanshi ta qarayi tace kai kuma uban me kakeyi baka fito ba ko isarce tasaka qin fitowar, sai alokacin tasamu yadago yana kallon ta ido cikin ido sannan yace bana jin dadine shiyasa banfito ba yana gama rufe bakinsa tace qarya kake shiru yayi be tanka mata ba qara harzuqata yayi tayi gaba kawai tacewa maidorina ya hukun tashi da dorina sannan sukashi dakin qasa tana gama fada ta tafi fuuuu kamar zata tashi sama sarki ma gaba yayi abunsa be saka musu baki ba, Sarkin dorina matsowa yayi kusa da hamza amma yakasa daga dorinar bare ma yakita jikinsa saboda har yau tabon da yayi masa bai goge ba yana nan shiyasa yake tsoronsa kuma tunda ta tafi kwa ba abun dazaisa yadake sa gwara yabarsa zaidai kaisa godan qasan shima saida yace yaje amma bazai yarda yabisa ba gudun kar yaqara mazgesa a hanya cikin lallami da lamana yafara yimasa magana kaga nifa ba dukanka zanyiba kawai katashi kaje inda tace din ni nabarka lafiya yafada yana saurin barin wajen gudun karma yayi masa wani jawabi tashi baba yayi yace ni bari intafi yaro kai kuma kaje inda yace maka din kar ka kuna jawowa kanka matsala tashi yayi shima yace baba muje ba inda zani inta isa tazo ta jani ta kaini wallahi matar inba bata bini ahankali ba sai na koya mata hankali(🤔uwar masarutar guda zaka koyawa hankali lalle wanga mutum akwai tsaurin ido yaseen nidai ba ruwana🤐 idan tajika), babane ya kalle sa yace a'a karkace haka kaje kawai ni wlh banason karinga yimata wannan abun kai ko tsoronta ma naga bakaji bakasan tasa ayi maka wani mummunan abun kallon baba yayi kawai yadanyi murmushi me cike da ma'noni kalakala sannan yace kar kadamu dani baba muje ba abun dazai sameni dan nafi qarfin ta wallahi bata isa tayi min wani abun ba yaqarasa fada yanayin gaba baba de da kallon mamakin irin qarfin halinsa yake sannan shima yabi bayansa yana dan jin dadin ganin shima ba ayi masa wani hukuncin ba lokacin da ya isa dakin su yatar da Hamza har yacire rigar jikin sa yayi kwanciyar sa hankalin sa a kwance baba ya kalle sa ya kar kada kai yace Allah ya shiryeka amma nide wlh inajiye maka abun dakanje yadawo nide wallahi ka barmin daki karkaja min kaga ahakama batasan guri daya muke kwanba da bansan wane danyen aikin zata kuma yimana ba dan Allah ka rufamin asiri ka rufawa kanka kazo ka tafi wajenan kaji yafada yana zama kusa dashi tare da zuba masa idanu yana jiran yaga ya tashi, tashi yayi zaune baba yama dauka tafiyar zaiyi hat yafara jin dadi aransa sai kawai yaga ya koma yaqara kwanciya yace baba nifa banason mita tunda nace bazani tofa ba wanda ya isa yasani inje ko itace tazo da kanta saidai idan daukata zatayi takaini in kwa ba haka ba saidai ta rabu dani yafada yana rufe idanun sa alamar bacci zaiyi, karkada kai baba yayi kawai batare da yaqara cemasa ko uffan ba yaja bakin shi yayi shiru daga bisani kuma yatashi ya shige bandaki, Kwan kwan kwan hamza yaji ana buga qofar bude idon sa yayi tare da jan tsaki ya kuma juyawa ya koma ya kwanta jin anqara bugawane akaro na biyu yasa shi miqewa afusace ya fito dan zabgawa koma waye masifa, yana bude qofar zai fara zazzaga masifar sai kawai bakin sa ya makale masifar ta koma ciki yakasa furta ko kalma daya sakama kon tozali da idanunwansa sukayi masa da ita cak ya tsaya yana binta da kallo itama shi take kallo...................✍️ tofa wa hamza yagani da yasahi kasa magana kode matar da yake cika bakine tazo da kanta abun da baitaba tunani ba shiyasa yakasa magana ko kuma watace daban saidai gobe maji ko wacece wannan da tasa sashi yin shiru muje zuwa.................✍️ [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿25&26 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ Kwan kwan kwan hamza yaji ana buga qofar bude idon sa yayi tare da jan tsaki ya kuma juyawa ya koma ya kwanta jin anqara bugawane akaro na biyu yasa shi miqewa afusace ya fito dan zabgawa koma waye masifa, yana bude qofar zai fara zazzaga masifar sai kawai bakin sa ya makale masifar ta koma ciki yakasa furta ko kalma daya sakama kon tozali da idanunwansa sukayi masa da ita cak ya tsaya yana binta da kallo itama shi take kallo................... "ita tafara kawar da idonta gefe tare da sunkuyar dakai sannan murya can qasan makoshi tace kaine Hamza? saida ya hadiyi yawu tare da abun da ya makale masa awuya sannan ya kuma dubanta tundaga sama har qasa kana daga bisani yace "eh" Sannan tace uwar masarautace take some ganin ka yanzu nan tace mutafi tare tana wajen gurin nan tana jiranka agun, "wani kallo ya watsa mata sannan yace ita me ya hanata zuwa da kanta kije kice idan ta isa tazo da kanta...yana gama fadar haka ya rufe qofar sa yakoma yayi kwanciyarsa, da mamaki Azeema tabi qofar da kallo tana tunanin wannan waye shikuma da har akace anakiran sa amma wai bazezo ba tazo da kanta amma koma waye yajawowa kamsabala'i dan bega ayanda tazo wajen take nemansa ba da baifara cewa ajen ace bazai zo ba yanda fuskarta take ahade nan kana gani kasan ba sauqi da fushinta ta taho wajenasa Amma shikuma ga abun da yace tabb babbar magana saida tagama tunanin nata sannan tayi gaba abunta, " tana zuwa wajen ta ta sunkuyar da kai tace ranki yadade nasanar dashi amma sai yace wai inje gashinan zuwa danace masa kince mutafi tare sai yace ba yanzu zaizo ba sai yayi wanka zaizo yasameki a sashenki wai kiyi hakuri yanzu zaizo tafa qarasa fada tana kifkifta ido dan itade ko hauka take bazata iya gaya mata abun da yace ba sai taga kamar ita tayi rashin kunyar da hakan be dace yafada ba to amma ita tayiwa zancen nasa kwaskwarima da dan mamaki fulani take kallonta a iya sanin ta da yaron baitaba bata hakuriba amma shine da kansa yanzu yace tayi hakuri lalle wannan abun abun mamakine agareta shiyasa daman da akazo akacemata hamaza yace baza adakesaba kuma bazaije gidan qasan da taceba akaisa ba yama yi tafiyarsa daki dataji hakan shine kawai tace bari tazo da kanta sai ta taho da sabuwar baiwarta Azeema dan takiramata shi ya fitoyasameta awajen, duk da taso yafito din amma jin ance harma hakuri yabata kuma zaizo yasameta shiyasa kawai taji ranta yadan kwanta har sukayi gaba ta tafi part dinta da niyar jiran sa yaqarasa..... (Tab nace kam zaki bushe kwa dazaman jiran sa dan ko qyeyarsa ba zakigani ba aradu) baba ne yafito daga bandakin da sauri ya qaraso wajen yace yarona murya wa naji kaidawaye? "dabansa Hamza yayi sannan yace wata yarinyace wai an aikota tazo ta kirani, "kaikuma me kace mata cewar baba,"nace mata bani zuwa " dafe kai baba yayi yace amma kaide wlh matsalace dakai yanzu har tazo da kanta kace bazaka ba"Hamza yace wallahi baaba baza niba saidai tarabu dani in kuma zata iya shigo wa sai ta shigo "baba yace ohh sai yanzu na fahimceka dan kasan bazata iya shigowa sashen muba ko shiyasa kake cika baki to wallahi idan bakai ahankali ba saboda kai zata iya karya dokarta nakin shiga sashen masu aiki ta shigo tazo wajen ka,"dan murmushi Hamza yayi me qayatarwa sannan yace to mutuncin waye yazube nata ne ai banawa ba ita zata ji kunya kuma daga lokacin zan qara dena ganin mutuncin ta kai bama nikadai ba duk wanda yaji abun da tayi sai ya kalli abun ta wata siga daban saboda a tarihin gidan nan sarakai da matan su basa zuwa sashen ma'aikata kai harma 'ya'ya yansu basa zuwa inda muke saboda girman kai da suka dauka suka dorawa kansu aganin su idan sukazo wajen mu kar sun qasqantar da kansu sai kace mu ba mutane bane, ni wallahi Allah yasa tsautsayi ya kawota nan har video sai nayi mata in watsawa mutane sai qarshen haukan nata. da mamaki baba yake kallon sa yace lalle ne wuyanka ya isa yanka wallahi sai yanzu naqara yarda ka raina matar nan kai kowa na tsoron ta amma kai ko dar bakaji aranka to da wacce wayar zakayi mata? nidai bantaba ganin ka da waya ba! "tashi zaune yayi sannan yace tana ajiye ne bana amfani da ita saboda bata dameni ba banma san abun da zanyi da ita ba agidan nan amma akanta zan daukota addu'a ta shine Allah yasa tazo taga yanda ake aiki da cikawa, "zama baba ya gyara sannan yace nikam inyi maka tambaya ta bakin nata me ka takame da kake ji da kanka har haka dole da abun da kake takama dashi shiyasa ka banbanta da sauran ma'aikata me yasa kake mata haka? "murmushin gefen baki yayi sannan ya mike batare da yace masa komai ba ya nufi hanyar toilet sai yakai bakin qofa sannan yace nataka abubuwa da yawa amma de sirrine asannu kowama zaisan abun da nataka acikin gidan nan saura kiris ta fashe kaida baba ka zuba ido kasha kallo, nan gaba ma sai na fitar da kai daga gidan nan lokaci kawai nake jira. yana kaiwa nan ya wuce cikin bandakin bai saurari cewa baba ba ya shege tare da rufar qofar, Shide baba shiru yayi yana daukar maganar sa duk ashirme da shiririta irin tasa dan gani yake ba wani abu da yataka kawai dai rashin jin tsoro ne kuma ya lura ajinin sa yake baya shakkar kowa shiyasa har yake neman ya gagari kowa tunda gashi ko masu yin hukun ci agidan yasaka musu tsoran sa babu me tunkarar sa yayi masa wani abun koda gimbiya uwar masarau ta tasaka su suyi masa sukuma baza suyi ba shiya sa yaqara samun damar yin abun da yaga dama yi batare da fargaba ba. yana zaune agun yana tunane tunane Hamza ya fito jikin sa duk ajiqe alamar de wanka yayi tunda yafito baba yake binsa da kallo Amma shi kam ko takan sa bebiba duk da yaji ajikinsa baba na kallon sa amma sa ya basar ko kallon inda yake ma beyiba yaqarasa gurin da kayan sa suke shidaman baifiya saka kayan da akabashi na ma'aikata ba duk abun da yaga damar sakawa sakawa yakeyi yanzu ma wasu riga da wando ya dauko kananu yasaka saidai basu kamashi ba kamar ba daidan sa ba haka yasaka su saida yagama shiryawa tsaf sannan ya dubi baba yace baba nayi komai yayi daidai yace kar naje taki kulani, da baba beyi niyar kulasaba amma jin abun da yace yadago yana kallon sa ga mamaki sannan yace wace zata ganka tace baki daidai ba uwar masarautar ko wa?? "dan bata fuska yayi yace haba baba waccen tsohuwar banzar zanyiwa kwalliya mata tafa nake nufi gurin ta zani yafada yana sakin murmushi da kana ganin sa kasan daga cikin zuciyar sa yake direct, "cike da mamaki baba yace daman kana da aure shine amma baka taba gayamin ba a ina matar take baba yafada cike da zumudin jin ta bakinsa , "dariya hamza yayi har kana iya ganin fararen haqoransa sannan yace baba naga har ka qagu kaji ko to nibanda aure kuma bantaba yiba yanzu de nakeson inje infara farautar samowa duk da bansan ina zangan taba amma koda tana wajen waccen wahalalliyar ne sai naje na nemota wauyar ta in fita amma ina fita zansan komai akanta " baba yace bakasan taba ma shine kakecewa matar ka a ina ka taba ganin ta? da har kake kiran ta da matarka? " tsayuwa ya gyara sannan yace baba kasan ance so gamon jini akwai wanda kuna haduwa zaka ji ya kwanta maka to nima hakance ta faru dani, "kallo daya bisa qa ida naimata zuciyata sai ta kamu " Wacce nace maka dazu tazo nemana tsohuwa ta aikota to ita zanje nema yarinyar tamin gashi kuma naga alamar ma bakuwace saboda bantaba ganinta ba sai yau kaga kwa dole inje injiyo news akanta, saboda mamaki kwa baba yakasa cewa dashi komai saidaga baya "yace to Allah yabada sa'a nide ba ruwana aciki idan ka dawo kanufi dakin ka kar inji kar ingani sai komai ya daidaita ka rage neman fitina sai kadawo, murmushi hamza yaqara saki tare da fadada fara'ar fuskarsa "yace baba wallahi ba inda zan koma ina nan idan nagama ganota ma harnan dakin zankawo ta itama daga qarshe innema mata 'yancin kanta tadena bautawa waccen matar, "baba yace dawa zaku zauna saidai idan ni zanbarmuku dakin amma bada niba aciki,"kai baba wallahi kafiya tsoro kai da kake dani kuma meyasa zaka ringa tsoro ko yatsa wani yanuna maka saina karya masa yatsa dan haka kadena tada hankalin ka ka kwantar da hankalin ka kamar kayi bako ya mutu "kaga ni ka isheni da surutu tafi kaban wajen Allah ya tsare dan Allah tafi cewar baba yana magana yana nuna masa qofa, kafada ya daga sama sanna yace ai ko baka koreni ba yanzu zantafi yafada yana nufar qofar fita tare da fara yin waqa......... *Dakece zanyi wuff, zanyi wuff..... Dakece zanyi wuuf zanyi wuuuf... zanyi wuf....... "Kece tawa innda rai da raboo... amanar zuciya kedamketa....* Ahaka yayitayin waqarsa yana tafiya har yafice daga sashen su ya nufi cikin masarautar kai tsaye da shi kansa besan ta inda zai faraba neman taba.....😜😜😜😜🫣🫣,(Allah kutayani da addu'a kar mukai wajen shekara bamu gama ba, wlh yanzu banason yin typing ina farawa sai inji nagaji😂 bansan me yasaba yaseen gaba daya sai ahankali) pray for me ko zanringaji inayi dayawa batare da nagaji ba [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿27&28 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     *__Bossay__*     "bayan ya fito daga gida yashiga mota yabar gidan ransa yana danyi masa zafi saboda maganar auren nan da akayima sa shikadai yasan abun da yakeji, aransa yana ayyaba irin abun da zaiyiwa wannan yarinyar bade tanace sai ta aure shiba kuma ta shiga tsakanin sa da mahaifinsa shine zata biyo masa ta wannan hanyaryasan halin mahaifinsa indai yace sai yayi abu to ba wanda ya isa yacanza masa ra'ayi dan haka. bashida wani abun cewa dole yayi hakuri yakarbi auren ta amatsayin qaddarar sa jiyake kamar yayi hauka afili ya furta duk ni najama kaina da tunfarko bance inason ta ba da shikenan amma yanzu gashi nan tazo ta zamemin qarfan qaya ana korarta tana qara naniqemin sai kace mayya mtsww ya buga tsaki kamar tana gurin, ahaka yayi ta tafiya saida yaje wajen wata kwana bayan ya shiga layin sai yasamu gefen titi yayi parking a gefen hanyar sannan ya dauko wayarsa yayi kira ana dagawa yace yawwa na shigo layin ina zanyi ko intsaya kafito, bansan me akace masa ba daga can bangaren kawaidai naji yace tom shikenan ganin nan zuwa kashe wayar yayi yana qara jan tsaki afili yake cewa yanzu dan rashin mutunci muyi wayar dakai zanzo amma ka wani ce min kuntafi asibiti cike da takaicin maganar da shettima ya gaya masa, kwafa yayi  tare da tayar da  motar sa yayi rivers yaja motar sa ya nufi hospital din kai tsaye dan bazai iya hakuri ba tunda ya fito dan yaganta dole sai yaga hasken idanusa  zaiji dadi.. bewani bata lokaci ba ahanya sakamakon gudun da yake kwararawa adan qanqanen lokaci yaqarasa bayan yayi horn me gadi ya bude masa yashiha yayi parking a parking lot sannan ya fito ya shiga ciki kaitsaye ya nufi office din shettima tunda daman yasani kuma yana kyautata zaton dole suna can shiyasa be qara kiranshi ba ya nufi gurin, "nocking yayi daga ciki akace masa "Come in" turawa yayi yashiga da sallama abakin sa, "amsa masa shettima yayi shikuma yaqarasa shiga ya zauna akan kujerar da take facing din shettima tare da miqa masa hannu suka gaisa yadan fara dube dube yana neman Ameesha dan murmushi shettima yayi yace neman ta kake ko dan sosa kai bossay yayi alamar yaji wani iri sakamakon kamansan da yayi, "tana ciki bacci take cewar shettima " joyowa yayi ya kalle sa "yace bacci kuma at this time? "shettima yace eh mana ai ita yanzu   kasan ba daidai take da sauran mutane ba kwakwalwar ta tana bukatar hutu akoda yaushe anfiso ta ringa bacci yanda zatafi samun sauqi da wuri idan tension yayi mata yawa zata iya samun matsala wani lokutan taringa yin abubuwa kamar ba mai cikakken hankali ba, "cike da gamsuwa da bayanin sa yadan jinjina kai yace ayya Allah sarki Allah ya qara mata lafiya wadanda kuma sukayi mata haka Allah yasaka mata Allah ya toni asirin su, "shettima yace Ameen thumma Ameen yauwa bari na in tabo sam ingaya masa kana nan kaga sai mufara ma maganar yanzu tunda duk mun hadu sai asan abun yi yafada yana qoqarin dauko wayar sa yana danna wa sameer kira, "bossay yace gaskiya de nima abun da nakeso ayi kenan wallahi naji shiru be nemeni ba har yanzu, "shettima dake qoqarin kiran sam yadan dakata ya dago yana kallon bossay shima shi yake kallo,    "Shettima yace ai inba kiransa nayi ba bazai taba kiranka ba bakasan me kayi masa ba ko ai sa'a ma kaci da yabarka haka ai kabata masa rai duk da kafi bata min raima amma ni nawa me sauqi ne shi sai yafini jin haushi saboda shi beda hakuri ko kadan nayima mamaki da har yayi wannan dadewar awajen batare da yataba lafiyar jikin ka ba, dariya bossay yayi yace ai naga alama wayagaya maka be tabani ba saida yabani ajiyar mari ai tundaga nan nadan qara tsorata dashi ni nasan ma watakil ba wani girmemin yayi ba amma wai har yadaga hannu ya kwasheni da mari duk girman nan nawa Allah ma yaso ni babyna bata gani da tuni yasani jin kuyarta wallahi wallahi kufara bashi ruwan buta yarage wannan zafi ran dan wallahi idan baidai na wannan halin ba. bazai samu matar aure ba, ba iyayen da zasu dauki yarsu su bashi dan wallahi wataran sai ya baballa musu ita ya cuce su kuma ya kora musu ita gida dan bazai iya hakurin halin mata ba nidai wallahi shawara nake baku kusamu ruwan buta abashi yasha ko bedena ba zai rage, "tunda yafara maganar shettima ke faman yin dariya saida yaji yayi shiru sannan yace to shikenan zan gaya masa kace abashi ruwan buta zaidena masifar da yake ko, "zaro ido bossay yayi sannan yace la rufamin asiri dan Allah karkagaya masa kaqara jamin yadena kulani tunda daman haushina yake ji" "shettima yace ai badaina kulaka zaiyiba wasu marukan zai baka kasan shifa yafi bawa mari muhimmanci fiye da komai "bossay yace ai naga alama tunda yayi min da yasa naga wuta ta wuce ta gefen idona amma de ba haka yakeyiwa mata ba iya maza yake mara "shettima yace har sumana saidai inbasuyi masa laifiba amma sunayi zai mare su kaamar yanda zai mari namiji haka suma zaimusu dan idan ransa yabaci ba ya bambamce mace da namiji kowa ma daya yake daukansa, "jinjina kai bossay yayi yace amma iya kannen sa dan wallahi idan kamari mace sai ancika tara duk mari daya dubu biyar bare shi nashi na dabanne saidai yabiya dubu goma dan Allah indai irin marin da yayi min ne wata macen saita bakunci lahira ko kuma ya canza mata kamanni hallitar da Allah yayi mata, shettima yace wayagaya maka zai biya ai ba wanda ya isa yasashi yabiya "bossay yace Allah nidai ina uban yarinya ya marar min 'ya sai ya biyani dan bazan rabu dashi ko yabiya ko in rama mata "shettima yace da kwa kaima kasha marin "bossay yace kasan Allah sai na rama mata kai nifa yanzuma idan yaqara dukana sai inda qarfina yaqare dan sai na nuna mishi nawa dantsen yafi nashi nifa ranar ma da ya mareni bansan meya hanani ramawa ba amma yayi nafarko yayi naqarshe kana ganin shi hakan nan ni ajikina inajin idan zamu danbatu sai nayi qasaqasa dashi dan nimafa ina da qarfin nan hmmm yafada yana cije baki irin zan kamashi dinnan ya dora da cewa Allah ya hadamu idan ya hadamu kar yaraba sai nasa yadena marin kowa aduniyar nan bare kuma mace danni su zan daukarwa ma fansar marin da yake musu dan dakatawa yayi da maganar....., "sosai shettima yake dariya saida yadan tsagaita sannan yace to shikenan yanzu muje filin dambe tunda gaka gashi sai kuraba raini nidai ina gefe duk wanda yayi winning zan mishi kyauta me tsoka "bossay yace fadi nawa zaka bayar kai nikuma ko beyi niya sai naje har inda yake nakira shi yanazuwa zanfara nannaushin shi idan yaji zafi sai yarama kaga daga nan sai mufara fadan rabaraini ko ya kace hakan ai yayi fadi nawa zaka bayar? "shettima yace ko nawa kake so zan baka kai bama nikadai ba shi kansa idan yaga kagi shi qarfi zai qaramaka wasu kudaden dan haka gaka gashi kawai farawa zakuyi basai kaje wahalar nemansa ba, cike da rashin fahimta bossay yace dan Allah zai biyani dagaske? "Shettima yace kwarai ma kuwa zai biyaka adadin kudaden da kakeso ma zai iya baka. cike da jin dadi bossay yace to shikenan angana yanzu de kaje kirashi, "shettima yace ai basai najeba shiyazo farawa kawai yarage muku yaqarasa fada yana riqe dariyar da takeson kwace masa, "bossay yace nifa bazanje office dinsaba kaje kai kakirawo sa yana zuwa zan fara aiwatar da nawa aikin amma fa kafin kafita duk wani abu dakasan yanada amfani ka dauke shi kar muyi maka asara, "shettima yace to shikenan ba matsala bari infita in baku guri yafada yana miqewa daga kan kujerar yace to bari inje intaya Ameesha zama adaki kar mujikun turo mana qofa kuma bana ma so ku tashe ta yana kaiwa nan ya juya zai shiga daki "bossay yace to ya kuma zaka shige baka kirashi ba nifa bazan iya kiranshiba saboda bana son yagane wani abun yaji tsoro yaqi biyoni shiyasa nakeso kai kaje "dan juyowa shettima yayi yana mishi murmushi me qayatar wa sannan yace wai a ina zan kirashi bayan gashi ga ka ai baka da matsala basai ka wahalar da kanka wake zuwa wajen saba tunda duk yaji tattaunawar tamu gashinan yafada yana nuna masa bayansa da da hannu alamar ya kalli bayansa, dasauri yajiyo dan ganin da gaske yake yana juyawa sukayi ido hudu da sam dake tsaye ajikin qofa a harde hannayensa guda biyu a kan qirjin sa ya zuba musu ido yana kallon su basu dade da fara zancen ba ya shigo dake beyi nocking ba kuma qofar ba qarane da ita ba shiyasa basu ji shigowar sa ba shima shettima sai daga baya yagansa saboda yana facing dimshi shiyasa ya gansa amma bossay baisan da zuwan saba shiyasa yazauna yana ta uwar zuba arashin sani, "da sauri yayi qasa da kansa tare da miqewa tsaye yana kallon shettima irin meyasa baka gaya min ba shikam shettima daiyar sa yake yace to bismillah let me caunt three 1yafada yana kallon bossay yanda yayi tsuru tsuru da idanu kamar jikaken bera "shettima yaqara cewa 2 ai kafin yayi na ukun bega tahowar mutum ba sai jin mutum yayi abayansa yana boyewa murya qasa qasa yace nifa ban shirya ba kace masa yatafi idan na shirya ni da kaina zanje insame shi "juyowa yayi yace au hakama kace to shikenan yace ka taho wai kuyi anan yafada yana kallon sam da yayi tsaye kamar gunki ko yatsansa yaqi motsawa kawai ya kafesu da idanu tare da qara hade fuska, "saida yagama shan qamshinsa sannan cikin takunsa na isa da qasaita yafara takawa zuwa cikin office din,"bossay naganin haka yana nufowa inda suke yafara juye juye yana neman gurin buya qofar da shettima yanuna masa dazu yace Ameesha na ciki tana bacci yatuna dan haka ya nufeta da sauri ya bude qofar ya turata zai shiga arashin sani Ameesha da tashin ta daga bacci kenan tazo wajen qofar zata bude shikuma ya turata da qarafi kafin tayi yunqurin matsawa yature ta tafadi qasa, qara tasakai tana dafe kanta saboda jin zafin da ya ratsata, da sauri yayi kanta tare da dagota shettima ma da sauri yaqarasa gurinsu yana cewa subhanallahi ya akai haka yaqarasa fada lokacin da yakai ga tsugunnawa agabansu cikin rikidewa yaqara dagota sosai yana kiran sunan ta amma bata amsaba kuma bata bide idon taba tsorata yaqarayi yace dan miko ruwa insaka mata shettima na qoqarin tashi yadauko sai kawai sam yamiqo musu karba shettima yayi ya shiga yayya famata amma nanma shiru bata motsaba shettima ne yace mayar da ita kan kujerar cen adubata da sauri ya sureta ya kaita kai ya kwantar da ita nande shettima yashi ga duddubata gashi ansaka mata ruwa amma taqi farfadowa yana kanta yana tunanin abun da zaiyi mata sam ya qaraso gurin tare da dan rankwafowa kanta yayiwa shettima alama da ido ya matsa tashi yayi yabasa guri shikuma sai ya tsugunnan agabanta yaqara diban ruwa atafin hannun sa ya shafa mata afuska yagade taqi bude ido daman kuma yasan hakan zata iya faruwa yanzu watakil faduwar ta taba mata kwakwalwa bossay ya matso ya riqe hannun ta yana dan jijjigata dan Allah kiyi hakuri baby wlh bansan kina wajen ba dan Allah kitashi sai faman surutu yake shikadai saida sam yace malam ka ishemu da surutun banza kafita daga nan yace gaskiya kayi hakuri amma qafata qafarta ba inda zani duk abun da zakayi mata kayi mata ina gun tunda ai ni mijin tane yakamata dukma abun da za'ayi ayi agabana ko "wani kallo sam ya watsa masa da yasashi yin shiru " sannan yadan sosa qeya yace kaifa matsala ta dakai kenan to maida wuqar ni bada fada nayi maganata ba kawai kawai de sai kuma yayi shiru "shettima dake bayansu yayi dan murmushi yace mutum de yadena cika baki da kurun banza inbahaka ba kuma jiki yayi tsami, bossay yasan dashi yake sai yayi masa shiru yana maida hankalin sa ga Ameesha maida dubansa kanta sai kawai ya zaro ido cike da mamaki ganin abun da sameer yake shirin yiwa Ameesha..........✍️✍️✍️✍️ Ba yawa ayi hakuri da wannan👏 Assalamu alaikum, kutsaya ku karanta kar ku wuce yana da matuqar muhimmaci agareku. *ILIMI HASKEN RAYUWA* Ina matan aure harma da 'yan mata wadanda basu samu damar yin makarantar islamiya ba ko kuma wadan da sunyi amma yanayi rayuwa yasa sun manmanta da wasu abubuwan to ga dama tasamu akwai mata dayawa wadan da suke cikin wannan halin suna bukatar ilimi kuma wasu suna so amma basusan ta inda zasu fara ba wasu kuma hidimar gida da iyalai bazasu samu damar fita su nema ba, To amma fa kusani hakan ba hujja bace awajen Allah domin acikin wani hadisi ance azaba ta tabbata gawanda be nemi yasani ba kuma ko kasani ma idan baka aiki dashi nan ma azaba zata tabbata agaresa dan haka kutashi kunemi ilimi kar kuzauna da duhun kai ko girman kai ilimi ba ai masa girman kai kitsaya ki fadada iliminki musamman bangaren akdari mata dayawa suna da qarancin ilimi akai, Duba da hakan yasa muka kawo muku hanya mafi sauqi na online class kina zaune a cikin gidan adakin ki azaune ko akwance ma zaki samu duk wani ilimi da kikeso dai dai iyawarki, yar uwa awa nawa kike batawa akan wayarki batare da ki qaru da ita baki koyi komai ba aciki awa nawa kike batawa akan karatun littattafen novel da kalle kalle da basu da amfani, zamu bude group iya mata zamu kawo muku littattafan addini sannan kuma zamu ringa qarin alqur'ani me girma duk surar da baka iya ba za akoya maka duk daga inda kake so zaka koya zamu koya muku baki kodaga alifunne baka iyaba za a koya maka kuma da yardar Allah zaka iya, Ga abubuwan dazamu ringayi kamar haka👇 1_ALQUR'ANI 2,HADISI 3,AKDARI 4,ARABIYYA, 5,SIRATUL NABIYYI 6,NURANIYYA DA dai sauran su duk waddannan abubuwan zaku samesu agarabasa me sauki naira dari ukun ka ta baka ilimi kuma idan kabiya ka ta samu kenan baza ataba cemaka wata yayi ba biya kudi ko shekara nawa zakai saidai idan kai kagaji da nema kace ya isheka domin karin bayani sai ku tuntubemu ta wannan number 08124226526 Pls duk wanda ya karanta yatayamu da share dinsa zuwa group group domin inkai baka ra ayi watakil wani yana da ra,ayi akai kuma be ganiba plss share it [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿29&30 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     bossay yasan dashi yake sai yayi masa shiru yana maida hankalin sa ga Ameesha maida dubansa kanta sai kawai ya zaro ido cike da mamaki ganin abun da sameer yake shirin yiwa Ameesha.........✍   "hannu ya sam yasaka ya riqe mata hanci tare da matsa bakin ta, jin anriqe nata hanci kuma taji zafi yasata saurin bude idon ta tare da cewa wayyo dadda ta kasakar min hanci kasheni zakayi taqarasa fada tana qoqarin tashi zaune " sakin ta yayi yabita da kallon mamaki gaba dayansu ma ba wanda beye mamakin jin muryarta radauba, Qarasa zama tayi da kyau tana fuskantar su daya bayan daya saida tagama kallon su kawai sai tasaka dariya tare da cewa ashede zan iya acting din film yanzu duk kwarewar ku ba wanda ya iya ganoni  to lafyata qalau inajin ku nayi shiru saida naji ana niyar kasheni taqarasa maganar da qarayin wata dariyar, duk ido suka zuba mata suna kallon ta sai da qyar bossay ya iya tsugunnawa agabanta yace haba baby meyasa zakiyi haka bayan kinsan hankalin zai tashi kidena irin wannan wasan ni wlh banaso kinji yanda nakeji idan wani abun yasameki amma kikazo kikayi mana haka plsss karkiqara kinji ni yafada yana bin beauty face dinta da kallo " itama shi take kallo saida yagama maganar sa sannan tace to yayana nadena daga yau bazan sake ba, yace yauwa babyna haka nake sonji yanzu babu wani abun da yake damun ki? kai ta daga masa alamar babu komai yace to shikenan haka akeso Allah yaqara miki lafiya,   "Ameen tace masa taqara jan bakinta tayi shiru" tundazu nazo na dade anan ma akace kina bacci tace ai da katasheni "yace a'a ai ba aso anatashinki inkina bacci tace to ai kaine kuma ni lafiyata qalau danasani da tun dazu nafito dan nama dan jima da tashi kawai de fitowar ce banyi ba yace ai shikenan yanzude ai gashi munhadu ko?kai ta kuma daga masa sannan tace jiya nayi missing dinku nikadai sai naji duk ba dadi da ba dadda akusa dani tafada tana dan marairaice fuska irin abar tausayin nan, bossay yace ayya kiyi hakuri zakisaba kinga ai kwananki daya amma nasan kinadanyi kwana biyu zaki saba dasu gashima kuma dayan yayanki zairinga zuwa dake nan kina gani mutane yafada yana nuna mata shettima "dake tsaye yana binsu da kallo sai yaji sun burgesa sai yakejin dama ace qanwarsace wacce suke uwa daya uba daya da tasha gata shide arayuwar sa yana son qanwa mace shiyasa ko gidan su sam yaje haka yake kula dasu gashi kamar qannen sa  haka yake son qannen sameer" dagowar da tayi suka hada ido tasakar masa murmushi shima saitaji dama batace gidan ba dadi ba kar shima yaji ba dadi aransa, shima murmushin yamayar mata dashi kawar da idon ta tayi ta qara maida dubanta ga bossay, dorawa yayi da cewa  nima kuma zan ringa zuwa muna fita yawo ai zakije ko dan murmushi tayi masa batare da tace komai ba tashi yayi yazauna akusa da ita yana kallon ta da kyau zai qarayin magana, Sameer da ya koma kan wata kujerar daban yana daddana wayarsa ya katse musu hirar da cewa malamai kun ishemu surutu kutashi muje muyi abun da yakamata yafada yana mikewa tsaye suma ba wanda yace masa komai bossay ya miqe daman shettima shi yana tsaye be zauna ba, itama ganin duk suna tsaye yasata tatashi tsaye itama tana dan hararar sam ta gefen ido saboda batason tashi tafiso suzauna ita da yayanta suyi ta hirar su sai tafi jin dadin hakan amma kawai ya wani zo yakatse su idan bayason ji shi basai yafita ba kowani yace nasa dole sai yazauna agun ita haushi na yake bata batason taga sun zauna guri daya dashi bata samun sakewa saboda haushin da yake bata, kamo hunnu ta dataji anyi ne  yasa ta katse tunanin da takeyi tare da kallon bossay da shima itan yake kallo suna hada ido ya daga nata gira daya yace yade me yake damun qanwata tunanin me kikeyi ne haka har sun fita sunbarmu,"kallon dakin tayi taga basa ciki bata bashi amsaba kawai tace mutafi ba komai, "beta kurata sai tagaya masa ba kawai shima yajata suka fita daga dakin lokacin su sam harsun bar office din suma suna fita suka hangosu dan haka sai suka nufi inda suka gansu da dan sauri har suka kamosu tare suka qarasa wajen parking lot din "shettima ne ya kalli sam yace wacce motar zamu shiga yace muje awace yanuna masa motar shi nan yaje suna duk suka qarasa shettima yana driver seat sam kuma ya shiga gefe Ameesha da bossay kuma suka shiga baya tayar da motar yayi  rivers tare da saita motar yaja suka qarasa bakin gate me gadi ya bude musu suka fita daga asibitin saida suka hau kantiti sannan shettima yace ina muka dosa? Sam yace masa tudun maliki prison, "dan juyowa yayi yana kallon sa alamar yana jiran qarin bayani jin yayi shiru be da niyar qara cemasa komai yasa shi cewa kunyi magana da itane yace masa eh naje da safe ai mungama magana da ita yanzu can zamu fara zuwa tagaya min sunan shi da inda ta taba zuwa taganshi komaide na rubuta direct zamuje ne dady yakira yasanar da zuwan namu bazamu samu wata matsalaba kawai zuwa zamuyi(dady mahaifinsa kenan saboda babban lauyane kuma sananne shiyasa bema fiya zaman gidan sarauta ba dan mutane da yawa ma basu san shi dan gidan bane saboda bema fiye aiki anan ba jefi jefi ake daukan sa wataran yazo yayi shari'a shiyasa ba kowa yasan asalin sa ba ande sanshi akan aikin sa, to wannama shiyasa sam ya roqesa akan yakira can prison din tunda yana da hanyar da zai iya nema musu alfarmar shiga kai tsaye ba bata lokaci kuwa kuma batare da ya tambayesa dalilin zuwan nasaba kawai ya amsa masa tare da gaya masa yana da aboki agidan dan haka zasuyi waya yaje kawai to kunji dalilin da yasa zasuje kai tsaye tasanadin dady mahaifin sam) jinjina kai shettima yayi yace kace tazo mana da sauqi ma kaga ko shari'ar ma za ayi sai dady yatsaya mana kawai basai munsha wata wahalar nemo lauya ba sam yace nima abun da nake tunani kenan amma da kyar dady ya yarda dan zai iya hadamu da wani yace zai tsaya mana yanzu kuma duniya ba amana watakil shi wanda yake tunanin zai yi da gaske azo abashi cin hanci daga qarshe azo asamu matsala amma de zan lallaba shi ko insa papa yayi masa magana nasan watakil ya amince, dan numfasawa shettima yayi sannan yace ai bayani zamuyi masa inyaji labarin kaga dole zai yarda ya tsaya mana bazai qiba ko yakace yafada yana dan juyowa ya kalli  gefen da sam yake azaune sannan ya mayar da hankalin sa tuqin da yakeyi, shiru sam yayi kamar ma bazai bashi amsaba sannan yace Allah yasa yauwa kafin nan inason mu fara biya gida zan dauki abu daga nan kuma a ajiye yarinyar nan saboda ba da ita zamu ba in mundawo sai kadauketa ku tafi, "ok" shettima yace masa sannan suka cigaba da tafiya batare da kowa yaqara magana, amma qasa qasa kanajin surutun su Ameesha da bossay saboda suma tasu hirar suke dan bama sajin abun da suke cewa kasancewar shi gogan bawani daga murya yake ba ahankali yake yi hadi kuma da surutun da sukeyi sai yazamana basu jin zancen  da sukeyi, da qarfi Ameesha tace dan Allah yaya da gaske kake tafada kana ganin ta yanayin da tayi maganar zaka gane daga cikin ranta take saboda kamar arazane tayi ta da harsaida shettima yajuyo yace me yafaru ne saurin sunkuayar dakai tayi saboda batama san maganar tata tafito da qarfi har haka ba, Bossay ne ya leqa fuskarta yana kallon ta cikin murya qasa qasa yace yanaga kincanza gaba daya ko kina kishine da sauri ta dago tana kallon sa tare da girgiza masa kai dan murmushi yayi yace fadi gaskiya de yarinya juyar da kanta tayi gefe batare da ta tanka masa ba kamo hannunwan ta yayi gaba daya biyu tare da juyo da fuskarta suna facing din juna cikin canza murya alamar rarrashi yace kiyi hakuri nima bada son raina bane nima bansan da maganar ba sai jiya take gaya min bangama yarda ba kuma sai dazu da Ammi ta tabbatar min da hakan bayanda zanyi ne saboda Abba yasa baki ban isa ince bazan aureta ba, kallon sa take da mamaki tace to yaya kana nufin baka sonta ne harka kai kudin auren ta, sakinta yayi tare da komawa baya ya kwantar da kansa akan kujera tare da lumshe idon sa murya cike da rauni da kanaji kasan mutum yana cikin damuwa, yabudi baki batare da yabude idonsa ba yace nima kuskuren danayi tunfarko kenan dade naso ta saidaga baya kuma nagane ba ita nakeso ba kinsan ance so tsuntsune to ya dade da tashi daga kanta yakoma inda yafi dacewa dashi  zuciya ta yanzu ba ita take qauna ba, zuciyata wata take muradi son danayi mata ko rabin rabin son da nakewa wata bekai ba nasotane arashin sanin zan hadu da wata nasotane arashin sanin meye ma son bantaba soyayya ba bansan ya akeji akan so ba shiyasa da nahadu da ita nazata abun danaji akanta shine so ashe abun ba haka yake ba ita nazauna da ita amatsayin ta burgeni daga baya kuma gabadaya naji burgewar ma banaji akanta, saboda haduwa danayi da wacce zuciyata takeso akodayaushe ita nake tunani ita nake jinta acikin zuciyata ina sonta so ba dan kadan ba son danakeyi mata bazan taba iya hadashi da wataba shiyasa banason in aureta saboda bazan iyayin adaci atsakanin su ba dan dakata wa yayi tare da bude idon sa ya saukesu akanta, "itama shi take kallo tana nazarin maganganun sa saboda ba komai tagama fahimta ba ganin ya kafeta da ido yasata kawar da idonta sannan tace to wacece wace kakeso din meyasa baza kakaita gidan nakuba kace ga wacce kake so ai zasu fahimceka sai su aura maka wacce kakeso girgiza mata kai yayi yace ko nakaita ai dady bazai taba canza maganarsa ba gashi kuma ita wacce nakeso bata isa aure ba kuma banfada mataba kuma banason infada mata har sai tagama makaran tar ta saboda banason infara soyayya da ita idan hakan ta faru to zai iya taba mata karatunta  saboda kullum zansakata taita tunani na shiyasa banason hakan tafaru dan dakatawa yayi da maganar da yakeyi yana kallon kwayar idonta ji yake kamar yagaya mata gaskiya yace itace wacce yake so amma wata zuciyar na gargadin sa da hakan gwara yabari kawai sai yafara koyamata sonshi duk da yaga alamar hakan a idonta amma yasan ita kanta batasan meye sodin so yake yasata tasoshi sosai yanda shi tafara so to do yake ta taso ahaka da sonshi acikin ranta yanda bazata taba son wani ba bayan shi yanda duk wuya duk rintsi bazata juya masa baya ba shiyasa beso komawarta gidan su shettima ba amma hakan ma bazai dame saba zairinga zuwa kullum yana daukarta suna fita yanda shakuwa zata qara shiga tsakanin su kuma ya siye zuciyarta gaba daya, jin yayi shiru ha tsawon wasu mintina ta lura kamar tunani yakeyi ta dan tabasa tace yaya me kake tunani haka dagowa yayi ya kalle ta yace wacce nakeso nake tunani inson ganin ta na dade banje naganta ba, wani iri taji aranta kamar zatayi kuka harga Allah da yabata labarin ta zata ko da ita yake amma jin yace yana tunanin wata kuma har yace wata yake tunani yadade be ganta ba tasan to bada ita yake ba kuma bahaka taso jiba taso ace ita yakeso ashe duk kulawar da yake bata ba sonta yake ba ashe ita fa yaudari kanta tun farko aikwa yazam dole tayi qoqarin cire shi aranta tun ba ayi nisaba duk da batagama sanin  soba amma tabbas tasan tana sonshi so tunfarkon haduwar su taji ya burgeta kuma insuna guri tare bata son taga sunrabu idan ta dade bata gansaba sai taji tana kewar sa tunawa tayi da wani lokaci da yadade be zo gurin aunty Rasheeda ba taji tadamu da rashin ganinsa agidan gashi bata da damar da zata tambaya yana ina sai kawai taje tana gyara mata daki sai tayi karo da qaramar wayar rasheeda kuma tasan daman da ita suke waya sai kawai ta dauka ta tura masa message akan dan Allah yazo tana bukaqatar ganin sa akwai wata magana mai muhimman ci da zasuyi haka ta rubuta ta tura masa amatsayin Rasheeda ce tana turawa tagoge message din daman kuna ranar rasheeda bata nan ba jimawa kuwa yazo gidan tanajin qarar motar sa ta fita tana ganinsa taji dadi aranta sai ta basar kawai ta nufi hanyar fita irin batasan da zuwan sa ba saboda tasan dole yakirata hakan kwa akayi tana danyi gaba ya kirata ta dawo bayan sungaisa tame cemasa ai bata nana yanzu suka fita amma watakil ba nisa tayi ba tayi masa hakane dan yajirata ita kuma tasamu dama sutayin hira tana kallon sa tanajin dadi, batasan lokacin da numfashi ta kufcema ta "baby meesha ya akayine naga sai faman murmushi kike ina ta magana ma amma kin tafi tunani me kika tuna haka bani labari ko kintuna saurayin kine dan wannan murmushin naki yayi kama da na soyayya, dan harar wasa tayi masa tare da basarwa da kawar da duk wani tunanin sa da yake neman hana ta sukuni lokaci daya taqara qaqaro wani murmushin dolen  sannan tace haba wace ni ina yar qaramata inkama tunani saurayi ni yanzu ina naga lokacin soyayya soyayya ai sai ku, kaga ma nidan gayamin ma budurwar taka a ina take haka inje infara nemawa yayana fada agunta kar wani yayi mana wuff da ita muyi dakon banza gwara inje inkafa in tsare in hana kowa kulata, duk wata damuwa da yakejin ta sai yanemeta yarasa yashiga yin dariya saida yayi me isarsa sannan yace to shikenan kar kidamu zan kaiki har inda take amma ba yanzu ba kiban lokaci, "wani abu taqara jin ya dakar mata zuciya qara dannewa tayi "sanna tace to Allah yakaimu lokacin dan har na matsu inganta "yace karkidamu zakin ganta very soon, shettima da duk suna jin hirar dasuke yayi mamakin jin abun davyake cemata sakamakon kuma agabansu yana cewa ita yakeso matar sace amma gashi ita ya boye mata, dan kallon sa yayi ta mudubi da har zaiyi masa shiru sai kuma yakasa  yace  malamin soyayya naceba ina da magana irin wannan tsara mutum haka, kalllon sa bossay yayi sannan yayi murmushi yace inajinka dalibin soyayya gaba dayansu dariya sukayi banda Ameesha da ta tafi duniyar tunani batasan me suke ba shikuma dayan wato sameer dake gefe tunfarawar surutunsu yaji sun damesa ya dauko headphones ya toshe kunnuwansa dashi ko me yake ji oho dan haka sukadai suke kidansu suke rawarsu bayajin abun da suke cewa, Shettima yace zanzo akoya soyayyar daman ban iyaba nima gashi kuma nima daman inason wata yarinya danake fatan nima ta zama matata, bossay da yagane da wacce yake tunda yana magana yana kallon Ameesha ta cikin mudubi, shikuma lura da hakan yasashi cemasa a ina take shettima yace anan gurin mana gashima ina kallon ta yanasane yayi masa haka saboda zacen da yaji yanayi shiyasa yakeson yagano da gaske itan yakeso ko kuma wata dince daban kamar yanda yafada din, kallon sa bossay yayi tare da hararars yace to kwa kwalelen ka dan bazaka taba samu ba gwara ka canza hanya tun kar lokaci ya qure maka dan wannan anriga da an siyar, dan murmushi kawai shettima yayi batare da yace komai ba kamar bazai yi magana ba sai kuma can yace kanaji  na ko kai yadaga masa yana qara kallon gefen fuskarsa tunda tuqi yake baya ganin fuskar sa gaba daya, zan baka shawara kar kayi wasa da damarka kadena boye abu ko riqe shi hakan zai iya haifar maka da matsala nan gaba kazo kana da nasani kasan kuma danasani bata dawani amfani kayi amfani da lokacinka alokacin da yazo maka inkabari yatafi tofa bazai taba dawowa ka riqe wannan duk abun da kasan kanaso to kawai go to the street point kar katsaya wani kwana kwana dan haka bashi da amfani yaqarasa fada masa daidai lokacin da suka qaraso tamfatsetsan gate din masarauta yayi horn aka bude suka shiga ciki, ganin inda sukazone yasa bossay bai bashi amsaba yashiga bin masarautar da kallo Ameesha ma haka dukan su kallo suka bi masarautar dashi kowa da abun da yake kiyastawa aransa da irin kyau da tsaruwar da tayi, parking shettima ya daidaita sannan ya bude qofa ya fito sam ma sam fitowa yayi ya rage daga Ameesha sai bossay acikin mota duk sun kasa motsawa bare su fito ta barin da Ameesha take shettima  yaja murfin ya bude mata ya leqa yana kallon su yace ko sai an fito da kune zaku fito kuntsaya kufito bossay ne yayi murmushin jin kunya sannan ya bude qofar ya fita ita kuma taqi fitowa sam ne ya cire abun da ya toshe kunnen sa yayo gaba wajen da suke yana binsu da kallon meye ya tsayar dasu ganin Ameesha aciki yace anan dinma sai kin bata mana lokaci kishiga taitayin ki wlh banason shirme duk inda akaje sai anjiraki yafada yana zabga mata harara kamar zai maketa, duk da ta tsorata dashi amma hakan besa taji zatafito ba hasalima sai ta make kafada murya ciki ciki tace nifa ba inda zani ku shiga kufito kawai duk tsayawa sukayi suna kallon ta da mamakin abun da tace bossay ne yace meyasa ke da za abarki anan bafa dake zamuba sai min dawo sai kutafi kofito dan Allah kinga kina qara bata mana lokaci yafada yana qoqarin kamo hannun ta zai fito da ita amma ga mamakin su sai kawai sukaga tasaka kuka tana ita baza ta fito ba da kyar de shettima da bossay suka lallabata akan zata fito din amma shikam sam ta kaishi qarshe kadan yarage ya hau kanta yavkoya mata hankali ya sauke mata wannan iskancin da takeji dashi, bossane ya miqa mata hannu dago nata tayi ta dora akan nasa yafara jawota daga cikin motar itama ta yunqura ta zuro qafafunta shikuma ya matsa dan bata damar gurin da zata tsaya qarasa fitowa tayi ta tsaya da qafafunta tana qara bin masarautar da kallo gaba suka farayi su shettima kuma abayansu tana daga qafa tayi tafiya daya biyu zata daga ta ukun kenan wata iriyar qara me kama da kururuwa da sauti me qarfin gaske da taqamaimai baza ka tantance qarar meye ba haka masarautar ta dauka gaba daya duk wani wanda yake cikin ta babu wanda be tsorata dajin ta ba masu qarfin haline kawai zasu iya tsayawa da qafafun su bayan qarara kuma sai masarautar gaba daya tayi wani duhu da dan gibgibtawar abubuwa kafin daga bisani kuma sai ta washe ta dawo yanda take lokaci guda kuma masarautar ta dauki shiru tsit kake ji bakajin sautin komai saboda yawancin mutane abun ya razanar da su da har yakai ga wasu sun sussuma a inda suke saboda babban al'amarin da sukaji wanda tunda suke arayuwar su basu tajin irinta ba Ameesha tana daya daga cikin masu suma inda saida tasaki qara itama kafin ta sume tunkan gurin ma yadauki duhu gaba dayansu sukayi kanta sukayi mata runfa, nanfa kankace me masarauta ta kidime wasu nasurutu da al'ajabi wasu kuma na koke koke inda zukatan wasu daga cikin masarautar ya girgiza su tare da furgice da tsoron faruwan abu duk yakamasu alokaci guda abubuwa da dama suka faru wannan ranace tadaban akan yawancin mutanen gidan wannan ranace ta farin ciki wasu kuma ranace ta baqin ciki agaresu...........✍️✍️✍️✍️ Hmmm shin me yake shirin faruwa amasarauta me yakawo musu wannan sabon yanayin ko kuma ince abun mamaki da ban tsoro😠😠😠, ga Ameesha acikin masarauta kuma ga Azeema aminan juna💏 [5/22, 10:45 PM] #momyn twins#: XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿31&32 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️            " wata iriyar qara sukaji da yasa mutanen da suke bakin ward din a tsaye susu biyu suna magana jin ihunta yasa suka  kwasa aguje suka shiga dakin ganin halin da matar take ciki yasa su shiga tashin hankali dayane yayi saurin rufe qofar  dayan kuma yayi kanta da sauri yanaso ya hanata kunce igiryar da takeyi dan already ma harta kunce na hannuwan ta tana qoqarin kunce na qafar sai wani fisfisga take kamar zata tashi sama tanayi tana jijjiga gadon asibitin da take kai shima kamar zata karyasa saboda wani irin qarfi da take ji ajikin ta, sosai hankalin su yaqara tashi, "gaba ki dayansu sukayi kanta suna rirriqeta tana tafaman fisge fisge gabaki dayan su babu wanda be tsorata da yanayin da matar ta shiga ba lokaci guda duk yanda zasuyi suriqeta amma sun kasa duk qarfinsu nema take tafi qarfin su sai wani irin kuka take tana fusgewa tana sunbatu ni kusakeni kar wanda yaqara riqeni idan bahaka ba duk sai na kasheku tafada tana zazzaro manyan idanun ta qoqarin saukowa daga kan gadon asibitin da take,   "Suna cikin haka aka turo qofar da qarfin gaske cikin tashin hankali da zafin nama yaqaraso wajen su, "da qarfi yace kusake ta!! matsawa sukayi suna faman rarra ba ido, da sauri yayi kanta yayi mata mugun riqon da bazata iya kwacewa ba tare da rungumeta da kyau saura kadan ta yardashi saboda duk da riqon da yayi mata bai hanata cigaba da kwace kwacen da takeyi ba daman shi kadai yake iyawa da ita duk lokacin da irin wannan ra faru , sauran ma ganin yayi nasarar riqeta yasa suka matso suka kakkamata wand ya riqeta dinne   ya zaro allura yayi mata anayimata jikin ta yasaki gaba daya tadena motsi kamar yanda akasaba yimata, "mayar da ita yayi ya kwantar akan gadon sanna yajawo igiyar da ta kunce yaqara mayar maya ya daure ta saida yaga ma da ita tsaf yana share gumin da ya tarar masa shikansa yayi mamkin irin qarfin ta nayau dan ba qaramar wahala yashaba gurin riqeta gashi itama ta riqeshi sosai da har saida yaji zafin riqon da tayi masa, " yajuyo afusace  yana kallon su rai abace yace  how dare u why u doing like nonsense fuck u yana fada kamar zai hausu da duka, dan matsawa sukayi daga gabansa  amma sai yaqara binsu baki sukeso subude suyi masa magana amma ya hanasu damar hakan , gaban su ya tsaya yana nuna su    meyasa kuka kunceta kunriga kunsan abun da hakan zai haifar kunsani amma kuka danne wannan kuskurene to kusani idan hakan taqara faruwa to kunyi abakin aikin ku duk sai na koreku last warning wannan yazama shine na farko shine naqarshe dan banason aiki shashanci, " sorry sir" gaba dayansu suka hada baki wajen fada, tsaki yaja sanan yace then get out of here kar naqara ganin qafar wani acikin ward din nan tunda baukasan aikin ku ba kuna wasa dashi yanzu da banzo ba kuna tunanin kun isa ku iya controlling din ta dama na barku da ita idan takai dayan ku lahira sai ku kiyaye nan gaba banzaye kawai wadan da basu san abun da suke ba daman na dorakune dan kuyi abun da kuka ga dama ko nace ku kunceta, waya baku damar haka eh  meyasa me yasa meyasa zakuyi haka yaqara sa fada cikin daga murya da daka musu tsawa, yaqarasa maganar yana wani irin huci saboda ransa ba qaramin baci yayi ba da abun da yazo ya tarar dan hakan da sukayi da baya nan da tuni zai iya rasata dan zata iya nufar wani gun idan kuma tafara gudu babu wanda ya isa ya tsayar da ita shikenan sun batamasa aikinsa, kallon su yakuma yi yana nuna su da yatsan hannunsa idon sa duk sun canza kala sunyi ha saboda tsabar bacin rai jijiyoyin kansa har miqewa suke duk wanda yaga yanayin sa sai ya tsorata dashi duk sun kuyar da kansu sukayi suna sauraron fadan da yake musu suna so suyi masa bayani akan bafa su suka kunceta ba amma suna tsoro saboda sunsan bazai taba sauraron su ba dan shirun nasu sai yafi saboda shi halinsane indai yana fada tofa ko bakayi laifi ba kar ka yarda kayi masa musu dan zai iya yi maka dukan tsiya awajen shiiyasa suma sukayi shiru suka barsa har saida yayi nai isarsa sannnann yaqara nuna musu qofa yace bacewa nayi kufita bane ko sai nayi maganin ku anan gurin, cikin fargaba murya narawa qasa qasa suka qara bashi hakuri tare dayin sum sum suka fice daga dakin ransu suma duk ba dadi saboda fadan dayake musu akan abun da basu suka aikata ba gashi basu da damar kare kansu haka suka fita kowa da abun da yake saqawa aransa,   "komawa yayi yaja kujerar dake gefe ya matsa kusa da ita ya zauna tare da dafe kansa da yake jinsa kamar zai tsage gida biyu daman tun yana gida jikin sa yake basa something is wrong shiyasa ma yabar abun da yake yataho wajen ta, hannun ta ya riqo tare da manna mata kiss a hannun can qasan makoshi yace Allah yabaki lafiya Allah yaye miki duk abun da yake damunki Allah ya nuna min ranar dazanganki kamar kowa sosai ya shiga jero mata addu'o'i batare da ya saki hannun taba yana cikin haka shikadai yakai wajen 20 minutes agaban ta sannan aka turo qofar dakin ahankali batare da anyi sallama ba, jin anbude qofa kuma ba ayi magana ba yasa shi yadan dago tare da juyowa yana kallon qofar shigowa matar da yagani ce yasashi dan sakin murmushi buda masa hannu tayi daga inda take itama tana sakin murmushi ahankali yataso duk da ayanayin da yake bayason tashi amma ita ta wuce haka agurin he can't reject   her hug dole yayi accepting dan haka jiki babu kwari ya taso yataho wajen ta yana qarasowa yafada kanta rungume shi tayi sosai ajinkin ta tana qarajin sonsa na ratsata shima awajensa hakance take faruwa yaji dadin zuwan nata be saketa ba harsai da yaji yadan samu nutsuwa sanna yaraba jikinsa da nata yana dagowa takamo fuskarsa tana kallon kwayar idon sa saida tagama qare masa kallo sannan tace  MA ASABAKHA ya hayatee (me yake damunka rayuwata) be bata amsaba kawai da hannu yayi mata nuni da wacce take kwance akan gadon, kallonta tamayar gun da yake nuna mata shafo fuskar sa tayi sannan ta danyi murmushi tare da kamo hannun sa taqara dashi gaban gadon ta zaunar dashi kan kujerar da yatashi itama ta jawo wata ta dawo gabansa ta zauna tana kallon sa hannuta ta dora akan nasa sannan ta shiga cewa don't worry ur self my dear any thing will be successfully just continue pray for her it's only she need, so mind ur self in sha Allah nan gaba saidai ma abun yazama past tense sai dai story, storyn ma wataran baza ka bayar ba komai zai wuce da yardar Allah kaji kai yadaga mata tace yauwa haka nakeso kacire komai aranka bakyau yawan damuwa ko wani abunne yaqara samunta kai yadaga mata sannan yabata labarin abun da yazo ya tarar tana yi yaqara sa bata labari fuskar sa dauke da damuwa, Sosai taji tausayin matar da kuma dana nata cikin kulawa tafara bashi baki da kwantar masa da hankali, ahaka tacigaba da rarrashinsa har tasamu yafara sakewa da ita, yabar fushin da wadan can mutanen suka hafar masa dashi kwantar da kansa yayi akan cinyarta yana maida numfashi batare da yayi magana ba ganin hakan tagane me yake nufi dan haka ta daga hannun tana shafa masa kwantacciyar suman kansa da ta sha gyara kana ganin ta kasan ankashe mata makuden kudi wajen gyara ta murya qasa qasa ta kira sunan sa ahankali shima ahankalin ya amsa mata da na'am cikin yaren su na larabci tace nifa ina ganin maganar danayi maka tun kwanakin baya kaqi yarda nake ganin fa indai ba ita zamubi bana ganin matar nan zata samu lafiya dukdade sauqi na Allah ne amma wannan allure alluren da kuke mata da kuma magungunan da kuke bata banajin zasuyi aiki dan da zasuyi da tuni sunyi yanzu fa tsawon shekaru biyar amma anata abu daya ba wani sauyi akan lamarin nata bisa ga dukkan alamu fa banajin wannan matar akwai wani sirri ajikin ta inba asiriba to da aljanu ajikin ta wannan ba maganin asibiti ne zaiyi aiki ajikin taba dole a kira malami yazo ya dubata ko kuma mu mukaita aduba ta tuntuni nake gaya maka amma kaqi amincewa kayi hakuri ka amin ce akaita wannan shi kadaine solution idan mukaje malamin yasanar mana babu komai ajikinta sai kaga sai nudawo muqara shiri akan abun koda fitane sai muyi da ita suma su gwada tasu basirar akanta tundade mude har yanzu Allah besa munyi nata abun da zaisa tasamu lafiya kayi hakuri nu jarraba wannan din shiru tayi tana kallon sa tare da jiran jin amsar dazai bata aranta tana addu'ar Allah yasa ya amince, shiru yayi yana nazarin maganar ta saida yadan dauki lokaci sannan murya cikin rauni yace ummy nima maganar da nakeson nayi miki kenan saboda naga abun yaqi ci yaqi cinyewa gashi haryanzu bata magana ba wani alamar zata samu lafiya musamman ma abun da naga tanayi dazu bakiga abun da tayiba ta tsorata ni sosai saboda bata taba yin abun da tayi yauba harni da take yarda dani inriqeta amma yau da qyar na riqeta amma abun da yafi ban mamaki shine maganar da tayi tsawon lokacin nan bata taba furta ko A ba amma yau naji tayi saidai kuma yanayin natane na daban da sauran da takeyi yaqarasa maganar cikin murya me cike da rauni da tausayi, Shafa fuskarsa tayi itama cike da tausayin dan nata tace plss ka kwantar da hankalin ka in sha Allah komai yazo qarshe bi iznillah muna zata samu lafiya zaka cika burinka kayi hakuri kaji,Kai ya yadaga mata sannan yace ummy yaushe za akira shi tace duk sanda kake so ko gobema zansa ka anemo mishi zaizo harna yadubata kar kadamu ka barmin komai a hannuna taqarasa maganar tare da miqewa tsaye tace oya get up qintashi yayi saboda yasan me take nufi shiyasa ma beso ta biyosa ba dan ko gaya mata ma beyi ba ya fito amma saida akasamu munafikin da yagaya mata yafito ba, ganin yaqi tashi tasan zancen daman yace mata anan zai kwana bazai bita ba ganin hakan yasata ta dan hade rai tace I get up ko bakaji ba tafada tana kama hannuwan sa tare da miqar dashi tsaye dan marairaice fuska yayi alamar tausayi, "kawar da kanta tayi tare da cewa u know de I can't leave without u dan haka don't waisting my time dare nayi ba yanda ya iya dole yabita suka fito daga ward din har sunzo bakin qofar ya tsaya tare da dubanta yace ummy bari ingayawa wadanda zasu kula da ita saboda wadancan nayi firing dinsu daga wajen ta saboda basu san me suke ba kallan sa tayi tace kar kadamu da wannan muje kawai idan munje gida zan kira insanar da wadan da zssu kula da ita nabar wayar agida bahaka yaso ba amma ba yanda zaiyi dole yabi bayanta suka tafi suna fita driver yaqarso wajen da sauri ya bude musu suka shiga shikuma ya shiga driver seat ya zauna tare da tayar da motar yaja suka fita daga asibitin tunda suka tafi bawanda yaqara cewa komai har suka qarasa bakin wani tanqamemen gate wanda girmansa yakusa cinye layin gidan kuwa yafi kowanne gida girma acikin unguwar horn ya doka tun kan yaqaraso gurin da sauri gate man din ya wangale musu gate din sukuma suka danna kai cikin gidan, Wow masha Allah saidai muce Allahumma arzukuni fi hazal bait,kana shiga gidan saboda tsabar fitulin da suke ciki masu tsada da yawa babu abun da baka gani komai tarwai kamar ma ba dare ba saboda ko allura kayar idan ka duba sai ka ganta wani qaton gidane wanda kana ganinsa kasan bana kananun mutane bane na masu hannu da shune manyan mutane masu kudi iya kudi saboda tundaga yanayin ginin zagane hakan ga gefe da aka zagayesa da fulawoyi koraye can gefe kuma guiding da aka qawatasa ga gurin shaqatawa acan gefe shima da fulawoyi sai tsuntsaye da suke sha qagi agun wani guri na qara hangowa inda tafkeken swimming pool yake ga kujeru agaban sa iska sai kada ruwan take gwanin ban sha'awa da burgewa kalar sa sky blue ne kalar sararin samaniya gashinan de abubuwa da yawa harabar gidan wanda wasuma bansan suba wasu kuma idan na tsaya kwatanta muku tofa zamu iya sati bangama ba shi kansa kasan gidan abun kallo ne da burge wa saboda wani abune a shinfide shi ba tiles shi ba interlock ba shi ba tarazo dan har fakar ido nayi na tsugunna na shafashi amma ban iya tantance menene ba haka naqara bin gidan da kallo komai yayi gida iya gida ina mamaki kuma yanda wajen take haka da kyau to ina ga cikin gidan kenan tode muje zuwa dan jin yanda yake, bayan driver ya tsaya a parking lot inda ya ajiyeta ajerin motocin dake gurin yayi saurin fitowa tare da sa hannu ya bude musu qofa suka fito ummy ce tafara fitowa yabiyo bayanta jira tayi sai da yafito sannan ta kama hannun sa suka nufi qofar wata irin qofa ce wacce ban taba ganin irin taba tunda nake adunyi ko a film ko littattafai bantaba gani ba banta jiba suna qarasowa gurin ummy ta daga hannun ta duk yatsu biyar abun mamaki sai kawai naga qofar ta rabe a hudu sama da qasa da kuma gefe da gefe suna shiga kuma sai wani abu ya fito takawa sukayi sai yayi qasa dasu dan garin leke na sai da nakusan faduwa amma de na dake bankai ga qasaba nayi saurin riqe kaina na labe abayan su inajin tsoron kar in fadi tundade babu a hause gidan miji babu mokotama kuma baza ataba baza ataba samuba bare ince wani abu kuma nasan me kuma duk babu agidanku idan akwai wadanda suke da sumin magana inzo ingani😎😎 bawani tafiya naga abun ya tsaya adaidai wani dan qareren falo me girma gaske wanda akacika shi da abubuwa daban daban abunde sai wanda yagani komai na falon white and goulding fent din falon fari sai kuma kwaliye kwalliyen falon komai fari harda labule suma farare ne sai kuma kujerun falon da suka kasance farare saiti biyu ga dinning area agefe inda can kuma daga gefe wasu twins din stairs wanda suka wani irin kanannade daya yayi dama daya yayi hagu wani babban mutum kyakkyawan gaske fari tas dashi nagani akan kujera dauke da space a fuskar sa sai kuma jarida a hannun sa gefen sa kuma wani dan qaramin table ne me dauke da fruit sai cup dake hannun sa yana sha jin sallamar su yasa shi ajiyewa tare da kawar da jaridar hannun sa gefe tare da sakar musu wani irin qayataccen murmushi irin nasu na manya, "qarasowa sukayi itama ummy nasakar masa murmushi tare da zama kusa dashi tana cewa ANA ASIF BADRIJAKA SAMHAINI YA ZAUJ.......✍️✍️✍️ to masu karatu karda ku wahalar da kanku wajen tunanin wannan page din duk acikin littafin sarki sameer yake kude muje zuwa yanzu akafara ✍️✍️✍️ [5/23, 8:38 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿33&34 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️    "qarasowa sukayi itama ummy nasakar masa murmushi tare da zama kusa dashi tana cewa ANA ASIF BADRIJAKA SAMHAINI YA ZAUJ.......      "daga zaunen sukayi hugging din juna tare da manna kowa kiss agefen kumatu barin dama da barin hagu irin de yanda larabawa suke yin  gaisawar su, "duban ta yaqarayi sannan yace da MA TAF'ALU(daga ina kk) tace masa YAZ HABU ILAL MUSTASHFAH(daga asibiti muke, tunda yaji haka yamaida dubansa ga dan nasa saboda yasan shine dalilin faitar nasu adaren nan ganin yayi sai faman qara damke fuska yake dan murmushi shi yayi sai yace kai kuma me yafaru naga kani tacin magani ko halin ne ya motsa bai bashi amsa ba illa ma tashi da yayi yana niyar barin falon, "MEER" Ummy ta kira sunan sa tsayawa yayi cak batare da ya juyo ba tasan bazai tasoba dan haka ita tashi taje inda yake tare da zagayawa ta koma gabansa idanu ta zuba masa tana kallon sa dauke kansa yayi daga gare ta fuskarshi ta riqo atafikan hannun ta duka biyun sannan tace to duk wannan fushin nameye ne banace za akula da itaba yanzufa zan kira insanar dasu pls kadena sawa ranka damuwa banason ina ganin ka irin haka saboda banajin dadi kaji hannun ta yacire daga kan fuskarta sannan murya qasa qasa kamar wanda bayason yi ko ince me koyan magana haka ya bude baki cikin rarraba maganar tasa yace I'm going to sleep bacci nakeji yana kaiwa nan yayi gaba abunsa batare da yajira cewar ta ba  bisa tayi da kallo har ya qulewa ganin ta sannan taja qafarta ta koma wajen mijin nata,   kallon ta yayi yana dan murmushi sannan yace me yafaru ne, dan gyara zama tayi sannan tace ai kasan ne zai faru kofa gaya min baiyiba ya fita shikadai acikin daren nan shiyasa nabinshi bangayama ka ba kuma naje zantaho dashi wai bazai dawoba yanuna min acan zaikwana shine na tilasta masa muka taho shiyasa kagansa haka, "Allah sarki hala shida mutuniyar tasane? "tace masa karshen zancen kenan nande tabashi labarin abun da yafaru da tattaunawarsu akan za akira malami gobe shima yanuna jin dadinsa da hakan da yaji sunce shima anasa wajen ba yarda beye da meer ba akan yabari akira amma yaqi amincewa dan shima yadade da sanin ciwon matar nan bana asibiti bane amma taurin kan dan nasa ya hanasa ya yarda sai yanzu da yaji uwar bari nande suka cigaba da hirar su basu tashi daga wajen sao wajen qarfe daya da wani abun kafin daga bisani suka tashi suka tafi makwancin su domin bawa gado hakkin, *Tambaya*     "Suwaye wadannan mutanen?   "Su 'yan garin yemen ne garin da yake yankin aqasar larabawa Alhaji Umar Ibarahim dan kasuwa ne sosai wanda shi asalin sa ba a yemen yake ba dan Nigeria acikin garin abuja yake da zama kasancewar sa me yawan fice fice saboda siye da siyarwa zuwa qasashe da ban daban saboda baya wasa da neman kudi tunda kan qananun sana'a yafara kasuwan cinsa har Allah yataimake sa yazama wani aharkar kasuwancin sa saboda rashin gata da rashin kudi da yataso yasa baiyi wata makaran tar boko ba iya kacin sa secondary hakanne yasashi dukufa gurin neman kudi wanda yace idan ya nemin kudin sai ya shiga makaranta saboda iyayen sa basu da hali gashi kuma irin kulawar da suke basa tasha bambam da yanda yaga ana kula da qannen sa tunda yafara neman kudi agarin yake shan wahala dan wataran ma sai yasamo idan yadawo sai akwace masa kuma wannan halin matar babansace saboda shi bashida uwa agidanagurin mahaifinsa kawai yake samun sauki dayagane haka sai yadena nunawa daga qarshe ma da yadan tara sai yayanke shawarar barin garin da farko da qin amincewa da maganar tasa akai saidaga baya kuma kishiyar mahaifiyar tasa ta tsaya masa tace yaje ahaka yabar gidan ya nufi garin lagos acan yake neman kudin sa be waiwayi gidaba sai bayan shekara biyu sannan yadawo ranar da yadawo kwa yaga gida agarqame da kwado alamar sunyi tafi wayoyin su yakira dan jin inda suka tafi amma sai yaji duk akashe makotansu yashiga dan tamabayar inda sukaje anan ake sanar masa da cewa sun tashi daga gidan yanzuma haka wasu sundade da shiga cikin sa yatambayi inda suke akace masa babu wanda yasan inda suka tafi hasalima ko sallama basuyi da kowaba suka tashi yaahiga damuwa sosai akan jin wannan batun aranar de sai hotel yakama ya kwana da sassafe kwa yaqara barin garin ya koma inda yafito kullum yana cikin zulimin ahalinsa da tunanin inda suke kullum waya ahannu yana gwada kiransu amma ko sau daya bata sake shiga ahaka har ayafara cire rai da su yacigaba da neman sa inda kuma maganar karatunsa ta kusan gogewa saida wani mutum yabashi shawara akan yanemi ilimi sai kasuwancin nasa yafi tafiya haka yafara makaran ta anan garin bayan ya kammala kuma sai ya watsar da wani batun karatunsa yaci gaba da kasuwancinsa dan shi agurin sa bega amafanin da zaiyi da kudin gwamnati ba dan haka bazai nemi aiki ba ahaka yafara zama wani daganan kuma ya koma yemen da nemansa anan ne Allah ya hadasa da matar auren sa Watakon ummy ummy kuma asalinta yar garin ce cikakkiyar balarabiyace kyakkyawar gaske asalin sunan ta shine ummu kursum bintu bilal(bafa kiba kirawa😜) iyayen tama duk yan nanne dayake shima ba qaramin kyakkyawa bane gashi fari tass sai ka rantse ma shima balaraben ne haka shakuwa tafara shiga tsakanin su tun suna soyayya aboye har tarafa bayyana lokacin da yan gidansu suka gano tana soyayya da wani yaren daban kuma dan qasar bakar fata sai suka hanata kulasa amma taqiji ta nuna musu itafa bazata iya rabuwa dashi ba, iyayen ta baqaramin bacin rai suka nunamata ba akan sai ta rabu dashi amma taqi duk da kasancewarsa fari tass amma hakan be hanasu hantarar sa ba saboda duk daya suke dakansa da sauran baqaqen babu yanda basuyi ba gurin rabasu amma abu yaki ci yaki cinyewa yarinya kullum bata ci bata sha tashiga wani hali daga qarshedai har kwantar da ita akayi a asibiti amma taqi samun sauqi dan har likitoci sun ma sana shaida musu akan tasamu ciwon zuciya kuma indai ba abata abun da takeso ba to koda yaushe zuciyar ta zata iya bugawa ta mutu, Nanfa hankalin su ya tashi gaba daya suka rasa madafa da suka gade basu da yanda zasuyi kawai suka amince akan yaron yaturo iyayen sa tofa anan akeyin ta bashi da iyaye besan kuma inda zaifara nemansu ba tunda yayi yayi iya qoqarin sa wajen neman ahalin sa amma be samu ba dan haka kawai yace musu bashida iyaye duk sun mutu nanfa suka ce tofa saidai tai hakuri dan bazasu taba bada yarsu wanda bashi da asali ba indai yansonta saidai yaje yanemo danginsa suzo har nan sai ayi maganar nande ya shiga tashin hankali wajen inda zai fara har unguwar tasu ya koma ko anji labarin su amma shiru babu wani labari daga garesu dawowa yagaya musu akan shifa bashida kowa su taimaka subashi bazai taba cutar da itaba sukace basu amin ceba, Ummu kursum dataga haka sai kawai tasamu waya ta kirasa aboye saboda wayama anhanata dashi amma kwace wayoyin ta gashi anhanata fita shine ta ari wayar qanwarta ta kirashi tace masa yazo ya gudu da ita suyi aurensu shikuma yace tayi hakuri su cigaba da lallaba iyayen nata da haka har su amince ba haka tasoba amma ba yanda ta iya dole tabi yanda yace ahaka kusan kullum hartafara satar hanya tana fita suna haduwa da taimakon kawarta da kuma me gadin gidan su ranar da aka gano hakan aka qaramata tsaro nanafa wata sabuwar damuwar tawarayi mata yawa mahaifiyar tace datagade dagske zata iya rasa 'yarta yasa tafitowa mahaifin ummu kursum akan gaskiya yabarsu suyi auren su tundade sunason junan su itafa bataso ayi mata asara tazo yarta ta mutu shima cikin bacin rai yace be amince ba nan fa suka barke da fada tsakanin maman ta da mahaifinta, daqyar yace ya amince amma da sharadi bashi ba ita kuma yacirera daga cikin yayan sa idan sunyi auren ma kar tasake tazauna aqasar kar su sake zuwa inda yake ahaka duk suka amince da sharadin sa ba awani dau lokaci ba akayi musu aure amma kamar yanda suka amince zasu bar qasar sai basu bari ba sukayi nesa da gidan inda yakama musu gida awata unguwar suka cigaba da gudanar da rayuwar su cikin so da kauna da kulawa tare da faranta ran junan su, Alhaji umar mahaifin meer shi ya yanke shawar yace mata su shirya suje ko Allah zaisa ya hakura bekamata suyi tazama hakaba itama tanason ganin mahaifin nata dan haka taji dadin shawar tasa haka suka shirya gabadayansu su ukun sukaje gidan lokacin da sukaje baya nan haka akai ta muranar ganin su ana gaggaisawa ranar wuni sukayi agidan sai dare mahaifin nata yadawo tunda yayi ido hudu da gabjejen saurayi kuma kallo daya yayi masa yagane jinin sane tunda ga kamar dasuke da mahaifiyar sa har cikin ransa yaji dadi ganin jikan sa agabansa amma sai bainuna ba yahade rai tare da samun waje yazauna batare da ya kalli inda suke ba gabansu na faduwa suka zube aqasa suna gaidashi tare da neman yafiyarsa ko motsi baiyi ba bare yadaga kai ya kallesu meer kam nakan kujera abunsa ko kallo kakan nasa bai isheshi ba ganin yanda iyayen sa suka wani dirshen aqasa yasashi jin haushin abun, tashi yayi yafice daga falon dan bayajin zaici gaba da kallonsu ahaka gwara yafita tunkan bakinsu yabude dan bazai fadi me dadi ba, sunakai wajen minti biyar awajen batare da kowa yaqara cewa komai ba, Mahaifiyarta ce data gaji tace bakaji anagaida kaiba tafada tana kallon sa dagowa yayi yana kallon ta cikin hade rai yace kunmanta yarjejeniyar da mukayi daku kukace kunyarda ba banason ganin su su tashi su ficemin daga nan in kuma ba haka ba ni zan barmusu gidan yaqarasa fada yana miqewa da sauri suka miqe tsaye suna bashi haquri tare da cewa zasu fita dakatawa yayi tare da nuna musu qofa jiki babu kwari suka fice daga gidan zuciyar kowa ba dadi, tundaga wannan lokacin basu qara waiwayar gidan ba daga qarshema Alhaji umar ya yanke shawarar komawa qasarsa dan yacigaba da neman danginsa dan yasan duk danrashinsu ne mahaifin ummu kursum yaqi amincewa dashi amma yasan idan yaje ya nemosu yakawo su komai zai wuce kuma wannan zuwan yayi alkawarin bazai qara dawowa ba sai tare da su duk inda suke zaije yanemosu, yayi tunanin idan yafadawa matarsa zatace aa amma sai ta amincemasa da wuri harda nuna jin dadin tama haka akagayawa mahaifiyartama itama bata hanasu ba nande suka fara shirye shiryen barin qasar daman tunkan yayi musu maganar yasa angama yimasa komai gidan da zasu zauna da komai na rayuwa anyi zama kawai zasu fara gida su yake jira basu fi sati da maganar ba suka hada kayansu saidai ba qaramar rigima sukayi da meer ba akan shibazaije wata qasar ba abarshi aqasar da aka ahaifesa su su tafi saboda komansa yana nan ga aikin sa da yake yi.shi bega amfanin tafiyar ba, da kyarde aka shawo kansa suka tafi akan zai ringa zuwa duk lokacin da yakeso haka ya hakura yabisu badan yanasoba bayan komawar su basu dade ba yaqara dawowa baikoma ba kuma saida yayi wajen wata shida saboda bayajin dadin qasar yafi sabawa da tashi qasar shima sai suka matsa masa akan ya koma din sannan ya koma yana koma yaga mahaifiyar sa har ta gina asibiti sannan tace ta dorashi akai angama komai kawai aiki zai fara sunyi masa hakane dan kar yakoma saidai kuma duk da haka saida yaqara komawa da kyarde yafara sabawa danan inda yaci gaba da kula da asibitin mahaifiyar sa asibitine amma ba nomal asibiti ba asibtin masu tabin kai ne saboda fannin kwakwalwa yakaran ta duk wani mai fama da maintal problem nan ake kawosa sai yazamaba kamar zamu iya kiransa da asibitin mahaukata amma fa ba jigari jigari bane asibitine qerarre wanda yasamu kwararun likitoci inda ke bada kulawa komansu a tsare yake dan zaman gaya muku yanda tsaruwar sa take zaman bata lokacine asibiti ne na musamman wanda adan kwanaki kadan yayi kaurin suna agarin abuja, Inda daga wasu guraren ma duk wanda yaji labarin sa sai ya kawo nasa marar lafiya saboda irin kulawar da suke bawa mutum, ahaka yaci gaba da gudanar da aikin sa inda kuma mahaifinsa yaci gaba da kasuwan cinsa gefe guda kuma yabada cigiyar danginsa har gidan radio da duk de an watsa harda jaridu abuka ga masu kudi sai wasu suka fara fitowa suba cewa sune sai yaje yagani yaga basu bane tun yana zuba idon har yafara cire rai, abagaren meer kuma yana kudanar da aikin sa cikin kwanciyar hankali amma fa beda mutunci ko kadan kowa tsoron sa yake ji saboda fadan sa gashi da fadan rashin gaskiya kuma abu kadan zakayi yace ya kore ka beda aboki be qawa saboda girman kasan da jijida kai babu wanda ya isa ya tunkare sa da wata maganar baya dariya baya magana sai yaga dama kuma itama sai ta zamar masa dole inbaiga dama ba idan kaje kana masa magana ko da zaka kwana agun ko daga kai ya kalle ka bayayi bare yayi maka magana gashi da shegiyar mugunta wanda inbaiga dama ba har marasa lafiya yakeyiwa saidai kuma duk abunsa yana dagawa marassa lafiya qafa yana kuka dasu yanda yakamata baya kuskurewa ko wasa awajen aiki shiyasa duk wanda yaga yasa wasa a aikin sa koda tsautsayi ne yajawo hakan tofa sai ya koresa koma yahada maka da duka ba ruwansa duk girmanka shiyasa kowa yaje shakkar ko anhanya su hadu dan akwai wadanda ma idan suka gansa kafi yazo waje sun nemi wajen buya basa hada hanya dashi, mata kwa dayawa suna crushing akansa amma ba wacce tayi gigin tunkarar sa wata sabuwar maikaciyace da ka dauka da bata sana halinsa ba tsautsayi yasa taje masa wai tana wani kwarkwasa da saka takalmi me tsini dan ta ja hankalin sa da tashiga office dinsa harda jan rigarta yanda qirjinta zaifito da kyau wai ita gata cikakkiyar yar iska yana zaune akan kujera yaji shigowar mutum amma be dago yavkalle ta ba bazato ba tsammani kawai yaji ana shafa masa baya tare da cewa hy dear tabb babbar magana marya mace kuma hannun ta ajikin sa cike da zafin nama yatashi tsaye yajuyo afusace sai kawai ta rungume sa cak ya tsaya be qara motsawa ba jin hakan yasa ta qara narke masa ajiki tare da goga masa kirjinta aqijinsa ganin be motsaba tafara tunanin tarkonta yayi kamu dan haka sai ta dago kanta tana wani kashe ido tare da fari da idanun ta ta shafa fuskarsa da hannu daya hannu ya dora agadon bayan ta tare da sauke zip din rigar ya balle bra din wani irin ajiyar zuciya tasauke jin saukar hannun sa ajikin farata qara narke wa tayi ta kwanta akan kirjinsa daman doguwar rigace ajinkin hannunta ma malline ajiki zip din kuma har wajen duwawun ta yake ga mamakin sa sai yaga ko pant bata sakaba kar kada kai yayi basani ba har ya sauke mata rigar harqasa tare da jefar da bra din har wani lunshe ido take tana sauke numfashi da shaqar daddadan turaren jikin sa kamar saukar aradu haka taji ya buga mata hannu sa atsakiyar kai ba shiri ta sakeshi wata qatuwar waya yajawo akusa da table dinsa tare da kaimata shaqa awuya ta hada ta da bango kanta ya bugu qara tasaki tana dafe kanta wayar ya daga yafara zuba mata ita ta ko ina ihu take kamar ranta zai fita amma babu wanda ya iya kawo mata agaji duk da kasancewar wasu mutanen suna jiyo ta amma suna tsoron shigowa, sosai yazage yana tafkarta harsaida yafara ganin jini ajikin ta amma be qaleta ba yace gaba da zuba mata taba ihu azabace tasata suma ganin ta dena motsi yasashi gane sume masa tayi ruwa yaje ya dauko me sanyin tsiya yazo ya juye mata roba daya afuska da sauri ta farfado tana qara sakin kukan azaba memakon yabar ta sai kawai yaciga ba da dukan ta kamar yasamu jaka saida yatabbatar da cewa ya hada mata jikin ta ya hadu sannan a haka a turarar ya ruqo qafarta yafara jawota zuwa hanyar waje acikin mawuyacin halin da take ciki ta bude baki da kyar tace kayana kar kafitar dan ahaka na roqeka ko kallonta beyi ba sai canqasan qasa da hausarsa da bata fita yace ba iskanci kike so ba aigwara kinunawa kowa ke shegiyace sai afiyarda daganan yayi shiru yajefota wajen tare da mayar da qofara ya rufe har ya rufe sai kuma ya tuna da kayan ta aciki budewa yayi yaga mutane har sun fara taruwa ana kallon ta suna ganin bude qofar sa kowa yafara beman hanyar guduwa tsaki yaja tare da nuna wani namiji da hannu alamar yazo gabansane yafadi yana tunanin karde ko shima dukan nasa zaiyi be isa yaki zuwa ba dan haka dole ya lallaba cike da fargaba ya shiga office din kayan kawai yanuna masa da hannu lamar yavwkashe su ajiyar zuciya ya sauke tare da kwasar su yayi saurin fita harda hadawa da dan gudu gudun sa, yana fitowa mutanen gurin harsun qara taruwa kowa na kallon ta babu wanda yayi yunqurin taimaka mata da wani abun da zafa rufe jikin ta dashi, ita kuma tana gefe ta takure guri daya sai karkarwa take tasaka hannun ta dafe qirjinta dashi sai faman kuka take jitayi andora mata kaya ajikin ta wani kukan taqara saki sakamakon zafin data qara ji da yadora mata akan ciwukanta jikin ta duk ya fara tashi yayi shatin bulala ture kayan tayi taci gaba da kukan ta saboda batason ma tashi qafafunta bazasu iya daukan ta ba ga kunya da tagama rufeta bazata iya hada ido da kowa ba, wata qawartace ta qaraso gurin da sauri tana cewa subhanallah tima me yake faruwa ta juyo tana kallon su da jiran qarin bayani nan fa akafara gayamata abun da suka gani wani ne daga cikinsu daman haushin ta yakeji tunfarkon zuwanta yace yana sonta amma taci masa mutunci saboda tana taqama da kyaunta da irin halittar da Allah yabata me daukan hankalin maza shiyasa take ji tawuce ajin kowa, budar bakinsa cike da sheqiyanci dajin dadin yanayin da yaganta yana dariya budar bakin sa sai cewa yayi iskanci taje aka koya mata anfita iyawa ga qarshen iskanci ne ta dauka irin tane amma yanzu ai tagane ba daidan tabane mudin da take rainawa yanzu bamaso abun da ake mana gadara dashi gashi abaina nasi abun ma ashe akayane yake kyau dan nidai yanzu ko kyauta baza mu karba ba sai akai wani wajen yaqara sa fada yana qara nunata da hannu tare da sakin wata dariyar kowa Allah wadai yake da abun da taje tayi, gashinan yanzu ankoya mata ai an koya mata hankali magnin dan iska kenan nan fa gurin yafara daukar magana kowa nafadar albarkancin bakinsa masu jin haushin ta sukaji dadin abun harda dariyar su wasu kuma tabasu tausayi sun tausaya mata, wasu kuma sun qara jinjinawa rashin tausayin sa da wulakancin sa abun har yakai ga kayiwa mutum tunbur tsirara haihuwar uwarsa sannan kadakesa kuma katurosa ahaka gaban mutane wannan abun baikamata komai taimaka baikamasa baikamata yayi mata irin wannan hukuncin ba hakade kankace me magana ta karade ko ina dan magana hartafara fita waje da kyar aka kawarta ta saka mata hijabi shima tana ta kukan zafi zafi da haka de da kyar da taimakon qawar tata suka fita daga asibitin atakaicedai tundaga wannan lokacin bata qara dawowa asibitin ba kuma babu wani mataki da zara dauka saboda tasan ita tajawa kanta kuma da kunya ta fada agida ga abun da yafaru da ita dole ta koma gidan su qawarta saida tagama jinuar jikin ta sannan ta koma garinsu daman irin masu zaman kannan nasune wanda sai yanda sukayi da iyayensu dan haka bamai tambayarta ina take kwana sude kawai tabasu kudi sukashe Koma ta wane hanya ta samo ba ruwansu basu tambayaba(hmmm Allah ya kyauta) "tundaga lokacin kowa yaqara baya baya dashi shikam abangaren sa yama manta da rayuwarta dalilin da yasa kenan har yanzu bashi da budurwa kuma basa gabansa dan haushinsu ma yake ji gaba daya shiyasa shi kadai yake rayuwar sa inka gansa yana hira me dan tsayi to da mahaifiyar sa ne dan ko mahaifin sa baifiya sakewa dashi ba kamar yanda yake sakewa da mahaifiyar sa duk da itama ba wani hira me tsawo suke da ita ba kawaidai gwara de ita akan kowa, "ranar wata lahadi aka kawo musu wata mata marar lafiya wanda natama yayi worst da yawa saboda a daddaure aka kawo ta kuma saida akayi mata allurai ma da yasata bacci sannan aka iya kawota asibitin, ba bata lokaci aka kaita inda za abata kulawa aka kwantar da ita dayane daga ciki yanemi iso ga doctor din bay an anyi masa rakiya wajen meer sungaisa yake masa bayanin marar lafiyar da suka dawo akan cewa motace ta bugeta tunda ganan kuma ba aqara gane kanta ba saboda sai da akayi mata aiki akanta da magunguna harta warke ta wannan bangaren to saidai kuma sunkasa gane kanta kullum cikin bige bige da fisge fisge akan sai anbarta ta fita kuma bata magana shiyasa suka yanke shawarar kawota wajensa nande meer ya nemi ganin ta bayan yake ya dubata yace ina iyayen ta kode wani nakusa da ita mutumin yake cemasa wallahi suma basu san kowa nata ba tsuntar ta sukai wani mutumine yakirasu akan suzo su daiketa ya bugeta to da sukaje bayan sun daukota amotar su mutumin na binsu abaya suna zuwa asibitin suka nemeshi suka rasa ya gudu haka suka cigaba da kula da ita aqarqashin kulawar me asibitin shine daga baya da yaga abun nata ba sauqi sai ya turosu wajen sa, sosai yagamsu da bayanen sa kuma yaji matar ta bashi tausayi sai kawai yace subar masa komai a hannun sa shima daga yanzu ya dauki nauyin ta suje kawai idan ta samu lafiya angano daga inda take zai nemesu nande sukayi sallama suna yi masa godiya da mamakin saukin kansa da tausayin sa yanda lokaci daya ya yarda dasu kuma ya amince gaskiya irinsa kadan ne aduniya bakowa bane lokaci daya zai yarda da hakan cike da jin dadi a zukatansu sukabar asibitin hankalin su na kwanciya saboda jinsu suke kamar sun sauke wani nauyi, tundaga wannan lokacin meer yake bawa matar nan kulawa ta musamma shide a iya binciken da yayi yaka sa gane wata matsala da take damunta saboda kwakwalwar ta bata da wani matsala amma gashi idan tana abu tanayi irin na mahaukata, hakannan yaji matar ta kwanta masa arai yaji yana sonta kuma yanaso yaga ta tashi lafiya qalau burinsa kenan kullum yana wajen ta bacci ne kawai yake rabasa da ita shima kuma saboda ummyn sa na hanasa amma da anan zai ringa kwana zuwa lokacin kuwa kowa yafara samun freedom saboda befiya bi takan lamuran suba ita kadai ce agabansa aikin ma yanzu ba sosai yake gudanar dashi ba indai kaga yayi maka fada to kataba tane ko kataba abun da ya shafi lafiyar ta nanne zaka ga bacin ransa inma takama da duka yayi maka, "ahaka yaci gaba da kula da ita tundaga wannan lokacin harzuwa yanzu da yakama shekara kusan biyar kenan yana abu daya akanta, Wannan kenan ina fatan kun fahimta inma baku fahimta ba zakufi fahimta nan gaba........✍️✍️✍️ [5/24, 9:35 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤         💅 💅💅💅💅💅 💅SARKI SAMEER......💅              (wasa farin girki)              💅💅💅💅💅💅💅💅💅                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿35&36 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ *cikin masarauta*      "yanda sukayi mata runfa bayan hasken yadawo baqin yagama daukewa suka fara matsawa daga gurin ta, "sameer ne ya dauketa batare da yace komai ba yayi gaba sukuma suka rufa masa baya yana tafiya suna binsa abaya part din momma dinsa ya nufa da ita har suka qarasa ko nocking beyi ba ya tura qofar ya shiga kai tsaye ya kaita kan kujera ya kwantar da ita tare da cewa mikon ruwa, "shettima ya nufi kan dinning yadalo ruwa marar sanyi ya kawo masa karba yayi ya yayyafa mata ajiyar zuciya ta sauke tana bude idon ta abun da yafaru yafado mata atai da sauri tajawo hannun sa  tare da qamqameshi duk tabi ta fita hayyacin ta can kuma tasaki kuka kawai tsayawa yayi yana kallon ta batare da yace ko uffan ba, "bossay ne yamatso kusa da ita yace ke kikwantar da hankalin ki babu komai jin muryar bossay yasa tayi saurin sakin sameer ta koma kansa tace mutafi dan Allah mutafi wallahi bazan zauna ba nidai mutafi gida mutafi gida nidai gurin dadda ta zani kaini gurin ta dan Allah ka kaini tana magana tana kuka gashi tabi ta ririqeshi qoqari yake yarabata da jikin sa amma yakasa cikin sigar rarrashi yace ya isa haka to kiyi shiru ki sakeni sai mutafi kinji sakeni nace mutafi makale kafada tayi ita sai yatashi suntafi sai wani kukan take saki, sameer da yaji ta isheshi ya daka mata tsawa dacewa dalla malama kiyiwa mutane shiru ki nutsu yafada yana kai hannun sa kanta zai cireta daga jikin bossay din, momma dake saukowa daga step din stairs tun shigowarsu tana kallon su saboda itama tana falon abun da yafarune yasata tashi ta koma daki ba shiri yanzu kuma da taji komai yayi shiru yasata fitowa dan tambayar yan waje abun dake faruwa sai kuma tace karo dasu, Qarasowa tayi  tace rabu daita ya isa haka tafada tana kamo hannun ta tace zonan "yata rabu dasu daina kukan sai amaida ke gidan ko kai tadaga tare da dagowa tana kallon matar hakan nan taji bazata iyayiwa matar musuba sabosa kwarjinin da tayi mata sakin bossay tayi tare da komawa kusa da momma kamota momma tayi da kyau ta rungume ta lokaci guda Ameesha ta sauke ajiyar zuciya tare da tsayar da kukan da take bakajin kukanta saidai 'yar shashsheqar da takeyi kadan kadan momma bata saketaba har saida taji tayi lufff ajikin sannan ta dagota tana kallon ta yarinyar taji hakannan ta kwanta mata arai sai take ganin ta kamar su Amra, "goge mata hawayen da suka bata mata fuska tayi sannan ta dawo da ita gefen ta tana kallon ta batayi mata magana ba sai ta maida dubanta ga su sam da duk sun tsaya suna kallon ikon Allah, "wannan abunne ya tsora tata ko shettima ne yace eh wlh har suma ma tayi cike da alamun damuwa afuskarta tace ai dole ta suma wannan abu da babu dadin ji ai nima kaina nakusan suman dan na tsorata da wannan abun, "Shettima yace momma ai inaga dama ba kya waje awaje yafi qara muna fitowa daga mota fa mukaji abun mamakin ma kiga yanda wajen yayi baki gaba daya abun abun maamaki wallahi, "Momma tace nagani mana ai duhun gaba dayane dan har daki watakil ko gaba daya duniyar ce al amarin ubangiji kuma shikadai yabarwa kansa sanin manufar wannan abun, "sam ne yace momma wanna fa a bun alamar tambaya dan iya cikin masarauta ne babu awaje yanzu na tambaya mukadai ne hakan tafaru damu, da mamaki momma take kallon sa tace iya nan kuma? cike da tabbatarwa yace mata eh amma momma hakan be taba faruwa ba ko abaya cen? tace bai taba wallahi yau nafara jinsa amma bari intambayi papa inji ko hakan ya taba faruwa atarihin masarautar nan dan abun abun adubane, "Sam yace gaskiya momma wanna fa babbar matsalace ni tunda nake bantaba jin irin wannan qarar ba qarin mamakin kuma ace gari da haske amma cikin nan yakoma duhu daga baya kuma yayi haske, shettima ma yace nimade gaakiya abun ya tsorata ni harmafa da kururuwa kamar mutane kamar a horow film dannidai anan nataba jina makamancin irin wannan  sai gashi kuma yafaru a gaske a gasken ma acikin gidan nana gaskiya da wani abun da yafaru acikin masarautar nan yakamata abincika, momma tace maganar ka gaskiyace amma ai nasan tunda bamu kadai muka jiba nasan dole za ayi zama akan hakan tunda wannan ba abune da kasaba jiba gashi kuma kunce a iya nanne ni wallahi duk azatona gaba daya duniyar ce tayi haka, hakade suka cigaba da tattaunawa akan wannan babban ala'amarin da yafaru dasu, "Bossay  dai baisaka musu baki ba tunda wannan abune na family be kanata ya tsoma musu baki ba duk da daman shi ransa fal yake da tambayoyin ganin wannan abun da baitaba gani ba yazata ko su sunsaba ko kuma sunsan dashi amma jin tattaunawar su yasamu amsar tambayoyin su saikawai yaja bakin sa yayi shiru bashida tacewa kawaidai yana mamakin hakan, Ameesha ma bata saka nata ba amma de har yanzu a tsorace take jikin ta sai bari takeyi taciki so take ta tashi taje gurin bossay tace masa su tafi amma momma ta hanata damar hakan saboda suk maganar dasuke hannuta riqe yake da nata shiyasa baza ta iya tashiba kodan kwarjinin matar, "bayan sungama maganar ne momma taqara dubansu "tace wanna fa daga ina tafada tana kallon ko qanwar wannance duk da shima de yau nafara ganinsa bansan ku tare ba taqarasa maganar  tana nuna bossay sai lokacin bossay yadan sunkuyar dakai tare sa gaida ita amsawa tayi tare da cewa munhau wata hirar bamu gaisaba ko dan murmushi yayi kawai batare da yace komai ba, "duk shiru sukayi saboda basusan ta inda zasu fara yimata bayani ba, "saida taqara nanata musu tambayar sannan sam yace momma not enough time in mundawo  zan miki bayani yanzu zata zauna daku zuwa dare zaizo su tafi tare, "tace to shikenan Allah ya kaimu ai yanzuma su sweetheart zasu dawo  daga makaranta taqarasa fada tana juyawa ta kalli Ameesha dake ta faman rarraba ido duk jinta take atakure takasa sakin jikin ta amma yanzu ta dena jin rawar da jikin ta yake mata, tanaji tana gani sukayi sallama da momma suka fita jitake kamar ta bisu amma ba halin dole ta hakura ta zauna, lokacin da suka fita,"cikin masarauta an cika dam da mutane kowa yafito Dan jin me yafaru yau amasarauta duk inda ka kalla mutanene a cure suna maida yanda akayi kowa nafadar albarka cin bakinsa, ahaka suka ratsa ta suka shige mota duk da mutane sai kallon su suke suna Jira suji ko zasuce musu wani abun amma shiru har suka shiga motarsu suka fice suka barsu," sukuma suka cigaba daga inda suka tsaya, "duk yanda momma taso Ameesha tasake da ita amma taqi saima qara nannadewa datakeyi ita kadai taqi sakin jiki da ita ko kallon tama batayi, datagaji da ita taga bazata sake ba sai tayi tunanin ko saboda itane yasa taqi sakewa sai kawai tace ta tashi ba musu kwa tayi saurin tashi tsaye itma tashi tayi tare da kama hannun suka hau sama ta kaita dakin su amra again ta watakil tafi sakewa idan taga ita kadaice shiyasa ta kaita tare da cemata ta zauna bari akawo mata abun da zataci kafin su dawo kada mata kai kawai taga mata batare da tace komai ba guri tasamu ta zauna aqasan carpet dinsu bayan fitar momma tashi bin dakin da kallo dakin ya burgeta sosai ba wani tarkace Kuma wai Ahaka dakin Yara ne dama ace nata ne da tafi kowa farin ciki gadon su ta kalla sai ta tuna nasu dakin da katifar na kamar carpet din dakin nasu amma su ga qatuwar katifa gashi kuma harda gado tunawa tayi itakan tunds take inba gadon asibiti ba sai kuma ranar da ta kwana akan agidan su shettima dan jiyama qin kwana tayi akan gadon hajiya sai aqasa ta kwanta wai bazata iya kwana da itaba gado daya bayan ba ayi da itaba amma taqi haka aka rabu da ita ta kwana aqasa to bayan haka bata taba kwana akan gado ba Koda na qarfe ne hannun ta daga ta shafa gadon sai kawai ta saki murmushi komai ta tuna oho daya bayan daya taringa kallon komai na dakin tana cikin hakane wata tashigo dakin da try din abinci ahannuta tare da sakin fuska ta qaraso inda take tare da zama akusa da ita, kwanukan ta shiga budewa sannan ta tura mata gabanta kayan fruit ne aciki anyanyan ka mata su tace maza kici ba musu kwa domin kayan marmarin sun burgeta shiyasa ta ci Saida ta cinyesu tas sannan ta ture kwanan, kallon tayi cike da mamakin cinyewar da tayi, "Aqaromiki? ta tambayeta " kai ta girgiza mata tare da cewa a'a " dan murmushi matar tayi sannan ta qara tura mata gasassun kaji da suka sha suya mai kyau har jajaja take tana shining indai ka ganta sai kaso kajita abakin ka yawun ka sai ya tsinke kamarde yanda na Ameesha yayi, "aikam tana ganinsu tafara hadiyar yawu tare kaimata cafka ta danna abakin ta tafara yaga taunawa tashigo yi sobada dadin da yaziyarci kwanyar ta batasan likacin da ta lumshe Ido ba saboda tsabar dadi kunnen ta har motsawa saida sukai gashi daman tana mugun son kaza kaf duniya inka bata kaza to kabiyata(kamar de ni anan ammadai wannan bata burgeni ba😋) gashi kuma andade ba ahaduba shiyasa nanma ba kunya tazage taci abarta ta qoshi saidai Kuma duk sonta da ita takasa cinyeta dole ta hakura, Itade tana zaune tana kallon ta har tagama ta kora da lemo mai sanyi sannan ta kwashe kwanikan tafita dasu bata dade ba taqara dawowa saboda momma tace ta zauna da ita dan haka ta dawo tacigaba da dan janta da hira dake matar tana da barkwanci harta fara sakewa da ita suna dan hira ammade ba sosai ba suna zaune agun aka turo qofar da qarfi, tana shigowa ta jefar da school back dinta aqasa tare da cilli da takalmanta hamra ce ta shigo tana tafam fada tace kedai wallahi hankalin ki ragagge ne yanzu tagaban uban mutanen cen kishigo aguje kuma ahaka ba hijabi ko to wallahi sai nagayawa yaya, lokacin datake wannan maganar Kam Amra harta shige toilet din taciki tace mata to ni ina ruwana da wasu mutanen ai ba hijabiba ko rigace babu ajikina sainabi ta gabansu wallahi ke angaya miki kashi qaryane to baya Jira idan yazo sai anyishi baya daga qafa saurafa kadan inyi awando ai wallahi da anqara second biyar ma sai nasakar muku shi amota shiru ta danyi da maganar tare da skin nishi sannan tace kai wallahi kashi duniya ne kinji yanda naji kamar ankwashe min wani mugun ciwon acikina... "tsaki hamra taja tare da cewa banza qazama ko kunyar fadarsa haka gatsai babu ai da kindan sakaya kodan saboda bakuwa inma ni kinrainani tafada lokacin da take cire kayan jikinta yazamana daga ita sai riga da sket din na makaranta sannan ta qarasa kusa da Ameesha tana sakar mata murmushi duk da batasan ta ba kallon matar dakin tayi tace iya ladi wannan bakuwar fa daga ina? ta tambaya tana kallon Ameesha tana qara washe baki saboda ganinta sa'arta iya ladi na dariyar wautar Amra tace bakuwar momma ce yayyan kune suka zo da ita ayya Allah sarki sannu ko tafada tana mika mata hannu alamar sugaisa itama mika mata tayi fuskarta ba yabo ba fallasa asake saboda tunda suka shigo take kallon su taji sunburgeta tana son taga 'yan biyu especially na irin wadannan masu kamadin sosai......✍️✍️ [5/26, 9:09 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿37&38 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️        "my name is Hamra Abdullah Sameer nice to meet you, Ameesha ce itama tace mata Khadijah Sameer zaki iya kirana da Ameesha. "Wow nice name Ameesha taqara nanatawa tana qara wage baki dan taji dadin haduwa da ita gata sa'ar ta kallo daya taji jinin su yahadu cigaba tayi da surutu tana tambayar ta a unguwar da take gwanin sha 'awa inkagansu kai kace sun dade yanda tasakaki jikin ta itama haka ta saki jiki saidai ba yawan magana daga uhm sai uhm uhm, Iya ladi dataga haka sai ta tashi tace to tunda kundawo ni bari intafi sai ku kula da ita bari innafiya sai insanar da momma kundawo ko kuma taga shigowar ku? taqarasa maganar tana kallon Hamra dake riqe da hannun Ameesha taƙi saki, "a'a bamuhadu da itaba, tabata amsa. "to shikenan zan sanar da ita ku kuma idan kunshirya sai kufito angama shirya muku abincin ku, tana rufe baki Hamra "tace a'a iya ladi kawai kikawo mana nan muci da ƙawata. iya ladi"tace shikenan zan shiryo muku yanzunan kuyi sauri kuyi wanka to iya ladi yanzun nan zamu gama waccen banzarce taqi fitowa tundazu sai kace mecanza fata, "iya ladi dariya kawai tayi tace Allah ya kyauta  inkikayi hakuri yanzu zata fito ai basu gama maganar ba suna cikin yi ta turo qofar, "maida dubansu sukayi ga Amra data fito daga banɗaki jikin ta sanye da towel da kyar take iya qafarta har ta qaraso kan gadon tana zuwa tafada batare da ta saka kayaba ruf da ciki tayi tana sauke numfashi jikin ta duk ya mutu saboda rudewar da cikin ta yayi hartakaita da yin gudawa shiyasa duk take jinta asama sama jikin yayi sanyi ba kuzari, "murya qasa qasa kamar ba Amra ba tace bakuwa ina zuwa bari jikina yadawo daidai kibani 3 minutes zanzo ki ganni in ganki zamu gana, "Shiru Ameesha tayi saidai tadanyi mata murmushi,   "Hamra ce tace Allah yaqara bake bakyajin magana ba kullum ciye ciye kici wannan kici wancen ba dole kitafaman shiga banɗaki banza me rubebben ciki Allah qara wallahi zantayi miki kuma sai nagayawa momma abun kikeyi  a school, "banza tayi mata tare da kawar da kanta gefe hartayi shiru sai kuma taji bazata iyaba sai kawai tayi tsaki tace malama ni yanzu bani da lokacin ki kibari nan da yan mintina sai inzo ki maimaita abun da kikace yanzu ta kaina nake, "mtsww tsoron ki nake jine dazan kasa maimaita wa ne banza marar kunya kawai tafada tana kallon ta da ta juya mata baya bata tanka mata ba, Miqewa tayi tace my qawa bari inyi wanka infito ko ta tashi karki kula wannan yarinyar zata rainaki dan raina mutane baya mata wuya, " yar ƙaramar dariya Ameesha tayi sannan tace ai ta girmeni wane raini kuma saidai ma ai kice kar ba rainata, "waya gaya miki kingirmeta inma baki girmeta ba to kin girmeta da hankali dan ita bata dashi domin jariri ma wataran yafita lissafi bare kuma ke da kike ahaka Nana san zaki girmeta, " wallahi Hamra kifita daga idona inbaki daina cewa bani da hankali ba wallahi sai na nuna miki danyan haukan ina gaya miki banaso amma kinqi kidaina ko abun har yakai agaban mutane to wallahi Allah yabaki sa'a da rabon jikinki yayi tsami , rai abace Hamra tabar qoqarin cire rigarta datake tajuyo tana  ta kalleta tace ni kike gayawa haka ni zaki daka to Bismillah dan halak ka fasa angaya miki din mahaukaciya kiyi abun da zaki inkin isa hannun ki yatabani idan kincika marar kunya mahaukaciya kawai tafada makawa bayanta harara qinkulata tayi hakan yasa taqara quluwa jitake kamar taje ta shaqota daga kan gadon tayi mata duka amma ba hali dan anhanasu dukan junansu idan kwa hakan tafaru ko kaine da gaskiya kai za ahukunta musamman ma da ta tuna yayansu yana nan shiyasa  kawai tarabu da ita tare da yin kwafa ta wuce bathroom tana tafaman bambami itakaiadai,   "kulawa yabawa  ancewa jaka adama cewar Amra tanatabe baki tare da yunqurawa ta tashi zaune, "itade Ameesha na zaune ta zuba musu ido ita abun nasuma dariya yabata dan bataga abun fada ba anan amma ta lura Hamra taji haushi ita da gaske ta dau abun, "bayan Amra ta tashi wajen wardrobe dinsu taje ta ɗauko doguwar riga marar nauyi tasaka sannan ta dawo gurin da Ameesha take zaune, itama zama tayi daf da ita tace bakuwa ganin nazo nidai sunana Amra yayar waccen yarinyar da tashiga banɗaki,kallon ta Ameesha tayi tace kuna twins amma har akwai wani yaya da qanin, Amra tace"eh mana amma ba rana ɗaya akahaifemu ni aka fara haifa ita kuma bayan kwana biyu aka haifeta kigakwa ai narigata zuwa duniya koda minti ɗaya na girme ta na girmeta bare kuma har kwana biyu, "Wallahi ƙarya take miki rana ɗaya aka haifemu kuma ni nafara zuwa duniya kafin tazo cewar Hamra da ta fito daga wanka, "harararta Amra tayi tace kinga rabu da ita ido ba muduba ai yasan kima kema ai kinga alamar nice babba ko? tafada tana kallon Ameesha,   "daga mata kai tayi tace eh naga alamar itace babba duk wanda yace shine to bashi bane kemeyasa kike son shekaru haka,   "Amra tace au hakama zakice to shikenan ba ruwana dake tunda kema ƙaryata ni zaki tafada tana ƙoƙarin miƙewa daga gurinbarin wajen kamota Ameesha tayi tace yi hakuri na yarda kece babba ni inkina soma sai inƙara miki da nawa shekarun dan murmushi Amra tayi sannan tace Allah ya taimake ki kinyarda amma da nikadai nasan zaman dazanyi dake saboda ƙaryatanin da kikayi to ai shikenan yanzude komai ya wuce tunda nayarda, hamra dake jinsu tana saka kaya bata yanka musuba ta juyo tace ƙawata kema kirabu da ita kike kiyi wankan kafin akawo mana abincin ba musu ta ce to tare da miƙewa daga gurin Amra ce tayi saurin tashi tace zo kikarbi towel tafada tana nufar inda suke a sakale ɗaukowa tayi ta bata tana karba bata cire kayan agun ba ta tashiga ahaka da kayan jikinta bata daɗe ba tafito bayan tayi wankan sai ta maida kayan jikin ta tan fito duk suka bita da kallo Amra tace naga kin mayar da kayan da kika cire kinga fa waɗanda na ɗauko miki kallon kayan Ameesha tayi sannan ta qara kallon ta tace "a'a Nagode wannan is ok ai dazan fito nasaka dan hade rai tayi tace Allah sai kinsaka su, hamra ce ta karaso wajen da take itama ɗauke da kaya ahannun ta tace dallacan ko zata sakama naki zata saka to nawa zata saka ungo dan Allah kicire waɗannan kisaka wannan Amra ce ta fusge kayan tace Allah nawa zata saka inbanda neman fada ma bani nafara bata nawa ba itama hamra tace nata za asaka itade ta zuba musu ido sunatayi kowa yaqi hakura suna cikin haka momma tashigo dakin tsayawa tayi tana kallon abun da sukeyi Amra ce tafara ganinta sai tace yauwa momma gwara da kika shigo kizo kiyiwa hamra magana tabari tasaka kayana mifa nafara bata nawa shine itama wai saidai tasaka nata kuma wallahi momma na rigata qaraaowa tayi sai ta karbi kayan gaba daya sai ta dauki ɗaya tabawa Ameesha tace saka wannan kuyi sauri nace baza akawo muku nan ba kufita muci gaba dayan mu,   "gwalo Amra tayiwa hamra saboda kayanta momma ta karba tabawa Ameesha, ita kuma Hamra haushi taji ta hade rai daman tasan hakan zata faru tunda taga shigowar momma tasan shikenan momma na Amra zata bata, Momma da ta lura da fushin da hamra take da harzata shareta sai kuma tafasa kawai sai tace ke kiyi hakuri tunda kece babba kuma ba ga ta nanba sai inroqi abarta tunda gobe ba makaranta sai ku zauna kinga kema sai tasaka naki gobe ba shikenan anraba ba, sakin fuskarta tayi harda dan murmushin ta tace to shikenan momma dama abarta muyi weekend dinnan tare wallahi naji dadin haduwa da ita, momma tace to saidai yayan naku yadawo sai ku tambashi da kanku ko ku tambayi yayanta danagansu tare kuma sunce tare zasu dawo cike da murna gaba ɗayan su suka hada baki wajen cewa Allah yasa abarta momma, tace Ameen, "bayan Ameesha tagama saka kayan sai momma ta tura su suka fita daga dakin zuwa falon dan cin lunch, agurin cin abincin ma saida suka kusa fada sude fada baya musu wuya komai ma nafadane haka ake fama dasu Hamra son girma da kuma tsokana ita kuma Amra rashin hakuri da indai tai mata sai ta rama ta wani bangaren Amra tafi hakuri kuma tafiya sauqin kai da saurin fahimtar abu saboda ita sai ka tabota kuma akwai yawan wasa dan ita sai taimaka magana wanjen goma amma bata gaskiya aciki kawai tayine awasa kuma koda kayi mata laifin da yabata mata rai to data rama anwuce wajen zata manta dashi saɓanin hamra da ita bata san wasa ba gashi wataran ita zata fara tsokanarta da fadan amma kuma ita idan tayi mata sainata ran yabaci ga riqo akwaita da riqo indai kayi mata abu ko bata ramaba to yana nan aranta dan badan Amra bata biye mata da tuni sunfara 'yar gaba saboda abu kadan yahadasu sai tafara daina mata magana itakuma Amra sai ta kurata to bayanda zatayi dole ta sauko shiyasa suke yawan samun saɓani saboda halinsu baizo ɗaya ba kuma kowa bazai barwa kowa ba idan rigimar ta tashi ahakama dan anayawan tsawatar musu akan kuma hana fadan dokeke acikin gidan shiyasa komai zasuyi iyakacin su na fatar baki,     "Bayan sundaidai ta parking agaban gidan prison din suka fito gaba dayan su tare da nufa ciki bayan sun shiga suka sanar da wanda sukazo nema akayi musu iso har zuwa office dinsa suka shiga su suka bayan sun suke qara sanar dashi daga inda suke da kuma abun da yakawo su duk da yariga da yasani amma saida suka qara yimasa bayani, ba bata lokaci yafara yi musu nasa bayanin,   kamar yanda nagayawa mahaifin ka gaskiya lokacin da abun yafaru banine anan ba saida yanzu zamuje daku kuduba ko ina idan kun ganshi to sai afara binciken inda file dinsa yake inyaso ku kuma sai shigar da qarar, sam yace idan kuma ba anganshiba kana nufin baza mugansa ba shikenan ko ko me kake nufi, da mamakin maganar mutumin yake kallon sa ganin shi ko ajikinsa maganar da yayi tunawa da ko shi waye sai kawai ya kawar da mamakin sa, yadanyi murmushi sannan yace bawai haka nake nufi ba ai ganin nasane zaifi sawa mugano bayanen sa da wuri amma idan baya nan kaga abun zai bamu wahalar gano inda yake kamar yanda kukayi min bayanin cewa tun alokacin bayan an hamada haduwa da kowa kaga kwa mai yiyuwa ne ace suncanza masa guri tunda har basa so azo wajen sa, yanzude abudaya zamuyi muje afara bincikawar idan babu shi zanduba cikin sunayen da suka yi aiki anan inayaso sai muduba na shekarar da yayi aiki anan koda yanzu baya nan sai muneme shi ko ya kace nidai inaganin wannan ce hanyar da Yakamata mubi dan inada tabbaci kaf cikin gurin nan ma baifi kasamu mutum biyarba waɗanda suna nan tunwancen lokacin har zuwa yanzu wasu dayawa sunbar nan wasu anyi musu transfer wasu kuma sunyi ritaya tunda gaskiya andade, shiru yayi yana kallon su danjin bun da zasuce game da bayanin da yayi musu, Shiru sukayi gaba dayansu saida ga bisani Shettima yace hakan yayi dole abi ta wannan hanyar yanzu kamata yayi aje aduba din gashi ma kuma matar tagaya masa inda dakin yake kaga shiga kawai zamuyi inba ya nan sai ko tambayane muyi dan nima bana tunanin zasu barsa anan haryanzu, sam ne yaja dogon numfashi tare da furzar da iska mai zafi daga bakinsa sannan ya miƙe yana zagaya office din tare da saqale hannun sa abayan sa batare da yace komai ba saida yayi yan mintina sannan ya juyo yana kallon sa da shima shi yake kallo aransa yana mamakinsa, ba dubawar da zamuyi yanzu abun da za ayi shine kawai ka dauko mana record din naku aduba sunan mutumin da yakarbi case din ta kansa zamu fara ai bama yacikin prison dinan dole sunfita dashi mutumin zamu fara nema kafin muyi komai shizamu fara kamawa zai fadi inda yakaishi kafin ya sauka, shiru mutumin yayi yana nazarin maganar sa kafin yace masa gaskiya yanzu baida alhakin da zai iya basu wani abun dole shima sai yayi magana da manyan sa kafin yabasu Shettima yace kamar nanda yaushe zakai magana da sudin yace musu subashi nan da gobe ma sai sudawo, nande ba wanda yaqara cewa komai banda kallo da sam ke binsa dashi babu abun da yake wanda kallon nasa har saida yasa mutumin yadan fara tsarguwa da kallon da irin kallon da yake masa, baide kulasaba har suka miqe tsaye su shettima sukayi masa godiya sannan suka fita daga ofishin, yana ganin fitar su hannun sa har rawa yake wajen saurin dauko wayar sa yadannawa wata number kira ana daga ya sheqe da dariya sannan yace ka kwantar da hankalin ka har na tsarasu sunma tafi yanzu haka ma inajin sun shiga mota nace gobe su dawo nikuma kafin goben baza su qara ganina ba duk sanda sukazo zance musu bana nan mahaifin nasama zanyi blocking din number sa ta yanda bazai qara samu naba duk wata hanya da zata hadamu dasu Bazan bari su ganni ba bare hartakai ga na basu sunanka daga can bangaren aka bashi amsa da cewa yauwa aikin ka na kyau zansa aqara maka salary wannan watan zaka samu kaso me tsoka kaide Kaci gaba da abun da nasaka inbahaka ba kuma kasan halina koda wasa karka kuskura kagaya musu inda nake kajini yana washe baki yace angama baza sutaba sani ai kasanni da iya aiki daga cen mutumin yace ai saboda haka na ɗoraka akai nasan zaka iya fiye da hakama jin anyabeshi yasa shi qara washe baki yana yimasa godiya daga nan sukayi sallama ajiye wayar sa kenan yamaida kansa jikin kujera yanajin dadin qarin kudin da za ayi masa, kawai yaji anturo qofa kallon qofar yayi dan ganin me shigowa zunbur yayi ya miqe yana binsa da kallo baigama kallon sa saiga sauran nan sun shigo suma wani qarin abu yahadiye da ya tsaya masa amaqogaro da tunanin me kuma yadawo dasu bayan sun tafi karde ace sunji maganar da yayi wata zuciyar tace taya za ayi sujika bayan qofar arufe take kuma na waje bai isa yaji na ciki ba sauke ajiyar zuciya yayi duk alokaci guda yayi wannan tunanin tare da dan basarwa harda qaqaro murmushin dole tare da cewa a'a kundawo ku kunyi matuqa ne yafada yana qara binsu da kallo tare da komawa kan kujerar yayi zamansa hankalin sa kwance, Shettima mane yace eh munyi mantuwa abun da muka manta shine baka fada mana sunan wanda ya sauka ba kafin ka hau tunda dole daga shi saikai kaga dole zakasan sunan shi, wanidan qayataccen murmushi yasaki tare da cewa taya zanyi insani dana sani ai da tun dazu nagaya muku ai shiyasa nace kubari sai zuwa gobe sannan na binciko ko waye, wani irin kallo sam ya wulla masa da yasa shi yin shiru takawa yayi har inda yake yana kallon sa da kyau kafa yaɗaga ya dora akan tebur din nasa sannan yazuba masa idanun sa sannan yace kace me banjiba sai ka maimaita shiru mutumin yayi bai tanka masaba sauke qafar yayi ya daki teburin da qarfi tare da buga masa tsawa yace maimaita nace mu zaka gayawa maganar banza suwaye manyan naka tsuru yayi yakasa magana yana faman rarraba lokaci guda wata zufa ta fara tsatstsafo masa dan matasawa yayi daga kusa dashi yaje inda ya tashi dazu wani abu yadaga sai ga qaramar waya agun zarota yayi yana nuna masa yadannan ta haske yakawo, ajiye masa ita yayi agabansa da kallo yabi wayar tare da miqewa tsaye yana zazzara idanu tare da kafe wayar da ido alamar kira yagani ajiki kuma kiran na tafiya sam ne yadanna wayar yasata a hands-free tare da dago tasa wayar itama yasaka ta a hands-free sannan ya karamasa ita akunne yace kagane ko har yanzu kana buqatar bayani? Bossay ne yace ah in baigane ba ai sai ayi masa bayani yanda zaifi ganewa yana fada ya matso kuda shi tare da kifa masa wani gigitaccen mari baigama tantancewa ba yaqara bashi ta dayan barin yace yanzu kagane, Adade baigane ba amma yanzu da aka mareshi kuma yaji duk muryoyin su acikin wayoyin yagane cewa sun ajiye masa waya tare da connecting din kira atakaicedai sunji wayar da yayi shiyasa suka dawo, tsoro da furgici duk alokaci daya suka riskesa tunda yadafe kumatunsa baqara yarda ya dago ba gudun kar yaji wani ammafa aransa yana ayyana duk abunsu saidai suyi sugama amma bazai taba gaya musu ba duk abun da zasuyi mishi saidai suyi surabu dashi inkuma suka nemi suyi mishi hauka yanzu yasa akamasu adaure su agun, bazato ba tsammani yaji wani irin duka ta tsakiyar kansa kamar an doka masa guduma da sauri yajuyo yana kallon sam da ya hade rai idonsa har sun fara canza kala cikin daga murya yace ya sunan shi kuma a ina zamu sameshi waye shi yafada yana tsatstsare sa da ido shiru ba amsa tsawa ya kuma daka masa yace waye shi zaka fada ko sai aikaka inda ba adawowa yafada tare da kaimasa shaqa kif kif yafara da ido shima cikin fakiya da daga murya yace bazan fada ba kuma kasake ni kasan matsayina anan gurin wallahi idan bakuyi wasaba duk sai nasa an kulle ku inga uban da zai kunceku kasakeni nace yaqarasa shima da yimasa tsawa yana rufe bakin sa ya kwasheshi da marin da saida yaga haske ya gifta cikin bacin rai yace kasaka inka isa nikuma sai nasa an qulle duka dangin ku ba kai kadai bama kaiwaye da har ka isa kayi min tsawa ko uwata bata min tsawa sai kai nace sai kai yaqara kai mishi naushi a kumatu na take bakin yafashe, Amma duk da haka bakin bai mutu ba yaqara cewa kodan waye angaya maka dan babanka yana lauya zanji tsoron kane ko shi bafi qarfin in kulle shiba kuma bai isa yasa akulle niba ko akoreni daga aiki shi asuwa wallahi matsayin sa baikai nan ba yafada yana qoqarin fusge hannun sa daga riqon da yayi masa amma yakasa saboda ba qaramin riqo yayi masaba, jin hakan yasa sam bayar da wayar kawai yahaushi da duka ta ko ina bossay ma ba abarsa abayaba haka yazo suka tarar masa suna duka suna dukansa suna yafadi gaskiya amma yace saidai su kasheshi amma bazai taba fada musu ba, saida suka gaji dan kansu suka ga daku iya dakuwa yafita hayyacinsa dan har numafashin sama yafara daukewa sannan suka rabu dashi shettima yace tunda bazai fada ba kawai su tafi da wayar inyaso sai suje sucire sim din su duba number da yayi waya da ita last, karkada masa kai sameer yayi sannan yace masa ai bazamu rabudashi ba mukai sa mota mutafi dashi duk sanda yagajida azabar da ake masa yafada kallon sa shettima yayi sannan yace kana ganin zasu barmu mufita dashi ahaka ai dole sai suntambayi ba'asi karmuje kuma suyi mana wani abun ma idan sukaga halin da yake ciki nide ina ganin kawai murabu da shi anan inyaso sai mudawo gobe sam kallon baka da hankali yayi masa sannan yace bakaji me yace bane bazai qara bari muhaduba kana ganin yanzu inmuka rabu dashi zamu qara kamasa ne bare kuma idan wancen yaji labarin munsan wannan qarya yake ai dole su qara canza wani daban kawai bets solution shine mutafi dashi inyaso sai mugano inda wancen yake takan wayar nan yafada yana nuna wayar hannun sa, Shiru shettima yayi yana tunanin ta yanda za suyi sufita dashi daga gurin nan batare da kowa ya gansuba dan nufasawa yayi sannan yace kai yanzu to wacce shawarar ka yanke taya kake ganin zamu fita dashi batare da kowa yagani ba, bai basa amsaba kawai suka ga yanufi hanyar fita saida yakai bakin qofa sannan yace musu kujirani ina zuwa bayan fitarsa da kamar minti hudu yadawo hannun sa roqi da wata baqar leda ajiyeta yayi agabansu sannan yadauki audiga ya gogewa wancen jinin da yadan bata masa fuska sannan wani abu aroba me kamar turare sai ya fesa masa shi afuska sannan ya zaro face mask yasaka masa sannan ya miqe yace ku kamo sa yatashi tsaye haka suka tasheshi tsaye kuma yatsaya da qafarsa idonsa abude yake amma kuma babu abun da yakeji kawaidai asama sama yakejin sa baisan ko shi waye ba komai zaiyi komai yakeyi shi mutum ne ko aljani oho, Sam yace kusake shi zai iya zuwa da kansa kawai mubi bayansa kafin nan da minti biyu mu isa cikin mota in bahakaba kuma zai iya faduwa ahanya muyi sauri lokacin mu na tafiya dan tattare furin sukayi yanda baza agane anyi wani abuba sannan suka dauko wayar sa tare da kashe komai na office din na wuta sannan suka fita suka jawo office din tare da saka masa key suka cire key din suka tafi dashi, suna fitowa mutanen dake waje suka fara binsu da kallo daya daga cikin su yace yallabai jiranka fa ake tundazu naga kuma zaka fita bossay ne yayi saurin bashi amsa dacewa yanzu zai dawo ba fita zaiyi ba ok dayan yace kawai dan baidamu da rashin amsawar yallabai din ba saboda baikawo komai aransaba tunda duk wanda yagan sa ba wanda zaice bashi bane ko kuma da abun da yake damunsa baya cikin hayyacin sa tunda ga fuskarsa nml idon sa abude gashi yana tafiya da qafarsa suna tafiya sam yana duba lokaci ahankali yace saura 59 second muyi sauri dan dudubawa sukayi suga ko ba mutane da sai suriqe hannun sa sujashi yanda zasu fiyin sauri amma suna juyawa sai suka ga idon yawancin mutanen akansu kamar ansan basu da gaskia, "wanine ya taho aguje yana cewa yallabai yallabai gashi ance inkawo maka wani file ne a hannun sa yana daf da cimmasu bossay yaqarayin saurin shan gabansa murya qasa qasa yace kai baka san meke faruwa ba ko da dan mamaki saurayin yake kallon sa sannan yace meke faruwa a ina kuma bossay yace kai yanzu tsakanin ka da Allah baka sani ba kode wasa. Kake min yace kamar ya wasa nataho zan basa saqo kuma ka tsareni kana cemin bansan abun dake faruwa ba to kagaya min me yake faruwa ni banji ance komai yafaruba ni matsamin kaga har yakusan kaiwa waje banaso yafita baisa hannnun ba qara shan gabansa yayi yace kai wallahi da akwai abun dake faruwa acikin nan gidan amma nayi mamaki dabaka sani ba to ni ya akai nasani mtsw dayan yaja tsaki yace nibansani kai nifa banma sanka anan ba kuma taya har zakafini sanin abun dake faruwa anan kasan kwa muqamina agidan nan bossay yace kai nima fa ma aikacine anan jiya nafara zuwa shiyasa baka sanni ba amma daga zuwana ni na gane abubuwa da yawa amma nayi mamaki da kai baka gane ba amma de bari indawo kajirani zangaya maka abundake faruwa kaima nasan sai kayi mamaki yanakaiwa nan yayi gaba da dan saurinsa ganin har sun fita daga gate din yana tafiya yana dariyar abun da yayiwa wannan kwata kwat zacen dayake masa bakai ba gindi amma wancen baigane hakan ba kuma yatsaya yabiye masa lalle sokone bashida wayo ahaka shima yafita daga gate din yana fita yaga suna kiciniyar shigar dashi mota saboda suna fitowa daidai minti biyu na cika abun kwa da aka fesamasa yafara aiki take yazube musu awajen Allah ma yasosu babu mutane awajen qaraswa yayi gurin su shima yaci gaba da taimaka musu suka shigar dashi da kyar saboda mutumin akwai dan jiki ba laifi bayan sun sakashi aciki sai sam yace shettima yashiga inda mutumin yake shikuma bossay ya shiga gaba shi kuma zaiyi tuqin gaba dayansu da mamaki suke kallon sa wai zaiyi tuqi da kansa musammanma shettima da shide tunda suke baifi ya qirga saunawa yataba yin tuqiba shima kuma tun loakcin yarintar su, babata lokaci bossay yashiga inda yace masa din shi kuma ya shiga driver seat yazauna tare da tayar da motar suna tayarwa saiga wannan saurayin ya qaraso wajen da gudun sa yataho yanaso ya tsayar dasu amma ina tuni sam yaja motar a 360 suka bar wajen tare da badeshi da qura suka qara gaba kwafa yayi yace amma yallabai bai kyauta min ba ina tayi masa magana amma yaki kulani daman ance bashida mutunci akwai wulakanta mutane amma shi baitaba yarda ba sai yau kwafa yayi cike da taqaici ya juya yakoma ciki yana tafaman mita dan har ga Allah baiji dadin abun da yayi masa ba, da gudu yake jan motar kamar zasu tashi sama shettima de da yaga yakasa hakuri saida yayi magana yace dan Allah kabimu ahankali gudun yayi yawa gashi kuma nidai baganin ka nake kanajan mota ba bare ince ka kware gaskiya kabimu ahankali, Banza yayi dashi saima qara qure giya dayayi dan kamar zigashi yayi haka yaje jan motar ga mugun overtaking din da yajeyi yanda bashi da hakuri a zahira haka atuqima bashi da hakuri baya dagawa mota qafa saidai ita ta daga masa haka yaje tayi akan titin wani wajen ma inyazo ya wuce sai anzageshi saboda irin gudun da yakeyi Allah nedai yakarsu babu abun da yasane su har suka qaraso wani dan qaramin gida sannan yayi parking awaje sannan yace wa bossay je kabude mana gate din budewa yayi ya sauka sannan yaje yabude musu shikuma yaja motar zuwa cikin gidan bossay ya mayar ya rufe sannan yabi bayansu, har gaban qofar da zata shigar dasu yakai motar sannan ya kashe ya fito lokacin bossay har ya qaraso gurin haduwa suka qara yi suka kamashi suka shiga dashi ciki,falo ne empty babu koma acikin sa wani daki suka nufa dashi suna shiga suka cillasa aqasa tare da rufe qofar sam yace musu su tafi sabar sa ahaka bossay yace idan ya gudu fa yace babu inda zashi zan kullesa ai kuma duk qofar da yataba ma shocking zaiji iya wannan ma kadai ya ishasa kama annan zai tazama har sai nakamo kowa nahadasu sannan inyafadi gaskiya yafita in kuma yayi wasa a fita da gawarsa, yana kaiwa nan yayi gaba ba wanda yayi magana acikin su sukabi bayansu suka fita daga cikin gidan ya kullosa aciki bayan sun fita ta wajema suka saka kwado ajiki ( padlock) sannan suka nufi motar su amma yanzu sam sai kawai yabude back seat ya shiga da suka ga haka sai shettima yakalli bossay yace yanzu kuma kai sai ka tuqamu tunda abun bidabi yazama ko cewar bossay shettima yace eh mana tunda nayi shima yayi kaga yanzu kuma kaine alayi,, toshikena cewar bossay sannan ya bude motar ya shiga shima shettima yazagaya ya shiga bossay ya tayar da motar suka bar unguwar sam ne yace mutafi office sai agwada wannan wayar mubincike ta daman akwai dayar nan ma da ban dubata duk sai adubasu yanzu shettima yace eh hakan yayi ma gwara aringayin komai da wuri dannaga alamar akwai aiki agabanmu sai munyi da gaske daga farawa munfara da mai taurin kai Allah yasa sauran kar subamu wahala irin tashi, bossay dake tuqi yace ai saima ansamu wadanda suka fishi shifa kawai kudin albashi za aqaramasa amma kaji yaqi fada ina wadanda ake turawa kudade kallifa lokacin da aka tura min kudin nan masu yawa yanzu in akasamu wanda baida shi meyema bazasu iya yiba dan ganin sun samu kudin ai ba qaramin shiri zamuyi ba dan sai ya dauke mu lokaci mai tsawo banajin za a iya kamosu duka a lokaci qalilan dole muna buqatar lokaci, Sam yace awajen ka ne kake ganin haka amma nan da sati sai mun kama duk wani mai hannu aciki indai inyi zamuyi da gaske, Shettima yace to Allah yasa mu iyayi amma nima ta maganar tasa nake ganin kamar zamu sha wahala wajen kamasu tunda kudi za abasu kuma fa kar kamanta koda munkama wannan mutumin shimafa sakashi akai shima kuma zai iya yiyuwa wanda yasashi din shima sakashi akai gano qarshen maishirya wannan abun ba abune mai sauqi ba wallahi, agurinku ba cewar sameeer daga nan kuma yayi shiru ahalade suka cigaba da tafiya kowa na fadar akbarkancin bakinsa da yanda zasu bullowa alamarin tayanda zaizo musu da sauqi komai batare da wata wahalaba ahaka har suka je asibitin basu dena ba bayan sun shiga sunfito daga mota suna qoqarin shiga ciki suka hadu da saleem da sauri yaqaraso gurin su tare da miqa musu hannu suka gaisa abun mamaki har sam ma baqi bashiba bashi hannun yayi suka gaisa kallonsa yamayar kan shettima yace dr. kwana biyu bana samun ka indai nazo hope dai lafiya fuska asake yace komai lafiya lau wallahi kuma ai ina shigowa kawai dai dadewa ne banayi kaima kuma naga kwana biyu baka zuwa inda nake , "yace wallahi dr ina zuwa bana samun ka yace to shikenan tunda haka kace na yarada suna maganar suna tafiya har suka qarasa gurin da zasu benen inda office din sam yake sai saleem yadaka ta yace to dr sai kafito bari nima inje inqarasa wani aiki dr yace to shikenan sai anjiman har yajuya zaitafi sai kawai Azeema ta fado masa shi sai yanzuma ya tuna dan yadan sha'afa ma da ganinta da yayi juyowa yayi yace saleem, saleem da har yadanyi nisa yajiyo kiran da shettima ke masa amsawa yay tare da juyowa yana shirin tahowa inda yake sai shettima yace aa basai kazo ba kawai idan kagama kafin katafi gida ina son ganin ka kanemeni ko awayane idan baka sameni a office ba, "saleem yace to dr in sha Allah afito lafiya daganan yajuya yaci gaba da tafiya shima shettima haurawa yafara yi dan tuntuni daman sam da bossay sunyi gaba sunbarshi, yana tafiya yana qara tunanin Azeema ransa fal sai yanzu tunanin ganin nata yadawo masa sabo dan yama manta tun awashe garin ranar yaso yakirata awaya amma ya manta yaukam idan ya koma gida zai kirata koda yaji ta bakin saleem din amma sai ya kirata yaji ta bakinta, tura qofar yayi ya shiga basame su a office din ba dan haka yanufi dakin da yake da tabbaccin suna ciki ajiye tunanin nata yayi agefe saboda kar yahanasa yin wani aikin da yakamata yayi da sallam ya shiga duk suka amsa samun su yayi akan kujera sun zauna bossay na danne danne awaya shikuma sam yana bude yar qaramar wayar da dadda tabasu shima guri yasamu ya zauna yana kallon wayar dake hannu sameeer ganin yana qoqarin budeta yasa shi cewa naga zaka bareta? "yace eh taqi kunnuwane watakil ta lalace shettima yace ba lalle ba watakil cajine babu agwada sakata caji mugani, miqama sa yayi sannan yace sakata to mugani nima manta nasa kata caji gashinan kasaka bari indan watsa ruwa kafin nan nasan lokacin sallah yayi idan munyi sallah sai mu hau kan aikin ko, shettima yace najima kamar anfara kiran sallah kayi sauri kafito, bandakin yanufa ba dadewa yafito sai ya canza wasu kayan sannan shima shettima ya shiga amma shi ba wanka yayi ba alwala ya dauro bayan ya fito yacewa bossay yaje yayo shima tashi yayi ya shiga yayo sannan suka jera suka fita zuwa masallacin dake cikin asibitin..........,✍️✍️ *bakwa comment shiyasa nima banason yi bakusan comment shine qarfin gwaiwar marubuci ba idan bakwayi sai mutum yaga kamar bakwa karantawa shiyasa nima bandamu da sai nayi ba watarana naken made hannuna inqi yi wlh gsky Yakamata ku gyara Ni in faranta muku amma ku bakuso bakwa bani kwarin gwiwa* [5/28, 10:18 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿39&40 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                   *Abuja*    ______MEER     "Tunda safe da yatashi yayi sallah be komaba yafara shiri yayi wanka ya shirya ƙarfe shida yafito daga part dinshi taku yake kamar baya don taka qasa a nutse yakeyin ta tamkar wani basarake farine sosai innace sosai irin sosai dinnan dogone amma ba can ba yana da faffadan qirji da cikar haiba sai sumar kansa da tayi wata iriyar kala me shegen daukar ido ko da kallon sumar aka barka sai ka kusan kwana agun kana kala batare da kagajiya ba saboda wani irin gyara da akayi mata gata awani irin kanannade kanannade tadan zubo gefen goshin sa ta barin hagu da barin dama sai tsakiya da shi gashin wajen baikai sauran tsawo ba wani style din akayi dashi can kuma tabayan ƙyeyarsa yadan sauko masa har wajen wuyan sa saida aka saita qarshen yanda suka tashi duk kai ɗaya kuma annade shi taciki sai yazamana idan ya motsa shima gashin sai ya motsa saboda ba amanne yake da kansa ba abunde duk yanda zan fasalta muku baza kugane ba har sai kungani da idon ku ammade kuyi qoqarin yin imagine din kannasa nasan zaku dan hasaso ko kadanne, kan fuskar sa nadawo inda yake kwantacciyar gira waɗan da suke ajere kamar anyi shaving dinsu sai eye lashes dinsa da sukaiyi zara zara idan yabude idonsa sai sun kusan tabo girar sa idonsa farine tass ƙwayar idon kuma brawn color ce dan zagayanta kuma yadanyi Goulding sai idon yanada wata iriyar kala me daukan hankali ga idanun sexy ne sai dogon hancinsa siriri wanda yaqara qawata fuskar tasa sai kwantaccen gemun sa da yafaro tundaga wajen sajensa zuwa habarsa kana gani shima kasan baqaramin kudi ake kashe masaba wajen gyarawa sai dan karamin bakin sa red colar kamar ya shafa masa janbaki gwani burgewa  wanda yake dauke da jerarrun haqora farare masu kyan gaske sai wushirya atsakiya data qarawa haƙoran kyau ga dimpuls dinsa sun lotsa sosai koya yadan motsa baki sai kaga sulotsa kana ganinsa kaga farin balarabe alarabawan ma irin masu kyau dinnan  kyaudai iya kyau kamar shi ya kanshi Allah ya hore masa indai kyaune ba ƙarya saidai kowa yabiyo bayansa duk da hakama fa wai dan baku gansa ba duk yanda zan fasalta muku shi u can't never imagine,   "lokacin da ya sauko qasa ummyn sa bata nan daman kuma yasan bazai sameta ba, sai masu aikin gidan suna ta aikace aikacen su suna ganin shi suka shiga gaidashi amma kamar da gini suke haka ya wuce yabarsu agun daman kuma sunsan za arina sunsan halinshi dan wasuma da basu dade da zuwa ba sai su rantsi basutaba jin muryar saba wadanda suka dade na baifi aqirga ba suka taba jin maganar sa ba,   yana fita yanufi parking lot saidai kafin yaqarasa driver dinsa ya rigasa qarasawa sauri yayi ya bude masa qofa shi kuma ya shiga sannan yazagaya ya shiga shima tare da tare da motar suka fita daga gidan basu dau lokaci ne tsawo ba suka qarasa asibitin bayan sun shiga ciki driver ya daidaita parking ya fito ya bude masa yafito cike da takunsa na isa da qasaita yake tafiya duk da ya matsu yaganta amma hakan baisa shi yayi sauri ba saboda shi haka yake a rayuwar sa bai iya sauri ba ko gaggawa komai a hankali cikin nutsuwa yakeyinsa ba garaje a harkarsa, ahaka yake tafiya har yaqarasa bakin qofar dakin da take kwance tura qofar yayi ahankali sannan yasaka qafa ɗaya sannan yaqara saka ɗayar yashiga tura qofar yayi sannan ya jingina da qofar tare da harde hannun sa ya zuba mata idanu sai yanzu yaji sanyi aransa da yazo yaganta akwance kamar yanda yabarta yakai wajen minti biyu awajen kafin yaɗaga qafarsa ahankali yafara takawa zuwa wajen gadon da take kwance kujera yaja ya zauna tare da zubawa fuskarta ga mamakin sa kawai sai yaga hawaye yana zubowa daga idonta zunbur yayi ya mike tsaye yana qara dubanta da kyau hannun sa yakai zai share mata sai kawai yaga ta bude idon ta dakatawa yayi tare da maida hannunsa yadan ja baya kadan ganin irin kallon da take masa kamar ya sha bambam da sauran dan yanzu sosai ta tsare sa da idanunta shima kallon nata ya tsaya yanayi, rufe idon tayi sai kuma taqara budewa juyawa taqara yi ta kalli gefen ta taqara juyowa ta kalli ɗayan gefen da aka daddaure mata hannu wani hawayen ne yaqara zubo mata, kallon sa taqarayi tana so tayi magana amma takasa, sukai wajen minti shabiyar ahaka batare da kowa yayi magana ba, "INA ƊANA? abun da yaji tace kenan da sauri ya juyo yana kallon ta da kayu tare da zaro kyawawan idonsa kana kallon sa zaka ga mamaki qarara a idon sa, matsawa yaqarayi daf da ita dan atunanin sa ko kunnuwasa ne suka jiye masa ba daidai ba,    "Ganin baiyi maga magana ba yasa tace ka kunce ni mainayi muku dan Allah, saura qiris numfashin sa ya dauke jin abun da baitaba tunani ba baitaba tunanin wannan ranar ba wai matar nace take magana haka cike da nutsuwa kamar ba itaba, kasa ko motsawa yayi saida taqara yimasa magana sannan yadawo hayyacin sa kamar marar laka ajikin sa haka yakai hannun sa ya kunceta kamar yanda tafada saidai yakasa iya yi mata magana, "yana kunceta ta yunqura zata tashi amma taji ta kasa ganin hakan yasa shi taimaka ta tashi zaune zama tayi tare da dafe kanta da duka hannuwan ta biyu, da kyar ya iya budar bakinsa yace mata sannu, dagowa tayi ta kallesa batare da ta amsaba, "bayan ta janye idon ta akansa ta shiga bin dakin da kallo sai kuma taqara juyowa ta kallesa,"inane nan kuma ina dana ina mijina da 'yan uwana  me nakeyi anan gurin kuma kai wane? shide shiru yayi yanajin yanda take jero masa tambayoyi batare da ta jira ya bata amsaba,, "yanda take kallon sa tana jiran amsa daga garesa shima haka yake kallon ta yana tunanin amsar da zai bata dan baisan amsa ko ɗaya ba daga tambayoyin ta wata dabara ce ta fado masa sai kawai yace mata duk suna gida ke kuma baki da lafiya kin sumane shiyasa bakisan lokacin da aka kawo ki ba,   "Amma kuma naga andaddaure ni me yasa aka daure ni ta tambayesa tana qara kallon sa, ki kwantar da hankalin ki yanzu zankaiki gida idan munje zakiji komai ammade yanzu babu inda yake miki ciwo kina jin kwarin jikin ki kai ta daga masa kawai sannan tafara qoqarin zuro qafafunta daga kan gadon datake, daram ta ajiye su aqasa tare da daidaita tsayuwar ta ta juyo ta dan kallesa sannan tace muje ka kaini gurin su inson ganin ƊANA,   "shide anasa bangaren baisan wane irin tunanin zaiyiba koma sa ya tsaya yakasa gane shin farin ciki  zaiyi ganin ta dawo hayyacin ta  ko kuma damuwa zai shiga ganin irin tambayar da take masa da baisan ta yanda zai fara yi mata bayani ba gashi kuma yayi mata qarya yace tazo yakaita gurin su idan yake kuma taga bahaka ba to wani irin tashin hankalin zata iya shiga gashi baya son yagaya mata anan aganin sa gwara ummynsa tayi mata bayani bisa ga dukkan alamu ada duk bata cikin hayyacin ta batasan me takeba sai yanzu hankalin yadawo jikin ta tunda gashi har tana tambayar 'yan gidan su akaita wajen su,  "tabashin datayi ne yasashi dawowa daga duniyar tunanin da ya lula, hannun sa ta kama tace muje mana inafa son ganin babyna nasan yanzu yana can yana ta kuka,    Allah sarki cike da tausayin ta yake kallon ta  abun nata abun tausayi ita kanta bata san adadin shekarun da tayi a kwance ba har take tambayar danta da baby watakil yanzu in yana da rai ma yazama qato dashi gudun karta qara yi masa magana yasa shi kallon ta sannan yace to shikenan muje amma ki kwantar da hankalin ki danki yana nan cikin koshin lafiya ba abun da yasameshi yanzu hakama yana can yana wasan sa, acewarta sai tace a'a baya wasa da kowa nasan yan can yana kuka wai nama kwana anan gurin tun yaushe aka kawoin nandin meyasa ma baku barsa anan ba nifa bana son arabani da dana koda yaushe so nake makasan ce tare tafada cikin murya me sanyi, be qara yi mata magana yakama hannun ta saidai kuma sai yanzu taji qafarta tana dan yi mata nauyi kamar bazata iya takawa ba jin tana tafiya da kyar yasa shi dafata yace kibi ahankali jikin ki ba kwari sai ahankali zaki dawo daidai kai ta daga masa sannan itama ta dafashi tare da riqeshi yanda zataji dadin tafiya, ahaka suka ringa takawa ahankali har suka zo bakin qofar fita sai wata mace ta kawo kai zata shiga ciki sukayi karo ahanya tsayawa tayi saurin yi tare da dan basu hanya sannan tace good morning sir bai kulata bare ya amsa mata gaisuwar tata gaba yayi ta bisa da kallon irin wannan wullakancin nasa tanama so tace wa me jiki ya jikinnata amma ba fuska dole ta hakura ta koma inda ta fito, Ahankali suka cigaba da tafiya da kyar har sukakai wajen qofar sai ya zaunar da ita yace bari yakawo motar nan sai ta shiga, bamusu tayi zamanta agun da yazaunar da ita dan daman ta gaji da tafiyar yana zuwa wajen motar driver yana gurin daman baibar wajen ba yana jiran fito warsa yana qarasowa da sauri ya bude masa qofa atunanin sa ko shiga zaiyi amma sai kawai yace masa key baigane me yake nufina sai yadan duburbuce alamun yana jiran qarin bayani amma yakasa tambaya, ganin yatsaya bata masa lokaci da kansa yaja murfin motar gaba ya bude sannan ya shiga saida ya shiga ma yaga mukullin ajiki harya tayar saidai yajuyo yakalesa sannan yace rufe,    shidai kamar wani soko haka ya tsaya yana kallon sa da mamaki to me yake nufi da shiga motar nufinsa da kansa zaiyi tuqin kenan ko mai, lokacin da shi yake wannan tunanin shi kuma har yaja motar yabar wajen gaban inda ya ajiye ta yazo yayi parking din motar sannan yafito ya taimaka mata ta shiga sannan yazagaya yaqara shiga motar duk wani wanda idon sa yagane masa merr acikin mota amazaunin driver ba wanda baiyi mamaki dandanan kuma wadanda suka gansu tare aka fara yaɗawa marar lafiyar meer ta tashi kowa yana mamakin hakan da akwai waɗan da ma lokacin da suke tafiya sun labe agefe suna kallon su, suna mamakin warkewar tata lokaci guda kowa yanason yaji yayansa ta samu lafiya amma babu mai basu rahoto wanda kuma suka san yasan tayanda tasamu lafiya babu wanda ya isa ya tunkare sa da maganar dole kowa yaja bakin sa yayi qum yabar maganar sa aciki,   "Musa driver ne ya qaraso wajen da sauri harda gudu gudun sa yazo gaban motar inda yake shirin tayar da motar jiki na karkarwa ya budi baki da ƙyar cikin in ina tare da miqa hannu yace dan Allah kayi hakuri ka kawo in tuqaqu agafarceni innayi wani abun ba daidai ba danshi duk atunanin sa ko ankore sane yasa shi shiga tashin hankali, dakatawa yayi da niyar tafiyar da yakeyi ya kalle sa yace kayi min wani abunne? "yace a'a naga ai baka taba tuqi da kanka bane shiyasa nayi tunanin ko nayi kafin da yasa ka koreni zakai tuƙin ka da kanka yaqarasa fada yana sunkuyar da kai,   babu abun da kayimin kawai ni naga damar yi kasameni agida kawai, wani sanyi yaji aransa jin babu abun da yayi da sauri ya amsa tare da juyawa har yadanyi gaba sai kuma yaji yakira sa da sauri yaqara juyowa tare da dawowa inda suke yace gani,   "saura ka gayawa ummy kaga yanda zanyi da fatar jikin ka kuma kayi sauri karka bari in rigaka zuwa yana kaiwa nan yaja motar yabar gurin batare da yajira amsar sa,    "Musa bin motar yayi da kallo sannan ya juya yacigaba da tafiya a fili yake cewa ni da wa yakaini jawa kaina ai ko baka faɗa ba bazan taɓa faɗa ba koda ta tambaye ni shikaɗai yana tafiya yana zancen sa tunawa da gargaɗi da akayi masa yasashi ɗaga ƙafa yafara sauri yana addu'a Allah yasa yasamu abun hawa da wuri, Allah yasoshi yana fita yasamu me napep yahau yagaya masa inda zashi tundaga dan nesa ya hango motarsu saboda ba gudu suke ba shiyasa, Me napep din yacewa dan Allah yadan qara gudu yanason sukamo waccen motar yanuna masa ita da hannu nan kwa me napep yaqarawa adaidai tarsa mai yafara gudu har suka kamosa sannan ya rage gudun suka cigaba da bin bayansu shaka har suka isa gidan yayi horn me gadi ya bude masu suka shiga shima Musa fitowa yayi yabisu kafin ma yagama daidaita parking Musa har yaqarasa yayi bude masa qofa idan kagani sai ka rantse tare suka dawo fitowa yayi Musa na shirin budewa matar dake dayan gefen meer yayi saurin dakatar da shi yace yaje kawai da kansa ya bude mata qofar sannan yakamota yafito da ita yanda sukayi dasu haka sukayi yanzuma har suka qarasa bakin qofar su me tafiya da imanina dan bazan taɓa deba gajiya da kallon ta, yanda tayi rannan haka yanzuma tayi ta rabe a hudu sannan suka shiga ciki suna shiga sukayi karo da ummy tana shirin fitowa mutuwar tsaye tayi ganin matar da bata taba tunanin ba ko da a mafarki cak ta tsaya takasa motsawa tare da sakin baki tana kallon ikon Allah, "ummy meer yakira sunan ta ahankali kallon sa tayi tama kasa magana qarasawa yayi kan kujera ya zaunar da ita, ummy ce ta qaraso gun sai yanzu tasamu bakin magana hayatee me nake gani haka kode mafarki nake, ummy ba mafarki kike ba gaskiya ne yaude Allah ya amshi addu'ar mu ummy taji sauki ta dawo hayyacin ta cike da farin ciki har rungume ta yayi sai yanzu murnar tasa ta bayyana nan ya kwashe duk yanda yaje yasameta da maganar da tayi masa komai dai ba abun da yarage mata tundaga A har Z sakin shi tayi itama cike da murna haƙoran ta sun kasa rufuwa ta koma kusa da ita itama ta rungumeta tana tafam bita da idanu kamar zata maida ita cikin ta hannuwanta ta ruqo cikin nata, "itade tana zaune kamar gunki sai faman binsu da kallo take takasa gane inda maganar su ta dosa ita da tace akaita gurin babyn ta amma kuma yazo ya kawota nan da batasansu ba, maida kallon ta tayi ga meer tayi shima da yadawo gefen ta yazauna wani irin dadi na ratsasa yau ya tsinci kansa cikin farin cikin da baitaba jinsaba tunda yake arayuwar sa baitaba jin farin ciki irin na ranar yau ,Yau ranace ta musamman awajensa yau ranace da bazai taba mantawa da itaba, "Wai inane nan ka kawoni kace zaka kaini gurin babyna amma kuma kazo ka ajiye ni anan ku suwa ye me yasa ka kawoni nan dan Allah kukaini gurin su ina son ganin su, " sosai ummy ta ƙara ruƙo hannuta duk da bata san sunanta ba amma sai kawai takirata da maama sunan da suka rada mata kenan tun kan farkon zuwan ta meer yasaka mata, cike da nutsuwa ummy tace maama ki kwantar da hankalinki yanzu kina buƙatar hutu kibari yanzu muje kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta idan kin tashi sai muyi maganar kinji, bude baki tayi zatayi magana meer yayi saurin dakatar da ita yace dan Allah kar kice komai maama kibari sai anjiman kinga yanzu safiyace kibari zuwa dare sai muyi maganar, kai ta girgiza musu tace bazanyi komaiba indai baku kaini wajen suba ni bansankuba bazan zauna dakuba kumayar dani gida kawai, duk yanda sukaso su shawo kanta ta amince da hakan amma taki yarda da ƙyarde tace musu tayarda zatayi wankan amma bazata yi bacci ba tana gamawa zasu gaya mata inda danginta suke da haka suka amince mata ta yarda, tashi sukayi gaba dayan su ummy tacewa meer yatafi yaje ya huta zata kaita daki idan ta shirya zata kirasa, ahaka suka rabu shi yatafi part dinshi ita kuma saboda yanayin jikin ta ummy da kanta takaita dakin dake qasa saboda tasan bazata iya hawa sama ba shiyasa takaita wani dakin bayan ta shiga taje ta haɗa mata ruwan wanka sannan ta dawo da taimakon ta takaita banɗakin sannan ta bata waje fita tayi daga ɗakain taje ta dubo mata kayan da tasan zasu yi mata saboda yanayin jikin su daya kawaidai ummy ta ɗan fita ƙiba da kuma mulmulewa saboda hutu amma kuma kana ganin maama kasan ta girme mata nesa ba kusa ba dan a haifema ta haifeta shiyasa jikin su ya bambamta ga kuma halin da ta tsinci kanta duk ta rame tsufanta ya bayyana sosai, Atamfa ta dauko mata riga da zani wadanda de tasan zata iya sakawa batare da sun ta kura mata ba dawowar ta dakin yayi daidai da fitowar ta daga bathroom din bakin gadon dakin tasamu waje ta zauna ƙarasowa ummy tayi gabanta tabata tace maama gashi kisaka bari inje inkawo miki abinci bata jira amsartaba ta tashi taƙara fita daga dakin ba jimawa taƙara dawowa da try ahannu ta yanda tafita tabarta haka tadawo ta sameta zaune agun ta zabga tagumi tana kallon gu ɗaya, dasauri ummy ta qarasa gaban ta tare da ajiye try din tace subhanallah maama me nake gani haka ya baki saka kayan ba kallon ta tayi bata ce komai ba ta dauki rigar kawai tasaka sannan ta tashi ta daura zanen sannan ta koma ta zauna, shayi ta haɗa mata me kauri ta miƙa mata ta karba ahankali tafara kaiwa baki tana sha saida tasha rabi sannan ta miƙa mata tace ya isheta haka, kiɗan ƙara cewar ummy, "Maama tace mata a'a ya isa haka nagode, bata takirata ba ta karɓa ta ajiye sannan ta zuba mata soyayyen dankallin turawa da ƙwai bayan tagama haɗa mata ta miƙa mata amma sai tace ta ƙoshi inma zataci sai anjima yanzu shayin da tasha ya isheta da Allah da Annabi ta hadata akan ta daure tace amma taƙi bayanda ta iya da ita dole ta rabu da ita saboda ba Safar tabace bekamata ta ringa jayayya da itaba, hade kwani kan tayi ta fita dasu sannan ta dawo ta zauna kusa da ita tace maama yanzu babu abun da yake miki ciwo babu abun da kike buƙata, buƙatata bata wuce sanin inda dana da 'yan uwana suke da kuma abun da yakwoni wajen, dan numfasawa ummy tayi tare da gyara zamanta tace bayan wannan buƙatar ba kya buƙatar komai? "eh" tace mata........... [5/29, 9:40 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿41&42 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️    "Ɗan numfasawa ummy tayi tare da gyara zamanta tace bayan wannan buƙatar ba kya buƙatar komai?    "eh" tace mata.... "tom shikenan maama yanzu zakisani amma bari nayiwa zauji magana yanzu yatashi daga bacci yana shirya wa ne yana gamawa sai mu zauna mu tattauna tafada tana miƙewa tsaye, idan ya shirya zanzo inkiraki ki jirani dan Allah, afito lafiya cewar maama, fita tayi tabarta adakin, dakinta ta koma tasamu mijin nata har yagama shiryawa yana zaune a falon sama yana breakfast ƙarasawa tayi gurinsa tare da join dinsa suka cigaba dayin breakfast tare tunda suka fara ba wanda yayi magana har saida suka gama wannan tsarin sune ahaka idan suna cin abinci basayin magana indai ba wai maganar takama dole ba to basayi harsai sun gama, "miƙewa tayi tana goge bakin ta da tissue sannan ta dubi minjin nata tace  masa muje ko tanacen tana jiran mu fa, shima miƙewa yayi yana gyara zaman galas din dake manne akan fuskarsa            cikin yaren su na larabci yake cewa nifa wlh har yanzu nakasa yarda da abun da kike fada dan wallahi abun yaban mamaki sosai ace mata tayi tsawon shekaru a kwance amma ace yau rana daya ta mike harma tana magana gaskiya wannan abun mamaki ne dan ya matuƙar daure min kai,    "kamo hannunsa tayi tare da daga kai tana kallon sa tace haba abu meer dan Allah kade ana maganar  wannan kwa ba wani abun mamaki bane babu yanda Allah ba yaso yayi yanda yaso shi ya dora mata kuma shi yaye mata lokaci guda dan haka ni banga abun mamaki ba daman kullum addu'ar mu kenan Allah ya tashi kafaɗunta kuma Allah ya amshi addu'ar mu kaga sai mu ajiye batun mamaki munan farin cikin mu da godiyar mu ga ubangiji Allah ya ƙara mata lafiya kuma yabamu ikon gano inda danginta suke domin muqarasa ladanmu da mukayi niyya Allah ya cika mana burinmu akanta musauke nayin da muka daukarwa kanmu, dan shafa fuskar ta yayi yana dan murmushi yace to shikenan na dena mata tagari Allah yayi miki albarka shiyasa nake sonki saboda sanin yakamatanki da kike dashi Allah yabaku lada keda babana du kuka tsaya ganin tasamu lafiya gashi kuma yau Allah yayi tashin nata Allah yataimakeku yabaku ikon cika aikin da kuka dauka, "itama cike da jin dadin maganar mijin nata tana ta faman smiling tace Ameen ai hardakai, "yace a'a ni mainayi akanta ai kune duk kuke dawainiya da ita saida Allah yabiyaku Ni ba abun da natsinana mata tunda tazo kune komai nata amma yanzu nima zan shiga ciki domin asamin ladan naku yafaɗa yana ƙara sakin wani murmushin rungume shi tayi kadan sannan ta sakeshi tace muje dan Allah nasanka zancen ka baya ƙarewa yanzu sai mufi awanni amma batare da ka gama ba to meye aciki dan nayi zancen da yar aljanna idan banyi dakeba dawa kikeson inyi,. bana gajiya wane dake shiyasa kikaga idan munatare inata riƙeaki da zancen, to naji tace tare da kamo hannun sa suka fito atare kamar wani ƙaramin yaro saida ta zaunar dashi akan royal chair din sannan ta juya ta tafi dakin da ta bar maama, yanzuma de kamar dazu haka tadawo ta same guri guda idan batayi ƙarya bama da saitace ko motsawa batayi ba, jin anshigo yasa maama dagowa ta dubeta, fuskar ta cike da murmushin farin ciki taƙaraso gabanta tana cewa afuwan nadade ko nsbarki kina ta jira, ba komai wlh cewar maama,. yafito zamu iya fita, tana rufe baki, maama ta miƙe tace yauwa to nuje ko dan jinta take kamar akan ƙaya take zaune ta matsu su mayar da ita gida, yanzuma saida ta kama riqeta sannan suka fita daga dakin,. suma ƙarasawa sukayi tare da zaunar da ita  kan kujerar da take facing din ta  Abu, Suna fitowa saiga meer shima ya fito tare da qaraswa kan kujera shima yasamu waje yazauna tunda yafito idonsa akanta har yakai ga zama bai janye ba saida bisani yajanye idon sa daga kanta tare da mayar dasu kan Abu sannan yace sabahul khairi ya Abu, ɗagowa Abu yayi yana duban nadan nasa sannan yace yau kuma ahaka za agaidani to ban amsaba yaƙarasa fadi yana sakin wani murmushin. kai kasamu gaisuwar ma ni yau ko irinta bansamu ba cewar ummy tunda suka fara maganar ba wanda ya tankawa hasalima daga ƙarshe mayar da kansa yayi jikin kujera ya kwantar harda rufe idon sama, tunda ta zauna bata dago ta kalli kowa daga cikin su  duk datasan su kallonta suke, ummy ce tafara magana "to Alahamdulillah sai mufara dayiwa annabi salati kamar yanda ya kamata (yana da kyau idan za ayi zama anaso afara bude taro da addu'a koda mutum biyune kufara dayiwa annabi salati sannan kuyi addu'a kafin kufara abun da ya haɗa ku) suma hakan sukayi bayan sungama salatin Ummy ta ɗora musu da addu'a, Sannan ta dubi abu tace to Abu meer ko kai zakayi mata bayani? a'a kawai kiyi mata wannan ai aikin kine kiyafi cancanta dakiyi shi, dan hararar wasa tayi masa taƙasan ido batare da kowa ya lura da su ba, be kulata ba sai kawai murmushi da ya mayar mata dashi, kawar da kanta tayi gefe sannan tace tom maama takira sunan ta sai lokacin maama ta dago ta dubi inda suke idonta tafara saukewa akan ummy sannan ta mayar dashi kan abu da ya sunkuyar da kansa yana ƙokarin ɗaukar glass dinsa da tun shigowar sa falon ya cire yanzu kuma yaji yana bukatar sa shiyasa bata samu damar kallon fuskar saba, ina saurarinki cewar maama, tare da mayar da kanta ƙasa, cikin nutsuwa maama tafara yimata bayanin yanda suka hadu da ita tun lokacin da aka kawota daga wani asibitin zuwa nasu da adadin shekarun da ta dauka akwance awajen su kafin gurin suma kuma tayi shekaru da yawa awancen asibitin dan a ƙalla de a ƙiyasi zatakai wajen shekara ashirin da wani abun tana kwance babu hankali ajikin ta basu rage mata komai ba saida suka bata labari har zuwa yau data farfaɗo,    wannan labarin ba ƙaramin girgizata yayi ba jin adadun shekarun data dauka kuma batare da wani ɗaya daga yan uwanta tane taba to me yafaru da ita, itade abun datake iya tunawa shine danta da kuma mijin ta sai kuma iyayen ta amma fa sudin ma bazatace gasuba kawaidai aranta tasan dasu, Ummy ce ta katse mata tunanin ta dacewa amma yanzu Alahamdulillah maama tunda har kindawo cikin hayyacinki munason kigaya mana ko ke wacece kuma awane gari kike kinga sai mu hadu gaba dayan mu muje, ɗagowa maama tayi tana dubasu da kyau sannan tace maganar gaskiya bansan daga inda nake ba abunde da zan iya  tunawa shine nasande ina da da kuma ina da miji amma ko kammanin su bazan iya tunawa ba bare kuma garin da nake, Amma kubani lokaci ko Allah zaisa intuna koda garin da nake ne amma daga wane gari aka kawo ni nan kugayamin ko zan iya tunawa taƙarasa maganar muryarta cike da rauni ga hawayen da ya ke zubowa daga idonta ita kanta batasan da zubarsuba wani iri take jin jikinta kamar tana son tuna wani abun amma takasa ga wani irin ciwon kai da taji yana shirin rufeta hannu kawai tasa ta dafe danji take kamar zai tsage gida biyu kuma dazu batajin sa yanzu kawai tafara jinsa lokaci daya, Abu ne dubi meer yace kasan daga inda aka kawota tunda kai aka kawowa ita, kai ya girgiza masa sannan yace amma de inada Number dinsa bari in kirasa daukar wayarsa yayi yashiga laluben number wancen mutumin da suka kawota cikin sa'a kwa yasameta danna masa kira yayi tare da sanya wayar a speaker yanda kowa zaiji cikin rashin sa'a kam yana kira akace layin akashe yake ƙara kirayayi nanma still akashe sai da ya gwada wajen sau biyar amma duk taƙi shiga dole ya haƙura yadena kira,ummy tace zuwa anjima ya gwada ko Allah zaisa ta shiga,.. Abu ne ya kalli maama yace maama yanzu ko sunanki bazaki iya tunawa ba kinga da sai muje gidan Radio da kuma  gidan tv da jaridu sai a watsa cigiyar ki ako ina ko Allah zaisa adace, ɗagowa tayi taba kallon suna hada ido taji kanta yaƙara sara mata da ƙarfi da harsaida takaita da sakin ƙara tare da cewa kaina kaina wyyo kaina tafaɗa ta na sake riƙe kan da hannuwan ta sosai take jinsa kamar zai rabe gida biyu, da sauri duk sukayi kanta suna mata sannu amma ba wanda ta iya saurara ciwon saima ƙara gaba yake, nanfa hankalinsu yaƙara tashi suna ta tunani abun yi ummy ce ta zauna kusa da ita tare da tayata riƙe kan ganin de abun is not easy yasa ummy cewa muje asibiti kawai meer kamota muje Abu ne yayi saurin dakatar dasu yace a'a wannan inma kunje asibiti ba abun da zaku iyayi mata saboda baku da maganin da zaku bata ko kun bata bazai taba yimata aiki bashi take buƙata ba a halin yanzu, yaƙarasa maganar tare da zaro wayar sa yace bari akira malami kawai shikaɗai ne solution a halin yanzu, Meer yace amma Abu.... Ummy ta daga masa hannun tare da cewa karkace komai hakan shi yakammata nikaina mantawa nayi da batun malamin da haryasa nace muje asibiti amma yanzu nagane hakan bata buƙatar wani drugs addu'a kadai take buƙata, shiru yayi be ƙara magana ba tunda sunrunjaye sa dole yabisu a yanda sukeso , cikin sa'a kuwa bugu daya malamin da abu yake kira dagawa akayi tare da cewa "Assalamu alaikum warah matullah amsawa abu yayi sannan suka shiga gaisawa kafin daga baya yayi masa bayanin abun dake faruwa , ba bata lokaci kuwa malamin yace gashinan zuwa abashi minti talatin zai iso daha sukayi sallama ya ajiye wayar,. yamaida kallonsa garesu sannan yasanar dasu yanda sukayi da cewa gashinan zuwa, Sosai sukaji dadin hakan cigaba sukayi da yi mata sannu,. ummy dake riƙe da ita duk addu'ar datazo bakinta yitake tana tofa mata, gaba dayan suma haɗuwa sukayi suna  yimata amma fa shiru kakeji itade bawani sauyi datake ji dan jitake ma kamar wani zafin suke ƙara mata, ahaka suna tsaye akanta cikin rashin hankali da damuwa da kowanne su ya tsinci kansa, ita kuma tanata faman damke kannata ga wasu zafafan hawaye masu dumi da suke zubo mata duk wanda yaga baiwar Allahn nan sai ya tausaya mata, Suna cikin haka wayar abu tafa ringing da sauri yayi picking din call din yana dagawa yace kazo ne?  ok kashigo kawai yana ajiye wayar yabar wajen ya nufi hanyar waje dan shigowa dashi, yana fita badadewa suka dawo tare ƙarasowa sukayi inda take kallo daya malamin yayi mata ya kawar dakai tare da dan girgiza kai sannan yacewa su Ummy su saketa dakinta tayi tare da tashi daga kan kujerar tabashi waje, wata roba yadauko ajakar da yazo da ita farin ruwane acikin ta budewa yayi sannan ya miƙamata yace ta sha ɗagowa tayi ta kallesa da jajayen idonta da suka canza launi abun tsoro kamar banata ba haka ta zuba masa su shima ita yake kallo ko ƙiftawa bayayi kasa jure wa tayi sai kawai ta kawar da nata idon daga gare sa ƙara miƙa mata yayi yace tasha, ƙin karba tayi tama fara ƙoƙarin tashi zata bar wajen, da hannu ya mayar da ita takoma ta zauna ruwan ya ɗiba a hannun sa ya watsa mata shi a fuska wani irin dogon numfashi taja tare da saukewa duk alokaci guda ƙara ɗiba yayi zai watsa mata tayi saurin cewa karka kuma watsamin Wannan abun, ba saurare taba ya kuma watsamata abun da tayi dazu shi ta kuma yi yanzu saida sukayi haka sau uku sannan ya rabu da ita Qur'ani yadauko ya budo surataul baƙara tunkan yafara yaji " tace kar ka konamu zamu fita yace karma kufita gwara ikonaku din meyasa baku da tausayi ku bakuga tsohuwa bace me tayi muku kuka sakata agaba kuka hanata tuna dangin ta bayan kunrabata dasu nan sukace muma ba yin kanmu bane turo mu akayi waye ya turo ku ya tambaye bazamu fada ba to idan na konaku ai zaku fada yana fara karanta aya daya sukace karabu damu zamu fita kishiyar tace tajamata halin da take ciki saboda ba ason zamanta acikin gidan ku kuma mugaye shine kuka hanata ko to nima bazan barta kuba nan yafara yi mata ruqiya tun anajin ihunsu har akadena ji bai rabu dasuba harsaida ya tabbatar yarabata dasu gaba ɗaya sannan yaƙara shafa mata ruwan afuska atake agurin ta sume gyara mata kwanciya yasa akayi sannan yabasu wani turare yace suyi mata kafin ta tashi daga baccin su yiwa duka gidan ma, godiya sukayi masa sannan Abu yace malam daman aljanune wajen fa shekara ashirin da wani abun tana kwance,. dan murmushi malamin yayi yace wannan ai ba aikin asibiti bane bayan aljanu ma akwai sihiri ajikin ta sannan aka hadata da aljannu ta yanda koda sihirin yakarye su kuma bazasu bari ta tuna komai ba abun da yafaru da ita kenan watakil asamu matsala daga gurin su shiyasa sihirin yakarye dalilin da yasa ta tuna wani abun kenan amma daga na bazata ƙara tuna komai ba amma yanzu komai ya warware suma kuma sun fita tana farkarwa zata dawo daidai koma ta zai dawo zata tuna da komai, gaba dayansu babu wanda baiyi mamaki ba dan tunda suke basutaba ganin irin haka ba saidai ko alabari ko a Film amma yau gashi anyi agabansu ,sosai suka nuna jin dadinsu sannan suka yiwa malam godiya sosai tare da yimasa alheri me tsoka dan acikin su babu wanda baiyi masa kyauta ba kuma kyauta ba yar ƙarma ba me tsoka dan aƙalla iya kudima sunkai 1.5m suka hada masa ajaka banda turaruka har da kaya shaddodi sababi waken guda goma sha haka Abu yabasa, kowade bayan kudin da yabashi saida suka ƙara masa da abubuwa duk suka hada masa dan su aganin suma basu biyashi komai ba akan abun da yayi musu shekara nawa suna wahala da kashe kudi amma basu bata lafiya ba sai gashi shi akwana ɗaya kuma alokaci ɗaya har ya magance matsalar dole subashi abun da yafi hakama, bakin sa harkunne sai faman washe shi yake kana ganinsa kansan ba ƙaramin farin ciki ya tsinci kansa ba malam yayi musu godiya sosai tare da yi musu addu'a sannan sukayi sallama yatafi da kyautar sa da tunda yake aiki baitaba samun irin taba cike da farin ciki yabar gidan, "bayan fitarsa meer yakasa zaune yakasa tsaye sai faman zagaye falon yake yana alajabin wannan al'amarin kamar amafarki wai duk tsawon shekarun nan da ya dauka daman akwai ta yanda za ayi taji sauƙi lokaci daya sai yaji duk haushin kansa da tun farko beye wannan tunanin ba gashi kuma dasu Ummu sukayi masa maganar nan ma yaƙiyarda da su da ya yarda tun alokacin da tuni ta dade da samun lafiya gani yake kamar duk shi yaja mata wannan dadewar datayi a kwance sosai yake jin haushin kansa kuma yake ganin baiyi mata adalciba, amma fa duk dahaka kuma yagani yaji da kunnen sa amma wani barin na zuciyarsa baigama yarda ba cewar ta tashi wannan dan abun da yayi mata ace wai shine silar samun lafiyarta yade yarda da aljanu kuma yasan anayin ruƙiyya amma me yasa zaice wai anyi mata sihiri kuma yakunce da kansa ajiye tunanin yayi agefe sannan yajuyo ya matsu kusa da ummy yakalle ta sannan yace Ummy wai da gaske yanzu idan ta tashi zata tuna komai kodai fadarsa nifa haryanzu I can't believe this thing, I think it's a lie yaƙarasa maganar fuskarsa cike da gasgata abun dake ransa, Abu ne ya tari numfashin sa yace I don't think so because magic is not a lie kanade gani yanzu yayi magana dasu kuma kaji da kunnen ka amma meyasa kake son saka kanka tunanin da bashi da amfani idan ma baka yarda ba yanzu idan ta tashi ai zaka yarda, Bansan yaushe zaka canza kadena wannan halin ba kanaganin gaskiya kuma kaima kasan hakane amma sai ka ringa takewa kana tambayar mutane tamkar bakason komai ba me yasa kake hakane, Abu yaƙarasa maganar alamunde baiji dadin abun da meer yace ba saboda daman yasaba haka wannan halinsane, tunda abu yafara bayanin sa bai daga kai ya kallesaba daga ƙarshema da yaji ya tsaya da maganar tasa sai kawai yatashi yabar falon tare da nufar part dinsa ransa yana mishi suya besan meyasa ba Abu yake son yayi masa fada koda yaushe ba shiyasa yafi son mahaifiyar sa bata masa fada duk abun da yakeson shi take masa bata son ɓacin ransa ko kadan al'adun Abu shikuma da yake ganin kamar ya takurawa rayuwar sa idan yana yi masa irin wannan abubuwan da bayajin dadin su , ganin yatafi yabarsa awajen yasa Abu jin ba dadi shima yana ganin shi yanzu bai isa ya nunawa yaron nan yayi ba daidai ba sai yakama nuna fushinsa saikace bashi ya haifesa ba a rana yace duk laifin Ummy ne da take biye masa yayi duk abun da yaga dama yanaso ya ɗorasa akan irin tarbiyyar nan amma shi kwata kwata zama da mahaifiyar sa da kuma zaman da sukayi a Yemen yasa shi dauko rayuwarsa tacen shiyasa watarana yake jin zafin abun aransa amma koda wasa baitaba nunawa mahaifiyar tasa haka ba duk wani abu da tanuna tanaso ayi yake biye mata saboda komai zatayi masa bazai taba mance halaccin da tayi masaba saboda ta zabeshi akan mahaifinta saboda son da take masa gashi ta zauna dashi a inda bata saba zamaba bata da kowa batasan kowa ba ta baro family dinta ta biyo sa dan haka shima dole ya jure duk wani abu da zataimishi domin rama halaccin datayi masa, jin antabashi yasashi dawowa hayyacin sa tare da sauri. kawar da damuwarsa yabasar, zatayi magana ya hanatayi ta hanyar cewa kinga kar ta tashi Yakamata kiyimata turaren kafin ta farka kamar yanda yace tafaɗa yana komawa kan kujera ya zauna, binsa tayi da kallo tasan da abun da yake tunani amma sai tabar zancen itama kawai, Sannan ta kira wata me aikin ta aikin ta ta haɗo mata gawayi takawo mata yanda malam yace musu haka sukayi mata turaren tare da yiwa gidan.........✍️✍️✍️✍️ [5/30, 10:26 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki) *littafin sarki sameer yana daya daga cikin sabon team da muka bude na marubuta biyar 5 me suna THE TALENT TROUPE WRITER'S masu tafe da nasu sabon salon nadaban domin farin cikin ku, ga dadi da ƙayatarwa da nisadantarwa da fadakantarwa masu ɗauke da zallar soyayya da ƙaunar juna kar ku bari abaku labarin daya daga cikin wadannan littafan domin za ayi babu ku........* 💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA* 👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA* by(mrs bmb) *2,GIDAN AUNTY* by(mss lee) *3,SARKI SAMEER* by(xeemat....love) *4, JINI DAYA* by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA* by(mum Sayyid)                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿43&44 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ "Bayan sun idar da sallar sun dawo bossay da sam ne kadai suka shigo shettima ma kuma yatsaya yayo musu order din abinci sannan yadawo gaba dayansu suka zauna suka sukaci suka kora da ruwa, Sam ne yafara miqewa daga gurin, wajen dakinsa na ajiye ajiye yanufa tare da daga labulen ya bude qofar sannan ya shiga yana shiga sai kuma yafito, dan leqo da kansa yayi yana kallon su ganin suna nan yanda suke basu da niyar tashi duk sun dauki wayoyinsu ma suna daddan nawa, dan daga murya yayi yanda zasu fi jinsa yace zaman me kuke kuma? miqewa sukayi gaba dayansu tare da ajiye wayoyin nasu bossay nacewa ni ai banma ga tashinka ba kallon sa sam yayi "yace daman ai baza ka gani ba tunda hankalin ka nakan waya yana kaiwa nan ya wuce ciki, binsa sukayi abaya suma suka shiga cikin dakin , lokacin da suka shiga ciki har yakai ga zaunawa akan kujera tare da jawo laptop din kan table din zuwa gabansa tare da kunna ta, tunda suka shiga dakin suke faman baza ido acikin sa musamman bossay da baitaba shigowa ciki ba idon sune yasauka akan board din da yayi rubuce rubucen sa, da sauri bossay yaqarasa gurin ganin sunan shi ajikin board din qara zubawa board din ido yayi yafara karan ta sunayen dake jiki tabbas wadan nan sunayen da dadda tabasu labari bisa ga dukkan alamu yasaka sunayen wadanda za ayi bincike akansune wadanda ake zargi ne to amma meyasa yasa da sunan sa ajiki alhalin shide yasan ba mailaifi bane to kenan yana nufin shima yana zarginsa akan wannan case din jiki asanyaye ya juyo yana duban sam ganin hankalin sa ba akan sa yake ba yana kan laptop din dake gaban sa yasashi maida dubansa ga shettima hada ido sukayi da shettima,shettima naganin yana kallon sa kuma shima yaga abun da yagani tunkan bossay yabudi baki yayi masa magana sai kawai ya girgiza masa kai alamar shima baisan komai ba, shiru bossay yayi bai yi maganar ba ya koma kusa da sam ransa duk ba dadi dan wani iri yake ji game daganin sunan sa da yayi, ashe duk abun dasuke akan idon sam duk yana kule dasu amma sai ya basar ya nuna baima san sunayi ba, "dagowa yayi sannan ya maida dubansa ga shettima yace ina wayar? zarowa yayi a aljihunsa tare da miqa masa, karba yayi ya zura mata USB yayi connecting dinta sannan ya maida hankalin ga computer din yafara aikin sa yadau lokaci me tsawo kafin yadago fuskar sa da alamun da muwa, duk kallon sa sukayi shettima ne yasamu damar tambayar sa me yafaru amma banda bossay dan shide zuwa yanzu jikin sa ya mutu ya kunce masa duk wan kwarin gwiwa shiyasa baiyi gigin tambayar sa ba yaja bakin sa yayi shiru, "Sam yace akwai matsala fa nagano number da yayi wayar saidai abun mamakin andatse duk wata hanya da zaisa abi didigin number, shettima yace andatse fa kace yafada cike da daga murya dan abun ba qaramin mamaki yabashi ba' cike da tabbatar wa shima sameer ya jinjina masa kai, " to ya akai suka datse ta kode sungano mundauke shi ne shiyasa suka datse cewar bossay da mamaki yasashi yin maganar da baishirya ba yamanta da wani zacen ganin sunan shi' "haka nake tunani cewar sam yafada tare da miqewa daga inda yake zaune ya hau zagaya dakin yama rasa wane kalar tunanin szaiyi, Ammafa nayi mamaki tayanda suka gane har suka datse layin cewar shettima da shima abun yazo mishi wani iri, maida kallon sa gare su tare da gyara tsayiwar sa yana fuskan tarsu da kyau, sannan yace" yanzu dole mu koma gurin sa muci gaba da dukan sa idan yaji wuya zai iya gaya mana inda yake in bahaka ba kuwa zamusha wahala gurin gano inda yake, "hakan yayi amma kana ganin zai iya fada mana kagafa dukan da mukayi masa dazu amma bakinsa bai mutuba gaskiya gayen yana da taurin kai zai waya yafada mana shettima ke wannan maganar, Bossay yakarbe shi da cewa zai iya fada mana idan mukayi masa barazanar zamu kashe shi dole yaji tsoro yafada, Sam yace ko munyi masa barazanar za mu kasheshi bazai fada saboda ya riga yasan dole baza mu masheshi ba saboda ta hanyar sane kawai zamu iya gano wancen din kuma idonsa abude yake kuma yana da wayo dan haka bazai fada mana ba, dan dakatawa yayi da maganar tare da numfasawa sannan yace hanya daya zamu bi nasan tabbas zai fada, " har suna hada baki wajen cewa wace hanyar? shiru yayi baibasu amsaba saida yayi taku biyu zuwa gabansu sannan ya juya ya dauki wayar mutumin sannan ya dauki wani dan qarfe me tsini sai ya cire condem din wayar(rigar waya) sannan ya zura siririn abun awajen da ake saka sim, Yana shirin ciro sim din kenan saiga kira ya shigo wayar da sauri yafasa cire sim din tare da kallon wayar, Suma gaba dayansu sukayo kan wayar dan ganin me kiran,, suna tsaye suna kallon wayar harta katse batare da sun daga ba wani kirannne yasake shigowa wayar da private number, da sauri Sam ya daga wayar tare da sakata a hands-free tare da yin shiru daga can bangaren ma shiru akayi ba ayi magana ba, jin anyi shiru suma yasa sukayi shiru kowa na jiran wani yafara magana, sunkai wajen 30 second kafin daga can bangaren suka ji ance "kunyi kuskure wajen shiga abun da bai shafe kuba ina mai gargadin ku da ku hanzarta mayar dashi inda kuka dauko shi kunsan matsayin sa da girman aikin sa yanzu ina turawa cewa kun saceshine to kusani fa gaba dayan ku bamai kubuta sai anyi muku hukun cin sace shin da kukayi za ayi muku hukuncin 'yan kidnapping kuma kunsan hukun ci naku yanda zai kasance dan haka nake baku shawara da ku mayar dashi dan bazaku taba samun abun da kuke nemaba sannan shawarata ta biyu shine kuyi gaggawar zare hannun ku acikin wannan abun da bai shafeku ba hakan zaifi muku kwanciyar hankali daga ku har dangin ku kar kubari infara bincike akanku......dif ya kashe wayar batare da yajira cewar suba ya kashe wayar....✍️✍️ *Ayi hakuri da wannan yau nashiga busy dayawa* [5/31, 8:58 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(mrs bmb) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)                              *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿45&46 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️       shawarata ta biyu shine kuyi gaggawar zare hannun ku acikin wannan abun da bai shafeku ba hakan zaifi muku kwanciyar hankali daga ku har dangin ku kar kubari infara bincike akanku......dif ya kashe wayar batare da yajira cewar suba ya kashe wayar....... Gaba dayansu bin wayar sukai da kallo kamar masu son ganoshi ta cikin wayar haka suka tsaya suna kallon ta duk sun kasa motsawa daga inda suke bare kuma wani yayi magana ba wanda yake da wannan karfin halin sun dauki wasu minti na batare da kowa yace kowa wani abunba,     "da kyar sam ya iya cewa qaryane baka isa ba karya kake sai na nemoka koma waye kai aduk inda kake sai na kamoka, yaqarasa fadar maganar da daga murya hannun sa har rawa yake idon sa sun canza kala saboda tsabar bacin ran da ya tsinci kansa aciki magan ganun mutumin sai dawo masa sukeyi acikin kwanyar kansa wai shi akecewa shida family din sa zasu shiga cikin matsala yasan ko shi waye yasan suwaye family din su lalle mutumin nan yajawowa kansa bala'in da yafi qarfin sa dole yakomo shi ya koya masa hankali ko dan gidan uban waye sai yayi da nasanin sanin shi cike da taqaicin maganganun da mutumin yafada musu yadaga wayar ya bugata da qasa take agun ta tarwatse ta fashe, sai wani irin huci me zafi yake fitar wa tare da komawa kan kujerar yazauna yana dafe kansa, duk tsorata sukayi da yanayin da suka gansa musamman bossay da baitaba ganin shi a irin wannan yanayin ba, inda ya jefar da wayar shettima yaje tsugunnawa yayi agaban ta tare da saka hannu ya dauketa sannan ya miqe gurin sameer ya dawo sannan yadauki abun cire sim din dake gabansa yazirashi ya zaro gaba daya sima siman dake cikin wayar, dafa kafadar sam yayi tareda cewa colm down coll ur mind wannan abun ba wani abu bane da zaisa ka tada hankalin ka already mun riga mun dauko shi kuma bazamu mayar dashi ba idan kuma ya nemi yadaga mana hankali muma sai mu shigar dashi qara koda wannan hujjar da muka kamashi yana waya zamu iya yin amfani da ita wajen shigar da qarar amma hakan baze yiyu ba dole sai munbi komai ahankali idan munaso komai ya tafi daidai duk da gargadin da yayi mana nasan shima dole yana cen cikin tashin hankali kawai kwarewa ce tahanasa nuna hakan badan hakaba kasan da tuni yasa ankamamu tunda har yasan mundauke shi to dole yana da wani labarin akan mu dole sai mun sake shiri mu juyar masa da nasa tunani ta hakane kawai zamu iya cinma abun da muke nema har mu gano inda yake, janye hannun sa sam yayi daga dafan sa dayayi sannan ya miqe tare da juyowa yana fuskantar su da kyau sosai maganganun shettima sukayi tasiri a zuciyarsa sai yanemi duk wani bacin ran ma yarasa, saima wani irin kwarin gwaiwa da yaji yazo masa, maganar ka gaskiya ne yanzu tunda ancire sim din sannan wayar ta fashe dan haka jefar da ita zamuyi sannan yanzu mu koma gurin shi ayau sai yagaya mana inda yake, Shettima yace " kana ganin zai gaya maka batare da anyi masa baranar dangin saba yakamata muafara bincike akansa mugano wani wanda yafi kusa dashi wanda idan aka tabasa zaiji aransa da har zaisakashi yagaya mana gaskiya, kawai muyi binciken yau inyaso sai mukoma gurin nasa koda zuwa gobe ne ina ganin hakan sai yafimana sauqi amma bana tunanin hakan nan zai fada mana dole sai munbi ta shawarar da ka kawomana tun dazu, Shiru yayi bece masa komai ba sai kuma yace hakan zamuyi yafada cike da qarfin gwaiwa sannan ya koma kan kujerar yazauna tare da miqa hannu ya karbi sim din dake hannun shettima, a flash yasaka sim din ya zura ajikin system din sannan yafara aikin sa bai wani dauki lokaci me tsawo ba ya tashi tsaye tare da cewa yess yafada da qarfi yana kallon su cike da jin dadin abun da yace da kuma ganin yanayin sa da ya tabbatar musu da anyi nasara kenan, bani wayar ka yafada yana kallon bossay da sauri bossay ya miqa masa copying din wata number yayi aciki sannan yace ka ajiye mana wannan number kayi saving dinta bayan yabasa ya karbi ta shettima ma itama wata number yayi copy ya miqa masa yace shima yayi saving sannan ya qara dauko tashi wayar yayi copy,   number suwa kagano? shettima ya tambayeshhi ,   "naduba naga numbers din  da yafi yawan  waya da su  naga  ansaka my wife  itace nabawa bossay yafada yana nuna bossay, tabiyu kuma ta mahaifiyar sa ce ita nabaka,      "ni kuma ta daughter din sa nadauka  kuma ina kyautata zaton duk sune dan haka yanzu su zamubi didigi mugano inda suke da zama  amma zamu rabune saboda naga kamar  duk ba aguri daya suke zaune ba, bossay " yace amma aganina ai bama sai anbi diddigiba kawai kiran su zamuyi awaya? yafada yana kallon, harar sa shettima yayi yace idan ka kirasu din kana da abun da zakace musu da zaisa suyi maka kwatancen inda suke ne ae dole sai munbi mungano da kanmu, dan nufasawa yayi sannan yace zamu iya sani wallahi amma basu zamu fara nema ba iyarinyar zamu fara nema ko ba budurwa bace yafada yana kallon sameer, dage kafada sameer yayi alamun shima baisani ba, hakan kuma yayi maganar ka abun dubawa ce nasan ma dole budurwace amma de sai nake ganin tunda batare suke ba ai kamar bazamu iya snin inda sauran suke ba, bossay yace to ai ko ita muka kama shikenan zamu iya yimasa barazana da ita amma ya kuke gani,   "aa bazamu bi ta wannan hanyar ba kawaidai yanzu abar batun sauran yanzu muje tare har inda yarinyar take sai mubi location inyaso idan yaganta kuma yaqi saduda sai mukamo sauran, duk sunyu ns'am da shawarar tasa dan haka ba bata lokaci suka tattara inasu insau suka fita daga office parking sapace suka zo kamar yanda sukazo dazu yanzuma haka sukayi bossay ne zaija motar, bayan sungama shiga gabadayan su yaja motar da gudu me gadi ya bude musu gate din ya kwasheta aguje suka fita daga hospital din, wayar yadauko ya kunna location din number nan yafara nuna musu hanya tun yanacewa bossay ga inda zaiyi daga qarshe kuma sai kawai ya miqa masa wayar gabansa bayan sunzo unguwar da take(unguwar sharada) wani layi suka shiga sannan suka qara yin kwana adaidai wani gida suka tsaya inda abun ya nuna musu parking sukayj abakin gidan sannan bossay yace "to ya za ayi kiranra za ayi awayar ko kuma turawa za ayi akirata?   "shettima yace habade saidai akirata awayar kawai sai yafi,    kana da abun da zakace mata idan kakirata din har inama kana dashi to idan tafito baizama lalle tayarda damuba saboda batasan muba bata taba ganin muba kawai yanzu wani acikin ku  yafita yaje yasa me gadi yakirata, ko kai bossay kaje saika san yanda zakayi ka jawo hankalin ta har ta yarda tashiga mota,    mukuma fita zamuyi daga motar mujiraku abakin kwanar cen idan kun fito sai ka dauke mu mutafi, "a'a wallahi bani yakamata naje ba kai yafi kamata nasan dole intaganka zaka iyayi mata kwarjini kuma sai tafi yarda dakai bazata iyayi maka musu ba tana ganin ka handsome din nan ai da gudu zata amince dakai bai rufe baki ba shettima ma yace gaskiya ne wallahi kai zakaje bazata taba bijere maka ba kawai kaje ayi awuce gurin dan nasan kafin ma kace ta shiga zata shiga saboda qaramin  tafiya da imanin ta zakayi ba bare ma taji kana sanbado mata kalamai tuni zata mace maka yaqarasa maganar yana kunshe dariyar da take son kwace masa dan yasan baqaramin abu suka daukowa kansu da wuya sam ya amince shida bama ya magana da wata macen amma shine yau za ace yayi magana da wata kuma harda kalamai tirqashi abun da kamar wuya, wata uwar harara ya watsa musu gaba dayan su tare da nuna kansa da yatsan hannun sa cikin hade rai da bata fuska alamar ba wasa din nan yace"ni ni zanje wajen mace mai kuka daukeni ta ba inda zani ni sa'ankune danma kunga ina kulaku shine zaku wani ce inje wai harda cewa inyimata kalamai saidai uwar kalamai zanmata nibanda mace taimin laifi indauki mataki akanta me na iya kai ai kasan halina ba wani abu zan iyace mata ba dan haka kawai ku ajiye wannan maganar saboda ba abune me yiyuwa ba bazan taba zuwa ince inason maceba harkuma inyi mata kalamai kai nifa kama rainamin hankali yafada yana kaiwa shettima bugu akafada kalmar kalaman nan da yafada ba qaramin tsaya masa tayi araiba, Wallahi ka kiyayeni kana mun abubuwa da yawa ina rabuwa dakai ko to bazanje ba shidinma yafasa zuwa kai zakaje, gaba dayansu dariya suka saka mishi sanna shettima yace kasan Allah ba maganar wasa ba kai yakamata kaje indai bawai kanason ka bata mana shiri ba kagade layin nasu da mutane bare ace za ayi mata taqarfi tana fitowa mu dannata amota dole sai dai mushigo da ita tacikin sauqi inbahaka ba kuwa tofa aikin mu bazai tafi yanda muke so ba zamu iya samun matsala dan haka malam kawai kafita kaje, still de kin amince musu yayi saida suka sake wani cecekucen kafin daga baya da kyar da kyar suka shawo kansa tare da yimasa dabara sannan ya amin ce da yaga ba yanda zaiyi, murna sukayi sosai tare da yi masa godiya sannan suka fita daga motar gabadayan su key din motar bossay yabashi sannan sukace to yafara tafiya sugani sannan ya su sutafi tare da yimasa fatan samun nasara, ko kulasu baiyi ba saboda haushin su yaje ji yayi gaba abun sa taku baifi biyu yayi ba, shettima yakira sunan sa dan dakatawa yayi batare da ya juyo ba, shettima tace fatan nasara fa mukayi maka bazakace Ameen ba ko duk zumudi ne yau za afara zuwa zance wajen budurwa to adai yimata ahankali kar akasheta da kalamai sanna kuma kar ashanyamu muyi tajiranku, dannasan za ayi wucewa da soyayyar gaske amanta damu dan Allah muna roqode kar ayimana haka romio tuzuru dan nasan ba asaba ba kuma wall......... beqarasa ba sam yayo kansa afusace, kafin yaqaraso sukuma sukayi saurin barin wajen suna mishi dariya, kwafa yayi ya tsaya yana binsu da kallo jiyake kamar ya fasa zuwan ma da haryayi tunanin binsu sai kuma yafasa kawai yayi kwafa tare da juyawa ya nufi qofar gidan, yana qarasawa sai ya tsaya  abakin gate din, ya kai wajen 2 minutes agun yakasa kwankwasa gate din wani tunanin ne yaqara fado masa yanzu idan ya buga aka bude wa zaice yana nema sai yanzu ya tuna ashe duk tsare tsaren nasu sun manta basu san sunan taba sosai ya shiga tunanin abun da zaice, wata dabarace ta fado masa da sauri ya zaro wayar sa dake aljihu sai ya bude ta ya shiga WhatsApp dinsa number ta ya lalubo sannaan yayi mata sallama da niyarsa idan yayi mata magana sai ya goge number ta ta daga kan wayar sa inyaso sai yakoma WhatsApp ya duba sunan da take amfani dashi tanan kawai zai iya gano sunan ta idan tasaka, bayan yayi mata sai ya fita yake contact din ya goge number ta sannan ya kuma shiga WhatsApp din ga mamakin sa yana shiga dak kawai yaga anbude sallamar da yayi mata alamun tana ma online da sauri ya bude tare da duba sunan da take amfani dashi ba SUMY yaga ansaka ajiki hamdalah yayi tare da sauke ajiyar zuciya, sannan ya duba yaga har tayi masa reply da hello " sai kawai yace sumy yakk?   "ba jimawa ta amsa masa da lfy pls waye? bangane me magana ba? "bazaki gane ba daman amma fito waje ina qofar gidan ku sai kiga ko waye... sticker zaro ido ta turo masa sanna tace aqofar gidan nufa kace anya kuma ni kake nema?   "of course yabata amsa, gani awajen amma banga kowa ba ta maido masa da amsa, duba qofar gidan yafara yi yana laliben ta inda zai ganta amma baiga kowa ba,   "baki fito ba yamayar mata da amsa,      "kaga malam nifa bazan fitoba saboda bansan ka ba wai waye ma yabaka number ta?   shiru yayi ya rasa amsar dazai bata shifa harga Allah yagaji saira kadan takaishi qarshe tun dazu sai wasu tambayoyi take masa,    daurewa yayi yacije yakai zuciyar sa nesa,     sannan yayi mata reply da    " idan kanason abu ai duk wani hanya dazakabi dan ganin ka mallakeshi bazai maka wuya ba dan haka samun number abune me sauki awajena dan haka kima daina mamakin inda nasamu number ki ki ajiye wannan maganar  kitaimaka kifito inga kyakkyawar fuskarki ni masoyin kine na gaskiya( duk wanda  ya tuba dan wuya ba lada ashede ka iya masoyin gaskiya 😂 lol), "hmmm kawai tayi masa reply"    baƙaramin haushi reply din nata yabashi ba amma ba yanda ya iya tunda shi yake nema haka yaƙara hauƙuri yace "zaki fito din?   " a'a tace masa, Why ? ya tambaye ta abun haushin kawai sai yaga tama sauka a online din,     mutuwar tsaye yayi agun tare da tsurawa message din da yatura mata ido  lalle ma yarinyar nan mai ta maida shi suna magana tasan kuma basu gama ba amma tasauka karkada kai yayi tare da cije bakin sa aransa yana ayyana kalar rashin mutun cin dazai mata batasan ko shi waye ba 🤔, haushi kamar yakasheshi haka yake ji zuciyarsa har wani zafi zafi take masa da radadi, kashe wayar yayi ya mayar aljihu yana tunanin irin wulakan cin da zaiyiba su shettima dan duk su sukajawo wannan yarinyar take wulakan tasa dabasu turo shiba da tuni hakan bata faruba da girmansa da komai amma yazo wata banza can tanayi masa abun da taga dama, babu wanda baiji haushin sa ba acikin su musamman ma su bossay  sai kace su sukayi masa abun da tayi masa din, cike dajin haushin yajuya dan bazai ƙara yimata magana ba tafiya zaiyi gwara yaje subi ta wata hanyar amma ba wannan ba, juyawa yayi yafara tafiya har yadan yi taku waken biyar kawai yaji ƙarar bude ƙofar amma takaici bazai barsa ya juyo ba dan haka kawai yaci gaba da tafiya ya nufi wajen da sukayi parking,   "tsayawa tayi tana kallon bayan sa farace doguwar bata da jiki kyakkyawa ce ajin farko  sanye take da wani maroon din hijabi har ƙasa dan hakama ganin kalar kayan da yasaka saboda ya rufe mata har ƙafafun ta, tunda yajuya yafara tafiya take bin sa da kallo tabbas ta yarda kuma tana zaton shine wanda suke chart dashi yanzu daman ta fito ne dan ta tabbatar kuma ta tabbatar din batayi masa magana ba itama ta daga ƙafarta ta fara bin bayansa, loƙacin data ƙarasa wajensa yasaka hannu ajikin motar zai bude, " sai tayi sauri  ta danyi gyaran murya tare da cewa nace ba... tsayawa yayi da ƙoƙarin buɗe motar da yake yi sannna ya shiga juyowa ahankali   har yaƙara sa juyowa gaba daya yana fuskantar ta ƙurawa juna ido sukayi na ƴan daƙiƙu ita tafara janye nata idon daga garesa, ahankali tace kaine wanda muke chart yanzu? tayi maganar batare da ta kalle saba har yanzu kam shi baidauke idon sa daga kanta ba ,   jin shiru baibata amsaba yasa ta dago dara daran idon ta takalle sa ganin ita yake kallo yasata sauri ƙara kawar da nata dan bazata iya jurar kallon sa ba, juyawa tayi da niyar barin tunda yaƙi magana, "eh nine'  taji ya bata amsa juyowa tayi ta kalle sa tace to gani  idan kuma baka da abun cewa intafi,   "wani abu yaji yazo masa wuya amma sai yadaure tare da basarwa harda ƙaƙaro murmushin dole yayi mata tare da cewa agafarceni sarauniyar mata kallon kine yasani manta a inda nake dan Allah inbaza ki damuba mushiga daga ciki sai mu tattauna ingabatar miki da abun da ya kawo ni gareki gimbiyata, tundaga kan ƙafarsa tarar kallon sa har kansa masha Allah tace aranta tare da fara kokonton anya kuwa wannan ba batan kai yayi ba kyakkyawa dashi amma yace yana sonta to a inama yasanta itade tunda take bata taba ganin saba ko a mafarki to komade meye gaskiya fa ya hadu iya haduwa tunda taganshi taji yamata ya burgeta yagama tafiya da imanin ta(tabb kina ruwa kam) saidai tasan ba class din tabane dan ta tabbata yafita komai kyau da kudi tunda alamu sun nuna hakan ajikin sa da kuma kalar kayan dake jikin sa gayen yayi ta ko ina baida makusa, amma fa saidai duk da haka bazata bari yagane hakan ba gudun kar ajinta ya zube gara itama ta nuna mishi tana da class kar yarainata,       "Hy yace mata tare da daga mata hannu asaitin fuskarta, hakan yasata dawowa daga tunanin datakeyi ,       dan kallon sa tayi sannan tace a'a duk maganar da zakayi kayi ta anan inajin ka basai mun shiga ba, "hmm yace aransa tare da watsa mata kallon banza afakaice batare da ta gani ba,sannan yace "haba gimbiyata ai ba girman kibane ace kintsaya anan kowane yana wucewa yana ganin ki hakan be dace dake ba yakamata mushiga ciki hakan sai yafiye mana safe ko ya kikace ammafa idan bakyaso shikenan bazan takura miki ba duk abun da kike so shi za ayi kawaidai cancanta na nuna miki gimbiyar mata, har cikin ranta taji dadin kalaman sa da fasa mata kan datayi tabbata wannan muƙamin da take ganin batakai matsayin nan ba,   jin tayi shiru yasashi cigaba da cewa kyakkyawa ta bakice komai ba nifa inason inji kina magana domin ba ƙaramin dadi nake jiba idan naji muryarki yakamata  ace kitausayawa wannan baƙon naki wanda yagama mutuwa akan sonki dan Allah karkice a'a kitaimaka mushiga ciki muyi magana nazo da alkhairi gare ki, yana ƙarasa maganar bai jira cewar taba kawai  ya bude mata back seat yace Bismillah sarauniya ta tafaɗa yana kafe ta da ido da yasata takawa batare da ta shirya hakan ba kamar wacce ake control din ta haka taji gaba daya yagama kashe ta da kalaman sa batasan lokacin da ta shiga cikin motar ba kawaide ta ganta aciki,   tana shiga ya rufe ƙofar tare da sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ahankali ya furta Finally mungama dake, sannan yazagaya ta dayan barin inda take ya bude ya shiga yana shiga ya rufe ƙofar tare da kafe ta da idanu hadi da sakar mata wani irin murmushi me cike da ma'anoni da ita bata gane hakan ba, murmushin da yayi har cikin can ƙasan zuciyar ta taji shi juyar da kanta tayi tana kallon window tare da sakin nata murmushin da bata san tanayin sa ba, shikuma hakanne yabashi damar zaro hanki din dake gefen kujerar ya lallaba yasakama ta a hanci kafin ta juyo ta kalle sa har ta sume luuu tayi zata fada jikin sa yayi saurin janyewa yana wani ya tsina fuska kamar yaga abun ƙyanƙyami haka ya kwantar da ita kan kujerar, kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa  tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️ 💓💓💓💓💓💓💓💓💓💓 [6/2, 11:30 PM] #momyn twins#: ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)          *💖the talent troupe💖*                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                          🅿45&46 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                      "kallon fuskarta yayi na yan sakanni sannan ya kawar da kansa  tare da buha tsaki sannan yabude murfin motar ya fita daga ciki yazagaya yashiga driver seat tare da yiwa motar key yayi reavers ya nufi inda su shettima suke jiran sa..........✍️✍️   Yana ƙarasawa bakin kwanar sai yaga baigansu ba hange hange yafarayi daga cikin motar amma baigansuba wani haushinne yaƙara kama shi tsaki yaja aransa yana tunanin kuma ina sukayi, cike da takaicin rashin ganin nasu yadauko wayarsa yakira shettima, ,,"kuna ina ne? yatambayesa bayan yaɗaga wayar, bayan yabasa amsa kawai ya kashe wayar tare da jan motar yayi gaba yana cikin tafiya ya hango su can wajen titi atsaye,    agabansu yayi parking din motar tare da yi musu horn atare suka juyo gaba ɗayan su ganin shine yasa shettima saurin bude gaban motar ya shiga tunka yagama shiga yake tambayar ta ina? shigowar sa  idon sa ya sauka akan ta hakanne yabashi damar samun amsarsa batare da sam yabasa amsa ba, bossay ma bude bayan motar yayi ya shiga  inda take, bayan ya rufe sameer yaja motar batare da ya kula kowaba ko kallon inda sukema baiyi ba saima ƙara hade rai da yayi shi adole bazai kulasu kar su samu damar yin wata magana shiyasa ya ɓata fuska gudun raini, saidai abanza dan hakan da yayi bai isa ya hanasu tambayar saba,bossay ne yafara yi masa magana dacewa  gaskiya aikin ka na kyau kace har ka ƙwmus ta kenan yafada yana kallon fuskarta da dan fara'a a fuskarsa yaƙara dacewa wannan ai tsaf zaka iya kidnaping mutane batare da bata lokaci  dan naga alamar zaka iya fiya da hakama koma waye zaka iya kwamishewa, da sauri yajuyo ya kalle sa sannan ya mayar da hankalin sa ga tuƙin sa da har zai tanka masa saikuma ko me yatuna sai yayi shiru kawai yacigaba driving din sa,     jin yayi shiru yasa shettima cegaba da cewa kai da angaya maka shidin nawasane ai tunda yaje dolene ta mutu akansa musamman ma da yayi mata kalaman sa nasan baiwani sha wuya ba wajen shawo kanta amma de abun tambayar anan shine dadewar me kukakyi tundazu kabarmu muna jira wallahi ƙafata har tafara ciwo saboda tsayuwar da kabarmu muna yi, dan gayamana abun da kace mata ta yarda ta shigo motar da wane kalami kayi alwala kadan bamu musha(murmushi yayi tuna inda yasan kalmar dan bamu musha) wani irin harara ya aika masa da ita can ƙasaƙasa da murya yace me ya hanaku zuwa kugani daga nan yayi shiru yasan idan ya biye musu ransane zaita ɓaci  dan ba barinsa zasuba agaba zasu sashi suyi ta tsokanar sa saboda yaga alamar sungama rainasa,      cigaba yayi da tuƙin sa tare da ƙarawa motar gudu,     yana jinsu sunata tsokanar sa suna dariya amma yaƙi ya kulasu duk abubsu dole suka hakura sukayi shiru da magana saboda sukai kiɗan su suke rawar su, unguwar da suka kaisa nan suka nufa adan ƙanƙanan lokaci suka ƙarasa gidan da suka ajiye sa yanzuma bossay ne ya fito yaje ya bude musu gate din sukuma suka shiga ciki bayan yagama yin parking duk suka fito, sameer ne ya bude bayan motar inda take kwance har yanzu bata farfaɗo ba ɗagowa yayi sai kawai suka hada ido da shettima dariya shettima yayi masa dan yagane abun da yake shirin yi, dan ƙaramin tsaki sameer yaja tare da kawai da idonsa daga kansa amma yayi tsaye yakasa taɓuka komai kuma bayaso wani yadauke ta acikin su shikuma bayaso ya dauketa suyi tunanin wani abun shiyasa yakasa tabata, ahaka bossay da yagama rufe gate yaƙaraso wajen yasamesu, shima tsayawa yayi ya kalli wannan ya kalli wancen ganin duk sunyi carko carko kamar nonuwan maza,    shettima ne yadanyi gyaran murya sannan ya kalli bossay yayi masa alama da ido akan sutafi, gaba sukayi suka barsa awajen, binsu yayi da kallo yama rasa me zaiyi har suka shiga cikin gidan bai motsaba daga inda yake ba, ganin tsayiwar baza takai shiba ya tsugunna ya shiga cikin motar yana ta wani taɓe fuska da yatsinata sai yasaka hannu zai taɓata sai kuma yafasa yajanye hannun sa yayi hakan wajen sau biyar amma yakasa tabata daga ƙarshema sai kawai ya fito daga cikin motar yana ƙara binta da kallo, ajiyar zuciya yasauke tare da furzar da iska me huci daga bakin sa tare da cije lip dinsa na ƙasa yana dan jijjaga kai, wata zuciyar ce tace masa wai meye hakan kake yi kashiga kawai kadauko kana ƙara ɓatawa kanka loƙaci wai sai kace kai bana miji ba wannan yarinyar zaka zauna kana wani jin shakkar tabata,   cike da dakewa yakoma cikin motar gadan gadan zai tabata sai kuma yafasa rintse idon sa yayi tare da dukan kansa yaƙara jan wani tsakin, da ƙyar ya runtse idon sa ya daure ya cize yasa hannun sa akanta bayan ya dora hannun nasama akanta kasa ɗagota yayi sai da yaja lokaci sannan ya ciccibofa ya fito da ita tare da ɗorata akan kafaɗarsa yadafe ta da hannu daya dayan hannun kuma ya rufe ƙofar da ita sannan yafara tafiya da ita aransa yake ayyana bata da nauyi juyayi kamar ba abun da yadauka haka yakeji saboda rashin nauyin ta,     ahaka yana zancen zuci yaƙarasa bakin ƙofara sannan ya tura ya shiga ciki yana shiga yayi karo dasu abakin ƙofa ashe duk abun da yake suna leken sa suna masa dariya da suka ga yakusa shigowa ne yasa su matsawa daga jikin ƙofar, tunda ya shigo suke binsa da kallo suna so yakalle su amma shikuma yaƙi yarda su hada ido ɗin, ganin zai sauketa yasa shettima saurin cewa dan Allah dan tsaya inyi muku hoto wallahi kaga kyaun da kukayi banza yayi masa saidai kafin yakaita ga kwantarwar har shettima yadauke su a hoto loƙacin da yakai ga dan durƙusawa zai kwantar da ita yaƙara yimusu wani aƙallade saida yayi musu wajen guda biyar kafin ya ajiyeta, bayan ya kwantar da ita yajuyo yana kallon sa wayar yazo zai kwace shettima yayi saurin janyewa tare da mayar da ita aljihu yana yimasa dariya, hade rai ya kuma yi sannan yace wai ku dan Allah me yake damunku yanzu loƙacin wasane bakusan abun da ya dace ba da wanda baidace ba kunzo sai faman shirme kuke to wallahi last warning kufita daga idona be for I losing my temper wallahi bazakuji da dadi ba yafada yana nunasu da yatsa alamar gargaɗi,     "Shettima na yar dariya ciki ciki ya ƙame kamar soja yayi salute dinshi tare da cewa  sorry sir bazamu ƙaraba, ciki ciki yace mutum sai shegen son girman tsiya duk de hade ranka bazan gogeba wannan hoton sai yaje har gaban Ammah, me kace cewar Sameer yana kallon sa , tabe baki Shettima yayi sannan yace mekwa nace ni ba magana nayi ba, jijjiga kai yayi kawai yana girgiza kai sannan yayi gaba batare da yaqara tanka musu ba shiga dakin da suka ƙulle mahaifinta tura ƙoafar yayi da ƙarfi, yana shiga yaganshi a tsaye yana faman rarraba ido naushi yakai masa abakin sa atake bakin ya kuma fashewa, ya ɗago kenan zaiyi magana ya qara kai masa wani sosai ya shiga dukansa kamar an aikosa kuma yaƙi bari yayi magana shima kuma ko A baice masa ba sai duka kawai, su Shettima ne suka shigo cikin dakin ganin yana niyar kaisa lahira, yasa su saurin dakatar dashi suka shiga tsakanin su, tsugunnawa yayi agurin tare da dafe kansa hakannan yaji yana mugun jin haushin shi da yagansa maganganun wancen mutumin ne suka shiga dawo masa cikin kwanyar kansa sosai yake jin zafi da ƙuna a zuciyar sa, mahaifin sumy kam yana gefe a yashe yajigata kana ganin sa kasan ya daku ba ƙarya, dan numfashin sa har daukewa yake yi idon sama duk sunyi ciki ciki baya ganin su sosai yajigata ko motsi yakasa yi, "sameer tashi yayi daga tsugunen da yake ya ƙarasa gaban shi tare da durƙusa gabansa yana kallon ɗago fuskar sa yayi da kyau yanda zaifi ganin sa cikin amon murya yace zaka fadi inda yake ko sai na karar da numfashin ka agurin nan waye shi kagaya min yafada cikin tsawa da daga murya kafada nace waye shi? "shiru ba amsa jin yaƙi basa amsa yasa yaƙara daga hannun zai kai masa duka yaji an riƙi masa hannun, bin hannsa yayi da kallo har zuwa kan nata hannun ahankali ya shiga bin hannun nata da kallo har yazo kan fuskarta hawaye yagani a fuskar ta, saurin kawar da kansa yayi tare da kwace hannun sa,yana maida shi kan mahaifin nata zai dake shi tayi saurin shiga gaban mahaifin nata ji kake tass akan fuskarta dafe kunci ta tayi tana wani sakin marayen kuka cikin kuka tace kadake ni kaci gaba da dukana mai mukayi maku nida mahaifina daman sato ni kayi shine zaka yaudarene maiyasa zakayi mana haka mai wane irin zunubi muka aikata maka da muka cancan ci wannan hukuncin daga gareka kallifa yanda ka maida mahaifina kuma hakan bai ishe kaba kake shirin ƙara masa wani, kai wane irin marar imani ne baka da tausayi me ya aikata maka takarasa maganar cikin daga murya tana share hawayen da suke rige rigen zubowa, cak ya tsaya yakasa motsawa saida tagama maganar tata sannan yasa hannun sa yajanyeta gefe taga taga tayi zata fadi yayi saurin tarato da hannu daya saida tagama daidaita sannan ya sake ta, ƙara riƙo mahaifin nata yayi sannan yace idan kana son ranka da na ƴarka kafada min kai bama ita kadai ba har matar ka da mahaifiyar ka duk nasan inda suke dan haka kazaɓa rayukan ku ko wancen azzalumin da kake karewa, ƙara matsowa tayi kusa dashi tace maizai fada maka? "banza yayi da ita baikalli inda take ba yaci gaba da tambayar sa amma yaƙi magana, shake wuyan sa yayi da kyau yanda zaiji ƙanshin rahila, cikin kuka ta riƙe hannun sa tana jansa amma ko gezau takasa juyawa tayi tana kallon su Shettima da sunyi tsaye suna kallon su sun kasa saka hannu kuma sun kasa cewa komai, dan Allah kuzo kuriƙeshi kar yakashe min mahaifi wallahi idan yakasheshi duk sai na shigar daku ƙara tunda kuma baku da imani kuma ganin za ayi kisan kai amma babu wanda yayi yunkurin hanawa, komawa tayi kansa taci gaba da jan hannun sa tana dukan sa tana kai masa cizo amma yaƙi saki daga ƙarshe ma sai yasa dayan hannun sa ya riƙe mata duka hannuwa biyun, da ƙarfi tace abbaaaa kafada musu abun da suke buƙata zasu kashe ka dan Allah kafada musu Abba kafada musu na roƙeka tafaɗa tana ƙara sakin wani kukan muryarta har tafara dashewa saboda tsabar kuka, kukan da take ni ya dami sameer yasa shi sakin mahaifin nata, yana sakinshi yafara tarin wahala harda amai ga jini da yagama bata masa fuska duk yayi gaja gaja dashi kuma yakasa magana duk da zuwa yanzu ya fara saduda musamman ma da yaga ƴarsa ahannun su, zaka fada din ko incigaba? cewar Sameer, cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace yana ABUJA................✍️✍️ [6/4, 1:34 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                💖NEW TEAM💖    💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️47&48 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️          cikin kasalalliyar murya da kyar ya iya bude baki yace yana ABUJA....          Abuja a ina? Shettima da yazo wajen ya tambaya,    "cikin mawuyacin halin yaƙara cewa nima bansani ba nade san kawai a abuja yake saidai kuje kunemo shi nikuma kusake ni in koma wajen iyalina,    "idan kaga munsakeka to yazo hannun mu cewar Sameer yana wani binsa da kallon tsana, mahaifin sumy yace nifa bansan komai ba akan case ɗinku meyasa kuma zakace baza kusakeni ba bana gaya muku abun da kuke buƙata ba kuma me ƴata tayi muku bani nayi muku laifi ba meyasa zaku saka ta aciki yaƙarasa maganar cikin sanyin murya, taya kake tunanin zan yarda dakai bakasan komai ba kuma kayi mana ƙarya saboda yabaka cin hanci shiyasa, daka gayamana gaskiya tun farko da tuni hakan bata faru ba amma kanuna son zuciyar ka saboda kudi kasan zunubin da ya aikata dakake goyon bayan sa kasan laifin yin hakan dakayi yanzu duk matsayin ka dakake taƙama dashi zan iya shigar dakai ƙara akan laifin da ka aikata na karbar cin hanci,  koma ince aikin daka hau daman badan Allah ka karba dan karinga tauye haƙƙin mutane waysani ma ko baka san komai ba kawai ɗoraka akayi kawai niban banma sam suwaye suka ɗoraka awannan matsayin ba saboda baka san abun da Yakamata ba kana goyon bayan rashiya gaskiya, to  bari inganta maka inma bakasani ba duk matsayin sai na iya  sawa anƙulleka wanda yakiraka yahada mu nasan kasan matasayin sa wanda sama yake da kai to ni kuma ɗane agaresa dan haka shigar dakai ƙara ba abune me wahala ba, dan dakatawa yayi yana cigaba da kallon sa suna hada ido da shi yayi saurin kawar da nasa idon   juyawa yayi ya kalle ta ganin yanda take ta faman  fusge fusge zata kwace hannun ta daga riƙon da yayi mata amma takasa shikuma yana jinta kuma yaƙi ya sake ta,        "harara ta watsa masa ga fuskarta duk ta jiƙe da hawaye,"cikin hawaye tace ni kasakeni mugu azzalumi marar imani koma me yayi muku Yakamata kayi masa irin wannan dukan so kake ka kashe shi saboda kawai yaƙi gaya maka abun da kake buƙata sai ka kamasa da irin wannan dukan jifa yanda ka mayar masa da fuska to wallah Allah ya isa Allah yasakamasa nima yaudarata dakayi banyafe ba in sha Allah yanda kayi masa kaima sai kasamu wanda zaiyi maka irin haka, "kai ko girmansa ma baka gani kuma agabana saboda baka da kunya bekamata amatsayina na ƴa awajensa kakama dukan sa agabana kai yanzu zakaji dadi idan wani yazo yana dukan mahaifin ka agaban ka wane me zakaji acikin ranka wane irin mataki ne bazaka dauka, amma ni saboda macece nasan ba abun dazan iya yi maka amma kaje kai da Allah zakaga sakayya wannan abun da ka aikata Allah bazai barkaba Allah ya........"ɗall taji abakin ta sameer ya dallar mata baki, nunata yayi da hannu yace ki iya bakin ki kisan da wanda kike magana inbahaka ba kuma zan saita miki shi bana daukan raini, "taji zafin dallar tata da yayi da yasa ta sakin kuka cikin kuka tace bakasan raini amma ni ka raina min mahaifi harkake dukan sa shi bai girmeka ba kuma agaban yar sa da yayi auren wurimada tuni ya ajiye ɗa kamar ka amma kayi masa abun da kayi niyya akwai abun da yakai irin wannan raini, "Bana raina mutane ba raina na gaba dani ina girmama duk wanda ya girmeni koda da kwana ɗaya ne, amma kaide bazan taba girmama kaba har abada saboda wanda baisan darajar mahaifin ka shima bazaka taba ganin darajar sa ba har abada taƙarasa maganar tare da ɗan ɗaga masa murya tana ƙara jan hannun ta amma haryanzu yaƙi saki ya kafe ta da ido kawai,   dataga yaƙi sakinta saida ta faki idon sa, sai kawai tasaka haƙoran ta akan hannun  sa ta gantsara masa cizo me zafi kamar zata cire masa fata kuma taƙi saki, "jin zafin ya ratsasa yasashi kwace hannun sa da sauri tare da kwashe ta da wani lafiyayyen mari cikin bacin rai yaƙara kwashe ta da wani marin, "cikin daga murya ya nuna ta da hannun ta yace wai ke wace irin jahila ce kinsan dawa kike magana Ni sa'anki ne bakida kunya ko harni zaki ciza, cizo cizo yamaimaita kalmar dan baƙaramin mamaki ta bashi ba cigaba yayi da cewa ke mayya ce daman to wallahi aniyarki tabiki dan nafi ƙarfin ki, "yanzu de bata kulasa ba tafaɗa kan mahaifinta tana fashewa da wani marayen kuka, har cikin ransa mahaifin ta yaji marin da aka yiwa ƴarsa mafi soyuwa agaresa daman saboda ita yafada musu amma badan haka ba ko me zasuyi masa bazai gaya musu ba kawai sunci darajar ƴarsane saboda bayaso ana dukansa agaban ta gashi kuma itama baisan me zasuyi mata ba idan bai gaya musu ba shiyasa kawai ya yanke shawarar gaya musu din shima kuma iya garin da yake yagaya musu baigaya musu unguwar da yake zaune ba kuma yasan har gidan da yake,   "rungume shi tayi sosai ajikin ta tana ta fama kuka harda sheshsheƙa idan kaga yanayin da suke ciki dole sunana tausayi,     "yarfe hannun sa yake tayi yana kallon gurin da ta ciza din har ya kumbura yayi kala ga zafin da yakeji duk dauriyar sa nema yake yakasa daurewa din, su Shettima ne suka shiga yi masa sannu ganin yanda gurin cizon yayi jaaaa abunka da da fari kuma ajeboo, cike da kausarsiyar murya me cike da abubuwa kala kala yace kufita da ita daga nan kafin inkasheta aɗau gawar ta anan yafada yana nuna musu ƙofa yaƙara cewa kufitar da ita nace, "Bossay ne yafara zuwa inda take yafara kanta amma sai ta riƙe baban nata gam, saida su kadage kafin suka rabata da jikin shi shima da ƙyar suka bambanreta suka nufi waje da ita tana kuka tana ɗaga murya tare da ƙara zage shi har suka fice daga dakin yana ganin fitar su ya rufe dakin sannan ya juyoasukwane yadawo kusa da mahaifin nata yadago sa tsaye da kansa sannan yace kanason ƴarka ta cigaba da rayuwa  kanason matar ka kana son mahaifiyar ka kanason kaci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar kowa?      daga masa kai yayi alamar eh" sameer yace to idan duk kanason to yazama dole kabamu bayanansa da address din unguwar da yake da kuma gidan da yake zaune inbahaka ba kuma wlh duk saina aikata abun da duk kaji dan saina tarwatsa farin cikin ka na tarwatsa rayuwar ƴarka?      "cike da dakiya duk da yanajin dan tsoro azuciyar sa amma yadake sannan ya kwace jikin sa daga rikon da yayi masa sannan yace kayi musu duk abun da kaga dama Allah yana tare dasu baka ida kayi musu abun da Allah baiyi musuba Allah yana tare damu tunda na riga bahaya maka abun da kake buƙata bayan nan kuma bansan komai zan ƙara gaya maka ba dan haka duk abun da ka yankewa ranka kawai  ka aikata Allah ne shaidata nibansan komai ba, shiru yayi yana bin fuskarsa da kallo tare da ƙara nazarin sa, duk da wannan bayanin nasa shifa haryanzu bai yarda dashi yasan dole akwai abun da yake boyewa saboda shi yana da baiwar saurin gane marar gaskiya wani tunanin ne yafado masa arai dan haka sai kawai ya sassauta murya tare da zama agabansa suna kallon juna sannan yafara magana yace nasan kasani dan ko rantsuwa nayi bazata cini ba naga rashin gaskiya a idon ka kuma wannan abun daka ga inayi maka akwai dalili  dan haka  karkamin ƙarya kar ka boyemin duk abun dakasani domin hakanne  kadai zaisa kabar gidan nan daga kai har ita din dan saina musguna muku kamar yanda kake shirin yimana Yakamata kakama kanka ka kama girman ka bazan ƙara taɓaka ba saboda ƴarka kasan inda dare yama kacire hannun akan wannan case din dan baƙaramin case bane bakasan komai ba bakasan kowaye mutumin nan ba bakasan labarin sa ba kawai andoraka akai kaikuma ka hau ka zauna zaka dauki alhakin sa dan haka ina gargadin ka da kacire hannun ka tun kafin lokaci yaƙure maka tun kan kafara da nasani abune hawa hawa shima da mukace kagaya mana bashi muke nema ba kawaidai ta sandin sa zamu iya gano wanda muke nema, kawai  zallar mugunta akayi masa aka rufe sa ba tare da ya aikata komai ba kuma sun hana kowa saboda wani ƙudurin su da yake kansa Ni yanzu bazan iya baka labari ba amma inason ko nawa yake baka ni kuma zan ninkamaka sau uku kagayaman duk wani abu da kasani akan wannan case din,     "sosai jikin sa yayi sanyi shiga daman kawai mayan kudine shiyasa yaƙi gaya musu saboda kar yarasa wancen kudin da za abasa amma yanzu tunda yaji za aninka masa to ba abun dazai hanasa fada mishi,    saida ya gyara zama da kyau yana fuskantar sa har zaiyi magana sai kuma yayi shiru, ganin hakan yasa sameer cemasa inajinka kafadi duk abun dake ranka,    dan numfasawa yayi sannan yace "zan gaya maka iya abun da nasani amma fa kafara min alkawarin tura min kudina saboda nasan wannanne ƙarshen aiki na aƙarƙashin sa dan haka dole ina buƙatar kudin da zan samu incigaba da juyawa yaƙarasa maganar yana kawar da idon sa gefe yanajiran jin amsarsa.... "baka da matsala karkadamu da wannan cewar sam,     "agaskiyar magana wannan case din naku bansan komai ba akai kamar yanda kasani kuma bansan mutumin da kuke magana akaiba ƙarewa ma ni bantaɓa ganin saba, iya abun da nasani shine wannan mutumin da kaji nayi waya dashi shine ya sauka daga kai kuma shi laluboni intaƙaice maka bayani ma bawannan fannin nakaran taba hakannan yasame ni da maganar abokin wani makocinane tun ada amma yanzu yama tashi daga unguwar alokacin yasameni yace yanaso yaban aiki gidan yari zaiban office dinsa nace masa nifa bawani karatune da ni me ƙarfiba da har za abani aikin office sai yace wannan ba matsala bane indai zanyi yanda yakeso shikenan shi zaji da komai ba ɓata loƙaci na amince masa saboda shine babba agurin kuma yagama siye kowa agun ba wanda baya bin umarnin sa sai abun da yace akeyi agidan nan shiyasa ma hukuma batasan me akeyi aciki ba koda anzo dubamu yana kafawa kowa abun dazaiyi baza ataba zuwa akamasa da wani laifi ba shiyasa ma yaɗorani akai saboda yana da muhimmin wani abun da yakeyi amma loƙaci zuwa loƙaci yana kawo mana ziyara sannan yana kiran waya yaji duk halin da ake ciki shiyasa tunda nafara nima ba ataba samun wata matsalaba ina aiki batare da gwamnati tasan dani ba, wata rana yazo yana neman wani file hankalin sa yayi matuƙar tashi da baigansa ba aloƙacin ya rufe ni da faɗa akan innemoshi duk inda yake inbahaka ba sai ya kasheni duk inda nasan nakaisa ma infito dashi, nima ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba jin abun da yace nan ya fita yabarni na hau bincike gabadaya office din Saida na hargitsashi ina neman sa amma bangansa ba haka na kira bagaya masa bansan inda yake ba, ƙara dawowa yayi shima ya duba dakansa amma baigansaba dayaga haka sai kawai ya yanke shawarar yace ko watakil yatafi dashi zaije ya duba amma nima intabbatar na ƙara dubawa, na amsa masa da yo, har zai tafi sai nace masa wane irin suna zangani ajiki sannan kuma wane irin case ne, nan yake cemin wani case ne daɗaɗɗe kuma wanda ake case din akansa anriga anfita dashi baya cikin prison din file din sane kawai aciki shima kuma za afita da shi yaɗora min da cewa ko ba dade ko najima yasan za azo memansa dan haka kar masake ma fadi wani abu ince bansan komai ba saidai akira wanda case din ke hannun sa tunda mukayi maganar kusan kullum sai yakira yaji batun ganin sa amma ince bangansa ba, bansan kuma ya akayi ba kawai yadena kira yatambaya ko ganin sa yayi oho baigaya min ba, ni kuma aloƙacin ne nafara binciken ko waye tunda naji abun da yace nafara zarginsa akan baida gaskiya akan wannan case din yaza ayi ace anfita da mutum daga ciki ba tare da angama bincike ba kuma har ana neman file dinsa wanna case din da alamar tambaya akansa, nan nafara tambayar wani tsoho ko yasan case din yace min eh yasan dashi a kawo sane kuma anƙi barin kowa yagansa sai wani mutum kuma ba afito dashi daga daki kamar sauran ƴan gidan kullum yana ɗaki kuma shi kadai babu wanda yasan me ya aikata saboda komansa ba irin na sauran bane, yataba bani labarin akwai wata mata datake zuwa wajen tana neman sa amma ance mata baya nan kullum sai tazo dayagade tanace da zuwa sai ya taimaka mata har inda yake yayi mata hanya aɓoye ta shiga tagansa tayi wajen zuwa biyar kuma sai akayi masa rasuwa mahaifin sane ya rasu dayatafi kuma sai matarsa ma tafara rashin lafiya aƙallade yakai wajen wata biyu baidawo ba da yadawo kuma sai yadaina ganin ta baima dadeba kuma sai shika sa wancen mutumin da take zuwa gurin sa sai akafita dashi daga gidan ma gabadaya tundaga nande bai ƙara samun labarin saba dagashi har matar datake zuwa wajensa bata ƙara dawowa ba abun da yasani kenan shima, "harzuwa loƙacin dana fara aiki, tunda ga laƙacin na ƙarfafa bincike gurin nagano inda file din yake amma shiru bangasaba har yanzu da nake maka magana, "tunda mukayi maganar wataran kwatsam ya kirani cewar yaga file din sannan yaƙara jaddadamin akan duk loƙacin da akazo neman sa  inyi saurin sanar dashi nace masa to, duk bayan sati daya sati biyu yakan kira yaji ko anzo nemansa amma ince a'a"aranar da mahaifinka yakirani na sanar dashi cewa wani yakirani akan zakuzo akan maganar mutumin nan da kuke magana shine yace kar nasake magaya muku inda yake kuma idan nayi hakan zai ƙara min kudi akan albashina kaji dalilin da yasa naƙi gaya muku iyakacin abun danasani kenan, yaƙarasa maganar yana dan kallon sa,   "miƙewa sameer yayi yafara zagaya dakin ransa na wani irin zafi yayi wajen minti biyu batare da yace komai ba saida yagama zagayan sa sannan ya juyo yana kallon sa sannan yace "a wace unguwar yake da zama kasan gidan sa?     "eh nasani nataɓa kaimasa saƙo har gidan sa da yake da zama, Shikaɗai yake zaune ko tare yake da iyalen sa?    shikaɗai yake zama ko aure ma baitaba yiba,        "zaka iya yimin kwatancen gidan da unguwar?      nan ma eh yaƙara cemasa, good 👍 ina jinka kwatan tamin, nande yabasa address din inda yake sannan yadora da rokon sa akan dan Allah karyagaya masa shi yagaya masa dan zai iya daukan mataki idan yaji koda akan iyalen sane shikuma bayason abun da zai shafi ahalinsa yafiso koma me za'ayi ayi masa iya shikaɗai,     nan yace babu abun dazai sameka muna nan daga ranar da yazo hannun mu to yagama yawo komansa yazo ƙarshe, nan yaji dadi sai yanzuma yake ta danasanin ƙingaya musun da yayi gashi yazo yasha najaki abanza,     "zakaci gaba da zama anan har zuwa loƙacin da zamu kamo sa, kamar aradu yaji maganar tasa shi duk atunanin sa tunda yafaɗa musu shikenan zasu rabu dashi kawai yabashi kuɗin shi yaƙara gaba bashi ba komawa aikin gidan yari watakil ma ya haɗa iyalansa subar garin amma sau yaji wannan zancen nasa da bai taɓa tunani ba,     sameer ne ya katse masa tunanin sa da cewa kaji de abun da nace ko saboda tsaro badan tsoro ba dole mu cigaba da riƙeka idan komai ya kammala sai mu sakeka katafi amma bazai taba yiyuwa nasake ba batare dashi yazo hannun muba idan mukai haka munyi kuskure,    "to amma ba na riga nagaya maka ba nikuma meye nawa aciki kaga dan Allah kabarni natafi duk abun da nagaya maka gaskiya nagaya maka kuma bazan yaidare kaba tsakanina da Allah nagaya maka kurabu damu mutafi katuramin kudina kuma,      bazai taba yiyuwa ba kama dena bata bakin ka zande mayar da ƴarka gida amma kaidai bqzan sakekaba sai gobe idan mun kamoshi sannan kai kuma in sallameka dan haka kamadena wahalar da kanka dan nariga dana gama magana, yana kaiwa nan ya fita yabarsa adakin,     "Yana fitowa yayi karo da sumy abakin ƙofar ta haɗa kai da gwiwa tana tafaman shashsheƙar kuka,   "tana jin bude ƙoafar tayi saurin ɗagowa ta kallesa kawar da kansa yayi gefe, kulle dakin yayi sa key,    da har yajuaya zaunar gurin batare da ya kulataba har yayi taku biyu sai kuma ya tsaya juyowa yayi yakalle ta ganin yanda fuskarta tayi gaje gaje da hawaye gashi tayi jaa idon ta duk sun kunkubura saboda kukan da tasha, hakan nan yaji ta ɗan basa tausayi maganar gaskiya maganganun ta sun dan tabashi yasan baiyi mata adalciba baikamata yadaki mahaifinta agaban taba gashi itama batasan hawa ba bare sauka yaje ya daukota yakawo ta nan sannan yadaki mahaifinta agaban ta itama kuma ya mareta kuma yarabata da mahaifinta, tuna maganar da tayi masa nacewa kai yanzu wani yadaki mahaifin ka agaban ka wane irin mataki nema baza ka dauka ba saboda ni macece shiyasa to kai da Allah in Allah ya yarda sai kasamu wanda zaimaka fiye da yanda kayi mana, tabas maganar ta gaskiya ne uba baifi uba ba bawanda za ayiwa haka ya ƙyale dan shi aganin sama idan wani yayi kuskuren aikata wata maganar ma da baigamshe sa ba sai ya canza masa kamanni sai inda ƙarfin sa yaƙare bare kuma takai ga agaban sa wani yadaki mahaifin sa ai inajin sai ya iya raba mutum da numfashin sa jikin sa yaji yayi sanyi ahankali ya shiga takawa har zuwa gabanta tsayawa yayi sai kuma ya rasa me zaice mata.... miƙamata hannu yayi batare da yace mata komai ba alamar takawo nata hannun,      "jin tsayuwar mutum akanta yasata dago kai karo tayi da hannun sa, hannun ta tsaya kalla sannan ta shiga bin hannun nasa da kallo har zuwa kan fuskarsa suna haɗa ido da ita ya gallamata harara tare da hade fuska, kasaƙe tayi tana kallon sa ganin hararar da yayi mata batasan loƙacin da itama ta mayar masa da harar ba tare da sakin dan siririn tsaki ta kawar da kanta,    sarai yaji tsakin da tayi masa kawaide ya rabuda itane saboda tausayin ta da yake ji idan yace zai biye mata zasu bata loƙaci ita rashin kunya shikuma bazai daukaba dukan ta zai tayi kuma ita zatasha wuya shiyasa kawai ya rabu da ita kawai yanzu baida loƙacin ta, janye hannunsa yayi daga miƙamatan da yayi ahankali tace tashi mutafi ko motsawa batayi ba bare yasa ran zata tashi ƙara maimaita mata yayi,   "amma still de bata motsa ba, tsugunnawa yayi agabanta yace bakiji me mace miki bane yafaɗa yana leken fuskarta afusace ta juyi itama ta hade ran tare da doka masa harara sannan cike da tsiwa tace naji din banzan tashin ba ba inda zani batare da nahaifina ba mugu kawai marar tausayi, kafeta yayi da ido baya ko ƙiftawa hakanne yasata hadeye sauran maganar da take shirin yi itama batasan lokacin da tasaki jiki takama kallon ƙwayar idonsa ba kallon juna suka shigayi batare da kowa yasan dalin kallon ba.........✍️✍️✍️                💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(mrs bmb) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)             [6/6, 9:40 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                💖NEW TEAM💖    💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️49&50 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ kafeta yayi da ido baya ko ƙiftawa hakanne yasata hadeye sauran maganar da take shirin yi itama batasan lokacin da tasaki jiki takama kallon ƙwayar idonsa ba kallon juna suka shigayi batare da kowa yasan dalin kallon ba.........✍️    "ita tafara kawar da idon ta daga garesa tana ƙara tamke fuska,   sai loƙacin shima yadawo cikin hayyacinsa dan sosa kai yama rasa yazaiyi da ita ya fuskanci inyaci gaba da biye mata rainasa zatayi gashi kuma sai ƙara bata masa loƙaci takeyi tunanin hakan yasashi baiƙara yimata magana ba bazato ba tsammani kawai taji ya miƙar da ita tsaye tare da kamo hannun ta zai fara tafiya da ita aikwa tayi saurin sakar masa kuka tana kwace hannun ta "kasakeni nace maka ba inda zani batare da mahaifina ba"ko kallon ta baiyi ba yaci gaba da janta suna dab da fita, "taƙara jan burki cikin sanyin da ita kanta bata san loƙacin da tayi ba, shima kuma sanadin hakan yasashi dakatawa da tafiyar da yake yi,   "dan Allah dan Allah fa nace taya kake tunanin zan iya tafiya inbar mahaifina anan acikin irin wannan halin kataimakawa rayuwata idan ma natafi nabar nan bazan taɓa samun kwanciyar hankali ba ko bacci bazan iyaba mahaifina shin uwata shine ubana shine gatana banida kowa aduniyar nan sama dashi taya kake expecting din zan iya tafiya inbarsa kasan radadin da nakeji acikin zuciya aduk loƙacin da naganka amatsayin wanda yadakar min uba agabana ubafa mahaifina ka daga hannu kadake shi agabana akan idona akan abun da bai taka kara yakarya ba meyasa meyasa zakamin haka bayan ka yaudareni kaje hargida ina kwance cikin kwanciyar hankali kaje  ka yaudareni nashiga motar,har abada bazan taɓa yafemaka ba Allah ya isa tsakanin na dakai taƙarasa maganar tare da ƙara fashewa da wani irin kuka kai kanajin kukan kasan cike yake da ƙunci da tsantsar ɓacin rai jitake kamar tashaƙeshi sai taga yadena nunfashi tukunna tasakeshi" "tana kaiwa nan da ƙarfi ta kwace hannun ta daga riƙon da yayi mata da sauri ta juya zata bar wajen yayi saurin riƙota tare da jawota tafaɗa kan ƙirjinsa, "jin haka ba ƙaramin tsorata tayi ba hakan yasata sakar masa kuka awajen saitin kunnen sa, damƙe idon sa yayi ƙam batare da yasan me yake ba ya rungume ta tare da tallafo bayan ta da duka hannu biyu atare suka sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ahankali yashiga dan bubbuga bayan ta alamar de kamar zai rarrasheta yanaso yace wani abu amma yakasa bude bakin sa saboda nauyin da yaji yayi masa, yafa fara kasa gane kansa tunda ya hadu da yarinyar nan sai sawa take yana yin wasu irin abubuwan da baitaɓa yiba amma yabar hakan kawai da tausayin ta dayake watakil shiyasa yake mata haka, kokarin miqewa takara yi amma ya hanata yaqara riqeta tayanda baza ta iya kwace kantaba, harcikin ransa yakejin kukan nata yanaso yace tayi hakuri amma yana jin bazai iyaba yasan baikyauta mata ba kuma saidai tayi hakuri dan bazai iya barin ta anan wajen ba kuma bazai iya sakin baban ta ba batare da sungama bincikensu ba dole sai sun riqeshi saboda har yanzu baigana yarda dashi ba yasan idan yasankeshi watakil yakira wancen din yagaya masa shikenan ya ruguza musu shirin sa shiyasa bazai sakeshi, Amma gashi ita kuma tasakanshi agaba sai faman rigima take masa kuma yarasa ta yanda zai fahimtar da ita, sai mutsumutsu take masa ajiki sanadiyar hakan kuma ya haifar masa da wani irin yanayi da be gama tantance na meye ba cikin qasa qasa da murya yafara yimata magana niba zan qarayiwa mahaifinki komai ba ki muje inmayar dake gida shima zuwa gobe da kaina zan kawosa har gida nayi miki alqawari bandauko mahaifin ki da wata manufa ba dan na cutar dashi nadauko shine da dalili wanda ko ke kika tsincin kanki a irin halin dole ki kama koma waye mahaifinki yayi wani kuskure ne ya boye gaskiya ne akan wani case da akeyi mu kuma muna son yagaya mana gaskiya ne shiyasa muka dauko sa kema kuma bamu dauko ki dan muyi miki wani abuba mundauko kine kawai dan muyi masa barazana dake yagaya mana gaskiya kuma gashi burinmu ya cika yagaya mana abun da nuke bukata amma dole sai mun kamo wancen zuwa gobe sai musakeshi, Amma daga yanzu babu abun da zai qara tabashi zanma saka azo adubasa abasshi kulawa, "kiyi hakuri kikoma gida zaman ki anan bazai yiyuba kinji?    Shiru tayi bata bashi amsaba saidai tadan rage kukan datake yi yazamana hawayene kawai yake zuba a daga idon ta, tawani fanni ta danji dadin bayanin da yayi mata ta wani bangaren kuma har yanzu inta tuna lokacin da yake dukan mahaifin ta sai taji wani irin haushin shi yazo mata wuya,    "bakice komai ba ya katse mata tunanin da take, still de shirun tayi masa bata tanka masa ba   jin shirun nata yasa yaqarajin ba dadi aransa yasan daman ba lalle ta fahimce sa ba zata dauka kawai shi mugune ya zalince ta ya zalinci mahaifinta dan komai zai fada bazata taba ganin laofin mahaifinta ba nashi zata gani,   dan raba jikin ta yayi da jikin sa yana kallon fuskarta da gaba dayanta ra wanke da hawaye idon ta duk sun kunkunbura sunyi ja duk ta canza kamanni kamar ba wacce ya dauko dazuba ras da ita amma yanzu ta sanadin sa ji yanda ta koma, baisan lokacin da yadaga hannun sa ba ya shiga goge mata hawayen da yabata mata fuska, saida yagama goge mata duka sannan ya tallafo duk fuskar ta a hannun sa sannan ya furta I'm sorry stop crying I hate it,   gefe tayi da fusakar ta sannan tace kanaso in tsaya kaci gaba da yaudarata ne ai bazan kara yarda da kalaman kai ba ba wani abu kuma da zaka kara fada min da zaisa inyarda dakai koma meye ni nace naji kaje kawai zanci gaba da zama anan duk sanda kasake shi nina na koma gidan amma ba inda zani, dafe kansa yayi tare da rufe idon sa da bude su duk alokaci daya aransa yace yau nadaukowa kaina bala'i wannan wacce irin yarinyace da har zai bata hakuri amma taringa yi masa abun da taga dama duk irin bayanin da yayi mata amma basuyi tasiri aranta ba wacce irin zuciya ce da ita watakil sai ya nuna mata ko waye shi zata fara fahimtar abun da yake cemata dan wallahi yafa fara gajiya da ita  ta fara isarsa bayaso takaishi bango yazo yanayi mata abun da bazataji dadi ba saboda yana danjin tausayinta  tundazu yake danne zuciyarsa amma tana neman takaishi karshi, taba kaiwa karshen maganar ta dan  matsa daga gurin sa ta juya zata bar wajen..... yanzuma kamar dazu haka haka yakara saurin riqo hannun ta saidai yanzu bata bari ta fada kansa ba ta tsaya da kafafunta,, zatayi magana kenan yadaga mata hannu shiru tayi kwa saboda ganin yanayin face dinshi ba alamar wasa acikin ta itama daman karfin hali kawai take amma zuciyar ta cike take da tsoro kawaide basarwa take tana nuna batajin tsoran sa amma taciki na ciki,      "baijira wata wata ba ko jiran taqara ce dashi wani abun kawai taji yayi sama da ita, zaro ido tayi tafara kokarin saukowa amma yahanata damar yin hakan, rikon jarirai  yayi mata yafara tafiya da ita, tana tafaman motsi sai wurwurga qafa take tana cewa ya sauketa amma ko kallon tama baiyi ba bare tasa ran zai ajiyeta din ahaka  yafita da ita,    "Su bossay 'yan muna furci ashe suna labe suna jin duk abun dasukeyi suna jin motsin su sukayi saurin barin wajen suka koma falon tare da zama akan wani benchi dake gefe agurin,    Suna zama shikuma yafi to da ita yana fitowa suka hada ido dasu sai kawai ya hade rai kuma kallo daya yayi musu yagane basu da gaskiya dan haka bai tankawa kowa ba yayi gaba abun sa saboda bayaso ma yatsaya su kawo masa raini dan haka yayi gaba har yakai bakin qofa sai ya tsaya batare da yajuyo ba yace inkun fito make sure kunrufe ko ina yana fada musu haka ya fice,     "kallon juna sukayi sai kawai suka kwashe da dariya harda tafawa saikace wasu mata sai da suka gama dariyar tasu, Shettima ne yafara cewa lalle mutumin nan mu zaina rainawa hankali sai yayi abu sai kuma yazo yana wani hade mana rai waishi dan kar agano wani abun baisan mun ranfo jirginsa ba tun wuri, bossay ya dora da cewa tab babbar magana karfa muje raishe ya juye da mujiya dan kwali zaija hula dan naga alamar watakil daga tsarin qarya za awuce da da tsarin gaskiya kajifa yanda yake mata magana dazu ni wai daman yana kula 'yan matane da har yasan yanda zaikwantar da murya yayi musu magana ya rarrashe su? "Shettima yace hmm wallahi ko daya ni tunda nake dashima bantaba ganin ya kula mace ba iyakacin sa da mace kyara da hantara da fada inta kama ma aje ga mari amma kaga yau shine wai harda bata haquri abun da bayayi iya zamana dashi baya bawa mutane hakuri mutane biyu zuwa uku yake iya bawa hakuri arayuwar sa shima sai yazame masa dole amma yanzu gashi yabawa wata macen lalle yau rana ce ta musamman badan halin da muke ciki ba da sai na hada mana dan qaramin oarty a masarauta ko ya shaida, dariya bossay yayi yace aikam de yakama muyi masa gaskiya nima nayi mamaki wai hardacewa I'm sorry stop crying I hate it hhhhhh gaba dayan su suka qara saka dariya, saida suka gana dariyar tasu da gulmar tasu  sannan suka miqe suma suka fita tareda kulle kofar sannan suka juya suka nufi inda sukayi parking din motar,     atare suka waro ido tare da kallon juna sannan suka qara mayarwa gurin ganin ba mota ba alamar ta,    " kamar wadanda ake juyawa atare yanzu ma atare suka juya wajen gate din ahangame suka gansa, "Bossay ne yace wai tafiya yayi?   Shettima "yace ga zahiri kana gani kuwa,   "to ina yatafi? ni ina zansani bayan munaa tare dakai rashin mutunci ne kawai nufin sa muhau motar haya, tab gaskiya yagama damu to meyasa zaiyi mana haka "duk borin kunya ne nasan yasa shiyimana haka cewar shettima, amma bari in kirasa inji wayarsa ya dauko ya kirasa saida baidaga ba wani kiran yaqara yimasa sai da takusan tsinkewa sannan yadaga shina kuma yana dagawa yace musu muhadu agida kawai ya kashe wayar, wayar suka shiga bi da kallo kamar shi suka gani ajikin wayar, bayanda suka iya dole suka hakura bayanda zasuyi dashi suka fita daga gidan suka rufe gate din sannan suka nufi titi aqasa shi kansa titin kafin suje aikine saboda nisan sa, suna tafiya suna jan tsaki da hirar abun da zasuyi masa zsai sun rama abun da yayi musu ko ta hanyar tsokanar sane wallahi idan suka sakashi agaba sai ya tsani kansa dan kowa sai yasani, ahaka suna surutansu har suka ƙaraso bakin titin napepe suka tara direct suka wuce masarautar abakin gate aka ajiye su suka biyashi kuɗin sa suka shiga ciki masallaci suka shige saboda harma antayar da sallar magariba' bayan sunyi sallar suka suka nufi can cikin masarautar inda part part suke, part din momma suka fara nufa dan sunsan bazai wuce can dinba dole nan zai fara zuwa, amma ga mamakin su suna shigowa suka duba parking space basuga motar da yataho da ita ba alamar de baidawo gida ba part din momma suka shiga,, basu tarar da kowa ba a falon sai kawai suka zauna akan kujerar suna zama momma ta fito daga kitchen hannun ta dauke da try tana ganin su tasaki murmushi tare da cewa sai yanzu kuka dawo tunɗazu nake zuba ido ganinku, taƙarasa maganar loƙacin da taƙarasa gaban dinning ɗin ta ajiye sannan tadawo wajen su tasamu waje ta zauna tana fuskantar su,"shettima shima yana dan murmushin yace ayya momma wallahi wani aikine ya riƙemu bamusamu damar gamawa ba sai yanzu, to ai shikenan tundade yanzu kundawo sai kuzo kuyi dinner tunɗazu daman nasa aka haɗa muku ku kadai yake jira ina me sunan baba naga kun shigo kukaɗai ko ya wuce part ɗinsa? "shiru duk sukayi sun rasa me zasuce mata, da har shettima zai fadi gaskiya sai kuma yayi saurin bugar bakinsa sannan yace a'a momma yana nan ƙarasowa yadan biya wani wajen ne yace mutaho yanzu zai shigo, tace to shikenan zaku jirasa ɗin ne ko zakuci? "a'a zamu jirasa ai yanzu zai shigo, "tace to bari inje in kungama kwamin magana tafaɗa tana miƙewa daga gurin ta hau upstairs tabar su agun, "hira sukaitayi abunsu suna jiran shigowar sa amma shiru har wajen ƙarfe tara bai dawo ba... aɓangaren sam kam tunda yafita da ita tasakar masa wani sabon kukan tana cewa ya sauke, shikuma bai kulata ba, dade yagaji da kukan nata saikawai yasamu bakin titi yayi parking tare da zuba mata idanu yana kallon ta shifa yarasa yanda zaiyi da yarinyar, kai ta kifa akan gwaiwarta tana ta faman raira kuka amma jin ya tsaya yasata ɗagowa titin tashiga bi da kallo ganin ba gida bane yasata tajuyo ta kalle sa haɗa ido sukayi tayi saurin jefa masa harara sannan ta kawar da kanta, ahankali yace dan Allah badan niba kitaimaka kiyi min shiru wallahi tun da muka hadu kike sakamin ciwon kai naji ban kyauta miki ba amma ai na baki haƙuri yakamata ki fahimceni kitaimaki rayuwata kidena wannan kukan wallahi banason kuka na tsani kuka badan nasan ninayimiki ba daidai ba wallahi da tuni na saitaki amma yanzuma bata ɓaci ba ina roƙonki da Allah da Annabi kiyi shiru wallahi karki kaini ƙarshe dan zan iyayi miki abun da baki tunani kibini ahankali, ɗagowa tayi ta kallesa ganin yanda ya hade fuska tana mamaki ace wai mutum yana magana cikin sanyin murya amma kuma har yakoma faɗa saboda tsabar yasaba da masifa wannan wane irin mutum ne haka da baƙin hali bashida tausayi, jin tayi shiru yasa yaci gaba da tafiyar sa atunanin sa shikenan ai ya tsoratar da ita bazata ƙara damun saba, kamar kwa yanda yayi tunanin kwa hakance ta kasance bata ƙara kukan ba har suka ƙaraso gidan, agaban gate din yayi parking tare da cire louck din motar ko kallon barinta baiyi ba yace mata fitar min amota, yanda kasan yayi magana da dutse haka ta mayar dashi ko motsawa batayi ba jin shirun ta yasa yaƙara cewa kifitar min nace miki ko bajiki ba nan ma shiru bata motsa ba, "afusace ya juyo zai balbaleta da faɗa sai kawai yaja stop yana binta da kallo hannu yakai saitin fuskarta da take arufe yadan hada hannun sa guri guda yabada ɗas ɗas yayi sau biyu amma bata bude idon taba, "bacci? yafaɗa a fili rabuwa yayi da ita ya koma ya kwantar da kansa shima yayi ajikin kujera tare da lumshe idanu yana jiran farkawar ta(Tabb😬) jin abu yayi akafadarsa ahankali yashiga bude idon sa akanta yasauke su datake kwance akan kafaɗar sa, maimakon ya tasheta sai kawai yadan ƙara gyara zaman sa yanda zatafi jin daɗi kwanciyar ahaka ya yakomar da kansa kan kujera ya ƙara lumshe ido, bazato ba tsammani shima baishirya ba bacci yayi awon gaba da shi ahaka sukayi bacci gaba dayan su tana kwance akansa...........                   💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(mrs bmb) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)             [6/8, 6:28 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️51&52 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ ___________*Abuja*      "tunda ta kwanta ta bata farka ba sai bayan sallar la'asr,     tun suna leƙanta suna jiran farkawar ta da wuri harde suka haƙura suka tashi daga falon amma jim kadan dai wani yazo ya duba ta,    bayan sun idar da sallar la'asr ne suka ƙara zama awajen ta gaba ɗayan su,    basu daɗe da zama ba suka ga tafara motsi dukkan su miƙeya sukayi suka koma kusa da kujerar ta suka zuba mata idanuwa,    ahankali ta shiga buɗe idanun ta tun tana ganin dishi dishi harta ƙarasa bude su tar ta sauke su akan su  ƙara mayar dasu tayi ta rufe sai kuma tasake budesu jitayi jikin ta gaba daya yana yi mata ciwo ahankali ta yunƙura zata miƙe zaune amma taji takasa,   'da sauri meer yakai hannu sa ya daugota da taimakon sa tasamu ta zauna' " jigina kan kanta tayi da jikin kujera tana dan dafe kanta saboda bata danji dadin sa jitayi yana danyi mata ciwo amma ba sosai ba,    Ummy ce tafara cewa sannu sannan Abu ma yayi mata sannun,        'meer kuma gefen ta yasamu yazauna  sannan yayi mata sannun, "bata amsa sannun kowa ba saidai duk wanda yayi mata sai ta bishi da kallo batare da amsawa musu ba,    "falon ta shiga bi da kallo tana mamaki aranta inane nan,   ba inda yake miki ciwo?    "Abu yakatse mata tunanin ta,   juyowa tayi tana kallon sa tare da kafesa da ido kamar zata ciro wani abun ajikin sa saida tagama ƙara masa kallo sannan takawar da kanta mayar dashi tayi kan meer shima haka tayi masa,    "saida ta dauki loƙaci me tsawo batare da ta iya budar baki ba tayi magana,     duk sun ƙosa da suji tayi magana amma taƙi yi,   A ina nake nan, nan gidan waye?   sukaji ta jefo musu tambaya bayan kuma kafin ta kwanta sungama magana da ita amma yanzu taƙara tambayar su ko da yake bai kamata ma suyi wannan tunanin tunda yanzu tadawo hayyacin ta watakil ta manta tattauna warsu, ' Ummu ce ta zauna adayen gefen nata tare da riko hannun bata wani dau lokaci ba kawai tayi mata bayanin yanda komai yafaru bata rage mata komai ba har zuwa yau da akayi mata ruƙeya komai Saida taba ta labari, "kuka tasakar musu jin yanda rayuwar ta takoma tsawon wasu shekaru sosai take kuka abun ba ƙaramin ciwo yayi mata ba ace tana gidan sarauta da iyayen da daginta da ƴan uwanta da mijin ta ga ɗan ta da tahaifa babude abun da ta rasa amma ace rayuwar ta taso ahaka kuma batare da kowa ya neme ta ba wannan wacce irin ƙaddara ce ta same ta wane irin zunubi ta aikata musu da har zasuyi watsi da ita haka shin wai nema yafito da ita daga cikin gidan tamabayar da tafi tsaya mata arai kenan, "cikin kukan tayi musu godiya da irin dawainiyar da sukayi da ita har ta samu lafiya, nan suma suka nuna mata ai bakomai ayi yiwa kaine har suna nunamata rashin jin dadin yawan godiyar datake tayi musu dan su har kunyama suke ji, ' da ƙyar suka samu tayi shiru da kukan da takeyi sannan, Ummy ta gyara zama tare da cewa Abu ka zauna mana, kujera yasamu yazauna sanshi yama manta atsaye saboda gaba ɗaya hankali sa yana kan ta, shiru falon yadauka na wasu yan daƙiƙu ,kafin daga bisani ummy ta katse shirun nasu, dacewa baiwar Allah inba damuwa ko zamu iya sanin ko ke wacece kuma daga ina kika fito dan inafatan yanzu kin tuna komai, ko ba hakaba ? "idan bangaya muku ba suwa zan gayawa ai kungama yimin komai arayuwa badan kuba ai da tuni na dade da mutuwa amma kukataimakeni wanda su ƴan uwana babu wanda ya nemeni ace har inkai tsawon wannan loƙacin bana tare dasu amma babu wanda ya nemeni ko kunji ana cigiyata ta ƙarasa maganar cikin raunin murya dan ita aganin ta tanaganin a iya saninta suna da mukami da da kudin da za'ace sun nemi inda suke a matsayin su na manya sanannu acikin garin amma ace babu wanda yayi cigiyarta ta tabbata da sunyi da tabbas zasu samu labarin ta tundade ba ƙasar ta bari gaskiya abun ba ƙaramin taba mata zuciya yayi ba, "gaskiya baiwar Allah bamu da masaniya akai sunyi cigiyar ki ko basuyiba saboda kinga mu ba ƴan nan bane daga baya muka dawo kuma da muka dawo gaskiya mude bamujiba Allah masani sunyi ko basuyiba, "ummy ce duk take wannan maganar, "basuyi bama ai dasunyi da tuni sunji inda nake tafaɗa ahankali taƙarasa maganar tare da share hawayen da suka tarar mata a ido, "kiyi hakuri kar kice haka dan Allah kidena faɗar haka nasan bazasu taba yi miki haka ba kinga ance ai da sihiri aka koreki daga gidan kinga watakil dole da wani abu aƙasa shiyasa kikaji basu nemeki ba amma nasan hakannan bazasuƙi nemankiba yanzu kawai kifada inda kike sai muje gaba ɗayan mu mukaiki har gida, "girgiza musu kai tayi tace ba inda zani tunda basu nemeni ba nima bazan nemesuba zande sa adauko min ɗana shikaɗai nakeson gani, Abu ya ce haba dan Allah wacce irin magana kike haka yaza ayi suƙi neman ki kinsan dole sun nemeki amma basu sameki kina da ƴan uwa fa kuma suna sonki dan haka duk inda ma suke tunanin neman ki nasan sunduba watakil ma gajiya sukayi da suka dena neman ki ko kuma ba gari daya kuke ba shiyasa cigiyar tasu da sukeyi batazo garin da kikeba kinga waɗanda suka kawo ki nan sunce agombe suka sameki kuma duk sunyi cigiya suma agarin Gomben amma basuji wani wanda yace yasanki ba tabbacin ke ba ƴar garin bace yakamata koyi musu kyakkyawar fahimta baikamata kina ganin kamar sonkine basayi da yasa basu nemeki ba, bayan Abu yagama nasa Ummy ma ta ɗora da nata sosai suka sa jikinta yayi sanyi bata ƙara cewa komai ba a game da rashin komwarta cikin danginta duk dade wani ɓnagaren na zuciyar ta yana bata kar takoma din, 'batace musu ta amince ba bata cemusu bata amince ba tayi shiru kawai, muna sauraron ki ummy taƙara katse shirun nasu, " A kano nake dazama Sunana *SABREENA* ni asalana ba ƴar ƙasar nan bace ƴar Sudan ce acan duk ƴan uwana suke amma banida iyaye iyayena duk Allah yayi musu rasuwa saboda accident da yasame su tun ina yarinya, Ina hannun ƙanin mahaifina loƙacin danafara karatu a Egypt annan na hadu da wani muka fara soyayya bayan nan kuma har maganar aure ta shiga tsakanin mu ƙanin mahaifina ya amince yabashi aurena sanadin hakan yasani baro can nadawo nan ƙasar da zama, ashe wanda na aura dan sarki ne loƙacin auren mu kuma loƙacin aka basa sarauta yazama sarki arana daya akadauramana aure tare da kishiyata da kuma nadin sarautar sa duk arana daya akayi, ina da yara biyu kuma duk maza amma daya ya ɓata har dakina aka shiga adauke minshi kuma akaƙi fito dashi wannan abun yamin ciwo amma haka na haƙura ban tada hankali na bawai dan banaso ba kawai dan asamu kwanciyar hankali, nadaɗe ba Allah yaƙara bani wani ɗan gashi yanzu shima anrabani dashi tun yana ɗan ƙarami nasan Allah sarki sameer duk ƙulaficin sa dani gashi ya taso batare dani ba ko yanzu yana ina ko me yakeyi nasan yanzu ya girma wataƙila ma yayi aure ko kuma ya mutu Allah masani shikaɗai nakeson gani...taƙarasa maganar cikin sanyin murya harda dan sakin murmushin dole saboda tunawa da tayi dashi tare da sa hannu ta share hawayen ta, gaba dayansu tausayi yabasu jin yanda ta ƙarasa maganar sun san tana jin ciwon abun aranta, shiru sukayi sunkasa magana kowa yana nasa kallar tunani ashe nan matar sarkice azaune agabansu cikin wannan halin lalle dole ajinjinawa duk wanda yayi sanadin barin ta gidan nan dan sun fahimci dole anasane aka koreta zaman tane kawai ba aso shiyasa akayi mata haka sai kuma gashi Allah ya yafisu ya tashi kafaɗunta sosai kowa yafaɗa duniya tunani kowa da kallar tunanin da yake yi, MEER da sai yanzu yasamu bakin magana yace to me yasakika fita daga ciki ko masarautar ba tsarone? kallon sa tayi jin tambayarda yayi mata yasata sakin murmushi me ciwo sannan tace yaro bani na fita dakaina ba fitar dani akayi ta dole saboda son zaciya daman sarauta ta gaji haka ba a iya zaman lafiya aciki duk da bansan waye ya aikata min hakan ba amma masan dole acikin kishiyoyi na ne kamar yanda naji kunce malam Yahaya muku kuma badan komai sukayi hakan ba sai dan saboda kawai ina da ɗa namiji shiyasa sukayi min haka da sun kwantar da hankalin suma ni daman basarautar nake soba koda yagirma bazan taɓa bari ya hau kan mulki ba saboda iya fara zamana acikin sa na fahimci abubuwa da dama shiyasa banayiwa ɗana sha'awar sa,   "amma saboda rashin sani da son zuciya irin nasu suka zaɓi jefa rayuwara ta cikin garari bayan sace min da da sukayi duk nayi shiru na rabu dasu yanzu kuma sun tarwatsa  rayuwata da ta ɗana wayasani na ko shima sun kasheshi tunda basason ganin gudan jinina adoraon duniya, shiru ta ɗanyi wani abu na taso mata daga ƙasan zuciya cikin ɓacin rai tafara magana adake tare da damke hannun ta tace ada na rabu dasu amma wallahi wallahi wallahi yanzu bazan rabu dasu sai na shigar dasu ƙara sai sun fito min da ƴaƴana kuma anbimin haƙƙina da suka zalince na rabani da ƴaƴana da kuma jefa rayuwata irin cikin wannan halin nayi shekara da shekaru akwance wallahi bazan taɓa yafe musu ba sai na dauki fansa saina biwa ƴaƴana haƙƙin su na rabasu da gidan ubansu da sukayi idan kuma kashe su sukayi suma sai na kashe su da hannu na duk wani me hannu acikin tarwatsa rayuwata da ta ƴaƴana sai yagane kuren su koda mahaifin sune keda hannu acikin wallahi bazan barsa sai naga bayansu ɗaya bayan ɗaya, nasan bantaso cikin gata ba bansan dadin iyaye ba amma naso inbawa nawa ƴaƴan kulawa fiye da yadda nataso amma suntaso cikin iyayen su cikin gata amma wasu banzayen mugayen masu son kansu sunzo sun lalata komai tunda na taso nake fuskantar wahala arayuwata nayi auren ma masamu miji me sona ina murnar rayuwata zatayi daɗi amma suka juya komai to wallahi ƙarya kuke yanda kuka tarwatsa ni kuma sai naga bayan ku bazan taɓa bari kucigaba dajin daɗin rayuwa ba duk wata hanya ta farin ciki sai na katse muku ita da zarar na dora ƙafata acikin garin Kano kowa sai nasaka shi girbar abun da ya shuka na rantse da wanda raina ke hannun sa taƙarasa maganar cikin ɗaga murya kamar su sukayi mata laifin ko kuma waɗanda sukayi laifin suna gabanta haka take magana tana wani huci idonta duk sun firfito waje sunyi jaa kana ganin su kasan tsantsar ɓacin raine acikin su zuciyar ga kuwa jitake kamar ana gasata da garwashin wuta  sai tafarfasa take, gaba ɗayan su babu wanda bai tsorata da yanayin ta ba ganin loƙaci daya ta burkice sai sambatu take kamar ma bata cikin hayyacin ta idan sukayi tunani kuma sai suga dole tayi fiye da hakama saboda kowa ma akayi wa haka dole yaji ciwo aransa dan haka basuga laifin taba, "cikin daga murya tare da sakin wani kukan me ciwo tace ƙarya kuke wallahi sai naga bayanku dakain zan kwatar musu ƴanci sarautar kuma da bakwaso suyi sai sunyi uban wani yahana idan ya isa azzalumai kawai mugaye duk inda ƴaƴana suke sai naje na nemosu dan nasan basu mutu ba suna raye kuma zanje duk inda suke zankawo muku su har inda kuke...!!!! ( Ehhh... jaruma marar tsoro sabreena🤣😂sai dake😜) karfa wani yace banda tausayi jarumtar tatace ta burgeni shiyasa na ɗan dara sannan daga baya nayata jimamin daga baya Allah sarki taban tausayi😱) taƙarasa maganar tare da  buga hannu ta akan kujera sannan ta miƙe tsaye tana ƙara sakin wani kukan tana rufe bakin da hannun ta saboda ta fahimci idan batayi wasa ba kuka ne zai ɓalle mata me sauti hanyar wajen ƙofa ta nufa dan ita kanta wasu maganganun bata san tanayinsu dan tafara fita hayyacin ta sai yanzu wasu abubuwan suka shiga dawomata nadaga irin rayuwar da tayi acikin gidan shiyasa abun yake ƙara yimata ciwo take ta faman zuba batare da tasan abun da take cewa ba, da sauri sukayi kanta gaba ɗayan su,    ummy ce tayi saurin rungumeta itama tana sakin kuka cikin kukan take tabata hakuri banda haƙuri babu abun da takeyi sai kuma kuka ita kukan nata ma har yaso yafi na nata saboda tsabar tausayi (kunsan mata da rauni abu kadan ma kuka yake sakasu bare taga babbar mace agabanta tana kuka dole itama ta zubar da nata)      Abu da meer duk tsaye sukayi suna kallon su kowa yakasa magana dan suma abun ba ƙaramin raɗaɗi yayi musu ba suma kawai daurewa suke amma zuciyar su ba ƙaramin karaya tayi ba dande mazane shiysa basuyi mata kuka ba ammade tabasu tausayi iya tausayi kai duk wanda yaga yana yin datake magana tana kuka dole ya tausayawa mata halin da take ciki, Abune yadafa su gaba ɗayan su yashiga rarrashin su sannan ya kamo hannusu yamaida su kan kujera ya zaunar dasu saidai yana zaunar dasu ma'ana(sabreena) ta ƙara miƙewa tsaye tare da cewa nifa bazan ƙara zama ako ina ba ayau nake so zuwa kano duk dare agarin Kano nake son kwana dan inbagani acan ba zuciya ta bazata taɓa samun kwanciyar hankali ba dan haka kawai kubarni intafi nagode da kulawar da kuka bani da kuma irin taimakon da kukayi min bazan taba mantawa daku ba Allah yabiyaku da mafificin alkhairi nasan kungama yimin komai badan kuba da tuni wani zance ake ba wannan da tuni ina nan akwance kamar yanda sukeso su taganin na ahaka, dan haka dan Allah kurabudani in tafi ko nasamu sauƙin abun da nakeji idan naje a aiwatar da ƙudurina, yanzu zan tafi Allah yabar yabiyaku idan komai ya tafi yanda nake so har nan zan kawo muku ƴaƴana kugansu zan kawo muku ziyara dan bazan taɓa mantawa daku ba acikin rayuwata kuɗin na musamman ne agareni nabaku wani gurbi acikin raina domin kuntaka muhimmiyar rawa acikin rayuwata duk godiyar da zanyi muku bazan taɓa biyanku taimakon da kukayi min, ni zan wuce Allah yaƙaddara saduwar mu tafaɗa tana ƙara miƙewa tsaye da sauri ummy tayi saurin dafa kafaɗunta ta tace dan Allah kaikitafi kibarmu kibari mutafi tare muma bamason kiyi mana nisa duk inda zaki munata tare dake zamu biki tayi maganar ta ƙokarin ganin ta zauna amma bata zauna ba taci gaba datsayiyuwa batare da ta tafi ba......✍️                                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(mrs bmb) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)             [6/9, 10:08 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️53&54 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     "Abu ne ya fara yi mata magana cikin  sanyin murya yafara cewa baiwar Allah kiyi haƙuri banga lafinki ba nahakan amma de zakai kiyi haƙuri abi komai asannu baikamata kije ahakaba kibari sai mun fara bincike kafin kije cikin gidan tunda kikaga haka tofa ba ƙaramin abune me sauƙi gurin gano koma waya yi miki haka Yakamata mufara zama ayi nazari akan  waɗanda kuke mu'amala dasu da kuma abun da yataɓata shiga tsakanin ku na saɓani ko makaman ci haka ko kuma faɗa dade sauran abun da ba arasa na zamantakewar yau da kullum wannan ce hanya me sauƙi kawai wajen gano wanda ya aikata miki hakan amma garaje da sauri duk bana mubane sai munbi komai asannu amma dan Allah ki ajiye batun tafiya ke kadai kibari tare zamu tafi sai mufara binciken ko ya kikace shiru yayi yana jiran jin amsarta       " shiru tayi tana nazarin maganganun sa kafin daga bisani ta kalle sa sannan tace naji bayanin ka kuma hakan yakamata ayi banyi Wannan tunani kwata kwata idona ya rufe tabbas bincike yakamata infarayi kafin su san da inaraye dan nasan yanzu gaba ɗayan su babu wanda baiyi tunanin na mutu ba mugaye kawai wallahi inna tuna abun da sukayi min sai naji kamar yanzu inganni agaban su in caccaka musu wuƙa musamman ma idan na tuna raba ni da ƴaƴana da sukayi tsakanina dasu saidai Allah ya isa Allah ya tona asirin su, "Ameen duk suka amsa mata dashi"   bayan tayi shiru ta cigaba da cewa  ammade kuyi hakuri bazan iya zaman nan ba zantafi kano acan zan zauna inyaso duk abun da zanyi nayi acan,   "ummy tace ai ba matsala duk sai mukoma can din amma to idan munje a ina zamu sauka?    Abu yaya saurin tarar numfashin ta kafin maama tayi magana yace habade gurin zama ai bazai mana wahala ba akwai wani abokina acan sai insakashi ya samo mana gida asaka duk abun da ake buƙata sai kawai mukoma gabaɗayan mu,     "Nifa yau nake son tafiya maama taƙara gaya musu,    "Abu ne ya bata amsa da cewa maama yanzu fa babu loƙaci kinga la'asr ta wuce magariba ake shirin yi kafin muce munje ai dare zaiyi mana kuma kinga ko gidan da zamu zauna ba asamu ba idan munje ina zamu sauka acikin dare, kiyi haƙuri kibari ko nan da jibi ko gata sai mutafi San  anshirya komai atsanake,    batare da ta tanka masa ba ta juyar dakai tayi irin alamun nifa ko me zakuce bazan yarda ba,      jin shirun nata yasa Ummy ƙara bata baki akan tabari din sa tafi nan da jibin ko gata, amma itama tace a'a itafa bataso ta kwana ako ina inba Kano ba batason ta ƙara kwana awani wajen sai acan garin,    duk yanda zasuyi mata bayani ta fahimta tabari din amma taƙi aminta tace ko ita kaɗai ce su rabu da ita ta tafi idan yaso su sako duk sanda suka shirya,        "meer ne yasaka baki shima ya gwada sa'arsa yace dan Allah kekwa kibari mana ko zuwa gobe amma yanzu kafin kije dare zaiyi sosai ga hanya bata da kyau sai kinke ansace ki  ahanya kinga ba ke ba daukar fansa kuma bazaki ga ƴaƴan naki dakikeso kigani ba, amma inbaki yarda ba   ga hanya nan inkinfi so a kwamishi ki sai ki tafi saidai muce ki gaida waɗanda suka kwamishe ki dan ba inda zamu,     "zazzara ido ta shiga ys tana tunanin maganar sa to kode da gaske yake kai kumafa hakan zata iya faruwa asace tadin koma aje idan ansace ta din aje akasheta ma gaba ɗaya kai inaa tafasa tafiya saboda maganar gaskiya ta yarda da maganar sa kuma tana tsoron hakan,       "dan murmushi Abu yasaki irin nasu na manya, yana ɗan satar kallon ganin yanda tayi zuru zuru da ita alamar tsoro, fakar idon ta yayi ya kalli meer tare da daga masa gira sannan yayi masa alama da hannu da yacigaba da abun da yake ma'ana yaci gaba da tsoratar da ita ɗin,   dan ya fahimci wannan tsohuwar taurin kai zatai baza a iya lankwasa ta  sauƙin rai ba dole sai da dabara,     "Meer yacigaba da cewa Ni wallahi ma kitaso in rakaki ki hau mota amma mu fara yin sallamar bankwana dan nasan bazamu ƙara haɗuwa ba saidai muce Allah ya jiƙanki dan kamar sunan ki gawa suna daukarki zasuje suyi romon ki abawa dodo jinin ki ya shanye shikenan ke kuma saidai idan munzauan muce Allah sarki baiwar Allah nan da muka taɓa haɗuwa da ita ansace ta akan hanyar ta ta tafiya daukar fansa da take ƙudirin yi,   "dan Allah yaro wai da gaske kake tafaɗa cikin nuna tsoron ta afili kai yaɗaga mata tare da cewa gasu Ummy ki tambaye su kiji idanni kin ƙarya ta ni idan kikaji daga bakin su sai kifi yarda tunda ni kin maidani maƙarya ci yanzu.... kaga ni rufe min baki da jawowa mutane bala'i fayaƙu khairan au liyasmut(kafaɗi alkhairi ko kai shiru),       da haka suka ci gaba da tsoratar da ita gaba ɗayan su babu wanda bai faɗi albarkacin bakin sa ba wajen tsoratar da ita ɗin aikam kuma sun ci nasara dan ta tsorata kam ba ƙarya amma fa duk da haka bata ce musu tayarda zata zauna ɗin ba,   saida suka sha wahala kafin ta amince musu shima kuma zuwa gobe da safe suka ce mata sun yarda da hakan, bayan da suka iya dole suka fara shirye shiryen tafiya kano gobe,   tun aloƙacin batare da kowa ya tafi ba Abu yakira abokin nasa yasanar masa buƙatar sa ya kuma tabbatar masa da zuwa gobe yake son komai ya kammala, abokin nasa ya amsa masa da angama bashida matsala za'asamu ko yau yake so zaiyi ƙoƙari yasa asamomu su,   nande yayi masa godiya sannan sukayi sallama, anan sukaci gaba da zama har aka kira sallar magariba sannan suka tashi Abu da meer suka ta tashi suka tafi masallaci ita kuma Ummy ta kai maama dakin da ta kaita ɗazu tana nuna mata de komai sannan ta fita itama dan gabatar da tata sallar,                 *Kano* *___S&S__ sam&sumy     "kiran sallar magariba ne ya farkar dashi daga baccin da ya daukeshi ba shiri,   ahankali ya shiga buɗe idonsa bai tun yana ganin dishi dishi har ya ware su amma baigama tantance a inda yake ba, dan yana budesu yaƙara rufesu tare da ɗaga hannayensa zaiyi  miƙa dan yama manta a inda yake yana ɗaga hannu sai ya bude idon sa basu sauka ako ina ba  sai suka sauka akanta da take kwance kan cinyar sa bacci yasa daga kan kafaɗar sa ta dawo kan cinyar sa baccin ta take hankali ta kwance kamar tana ɗakin uwarta.. ai baigama yin miƙar ba ya katseta tare da zaro ido da mamakin kansa sai yanzu ya tuna wai bacci yayi agurin nan zuba mata idanu yayi yana kallon ta ganin ko motsawa ma batayi baccin ta kawai take yana so ya motsa amma yakasa hakannan yaji bayaso ya tashe ta, mayar da kansa yayi jikin seat din motar tare da ƙara lumshe idon sa hakan nan yaji duk wata kasala ta saukar masa kodan daman ance ba kyau bacci bayan sallar la'asr idan ka tashi sai kaji jikin duk ya mutu ga ɓacin ra da zaka tashi dashi to watakila shima hakan ce ta faru dashi,     yana ahaka shi ba bacci ba shi ba ido biyu ba yanajin har aka tayar da sallah a masallaci amma yakasa motsawa Saida aka kusa idarwa sannan yasamu damar buɗe idon sa still de ya da take tunɗazu ha take har yanzu bata motsaba, ahankali ya shiga ɗaga hannun sa za tashe ta sai kuma yafasa yana tunani ta yanda zai tashe ta din tsoron shima kar ya tasheta tazo taci gaba da yi masa kuka kamar ɗazu,     ba yanda ya iya haka ya daure yakai hannun sa zai ɗan daki gefen ta sai kawai yaga tayi juyi ta juyo da fuskarta gabansa da fuskarta can wajen staring take kalla yanzu kuma da ta juyo sai yazamana suna facing din juna yana kallon fuskarta sosai, acikin rashin sani cikin magagin bacci ta ɗora hannun ta akan cinyar sa ashe shikuma hannun ta tunda ba controlling dinsa akeba sai ya wuce inda ba a akeshiba, ya sauka akan Alulun sa (bana dinsa sandar girman sa) , zabura yayi jin inda ta taɓa tare da kallon gurin zaro ido yayi ganin batama san tanayi ba kuma hannun nata nakan Alulun sa bata cire ba runtsi ido yayi ƙam jin wani abu ya taho masa tundaga kan ɗan yatsan sa ƙafa harzuwa can ƙololuwar kwanyar kansa take yaji jikin yayi masa yimmm gaba ɗaya sai kace wanda sanyi yake shiga haka yake jinsa yimmm abu na mishi yawo acikin kansa, shide tunda yake baitaɓa tsintar kansa cikin irin wannan yanayin ba duk dazaman waje da yayi amma baitaɓa riqe wata maceba bare har ya haɗa jiki da ita bare kuma takai ga antaɓa masa babbar masarautar sa, shiyasa yake jin abun kamar a mafarki kamar ba gaskiya ba wai yau shine guri ɗaya da mace kuma ta kwanta masa akan jikin sa harda taɓasa amma yakasa ɗaukar mataki lalle wannan yarinyar ba ƙaramar sa'ace da ita ba data nemi dagula masa lissafi loƙaci guda, dafe kansa yayi kawai tare da ƙanƙame idon sa sannan ya budesu duk aloƙaci guda sannan yakai hannun sa kan nata hannun da niyar ya dauke shi daga kansa sai kawai yaga tajanye hannun tare da ɗora kanta akan hannun ta kuma still de agurin ta ƙara kwanciya tana wani mitsin mitsin da bakai alamar de bacci yaƙara yi mata daɗi tashi ba yanzu ba kenan, Oh my God yafaɗa a fili tare da kaima ta dukan da bai shirya ba dan ya fahimci inyaci gaba da biye mata za a iya samun matsala kuma shine aruwa shiyasa ya ɗalamata duka a dantsen ta na hannu,. azabure ta tashi zaune ba shiri tana warwaro manyan idanun ta waje kamar zasu faɗo tare da dafa gurin da yadake ta dan taji zafi sosai cikin motar ta shiga bi da kallo tare da juyawa wajen window tanakallon waje ganin duhu yasata juyowa da sauri ta kalle sa tace naga dare yayi me nufinka tun ɗazu ina cikin motar nan tungari da haske fa muka taho amma yanzu inga dare yayi ya akai hakan ta faru dan Allah me kayimin meyasa nakai tsawon wannan loƙacin kagafa dare yayi wayyo Allah na Abbana na shiga uku na dan Allah ka faɗa mun abun da ka bani nasha da yasa na fita hayyacina har nakai tsawon wannan loƙacin dan Allah ka gaya min?   duk surutun da take masa bai tankama ta ba kuma baya jin zai iya  tanka mata ɗin ahalin yanzu  saboda halin da ya kuma tsintar kansa bayan ta tashima daga kan sa yafi jin abun akan yanzu akan ɗazu, magana fa nake maka kayi min banza ka gayamin abun da kayi min acikin motar nan tafaɗa tare da ɗan daga murya, yanzuma banza yayi mata sai kawai ma ya kifa kansa akan staring din motar yana damke ido shi kadai yasan yanda yake ji sauƙin sama ɗaya batasan abun dake faruwa ba yasan da shikenan rainasa zatayi amma tunda batasan aika aikan da tayi masa shikenan gwara yayi mata banza dan hakan sai yafiye masa, magana taƙara yi masa yagaya mata meyasa takai wannan loƙacin acikin motarsa amma nan ma bashiru ba amsa, haka taci gaba dayi masa bala'i tana ɗaga murya saboda shirun da yayi mata ba ƙaramin hassalata yake ba,   jin ta damesa ta isheshi ta takura masa yasashi ɗan ɗagowa batare da ya kalleta ya kalli gefe sannan yace fitar min amota  yafaɗa alamun rai aɓace,     bazan fita ba sai ka gaya min abun daya faru dani yaza ayi ina maka magana kayi min banza kagaya min abun da kayi min,    "Jijjiga kai kawai yakeyi kiris yake jira dan tagama kaishi ƙarshe kawaide yana ɗan ɗaga mata ƙafane saboda yasan shine bashi da gaskiya kuma bama yaso ta fahimci halin da yake ciki tafara zargin wani abun shiyasa amma badan hakaba da tuni ya fita ya buɗe mata ƙofa ya jefata waje,     "so yake kawai  tafita yana buƙatar zama shikaɗai amma sai ɓata masa loƙaci takeyi ganin hakan yasashi miƙa hannu  batare da ya kalleta ba ya buɗe mata ƙofa yace fita kuma bai matsa daga jikin motar ba dan hannun sa har hana gogan ƙirjin ta ɗan baya tayi tana mannewa jikin kujera numfashin ta har daukewa yakeyi  saboda kusancin da sukayi Allah Allah take ya matsa amma yaƙi matsawa jin yaƙi matsawa yasa ta bude idon ta da ta rufesu, tana budewa suka haɗa ido da ita harara ya wurga mata tare da yayimata kallon up and down ganin yanda duk ta bi ta takure ajikin kujerar wai duk dan kar ya taɓata, tsaki yaja cikin ƙasa ƙasa da murya yace ai ke kin iya taɓa wani tare da matsawa daga gurin yakoma kan kujerar sa, sarai taji abun da yace amma takasa fahimtar inda maganar tasa ta dosa, itama tsakin taja kamar yanda yayi mata tace zamu kwana anan kenan dan ba inda zani sai naji abun da kayi min wayasani ma ko wani abun ka shaƙamin ka kaini wani wajen daban Allah kaɗai yasan adadin cutarwar da kayi min ayau saidai ince Allah yasakamin Kuma wallahi Allah ya issss..... bum taji ya doke mata baki, rau rau tayi da ido hawaye har sun taru a idon ta, ' dafe bakin tayi da hannu dan baƙaramin zafi taji ba aranta taci gaba da jera masa Allah ya isa mugu azzalumi ba kalar zagin da batayi masa ba amma acikin ranta, muryar sace ta katse mata abun da takeyi, zaki fita ko sai nayi maganin ki yayi maganar a ɗan fusace dan yagaji da abun da take masa, itama afusacen cike da taƙaicin dukar mata baki da yayi tace " sai naji inda ka kaini tsawon wannan loƙacin kamo kwalar hijabin ta yayi tare da jawota daf da fuskarsa har suna iya jin numfashin junan su zuba mata rikitattun idanun su da har yanzu basu gama dawowa daidai ba, kasa jura tayi kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke idon ganin irin kallon da yake mata yasa taki loƙaci ɗaya tsoro ya dirar mata taji ma takasa faɗa masa abun da tayi niyya, look at me taji yace mata amma sai ta kasa ɗagowa ta kalle sa, "kinaso kiji abun danayi miki right? sai yanzu ta ɗago ta kallesa ido cikin ido sannan tace "eh" wani gida nakaiki nayi miki ciki..! pls kuyi haƙuri zaku ga kwana biyu banayi dayawa wani sa'in ma banayi gaba ɗaya wallahi biki mukeyi wannan satin nayi busy dayawa sai ahankali,                                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)             [6/14, 8:40 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️55&56 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️        "kinaso kiji abun danayi miki right?   sai yanzu ta ɗago ta kallesa ido cikin ido sannan tace "eh"    "wani gida nakaiki nayi miki ciki..!!   zaro ido tayi tare da ware su akan sa bata taɓa tunanin jin hakan daga gare sa  ba ita duk atunanin ta zai nuna wata rashin gaskiya daga tambayar datayi masa bata taɓa kawo hakan ba sai taji dama bata tambaye sa ba da tasan zai iya gaya mata wannan maganar,  " tazata irin zaiyi mata wani kwana kwana yanda zatasamu damar yi masa abun da taga dama amma saitaji akasin haka shi ko kunyar faɗan cikin beye ba duk da tasan ma bahakan bane ashe sarai tasan bacci tayi amma take masa wannan tambayar daman ance tabarmar kunya da hauka ake naɗeta dan kar yakawo mata wani zancen akan ta kwanta masa ajiki shiyasa tayi masa haka ashe daidai da ita yake, cike da borin kunya ta sunkuyar da kanta tare da ƙoƙarin kwace kanta daga riƙon da yayi mata daman ya riga da ya buɗe motar tun ɗazu dan haka bata yarda taƙara haɗa ido dashi ba tayi saurin juyawa zata fita ya riƙo hijabin ta tsayawa tayi cak batare da ta juyo ba, murya na rawa tace ni kasakeni dan Allah banason kallar iskancin nan dakakeyi min duk kazo ka addabi rayuwata ni wallahi nayi danasnin sanin ka ayau din nan yau baƙar ranace agareni ranar da bazan taɓa mantawa ba ka cuceni ka cutar min da mahaifi kaje kai da Allah, Allah ya fika mugu kawai mayaudari tana faɗa tayi saurin kwace hijabi ɗin ta tare da fita daga motar sai da tafita sannan ta juyo tace ɗan iska kawai badai cikin ka ajikina ba saidai kaje kayi da waɗanda kasaba mutum banda latsa ƴaƴan mutane ba abun da ya iya mtssww taja tsaki ganin ya yunƙura kamar zai fito yasa ta kwasa aguje sai kace ƙaramar yarinya haka ta kama gudu, ' tsayawa yayi ta cikin motar yana kallon ta baisan loƙacin da yasaki wani ƙayataccen murmushi ba gudun nata ba ƙaramin burge sa yayi ba ga tsoro ga rashin kunya, ya zuba mata ido saboda haryanzu ba abuɗe mata ƙofa ba sai faman bugawa take da ƙarfi ta ayi tana juyowa dan ganin kartaje yafito yakama ta, yana sane dan yaga yazatayi sai kawai ya buɗe motar ya fito, duk da darene amma hasken kwan na ƙofar gidan su bai hanasa ganin yanda tazaro idanu ba kamar zatayi kuka tana ɗan manmannewa ajikin gateɗin kamar zata shige ciki kuma bata bar kwankwasa ƙofar datakeyi ba amma har yanzu ba a buɗe ba, ahankali yashiga takawa zuwa inda take acikin ransa dariya ce take cinsa amma a zahiri sai ya wani haɗe rai kamar me shirin zuwa dambe, jitakeyi kamar ta nutse dan batason yakamata wani bugun ta ƙara kaiwa ƙofar da ƙarfin tsiya, yana daf da ita yakusa zuwa inda take dan har ta saddaƙar ma yakamata kawai taji an buɗe ƙofar da sauri kaamr wacce aka hankaɗa ciki haka tayi saurin faɗawa gidan har tana ture me gadin da ya buɗe mata ƙofar, "tana shiga ta turo ƙofar da ƙarfi, ganin ta shige yasashi yin ƙwafa tare da juyawa aransa yace Allah ya taimakeki yarinya da kinga yanda ake iskanci, yana cikin tafiya yajiyo muryar tanacewa wooooo aide baka kamani ba inka isa ka dawo wooooo woooo juyowa yayi ahankali yana binta da kallo tunda ga up har down ganin ta yayi ta zuro kai tana leƙensa suna haɗa ido tayi masa gwalo tana hararar sa jinjina kai kawai yayi ya juya yatafi yana mamakin irin shirmen da takeyi da yaganta doguwar yayi tunanin wata babbace ashe girmanne ya riga hankalin zuwa yarintace kawai take ɗawainiya da ita dole yayi mata uzurin wasu abubuwan da take masa, yana ta tunanin shirmenta har ya ƙarasa wajen motar ya buɗe ya shiga har yanzu bata bar bakin ƙofar ba tana tsaye tana kallon sa har ya shiga mota ba ɓata loƙaci yayiwa motar key sannan yaja batare da ya ƙara kallon inda takeba yayi gaba abun sa, saida taga shiga motarsa da tafiyar sa sannan ta koma ciki ta rufe ƙofar tana sauke ajiyar zuciya dan har ga Allah tagama tsorata ɗazu da ba abuɗe gidan ba tasan da bazai taɓa rabuwa da itaba da yakamata saitagane kurenta, cikin gidan ta nufa har taje bakin ƙofa sai kuma wani tunani ya faɗo mata burki taja ta tsaya gaban ta na faɗuwa yanzu me zata gayawa wannan masifaffiyar matar idan ta tambayeta inda taje bataso ta gaya mata cewar wasu sun kama mahaifinta kuma batasan ƙaryar da zata haɗa mata ta yarda da itaba, sosai ta shiga tunanin abunyi, tana tsaye agun tana tunanin mafita taji ance to munafuka kini babbiya kinje kingama yawon biɗiɗin naki zaki tsaya kina ɓoye ɓoye saboda tsabar kawarewa da barikanci ko inda sabo ai nasaba da wannan munafurcin naki sai kinsan kinje ki aikato alfasha ɗinki saikizo kina rarrabewa awaje shi saurayin da yazo ya ɗaukeki loƙacin bakiji kunyar fita ba har Saida kikaje ki ka sauke abun da yake damunki idan bakiyi ba bakyajin daɗi to hankalin ki ya kwanta kinje kin aikato abun da kika saba sai ki wuce ciki kuma wallahi kin kusan barin gidan nan gwara ki tattara inainaki inaki kibarmin gida dan bazan cigaba da daukar wannan iskancin naki ba nan gaba ki lalata min ƴaƴa shigiya munafuka kin wuce ko sainayi ball dake anan gurin, Sunkuyar da kanta tayi idon ta har yakawo kwalla kanta aƙasa tabi ta gefen matar datake tsaye abakin ƙofar tana zazzaga mata wannan masifar, dundu ta buga mata abaya loƙacin da tazo daidai da ita sannan ta ɗora dacewa Allah wadaran da halinki kullum cikin hijabi harƙasa saboda tsabar kwarewa a karuwanci shiyasa kowa yake cewa ba ruwanki saboda basaja dakike musu da hijabi sumimi kasum basu san musa abaka fir'auna azuci bace ke, itade bata kula taba tayi wucewar ta ɗaki ita kuma matar ta tsaya taci gaba da ɗaga murya tana zazzaga mata masifa da jifanta da baƙaƙen magan ganun da duk suka zo bakin ta taitayi ko gajiya ma batayi ba anƙi kulata amma takasa denawa, sumy na shiga ɗaki ta faɗa kan gadonta ta kifa kai ajikin filo ta shiga raira kuka tana cikin kukan taji wayar ta ta shiga ringing kin ɗagowa tayi bare ta amsa wayar bayan kiran ya katse wani ya ƙara shigowa jin antakura taɗan tsagaita da kukan tare d jawo wayar batare da ta duba me kiran ba ta ɗaga wayar haɗi da karawa akunne tayi shiru tana jiran taji me magana, kamar amafarki muryarsa ta daki dodon kunnen ta cire wayar tayi akunne ta tare da kallon number tabbas itace ta faɗa aranta mayarwa tayi kan kunnen ta, "ko baki ji me nace ba ne" memakon tabashi amsa kawai sai tafashe da kuka sosai takeyin kukan kamar ranta zai fita ita kanta bata san loƙacin da ta fara irin wannan kukan ba daga jin murya sa duk daman kukan take amma na yanzu yafi naɗazu batasan dalili ba kuma kodan shi yaja mata akayi mata faɗan saboda baisan shiba da yanzu tana nan hankalin ta akwance haushi biyu ne ya haɗar mata loƙaci guda dan haka kwa taci gaba da kukan ta ba ƙaƙƙautawa duk maganar da yake mata bata tsaya ta saurare sa ba, "gefen titi yasamu yayi parkin jin yanda take kuka hankalin sa ba ƙaramin tashi yayi ba hankali tashe da mamakin abun da yasata kuka haka ya shiga tambayar ta abun da yake damun ta amma kamar ma ya ƙara zigata yake, wani kukan take bata ko tsagaitawa kuma bata kashe wayar ba, shiru shima yayi kawai yana sauraron sautin kukan nata da yakejin sa kamar daga ƙasan zuciyar sa yake, bai ƙara yin magana ba bai kuma kashe wayar ba itama kuma haka bata fasa kukan ba kuma bata kashe wayar ba haka sukai ta tsayuwa har tsawan wasu luƙutan, jin bata da niyar daina kukan yasa shi cewa pls I'm so sorry indai ni nayi miki laifin dakike wannan kukan to kiyi haƙuri idan kuma mahaifin kine ki kwanrar da hankali namiki alƙawarin gobe kafin kitashi daga bacci zaki ganshi agida amma dan Allah kidena wannan kukan karkisakawa kanki wani ciwon kinji, Allah sarki shi duk atunanin sa duk saboda shi take wannan kukan saboda shi kansa yasan baikyauta mata ba, jigaba yayi da rarrashin ta har yasamu ta ɗan tsagaita kukan nata ta koma shashsheƙa, jin yanda yake mata magana yasa taɗanji sanyi aranta yaude rana ɗaya tasamu wanda ya share mata hawayen ta aduk laƙacin da irin haka ya faru da ita saidai tayi kukan tagaji ba mece mata tayi shiru saidai tayi shiru dan kanta idan tagaji, amma yau gashi harda Allah ake haɗata akan tayi shiru, duk da ta kuntatawa rayuwar ta a iya yau da suka haɗu dashi amma sai taji bazata iya cigaba da kukan ba gwanda tayi shiru kodan abun da yayi mata na rarrashin ta da yayi tasan idan taci gaba batai masa adalciba duk da shine silar shigarta wannan halin amma ta gwammaci tayi tayi shiru saboda shi, jin tayi shiru kuma batace masa komai ba yasa ya ɗan gyara zaman sa aka kujerar tare da jigina kansa da jikin kujerar ahankali yace "nine ko?" baiyi tunanin zatayi magana ba amma sai yaji tace "a'a", da sauri yatashi daga jikin kujerar yana buɗe idon sannan yace to me yafaru me yasakaki irin wannan kukan haka naga kuma lafiya kika shiga gida me yafaru uhm, " babu komai yaji tabashi amsa" "really? Shima yace mata "eh tabashi amsa ni ba taɓa ganin inda akayi kuka hakannan ba duk inda akayi kuka dole akwai dalili musamman ma irin wannan kukan dakikeyi kar ki ɓoue min gaya min abun da yasaki kuka haka, Shiru tayi bata basa amsa ba saboda batason tagaya masa ainahin abun da yafaru da ita hartayi kuka, cikin ƙasa ƙasa da murya tace kawai na tuna mahaifina ne dan Allah karka cutar min dashi ka taimaka kadawo min dashi goben kamar yanda kayi min alƙawari ɗazu ina kewarsa da yawa ina buƙatar sa akusa dani bani da kowa sai shi Please and please na roƙeka kar kucutar dashi ta ƙarasa maganar tana shirin fashewa da wani kukan, shiiiiit taji yace ta cikin wayar sannan ya ɗora da cewa ya isa haka kar kisake yin kuka nibnayi miki alƙawari kuma zan cika miki shi da yardar Allah amma nima kimin wani alƙawar kar kisake kukan akan wannan maganar ki kwantar da hankaliki zan kawosa da kaina kamar yanda nagaya miki sannan kuma ki yafe min duk abun danayi miki tun farkon haɗuwata dake har zuwa yanzu karki ƙara dangantani da kalomomin da kike kirana dasu ni ba mugu bane kamar yanda kike tunani kuma ba ɗan iska bane bana kula kowa bana shiga harkar kowa duk wanda kikaga nayiwa wani abu to shi ya shiga harkata idan baka kulani ba ko inda kake ban kalla bare inshiga harkar da batawa ba dan haka kiyaye kar nasake jin wata kalma marar daɗi ta fito daga gare ki kuma kidena kukan nan ina ƙara gaya miki kinji abun da nace ko, cikin sanyin jiki tace to kayi haƙuri bazan ƙaraba, "tom shikenan komai ya wuce sai anjima, zai kashe wayar kenan yaji yace gobe da ƙarfe nawa zaka kawo shi? ina ruwan ki bade nace zan kawoshi da safe ba sai kijira kigani ko sai kinsani abun da banga dama ba mtswa yaja tsaki tare da kashe wayar, ɗif taji ya kashe wayar zare wayar tayi daga kunnen ta tare da hararar wayar kamar ita tayi mata laifin aranta tace masifaffe kai ba agama magana ta arziƙi dakai yanzu yagama yimaka magana cikin sanyin murya kugama lafiya amma sai ka ƙara jinsa yayi sama kamar me almutsutse ta faɗa tana turo baki sannan ta ƙara kiran sa amma sai taji wayar ma akashe tsaki taja daman tanaso yagaya mata loƙacin saboda bataso matar gidan taga loƙacin da za akawosa dan batasan awane irin yanayi za akawo sa ba tunda duk taga jini ajikin sa ɗazu kuma duk yabi yajigata bataso sauran mutanen gidan susan halin da yake ciki, amma tunda yakashe wayar ta ƙara gwada kiran nashi gobe da safe kafin yataho sai tagaya masa inda zai kaisa, tashi tayi daga kan gadon ta cire hijab ɗin da tun ɗazu takasa cire wa sai yanzu bayan ta cire ta hau cire kayan jikin ta ta ɗaura zani sannan ta shiga banɗaki dan gabatar da wankan ba jimawa ta fito tare da canza kaya sannan ta shinfida sallaya tafara jero sallolin da ake binta, yana kashe wayar yasakata a airplane mode,saboda yasan zata iya kirannasa shikuma yagaji da wayar shiyasa yayi hakan duk da yana tausayin nata amma ta wani ɓangaren na zuciyar sa hakannan yakejin haushin abun da takeyi masa kuma ya biye mata, ɗora kansa yayi akan staring din motar tundaga farkon haɗuwar su da loƙacin da tatafito har tazo inda yake kalaman da yayi mata ne yashiga dawo masa da loƙacin da harta shiga mota har zuwa can da abubuwan da suka faru acan da baccin da tayi masa akan cinya da abun da tayi masa harde zuwa rabuwar su da kuma wayar dasukayi yanzu babu abun da bai tunaba kansa ne ya ƙulle ya rasa wane kalar tunani zaiyi da irin wannan sabon halin da ya aro yakeyi dan yasan ba halin sa bane, yana mata magana cikin sanyin murya harda rarrashinta da bata haƙuri da naiman yafiyar ta shi shi da kansa kamar ba Sameer ba yau wata na niyar canza masa tunani dole yadakatar da wannan tafiyar tasu zaima sakata a blacklist sannan ya goge number ta gaba ɗaya mahaifinta kuma yafasa kaishi da kansa zai sallame sa kawai ai ba ƙaramin yaro bane da har sai ankaishi agida shima idan akarabu dashi zai iya zuwa da kansa, shikenan ya rabu dasu bazai ƙara shiga harkar suba yarinyar kuma bazai ƙara ganin taba itama bazata ƙara ganin saba daga yau yau suka haɗu kuma yau zasu rabu duk dade acikin mata tayi masa abun da ba macen da ta taɓa yi masa makamamcin irin abubuwan da tayi masa ayau kuma ya rabu da ita, atake agun yagama yanke sharar duk yanda zaiyi tare da yin blocking din ta sannan ya goge number kamar yanda yace zaiyi, saida ya kawar da komai da tunanin ta aransa da duk abun da ya wakana atsakanin su, sannan ya tayar da motar ya cigaba da tafiya yamaida akalar tunanin sa kan yanda zasu shirya tafiyar tasu gobe yana tunani yana tuƙin sa ahankali kamar ba abun dake damunsa bai isa gida ba sai wajen ƙarfe tara da wani abun ya ƙarasa, bayan ya shiga ba zarce ko ina ba sai part ɗin fulani inda nasa part ɗinsa yake baibi takan su shettima duk da daf da shigowar sa yaga kiran shettima yasan basu tafi ba amma ayamzude baida loƙacin su hutu kawai yake buƙata a halin yanzu, momma ce ta sauko daga step din upstairs, maida hankalinsu sukayi gareta kafin tafi magana ma ta rigasu da cewa yanzu na hango shigowar sa ta window ya tafi part ɗinsa yabarku da jira, cike da ƙosawar gajiya da zaman gurin shettima yace momma rabu dashi wulaƙanci yakeji dashi yasanu sarai jiransa muke kuma sai kiran sa nake baiɗaga ba shine ya shigo gidan ya tafi yayi wucewar sa bari muje mu same sa dan ina so in wuce gida da wuri gashi har goma ta kusa, wannan yaron wallahi wulaƙancin sa dayawa yake kuɗin ma da kuke tare ashe bai tsallake kuba kowa sai ya nuna masa halin sa Allah ya shirye sa ya rage wannan mugun halin nasa, dan murmushi shettima yayi yana miƙewa tsaye sannan yace haba momma inda sabo ai munsaba wataƙil yagaji ne shiyasa kikaga yayi mana haka amma masana ko ba muje ba ma zai mememu saboda wani aiki da muke bari kawai muje, tace to Allah ya kyauta dan mutum kuma yagaji sai ya sauke gajiyar tasa akan kowama nidai wannan halin nasa ba ƙaunar sa nake ba, momma sai haƙuri wataran zaidaina dayayi aure ne zai rage wasu abubuwan, Mamman tace to ahaka taya zai samu matar auren duk wacce aka haɗasama da ita wallahi an cuceta dan wuya zata sha ba matar da zata ita zama dashi da wannan halin nasa, shida matan ma ba kulawa yake ba yace ai nan duk ba matar da zai iya aura duk faɗan da nake masa ba saurara ta yake ba saidai ma yafaɗi abun da yayi niya yaƙara gaba yabarni agun, cikin dariya shettima yace kar ki damu momma sirikar is coming very soon keda ki zuba ido kawai ki sha kallo, har cikin ranta kuwa taki daɗin abun da yace sannan tace banason wasa da gaske kake yana da budurwa? a'a momma baza aji mutuwar sarki abakina ba kibari idan tayi tsami kyaji da kanki kinsa ance waƙa abakin me ita tafi daɗi, aikam cike da farin ciki da annashuwa tace to Allah ya nuna min wannan ranar idan da gaske kake danni nasan wannan abune me wahala bazan yarda ba har sai lokacin da ya tabbata, to shikenan momma zaki yarda ne bari de muje kawai muna ƙara ɓata loƙaci to shikenan sai kundawo ku tuso min ƙyeyarsa yazo yaci abinci kafin ku wuce, "yace to momma ai zama mubiyo mu ɗauki Ameesha idan zamu tafi, dan taɓe baki tayi tace ai bangaya muku bama ai yarinyar nan tazama ƴar gida yanzu hakama basa cikin nan bakuji ba hayaniyar suba sunshiga cikin gida wataƙil ma suna sashen su Maman Ammar (yar uwar ta wacce aka haifesu tare me suna karima), kubarta tunda ba makaranta tayi week end anan agayawa mahaifiyar ta kun ara mana ita dan haka kuje abun ku dan tasamu ƙawaye baka ga yanda ta sake acikin suba, duk shiru sukayi babu wanda ya iya tanka mata, naji kunyi shiru ko baza kubarta bane ta katse musu shirun nasu da sauri bossay yace a'a shikenan ba matsala Allah yakaimu, shide shettima ba haka yaso ba gaba ɗayan suma ba haka suka so ba amma ba yanda suka iya baza su iya cemata a'a ba suna ganin girmanta baikamata tazo musu da wata buƙata ba su hanata bata cancanci haka agare suba dole su amince ko suna so ko basa so, sallama sukayi mata sannan suka tafi shettima ne yayi bossay jagora har suka ƙarasa part ɗin mama fulani suna shiga ba kowa afalon direct suka nufi dakin sa afalo sukayi sallama amma ba amsa dan haka kai tsaye shettima yatura kofar suka shiga ciki, nan made bayanan dan haka suka ƙara nufar ɗakin sa, "akan sallaya suka gansa yana sallah zama sukayi sukajira har ya idar sannan suka fara yi masa magana suna tsokanar sa yanzu ka kyauta mana dan Allah awa nawa mukayi muna jiranka ko soyayya ce tayi daɗi ka manta damu, banza yayi dasu ya tashi daga kai yadauke sallayar sannan yasaka kayan bacci yagama duk yana jinsu amma yaƙi tanka musu har yaƙarasa duk abun da zaiyi ya haye gado tare da jan abun rufa, kutumar ubanan shettima yace tare da miƙewa tsaye ya doshi inda yake kwance yana zuwa ya yaye abun rufar tasa..............✍️✍️✍️                                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid) [6/15, 11:22 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️57&58 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️               "kutumar ubanan shettima yace tare da miƙewa tsaye ya doshi inda yake kwance yana zuwa ya yaye abun rufar tasa..............✍️ wallahi sai ka tashi saboda tsabar rashin mutun ci tun dazu muna jiranka amma kazo kayi kwanciyar ka kana shirin yin bacci saboda ka maida mu ƴan isaka, tashi zaune yayi tare da dafe kansa batare da yakalle saba yace dan Allah karabu dani da abun da yake damuna kar ka ƙara min wani ciwon kan,     "au haka ma zakace mune ciwon kan Kenan?   to ai naga bakuzo da niyar jin komai ba shiyasa nayi muku haka idan kun gama sai kutafi inyaso gobe mayi magana yaƙarasa maganar tare da komawa ya kwanta,   shettima yace to shikenan  badama mutum yaga abu bazai faɗa ba mufa duk abun da muka gani sai munfaɗa ko me zai faru saidai yafaru ah to idan kuma mutum bayaso afaɗa sai ya dena yin abun gaɗan danma kaci sa'a bangayawa momma ba, Ina jin tsotone kaje kafaɗawa duk wanda zaka gayawa kuma kufitar min daga ɗaki gobe da safe ƙarfe takwas zamu bar garin nan zuwa Abuja kar wanda ya ɓata mana loƙaci mu haɗu a hospital,    in kunfita kurufe min ƙofa yana kaiwa nan yaƙara jan blanket ɗin saya rufe har kansa,   tseye shettima yayi batare da ya motsaba Saida yagama tsayiwar SA Dan kansa sannan ya matsa daga gurin sa inda bossay yake ya kalla yaga har yafara gyangyaɗin bacci tashin sa yayi yace mutafi kawai sai gobe,    "dan murza idonsa yayi tare da yin miƙa da hamma duk aloƙaci ɗaya sannan ya gyara tsayuwar sa yace me yace maka dan shi tun shigowar su ya fara gyangyadi dan duk ba jin zancen su yake ba,    kasan shi de me hali baya fasa halin SA yau mutanen ne suka motsa yaƙi cewa komai kawide yace  mutafi wai gobe ƙarfe takwas mi haɗu a hospital zamu tafi abuja,     "abuja Kuma?  bossay yatambaya, "Eh haka yace" me zamuyi acan?    "nima bansani ba muje kawai muna ƙara yin dare Allah yakaimu gobe maji duk ma abun dake wakana tunda bega damar sanar damu ba  sai mu hakura, ok to shikenan mu wuce, tare suka jera suka nufi ƙofar waje har sun kusa fita dan har sun saka ƙafar su awaje shettima yayi saurin dakatawa tare da juyowa yace ai bamu karɓi key ɗin ba yana faɗar haka ya koma da baya tare da ɗan ɗaga murya tun kafin ya ƙarasa wajen sam ɗin yace where is the key?       shiru baibasa amsa ba, har yana Shirin ƙara tambayar sa yaji yace yana jikin motar mana me zanyi dashi anan ko anacin muƙulli ne duk kunbi kunta kurawa rayuwata wallahi,      tsaki shettima yaja batare da ya kulasa ba ya juya suka fita, suna fita suka shiga motar tare da barin masarautar saida yafara kai bossay gida sannan shima ya wuce gida,     bayan yaje gida tunkan ya buɗe ƙogar hajiyar sa ta rigasa buɗewa tare da cewa ina take naganka kai kaɗai tunɗazu kasa nakasa tsaye nakasa zaune ina jiranku,   Oh hajiya  to meye na damuwa kinsande bazan bari wani abun yasame ta ba yafaɗa yana jan hannunta suka koma cikin falon,     "to inba abun davyasame ta inganta mana yanzu kuma me katsata yi yanzu fa shaɗaya saura,     zuba mata ido yayi saida yabari takai aya sannan yace hajiya yau nafara kai shaɗaya awaje naga har sha biyu ina kaiwa amma baki taɓata tamyata ba sai yau naga alamar wannan yarinyar inbanyi wasa ba kwacen uwa tunda anfi damuwa da ita akaina,    ɗan murmushi hajiya tayi masa tare da lakace masa hanci sannan tace naji koma me zakace kace ayanzu de nafi ji da ita akan ka dan haka gaya min inda ka kaimin yarinya kafin muhau sama dakai yanzun nan,     "siyar da ita nayi fa yanzu haka ma kuɗin suna cikin boot masu yawa zo muje ma kigansu kuma ki shirya gobe zamu bar ƙasar nan dan mungama kuɗi yaƙarasa maganar cike da basarwa kamar da gaske yake,      ahh ashe bani kaɗai nake wannan hasashen ba tun farkon ganina da yarinyar nasan zatayi tsada idan akasiyar da ita mungama kuɗi  daman shirya yanda za ayi nake ta faman yi nakasa yanda zan ɓullowa abun sai gashi kai harka gama min da ita gaskiya kayi namijin ƙoƙari yakamata injinjinawa jarimin ɗana to yanzu ya akeciki wacce ƙasar Ka shirya mana zamu koma dan harna ƙosa ma gari ya waye inganni aƙasar waje, ya kaganni acan tafaɗa tana wani ɗage masa gira tare da kallon kanta tundaga sama har ƙasa tana ɗan karkaɗa kai,   tunda tafara maganar yake faman tiƙar dariya harda dafe ciki jin yanda ta bashi amsa daidai dashi saida yayi me isarsa sannan ya dakata yace hajiya kinfi ƙarfina ai,  to ƴarki tana gidan su sam momma tace abarta tayi weekend tare da su Amra, itama dariyar tayi sannan tace to ai shikenan Allah yakaimu, daga nan de suka ɗan taɓa hira har yasanar da ita tafiyar dazasuyi gobe, daga nan sukayi sallama kowa ya nufi ɗakinsa,    *Washe gari* kamar yanda yagaya musu hakan sukayi gaba ɗayan su babu Wanda ya wuce loƙacin da yabasu amma duk da haka yariga su zuwa a can suka sameshi ,    bayan sun shiga ciki sun haɗu sun gaisa fuska ba fus ba asss suka gaisa dasu sannan yasanar dasu duk yanda sukayi da mahaifin sumy har zuwa inda zasu da kwatancen da yabasu bai rage musuba bayan ya gama yi musu bayanin, shettima yace to Allah yakaimu lafiya yadawo damu lafiya Allah yabamu nasara, ɗan dakatawa yayi sannan yace yauwa munji wannan bayanin amma baka yimana ɗayan bayanin ba Ka barmu cikin duhu har yanzu bamu kawo haske ba, cike da rashin fahimta sam yake kallon sa har yagama maganar sannan yace wane bayanin kuma banfahimce ka ba,    ɗage masa gira ɗaya yayi yana dan sakin murmushi  sai kuma ya kwantar da hannun wansa duka kamar za aɗora masa abu sannan  yafara yawo dasu kamar yaɗau jariri yanayi yana kallon sa  shide Sam har yanzu bai gane me yake nufi ba,   ganin bai fahimta ba yasa sam cewa I'm so sorry pls stop carrying I hate it yaɗa cike da kwaikwayon irin muryar sa,    sai yanzu yagane abun da yake nufi duka yakaima sa adantsen hannun sa shettima yayi saurin gocewa yana dariya bossay ma dariyar yake masa,     memakon yaji haushin dariyar da suke masa, kawai baisan loƙacin da shima murmushi ya kwace masa ba,    Ahhhh ehh shikenan wlh ai bama sai kabamu amsaba mungane komai awannan murmushin cewar shettima,    bossay ya ɗora dacewa nidai tunda nake dashi bantaɓa ganin murmushi akan fuskar saba amma yau dalilin wata nagani kagafa har yanzu yakasa dainawa yaƙarasa maganar yana nuna sam,    ai nagani yau dole inkaiwa momma albishir daman ban tabbatar bane shiyasa bangaya Mata ba tun ɗazu amma yanzu zataji komai,    haɗe rai yayi kamar bashine ya gama yin murmushi ba, cike da dakewa yakalle su yana nunasu da yatsa yace wallahi bana son shirme da shiririta ku bakusan aikin da yake gaban kuba ko to koma me kuke tunanin da yarinyar nan ba hakabane babu wani abu da yashafi abun da kuke tunani dan haka kubar duk wani banzan tunani agefe mufuskan ci abun da yake gaban mu in kunga dama kufito mutafi in kuma zaku cigaba da zama sai kuyi tazama agun ni kunga tafiyata yana kaiwa nan yayi gaba yabarsu agun da baki sake, yana jiyo su suka cigaba da dariyar su da kuma surutun su basu fasaba bayaso suyi tunanin wani abun danshi bahaka bane agurin sa abun da basu sani ba akwai abun da yatuna da yasashi yin murmushi amma sunzo suna ta shirmen su akan wani tunanin daban,   yana zuwa wajen motar suma suka fito baya ya buɗe ya shiga sukuma suka shiga gaba shettima ne a mazaunin driver bosssy kuma agefen sa ahaka ya tayar da motar suka fice daga cikin asibitin.  suka dauki hanyar Abuja....... *ABUJA* tunda maama(sabreena)  ta idar da sallahr asuba bata koma ba tayi zaune bayan ta gama addu'o'in ta ta zauna abakin gadon tana jiran gari yayi haske taje tace musu zata tafi dan bacci ma da ƙyar tayi shi jiya so take kawai tagan ta agarin kano... har gari yayi haske sosai amma bata ji motsin kowa ba datagade tagaji da zam kuma bataji ɗuriyar su yasata fitowa daga ɗakin ta dawo falo tsayawa tayi ta shiga ƙarewa gidan kallo daki daki take bin ki ina na falon da kallo ahaka har idonta ya faɗa kan wani tafkeken hoto da yake can wani lungu gabanta taji yayi wata iriyar mummunar faɗuwa da har saida ta dafe gefen zuciyar ta sannan tashiga karanto sunayen Allah saida taɗanji daidai sannan tafara takawa ahankali zuwa wajen hoton tare da kafe shi da ido bata ko ƙiftawa,. tana daf da ƙaraswa gurin taji takun mutum alamar ana daukowa daga bene tsayawa tayi tare da ɗan juyowa dan ganin wanda yake saukowa, ido biyu sukayi da ummy da take sanye cikin abaya pitch collar da miyafin ta Kalar ta, tunda taga maama ta shiga sakin murmushi harta ƙarasa  saukowa takowa tayi har inda take tana ƙara faɗaɗa murmushin ta sannan ta gaida ita , bayan sungama gaisawa, ma'ana tace yauwa tunɗazu nake jiran fitowar ku danni na riga da nagama shiryawa tafiya kawai nake sonyi kigayawa me gidan naki, sosai abun yabawa ummy ba yanzu duk bayanin du sukayi mata jiya bata yarda ba ashe ya shiga ta hagu ya fita da dama, ajiye duk wani mamakin ta tayi agefe sannan ta sakar mata murmushi tace to shikenan maama bari zan kirasa ai yama tashi shima amma bari kifara karyawa sai inkirashi ɗin tana gama maganar ta kamo hannun ta suka koma kan kujera ta zaunar da ita, maama kam binta kawai take bata ƙara cewa komai ba, bayan ta zauna ta kwalawa me aikin su kira tasanar da ita cewar ta haɗo mata breakfast bata dau loƙaci ba taje ta haɗo ta kawo, zatayi saving ɗinta ummy tayi saurin dakatar da ita dacewa taje kawai, da kanta ta sauko tayi saving ɗin maam ƙarɓa tayi tare dayi mata godiya sannan tafara ci yaude tace da ɗan yawa ba laifi bayan ta tagama, aka kwashe kayan, sannan ta maida hankalinta ga ummy tace to nagama ci sai kije ki sanar dashi dan bana so ƙarfe goma tayi min acikin garinnan, ba yanda Ummy ta iya dole ta tashi taje ta sanar dashi duk yanda atakaicedai duk yanda sukaso su shawo kan abun ta haƙura sai gobe ƙin yarda tayi daga ƙarshe ma tace zata tafi da kanta sai da suka ga haka sannan suka ce mata sun yarda zasutafin ba shiri suka hau harhaɗa kayan da zasu tafi dashi duk da bawani kayan shirgi suka ɗauka ba iya abun da yazamar musu dole ne suka ɗauka loƙacin da suka gama shirya wa suka fito loƙacin ƙarfe shabiyu saura, jirgi suka so suhau amma babu dama saboda basuyi boocki ɗin ticket ba tun wuri, dan haka dole suka tarkata inasu inasu suka shiga mota har driver yazo zai jasu amma abu ya dakatar dashi yace meer yajasu saboda basu san ranar dawowar suba bazai yiyu su tafi dashi can ba gwara yake gida idan sun dawo sai yadawo, godiya yayi musu yaƙara gaba abunsa, shikuma meer badan ransa yasoba zaiyi tuƙin nan ba wallahi dan shifa arayuwata sa bayason aikin wahala duk abun dazaisa yaji yagaji baya yayi bare kuma tuƙi da basaba yi yayiba ace kuma tundaga nan har zuwa wani garin duk dade bai taɓa zuwaba amma yasan dole yayi nisa, yanata cika yana batsewa ya shiga ya tayar da motar aransa yana rayawa dabadan wannan matar ba wallahi ba abun da zaisaka shi yin tuƙin amma anci darajar wannan matar, kan titi suka hau sai kuma yace wacce hanyar zanbi yafaɗa batare da ya kalli inda Abu yake ba dake gefen sa azaune, da hannu Abu ya nuna masa inda zaibi da gudu kuwa yaja motar kamar zasu tashi sama haka yake jan motar saida Abu yayi masa magana akan ya rage gudun da yake amma kamar ma zigashi yayi haka yake tafiya, sunzo wajen danja inda aka tsayar da motoci tsayawa yayi badan yasoba yana ta faman jijjiga kai kamar yaci gaba da tafiya haka yakeji jikin sa ha tsuma yake, ana basu hannu kuwa yaƙara jan motar aguje tare da buge motar gaban sa batare da ya bi takan buge motar dayayi ba kuma sarai yaji ya gani amma yaƙara gaba ko waiwayar su baiyi ba, motar da suka buga suma da gudu me jan motar yaja motar tare da bin bayansu, kusan yar tsere suka fara su meer nagaba motar da suka bige na bayansu shima yana zuba nasa gudun dan ganin sun cimma su meer, Saida ya ƙure wuta sosai sannan yakamosu wuce su yayi tare da shan gaban motar su meer,. wani wawan burki meer yaja da saida yasa su ummy sakin salati gaba ɗayansu dan sun saddaƙar ma ya buga musu motar, meer na jan burki ya ɓalle morfin motar tare da fitowa azafafe Abu na kiranshi kar yafita ya tsaya amma ina baisaurare sa yafita, shima wancen ɗin azafafen ya fito daga tasu motar zuciyar sa na tafasa , gaba ɗayan su suna fitowa kowanne su gadan gadan sukayi kan juna batare da kowa ya tankawa kowa ba saboda daman kowa yasan laifin da yayi, da sauri su ummy da abu suka fito daga motar suka nufi bayan meer zasu riƙeshi dan gudun abun da suka ga yana shirin yi............✍️✍️✍️✍️✍️ Tofa wata sabuwa🤔 masu karatu me kuke tunanin zai faru anan gurin????                                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)           [6/19, 7:23 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️59&60 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️               "da sauri su ummy da abu suka fito daga motar suka nufi bayan meer zasu riƙeshi dan gudun abun da suka ga yana shirin yi............✍️     saidai ina tunkafin suƙarasa garesa har sunkaiwa juna shaƙa atare meer ne yafara kaiwa ɗayan duka abaki atake bakin ya fashe shima cikin zafin nama da taƙaicin naushin da yayi masa shima yaɗaugo da nasa hannun yakai masa naushi amma sai kafin yakai ga fuskar meer, meer yayi azamar cafke hannusa kuma yana cafkewa ya murɗe hannu,    jin zafi da yayi yasakashi dauko duka ƙarfinsa da jarumtarsa shima ya murɗewa meer hannu duk da bawani sosai ya murɗa masa ba saboda ƙarfin su ba ɗaya bane duk da kowa yanaji da nasa ƙarfin amma zubin hallitarsu ma ba ɗaya ba meer yafishi ƙirar maza amurɗe yake,    duk ƙoƙarin Abu da su ummy da sukeyi wajen ganin sun rabasu amma hakan  ya gagara, dan caƙumewa sukayi da faɗa kowa zuciyarsa akusa take kamar zata fito waje su shettima na suma suka fara ƙoƙarin rabasu amma sunkasa sai dukan jikin su suke kamar suna filin daga haka suke dukan junansu daga ƙarshede meer yayi kukan kura ya tattaro duka ƙarfin sa ya cukwikuye sam ya ɗaga sa sama ya nunawa Allah yana shirin direshi ƙasa (oh 🤔ashede gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta yau sam ya anhaɗu da  wanda ya fishi zafin rai) maama da su ummy gaɗayan su babu wanda baije gurin ba sukayi saurin ririƙe hannun sa  suna haɗasa da Allah akan ya daukesa  cikin ɓacin tai Abu yace wlh idan baka saukesa ba sai ranka yayi mummunar ɓaci dan sai na nuna maka fushin dabaka taɓa gani ba  tunɗazu muna maka magana amma kaƙi sauraron kowa saboda raini to dan ubanka kar ka fasa kaci gaba kaga yanda zanyi dakai agurin nan yaƙarasa maganar yana sakin hannu sa da yariƙe shi saboda shima fa zuciyar tazo kusa kiris yake jira shima yafara kai dukan saboda yanda kukaga meer shima haka yake dan meer gada yayi daga garesa saidai bambancin su shi Abu yanzu da ya manyanta ya rage sosai baya sai kakaishi ƙarshe nan zaka ga ɓacin ransa saboda wata irin zuciya garesu me abu kaɗan zasu maida shi yazama babba musamman meer bashida haƙuri kwata kwata baima sanshi ba,    yasan halin mahaifin nasa sarai tunda yaji yafara irin wannan batun to yasan zai iyayin komai akansa koda ba duka bane to zai iya musguna masa ta wani fannin shiyasa badan yaso ba kuma azuciyar sa bawai dan yana tsoron mahaifin nasa bane kawadai baisan me zai mishi bane bayaso yayi masa wani abun da zai ja masa raini agaban waɗan nan yaran,(kunji fa tsaurin ido wai su sam ɗinne yara tabb)   kuma duk abunsa ba yana ɗagawa mahaifinsa ƙafa ƙarewa ma baifiye shiga harkarsa ba saboda irin waɗannan abubuwan dan inbeyi baya baya dashi ba wataran za a iya samun matsala atsakani shikuma bayason hakan tafaru saboda yasan halin zuciyar ba daidai take da ta mutane ba,.   sauke sa yayi saida fa kuma yana saukesa ya hankaɗa sa gefe yafaɗi,    tofa mutumin bai daddara ba da sauri yasake miƙewa tare da narko masa wata ƙatuwar ashar da tunda nake ni bantaɓa ma jin irin ta ba ko a ina yasamo ta oho dande maimaita saɓo, saɓo ne da nafaɗa muku irin zagin nasa,    saidai abanza dan ko akwalar meer saboda baisan ma zagi bane haka su abu ma duk ba wanda yasan me yace saidai su shettima sungane kalar zagin nasa duk da halin da suke ciki hakan bai hana dariya  fitowa ba dariya suka shigayi, da sauri sam ya juya yakalle su da mamaki ƙarara a fuskar sa suna nufin su abunma dariya yabasu meyasa suna ganin halin da yake ciki amma su shiga yi masa dariya,   suna ganin ya juyo yana kallon su sukayi saurin haɗiye dariyar su ganin irin kallon da yake musu ya suka shiga sunnar da kai ƙasa suna wurwurga ido ba wanda ya ƙara iya haɗa ido dashi,   jinjina kai yayi tare da barin abun da zai musu acikin ransa yayi sannan ya juya ga meer da yake ta faman fitar da huci da iska me zafi daga bakin sa haɗi da jefawa sam kallo me ma 'anoni da yawa da kuma gargaɗi,      ganin irin kallon da yayi masa batare da ya karaya ba yaƙara yin kansa yana zaginsa yanace wallahi sai na kasheka bade ni kayiwa hakaba sai ka gane baka da wayo sai nasaka nadamar sanina arayuwarka wallahi sai na kasheka saidai uwarka ta haifi wa........tassss yaji andaukesa da mari bai ankara ba yaji an ƙara sauke masa bashi kaɗai ba gaba ɗayansu babu wanda beyi mamakin  marin da maama tayi masa ba,   dafe fuskar yayi tare da saurin ɗagowa dan ganin wanda ya mare sa waro ido yayi  da mamaki yake binta da kallo aransa yake ƙara mamakin meyasa wannan tsohuwar marinsa me yayi mata,     sauke hannusa yayi zuciyar sa na tafarfasa yace saboda son kai zaki mareni shi bakiga abun da yayi mana ba amma ba wanda yaga abun da yayi shine zaki mareni saboda ku kukakawo sonkai duniya ko kuma angaya muku shikaɗai ne ɗa me  gata to muma ai bada gidan matsiyata muka fito ba da gatanmu badaga sama aka jefo muba kuma wallahi sai na iya sawa anɗaure duka dangin ku kubar ganin kuna da kuɗi kai kuma ka ɗauka ƙarfina kafi ko yafaɗa yana maida kallon sa ga  meer to wallahi baka daki banza dan bazan taɓa barin kaba duk inda ka shiga sai na memoka sai nasa anƙulleku gaba ɗayan ku matsiyata kawai,    jinjina kai shettima yayi jin ƙarfin hali irin na sam wai matsiyata kuma zaisa a ƙullesu shi a iya kallo ɗaya ma kayiwa mutanen nan ai kasan ba ƙananun mutane bane acan de kano kayi gadara da gidan sarautar da kake ji dashi amma anan wayasan ko kai waye duk aransa yake wannan tunanin,   jin maganar tsohuwar yasashi dawowa daga tunanin da ya tafi,   wai ku wacce irin zuciya gareku da bakwa ganin mutane da mutunci to inbaka fasa ƙulle muɗin ba bakaci ka dan halak ba kunzo kuncikawa mutane kunnuwa da surutun banza to wallahi inƙara jin bakin ka anan gurin kaga yanda zanyi dakai marar kunya kai shi baka ga anmasa magana ba yayi shiru ya rabu da kai shine kai dan ba a isa dakaiba kaci gaba da abun da kake saboda baka da kunya agaban mu zaka kama yiwa mutane zagi ko bakaji kunyar saba amatsayin sa na wanda ya girmeka ai kaji kunyar iyayen sa amma kake kiran iyayen nasa kana zaga to wallahi ka ƙara magana sai nayi ƙasa ƙasa dakai anan gurin, buɗe bakin kuwa yayi zaiyi magana ta ɗaga hannu itama zata kai masa duka abaki ba shiri kuwa ya haɗiye maganar tasa ganin da gaske take, sai kawai ya shiga gungunin wannan tsohuwar ta cika faɗa wallahi koma inaruwan ta da shiga abun sa shi ɗayan bata yi masa amma ni tazo tana balbale ni da faɗa saikace wani ɗanta sa'arta ɗaya wallahi kawai dande tsohuwa ce amma da sai ya rama marin da tayi masa,     marar mutunci ai faɗa zakayi inji da kyau baka tsaya kana ƙunƙuni sai kafito fili kayi magana zan gane kai cikakken marar kunyar ne,     ummy ce ta matso kusa da ita tare da riƙo hannun ta tace haba maama ki rabu dashi dan Allah tunda yayi shiru kowa yayi haƙuri kizo mutafi kawai Allah ya kiyaye gaba,   kallon sam tayi tace ɗan kayi haƙuri abisa abun da yayi maka bawai muna goyon bayan sa bane yasa kaji tayi maka haka tayi makane bisa rashin kunyar da kayi agaban mu baikamata ka ringa zagin mutum agaban iyayen saba kasan nadan mu ba zaginnan da kayi masa ba rabuwa zaiyi dakaiba kana gani tunda yafito muke kiran sa akan yatsaya kada ya taɓaka amma bai saurare muba amma kuma kai ka maida laifin kanmu duk ƙoƙarin da mukayi baka gani ba kana ganifa mahaifinsa gashi can ya koma mota yayi fushi dashi kuma tunda ya hanasa bazai ƙara taɓaka ba amma kai kazo kama ta zage zage wanda hakan baidace ba amatsayin ka na ɗa musulmi kadena zagi ko nan gaba ka gyara halin ka bakasan wataran dawa zaka haɗuba arashin sani kuma kaje ka jawowa kanka danasani da jin kunya,    kirabu dashi yayi duk abun da yayi niya jan abun kunya Kum ai yariga da yaja shi, sam de shiru yayi sai kuma jikin shi yayi sanyi jin ƴar nasihar da ummy tayi masa sai yaji ma kunya ta kamasa, shide inzai iya tunawa ma a kaf rayuwar sa da yataso baitaɓa haɗuwa da mutanen da yaji shakkar su ba irin waɗannan mutanen musamman tsohuwar da yaji yakasa tanka mata duk irin abubuwan da take gaya masa wai harda su mari lalle sunci sa'ar wannan rana ga baɗayan su (nikam nace bawan Allah faɗi gaskiya kace de ka haɗu da wanda yafika karkaje ya ƙara naɗa maka na jaki shiyasa kake shakkar su nide anawa tunanin kenan)    maama muje dan Allah juyawa tayi suka tafi yakin su uku zuwa huɗu sai kuma ta tsaya tare da juyowa ta kalli sam a inda ta barsa ahaka ta gansa, "ya sunanka ta tambaya gaba ɗayan su suka dago suna kallon ta da kai nake kabi ka tsare ni da ido tafaɗa tana itama tana kallon sa kamar yanda yake kallon sa, saida yagama jan loƙaci kafin yace SAMEER dam taji gabanta ya faɗi da meer da ummy jin sunan da yafaɗa ya gaba ɗayansu saida suka juyo suka kalle sa jin sunan su iri ɗaya, ummy ce ta dawo da baya tana ɗan murmushi tace ahh ashe ɗana ne sunanku iri ɗaya kuna faɗa takwara da ta kwara ne ashe, "jin abun da tace yasa sam ɗaga idonsa yakalli meer caraf suka haɗa ido dashi wani kallo meer ya watsa masa tare da harara irin karka min maganar banza dan kaji ance sunan mu ɗaya shima sam hararar yamayar masa da ita tare da kawar da kansa gefe, 'meer kuma gaba ɗaya ma yabar gurin ya koma can wajen motar sa saidai baishiga ba saboda kallon da yaga Abu nayi masa yasa shima haɗe rai tare da kamewa waje guda ajikin motar yana jiran ƙarasowar su ummy dan yagama gajiya da tsayuwar gurinnan ji yake ma kamar yace yafasa zuwa kano ɗin wannan yaron yazo ya ɓata masa mood ɗin sa gaba ɗaya, Abu ne ya fito daga motar ganin basu da niyar tahowa, har yayi gaba zai tafi sai kuma yatsaya batare da yajuyo ba yace follow me yana kaiwa nan yayi gaba meer dake tsaye yasan dashi yake beyi wata wata ba yabi bayansa kamar yanda yace duk da bayason komawa kusa dasu, daidai loƙacin da suka ƙarasa daidai loƙacin sukaji maama na tambayar sa sunan sa dan haka sai suka dakata duk da sunji sunan da yace ɗazu amma yanayin da ta tambayi sunan sunsan harda na na mahaifin sa take nufi "ur full name? maama taƙara tambayar sa, "Sameer Abadallah Sameer (SAS)" jinjina kai tayi tare da yin shiru na wasu ƴan daƙiƙu, kafin daga bisani ta buɗi baki tace awane gari kake? zaiyi magana kenan meer ya rigasa da cewa maama wai me zaki mishi sai faman tambayoyi kike masa dan Allah kizo mutafi ni nagaji da wannan surutan kuntsaya da yaro salon jawa kai raini yanzu wannan yaron har yakai matsayin da zaku ringa sa'insar baki dashi shi waye ɗan uban waye ni inbaza kutafi ba wallahi zan fasa zuwa saidai ku nemi wanda zaiyi driving ɗinku yaƙarasa maganar yana ɗan ja da baya saboda jin idon mahaifin sa dayayi akansa yasan sarai kallon sa yake kuma yana so ya kalle sa dan yayi masa gargaɗi amma yaƙi bari su haɗa ido da yagama maganar ma sai ya matsa daga kusa dashi, "yi haƙuri yanzu zamu tafi cewar maama.. ina jinka kai ɗan inane ko ɗan nan garin abujar ne, "A'a ba anan nake ba ni ɗan garin kano ne, kano wacce unguwa? tasake jefa masa tambaya gabaɗayan su babu wanda beyi mamakin jin irin tambayoyin da take masa ba, shiru yayi kafin daga bisani ya daure yace mata unguwar laraba cikin masarautar sarki Salahuddenu Muhammad sameer anan nake ko zaki sa akamani ne to ga address ɗin nan nabaki idan kinshiga cikin kano duk wanda kika tambaya gidan sarki Salahuddenu Muhammad sameer za akaiki, wani irin abu taji yataso mata tundaga ƙafarta har tsakiyar kanta gaba ɗaya jikin yaɗau ɓari taciki loƙaci guda taji wasu zafafan hawaye nasan zubo mata tayi saurin tare su ta mayar da su gudun kar su zuba agaban su, ɗan murmushin yaƙe ta ƙaƙaro tayi tana so tayi magana amma tana tsoron idan ta buɗi baki tayi magana hawayen da take riƙewa zasu iya zubowa, juyawa tayi yazamana ta juya musu baya basa kallon fuskarta cikin rawar murya ta buɗi baki da ƙyar tace idan kaje ka gaida Muhammad sameer ɗin tana kaiwa nan tabar gurin da sauri saboda kukan da taji yataho mata gadan gadan.... tana zuwa ta buɗe motar ta shiga baya, duk mutuwar tsaye sukayi agun kowa na mamakin halin da suka ga ta shiga kowa da kalar tunanin da yakeyi su sam suna tunanin to tasan kakan sane itaɗin wacece saboda wanda tace agaida bama Sarkin ba baban sarkin kakansu kenen tabbas kwa yabi bayanta yaji ko itaɗin wacece? sukuma su ummy suna tunanin meyasa tayi hakan kode sune ƴan uwannata datake nema dole akwai wani abu da tasani akan wanann yaron da kuma labarin inda yaron yagaya mata, duk a ƴan minti na sukayi wannan tunani saboda yanda tayinne loƙaci ɗaya babu wanda yataɓa kawo hakan zai faru, atare suka bi bayanta gaba ɗaya suna zuwa suka shiga tambayar me yasata kuka kawai hawayen ta ta goge sannan ta girgiza musu da ƙyar tace mutafi dan Allah tafaɗa batare da alamar wasa a fuskar ta ba yanda tayi maganar dole yasaka duk wanda yaji yayi abun da tafaɗa batare da sun ƙara tanka mata ba kowa ya shiga inda yake suka rufe ƙofar, daidai loƙacin kuma sam yaƙaraso gaban motar tasu suna ganin sa tacikin glass ɗin amma sai maama tace muje kawai karku saurare sa daman meer haushin shi yake ji dan haka yatayar da motar yajata da ƙarfi badan sam yayi saurin matsawa ba da ta kansa zaibi.... tsaye yayi agun yakasa motsawa yana faman bin motar da kallo har ta ɓace ma ganin sa... sannan yadawo hankalin sa dasauri yakoma wajen su shettima da suka zama ƴan kallo agun, da sauri ya buɗe gaban motar yashiga sannan yace kuyi sauri binsu zamuyi kar mubari su ɓace mana da sauri suma suka shiga shettima nacewa amma kasan zamu bisun ka tsaya har suka bace bai saurare sa ba suna shiga yana motar a 360 yabi inda yaga sunyi addu'a yake kawai Allah yasa yakamosu to mumade zamu tayaka da addu'ar dan kamosu saidai addu'ar amma da kamar wuya.......✍️✍️✍️✍️                                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)            [6/20, 7:46 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️61&62 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                  suna shiga yaja motar a 360 yabi inda yaga sunyi addu'a yake kawai Allah yasa yakamosu to mumade zamu tayaka da addu'ar dan kamosu saidai addu'ar amma da kamar wuya....... anan muka tsaya yanzu kuwa zamu ci gaba sunana Ahmad isah shirin nan dakan ilimantar ya nishaɗantar da masu sauraro😂😂😂😂😂😂😜raidangi goro sabon shirinmu na radio📻 (ina masu jin rai dangin goro ga wata Ahmad isah ɗin💃💃😜😂)     "sosai yake kwarara gudu dan ganin yakamo su sai yanzu yake tajin haushin tsayiwar da yayi da yabisu tun aloƙacin da basu ɓace masa amma yanzu da wuya ya tadda su sai faman sakin tsaki yake yana dukan stirring ɗin yana cigaba da gudu dan bai karaya ba tundade yasan gurin babu kwana dole miƙewa sukayi dan haka shima ya miƙeɗin yayi wajen 15 minutes yana tafiya be gansuba dan sun riga da sunyi masa nisa,    Shettima ya dubesa yace yakamata mu haƙura dan ba ganin su zamuyi dan naga muna shirin barin garin ma gaba ɗaya gwara mukoma muyi abun da ya kawo mu inyaso sai mufara nemansu anan tunda daga gani kamar anan suke da zama kaga sai mu faɗaɗa bincike ko Allah zaisa da rabon muƙara haɗuwa dan ko ni zanso muƙara haɗuwa da matar nan dan ina ɗan hasaso wani abu game da ita amma kuma bansan meyasa tayi mana hakaba indai hartasan inda aka bata labari harda cewa kuma agaida papa daga nan kuma tayi tafiyar ta batare da tagaya mana a inda ta sanshiba gashi kuma bisa ga dukkan alamu inajin ko akwai abun da ya taɓa haɗata da papa ko kuma gidan ku tunda in ka lura fa tunda kagaya mata inda kake yanayin ta ya canza sannan kuma saida ta juya mana baya kafin tafaɗi agaidashi ɗin cikin rawar murya,           shide duk wannan jawabin da yake masa jinsa kawai yake dan baida niyar juyawa shima tunanin sa yana wajen dan ba komai ma yakeji ba, shikaɗai kawai yake surutun sa,      bossay dake baya duk yanajin abun da Shettiman yake cewa saidai shima abun da yatsaya masa arai yasa yakasa tanka masa har saida yaji yayi shiru sannan shima ya buɗi baki domin fito abun dake ransa tun tsayiwarsu agun,     ""nikam wai dan Allah bakuga abun da nagani ba ko nikaɗai nake ganin hakan? cewar bossay,    shettima ne yaɗan juyo ya kalle sa sannan yace me kakegani?    wallahi ni wannan tsohuwar matar nan tunda tafito nifa ido na nakanta nake kallon ta sai kuma yayi shiru,        "me tayi ?" cewar Shettima yafaɗa tare da juyowa gabaɗayan sa yana kallon bossay danjin me zaice,    "wallahi sai naga kamar suna kama da baby kai bama kamar ba sunyi kama sosai kodanni nafi zama da ita amma akwai abubuwan da tayi da yawa agun sai inga kamar baby ce ta girma,    cike da ɗan rashin fahimtar wacce yake nufi yace wake nan wace kuma baby dan baikawo kowa komai ba da yace masa baby sai yasa yatafi tunanin wace baby shiyasa baigane me yake nufi ba,     "AMEESHA!!" mana   wani wawan burki sam yaja sakamakon jin numfashinsa nasarƙewa stirring ɗin nashirin barin hannun sa shiyasa yayi saurin taka burki da gaba ɗayan su saida sukayi gaba suka dawo dan Shettima dake gaban motar sai da kansa  yaɗan bugu da jikin motar,    hakan yahanasa bawa bossay amsar maganar da yayi,      har suna haɗa baki wajen tambayar sa lafiya yayi irin wannan taka burkin  yana shirin kaisu lahira ,    jiyayi yawun bakin sa ya daskare gaba ɗaya yana son yin magana amma ya kasa sai zazzare ido kawai yake yana kallon Shettima dake gefen sa,    kai lafiyar ka ƙalau kwa? cewar Shettima,   bossay ne yafara fahimtar halin da yashiga saboda abun da yafaɗa ne yasashi shiga wannan yanayin tunda inzai tuna yana faɗar sunan baby ya taka wannan burkin, ruwan gora dake gefen sa ya ɗauka ya miƙawa sam tare da buɗe masa murfin robar sannan yabasa,      ba ɓata loƙaci kuwa sam ya karɓe saboda daman shi yake buƙata ahalin yanzu yana karɓa ya kafa kai bai sauke ba saida ya shanye duka sannan ya sauke robar numfashi ya shiga saukewa saida ya tabbatar da nutsuwar sa ta dawo jikin sa yadawo hayyacin sa,.... sannu suka shiga yi masa batare da ya amsa ba yace yarinyar da nakai gidan mu ita kake magana akai ko yafaɗa yana kallon bossay,   bossay yace eh ita wallahi ni sosai naga suna min kama ko ido nane,   shettima yayi saurin cewa wallahi ba idon ka bane saida kafaɗa kuma nake ta hango kamannin su,    da ƙarfi sam yace no wonder wallahi tunda naganta nima kawai nake mata kallon sani amma na rasa a inda nasan ta tabbas suna kama yazama dole mune mo matar nan duk inda ta shiga shiru yayi na wasu ƴan daƙiƙu yana nazari.... kafin daga bisani ya gyara zama yana fuskantar su da kyau sannan yace to amma me yahaɗa yarinyar da wannan matar da kana ganin tama kasan ba ƴar nan bace ita dan ko dangi ma bazaiyiyu su haɗa ba saboda kowa inda ya fito da ban to amma abun da yaban mamaki  shine wannan maganar da matar nan tayi ta in gaida papa amaganar ta kuma da yanayin ta ya nuna tasanshi to taya tasanshi a ina tasanshi me yakaita kano kuma ni da ace bata nuna ko wata alama ba game da papa to da kamannin ta da yarinyar nan bazai dame niba saboda ana haka daman some times kana iya haɗuwa da irin hakan kaga wani yana kama da wani kuma batare da sun haɗa dangi ba to amma wannan maganar da tayi yasa gaba ɗaya na shiga ruɗani nama rasa wane kallar tunani zanyi akai amma koma meye ina zuwa zan tambayi papa sannan in faɗa masa saƙon ta sai inkwatan ta masa kammanin ta ko zai ganeta ta haka kawai zai sa tunanin ya tsaya waje guda,   shettima yace hakane nima wallahi lamarin yaban mamaki yakamata musan ko wacece wanann matar dan amsoshin tambayoyin mu suna gurin ta ita zata warware mana tunanin mu tagaya mana inda tasan papa da kuma dalilin da yasa ta canza ana batar sunan sa wannan shikaɗai muke buƙata dan maganar kamanni da Ameesha ma a ajiye shi gefe kamace kawai daman hakan tana faruwa aduniya kowa akwai me kamannin sa aduniya dan haka wannan ba abun damuwa bane,     caraf bossay yakarbe shi da cewa a'a wallahi wannan ba kamace kawai ba nidai anawa ganin kamar da akwai alaƙar jini a tsakanin su dan wannan kamanni yayi yawa har maganar kusan iri ɗayace da yanayin karya harshen su nifa tunda muka fito a kanta nake saida nagana ƙare mata kallo tass tunda ga sama har ƙasa kuma in baku manta ba a labarin da dadda ta bamu ai ba asan inda dangin mahaifin ta  suke ba kunga kwa ai a ko ina ma zamu iya haɗuwa danginta mahaifin ta to nide aganina akwai dangantaka  atsakanin su me ƙarfi ma  kuwa,    "eh maganar ka kusan gaskiya ce saidai kuma inde suna da alaƙa da wannan yarinyar to kuma taya akai tasan papa kuma har yanayin ta ya canza ni gaskiya bana tunanin suna da alaƙa kawaide kasan papa ba anan yayi karatu ba dan yataɓa bani labarin loƙacin da nima aka fita dani karatu naƙi yarda yake gaya min shima ai ba anan yayi karatu acan yafi  to wataƙil zai iyayiyuwa ko sunyi makaran ta ɗaya dashi dan naga gaskiya wannan ba ƴar nan bace  ko kuma de wani abun ya taɓa shiga tsakanin su shiyasa da taji sunan yasa ta shiga damuwa, shettima ma yace zancen kenan nima nafi tunani ko haɗuwar wani gurin ce abu yashiga tsakanin su da yasa ta riƙeshi ko kuma soyayya kasan papa akwai ɗaukar wanka ga kyau inajin ko ya yaudare tane kode makaman ci haka, "hararar sa sam yayi yace me kake nufi kenan kakan nawa kake cewa  mayaudari to kwa kamar a kunne sa kafaɗa dan sai nagaya masa, "ɗan murmusawa shettima yayi yace to ai ba ƙarya nayi ba wallahi indai kaga mace tayi kuka ko ta shiga wani yanayi idan aka ambaci mutum to ya yaudare tane ko kuma tasoshi shikuma be sota ba tayi son maso wani daga baya kuma harta haƙura ta auri wani to sai kaga idan suka haɗu dashi ko kuma ƴaƴan sa kode wani abun da ya tuna musu dashi sai kaga sun tsinci kansu cikin wannan halin....    "Sameer yace to nide bansanu ba zan tambaye sa inji idan yasanta zai gaya mana inda take daga nan kuma sai munemi yanda zamuyi idan tana da amfani sai mune meta idan kuma munga ba abun da muke tunani bane akanta kawai sai murabu da ita kawai muyi focusing ɗin abun da ke gaban mu,        bossay dake baya yace to yanzu meye abun yi danni yanzu hankalina ma gaba ɗaya ya tafi kan waccen matar dan gaba ɗaya tafara canzan tunani yakamata muyi nazari akanta sosai wannan abun yana buƙatar tunani da dogon nazari  amma de Ubangiji shi yabarwa kansa sani shiyasa ya haɗamu da su kuma muka rabu dasu akwai abun dazai faru watakil rabuwar ce mafi alkhairi shiyasa muka rabu batare da munji wani ƙarin bayani ba sai yazamana kamar ansaka mu cikin duhu da wani tunani amma de kuma idan muka ƙara nazarin faruwar wannan abun da haɗuwar tamu zamu fahimci kamar wani ƙarin haske ne Allah ya nuna mana a binciken da zamuyi ina ganin ayanzu idan muka samu matar nan akusa damu zamu samo bakin zaren wani abun, ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yace ko ya kukace maganata abar dubawace kuyi tunani akai sosai zaku gane abun da nake nufi amma fa ni anawa ganin kenan da kuma hasashen da nakeyi wannan matar itace muƙullin wata ƙofar tamu wanda saida ita zamu shiga wani wajen.... shiru yayi yana jiran jin ra'ayoyinsu game da bayanin da yayi musu,    "shiru motar ta ɗauka gaba ɗaya kamar babu kowa acikin motar,   sam ne ya katse musu shirun da cewa  "zamu duba maganar ka amma sai mun samu loƙaci sai muƙara tattaunawa akai amma saima na tambayi papa abun da yace duk saimu tattara maganganun muga inda kuma yakamata mu dosa....     shettima yace hakan yayi kaga loƙacin komai zai fara tafiya bayan munɗauko wannan mutumin shima kuma awajen sa zamu samu ƙarin baya ni duk sai mu haɗa su waje ɗaya, to hakan ma da kukace yayi Allah ya dafamana ya shige mana gaba akan abun da mukasa gaba Allah ya taimakekum da tai makon sa yabamu ikon cika alkawarin da muka daukar wa kanmu,           "Ameen!" suka amsa masa dashi gabaɗayan su.,     daga nan ba wanda yaƙara magana Sameer ya tayar da motar suka juya saboda daman banan hanyar zasuyo ba unguwar da mahaifin sumy ya kwanta ta musu suka nufa tunda suka fara tafiya bawanda yaƙara magana saidai kowa yana tasa maganar da zuciyar sa kowa na saƙa da warwara shi kaɗai.............,             *maama*     "dan Allah maama kiyi haƙuri kiyi shiru  wallahi muma zaki iya saka mu kukan ummy ce me maganar muryarta cike da damuwa take bawa maama haƙuri da tunda suka baro wajen ta fashe musu da kuka kuma tambayar duniya sunyi mata akan tafaɗa musu dalilin kukan nata amma taƙi buɗa bakin ta sai kuka kawai harda me sauti  take duk tabi tasaka su a damuwa(daman idan babba yana kuka ai kaima dole kaji kamar kayi kukan nidai saida nayi ma😭, wallahi koya kaga nagaba da kai na kuka saikaji jikinka duk yayi sanyi😢😢)      "da ƙyar suka samu ta ɗan tsagaita kukan nata baya fita sosai yanzu ahaka suka ciga ba da tafiya ba wanda yaƙara magana suna so su tambayeta amma suna tsoron kar su tsokano ta taci ga ba daga inda ta tsaya shiyasa kawai suka rabu da ita suka bari idan sun sauka ta dawo daidai sai su ƙara tambayar ta........               ************************                 *Masarauta* __________cikin fada.        Sarki ne akan ƙasaitacciyar kujerar sa ta mulki wacce aka ƙawata ta da ado kala kala na sarauta ajiki kana kani kasan ba ƙaramin kuɗi aka kashe mata ba wajen ƙawatata iya adon ma da aka yi ado dashi wasu maƙudan kuɗaɗen aka kashe mata ba,       gefen kujerar sa kuma Fulani ce itama a hakinmce akan tata kujerar sai wata kujerar daga can gefen ta papa ne da Ammah a azaune suma atasu kujerar da batakai ta fulani ƙawatatuwa ba,     ƙasa kuma su waziri ne da galadi ma da sauran de duk wanda yadace nakusa kusa de duk de ajali ne awajen amma banda yara dan ko su momma babu su aciki iya manyane kawai agun, waziri ne ya fara ɓude taro da addu'a dayiwa annabi salati kamar yanda yake a addinan ce idan za ayi taro ya wuce mutum biyu zuwa sama anaso kafin afara maganar sai abuɗe zaman da addu'a, "bayan sunyi addu'ar ne" "fulani ta gyara zama tare da bin kowa da ido saida ta gama shan ƙamshinta kamar yanda ta saba aduk loƙacin da taga kowa cewar ta yake jira to fa anan ƴan mulkin suke motsawa saitagama ja muku aji da ƙara ɓata muku rai sannan zata faɗa muku buƙatar ta, yanzu made hakan take bata canza zani ba saida tayi musu haka sannan ta fara magana, "ƙara gyara zama tayi sannan tace tom duk danasan kowa yasan shine dalilin taruwar mu anan maganar da tasa nace kowa ya hallara anan kenan ina fatan kowa yana da masaniya akan abun da yafaru jiya ko? daga cikin mutanen wasu suka shiga jinjina kai alamar eh... cigaba tayi da cewa jiya wajen yamma ansamu wani babba alamari da ya firgitar da al'umma ajiyan nayi tunanin gabaɗaya duniyar ce ko ince garin nema, saidaga baya kuma nakejin labarin wai iya cikin masarautar ne abun yafaru, a gaskiya lamarin yayi matuƙar furgita ni yasakani aruɗu kuma yaban mamaki kai ba abunma da baibanba saboda al'amari wanda nide iya tasowa ta arayuwata bantaɓaji ba kuma bantaɓa gani ba abu kamar almara kamar a mafarki, shiyasa na taraku anan dan jin ta bakunan ko da wanda yake da masaniya da abun da yafaru domin wannan ba abun zama bane dole atashi tsaye dan magance gaba karmuje nan gaba muna ciki muji munkifa ankashe mu loƙacin mu beyi ba yakamata asan abunyi, maganar ta saida tabasu dariya jin yanda ta tsorata kamar ba sarauniya fulani ba yau itace da tsoro ƙarara afuskarta kuma har wai su kifa ko wazai kifar dasu, dan haka saida wasu suka ɗan dara, itama ɗan dan murmushi tayi tace kuna dariya Allah gaskiya nake faɗa wannan ba abun wasa bane maƙiya kuma meye bazasu iyaba muna zaman zaman mu sai kuga anyi abun da zai halakar da mu gaba ɗaya tunda suka fara da haka danni de wannan abun cewa zanyi turo mana akayi da ranar Allah amma gida yayi duhu ga ƙara yaseen wannan ƙarar turo mana akayi sufa maƙiya da mahassada ba abun da bazasu iyayiba, dan haka dole mutashi tsaye dan kare martabar masarautar mu da tsirar da rayukan mu, "a'a wannan fa ba wani ture kar kuyiwa wani ƙazafi aradun Allah kuka shuka abunku kuma zaku girba ai ni ajikina wannan ƙarar wallahi domin wanna abun da yafaru ƙullallan makirci ne kawai na asiri shine ya warware saida kuma nima bazan muku ƙazafi ba akan kune saboda daman sarauta ta gaji haka mebi andaɗe da binne shi sai ajiyan Allah yayi kuncewar sa domin sarauta ce daɗaɗɗiya baza ace ga wanda yayi ba amma dole wannan abun karyewar wani asirin ne daman shi asiri ai haka yake akwai wanda in ya tashi karyewa har jijjiga guri yake ginin wani gurin ma zai iya faɗowa wannan ai yazo da sauƙi, a zamanin mu meye ba magani, irin waɗan nan abubuwan ai tsohon abune awajen na wallahi bayau fara ji ba kuma nasan bayau zan gama jiba saboda wannan haline na mutane ga duk wani wanda ke zaune acikin masarauta sai yayi saidai wani yafi na wani muma da ba muyiba ai da ba mukai wannan loƙacin ba araye, in asirce asircen nanne ba wani ɓoye ɓoye kuma duk munyi saidai namu na hankali mukayi bare kuma ku da kullum kai ƙara buɗewa yake duniya ta zama abun da ta zama, kuma kuma nasan kunyi kallon ku kawai nake ina kawar da kai duk wani mitsin mutum saidai inbeye agaban ido na ba amma yar nake kallon ku shiyasa ma zakuga bana shigowa saboda inna ce zan dawo nan to wallahi ruwa ma sai ya gagari wasu sha ajirayi ranar ƙin dillaci kuma ajuri zuwa rafi watarana tullun zai fashe ne........ wata tsuhuwace da tafi kowa tsufantaka agurin take faman wannan zuba surutun itaɗin uwa ce ga sarki me murabus(papa) mahaifiyar suce wacce suke kira da gwaggo ita ba a ɓangaren take zaune ba tana cen ɓangaren autan ta Ibrahim dan ɓangaren suma sai ka fita daga masarautar tunda mijin ta *sarki Sameer* ya rasu bayan ɗan ta ya hau mulki ita kuma tace ta gama zaman cikin masarautar ita da zaman ta aciki saidai ta kawo ziyara ko kuma idan wani zama yakama akirata ayi shine suka koma wajen masarautar ita da autanta da kuma matarsa da ƴaƴan sa saidai duk da haka shi autan nata Ibrahim yana da part ɗin sa acikin masarautar dan haka ƴanƴan sa ma sunfi zama acikin tunda suka girma kuma suka koma ciki ga ɗaya yarage daga ita sai shi sai matar sa amma awajen ma ɓarin ta daban ita da me aikin ta shiyasa ma batafiye shigowa masarautar ba sosai a iya can take rayuwar ta kuma ba komai dake faruwa aciki take sani ba ba ta tambaya kuma ba a gaya mata saboda tana da zafi mafaɗaciyaci tana da faɗa sosai ga zuciyar bala'i dan zan iya cewa ma duk wani wanda ya fito daga tsotstsonta tofa sai yagado wannan zuciyar kama ga ƴan ƴanra ga jikoki harma tattaɓa kunen ta watakon irin su sam da suke tattaɓa kunne awajen ta....(ashe su sam ba abanza ba wannan zuciyar) duk da ta tsufa idan ka taɓota ka shiga uku dan duk min tsufan ta zata iya cewa zata dake ka dan ta wani wajen bata da mutunci ta wani wajen kuma akwai haƙuri ga abun dariya da barkwanci idan taso amma idan bataso abuba sai kace tafi kowa rashin fara'a da wulaƙan ta abu ita ba mutum ba kowa da komai ma yi mishi take dan ita har abinci ma wataran faɗa take dashi bare kuma ɗan adam ga bata ɗaukar wurgi da raini ko loƙacin baya da ƙuruciyar ta yanzu zakai mata abu duk girmanka tace ka rainata akwai son girma, duk iskan cin fulani tana shakkar gwaggo idan tana gurin to bata yin abun dataga dama tane denawa saboda bataƙi taci mutun cin ta ba ko agaban waye idan tayi ba daidai ba shiyasa basa son ma abun da zaishigo da ita cikin duk sanda tazo sai tayi musu abun da zaisa su ƙara jin tsanar ta kuma suna ganin kamar da gayya wataran take musu abu dan tasan babu yanda za ayi da ita, musamman fulani jitake kamar ta shaƙeta idan ta ganta.. itama kuma gwaggon bata giya shiga harkarta ba shiyasa ma halin su baizo ɗaya sunfi mutun ci da Ammah dake ita Ammah babu ruwan ta da ita koda tayi mata wani abun da bataji daɗin sa ba bata taɓa nuna mata saboda ta ɗauke ta kamar uwa tana yimata biyayya sau da ƙafa shiyasa itama gwaggo bata fiye yi mata wasu abubuwan ba take ɗaga mata ƙafa saboda taga bata da matsala daman ɗayar ce me shegen tsiwa tun tana ciki ta fahimci hakan shiyasa ma koda ta fita indai ta shigo tofa saitayi abun da zata musguna mata dan wataran ko ganin tama batason yi.........gashi kuma ba yanda zatayi da ita itace uwar sarki......, fulani sunkuyar da kai tayi duk sai tajita wani iri aranta kuwa ta zagi gwaggo yafi cikin carbi sai taji dama bata haɗa zaman ba koma waya gayyato ta itade batace akirata ba kawai sai ganin ta tayi aciki tasan hakan zata iya faruwa amma bata taɓa tunani zai kai haka muni ba yaza ayi taso gaban mutane ta ringa cewa suna asiri to uban wa zasu asir ce lalle sai ta koyawa wannan matar zama abun nata yayi yawa dole ta saita ta dan ta kaita ƙarshe duk da tana uwar mijin ta hakan bazai hanata ta koya mata hankali ba dole yasan abunyi akanta bazai yiyu tana abu ita kuma tana warware mata ba tana sama da kowa tafi ƙarfin kowa acikin masarautar amma ita zata zo tana gaya mata abun da taga dama dole ta gane kuren ta nan kusa basai anje ko ina ba..........✍️         more comment more typing, no comment no update.                             💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY   by(mhiz innocent) [6/22, 11:09 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️63&64 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                  "bayan gwaggo tagama magana nan yashiga tofa albarkacin bakinsa wasu suna goyon gwaggo akan maganar datayi gaskiya ce wasu kuma basu soba saboda jam'u da tayi nacewa suma duk suna yi suna ganin hakan baidace ba tace wasu suna asiri acikin masarauta kuma sude sunsan ba abun da sukeyi wannan kamar ƙazafi da cin fuska tayi musu agaban mutane..,,   wasude basuyi magana ba saboda sunsan gaskiya ne anayi amma basu da bakin magana ahakade zuciyoyin wasu babu daɗi taro yatashi batare da ansamu wata mafita game da faruwar wani abun da yafaru kowa yafita daga fadar rai ba daɗi.........    _____Ameesha    zaune take kan gadon su Amra ta zuba uban tagumi ta tafi duniyar tunani,   momma ce ta shigo ɗakin ganinta tayi tagumi yasata ta ƙarasa gabanta da sauri tare da riƙo hannu wanta tace me yafaru haka kika zabga uban tagumi me kike tunani firgit tayi tadawo daga tunanin nata cikin inda inda tace ba komai kawaide zama nayi natashi ne naga su Amra basa nan,   ɗan kallon ta momma tayi badan ta yarda ba tace ayya to yi haƙuri tashi inkaiki wajen su sunje wajen kakan sune sugaida shi nazata ma bazasu daɗe ba shiyasa nace suje da naga kina bacci amma yanzu kiyi haƙuri zo muje inkaiki kema sai ki gaida shi ko kai ta ɗaga mata tare da miƙewa tsaye sannan suka fita daga ɗakin atare tana riƙe da hannun ta,.   saidai ma suna zuwa falo basukai ga fita ba sai ga su Amran sun shigo da gudu Amra agaba hamra abayan ta ɗaya tana cewa Wallahi ni zankaita itama Amra nacewa bana rigaki zuwa ba kuma daman ai ni yace ba ke ba wallahi baki isaba su duk abun da suke ma basu lura da su momma ba saboda hankalin su ba awajen yake ba saida momma ta dakatar dasu sannan suka lura dasu da sauri Amra taje ta riƙe Ameesha tace zo muje yi sauri, momma ce ta kwace Ameeshan daga riƙon da Amra tayi mata tace ke wai lafiyar ku ƙalau ina zakuje kunshigowa mutane guri ko sallama babu,.   cikin haki Amra tace momma yaya Ammar ne fa yace muzo muɗauko duk wanda ya riga kaita zai masa babbar kyauta shiyasa kika ga muna gudu taƙarasa maganar tana ƙara jan hannun ta momma tace to me zaimata yana ina shiɗin meyasa shi bazaizo ba saidai akaita kuje kuce idan son ganin ta yake yazo inda take amma ba inda zata saura kaɗan Amra ta saki kuka jin abun da momma tace duk wannan gudun da tayi abanza kenan momma da wani zance wai yazo da kansa tade san halin ya Ammar ba zuwa zaiyi ba, cikin turo baki tace momma dan Allah kirabu damu mutafi yanzufa zamu dawo kuma idan yamin kyautar nan fa zan sanmiki Allah kisake ta mutafi shifa ganin ta yace mana kawai zaiyi saboda labarin ta da muka bashi shine yace muje mu ɗaukota,          "eh wallahi momma dan Allah kibarmu mukaita cewar Hamra, momma riƙe baki tayi sannan tace to Allah ya kyuata gata nan tunda kunfi ƙarfina amma karkuɗaɗe kunji ni dariya Amra tayi tace bazamu daɗe ba momma mungode tana faɗa taja hannun Ameesha suka fita waje hamra na binsu abaya itade Ameesha binsu kawai take batare da tace musu ƙala ba,     ahaka suka fita daga part ɗin suka nufi part ɗin su Ammar suna ƙarasawa suka shiga ciki yana zaune afalon yanda suka barsa haka suka dawo suka sameshi yana jiran su,     da sallama suka ƙaraso falon ya amsa musu fuska asake idon sa akan Ameesha yana ƙara faɗaɗa murmushin sa dan yanda suka bashi labarin kyaunta sai yaga tama fi haka. masha Allah kawai yake faɗa acikin ransa har suka zo kusa dashi,    Amra "tace wallahi ni na kawota dan haka ni za aba kyauta badanni bama momma cewa tayi baza tazoba Hamra ta harare ta tace yaya wallahi ƙarya take nima nasaka baki Saida na saka bakima sannan momma ta Amince muka fito da ita,    shi duk surutun ma da suke masa hankalin sa ba akansu yake ba gaba ɗaya yatafi gurin Ameesha ita kwa ta sunkuyar da kai saima wani iri da take ji jin idonsa akanta na yawo saitaji soma take tabar wajen dan ta tsani kallo arayuwarta,   "saida Amra ta taɓasa sannan yadawo garesu yace me kuke cewa nan suka ƙara maimaita masa abun da suka ce yace to yanzu de duk kunci kyauta kunsan me za ayima?     "a'a suka haɗa baki wajen faɗa" kushirya gaba ɗayan ku har ita sai mufita inkaiku duk inda kuke son zuwa muje shopping kowacce tazaɓi abun da take so,    atare suka tsalle harda rungume juna sukace yawwa yayan mu shiyasa muke sonka nan suka shiga lissafo inda suke son zuwa yace to kuje kushirya har suna shirin barin wajen yace to ni baƙuwar taku ko gaida ni batayi ba bamu gaisaba kuke shirin fita,      ɗan murmushin yaƙe Ameesha tayi cike da jin kunya tace ina kwana katashi lafiya?   "bana amsawa saida na roƙa zaki gaida ni,    to yi haƙuri ai naga kuna magana ne shiyasa nayi shiru inajiran idan kungama sai mu gaisa, tunda tafara maganar yake bin bakin ta da kallo har saida tayi shiru sannan yace to shikenan na haƙura badan halinki ba,  sunana Ammar duk danasan ma kinji abakin su Ni yayane awajen su inafatan kema zaki ɗaukeni amatsayin yaya ni kuma zan ɗaukeki amatsayin ƙanwa kamar su ina fatan hakan ba wata matsala,?    "ba komai nikuma sunana Ameesha     "nice to meet you"   "same here" ta bashi amsa sosai ya shagala da kallon ta shide ganin ɗaya yayi mata amma duk tagama tafiya da imanin sa jiyake kamar ya tashi yayi ta tsalle ya rungume ta saboda yanda yake ji acikin ransa,   "yaya bari muje mu shirya "Ok"   kawai ya iya basu amsa sukuma suka juya suka nufi hanyar fita tunda suka fita yake zubawa bayan ta ido bai ɗauke ba saida suka fita daga falon yadena ganin su sannan ya miƙe shima yana ƙara sakin murmushi da saƙe saƙe fal zuciyar sa ya nufi nasa part ɗin dan shiryawa shima, tunda suka fita suka fara tsokanar ta wai daga gani fa yayansu ya ƙyasa da ita itade saidai tayi musu murmushi batace musu komai ba har suka ƙarasa part ɗinsu suka shiga da murnar su suka sanarwa momma dake falo tana jiran shigowar su,   itama da murnar tace kaga ƴan gatan Ammar to sai kuyi sauri kar kuɓata masa loƙaci yace ya fasa musamman ke Amra me shegen nawar shiryawa sai kiyi sauri tace momma ai ni zan fara shiryawa ma duk saina rigasu shiryawa,   momma tace  dade bansan halinki ba sai kice haka,   "Wallahi momma da gaske nake, momma tace "to Allah yasa da gaskenne,   "tace "Ameen" tana dariya    Hamra tace "wallahi momma karma ta shirya taga inzamu jirata tana zama zamuyi tafiyar mu mubarta taji asalan sa,    "ku kun isa ku tafi kubarni ai wallahi indai banje ba to babu me zuwa aciki kinku gwarama ki gyara maganar ki yarinya,   "au nice yarinyar taki ni kike cewa yarinya momma kina jin abun datace ko,     *Momma tace "ku tsaya faɗa ku ɓata loƙacin ku anan ku daman ai ba a abun arziƙi da ku lafiya sai kunsa mutum yi da baki, ƙwafa Hamra tayi tare da jen hannun Ameesha suka wuce tana gunguni ƙasa ƙasa, Amra ma bata ƙara cewa komai ba tabi bayansu suka tafi ɗakin su.....     da kallo momma tabisu tana jinjina irin wannan halin nasu na faɗa da bazasu taɓa zama lafiya ba sai kaji kansu ko yaushe zasu girma su dena wannan halin nasu...... "Assalamu alaikum ina masu gidan nan ? sallamar ce ta katsewa momma tunanin da take da sauri ta miƙe tsaye tana washe baki tace lale marhaban hajiya gwaggo yau kece awajen namu sannu da zuwa tafaɗa tana nuna mata waje,   zama gwaggo tayi itama fuskarta dauke da murmushi    bari inkawi miki abun motsa baki gwaggo dan nasanki da kwaɗayi bakin ki besan tsofa ba,    dariya gwaggo tayi tace naci ƙaniyar ki kinji mun yarinya nikike cewa ina kwaɗayi yo inama ruwanki da bakina daman baki na tsufa to saidai ko inna uwacen taki ne ya tsufa amma banawa ba dannawa yama fi naki kwari aradun Allah, ni yi saurima kisamo min abu me ɗan daɗi daɗi kinsan banason barin bakina hakan nan ba abu acikin sa nafiso kullum inganshi yana motsi,   dariya momma tayi sanann tace kingani ko ai kwaɗayin kenan idan so kike kiji bakinki kullum cikin motsi ai goro yakamara ki nema kamar yanda ko wane tsoho yake ciki idan ya tsufa amma ke saboda kwaɗayi kinƙi cin goro sai abu irin na matasan mutane irin mu kinci zamanin ki kinci na ƴaƴan ki ga na jikokin ki amma duk dahaka be ishe kiba sai kinci na tattaɓa kunnen ki gaskiya yakamata kibarmu haka kiɗan bamu guri musha iska ko masumu muci wani abun muma amma duk kinbi kin handime na kowa,    uwarki sa'adatu nace uwarki sa'adatu ko bakiji ba in ƙara maimaitawa uwarki sa'adatu tafaɗa tana cilla mata daƙuwa kinji mu da ja'irar yarinya uban me zanyi da goro ai ni haryanzu banyi tsufan da zanci goro ba ke koma nayi bazanci ba cin goro ai na marasa aikin yine abun da inkana cinsa kamar taba yake zamemaka idan bakaciba kashiga wani tashin hankalin gashi kuma daman lafiyar ka kake lalatawa shiyasa ma masu cin suke mutuwa da wuri basu san kashe kansu suke ba, ke wallahi ma Allah ya isana idan kika ƙara cemin inci goro bansan me yasaba kaf cikin ku kinfi rainani wallahi to wallahi saidai uwarki ta baku gu kusha isakar dan duk sai kun mutu kunbarni sai naga gawar kowa acikinku har ubanna ki daman shi naga harma yafini tsufa da wuri zai mutu wannan wallahi bai gaji jiki irin nawaba duk wanda ya biyo ni bazai mutu da wuri ba amma duk da haka sai ya rigani mutuwa,     ohh gwaggo ai namanta ashefa ke za abawa gadin duniyar ma gaba ɗaya kece me gadin ta sai kowa na duniya ya mutu ya barki ko hajiya gwaggo,   aniyarki ta biki komade menene sai kun mutu kun barni ko banyi gadin duniya ba ammade kiris zai rage bankaiba dan ina mutuwa ba daɗewa za ayi tashin duniya kowama ya mutu a huta,    dariya momma tayi ganin gwaggo zata fara sakin layi yasatayi saurin cewa bari inkawo miki wani abun idan kinci maci gaba daga inda muka tsaya Hajiya gwaggo me ranƙafe Allah ya nuna min ranar mutuwarki ranar har ƙaramin shagali zamu haɗa tana tafaɗa tayi saurin barin wajen amma duk da haka saida gwaggo ta jefe ta da filo tana ƙara sirfa mata wata masifar harda su zagi itade momma dariya kawai take har ta ƙarasa kitchen daman sun saba indai suka haɗu sun ringayi kenan har sai sun rabu kuma daman duk cikin jikokin ta sunfi wasan jika da kaka shiyasa yanzuma da suka gama zaman fadar da harta tafi sai kuma ta fasa tace sai tazo wajen ta.......     ba jimawa momma ta fito da try cike da kayan marmari data yanyanko mata sai sai juce da kuma snaks duk ta haɗo mata ta ajiye mata agaban ta sannan ta kalle ta tace to acici dame za afara gashinan kicinye idan ma bai ishekeba sai aƙaro wani tafaɗi maganar tana tashi ta koma gefen kujerar ta ta zauna tana kallon ta,     gwaggo kam sai faman washe baki take saikace bata taɓa ciba ko kuma bata saba ciba haka take intaga abinci itade tana son abinci koma meye kawai taga bakin ta na tauna,     meat fie ta fara ɗauka takai baki saidai tauna ɗaya tayi masa ta dawo dashi saboda yaji da taji,     "Amma kede akwai muguwa wallahi kinsan bana son yaji ko kaɗan amma shine kika kawo min shi danki cutar dani ko to ke da Allah ga abunki nan ni nama fasa ci gaba ɗaya sai ki kwashe kayanki hankalin ki ya kwanta naƙi ci daman haka kike so tafaɗi maganar harda hararar ta tana kawar da kai gefe,     "momma saura kiris dariya ta kwace mata ganin yanda tayi saurin kaiwa baki kuma tayi saurin dawo dashi kunshe dariyar ta tayi gudun karta ƙara harzuƙa gwaggo tayi saurin saukowa ƙasa tace haba gwaggo ta kinsan de ai bazan taɓa baki abun da zan cutar dake ba kiyi haƙuri kici wani abun wallahi bansan da yajiba aciki bani nayi ba kuma banci ba ga fruit nan kisha bari insamo miki wani abun marar yaji wallahi bansan da yaji ba Allah da gaske nake, "dalla malama rufe min baki kina sane ai kikawo min bazan taɓa yarda bakisane ba ni bari ma kiga tafiyata basai na ƙara dawowa wajen ki ba bare kicutar dani sokike daman kiga bayana ai to saidai ni inga bayanki duk baƙin cikin ki, tafaɗa harda dungure mata kai sannan ta miƙe tsaye, da sauri momma ta miƙe itama tace dan Allah gwaggo na kiyi haƙuri kici wani abu inma baza kici komai ba kizauna muyi hira kinga kindaɗe daman bakizo ba kuma nasan inkika tafi zamu daɗe bamu ƙara haɗuwa ba, "ni bazan zauna ba idan kinason ganina kibiyo ni inda nake amma bazaki ƙara ganin ƙafata anan gurin ba, ke karma kizo inda nake na hutar dake daga yau bani bake munkunce mutun cin dake tsakanin mu mun raba gari dake tunda ke muguwa ce, "haba gwaggo tunda muke dake haka ta taɓa faruwa banda yau yauɗin ma kuskure akasamu dan Allah kizauna, da ƙyar tasamu ta lallaɓata ta haƙura ta zauna itama ɗin daman ba tafiya zatayi ba tsokanar ta take kawai,    zama tayi taci gaba da shan fruit tana sha tana lumshe ido saida ta kusa rabi sannan tadakata tare da kallon momma tace ke wai ina wannan marar mutuncin ɗan naki da baya ganin kowa da gashi naji ance yadawo amma bantaɓa ganin saba, "ai ya daɗe dawowa ma gwaggo dan yamafi wata ɗaya baizo ya gaidake ba?     "kinturo sa ne ai bakice yazo ba duk wani hali da yakeyi ai ku kuke ɗaure masa gindi shiyasa yake ƙara raina kowa ni asuwa zaije inda nake harma ya gaida ni yaron da wataran zaka haɗu dashi ahanya amma yanuna baisan dakai aduniyar bama bare yasan kana gurin ai wannan yaron wallahi kaf zuri'ata bame baƙin hali irin nasa ga shegen taurin kai bansan inda ya ɗauko wannan mugun halin ba dannidai bahaka nakeba kuma ƴaƴana ma bahaka suke ba kuma Sa'adatu ma bahaka take ba bare ince ki ita yagado, cikin sanyin murya momma tace wallahi gwaggo ba wanda yake ɗaure masa gindi kullum cikin faɗa nake masa amma kullum abun nasa gaba yake saidai mucigaba da yi masa addu'a itakaɗai ce zata gyara sa, taɓe baki gwaggo tayi cikin ko inkula da yanayin da momma tayi magana saima ciga da cewa tayi kedai wallahi baki yi sa'ar ƴaƴa ba hargwangwan da ɗayar ma akan wannan ja'irar yarinya me kama da tsutsotsi kullum cikin mutsul mutsul take sai fitina kamar beranniya batason zama guri ɗaya ni harna tsani ma tazo inda nake ganaci kuma ina koranta tana ƙara danno kai  kace kuma zaka daketa tasa kajiwa kanka ciwo abanza shiyasa bana kulata idan tazo nake mata banza tagama abunta ta tafi dan wallahi tafi ƙarfin.......   "bata ƙarasa maganar ba taji faɗowar mutum akanta...   "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un nashiga uku zata karya ni wallahi zata karyani abun da gwaggo take ta faman faɗa kenan tana ture Amra dake kanta ɗane ɗane akanta tana mata dariya, "ɗaga ni dan jakar ubanki kedai wannan bazaki ga annabi ba iya cin zalina dakike zai hanaki ganin annabi muguwa kawai nadan ƙashin nawa me ƙwari bane ai da tuni kindaɗe da ɓaɓɓllani kin karairaya min ƙafafu bazaki ɗagani ba sai nacimiki uwa agunnan wallahi kifita daga idona inrufe tana maganar tana tureta daga kanta amma taƙi tashi sai faman dariya take mata tana cewa "Allah bazan sauka ba nayi missing ɗinki dayawa fa yau wajen kwana uku kenan banga wannan ya gwalgwalalliyar fuskar taki ba me kama da ruɓaɓɓan tumatur  wallahi matar nan ki tusfa da yawa bari muji da sauran ki ko kuma kinzama laida tana faɗar haka tasauka daga kanta duk a tunanin gwaggo ɗaga tan datayi tarabu da ita kenan dan harda murna ganin ta ɗagatan saidai kuma bazato ba tsammani taji an yago mata fatar fuskar ta wajen kumatu ai ba shiri gwaggo tasaki ƙara tana riƙe gurin tama cewa shikenan yau tarabani da fuskata ku dubamin babu komai anan gurin tafaɗa tana nuna musu inda takejin zafin Allah sarki tsohuwa ta rikice abun tausayi abun dariya,    ita kwa Amra dariya take harda riƙe ciki tanayi tana nunata da yatsa sannan tace wai daman kinajin zafi har yanzu fatar nan daman bata mutu ba ai ni nazata fa bazakiji zafi ba ayyya gwaggon mu me ran roba yi haƙuri bansan da zafi ba wai nan haƙuri take bata amma tana maganar tana dariya data gama maganar ma ta ƙara kwashewa da wata dariyar muguntar,      "momma ce tayi mata magana tace meyasa zakiyiwa gwaggo haka dan Allah kinga yanzu kinjawo mana bala'i tunda kika sa ta zubar da hawaye itama momma dariyar take son yi amma ta dake saboda kar gwaggo ta haɗa da ita idan ta dawo hayyacin ta, Allah ya isa tsakanina dake wallahi bazan barki ba sainasa an zane minke sai an farfasa miki jiki ni zakiyi wa wannan rashin mutuncin cire min fata to kwa wallahi bakiyi a abanza ba wannan karon sai rama duk muguntar dakike min sai narama ta yauɗin nan bari wancen marar mutuncin yadawo tunda shi kike tsoro daman zan sakashi ya karairaya min ƙasusuwan ki Allah wadarai da halinki gwaggo ji take kamar ta shaƙota amma tana tsoron abun da yarinyar zata iya aikata mata idan ta taɓata shiyasa ta rabu da ita kwai saboda tana tunanin yarinyar nan ba ita kaɗai bace tana tare da mutan ɓoye shiyasa ko tayi niyar yi mata wani abun take kasawa,    Woooo wooo waya ce kikawo har loƙacina da kin mutu ai da tuni kin huta amma kinƙi mutuwa nifa nagaji da ganin ki ma shiyasa nakeso na ƙarasa ki yaseen da sauri gwaggo ta miƙe tsaye tace bari ni kafin ki ƙarasani ni inƙarasaki dan jakar ubanki shegiyar yarin kai dan kinga ina rabuwa dake ko to wallahi ba ƙarfina kika fi ba,    da sauri Amra tabar wajen tana mata dariya ta haye sama gurin su Ameesha kamar yanda tace ita zata fara shiryawa hakan kwa tayi ita tafara shiryawa shiyasa ta sauko dan nunawa momma shirin nata dace ita zata farayi sai kuma tayi karo da gwaggo shiyasa ta tsaya neman magana bata faɗi abun da yakawo ta ba, [6/22, 10:59 PM] Rashh: komawa gwaggo tayi kan kujera tazauna tana faman sauke numfashi tana zabgawa Amra Allah ya isa da zagi kala kala itade momma hakuri kawai take bata tana yi mata sannu dake farace kwa gurin da Amra taja mata har yayi ja, ruwa momma ta dauko mata sanyi tabata atake kwa ta karba ta shanyi shi tas tana sauke ajiyar zuciya tayi lamo ajikin kujera sai faman wuqi wuqi da ido take ido ya raina fata...... [6/22, 10:59 PM] Rashh: da gudu Amra ta fada dakin nasu tana dariya tana shiga ta qulle qofar da muqulli Hamra tace ke meyafaru harda sawa qofa maqulli wa kika tsokano,   "cikin dariya tace gwaggo ce ta biyoni wai dannaja mata kumatu kinga yanda tayi harda kuka wai taji zafi hhhhh taqara sakin dariya,    "Allah ya shirye ki wallahi kin takurawa wannan matar kina shiga haqqin ta da yawa dan wulaqanci yau abun naki harda sakata zubar da hawaye gaskiya baki kyauta ba daman mungama muje kuma idan muka fita sai munyi miki calin calin da sister Ameesha munkaimata ke ta rama abun da kikayi mata ko kuma murama mata ko ya kikace sister tayi maganar tana kallon Ameesha data gama shiryawa itama dan dariya tayi sannan tace gaskiya de haka yakamata muyi mata kakar kuce ko?    a'a wallahi babar kakan muce fa shine dan taga ta tsufa dayawa take mata abun dataga dama ta rainata da yawa,    "a'a bangane ba kamar ya babar kakan ku nufin ki bama kakar kuba kakar maman ku kenan ko?     "Eh" " tab amma har yanzu tana raye amma ta tsufa da yawa? "Eh mana tsohuwa ce amma inkika ganta bazakice takai haka ba tana da kyaun jiki ne kawai,    "gaskiya de nikam zanso inganta wallahi  kalli fa ko momma ta kusan tsufa bare kuma kakan ku shima nasan tsoho ne amma ita kuma ace tana raye Allah me iko amma ta kusan kaiwa shekara dari biyu ko?   dariya suka yi gaba dayan su suka ce mata wallahi bata kaiba amma de basu san shekarar ta nawaba,    " to dan Allah idan munje ku gwada tambayar ta muji,   Hamra tace "saidai Amra ta tambayar miki itace daidai da ita ni yanzu dake ta rainani sai ta hauni da masifa saboda masifaffiyace amma tana shakkar Amra,  Amra saitayi mata abu ta rabu da ita amma ni inayi mata zata hauni da masifa dan taga ni bana yimata abun da Amra take mata, ko gigin tsufane yake rudata wanda yake mata rashin mutunci bashi takewa ba wanda kuma yake mata biyayya akanshi take saukewa, "Hhhh" ita kuma haka take to wallahi tsufane dan Allah kuzo muje karta tafi ina so inganta ke kuma Amra idan munje kiqara tsokano mana ita nifa wallahi inason inga tsoho na masifa ko yace zaiyi gudu ko duka abun na ban dariya wallahi,     " lalala kice kema irin Amran ce to wallahi nidai ba ruwana ke da ita duk da kina baquwa ba ruwanta sauke miki zatayi dan ba mutunci ne da itaba,    "Eh na yarda aide nasan bata fini gudu ba danni zan iya satama muyita yar guje guje a falon nan nasan zata gaji dan kanta,    "yauwa yar gari ashe halin mu daya dan Allah zo muje mu dan wahalar da ita kafin mu wuce nasan yaya ammar yana can yana jiran mu kar yayi fushi yafasa zuwa,    "Hamra tace ai ko awa nawa zamuyi bazai fasa ba tunda daman badan mu zaiyi ba ga dan wacce zaiyi kinga kwa dole ya jiramu dan fitar nan tashi ce saboda kansa zaiyi ta ke kinga wani kallo da ya ringa yi miki gaba daya fa yagama tafiya,   sister gaya mana siriin dan naga loqaci guda ya kware miki cewar Amra tana dan daga mata gira daya,    "ni dan Allah kubar wannan maganar ba wani danni kawaide zaikaiku ne dan ra ayin kansa badan niba kuma ni ba abun danakeyi kai nifa inama da wanda nakeso karma kuyi tunanin wani abun,     "muma ai bamuce komai ba muje de kawai ai wannan ne haduwar farko loqacin da za azo ana cewa wallahi nayi missing dinshi na dade bangansa ba yen yen yen nande gaba wallahi kar azo ana mana yar murya akan yayan mu ehe cewa Amra,      " Allah ya kiyaye ma ranar kwa bazata taba zuwa ba kunga ni dan Allah a ajiye zancen nan idan kuma bahakaba wallahi zan iya fasa zuwa,    tab da kwa kinga yaya ammar har cikin dakin nan dannasan tsaf zaishigo ya fita dake dan ba kunyar kowa zaji ba acikin gidan nan har gwarama da ace ya sam yana nan to shine ma watakil bazai shigo ba amma kinga yanzu tsaf zai shigo ya fita dake,     "hmmm kanku ake ji ni mutafi dan Allah banason wannan surutun naku in kuma bazaku fita ba incire kayana in kwanta daman baccin be isheni ba, "mu mun isa mufasa fita yanda na tamawa fitar nan ai bazanso wani abun da zaisa afasa ba, cewar Amra kenan,    ke kika sanide kuma de kunsan inna fasa ba fita ko, Hhhh munsani mana auntyn mu muje kawai atare suka fito suna ta kara tattaunawa har suka fito falon, momma kadai suka gani acikin falon da sauri Amra tace momma ina gwaggo tayi tamayar tana dariya tina abun da yafaru dazu,   itama momma tana dariyar tace bayan kingama wahalar da ita din zata zauna ai ta tafi kuma wallahi tace saita kai qararki wajen papa tunda me sunan baba be dawo ba,     "Momma yanzu haka tana cen wajen papa hamar ta tambaya,   "Eh tana cen amma de bansan a ina zata same shi ba ko yana part din mama fulani ko kuma yana part din Ammah saidai kuje ku duba,    Amra tayi dariya tace lalle ma matar nan angaya mata ina tsoron papa ne ai saidai ma yagoyi bayana papa ai nawane kuzo mutafi yau akwai wata dramar naga kuyi sauri tafada tanayin gaba,   momma tace fitar taku fa ba gwara kuje inda zaku ba da kutsaya kuna batawa kanku loqaci yazo yayi ta jiranku dan Allah ku haqura ku tafi kar ku bata masa loqaci, [6/22, 10:59 PM] Rashh: "a'a momma wallahi sai munje ai ba dadewa zamuyi ba inji hamra tana jan hannun Ameesha suka bi bayan Amra da har takai ga fita waje,   Atare suka jera gwanin ban sha'awa suna tafiya abun su har suka karasa part din Ammah suka fara zuwa tundaga qofar shiga wata jakadiya ta sanar dasu cewa basa nan, part din fulani suka nufa saida kashe nan ma suna shiga basuga kowa a falon ba dan haka sai hamra da Ameesha suka zauna afalon ita kuma Amra ta qarasa can cikin dakin fulani bayan tayi sallama an amsa mata ta shiga sai ta samu fulani ita kadai nan suka gaisa sama sama saboda har yanzu bata dawo daidai ba daga abun da gwaggo tayi dazu, mama fulani dan Allah gwaggo fa bata shigo nan ba?     data shigo ai da kinganta da kika shigo ko, oh ai nazata ko ta shigo ta fitane shiyasa na tambaya,    " to bata zoba, Ok to sai anjima.... tana fadar haka ta juya ta fice daga dakin, tana fita tace bata nan muje kawai idan mundawo sai muje har inda take mu same ta.. dukansu mikewa sukayi suka qara fita daga part din, tundaga waje suka hango Ammar har ya fito cikin shirin shi tsaf yayi kyau kuwa abun sa daman kuma me kyau din ne sai kuma ya qara da wanka sai abun yayi gwanin sha'awa yayi kyau sosai,   da sauri suka qarasa inda yake suna yabon kyaun da yayi shikam sai faman sakin murmushi yake daman yana sane yayi wankan dan ya burge Ameesha sai kuma gashi ya burgeta din duk da batace komai ba amma yasan aranta ta yaba da kyaun nasa,   da kansa ya bude mata gaban mota yace ta shiga qin shiga tayi ta juya ta kalli su Amra suna hada ido suka dage mata gira daya tare da bude bayan motar suka shige sunyi mata dariya qasa qasa,    bayanda ta iya haka ta  ta shiga batare da ta kalle saba, tana shiga ya rufe shima ya zagaya ya shiga ba bata loqaci yatayar da motar yajata suka fita daga masarautar ransa fal da murna,   saida suka dau hanya sannan yajuyo yana kallon ta tare da yi mata magana yace awace unguwar kuke shiru tayi taba tunanin amsar da zata basa jin bata basa amsa ba yasa yaqara cewa wacce makarantar kike nan tabashi amsa da haka de yadin ga jefo mata tambayoyi wasu ta amsa wasu kuma tayi masa shiru so yake tasaki jiki dashi amma hakan ya gagara amma yabawa kansa daga nan zuwa gobe sai ta saba dashi,      wajen wani shaqatawa yakaisu yasa kowa ya zabi abun da yake so akawo masa saida yajira ta zabi nata sannan shima yace akawo masa irin sa, bayan ankawo musu sunci sun sha kowa yaci itana kuma bata tsaya fulako ba tasaki jiki taci abun ta son ranta,   daga nan kuma yaqara dibansu sukaje wajen wasanni zuwa loqacin kuwa har yayi nasara dan tafara warewa dashi su Amra sai tsokanar ta suke, bata biye musu saidai tayi murmushi kawai wani kuma tace musu su dena bata so ahaka suka wuni suna zagaya gari sai dab da magariba  suka nufi wani dan qareran shopping mall nan suka tsaya bayan sun fito daga mota suka shiga ajere shida ita agaba su Amra abaya suna gulmar su har suka shiga ciki nan fa kowa yafara diban abun da yake so kuma harda ita batayi fulako ba anan ba ta zage duk abun da taga sun dauka itama idan ya burgeta sai ta dauka hakade sukaita daukan abubuwa kala kala sannan suka hakura suka barshi haka bayan kowa yagama kwasar abun da yakeso,   wajen biyan kudi sukaje aka lissafa Ammar ya biya aka saka musu kayansu aleda kowa da ledar sa,    Ammar ne yafara kwasan ledojin masu nauyi yayi gaba dasu sukuma yace su dauko sauran amma banda Ameesha ita ba ta dauki komai ba,   Su hamar ne kawai suka kwaso sauran kayan sannan sukayi gaba ita kuma tana binsu abaya, wajen motar suka qaraso inda Ammar yake ajiye kayan abayan mota suma nan suka nufa suka ajiye nasu sannan ya rufe yace su shiga shiga sukayi shi kuma ya zagayo dayan barin dan budewa Ameesha sai yaga bata wajen ciki ya leqa amma nanma baiganta ba sai ya leqa gurin su hamra dasuke ta faman surutu akan kayan da suka dauko sai yaga su biyune kawai aciki,   ina take ne nagan ku kukadai ina kuka barta kallon sa sukayi gaba dayan su tare da cewa aa tare fa muka fito,      to ko komawa tayi cewa Ammar,   bude motar sukayi suma suka fito sukace to watakil bari muje muduba ko ta manta wani abunne nan suka sake komawa ciki gaba dayan su,   suna shiga tundaga farkon qofar suka tambaya ko wata yarinya ta dawo sukace gaskiya bayan fitar sude ba yarinyar da ta dawo amma de su shiga su duba kobasu lura da shingan ta ba, shiga sukayi suka fara duba lungu da saqo suna nemanta amma ba ita ba dalilinta wajen suka qara dawowa suka dudduba amma basu ganta tofa abu kamar wasa yana shirin zama gaske hankalin sune yafara tashi ciki suka qara komawa akaci gaba da naimanta tun suna abu su kadai har ya koma ga kowa ma yaji nan aka shiga nemanta har manajen wajen ma saida yaji hankalin kowa yatashi wajen nemanta........    Nimade hankalina yatara tashi shin Ameesha ina kika shiga kika boye????                       💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [6/24, 7:10 AM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️65&66 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                  tofa wata sabuwa inji dan caca ana wata ga wata anduba ko ina na wajen babu Ameesha babu me kamar ta sama ko qasa babu Ameesha, Allah sarki twins har sunfara kuka hankalin su gaba daya baya jikin su dan sun fara fita hayya cinsu sai faman kwala mata kira suke kamar sunganota awani wajen duk sunbi sun furgita shima Ammar dauriya kawai yake yana basu baki dan shi yama fisu shiga tashin hankali saboda shi yadauko su yanzu idan ya koma me zaice taya zai fara tunkarar gida da wannan zacen ace yarinya sukutun guda anne meta anrasa gashi kuma bakuwa ce danshi da ace acikin twins ne bazai tada hankalin sa kamar yanda yaje ji akanta ba babban yayan sune ya fado masa arai take yaji wata sabuwar zufa na wanke masa jiki duk addu'ar da tazo bakinsa karanta yake kansa ya qulle gaba daya yama rasa wane irin tunanin zaiyi abun abun mamaki ace yanzunan su fito tare kuma ace anne meta anrasa to kode sace ta akayi, kai a'a wata zuciyar ta basa amsa to idan ba sace ta akayi ba ina tashiga ai duk inda taje da suganta to inama zataje ita datake baquwa ba inda tasani, kawai hannu ya dora akai yanaso hawaye suzubo masa ko ya samu rangwamen abun da yakeji game da wannan al'amarain da yayi mugun daure masa kai, cikin kuka Hamra tace yaya mu koma gida ko zamu ganta acan, dagowa yayi ya kalleta jin shirmen da takeyi yama kasa tanka mata sai faman binta da ido da yake azahiri ita yake kallo amma a badini bahaka bane hankalin sa ba akanta yake ba, Amra ce itama cikin hawaye shabe shabe da ya wanke mata fuska tace yaya mutafi gida muje mudubo ta ni nasan tana gida watakil tsokanar mu take ta tafi ita kadai kataso mutafi, duk surutun da takeyi itama ba sauraron ta yake ba, tashi yayi daga bakin mall din da yake zaune yaqara komawa ciki dan ji yake kamar zai ganta amma yanda ya shiga haka yaqara fitowa shikadai wajen suka qara dubawa har tafiya suka danyi aqasa me tsayi suna nemanta wai ko zasu ganta tabi wata hanayar amma shiru basu ganta ba, ba yanda suka iya haka suka koma mota suka shiga sannan yaja motar da kyar suka dauki hanyar gida zuciyar sa na ta bugu saboda baisan me zai faru ba idan akaji wannan batun agida, ahaka yaringa tuqin hankalin sa rabi akan tuqi rabi a tunani da haka har suka qaraso gida bayan an bude masa gate ya shiga yanufi parking lot yayi parking amma da yayi parking din sai yakasa fitowa daga cikin motar yana fargaba suma su Amra ganin baifito ba sai suma suka kasa fitowa sai sukaji wani tsoro ya qara dirar musu loqaci guda, juyowa yayi yakalle su ganin sunyi tsuru tsuru sun hade guri daya sunkasa motsawa sai suka bashi tausayi da saboda su kawai yadan yi qarfin hali ya bude qofar sannan ya bude musu sunma yace sufito kamar jira kwa suke haka suka fito da sauri suna fitowa basu tsaya bi takansa ba suka kwasa aguje suka nufi part dinsu, da sauri shima yabi bayansu yana kiran sunan su amma ina har sunyi nisa basu saurare saba, saurin yaqara shima yabi bayan su cikin sarssarfa gudu gudu sauri sauri saboda so yake shiyafara fada kafin su sufada saboda bazasu fada cikin sigar kwantar da hankali ba shiyasa bayaso suriga sa zuwa, aikin gama yagama domin kwa yana saka qafarsa a falon, "Amra nacewa momma ansace Ameesha, tsayawa yayi cak tare dacewa damm it yana furzar da iskar bakin sa me zafin gaske, momma da fitowar ta kenan daga kitchen taji maganar wani iri ban barakwai ta dake ta, tunanin ta ko bataji abun da Amran tace bane dan haka tayi saurin matsawa kusa da ita tana riqeta tace ke menaji kince kode kunena ne yaji min ba daidai ba, "momma bamuga Ameesha ba mun nemata munrasa, hamara tafada cikin sanyjn murya tana goge hawayen fuskarta, mutuwar tsaye momma tayi tamakasa kwakkwaran motsi da kyar bakinta na rawa tace bangane abun da kuke nufi ba kuyi min bayani yanda zan gane j na kuka baro yar mutane kuma har kuka iya dawowa cikin gidan nan batare da ita ba, ina take !!!? tayi maganar cikin daka musu tsawa datasasu hadewa waje guda suka riqe junan su tare da sakin kuka, "baza kumin bayani ba sai nayj maganin ku anan gurin, Ammar ne ya runtse idon sa tare da budesu har sun canza kala ahankali ya shiga takowa zuwa gurin su, cike da murya me rauni dan shima muryar tasa har rawa take yace momma kiyi hakuri ba laifin subane laifinane ni babba duk wani hukunci ni za ayankewa shi amatsayina na babba kuma ni na dauke su na fita dasu da banfita dasu. ba da duk hakan bata faru ba, kasaqe momma tayi tana jin maganganun sa juwa taji tana neman yarda ita da sauri tayi saurin dafa kujerar gefen ta sannan ta zauna dan idan bata zauna ba sai ta iya faduwa agun gumine ya shiga tsatstsafo mata duk sanyin Ac dake tashi afalon amma haka tafara gumi saboda tsabar shiga rudani dan maganar ba qaramin dakar mata zuciya tayi ba, tsugunnawa yayi agaban ta idon sa aqasa ya sunkuyar dakai sannan yashiga zayyano mata abun da yafaru tundaga A har Z, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take maimaita wa a fili tayi yafi aqirga sannan tace kunkashe ni wallahi kun kashe ni yarinya daga zuwa amma kuce min wai kune meta kun rasa da wane idon kuke so inkalli yaran nan wallahi basason bani ita tayj weekend din dan na fahimcj dan ba yanda zanyi dasune shiyasa s h ka bani ita amma yanzu suzo daukar ta kawai sai ince musu ta bata taya kuke tunanin zasu dauki maganar to wallahi daga nan zuwa gobe duk yanda zakuyi ku nemota kuje ku nemota dan wallahi bame kwanar min agida kifita kuje kunemota saboda tsabar shiririta kunsan batasan wajeba meyasa bazaku sakata agaba ba kuna kallon ta shine kuka barta abaya to wallahi kwa duk indama tashifa sai kun lalubota adaren nan dan bazaku jamin bala'i ba ina zaman zaman zamana idan wallahj ku tafi kunemota tunkan yayan ku yasa qafa acikin gjdan nan idan yaji labari kashin ku ya bushe kunsan halinsa sarai basai nagaya muku ba baza kuji dadi ba gaba dayan ku, tsoro ne yaqara kamasu jin batun da momma tayi, sosai zuqatan su suka sake tsinkewa su yanzu ta ina zasu fara neman ta, tofa wata sabuwa inji dan caca ana wata ga wata anduba ko ina na wajen babu Ameesha babu me kamar ta sama ko qasa babu Ameesha, Allah sarki twins har sunfara kuka hankalin su gaba daya baya jikin su dan sun fara fita hayya cinsu sai faman kwala mata kira suke kamar sunganota awani wajen duk sunbi sun furgita shima Ammar dauriya kawai yake yana basu baki dan shi yama fisu shiga tashin hankali saboda shi yadauko su yanzu idan ya koma me zaice taya zai fara tunkarar gida da wannan zacen ace yarinya sukutun guda anne meta anrasa gashi kuma bakuwa ce danshi da ace acikin twins ne bazai tada hankalin sa kamar yanda yaje ji akanta ba babban yayan sune ya fado masa arai take yaji wata sabuwar zufa na wanke masa jiki duk addu'ar da tazo bakinsa karanta yake kansa ya qulle gaba daya yama rasa wane irin tunanin zaiyi abun abun mamaki ace yanzunan su fito tare kuma ace anne meta anrasa to kode sace ta akayi, kai a'a wata zuciyar ta basa amsa to idan ba sace ta akayi ba ina tashiga ai duk inda taje da suganta to inama zataje ita datake baquwa ba inda tasani, kawai hannu ya dora akai yanaso hawaye suzubo masa ko ya samu rangwamen abun da yakeji game da wannan al'amarain da yayi mugun daure masa kai, cikin kuka Hamra tace yaya mu koma gida ko zamu ganta acan, dagowa yayi ya kalleta jin shirmen da takeyi yama kasa tanka mata sai faman binta da ido da yake azahiri ita yake kallo amma a badini bahaka bane hankalin sa ba akanta yake ba, Amra ce itama cikin hawaye shabe shabe da ya wanke mata fuska tace yaya mutafi gida muje mudubo ta ni nasan tana gida watakil tsokanar mu take ta tafi ita kadai kataso mutafi, duk surutun da takeyi itama ba sauraron ta yake ba, tashi yayi daga bakin mall din da yake zaune yaqara komawa ciki dan ji yake kamar zai ganta amma yanda ya shiga haka yaqara fitowa shikadai wajen suka qara dubawa har tafiya suka danyi aqasa me tsayi suna nemanta wai ko zasu ganta tabi wata hanayar amma shiru basu ganta ba, ba yanda suka iya haka suka koma mota suka shiga sannan yaja motar da kyar suka dauki hanyar gida zuciyar sa na ta bugu saboda baisan me zai faru ba idan akaji wannan batun agida, ahaka yaringa tuqin hankalin sa rabi akan tuqi rabi a tunani da haka har suka qaraso gida bayan an bude masa gate ya shiga yanufi parking lot yayi parking amma da yayi parking din sai yakasa fitowa daga cikin motar yana fargaba suma su Amra ganin baifito ba sai suma suka kasa fitowa sai sukaji wani tsoro ya qara dirar musu loqaci guda, juyowa yayi yakalle su ganin sunyi tsuru tsuru sun hade guri daya sunkasa motsawa sai suka bashi tausayi da saboda su kawai yadan yi qarfin hali ya bude qofar sannan ya bude musu sunma yace sufito kamar jira kwa suke haka suka fito da sauri suna fitowa basu tsaya bi takansa ba suka kwasa aguje suka nufi part dinsu, da sauri shima yabi bayansu yana kiran sunan su amma ina har sunyi nisa basu saurare saba, saurin yaqara shima yabi bayan su cikin sarssarfa gudu gudu sauri sauri saboda so yake shiyafara fada kafin su sufada saboda bazasu fada cikin sigar kwantar da hankali ba shiyasa bayaso suriga sa zuwa, aikin gama yagama domin kwa yana saka qafarsa a falon, "Amra nacewa momma ansace Ameesha, tsayawa yayi cak tare dacewa damm it yana furzar da iskar bakin sa me zafin gaske, momma da fitowar ta kenan daga kitchen taji maganar wani iri ban barakwai ta dake ta, tunanin ta ko bataji abun da Amran tace bane dan haka tayi saurin matsawa kusa da ita tana riqeta tace ke menaji kince kode kunena ne yaji min ba daidai ba, "momma bamuga Ameesha ba mun nemata munrasa, hamara tafada cikin sanyjn murya tana goge hawayen fuskarta, mutuwar tsaye momma tayi tamakasa kwakkwaran motsi da kyar bakinta na rawa tace bangane abun da kuke nufi ba kuyi min bayani yanda zan gane j na kuka baro yar mutane kuma har kuka iya dawowa cikin gidan nan batare da ita ba, ina take !!!? tayi maganar cikin daka musu tsawa datasasu hadewa waje guda suka riqe junan su tare da sakin kuka, "baza kumin bayani ba sai nayj maganin ku anan gurin, Ammar ne ya runtse idon sa tare da budesu har sun canza kala ahankali ya shiga takowa zuwa gurin su, cike da murya me rauni dan shima muryar tasa har rawa take yace momma kiyi hakuri ba laifin subane laifinane ni babba duk wani hukunci ni za ayankewa shi amatsayina na babba kuma ni na dauke su na fita dasu da banfita dasu. ba da duk hakan bata faru ba, kasaqe momma tayi tana jin maganganun sa juwa taji tana neman yarda ita da sauri tayi saurin dafa kujerar gefen ta sannan ta zauna dan idan bata zauna ba sai ta iya faduwa agun gumine ya shiga tsatstsafo mata duk sanyin Ac dake tashi afalon amma haka tafara gumi saboda tsabar shiga rudani dan maganar ba qaramin dakar mata zuciya tayi ba, tsugunnawa yayi agaban ta idon sa aqasa ya sunkuyar dakai sannan yashiga zayyano mata abun da yafaru tundaga A har Z, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kawai take maimaita wa a fili tayi yafi aqirga sannan tace kunkashe ni wallahi kun kashe ni yarinya daga zuwa amma kuce min wai kune meta kun rasa da wane idon kuke so inkalli yaran nan wallahi basason bani ita tayj weekend din dan na fahimcj dan ba yanda zanyi dasune shiyasa s h ka bani ita amma yanzu suzo daukar ta kawai sai ince musu ta bata taya kuke tunanin zasu dauki maganar to wallahi daga nan zuwa gobe duk yanda zakuyi ku nemota kuje ku nemota dan wallahi bame kwanar min agida kifita kuje kunemota saboda tsabar shiririta kunsan batasan wajeba meyasa bazaku sakata agaba ba kuna kallon ta shine kuka barta abaya to wallahi kwa duk indama tashifa sai kun lalubota adaren nan dan bazaku jamin bala'i ba ina zaman zaman zamana idan wallahj ku tafi kunemota tunkan yayan ku yasa qafa acikin gjdan nan idan yaji labari kashin ku ya bushe kunsan halinsa sarai basai nagaya muku ba baza kuji dadi ba gaba dayan ku, tsoro ne yaqara kamasu jin batun da momma tayi, sosai zuqatan su suka sake tsinkewa su yanzu ta ina zasu fara neman ta, haka momma ta fatattake su suka fita shiri, awaje suka tsaya suka kasa gaba suka kasa baya saidai suka dauki loƙaci me tsawo sannan da ƙyar Ammar yace musu suje wajen momy sujirasa yaje ya dawo da, a'a suka cemasa gwanda su tafi tare, yace a'a suyi haƙuri dare yayi subarshi shi zaije, bayan da suka iya haka suka rabu dashi yatafi sukuma suka nufi part ɗin momy san jiran sa acan tunda momma ta kore su, gurin motar ta koma ya bude ya shiga amma sai yakasa tayar da ita shiru yayi ya shiga tunanin haɗuwar su tundaga fito warsu da loƙacin da ya buɗe mata ƙofa ta shiga har yawon shaƙatawar da sukayi duk abun da yafaru tsakanin su aranar yau gaba ɗaya, sosai yayi dana sanin fitar nan tasu da yasan haka zata faru da bai ɗauke suba wallah da tuni yanzu suna cikin kwanciyar hankali batare da wata matsaba, shi yanzu ya zaiyi ya nemota gashi bayason haɗuwar sa da sameer baisan me zaifaruba dan ba ƙaramin aikin sa bane yasa hannun sa ajikin sa ba, yadaɗe agurin yakasa tayar da motar....... ________*SAM* Unguwar maraba dake cikin abunjan suka dosa basu wani sha wahalar gane gurin ba suka isa har bakin gidan da kaka kwatan ta musu awaje sukayi parking daga dan nesa da gidan sannan suka fito gada dayan su suka nufi bakin gate din gidane tafkeken gaske da tundaga wake zaka gane ankashe masa kusɗi, gate ɗin suka bubbuga amma ba abuɗe saida sukayi wajen sau uku sannan daga ciki akace wai waye ne, shiru sukayi basu bashi amsaba sai suka ƙara bubbuga gate ɗin, azafafe me gadin yabuɗe ƙofar yana cewa wai waye ne yake damun mutane ganin zaratan maza har uku yasashi yin ƙasa da murya, yana binsu da kallo daya bayan ɗaya, "waye kuke nema anan? " bossay yace me gidan idan yana ciki kayi mana magana dashi, saida yagama nazarin su tukunna yace baya nan, baya nan kuma yace mana muzo cewar Sameer, tunani yayi to kode da gaske suke amma de duk da haka baiyarda ba sai yace dasu to bari ina zuwa, yafaɗa yana komawa ciki ai baigama rufe ƙofar ba bossay yayi saurin danna kai ciki yana shiga ya shaƙe mutumin baisake saba saida yaga ya sumar dashi sannan ya turasa dakin sa yaƙullo sa, su Shettima ma da suka zama ƴan kallo suka bishi da ido kawai saida yagama sannan shettima yace me yasa kayi masa haka, dan murmushi yayi yana sosa ƙeya yace ai wannan ɗan iskane muna fiki ne idan bahaka mukayi masa ba bazai bari mushiga ba bakuka ga irin kallon da yaringa yi mana ba da mun rabu dashi yashiga bazai fito ba dan idan yaje zai sanar dashi kunga shikuma tunda yasan bai haɗa appointment da kowa ba bazai fito ba zai iya cewa ace bama nan amma yanzu da nayi masa haka sai muje mugama binciken mu kami lafiya batare da wata matsala ba indai yana ciki bamu da wata fargaba, yanzu de gaba ɗayan su saida suka jinjinawa ƙoƙarin sa da yayi dogon tunani a ɗan ƙanƙanen loƙaci da su basuyi ba sunji daɗi sosai da har saida sam yakasa ɓoyewa saida yace gaskiya kayi ƙoƙari gud thinking kace za muje dakai haka kake da zafin nama daman bansani ba, sosai bossay yayi dariya jin ana yabonsa yace ai nafi haka kaima daga maka ƙafa kawai nake ne saboda.... sai kuma yayi shiru yana dariya, shima sam ɗin yar ƙaramar dariya yayi sannan yace to shikenan zamu raba raini dakai daman rannan kace kafi ƙarfina ko to kabari duk san da komai ya daidaita zamu haɗa kwanji in koya maka hankali, haka suka cigaba da ɗan sa in sa akan batun ƙarfi kafin daga bisani shettima ya tunasar dasu abun da sukazo yi, nutsuwa sukayi suka tunkari cikin gidan saɗaf saɗaf sukayi suka tura ƙofar falon suka shiga ciki sallama sukayi afalon amma sai sukaji shiru ba amsaba ɗakunan dake ƙasa suka shiga duddubawa amma basu ga kowa ba upstairs suka nufa da suke da tabbacin yana can ahankali suka shiga takawa har suka gama haurawa dakuna biyu ne asaman bakin ƙofar na farko sukaje suka tsaya sai sukaji kamar ba kowa ɗayan suka koma suka kara kunnen su sai sukaji kamar murya ƙasa ƙasa sosai suka ƙara manna kunnen su jikin ƙofar saida suka tabbatar da mutum aciki, ɗagowa sukayi suka kalli juna shettima yayi musu alama da ido akan su afka kawai atake kwa suka tura ƙofar da ƙarfi Allah yasama ba muƙulli ajiki dan haka suna turata ta buɗu, "zunbur sukayi daga kan gadon da suke akwan ce mace da namiji ne namijin ma magidan ci dan kana ganin sa kasan ya manyan ta dan harma yafara tsufa ita kuma macen budurwa ce dan zauna kusan haifar ta hakanne zaisa kagane ba matar sunna bace wannan duk yanda akayi suna kan gadon manne da juna suna morar loƙacin su sunade jin daɗin yanayin da suke ciki kawai sukaji turo ƙofa ankatse musu jin daɗin da suke ciki suna farantawa junan su, namijin ne yafara tashi zaune san ganin wane isasshen da maine ya shigo masa gida kuma har cikin uwar ɗakin ya katse masa jin daɗin sa, zaro ido yayi ganin zaratan maza agabansa, tunani yafara akan suwaye waɗan nan, daman Allah ya taimake shi jikin sa da gajeran wando ajikin sa dan haka yayi saurin saukowa yana shirin dauko rigar sa da sauri su sam sukayi kansa suka rufe sa da duka ta ko ina macen ce tafara ihu da kuka tabi ta tuƙuiƙuiye da zanen gadon tana faman sharɓar kuka tana basu haƙuri su rabu dashi amma basuma san tanayi ba, saida suka tabbatar da yadaku sannan sukayi masa cali cali suka fita dashi ahaka suka fita dashi da gajeran wandon, bayan sunkai shi mota acikin suka sakasa abaya suka ƙullo sanann suka dawo gidan suka hau bincike suka tarkato duk wasu takaddu da suka gani da kuma wayoyin sa harda laptop ɗinsa komai de ba abun da suka bari me amfani saida suka ɗauko sannan suka fito matar kwa harwaje tabiyo su tana yi musu magiya akan su rabu dashi bai turamata kuɗin da yayi mata alƙawari ba subari idan ya tura mata sai su tafi dashi wani kallon banza da sameer yayi mata ne yasa tayi shiru da maganar ta, agurin suka barta suka ja motar su sukayi gaba sai kano ranau fari tass ganin sunyi nasara batare da sun sha wata wahala ba wajen ɗauko sa, Suna tafiya suna hirar su cikin kwanciyar hankali da farin ciki ahaka har suka ƙaraso kano loƙacin da suka shiga garin kano biyar ta wuce direct inda suka kai mahaifin sumy nan suka kaishi shima saidai basu kaishi ɗakin da yake suka kaishi wani ɗakin daban batare da sunce masa komai ba suka ƙullo sa aciki suka fito, saida sukaje sukayi sallar magriba sannan suka dawo gidan baban sumy sukaje suka fito dashi suka kaishi ɗakin da suka kai ɗayan da har yanzu baigama dawowa hayyacin sa ba, "tambayar mahaifin sumy sukayi wanann shine mutumin nan ya tabbatar musu da cewa eh shine yana ɗan ɓoye fuskar sa saboda baya so yagane sa, saboda yasan da wuya ya gane sa a irin halin da yagansa yasan ba lalle yagane shi ba, mayar da shi sukayi ɗakin sa sukace dashi yabari gobe zasu sallame sa yayi haƙuri zuwa gobe bayanda ya iya dole ya koma ɗakin yaci gaba da zama sukuma suka ƙara ficewa daga gidan saboda duk agajiye suke bazasu iya zama wani tattaunawa dasu ba yanzu dole sai sunke gida sun huta zuwa gobe sai su dawo, mota suka koma suka shiga yanzu bossay ne yajasu zuwa gida suna kan hanya wayar sam tayi ƙara da bazai ɗaga ba sai kuma ya duba yaga momma ce ke kiran sa da sauri yaɗaga tare da kara wayar akunne daga kwancen da yake yayi saurin tashi zaune yace momma meke faruwa kisanar dani bansan me tace masa ba daga cen ɓangaren, yace to shikenan gamunan munkusa ƙarasowa ma muna hanya ajiye wayar yayi shettima dake gaban mota ya juyo yace ya akayi ne lafiyade ko, Sam yace wallahi bansan meke faruwa ba momma ce ta kirani tace wai gida ba lafiya komai nake nabari muje yanzu nan, tofa Allah yasade lafiya cewar bossay, sam yace anya kuwa lafiyar nan da sauƙi ka ƙara gudu de kawai muyi sauri muje tunda naji momma ta nemeni ni nasan ba ƙaramin abu bane zaisa momma kirana, Allah de ya taƙaita ta kawai koma meye yazo da sauƙi..... "Ameen suka amsa masa dashi dagana kuma suka cigaba da tafiya batare da sun ƙara cewa komai ba........ motar su na shawo kwana shikuma Ammar tasa na fita daga layin dan haka basu haɗu ba, shiga sukayi suka nufi parking space suna gama daidaita parking sam yafara fitowa da sauri ya nufi part din momma suma su bossay da sauri suka fito suka rufa masa baya da sarsarfar su suka qarasa cikin falon ko sallam basuyiba suka afka ciki momma suka gani a tsaye sai faman zarya take a falon takasa zama tana ganin gabanta ya tsanan ta bugawa ganin bossay datayi dan ita duk atunanin ta shine yayan Ameesha shiyasa tafi jin kunyarsa, momma lafiya meyake faruwa kince muyi sauri muzo gida ba lafiya kuma nibanga komai ba na tashin hankali meyake faruwa? ajiyar zuciya ta sauke me nauyi da kyar ta iya cewa eh ai ganine ba ga masarauta ba amma inbada muwa mushiga daga ciki sai insanar dakai afuwan dan Allah tafada tana kallon su bossay saboda taja sam zuwa sama hannunta riqe da nasa tajasa har zuwa dakin ta saida suka shiga sannan ta sake sa shide binta kawai yake da kallo yana jiran jin abun da zatace masa dan shima hankalin sa yadan tashi ganin furgici a idon mahaifiyar tasa, "Momma nifa duk kinbi kin saka ni araduni dan Allah kigaya min abun dake faruwa mana kin kawo ni nan kuma kintsaya bakice komai ba, "Sameer takira sunansa gabansa yaji ya fadi tunda yaji ta kirasa da ainahin sunan sa to hakanne yakara tabbatar masa da lalle ba lafiya ba dan ba qaramin abune kesa momma fadar sunan saba kai tsaye. batare da ta sakaya ba, "momma ina sauraron ki me yake faruwa kisanar dani mana koma menene , sameer akwai damuwa sosai kuma akwai matsala narasa ma tayanda zan sanar dakai, "kifada kawai momma i na sauraronki niduk kinbi kinsani arudani, cikin sanyin murya tanaso tayi maganar amma tana qara jin nauyin fada masa, shiru yayi tare da kafe ta da ido yana mamakin yanayin mahaifiyar tasa da dan tunda suka taso da ita inajin bai taba ganin taji nauyin fada masa wata magana ba sai yau hakan yasa yadan ji faduwar gaba da tsoron jin abun da zatace masa, matsawa yayi kusa da ita tare da kamo hannuwan ta duka biyun yajata zuwa bakin gado ya zaunar da ita sannan ya fuskance ta da kyau yace momma plss calm down momma ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki sanar dani abun dake faruwa duk kinbi kin tada hankalinki nima kuma kina so kitayar min da nawa hankalin dan Allah kisanar dani damuwarki, Memakon tabasa amsa saikawai tayi zunbur ta mike tana girgiza kai tace "sameer ina ni i na nutsuwa ai banga ta zamaba zama bai kamace niba ahalin yanzu bani da ikon zama hankalin bazai taba kwanciya ba, ya ilahi sam ya fada afili tare da dafe kansa da yaji yana sara masa cike da gajiyawa yace momma nifa nagaji tundazu sai abu daya kike fada kinqi sanar dani yakike so inyine yana kaiwa nan ya mike tsaye ganin haryanzu batayi magana ba yasa shi nufar hanyar waje dan zuciyar sa tagama kaiwa karshe yaga inba haka yayi mata ba bazata fada zata cigaba da bata masa lokaci ne kawai, ganin zaifita yasata da sauri cikin rawar murya tace sameer daman akan batun yarinyar da kukawoq jiya ne........sai kuma tayi shiru takasa qarasawa, cak ya tsaya tate da juyowa asukwane yadawo da baya yazo gabanta, WHAT...!!!? yafada da qarfi yana kara matsowa kusa da ita, "momma what u say yarinyar da muka kawo jiya kike magana akai me yasame ta me yafaru da ita wayataba ta? tsorone yaqara kama momma ganin yanda duk ya rude lokaci daya sai faman tambayoyi yake jero mata, shiru tayi bata basa amsaba, "momma kigaya min abun da yafaru da yar mutane, "daman dazu da safe tunda suka tashi bayan sunkarya suka fita cikin gida suka gaiggaida mutane suka dawo sai ita ta kwanta bacci sukuma suka qara fita, Sainaje dakin ingano lafiyar ta sai kawai na tarar da ita azaune tayi tagumi nake tambayarta abun dake damun ta take sanar dani cewa ai ta tashine bataga su Amra ba shiyasa tayi ta gumi nace tayi hakuri tazo nakaita gurin su shine muna fitowa ma sai mukayi karo dasu sun shigo da gudu sukace wai yaya Ammar yace taje yana son ganin ta da farko ma kin amince musu nayi sai da suka hadani da Allah da annabi sannan nace to suje basu dade ba da fita ba suka qara dawowa sukace yace wai sushirya zai kaisu shopping da murnar su suka shiga suka fara shiryawa..... dan dakatawa tayi da maganar tana kallon sa ganin yanda ya zuba mata idanu yana kallon ta ko kiftawa bayayi, hada ido sukayi dashi hakan yasa tayi shiru takasa cigaba tare da yin qasa da kanta, hannu yasa yadago da ita suna facin din juna sannan yace momma me kikeson kice min kiyi maganar ki kai tsaye kigaya min abun da yafaru da ita kawai kibar duk wani bayani a yishi daga baya ina jinki accident sukayi ko kuma wani mugun abunne yasameta, janye jikin ta tayi daga riqon da yayi mata sanan tace gaba daga inda ta tsaya batare da tabi tayanda yakeso din ba, "tace dole inyi maka bayani ko kanaso ko bakaso, shiru yayi tare da nade hannayen sa a kirjin sa yaci gaba da sauraron ta, bayan sungama shirya suka fita to tunda suka fita basu dawo ba sai bayan sallar magariba dan har ina tunanin kiransu sai gasu sun shigo da gudu suna kuka natare su nace me yake faruwa suke sanar dani wai bayan sunshiga sungama yo shopping suka fito tare amma da suka shiga mota sai suka nemeta suka rasa sama ko qasa sun nemeta sun rasa....... sun nemeta sun rasa sun nemeta sun rasa yafada yana jinjina kai momma me kikeso kice atakaice de kina nufin kice basu ganta ba tabata kenan ko me kike nufi, "Eh" wallahi haka nima naji abun kamar amafarki wai basu ganta ba, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, inna lillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake nanatawa a fili yace momma momma momma saida yakirata sau uku yakasa kuma cemata komai, idon sa har yafara canza kala, da sauri tayi kansa tare da riqo hannun sa tace yanzu meye mafita nagaya maka dan kasamo mana mafita gashi kuma naga kai kana ma neman kafini shiga damuwar ni wallahi ma iyayen yarinyar nan nake ji ga wancen yayan nata ma dake waje bansan da wane ido zan kalle sa ba yaran nan sunso su tafi da ita jiya na hanasu suka hakura saboda bayanda zasuyi amma gashi kuma abun da yafaru yanzu meye abunyi, daurewa kawai yayi tare da cewa ina su Ammar din suke, "na korasu nace suje su lalobota kar wanda yasake shigowa inda nake inba tare da itaba gabadayan su na kora daga shi har su Amran wannan ai shirmene da shiririta ace kuna tare da mutum har yayi wani wajen baku kulaba koma dauke ta akai ai kamata yayi ace sunga wanda yazo daukan nata amma dake daga su har shidin bamai cikakken hankali sunje sundawo batare da ita ba kuma suka iya dawowa cikin gidan nan suka gaya min saboda tsabar sakarci, "bawani zancen su koma nemota gwara ma kiyi musu waya sudawo kawai fitar suma baida amfani gwara sudawo kawai dan ba ganin ta zasuyi ba, ina ganin ba laifin subane anshirya dauketa ne tun farkon fitar su shiyasa har akayi nasarar dauke ta batare da sanin suba, idan Ammar din yadawo kice yazo ya sameni a part dina, yana kawaiwa nan baijira cewar taba kawai yayi saurin barin wajen ya nufi hanyar fita yana jinta tana tsayar dashi amma baisaurare ta ba ya bude kofa ya fita tare da jan kofar abakin kofar ya tsaya tare da dafe kansa shikadai yansan abun da yakeji aransa duk wani tunanin sa nema yake ya tsaya yana tunanin sunkusa toshe wata hanyar gashi ankuma jawo musu wani aikin yanzu ta ina zata fara neman tama kuma yana da tabbacin wannan abun yana daya daga cikin shirin wadannan mutane su suka sace ta ko tantama babu, wani tunanin ne yaqara fado masa to idan sune meyasa basu sace ta tun lokacin da take hannun dadda ba lokacin ma da bawani tsaro da ake bata gashi taba zuwa makaran tama ita kadai duk tsawon lokacin da ta dauka awajen ta ba taba kokarin dauke taba amma sai gashi daga zuwan ta gidan su kwanan ta daya ansace ta shida yake tunanin ma ta dawo nan da zama gashi ba aje ko inama ba ansamu matsala abun da baitaba tunani ba, yanzu tunanin da fargabar sa shine idan dadda taji labarin batan ta yasan bazata taba yarda dasuba bama ita kadai ba gaba dayansu har su bossay kunyar gaya musu yake ace wata matsalar daga gare sane tasanadin sa hakan yafaru shikam yau ina zaisa kansa taya zai sanar dasu wannan labarin marar dadin ji, ya dauki lokaci me tsawo agun kafin ya daga kafafun su da kyar yajasu yatafi wajen su ransa fall tunani kala kala, yana shiga falon duk sukayo kansa suna tambayar sa lafiya me yake faruwa amma bai iya basu amsaba, abun da yafi basu mamaki ganin idonsa ya canza kala gashi kallo daya zakai masa ka fahimce halin da yake ciki basugana cika da mamaki ba saida suka ga yasa hannu yakamo duka hannayen su ya shiga jansu kamar wasu sukaye haka suka shiga binsa abaya batare da kowa yaqara magana ba suka nufi hanyar waje ahaka suka cigaba da tafiya har sukaje part din fulani ba wanda yayi magana, duk sun zuba ido suga iya gudun ruwan sa, saida sukaje bakin qofar sannan yasake su tare da tura kofar suka shiga ciki su shettima mane suka samu damar yin sallama amma banda sam da ahalin da yake ciki bazai iyayin magana ba bakin sa yayi masa nauyi, fulani ce zaune kan kujera tana waya shigowar su yasa tayi saurin katse wayar tare da amsa musu sallamar su ba yabo ba fallasa suka gaisa amma banda sam da suna shigowa ya wuce part dinsa, fulani tace lalle yaran nan kuna sha'anin ku yanzu kaima saikaga dama kake zuwa inda nake yanzuma nasan badan munhadu ba wucewa zakayi baza kanemeni ba daman ance zama da madaukin kanwa shike kawo farin kai yanzu kaima kafara daukar dabi'ar wancen marar mutun cin da baya ganin mutane da gashi kaima haka kake so ka koma kaima ko to sai kuje kuyi tayi kar kufasa, dan shafa kai shettima yayi sannan yana dan murmushin dole sannan yace tuba muke mama wallahi ba abun dakike tunanani bane abubuwane yanzu sukai min yawa nan dinma yanzu ba kullum nake shigowa ba wataran kuma idan nashigo bana samun ki anan shiyasa amma de kiyi hakuri za'a gyara, kai kasani bawani ba ka shigowa jinake ko jiya dare anan yayi muku amma baka nemeni ba idan baka gani anan ba bakasan inda dakina yake ba ko kodan baikamata ma inga laifin kaba wanda kaci kashin sama kaci futsarin sa baigirmamakaba baka da daraja awajen sa bare kuma wanda bakai mishi komai ba shi kallon arziki ma wataran baka isa kasamu daga gurin sa bare har yadaga kai yazo inda kake ya gaida kai, nidai shawara wallahi ku gyara halinku dan wannan ba hali na gari bane, to mama fulani zamu gyara in sha Allaha kiyi hakuri yanzude komai ya wuce tuba muke kanmu bisa wuya, "zadai ka canza amma wancen murdadden bazai taba canzawa ba, kidai yimasa addu'a zaidaina in Allah ya yarda, tabe baki tayi tace oho de kuka sani, dahaka de sukayi sallama da ita suka bi bayan sam daman Allah Allah suke tayi ta sallamesu tabi ta tsaresu da surutu, suna karasawa suka shiga da sallama abakin su, can kan kujera suka hango sa ya hada kai da gwiwa ya kifa kansa akan gwiwowin sa da sauri suka karasa inda yake shettima ne yafar zuwa yace, "Subhanallahh" "sam lafiya meyake damunka haka me yake faruwa? dagowa yayi yana kallon su daya bayan daya da jajayen idanun sa da suka canza kala, kawai kallon su yake yakasa ce musu komai. kallo daya zakai masa ka fahimci tsatsar bacin rai da damuwa da yake ciki, sosai suka shiga damuwa ganin damuwar da yake ciki, cike da damuwa shettima ma yace haba sam kasanar damu abun dake faruwa duk kasakamu acikin damuwa, bossay ne shima da yagama karan tar yanayin sa yaji gaba daya jikin sa yayi wani irin sanyi ya mutu dan haka kawai jikin sa yaba sa damuwar sam ta dagan ta da Ameesha tunda mahaifiyar sa taja sa daki dan sanar dashi abun dake faruwa tundagana kawai yaji something is wrong game da Ameesha zuciyar sa tabasa Ameesha ba lafiya take ba, shettima ne yaci gaba da cewa sam bansaka da shiga damuwa ba irin haka ba kaida nasanka da jarumta nasanka haba saikace bakai ba ka kwantar da hankalinka ka sanar da mu matsalar da take damun ka matsalar ka matsalar muce ka gaya mana ko zamu iya magan ce maka ita, danshi baitaba kawo wani zancen Ameesha ba duk atunanin sa ko wata matsalar ce da ta shafeshi ko kuma ta family ce... cikin sanyin murya bossay yace "Ameesha ko wani abunne yasame ta??                       💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [6/25, 10:58 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️67&68 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                      cikin sanyin murya bossay yace "Ameesha ko wani abunne yasame ta?? da sauri sam ya ɗago yakallesa sai kawai yaji yabashi tausayi daman yasan sai yafisu shiga damuwa saboda sunfi sabawa da ita dan ya ɗan fahimci ma kamar da so atsakanin su a iya zaman da sukayi yafahimci hakan dan yasan da shaƙuwa atsakanin su ita dashi yanzu ta ina zaifara gaya masa aya zai ɗauki maganar shide yau yaga takansa yau ina zaisaka ransa inajin tunda yake bai taɓa shiga damuwa irin wannan tayau, tundaga irin kallon da yaga sam yana masa hakan ya tabbatar masa da tunanin sa gaskiya ne tabbas zarginsa ya tababbata ko da baigaya masa yaga amsar sa a cikin ƙwayar idon sa, dan haka baiƙara ce masa komai ba kawai ya miƙe daga kusa dashi tare da komawa kujerar gefen su ya zauna kawai shima yazubawa Sameer ido zuciyar sa na wani irin harbawa, yanajin tsoron abun da zaiji daga sameer tunda haryagansa cikin damuwa irin haka to yasan ba ƙaramin abu bane yasaka shi hakan ba, shettima ne da yaji tambayar bossay wata iri kamar daga sama shima sai yanzu zuciyar sa da ɗarsu da farko baiyi tunanin wani abun ba amma da yaga sameer yayi saurin kallon bossay hakan ne yasa shima yafara tunanin ko hakanne, gyara zaman sa yayi ya kalli sam da kyau sannan yadafe kafaɗar sa tare da kiran ainahain sunan sa yace sameer kasanar damu abun dake faruwa shirun baida amfani sanar damu ɗin shine mafita asan yanda za a shawo matsalar, wani irin numfashi me zafi sam ya fitar daga bakinsa tare da iska sannan ya nufasa batare da ya kalli bossay ba dan yanzu yafi jin nauyin haɗa ido dashi akan shettima dan haka sai yakalli shettima cikin sanyin murya yace shettima bansan taya zaku fahimci maganar nan ba sunƙara ɓata mana aiki shirin mu yadawo baya kaina ya ƙulle mutanen nan basu da imani abunsu kullum gaba yake muna murnar munyi nasara ashe abun bahaka yakeba wani abun suka ƙara shirya mana mutanen nan suna sane damu duk inda mukaje idon su yafara yawo akan mu, duk yanda akayi shiga da fitar mu akan idon su mukeyi bamu sani ba yazamuyi dasune dannidai wallahi abun yafara bani tsoro anya baza musa hukuma aciki ba? duk shiru sukayi suna sauraron sa da sun kasa fahimtar inda maganar sa ta dosa, shettima yace sam wai me kake shirin cewa ne nifa bangane bayanin ka ba me kake so kace, "Sun ɗauke yarinyar nan da mukawota gidan nan sun sace ta ɗazu" "ME...!?" bossay dake ɗayar kujerar yataso da sauri yazo gaban sameer yace "kamar ya sun saceta kana nufin kace duk girman gidan nan suka iya shigowa har ciki suka ɗauki baby ko kwa ya akai tayama hakan zaiyiyu me yasa duk rashin tsaron gidan da take zaune basu shiga sun sace taba sai nan gidan da yafi nasu tsaro shine zasu iya shigowa su sace ta wannan wacce irin maganace? [6/25, 5:05 PM] #momyn twins#: shettima ne ya miƙe tsaye shima yana kallon bossay yace "kamar ya wannan wacce irin magana ce kama nufin kenan baka yarda ba ko kuma da sanan su hakan tafaru ko su suka ɗauketa wanne kake nufi daga ciki? "nima bansani ba kawaide maganar naji wata iri wai ansace tayaya hakan ta faru gaskiya wannan maganar da sake dole a fito da wanda ya ɗauke ta adaren nan tunda de tana cikin gidan nan ba fita akayi da ita ba idan kuma fitama akayi da ita to dole za asamu wanda yaga anfita da ita nan gidan ba kamar ko wane gida bane tunda kuma da tsaro bazaiyiyu ace anshigo daga wajeba anɗauke ta anfita da ita batare da sanin wani ba, "shettima yace yakamata karinga gyara kalaman ka katsaya kaji ta yanda akayi aka ɗauke ta ɗin baikamata kazo kana faɗar abun daka ga dama ba kasan a inda kake da kuma wanda kake magana dashi kai ko halin da kaga ya shiga ma ai baikamata ka faɗi wata maganar da bata dace da shiba idan kai lura da yanayin sa ai kasan baƙaramin tashin hankali yashiga ba amma memakon mubi komai ahankali muji yanda za amagance matsalar amma sai kazo kana surutun banza haba Aliyu wannan abun dakake kwatakwata bai dace ba, "bossay yace nifa ba wata magana nafaɗa ba kuma banyi dan ina zargin wani abun ba kawaide abunne yaban mamaki amma tunda haka kuka ɗauki maganata kuyi haƙuri bazan sake saka muku baki aciki ba kuyi duk yanda kuke so tunda duk abun da zan faɗa laifi zai zama awajenku, yana kaiwa nan ya nufi hanyar waje batare da yaƙara waiwaiyen suba ya fice daga ɗakin zuciyar sa nayi masa wani iri, haka suma basu dakatar dashi ba har ya fice...... shettima ne yaƙara dafa sameer yace "dan Allah ka kwantar da hankali ka abi komai asannu ni ina ganin wannan ba abun tada hankali bane ai cikin nan yana da tsaro kaga nemanta bazai bamu wajaba koda ace ma sace tan akayi zamu samu wanda yaga anfita da ita tunda ko daddare mutane basa kasa yawo anan bare kuma ace da rana kaga idon kowa yana kai zamuyi saurin samun labarin ta ni banga abun shiga damuwa ba har haka, ɗan numfasawa sameer yayi tare da kallon shettima da kyau sannan yace nima da hakanne ai bazan damu ba dole insa afito da ita duk inda ta shiga to amma matsalar ba anan gidan aka ɗauketa ba Ammar ne ya fita dasu ita dasu Hamra to awajen shopping ɗin aka ɗauke ta to abun kuma da yafi bani mamaki wai tare suka fito da ita daga ciki amma suna ƙarasowa wajen motar suka neme ta suka rasa tunda kaji haka kwa kai kasan da shiri akayi hakan zai iyayiyuwa ma tun fitar tasu ake bibiyar su ba asamu damar ɗauke ta ba sai loƙacin da suka fito aka faki idon su aka ɗauketa ta hanyar da bazasu ji ba, "wai daman ba acikin nan aka ɗauke taba?? shettima yayi maganar shima cike da shiga ruɗani danshi duk atunanin sa anan aka rasata shiyasa baidamu ba sosai, "nima shine abun da yasani shiga tunani shine dalilin da yasa nama kasa sanar daku, "to yanzu meye mafita"? "Ina tunanin fa saidai gobe mukoma can inda sukaje ɗin nasan baza arasa CCTV camera ba awajen inyaso sai aduba mana muga tayanda aka ɗauketa ɗin nasan ta nanne kawai zamu ɗan gane wani abun amma inba hakaba tofa saidai mu roƙe Allah ya kare ta ya bayyana ta ni tsoro nama karsuje su cutar da ita, "insha Allah ma babu abun da zai sameta tunda basuci masara akanta ba tun loƙacin baya yanzuma bazasu taɓa ciba da yardar Allah, "to Allah ya yarda" cewar Sameer" "Ameen " nande kowa yayi jigum jigum suna tunani kala kala a ran su.... Bossay yana fita ya nufi wajen motar da suka dawo da ita yanzu sai kawai ya tsaya abakin motar tunawa da yayi ashe ba muƙullin motar a hannun sa sai kawai ya kifa kansa ajikin motar ya shiga tunani wai Ameesha ta taɓata ansace ta abun yakeji kamar almara juya jiya suka kawo yarinyar amma ace wai yau ansaceta gaskiya wannan maganar da alamar tambaya shide har yanzu yakasa yarda mutanen nanne suka ɗauketa da tuncan baya basu ɗauke taba sai yanzu ace sun shigo har cikin masarauta sun sace ta gaskiya bazai taɓa yarda da hakan ba saidai kawai idan da wani abun da yasa ɓatan nata acikin nan wataƙil ma tana wani wajen acikin Masarautar da yasa ta kasa fitowa tunda masarautar da girma sukuma basu bincika ba kawai suka yanke shawarar ta ɓata anzo ansace ta, ,"sosai ya shiga tunanin yanda zai ɓullowa al'amarin yama rasa wane kalar tunani, yakai wajen awa ɗaya agun yana tsaye yarasa mafita kuma baikoma ba kuma bai kuma tafi ba, tuna rayuwar su ya shiga yi tun loƙacin haɗuwar su wata yayi murmushi idan kuma ya tuna wani abun sai yaji ransa ba daɗi wani irin ɗumi yaji akan fuskar sa hannu yasa ya shafi gurin da yaji danshi saboda tsabar shiga da damuwa da yanda yakejin zuciyar sane yasa hawaye sauko masa daga ido batare da ya shirya yinsu ba sosai yakejin sonta naƙara shigar sa ahankali ya furta I love u baby Ameesha Allah yakare min ke aduk inda kike Allah ya bayyanaki sosai ya shiga jero mata addu'a tare da goge sauran hawayen da yaji sun ƙarasa sauko masa yanke shawara yayi kawai yaje ya tari napep yatafi gida dan bayajin zai iya komawa wajen su yayi musu magana..... ɗagowa yayi yana niyar barin wajen kawai sai idon sa ya sauka akan wata inuwa da tayi saurin giftawa wani lungu da sauri ya juya gurin amma sai yaga ba kowa da har ya basar amma sai wata zuciyar take ingizashi akan yaje yaga komenen ya wuce yana gama ayyana hakan ya nufi wajen saidai yana zuwa yaga wayam ba kowa ƙarewa ma hanyace miƙaƙƙiya awajen hanyar yaci gaba da bi dake gurin da haske dan haka yana ganin komai kawai yaci gaba da bin wajen saida de yaga kamar ma idan yabi ƙarshen sa dajine ba wani kwana ko kuma ɗaki awajen dan baka kawai sai ya juyo yadawo yana cikin tafiya kamar amce masa ya kalli ƙasan sa idon sa na sauka ya sauka akan wani abun hannu da sauri ya tsugunna yana tunanin a inda yasanshi saurin miƙewa yayi daga gurin tunawa da inda yasanshi a fili ya furta tabbas natane wallahi na gansa a hannunta ji da muna mota loƙacin da ya riƙo hannun ta yaganshi.... damƙe abun hannun yayi yanajin kewarta tabbas wannan abun hannun tane to me ya kawo shi nan to sunzo wajen tayardashi wata zuciyar kuma tace masa to kode nan tashigo ta ɓata agun takasa komawa gida saka abun hannun yayi a aljihu yashiga dudduba gurin har inda yabaro ya koma amma baiganta ba da sauri yabaro wajen ya nufi inda part ɗin da yabaro wajen su sam, da sauri yake tafiya dan har yana harɗewa wajen tafiya da haka ya ƙarasa part ɗin kamar daga sama suka gansa ya turo ƙufar da ƙarfi dukan su suka zuba masa idanu suna tunanin kuma me yadawo dashi dan atunanin su ya daɗe da tafiya ma, ƙarasawa yayi inda suke tare da zaro abun hannun ta yana nuna musu batare da yace komai ba da sauri shettima ya miƙe yace a ina kasamoshi ko ka ganta ne naga abun hannun ta agunka, yaƙarasa maganar tare da karɓar abun hannu yana kalla yace ai jiya jiyanannan nasiya mata loƙacin da muka fito tanuna tanaso nasiya mata a ina ka ganshi? "awani guri na tsince shi acikin nan basu labarin abun da yafaru har yaje gurin daga nan kuma yagansa ya kawo musu, da sauri Sameer ya miƙe tsaye shima ya karɓi abun hannun yana mamakin jin inda aka gansa to me yakai abun hannun ta gurin gurin da ba kowa bane yake zuwa dan yana da tabbacin babu abun da zaisa su Hamra zuwa gurin barai ace garin zuwa ta jefar dashi bata sani ba.... to yake shirin faruwa abun hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [6/26, 9:53 PM] #momyn twins#: ,  ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️69&70 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                  to me yake shirin faruwa abun  hannun ta acikin masarauta bayan kuma ba anan aka sace taba,....  shettima ne ya karɓi abun hannun daga hannun sameer yana ƙara nazarin abun acikin ransa shima abun da sam yayi tunani shima ai yayi tunani maida duban sa yayi ga sam sannan yace sameer ina twins suke yakamata muji ta bakin su ko iya zuwan ta sunje wajen idan kwa bataje wajen ba tofa akwai matsala yakamata musan wani abun game da ganin wannan abun hannun ace inda aka ɗauketa daban kuma a tsinci abun hannun ta acikin nan to taya hakan tafaru anya ka tabbatar ma kuwa acan waje aka ɗauke ta kode Sundawo tare ne daga nan kuma tayi wani wajen, "ba anan ta ɓata ba momma ta tabbatar min da hakan tace sukaɗai suka shigo suna kuka tundaga can suka rasata amma fa abun ya ɗaure min kai to me yakawo abun hannun ta shi tsoran sama kar ayi zargin familyn ɗinsa daman ɗazu bossay yagama faɗar abun da yaga dama yanuna shi baiyarda ba gashi kuma yaje ya nemo abun hannun ta hakan kuwa zaisa yaƙara zargin wani abu yaƙi yarda da cewa ba anan gidan aka ɗauke ta ba, "bossay ne yace wai kuna nufin ba acikin gidan nan ta ɓatan ba a ina ta ɓata ko ince a ina aka sace ta??    shettima ne ya kalle sa da sannan yayi masa bayanin yanda ɓatan nata yakasan ce kamar yanda sam yabashi dafe kansa yayi yana ambaton sunan Allah dan shi yanzu bama shi da bakin magana bayaso ya ƙara sakasu cikin damuwa amma bakin sa taf yake da maganganu amma faɗarsu zai iya sawa su samu matsala dan haka kawai yaja bakin sa yayi shiru tare da koma ya zauna yana kallon su yana jiran jin hukuncin da zasu yanke game da wannan lamarin me ɗaure kai,    "yanzu meye mafita? sameer yafaɗa yana kallon su gaba ɗaya,   "shettima yace mafita ai guda ɗayace kamar yanda na faɗa maka ɗazu dole bari zamuyi zuwa gobe sai mu koma inda sukaje ɗin aduba mana ina ganin hakan shikaɗaine best solution amma ku ya kuke ganin taku shawarar, "sam yace hakan yakamata muyi amma suma mufara tambayar su tunda suka fita ba wanda suka lura da yana binsu abaya ko kuma sunga wani kusa dasu da yanuna alamun rashin gaskiya danni fa tunanina yafi bani tun fitar su ake bibiyar bayan su har suka cika ƙudirin su akanta, "shettima yace nima nayi wannan tunani wannan abun dole yana buƙatar mu gaggauta bincike akai yaƙarasa maganar yana mayar da sunansa kan bossay sannan yace "Aliyu baka ce komai ba kasamu waje ka zauna"'    "to mezan ce ai kune manya sai abun da kukace duk shawarar dakuka yanke daidai ne,   kawai kallon sa shettima yake batare da ya yarda da maganar da yayi masa ba yasan dole akwai magana abokin sa saidai kawai bazai faɗaba,   "Shima guri yasamu ya zauna tare da cewa sameer shima yazauna gaba ɗayan su azaune suke sam da shettima suka cigaba da tattaunawa akan lamarin amma banda bossay tunda suka fara bai tanka musu ba,   daga ƙarshe de suka yanke shawarar sukwana atare inyaso gobe asubar fari su nufi gurin da mall ɗin, suna zaune suna ƙara tattaunawa sukaji sallamar Ammar ya shigo ciki amsawa sukayi ciki yaƙaro so kusa dasu ya zauna tare sa lanƙwashe ƙafafun sa ya durƙusa agaban sameer zuciyar sa na dukan uku uku tunda momma tace yaje yana neman sa hankalin sa yaƙara tashi dan ba laifi yana tsoron sa har cikin ransa koda ba abun da yayi masa bare kuma ace gashi yau ya aikata babban laifi yasan da ƙyar in jikin sa bazaiyi tsami ba.....   "yaya gani yafaɗa cikin sanyin murya da fargaba, sameer dake kishin hiɗe ajikin kujerar duniya tayi masa zafi ya ɗago ya kalle sa kallo ɗaya ya fahimci halin da yake ciki dan haka kawai sai yace masa daman ba wani abu bane kaje kawai amma gobe da safe kashirya zamuje inda kukaje ɗin kade tabbatar agun aka sace ta kuma kana da tabbacin kun fito tare da ita daga gurin?    Ammar baisan loƙacin da ya sauke wata sanyayyiyar ajiyar zuciya da har saida sam yajishi sannan ya gyara zama yace" eh wallahi tare muka fito da ita,     Sameer zaiyi magana kenan bossay yarigashi da cewa zaka iya tunawa tunda kuka tafi baku lura da kowa na binku ba abaya ko kuma loƙacin da kukaje wani wajen babu wanda ka lura dashi da yanuna rashin gaskiya akusa daku ko kuma a shopping mall ɗin da kukaje kayi tunani da kyau babu,   "shiru Ammar yayi alamar yana tunani duk zuba masa ido sukayi sunajiran suji me zaice,    can de yace gaskiya babu amma bari inkira twins ko su sun lura da wani abun amma nidai gaskiya ba luraba saboda hankalina yana kanta itakadai nake kallo (inji nifa ba inji shiba)    No rabu dasu kawai nasan yanzu sun kwanta,    yaya bamu kwanta ba tsulum sukaji muryar Amra tafaɗa tana danno kai ciki gaba ɗayan su suka juya suna kallon ta ƙarasowa ciki tayi Hamra abayan nabinta ashe tare suka taho da Ammar ɗin sai yace su jirasa awaje, akusa da Ammar suka zauna suma suna fuskantar yayan nasu,   Bossay ne ya tashi daga inda yake yadawo kusa da su shima a ƙasa ya zauna inda suke sannan ya kalli ɗaya daga cikin su yaƙara maimaita musu tambayar da yayiwa Ammar, Suma tunanin sukashigayi da sauri Amra tace wallahi loƙacin da muka zazu restaurant naga wata mota ta tsaya abayan mu amma de banga wanda ya fito daga ciki ba muka shiga da muka fito ma kuma muna tafiya a hanya wallahi naga motar abayan mu amma daga nan ban ƙara bi takan taba bansan de ina tayi ba ko taci gaba da binmu ko wani gurin tayi wallahi bansani ba, mtsww sam yaja tsaki yace ke matsalata dake kinfiya shirir ta to meye nagaya mana wannan abun baki tantance ba, bossay yace a'a ba wani shiririta tunda har taga motar itama alamar tambaya ce bai kamata ace tayi shirya ba tunda tace loƙacin da suka tsaya sannan kuma me motar baibar gurin ba har saida suka fito kaga kwa shima dole da alamar tambaya akan sa zai iya yiyuwa yaci gaba da bin nasu ita kuma hankalin ta ba abun yake ba ba yanda bazai iya kasan cewa ba, ke yanzu idan kika ga motar zaki iya gane ta da sauri tace baƙa ce amma idan naganta zan ganeta saboda tana da ɗan tudu,   good bossay yace sannan ya kuma cewa gobe kema zamu tafi dake saboda idan anduba CCTV camera za agani indai har ya biyo ku za aga motar sa inma aƙafa ne za agani nasan bazamuyi wahalar ganowa ba,   gaba ɗayansu suka goyi baya da shawarar sa sannan suka yarda da abun da yace daga nan suka sallame su akan sai sun haɗu goben sannan suma suka tashi ga baɗayan su ɗakin sam suka shiga dan anan zasu kwana gaba ɗayan su,       ________meer    gidan da Abu yasa akama musu tun kan sun karaso yazama ready ansaka musu komai aciki wanda zasuyi amfani dashi na wasu lokutan,   gidane madaidaici bashida wani girma sosai, tundaga wajen gidan meer yake ta faman yatsina fuska saboda gidan kwata kwata baiyi masa ganin yake ko shikadai zai zauna agidan yayi masa kadan amma wai su duka duk ji yayi gaba daya bayason zaman garin gaba daya yakara fitar masa arai horn yayi me gadin da suka tanada yayi saurin bude musu gate ɗin shiga sukayi yayi parking ɗin motar duk suka fito  atare suka jera suka shiga cikin gidan me gadi ne ya shigo musu da kayan da suka zo dashi ɗakuna ukune agidan sai guda ɗaya asama sai ƙaton falo dake ƙasa sama kuma ɗaku daya da falo ne acan dan haka tunda suka ga yanayin gidan sai suka bawa meer shi sukuma suka zauna aƙasan maama ɗaki ɗaya sa Abu da ummy suna ɗaki ɗaya, ɗayan ɗakin kuma babu kowa aciki,    sai kitchen har da dinning area afalon ashe gidan ta ciki ba laifi yana da girma saidai idan kayi comparing ɗin sa da nasu nacan ko kwata kwatan nasu baiyi ba saidai suyi maleji da wannan kawai, loƙacin da suka gama komai loƙacin dare yafarayi dan haka kawai sai suka bari sai gobe sa fita yanzu zasu zauna su huta gajiya, dan haka abinci kawai suka sa me gadin yayo musu order sukaci suka kwanta saida fa meer tunda ya hau sama bai ƙara saukowa ba kuma abin cinma da aka kaimasa bai iya ciba wata jakar sa kawai yajawo yabuɗe ta yazaro wata chocolate wajen guda biyar haka yashiga shansu yana sha yana lumshe ido saboda daɗi  shikuma haka halin sa yake akwai sha zaƙi baiƙi yaƙi cin komai ba kawai yayi ciye ciye sai yaji ya ƙoshi dan ba kullum yake jin abinci ba baidame sa ba kwata kwata, haka yagama shan abar sa ya sha ruwa sannan ya tashi yaje yayo wanka tare da ɗauro alwala yazo ya gabatar da sallolin da ake binsa ya ɗora da nafila sannan yayi addu'o'i ya tashi ya koma kan gado yayi kwanciyar sa hankalin sa kwance.......       *************************    "dan Allah kusake ni menayi muku kar kucutar da rayuwata niɗin marainiya ce bani da kowa kurabu dani dan Allah na roƙeku Ameesha ce take wannan magiyan loƙacin da take ɗaure acikin wani ɗaki ko ma ince kango dan ba komai acikin ɗakin anɗaure mata hannunwa gaba ɗaya ƙafafun ta kuma sun warwara mata su, sai kuka take tana musu magiya,    maza ukune acikin ɗakin yayin da ɗaya yake shirin cire wandon jikin sa yana washe baki duk roƙon nasu da takeyi babu wanda ya ji tausayin ta ɗaya yace mutumina zafa ka kwashi romo kasan yara irin waɗannan sunfi maiƙo dan wallahi nima tunda naganta naji na kwaɗaitu hakannan har ta tayar min da sha'awa dan Allah inka gama nima zan ɗan ɗana dan wallahi na kwaɗaitu da ita yarinyar fa akwai kaya kalli yanda waɗannan abubuwan suka mimiƙe yafaɗa yana shafar ƙirjin ta,   taƙaicine ya isheta da ta rasa abun da zatayi masa bata bari ya matsa daga gurin ba ta tofa masa yawu tare da watsa masa harara, jitake kamar ta shaƙeshi ta kashi haka take ji.. daya daga cikin sune yace Garbe ka yarda tayi maka haka ai wallahi dani tayiwa ba marinta zanyi ba kara tabawa zanyi inga abun da zatayi, "wanda yake kamar oga awajen sune yace kai ya isheku haka gwanda ma da tayi maka haka kai banda abun ka ban fara tabawa ba zaka taba kabari infara dandana kafin kai shina yakarasa maganar yana washe baki tare da zaro harshe ya lashe bakin sa yana shinshina wuyanta tare da saka hannu ya shafo gefen fuskarta, gefe tayi da kanta aranta tana jera masa Allah ya isa tafi cikin carbi matsawa yayi daga kusa da ita yafa ra kunce tazugen jikin sa cire wandon yayi yakama daga shi sai dan karamin wando, "juyawa yayi ya kalli sauran sai yace su dan je daga waje idan yagama sai su shigo wanda aka kira da garbe ne yace dan Allah oga kayi sauri dan wallahi a matse nake na matsu inji a kogin linqaya dariya dayan yayi sanna yace to sai ka jira ai duk gaggawar asara ai tajira samu gaba dayan su suka sake kwashewa da dariya, shide dayan baice musu komai ba dan yasan ma ko yace zaiyi ba dama zasu bashi ba shiyasa ma yayi shiru amma de shima ya kwadaitun da ita dan takobin sa har ta harba jin irin zancen da suke da kuma haskosu da yake sai yaji dama shine, da har sun nufi hanyar waje zasu fita sai ogan nasu ya dakatar da su yace kunga kuma tsaya agaban ku zanyi kuyi min video inason ingani idan nagama ba musu kuwa garbe yayi saurin zaro wayar a aljihu ya shiga video din jira kawai yake yafara.... tsugunnawa yayi suka yafara kokarin cire mata rigar dake jikin ta ganin hakan yasa ta kara shiga tashin hankali fusge fusge ta shiga yi tana kokarin kwace kanta nan suka shiga kokawa da shi yana dukan ta yana kwantar da ita amma itama bata dena kokarin kwatar kanta ba yakasa nasara sai kokawa suke garbe ne yace yarin yar nan fa taurin kaine da ita kabari kawai inzo in banqare maka ita, to zo kariqe min ita wallahi yarinya duk bakin cikin ki sai nayi abun dana ga dama yar bakin ciki sokike kiyimin buqulu ko to baki isa ba wallahi garbe zo ka rike min hannuwanta, garbe yana dariyar mugunta ya mikawa dayan wayar sannan ya nufi wajen dan riqeta, yana zuwa ya rirriqe hannuwanta da iya karfin sa tare da danne mata fuska ta yanda bazataga komai ba, shikuma ya buda mata kafafu yana shirin cire mata under din ta, magiya ta shiga yi musu da roƙon su tana haɗasu da Allah su rabu da ita kar kucutar da rayuwata na roƙeku ka rabu dani intafi gurin dadda ta wallahi idan kukayi kasheni zamuyi mutuwa zanyi wayyo wayyo dadda ta dadda zasu kasheni dan Allah kizo ki ceceni zasu kasheni wallahi mutuwa zanyi yaya bossay zasu kasheni kuma ina kuzo ku ceceni wayyo zan mutu wayyo Allah inna lillahi wa inna lillahi rajiun gaba ɗaya tagama fita hayyacin ta saboda zuwa yanzu jikin ta yayi kaishi bata da larfin cigaba da ƙwatar kanta.... ""Kai kai kai me nake gani haka Abbati me kake shirin yi haka, cak yatsaya da abun da yakeyi jin muryarta baita ba tunanin zuwan taba yanzu awannan lokacin juyowa yayi yana kallon ta sai kuma ya sunkuyar dakai, qarasowa tayi inda suke sanye take da blue din lace me shegen tsada da kyau sai mayafi da ta yafa black da dan ratsi ratsin blue ajiki ta dorasa akanta fuskar ta dauke take da face mask hakan yasa ban iya ganin kamannin ta ba, kallon su tayi cike da takaicin abun da taga suna shirin aikata mata, saida tagama kare musu kallo tare da bin Ameesha da kallo itama dake kwance akan wata kujera, batare da ta ce musu komai ba ta qarasa inda Ameesha take sai tace tashi mata tashi zaune Ameesha na karkarwar jiki ta tashi zaune jikin ta duk ya mutu amugun tsora ce take dan tama gama saddakar wa sungama rabata da mutuncin ta saboda zuwa yanzu tagama gajiya da kwatar kannata sai kuma Allah ya kawo mata dauki dan atunanin ta taimakon ta matar zatayi...... bayan ta tashi zaunen tana rawar jiki tafara rokon matar dan Allah ki fitar dani daga nan gurin mugaye ne so suke su rabani da mutuncina wallahi idan sukayi kashe ni zasuyi mutuwa zanyi tayi maganar tana kara sakin kuka tana ruqo hannun matar, kwace hannun ta matar tayi tare da mikewa tsaye ta dakamata tsawa tace dalla rufe min baki angaya miki nazo nanne dan naitaimaka ki to idan ma haka kike tunani kinyi ba hagon tunani yarinya nidaman ai mutuwar nake so kiyi kashe ki nace suyi dan haka kisani baza ki kara kwanan duniyar nan ba karshen ki yazo dole ki tafi inda iyayen ki suke bazan taba bari kici gaba da rayuwa ba tunda idona yayi tozali dake na kudurci sai na aikaki inda suke baza kitaba cigaba da rayuwa ba dole ki mutu, cak Ameesha tayi komanta ya tsaya cak ya dena aiki kanta wani irin nauyi yayi mata jitayi jinta da ganin ta duk sun tsaya suman wucin gadi tayi ta dawo bakin ta na rawa tana so tayi magana amma ta kasa, bata gama dawowa daga tunanin ba taji wani wawan mari a fuskarta har guda uku alokaci guda agigice ta dago tama rasa inda zata tsoma ranta domin abu biyu ne suka hadar mata ga zafi ga tsoro da furgice da ta tsinci kanta..... Yau wacce irin ranace agareta yau me yake shirin faruwa da ita wacece wannan matar da ta shigo cikin rayuwar ta take shirin kasheta Haryana cewa zata aika ta inda takai iyayen ta kenan wannan ce silar rabata da mahaifanta shin me suka aikata mata,   matar ce ta nuna sauran mazan da duk sunyi tsuru tsuru sun kame gefe guda da yatsa tace bance wani yakara yunkurin lalatata ba abun da nakeso shine kuyi tagana mata azaba daganan har wayewar gari gobe asubar fari kar kowa ya tashi kufita da ita kuyi nesa da gari kusami wani katon ruwan ku jefata ciki ko kuma rijiyar da ba a amfani da ita kusaka ta aciki amma lafin kusaka ta aciki inason ku tabbatar da gawarta zaku saka aciki saboda ko gawarta banason agani ku batar da ita bat kunji abun da nace muku gaba dayan su suka amsa mata da to saida ta kara gargadin su akan karsuyi mata abun da taga suna kokarin yi idan ba hakaba kuma bazata biyasu kudin aikin suba, sannan ta fice daga dakin fuuuuu kamar kukar bulukiya, itade Ameesha ko kwakkwaran motsi takasa yi daga gurin domin komanta ya tsaya tazama kamar mutum mutumi kukan ma takeso tayi amma takasa hawayen sunki fitowa.......   dariya suka kwashe da ita bayan fitar matar ogan nasu yace ai wallahi tunda na ƙyasa babu abun da zai hanani yi zade muɗaga mata ƙafa kawai mubarta zuwa gobe idan muka fita sai mukaita dandalin ƙare kuka kaga sai muraƙarƙashe ta son ranmu danni inajin wuni zanyi akanta sai naci na ƙoshi sannan zan baku kunga daganan kawai sai mu aikata can inda ba adawowa bayan mun gama kwasar daɗin mu ko ya kuka ce yafaɗa tare da miƙa musu hannu suka tafa suna ƙara sakin dariyar farin cikin wannan dama da suka samu........✍️✍️✍️ Shin wacece wannan matar da ta shigo a ina taga Ameesha me kuma tayi mata take son kashe ta?                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [6/27, 8:49 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️71&72 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                     "Ameesha ce kwance cikin daji a ƙasa hankalin ta gaba ɗaya baya jikin ta tagama galabaita ta fita hayyacin ta tana cikin mawuyacin hali mazan nan suna kanta inda ya fara koƙarin keta mata haddi dan har ya cire kayan jinkin sa inda sauran biyun suka rirriƙeta shikuma ya daidaita ya shigeta wata irin ƙara tasaki ta azaba da taji loƙaci ɗaya nunfashin tane yashiga ɗaukewa amma shikam ko kaɗan bai saurara mata ba sai aikin gabansa yake sauran kuma suna ƙara zugashi bai ɗaga taba saida ya tabbatar yayi mata kaca kaca har ta dena motsima sai da yaji ya gamsu sannan ya murgina gefe yana sauke numfashi ɗayan ya kuma yowa kanta yana washe baki saboda shine alayi duk da halin da take ciki amma bai dameshi ba haka shima ba kunya ba tsoron Allah ba tausayi shima ya hau kanta kwata kwata ko motsima batayi amma ko ajikin sa hakan baidame saba damuwar sa kawai yajisa ajikin ta shine cikar burin sa, haka shima yasaita ta yafara aiki akanta shima baiɗagata ba saida yajisa daidai sannan ya ɗaga ta shima yana maida numfashi,shide ɗayan zuwa loƙacin ya haƙura da ita dan yama lura kamar ba numfashi ajikin ta kallon su yayi yace oga yarinyar nan da kamar bata numfashi da sauri suka tashi suka duba ɗaga hannun ta sukayi tare da kara kunne su asaitin ƙirjinta tabbas bata numfashi ogan nasune yace amma wannan yarinyar akwai ragonta yanzu ɗan wannan abunne yasa ta mutu garbe ne yace wai da gaske ta mutu kode suma tayi ƙara dubata yayi da kansa sannan yaɗago yana kallon su yace wallahi kwa ta dagske ta mutu 😭😭,   "inna lillahi wa inna lillahi rajiun, inna lillahi wa inna lillahi rajiun, muryar dadda ta karaɗe ɗakin da take kwance cikin tashin hankali ta sauko daga kan gadon tana dafe kanta a furgice ta fito falon tana kwaɗawa Ammi kira, Ammi dake bacci taji kira kamar a mafarki hakan yasata buɗe idonta ahankali tana buɗewa tajiyo murayar dadda na ƙara kwala mata kira a furgice itama ta sauko daga kan gadon ta fito waje ko dan kwali babu ajikin daga ita sai kayan bacci haka tafito da sauri,    ganin dadda na kuka shaɓe shaɓe yasa taƙara tsorata da sauri ta ƙaraso wajen ta riƙe dadda da kyau tana tambayar ta lafiya me yake faruwa dadda takasa magana sai kuka da take kawai sosai hankalin Ammi ya tashi kokekoken ta yasa sauran mutanen gidan tashi suma daga bacci duk suka fito falo hankalin kowa atashe nan kowa ya shiga tambayar me yafaru da ita,   Amma basu samu amsa daga gurin dadda ba saida taga shan kukanta ta more sannan cikin shashsheƙar kuka tace sun kashe min ita sun rabani da ita sun kasheta sun yaudareni sun ɗauketa sunkaita can sunkashe ta meyasa zasuyi min haka me yarinyar nan tayi musu daman dan su cutar da itane sukazo sukayi min daɗin baki suka rabani da ita yanzu sunzo sunci zarafin ta sannan suka rabata da da duniyar wallahi bazan barsu yanda suka kasheta duk sai sun mutu suma sai na kashe su wallahi saina kashesu,    Sude su Ammi sunga tashin hankalin da basu taɓa gani ba agurin dadda gaba ɗaya sun kasa gane inda maganar ta ta dosa da ƙyar de suka samu suka tambaye ta suwaye kuma wa aka kashe,   mutanen da suka zo suka ɗauke ta yanzunnan nayi mafarki sun lalata mata rayuwa sunkashe ta wallahi sune maza uku nagani kuma daman su ukune harda ɗanki aciki shiyasa daman bai kwana agida ba to wallahi sai na kashesu ga ɗayansu babu wanda zai ƙara rayuwa kamar yanda suka rabata da duniya cikin kisan wulaƙanci to suma dole suyi mutuwar wulaƙanci tafaɗa tana karkaɗa kai,   sude yaran gurin dariya ma abun yabasu wai ashe duk wannan uban kwakwazon da takeyi mafarki ne wallahi duk a tunanin su wani da gaskene gaya mata akayi ta mutu wai ashe duk mafarki take wasu kuma taƙaicine ya ishesu na tashinsu daga bacci da tayi duk matan komawa ɗakunan su sukayi Farouk ne kawai da Ammi suka tsaya agun suna bata baki, Ammi tace "dadda dan Allah ki kwantar da hankalin ki kinsande mafarki ba gaskiya bane meyasa kuma zaki tashi hankalin ki har kina ikirarin wani abun da bashi da amfani yanzu taya kike tunanin su Aliyu zasu cutar da ita duk ƙoƙarin da suke shirin yi akanta waɗannan mutanen ba macuta bane duk da bansan suba amma ni na yarda dasu kuma ga Aliyu ma shima na yarda dashi nasan bazai taɓa bari wanima ya cuceta ba bare kuma harda sa hannun sa a haɗu akashe ta hakan ma bazata taɓa faruwa ba kiringa tunani kafin ki yanke hukunci haka Ammi tayi tamata saboda harga Allah abun da tace wai sune duk da mafarkine ta ɗanji ba daɗi har cikin ranta, da ƙyar suka samu dadda ta dena yi musu raki amma fa tace wallahi saidai akira mata shi Aliyu taji dalilin da yasa baidawo gida ba kuma yahaɗa ta da Ameesha bayan da suka iya dole Farouk yaje ɗakin sa ya ɗauko wayar sa sannan ya dawo falon agaban su yakira shi loƙacin dare yayi sosai da ƙarfe biyuna ta wuce, suna cikin baccin su duk da daman basu daɗe da kwanciyar ba kuma ba baccin daɗe suke ba kawaide dande bacci ɓarawone shiyasa ya sace su, ana kiran wayar kuwa ƙarar ringing ɗin ya farkar da su saidai basu tashi zaune ba bossay yajawo wayar da ƙyar yana mamakin me kiran sa a irin wannan loƙacin ganin sunan ƙanin sa yasa shi faduwar gaba da sauri ya ɗaga tare da yin sallama daga can wajen su Farouk suna ganin anɗaga suka sauke ajiyar zuciya dan duk atunanin su idan sun kira baza su same shiba daga nan kuma dadda ta ƙara tayar musu da hankali, "wa'alaikassalam" farouk ya amsawa bossay sallamar da yayi sannan yace yaya daman Ammi ce keson magana da kai, "lafiya de ko? " eh lafiya gata yafaɗa yana miƙawa Ammi wayar, karɓa tayi tare da kara wayar akunne tace Aliyu kana jina? "Eh Ammi, "meyasa baka dawo gida ba? taƙara tambayar sa, Ayi haƙuri Ammi ban kira na sanar dake ba Wallahi wani aikine ya riƙemu yanzu haka duk muna guri ɗaya kuma gobe da safe zamu ƙara fita, ok to shikenan Allah yakaimu daman dadda ce tayi mafarki shine duk ta taso mu wai ta ganku kuna azabtar mata da jika kuma kun kashe ta daga baya shine duk tabi ta tayar da hankalin ta da ƙyar muka samu tayi shiru amma ita tace mafarkin ta gaskiya ne indai kuma ba gaskiya bane to akiraka taji, to kaji dalilin kiran, gaban sane yaji ya tsananta faɗuwa ɗif yayi ya kasa cewa komai, "Hello Aliyu Aliyu kana jina kuwa naji kayi shiru ko akwai abun dake faruwa, Da sauri yadawo cikin hayyacin sa cikin inda inda yace a...a Ammi babu komai amma de yanzu Bama tare da ita hasalima ba agidan datake muke ba mu muna can masarauta gidan su Sameer kice mata tayi haƙuri zuwa gobe sai a haɗasu Ameesha tana nan cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali babu abun da yasame ta dan haka ta kwantar da hankalin ta, daman a hansfree tasaka wayar dan haka duk sunji komai amma fa dadda sai ta rufe ido ita duk da haka bata yarda ba gobe goben nan adawo mata da jikarta duk abun da zasuyi suyi shi tana gaban ta ita saitafi kula da ita bazata bari ta ƙara nesa da itaba ƙafarta ƙafarta saidai kuma idan itama ta koma can inda take amma bazata ƙara kwana batare da itaba, Shide bossay kawai to yake cewa tunda tafara maganar zufa take tsatstsafo mishi duk sanyin Ac dake aiki aɗakin amma tayi masa kaɗan daman ance marar gaskiya ko aruwa gumi yake haka de suka rabu akan gobe zai kawo mata Ameesha babu abun da yasameta, ahakan ma da ƙyar su Ammi suka lallaɓa dadda ta koma ɗakin ta ɗan cewa tayi a falon zata zauna har gari ya waye a haɗara da jikarta sannan hankalin ta zai kwanta.....to da ta koma mama ɗakin ta kwanta tana ganin fitar su ta tashi zaune dan bazata taɓa iya komawa bacci ba ji take idan ta koma za'ace mata shalelan ta ta mutu da tagaji de da zaman sai ta ta tashi taje tayo alwalla tazo ta fara sallah, Bossay kam shimade anasa ɓangaren bacci ƙauracewa idon sa yayi yarasa ina zai tsoma ransa yayi mamakin jin abun da dadda tace shima hankalin sane yafara tashi tunanin ya shiga yi karde mafarkin dadda yazama gaskiya wataƙil tana can ana gana mata azaba ko kuma ankashe shiyasa dadda tayi mafarki, Nooo! yayi saurin faɗa yana girgiza kai nasan ma bata mutu ba baza ta mutu ta barni ba nina sani tashi yayi zaune gaba ɗaya jikin sa yaɗauki ɓari ya shiga karkarwar sanyi shi kaɗai yasan halin da yake ciki, duk abun da yake sam yana jinsa amma yakasa tashi yayi masa magana saboda yagama fahimtar duka zancen da yayi yasan daga gida aka kirasa yanayin amsar da ya bayar ne yasashi fahimtar abun dake faruwa, shettima kam tunda ya buɗe ido yaji ba shi ake kiraba yayi juyi ya koma yaci gaba da baccin sa, "bossay fa abu na neman yafi ƙarfin sa dan har ya fara zubar da hawaye ga zazzaɓi da ya rufe sa loƙaci ɗaya amma duk da sanyin da yafar ji yakasa komawa ya kwanta bare ya lulluɓe jikin sa san gujewa sanyin da yakeji kawai ya zauna yana ta karkarwar jiki.... Sameer da yaji abun nasa yafara yin yawa sai yataso da ƙyar yazo inda yake saboda shi bossay yana kan kujera sukuma suka kwanta akan gado saboda idan suka kwanta su uku gurin yayi musu kaɗan shiyasa shi ya kwanta akan kujera, "yana zuwa wajen sa ya taɓa jikin sa yaji shi yayi zafi rau tashi yayi daga gurin yake wajen wata drawer ya bude ya ɗauko masa magunguna tare da buɗe frigh ya ɗauko masa ruwa sannan ya dawo gurin ɓalle masa maganin yayi ya bashi karɓa yayi ya sha, sam yayi masa sannu sannan ya gyara masa gurin yace ya kwanta, kwantar yayi shikuma sameer ya lulluɓesa tare da ƙara yi masa sannu, kai kawai yake ɗaga masa dan magana ma bazai iya yiba baida wannan ƙarfin halin, dake amaganin da sam yabashi harda na bacci dan haka baidaɗe da kwanciyaba wani wahalallan bacci yayi awongaba dashi, sam ya tausaya masa kuma ya tausayawa kansu gaba ɗayama dan yasan idan wannan tsohuwar taji wannan labarin basu san ya zasuyi da rigimar taba abun da yake gudu kenan gashi kuma zai kasance yanzu yayi mata alƙawari zai kai mata ita sukuma ƙarewa ma basu san inda take ba kuma koda sun gantanma basusan awane irin hali zasu tsince taba, shimade adaren da ƙyar ya iya komawa baccin dan tunane tunane yake tayi ahaka har bacci ya yasace sa... ************************** ______*AMEESHA*     Aranar de Ameesha taci baƙar wuya awurin su dan ko runtsawa batayi ba ahaka suka kwana suna bata wuya ko tausayin ta basuyi suma kwa tayi shi yafi a ƙirga saidai inda Allah ya taimaketa adaren de basuyi yunƙurin yi mata faɗen ba kamar yanda suka ce sai sun fita daga gurin zasuyi mata haka suka barta daf da gabanin asuba suka rabu da ita ta ɗan huta saboda kar suzo fita da ita ta basu matsala har wani yagan su, saida akayi kiran sallar asuba sannan suka fara shirin fita daga wajen suna daf da fita aka shiga sallah dan haka saida suka bari aka shiga sallah masallaci yanda suke da tabbacin babu kowa awaje kowa ya tafi masallaci dan yin Sallah sannan suka fito inda suka yi parking ɗin motar su awani lungu nan sukaje suka shigar da Ameesha da take kamar marar rai saidai duk tana ji motsin su babu abun da bataji kuma loƙuta zuwa loƙuta tana ɗan buɗe idon ta sai kuma ta ƙara rufewa tana jinsu har loƙacin da suka shigar da ita motar, sauri sukayi suka ja motar suna zuwa bakin gate daman gate ɗin a buɗe yake sai kawai suka fice daga ciki batare da sun haɗu da kowa ba, "Sisi yi sauri kigani dan kiyi sauri zata fita, da sauri hamr ta ƙaraso bakin window ɗin da Amra take tsaye agun tace wai ke meye hakan wacece zata fita, ,"Amra tace motar da nake cewa jiya nagani wallahi itace dan har mafarkin ta nayi jiya wallahi Allah itace, "Tsaki Hamra taja tare da matsawa daga gurin tace dalla malama ni kin ɓata min loƙaci da tuni nayi raka'a ɗaya ke mema yakawo ki gun window da asubar nan, "Amra tace zafi nake ji wallahi shiyasa nazo zan buɗi window ɗin sai kawai naga motar ta nufi hanyar waje ke kuma banza anacewa kizo ki gani ko ƙi ni kin ma ban haushi wallahi, tsaye hamra tayi tana kallon ta saida tajira tagama maganar tata sannan tace daɗina dake rashin hankali wani loƙacin inbanda abun ki me zai kawo motar nan gidan kuma har ta fita daga asuba wataƙil ko mafarkin da kikaine yanzu kuma ta koma yi miki gizau shiyasa kika zo kikatsaya kike ganin ta ko to Allah ya kawo sauƙi tana gama faɗa mata haka ta tayar da sallar ta, "Amra taji haushin maganar da tayi mata tana son mayar mata da martani amma taga ta tayar da Sallah shiyasa kawai ta rabu da ita ta wuce bathroom dan tayo alwalla itama, tunda suka fita da ita suke faman kwarara gudu akan titi sai da sukayi nisa da masarautar sannan suka ɗan fara rage gudun wata unguwa suka nufa inda suke da wani gida madaidai ci, gidan garbe ne da daman nanne wajen shagalin su wataran ma anan suke kwana a waje sukayi parking sannan suka fito tare da ciccibo Ameesha sannan suka shiga gidan afalo suka ajiye ta, Sannan ogan nasu yace suje suyi ƴar fakiki su miƙa asubar su sannan su dawo sufara abun da yakawo su oganne yafara yin gaba har zai shiga wani ɗaki sai kuma ya tsaya ya juyo ganin garbe ya tsaya bai taho ba yace kai kuma me katsaya jira garbe "yace wai injireta ko idan kun gama sai inje ni in wataƙil ma bayi zanyi ba kasan k customer sai da bashi, kallon sama da ƙasa yayi masa yace ni ai duk iskanci na inayin sallah koda ba aloƙacin ta ba amma kai baka son yin sallah sai kayi sati bakayi ba shiyasa kullum kake ƙara baƙi, "eh najide koma me zakace kace kuje kuyi ni ina nan, "to wallahi baka isaba sai muntafi tare dan banyarda da kai ba nasan idan na tafi lallataeta zakayi shiyasa kake son abarka kaikaɗai to wallahi baka isaba wuce mutafi, shide garbe ba haka yaso ba wallahi yaso ace sun rabu dashi da wallahi kafin sudawo yayi abun da zaiyi dan bayaso ace sai wani yafara kwanciya da ita kafin shi so yake ace shi zaifara ɗanɗa nata bayanda ya iya dole yabisu suka shiga ɗakin tare gudun kada garbe ya fita idan ya shiga banɗaki sai kawai yasawa ɗakin muƙƙuli sannan ya shiga banɗaki sukuma suka zauna akan kujerar ɗakin suna jiran fitowar sa yayi yayi su fita, "duk abun da sukeyi akan kunnen Ameesha dan haka tana ganin shigarsu ɗakin ta yunƙura zata tashi amma sai taji kanta yayi mugun sarawa sai ta koma ta kwanta tayi haka yakai wajen sau biyar amma takasa tashi da ƙyade tayi jarumta ta daure tunawa da wasu abubuwan da kuma tuna abun da suke shirin yi mata yasa ta tashi da ƙyar jikin ta duk babu kuzari haka ta miƙe tafara jan ƙafafunta da sukayi mata mugun nauyi ahaka harta ƙarasa bakin ƙofar tana murɗawa kwa tajita abuɗe ba muƙƙuli ajiki daɗi taji ya ziyarce ta take taji wani ƙwarin gwiwar yazo mata da sauri ta buɗe ta fita da falon can wani waje ta hango da take da tabbacin nan ce hanyar fita daga gidan ahaka taci gaba da takawa tana cije baki tana daddafa bango da taimakon Allah tazo wajen ƙofar fita jan ƙofar tayi saitaji taƙi buɗuwa daga kanta tayi sai kawai taga saƙata ajiki gashi kuma tsawon ta baikai ba tunanin mafita tafarayi yau ita taga rashi ga ƙoshi ga kwanan yunwa, jingina kanta tayi da jikin bango tare da dafe kanta da taji yana sara mata kamar zai rabe gida biyu ta ɗau wajen minti biyar ahaka batare da ta ɗago ba da ƙyar ta iya ɗaga kanta ta shiga dube duben wajen can ɗan nesa da ita ta hango wata jarka kamar ta jarkar mai da sauri ta nufi wajen da dauriya taje ta ɗauko ta takawo wajen takawa tayi saidai tana ɗora hannun ta akan saƙatar tajiyo murayar ɗaya daga cikin su yana cewa gata cen ai saidai nace maka kabari na tsare ta kaƙi yanzu gashinan da ba muyi saurin fitowa ba da tuni ta fita, jin hakan yasa jikin ta na rawa taja saƙatar tana cire wa ita kuma tafaɗo daga kan jarkar bakin ta har fashewa yayi jini yafara fitowa amma bata bi takan zafin da taji ba ta kuma yunƙurawa ta miƙe da sauri kafin su ƙaraso inda take tayi saurin buɗe ƙofar tafice da gudu ita kanta batasan daga ina tasamo ƙarfin yin gudun ba kawai cilla ƙafa take kawai ita kanta batasan inda take dosa ba, yayin da sukuma suke binta abaya saura kiris sukamata dan har tana jiyo takun su abayan ta juyowa tayi danganin sunkusa kamata ko kuwa ta juyowa tayi tuntuɓe ƙafarta ta sarƙe ta faɗi ƙasa timm da ruf da ciki ɗagowa tayi sai kawai idon ta yasauka akan wata farar ƙafa da take cikin wani baƙin takalmi me laushi jikin sa duk gashi ƙafar ta ƙuarawa ido batare da ko ƙiftawa ba haka take kallon ƙafar tade san tabbas batayi mata kama da ƙafar waɗan cen mutanen ba....... Ayi sallah lafiya gobe sallah baza kusame update ba saidai zuwa jibi ko gata idan Allah yakaimu                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [6/30, 10:03 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️73&74 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                     "  "ɗaya daga cikin sune takai hannu zai kamota yana dariyar mugunta yace ke har kin isa ki gudar mana zonan wallahi baki isa kin gudar mana ba duk inda ma zaki sai mun kamaki yana wannan maganar loƙacin da yakai hannu zai taɓata saidai bekai ga kaiwa jikin ta ba yaji an riƙe masa hannu ƙam a harzuƙi ya ɗago dan sauke wa mutumin dake tsaye sarai sun gansa amma suka nuna kamar ma basu san da zaman sa ba, bai gama daidaita tsayiwar sa ba yaji ya murɗe masa hannu azaba tasaka shi sakin ƙara wata razananniyar ƙarar yasaki sakamakon jin ƙarar karyewar ƙashin hannun sa, da sauri su garbe sukayi kanta zasu ɗauke ta tayi saurin tashi tana tashi tayi kan mutumin da ya taimaketa ɗin bayan shi taje ta ɓuya,   ogansu ne da ransa yagama dugun zuma yakai ƙololuwar ɓaci yayi kan mutumin da niyar kai masa naushi kafin yakai nasa naushin yaji ansauke masa wani wawan bugun da atake bakin sa ya fashe yafara zubar da jini amma duk da haka bai daɗara ba ya ƙara kaimasa hannu zai buge sa aikwa nan mutumin yakaiwa wuyan sa damƙa ya shaƙe masa wuya ya fara naushin bakin sa ga shaƙa ga naushi ba saki bakin sa ba saida ya zubar masa da haƙoran bakin sa sannan yasake sa daga nan kuma yabi jikin sa da suka saida yaga ta dena motsi sannan ya rabuda shi yakoma kan garbe dake faman ja da baya yana niyar guduwa taku biyu yayi ya shaƙosa shima nan ya shiga dukansa ya fasa masa kai sakamakon bugashi da ginin wajen da yayi atake kansa ya fara zubar da jini shima ya sumar dashi ataƙaicede saida yayiwa kowa lilisa ɗayan kuma baɓɓalasa kawai yayi ƙafa da hannu ba inda yabari da za amora sannan ya rabu dasu haka, "cikin takunsa na isa da ƙasaita ya fara takawa zuwa inda tayi suman tsaye tana kallon sa tunda yafara dukan su ta zubawa bayan sa ido duk da tagaji da tsayiwar ƙafafun ta sunyi mata nauyi amma saboda tsabar al'ajabi da mamakin ganin yanda yake faɗa hakan ya hanata motsawa daga gurin, ga mamakin ta yana zuwa kusa da ita kamar zaiyi mata magana sai kawai ya gota ta gefen ta yayi wucewar sa batare da yace mata komai ba, juyawa tayi da ƙyar tabi bayansa da kallo ganin de da gaske tafiya zaiyi yasa tayi saurin bin bayansa da ɗan gudun ta tana zuwa ta faɗa kan bayansa ta riƙesa gam  tare da zagaye hannun ta akan cikin sa,   cak yaja ya tsaya yakasa ci gaba da tafiyar da yake yi sarai yasan itace dan haka baiyi mamaki ba saidai yayi mamakin meyasa kuma zata biyo sa kin cemata komai yayi kawai ya tsaya yaga iya gudun ruwan ta yanaso yafaraji daga gareta yaji me zatace, itama kuma anata wajen so take yace mata wani abun amma taga baida niya dan haka kawai itama saitaja bakinta tayi shiru kuma batare da ta sake shi ba harda ƙara kwantar da kai abayan sa kuma duk yana jinta amma baice mata komai ba,   sunkai wajen minti goma ahaka daga ƙarshede da yagaji cike da taƙaicin yarinyar yasaka hannun sa yaraba jikinsa da nata tare da matsawa gefe ya watsa mata kallon banza sannan ya sake juyawa zai tafi, bata daddara ba taƙara binsa tayi saurin shan gabansa, harara ya wurga mata yana haɗe girar sama da ƙasa aransa yake ayyana wannan mayyace ko aljan yau yagamu da ita tana neman ta takurawa rayuwar sa, tagefenta ya ƙara ratsawa zai wuce tayi saurin riƙo hannun sa tana girgiza masa kai tana hawaye fuskarta duk ta ɓaci da hawaye,   ko kallon ta baiyi ba ya  runtse idon sa cikin kausarsiyar muraya ya daka mata tsawa da cewa "How dare you.. don't touch me again if not I will teach you a lassen, leave me alone yana gama faɗar haka cikin daka mata tsawa ya fusge hannun sa ya ƙara gaba, batare da ya tausawa halin da take ciki ba,    yana tafiya yana ta faman zabga tsaki ji yake dama baifito ba shide tunda yafara tahowa garin nan yake fuskantar ɓacin rai tun jiya ake ɓata masa rai gashi yauma da sanyin safiya ya haɗu da wasu mahauka tan musamman waccen yarinyar dan yafi jin haushin ta ɗan duk atunanin sa itace tajawa kanta inbanda haka tana ƴar ƙaramarta yarinya da ita ina ta baro iyayenta tafito da safennan Allah yaƙara ma sai yaji dama bai taimake taba ya rabudasu suyi mata abun da suka ga dama inyaso gobe bazata ƙara fitowa waje ita kaɗai ba, sai da nasani ma yakeyi, yaɗanyi nisa da tafiya yajiyo takun tafiyar ta abayan sa bai tsayaba yaci gaba da tafiya batare da ya tsaya ba, shan gabansa ta karayi cikin kuka shaɓe shaɓe harda shashsheƙar ta kuma takasa magana ba zato ba tsammani kawai yaji ta faɗa masa kan ƙirjin sa rungume shi tayi sosai sai kuma ta fashe masa da kuka sai yanzu abubuwan da suka faru da ita suka fara dawo mata arai tunawa da tayi da tuni yanzu tana cen hannun su suna wulakanta ta da tuni yanzu wani labarin ake ba wannan ba da tuni sun rabata da mutuncin ta daga nan kuma ta barmusu duniyar dan bata tunanin idan sukayi mata haka zata iya cigaba da rayuwa tasan mutuwa zatai da tuni yauce ƙarshen ta aduniya shikenan bazata ƙara ganin daddar taba da ta rage mata gatanta aduniya sosai tashiga tunani kala kala tana ƙara riƙeshi kamar zata shige jikin sa tana kuma sakin wani irin kuka ga duk wanda yaji irin sa dole ya tausaya mata dan ba ƙaramin kuka take ba kuka take me tsuma zuciyar me sauraro, dan kamar ranta zai fita haka take kuka..... shiru yayi yana sauraron kukan nata duk rashin imanin sa saida yaji ta bashi tausayi amma shi baisan yanda zaiyi da itaba dole ta rabu dashi yatafi baisan ta batasan shiba kuma bazai iya kaita can gidan suba to idan ma yakaita yacewa su ummy a ina ya samota kai inama zaman mace a inda yake bazai iya ba yana gama tunanin hakan ya yanke shawarar tafiya ya rabuda ita saidai kuma yama fara ƙoƙarin raba jikin sa da nata ta ƙara riƙeshi ta cukuikuyi shi tana ƙara shigewa jikin sa, abufa yakusan fin ƙarfin sa duk yanda yaso ya rabata da jikin sa ya gagara yarinya tabi ta riƙeshi ta hanasa  tafiya da yaga abunna ta hakane baza ta rabu dashi ba  sai yace mata  sakeni mutafi to amma duk da haka taƙi yarda ta sakeshi, shide yarasa yau da wacce irin yarinya ya haɗu da ita badan yana ɗan jin tausayin ta ba da tuni ya fatattake ta amma ba yanda ya iya dole ya taimaketa tunda shi yajawo wa kansa da kansa, daga inda suke a tsaye ya kawai ya ɗagata cak ya saɓata akafaɗa yashiga tafiya da ita amma zuwa yanzu ta rage kukan da takeyi sai shashsheƙa kawai takeyi....., ahaka yaci gaba da tafiya cike da taƙaicin abun da yafaru har ya ƙarasa gida kwankwasa wa yayi me gadi ya buɗe masa yana masa sannu da zuwa cike da mamakin ganin sa da yarinya akafaɗa amma de amatsayin sa na me gadi ba hurimin sa bane dole yaja bakin sa yayi shiru yana binsu da kallo har suka shige, da sallama ya shiga falon gidan amma kasancewar safiya ce babu kowa acikin falon yasan duk suna bacci basu tashiba kuma aƙa idarsa indai mutum yana bacci baya tashin shi daga bacci dan haka kawai yayi sama da ita zuwa ɗakin sa, itade tayi lamo ajikin sa tana kallon gidan ahaka har ya haura upstairs ɗin da ita yakaita ɗakin sa yana shiga ya kwantar da ita kan Capet ɗin ɗakin dan acewar sa baza ta taɓa masa wani daga cikin dakin ba saboda kayan ta duk sunyi datti, yana shirin tashi ta ƙara riƙoshi kallon da ya watsa matane yasa ta haɗiye kukan da take shirin yi kuma tayi saurin sakin sa, kaɗa kai kawai yayi batare da yace mata komai ba ya nufi bathroom dan yin wanka saboda gaba ɗaya ƙyanƙyamin kansa yake da kayan jikin sa dan ba yanda zaiyi ne ta riga ta taɓashi tun farko batare da sanin sa ba amma da bazai bari ta raɓe saba, kayan jikin sa ya shiga tuɓewa yanayi yana taɓe fuska kamar me taɓa kashi haka yakeyi da fuska haka yagama cirewa daga shi sai gajeran wando yayimar kayan yayi ya buɗe ƙofar ɗakin yafita waje ya watsa su waje  ta window sannan ya dawo Allah sarki baiwar Allah dake agajiye take taji sanyin Ac ya ratsata ai tunda ta rufe idon ta loƙacin da taga yana ƙoƙarin cire kaya tayi saurin rufe idon bata ƙara buɗewa ba bacci yayi gaba da ita tun kan yadawo cikin ɗakin, yana shigowa bai kalli inda take ba ya wuce banɗa ki yayo wanka sannan ya fito ya shafe jikin sa da mayukan da yazo dasu,   sannan ya sauya wasu kayan ya ɗauko kayan ciye ciyen sa yaci abun sa duk abunnan da yake yana sane da ita aɗakin saidai bai kalli inda take ba saida yagama komai ya hau kan gadon sa sannan batare da ya kalle ta ba yace idan kin gama zaman ki tashi kije waje idan mutanen gidan sun tashi sai ki gaba tar musu da kanki  suyi yanda zasuyi dake idan taimako kuma kike so kigaya musu suyi miki abun da zasuyi miki ki ƙara gaba nagama yi miki abun da zan miki kuma kar kibari intashi inganki acikin gidannan ni na kawoki amma banason zamanki anan kiyi kibar gidan yana gama faɗar hakan ya juya mata baya yayi kwanciyar sa batar da yasan halin da take ciba kuma baidamu da rashin amsar taba......, aɓagaren ta kuwa batama san yanayi ba dan bama ta duniyar ta tafi duniyar bacci......,        ************************* tunda safe su sameer suka haɗa kansu alahamdullillh jikin bossay da sauƙi yana tashi yajishi garau saidai kuma tunda safe Sameer yace ya kashe wayarsa shima kuma daman tunanin hakan yake dan yasan dole akira shi daga gida kuma yasan halin dadda tunda tace sai anhaɗa ta da Ameesha tofa yau saita Allah dan haka gwara ta kira layin sa taji akashe ammade bata ɗaga musu hankali ba kuma batasan inda suke ba dan haka dole tayi haƙuri tabari har sai ya koma gida hakan sai ya fiye masa kwanciyar hankali, Wajen ƙarfe goma da rabi suka fita daga gidan gaba ɗayan su harsu hamra da Ammar, acikin mota hamra ta ƙara basu labarin motar da tagani ɗazu da safe gaba ɗayan su sunyi mamaki amma wasu daga cikinsu basu yarda ba, Sameer ne yace amma meyasa baki faɗa mana ba tun kan mufito daga gida shiru tayi bata basu amsa ba, shettima ne ke tuƙi dan haka daman basuyi nisa da fitowa ba sameer ya kalle sa yace mu koma gida, shettima ya kalle sa yace mukoma fa kace yaza ayi mukoma bayan mun kusa ƙarasawa ai ni ina ganin gwara mufara zuwa can kar su rigamu zuwa suje suyi wani ƙulla ƙulan nasu mukasa samun wata sheda ko ɗaya inyaso wanann me sauƙi ne idan mun dawo gida mayi duk abun da zayi saboda mutum ɗaya zamu riƙa me gadi tunda ya buɗe musu ƙofa suka shigo kuma suka fita ai dole yasan ko suwaye suka fita nidai ina ganin gwara mufara zuwa ɗin tunda wannan bama mu da tabbas kasande halin Amra da shiriri ta wataƙil ma wata motar ta gani ta zata waccen ce amma in ba hakaba me zai kawo motar cikin gidan nan batare da sanin kowa ba indai har ta shigo koma waye ya shigo ai ansan dashigowar sa, gaskiya ne maganar ka hakan yakamata mufara yi kaga idan mugano wani abun sai nufi tabbatar wa saboda muna da hujja a hannun cewar bossay da haka suka yarda kowa yayi na'am da maganar akan sai sun dawo sai kuma a tambayi me gadi....         ********************** tunda asuba dadda take nacin sai ankira mata bossay amma ankira wayar taƙi shiga dan haka tasakasu agaba sai anfito mata da jikarta dan Wallahi baza ta yarda ba idan ba da rashin gaskiya ba a al'amarin me yasa zai kashe wayar sa saboda yaji tace sai taga jikarta yau shine yaƙi dawowa kuma ya kashe wayar sa saboda yasan basu da gaskiya, Sude su Ammi sun rasa yanda zasuyi da ita sunyi iya bakin ƙoƙarin su wajen sun ganar da ita amma ta rufe ido taƙi sauraron kowa dan haka kuwa kowa yarabu da ita kowa yaci gaba da sabgar gaban sa, dadda da taga haka sai ta koma ɗaki ta ɗauko mayafin ta da ɗan canjin da take dasu ta fito falo tana shirin fita daga gidan Ammi ta fita daga kitchen da sauri ta ƙaraso wajen tana cewa dadda yanzu fisabilillahi bazakiji maganar da muke miki ba meyasa kikeyin haka waɗan nan mutanen ba mayaudara bane bazasu taɓa cutar da Ameesha ba amma kinƙi sauraron kowa yanzu dakike niyar fita kinsan inda take ne ina zakije, Kinga Aminatu nifa wallahi babu wanda ya isa ya rabani da jikata wallahi sai naje sun fito min da ita idan kuma sun kasheta ne saidai hukuma ta rabani da su idan ku kun kasa ni zanje da kaina bade ance ɗan sarkin garin nan bane to ai matambayi baya ɓata zanje har gidan sarkin insanar dashi abun dake faruwa asan yanda za ayi a fito min da jikata dan bazan juri rashin ta ba wallahi bazan taɓa lamin taba akan duk wanda ya taɓamin jika yarinya marainiyar Allah amma anbi an takurawa rayuwar ta anrabata da iyayen ta shine itama sai anga bayan ta so na kuɓuta daga sharrin waɗan cen su basu kasheta sai sune zasuzo har gida su ci amanata ingama basu labarin ta amma memakon su tausayawa rayuwar baiwar Allah amma sai sunemi suci zarafin ta su kasheta to duk ma wanda ya aikata mata hakan wallahi idan mafarkin nan ya zama gaskiya sai inda ƙarfina ya ƙare ko zan rasa komai arayuwata sai na ƙwatar mata ƴanci sai wallahi sai duniya tasan abun da akayi mata dan haka koyi haƙuri kibarni dan bazan taɓa sauraron duk abun da zakice min ba nasan ke mutuniyar kirkice amma daman ance ka haifi ɗa baka haifi halin saba bazan iya yabon ɗanki ba akan basa hannun sa aciki ba tunda har dashi nagani amafarki kuma ga alama nagani da yaƙi dawowa kuma yakashe wayar sa kinga kwa dole inyi zarginsa kiyi haƙuri idan kinji haushina akan zargin da nayi masa saduwar alkhari nagode da mutuncin da kiakyi min bazan taɓa matawa dake ba arayuwata kingama yimin komai kuma nayarda dake dan haka natafi kuma ba lalle indawo cikin gidan nan ba koda ace naganta to zan ɗauketa ne muyi nesa da garin nan shiyasa daman tunfarko bana son inhaɗa mu amala da kowa saboda gudun matsala irin wannan tana gama faɗar haka ta share hawayen da ya zubo mata tare da rungume Ammi sannan ta ra jikin ta da nata sannan tayi saurin juyawa ta fice daga gidan tana share hawayen ta, mutuwar tsaye Ammi tayi bata taɓa tunanin dadda zatayi mata haka ba yanzu tana nufin ta tafi kenan baza ta dawo cikin gidan ba me yasa dadda zatayi mata haka me yasa dadda bata jin magana, jiri taji yana niyar ɗinbanta da sauri tayi saurin dafe bang, tunanjn me ya hana bossay dawowa gida da kuma kashe wayar da tayine ya tsaya mata arai ga kuna abubuwan da dadda ta fada tana cikin tunane tunanen naji zubar hawaye akan kumatun ta hannu tasa ta share tana me jin quna acikin zuciyar ta wani abune yazo ya tokare mata arai jitake kamar ta dora hannun akai ta kurma ihu haka take ji, jitayi andafata da sauri ta dago duk atunanin ta ko dadda ce tadawo hada ido sukayi da farouk cikin sanyin murya yace Ammmi me yafaru naga kina kuka kasa bashi amsa tayi saboda wani kukan da taji yana shirin tahomata, rungumeta yayi yana bata hakuri da kyar ta iya cewa farouk dadda ta tafi ta tafi ta barmu tace bazata dawo ba, ta qarasa maganar cikin matsanaciyar damuwa, da sauri ya raba jikin sa da nata shima cikin damuwa kamar zaiyi kuka yace Ammi me yasa kika barta ta tafi Ammi zata iya fadawa wani halin fa tun yaushe ta tafi Ammi kikara kiran yaya ko zai dauka kiji ina yake kinji Ammi duk yabi ya rikice sai faman jero mata tambaya yake jero mata, riqo hannun sa tayi tace kwantar da hankin ka in sha Allah babu abun da zai sameta kuma in Allah ya yarda zatadawo kar kasaka kanka adamuwa Allah sarki uwa ganin yafita shiga damuwa yasa itama kwantar da damuwarta dan taga ta cire shi daga damuwa haka taita rarrashin sa har yasauko amma gaba dayansu ba sukuni agaresu kowa yayi jigum jigum abun duniya ya ishesu......, ************************ Su sam suna karasawa wajen mall din suka fito gaba dayan su suka shiga ciki inda suka nemi ayi musu iso ga managen gurin ba bata lokaci kuwa aka kaisu har office din sa sameer da bossay ne da shettima kadai suka shiga sukuma suka tsaya daga bakin kofar, bayan sun shiga sun gaggaisa da managen suke sanar dashi abun da ya kawo su atake shima hankalinsa ya tashi yashiga basu hakuri sannan akace aduba cctv camera din na jiya ko za aga wata alama nan ya shiga duba computer din dake gabansa bincike ya shigayi da ido sameer yayi wa bossay alamar yaje ya duba shima bossay ya zagaya ta bayan sa yana ganin dubawara da yake yi daga bayama gaba dayan sune sukaje suka tsaya suna kallon videon tundaga safe har zuwa yamma aka nuno lokacin da suka shigo gurin aikam suna tsayawa da motar su sai ga wata motar ta tsaya daga bayan su, anan sam yasa aka saka pause sannan akace su Ammar su shigo suna shogowa aka nunawa Amra akace itace motar da sauri tace eh wallahi itace kuma itace dazu ta fito daga gida wallahi nagane ta itace, play aka saka videon da suke kalla yaci gaba da tafiya saida babu wanda yafito daga motar... cigaba da kalla sukayi har lokacin da su hamra suka fito tabbas tare suka fito saidai kuma abun mamakin suna fitowa kuma sai camera din ta dauke gaba daya ashe tundafa lokacin ma bata kara aiki ba har sai washe gari taci gaba da aiki, gaba dayan su dagowa sukayi aka shiga kallon kallo gaba dayan su sun kasa magana, managen gurin ne yayi karfin halin cewa to kungade abun da yafaru ni kaina ma bansan da hakan ba bansan ya akai hakan ta faru ba amma de kuyi hakuri kuje zuwa gobe insha Allah zan bincika ahankali har ingano inda aka samu matsar bazai yiyi muyi yanzu ba saboda idan nace za ayi to za aja hankalin customers kuma baza asamu ma'aikata ba dole sai zuwa dare zan tara su gaba daya sai aduba daga ina matsar take kuyi hakuri amma in Allah ya yarda kar kudamu zanyi kokarin gano muku zan kira wani abokina shi zaifi dubamin abun dake faruwa dan zai iya sawa ma gurin haske aga koma menen awajen kar kudamu da wannan, Sai yanzu duk suka samu bakin magana kowa na tofa albarkacin bakin sa game lamarin amma basu tashi hankalin suba tunawa da inda Amra tace taga motar sunsan bazasu sha wahalar bainceke ba da zarar sunje gida suna ganin komai ya daidaita, dan haka ba bata lokaci suka kara kwasar jiki suka nufi hanyar gida suna tafiya suna hirar jefi jefi ahaka har suka karasa unguwar suka nufi masarauta suna shiga gate na farko da yake abude koda yaushe sun nufi gate nabiyu da zai sadaka da cikin masarautar bossay dake tuke yayi saurin taka burki da mamaki duk suke kallon sa shettima yace ya akai lafiya de ko da hannun yayi musu alamar bakin gate din masarautar kallon sa yayi yace me fa yafada cike da rashin fahimta, bossay ne ya dafa kai yace akwai matsalafa kunsan me nagani duk suka ce aa suna duban bakin gate din da yake nuna musu sude sunga wata mata abakin gate din kuma bisa ga dukkan alamu fada akeyi da ita watakil ko hanata shiga akayi, da kyar bossay ya ce abun da muke gudu ya faru shikenan dan haka kowa yasamo abun cewa saboda tsohuwa ta bayyana kowa ya tanadi abun cewa, Sameer ne yace wai me kake nufine sai faman zance kake mana bamu fahimce kaba, Cike da tashin hankali bossay yace dadda ce kakar Ameesha wallahi itace waccen ake rigima da ita, cike da tashin hankali har suna hada baki wajen cewa dadda fa kace..........🙆‍♀️ barkan ku da sallah fatan kowa yayi Salla lafiya........                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/1, 9:32 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️75&76 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                         "cike da tashin hankali har suna hada baki wajen cewa dadda fa kace..........🙆‍♀️ "kwarai kuwa wallahi itace waccen yanzu yazamuyi, "Sameer me yace anya ba juyawa zamuyi mubari idan ta tafi sai mushiga yanzu idan ta saka mu agaba fa me zamuce mata kumsande wannan matar ba ita kaɗai bace yanzu tana ganin mu zata nemi ta tara mana mutane anan gurin kaɗan daga cikin aikin ta dan haka wallahi masalaha shine mujuya kawai mujira tafiyar ta, bossay yasaki murmushin yaƙe dan shi kaɗai yasan halin da yake ciki saboda duk yafisu sanin wacece dadda idan ta kafe akan abu ɗan juyowa yayi ya kalle sa yace wallahi bakasan halin ta bane shiyasa kace mujuya ai indai ba in muka juya to daga nan bazamu dawoba har abada dan wannan matar da kake gani zafin kanta yawuce tunanin ka ai tunda ta riga tasaka ƙafarta ta fito daga can gidan kuma har tazo nan tofa wallahi babu wanda ya isa yasa ta koma sai tayi abun da yakawota koda kuwa zata sha wahala to idan tasa abu gaba saitaga tasamu zata bar wajen, yanzu da kuka ganta acan ko tofa babu inda zataje sai tashiga gidan nan dan hakama ka canza wata shawarar amma banda wannan, sosai suka ƙara mamakin irin wanann halin na dadda, Sude su Ammar sunyi jigum jigum suna sauraron hirar su suna jin jinawa me wannan halin koma wacece saboda basu santa ba, shettima ne " yayi gyaran murya yace nifa inaga kunsan me za ayi "duk suka ce a'a" sannan yace kawai muje musame ta inyaso sai mu lallaɓata ta koma gida muce kuma yarinyar tana wajen Hajiya daman kuma tasan ai ba anan aka ajiye taba tana cen gidan kunga idan ta ƙara nacewa sai taje canɗin mukuma sai muyi tayi mata  yawo da hankali da haka har ta haƙura mumaida ita gidan da ta baro ko ya kukace, "Bossay yace Hmmm lalle baka san taba ne shiyasa kake wannan zancen itace zata yarda har kayi mata yawo da hankali kuma kurabu lafiya da sake Maganar nan taka, sameer da duk kansa ya ƙulle akan dadda saida yaɗau loƙaci kafin yayi magana da ƙyar ya iya cewa muje kawai ni nasan yanda zanyi da ita, jinjina kai kawai bossay yayi yana ayyana abubuwan da zasu faru idan sun haɗa da dadda shide gabansa sai dukan uku uku yake baice komai ba ya tayar da motar suka nufi inda daddar take, **Wallahi baka isaba sai na shiga gidan nan ko kuma kaje kayo min magana da sarkin gidan inma baza kubari inshiga ba uban me zan ɗauka acikin gidan ni yarinyata nazo ƙarɓa tun ɗazu nake tsaye agunnan ina fahimtar dakai amma baka fahimta nabika ta lallami nabika ta salama amma kaƙi ji ko to wallahi zan ture ka inshiga cikin gidan nan kabar ganin ka gabjeje wallahi ba wahala zakayi min ba wajen ture ka dan kaga ina ɗaga maka ƙafa to ko shi sarkin ya isa yayi min abun da kayi min to wallahi duk bakin cikin ka sai na shiga sai anfito mun da jikata acikin gidan kafin a zauna lafiya inkwa ba a fito min da itaba wallahi sai na ɗagawa kowa hankali cikin gidannan sai na daga hankalin kowa da kowa, shide me gadi yabi ya garƙame ƙofar dan shi duk atunanin sa mahaukaciya tazo zata shiga dan gaba ɗaya bayanin ta datakyi baiga meye amfanin su ba dan shi duk a shirme da shiririta yake ɗaukan zancenna ta,   dadda da tagade da gaske me gadin baida niyar bari ta shiga yasa  ta aro duka ƙarfin ta  zata ture shi taji an riƙe mata hannun,   cak ta tsaya tare da ɗagowa  dan ganin ko waye tana ɗagowa tozali da fuskar bossay saurin wara idanun ta, ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da kallo dan suma duk sun fito waje kawaide bossay ne yarigasu saurin zuwa saboda ganin abun da take shirin yiwa me gadi, Kamar wacce aka tsikarawa haka tayi saurin kwace hannun ta Sannan ta shiga tafa hannu da yiwa Allah godiya tana cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Allah na gode maka daka haɗani da waɗannnan mayaudaran munafukan Allah ta'ala nazo har inda kuke kuzo mushiga ku fito min da jikata ko ku haɗani da sarki idan bakuji maganar tawa b ai zakuji ta Sarkin ku ai ku muje yanzunnan mu je gabansa yaraba mana faɗa dan banyarda daku ba gaba ɗaya ku baku da gaskiya idan kuma kunsan kuna da ita to akaini duk inda take yanzunnan dan ba inda zan ƙara zuwa batare danaje ko inaba ƙafarta ƙafata eheee......, bossay ne yace dadda wai meye hakane kike yi dan Allah kidena irin wannan abun bashida amfani  kinsan kwa a inda kike wannan maganar  duk maganar da tazo bakin ki faɗar ta kike kai tsaye gashi kina ai bantamu da wani laifi taya kike tunanin zamu cutar da yarinyar da nayi niyar cutar da ita daba tuni na cutar da ita ba tun kwanakin baya da wataran ma idan mun haɗu baki saniba saunawa zamu haɗu batare da sanin kiba kuma duk loƙacin banyi yunƙurin cutar da ita akan me kuma zan cutar da ita yanzu alaƙocin da tafi buƙatar taimakon kowa duk nan da kika ganmu kullum burinu mu muga munnemo mahaifan yarinyar tunda kika bamu labari kowa ya katse uzurin gaban sa mun dawo muna nata safe rana dare koman mu akan ta yake ko loƙacin kanmu bamu dashi isasshe sai nata amma ke duk abun da ake bakya gani to baza akaiki in taken ba kiyi duk abun da zakiyi duk tunanin da kikeyi akan munyi mata wani to hakanne munyi mata duk abun da kike tunani sannan kuma mun kasheta bade haka kike so kijiba to mun kasheta muma kizo ki kashemu ko kisaka akashemu yana kaiwa nan cikin fushi yayi fuuuuu ya koma cikin mota yashiga saboda har ga Allah abun da takeyi yafara isarsa duk da biyu yayi maya haka yayi mata saboda yaɓata masa rai kuma yayi mata haka saboda yasan hakanne kawai zaisa tadena maganganun datake yi idan baifito mata ta bayan gida ba zata shiga hankalin ta ba amma yanzu yasan ya kashe bakin magana dole tabi yanda suke so...., guri dadda tasamu tayi zaman dirshen aƙasa tare da nannaɗe kafafunta tayi zaman musulunci sai kuka hawayene kawai yake wanke kwaranyowa daga idon ta yana saukowa ta rasa bakin magana kuka kawai takeyi abun da bossay yayi mata ba ƙaramin tsaya mata arai yayi ba, da su shettima suma har zasu juya subarta agun sai kawai sukaji ta basu tausayi sameer ne ya tsugunnna agabanta tare da cewa kiyi haƙuri ta shi mushiga amma de ita bata nan tana cen gidan wajen Hajiya kamar yanda muka gaya miki idan kuma baki yarda damu ba ai zaki yarda da hajiya bari akira miki ita sai ki tambaye ta kiji  jikarki tana cikin ƙoshin lafiya babu abun da yasameta mude bazamu taɓa cutar da itaba amma tunda baki yarda ba yanzu kitashi ki koma gida ni da kaina zan kawo miki ita har gida nayi miki alƙawari daga nan zuwa dare zan kawota kinji yaƙarasa maganar yana kafe ta idanun sa, zunbur tayi ta miƙe tsaye tare da cewa ƙarya kuke wallahi ƙarya kuke har ni za azo ana tsarawa to aheer ɗin ku kunyi kaɗan inbiku yanda kuke so ni banason daɗin baki ai abu mafi masalaha anan shine kode akawo min ita yanzu nan ko kuma akaini inda take amma inbahaka ba kuma  ba gidan dazan koma ni kaɗai dan haka sai kusan yanda zakuyi dani idan kuma bahaka ba wallahi zan shiga in sanar da sarki idan shima ya kasa zan kaiku wajen ƴan sanda dole kufito da yanda kukayi da ita dan ni Wallahi jikina yabani baku da gaskiya akanta da abun da kukayi mata in kuma ƙaryane inganta mana yanzu tare daku ammade kace ai tana awancen gidan kuma ga motar ku indai da gaskene mushiga kawai mutafi cen ɗin, dafe kansa Sameer yayi azuciyar sa yana jinjina irin wannan taurin kan da kafiya akan abu to shidai baisan yanda zaiyi da itaba dan haka sai kawai yace to muje gidan ya faɗa mata tare da muƙewa kamar gaske gidan zaikaita, binsa ta shiga yi abaya tana tafiya ta na ƙara yin maganganu har sukaje wajen motar baya ta buɗe zata shiga sai taga ƴan biyu aciki dakatawa tayi sannan ta juyo ta kalli sameer dake gefen ta gira ya ɗage mata suna haɗa ido sannan yace kishiga kawai,,, ina shiga ina zan zauna ko akansu kake so in zauna Ammar ne yayi saurin buɗe ɗayan barin ya fito sanaan yace ta shiga bari shi yaƙarasa ciki aƙafa shiga tayi ta zauna tana ta faman cika tana batsewa tunda ta shiga take makawa bossay harara Sarai yaganta amma sai yanuna baima san tanayi ba yanzu Sameer ne yajasu zuwa cikin masarautar zuciyarsa cike da tarin damuwa yanzu kuma ina zaikaita da yaɗauketa wata zuciyar ce kawai tace kugaya mata gaskiyar abun dake faruwa wata zuciyar kuma tayi saurin kwaɓar sa akan karya kuskura Yahaya mata idan kwa tasani abun nata sai yafi haka dan haka gwara ma yakaita wajen momma ta riƙe mata ita ahanata fitowa sukuma sai su fito suci gaba da aikin su da wannan shawarar ta zuciyarsa ya samu kwarin gwiwar ƙarasawa cikin gidan... _______hamza Yaron nan wai me yake damun ka a yan kwanakin nan duk kabi kazama wani iri baba ne yakewa hamza magana dake kwance kan yayi ruf da ciki kamar me bacci, dagowa yayi tare da tashi zaune yana fuskantar baba sannan yace baba ciwon sone yake damuna kataimaka kaje kayo min bikon yarinyar nan wallahi ta shiga raina ta zauna amma duk sanda zamu hadu duk maganar da zan mata bata kula ni narasa ya zanyi da ita amma gaskiya ina sonta baba yazanyi da sonta, baba ne yayi dariya irin tasu ta manya sannan yace hamza kenan bakajin magana yanzu duk iya tsarin naka da dauriya irin taka amma kake son mace ta canzaka ai bai kamata kana jin shakkarta ba kawai kaje gadan gadan kasame ta ka gaya mata abun dake ranka idan taga zata amince dakai to idan kuma bata amince ba sai ka hakura ai ba awa mutum dole akan soyayya, baba wallahi masifaffiya ce kuma ina ganin kamar tainani tayi shiyasa taki kulani saboda na lura kamar ba baiwa bace saboda jikin ta bai nuna wata wahala ba ranar fa dana fara shan gabanta zan mata magana saura kiris ta kwashe ni da mari nayi saurin matsawa amma badan hakaba sai ta mareni saboda na tari gabanta kawai sannan ta gargadeni akan ko a hanya naganta kar nasake na kara yimata magana amma ni bana ji sonta ya rufe min ido duk sanda naganta sai na kuma yi mata magana baba wallahi kai kadai zaka iya taimakamin, dariya baba yayi sosai dan har hakuran sa saida suka fito cikin yar dariyar yace ni kuma dame zan iya taimaka maka da girmana ina ni ina yiwa yarinya magana akan soyayya wanna yakin kai kadai zakayi shi ba ruwana aciki, to wallahi baba indai baza ka taimakamin ba zansan yanda nayi na sace yarinyar nan in boye ta inta kallon ta ina yimata abubuwan da dole sai ta soni, "Au daman anayiwa mutum dole akan so taya zaka ta soka bayan ka saceta to wai ta inama zaka saceta kuma ka kaita ina idan kasace ta din? "kai baka jin tsoron akamaka wane irin hukun ci za ayi maka idan ka aikata hakan, Baba tsorofa kace ai wallahi cikin gidan nan babu wanda ya isa yasa inji tsoron sa kaf cikin gidan nan baba nifa ko fita nayi niya babu wanda ya isa ya hanani kawaide saboda inma nafita bansan inda zani ba kuma anan din ina samun yanda nake so amma bana zaman gidan nan saboda wani dan haka ka ajiye maganar tsoro ma agefe ni hamza bana tsoro saidai inbada tsoro, "eh baka jin tsoron mutane amma ai ga mace nan zata saka ka agaba tunda hartayi yunkurin marin ka ka kasa komai kaga kwa ai kasamu wanda kakejin tsoro din, Dan shafa kansa yayi sannan yace baba itama ai dan ina sonta ne shiyasa na daga mata kafa amma badan haka ba kaikasan bata isa ta mareni ba ko niyar da tayi ma sai na koya mata hankali amma dake sonta nake nakasa yi mata komai kuma ahaka naci gaba da son nata, yana gama maganar ya kara gyara zama sannan yace baba nifa taimako daya zaka min muje tare kawai sai kace mata kai mahaifinane kana neman min auren ta tayi maka magana da manyan ta nasan de kai babbane baza tayi maka abun da take yi min ba, daga nan nikuma nasamu dama sai in kuma tsarata har ta amince dani ka yarda baba, baba yace nidai ba inda zani da girmana kasa yarinya ta dena ganin mutun cina idan wani abun ya hada tunda tace bata sonka to bata sonka din ka hakura da ita kawai, "Wllahi baba bazan iya hakura da ita ba kawai kayi hakuri muje tare ni inaji ajikina idan mukaje tare Allah zata amin ce idan taga da gaske nake de sonta nake kuma auren ta sai tafi yarda dani,   "nifa ba inda zani kaje can kai kaɗai amma babu ruwana, baba wai yanzu haka zamuyi dakai tunda muke bantaɓa neman wata alfarma ba awajen ka amma yau ɗaya na nema amma kaƙi amincewa shikenan baba nagode, yana gama faɗar haka ya tashi yana niyar fita, yazata baba zai dakatar dashi amma yaga har yakai bakin ƙofa baba baice komai ba, sai kawai yadawo yashi ga yin murmushi tare da tsugunna wa agaban babba yafara roƙon sa akan dan Allah ya taimaka suje tare baba kuma yaƙi amincewa de da haka baiyi ƙasa agwiwa ba yaci gaba da lallaɓa baba da haka har yasamu yayi nasara baba yace zaije ammade shi bazaije can ɓangaren wajen Fulani ba saidai yasan duk yanda zaiyi idan yarinyar ta fito sai su haɗu amma shide bazaije can ba wannan matar ta gansa tasaka aci mutuncin sa shiyasa duk wani abu idan zaiyi yake taka tsantsan baya yarda su haɗa hanya da ita indai ba dole ba wani abun ya haɗasu ba shima bada son ransa ba shiyasa yanzuma yace bazai je can ba saidai ita yarinyar idan tafito sai su haɗu, Sosai hamza yayi murna da hakan ma yace ni baba ai indai zakayi mata magana to koma tayayane zakaganta yanzude bari in shirya sai mufita tare inyaso sai ka tsaya daga ɗan baya ni kuma zanje har inda take in taho da ita ko agaban wa take, Allah ya shirye ka nidai na matsu inji abun da yasa ka raina matar nan baka jin tsoron ta kwata kwata abun naka har mamaki yake ban wallahi gashi kullum abun naka gaba yake ba ya raguwa baka shakkar ta ko kaɗan,   "Hhhhh baba kenan kabari very soon zakaji komai ka kwantar da hankalin ka so nake ta kaini ƙarshe inci mutun cinta agaba kowa wallahi nifa ahakan ma ni nake haƙuri da abun da take min nake daga mata ƙafa amma akwai ranar da zan danneta tagane bata da wayo, "to Allah ya kyauta ni ai yanzu kafi ƙafina Hamza saidai kawai inci gaba da yi maka addu'a Allah ya shiryeka sannan kuma inci gaba da zuba ido inga ƙarshen wannan cika bakin naka, "Wallahi baba ba cika baki bane amma de shikenan kawai abar kaza cikin gashinta abar wannan maganar bari inji insake wanka saboda gudun raini kaima kuma baba sai canza kaya dan baza muje dakai ahaka ba, Kade san idan aka ganni da wasu kayan ba kayan aiki ba kuma ina yawo akwai matsala dan haka kabarni inke ahaka ni bana ƙarya kaide da kake da ƴancin canzawa sai kai ta canzawa amma nidai kabarni haka sai nafi jin daɗin fitar ma inkuma baka yarda shikenan sai inyi kwanciyata ince adawo lafiya, "A'a baza ayi haka bama shikenan muje ahaka ɗin nidai kam sai na canza yana gama faɗar haka yashige cikin bandakin, bai jima ba ya fito jakar kayan sa ya ɗauko yazaro wani yadi fari tass me laushi daga gani ma me tsadane ya ɗauko ya saka aka dauko hula itama aka saka yafito dos dashi kamar sabon ango, Shidai baba yana zaune ya zubawa sarautar Allah ido duk inda yayi sai yabisa da kallo har yagama shirya wa yaɗauko turare ya feshe jikin sa dashi take ɗakin ya kauraye da ƙamshi, saida yagama shirya wa tsaf sannan ya kalli baba "yace baba ya kaganni zan burgeta idan taganni, "Ah ba dole ba irin wannan kyau haka a ina kasamu kayan nan nidai tunda muke bantaɓa ganinsa ba, wata ƙayatacciyar dariya hamza yasake sannan yace lalle baba kana wasa dani iya haɗuwata da ita nasa aka ɗin ko min su baka gansuba sababbi ai yanzu nafara ɗinkuna agidan nan tunda na haɗu da ita kuma ai magana ta ƙare yanzude duk ba wannan ba baba kar kwalliya ta 5a fara samun mushkila taso mutafi, shide baba yau yana ganin abun mamaki da farko in akace masa Hamza zai iya yin irin waɗannan abubuwan bazai yarda sai gashi yanzu nema yake yafi ƙarfin tunanin sa, Miƙewa yayi yana riƙe baki ganin irin takun da hamza yake yana dariya suka fito daga ɗakin atare suka nufi hanyar can cikin masarauta saboda tsakanin su da ɓangaren masu gida da tazara dan haka dole sai baba yaƙara gaba sosai kafin yasamu inda zai tsaya ya jirasu, ________Azeema tana zaune gaban Fulani tana yi mata tausa zuwa yanzu tasaba da gidan amma akullum cikin kyalla ido take ko zata ga mahaifin ta amma shiru bata taɓa haɗuwa dashi ba dan hartafara fidda rai da ganin sa kuma yanzu ba koda yaushe take samun loƙacin kantaba ko da yaushe suna tare da fulani tana yi mata bauta wataran ma idan papa baya ɗakin kusan kwanan zaune take wajen yi mata bauta itace ɗauko wannan ɗauko wancen share nan goge nan duk wani aiki ya dawo gurin ta girkine kawai ba abarta tayi ba saboda ba ayarda da ita ba sosai baza a iya bata girki ba saboda tsaro, idan tagama wannan wahalar kuma loƙacin da takeso ta keɓe tayi waya da yaya saleem sai ɗayar me aikin da suke kwana ɗaki ɗaya sai ta hanata tun abun baya damunta har ta fara shiga damuwa ta fara tunanin ma kamar da gayya ake mata haka ba aso aganta ita kaɗai shiyasa gaba ɗaya yanzu ta canza gata nan sai ahankali goma da ashirinne suka haɗar mata ga rashin ganin mahaifin ta ga kewar su mama da take ita da saleem tana son kiran sa amma babu dama hakan ya gagara ga kuma masoyin ta datake ta son gani kuma shima basu ƙara haɗuwa ba zuwa yanzu tasan ba aljani bane saboda Fulani ma ta taɓa sakata take ta gyara part ɗin sa batare da ya sani ba amma kuma da taje ta gagga hotunan sa da hakan yaƙara tabbatar mata ba aljani bane kuma ɗan gidanne amma haɗuwar su tayi wuya, ji take kamar ta bar gidan amma ba dama dole taci gaba da zaman gidan, tana zaune awajen sukaji an turo ƙofa batare da anyi nocking ba fulani ce ta fara dagowa dan ganin me shigowa dan atunanin ma ko mutumin natane da yasaba shigowa kai tsaye amma sai taga akasin haka zuba masa ido tayi tundaga sama har ƙasa tana mamakin abun da ya shigo dashi kai tsaye batare da ambasa iznin shigowa ba ga kuma kalar shigar da take jikin sa to me yake nufi da hakan, shiru de tayi bata tanka masa ba tana jiran taga iya gudun ruwan sa, Azeema kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kanta daga gare sa itama de tayi mamakin ganin sa cikin irin wannan shigar bayan kuma tasan shima bawane agidan wata zuciyar ce ta shiga ce mata kikasani ko ba abun dakike tunani bane wataƙil ba ɗan aiki bane tunda har yayi irin wannan shigar gashi kuma ya shigo kansa tsaye batare da ko sallama ba kuma bataji Fulani tace mata komai ba dan haka tayi saurin kawar da tunanin sa taci gaba da abun da takeyi, ahankali ya shiga takawa ko takalmin ƙafar sa bai cire ba yake takawa zuwa inda suke yana zuwa gaban su batare da ya kalli inda fulani take ba yace minti biyar ina son magana dake in ba damuwa mu ɗan je waje ko ɗagowa batayi ba bare yasa ran amsawar ta duk da tasan da ita yake amma sai ta nuna batama san yanayi ba, fulani kam mamaki yagama kashe ta a zaune tana tunanin yaushe yaron nan ya riƙa irin haka yaushe rashin mutun cin nasa yakai haka abun har yakai yashigo mata guri batare da izinin taba kuma har cikin falon ta da takalmi kuma yazo yana magana da wata daban agaban ta lalle wannan yaron yagama riƙa yaukam yakaita ƙarshe sai ta nuna masa asalin kalarta abun nasa yayi yawa batasn meyasa ya rainataba haka amma yau zata sauke masa duk wani hauka da yake damun kansa duk abun da yake masa yawo akansa zata saita masa shi dan sai ya fuskanci mugun hukunci sai yayi nadamar sanin ta arayuwar sa sai tasa ya tsani kansa,   "magana nake dan Allah kizo ba daɗewa zakiyi ba zaku zaku gaisa ne da mahaifina shi yazo har inda kike idan zai ne ma min auren ki amma yace yana son ganin ki yanzu ɗan Allah ki taimaka kar ki watsamin ƙasa a ido kizo muje, da mamakin jin furucin sa ta ɗago ta kalle sa jin ya ambaci mahaifin sa to me wannan mutumin yake nufi da ita bata gama tunanin ba taji fulani ta kwace ƙafar ta daga hannun ta hakan yasa ta katse tunanin ta ta maida duban ta ga Fulani, cikin ɓacin rai fulani ta ɗaga hannu zata kifa masa mari amma sai akai rashin sa'a ya cafke hannun ta tare da nunata da yatsa yace kar ki kuskura hannun ki ya taɓa min fuska ba gurin ki nazo ba dan haka kar kishiga hurumin da ba naki ba ki tsaya amatsayin ki idan kuma bahaka ba hmmm yafaɗa yana girgiza kan sa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa irin ba mutun cin nan,   "tsugunna yayi gaban Azeema tare da kai ƙafafun sa ƙasa ya shiga roƙon ta da yi mata magiya kawar da kanta tayi gefe daga ƙarshe ma sai kawai ta miƙe tsaye zata bar wajen yayi saurin kamo hannun ta aikam tana juyowa ta sauke masa tafikan hannun ta afuskar sa tare da nuna shi da yatsa murya kamar zatayi kuka tace dan Allah ka rabu dani ka rufamin asiri nace bana sonka ko anaso dole ne  so ko sokake sai kajawo min wata masifar ina zaman zamana bandaɗe da zuwa gidan nan ba amma kabi ka uzzirawa rayuwata tunda nazo kake takura min dan Allah karabu dani haka, safe gurin da ta mare shi yayi tare da shafar wajen saidai yana shafi gurin sai yayiwa hannun sa kiss tare da sakin murmushi sannan yace daman idan budurwa ta mareka to marin soyayya ne dan haka ni banji zafi ba kuma duk abun da kike faɗa baidame ni ba dan haka kar ki zata wai zandena abun da nake zanci gaba daga nan har loƙacin da zaki fara sona nidai yanzu buƙata ta ɗayace kizo muje inkuma sai na ɗaukeki ne to zan iya ba abune me wuya ba agurina, Kai karamin marar kunya ɗan iska uban wa kake nunawa fistara anan gurin kai ɗan gidan uban waye da uban me kake taƙama uban wa ya tsaya maka da kake gadara dashi ɗan matsiyata matalauci tsintacce kai har kana da damanr da zakaringayin abun daka ga dama anan to wallahi kaci ƙarya ka kwana da yunwa yau sai naga uban wanda ya tsaya maka adoron duniyar nan sai na wulaƙanta ka sai masa ka kwashi kashin ka a ahannu, dariya ya shiga yi mata saida yayi me isarsa sannan ya shiga nunata da hannu yace saidai mu kwashi kashin mu tare nikuma bari ingaya miki wani albashir da baki sani ba daga ranar da kikayi ƙoƙarin aikata wanj mugun abun akaina nikuma ranar za tona miki asiri kowa sai yasan ko ke wacace acikin gidan nan kinsan kuma daga loƙacin zaman ki anan ya ƙare ko angaya miki ba wanda yasan abun da kika shirya to idan kin manta intuna miki kibi ahankali tsohuwa ina tausayin ranar da asirin ki zai tonu kuma inbakiyi wasaba ni da kaina zan tonashi abu shekara da shekaru da ba wanda yasani awa ɗaya tak ta isa insaka kowa yasani dan haka kibini ahankali kar kiƙara shiga sabgata kiyi rayuwar ki inyi tawa sai mu zauna lafiya ina fatan kin gane yauwa abu na ƙarshe ina so kisaka wannan yarinyar mutafi tare zan fita ina jiranta awaje wannan umarnine ba taimako nake nema ba idan kunne yaji jiki ya tsira yana kaiwa nan yayi gaba, wani mugun fitsari Fulani taji ya taho mata ga uban zufa datagama wanke ta loƙaci guda kwakwalwar ta tadena aiki ta rasa wane irin tunani zatayi kuma takasa furta koda da kalma ɗaya ce da lalibe tasamo kan kujera tayi saurin zama gudun karda ta faɗi har ta manta da gargaɗin sa na ƙarshe sai yanzu ya faɗo mata da sauri tayi wa Azeema nuni da ƙofa alamun taje batare da ta iya haɗa ido da itaba, Azeema da itama kanta yagama ɗaurewa da wannan lamarin da bata taɓa zaton sa ba ko a mafarki sai gashi a zahiri yau fulani ce gaba wani yaro yagama gaya mata magana son ransa ya kuma tafi abunsa duk ƙarfin izzarta da mulki amma ta rabu dashi to wannan wane irin sirri ne da bata son kowa yasani to shi ya akaima yasani no wonder taga yana abun da yaga dama ashe akwai abun da yasani game da ita shiyasa yake abu kansa tsaye, wani tunani ne ya faɗo mata hakan yasa ta sakin kayataccen murmushi ko me ta tuna oho mata, da sauri ta nufi hanyar fita saidai tundaga bakin ƙofa tahango yanda gari yayi baƙi alamun hadarine agarin sauri tayi ta ƙarasa fita wajen tana fita kwa tagansa abakin ƙofar kallon kallo suka shiga yima juna kafin daga bisani tayi saurin janye nata ido tare da sunkuyar da kai, yaf yaf yaf ruwa yafara saukowa suna dan gefe baya taɓasu da yagade kamar ruwa zai tsuge kuma yasan ma baba yatafi tunda ya dade agurin gashi kuma hadari ya haɗo yasan dole yanzu ya koma ɗaki baizai jira saba, dan haka kawai sai yace "kije ki koma ciki idan ruwa ya tsaya zan dawo yanzu baban nawa ya koma ɗaki saidai anjima zan ƙara kiranki, to kawai tace sannan ta juya ta koma ciki, shikuma cikin sauri zuciyarsa fal da farin ciki yasan ko banzade zai ringa samunta duk sanda yake so tunda gashi waccen matar ta korota dan yasan badan ita ba da bazata zoba amma yanzu shikenan yasamu mafaka kullum ita zaisa ta turota shi kuma zai dage har yajawo hankali ta gare sa murna kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha haka yake jin sa yana tafiya loƙaci zuwa loƙaci yana sakin murmushi ruwa na saukkowa kansa sai yaji hakan yaƙara sakashi cikin annushuwa....... **************************** cikin bacci taji wani irin sanyin na ratsata duƙunƙinewa waje ɗaya ta shiga yi tana karkarwar sanyi tun tanajin abun kamar amafarki har ta fara buɗe idon ta tsorone yakamata ganin dakin yayi duhu ga ruwan da yafara sauka da ƙarfi sosai hankalin ta yatashi tashi ga yin kuka ƙasa ƙasa datajide abun bana ƙare bane sai ta miƙe tsaye cikin laluɓe tafara tafiya hata isa gaban gadon ɗakin saboda zuwa loƙacin idonta ya washe tana ɗan iya ganin abubuwan ɗakin tunda ba dare bane hadarin da ya haɗo yasa ɗakin yin duhu, tsayawa tayi tana kallon sa yanda ta nannaɗe jikin sa a bargo yana baccin sa cikin kwanciyar hankali, rasa yanda zatayi tayi sanyi ne yake ratsata kuma bataso ta tasheshi daga bacci sai kawai ta zagaya ta ɗayan ɓangaren ta lallaɓa ta haye gadon kusa dashi sosai ta ƙara matsawa saboda tasamu ta rufa itama duk girman bargon ya kusa nannaɗe sa ajikin sa ɗan guri kaɗan yarage, sauran gurin ta kamo ta ɗaga shi ahankali sannan ta kwanta tare da juya masa baya abun rufar ne baigama rufe ta ba sai ta ƙara matsawa kusa dashi sosai har bombom ɗin ta na ɗan gogar jikin sa saida ta tabbatar ko ina ya rufu sanann ta rufe kanta tare da sauke ajiyar zuciya jin ɗumi yafara ratsata ai tuni ta ƙara lulawa duniyar bacci...........✍️✍️✍️ tofa wanga ɗiyafa zata jawowa kanta bala'i ke wa ga aike ki bakinsan yagama korankiba daga ɗakin amma shine harda hawar masa kan gado abun harda su cikin bargo🤔🤔🤔                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/2, 8:56 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️77&78 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️              "ruwa ake sosai kamar da bakin kwarya, yayin da bayin Allah biyun nan suke sharar baccin su hankali kwance tare da mannewa da juna batare da sanin su ba meer cikin bacci ya runggumo ta saboda duk atunanin sa filo ya rungume ita kuma batasan ma yana yiba baccin ta kawai take shara (daman kunsanta da bacci gashi kuma daman ta kwana batayi ba  ga lafiyayyen gado da bargo ga kuma dumin jikin sa ina ai tuni ta manta aduniyar da take hankali kwance take baccin hani'an sunkai wajen awa  daya suna bacci lakacin kuma ruwa yafara tsagaitawa, ruwa na gama daukewa meer yafara juyi alamun zai tashi hannun sa yadago da niyar cire abun rufar daga kansa amma sai yaji hannun yayi masa nauyi alamun kamar andanne masa hannun ahankali ya shiga bude idon sa yana budewa kwa ya saukesu akanta da sauri yasake ta daga rikon da yayi mata saida hannu daya yasamu damar janyewa dayan kuma tana kai ta danne masa tsoro ne yakamasa lokaci guda jin mutum akusa dashi dan baigama ganin fuskar ko wacece ba kuma shi harga Allah yama manta da babun ta shiyasa bai kawota aransa, tunani ya shiga yi waye akusa dashi rashin me basa amsa da ɗayan hannun ya ɗaga bargo ya buɗe su gaba ɗaya tsulum idonsa ya sauka akan fuskarta daman facing ɗin juna suke yi zaro dara daran idon sa yayi akan ta yana mamakin ganin ta kwance akusa dashi daman duk gargaɗin da yayi mata bataji ba bayan yace kar yatashi yaganta agidan ma gada ɗaya amma shine abunna ta har kan gadon sa kuma kusa dashi akan hannun sa wannan wacce irin yarinya ya haɗu da ita  anya ba mayya bace ko aljana daga haɗuwa tabi ta nace masa ta maƙale masa yau ya ɗebowa kansa bala'i,   da ƙarfi yaja hannun sa da take kai zai janye amma ga mamakin sa sai kawai yaga ta riƙo hannun da sauri tare da kwantar da kanta akai taci gaba da baccin ta mamaki ne ya kuma cikashi dan atunanin sa tana sane take masa haka, tunanin abun da zai mata ya huce ya shiga yi dan haushin ta da yake ji yagama cika da taƙaicin ta, meƙewa tsaye yayi tare da zare hannun sa da ƙarfi yana zarewa yaje wajen kayan sa cajar wayarsa ya ɗauko ya nannaɗeta yadawo inda take kwance sannan yaye bargon daga jikin ta yana yayewa yaga ta wani haɗe jikin ta waje ɗaya alamun sanyi take ji amma duk da haka bai tausaya mata ba ya shiga tsula mata ajiki da iya ƙarfin sa, amugun razane ta miƙe zaune tare da fashewa da kuka me ƙarfi  baidaina ba kuma yaci gaba da zuba mata wayar cazar ta ko ina,   sosai ta shiga rera masa kuka tana jawo bargon dan ta rufe jikin ta amma sa yasa ɗayan hannun ya janye yaci gaba saida ya tabbatar da ta daku sannan yace get out of my room before in canza miki kammani bance kar na tashi naganki acikin gidan nan ba shine harda hawar min kan gado uban wa yabaki izinin kwanciya kusa dani ya faɗa yana daka mata tsawa memakon ta tashin saita ƙara matsawa kusa da fuskar gadon tana kuka tana girgiza masa kai,    "baza ki tashi kifitaba ina miki magana ƙin tashin tayi ta ƙara mannewa da bangon tana karkarwar jiki, girgiza kansa yayi sannan yace wannan baki ɗaku bane jefar da cazar yayi yaje ya ɗauko ballet ɗin wandaon sa ya tunkaro ta tunda tagansa ta saki wani kukan me sauti tashiga basa haƙuri amma da tagade da gaske dukan nata zaiyi da sauri ta sauka daga kan gadon ta nufi hanyar ƙofa tana zuwa wajen ƙofar cikin rashin sa'a ta zame agun ta faɗi wata ra zananniyar ƙara tasaki sakamakon buguwar da ƙashin ƙafarta yayi da jikin ƙofar, dafe kansa yayi tare da ajiye ballet akan gado ya nufo inda take tsayawa yayi akanta tare da buɗe ƙofar yace fita ihu gagara yi tana cewa wayyo ƙafata wayyo ƙafata ƙafata zata cire wayyo Allah na dadda ta fadada ƙafata, tsugunnawa yayi zai fara janta ya fita da ita saiga Ummy ta shigo da saurin ta ganin su ahaka yasa tayi turus ta tsaya tana binsu da kallo dakatawa yayi da niyar fitar da ita ɗin ya miƙe tsaye yana kallon ummyn tasa, da mamaki ummy tace hayatee me nake gani mace aɗakin ka me yafaru waya shigo da ita daga ina take tun ɗazu nakejin kukan mace na ɗauka ko maƙotane Saida nafito najide anan samane me ya haɗaka da ita me kuma kayi mata? ummy wacce tambaya kike so in amsa miki kinbi sai jero min tambayoyi kike, hararar sa tayi sannan tace duka zaka bani tana masa magana amma hankalin ta nakan Ameesha ganin de yarinyar da gaske take kuka kuma gashi ta riƙe ƙafarta sai tabawa ummy tausayi cike da tausayawa ummy ta tsugunna agaban tana yi mata sannu tare da kamo ƙafar taba ɗagata kwa taga ƙafar har ta kunbura sunnu tashiga yi mata sannan tace subhanallah garin ya akai haka ta faru ƙafar ai har tayi tsami gashi ta kunbua,   cikin kuka Ameesha tace" faɗuwa nayi na bugu da ƙofar nan,   "Ayya sorry amma garin ya akai kika faɗi har kikajawowa kanki wannan abun, shiru tayi bata amsaba hakan yasa tagane meer ne sanadin faduwar tata waƙil biyo ta yayi da gudu, amma de yanzu ba wannan loƙacin tambayar tata kamata yayi tafara bawa yarinyar taimako kafin kuma shi yaga mata inda yasamo ta,ajiye tunanin tayi ta maida dubanta ga Ameesha sannan tace bari ayi miki ruwan zafi zaki iya tashi? kai ta girgiza mata alamar a'a, miƙewa ummy tayi sannan ta dubesa duk yabi ya wani haɗe rai ya haɗe girar sama da ƙasa yana ciccin magani, sai ka ɗaukota kafito da ita dan bana raba ɗayan biyun kaine sanadin faduwar tata kayi sauri ka sauko da ita bari in ɗora ruwan ɗumin tana faɗa tafara niyar fita daga ɗakin, Meer yace ummy ki tafi da ita kawai ni bazan iya daukan ta ba bana son ganin ta dan Allah ta tafi tabar gidan nan kar ta bari in sauko inganta agidan nan wallahi sai kusa ɓaɓɓallata, da mamakin furucin sa ma ummy ta tsaya tana kallon sa saida yagama sannan tace kamar ya ba fahimci maganar kaba ince bakai ka kawota kuma shine kake wa mutane wani zancen da ban dan bangane masa ba waye ya shigo da ita gidan, cikin ɗan turo baki kamar wani ƙaramin yaro yace ummy nifa bansan taba nima ɗazu ne kawai dana  ɗan fita in zagaya garin na haɗu da ita yake ta tsokano ƴan iska sun biyo ta shine fa na taimaketa daganan kuma tanace min saida ta biyo ni har gida bayan mun shigo na ce mata tazo wajen ku tagaya muku amma shine da yake ita mayyace ina farkawa daga bacci naganta akusa dani shine......sai kuma yayi shiru., ummy tace shine kayi mata me ka daketa kuma ka biyo ta ko haka kake so kace mun ba, kai me yasa baka da tausayi ban hanaka taba mace ba me yasa baka dauki mace da daraja ba yanzu kamar wannan yarinyar ma yar karama me tasani kamata yayi ai kajata ajiki kaji matsalarta tunda har kaganta cikin wannan halin ai kasan de ba dadi ne yafito da ita daga gida ba kasani ma ko bata da iyayen shiyasa ta nace maka tabiyo ka tunda taga ka taimaketa amma shine zakazo kasaka ta adaki ka daketa kuma kabiyota gashinan yanzu kaji mata ciwo watil kashin ta ya goce yar karamar yarinya itama sai ka nuna mata halin ka wannan ai abar a tausayawa ce amma kai bansan me mata sukayi maka ba da ka tsane su dan Allah na rokeka da Allah karage wannan halin karin ga jin tausayin mutane ko ba komai wannan yarinya ce inma zaka nuna tsanar taka ga wasu amma bai kamata ace har yara zaka ringayiwa haka ba ka can za hali dan Allah wallahi banason ganin kana irin wadannnan abubuwan bana jin dadi daman nice ma me biye maka kasan mahaifinka baya son irin wadannan abubuwan dan haka wallahi tun kan yafito yaji abun da ka aikata kayi sauri ka dauko ta muje agasa mata kafar ashafa mata man zafi idan kwa ba hakaba kasan halin sa sarai ni da kaina zanje in sanar dashi abun da kayi inbanda abunka ma kai da kayi aikin lada ka ceceta daga gurin su ai kamata yayi ka karasa ladan ka ni ko ni ka kawowa ita ai zamu kula da ita sannan muji daga inda take amma kazo ka lalata komai dole ma sai taji sauki kafin mahaifin ka yaganta dan in yaga kafarta haka kuma yaji kaine sila ranka sai ya baci,   ka dauko ta muje kamar ya fasa ihu haka yake ji ji yayi kaf duniya ba macen da yafi tsana irin wannan yarinyar gashi sanadin ta tasa mahaifiyar sa nayimasa fada shikuna aduniya inda abun da ya tsana shine fada ya tsani ayi masa fada ko kadan, yasan duk abun da mahaifiyar sa ta fada gaskiyane hakan zai iya faruwa indai abu yaji labari to shima fadan zaiyi masa shiyasa bashiri badan yaso ba yana bata rai yasa hannu daya ya dagota, ummy ta kalle sa tace oh yanzu kuma karya mata hannu zakayi to Allah baka sa'a tana kaiwa nan tayi ficewar ta daga dakin, tsaki ya doka tare da janta zai fita da ita Ameesha ta saki kara saboda bazata iya taka kafar ta ba shikuma ya tsayar da ita da kafafun ta saboda tsabar mugun ta yasani sairai zataji zafi saboda yaga kunburin da kafar tayi amma ya maze yake niyar janta jin tasaki kara yasa ya galla mata harara murya kasa kasa yace wallahi na kara jin kin daga min murya sai shakeki anan kin mutu banza mayya kawai, Shiru tayi bata kara buda baki ba, shikuma ahaka yafara janta tana dan dingishi tana dafa bango tana cije baki take taka kafar da kyar tana jin azabar da take mata amma sai hawaye kawai yake fitowa ba karar kuka saboda zuwa yanzu amugun tsorace take dashi, gani take idan tayi yunkurin daga muryar zai kashetan kamar yanda yace dan haka tayi shiru tana karbar azabar da takeji, ahaka suka fito har suka wuce falo suka fito waje suka fara taka bene saida yaga sun kusa saukowa falon gudun kada ummy taga ayanda suka fita yasa ya dauke ta ya karaso falon da ita saida ya duba ko ina yaga ummy bata falon sannan ya dire ta da karfi yanda yasan zata kuma bige kafar haka yayi mata ya tsayar da ita da kafafun ta kuma yasake ta, kasa kasa tasaki kuka tare da saurin zama kan kujerar da take kusa da ita tana hawaye, hada ido sukayi da shi ya galla mata harara yana girgiza kai irin sai naci uwarki, da sauri ta sauke kanta kasa, ganin ta sunkuyar da kanta ya kuma duba yaga har yanzu ummy bata fito falon ba yasa ya matsa kusa da ita kamar abun arziki zaiyi sai kawai yasamu daidai gurin da ya kunbura yataka da kafarsa harda cije baki sannan ya dagata take ta saki wani kukan me sauti tanayi yamake mata bakin yace wallahi idan kibari taji sai na balla miki dayar kafar shifa haushin ta yake ji so yake yaga kawai yayi mata duk abun da zai mata da zasa taji zafi tayi da nasanin biyoshi shi yake so yayi mata, da sauri ta kara hadiye kukan, amma saboda rashin imani irin nasa sai ya kara daga kafar zai takata caraf akan idon ummy kafin yakai yajiyo muryar ta, "au daman rashin tausayin naka har yakai nan bansani ba yaushe ka kara zama haka ta fada tana karasowa gurin kallon ta yayi cikin hade rai yace ummy me kuma nakara yi bakince in kawota ba kuma gata nan ko kinga nakara yimata wani abun, "bakayi ba amma ai kana shirn yi din ko yanzu ba taka ta naga kana kokarin yiba saboda tsabar mugunta ko to ka kyauta kayi daidai, cike da jin kunyar kamasan da datayi yace nifa ba haka zan mata ba kawaide idon kine yagane miki haka yana gama fada ya juya zai bar wajen tace dawo kazo ka fita kasamo mata maganin zafi, ummy ina dashi ai shi zanje in dauko ko kuma idan kingama gasa mata kawai ki kawota sai inshafa mata yayi maganar ahankali kamar gaske, da dan mamaki ummy ta kalle sa amma ganin fuskar sa ba wata alama na rashin gaskiya sai taji dadi ta dauka yafara saukowa ne ya dauki fadan da tayj masa saikawai tace to shikenan bari in gasa mata amma de kasan bazan iya daukan taba kabari kawai ingama gasa mata sai kuje tare ka dauketa ka shafa mata nikuma sai inje in hado mata abun da zataci, dawowa yayi falon ya samu kujera ya zauna yace to ummy ba komai gama matan sai mutafi, nan ummy ta shiga gasa mata kafar ita kuma tana kuka dan da kyar ma tabari saida taji meer yace zai karba yagasa mata tasan halin sa sarai shiyasa tayj saurin tsayawa ummy ta fara gasa mata tun tana kuka har tafara yin shiru saboda taji dadin gashin ya ratsata taji damadaman kafar, ana gamawa ummy tace yazo ya dauke ta tashi yayi kamar na kirki ya dauke ta yafara hawa saman benen da ita, suna tafiya yana zabga mata harara ta gefen ido itade tunda ta fahimci hararar ta yake ta dauke kanta daga kansa ta kawar gefe, saida ummy taga hawansu sanna ta bar falon ta nufi kitchen din dan ganin abun da zata dafa musu gaba dayan su saboda suma basu karya ba duk suna bacci, yana shiga falon ya direta akasa yanzu bataji zafi ba kamar dazu dan haka kawai ta dafa bango ta tsaya tare da dan dage kafar me ciwon,, gaba yayi abun sa batare da ya kulata ba ganin hakan yasa tafara binsa abaya har suka shiga dakin kan capet ya nuna mata yace ta zauna, zama tayi tana tunanin Allah yasa kar yayi mata wata mugun tar wajen shafa mata dan bata yarda dashi ba wataƙil yayi hakane kawai dan yana gaban mahaifiyar sa, tana zaune agun yaje ya ɗauko mayuka biyu ya dawo daga ɗan nesa da ita ya zauna sannan yace ta miƙar da ƙafar kamar abun arziƙi ta miƙar da ƙafar har ta ƙarasa inda yake aboniki ya yafara buɗewa sai ya laƙato ɗan kaɗan ya shafa shi ajikin murfin ya miƙa mata hannu tasa ta karɓa tana jiran jin me zaice sai yace ki shafashi a hannun ki kamar mai haka ta lakace shi daga murfin tasaka atafin hannun ta tafara murtsikawa da tagama sai ta ɗago ta kalle sa cikin ƙara haɗe rai baice mata komai ba sai ya ɗaoko wani kwalban na wani mai kuma ba man zafi bane kamar ma nml man shafawa shi ya lakato wajen kwatan roban ya dan ɓara mata akan ƙarfar sannan cike da mugun ta yafara danna mata ƙafar take ta saki ƙara bai saurareta ba harda cije baki wajen ƙara dannawa gashi ya riƙe ƙafar da ɗayan hannun ba dama ta kwace, sosai ta shiga yin kuka tana kwace kwace zata kwace ƙafar amma takasa hawaye duk yagama wanke mata fuska harda majina gaba ɗaya fuskar tayi wani gaje gaje da ita, batare da yasaki ƙafar ba ya ɗago kansa ya dubi yanda fuskar ta tayi, wani daɗi yaji aransa daman haka yakeso yagani dan haka sai yace idan kina so insakar miki ƙafa to kifara saka hannun ki ki goge hawayen nan kar inga ko ɗigon danshi akai, Allah sarki baiwar Allah jin hakan yasa da sauri tashiga goge hawayen ta da hannun ta manta ta taɓa aboniki shikuma yana sane daman yayi mata haka shiyasa yafara bata ta shafa ahannu sannan yace ta goge fuskar ta dashi saboda idan ta goge hawayen man jiki zai taɓamata fuska gaba ɗaya , take tafara jin zafin abonikin a idon ta kif kifta idon tafara yi tun tana daurewa har taji ina abun yafi ƙarfin ta fuskar ta gaba ɗaya ta ɗauki zafi, yana ganin haka ya tashi yaje ya rufe ƙofar harda saka key ajiki sannan ya koma kan kujera yayi zaman sa yana jinta tana kuka saima ya ɗauko wayar sa ya toshe kunnuwansa yana danne danne wayar sa, ita kuwa idon ma ya rufe gaba ɗaya ga zafi ga hawaye sai abun ya haɗu ya caɓe mata ga ƙafar sai zugi take mata kamar zata cire haka take ji, ji tayi ana buga ƙofar amma ba halin tashi ta buɗe saboda tanajin sa loƙacin da yasaka key ajiki kuma yama cire key ɗin daga jiki, Ummy da tagaji da bugawa gafara kiran sunan sa hayatee ka buɗe ƙofar mana tana magana tana cigaba da bubbugawa amma baisan ma tanayi ba, loƙaci zuwa liƙaci de yana ɗagowa ya dubeta yaga yanda take kuka sai ya kuma juyar da kansa ransa fari tass haka yake ji yasan zuwa yanzu zafin abun yafara barin ta saboda ɗaki akwai Ac, amma duk da haka ba yanzu zai kulata ba sai tagama gajiya dan kanta ta tashi tace zata fita sannan yayi mata gargaɗin idan tafaɗawa ummy wani abun sai yayi maganin ta, ummy da tagaji da bugu hankalin ta gaba ɗaya yatashi tayi saurin ajiye try din da ta ɗauko abinci agefan ƙofar ta ajiye sannan tayi sauri ta sauka ta ɗauko wayar ta ta dawo bakin ƙofar sannan tadanna masa kira yana zaune yaga kiran ta ya shigo wayar fara tunanin abun da zaice mata ya shigayi bai ɗaga ba har kiran ga katse yana katsewa sai kawai ya tashi yaje ya buɗe ƙofar yana buɗewa ummy ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa me yafaru ina ta bugu baka buɗe ba na daɗe anan amma bakuji ba lafiya de ko? tayi maganar tana shigowa ciki gurin Ameesha taje da sauri tana yi mata sannu kallon fuskar ta tayi taga duk tayi jaa, tana ɗagowa tunkan tayi magana meer yayi saurin cewa ina cikin shafa matane taje ta taɓa gurin bayan kuma nagama shine ta taɓa fuskarta da hannun tun ɗazu nake bata haƙuri taƙi yin shiru, sosai Ameesha tayi mamakin abun da yace amma bayanda zatayi bazata iya ƙaryatasa ba shiyasa tayi shiru kawai tana faman shashsheƙar kuka tare da sauke ajiyar zuciya akai akai, kallon sa ummy tayi kamar de bata yarda da zancen sa ba amma sai kawai tace ayya sorry kiyi haƙuri ko awanke miki fuskar ko zaki fi jin dama dama, kai ta ɗaga mata alamar eh, to zaki iya takawa nan ma kai ta ɗaga mata amma aranta tasan bazata iyaba amma bataso tace bazata iyaba ace ya ɗauke ta daga nan kuma yasamu damar da zai ƙara yi mata wata mugun tar, da taimakon ummy ta miƙe tsaye amma tana miƙewa sai tayi saurin riƙe ummy saboda azabar da taji tama fi ta koyaushe, sannu ummy tayi mata sannan tace hayatee kaga bazata iyaba ɗauko ta kawai muje wannan ai saidai ma ayi mata wanka dan naga alamar duka jikin tama ba daɗi yake mata ba duk yayi tsami muje agasata da ruwan zafi sai tafi jin daɗin jikin ta, tabb Ameesha ba ƙaramin tsorata tayi ba jin ance wai za ayi mata wanka da girman ta za ayi mata wanka duk da itama tana mugun buƙatar wankan amma bazata taɓa yarda ayi mata ba gwara tace gaba da zama ahaka, kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu dan baƙin ciki haka yake ji shifa ya tsani ya haɗa jiki da ita bayanda ya iya dole ya sunkuceta cikin fushi yakaita banɗakin yana gama ayyana abun da zai kuma yi mata dan wallahi tunda ta shigo rayuwar sa ba shi kaɗai zai shiga uku ba itama ta shiga uku duk sanda zata sa ace yayi mata wani abu to sai yarama ta wani ɓangaren, ummy ce taje ta haɗa mata ruwan zafi me ɗumi sannan da taimakon ta cire kayan ta sai Ummy ta haɗa mata komai sannan tace to tayi bari ta bata waje, ajiyar zuciya ta sauke ganin ita zatayi wankan ta ba yimata za ayi ba dan haka tashiga yin wanka daman abuƙace take dashi, Ummy na fitowa meer ya dubeta cike da damuwa da ta arota yanzu yanzzunnan yace ummy ya kuka fito kika barta bafa zata iyayi da kanta ba ko inje inyi mata kinga ƙafarta da ciwo ba sauƙi tayi ba bazara iya ba, "ai na haɗa mata komai zata iya yanzu kawai kajira kai banda abubkama inakai inayiwa mace wanka kana ƙatoto dakai wannan ai baidace ba kade tsaya anan idan ta gama sai kaje ka fito da ita nasan zatayi magana ka zauna bari ni kuma inje in samo mata abun da zata saka idan tafito, To kawai yace bahaka yaso ba yaso ace yaje yayi mata da taga mugunta shikaɗai ya tana abun da zai yi mata sai kuma aka hanasa kodan yanzun ma ai bata ɓaci ba tunda ummy ɗin ta fita bari kawai yaje ya tarfata a banɗakin, yana gama ayyana hakan ya nufi ban ɗakin kansa tsaye shi anasa wajen baya tunani wai ai bai kamata ta shiga yaganta ayanayin da baidace ba saboda kallon yarinya yake mata(hmm yarinya ko) san haka bayasa wai zaiganta tsirara shi ba wannanne aransa ba burinsa kawai yaje yaƙara sakata kuka yafito, ahankali ya shiga tura ƙofar har yagama budeta gaba ɗaya, bataji buɗe ƙofa ba bataga shigowar saba saboda wanke fuska take ƙarasawa yayi gaban ta tare da binta da wani banzan kallo tundaga sama har ƙasa da ƙirjinta ya zubawa ido yana kallo baya ko ƙiftawa, ɗauraye fuskar ta tayi bude idon da zatayi tayi karo da gardin namiji agaban ta loƙacin da ta buɗe ido shikuma loƙacin ya ɗago kansa haɗa ido sukayi dashi, atsorace ta buɗe baki zata saki ƙara yayi saurin saka hannun sa ya toshe mata baki gudan kada ƙarar ta fito ummy taji ta taho ɗakin...........✍️✍️✍️                              💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/3, 7:40 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️79&80 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️              __________*Sam*__________ suna shiga part ɗin mommo aka fara ruwannan gaba ɗayan su afalo suka baje dadda sai faman baza ido take acikin falon jira take kawai ruwan ya tsaya dan har yanzu tana kan bakarta saitaje har gaban sarki ta sanar dashi abun dake faruwa dan bata yarda dasu ba har yanzu, suna shiga daman twins suka wuce gurin momma sukaje mata da labarin duk abun da yafaru har da labarin dadda saida suka bata hankalin tane ya ƙara tashi ta shiga damuwa, suna zaune ita da su Amran sameer shima ya shigo ɗakin momma ɗin guri ya samu ya zauna kusa da ita tunkan yayi maganar ma momma tafara yi masa,    " yanzu su hamra suke ban labari ina matar take yanzu momma ta faɗa tana kallon sam ɗan numfasawa yayi sannan yace momma tana falo nasan ruwannan ne yasatayi shiru da tuni kinjiyo maganar ta ma ai momma bansan yazanyi da matar nan ba gashi kuma inda mukaje babu wani tsayayyen labari abu guda de da muka sani shine motar da Amra ta gani tana binsu wai ɗazu taga fitar daga cikin gidan nan,   "au da gaske ne ai tagagaya min na ƙaryata tata tun ɗazu da safe na ɗauka ai shirmen tane shiyasa banɗauki maganar tata serious ba, "mumade bamu da tabbas ammade so muke idan ruwan nan ya tsaya muje musami me gadin da maganar mu tuntuɓeshi muji, "gaskiya de yakamata agwada ko Allah zaisa yasan suwaye kaga abunma zaizo da sauƙi wajen gano su waye amma fa abun yaban mamaki ya za ayi ace anɗauke ta acan waje kuma ace anga motar da ta sace tan agidan nan anya ba shirmen Amra bane, "ba wani shirme momma da gaske ne muma duk abun da ya ɗaure mana kai kenan saboda jiya da daddare ɗayan abokin mu ya tsinci abun hannun ta acan wajen bayan parking space, "abun hannun tafa kace acikin nan gidan kuma ba wajen sukaje ba ta jefar dashi ga su Amra nan ki tambaye su kiji sunce su basuje ba gurin, da sunje ma ai da zaki sani, "cike da al'ajabi momma tace tofa wata sabuwa amma abun akwai ban mamaki ah dole a tambayi me gadi dole ma motar ce tunda karde an tsinci abun hannun to babu shakka motar da Amra yagani itace, ,"nima shiyasa na yarda da hakan amma daman da bazan taɓa ɗaukan zancen ba amma yanzu dole na yarda, ,"Momma to yanzu de yazanyi da matar cen dan wallahi idan tasan yarinyar nan ta ɓata to wallahi gaba ɗayan mu sai ranmu ya ɓaci dan wasan bazata taɓa haƙura ba sai ta ɗaga mana hankali gashi kuma munshigo da ita bansan yanda zamuyi da itaba yaƙarasa maganar cike da damuwa a fuskar sa, kamo hannu sa momma tayi sannan tace kar kadamu kanka yanzu de kaje har ƙasa ka hawo da ita nikuma duk wani abu da zaisa hankalin yakauda ga gurin ku ku kuma kuje kuyi aikin gabanku daga yau zuwa gobe ku tabbatar kunyi ƙoƙarin kun nemota kafin ta ankare inyaso koda ansamu waɗanda suka ɗauke ta ɗin inyaso sai ayi mata bayani daga baya ina ganin hakanne kawai masalaha amma inba nan tazo ba bazata taɓa barinku ku fita daga nanba sai ta biku idan kuma tabiku ba yanda za ayi kuyi maganar agabanta, eh hakan kwa za ayi bari in kira miki ita Allah yasanya tazi ṣin dan waccen matar bata da kirkir idan taso ga masifa, momma tayi murmushi sannan tace batsohuwa bace ai daman duk wani tsoho haka yake da faɗa ɗaiɗai kune masu sauƙin kai nasande duk tijararta bata kai gwaggwa ba, "kai momma wallahi zasu iya yin kai ɗaya ammade ai zaki zauna da ita yanzu da kanki zaki bada labari, "ai na saba da fitinar gwaggwo nasan wannan bazata ban wata wahalaba, "hakade kike gani momma amma bari inje in kawo miki ita sai ku zauna yauwa hamra ki ince ma Amra nasanki da surutu kamar aku to ayau nake son surutun nan yayi aiki kusaka ta agaba kuyi ta bata labari ku cikata da hira ku mantar da ita abun dake damun ta kun gane yafaɗa yana kafe su da ido duk amsa masa sukayi da to,  sannan shikuma yafita dagaɗakin, yana zuwa falo yaga dadda a tsaye wai ai ruwa ya tsaya ita zata fita akaita wajen sarki haƙuri suka bata da cewa ai sarki yanzu yana wajen iyalin sa baya fada kuma indai yana tare da iyalen sa ba aganin sa har sai yafito saidai tajira zuwa anjima idan ya fito sai akaita har gabansa da wannan batun ta yarda ta koma ta zauna, tana zama kuma tace to yaushe zamu tafi can gidan ɗin sukace mata anjima kaɗan yaude duk yanda dadda take so binta suke sau da ƙafa suna mata komai cikin lallami da lamana gudun karta ƙara tubure musu su rasa yanda zasuyi da ita, Amma banda bossay saboda har yanzu da guntun haushin ta aransa itama kuma ta lura da hakan amma bata kulasa itama ta share shi "cikin sanyin murya Sameer yace tazo suje wajen mahaifiyar sa su gaisa batayi wata wata ba kuwa ta tashi suka tafi ɗakin momma yakaita suna shiga momma ta tashi taje ta rungume ta tana faman sakin murmushin dole sannan faran faran ta shiga gaida ita aikwa dadda taji daɗin yanda momma tayi mata dan haka itama tasaki fuska wajen amsa mata gaisuwar sannan momma takamata ta zaunar da ita kan gado, Sameer ne ya kalli su hamra da ido yayi musu alamar suje kusa da ita da sauri Amra ta fara tashi daga kan kujerar  da suke tana zuwa ta faɗa kan dadda tana dariya sannan ta shiga gaida ita tana cewa ai kema kaka tace tunda ke kakar Ameesha ce to Nima daga yanzu kin zama kakata amma fa sai kinyi haƙuri dani dan bana jin magana zan ta tsokanar ki har sai kingaji dani da halina dan haka nakewa gwaggwo na kema kuma haka zan ringayi miki kinji tafaɗa tana jawa dadda kumatu, da sauri dadda ta dafe fuskar ta tace ke ni kuma bazan ɗauki hakan ba ɗaga nima wallahi da kwarina bazan bari ki nakasani  ba kinji da ƴa to yaseen ɗagani na ba gwaggo bace idan kina mata ta ƙyaleki to ni duka nake bana wasa da yara, dan haka maza ki ɗagani kar na mazgeki anan dan dukana zafi gare sa zaki iya yin bunga dariya Amra tayi ba ita kaɗai bama su momma saida suka ɗan dara jin yanda take magana da iya gaskiyar ta ta kuma haɗe rai amma hakan baisa Amra ta ɗagataba cikin dariyar tace dadda meye kuma bunga, mutuwa mutuwa itace bunga idan kuma kinso kiyi to kici gaba da abun da kike min nikuma zansa kiyi bunga ɗaga ni nace, maƙalƙaleta Amra ta ƙarayi tana dariya tace Allah kam bazan tashiba sai kinsa nayi bunga ɗin indai kinga na ɗagaki to nayi bunga ta ƙarasa maganar tana jan gashin kanta da yaɗan leƙo waje, da sauri dadda ta riƙe mata hannu tace Allah kam yarinyar nan da sauranki yanzu gashin zaki cire min dan kina baƙin cikin na fiki ko wai duk kuna ganin ta abun da take min amma bamai hanata to wallahi kar kuganni baƙuwa danni ban iya baƙunta ba zan cire kunya in zane muku yarinya tunda kuna kallon ta kun kasa hanata wannan ai rashin mutun cine, momma tayi yar dariya tace wayake shiga tsakanin jika da kaka ai idan kaga suna abu ido ake zuba musu idan ka shigama kai zakaji kunya dan haka ke da ita babu ruwan mu aciki, gashin Amra ta ƙara jawowa wanda na yanzu yafi na da zafi da sauri dadda itama ta cire hular dake kan Amra taja mata itama da ƙarfi to fa uwar tsokana saigashi tafara hawaye saboda ta tsani ataɓa mata kai shiyasama ko kitso batayi kanta sai yafi kwana nawa a ɗaure sai anyi da ƙyar wataran ma yake samun ataje shi sai gashi dadda ta kama kan da iya ƙarfin ta taja mata shi,   tun tana kwalla har tafara fitar da kuka me sauti sannan dadda ta sakar mata kan tace ashe ba daɗi kai ai ba fin kai yayi ba ni da kika jamin kan robane dani da bazan ji zafin ba to kaɗan ma kika gani ɗagani,   " cikin turo baki Amra ta sauka daga kan dadda tana ciccin magani ita adole tayi fushi da ita, Hamra ce tayi saurin riƙe Amra tace haba sister yaza ayi kibari tsohuwa tayi galaba akan ki har tasaki kuka kuma kika rabu da ita wallahi idan nice bazan yarda ba kije ki rama kar ki rabu da ita, ƙaton filo dadda ta ɗauka ta makawa hamra tace to mazigiya ina ganinki tun ɗazu shiru shiru ashe kema baki da mutunci to ke kizo ki rama mataɗin kiga yanda zanyi dake kema bana gaya mata dukan yara nake ba bata yarda ba ni wallahi ma har tasa kaina yafara ciwo kawai daga zuwa sai afara cin zalina to kwa bawanda zan ɗagawa ƙafa, dariya sukayi mata gaba ɗayan su sameer de da yaga abun nasu ba ƙarewa zaiyi ba sai yayi ficewar sa yana jin daɗin hakan da sukeyi har ya fitama dadda bataga fitar sa ba, share hawayen ta Amra tayi tare da ƙara juyawa kan dadda da sauri tana zuwa ta sauke mayafin dake kanta ta tare da ɗan kwalin daman dadda batayi kitso ba Ammi ce keyi mata kuma ta tsife shi jiya yau za ayi mata kitson kuma saiga abun da yafaru hakanne yasa kanta yakasance a tsefe, Amra naganin gashin ta a tsefe batasan loƙacin da tasaki dariyar mugun taba kafin dadda tayi wani yunƙuri har ta danna hannuwan ta akan ta fara ya mutsa mata gashi tare da jansa da ƙarfi duk yanda dadda taso ta kwaci kanta taka sa idon ta har ya kaɗa yayi ja saida Amra ta tabbatar da ta rama sannan ta sake ta tare da guduwa bayan momma tana ɓuya, numfashi sadda tashiga sauke wa na wahala tana dafe kanta ita kaɗai tasan abun da zatayiwa yarinyar idan ta tashi, "Hamra na dariya ƙasa ƙasa taje wajen dadda tana bata haƙuri ayya tsohuwa kiyi haƙuri bari in ɗaura miki ɗan kwalinki ke kuma Amra gaskiya baki kyauta ba yanzu abun da kikayi ke idan akayi miki zakiji daɗi tana maganar ta ɗauko ɗan kwalin dadda zata ɗaura mata dadda ta kwace abunta tana ture ta tace to munafuka bake kika zigata ba yanzu zakizo min da wani guntun munafurcin ki ai wallahi zaku gane baku da wayo daga ke har itaɗin bade ni kuka yiwa hakaba zakuyi bayani, Amra ce ta leƙo daga bayan momma tace kinga dadda na ɗagowa tayi mata gwalo tace in kin isa taso ki kamani yanzu in ƙara wahalar dake wallahi,   "hararar ta kawai dadda tayi batare da tace mata komai ba ta jinjina kai irin zan kamaki ne yarinya, hakade sukai tasaka ta gaba suna tsokanar ta suna kunna ta ita kuma tana biye musu tunanin su momma yayi aiki dan bata ƙara zancen zuwa gun sarki ba ko ganin Ameesha ta biye musu suna ta faɗa su tsokane ta ta rama hakade suke ta abu ɗaya....., sameer na fitowa falo yayi musu magana suka tashi ga ɗayan su suka fita aƙafa suka taka har zuwa wajen me gadin, yana ganin su ya taso da saurin sa yana gaida su babban mutum ne,   dan haka suma sai sukayi saurin mayar masa da gaisuwar ya amsa yana ɗan sunkuyar da kai, bossay ne yafara cewa yau baba magana zamuyi kuma muna so ka faɗa mana gaskiya kar ka ɓoye mana komai kanaji ko, da sauri mutumin ya karkaɗa gaban sa na  faɗuwa  da ya ɗan tsorata da ganin su sannan"yace in sha Allah   "yauwa muɗan ƙarasa can gurin sameer yafaɗa yana nuna musu wani waje da ba mutane, gurin sukaje suka tsatstsaya sameer ne ya gyara tsayiwar sa da kyau sannan yafara magana idan zaka iya tunawa ajiya tundaga safe har dare zaka iya tuna adadin motocin da suka shigo kuma suka fita, ɗan jimm yayi kafin yace gaskiya bazan iya tunawa ba saboda da yawa wannan yashigo wancen yashigo bazaiyiyu insan adadin suba, to daga magariba fa zuwa dare eh to wannande zan iya tunawa akwai motar matan mai martaba da suka fita ana daf da magriba sai kuma suka dawo bayan an idar da sallah sai waziri da ɗan sa shima yafita gaba ɗayade baifi motoci huɗu bane suka fita suka dawo ba aciki harda taku yauwa sai ta su yarannan ƴan biyu suma sun fita amma su tunkan la'asr ma suka fita kuma sai dare ma suka dawo bayan nan kuma sai motar tasu ta ƙara dawowa tafita yana fita ku kuma kuka shigo to nide inajin abun da zan iya tunawa kenan,   bossay yakalle sa yace bakaga wata baƙar motaba bayan sallar magrib,   gaskiya bangan taba amma bansaniba ko loƙacin bana gurin ta shigo natuna ma aloƙacin naje karɓo abinci wataƙil ko anan yashigo bansani ba, "daman ana iya buɗe gate idan baka nan ko akwai wanda yake fansar ka idan bakan? cewar shettima a'a gaskiya ni kaɗai ne wallahi ba wanda yake karbar min amma  wataƙila ma ko ba wanda ya shigo ɗin daman tunanin  hakan nayi tunda de nasan nabar wajen shiyasa nayi tunanin hakan zata iya faruwa,   "Sameer yace to munji wannan baka sani ba to ɗazu da asuba fa tabbas inma baka ga shigowar suba to kaga fitar su tundade asubace babu inda kakeje ko, "tobbas ɗazu dana fito daga masallaci naga gate abuɗe alamun anfita nayi mamakin ganin sa ahaka sai nayi tunanin ko fitar gaggawa ce takama ko babu lafiya shiyasa aka buɗe aka fita kuma aka barsa ahaka saboda saurin da akeyi, kawai sai na rufe naci gaba da harkar gabana, wayyo gaba ɗayan su babu wanda yaji daɗin wannan labarin shikenan yanzu inda suke tunanin zasu samu wata shedar yanzu ta ruguje gaba ɗayan su jikin su yayi sanyi duk atunanin su wannan abun bazai basu matsala ba sunso wanda yafita daga motar da shikenan bazasu sha walaha ba amma yanzu koman su ya dawo baya, *dukan su jiki babu kwari haka suka sallame sa suka juya suka tafi part ɗin fulani suka nufa dan bazasu ƙara komawa gurin dadda ba ayaude baza ta ƙara ganin suba, suna ƙarasawa da sallama ɗauke abakin su suka shiga ciki sameer ne yafara shiga yana shiga yayi karo da mutum kafin kace me ta tafi luuuuu zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta saboda ruwane awajen idan takai ga ƙasa zata ji ciwo, mopping take yi afalon tana jin sallamar su kuma ta rikice ruwan ya zube a ƙasa zuyowar da zatayi kuma sukayi karo dashi ta zame zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta, saura kaɗan numfashin ta ya ɗauke yin tozali da fuskar sa, dagota yayi ta tsaya da ƙafafuwan ta amma saboda ba nutsuwa a tattare da ita  sai ta ƙara yin baya zata faɗi yaƙara riƙe ta yana mamakin wannan wacce irin yarinyace haka da bata da nutsuwa atare da ita kallon ɗaya yayi mata yagane ba nutsuwa atare da ita, sakin ta yayi batare da yace komai ba ya ratsa ta gefen ta ya wuce bossay ne abayan sa kallon ta yatsayi yana tunanin inda yasanta yana kallonta yaga yasanta amma kuma yarasa a ina yasan ta ɗin,   ahankali ya nunata da yatsa yace amma kamar na sanki ko ɗagowa tayi ta kalle sa atake ita kuma ta tuna inda tasanshi amma sai tayi saurin girgiza kai tace a'a tana sunkuyar da kai yace oh sorry kamace kawai wataƙil yana faɗar haka yayi wucewar sa shettima dake tsaye  ya harɗe hannuwan sa ya kafeta da ido yana jiran sugama shi yama manta da ita sai yanzu da suka haɗu, kwata kwata batasan da tsayiwar sa ba agun amma jin kamar ana kallon ta yasa ta ɗago kanta caraf idon su ya haɗe waje guda cikin duburbur cewa tayi saurin janye idon ta ta juya zata bar wajen yayi saurin riƙo hannun ta tsayawa tayi cak batare da tajuyo ba dawowa yayi gabanta tare da kallon fuskarta, idon tane yayi rau rau ya taru da kwalla alamar zatayi kuka ganin hakan yasa kawai ya shiga janta suka fara tafiya batayi yunƙurin kwace hannun taba tace gaba da bin sa, part ɗin sam ya nufa da ita, yana shiga ciki duk suna falo azaune kan kujera bai kalli kowa ba kuma baice da su komai ba ya wuce ɗaki da ita, duk da kallon mamaki suka bishi ganin baice musu komai ba yasa suma sukayi shiru da bakin su suka zubawa sarautar Allah ido, yana shiga da ita ya jefata ciki sannan ya juya  ya rufe ƙofar tare da saka mata key sannan ya juyo suna fuskantar juna kallon kallo suka shiga yiwa juna kafin daga bisani ya buɗi baki yace inajin ki kimin bayani shiru tayi ta sunkuyar da kanta tasan me yake nufi amma batasan ma ta ina zata fara yi masa bayanin ba , "magana nake miki kinyi shiru yayi maganar cikin ɗan ɗaga murya, daman kiris take jira ta daɗe bataga wanda tasani ba akusa da ita dan haka akusa take kiris take jira a taɓata, *dan haka daga wannan maganar sai kawai ta fashe mishi da kuka sosai tafara kuka duk wani baƙin ciki haɗuwa dashi yasa tafara tunanin halin da take ciki na damuwa, mamakine yakamasa daga magana sai kuka to me yake damun ta haka tausayin tane ya kamasa sai kawai ya kamo hannun wanta yajata sukaje bakin gado ya zaunar da ita ita Kuma bata dena kukan ba jin kukan nata yayi har cikin ransa baisan loƙacin da yajawota jikin sa ya rungume ta alhakin da take ciki a yanzu bata da zaɓin da zata hanasa saboda itama tana buƙatar wanda zai rarrashe ta ahalin yanzu, kamar zigata yayi tanajinta ajikin sa ta ƙara sakin wani kukan me tsuma zuciyar me sauraro sosai ya ƙara ƙanƙame ta ajikin sa daidai saitin kunnen ta yakai bakin sa ya shiga hura mata iska acikin yana cewa shiii yana ɗan shafa bayanta da ɗayan hannun sa ahankali duk de salon rarrashi shi yake mata, tun tana kukan da karfi har ta fara yin low da muryarta shikuma yaci gaba da rarrashin ta sunkai wajen 20 minutes ahaka kafin daga baya tayi shiru tare da yin lamo ajikin sa sai kace wata ƴar baby....., saidaya tabbatar da ta samu nutsuwa sannan ya ɗagota daga jikin sa fuskar ta ya shiga kallo sai tayi saurin kawar da fuskar ta gefe saboda wata irin kunya taji ta kamata na kwanta masa ajiki da tayi, hannu yasa ya juyo da fuskar tata sannan yaƙara saka ɗayan hannun hannuwa biyu yasa ya tallafo fuskar ta yana kallon cikin ƙwayar idon ta sannan,  in a slowly voice yace what happened? umhum "gaya min, yayi maganar cikin wani salo da saida tasa tsigar jikin ta tashi, janye fuskar ta tayi daga hannun sa baihana ta ba yasake ta saboda yabata damar gaya masa abun dake faruwa, shiru tayi takasa magana saida yaƙara tambayar ta sannan da ƙyarde ta shiga bashi labarin dalilin ta na zuwa gida har ɓatan mahaifin nata tun farko saida ta bashi labari da loƙacin da mutumin yaje yagaya musu inda yake sannan ta shirya tazo gidan amatsayin mabaraciya daga haka kuma har Ammah ta ganota amma bata ce mata komai ba bayan nan kuma ta dawo wajen fulani da zama komaide ta kwashe ta gaya masa amma banda son sameer da take da kuma dalilin suman da tayi rannan duk de abun da yashafi sameer bata gaya masa ba bayan shi kuma babu abun da ta boye masa kuma ta sanar dashi tunda tazo bata taɓa haɗuwa da mahaifin nata ba.....,✍️✍️ ayi haƙuri da wannan amma ba anan naso tsayawa ba amma ba dama saidai idan Allah yakaimu gobe da rai da lafiya.                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/5, 7:27 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 81 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️               babu abun da ta boye masa kuma ta sanar dashi tunda tazo bata taɓa haɗuwa da mahaifin nata ba.....,✍️   "yayi mamakin jin labarin data bashi baitaɓa tunanin abun da ake amasarautar har yakai haka ba, cike da tausayawa ya riƙo hannun ta yana kallon ta yayi shiru yana rasa ta ina zai fara yi mata magana saida suka ƙara ɗaukan loƙaci ahaka batare da ya tanka mata ba, har saida tayi tunanin ba abun da zaice mata tafara ƙoƙarin tashi daga gurin yayi saurin mayar da ita ta koma ta  zauna cikin ƙasa da murya yace sorry amma me yasa baki taɓa gaya min ba sai yanzu ai da kingaya min tun kafin kizo nan shigowar ki nan shima ai kinyi ganganci ke ahakan ki har kike tunanin zaki iya fita dashi daga cikin nan, kamar zatayi kuka cikin muryar damuwa tace nima bansan kana da alaƙaba da nan ɗin ai da tuni nagaya maka sai washegarin ranan sa kukazo naganka amma bansani ba nima kuma banyi tunanin abun yakai har hakaba nazata zan haɗu dashi ta cikin sauƙi ashe abun is not easy yanzu dan Allah kataimaka min ko da mahaifina ne in haɗu wallahi inason ganin sa kuma haryau bangansa ba dan Allah kataimake ni, kar ki damu in sha Allah zanhaɗaku amma idan na haɗaku zan fidda ke daga cikin gidan ki koma gida inyaso kibarmin komai zan dawo dashi amma sai anbi komai ahankali saboda nima da kika gani bawai ɗan gidan bane abokina ne tun na yarinta dan anan ma kusan nayi rayuwata amma duk da haka banda wani iko da zan iya zuwa kai tsaye in faɗi buƙatata ayi min ba bazai yiyu ba musanman irin wannan da sunriga da sun maidashi bawa da sarki da mahaifiyar sa baza su taɓa bari ya tafi ba saidai kawai yafita batare da sanin su to amma fitar ce abu me wahala amma de zansan yanda zanyi infito dashi batare da sanin kowa ba dan ko abokina ma ba lalle ingaya masa saboda idan nagaya masa bashi da haƙuri bazai yarda a fita dashi ba batare da kowa yasani ba sai ya ɗaga murya kowa ma yaji daga nan kuma azo asamu matsala anuna masa fin ƙarfi koma su canza masa wani gurin da bazamu taɓa ganin sa ba shiyasa zanyi komai ni kaɗai idan yaso daga baya sai ingaya masa, wani irin daɗi taji ya ziyar ceta take tashiga yi masa godiya harda ɗan guntun kukanta saidai kuma a ƙasan zuciyar ta bataso yace wai zai fita da itaba dan tanason fita bata son fita dan wahala tana cin wahala agidan shiyasa take son tafi abun da kuma yasa bataso tafi saboda idan ta tafi shikenan bazata ƙara ganin abun sonta ba bazata ƙara sakashi a idon taba kai inna gaskiya bazata iya juraba gwanda kawai taci gaba da zaman gidan duk sanda suka haɗu tagansa tana jin daɗi aranta hankalin ta yana kwanciya, "me kike tunani ya tambaye ta yana juyo da fuskar ta da sauri ta girgiza masa kai tace babu komai, "Ok"  to yanzu inasao kishirya daga yau zuwa gobe koda yaushe ma zan iya sanar dake tafiyar mu tamu yakamata ki koma gida zamanki anan gangan cine idan suka riƙeki to wallahi har mutuwar ki babu inda zakije saidai afita da gawar ki bakisan halin mutanen ba daman da bakizo ba hakan ma ai yazo miki da sauƙi nayi mamaki ma da babu wata matsala har kikashigo kika zauna batare da wata matsala ba, koda yake kinci sa'a hannun Amma kika faɗa amma da ace farkon shigowar ki kika haɗu da waccen matar da jikin ki yagaya miki dan baza ta taɓa yarda dake ba loƙaci ɗaya, ki godewa Allah da komai yazo miki da sauƙi, nima kaina wallahi nayi mamaki saboda bansha wahala ba nashigo daman tun kafin ma nazo aranar da mutumin nan yaje yasanar damu nace zanzo yace kar nazo akwai matsala idan nazo amma nidai banjiba mama tayi tayi kar nazo harde muka lallaɓata nida yaya ta amince na taho kuma da nazo sainaga komai yazo min cikin sauƙi dan a ƴan mintina nasamu dama har na shigo ciki, ɗan jinjina mata kai yayi sannan yace nima nayi mamaki, "dan wallahi ranar da nafara ganin ki ranar ba ƙaramin mamaki nayi ba koda na haɗu da yayan ki naso muyi maganar dashi kuma bamu samu damar zama ba saboda nima ƴan kwanakin nan muna busy bana samun loƙaci shiyasa bamuyi ba amma yanzu tunda nasani bama sai namasa maganar ba kawai zan rabu dashi in mayar dake gida kawai, "to kawai tace masa badan tana son tafiya ba saidan ba yanda zatayi, hakade suka cigaba da ɗan tattaunawa kafin ta tashi zunbur tana wurga ido tunawa datayi da aikin da takeyi na mopping ɗin datake ashe bata gamaba ita tama manta sai yanzu ta tuna cike da tsoro ta kalle sa yace nagode sosai Allah yabar zumun ci bari inje inƙarasa aikin da nake Allah yasa bata fito ba ta nemeni,   ganin duk tabi ta tsorata loƙaci ɗaya sai ta ƙara bashi tausayi hannu ya miƙa mata alamar ta tasoshi noƙi kafaɗa tayi sannan tace Allah fa ba kyau ana taɓa mutumin da ba muharramin kaba nidai kawai ka tashi da kanka inkuma in tafi in barka anan shikenan sai anjima tafaɗa tare da juyawa zata bar wajen caraf ya riƙo hannun tsayawa tayi batare da ta juyoba tafara jan hannun ta zata kwace shi kuma yaƙi saki yaƙara riƙeshi da kyau sannan ya yunƙura ya tashi abayan ta ya tsaya bazato ba tsammani kawai taji ya rungumo ta ta baya tare da ɗura kansa akan kafaɗar ta daidai kunne murya ƙasa ƙasa yace babu kyau ko kinsan babu kyau ɗin kika kwanta min ajiki ni bance miki ba kyau ba saike, runtse idon ta tayi da ƙyar ta iya cewa dan Allah kasake ni intafi kuma ma ai bani na kwanta maka ajiki kai kajawo ni tayi maganar tana turo baki kuma bata buɗe idon ta ba, shima cikin kwaikwayon irin muryar ta yace to da na jawoki meyasa kikazo bakice min ba kyau ɗin ba kuma nima ai da na jawoki bacewa nayi ki kwanta ba amma ki kwanta min akan ƙirjina gashi yanzu zafi yake min dan haka sai na rama indai kina so kifita daga ɗakin nan shima ya ƙarasa maganar yana turo baki kamar yanda tayi, ji tayi kamar ta nitsi agurin saboda ta ƙaicin sa da yagama kamata, uhm uhm uhm dan Allah kasake ni wai me nayi maka duk sanda muka haɗu sai ka raɓe ni bansan meyasaba kai hakan daɗi yake maka kana taɓa macen da ba maharramar kaba,   "Uhm sosai ma inbantaɓa ki ba bana jin daɗi amma idan na taɓaki sai inji daɗi tunda haka kikace, "barima inƙara yin abun da zaifin daɗi  dan naga alama iya taɓawa bazai gamsar dani ba gwara inƙara da yin wani abun ina ganin yin hakan sai yafi kema nasan zakiji daɗin ko yaƙarasa maganar tare da leƙo fuskar ta,   da sauri ta ƙara rufe idon murya kamar zatayi kuka tace wayyo Allah  mama na, dawowa yayi gabanta tare da ɗago haɓarta yana kallon ta ganin ya sakar mata hannu yasa ta faki idon sa ta kwasa aguje ta nufi wajen ƙofa tana zuwa da sauri ta murɗa key ɗin ƙofar na buɗuwa shikuma ya ƙaraso inda take da sauri yakai hannu zai riƙota itama tayi saurin ficewa daga ɗakin data fitama bata tsaya ako inama ko takan mutumin ta bata biba duk da taganshi da tafito amma bata tsaya ta fice daga falon bata daina guduba saida taganta agaban inda take mopping sannan ta zauna tana maida numfashi harda dafe ƙirjin ta afili tace lalle ma wannan mutumin shi ba a abun arziƙi dashi wallahi idan yana wani abun kai ka ɗauka na Allah ne amma sai ɗan iskan son taɓa mata ko kunyama bayaji oh Allah ya taimakeni da bansan abun da zai min ba aikwa da ya cuceni shiru tayi tana tunanin abun da yace mata sai kawai tasaki murmushi ta tashi tacigaba da mopping ɗin tanayi tana tuna moment ɗin su da yafaru yanzu, aɓangaren sa kam tsaye yayi yana dariya yanda take gudun ba ƙaramar dariya ta bashi ba ita nan aganin ta gudan mishi tayi batasan rabuwa de kawai  yayi da ita ba shi kansa baisan me yasa yake mata hakaba idan suna tare kwata kwata controling ɗin kansa sai yaga yana tayin wasu abubuwan da baisaba ba kuma bayi yake ba sai akanta kawai yake jin hakan dagaskiyar ta tunda suka haɗu indai yaganta akusa dashi sai yaji yanaso yajita akusa dashi ba halinsa bane amma haɗuwar sa da ita tasa ya canza hali amma duk da haka a iya kanta yake iya hakan, haka yai ta tunani shikaɗai a tsaye abokin ƙofa saida de yaga tunanin bayi masa zaiyi ba sannan ya fara takawa ahankali ya fito daga ɗakin zuwa falo inda ya tadda su sam azaune kamar yanda ya barsu,   duk zuba masa ido sukayi suna jiran bayani amma sai ya wani basar ya nuna baisan sunayi ba kamar ma shi ba abun da yafaru guri yasamu kusa da Sameer ya zauna yana cewa to yanzu ya muke ciki ne meye mafita wani mugun kallo da sameer ya watsa masane yasa saura koris ya kwashe da dariya saboda yasan ma'anar kallon da yayi masa,  cike da ƙara basarwa ya dake yace naga kana hararata daga magana nufa tambaya kawai nayi ba wata baƙar magana nafaɗa ba ko nayi kuskure ne a maganar danayi,   "bossay ne yace haba bawan Allah kaima ai kasan me kayi ba sai anfaɗa ba nan duk kai muke jira, "ni kuma to gani ai me yake wakana agaya min, Sameer ne yakai masa duka akai yace wallahi ranka zai ɓaci waza ka mayar shashakai bamason rainin hankali, kaja yarinyar mutane ɗaki kuma kafito kace zaka raina mana hankali uban me kayi mata harda sakawa ɗaki key, "Bossay wacece waccan yarinyar? ɗan shafa ƙeyarsa yayi sannan yace oh wai wannan maganar kuke nufi ai ni ban fahimta ba ƴar aikin kuce fa ai kai yakamata intambaya ko wacece nima bansan taba yau nafara ganin ta, "Sameer ya ƙara harar sa yace "eh shiyasa naga kariƙo mata hannu ka kaita ɗaki sannan ka ƙulle ahakan shine baka santaba ko ɗan iska maƙaryaci dan tsabar rashin kunya ma bakaji kunyar muba zaka wuce da ita ta gabanmu kushiga ku daɗe duk acikin rashin sanine ko, dariya yayi har haƙoransa na fitowa sannan yace to ba me aiki bace ai wani aiki makirata tayi mun ɗakin ka ta gyara ta wanke banɗaki shiyasa uaga mundaɗe amma bawani abu da yafaru bayan wannan dan haka ku kwantar da hankalin ku,   "lalle ma yaron nan kasan Allah idan baka gaya min abun dake faruwa ba sainayi mugun ɓata maka rai me ka mayar damu mahaukata kaga Aliyu jeka kakiramin yarinyar cen da tafita in haɗasu dukan su inci mutuncin su arasa a inda za ayi sai aɗakina kuma karasa ma wacce zaka kaimin ɗaki sai ƴar aiki to wallahi daga kai har ita sai kunyi bayani sai kun faɗan abun da yahaɗaku, hhhhhh shettima yasaka dariya sannan yace nine ma yaron naka wai kai ban girme kaba mutum sai ɗan iskan son girman bala'i, kai kuma bossay wallahi kar kasake ka kirata nan gurin magulmata kawai ina ruwan ku da abun da yafaru bazakuji komai ba to tsakanin na da ita sirri ne dan gwarama ku haƙura amma duk abun da kuke tunani ya faru to shiɗinne yafaru yaƙarasa maganar yama gyara zama yayi kwanciyar sa akan kujerar da yake kai, acikisu babu wanda maganar bata ɗaure masa kaiba duk yagama rufe musu baki sunma rasa amsar da zasu bashi, yagama kai sam ƙarshe da mamaki tunda suke baitaɓa ganin sa da mace ba kuma irin haka bata taɓa faruwa ba amma wai yau da me aiki ya shiga ɗaki kuma suna tambayar sa amma yaƙi yagaya musu yana faman raina masa hankali, to kwa wallahi ba isaba bari shi yaje da kansa hakira yarinyar zasu cu ubansu dukan su dan bazai ɗagawa kowa kafa ba yana ayyana hakan yamiƙe tsaye da sauri zai fita waje wayar sa dake kan  center table ta fara ringing dawowa yayi ya ɗauki wayar sabuwar number yagani sai kawai ya maida wayar ya ajiye sai kuma yatuna  kode managen nanne yake kiran sa ko kuma wani ne daban kira me amfanine yana wannan tunanin har wayar ta katse  wani kiran ne yaƙara shigowa akaro na biyu hannu yakai ya ɗauki wayar sannan ya amsa kiran tare da saka wayar a speaker sai yayi shiru yana jiran yafara ji daga can, kukan tane yafara dakar dodon kunnen sa atake yagane ko wacece me kiran sauri yayi yacire wayar daga speaker yasaka ta a kunne sa tare da saurin barin wajen ya nufi ɗakin sa, yana tashi shettima yayi zunbur ya tashi tsaye daga kwance da yake yana faman washe baki shima yabi sam inda yaga yana niyar tafiya acewar sa tunda yaji kukan mace kuma yaji ya cire wayar daga hans free yana niyar barin wajen yace to sai yabishi yaji abun da zaice, shide bossay bai tashiba yana gurin yana musu dariya ganin yanda suke abunsu sai abun ya burgesa watakon shi shettima yaƙi faɗa masa komai game da yarinyar da suka shige ɗaki amma yanaso shi yaji abun da sameer zaice shikuma sameer shima bayaso kowa yaji wayar da zaiyi kowade kansa yasani,   yanda suke abun nasu sai suka tuno mishi da Ameeshan shi yasan da ba aɗauke taɓa da tuni shima yanzu yana tare da ita jikin sane yayi sanyi 😢 cikin sanyin murya yace Allah ya bayyana minke aduk inda kike Allah ya kareki da kariyarsa aduk halin dakika tsinci kanki Allah yabaki ikon haƙuri da juriya bakiji ba baki gani ba tun kina ƙarama antakurawa rayuwar ki Allah yakawo miki ƙarshen wannan abun, Allah sarki baby meesha na ina sonki sosai Allah ya nuna min ranar da zan kasance dake ranar da zan wayi gari inganmu ɗaki ɗaya inganki amatsayin mata agereni ranar sai nafi komai farin ciki zan baki kulawa daga nan har ƙarshen rayuwa ta in sha Allah tsakanina dake mutuwace kawai zata rabamu, ji yayi hawaye na niyar taho masa da sauri yayi rufe idon sa yana karanto addu'ar neman sassauci game da abun da yake atare da ita, kwantar da kansa yayi ajikin kujerar tare da ɗora hannu akan ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa idan yana tuna yanda yake sonta sai yaji zuciyarsa kamar zatayi tsalle ta fito waje haka yake ji aransa....., sam tunkan yakarasa wajen kofar yaji tafiya abayansa juyawa yayi sai yaga shettima wani mugun kallo ya wurga masa me ciki da abubuwa da yawa, dan juyar da kansa yayi yana magana kasa kasa yace Allah kwa sai naji ko wacece dan munafurci shine baza kayi wayar agaban muba zaka wani tafi daki to wallahi kafata kafarka sainaji duk abun da zakace, girgiza kai sam yayi kawai batare da yayi masa magana ba ya wuce yana shiga dakin yayi sauri yarufe ya murda key yabarsa awaje , shettima buga kofar yashiga jin da gaskede ya kulle yayi tsayawa yayi awajen yana kara kunne ko zaijiyo muryar sa amma ba abun da yake jiyowa, sam yana shiga dakin ya koma kan gado ya zauna yayi shiru yana cigaba da sauraron kukan nata baice mata komai ba harsaida ta dan tsagaita da kukan sannan tace hell cikin muryar kuka, kasa amsa mata yayi saida takara magana sannan yace wa mai magana banda wannan number kuma ankira anata kuka wacece? cikin kukan tace nice, "ke wa? "sumayya" tabashi amsa tana shirin fashewa da wani kuka yayi saurin da katar da ita yace ya akai? "tace tunjiya nake kiran wayarka bata shiga yauma haka kuma kace ajiya zaka dawo min da mahaifina amma bangan shiba dan Allah ka taimaka kadawo min dashi shikadai ne gata na aduniyar nan kar ka cutar min dashi tana gama maganar ta fashe da wani kukan kuka biyu ne ya hadar mata ga na rashin mahaifimta ga kuma matar da tayi mata duka da safe dan bata tashi da wuri tayi aiki ba, shiru yayi na dan dakiku sannan ya bude baki zaiyi magana yajiyo ta wayar kamar anamata magana zagi yaji ana kutuntuma mata cikin kuka ta shiga bawa matar hakuri bata gama bada hakurin ba yaji tass ankwashe ta da mari runtse idonsa yayi kamar shi aka mara haka yaji marin acikin ransa kasa magana yayi yana cigaba da sauraron fadan da waccen matar  take mata ta kara marinta duk yanajiyo sai kuna can yaji yadena ji sai ihunta da yake ji kasa kasa kashe wayar yayi saboda wani irin abu da yaringa ji yana taso masa daga kasan zuciyar sa yana tunani to wace wannan me dukan nata anya kuwa mahaifiyar tace tunawa yayi tana cemishi shikadai ne gatan ta to anya kwa ba mahaifiyar ta tarasa ba waccen kuma take cutar da ita  tsaye yatashi yafara zagaya dakin yana tunani yanajjn ransa namasa ba dadi, saida yabada kamar minti goma sannan ya dauki wayar sa yakira number da ta kirashi ga mamakin sa sai yajita akashe kara gwadawa yayi amma ana cewa switch up saida yakira wajen sau goma bata shiga ba sai kawai ya mayar da wayar aljihu ya dauki key din motar da zai fita da ita yasa shi shima a aljihu saboda bayaso su bossay sugani suce zasu bishi ko su tambaye sa ina zashi shiyasa yasaka komai a aljihu tare da shga bandaki dan ya wanke fuskar sa kar suga alamun damuwa agareshi suyi tunanin wani abun.. "Shettima dake tsaye har yanzu yanaso yajiyo abun da sam keyi amma bai ji komai ba kawai yajuya tare da yin kwafa ya juya ya koma falon bahaka yaso ba yaso yaji kodawa yake wayar amma yayi masa haka hmm zai zaka fito ne kasame shi yayi maganar yana zama akan kujera, jin maganar shettima yasa bossay ya bude idon sa dakana gani kasan akwai dam uwa atattare dashi,   "bossay yakalli shettima yace ya naga kadawo har angama wayar ne, "hmmm rabu da dan iskan ya rufe dakin munafuki sai yafito kaga yanayiwa mutane zare zaren ido da hade rai shi adole kar ace wani abun kuma wallahi sai mun fada hakan ma ai ba tsira yayi ba yagama yafito ya sameni anan, dan murmushi bossay yayi yace to yanzu sai kaga laifin sa naga kai nakama yafi nasa yanzu fa kazo ka shige daki da yarinyar mutane baka gayawa kowa ba kukaje kuka dade adaki kuka fito kuma kaki fadar komai shine yanzu kai kake so kaji tasa hirar da zaiyi, "kai manta da wannan ni ai ba budurwa ta bace shikam nasan budurwa ce kasan ma ni wacce nake zargi? bossay yace "a'a shettima harda gyara zama yana kallon bossay da kyau sannan yace wallahi ina tunanin wannan yarinyar ce da mukaje gidan su wacce muka kama mahaifin ta, bossay yayi dariya yace ai babu watakil ma amaganar ka itace idan ba itaba wace macence zata kirasa tunda kace bashida budurwa baya kula mata kuma nima naga alamun hakan kaga kwa waccen daga haduwa da ita mukaga sauyi saidai muyi musu fatan alkhairi, Gaskiya de kam hmmm wai nake shiga yayi sauri ya kulle ni abun harma mamaki yaban wai sam ne yau dakansa yake daga wayar mace tare da barin wajen tunda muke dashi ko  baitaba boyemin wani abu ba ko kuma yakasa yin abu gabana komeye agabana yake bayajin kunya bayajin tsoro amma yau gashi Allah yanunamin karshen abun gasky wannan wabun dole inyi mamakin sa, ah kadan ma kagani bade mace ce ba zata sauya sa fiye da yanda kake tunani kaima bagashi nan ta canza ka  ba kaki gaya masa shiyasa shima yayi maka haka, yana gama fadar haka ya dan matso da fuskarsa wajen shettima sannan yayi kasa kasa da murya yace yauwa yanzu bayanan ni gaya min abun da yafaru dan fa har ihunta najiyo tana cewa wayyo mama na kuma daga jin ihun ni nasan na menene dan haka dan gaya min bazan fadawa kowa ba wallahi, fulon dake gefe shettima ya dauka yajefa masa yace to muna fuki dan iska ashe kunnuwan ku yana kaina to bazakaji ba yara basa jin irin wannan maganar kabari duk sanda ka girma zan fada maka abun da yafaru, rike filon bossay yayi yana dariya yace au nine ma yaron naka kasande da nayi auren wuri da tuni na ajiye yara kusan biyar yanzu amma zaka cemin yaro nade san ba abun da zaka nuna min da bandashi, suna cikin haka saiga sameer nan yafito daga dakin fuskar sa adaure yazo zaiyi hanyar waje shettima yayi saurin dakatar dashi da cewa alaramma ina zuwa haka ba sanarwa kuma meye na daure fuskar dama kasaketa kafi kyan gani dan mude kasan ba tsoron ka zamuji ba, gwanda ma kadena wannann abun duk abun mutum yanzu munsan kowaye shi da kuma abun da yake aikatawa adena yimana wata fusfusga ana cin magani, juyowa sameer yayi tare da cilla masa dakuwa yace fuck u wallahi kafita daga idona naga alamar yan kwanakin nan raini yafara shiga tsakanin mu ko to wallahi kabini ahankali kasanni sarai banda mutunci kar kabari inkulla takun saka dakai bazakaji ta dadi ba dan haka kafita aharkata sai mu zauna lafiya, "inna ƙi mai zai faru ko zan dakune inzaka iya dukana kuma bismillah ga jiki ga tsoka ga kuma fata kadaki inda yayi maka saurayi mijin yan mata, hmmm zakayi bayani ne ni yanzu bani da lokacin ka ina da abunyj agabana  zan fita amma ba dadewa zanyi ba, cike da tsokana shettima yakara cewa ah daman ina kato dani ina za aban lokaci daman lokacinka ai banawa bane nata ne dan haka aje abata lokacin ta nima dakwai inda zanje abani nawa lokacin, bossay yace banda wanda aka baka dazu sai ankara baka wani yanzu yakamata kabarta ta huta ai ko na mamajo kazamane bamu sani ba, dariya suka saka gaba dayan su dan har sam saida yadan dara yana girgiza kai yace ni kunga tafiyata sai nadawo yajuya zai fita bossay yayi saurin cewa uhm naceba dan Allah idan hanya ce muje kasauke ni agida daman nima yanzu nake tunanin inje indawo ka ajiye ni inyaso sai indawo idan kadawo sai kayi min waya, sameer yace to muje amma fa bazan kaika har gida ko kuma muje sai driver yakai ka kawai ma basai ka wahalar dani ba, bossay ya nike tsaye yace to hakan ma yayi nagode muje, shettima ma tashi yayi yace to nikuma fa waye zai maidani gida ko ni bamu da gida da duk kuke so kutafi ku barni anan, hararar sa sameer yayj sannan yace bamu sani ba bazamu tafi dakai ba wallahi kayi zaman ka anan sai ka kirata ku dora daga inda kuka tsaya yan iska kawai,, dariya shettima yayi yace wai dan Allah ku mai kuke tunani munyi da yarinyar nan nifa babu abun da nayi mata wallahi kuma dena tunanin wani abun yafaru babu abun da yafaru kawaidai wata yar magana mukayi da ita, "Sameer yace kaide  kasani can ta matse muku kai da ita sai kafadawa wanda baisan halin ka muje kai in kuma zaka tsaya kaci gaba da jin karyar da yane zubowa to sai kataho yana kaiwa nan yafita daga  falon da sauri bossay yabi bayan shima shettima yabi su yana dan murmushi dan shi mamakin su yake su duk atunanin wani abun sukayi da suka shiga dakin..., akusan tare suka karaso falon fulani suna fitowa Azeema ma na fitowa daga kitchen tana ganin su ta koma ciki da sauri ta rufe kofar tana sauke numfashi, sam ne yaja tsaki yace munafuka sai yanzu zakiji kunyar lokacin da kika zo kika wuce mu kika shige har uwar daki bakiji kunyaba sai yanzu, to ina ruwanka da ita shishshigi to tayi din me ruwan wani aciki, "Babu " sam yabasa amsa yaci gaba da tafiyar sa, har suka karaso wajen motar babu wanda ya kara yiwa kowa magana saida sukazo gurin drivern sameer ya karaso wajen sai sameer yagaya masa yakai bossay gida ya kalli shettima yace kai kuma ga motar kanan daman baka dauka ba sai ka tafi gidan ku da ita, "ai basai kamin gorin gida ba  amma de ba inda zani da motata ataka zamu tafi tare muje mu dawo ni ba gidan da zani raka ka zanyi duk inda zaka, "baka da hankali naga alamar wannan yarinya tafara saka abun da ba daidai ba tunda kafito ka ishi mutane da surutu ka damemu daga kace wannan sai kace wancen to wallahi ba inda zani dakai malam kawuce ka shiga motar ka katafi gidan ku inkuma baza ka tafi ba ka koma ciki kajira indawo kazabi wanda yayi maka daman nasan so kake mutafi ka koma gurin ta to ga damanan munbaka ka koma ciki dan Allah nasan abunne yake cinka kake neman zaucewa akan mutane to mu bamu da maganin abun kaje tayi maka magani, kafin shettima yace wani abu sam yayi sauri ya  bude motar sa yashiga yana shiga kuma yasata a louck yana masa murmushi sannan ya zuge bakin glass din motar yana daga masa hannu tare da tayar da motar yaja yabarsa agun atsaye kamar gunki dan yau sameer yagama gaya masa maganar da baitaba ji yayi irin taba yabasa mamaki, bossay ma saida yayi masa dariya sannan yace sai anjima ade bi ahankali kar awuce da abun kunya azo ana dana sani kar ka cuci yarinyar mutane de kabarta kuma kade ji ba dadewa zamuyi ba dan haka kayi ka koma dan nasan amatse kake dan ana kallon idon ka za agane ba lafiya kake va nidai inkara baka shawara kar awcu gona da iri ayi komai baya baya, da sauri shettima yayi kansa zai kaimasa nausi yayi saurin matsawa tare da shigewa mota shima yana masa dariyar mugunta yacewa driver yasaka motar a louck sannan ya tayar haka kuwa driver yayi shima yana yar dariyar sa kasa kasa dan yagane hirar da suke yi yasan me suke nufi tayar da motar yayi yaja suma suka tafi bossay harda lokowa ta windo yana kara tsokanar sa, shettima kamar ya nutse agun haka yake ji wai har bossay ma yasamu damar yi masa irin wanna zancen aikwa zasuyi bayani wallahi duk sai yarama abun da sukayi masa daya bayan daya sai yarama sai sunyi danasanin wannan abun da sukayi masa yau shi zasu gayawa magana irin wannan kuma sugudu yama fasa tafiya gida zai koma yajirasu su dawo takan sameer zai fara sai ya kunce mai zani agaban kowa da kowa bade yana da videon sa ba yana daukar mace to wallahi ha momma sai ya nunamata yaga karshen rashin mutuncin irin nasa shikuma bossay zai duba yaga ta inda zai rama dan shi nasa magan ganun ma sunfi na sameer zafi zai sanine shima sai yagane bashi da wayo in yasakasu gaba sai yasa duk sun tsani kansu dan bazai raga musu zai hada da karya da gaskiya da abun da yafaru da abun da bai faruba ma duk sai ya hada yagayawa mutane da sukeyi.....,, yana wannan tunanin  har yakoma part din fulani yan shiga falon ya shiga rarraba ido ko zai ganta amma bai gantaba tunawa yayi da tashi ga kitchen dazu dan haka kansa tsaye bawata fargaba ya tura kofar kitchen din ya su biyu  ya gani aciki ita tana wanke wanke dayar kuma tana girki saida yagama karewa bayan ta kallo sannan yadan yi gyarab murya atare suka juyo suna kallon sa gaban Azeema ya shiga dukan uku uku shikenan yanzu ba damar guduwa yakata, dayar kuma tunda tasanshi kamar dan gida yake awajen kowa yanda za agirmama dan gidan shima haka suke girmama shi dan haka da sauri ta tsugunna ta gaidashi sanna ta shiga tambayar sa abun da yake bukata yace mata ba komai tana ta mamakin abun da yakawo sa kitchen din kuma yace babu abun da yake so to me yakawo shi har ta juya zata cigaba da aikin ta ya kira sunan ta tana amsawa yace mata in badamuwa kidan ban guri kifito waje, da sauri tace babu komai ita duk tunanin ta bai bata gurin dayar yazo tayi tunanin idan ta fito zace Azeema ma tafito amma sai taga tana fita daga kitcshen din ya mayar da kofar ya rufe da mamaki tayi tayi tsaye abakin kofar tana tunanin to me zaiyiwa yarinyar aikwa bazata bari wannan labarin ya wuce uwar dakin taba da sauri ta juya ta nufi dakin fulani dan ta sanar da ita abun dake faruwa tazo ta ganewa idon ta da kanta gani da ido yafi abaka labari....... Suna karasawa unguwar bossay  yace ya sauke sama akofar gida ya gode a kofar gida aka saukesa ya kwankwasa me gadi ya bude masa ya shiga ciki shikuma drivern ya juya yatafi, da sallama ya shiga falon gidan nasu amma babu kowa afalon dakin Ammin sa yafara zuwa yana shiga kuwa ya tara da ita tayi wanka ta saka wani less me dan karan tsada da kyau taci uban dinki ga stone ta ko ina sai kyakyali take, tsayawa yayi yana kallon ta ko kiftawa bayayi har sada tagaji da kallon da yake mata tace kaiafiya ka kafe ni da ido haka tayi maganar tana danyi mishi hararar wasa murmushi yasaki yace Ammi ganin nai kindau wanka irin wannan kyau haka kamar baki ajiye irin mu ba kamar fa budurwa haka kika koma kinganki ku da kyau amma de wannan kwaliyar da walakin wai goro a miya kamar fa amarya haka kika koma kode angon ne zai dawo ba'asanr da muba muma munyi shiri, murmushi tayi tace bana son iskanci yaushe nafara wasa daki mahaifin nakune ango to kamar akunne sa sai nagaya masa, to Ammi tunda ga amarya anan kinga kwa wanda zaizo ai angone dan Allah Ammi dagaske yau zai dawo, dagske kam yau zai dawo kagama iskancin ka zan sanar dashi daman da guntun haushin ka da yakeji kaga sai yaji dadin sauke maka, lokaci guda mood din sa ya canza tunawa da sanadin abun da Abban sa zaiyi saboda shirye shiryen bikin sa da zayi wani irin haushi ne da ta kaici yazo masa wuya ya tsaya masa, "Ammi wai dan Allah bazaki saka baki ba abar maganar auren nan wallahi ina cikin tashin hankali  yanzu ko nutsuwar kirkima bani da ita kallon sa tayj cike da tausayawa dan nata ta kalle sa tace Aliyu babu yanda zanyi kasan halinsa tunada yayi magana babu wanda ya isa yasa afasa auren nan saidai kayi hakuri kabi umarnin mahaifin ka Allah yasa hakan shi yafi alkhairi kaci gaba da addu'a idan ba alkairi bane zaka ga sauyi kaga anfasa idan kuma da alkhairi acikin sa dole sai anyi shi babu wanda ya isa ya hana ka kwantar da hankalin ka nasan da wacce kake so amma hakan bazaisa kaki samun taba sai hadasu su biyun saidai kayj hakuri ka kwatanta adalci a tsakanin su kar ka zalunci kowacce daga cikin su nasan kana da hakuri amma ka kara akai ka saukewa kowacce hakkin ta tundade dukan su suna sonka  ina ganin hakan bazai baku matsala ba kade kaci gaba da addu'a itace kawai mafita, sosai jikin sa yayi sanyi sai yaji kamar ma anriga da andaura da su dukan da yaji irin nasihar da take masa, cikin sanyi jiki yace Ammi baki san abun dake faruwa ba ko, kamo hannu sa tayi suka zauna akan gado saboda taga tsantsar damuwar a fuskar shi da kuma idon sa tasan yana cikin wani halin, dan shafo fuskar shi tayj tana kallon sa tace gaya min me yake faruwa, kamar zaiyi kuka yace Ammi sun sace tafa tun jiya muke nemanta bamuganta ba yanzu bansan halin da take ciki va taba raye ko tana mace bansani ba Ammi sun raba ni da ita Ammi bazan juri rashin taba wallahi ina sonta Ammi yana fada sai ga hawaye yafara saukowa, cike da tausayawa tafara share masa hawayen sa tana cewa yayi shiru saboda ita batama kawo wacce yake nufi ba duk atunanin ta budurwar da yace yana so ita aka sace saida tagama goge masa hawayen sannan tace a wace unguwar take kuma garin ya akai aka saceta ina iyayen ta,   kasake yayi yana kallon ta jin abun da tace tana nufin ma bata gane wacce yake magana ba, "zuciyar sace takara karaya wata kwallar na kara taruwa acikin idon sa yace Ammi bakisan wacce nake nufi ba ko? tace "eh mana" ai baka taba nuna min koda hoton tane bare ka kawota mungaisa, Ammi Ameesha fa nake nufi, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un Aliyu me kake sanar dani abu haka ba dadin ji ya akai haka garin yaya kukayi sakaci har aka dauketa, Ammi wallahi bamu bane daman ranar da natafi naje gidan sai akace antafi office da ita sai na bisi can daga can kuma muka tafi gidan su dayan wannan wanda akace agidan sarki yake bayan munje muka barta agidan muka tafi..........nanade ya kwashe duk abun da yafaru yabata labari, Sosai itama ta tsorata da wannan labarin tayi mamaki, nashiga uku ni Ameena yanzu in ba aganta ba taya zaku tari wannan baiwar Allahn ku gaya mata Allah sarki ashe batayi karya ba jikin ta yagaya mata gaskiya da har ina ganin rashin hakurin ta ashe ta fini gaskiya Allah sarki dadda amma bazanso taji wannan labarin ba kuma nasan muddin baku nemota ba ko ba dade ko bajima sai tasani bazata iya jure rashin taba nasan zata shiga mawuyacin hali inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un  gaskiya wannan abun baiyi min dadi ba bantaba kawo hakan zata faru ba yanzu ita dadda tana can gidan, "Eh Ammi tana cen yanzude ansa yara suna ta hira dan adebe mata kewa karta tuna da ita dan tace sai ankaita har wajen sarki ta sanar dashi mun dauke mata jika da kyar de ta hakura ta zauna yanzude bansan halin da take ciki ba tana cen ko ta hakuran ko kuma de me yafaru oho sai na koma zanjiyo sode muke zuwa gobe idan munkoma gurin munsamo wata shedar to idan kuma bamu samu ahaka zamu daure kawai mu gaya mata halin da ake ciki tunda ko mun boye yanzu dole tasani nan gaba kuma abun dai yafi mata rashin dadi zata iya cewama bata yarda ba karya muke, Ammi "tace aikwade ba abun da bazata fada ba bakaga yanda mukayi da itaba dazu da jiya itama labarin abun da yafaru da abun da dadda tace tabasa labari.........,         **************************** ______*meeshmeer*______ cizo da ta dasa masa ahannu baisan loƙacin da yayi sauri ya sakar mata bakinba kuma yana saki ta ƙara fasa ƙara da saida ta karaɗe duk banɗakin hannu yasa ya toshe kunnuwansa jin tana niyar fasa masa dodon kunne, tsawa ya daka mata ke wace irin marar hankali ce baki da hankali kinaso ki kashe min dodon kunne ne ko me kike nufi me nayi miki zakisani agaba nida kika cije ni bance komai ba sai ke zakiyiwa mutane ƙara akunne, sauri tayi ta ta tsugunna tana karkare jikin ta tanayin kuka ƙasa ƙasa jikin ta sai faman ɓari yake, ba magana nake miki ba? "cikin kuka tace dan Allah kayi haƙuri nidai kafita bazan ƙaraba dan Allah kafita, shiru yayi yana binta da wani irin mugun kallo yarasa ma wane irin hukunci zaiyi mata nayi masa wannan ƙarar acikin kunne gashi kuma ta cije shi ji yake kamar ya rufeta da mugun duka da zaisa tadena numfashi haka yayi tsaye akanta shi baifitaba kuma shi bai daina kallon ta ba kuma baita ɓata ba,..... itama kuma bata tashi ba daga gurin tana nan yanda take sai hawaye dake zubo mata kamar famfo..... ummy dake ɗaki ma saida tajiyo ƙarar duka gidan ma saida yaɗauki ƙarar da tayi maama da bacci tajiyo ƙarar kamar amafarki ahankali ta shiga buɗe idon ta tana salati ta tashi zaune tare da dafe kanta tana tunanin ƙarar wacece haka ta tasheta daga baccin da take me daɗi tana mafarki tashi tayi ta wuce bandaki dan tayi wanka tafiya taji meke faruwa ko ba lafiya ba, ummy dake ƙoƙarin dauko mata kaya jin ƙarar yasata tabar ɗaukowa ta fito da sauri ta fara taka benen dan ita atunanin ta ko faɗiwar ta ƙara yi, tana zuwa taji ƙofar ɗakin arufe da ƙarfi ta bubbuga tana kiran sunanshi, yakai hannunsa kenan zai damƙo gashin kanta yaji bugun ƙofar ko ba afaɗa ba yasan ummy ce dan haka da sauri ya janye hannun sa tare da fita daga banɗakin ya nufo wajen ƙofar yana ja ta buɗu ashe daman ƙofar ba akulle take ba kallon sa tayi tace me yake faruwa najiyo ihunta ko wani abun kayi mata? kai ya girgiza mata yace ni kuma ummy me zan mata ba abun da nayi mata nima ina nan azaune najiyo ƙararta shine naje bakin ƙofar nake tambayar ta me yasameta tace faɗuwa tayi amma yanzude ta tashi tama ce ta kusa gama wankan, "ayya Allah sarki wallahi nima saida nayi tunanin hakan nace ko faɗuwa tayi ashede hakanne daman nasan da ƙyar zata iya yin tafiya ƙafar nan fa naga alamar wataƙil sai mun kaita asibiti dan kamar ƙara kunbura tayi, Meer yace eh nima haka nake tunani bari mugama sai muje adubata ko tasamu gocewar ƙashi, ummy tace to shikenan yanzu bari in maida itama can ɗakin kawai ta shirya idan muka karya sai mutafi gaba ɗaya yanzu je ka taso maama ta shirya muci abinci bari ni intaimakawa wannan yarinyar infito da ita, badan yaso ba ya amsa mata sannan ya fice daga ɗakin ransa babu daɗi na rashin hukunta tan da baiyi ba amma ba komai zasu haɗu agaba dan haka ya sauka ƙasa ya nufi ɗakin maama nocking yayi ta bashi izinin shigowa yana shiga yama tarar har ta shirya gaida ita yayi sannan yasanar da ita aiken ummy tace ai tama gama suje kawai dan haka atare suka fito dashi inda yaga an jajjere abinci wajen dinning nan yajata sukaje suka zauna yace sujira anan yanzu zasu fito, kai yaro nikuwa intambaye ka ɗazu ina bacci naji kamar ƙarar yaro bande saniba macece ko namiji ko ba anan gidan bane, yatsina fuska yayi yace eh anan gidan ne munyi baƙuwa ne ɗazu shine ta faɗi aƙasa shiyasa kikaji tayi wannan ƙarar suna tare da ummy yanzu zasu fito, maama tace baƙuwa kuma daga ina daga zuwan mu sai baƙuwa ko daman kuna da ƴan uwa anan ne, "a'a bamu da kowa" ammade yanzu kiyi shiru kawai kibari idan ummy tafito tagaya miki ko wacece ita danni bazan iya doguwar magana ba ina baki labari..... da mamaki ta kalle sa amma batace masa komai ba kawai tayi shiru kamar yanda ya nuna yana da bukatar hakan dan haka bata ƙara ko kallon inda yake ba bare tayi masa magana dan itama fa akwai miskilan ci dan yama fi yawa a halaye ta dan magana bata dameta ba....... ummy nashiga taga Ameesha tsugunne tana faman kuka da sauri taje tana yi mata sannu sannan ta miƙar da ita da ta tai maka mata ta ƙarasa wankan tana ta faman jijjin kunya shaka har suka ƙarasa ta kamota suka fito jikin ta ɗaure da towel suna tafiya tana yi mata sannu har suka fito daga ɗakin suka fara saukowa kan benen dake yana yin falon mutum idan ya sauko daga sama bazaiga na kan dinning ba haka shima nakan dinning ɗin bazaiga me saukowa ba dan haka har suka sauko suka shige basu gansu ba, ɗayan ɗakin da yake extra ta kaita ta zaunar sannan taje ta lalubo mata wata ƴar doguwar riga da ita ta ɗage mata kuma tayi mata kaɗan daman sannan ta kawo mata tabata ta saka amma duk da haka ta yi mata yawa yawo take aciki bata daura ɗan kwali ba tabar gashin ta dake daure babu komai afuskar ta amma tayi kyau dan ma fuskar tata ta ɗan kun bura saboda kukan da tasha, kamo hannun ta ummy tayi tana ɗan ɗingisawa ta taka ƙafar da kyar da kuma taimakon ummy suka fito daga ɗakin dinning ɗin ta nufa da ita acewar ta idan ta zaunar da ita sai taje ta taso sauran kowa yafito suci abinci sai kuma taga harma sun rigata zuwa, da ɗan fara'arta ta ƙarasa gurin tana gaida maama, maama ta amsa mata gaisuwar idon ta yana kan Ameesha da kanta ke ƙasa batare da ta ɗago ba kawai tace ina kwana, maimakon maama ta amsa mata gaisuwar sai kawai tace a ina kuka samo yarinya naji ɗanki yace wai baƙuwa kukayi amma inbari inkin fito in tambaye ki ko wacece, jin abun da tace yasa Ameesha ɗagowa dan ganin mai maganar caraf idon su ya haɗe da na juna, maama ba ƙaramin tsorata tayi ba da ganinta ji tayi ƙirjinta ya wani irin bugawa sakamakon kamanni da tagani a fuskar yarinyar, da ƙyar ta iya haɗo kalmomin bakin tace ya sunanki? kallon ta Ameesha ta ƙarayi sannan tace Ameesha, "A'a na gaskiya kuma full name zaki gaya min, dan numfasawa Ameesha tayi sannan tace Khadijah Sameer ya......... ai bata ƙarasa faɗar sunan ba maama tayi zunbur ta miƙe cikin ɗaga murya tace Sameer Sameer Sameer de...... sai ambaton sunan sameer take takasa wata maganar, gaba ɗayansu suka shiga binta da kallon mamaki.......✍️✍️ Please more comment                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/6, 11:35 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 82 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️      " maama ce ta fara takawa ahankali har ta karasa gaban Ameesha taba zuwa takara kurawa fuskarta ido tade tabbatar da kamannin de datagani da gaske ne, "ina iyayen ki suke ina kuma mahaifin naki, maama ke tambayar ta, Ameesha shiru tayj takasa bata amsa itama tana kallon ta, Ummy tace "maama wai meke faruwa kin santane naga kina mara kallon sani, Juyo maama tayi tana kallon ta tace ko bansan taba amma wannan duk inda ta shiga ta fito tabbas jini nace wallahi yarinyar nan jinina ce ni naji hakan ajikina kallo daya naimata nagane hakan domin ga kamannin dana nan afuskar ta kamar su daya sak tana fitowa naga kamar shi sak, duk mikewa sukayi suna kara duban su da mamaki dan har suna tunanin anyama kuwa ba ciwon tane ya tashi ba, ummy ce ta karasa gabanta tare da riko hannun ta tace maama anya kuwa dagaske ne wannan fa yarinyar dazu suka hadu da babana yanzu kina ganin har zaki iya tuna kamannin sa bayan kindade rabon ki dashi inaganin de gaskiya kamace kawai ki manta da wannan maganar kawai kizo muci abinci sai kisha magani, Kasake maama tayi tana kallon ta idanun ta har sun cicciko da hawaye ta bude baki da kyar tace me kike nufi da insha magani kina nufin ina haukane bansan me nake ba bani da tunani bansan kama ba nida dana taya kike tunanin zan iya manta kamannin sa har yanzu kamannin sa basu bar idona ba ina tuna lokacin da mukayi rayuwa dashi dan haka koma me zakuce kuce amma nidai nasan wannan yarinyar jini nace gashinan tace sunan baban ta sameer kuma nima dana sunan shi sameer, wallahi ke jini nace kar ki dauki maganar su ina cikin hankalina nake wannan maganar kitaimaka maama duk tabi ta rude sai zuba surutu take tana hawaye tana jan Ameesha sutafi ita kawai akaita wajen danta, ita kuma Ameesha taki binta kuma taki cewa komai sai kuka da takeyi itama takasa magana, Abu ne da yagama karantar su gaba dayan su yakaraso gabansu batare da yace da su komai ba ya riko hannun Ameesha itama maama ya riko hannun ta sannan yace ya kamata mu zauan sai anfi fahimtar juna yana fadar haka yajasu zuwa falo suma su ummy da meer binsu sukayi abaya, Afalon kowa yazaunada kyar maama ta zauna shima tare da Ameesha kujera daya suka zauna tarirrike mata hannu dan jitake kamar zata gudu idan tasake ta, Abu ne yafara magana sunan maama ya kira ta bata amsa masa ba kuma bata dago ba saboda hankalin ta gaba daya yana kan Ameesha sai kara kallon ta take, maama yakamata kafin kifara yanke hukun ci kifara jin ko ita wacece ban karyata kiba nacewar jinin kice domin jini ba karya bane ko baki fada ba ga kamannin ku kuna kama ana kallon ku ansan jini daya ne saidai kuma banda tabbacin hakan saboda hakan tana iya faruwa kaga me kama dakai alhalin kuma baku hada dangi ba amma de yanzu muna so kifara bamu labarin ki inyaso sai itama muji nata labarin kinga tanan za agane idan kuna da alaka idan kuma labarin ku yasha bambam kinga baku da wata alaka sai mu dauka amatsayin kama ce kawai, tana gama fada mata ta share hawayen ta tare da kara komawa wajen Ameesha da tayi tsaye agun kamar gunki tana jin maganar matar kamar amafarki, taba zuwa gaban ta ta rungumeta tana kara sakin kuka kamkam takara yi mata ajikin ta kamar zata mayar da ita cikin jikin ta kaunar yarinyar nakara shigar ta, sude ba wanda yakara magana agun duk sun zama yan kallo kamar sun samu tv, har Abu ma da tun farkon faruwar abun yake tsaye daga bayan su yana kallon su, saida ta dauki lokaci tana rungume da Ameesha sannan ta raba jikin ta da nata ta kamo hannun ta tace muje kikai ni wajen mahaifin ki inason ganin sa ni nasan jikina bazai bani karya ba ammade nafi so ingansa, tayi maganar tana niyar fara jan Ameesha wai su tafi, ahankali Ameesha ta shiga girgiza mata kai sai hawaye kuma yafara saukowa zirrrr kamar ana turo sa, Sannan cikin kuka tace nibanda iyaye iyayena sun rasu, cak sukayi gaba ɗayan su suna kallon ta amma duk da haka maama bata yarda ba, tsayawa maama tayi agaban ta sannan  tace dan Allah yarinya karkice min bazaki ba kitaimaka kizo muje inga dana ke kadai ce zaki iya hadani dashi na matsu inganshi Kitaimaka min kefa jikata ce ni na haifi mahaifinki awannan cikin nawa tafada tana nunamata cikin ta, tace ni na raine shi inason sa ina kaunar sa amma aka rabani dashi, sai yanzu ta dago ta kalle sa sannan tace kafin aji nawa ina so tafara bani nata tunda tace bata da iyaye to daga ina tafito ina danginta, Abu yace "hakane to yarinya ya sunanki? "Khadeeja ta bashi amsa murya can kasa kasa, to malama khadeeja muna sauraron ki zaki iya bamu dan takaitaccen bayani game da rayuwar ki kibamu labarin ki tundade ai duk kinde ji abun da akace kuma matar nan tace ke jinin tace tana tunanin ke jikar tace dan haka sai ki bamu labari ko Allah zaisa tunanin ta yakasance gaskiya kicire mu daga kokon to gaba dayan mu dan nima kaina ina bukatar jin karin bayani saboda nima naga kamannin ku da ita shiyasa muke so ki warware mana wannan zargin da muke muna sauraron ki malama khadeeja, shiru Ameesha tayi kamar bazatayi magana ba sai kuma ta gyara zama kalamar da ta fara fitowa daga bakin ta sai cewa tayi tunanin ku zai iya zama gaskiya kamar yanda nace muku iyayen na sun mutu to dagskede mahaifiyata ta rasu amma mahaifina bai rasu ba amma ni kaina bansan shiba bansan ya kamannin sa suke ba ban taba ganin saba, ni na taso ahannun kakata ne mukadai na taso nagani daga ni sai ita tunda nafara mallakar hankalina nake tambayar ta ina iyaye na da kuma dangina sai taki gaya min dan munsha fada ma da ita saboda ina aiki awani gida to mutanen gidan innayi laifi suna dukana sannan su zageni akan ni wai yar shegiya ce tsintacciya zagide ba irin wanda basamin ni kuma innakoma sai insaka ta agaba ince sai tagaya min amma bata gaya min muna haka wataran wani saurayin yarinyar gidan muna mutunci dashi wani zuwa da yayi sai ya tarar sundakenin yatadda ni ina kuka anan yake tambayata nikuma na bashi labarin halin da nake ciki shine yace zai daukeni yamayar dani gidan su da farko kakata taki amincewa sai da kyar de ta amince zamu koma aranar da zamu koma kuma wasu mutane suka shigo gidan sukayi min duka har suka kusan kasheni suna cewa wai ai kakata ta basu abun dasuke bukata in bahakaba kuma zasu kashe ni nan tace musu zata basu amma duk da haka saida suka dakeni suka bugan wani abu su atunanin su ma na mutu, daga nan bankara sanin halin da nake cikiba sai bayan wasu kwanaki danayi a asibiti......labarin de duk abun da yafafu da ita tundaga farko har karshe tabasu bata boye musu komai ba har labarin da dadda tabasu da barin ta gidan su bossay har kawo yanzu zuwanta gidan su sama da sacetan da akayi da gargadin da matar nan tayi mata zuwa fitowar su har kawo yanzu da meer ya taimaketa ahannun mutanen nan, gaba dayan su jikin sune yayi sanyi sun tausaya mata sosai maama kam harda kuka ummy ma saida ta zubar da hawayen tausayin ta yarinya karama da ita amma ta tashi cikin rashin gata,  tunda take ma ita bata taba jin labari irin wannan ba sosai labarin ya girgizata, saida suka gama koke koken nasu sannan Abu yace ummy "a labarin da tabayar kamar sunyi kai daya da labarin da mutanen nan suka gaya min lokacin da suka kawo maama  suma sunce ai tare da yaro aka ganta mutumin da yakira su sukadauketa suka  kaita asibiti tundaga lokacin baisake dawowa ba, kunga kuma gashi itama haka tace labarin nasu kamar yayi daidai da hakan amma de kar mu yanke hukun ci maama ki fara bamu naki labarin muji, maama da tunkan tagama bada labarin tasan ma dole wannan jikartace yaron da ake nema kuma danta kuma tagane babu wanda sukayi mata haka sai yan gidan su duk yanda akayi yanda aka koreta daga gidan shiyasa ake so akashe duk wani jinin ta sai yanzu take tunanin tun farko ma cikin ra da yaringa zubewa da sa hannun wani aciki saboda ba aso ta haihu da Allah kuma yayi sai ta haihun sai suka sace mata danta na farko da takara haihuwa kuma suka hada da ita da dan suka rabata daga cikin gidan tabbas bazata daga kowaba duk wanda yayi sanadin barin gidan mijin ta kuma ya rabata da yayan ta saitaga bayan koma waye, Ummy ce ta kalli maama dataga gaba daya hankalin ta baya tare da su ta katseta da cewa "Maama muna sauraron ki kinyi shiru bakice komai ba, kallon ta maama tayi sannan ta mike tsayi tare da harde hannuwan ta akan kirjin ta tana kallon su daya bayan daya said tagama kare musu kallo cike da dakakkiyar murya tace, "Ni haifaffiyar garin Egypt ce kuma iyaye na ga a dayan su Allah yayi musu rasuwa tun ina yar karamata sukayi accident suka rasa rayukansu, a hannun kanin mahaifina na taso,   aure ne yakawo ni nan na hadu da mahaifin su acan garin lokacin da yake karatu alaokacin da yanuna yana sona da aure kawu na yaki amincewa har saida iyayen su sukaje suka saka baki sannan ya amince ko shekara banyi ba da aure shima ciwon siga ya kasheshi matar sa bata da mutunci daman bata sona bata son zaman gidan danakeyi dan de bayanda zatayi ne yasa take zaune dani da ya mutu kuma tattara ita da ya yanta suka bar garin ma ni kaina yanzu bazan ce ga inda suke ba nima kuma banne mesuba tunda nasamu miji na yana kaunata muna zaman lafiya dashi babu wata matsala dake faruwa a tsakanin da shi hakama kuma mutanen gidan mana zaman mutunci da kowa ba wanda wani fada ya taba shiga tsakanin dasu, mijina dan sarkin garin nanne lokacin kuma da za adaura mana aure tare da sarautar sa aka daura aranar aka bashi sarautar yazama sarki kasan cewar a al'adar su ba a zama da mata daya dan haka mubiyu aka daura auren mu atare rana guda, bamu dadeba da aure na samu ciki saidai cikin baije ko ina ba ya zube nakara samun wani shima yazube tun ina hakuri har abun yafara ban mamaki na fara zargin wani abun amma kuma bansan wa yake aikata min hakan ba saboda kishiyata muna zaman lafiya da ita nasan bazata taba cutar dani ba daga baya kuma nama ajiye wannan tunanin naci gaba da rokon Allah yakara bani wani bayan kwanaki kuwa nakara samu saidai shi bai zube ba da taimakon Allah har lokacin haihuwa yayi na haifi da namiji aka saka masa sunan kakan sa sameer bayan suna da yan kwanaki na shiga wanka na barsa akan gado fitowar da zanyi naga babu shi bandamu dan duk azatona ko wanine ya shigo ya dauke sa saida na gama komai sannan nafito nake tambayar me aikina waye yazo ya dauke sa take cewa bata sani ba abu kamar wasa nashiga cigiyar sa amma kowa yace bai dauke saba sama ko kasa aka nemesa aka rasa haka nasha kukana mahaifinsa yana ban hakuri akan za ayi bincike ko sati biyu ba ayi ba aka watsar da maganar saidai nikadai inyi kukana in godewa Allah, Tundaga nan ban kara samun ciki ba  ita kuma dayar matar bata haihuwa anje asibiti ance bazata haihu ba ganin hakan yasa mahaifiyar mijina tace yakara aure haka baya so yakara auren yar kanwar kishiyar ta, bata dade da shigowa ba ta haifi yan biyu mata, "suna da wajen shekara biyu da wani abun nima nakara samun wani cikin haka naita rainon cikin har Allah yakai ni lokacin haihuwa na haifeshi lafiya qalau ranar suna yaci sunan kakan sa sameer, sameer yana da farin jini sosai yana da shiga rai saboda yana da fara'ar sa har yan biyunta suka fara girma kullum sai sunzo wajen sa tare suke wuni kuma muna zaman lafiya da kowa babu wani tashin hankali dake tashi atsakanin mu da yaran mu gaba daya, bazan taba manta ranar wata lahadi tunda na tashi da safe nake fama da ciwon kai aranar ko fitowa ma ban iyayi ba kuma babu wanda yaje inda nake daga ni sai sameer yasakani agaba yana ta kuka ganin halin da nake ciki saboda sameer akwai tausayi koya yaga kashiga wani hali yaga baka mishi dariya zaisaka kuka yana rirrikeka to ranar ma haka yayi kwance ajikina yana kuka amma nakasa tashi inajin sa kuma nakasa rarrashin sa, nayi mamakin ganin babu wanda yazo inda nake har dare yayi daman adakina sarki yake amma har dare yayi banga shigowar sa ba haka muka cigaba da kwanciya akan gado daga karshe de sameer yayi bacci yabarni ina ta fama da ciwon kai, dishi dishi nafara ganin a idona ina ganin abubuwa bibbiyu ina cikin wannan halin naji kawai ance taso nidai bazan iya tantance muryar da najiba saboda kamar de hankali na yafara barin jikina, duk son danakeyi intashi ɗazu nakasa amma anacewa taso bansan loƙacin da na tashi aka kuma cewa dauko ɗanki nan ma na tsugunna na ɗaukesa inajin wani abu yanayi min yawo akai kamar sauraye kamar ƙudaje haka naji abun kamo hannu na akayi aka fara tafiya dani nidai bana sanin ina ake zuwa dani ammade inajin duk maganar da akayi min kuma inaji ina tafiya amma banma san a inda nakeba waɗannan abubuwan kawai nake iya tunawa, ina jin loƙacin da aka sakani amota akaja aka fara tafiya bana iya gane hanya kuma bana gane mutanen da suke tafiya damu acikin motar duk da inajin muryoyin su amma sai inji kamar waƙa kamar ihu haka kawai nake jin muryoyin nasu bana tantance me suke cewa, ji nayi andena tafiya sai aka buɗe motar kawai naji anturoni daga cikin motar aka ƙara turo Sameer dake ta bacci banma sani ba ko loƙacin bayama cikin hayyacin sa shima daga nan banƙara sanin inda nake ba saida gari yayi haske rana ta hasken idona tashi nayi sai naga sameer agabana yayi tagumi yana kallona gaskiya aloƙacin da na tashi bana iya tuna komai da kowa ammade ina ganin sameer amatsayin sa na sameer amma ni kaina bansan me mukeyi ba awajen ba kuma inaso inyi masa magana amma nakasa sai na buɗi baki zanyi magana sai inji kamar anɗaure min harshena haka natashi daga gurin gurin babu komai kamar ma daji kawai na ɗaukesa muka fara tafiya dashi bansan inda zamu ba kawaide tafiya muke har nazo wajen da naga mutane na ɗan wucewa wajen shine naje wajen wata bishiya nazauna nariƙe sameer akan cinyata kawai ina bin mutanen gurin da kallo har dare babu wanda ya kulamu gashi yunwa nakeji kuma ga kuma Sameer da shima yana tamin kukan yunwa amma nakasa buɗar bakima bare in rarrasheshi ahaka muka kwana baci ba sha sai da safe wani yabamu abinci amma sai nakasa ci kawai saidai inbashi shi yaci ina son ci amma yagagare ni,  ataƙaicedai bansan adadin kwanakin da nayi awajen ba, inajin ranar da abun yafaru aka bigeni ina tunawa natashi daga barci na hango sameer can shida wani mutumi  kamar zai ɗaukesa nikuma na tashi da sauri dan inje inɗauko sa ina hawa kan titi naga wata mota duk da bana cikin hankalina sosai amma da naga motar sai naja dabaya ina kallon nacikin motar sai kawai naga yayi dariya tare da nufo inda nake duk da ba asaitin sa nake ba nikuma sai na tsaya naci gaba da kallon sa daga nan kuma bansan me yaƙara faruwa ba sai ranar da na farka awajenku..........✍️👍✍️ kuyi haƙuri da wannan ɗan Allah wallahi yau kwata kwata banajin daɗi, amma gobe in sha Allah zanyi ƙoƙarin yin me yawa.,                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/7, 7:59 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 83 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ _______*sam*_______     Adai adai ƙofar gidan su sumy yayi parking ɗin motar sa sannan ya fito daga cikin motar yana fitowa ya jingina da jikin motar wayarsa ya ƙara ɗaukowa ya gwada number ta amma still akashe yanzu ma bata shiga ba mayar da ita yayi cikin aljihu sannan ya ƙarasa bakin gate ɗin ya kwankwasa tsawon minti biyu yana gurin ba abuɗe ƙara bugawa yayi amma ba abuɗe ba saida yayi wajen minti goma da wani abun ba abuɗe ba da yagaji da tsayiwar sai ya koma cikin motar zuciyarsa duk babu daɗi kawai kukan tane yake masa yawo akai yana tuna marin da yaji anyi mata runtse idonsa yayi jin marin acikin kansa kamar yanzu akeyin sa haka yake jin ƙarar sautin sa, buɗe idonsa yayi da har sunfara canza kala damƙe hannun sa yayi tare da kaiwa stirring ɗin motar duka, yana zaune acikin motar yakasa tafiya daga ƙarshe ma kifa kansa yayi akan stirring ɗin gaba ɗaya yakasa gane kansa ji yake bazai taɓa iya tafiya ba batare da yaganta ba, ihunta yaki ya daki kunnen sa kamar daga sama da sauri ya ɗago dakan sa zuwa inda yajiyo sautin nata, idonsa ne ya sauka akan ta anturota daga cikin gidan tare da watso mata kaya ajiki tashi ta ƙarayi daga faɗuwar da tayi ga ƙara nufar bakin ƙofar, da sauri ya buɗe motar ya fito ya nufi wajen, Wallahi sai kinbar gidan nan bazan iya cigaba da wahala dake ba kina lalatamin ƴaƴa ba tunda uban naki ya gudu yabarmu sai kikama gaban ki daman arziƙinsa kike ci tunda kwa yanzu baya nan dole kema kiyi gaba sai kije kicigaba da karuwan cin dakikeyi kamar ya da uwarki take sai kije ki tayata dama tasamu da ina hanaki bakiji to yanzu na buɗe miki ƙofa kije duk inda zaki ai ku abun kunya gaba yabaku ba baya ba shegiya matsiyaciyar ƴar gidan karuwar masu baƙin hali, sai faman cimata mutunci take awaje, Ita kuma sai faman kuka tana roƙonta amma bata saurare taba tana gamawa ta koma ciki tare da banko ƙofar gate ɗin ta rufe, bakin gate ɗin sumy taje ta tsugunna tan ƙara fashewa da matsanancin kuka ita yanzu idan ma ta tafi ina zata babu wanda ta sani bata da kowa, duk abun da ke faruwa gaba ɗaya akan idon sam jin maganganun matar ya hanashi ƙarasawa wajen sai yanzu yafara takawa ahankali zuwa gurin ta zuciyarsa nayi masa wani irin suya tausayin tane yakama sa duk rashin tausayin sa yaude yaji wani irin mugun tausayi akanta, tsayawa yayi abayanta tsawon ƴan mintina baice komai ba, batare da yace komai ɗin ba yaɗan ranƙwafa kanta yasa hannu gaba ɗayan ta ya ɗago da ita ya tsayar da ita tsaye, atsorace ta juyo dan ta tsorota saboda batasan da zuwan saba gurin suna haɗa ido dashi tagane sa ai tunkan ya buɗi bakima yayi magana ta faɗa kansa ta rirriƙe sa tasake fashewa da wani kukan da yafi na ɗazu ita kanta batasan dalilin yin irin wannan kukan da tayi ba yinsa kawai take ba ƙaƙƙautawa hannun sa ya ɗaga zai ɗora abayan ta sai kuma yafasa yayi hakan wajen sau uku yana kai hannu yana janyewa da ƙyar de ya rufe ido ya ɗora hannun sa akan bayanta shima ya rungumo ta atare suka sauke numfashi, ahankali ya shiga bubbuga bayan ta alamar rarrashi baide ce mata komai ahaka suka cigaba da tsayiwa awajen ba wanda ya iya cewa komai, ganin taƙi shirun ne yafara ƙoƙarin ɗago da ita daga jikinsa amma saita ƙara riƙeshi zuwan shi ba ƙaramin taimaka mata yayi ba daman tana son ganin sa sai gashi yazo adidai loƙacin da take buƙatar sa, jin ta riƙeshi bai takura mataba wajen rabasa da jikin nasa ba ɗan ɗagata yayi kaɗan yarabata da jikin sa  ahaka tana jikin sa yafara takawa da ita ya nufi wajen motar sa da ita, yana zuwa ya buɗe gaban motar yasaka ta aciki sannan ya zagayo shima ya shiga yana shiga kuma baicemata komai ba haryanzu ya tayar da motar kawai yayi rivers yabar unguwar da ita......... _____*shettima& Azeema*______    cike da tsoro take binsa da kallo, shikuma yana takowa wajen ta yana sakin murmushi ganin yanda ta tsure ta zazzaro ido sai abun yasa shi nishaɗi hannunwa a harɗe akan kirjin sa yake takawa zuwa wajen ta, ganin yakusa zuwa inda take yasata fara ja da baya da baya shi kuma yaci gaba da binta ahaka suka cigaba yana binta tanayin baya har suka kai ƙarshen bango sannan ta dakata da tafiyar matsowa yayi jikin ta sosai har tana jin saukar nufashin sa akan fuskar ta,   cikin wata irin murya da ita kanta batasan loƙacin da tayi taba tace "Please stop it tayi maganar can ƙasa ƙasa ƙurawa fuskar ta ido yayi yana kallon bakin ta da tayi maganar dashi wani abu yaji ya taso masa tundaga kan yatsan ƙafar sa har tsakiyar kansa ahankali ya lumshe idanun sa tare da buɗe su aloƙaci ɗaya ya saukesu akanta haɗa ido sukayi tayi saurin janye idon ta daga garesa ganin wasu abubuwa da suke fitowa daga idon sa suna shiga nata dan haka bazata iya jurar kallon nasaba, raɓawa tayi ta gefen sa zata wuce yayi saurin tare ta ɗayan gefen ma ya tare da ɗayan hannun sa maganganun su sam me ya shiga dawo masa arai saurin kawar da tunanin yayi, tagaji da abun da yake mata duk yabi yasakata awani hali ya hanata tafiya, buɗar baki taƙara yi kamar yanda tayi magana ɗazu haka yanzuma ta ƙara yi cikin sanyin murya me kama da shagwaɓa tace "pls kabar ni intafi aiki fa nake na roƙeka plsssss, yanda ta ƙara yin maganar tama fi ta ɗazu sakashi a wani halin, "kinga yace da ita, dagowa tayi tana kallon sa cikin marairacewa da murya yace nima plss sau ɗaya kawai da mamaki take kallon sa batare da tace komai ba me yake nufi da sau ɗaya kawai dan haka sai tayi shiru bata basa amsa ba ta juyar da kanta gefe, hannu yasa ya juyo da fuskar tata suna fuskantar juna ya ƙura mata ido itama shiɗin take kallo yanzu bata janye ba, da ƙyar ya buɗi bakin sa yace "kibani dama plsss ya faɗa yana lumshe ido yana buɗewa, duk da batasan me yake nufi ba amma sai ta shiga girgiza masa kai.. wallahi ranki ya daɗe suna ciki yanzu nan fa yace infito daga ciki kuma ita baice ta fito ba shiyasa nayi gaggawar sanar dake saboda kizo ki kallewa idanun ki ganin ya kori ji, atsorace Azeema ta kalle sa tace wayyo Allah na kajawo min masifa dan Allah kafita kar suzo sutarar damu ahaka, ko gezau bayi ba saima ƙara matsawa dayayi jikin ta ya mannata da jikin sa, kuka tashigayi masa tana roƙonsa tana ƙoƙarin kwace jikinta amma ya hanata damar yin hakan, da ƙarfi fulani ta turo ƙofar ta shiga ciki, kitchen ɗin ta shiga bi da kallo sai ta juyo ta kalli me aikin da alamar tambaya a cikin idon ta, kafeta da ido Fulani tayi kafin tace ya banga kowaba kinsande babu abun da nafi tsana arayuwa ta kamar ƙarya baki tabbatar ba kikaje kika taso ni har inda nake   girgiza kai tana cewa wallahi ba ƙarya nake ba ta faɗa tana  bin kitchen ɗin da kallo tana inda inda tace wallahi Allah anan nabarsu dakansa ya koreni daga ciki itama kuma tana ciki ya rufe ƙofar tayi maganar tana rarraba ido da tunanin to ina suka tafi sunsa taji kunya  ance ƙarya take, wallahi saidai idan ɓuya sukayi amma suna cikin nan gurin ni nasan basu fita ba bari induba ko ina suna cikin nan ba inda sukaje, "kin tabbata suna cikin nan? "eh wallahi" su Azeema dake laɓe abayan ƙofar store  ɗin kayan abinci dake kitchen ɗin tunda sukaji muryar su dab da shigowa cikin kitchen ɗin yayi sauri yajata suka shige suka ɓuya, Azeema jin batun za afara dubawa ta tsure saura kaɗan ta saki fitsari jikin taba ɗaya ya ɗauki ɓari,   ahankali yace "ke ki nutsu babu abun da zai faru baza sugan muba, "Wallahi sai sun ganmu gashinan fa zasutaho wallahi duk kai kajamin nashiga uku jin zata tona musu asiri yayi saurin toshe mata baki da hannun sa shi ba tsoro yake jiba kawaide yasan idan aka gansu abun akanta zai ƙare kuma ya ƙudartu niyar wallahi sai yaci uban matar nan da taje ta faɗa ma fulani gobe ma idan akace taje tayi munafurci bazata yiba ko aiken ta akayi bazata faɗa ba, ɗan ɗaga murya Fulani tayi tace "tunkan ku wahalar dani wajen neman ku inkunsan kuna ciki kuyi gaggawar fitowa ku amsa laifin ku idan kuma ba hakaba kuka bari na nemoku da kaina to bazakuji da daɗi ba nagaya muku, sosai Azeema ta ƙara tsurewa ƙafafun ta har suna karkarwa zasu kasa ɗaukan ta sanin halin ta kuma tasan tabbas aka duba sai ankama su,kuma abun da tafaɗa sai ta tabbatar dashi musamman ita dan tasan ba lalle shi a hukuntashi ba kamar yanda za a hukun tata, dan haka tunkan ake ga nemosun ta yanke shawarar tayi magana kawai aji inda suke wataƙil idan tayi haka hukuncin yazo mata da sauƙi kamar yanda taji fulanin ta faɗa, dan haka ta buɗe baki zatayi magana tunkan ta idasa buɗe bakin shettima da ya fuskanci abun da take shirin yi,shima atsorace yayi saurin ɗora bakin sa akan nata dan ya hanata damar yin maganar... zaro ido tayi aranta tana ayyana lalle wannan mutumin bashida saiti su da suke cikin wannan halin na tsaka me wuya amma yakeso yaƙara jawo musu wani laifin yanzu idan aka gansu ahaka da da wane ido zata kalli mutane, ƙoƙarin ƙwace kanta tafarayi ya riƙeta sosai gudun kar ta tona musu asiri shi kansa zaiji kunya idan hakan ta faru......., me aikin ce ta fara takawa taje ta leƙa wani lungu dake gefe can kitchen ɗin sannan ta leƙa ta ƙofar waje ko zata gansu amma bata gansu ba, Fulani kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......😜😜😜 Kai wannan page ɗin akwai yawa nasan kowa saida yagaji da karanwa 😬 ku jinjina min                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/8, 9:24 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 84 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ ____HAMZA___ tun loƙacin da yataho ruwa na dukansa ya ƙarasa ɓangaren su ɗakin su yashiga yana shiga ya tadda baba azaune wajen sa yaje ya tsugunna duk da kayansa sunjiƙe amma hakan baidamesa ba burinsa kawai ya bawa baba labari, gyara zama yayi yana washe baki kamar gonar auduga yace "baba albashirin ka? baba shima yana kallon sa da ƴar fara'ar sa akan fuskart yace "goro" "baba yau munyi magana da ita har waje tafito wannan ruwanne ya hanamu yin soyayya amma de nace mata zan koma idan ya ɗauke kuma tace to sannan kuma na sanar mata dakai zaku gaisa ɗin anjima ta amince, sosai baba yanuna masa jin daɗin sa akan nasarar da yayi yau,   ,"gaskiya nataya ka murna Allah yasanya alkhairi Allah yasa matar kace yanda kake sonta Allah yasa itama tasoka,   "Ameen' Ameen" baba Allah ya amsa , ince dai ba dole kayi mata ba ya akai ma ta amince dakai yanzu bayan kace koda yaushe wulaƙantaka take? hmmm baba bawa ai ba a cewa komai kaide kawai kacigaba da tayani addu'a amma yau ai har marin da ba ayi min ranar nanba shi aka sauke min yau, "mari fa Allah dagaske kake wai mace ce ta mareka lalle so ba abun da bayasawa nikam dole inga wannan yarinyar da takeyi maka abun da kaga dama kuma karabu da ita lalle ta ciri tuta jarumi guda irin ka ta ɗaga hannu ta mare ka? "hmmm baba abar maganar kawai nidai yanzu ka shirya anjima da yamma zamu ƙara komawa, "to Allah yakaimu ammade wannan abu yaban mamaki wallahi mari tabb, "baba dan Allah kabar maganar nan wai sai nanatawa kake ni banɗauke sa komai ba dan ko zafima banji ba, burina kawai ta kulani kuma ta kulani naji daɗi kuma anjima ma zata kulani, bai basa labarin yanda sukayi da fulani ba, "baba yace "natayaka murna sosai  Allah yakaimu jimawar da rai da lafiya, "yauwa baba Ameen abun da nakeso inji kace kenan, tashi yayi daga gurin ya hau cire kayan jikin sa sannan ya canza wasu busassun yayi kwanciyar sa yana ta tunanin yanda sukayi da fulani shikenan yasan yanzu duk sanda yake buƙatar ta zai ganta akoda yaushe wayyo daɗi zai ringa kasancewa da ita koda yaushe, baba na kallon sa duk abun da yakeyi amma saidai kawai yayi murmushi yana jinjina irin son nan da yakewa yarinyar nan abun har mamaki yake basa........   'Fulani  kuma ta shiga takawa zuwa ɓangaren store ɗin tana zuwa ta tura ƙofar store ɗin tare da saka ƙafar ta ɗaya aciki......✍️ da sauri me aikin nata ta taho dan itama ta leƙa saidai cikin rashin kula tabi ta wajen sa Azeema take wanke wanke kuma ta zubar da ruwa agun dan haka tana takawa ta ta zame ta faɗi ji kake timmm ƙatuwar mata aƙasa ta faɗi da bombom ɗin ta tayi zaman dirshen agun, ihu tasaki me ƙara sakamakon zafin da taji abombom ɗin nata, hakan da tayi ya dakatar da fulani daga ƙoƙarin shiga store ɗin datake ta juyo dan ganin abun da ke faruwa, azaune ta ganta tayi zaman dirshen tana wurwur ga ido kamar na mujiya, fulani tace "me yasameki kikewa mutane irin wannan ihun? haba murja sai kace wata ƙaramar yarinyar... kinsan dai bana son haniya da yawa bare kuma aringayi min ihu aguri, "fɗuwa nayi  nataho da sauri  ban kula da ruwan ba na zame,   fulani tace to ai sai kitashi tunda ba wani ya yarda keba gobe idan kin taho sai kiringa kallon gabank...... bata ƙarasa ba sakamakon jin ringing ɗin wayar ta dake hannun ta yasata katse maganar da takeyi, duba wayar tayi dan ganin me kira da sauri ta ɗaga kiran saboda daman shi take jiran  tsammani tunɗazu, tana ɗagawa tayi saurin ficewa daga kitchen ɗin har tana haɗawa da ƴar sarsarfar ta gurin yin sauri, taƙaicine ya ishi murja yanzu ta faɗi maimakon tayi mata sannu amma saima faɗa da zata hauta dashi sannan kuma tayi ficewar ta saboda bata da tausayi, da ƙyar ta iya yunƙurawa ta miƙe tsayi azaba tasama ta manta da waɗanda take nema daman ta gama girkin da takeyi jerasu yarage dan haka kawai itama tafita daga kitchen ɗin dan sai taje tayi jinya kafin ta iya ci-gaba da aikin..... duk abun dake faruwa akan kunnen su Azeema dan haka suna jin fitar su Azeema tafara ƙoƙarin ƙwace kanta sakin ta yayi yana kallon ta itama shi take kallo sai tayi saurin janyewa saboda hakannan sai tafara jin kunyar abun da yayi mata yana ganin haka yasaki kayataccen murmushi sannan yace ,"matsoraciya kawai daman haka kike da tsoro to wallahi ki rage tsoro, bata ce masa komai ba ta ɗago ido ta hararesa tare da cewa ni matsamin in wuce wallahi kar ka ƙara zuwa inda nake bazakajamin bala'i ba ina zaman zamana inji da abun da yake damuna ma basai ka ƙara da naka ba, "au hakama zakice ko danma kinsamu na taimakeki shine kuma yanzu zaki min rashin kunya to wallahi inbaki bini ahankali ba sai in ƙara wani yanzu kuma inbari har sai kowa yazo ya ganmu ahaka ana tambaya kuma ince ke kika jawo ni, "inbaka fasaba dake su basu da hankali sai su yarda dani najawo ka ƙarfinka nafi da zan iya jawo ka kuma ka biyo ni ai duk wanda ma kagayawa wannan abun babu wanda zai yarda dakai saboda wannan ai maganace da ba wanda zai yarda, "haka kika ce to bari inyi sai mugani, "wai me zaka ƙara yi? kashe mata ido ɗaya yayi yace "shan sweet sweet ɗin nan akwai daɗi yafaɗa yana ɗora hannun sa akan lip ɗin na ƙasa yaɗan shafa shi, wani irin yam taji jikin ta yayi mata da sauri ta kai masa duka a hannun tanaso tayi magana amma takasa sai faman hararar sa take kamar idon ta zai faɗo, dariya yayi kawai tare da cewa "kinaso kina kaiwa kasuwa ko to shikenan zo ki wuce kar na ɗora ki akan network dan naga kina niyar hawa, matsama ta yayi batayi wata wata ba tabi ta gefen sa ta fita  kuma bata gane ma network ɗin da yake nufi ba kawai itade burin ta ta fice daga gurin, tana fitowa shima yafito akusan tare suka fito, tayi wajen wanke wanken ta tana Allah Allah tayi sauri tagama kar fulani ta dawo ta ganta a kitchen ɗin, da har zai ƙara zuwa ya takura mata sai kuma ya tuna any time fulani zata iya dawowa kuma baisan hakan ta faru dan haka sai yayi saurin fita daga kitchen ɗin yana daf da fita daga falon saiga murja ta fito daga ɗakin su caraf kwa idon ta ya sauka akan sa shi baiganta saboda yajuya baya kuma har yafita bai san da itaba da yazo yayi mata gargarɗi, tana ganin fitar sa ta girgiza kai tare da saurin nufar kitchen dan taga Azeema na ciki tana leƙawa kuwa ta ganta a tsaye tana wanke wanke ƙarasa shiga tayi har gaban ta sannan tace "ke munafakar ina ce ina kuka shige daman nasan kuna ciki ɓuya kukayi  ke ƴar iska ce ban saniba daman daga kallon idon ki nagane fitsararriya ce ke bada abun kima har kinkai matsayin da zaki kula ɗan masu gida ke asuwa to wallahi sai na sanar da ita anɗau ƙwaƙƙwaron mataki akanki zama masarautar nan sai ya gagareki daman duk wani take taken ki akan idona kikeyin sa kuma ina nan tara ki nakeyi akwai ranar ƙin dillanci kicigaba daga inda kika tsaya kar kifasa, duk wannan abun da take ko ɗaga ido ta kalle ta Azeema batayi ba tacigaba da aikin da take har tagama murja na gurin tana surfa mata maganganun jin taƙi kulata yasata taita fusata tanajin haushin abun da tsanar yarinyar.........,, ita kwa Azeema tana gama wanke wanken ta daman ta kusa gamawa basu abu uku ne suka rage mata tana gamawa tayi ficewar ta tabatar da luguden laɓe a kitchen ɗin,....... Fulani can uwar ɗaki ta shige gudun kada wani yaji wayar da take, cike da damuwa akan fuskarta tace Hajiya sarah kinsan tunyaushe nake neman layin ki yaƙi shiga sai ɗazu dana gwada naga ya shiga ke kuma baki ɗaga ba, daga can ɓangaren Hajiya sarah tace gode yanzu bagashi na kiraki ba gaya min me yake faruwa kike nemana haka, kinsan tun ranar da nazo gidan ki washegari nabar ƙasar sai shekaran jiya nadawo, ajiyar zuciya Fulani ta sauke sannan tace gode yanzu duk ba wannan ba ina cikin tashin hankalina ga ɗaya baya jikina akwai matsala fa, ina jinki ai daman tun ranar danazo nasan za asamu matsala tunda saida nagaya miki tunwuri ki gaggauta korar wannan mutumin danagani amma kika ƙi matsala kwa ai yanzu kika fara gani muddun yana cikin gidan nan, "nifa ba wannan ne matsalar ba bana ta wannan danni ba matsalar da na fuskanta daga gare sa, "to meye matsalar? Hajiya sarah ta tambayeta, gefen gado fulani tasamu ta zauna sannan tace matsala ta wani yaro ne da acikin masarautar nan kuma bawa ne tun yana ƙarami yake cikin masarautar nan loƙacin da yazo kamar almajiri wani tsoho yakawowa sarki shi yace ya taimaka masa asamawa yaron aiki bashida kowa shine fa sarki ya karɓesa  yazama bawa, amma yaron nan tunda yafara girma na fahimci yaron taurin kaine dashi baya nuna tsoro ga kowa haka yaron yake to daga baya kuma rashin mutuncin nasa ya wuce kan kowa har yafara dawowa kaina idan nayi magana bayajin maganata idan hukunci nasa ayi masa sai tsoratar da masu hukunci idan dukane baza adake saba idan wani hukuncin ne sai yayi tafiyar da yace bazaiba har da kaina naje inda suke nayi kiran yaronnan amma yaƙi zuwa abun idan nazauna ina mamaki sosai me yaron nan yake taƙama dashi da yake min irin waɗannan abubuwan abun na damuna narasa yanda zanyi dashi yafi ƙarfin kowa, to babban abun da yayi min na ƙarshe ɗazu ɗazunan shi yafi komai tsaya min arai ya firgita ni sosai ina cikin nan nida wata me aiki sai ya shigo ciki kansa tsaye ko sallama babu kuma da takalmi yatako har inda muke sai ya tsaya wai yanason magana da mai aikin abun yaban mamaki sosai natsaya inga iya gudun ruwansa dana ga abun nasa yayi yawa natashi tsaye zan maresa sai yariƙe min hannu, "ataƙaicedai hajiya sarah da na takurawa yaron nan nayi masa barazana ai sai ya dawo min da tasa barazanar da ta taka tawa ninkin baninkin, "tofa lalle wannan yaron da abun da yataka amma de kaini ƙarshen labarin.... hajiya sarah keyin wannan maganar, "hmmm fulani tace kedai bari ai bangama kaiki ba, "kinsan me yace min, "a'a" wai duk abun danake atafin hannun sa idan nayi wasa sai ya fasa siriina kowa yaji abun da nake ɓoyewa tsawon loƙuta, dan haka kar nasake ɗaga masa yatsa ko in ɗaga masa murya abuɗe yaringa gayamin yana gamawa ya fice abunsa babu ko ɗar, abun ya mugun ɗaure min kai shin shiɗin waye dan ina tunanin ma loƙacin da abunnan yafaru wataƙil ko haifar da ba ayiba inma an haifeshi to bashi da wayo ƙarewa ma kuma baizo nan gidan ba to a ina yaji waya basa labari, wannan sirrin dai nasan daga ni sai ke sai mutum ɗaya shima kuma yanzu baya raye to ta ina maganar nan tafito abun ya ɗaure min kaifa sosai, dariya Hajiya sarah tasaka mata wanda har tana jiyo sautin ta da mamaki take bin wayar da kallo kamar Hajiya sarahn ce agabanta, saida tabari ta tsagaita dariyar dan kanta sannan tace "lafiyar ki ƙalau kuwa yaza ayi ina gaya miki damuwata amma kina min dariya kuma...... hhhhhh Hajiya maryama ai dole inyi dariya wallahi kinban dariya sosai yanzu banda abunki dan Allah ina tunanin ki yatafi yanzu wannan ɗan abunne zai sakaki adamuwa kinajin maganarsa ai kinsan kawai barazanace ba gaskiya ba ta ina zai sani kawai bugar cikin ki yayi saboda ɗan duniya ne yayi miki haka dan yagane lagonki kuma yagane kinyi ganganci da kika nuna masa kinji tsoron sa yayi galaba akanki ko kinji yace ga abun da kike ɓoyewa?   "A'a kawaidai ca yayi zai tona min asiri ni kuma nasan inada sirrin shiyasa nayi tunanin ko shi yake nufi, "to gaskiya kinyi kuskure har ɗan yaro yafiki wayo yasan yanda zaibi ya tsoratar dake, to wallahi tun wuri ma kisan yanda zaki ɓullo masa ki nuna masa asalin kalar ki, ki dakatar dashi daga abun da yakeyi ko kuma abu me sauƙi ma kifata daga harkar sa kar kishiga harkar sa bare har yasamu dama yaci gaba da tsoratar dake tunda de fitinanne ne zai iya jawo miki wata matsalar nan gaba tunda kika nuna masa kin tsorata akwai sirrin kenan kinga daga nan zai fara ƙoƙarin bincike akanki har ya tabbatar da abun da kike ɓoyewa ɗin kuma yana sani tofa ba shakka kowa sai yasan abunnan gwara jini dashi ku rabu lafiya da dayanda zakiyi ma da kinsa an fitar dashi daga gidan dan wannan zama dashi haɗari ne dan sai yayi abun da baki taɓa tunanin ba, sai yanzu fulani ta ɗanji dama dama aranta duk atunanin ta yaron nan da gaske yasan sirirrin ta ashe duniyan ci kawai ya nuna mata, "to yanzu ya kike gani zanyi dashi inbarsa yaci gaba da zama bakya ganin idan na Kore shi zai iya yimin wani sharrin ma ko kuma yayi wani abun da zai cutar dani bakiga fa yaron ba wallahi bayajin magana zai iyayin komai tunda kikaga kaf cikin masarautar nan kowa na tsorona amma banda shi ai kina kwa banga wanda zaiji tsoro ba suma kansu ƴan gidan tsoron sa sukeji dan wani daga cikin su ya taɓa ban labarin dukan da yayi musu shiyasa suke shakkar sa kuma wallahi duk daga baya ya tsiro da waɗannan abubuwan da ba yayi ammafa ina tunanin anya ba wannan tsohon da kika ce in kora bane yake zugashi  saboda kullum suna tare yanda ba ataɓasa haka yakafa ya tsare babu wanda ya isa ya taɓa tsohon nan, "afff bana gaya miki ba kince ai shi baida matsala zancen kenan ki koresa shine abu mafi sauƙi shikuma yaron kawai kibarsa yaci gaba da zamansa amma karkiringa takura masa da zaisa ya fusata yaje yayi muku wani abun kawai kurabu dashi kifita daga harkarsa, "to shikenan nagode da shawarar ki har kinsa na ɗanji sassauci amma wallahi da gaba ɗaya hankalina ya tashi amma yanzu kin kwantar min dashi shiyasa akullum nake sonki akusa dani saboda kinfini tunani me kyau ina ƙara godiya sosai sai kinji alart dan wannan shawarar dole inbaki tukwicin ta, "ba komai wallahi ai kinfi ƙarfin haka agurina wannan ba komai bane Allah ya tsare nan gaba nagode noma sai najiki, "in sha Allah kwa yanzunnan zakijini, daga nan sukayi sallama kowa ya kashe wayar, atake ta tura mata maƙuden kuɗaɗe ta account ɗin ta sannan ta tashi zuciyar ta fess bawani taƙaici ta faɗa bathroom saboda futsarin da take taji tunɗazu tashin hankali ya hanata yi..., *Sam* tunda suka fara tafiya babu wanda yasamu damar yin magana kowa da abun da yake tunani har suka ƙaraso wani babban gida horn yayi me gadi ya buɗe suka shiga ciki a parking lot yayi parking sannan ya buɗe ya fito daga motar yayi sauri yazagaya ta inda take yasa hannu da kansa ya buɗe mata ƙofar tare da miƙa mata hannu, nata ta ɗora akai yakamota yafito da ita daga cikin motar, hannun sa riƙe da nata suka nufi cikin gidan bayan sunyi sallama aka amsa musu suka shiga cikin falon gidan, saida suka shiga ya sakar mata hannun, wata mata nagani a hakimce akan kujera hannun ta riƙe da waya tana lallatsawa ba tsohuwa bace kuma baza kace mata yarinya ba kanade ganin ta kasan ta manyan ta sosai, jin murayar sa yasata ɗagowa tana ganin shine ta faɗaɗa fara'ar fuskarta tana miƙewa tsayi tare da cewa oyo oyo wata sabon gani kode ɓatan hanya kayi baka saniba shima fuska aɗan sake yace inajin dai nayi ɓatan hanyar bari injuya wataƙil bana nan bane yafaɗa tare da ɗan juyawa kamar zai koma tayi saurin dakatar dashi murmushi sukayi gaba ɗayan su sannan yasamu kujera yazauna  itama zama tayi sannan suka shiga gaisawa cike da kewar juna na andaɗe ba ahaɗu ba, tace "wallahi yaron nan baka da kirki yanzu ga baki ga hanci amma sai infi shekara bangan ƙeyar kaba acikin gidan nan, "kinsande ai ba agarin nake zama ba kuma idan nazoma bawani daɗewa nake ba, nake komawa shiyasa, "daman haka kake cewa kullum idan anyi maka magana yanzu ko kwana 2 kake a garin bazaka iya bada awa ɗaya ba kazo mugaisa ba bare ma kanafin kwanakin 2 bade kayi niya ba kawai, "tode yanzu kiyi haƙuri hajjaju abar abun da yariga ya wuce tundade yanzu gani agabanki,   "kace haka mana yanzn ma ni banyarda dakai ba nasan wani abunne yakawo ka, "aidai nazo ke nifa idan kika takura min sai intashi in tafiyata, "hmmm to ai shikenan nayi shiru da bakin amma kuma wannan yarinyar fa bansan taba a ina ka samota, kallon sumy yayi da ta wani takure guri ɗaya tunda ta suka shigo ta gaida matar bata ƙara ko motsawa ba kamar wacce take a tsorace haka take zaune awajen, "wannan baƙuwa ce nakawo miki ita, ɗan harar wasa tayi masa tace" bangane baƙuwa ba  kode sirikar ce sai yanzu Allah ya kawota, "kinga matsalara dake kenan shiyasa bana son zuwa wajen ki to ba wata sirika tana cikin wani haline shiyasa nakawo ta nan ki ɗan riƙe min ita kafin nan da wani loƙaci zanzo na ɗauketa, yanzu de bani da loƙacin yi miki bayani zan dawo gobe sai muyi maganar, "tofa wane irin hali kuma ai yau yakamata kayi min bayani ko sai infi jin daɗin zama da ita amma kawai ka kawota kace zaka wani dawo gobe salon innemeka in rasa dan nasan halin ka bakada tabbas, "Allah hajjaju zan dawo tunda nafaɗa yanzu sauri nake ne zanje wani wajenne shiyasa nabiyo nakawo miki ita kuma nasan ke kaɗai ce zaki iya yimin wannan abun, "nifa bana son wani daɗin bakin ka daka saba yi min amma de shikenan na rabu dakai kaje kadawo ɗin ina jiran ka, "yauwa hajjajuna nagode bari inje yafaɗa tare da muƙewa tsaye sannan ya kalli sumy da takejin kamar tace masa bazata zauna ba amma ba hali dole ta zauna duk da bata san ko ina ne yakawo ta ba tade san kawai bazai taɓa cutar da itaba, "kizauna anan zan dawo gobe zamuyi magana dake kisaki jikin ki anan wannan kakata ce bakida matsala da ita komai kikeso ki tambayeta kinji? kai ta ɗaga masa sannan tace "nagode cikin sanyin murya, jiyayi tausayin ta yaƙara kamasa yanasane yaƙi tamabayar ta abun dake faruwa da ita saboda yasan yanzu take cikin halin ba lalle tagaya masa komai ba idan ma zata gaya masa to sai tayi masa kuka shikuma bayaso shiyasa yabarta zuwa gobe koma jibi dan baya tunanin zaizo goben faɗe dai kawai yayi yasan zuwa loƙacin ta dawo cikin nutsuwar ta..., sallama yayi da su sannan yafita daga gidan, tanaji tana ganin yafita yabarta badan tasoba hakannan taji gidan bai kwanta mata araiba, yana fita hajjaju ta kalleta awani wulaƙance tace keɗin wacece daga ina ya ɗauko ki shi duk wani shirgi ya iya jajubowa kansa yarasa inda zai zuba bolar sa sai gidana, gabanta taji yafaɗi daman shiyasa taji batason gidan yanzu agaban sa ta nuna komai nml amma daga fitar sa zata fara yi mata wannan abun to inaga taci gaba da zama aikwa yana zuwa gobe zata bisa gwanda yamayar da ita gida tasaba daman da waccen wahalar amma wannan bata san ya kallar halin ta yake ba, tsawa ta daka mata "ba magana nake miki ba kinyi min shiru wata kon ga ƴar iska namiki magana ko, aɗan zabure tace "a'a " kiyi haƙuri amma nima kaina bansan ko ni wacece ba nade taso a hannun mahaifina kishiyar mahai.... "ke ke ke dakata ni ba dogon zance na tambaye kiba meye alaƙarki dashi me ya haɗaku, hawaye har yafara zubo mata  cikin muryar kuka tace "babu abun da yake tsakanin mu,   ƙarya kike banyarda ba to barima kiji ingaya miki idan ma bacci kike ki farka Sameer ba sa'an yin kibane yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba kifita daga harkar sa inma kina tunanin wani abun akansa to kicire tun kan loƙaci ya ƙure miki, shiru sumy tayi tana tunanin ikon Allah yau taga takanta daga zuwa sai faman uban surutu takeyi da wani abunma bata gane me take nufi ko wayace mata tana da wata manufa akansa shikenan yanzu mutum bazai taimake ka ba sai da wata alaƙa a tsakanin su tab aikam yazama dole tabar gidan dan bazata juri cin mutumci da zarafi ba bataji ba bata gani ba ta gwammace ta koma gida aci gaba yimata tasan wannan gidan ubantane kuma tasaba dashi, haka matar nan taitayi mata bala'i ta inda take shiga batanan take fita ba daga haɗuwa sai masifa sai kace daman ƙiris take jira, saida tagaji dan kanta sannan ta tashi tabarmata falon tare dayi mata gargaɗin koda wasa tasake ta sanar sam wani abun na lahira sai yafita jin daɗi, zaune tayi afalon duk jikin ta babu daɗi tana tunanin kode tayi tafiyar tama kawai yanzu sai kuma tayi wani tunani gwanda ta tsaya inyazo gobe sukayi maganar ita tayarda ma yakaita inda ya rufe mata mahaifi itama ya haɗa da ita ya rufesu hakan sai yafi mata kwanciyar hankali, da wannan shawarar ta barwa ranta tayi haƙuri taci gaba da zaman falon ita kaɗai, (wannan matar itace ƴar autar su Ammah ƙanwa take ga Ammah saidai ita halin su baizo ɗayaba dan bata iya zama da mutane ba ita komai sai nata idan kaga kuna shiri da ita to kai najikin tane ko kuma tana son wani agurin ka sai kaga tana nan nan dakai abun da yasa kuma take son sam shikuma saboda tanaso ahaɗa auren su da jikarta itama kaf jikokin ta tafi ji da yarinyar shiyasa take jansa ajiki wannan kenan,,           ************************ *Maama* bayan maama tagama basu labari tabari ta fashe da kuka tare da komawa kan kujera ta zauna gaba ɗayan su cike da tausawa suka shiga bata haƙuri, Ummy ce tafara magana "gskiya waɗannan mutanen basu da imani yanzu mutum da gidan mijin sa da ƴaƴan amma arabasu ta ƙarfi da yaji saboda da tsabar son abun duniya meye abun soma asuarauta nasan duk dan saboda itane suka rabaki da iyalan ki irin waɗannan bai kamata ana barin suba ai wannan abun da suka aikata miki maama bake yakamata ki ɗauki mataki da kanki ba da hukuma yakamata ahaɗasu duk wani wanda yake cikin masarautar sai ankamasa zasu fito da wanda yashirya miki wannan ƙullin kamar fa kisan kai sukai yara tun suna ciki aringa kashe su ansamu kuma ɗaya yazo duniya shima  arabasa da mahaifiyar sa wataƙil ma kuma kashe shi sukayi fa ai wallahi maama yanzunnan basai anjima ba za muje gidan mutafar musu da hukuma abi miki haƙƙin ki dan wallahi sai inda ƙarfinmu ya ƙare, ummy sai faman zuba take ko numfasawa batayi jitake kamar ita akayiwa haka ko kuma wani ɗan uwanta najiki abun ba ƙaramin haushi yabata ba, Abu ma ya ɗora da nasa nima hakan nayi tunani ai bawani ɓata loƙaci kawai muje yanzu mu shigar da report sannan mu tafi gidan ba gidan sarki ba ko gidan shugaban kasa ne yau sai hukuma ta shiga kuma anyi sharri'a ko shi sarkinne da laifi wallahi sai ankamasa tunda ga hujjoji abayyane ba a ɓoye ba, abun haushin ma indai basa sa hannun saba meyasa tsawon loƙacin nan basu nemetaba ai kamata yayi ba ko ina su baza neman ta gari gari basai iya garin suba amma duk sunyi burus to kowa sai ya kwashi kashin sa ahannu duk wani me sa hannun a al'amarin, ummy tace "dole kuwa koma waye sai anɗau mataki akansa, gashi kuma duk de mugun tarsu Allah yayi bazata mutuba kuma gashi Allah yanuna musu ishara ya haɗata da jikarta ta hanya mefi sauƙi kuma in sha Allah ɗanki bai mutu ba  sai anbinciko mahaifin ta aduk inda yake  yanda baki mutuba da yardar Allah ma gaba ɗaya ƴaƴan ki suna raye babu wanda yarasa ransa sai kun koma cikin gidan ku ko suna so ko basa so Allah yafisu, Abu yace insha Allah wannan azaune take shigarta gidan kamar ta shiga ne domin yanzu za ayita ta ƙare basai anje ko ina ba dan haka zama bai ganmu ba ku tashi gaba ɗayan ku mutafi, MEER ne yayi saurin miƙe tsaye yace ba wata hukuma da za akira ni nan da kaina zanyi maganin ko wane ɗan iska ɗaya bayan ɗaya sai na halaka su wallahi bazan barsu ba, maama sai murmushi jin daɗi take tasamu masu ƙwato mata ƴancin ta ba dangin iya bana baba amma gashi sunzame mata gatan rayuwa badan suba tasan da tuni wani labarin ake ba wannan ba, cike da farin ciki tace "tace"kuyi haƙuri bari inkatse muku hanzarin ku ta bakin yaron nan wannan ba maganar hukuma bace nima nafiso inɗau mataki da kaina inyaso daga baya idan aka gama tara komai akasan masu hannu aciki sai a shigar da ƙarar daga baga baya ina ganin hakan sai yafi mana sauƙi, yanzu tunanin ta inda zamu fara yakamata muyi tunda tace wasu sun fara bincike aciki yakamata ta haɗamu dasu inyaso sai muji wane abu suka gano daga nan sai mu ɗora daga inda suka tsaya, ina so ta farar ɗaya inyi musu dirar maƙiya tayanda kowa sai ya girgiza da lamarin ina so inbasu mamaki amma saida haɗin kanku sai mun haɗu ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar maƙiya, domin wannan faɗan ba mutum ɗaya bane da hannun mutane da yawa aciki bayanda za ayi ace wannan shirin duk Mutum ɗaya ne yayi shi kuma batare da sanin kowa ba dake cikin gidan wannan ƙarya ne bazai taɓa yiyuwa, Abu ne yace "gaskiya ne wannan maganar taki haka take dole sai anyi shiri yanzu meye abunyi, "abunyi ai shine kawai ku taso mutafi ita wannan yarinyar ta kaimu gidan waɗancen ɗin inda kakar ta take, "shikenan ma kawai ƴata zadai ki gane gidan ko yanzu idan muka tafi,ummy ta tambaye ta tana riƙo hannun ta, ɗaga mata kai tayi dan ita zuwa yanzu kanta yayi mata nauyi wani irin ciwo take ji yanayi mata shiyasa bata da bakin yin magana abun yafi ƙarfin ta har yanzu takasa yarda wai kakar tace wannan akusa da ita wacce ta haifi mahaifin ta daman tana da rabon ganin dangin ta aduniya kafin tabar duniya abun saba ta taɓa tunani ba bata taɓa kawowa aranta ba ita duk a lissafin ta bata taba kawo wai masarautar da taje ta kwana ba ita ake magana yanzu akai kwata kwata bata kawo wannan aranta ba wani tunanin take daban, maama ce ta kamo hannun ta ta miƙar da ita tsaye sauran duk suka miƙe meer ne kan gaba dan kafinma suyi wani yunƙuri har yafice daga falon saboda jikin sa har tsuma yake ji yake kamar ace masa ga masu laifin agaban sa yafara dukan su haka yakeji hannun sa har ƙaiƙayi yake masa nason duka Allah Allah yake suyi sauri suje ai mutum ko ƙishin ƙishin rashin gaskiya ne dashi acikin al'amarin sai ya daku bazai barsa ba, fitowa sukayi gaba ɗayan su suka shiga motar Meer da Abu agaba sai su ummy abaya tundaga cikin gidan yafara gudu tunkan yaƙaraso kwa bakin gate ɗin yadanne wajen horn ba shiri me gadi yayi saurin wangale masa gare ɗin yaja motar aguje yafita daga gidan, Abu ne ga kalle sa yace malam karage gudun nan mana duk gaggawar asara ai ta jira samu ko kasan gidanne basai anyi maka kwanta ce ba, "Ummy tace "ina fa saurin kawai shida ko unguwar ma baisaniba taya zai san gidan, yana jinsu yarage gudun dan shi saida suka faɗama yatuna ashefa baisan inda za"aba, ummy ce ta tambayi Ameesha sunan unguwar nan take tafaɗa musu maama tace ai tasan unguwar dan haka ba ɓata loƙaci Ameesha tayi musu kwatance har gidan dan haka suna tafiya maama nayi masa kwatancen hanyar da zaibi, dan har yanzu bata manta cikin kano ɗinba ita kuma Ameesha tade san sunan unguwar kuma tasan gidan ammade bata san inda za'abi aje gidan ba, ahaka suka cigaba da tafiya maama na kwatance har sukaje unguwar Ameesha kuma ta karɓeta taciga da nuna kwanar da zasu bi har sukazo ƙofar gidan, horn sukayi abakin gate ɗin akabuɗe musu suka shiga inda suka ga anyi parking anan Meer yayi sannan suka fito, Ameesha ce agaba suna binta abaya har suka kai falon nocking sukayi amma shiru ba abuɗe ba sai sukayi sallama nan ma shiru kuma suna jiyo hayaniya aciki, ummy ce ta gwada murɗa handle ɗin sai taji ta buɗu dan haka suka shiga ciki gaba ɗayan su suna ƙara yin wata sallamar sai loƙacin ƴan falon sukaji da suna ta ihun dady yadawo yajawo musu tsaraba sun tsaya ana ta raɓawa shiyasa basuji sallamar da suke yiba  sai yanzu, Ameesha na fita duk hankalin su yakoma kanta bossay kam yama ƙame agun dan yafi tunanin kode mafarkin ta yake ba gaskiya bane ko kuma gizau take masa yadai kasa tantancewa, da sauri Ammi ta tashi tsaye tare da cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Allah kaine abun godiya Ameesha ke nake gani kode mafarki nake ƙarasawa Ameesha tayi gurin ta tare da rungume ta tace nice Ammi, gaba ɗaya babu wanda ya lura da su maama duk hankalin su yakoma kan Ameesha sai murna Ammi take bossay kwa har yanzu bai iya buɗar baki ba yayi magana, saida Ammi ta sake ta sanann idon ta yasauka kan su ummy dake tsaye suna kallon su kamar tv, sannu ku da zuwa bayin Allah hankalin duk yayi kanta ban lura dakuba Bismillah kuzauna zama sukayi sannan suka shiga gaggaisawa yaran ma suka gaisar da su Abu sannan suka bar falon zuwa ɗaki haka suke daman indai akayi baƙi babu wanda yake zama agurin wannan tarbiyyar Ammi ce ahaka ta horar dasu, Ameesha ganin bossay bai kulataba yasa taji wani iri aranta tanaso taje wajen sa amma Ammi ta riƙe mata hannu dan haka ta tsaya bata jeba amma hankalin ta na kansa, shiru falon ya ɗauka na ƴan da kiƙu, Abu ne yayi gyaran muraya zai fara magana, da sauri maama ta miƙe tsaye tana zazzara ido ta miƙa hannun ta tana nuna wani waje wallahi shine....... ɗagowa sukayi ɗayansu suka bi gurin da take nunawa da hannu suka kalla........✍️✍️ tofa🤔🤔🤔                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/9, 8:47 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 85 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ "ɗagowa sukayi ɗayansu suka bi gurin da take nunawa da hannu suka kalla........✍️✍️ tsaye suka tashi gaba dayan suna mamakin jin kalaman ta babu wanda ya iya yin magana acikin su duk sun zuba masa ido suna kallon sa kamar yanda maama take kallon sa itama, adan tsorace ya shiga takowa zuwa gurin su cike da rashin fahimtar kallon masa da sukeyi yace me yake faruwa ne naga duk kun mike lafiyade, Ammi ce tace muma bamu sani ba munga de ta tashi kuma tana n h naka tace kaine, kasan tane ko ince kunsan junane? girgiza kai yayi yace ko kadan bantaba ganin ta ba yau nafara ganita, karyane wallahi karya kake kasanni nizakacewa bakasan wacece niba idan kamanta ni banmanta ba bazan taba mance kaba, Ummy ce tayi saurin kamota ta zaunar da ita sannan tace dan Allah ki hakuri ki nutsu sai kiyi mana bayanin inda kika sanshi baikamata kina dafa murya hakaba kodan saboda iyalen sa koma me yayi miki yakamata ai abi komai ahankali, yanzu gaya mana a ina kika sanshi, shiru tayi takasa magana sai tayi niyar budar baki zatayi magana sai taji bakin kamar anrike mata harshe takasa magana, shide dady na tsaye kamar gunki mamaki yagama cikashi shi baitaba ganin mataba amma tazo tanayin wasu maganganu dashi bai gane kansu ba, shi da baya kasar ma kuma baifiya zaman kasar ba to a ina tasanshi kode mahaukaciya ce to idan ba mahaukaciya ba wace daga ganin mutum farar daya takama nuna sa tana cewa shine, shi abun ma haushi yabashi dan haka ya koma kan kujera yanama so yaji SUWAYE SU, me yakawo su gidan sa, Ammi dataga abun nasu wani iri batasan ko su suwaye ba ta matsa kusa dasu tare da cewa baiwar Allah inaganin dai ko batan hanya kukayi ne daman nima ban waye ku ba yakamata afara sanin juna, baiwar Allah a ina kikasan mijina dawor sa kenen yau yaudin nan daga wata kasar ammade bansani ba ko tun kafin yatafi kuka hadu, kallon ta kawai maama take takasa magana dafa ta kalle ta sai ra juya ta kallesa, sude yan falon kowa yayi shiru yana jiran yaji me zatace kowa ita yake jira, jin shirun yayi yawa yasa meer dake tsaye kekam tunda suka shigo daman yake a tsaye bai zaunaba, takawa yayi har zuwa gabanta sannan ya tsugunna tare da riko hannun cikin nasa sannan yace yana daya daga cikin wadan daga cikin masu cutar dake? kai ta daga masa alamar "eh" mikewa tayi tare da cewa angama kashiga hannu yafada yana kallon dady da ya zaro ido jin abun da yake cewa, a masifance dady ya mike tsaye yace "bangane maganar kuba wai kudin suwaye me ya kawo ku gida na da har kuke wani banzan zance ban gane nufin kuba akaina, zaka ganene nan gaba meer yabashi, Bossay dayaga abun na neman wuce gona da iri shima yatashi daga inda yake yace me kuma mahaifina yayi da har ake kiranshi da mai laifi yakamata ka iya bakinka kasan da wanda kake magana bada sa'anka kake magana ba, nasan laifine kuma mu mukayi muku dan me zaku biyo mu hargida kuma wanda yayi muku laifin ma baku nemi gidan su ba kuka nemi gidan mu ji nake angama magana tun alokacin kun tafi kuma shine zaku biyo mu har nan abunma kuma bai tsaya iya kaina ba asai kunje ga mahaifina, duk kallon sa sukayi ga mamaki dan sai yanzuma suka gansa ashe shine wanda sukayi fada ahanyar abuja da meer da sam su sai yanzu suka gane sa shi kuma tun dazu ya gane su suna shigowa mamaki biyu ne daman yanasa magana da ganjn Ameesha da kuma ganin su,a tunanin sa abun da ya hadasune a hanyar abuja yasa suka biyo su har nan, Abu ne ya kalli bossay ycea yaro kwantar da hankalin ka ba wannan ne yakawo mu ba baku muka biyo ba hasali ma bamusan zamu hadu dakai ba, wannan yarinyar ce ta kawo mu nan yafada yana nuna Ameesha, ajiayar zuciya bossay ya sauke sannan yace to kuma maganar me yakeyi akai me dadyna yayi da ake cewa yana daya daga cikin masu laifi wane irin laifi ya aikata? yanzu duk ba wannan maganar ba abarta agefe, ayita daga baya, cewar Abu sannan ya dora da cewa, yanzu ina bukatar kowa yazauna mu tattauna akan abun da yakawo mu duk ma wani sai yabiyo daga baya, Alhaji kayi hakuri da maganar sa kazauna ayimana afuwa munshigo kai tsaye batare da sanin kuba, maganar da Abu yayi ce tasa dady dan jin dama dama sannan yasamu waje ya zauna gaba dayan su zama sukayi banda meer, yana tsaye saifaman harhade rai yake ya cika yayi fal kiris yake jira ya fashe, dady kwa sai tukwicin harara yake samu daga gare sa sarai kuma yana sane da irin kallon da yake masa kawai rabuwa yayi dashi, shiru falon ya dauka bKajin motsin kowa kowa yayi shiru ana sauraron Abu, gyara zama Abu yayi sannan yace "kamar yanda nagaya muku sanadin wannan yarinyar muka hadu ina fatan ai kunsan sanadin barinta nan kunsan da batan ta, to dan gurina ne ya hadu da ita a hanya wasu sun biyo ta yataimake ta ya kwace ta a hannun su bayan ya kaita gida kuma wannan baiwar Allahn da kuke gani ya nuna maama da tayi jigum kana kallon ta zata baka tausaayi ita kadai tasan kalar tunanin da take aranta, cigaba yayi da cewa"tana ganin ta tace wannan duk inda ta shiga ta fito jinin tace munajin haka duk abun yabamu mamaki dan har muka fara tunanin ko ciwon tane yatashi saidai da mukayi duba sosai sai muka gano kamannin da suke da ita shine muka zauna muka tattauna yarinyar tafara bamu labarin ta tunda taji labarin ta ta kara tabbatar mana da jikarta ce dan haka itama tabamu nata labarin yanayin labarirrikan su shiyasa muka kara yarda da gaskiyar maganar ta, duk abun da kakarta ta baku labari muma tagaya mana anan take sanar damu kune kuka taimake su suka zauna anan tare daku ita kuma ta koma wani gidan da zama dalilin hakanne yasa mukace ta rako mu nan dan muga kakartata kuma wadanda suka ce zasu fara bincike akai muka suma mugana dasu dan muji ko sun samo wani labari sai sugaya mana sai muci gaba daga inda aka tsaya mu hada hannu karfe wajen gano masu hannun acikin wannan lamarin, maganar da nake muku yanzu wannan baiwar Allah da kuke gani itace kakar wannan yarinyar itace uwa ga wannan yaron da aka buge masa ita akan titi atakaicedai wannan mata da kuke gani matar sarkin garinnan ce tun ada amma yanzu bansani ba shine sarkin ko kuma wani halin gidan sarauta aka nuna mata aka koreta daga cikin gidan ita da yayan ta bayan ta fita daga cikin gidan ma aka kara binta aka bigeta da mota saboda ba aso taci gaba da rayuwa sai kuma gashi Allah ya nuna musu karshen su ta warke sumul ta samu lafiya kuma babu abun dabata tunaba saidai makara yiwa Allah godiya da samun lafiyar ta, har gidan tasani saidai yanzu baza mushiga gidan kai tsaye ba dole sai mun fara bincike tukunna mutunkari cikin gidan ayi kan me uwa jawabi domin da shedarmu zamu shiga tayanda zamu kama mutum dumu dumu bashi da damar kare kansa ko kuma yayi yunkurin kai wani harin ga rayuwar ta ina fatan kun fahimci inda maganata ta dosa,   "Ammi ce ta tashi daga inda take ta dawo kusa da maama tana ta sakin murmushi tana cewa Alahamdulillah Allah kaine abun godiya ashe zanga wannan ranar yau naga jinin Ameesha abun da bantaɓa tunanin ba ko amafarki gaskiya naji daɗin wannan lamarin su  kuma waɗanda sukayi muku wannan abun Allah ya toni asirin su Allah habayyana su, juyawa ta ƙara yi ta kalli bossay tace Aliyu kaji fa yanda Allah yake haɗin sa ta inda ba azata su saceta daga gurinku gashi kuma fitar tata daga gidan daman shine sanadin haɗuwar tasu maza ka kira dadda Allah sarki nasan yanzu tana cikin damuwa baiwar Allah yau tazo taga mahaifiyar ɗanta nasan sai tafi kowa farin cikin wannan rana, Ammi duk tabi ta rikice kana ganinta zakaga tsantsar farin cikin da take ciki, bossay ma sosai ya nuna farin cikinsa da wannan labarin daman yagaywa su Sameer matar nan suna da alaƙa da Ameesha suka ƙi yarda amma shima baitaɓa kawowa wai ko kakar ta bace shidai kawai yaga sunyi kama sosai ashe babbar alaƙa ce atsakanin su, baisan loƙacin da yatashi ba yaje ya rungume Ameesha yana tayata murnar haɗuwar ta da kakar ta kuma zata haɗu da danginta, agurin dai babu wanda bai nuna farin cikinsa ba amma banda dady da komai yatsya masa abun damuwar shine maganar da maama tayi masa wai tasanshi kuma yana ɗaya daga cikin masu laifi wanann maganar ba ƙaramin ɗaga masa hankali tayi ba, bayan sun ɗan tsagaita da surutun ummy   tace  "yanzu tana ina kakar ta take akira mana ita ina ta tafi, Ammi ta kalle su tace dadda ai tafi neman Ameesha tace bazata sake dawowa nan ba saida jikarta nan dai ta basu labarin abun da yafaru tabar gidan sannan tace musu ayanzu dai dadda tana gidan sarki taje nema jikar ta cikin gidan sai daru take musu wai sai sunkaita wajen sarki takai ƙarar su Aliyu wai su suka kashe mata yarinya saboda tayi mafarki ta mutu kuma sutagani dan haka dole mafarkin ta gaskiya ne da ƙyar de aka lallaɓata ta haƙura tana cen ita da yara suna ɗebemata kewa amma nasan suna gamawa ne dadda da bata da mantuwa yanzu dai bamusan meke faruwa ba, Aliyu ka kiramana su muji sai agaya musu suma duk suzo ana neman su, ummy tace Allah sarki gaskiya ta burgeni ai gwara da take jajirtacciya badan hakaba ai da tuni sunci galaba akanta kuma mutane da yawa zasuna cutar ta amma data tsaya tsayin daka akan ta kinga gashi sunkawo har yanzu kuma Allah zai fara bayyanar da gaskiya, zanso ganin matar nan wallahi dan tayi matuƙar burgeni kwazonta ya burgeni, "nima dai haka wallahi jin tana mace tayi irin waɗannan abubuwan shekara da shekaru ta iya jurar ko wane irin tashin hankali ba ƙaramin ƙoƙari tayi ba,Abu ke wannan maganar..... cike da murna bossay yazaro wayar sa a aljihu ya dannawa sam kira batai wani ringing me yawa ba sam ya ɗauka yana ɗauka bossay yace "ka koma gidane? sameer yace "a'a " amma ina hanya yakamata kaima ka komo yanzu saboda ina dawowa zamu tafi wajen mutanen nan, bossay yace ok amma kafin nan idan ka koma ka ɗauko dadda kutaho gidan mu gaba ɗayan ku ga Ameesha agidan mu amma dai sauran labari sai kunzo kudai yi sauri kawai, aɗan zabure sam yace kamar yafa wacce Ameeshan kake nufi yayi tambayar a mamakin ce, jin yanda yayi tambayar saida yasa bossay ɗan sakin murmushi sannan yace"Ameesha nawa kasani wacce dai muke nema gata nan agabana kaidai kuyi sauri kuzo akwai labari kwaji idan kunzo, duk yanda sameer yaso bossay yagaya masa abun dake faruwa amma yaƙi gaya masa har ɗan ɓata rai sam yayi wai duk dan yagaya masa amma yaƙi daga ƙarshe ma sai ya kashe wayar yana masa dariya, duk sunajin sa abun da yakeyi ɗin amma suma daman hakan suke so gwanda kar agaya masa ɗin in yazo yagani, ummy ce tace "wai nikam kamar naji kince kakar tata tana gidan sarki sarki nawane anan garin, Ammi tace "sarki ɗaya ne mana nima abun da nake taso intambaye ku kenan naji kunce matar sarkin garinnan ce ko, Ummy tace "eh haka tace, tofa nan ake yinta ana wata gawata kenan shi ai yaron da Aliyu ya kira yanzu yaron gidanne yanzu hakama kakar tata tana gidan sarkin da kuke magana, gaba ɗayan su sai yanzu suka kawo abun da ake magana akai bossay ne yafara magana, wai daman kuna nufin gidan su sam anan take abun nufi yanzu shin sam da Ameesha ƴan uwane kenan, yayi maganar yana rarraba ido ya kalli Ameesha ya kalli sauran itama kanta Ameeshan jinta tayi wani iri wai daman ita jinin sarauta ce gidan da taje har taji bata son zaman sa daman nanne asalin ta su Hamra da Amna duk ƴan uwanta ne na jini Inna lillahi wa inna lillahi rajiun wannan wane irin abune yazo mata sama taka jin maganar tasu take kamar amafarki har yanzu bata gama yarda da abubuwan da suke faruwa ba, Ameesha bossay yakira sunanta ɗagowa tayi ta kalle sa sai yasakar mata murmushi yace congratulation ashe keɗin jinin sarautace bamu saniba keɗin jikar sarki ce nataya ki murna kasaƙe tayi tana kallon sa dan ita har yanzu bata yarda ba da abun da yake faɗa, Abu yace "gaskiya wannan abu yayi kyau daman shiyasa arayuwa akeso ka kyautata mu'amalar ka da kowa karka wulaƙanta kowa dan aduniya bakasan da wanda Allah zai haɗakaba yanzu kuma zaune tare tsawon loƙaci batare da kunsan da hakan ba gashi shi hana niyar taimaka miki baisan ƴar uwar sa yake taimaka ba wannan abu sai lamarin Ubangiji shi yasan yanda zaiyi da kowa yabayar asanda yaso kuma ya hana asanda yaso inmukayi duba gaba ɗaya da haɗuwar tamu da gano wasu abubuwan duk ba wani loƙaci aka ɗaukaba duk tsawon loƙacin da muka ɗauka muna tare da baiwar Allahn akwance bata tashiba Saida Allah yaso ta tashi sannan ta tashi kuma da tashin nata da barowar mu can ɗin gaba ɗaya akwana biyu hakan tafaru, gaskiya ne maganar ka cewar ummy gaba ɗayan sudai kowa saida ya tofa albarkacin bakinsa, Meer yace "yauwa to Abu kace abari sai angama tattaunawa to angama yanzu sai adawo maganar kan wannan mutumin da tace tasanshi tun ɗauzu take son yin magana kun hanata sai faman surutu ake, jikin Ammi ne yayi sanyi jin yanda meer yake magana kansa tsaye yana nuna dady da yatsa yana cewa wannan mutumin itadai tasan mijin ta mutumin kirki ne bata tunanin aduka labarin nan da aka bayar zai iya saka hannun sa aciki wajen cutar da rayuwar su, da ƙyar ta daure ta buɗi baki tace dadyn su kagaya mana wani abu yataɓa haɗaka da matar nan ko kuma dasaka hannun ka acikin ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da aka bada labari ka gaya mana gaskiya dan Allah, da sauri ya girgiza kan sa yace "nikuma mai zaisa incutar da wani ko kuma insaka hannu acutar da wani ba ɗaya daga ciki ni bansan taba yau nafara ganin ta saidai kawai ko in kama nake mata da wani daban amma bani bane, kallon Meer zatayi masa magana taga irin kallon da yake bin dady dashi yasa takasa magana, Meer yace ai bashi zaki tambaya ba, Maama kigaya mana a inda kika sanshi kigaya mana abun da yayi miki, Abu ne yace "SAMEER !! wai me yake damun kane ko da sa'anin ka kake magana baza kabari mubi komai ahankali ba, "Abu yanzu me nayi kuma anan tambayafa kawai nayi meye kuma abun rashin daidai amagana ta, banza Abu yayi dashi bayaso yabiye masa suzo suna kace nace agaban mutane, baidamu da abun da yayi ba yaci gaba cewa, "maama kinyi shiru kifaɗi abun dake ranki kar kiji komai ina tare dake..... maama da tazama kamar ma babu ita afalon duk abun da suke saidai ta bisu da ido takasa magana jin bakinta na ƙara yi mata nauyi ta shiga karanto duk addu'ar da tazo bakinta ahankali tafara jin ta nml, kallon Meer tayi na wasu ƴan daƙiƙu kamar meson gano wani abu sannan tace kana da saurin fushi kamar wata mata duk wani irin masifar nan da kake yi wallahi idan inaji sai inji kamar gwaggo ce takeyin ta kai anya ma kuwa baka haɗa jini da itaba dan yanayin zafin ku ɗaya wallahi tun acan nake ganin yanayin naka amma nakasa gano da wa kake min kama sai yanzu, haɗe rai yayi yace "ni banda wata alaƙa da kowa anan garin ko nayi kama da ɗan nan garin kodaina haɗani dasu nifa tambayar da nayi miki daban kuma amsar da kikaban da ban, ɗan murmushi tayi aranta tana cewa inma zan faɗa ba yanzu ba zan bar wanan araina saina gama tabbatar wa zan faɗa maka tundade kai naga alamar baka san ta ido ba agaban iyalen sa zaka iya cimasa mutum ci, meer ne yakuma katse mata tunanin ta yace tunanin me kikeyine ana magana kinyi shiru, ƙura masa ido tayi maimakon tabasa amsar da yake tambaya sai kawai tace wallahi sai na kaika wajen gwaggwo taganka ni bantaɓa ganin wanda ya ɗauko halin taba sak kamar kai ƴaƴan ta duk sanyi ne dasu babu wanda yayo ta har gwanda jikoki ma akwai masu zuciya dan sameer tun yana ƙarami yake da zuciyar bala"i, dukan su babu wanda baiji daɗin yanda ta zage take magana ba duk sunyi shiru sunzuba mata ido, "juyawa me yayi zaibar falon dan tagama bashi haushi ganin yake kamar ma ta mayar dashi mahaukaci yayi mata wata tambayar daban amma tana yi masa wasu maganganun daban, da sauri maama tace dakata mana ɗan gidan gwaggwo meye na zuciyar dawo inbaka wani labari banza yayi da ita yaficewar sa, dariya ummy tayi tace ai zuciya kaɗan ma kika gani aini har mamaki ma nake watarana idan zuciya ta ɗebesa babu abun da baya iyayi nidai nasan bahaka halina yake ba saidai daman kuma ba abanza ba daman abace kyan ɗa ya gaji ubansa to shidai wannan uban ya ɗauko dan duk haka suke da wannan zuciyar kawai da tashi da ɗan sauƙi bayama yanzu da ya manyanta shiyasa ya rageta sai antaɓoshi ake ganin ta saɓanin shi kuma wancen koda yaushe ma daman akusa take dan shi ko zama ma da mutane bai iyaba, ahaka ma anamishi addu'a da ba a san me zai zama ba nan gaba, Abu ne ya harare ta ƙasan ido sanan yace ni ba ruwana bani yagada ba shi yasan inda yake ya ɗaukota gashinan maama tace halin sa ɗaya da gwaggwo ita ya ɗauko amma bani ba, Wallahi ka ya ɗauko idan bakaiba taya zai ɗauko wacce ba dangin sa bama ka taɓa jin inda akayi haka, Abu yace "ake kamannin fuska ma ba dangin iya bana baba bare kuma halayya Wannan ai abune me sauƙi, hmmm "haka dai kace ai zasu ganni idan ƙarya nayi maka tunda ai ba dainawa kayi ba saida idan ba ataɓo kaba, yanda suke ta hirar su yasa su Ammi kawai zuba musu ido suna kallon su abun burgewa, ummy ta juya wajen maama tace "maama dan Allah kin taɓa ganin inda akayo gadon halayya hakannan batare dangan taka ba me ƙarfi, shiru maama tayi tana tunani kamar ma bazata bata amsaba sai kuma tace a'a ba ayi gaskiya, Amma ku asalin ku ƴan inane???????                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/10, 8:47 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 86 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     Amma ku asalin ku ƴan inane????? Ummy tace nidai ba ƴan nan bace amma dai shi haifaffen garin nanne sanadin hakanne ma muka dawo Abuja da zama amma ni a agarin yemen nake, haba ko da naji mana nidai nasani Allah maganar gaskiya yaron nan sun haɗa alaƙa da gwaggwo wataƙil ko tana ɗaya daga cikin dangin mahaifin nasa nan, tunda suka fara maganar dangi Abu yaji jikin sa duk ba daɗi tunawa da yayi yanzufa shi kusan baida dangi yake tunda daman baitaso yaga mahaifiyar sa ba mahaifin sa kuma ya tafi ya barsa yana raye shima ko ya mutu Allah masani amma dai zaiso ganin gwaggwon da maama take magana akai wataƙil maganar ta tazama gaskiya ko itace matar da yataso ahannun ta tunda itama masifaffiya ce saidai gaskiya bata da zuciya kamar yanda maama take faɗa amma dai duk da haka zai tambayeta inda take tunda yaga maama akwai saurin gano abu gashi duk abubuwan da tafaɗa sun zama gaskiya Allah yasa shima hakan ta zama gaskiya da yafi kowa jin daɗi yadaɗai yana neman danginsa ya rasa su, ummy ce ta lura dashi tasan kuma tunanin me yake dan haka tayi saurin kiran sunan sa, amsa mata yayi tare da kallon idon sa har yafara canza kala saboda tsabar tunanin da yashiga  "sorry" ummy tace dashi, kaɗa mata kai yayi kawai sannan yakalli maama da itama shi take kallo kuma duk tagama karantar yanayin sa daman tana sane tayi wannan maganar dan ta tabbatar wa da kanta zargin takeyi akansa, maama zanso ki nunamin wannan gwaggon da kike magana akai saboda maganar ki zata iya zama gaskiya ni bansan inda dangina suke ba nadai san na taso da mahaifin na sannan da matar sa da ƙannena wanɗanda muke uba ɗaya dasu mahaifiya ta kuma banma taso da itaba bansan taba ancemin tun ina yaro ta rasu, sukuma ƴan gidan mu tunda natafi neman aiki ina kasuwanci naɗau loƙaci me tsawo banzo gida loƙacin kuma da nadawo gidan natar dashi arufe dana tambaya ake cemin ai sundaɗe da tashi kuma ba'asan inda suka koma haka nai ta nemansu bansamu inda suke har na haƙura na koma naci gaba da rayuwata ni kaɗai bayan nayi kuɗi ma naƙara bada cigiyar su lungu da saƙo harda gidan jaridu da tv amma ba asamu inda suke ko kwanaki ma anƙara cigita min su haryanzu shiru bansan inda suke ba maganar da nake miki dai yanzu mutane biyun nan da kika gani su kaɗaine dangin na daga ɗana sai matata banda kowa bayan su, ya ƙarasa maganar cike da kalar shiga damuwa, gaba ɗaya ƴan falon babu wanda bai tausayawa rayuwar sa a duniyar nan kowa kagani da kalar tasa damuwar shidai yanzu idan kagan sa bazakace yana cikin damuwa ba sai ka rantse da Allah bashi da wata matsala arayuwar gani zakai duk abun da yake nema yasamu ashe haka Allah yake tsarin sa baya haɗawa mutum duka gashi da uwar kuɗi amma kuɗin basu isa sun siya masa abun da yarasa ba, idan yabaka wani abun sai ya hanaka wani abun haka Allah yake tsarinsa, maama ce tace Allah sarki "zan haɗaku kwa kaganta dangin ka kuma kar kaƙara cewa baka dasu ba mutum biyu bane suka rage maka mutane ba adadi ne kaiɗin ɗan dangine cikakke ma kuwa uwa da uba, babu yanda za ayi ace mahaifin da ya tsugunna ya haifema ya yafi yabarka ina tabbatar maka da duk binciken da kake musu suna jinka kawai basu da ra'ayin kane akusa dasu saboda basu suka haifeka ba shiyasa basu damu dakai ba, mahaifiyar ka kuma tana raye ba mutuwa tayi ba amma dan in tabbatar maka da hakan in ba damuwa ina so ka aske wannan gemun da yacika maka fuska ya canza maka kamanni gaba ɗaya idan ka sake akwai wani baƙin tabo agefen ƙasan haɓarka idan nagansa to tunanin danake ya tabbata idan kuma bangani ba to bahaka bane duk da nagani a hoton da kuka ajiye afalon ku loƙacin babu gemu amma ina son ingani azahiri in tabbatar da ba camera bace zahiri ne, da sauri Abu ya tashi tsaye yana kallon ta da hannun ya nuna ta yakasa magana da ƙyar ya iya haɗo kalaman bakin sa yace maama wane irin tunani kike akaina karkice tunanin danakeyi zai zama gaskiya taya kika san da tabo a fuska ta kuma meyasa kike tunanin waɗan cen mutanen ba iyaye na bane taya duk hakan tafaru, Saboda nice  mahaifiyar ka labarin da nabaku cewar anfitar min ɗa daga ɗakina ansace shi na nemeshi na rasa to wannan yaron bakowa bane face kai!! tsit falon ya ɗauka jin furucin ta shikam Abu mutuwar tsaye yayi yayi ƙeƙam agurin kamar gunki, batabi takansa ba ganin yanayin da yake ciki kuma bata jira wani daga cikin su yayi magana ba saboda tafiso sai taje ƙarshen maganar ta kafin ta bawa kowa damar yin magana, cigaba tayi da cewa   "kaiɗin ɗana ne dan cikin nane tunda nafarka acan gidan naku natashi naganka nagane hakan amma ban tabbatar ba saboda gemun da ya rufe maka fuska kuma ina tunanin kode gizau kake min amma da naga hoton ka wanda baka da gemun sai hakan ya tabbatar min da kamannin ka da mahaifin ka aduk inda naga jinina sai ganesa koda ba wani jini muka haɗaba sosai amma ina ganewa abun da yasa aloƙacin ma banyi maka magana ba saboda nafi so sai mun dawo nan sannan kakaini har wajen iyayen ka sai intambaye su shin su suka haifeka nasan zasu iya faɗar gaskiya sai kuma gashi bamuje ko ina bama nagane hakan ta labarin da bakayar yanzu, tofa kowa yayi saranda afalon yaudai so ake akashe su da al'ajabi daga wannan labarin sai wancen labarin, babu wanda maganarta bata dake saba suma kenan bare kuma wanda akayi domin sa jinsa yayi wani iri kansane yafara sara masa da wani irin ciwo kamar zai tsage dan wannan lamarin da yadawo kansa nema yake yagagaresa ɗaukan sa taya za ace wannan matar itace mahaifiyar sa kai wannan ba gaskiya bane shifa mahaifiyar sa ta rasu, saura ƙiris ya faɗi Ummy tayi saurin riƙo shi ta rungume sai kawai tasaki kuka, cikin kukan take cewa Alahamdullillh Alahamdullillh Alahamdullillh kawai abun da take iya nanatawa kenan tama kasa magana saida ta daɗe ahaka sannan ta sakesa tace kaje kaje gurin mahaifiyar ka kaje  ka rungume ta karungumeta kaji ɗumin mahaifiyar ka da kadaɗe baka jiba  kaje" kai ya shiga girgiza mata alamar bazaije ba dan shi ganin abun yake bambarakawai wani iri kamar almara haka yakeji yakasa yarda da maganar ta, ummy taci gaba da cewa wannan itace mahaifiyar ka ni naji ajikina hakan gaskiya ne gaya maka ne kawai banyi ba amma ni tunda kabani labarin dangin ka nima nayi tunanin anya kuwa su suka haifeka iyayen da suka haifeka bazasu taɓa guduwa su barka ba wallahi waɗan can ba iyayen ka bane maama itace mahaifiyar ka ta asali kaje gare ta, ahankali yashiga takawa zuwa gaban maama, yana zuwa kuma sai ya tsaya yana kallon ta, hawayen da suka tararwa maamane tasa hannun ta share su tare da miƙewa tsaye ga hawaye na sauko mata ita kaɗai tasan halin da ta tsinci kanta ahaka ta daure ta sakar masa murmushi tare da ware masa hannun ta tanaso yayi hugging, ƙinyi mata yayi saida ummy ta ƙara yi masa magana sannan ahankali ya buɗa hannun sa yaje ya rungume ta itama ta ɗora hannun ta akan bayansa, wani abu sukaji gaba ɗayan su yana shiga zuciyoyin su yana ratsa su kaunar uwa da ɗa na ratsasu, baisan loƙacin da hawaye suka shiga gangaro masa kan kumatun sa sosai yashiga zubda hawaye shi kansa baisan name yake ba sun daɗe ahaka rungume da juna, su Ammi babu wanda bai zubar musu da ƙwala ba sun matuƙar basu tausayi  uwa da ɗanta amma anrabata dashi tun yana jariri amma sai bayan shekar masu yawa zasu haɗu wannan wacce irin rayuwa ce me zasuji aransu wane irin farin ciki zasu tsinci kansu aciki, da ƙyar suka iya raba jikin su maama ta share masa hawayen sa tana kallon sa tace saida najika ajikina na ƙara tabbatar wa da ɗana ne da gaske, naga har yanzu baka yarda dani ba amatsayin mahaifiya ba kana kokonto ko to zan cire maka kokonton idan kaga mahaifin ka domin kamannin ka sak dashi Kadena wasi wasi akaina bana faɗar abun da banda tabbaci akansa  sai nasamu hujja sosai kuma jikina yagaya min sannan nake faɗar magana bana faɗan abun da nasan ba gaskiya bane dan haka ka yarda dani amatsayin uwa agare ka, da sauri yaƙara rungemeta batare da ya sake taba yafara magana cikin hawaye yace "nima haka saida naji ɗuminki nafara yarda ɗumin mahaifiya daban yake tunda nake bantaɓa tsintar kaina cikin irin wannan yanayin ba, koda hakan bai kasance gaskiya ba ni bayarda na ɗaukeki amatsayin mahaifiya nayarda dake na na karɓeki hannu bibbiyu duk wani abu da ɗa zaiyiwa mahaifiyar sa nima zan miki bare ma kuma nima naji ajikina ke ɗin uwace agareni ni nasan soyayyar da muke yi miki muduka ba abanza ba rashin sani ashe keɗin uwace gare ni sosai Abu yashiga yin maganganu da har saida maama ta dakatar dashi sannan ta raba jikin ta da nasa, Suna rabuwa  ya ɗaga hannun sa  sama yafara godiya ga Allah da ya nuna masa wannan rana wannan ranace da bazai taɓa mantawa da itaba arayuwar sa baima san da wanne irin kalamai zaiyi amfani ba wajen nuna farin cikin sa ga mahaliccin sa, sai loƙacin ƴan falon suka shiga tofa albarkacin bakinsu suna ƙara taya su murna, Maama sosai ta tsinci kanta cikin farin ciki mara misaltuwa wai yau gata ga ɗan ta ga kuma jikokin ta har guda biyu koda iya wannan aka barta tagama samun duk abun da take nema arayuwa ko a iya hakane taci galaba akansu su da sukayi ƙulla ƙula suka tarwatsasu sai gashi Allah ya haɗasu duk loƙaci ɗaya me yakai wanann abun farin ciki saura ɗayan kuma shima tana fatan Allah ya haɗata da shi nan kusa in sha Allahu bai mutuba yanda taga sauran shima sai tagansa kafin tabar duniya, afili tayi ce Allah yabayya na min kai Sameer Allah yakare min kai aduk inda kake, "duka falon suka amsa mata da  "Ameen'" komawa kowa yayi ya zauna duk wanda ka kalli fuskar sa kasan yana cikin farin ciki ayau ɗin nan, bossay saboda zumuɗi miƙewa yayi yace bari yaje ya taho da su sameer su taho tare, Ammi tace "gaskiya dai yakamata suyi sauri suzo suji wannan abun farin cikin zanso inga dadda inga yazatayi idan taji wannan labarin, "gaskiya dai nima zanso ganin ta cewar ummy, maama ce tace "a'a rabu dasu suzo atsanake ba sauri muke ba muna nan daku har dare ba inda zamu, kawaidai je waje ka kiramin wancen yaron me zuciyar kutare yazo yaji, dariya suka ɗanyi sannan bossay badan yaso hanasan da tayi ba yace mata to sannan ya fita zuwa wajen Meer yana fita suka ci karo dashi abakin ƙofa yana shirin yi masa magana kawai ga watsa masa harara yabi ta gefen sa ya shiga falon da kallo bossay yabishi har yagama shigewa cikin falon, sannan yabisa abaya, akusan tare suka shiga ciki yana shiga rai aɓace bai kalli kowaba yace ummy zan koma gida idan zaku tafi kutashi mutafi inkuma kuna nan inyi tafiyata danni banga amfanin zuwan nan ba, wakake da suna ne wai me naji kuna cemasa maama tayi maganar tana kallon su ummy ɗan murmushi ummy tayi tace Meer muke cemasa amma cikakken sunan shi Sameer, maama tace ashe suna me daraja gare kice samari na tara ƴaƴa da jika suna iri ɗaya duka ƴaƴana sunansu sameer baban sa ma Sameer aka raɗa masa da ya ɓata ne naƙara haifar ɗayan aka ƙara saka masa sameer mahaifin khadeeja kenan amma shi naji ba acanza masa sunan ba tunda loƙacin yana ɗanyin magana shiyasa bai manta sunan sa ba gaskiya naji daɗin hakan, kallon Meer tayi tace gto gaskiya kaidai ba  ɗauko halayen masu sunan kaba saboda duk bahaka suke ba duk acikin mu ka tsallake kowa ka tsallake mahaifiyar ka da mahaifin ka ka tsallake kakannin ka na farko ka tafi kaje ka ɗauko halin kakar ka tabiyu, tunda tafara magana yake kallon ta yana yatsina fuska shi akan meyasa zata ringa haɗasa da wata can bare agefe har zai buɗi baki yamayar mata da amsa, Abu ya dakatar dashi sannan tace Meer kasan wacece wannan kasan wa ka daɗe kana taimakawa kwance a asibitin kasan meyasa kaji kana sonta kake bata kulawa fiye da kowa kake yawan shiga damuwa idan antaɓata ko wani abun yasameta kake rikicewa kasan wacece ita, cike da rashin fahimta Meer yake kallon sa sannan ya girgiza kai batare da yace komai ba yana cigaba da kallon mahaifin nasa, miƙewa tsaye Abu yayi sannan yakama hannun me yakaishi har gaban maama yace wannan da kake ganin ta azaune itaɗin mahaifiya tace uwace agareni kai kuma kakar kace duk abun da kayi mata na taimako kakar ka ka taimaka, zaro ido yayi yana maimaita maganganun Abu ɗin na ƙarshe sai maimaita wa yake kamar me koyon karatu, Abu taya hakan zata faru meyasa tun acan duk bamu saniba sai yanzu anya kuwa hakan me yiyuwa ne gaskiya wannan maganar ba gaskiya bace wai bama ka taɓa cemun mahaifiyar ka ta rasu kuma taya za ayi wannan ta zama uwa agare ka, ummy ce ta tashi tana ɗan murmushi daman tasan ko kowa ya yarda bazai yarda ba saboda shi amurɗe yake ba a iya tanƙwara shi ta daɗin rai sai anyi masa da gaske yake fahimtar wani abun, kamasa tayi ta zaunar dashi tace "nutsu kaban hankalin ka nan gaba ɗaya kamar yanda tace hakan kwa yayi a tsanake tafara bashi labarin duk yanda akayi sosai tayi masa bayani tun baya ganewa har yafara ganewa, sosai kwa shima lamarin yayi shocking ɗin sa da ƙyar ta iya yarda da hakan dan ba ƙara min mamaki yayi ba, ana gamawa ya miƙe tsaye yace "dole su gane basu da wayo ko su waye ashe daman harda mahaifina acikin wannan zalincin nasu tabb akwa sunjawa kansu masifar da tafi ƙarfin su ko suwaye sai sun ɗanɗani kuɗar su domin sai na gana musu azaba me matuƙar wuya kafin inkasu lahira, dukan su sai sun ziyarci lahira da hannuna zan raba kowa da ransa tunda basu kashe ba to ni zan kashesu, (tofa daman lamarin ba dangin iya bare na baba ya zafafa akai zai ɗau mataki ina kuma ga shi aka taɓo faɗan nasune bana wajeba ai sa inda ƙarfi kuma yaƙare) aloƙacin da yake waɗannan maganganun duk wanda yakalle sa sai ya tsorata dan sosai ya canza halittar sa yajuye ta ta koma ta mugaye marassa imani hannun sa kuwa sai faman karkarwa yake idonsa yayi ja jijiyo yin kansa sun tashi sunyi ruɗu ruɗu dasu daman shi haka yake bai iya fushi ba daman mutum kullum fushi da harhaɗe rai batare da anyi masa komai ba ina kuma ga antaɓo sa taɓowa ma me muni irin wannan ai duk wanda yafara shiga hannun ya shiga uku wataƙil saidai uwar sa ta haifi wani idan kuma ta daina haihuwa ta ɗakko agidan marayu ko tagama rayuwar ta ahaka, dadyn su bossay baisan loƙacin da jikin sa yafara rawa ba babu wanda ya lura dashi ya tashi daga gurin yana niyar barin falon, caraf idon Meer yafaɗa akansa yana ɗaga ƙada zai fara taka benen babu wanda ya ankara sai ganin Meer akayi yayi tsalle ya dire agaban dady da hannu ɗaya yajawo sa yadawo dashi gurin cikin wata iriyar murya me amo da karsashi irin ta jaruman maza yace maama kifaɗan abun da wannan mutumin yayi ninasan baida gaskiya gashi yanzu ya tashi zai gudu daga gurin amma kinƙi kifaɗi abun da yayi ko to wallahi idan baki faɗa ba hukunci na zai fara aiki akansa, gaba ɗayan su miƙewa sukayi Ammi kam har tafara hawaye, bossay cike da tashin hankali yayi kan dady zai ƙwace sa Meer ya turasa gefe saura kaɗan ya bige da jikin ƙarfen kujera Allah ya karesa, gaba ɗayan su babu wanda ransa bai ɓaci ba Abu ya daka masa tsawa yace kai wai kafara haukane yaza ayi kazo gidan mutum kuma karinga tuhumar sa gaban iyalen sa kai idan akayiwa naka iyayen zakaji daɗi meyasa baka tunanin kafin ka yanke abu, Abu wai meyasa kake min haka idan ina abu kadena dakatar dani ko ni bansan me nakeyi ba tunda muka shigo matar nan ta nuna sa kuma shima ya nuna rashin gaskiya taya kake tunanin zan rabu dashi ai wallahi duk wanda nakama a case ɗin nan sai na kamasa koda basa hannun aciki amma matuƙar yasan wani abun ko anyi agaban sa wallahi shima sai kamasa dan haka wannan mutumin ma ba ruwana da iyalen sa inkaga na rabu dashi to sai na gane gaskiya, tasss yaji a akan fuskar sa Abu ya kwasheshi da mari rai aɓace yace kaci gaba ina magana kana magana muzuba nida kai muga ɗan halak kafasa kuma kasake shi inbaka son ranka ya ɓaci anan gurin, maama ce ta miƙe tsaye tace karda kasake taɓashi kayi nafarko kayi na ƙarshe indai akan case ɗin nanne yayi duk abun da yaga ya dace yanda basu da zuciyar imani nima haka nakeso ya nuna musu rashin nasa imanin ya taka nasu so nake susan bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane nasan ku ƴaƴan na kun manyanta baza ku iyayin komai ba dan haka bani daɗin wannan yaron da yakasance jinina yakasan jika agareni dan haka inban haifi wanda zai rama min mugunta da mugun taba to nahaifi wanda ya haifi wanda zai ramamin dan haka nagoyi bayan sa ɗari bisa ɗari, Ammi da bossay ta kalla da suka ƙame suna jin zigar da take yimasa, tsayiwar ta ta gyara tana kallon su da kyau tace ina mai baku haƙuri abisa abun da yafaru koma ince zai faru tun ɗazu yaron nan yake min zancen sa amma saboda ku da kuma mutun ciku da taimakon da kuka bawa jikata makasa cewa komai amma yanzu dole kuji wannan yazama dole ɓoyewar ma bata da amfani domin ko ban faɗa ba wannan yaron ba rabuwa zaiyi dashi ba, gabansu ne yafaɗi tsakanin bossay da Ammi kowa na tunanin jin me kuma ya aikata haka mai mune akan baiwar Allah nan Allah yasadai bada sa hannun saba acikin zalunci da akayiwa waɗannan mutanen idan hakan ta kasan ce ina zasu tsoma rayuwar su, basu kaɗai ba su kansu su Abu baƙaramin mamaki sukayi ba da jin batun ta, cigaba tayi da cewa "ba ƙarya zan masa ba kuma ba sharri ba ba ƙazafi ba shi kansa yasan abun da ya aikata min amma duk da haka bazan faɗi abun da yayi ba saboda ku amma ina so yafaɗa da kansa kuma hafaɗi wanda yasa shi da dalilin da yasa yayi min haka ɗin, babana sakar shi zaiyi bayani da kansa yaci darajar matar sa da ɗansa amma badan haka ba sai yafara ɗanɗana kalar irin azabar da yayi min kafin ma abarshi yayi bayanin amma yanzu saboda masu daraja irinsu za 'a ɗaga masa ƙafa, yayi bayani da kansa, kallo fa yakoma kan dady kowa shi ya zubawa ido yana jiran yaji me zaice amma yaƙi magana saidai kuma kallo ɗaya zakai masa kagane tsantsar tashin hankalin da yake ciki kana ganin sa kasan baida gaskiya........., ************************ _______*Dadda* saida su Amra suka gaji da tsokanar tafa dan kansu sannan suka rabu da ita sai sunga tana niyar tashi zata fita sai suƙara hanata ahakadai sukai ta wahalar da ita itama ta wahalar dasu momma tafiya daga ɗakin dan taje takawo mata abinci aikam dadda naganin fitar ta tashi zata bi bayan ta Amra tayi saurin tarar gabanta zata cigaba da tsokanar ta dadda ta haɗe rai tace wallahi ko ta matsa mata ta rabu da ita ko kuma tayi mata abun da ta tsana idan taja gashin ta bazata saki ba har sai tagansa a hannun ta tsoro ne yakama Amra tasan kaɗan daga cikin aikin ta ta aikata mata hakan dan haka ba shiri ta matsa tabata hanya dadda ta fita daga ɗakin, tana zuwa falon tayi turua ta tsaya ganin duk basa nan babu kowa afalon, ranta ne ga ɓaci watakon mutanen nan shanyata sukayi suka gudu suka barta ita tana nan tana jiransu ashe su guduwa sukayi to zasu gane kuren su badai ta riga da ta shigo gidan ba yanda neman gidan bai bata wahala ba haka neman gurin sarki bazai bata wahala ba dan haka bata tsaya wani tunani ba kawai tabi ƙofar da ta shigo ta buɗe ta fita tana fita su Amra suka fito suna kiran ta amma ina ko jinsu ma batayi ba ta riga da har ta fita,,, tana fitowa sai ta tsaya rarraba ido tana tunanin hanyar ina zata nufa wata hanya kawai tabi batare da tasan ina zata ba kawai tafiya take, shettima da yafito waje daman gurin motar sa ya nufa har zai shiga yatafi gida sai ga kiran sam yashigo wayar sa yana ɗagawa kawai yace "kana gidan har yanzu ko ka fita? shettima yace "a'a yanzu dai nake son fita inama gurin mota shiga zanyi ka kirani, "Ok" 'to kajirani karkafita yanzu zan ƙaraso, "Ok" sai ka ƙaraso ɗin yana gama faɗar haka yakashe wayar, rufe motar shettima yayi tare da juyawa dan komawa inda yafito yana shan wata kwana ɗaga idon da zaiyi ya hango dadda tana tafiya da sauri ya juyar da kansa dan karta gansa yafara sauri yana ɗaga ƙafa dan ya ɓacema ganin ta, saidai abun da baisani ba yana shawo kwana ta gansa kuma taga duk saurin da yake dan haka itama ta ɗaga ƙafa tabi bayansa tana ganin part ɗin da yashi ta rage saurin ta saboda daman tagaji tayi tafiya me tsawo gashi kuma yanzu tana ta sauri shiyasa da taga inda ya shiga sai tarage saurin ta shiga tafiya ahankali, awa yana shiga ya sauke ajiyar zuciya afili yace Allah ya taimakeni bata gannin ba dana shiga uku koma mai yafito da ita oho mata wannan tsohuwa tafiya bala'i wallahi yana gama surutan sa yayi sauri ya nufi part ɗin sam, Azeema da taji motsin kamar fulani zata fito daga ɗakin ta tayi saurin yin saɗaf saɗaf ta juya tabar wajen zuciyar ta kamar zata fito waje saboda tsoro sai yanzu take ƙara jin tsoron matar ashe tana gama wanke wanke ta ta taho zata gayawa Fulani sai kuma taji wayar da take dan haka ta kasa kunne rabi da wani abun na abin da Fulani tace duk taji akan kunen ta tafaɗa, harta tana harɗewa wajen yin sauri da sauri ta ƙarasa ɗakin su tana shiga ta faɗa kan katifar ɗakin tana sauke ajiyar zuciya sai yanzu da ta ganta aɗaki hankalin ta ya kwanta tunanin tashiga yi shin me wannan matar take ɓoyewa da take jin tsoron asani aikawa indai hakane zata bibiyi wannan saurayin da ya nace mata zata tambaye sa tunda taji yace yasan komai itama kam sai ta gano komenen haka ta zauna tarin ga tunani kala kala akan fulani......, dadda na ƙarasowa part ɗin batare da tayi sallama ba ko ta nemi iznin shigowa ba kawai ta tura ƙofar ta shiga kanta tsaye shigar ta tayi daidai da fitowar Fulani daga ɗakin kallon kallon suka shiga yiwa juna......, dadda ce ta fara kawar da kanta daga gareta sannan tace barka da gida dan Allah wani yaro da ya shigo yanzu nake nema naga kamar nan yashigo, yanda kasan da gini tayi magana haka Fulani tayi da ita bata yanka mata ba, Ganin haka yasa dadda ta girgiza kai kawai bata ƙara cewa komai ba sai kawai ta shiga dube dube afalon tana leƙeƙe tana so ta gano inda shettima yake, Fulani bata ɗauke idon ta daga gare taba taci gaba da takowa zuwa inda take tana me mamakin ganin ta acikin, "Nace ba keɗin wacece da zakishigo min kai tsaye ba abaki iznin shigowa ba waya ce miki ana shigo min guri kai tsaye idan barar ki zakiyi bana nan zaki shigo ba ba asanar dake yanda tsarin yake ba wayema yabarki kika shigo cikin gidan nan kuma har bangarena, banza dadda tayi da ita wata ƙofa ta gani tayi lungu a hasashen ta ko nan shettima yabi dan haka bata kula fulani ba tayi gaba zata wuce, taƙaicin ranin hankalin da fulani taganj matar na shirin yi mata yasa ta riƙo rigar ta baya tajawo ta ta dawo gabanta cikin daka mata tsawa tace ke wacce irin mahaukaciya ce anan miki magana kin maida mutane ƴan iska kishigo har inda nake kice zakiyi abun da kika ga dama gidan ubanwa kike shirin zuwa, "gidan ubanki nace gidan ubanki zani kinji mu da ƴar iskar mata anshigo ɗin ko gidan nakine ke kaɗai bakisan manya ba bake yakamata kifara gaidani ba amma maimakon kimin magana mai daɗi shine zaki min hauka akai to ni nawa haukan yafi naki da kinbini ta lallami da kinsamu amsarki amma tunda tahaka kika biyo sai ki shaƙeni ingaya miki idan kina da ƙarfi, dalla malama sakarni kibari masu gidan suyi magana danni da ƴar aiki ma kikafi kama daman ance irin ku idan suka samu waje sunfi ɗan gida iya shege to wallahi kibini ahankali idan bahaka ba jikin ki yagaya miki danni bana ɗaukar hauka yanzu zan saitawa mutum hanya ya shiga taitayin sa, tana kaiwa nan ta fusge jikin ta daga hannun fulani tana shirin ta cigaba da tafiya inda tayi niyar zuwa, da sauri fulani ta ƙara jawota a harzuƙe ta ɗaga hannun zata sauke mata shi afuska, caraf dadda ta riƙe hannun ta tare da wurgi dashi da ƙarfi da har saida yasa Fulani tayi baya kaɗan kamar zata faɗi, da yatsa dadda ta nunata wallahi idan kika kuskura hannun ki yataɓa jikina sai kinyi da nasani na rantse da Allah saina koya miki hankali, azafafe fulani tace ke kinsan wacece ni da kike gaya min duk maganar da kika ga dama kizo har masarauta ta kice zaki gaya min magana kuma ki kwana lafiya to wallahi baki isa kinbar cikin gidannan lafiya ba yau sai kingaya min uban da ya tsaya miki kikazo kikewa mutane hauka anan dan naga alamar ina jin bakya cikin hayyacin ki kike wannan maganar kina buƙatar adawo dake hanyar daidai, sai ansai ta miki tunanin ki da ƙarfi ta kwalawa murja kira tana amsawa yafito da sauri hartana haɗawa da gudu gudun ta ta ƙaraso wajen tana zuwa fulani tace "je kikira min sarki dorina da bafade da Sarkin su duk kice suyi sauri suzo kiran gaggawa ne, da sauri ta fice daga falon ta, dadda ce ta kwamshe da dariya tace aikin banza ashe ma taƙamar taki ta banzace tunda bazaki iya ɗaukar mataki da kanki ba sai kinsaka an ɗaukar miki wallahi kinban mamaki tsohuwar banza kawai, ni banda loƙacin ki ba gurin ki nazo ba da harkike cewa nazo bara kalata da shiga ta tamiki kama da wacce ta nemi wani abun arayuwata ta rasa ko tufafina sun miki kama da hakan saboda tsabar wulaƙanci da cin fuska ne yasaki faɗar haka ko? Azeema da tajidai hayaniyar tayi yawa yasa tayi saurin fitowa daga dakin ta ɗan leƙo tana leƙowa idon ta yasauka akan dadda zato ido tayi tana me mamakin ganin ta me yakawo dadda gidan nan inna lillahi wa inna lillahi raji'un Allah yasa ba mama ce ta turo taba da sauri ta koma ɗaki dan tana godewa Allah da bata fito gaba ɗayan ta ba tasan idan dadda taganta shikenan asirin ta zai tonu, duk abun da suke shettima na kallon sa daga bakin ƙofa kawai so yake yaga yanda wasan nasu zai ƙare yasan halin ko wacce daga cikinsu dan haka babu wacce zata ɗagawa wata ƙafa kowacce ƴar kanta ce basu da haƙuri gaba ɗayan su ita fulani nuna isa da gadara da wulanƙan ci ita kuma dadda bata ɗaukan raini ko kai waye baka isa ka taka taba kuma ta taku dan haka yana gurin har dariya yakeyi ƙasa ƙasa saboda faɗan nasu ba ƙaramin ƙayatar dashi yayi ba zaiso yaga ƙarshen faɗan nasu yaga wace zata haƙura ta barwa wata, a harzuƙe fulani ta buɗi baki zata mayar mata da martani aka turo ƙofar daka tawa tayi batare da tayi maganar da tayi niyya ba, bata kalli ƙofar ba tace maza kufitar min da wannan mahaukaciyar daga nan gurin ku fita da ita ku koya mata hankali, shiru taji sunyi basu yi abun da tace musu ba, jin hakan yasa ta dago dan tayi musu masifa sai kawai taga wayam basu bane ashe sam ne yashigo ita kuma duk atunanin sune, idon sa akan dadda ko bai tamabaya ba yasan abun da yafaru dan haka bai tanka musu ba kawai ya wuce zai tafi part ɗinsa dadda tayi saurin cewa kasan de ku nake nema zaka wuce kamar baka taɓa gani na bama, "kiyi haƙuri ina zuwa, kawai yace da ita sannan yayi gaba tunkan ya ƙarasa ma yaga shettima a tsaye na dariya tsayawa yayi yana kallon sa yace kai kuma me kakeyiwa dariya da hannun shettima ya nuna masa su dadda sannan yace ya akai zaka katse min kallon da name dama kabarsu wallahi faɗan nasu nishaɗan tar dani yake, mtsw bakada aikin yine shiyasa kana kallon su suna faɗan amma ka kasa shiga tsakaninsu kadai san halin waccen rikitar tiyar tsohuwar yanzu sai tajamana abun da zamuyi danasani kafito mu wuce gidan su bossay yace muje ana neman mu wai yarinyar nan tana gidan, "habadai wacce yarinyar kake nufi kuma, sameer yace yarinyar da muke nema mana shiyasa yanzu ai hankalina bai tashiba dana ga matar nan agurin nan dan haka tun kan su kacame azo asamu wata matasalar kazo mubar gidan arabu da ita lafiya dan ko gurin momma bazamu komaba mu wuce canɗin kawai daganan, "to wai dan Allah taya ta koma abun da yaban mamaki wannan wane irin juye juye ne ansace ta awani waje anga alamar ta acikin gidan nan yanzu kuma ace anganta acan wannan lamarin fa ni yafara bani tsoro wallahi, kadai zo muje kawai nima bansan ya akai hakan ta faruba sai muje zamuji, "Ok to muje, atare suka juya suka ƙarasa wajen su Fulani da suka cigaba da cece kucen su irin nasu na manya, suna zuwa sam bai saurare suba kawai yaja hannun dadda tana ƙwace tana cewa yasake ta sai ta koyawa fulani hankali itama fulani tana cewa wai a ina yasamo wannan mahaukaciyar matar yasake ta kar yasake tafita da ita daga cikin gidannan sai tasa an ɗaure mata ita, kowacce dai da kalar maganar da take amma yaƙi sauraron ko waccen su yacigaba da tafiya da ƙyar dai aka samu aka raba su suna fita shettima yajawo ƙofar ya rufe fulani aciki sannan suka wuce suna zuwa suka danna dadda a mota suka rufe suma suka shiga sannan sameer yatayar da motar da gudun gaske yabar masarautar dadda sai surfa masa masifa take yayi mata bazan yace gaba da tuƙin sa ya ɗauki hanyar gidan su bossay........✍️✍️                           💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/12, 9:47 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 87 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     *Ina masoyan dadda wannan page ɗin nakune*💃💃💃💃 ______*Dadda*______   "tunda suka fara tafiya dadda take surfa musu bala'i  kamar su sukayi mata laifin sunyi mata magana tayi shiru sun bata haƙuri amma duk da haka da haka taƙi sauraron su...., Sameer da yagade abun nata bana ƙare bane da yaga ta damesa taƙi yin shiru sai kawai yafara yawo da motar kamar zai bugata da wani abun suyi accident aikwa tana ganin haka ta sakar musu ihu tana cewa kashe mu kake so kayi nashiga uku na yaron nan anya kana da hankali yace bani dashi ai shiyasa zan nuna miki rashin hankalin wallahi idan bakiyi mana shiru da bakin kiba sai buga motar nan da abu kin mutu daman kece abaya kuma idan na bugata ke zaki mutu bamu ba, "wallahi bazan shiruba da bakin ka nake maganar, jin hakan yasa yaƙara jan motar da ƙarfi sannan ya taka burkin da ƙarfi, talau talau tayi zata faɗa gaba sai kuma tadawo da baya atake ƴaƴan hanjin ta suka motsa saida taji kamar zasu fito saboda tsabar tsurewa da tayi saida hawaye suka ta rar mata atake kwa tayi tsit kamar babu ita amotar, atare suka juyo shida shettima suna kallon ganin yanda ta koma yasa suka saka mata dariya taƙaici da haushi yama hanata magana amma ita kaɗai take raya abun da zatayi musu ta rama wannan rashin mutuncin da sukayi mata tunda take babu wanda ya taɓa sata gaba yayi mata haka waccen akuyar ta gama ɓata mara rai shine suma yanzu suka zo suka ɗora akai, sam yace "akaro na farko da yafara kiran sunan ta yace "hajiya dadda yadai bakin ya mutune ko kuma inƙara kashe shi da mota, banza tayi dashi tare da galla masa wata uwar harara kamar idonta zai faɗo, "Au bazakiyi magana ba kuma harda hararata to bari inƙara suma idanun in kashe su yana faɗar haka yaƙara sakin murmushin mugun ta sannan ya juya ya tayar da motar yana shirin fara tafiya dadda datagade yaron da gaske bashida hankali kuma inbata dakatar dashi ba sai yaƙara yi mata itakuma ahalin yanzu ai bazata taɓa son ta ƙara jin abun da yayi mataba yanzu dan tasan tsaf zata iya rasa ranta idan yaƙara dan haka sai ta sauke makaman yaƙin ta tayi saurin cewa wallahi ya mutu bazan ƙara yin magana ba na rantse muku da sarkin gidan ku🤣 sosai sukayi mata dariya tare da kallon ta shettima yace "daman haka kike da tsoro yau naga logonki hajiya dadda, Sam ya ɗora dacewa "daman tun can bata samu daidan ta bane nidaman bata taɓa shigowa hannu na bane da tuni na daɗe da saita wallahi duk iskancin nan nata tana sane take yinsu, Allah sarki dadda yaudai da gaske bakin nata ya mutu dan bata da halin magana shiru tayi duk abun da suke mata bata tanka musu ba dan har ga Allah yauɗinnan ba ƙaramin tsorata tayi ba dan haka ta siyawa kanta zaman lafiya tasawa bakin ta saƙata, sukuma sukaci gaba da tafiya suna ƙara yimata abun da suka ga dama suna mata dariya yau sun samu dama.....,          ***************************    "kallo fa yakoma kan dady kowa shi ya zubawa ido yana jiran yaji me zaice amma yaƙi magana saidai kuma kallo ɗaya zakai masa kagane tsantsar tashin hankalin da yake ciki kana ganin sa kasan baida gaskiya........., "muna sauraron ka maama ta ƙara yima sa magana, da ƙyar dady ya iya ɗaga kai yakalle ta sai kuma yayi saurin ɗauke kansa ganin yanda fa kafesa da ido, yakai wajen 15 minutes bai iya cewa komai ba saida meer yaƙara gargaɗin sa sannan murya ƙasa ƙasa yace da farko dai ina mai baku haƙuri gaba ɗagan ku laifine na riga na aikatashi tunda daɗewa kuma har yanzu abun bai bar raina ba nayi da nasani nayi nadamar abun da na aikata saboda nima ba ason raina hakan tafaru ba dole akayi min kuma abun da ya daɗe yana min yawo akai bansan mutumin ba, ranar da bun ya faru ina cikin tafiya amotar wani uban gidana saboda aloƙa ci banda aikin yi... ina cikin tafiya ta sai nayi parking ɗinta abakin hanya zan siyo ruwan sanyi awani shago bayan naje nasiyo ne nadawo na shiga motar na tayar naci gaba da tafiya na ɗanyi nisa kenan sai kawai naji an ɗora min wuƙa a wuya ba ƙaramin tsorata nayi ba dan saura kaɗan inje indaki wata motar Allah ya kiyaye nayi saurin taka burki ina shirin juyawa inga waye sai yace idan kajuyo sai caka maka wuƙar nan, nandai nakasa juyowa daman sai aloƙacin na kula ashe ya juyar da mirror ɗin gaban motar bare in kallesa ta ciki.., haƙuri nashiga bashi ina cewa me nayi mishi me yake nema awajena, sai yace intayar da motar duk inda yace min inyi ban Musa masa ba saboda ina son raina dan na lura idan nayi mishi taurin kai zai iya buga min wuƙar nan, haka na tayar da motar yana kwatan tamin duk hanyar da ya nuna ita muke bi muna miƙe wani layi yace dani kaga waccen matar dake tsaye nace eh yace to ita nakeso kabi ta kanta da motar nan, ba ƙara min tsorata nayi ba dajin furucin sa cike da fargaba nace dan Allah kayi haƙuri bazan iyaba idan nakashe tafa shikenan nayi kisan kai kuma nasan hukuncin me kisa awajen ubangiji nidai bazan iyaba kayi haƙuri ka barni intafi, sai kawai gasaka min dariya yace ai tunda ya shigo motar nan sai nayi abun da yasani nidai ban mara cemasa komaiba kuma ban tsaya da tafiyar ba muna daf da ita sai naga ta matsa ina shirin incigaba da tafiya batare da na ƙara bi ta kantaba, amma ban ankaraba wannan mutumin kawai yasaka hannun ya juyar da sttiring ɗin motar kan ta tabugeta atake kwa tafaɗi a wajen sai nayi saurin taka burki na buɗe motar nafito nayi kanta atakaicedai mutumin nan dana koma motar banga kowaba aciki har ya fice saboda murfin motar ma abuɗe yabarta banga fitar saba...... danaga yanda  ta bugu sosai sai kawai nakira motar asibiti na kwatan ta musu inda nake shine suka zo suka ɗauketa bayan munje kuma sai akace bata mutubu kuskuren da masana nayi shine gudawar da nayi nabarta amma shima banayi bane dan son raina sai dan jin yanda aka lissafo kuɗaɗen da zanbiya loƙacin kuma banda su banda dalilin su bansan ta inda zan samesu ba dalilin hakanne yasa na gudu daga asibitin sannan kuma number mutumin da nakarɓa wanda ya karɓi yaron banyi saving ɗin taba namanta na share ta shiyasa bankira saba amma duk dahaka daman nayi niyar kiranshi insanar dashi halin da ake ciki ko zai iya taimaka mata sai kuma narasa number har gurin da abun yafaru naje na tambaya koda wanda yasan gidan mutumin akace ba asan daga inda yake ba bantafi ba saida nabada number ta awajen nace musu dan Allah duk sanda akaga ko wucewar sa ne adakatar dashi sannan a haɗani dashi amma shiru shiru babu wanda ya kirani tun abun na damu nama har na fara cire shi araina sai da nagan ta yanzu nafara tunanin inda nasanta hirar da kukayi kuma yanzu ita ta ƙara tunamin inda nasanta wannan shine gaskiyar abun da nasan nayi, inna lillahi wa inna alaihi raji'un nashiga uku ni Aminatu, Ammi tashiga yin salati tana tafa hannu dan jitake kamar shi yaso yayi kisan kan Allah yaso bata mutuba, sai sallallami take takasa magana hawaye kuma nabin kan fuskar ta bossay kam jin kansa yayi a sama kamar a wata duniyar yake ta daban saboda shima anasa bangaren yanda Ammi take tunani haka shima yake tunani, Meer da ya kafesa da ido yana so yagano gaskiyar maganar sa amma yakasa tantancewa ya ɗago ya kalli maama itama shi ta kalla ganin yanda yake kallon tasa tayi masa alama da ido akan ya rabu dashi kada tace komai hakanne yasashi yin shiru tare da kawar da kansa, a tsanake  maama tafara magana, "kallon dady tayi tace "a labarin da ka bayar na yarda dakai idan da gaske kake idan kuma ƙarya kafaɗa to kasani zamu gano ka kuma idan hakan ta faru bazakaji da daɗi ba domin ko wani ya ɗaga ma ƙafa kasan wannan yaron bazai ɗaga maba dan haka ka nutsu da kyau kayi bayani da kyau idan kasan wanda yasaka ka buge gwanda tun kan loƙaci ya ƙure maka ka hanzarta sanar damu kafita daga cikin zargin mu saboda inba mu gano ko waye ba kai zamu riƙa saboda nidai da idona kai nagani kuma kaima kasan da hakan kamar yanda kabada labari yanzu ina me jan kunneka da kaje kasake tunani kasamo mafita tunkan binciken mu yafara aiki agano kana ciki yanzu ina ɗaga maka ƙafa ne saboda iyalen ka dan darajar su kake ciki ina fatan ka fahimta, dady ya buɗi baki zaiyi magana ta ɗaga masa hannun tare da cewa "kar kace komai yanzu zan nemeka yanzu na barka kayi nazari tukunna zaka iya tashi kar kuma kasa kanka adamuwa kasaki jikin ka kaci gaba da harkarka da iyalen ka, ku kuma nadawo kanku ta maida dubanta ga su Ammi tace "ku kwantar da hankalin ku kuma babu abun da za'ayi masa har sai munyi bincike akai banason ɗayan ku yayi wani tunani akansa marar kyau baku kaɗai bama kowa dake falon nan banason kowa ya ƙara tada zancen harsai loƙacin yin hakan yayi ina fatan kun gane kowa yasaki ransa, Ammi ce ta tsugunna agabanta tana zubar da hawaye tace dan Allah dan Annabi kuyi haƙuri abisa abun da yayi muku sannan kuma mungode sosai da karamcin da kikayi mana domin ba kowa bane da zai fuskanci irin abun da ki fuskanta kuma yaɗa gawa wani ƙafa nasan kinyi mana karamci sosai kuma ina fatan kada Allah yasa mijina yanadasa hannun aciki idan hakan ta kasance bansan inda zan saka rayuwata da ta ƴaƴana ba nasan sai nayi danasnin auren sa bazan taɓa yafewa kaina na auren sa batare da nasan halayen saba nazaɓeshi amatsayin uban ƴaƴana ba bazan taɓa j........ da sauri ummy ta tsugunna agabanta tare da dafata tace ya isa haka ki daina irin waɗannan maganganun ki kwantar da hankalin ki in sha Allah mijin ki bashi da laifi kamar yanda yafaɗa in Allah ya yarda hakanne gaskiya dan haka kar ki ƙara cewa komai kiyi shiru, Ammi na shirin yin magana kenan sukaji anyi nocking ɗin ƙofar falon bossay ne yataka da ƙyar yaƙarasa bakin ƙofar ya buɗe da dadda suka fara karo da sauri ya sunkuyar da kansa dan sai yaga kamar zasu gane abun dake faruwa su tsanesa, saura kaɗan dadda ta bugesa ta shigo falon cike da masifa ko kallon ƴan falon ma batayi ba idon ta akan Ammi tace wallahi wallahi wannan matar inajin sai na koma naci mata uwa dan wallahi bazan haƙura ba ai duk kuka jamin kubarni da abun dake damuna ma amma kunkai ni waccen me zubin albasa me lawashiɗin tazo tana gaya min magana shegiya da kai kamar fitilar ɗan iska  ya wani mulmule ita bajiki ba sai ɗan iskan ƙaton kai bakin rijiyar ƙauye, bossay ne ya kalle ta da mamaki yace "dadda ke dawa kuma Ni kinzo kinsaka ni agaba saikace ninayi miki laifin, duk ai ka kajawo mi da baka fitar min da jika ba ai da banfita daga cikin gidan nan ba wallahi danasan zan haɗu da wacce agwagwar da ban fitaba banza da ita kamar tsohuwar saniya, "Dadda dan Allah ya isa haka kishiga ciki ki kizauna, bazan shiga ɗin ba kai wallahi idan ban sauke haushina akan kaba Allah ya kwashe min albarka, sam dake bayanta yace " daman ai bakida ita andaɗe da kwashe ta, juyowa tayi zata kaimasa bugu yayi saurin shigewa falon tabi shi abaya tana cewa wallahi yanzu kayi min iskanci sai nayi maganin ka yanzu ba ɗazu bane bare kace zaka kashe ni da motar kuma nan ba motar kabace bare ka hanani magana yoo inbanda iskanci Allah ya yanka ma baki dan kabuɗa shi kuma ace za ahanaka magana bare kuma anyi maka laifi......, Mugu kawai azzalumi nadawo kanka wallahi sai Allah yasakamin cutar dani ɗin da kayi yau wallahi alhakina nayau bazai barkaba kaidai Allah wadai da halinka kuma wallahi kasani duk wanda yaci tuwo dani miya yasha domin dadda bata yafiya ko ba daɗe ko ba jima sai narama wulaƙancin da kayi min yau, ɗan ɗaga murya sameer yayi yace saidai ki rame kuwa san kurwata tafi ƙarfinki bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane idan kika kuskura kika bari muka ɗaura dake to wallahi saina baki kashi, da sauri ta ɗaga ƙafa zataje inda yake tare da cewa saidai kabawa waccen figargiyar uwar taka kashi marar mutunci yaro wallahi sai....... cak ta tsaya  da tafiyar da take tare da yin shiru sakamakon tozali da tayi da Ameesha agaban ta, dan ita duk wannan zubar da take bata kula da itaba tadai san da mutane afalon amma bata tsaya tantance fuskokinsu ba kasa motsawa tayi har saida dadda ta ƙaraso gabanta ta kira sunan ta sannan tace dagaske ne ko mafarki nake ko kuma gizo ne, ɗan murmushinn jin daɗin ganinta Ameesha tayi sannan ta faɗa jikin ta ta rungume ta tana cewa dadda nice fa ba mafarki kike ba kuma ba gizo bane niɗin ce da gaske dadda ta, itama rungumeta ta tayi sosai kamar zata mayar da ita cikin jikin ta saida suka daɗe suna rungume da juna sannan ta riƙe fuskar ta tace da gaske ne shalelena ce wannan ina suka kaiki  suka ɓoye min ke ina ta nemanki babu abun da ya sameki jiya dan nayi mafarki kina cikin mawuyacin hali faɗa min abun da yasameki danni naji ajikina mafarkin danayi bana banza bane dole da kwai ƙanshin gaskiya aciki wallahi saboda idan nayi mafarki da wuya baizama gaskiya ba...., Ameesha ta buɗe baki zarayi magana kenan maama tayi saurin dakatar da ita tare da cewa ya isa haka ku shigo ku zauna jin baƙuwar murya yasa dadda saurin maida dubanta ga inda tajiyo muryar suna haɗa ido da maama, maama tasakar mata murmushi,  murmushin da yasa dadda saurin ɗaukewa gaba ɗaya al'ajabi da mamaki da tashin hankali da shiga ruɗu duk aloƙaci ɗaga suka risketa domin kallo ɗayan da tayi mata tagama karantar ta gaba ɗaya, fuskarta ɗauke da mugun mamaki ta shiga kallon maama ta kalli maama na ƴan daƙiƙu sannan ta kalli Ameesha haka ta shiga yi ta kalli wannan ta kalli wancen, Ameesha ce tasaki lallausan murmushi ganin yanda dadda take kallon ta tasan dole tagane kamannin su shiyasa take binsu da irin wannan kallon, cike da murmushin da yaƙi ɓoyiwa akan fuskar ta ta kamo hannun dadda tace "dadda kingane tane irin wannan kallo haka mu zauna kisha labari wannan da kike ganin ta kakatace itace mahaifiyar ɗanki mahaifina....., wani irin yimm dadda taji ajikin ta yana mata yawo kamar sokuwa haka Ameesha take janta ita kuma na binta har takaita kan kujerar kusa da maama ta zaunar da ita sai kawai ta shiga kallon su abun sai burgeta ba ƙaramin farin ciki taji yana ratsata ba yau ga kakannin ta guda biyu agabanta tana kallon su mayar da idonta tayi kan meer yanzu shima ɗan uwanta tane sannan ta kalli Abu da shima yake kamar uba agare ta yau gata cikin dangin ta kuma nan bada jimawaba zata koma cikin gidan su abun da bata taɓa tunanin zai faruba arayuwarta tayi tunanin ahaka zata ƙare rayuwarta cikin wahala ashe akwai ranar farin ciki gashi yau tagani.........., duk abun da takeyi kowa ya zuba mata ido cike da tausayin ta ko ba afaɗa maka ba kana ganin yanayin ta kasan halin datake ciki, har yanzu murmushin da take baibar kan fuskar taba "tace dadda kinyi shiru kitayani farin ciki yau gani ga dangina, har loƙacin dadda takasa magana tayi shiru kurum ko mai take tunani da yasa ta kasa magana🤔..........✍️✍️✍️ *Special thanks 2 u♥️ina godiya da haɗin kan da kuka bayar jiya da waɗanda suka yi da waɗanda ma basuyi ba duk ina godiya gareku Allah yabar zumun ci yaƙara danƙon♥️* bansan sunankiba amma nagadai kina amfani da ALAHAMDULILLAH, ina godiya da irin comment ɗin inajin daɗin sa ɗari bisa ɗari amasu comment kece 1, kuma sauran masu yi ina godiya irin su👇 Maman amira Maman fateema Maman arman Maman faruk Mamma Rabi'atu mu'azzam Zulailkha ummu houria and Sameer fateema Usman Muhammad Ɗahiru mu'azzam duk wanda baiga sunan saba kuma yana yin commente to yayi haƙuri dan akwai waɗanda da Number ɗinsu ahaka nayi saving ba suna amma zan tambaye ku nan ba insha Allah sai mu haɗe ina fatan kun fahimce ni, Masu wannan number hardaku acikin +234 703 648 4184 +234 704 258 2726                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/13, 10:20 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 88 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️       "har loƙacin dadda takasa magana tayi shiru kurum ko mai take tunani da yasa ta kasa magana🤔..........✍️ ashe ba ita kaɗai take mamakin ba a ɓangaren su sam ma hakan take mamaki yagama cikasu jin maganar suke kamar amafarki, saida Ameesha ta girgiza ta tace  "dadda wai bazakiyi magana ba, kallon ta dadda tayi sannan tace"dagaske ne wai abun da naji kina faɗa kuma nagani da idona dan Allah idan bacci nake kar ki tasheni dan nasan wannan mafarkine ba gskiya bane nasan hakan bazai taɓa kasancewa gaskiya ko amafarki bantaɓa gani ba sai yau Allah ya nuna dan Allah karda wanda ya yashe ni daga baccin nan, mintsi ninta Ameesha tayi tare da yin wani murmushin tace dadda kin tabbatar yanzu ba mafarki bane ko in ƙara miki wani nasan idan kikaji zafi sosai zakifi yarda, kallon ta kawai dadda take amma duk da haka bata yarda ba kuma bata bar kallon taba saboda sai yanzu komai yadawo mata sabo fuskar sameer ɗanta take kallo kawai afuskar Ameesha sai taga kamar shine loƙacin da yake kamar ta daman Ameesha kamannin sa ta ɗauko sak shi kuma kamannin mahaifiyar sa ne (maama) dan haka duk wanda ka gani acikin su sai kagane kamannin su ɗaya, Ammi da ta lura da dadda fa kamar bata cikin hayyacin ta har yanzu yasa ta ajiye halin da take ciki agefe sannan ta dawo kusa da dadda ta riƙo hannun ta tace daddar mu ko nima sai nayi miki ta Ameeshan ne zaki dawo hayyacin yakamata idan ma mafarki kike ki farka ki kalli mahaifiyar ɗanki da kuma yayan ɗanki da ɗan sa gasu agaban ki nan duk dangin kine, dadda ta kalli Ammi sannan tace taya hakan zata faru nifa banyarda daku ba taya mahaifiyar sameer zatazo nan taya hakan zata kasance haba dan Allah ya kuke abu kamar shirin film, Ammi tace "to ki kalle su mana bagasunan agabanki ba kuma kema nasan kinga kamannin ko ba afaɗa miki ba sai kinfi kowa gane me kama da ɗanki, "eh nagani amma wannan ai idona ne yake min gizo nasan ba gaskiya bane kuma nasan ba gaske kuke ba tsokanata kawai kuke dan haka mubar wannan wasan tun wuri wannan bamai yiyuwa bane, tofa duk mamakin dadda suke da furucin ta duk wanna hujjoji gashi angaya mata kuma itama tagani da idon ta amma taƙi yarda sai antaro ta tanan sai ta kufce tacan taƙi fahimta har yanzu, maama ce ta tashi da kanta taje gaban ta ta tsugunna sannan tace baiwar Allah ba mafarki kike ba ki kalle ni da kyau nice mahaifiyar sameer kuma kakar jikar ki Ameesha sannan wannan da kike gani shima ɗana ne wancen kuma jikanane tana yi mata maganar tana nuna mata su duk wanda ta faɗi sunan sai ta nuna mata da hannu, da ƙyar dai dadda ta dawo hayyacin ta ta yarda sannan maama da kanta tabata labarin duk abun da yafaru, har haɗuwar su da su Abu da ganewar da tayi shima ɗan tane da aka sace mata shi acikin masarauta sai gashi yanzu Allah ya haɗasu duk aloƙaci ɗaya, amma bata bata labarin cewar baban su bossay shine wanda ake zargi ya bugeta ba a motar saboda tana jin tsoron abun da zatace akansa tunda taga itama bata da haƙuri kar take tayi masa tijara agaban matar sa da ɗansa shiyasa taƙi gaya mata wannan maganar, tana gama bada labarin dadda ta fashe da kuka ta jawo Ameesha ta rungume tana cewa Allah na gode maka Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana ashe burina zai cika kafin inbar duniya haka tashi ga jero godiyar ta ga Ubangiji tana kuka tana murmushi haka ta haɗa abu biyu aloƙaci guda yana yin da take maganar saida tabawa kowa tausayi Saida tasaka Ameesha kuka haka suka ringayin kukan su sannan suka raba jikin su da na juna, su sam ma ba ƙaramin mamakin wannan labarin sukayi ba shikenan suna sa ran zasu sha wahala sosai wajen gano su sai gashi Allah yakawo musu sauƙi sosai suka taya dadda da Ameesha murna, haka Abu ma yazo suka gaisa da dadda Ummy suka gaisa ummy nata tsokanar ta dan taga faɗan ta ita tun kan taganta taji matar ta kwan ta mata arai yanzu kuma da taganta sai taji abun yamafi wanda aka bata labari gaba ɗayadai falon bayan sun gama koke koken su suka dawo kuma taya juna murna cike da farin ciki amma duk wannan bidirin da akeyi banda sam ɗan yana tsaye inda yake ko motsawa baiyi ba shi ko gajiyama da tsayiwar bayayi kamar tsohon soja haka yayi musu aka kuma yaƙi buɗe baki yayi magana sai ma haɗe rai da yaƙarayi kamar anyi mishi albishir da gidan wuta haka ya haɗe rai tamau kamar anƙulle kunnu alaida haka yake ga idon nan har yanzu kalar su bata dawo daidai ba yana nan ajansa tun marin da Abu yayi masa baibar yi masa yawo akansa ba dan ji yake yau da wanine ya maresa ba Abu ba da wallahi saiya kaisa inda ba a dawowa sai ya rabasa da ransa, kiran sallar la'asr ne ya katse su sannan kowa yaje yayi Sallah suka dawo suka ɗora daga inda suka tsaya, bayan duk sundawo sun zauna dadda tana so tayi magana akan Meer amma takasa saboda taga ba kalar tabane tunda tazo bai kalli inda take ba kuma taga babu wanda yayi masa magana dan haka tayi tunani ma ko sojane shi idan yana abu ba tanka masa shiyasa iyayen sama suka kasa yi masa magana, ina ga ita kuma taje tayi masa magana ya zuciya ya harbeta agun bada itaba wannan kasadar shiyasa taja bakin ta tayi shiru amma duk da haka akai akai sai taɗan saci kallon sa ta gefe cikin rashin sa'a tayi masa wani kallo shima loƙacin ya ɗago jajayen idon sa suka haɗa ido da sauri ta kawar da idon ta tana tsoron Allah yasadai kar yace ta fito tundaga loƙacin bata ƙara gigin kallon inda yake ba ta maida hankalin ga hirar da akeyi acikin mutane tabar batun wancen me zubin yahudawan, sam dai yakasa yin sukuni agurin saboda tunda yaji an ambaci masarauta kuma baiji masarautar inba hankalin sa yaƙi kwanciya dan yana tsoron yaji ance masarautar suce akayi wannan zalincin duk da inma hakan ta kasance akwai wacce yake zargi daman aikwa idan yakasance gaskiya masarautar su ake nufi ai kai tsaye ita zasu damƙa basai sunjira wani dogon bincike ba, bossay ne yaƙara inda suke su biyu shima ya zauna akusa dasu tunda sauran ma duk suna surutu dan haka ba lalle aji maganar da zaiyi ba, kusa da kunnen sameer yakai bakin sa yace wai ya banga kana farin ciki ba kamata yayi kaima ka shiga cikin su nanfa duk ƴan uwanka ne wacen sojan ma dakukayi dambe ashe faɗan ƴan uwantakane, gabansa yaji ya faɗi yace wai kana nufin wannan labarin da masarautar mu yafaru wannan matar papa ce, bossay yace eh mana kai alabarin bama ka fahimci inda ake nufiba kenan kamanta loƙacin da muka haɗu dasu har na cemuku suna kama da Ameesha kace zaka tambayar mana kakan ka ko yasan ta ashema matar sace da ka tambaye da kaji me zaice, Shettima yace "kai to ai koni ban fahimci komai ba sai yanzu daka faɗa kumafa ka kallesa ka kallesu sai yanzu naga suna kama da wancen yafaɗa yana kallon inda Meer yake caraf suka haɗa ido ashe duk abun da suke idon sa akan su shi da yariga yasan komai akansu yasan ƴan uwane amma baijin zai iya karɓarsu amatsayin ƴan uwa dan har yanzu haushin sam yakeji da yasa ta dalilin sa mahaifin sa yayi masa abun da yafi tsana aduniya mari dan haka sai yarama akansa zaiji daɗi aransa kuma bazai taɓa kallon sa amatsayin ɗan uwaba, suna haɗa ido da shettima Meer yace"uban me kuke cewa anan kun haɗa kai kuna munafurcin mutane harda magana ƙasa ƙasa munafukai kawai sai nayi maganin ku dukan ku duk ɗagowa sukayi suka kalle harda su maama kallon sa sukayi saidai kuma idan ka kalli bakinsa sai ka rantse bashi yayi maganar ba saboda yana gama faɗar abun da zaice yamayar da bakinsa yanda yake, maama ce ta girgiza kai bata yi masa magana ba kawai ta mayar dakanta kan su sam da hannu tayi masa alamar yazo, jiki babu kwari yatashi yafara takawa har zuwa inda take zai tsugunna agabanta kenan tayi saurin saka hannu ta ɗagosa tare da rungume sa tace kasan ko ni wacece shine yanzu ma bazaka gaida niba  ni daman nasan taurin kan nan ba abanzaba na gwaggwo ne shiyasa ranar tun kan naga kamannin ka nagane halayen ka shiyasa ma na tsawatar maka danaga zaka yimin rashin kunya, "kai ɗan waye acikin gidan dan nasandai ba kai ba ɗan sarki Muhammadu bane, saidai jika, kansa asunkuye dan gaba ɗaya jikin sa yagama mutuwa kunya da nauyin matar duk sun mamaye sa yayi dana sanin abun da yayi musu ahanya baisan haka abun zaije yadawo ba gashi yanzu shike da kunyar abun, ahankali yace "eh ni jikan sane kuma jikan ɗa ga munbiya itace mahaifiyata, Masha Allah kai jikan Sa'adatu ne kenan Allah sarki matar nan akwai mutunci munyi zaman amana da ita  tana nan lafiya dai ko, "Eh" kawai ya iya ce mata ita kuma taƙara ce masa ina maryama itama tana nan ko, Eh yace maimakon ya kalli ta sai kawai ya gun da dadda take duk da halin da yake ciki saura kaɗan yasaki murmushi sannan yace ai da itama sukayi faɗa da wannan tsohuwar ya nuna dadda, kai kai maryaman ce take faɗa da wani ammadai to saidai idan ƙarshe ta kaita matar da take da haƙuri tunda muke bantaɓa jin ta ɗaga murya ga wani ba gaskiya saida idan ƙarshe aka kaita, ai kafin ma sameer yabata amsa dadda tayi saurin karɓe maganar da cewa wanna shegiyar matar ce ba ruwan ta to kwa saidai idan sanin da kikayi mata dan nidai akamannin ta banga haƙuri akan fuskarta ba ko kaɗan baya dashi da wani kanta kamar murhun giya, wai daman inda naje ne nanne masarautar da kuke magana akai ai bansani ba sai yanzu muna da alaƙa da cikin gidan ai zama bai kama muba yakamata kutaso yanzu muje gidan ko, maama ce ta ɗanyi murmushi sannan tace a'a bayan zuba sai mun fara bincike domin mugayen acikin gidan suke kuma bamu san suwaye ba dan haka muke so sai mun fara samun hujjoji tukun zamu je yanda muna zuwa muna da hujjar da zamu kama duk me hannu aciki yanzu daman waɗannan muke jira suzo su gaya mana abinciken da suka fara me suka gano tafaɗa tana kallo sam da yake zaune agaban ta, kai kai waɗannan mutanen saidai Allah yasaka muku dan sunriga da suncuce ku saidai muce   Allah ya isa tsakanin mu dasu mugaye azzalumai in Allah ya yarda sai Allah ya toni asirin su kuma ba wani ɗaga ƙafa da za'ayi wai sa anfara bincike wannan maganar ma ku manta da ita dole daga yau zuwa gobe ahaɗu amasarautar idan kuna nan taya zaku gane mugayen ai zuwan musu za ayi kai tsaye inyaso daga baya ayi binciken acikin gidan wannan shine babbar masalaha dan wallahi muna nan bata yanda za ayi agano su waye saboda ba ƙaramin shiri sukai ba ƙananun mugaye bane tsaf yanzu kina nan ke baki gano suwaye ba su su ganoki suƙara rabaki da gidan ko su salwantar da rayuwar ku gaba ɗaya tunda har suka koreku daga gidan baza su taɓa bari ku koma cikin gidan Indai suka gano kuna raye nidai anawa ganin gwanda kawai aje musu zuwan bazata atayar musu da hankali mukuma anan zamu zuba ido akan kowa mugane take taken marassa gaskiya sai mu maida hankalin mu kansu duk wani motsinsu yazamana akan idon mu zasuna gudanar dashi daganan har loƙacin da zamu kama mutum dumu dumu sai mukamasa da hujja ina ganin hakan sai yafi mana sauƙi kuma tahakane zamuyi saurin gano su, "Good thinking 👍, suka jiyo muryar Meer yace, sai yanzu ya matso kusa dasu sannan ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya tare da cewa "wannan tunani ne me kyau hakan yakamata ayi idan kun ɗauki shawarar tafa amma idan ma kuma baku ɗauka ba da banyi niyar sanar daku ba amma yanzu zan gaya muku ko bakujeba ko ninikaɗai me sai naje kuma ayu ɗinnan dan bazan iya barin abun araina ba ace anzalin ce ku kuma kunsan ko su suwaye kuma kunsan har cikin gidan da abun yafaru shekara da shekaru maama ba kya cikin gidan kuma ace ayanzu kindawo hayyacin ki kindawo cikin garin kuma zaki wani zauna aɓoye awani wajen inkikai hakan kina tsoron suma ai tun yanzu yakamata ayi duk abun da za ayi dan banga amfanin yin wani bincike wai abayan idon su abun da wannan matar ta faɗa shine gaskiya nafaɗa muku hakan bawai dan dole sai kunjeba amma nidai yazamemun dole inje kuma inna je zan iyayin abun da ba daidai ba dan zan kama duk wanda yazo hannu na da mai gaskiya da marar gaskiya sannan kuma zan sanar dasu ko ni wane agurin su....... maama ce ta shiga tafa hannun tace maganar ku gaskiya ce nima na goyi bayan hakan amma ba yau za ajeba mubari sai gobe sai muhaɗu gaba ɗayan mu muje kaima kayi haƙuri kar kace zakaje yau kabari muje tare gobe gaba ɗayan mu, maƙe kafaɗar sa yayi tare da taɓe baki irin duk yanda kukayi tundaga nan bai ƙara cewa komai ba nan dai suka cigaba da tattaunawa atsakanin su daga ƙarshe su maama sukace zasu koma gida inyaso gobe idan za atafi sai ahaɗu har su Ammi aje gaba ɗaya, gaba ɗaya sukayi na'am da wannan shawarar akan goben za ahaɗu, amma fa da jikata zamu tafi dan bazan iya tafiya inbarta ba, tayi maganar tana kiran Ameesha tazo zuwa tayi gabanta sannan ta riƙo hannun ta tace ai zaki bini ko..? kai ta ɗaga mata tana murmushi, dadda tayi saurin cewa au yau baya za anuna min shalele na tafiya zakiyi kibarni bayan kinsan nima na daɗai banganki ba ina buƙatar ki kusa dani na daɗe banji ɗumin kiba akusa dani kizauna tare dani tunda gobe zaku haɗu kinji, Ameesha ce ta kalle ta tace dadda kefa mundaɗe tare dake ita kuma fa yau muka fara haɗuwa dan haka nidai ita zanbi ida kuma baza ki iyaba sai kizo mutafi tare kawai muje can mukwana amma ni bazan zauna ba anan ai komai yana son canji dan haka na canzaki kema tayi maganar tana yiwa dadda gwalo, dadda ta riƙe baki tace au haka kikace ko to jiki adawo lafiya tsohuwar zuma ai da ita ake magani zaki dawo kisame nine duk inda kikaje, loƙacin kuma nima na daɗai da canzawa zan canza jika ne danma jikan todai bari inyi shiru dana ce wani abu amma dai shirun yafimin alkhairi, dariya wasu suka sa mata saboda sun gano ta jikan da take nufi Meer ne shikuma bataga fuska ba shiyasa tayi wannan furucin, Ameesha ma tagane ta dan haka tayi dariya itama sannan tace duk inda zakije ki ɗauko baza ki taɓa jin daɗin zama dashi ba, au🤭 namanta ashefa baki faɗi jikan namiji ne ko mace bamu san wanda kike nufi ba, harar ta dadda tayi sannan tace abar maganar ni ba wanda zan canza amma fa kema bazan karɓe kiba idan kindawo idan kika tafi kintafi kenan dadda tayi hakane saboda abar maganar meer dan taga alamar wasu sun ɓaro jirgin ta..., hakadai suka cigaba da wasa da dariya kamar babu abun da yafaru dasu (daman ance duk halin da kaka tsinci kanka kar kabari karasa farin ciki kayi ƙoƙari ko murmushi ne kasanyawa fuskar ka hakan zai rage maka wani raraɗaɗin dake cinka amma ace kullum dan abu yasameka ka tsaya kai ta sanyawa kanka damuwa abanza zaka cuci kanka wallahi kayi ƙoƙarin yakicesa gefe kayi rayuwar ka idan loƙacin damuwar ta tashi sai kayita aloƙacin sannan kaƙara kawar da ita) ataƙaicedai basu suka bar gidan nan ba sai bayan sallar magrib sannan suka tafi kowa yayi nasa guri sai kuma haɗuwar gobe me ban mamaki, acikin su ba wanda baya jiran goben nan tayi (daga ciki kuwa harda ni dan na matsu inga me zai faru gobennan Allah dai yakaimu da rai da lafiya daman ance inda ranka kasha kallo aduniya) amma duk wannan farin cikin da sukeyi banda sam dan gabansa har faɗuwa yake dan baisan me zaije yadawo ba gobe agidan su yana tsoron jin wani abun daban da baishirya jin saba ji yake kamar yaje ya sanar dasu kafin goben amma ba halin yin hakan shima dole yajira goben yaga abun da zai faru......., ************************* *MASARAUTA* _____*Fulani* " Fulani tunda su dadda suka fita itama anata bangaren take tayi tata masifar ita kadai bata da wanda zata sauke bala'inta akan sa tadade afalon guri guda takasa tashi daga gurin sai faman lissafo abun da zatayi wa matar nan duk inda take saitasa an lalubo mata ita dan bazata taba rabuwa da ita ta tafi hakannan taci galaba akanta tazo har inda take har cikin masarautar ta tagaya mata magana kuna ta tafi batare da andau kwakkwaran mataki akan taba ta dau lokaci me tsawo agurin kafin ta yunkura tana niyar barin wajen sai kawai taji turo kofa dakatawa tayi daga tafiyar datake tare da juyowa idon tane suka sauka akan hamza zaro ido tayi waje watakon wannan yaron bazai daina shigo mata guri kai tsaye ba kenan, da farko ta tsorata da ganin sa amma tunawa da magan ganun hajiya sarah yasa ta cire tsoran sa aran ta cike da masifa tace uban me yakawo ka kuma kashigo min guri batare da izinina ba wai kai dan gidan uban waye agarin nan, duk wannan abun da take masa ko ajikin sa sai murmushi ma da yasakar mata wanda yayi mata ciwo arai, ciki yatako kuma yanzu ma bai cire takalmin ba ya shigo har ciki yakaraso gabanta yana binta da wani banzan kallo sannan yace akwai abun da zakiyi ne anshigo din idan zaki fidda ni kuma sai kifitar dani dan na fahimce kin manta kashe din danayi miki dazu shiyasa har kika samu damar magana to kiyi duk abun da kika dama nima zanyi nawa muzuba mugani wanda yaji tsoro ya bari, haka kace ko haka kace ko to kwa zaka gani sai kasan yau wacece ni naga har yanzu baka san wacece niba labarina kake ji ko, nikwa nasan ko wacece ke saidai ki nunawa wanda baisan kiba ko wanda yake jin tsoron ki yafada yana galla mata harara sannan ya matsa daga kusa da ita tare da daga murya yace budurwata babyna kina ina haka yai ta kwalawa Azeema kira tunda baisan sunan taba daman dan haka yake ta kiranta da hakan, Azeema dake daki sarai tajiyo sa tun lokacin da yafara kiran ta kuma tagane muryar sa dan haka sai tayi banza dashi, itadai fulani ta zuba masa ido tana kallon sarautar Allah tanaso ta nuna dakewar ta amma takasa saboda idan ta kalli idonsa saitaji tabbas wannan yasan wani abun akanta saboda zakewar sa tayi yawa babu yanda za ayi ace yana irin wadannan abubuwan batare da yataki wani abun ba inagadai hajiya sarah bata fahimci maganar da tayimata ba da kyau bata gane zancen taba kodan bataga yaron ba amma wannan yaron akalaman sa ba wani bugun ciki dole yasan wani abun ammadai zata kara tuntubar ta takara gayama ta abun dake faruwa ko zata fahimce ta, wannan tunanin da takeyi ne yasa takasa tanka masa ta rabu dashi yagama abun da yake ya fice mata daga gurin, juyowa hamza yayi ya kalle ta sai kawai yace dan Allah dan kiramin ita najita shiru idan bacci kuna take kar ki tasheta kinji uwar masarautar su, yayi magana yana kara sakin murmushi, banza tayi dashi tasan so yake ya kunna ta daga baya kuma ya yabamata maganar da yaga dama yatafi yabarta dan haka kawai ta watsa masa mugun kallo me kama da gargadi sannan ta juya tabarsa agun ranta kamar zai fasa kirjin ta yafito saboda halin da take jin kanta ayau, yau abu biyu sun hadar mata ta rasa mafita dole taje takira hajiya sarah, binta yayi da kallo sannan ya girgiza kai tare da cewa "kadan ma kika gani wallahi sai nasa kin tsani kanki sai nasa duk sanda kika ganni sai nasaka miki faduwar gaba sai kin tsani ganina, har yana niyar juyawa yafita saiga Azeema ta fito tsayawa yayi yana kallon ta itama shi take kallo bata kalle sa da yawaba ta dauke kanta daga gare sa tana takowa zuwa inda yake saboda itama daman tana so suyi magana dashi akan wane irin sirri ne da matar nan take boyewa, dan haka sai kawai ta sakar masa murmushi, murmushin da ya kusa sa hamza zaucewa baigama cika da mamaki ba sai da yaji tace yi hakuri inajin kiranka ban fito ba ina shiryawa ne nayi wanka I'm sorry muje ko tafada tana nuna masa hanyar fita, ba karamin mamaki tabashi ba baitaba tunanin haka daga gareta ba ko kusa dan harma yacire rai da fitowar ta dan yasan baza ta fito ba idan taji muryar sa amma saigashi ta fito harda murmushi da bashi hakuri shikam yau ina zaisa kansa da farin ciki, hartaje wajen kofa bai iya motsawa ba saida tajuyo takara yi masa magana sannan yafara daga kafarsa yana takawa kamar wanda baida laka ajikin sa haka yake tafiya har yakarasa gabanta ita tafara fita sannan yabita abaya kamar rakumi da akala haka suke tafiya, suna fitowa waje ta tsaya shima ya tsaya kallon sa tayi tana jiran taji ta bakin sa amma shi saboda tsabar mamaki ya kasa magana saida tace inajin ka me yake tafe dakai, duk tana yi masa hakane dan tasamu sudan saba daganan sai tayi masa maganar fulanin dan yanzu bazai yiyu ace daga haduwar suba tafara yi masa maganar ba lalle bama ya kulata amma idan suka saba tasan wannan normal ne zata iya yimasa maganar kanta tsaye, zai bude baki yayi mata magana kenan sai tayi saurin dakatar dashi sannan tace "nan gurin da mutane da tawa na wucewa muje wani gurin ina ganin sai ya fi mana safe, "wai dan Allah da gaske kike wannan batun anya kuwa kece? Azeema tace da gaske nemana inkuma inkoma to sai intafi idan kagama mamakin sai kakirani, da sauri yace "a'a dan Allah karkitafi muje to saima in hadaki da baban nawa daman nace zan kai mashi ke dan yau cewa yayi bazai biyo niba, "Allah sarki ba komai muje ai yayi kokarima saboda nasan daga ji kai ka takura masa bayin kansa bane, dan murmushi yayi sannan yace " ya akai kika gane Wallahi kamar kinsani amma dan Allah kada kice a'a bazaki ba, akan me zance a'a nima ai zanso inje in gaida surikina, juyowa yayi da sauri ya kalle ta dan yakara tabbar wa wai itadain ce kuwa da gaske kokuwa watace adai daban dan baitaba tunanin tana magana ba haka kuma maganar ma dashi takeyin ta harda cewa sirikin ta ita ko kunyar sama batajiba to kodai daman tana sonsa itama tunda yace yana sonta itama take sonsa kawai taki nunawa ne saboda jan aji irin na mata, ganin yatafi tunani ya s a ta dan daga hannun ta tana cewa "hy" da sauri ya dawo hayyacin sa , tunannin me kake ne haka tun adazu ina ta magana, tunanin ki nake wallah ai ni kullumma cikin tunanin ki nake tunda naganki har yau bansake jina daidai ba sai yau ada naganki gani gaki hakan bakaramin farin ciki bane agare ni bazan taba mantawa da wannan ranar ba yaudin ta musamman ce agareni babbar rana dan tunda na hadu dake ranar farko nake wannan mafarkin inaso in kasance dake akoda yaushe Allah yasa yanda nakejin ki araina kema kiji koda rabin yanda nakejine zanyi farin ciki da hakan dan Allah ki taimakawa rayuwata yayi maganar yana kafeta da ido shiru tayi takasa basa amsa, ganin hakan yasa jikin shi yin sanyi dan haka sai kawai yayi shiru baikara cewa komai ba yafara tafiya, ta fahimci halin da yake ciki sai taji kamar bata kyau tamasa, atsanake tafara magana yanzu haduwar muce tafarko dan haka bazaiyiyu kace duk wata tambaya sai na baka amsaba kabari zuwa wani lokacin sannan nagama karantar hakayen ka dan haka karkasawa kanka damuwa akan naki cewa komai game da baya nan dakake min ina fatan ka fahimce ni, yaji dadin bayanin da tayi mishi dan haka sai kawai yace babu komai wallahi nikoda iya kulawar da kika yiminne ma kadai ta wadatar dani babu abun da zance miki sai godiya, ahaka suka ringa tafiya sauna hirarsu kamar daman tuncan sun daade da sanin juna saida suna tafiya wasu na kallon suna gulmar su babu dai wanda ya iya tarar su yace musu wani abun dan ansan halin hamza yanzu zaici uban mutum ko waye shi shiyasa saidai suyi abayan idon sa babu wanda ya isa yayi agaban sa, saida sukaje wajen wata kwana sannan yace ta tsaya anan bari yaje ya kira shi tace a'a mutafi tare kawai ni bazan iya tsayawa anan ba naga tunda muka taho yan sa'ido sunyi yawa bana son wani yayi magana iadan suka ganni anan gurin duk da nasan idan nashiga cikin ma zan kara jawa kaina magana ammadai gwanda hakan da wasu suganni nikadai anan, washe baki yayi yace to shikenan muje nima zanso haka daman abun da yasa nace ki tsaya nayi tunanin ko baza kiso shigar ba, mezai hanani kwa shiga tunda har nataho ai shiga bazata min wahala ba, to godiya nake muje gaba yayi ta ashiga binsa abaya har suka karasa bangaren su, abakin kofar suka tsaya sai hamza ya kwankwasa kofar tare da cewa baba yi sauri ka bude, shiru basuji muryar baba dan haka sai yatura kofar yasakai ciki yashiga sannan yace ta shigo ganin adakin yayi babu kowa atunanin sa ko bandaki yashi ga dan haka sai yadan nuna mata wani kan benci dake cikin dakin daga gefe yace ta zauna akai, shiru shiru baba bai fitoba kuma baiji motsin ruwa ba sai yadan matsa kusa da kofar yace "baba kana ciki kuwa shiru nan ma dan haka sai ya kwankwasa kofar amma baiji motsiba sai kawai yatura kofar wayam baba baya ciki, kashhh yafada tare da juyowa yana kallon ta yace ashe duk wannan jiran baya ciki ko ina yatafi anan fa na tafi nabarsa akwance yace min baya son fita ba inda zashi ashe ya canza ra'ayi ya fita bari inje induboshi ki zauna anna kijirani yanzu zan dawo kinji ko, da har zatabishi sai kuma dai kawai ta tsaya tace to adawo lafiya amma kayi sauri, yace yanzu kuwa ai nasan ba nisa yayi ba yafada yana fida daga dakin da sauri, fitar keda wuya yana dan yin wata kwana kawai sai yaga dandazon fadawa suna tunakarowa wajen sa suna nuna sa da hannu, cak ya tsaya yana jiran karasowar su yaji dame suke tafe, suna karaso basu jira wata wataba bazato ba tsammani kawai yaji sunyi sama dashi duk son nuna karfin sa wajen kwaton kansa amma ina yakasa sarkin yawa yafi sarki karfi haka suka dauke sa cak sukayi hanyar fada dashi...., agaban sarki suka dire sa sannan suka ƙara komawa ba jimawa sai gashi sun shigo da Azeema ciki still dai ƙara fita sukayi sai gashi sun ƙara dawowa yanzu kuma baba suka ƙara shigowa dashi loƙacin da suka shigo da baba su Azeema kansu na ƙasa domin indai kana gaban sarki baka isa ka iya ɗaga kanka ba, shima bayan an ajiyesa ya sunkuyar da kai yana tunanin me kuma yayi dan hakannan yana zaman sa awajen wata bishiya sukaje suka kamosa yasan ko ya tambaye suma ba amsa zai samu ba dan haka yayi shiru bai tambaya ba, ran sarki yagama ɓaci inyayi dubu to duka ya ɓaci domin ƙarar su aka kawo wai angan su tare sun shiga ɗaki suna baɗala duk wani halin hamza da yakeyi Saida aka gaya masa da rashin wulaƙancin da yakewa fulani shi duk bai san abun dake faruwa ba sai yau, dan haka baijira jin ta bakin suba ya umarci ta afara yiwa Hamza dukan mutuwa sai anga yadain motsi sanann akoma kan tsohon shima ayi masa duka mutuwa sai anga baya motsi saboda ance shiyake zuga Hamza yake yin duk abun da yaga dama sannan itama yarinyar ayi mata har sai ta daina motsi sannan akwashe su aje can dajin masarauta a haƙa rami me zurfi asaka su gaba ɗayan su aci arufe da ƙasa, jin irin wannan hukuncin ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba gaba ɗayan su domin hatta Hamza yau ya tsorata da jin wannan abun ko ba agaya masaba yasan munfurcin su akai gashi kuma mutanen da zasuyi dukan hayar su sarki yasa akayi masa manyan mutane ne ƙarfafa bama na cikin masarautar bane bare yace zai iya dasu yasan sunfi ƙarfin sa bazai iya ƙwatar kansa ba gashi kuma abun da yafi tsaya masa arai shine jin za ataɓa baba da kuma masoyiyar sa yanzu wazai taimakawa acikinsu yasan muddin akayi musu wannan dukan tofa babu me rayuwa acikin su duk sai sun rasa rayukansu yanzu ta ina zai samo mafita yana wannan tunanin bai gama samo mafita ba yaji anfara sauke masa bulale mutane sunfi biyar ko wanne ɗauke da tasa wasuma da katako suke dukan sa hannun yasa yana kare kansa tare da runtse idon sa duka ta ko ina yimasa suke kan kace me jikin sa har yafara farfashewa jini na fita daga jikin sa ana dukan sa yana jin zafin amma hangowa yake anayiwa su baba bare Azeema da take mace shi kansa ya yakejin zafinta bare kuma ace su ake daka tausayin sune yakama sa duk dauriyar sa da jarumtar sa baisan loƙacin da hawaye suka fara saukowa daga idon saba, Azeema da taji dukan yayi yawa duk da atsorace take amma batasan loƙacin da wata jarumta tazo mataba yaji bazata iya ci gaba da jin hakan ba duk da aƙulle idon ta suke bata gani amma kunnuwan ta suna jiyo mata ƙarar saukar bulalen da kata kwaye tun tana sa ran zasu daina hartagaji da sai rai fuskar ta kwa ta gama wankewa da hawaye, tagama shiga tashin hankali bata taɓa tunanin muguntar tasu takai haka ba sai yau ta tabbatar da cewa suɗin azzalumai ne basu da imani, aɓangaren baba ma hakan take baba ya tsinci kansa cikin tashin hankalin da bai taɓa shiga ba tunda yake dan ko dukan da akayi masa ranar da yafara zuwa baikai ko rabin wannan bai kamata ace yana kallon wannan yaron cikin wannan yanayin ba duk da yasan shima za azo kansa amma ayanzu dai shi yake tausayawa jiyayi bazai iya cigaba da kalla ba gwanda ya shiga shima su haɗasu loƙaci guda idanma kashe sunne su kashe su atare su huta kamar haɗin baki atare Azeema da baba suka miƙe cike da kwarin gwiwa suka nufi gurin Hamza duk da su kansu sun san baza su taɓa ƙwatan saba daga hannun su, Hamza da zaman yagagara har yakai ga kwanciya ƙasa tun yana kare kansa har yadaina domin babu inda yarage ajikin sa da ba adaka ba amma duk da halin da yake ciki hakan bai hanasa ganin su baba zasuyo kansa cikin wahalalliyar murya yace kar kuzo karki zo amma ina bashin zasu dakata kuma duk wannan abun tsakanin baba da Azeema babu wanda yakalli ɗan uwansa gaba ɗaya hankalin su yana kan hamza, suna ƙarasawa baba ya durƙusa kan hamza dan sukan da ake masa yadawo kan gadon bayan sa ɗaya ne daga cikinsu ya riƙe Azeema tun kan takai gare su, wani kuma yasa hannu ɗaya ya finciko baba daga kan hamza yana ɗagosa ya ɗauke sa da mari atake jin baba yaɗauke gaba ɗaya idon sa suka fara ganin dishi dishi ɗagowar da akayi masane yasa Azeema ganin fuskar sa amugun haukace ta ƙwace jikin ta daga hannun ɗayan zatayi kan baba yayi saurin tiƙeta ƙam yanda bazata iya ƙwacewa ba, wanda ya riƙe baba ne yaƙara ɗaga katakon hannun sa ya bugawa baba akai take baba yatafi Luu yafaɗi aƙasa, da ƙarfi Azeema tace babaaaaaa!!!!!!!! muryarta Saida ta karaɗe duka cikin fadar ƙoƙarin ƙwace kanta take amma takasa sai fusge fusge take tana cizonsa da ya ƙushinsa amma yaƙi sakin ta duk tabi ta fice daga hayyacin ta ta koma kamar zararriya hawaye kwa zubowa kawai suke kamar anjima famfo, wani rin wurgi mutumin yayi da ita ta faɗin ƙasa kan ta ya bugu da bango amma duk da azabar da taji haka ta ƙara tasowa da gudu tayi kan baba tana daf da ƙarasawa wani yasaka mata ƙafa tafaɗi aƙasa faɗuwar da tayi saida bakinfa yafashe amma duk dahaka ta mahaifinta take so take kawai taje wajen sa da rarrafe tafara jan jikinta zata ƙarasa wajen sa daidai kan ya tsunta wani ya taka mata shi da iya ƙarfin sa yataka duka hannu biyun, ƙara tasaki tare da ƙara komawa ta kwanta tana kallon ya tsunta dan atunanin ta ko suncire ma gaba ɗaya, kuka sosai ta fashe dashi, duk abun da ke faruwa duk sarki na kallon su kuma hakan nayi masa daɗi, dake yanzu hankalin su baya kan Hamza hakan yabawa Hamza damar ɗaga hannun sa da ƙyar yasakashi a aljihun wando sannan ya lalubo wata ƴar ƙaramar waya da baza kataɓama tunanin waya bace a ɓoye ya shiga daddannata batare da yana kallon taba ya daddana wasu nambobi sannan ya dannawa number kira kuma yaskata a hansfree sannan ya danneta nan take ta shiga ringing da ƙarfi bugu biyu aka ɗaga yana jin anɗaga yayi dauriya da ƙyar ya iya buɗe bakin sa tare da ɗan ɗaga murya sama yace ummaaa kiyi sauri kizo akwai matsala zasu kashe mu, cike da ɓacin rai muryar wacce aka kira da umma tace suwaye kuma kana ina!? "cikin fada.............✍️✍️✍️ "sainaga ruwan comment yaseen zanyi typing gobe idan kuma kuka naɗai hannun ku kuka ƙiyi nima zan naɗe nawa naƙi yi gobe💃💃💃💃💃😜😜                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖 *LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent)          [7/15, 8:23 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 89 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️         ________*RASHEEDA*😜😜🤣 "zaune suke ita da ƙawayen ta wajen susu biyar ita ta shida ko wacce taci uwar kwalliya sun saka kaya ɗamammu mayafai akafaɗa ga ɗaurin ɗan kwali ko wacce da kalar nata saikace masu zuwa gidan biki saɓanin  Rasheeda da take sanye da doguwar riga kawai ta ɗan ɗora mayafin kanta tare da ɗan zamashi kaɗan gashin ta yafito ba laifi itama fa kyakkyawa ce son kowa ƙin wanda ya rasa,suna cikin wani restaurants ko wacce gaban ta cike da abinci me rai da lafiya da sukayi order awajen bakajin bakin kowa saboda cin abincin da sukeyi kowa hankalin sa nakan kwanansa banda Rasheeda da tayi zaune tana kallon su  saboda ita bata cin abincin sukaɗai ta siyawa ita banda ita ake ci tanaso sugama su tashi daga gurin dan ji take zaman gurin ya isheta dandai sun takura matane shiyasa suka fito adaren nan suɗin ƙawayen tane da suka fara zuwa tunyanzu ace warsu gwara suzo ayi komai dasu daman kuma ita takirasu suzo afara shirye shiryen biki saboda sai anyi kwana goma cif ana kwasar sabada dan haka dole sai anfara shiri sa wuri, duk yau sukazo daga gida jensu suka sauka agindasu bayan sungama hutawane suka sakata agaba sai takawo restaurant dan anan suke sha'awar suci abinci yau saida tace dasu ma zata saka ayo musu order amma sukace su sunfi so suje da kansu dan haka bayanda ta iya dole ta kwasosu amota suka fito bayan sun fito ɗin ma zata kaisu wani waje ɗaya daga cikin su tagaya mata ai ga gurin da suke son zuwa wajen babban restaurant aduk cikin kano babu restaurant irin sa yafi kowanne tsaruwa da tsada da komai da komai saboda ko baƙi akai daga wasu ƙasashen ko kuma masu kuɗin garin da ƴan ƙarya duk nan suke zuwa gurin yayi fice ako ina da ina kowa yasanshi sunan gurin(XEEMAT RESTAURANT) ga masu son zuwa sai su gaggauta zuwa dan bawa idon su abinci suga tsaruwar gurin😜😜, ɗaya daga cikin sune tafara gamawa ta ɗau tissue ta goge bakinta sannan tace nagama saura ku wata tace nima na kusa gamawa ai bajimawa mutum biyu suka ƙara gamawa yarage saura mutum biyu su gama suma kuma sun kusa gamawa dan ma yanga suka tsaya da tuni sun gama, cikin zaro ido ɗaya daga cikin su ta furta "wow!! oh my gosh tafaɗa tana yarfa hannu, duk ɗagowa sukayi suna kallon ta ɗaya ta taɓota tace zee yadai me kika gano saboda sunjuya inda sukaga tana kalla basuga komai ba shiyasa ɗaya tayi saurin  tambayar ta, saboda tsabar ruɗewar da tayi tama kasa bata amsa sauran saida suka shiga tambayar ta kafin ma ta basu amsa ta ƙara ganin sa gurin ta ƙara kalla tace nashiga uku ku kalla wayyo Allah na gaba ɗayan su suka maida dubansu gun datake kalla ai sai suka nemi su fita haukacewar, Rasheeda ita harda miƙewa ma wajen kallon sa bakinta yama kasa motsawa haka suka zubawa masa ido har ya fice daga gurin, sannan wata tace "daman akwai irin waɗannan mazan agaske? wata ta karɓeta da cewa "nima dai abun da nake tunani kenan kowacce da abun da take faɗa, buɗar bakin Rasheeda sai cewa tayi 'ina son sa gayen yayi min banason in rasa wannan daman kutashi mubi bayansa dan wallahi bazan bari ya kuɓuce min ba sai nayi masa magana kutashi mutafi ta faɗa tana miƙewa daga gurin, Wacce tafara ganin sa tayi saurin miƙewa tace haba baby Rash ke da aka kusa bikin ki me zakiyi da wani ai mu yakamata kibari mu yaƙeshi kedai kuyi haƙuri da wanda kika samu ko ya kukace biyu daga cikinsu suka ce zancen ki babu ƙarya aciki baby Rash hakan yakamata ayi, wata mahaukaciyar harara ta maka musu tace ku kun isa ina ruwana  da bikina da aka kusa ai ko ranar ɗaurin aure ne nayi tozali da wannan guy ɗin zance nafasa ne bare kuma bikin ko zuwa baiyi ba ina gayawa dady na nasan zai yarda afasa wannan ba matsala bane, dan haka kada wacce ta sake magana akai inma da wacce take sonsa ta haƙura zan biyaku ko nawa kuke so ku tayani farautar  kar wacce kuma ta ƙara yimin maganar wancen kumanta dashi, ihu sukayi jin zata biyasu daman sunsan tafi ƙarfin su ita zata iya gogawa dashi su daman basu ɗorawa kansu ba dan haka rabuwa dashi abune me sauƙi, Suna murna suna cewa wallahi munbarmiki indai zaki biyamu bamu da matsala da hakan muje kawai kar ma yayi mana nisa dannaga yanda yake tafiya ba wani sauri yake ba, zee tace "daman yana kalar madara taya zai iya yin wani sauri gayen fa ta ko ina yayi ba ƙarya daga gani kuma mugun me kuɗi ne wallahi Allah dandai hajiyar mu ta ƙyasane amma da ko ba boka ba malami da kisisi na sai nayi wuff dashi, Rasheeda ta harare ta tace "basai kiyi mugani ba ni dan Allah ku muje kun tsaya kuna ta surutu har sun juya zasu tafi sai Rasheeda ta tsaya tare da juyowa ta kalli wata daga cikinsu da take zaune agun bata da niyar motsawa kuma tunda suka fara surutun su babu wanda yaji bakin ta batace ko A ba azancen nasu, kafin ta buɗi baki rayuwa ɗayar magana zee ta ƙara cewa yadawo yadawo kunganshi kunganshi duk rikicewa suka ƙarayi suna sunbatu akansa ta gefen su yazo yaƙara wucewa basudaina kallon saba saida kaga ya shige wani waje sannan suka fara dawowa cikin hayyacinsu, cigaba sukayi da kuruntashi suna yabon irin zubinshi da halittar su da irin kyaun da Allah yayi masa kamar shi yayi kansa, Zee tace ƙawata idan kika samu  wannan guy wallahi kinyi wa sauran mata fintinkau dan ba wacce zata kai ki ke ko ƙafarkima baza akamokiba har na haskoko wallahi baƙaramin dacewa kukayi ba kingani kuwa, fari Rasheeda tashiga yi da ido tare da sakin wani kayataccen murmushi tana jin wani farin ciki da sonsa na ratsata jitayi da yazo wucewa kamar take ta rungume shi kallo ɗaya yagama tafiya da imanin ta dan har tanaji aranta idan bata sameshiba zata iya shiga mawuyacin hali daman irin mijin datake mafarki kenan kuma gashi yau Allah ya haɗata dashi dan haka dole tabi hanyar da zata sameshi dan ganin bai kuɓuce mata ba bata son tayi wasa da wannan damar da tasamu yanzu ita kaɗai yasan abubuwan datake ƙissimawa aranta idan suka fara haɗuwa dashi sai ta rikikkishi da nata salon saitasa kallo ɗayan da zai fara yi mata yaMana yagama susucewa kanta loƙaci ɗaya zatasaka masa sonta aransa, juyawar da zatayi idonta ya sauka akan ɗaya daga cikin ƙawayen nata dake zaune akan tabur ɗin bata tashi  ba tun ɗazu yanzu kuma sai suka ga ta kifa kwanta da tabur ɗin ta ɓoye fuskarta, gabanta Rasheeda ta ƙarasa tare da ɗan buga tabur ɗin, tana ɗagowa suka haɗa ido da ita sai ƙawar tayi saurin janye idonta tana shirin ƙara mayar da kanta ta kwanta, Rasheeda tayi saurin dakatar da ita tare da cewa "ke kuma baƙin ciki kike munne da kikayi zaune baki da niyar tashi zee tace nifa tun ɗazuma nake lure da ita batayi magana ba kuma dai nasan halin momy da son maza masu kyau da surutun tsiya amma banji tace komai ba anya lafiya kuwa kodai wani abun kike shiryawa daban, da ƙyar ta tattaro sauran yawun da baigama bushewa ba abakin sannan ta ɗan samu damar miƙewa jikin ta har karkarwa yake ta matso kusa dasu sannan ta kalli Rasheeda tace bana miki biƙin ciki tunanin zakice hakanne ya hanani magana tun wuri amma nidai shawarata agare ki da zan baki shine duk inda tunanin ki yake kiyi gaggawar dawo dashi cikin jikinki kidaina furucin da kike ki koma gurin wanda kike so yake sonki gun da za ariƙe ki da mutunci domin wannan mutumin da kike gani ba alkhairi ne agare kiba karkiyi kuskuren shiga hanyar sa kijawowa kanki bala'in da baki taɓa gani ba, domin wannan da kike kira da gaye ba gayen arziƙi bane yafi ƙarfin ajinki da tunanin ki, cike da zafin rai da masifa Rasheeda kamar ta rufe ta da duka tace ta daka mata tsawa da cewa momy ya isa haka nace ya isheki haka afaɗin garin nan ke harkina da bakin cewa wani yafi ƙarfin ajina ki kalle ni da kyau meye bani da shi da akesonshi ajikin mace wanda bani dashi idan kuɗi kike magana kekinsan ko ni wacece basai angaya miki ba dan haka wallahi naƙara jin kinfaɗi kalmar da bata dace ba sai nayi ƙasa ƙasa dake agunnan nidaman nasan baƙin ciki ne da hassada ne suka hanaki magana tunɗazu sai yanzu da kika kasa riƙewa hassadar tafi ƙarfinki kinkasa jurewa sai yanzu zaki bayyana ta daman ana gayamin kina min zagon ƙasa bana yarda sai yau da kika nuna min halinki a fili nagane hakan to zansan zaman da zanyi dake daga yau, murmushin ta ƙaice momy tasaki sannan tace kinsan ai da halina ne hassada da tuni kin sani waɗanda suke zuwa suce miki ina miki zagon ƙasa saidai idan su suke miki amma bani ba ni bana mufurci bana yin zancen wani abayan idon sa kana min ba daidai ba zan gaya maka kayi min ba daidai ba danni banga abunda wani ya isa yamin ba wanda Allah baiyi min ba shiyasa banajin tsoron mutum da zan kasa cewa wani abu gaban sa ba indai kinga nayi zancen wani abayan idon to na tabbatar zan iya yi agaban sa koma na riga nafara gaya masa kafin inje wani wajen inyi dan haka ki adana kalamanki ba akain yakama kiyi suba kije kiyi a inda ake munafurtar taki amma ba waje naba, ɗan dakatawa tayi sannan ta juga ta kalli sauran ƙawayen tace Inma acikin kune wasu suke faɗa mata haka to kuci gaba kunriga da kunsan halina wallahi duk wacce nakama tana min munafurcin abun da banyi ba to ta kuka dakanta dan ba wacce zan ɗagawa ƙafa kunfi kowa sanin halina kunsan kuma ko ni wacece dan haka muzuba mugani wata ta buɗi baki zatai magana Rasheeda tayi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannun, wacce suka kira da momy Rasheeda ta shiga bi da kallon banza tunda ga sama har ƙasa sannan tace kingama borin kunyar taki daman ance tabar mar  kunya da hauka ake naɗai ta saboda ankama ki ƙiriƙiri kina min hassada da baƙin ciki shine kike wannan zubar to kodan saboda ke nikuma zan nunamiki iyakata zannun miki ajina yawuce nasa saina kawo miki shi har gabanki sai yazama atafin hannu na sai najuyasa yanda nakeso sai nasa ya mutu akan sona idan kin isa ke kuma ki dakatar, wata mahaukaciyar dariya momy ta saki da har saida ta ɗan basu tsoro suka fara tunanin me yame damun ta kodai ba ita kaɗai bace, saida tayi mai isarta sannan tashiga nuna Rasheeda da hannu wata dariyar na ƙara cinta da ƙyar ta daure tace wai kijuya sa lalle wannan mutumin ne zakisa ya mutu akan sonki ko to Allah yabawa me rabo sa'a da nayi niyar sanar dake ko shiɗin waye amma tunda ta haka kika biyo zan barki kije jiki magayi domin wance mutumin ba irin mutanen da kika sani bane idan nace miki nasanshi bazaki yarda ba amma idan kun haɗu dashi kyafi yarda dani sannan kuma nima zan ƙara miki ƙarin bayani akansa duk iskan cina da jiji da kaina da surutu na kika ga nayi shiru ai kinsan ba ƙalau ba saboda tunda muke daku nasan baku taɓa ganin hakan daga gare ni ba kamata yayi ku tambayeni dalili amma kuma alaƙanta hakan da hassada nake to naji muje ahakan bazan ƙara ƙoƙarin dakatar daku ba sai kundawo danni nan ko ta hanyar da yafita bazan fita tanan ba zanbi ta hanyar baya intafi insamawa kaina lafiya da kwanciyar hankali dan wallahi duk wannan maganar ma danake muku dauriya ce kawai amma ba adaidai nake ba idan naje gida nasamu nutsuwa zan kiraku adawo lafiya Mrs MEER in antashi biki zan tayaki murna koda ta wayane amma bazan zoba saboda ina kishi dake ga hassada da baƙin ciki da sukayi min yawa kamar yanda kikace kuje Allah bawa mai rabo sa'a Allah ya haɗaku kuma idan ya haɗaku kar yarabaku sannan kuma karma wani yarabaku Allah yabarku tare dan wallahi wannan gayen da kike gani babu abun da baidashi domin irinsu aduniya basu da yawa basufi su ukuba shiɗin na musamman ne gashi kema ta musamman ba ƙaramin dacewa kukayi bafa badan badan ba dana tsaya naga yanda zaku bada kala idan kun haɗu nasan ba ƙaramin matching zakuyi ba hmmm kar na cikaki da surutu bari inbarki haka ni kinga tafiya ta daga nan kuma sai gidan mu taba kaiwa nan bata jira cewar su ba ta juya tabar wajen da suri daya daga cikin su tayi saurin tarar gabanta tace momy dan Allah ki gaya mana abun dake faruwa mana ya kike mana magana me harshen damo nidai daman bance kina hassada ba amma kada kibari kawarmu ta cutu idan kinsan mutumin nan da wani mugun hali ki sanar da ita kawai, waima dan Allah intambayeki a ina kikasan wannan mutumin nidai tunada nake dake bantaba ganin saba kuma bantaba jin kin bamu labarin saba yakamata ki sanat damu inda kika sansa nasanki da shige shige watakil awajen shige shihgen naki kika gano sa yayiwa wani rashin mutunci shiyasa kema kika tsorata dashi dan na fuskanci kamar kina tsoron sa, Rasheedace ta daka mata tsawa tace ke bibi ki rabu da ita akan me zaki dakatar da ita ki barta ta tafi taje duk inda zata kuma bana bukatar sanin komai daga gare ta indai akan wannan guy din ne tagama haukan ta ta tafi nikuma zan bata mamaki sai na nuna mata ko wacece ni, dan murmushi momy tayi sannan ta kalli yarinyar da ta dakatar da ita sannan ta make kafada tare da tabe baki sannan tace to kinji me tace ko dan haka wannan ba matsalara bace sai kuntaho idan kuma da wacce take son ranta da lafiyarta tazo mutafi ta mutu adakin uwarta maza sukaita to ta rufawa kanta asiri tazo mutafi idan kuma kun zabi zama da ita sai kuzauna jiki magayi tana fada ta juya taci gaba da tafiya har tayi nisa bibi ta kwala mata kira tare da cewa momy jirani mutafi tare dan wallahi bani tsayawa nima jiran ta tayi tana karasawa kuwa gurin ta sukayi tafiyar su susu biyu, Rasheeda in ranta yayi dubu tofa gaba dayan su sun baci yau wadannan yaren sun nuna mata halinsu aikwa yanda suka tafi ko gidan su ta koma ta gansu sai taci musu mutuncin da basu taba tunani ba dan tasan basu da inda zasu kwana saboda basu da kunya yanzu gidan su zasu koma suce zasu kwana  har ita zasuyi wa haka, sauran yan matan ne suka shiga bata hakuri suna zizzigata akan ta rabu dasu wallahi kar ta daga musu kafa, tunda har suka juya mata baya alokacin da take bukatar taimakon ko wannen su amma zasuyi mata haka musammanma momy da tagama yaba mata magana son ranta kamar Rasheedan ba gaba take da ita ba dan agirme Rasheeda ta girmi wajen mutum uku acikin su, nan dai suka shiga famfata suna kurantata, sannan suka shiga bata shawarwari akan kar tabari maganar su ta bata mata rai da bari yanzu su fara zuwa wajen wancen din ta gyara kanta ta saita kanta ta dawo normal kamar babu abun da yafaru da ita ta kimtsa jikin ta yanzu su nufi inda suka ga ya shiga, wata tazaro mata  powder tabata ta shafa sannan tasaka turare me ƙamshin gaske da ɗaukar hankalin wanda ya shaƙa, zee tace ƙawata naso wallahi ba wannan rigar kika sakaba gashi yanzu duk ta ɓoye miki kayanki naso ace wata fitinanniyar riga kika saka yanda kike da shape ɗin nan nasan yana gani zaki ɗaga masa hankali, ɗan murmushi Rasheeda tayi tace kar kudamu da wannan hakan ma nasan yanda zanyi tafiya komai ya girgiza taku ɗaya girgiza saba'in kwashewa sukayi da dariya daya tace ta gurina shiyasa kike burgeni kinsan takan komai, hmm kedai bari muje dan na ƙosa ingansa kusa dani banaso yagama abun da yake son samuma insame sa yana cin abinci hakan zaiyi min daidai, gaskiya ne babbar yarinya kinsan takan komai muje to tafiya suka shigayi gaba ɗayan su itace agaba tundaganan ta canza takun ta tashiga tafiya cikin rangwaɗa da karairaya kamar za aɓala jiki anayi ana girgiza jiki komai na motsawa ahaka suka ƙarasa gurin suna shiga kuwa suka hango sa can kan wata kujera sai ɗan ƙaramin table agaban sa ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yana girgiza ta, wani farin ciki taji yaƙara nunkuwa akan nada daga bakin ƙofa suka tsaya ita kuma ta shiga takawa ahankali zuwa garesa anayi ana girgiza dan ta yanzuma tafi ta ɗazu ta nufi wajen sa......✍️✍️✍️✍️ masu karatu mai zai faru da Rasheeda mugaya mata gaskiya ko abarta Meer yagaya mata                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [7/16, 11:20 PM] #momyn twins#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 90 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️         gaba dayan su dakatawa sukayi da abun da sukeyi tare da mayar da hankalin su kan wayar da hamza yake kana ganin fuskokin su zagaka cike suke da mamakin sa, sarki ne ya mike tsaye cike da bacin rai yatako har zuwa inda hamza yake kwance, umarni yabasu da su dago wayar da yayi waya sannan aduba number da yayi waya da ita atake kwa suka dauko wayar saidai da security akai mika masa akayi ya bude amma saima yamayar da idon sa yarufe tare da yi musu banza, sarki da kansa yadaka masa tsawa tare da uban waye kai waye ya turoka cikin masarautar nan ana yi maka magana kamayar da mutane yan iska abun da kake wa mahaifiyata shine yau zakamin kai dan gidan uban waye? Turo kofar akayi da karfi cikin daga murya akace  dana ne...!! da mamaki gaba dayan su suka juya suna kallon matar da tashigo musu cikin fada kai tsaye, karasowa tayi ciki cikin takun isa da takama take tafiya tazo hargaban sarki da yatsa ta nuna sa tace wallahi duk wanda ya kuskura yakara taba min yaro kai bama shikadai ba duk wanda yakara taba daya daga cikin wadannan sai yayi da nasanin haihuwar sa tunda ku babu abun da kuka sani sai zalinci da mugunta mugaye kawai azzalumai, bata ankaraba taji an wanke fuskarta da mari tare da cewa kiringa iya bakin ki kisan dawa kike magana anan gurin na farko kinshigo cikin fada batare da izinin ba kuma kinzo kina magana dabata dace ba agaban sarki saboda ke mahaukaciyace jahila to da kika zo in kin isa ki hana mu dukansa ne me kika isa kiyi anan ke wace wane matsayi kike dashi dakika isaki dakatar da abun da akayi niya, kince duk wanda yakara tabashi sai yayi danasni ko to bari adakesa sai muga abun da zaifaru ke bama duka kadai na rantse saina rabasa da ransa agabanki zan kasheshi ki hana yakarasa maganar yana daka mata tsawa, juyawar da zaiyi yaji ankaiwa wunyan sa mahaukaciyar shaka ana cewa kafin ka kasheni ni bari inkashe ka uwata zakanayiwa magana haka bata girmekaba zaka iya tabani in kyaleka amma baka isa ka taba min mahaifiyata ba ka tsira hamza ke wannan maganr da yaji lokaci daya wani karfi yazo masa da da kwarin gwiwa, ita kuma matar da tashigo da sauri taje wajen baba tana girgiza shi tanacewa kar ka mutu yanzu ba lokacin mutuwar ka bane ina bukatar ka araye kar ka mutu katashi juyowa tayi taba kallon sarki da shi mamaki ma yahanasa magana yabari sauran sugama nasu ya yanke nasa hukuncin me gaba daya dan ya riga ya kistimawa randa babu ma kara kwana da ransa ayau dinnan sai yasa ankashe kowa da su har matar da takawo kanta tunda yake babu wanda yataba yi masa makamanicin abun da sukayi masa jin zuciyar sa yake kamar zata fashe saboda tsabar bacin ran da yakike cinsa, cike da daga murya ta kalli sarkin tace kaidai ba halinka mugunta ba to daga yau baza ka karayiwa wani ba kuma wannan abun da kayi kayi na farko kayi nakarshe dan sai kayi da nasani arayuwar ka kuma har abada baza kadaina ba wannan abun sai yazamar maka tabo acinki zuciyar ka tabo ma kuma wanda bazai taba gogewa ba har abada sai nasa ka tsani kanka sai kayi da nasanin da baka taba yiba arayuwar ka, tunda tafara magana sarki yake kallon ta kawai ko kiftawa bayayi ya kafeta da ido har saida ta gama sannan ya dauke idon sa daga kanta ya mayar dashi kan hamza dake rike ds wuyan mutumin nan har yanzu yaki saki ga sauran suna ta kokarin rabasu amma sun kasa nan ma dauke idon sa yayi yamayar kan Azeema dake kwace kamar matacciya amma idon ta abude yake kawai tsabar azabace yasa takasa motsawa duk da hankalin ta yana kana babanta da matar kuma datake masa magana tana cewa kar ya mutu, cike da kasaita sarki yafafa zagaya su yana kara binsu da kallo daya bayan daya, sannan yakira wani daga cikin su yana zuwa ya rada masa abu akunne da sauri yafita daga cikin fadar,, da kyar aka iya raba hamza da wanda ya shakesa ana rabasu kuma suka cigaba da dukan hamza basu dade suna dukansaba sarki yadakatar dasu tare da cewa azubawa tsohon cen ruwa atake suka kwarawa baba ruwa me yawa, da sauri baba yasauke numfashi me karfi cikin mawuyacin hali lokaci guda duk yatuna abun dake faruwa baisan lokacin da yafara zubar da hawaye ba wannan wacce irin masiface ta sameshi tunda yataso daga yaro har kuruciyar sa bai taba fadawa irin wannan makamancin halin ba baitaba ganin bala'i irin wannan ba amma sai gashi yanzu da tsufa yazo masa wannan masifar ta sameshi shida baisani ba ko Allah yayi laifi ya jarabcesa da wannan masifar ta mutanen nan, da sauri matar ta kara tashi daga wajen baba ta koma wajen hamza rungumo shi tayi tana cewa kayi hakuri nasan duk ni najefa ka cikin irin wannan halin nacuci rayuwar ka da naturo ka nan amma kayi hakuri nima bada son rainaba bani da zabin da ya wuce inyi hakan hakan shikadai ne mafita agare ni kayi hakuri, cikin sanyin murya yace umma nasani ya isa haka kiyi hakuri kidaina wannan maganar dan Allah, Azeema ganin baban ta ya farfado yasata rarrafa da kyar taje wajen sa tana so ta tashi amma takasa, shikuma baba har yanzu baiganta ba, ganin hakan yasa hamza raba jikinsa da na mahaifiyar sa yayi wajen su Azeema duk da yayi mamakin ganin yanda Azeema ta damu da baba amma yanzu ba wannan lokacinne dashiba yafi barin abun akan kawai ta tausaya masane amatsayin sa tsoho shiyasa tafi tausaya masa, yana zuwa wajen ya dagota da kyar ta samu ta iya zama da mazaunan ta, kuka ta fashe da shi tare da dora hannun ta akan sa tace baba da kyar baba ya iya juyo da kansa yasauke idon sa akan da sauri ya mayar da idon ya rufe tare da kara budesu dan ya tabbatar wa dana kansa abun da yagani, ba karamin mamaki yayi ganin dai dagaske itadin ce, Ahanakali ya yaɗaga hannun sa zai taɓata tayi saurin riƙe hannun tana ƙara fashewa da kuka tana cewa baba baba katashi karka mutu dan Allah katashi mutafi gida... ahankali baba ya ƙoƙarta tashi tare da taimakon hamza yaƙarasa zama shima yana zama Azeema ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai tana kuka shima saida ta zubar da kwalar tausayin ta daman mutumin da suka aika yazo yagaya musu yace yarinyar sa tace zatazo cikin gidan nemansa amma yasanar dasu ya dakatar da ita yace kar tazo ya gargaɗe ta kar abarta tazo shiyasa baba bai taɓa tunanin zatazo ɗin ba ashe kwa sai da tazo yanzu gashi za ayi biyu ba ko ɗaya ita bata fita shi baifita ba daman abun da wancen mutumin yayi musu gudu kenan kuma gashide saida hakan ta faru, da mamaki Hamza yake kallon su Saida yabari suka ɗan tsagaita da kukan kenan sannan ya dubi baba yace baba "kasanta ne daman? kai baba ya ɗaga masa tare da cewa "ƴata ce zaro ido Hamza yayi ba ƙaramin mamaki yayiba jin wai ƴarsace daman ƴar sa yake so duk loƙacin da ya haɗu da ita basu taɓa haɗuwa da baba sai yau yauɗin ma cikin mawuyacin hali irin wannan da ba damar farin ciki saidai ma baƙin ciki gaskiya baiso ta wannan hanayar suka haɗuba da yasan hakane ai da tuni ya haɗasu kash rashin sani yafi dare duhu, itama matar gurin ta tsugunna tunda yanzu kamar sarki yabasu damar su tattauna ne dan ita atunanin tama ko angama yimusu hukuncin ya rabudasu shiyasa ya dakatar da sauran ga dukan su, zama tana zama tace Alahamdulillah naji daɗe da ka farfaɗo da Allah yasa baka mutu ba, kallon ta ta mayar ga Azeema tace sannu yarinya wannan mahaifin kine ko kai Azeema ta ɗaga mata,  sannan ta ƙara cewa amma me yakawoki gidan nan, shiru tayi bata bata amsaba tana tunanin ya za'ayi ta gaya mata agaban sarki ta karawa kanta laifi shiyasa tayi mata shiru, Hamza zaiyi magana kenan saiga wannan mutumin da yafita yadawo da sauri ya shigo yana haki yace ranka yadaɗe angama shirya komai fitar su kawai ake jira, bayan ya shigo sai ga wasu mutanen wajen guda shida manyan maza dan su ko uniform ma irin na bayi babu ajikin su suna shigowa sarki ya umarcesu da su ɗauke su baba afita dasu inda yace, mutum ɗaiɗai aka fara ɗaukan su baba aka fara ɗauka Azeema nata kuka tana rirriƙeshi taƙi saki daga ƙarshema saida tasamu tuƙwicin mari zafafa guda biyu sannan tasakeshi aka fita dashi itama wasu suka ɗauketa suka fita da ita sai matar da ta shigo tana tayi musu masifa su sauketa wallahi zata ɓata musu rai amma basu saurare ta suka fita da ita, sunzo ɗaukan hamza, Hamza yace musu dalla malamai kar ku taɓani zan fita dakaina wanine yabiyo ta bayan sa gabuga masa katako akai yace kai akomai saika nuna taurin kai ko to bari muga iya ƙarshen taurin kannaka dafe kansa yayi take yaji yana yimasa wani irin ciwo bibbiyu yafara gani yana niyar faɗuwa wani yajawosa ya miƙar dashi ya tsaya da ƙafafun sa sannna suka shiga tura ƙyayar sa suna dukan sa suna turasa ahaka suka fita dashi daga fadar, bayan fitar su sarki da masu rufa masa baya suka bi bayansu suma suka fita, afarfajiyar masarautar aka jeresu da ƙuƙƙule musu hannuwa da ƙafafu, ƙarasowar sarki kawai ake jira afara zartar da hukuncin da yace ayi musu gefe guda kuma wasu mugayen wuƙaƙene masu kaifin gaske wanda ana ɗora ma ita zata iya yanka ka, guri har yafara taruwa da mutane sunzo kallo, sarki na ƙarasowa gurin yasa aje akirawo fulani dan tazo a yanke hukuncin agabanta, kowa na gurin sai mamaki me suka aikata haka za a yanke musu hukuncin kisa dan andaɗe ba ayi hukuncin kisaba Saida ahukun ta mutum ta wani fannin daban amma banda kisa yau kuma gashi za ayi daga gani to ba ƙaramin laifi suka aikata ba wasu kuma sunsan laifin da sukayi wasu su tausaya musu masu jin haushin Hamza kuma nayi masa Allah yaƙara duk dade sun tausayawa masa saboda duk wanda yaga halin da yake ciki sai ya tausaya masa basu kaidai bama har sauran gaba ɗaya abun a tausaya musu ne domin sunji jiki ba kaɗan ba gashi kuma za aƙara musu da kisa..... magana har ta fara karaɗe masarauta yau za ayi hukun kisa har mutum huɗu tofa kowa fitowa yake yaga suwaye haka kuma wane irin laifi suka aikata, ana cikin haka saiga motar sam nan ta shigo tundaga nesa yake kallon gurin taron da mutane suka cika amma dai baidamuba saboda inda sabo yasaba ganin yasan bazai wuce halin nasu suke ba na cutar bayin Allah tsaki yaja tare da cewa gobe inyanzu wani zancen aike ba wannan ba kuyi na ƙarshe ku gama yaune ranar ku ta ƙarshe cike da taƙaicin halayen su na masarautar ya ƙarasa parking lot shidaman arayuwar sa ya tsani wannan mulkin da sukeyi da bashida wani amfani dan baiga amfanin sa saboda ba abun da akeyi asauran masarautu suke ba su nasu na mahaukata suke bana mutane ba abu kwata kwata babu tsari ba a san me yakamata ayiba da abun da bai kamata ba yamaji daɗin  zuwan waɗannan bayin Allah, haka yai ta saƙe saƙen sa shikaɗai, saboda shikaɗai ya shigo, ya ajiye shettima agida, fitowa yayi daga motar ya nufi part ɗin fulani jikin sa duk akasalan ce babu daɗi so yake kawai yaji sa akwance yana buƙatar hutu sosai kwakwalwar sa ta huta.., akan hanya sukayi karo da fulani ta fito afusace cikin fushi ko takansa bata biba ta wucesa fuuu kamar zata tashi sama, binta yayi da kallo kawai tare da girgiza kai yayi wucewar sa ciki, kamar anjefota gaha fulani tashiga wajen taron tunda tashiga kanta yana kan hamza ganin sa cikin mawuyacin hali irin wannan hakan ba karamin dadi yayi mata ba, gaban sa taje tare da dago da kansa tana kallon sa tare da sakin wani shu'umin murmushi tace to karamin dan iska ina cika bakin naka yaje waye yau agaban mutane cikin mawuyacin hali kuma yanzu zan saka arabaka da duniyar ma gaba daya bance kafita hanyata ba bance karka sake shiga gonata ba amma bakajin magana kullum cikin nuna isa da takama kake kaidin waye me kake dashi me katara me ka ajiye me ubanka yatara me na kasa yaci bare yaba na sama kaidin asararre ne kazo a asara kuma zaka koma asara, tana gama fadar haka ta mike tare da canza kalar fuskarta ta koma ta marassa imani ta kalli sarki tace amatsayina na mahaifiyar ka ina umarrar ka da kakasheshi da hannun ka so nake kasa wuka ka fillemin kansa anan gurin kafin kafara ina so wani ya fito ya fara saukewa tsohon nan kansa a fille masa kai agaban sa in ya isa ya hana sannan ga budurwar sa nan tunda ita yakeso ina so itama akashe ta agaban sa sannan adawo kansa sarki da kansa nake so yayi min wannan aikin hakan sai yafimin farin ciki inaso dan da nahaifa acikin cikina ya daukar min fansar cin zarafin da wulakan ci da rainin da yake min inga jinina ne zai kashe shi ina fatan kungane, "bamu gane ba muna bukatar karin bayani maryama, da sauri fulani ta juya jin muryar da bata taba tunanin jintaba agurin, kafin fulani tace wani abu matar tayi saurin dakatar da ita tare da cewa kisa akunceni, cikin tsawa sarki yace baza a kunceta ba mama yanda za akashesu itama yazama dole asauke kanta anan gurin, fulani ce tayi saurin daga masa hannun tare da cewa ya isa haka kar nakara jin muryar ka anan, da kanta taje ta kunceta tana cewa wai ya akai waye yayi miki haka me kike yi yaushe ma kikazo bansaniba, banza tayi da ita tana kunceta ta mike tsaye itama cikin bacin rai ta kalli fulani tace ki gaggauta sawa akunce wadannan mutanen gaba dayan su, fulani itama cikin bacin ran tace akan wane dalili zakice haka, kedai kawai kiyi hakuri akan abun da yayi miki acikin rashin sanine baidan matsayin ki awajena bane amma hakan kar yasa wai kice sai ansakesu wannan hukunci ne da nariga na yanke tun wuri kuma dole a zartar dashi babu wanda ya isa ya hana tayi maganar cikin daga murya, kuma hurumin ki bane meye alakar ki dasu kima canza magana wadannan mutanen dakike gani ba mutanen kirki bane basu da mutun ci ko kadan basu sansaba musamman wannan dan iskan yaron da yagama rainamin hankali yau dole ya karbi abun da ya dade yana aikatawa, ko kuma ke ki karba ba nace masa kisake shi wallahi aka kashe shi sai namiki abun da baki taba tunani, matar take fadawa fulani tare da kada mata hannu afuska, bakaramin mamaki fulani tayi ba da jin batun ta aikam cikin bacin rai tace sarki afara takansa yanzunnan tagani agabanta, dariya matar tasaka tace da kwa kin tafka babban kuskure arayuwar ki ko kina tunanin alakawarin da na daukar miki yakai karfin da bazan iya karyawa ba to kiyi abun da nace miki inbaha ba kuma hmmm kinsan mai zaibiyo baya, dan dagatawa tayi sannan taci gaba dacewa ko dayake karfin alkawarin ne yasa nakai har yanzu ina danne wa to kar kibari ki kaini karshe da hakan zai gagara rikewa agareni yanzuma ba karamin kokari nayi ba wajen danne duk abun da yafaru agaba na batare da na dau mataki ba amma daman nafiso inma rashin juriyar ne da daukar mataki to yazamana agabanki ne kuma gaki dan haka idan baki dakatar da komai to nimafa kisani zanyi abun da yadace ina fatan zaki gyara barnar da kike shirin yi domin idan baki gyara wannan ba to waccen ta tashi daga gyaran da take kina bata wannan waccen zata baci gaba dayanta ina fatan kin fahimce ni da kyau, takarasa maganar tana watsa mata wani irin kallo me cike da gargadi, cike da bacin rai da fulani ta dade batayi irin saba muryar hardan dasdaskare wa take ta daga murya da iya karfin tare da tsawa tace HAJIYA SARAH.....!!!!! batare da ta sausauta murya ba tace yakamata ki iya bakin ki kisan abun da yakamata kiringa fada anan gurin domin nan bada gani sai ke bane awajen ki gaggauta janye wannan bukatar taki saboda ba mai yiyuwa bace ki canza wata bukatar taki amma ba wannan ba, juyowa hajiya sarah tayi cikin sanyin murya tace "ni kuma wannan bukatar nake so kuma dole ayi yanda nake so, kamar fulani zata rufeta da duka ta kara daga murya kamar zata cire mako garon ta tace SABODAME DOLE SAI WANNAN......? itama hajiya sarah cike da daga murya kamar yanda tayi mata itama tace SABODA DANA NE...!!! dif gurin yayi bakajin motsin komai sai can daga baya fulani ta dan saki murmushin mamaki sannnan cike da rashin fahimta fulani DA kuma bangane ba yi min bayani yanda zangane kodai kinsha wani abunne kafin ki taho inaga, babu abun da nasha wannan dai yaro dakike gani dana ne inbaki yarda ba kuma ki kallesa ki kaleni zaki ga kamar da muke indai kuma ba dusace a idon ki ba ko dayake naga alama da dusa acikin idon ki shiyasa tun wuri kika kasa gane hakan duk tsawon zaman da mukayi dake kuma kukayi dashi amma baki iya ganewa ba kinga kwa bazaki taba ganewa ba, kamar yanda tace ai bama iya fulani ba gaba daya mutanen wajen sai da suka shiga kallon su ba karya kam suna kama kana gani zaka gane hakan, jin fulani takasa magana yasa ta shiga zagayata tare da cigaba dacewa "duk wani abu da yake miki ninake sakashi kuma kamar yanda nagaya miki baisan komai ba to baisani ba din nice na dorasa yaringayi miki duk abun da kika ga yanamiki kuma ni nacire mishi tsoron ki sannan nasa karyaji tsoron kowa daga ciki hardake idan kuma kika zafafa ta kura masa yace miki zai tona miki asiri idan yace miki haka zaki daina takura mishi sannan yana da damar dazaiyi duk abun da yaga dama zaiyi sa batare da an dakatar dashi ba ke kinsan baisani bane dan da yasani wannan wahalar da aka bashi da tun kan afarata ma zai kunce miki zani sanin shi yarone bazai iya rikewa ba yasa naki gaya masa saboda ban taba tunanin irin wannan ranar ba amma da tuni na sanar dashi ke kinsan ko ni wacece duk abun da zanyi a lissafai nake yinsa shiyasa nasa aka kawoshi nan tun yana yaro inbaki saniba kisani duk zuwa gidan nan da nakeyi bawai dan ke nakeba dan shi nake kuma nayi hakane dan insakashi yasaka min ido akanki duk abun dakike yi akan idonsa ko wannan ranar batazo ba daman daf nake da toma miki asiri sai kuma gashi kin jawo lokacin da kanki dan haka lokaci yayi dole kowa yasan abun da kikayi tsawon lokuta, jikin fulani ba karamin sanyi yayi ba kuma ta tsorata sosai da maganganun hajiya sarah duk da tana tunanin duk barazana take mata ba iya fada zatayi ba kawai kurarine amma saboda kar yan gurin suyi zargin wani abun sai kawai ta basar tashiga dariyar borin kunya tare da cewa au sharri kuma zaki min ni nake da wani siri to in baki fasa fada ba ba kya tsoron Allah, "au haka kika ce? "eh haka nace, girgiza kai hajiya sarah tayi tana so ta fada amma idon wani dake kallon ta a filin wajen cike da gargadin ta kar tafada yasa tayi shiru taka sa fada amma da dan fulani ne da tuni ta dade da fada amma idan aka kaita karshe wallahi sai ta fada saidai duk abun da zai faru yafaru amma sai ta fada, ganin tayi shiru yasa fulani sauke ajiyar zuciya a boye tasan daman bazata iya fada ba kurarine kawai amma saboda kar taje ta fada din idan tasa akashe mata da tasan dole zata fada dan haka ta juya kamar ba ita ba ta kara hade rai sai tace yanzu adakata da hukun ci akan yaron nan sai nakara bincike akan sa kafin azo ayanke masa nasa hukuncin mai muni da yafi kisa tare dashi da mahaifiyar tashi abisa kazafin da tazo tayi min agaban ku wani satin irin rana tayau za ku dawo azartar musu da hukun ci agaban ku, maida dubanta tayi ga sarki da ya riga da yazaro wuka jira yake kawai takara basa umarni yakaita kan hamza sai kuma yaji wannan batun ransa yaji yayi mummunar baci dan haka tunda yazaro ta bazai baza ta koma ba sai tasha jinin wani, yanda take kallon sa shima haka yake kallon ta tasan ne yake shirin yi dan haka tsce masa "ka kwantar da hankalin ka ai ga wasu nan ka dauki daya acikin su kabawa wukar ka abinci nasan tunda tafito sai tasha zata koma, kawar da idonsa yayi daga kanta tare da matsawa kusa da Azeema har yadaga wuakar zai sauketa akanta sai kawai maganganun hajiya sarah suka shiga dawo masa maganganun da tayi masa akan baba hakanne yasa yafasa da Azeema yanufi inda baba yake saboda yana so ya kasheshi yaga abun da ta isa tayi masa, yana zuwa yadaga ta zai sauketa yaki anrike masa hannu da mamaki yashiga bin hannun da kallo mamaki ne yakara kamasa wai mai wannan matar take nufi dashi ne duk inda akace za ataba sai ta hana, bashi kadai bama kowa kallon ta yake cike da mamaki sarki guda ta rikewa hannu lallai ta wuce gona da iri wuyan ta ya isa yanka, shikam baba yarufe ido dan har yafara kalmar shahada ya riga da yagama saddakarwa ya mutu,, sai kuma yaji shiru, Azeema kam jikinta sai rawa yake muryart ta dashe tanaso tayi ihuma amma miryar ta taki fita sai uhm uhm take hawaye ma rahama ne amma sobada tsabar tashin hankali sun kafe sunki zubowa so take tayi ko zata samu sassauci Amma suma sunki fitowa, fulani ce tace hajiya sarah wai lafiyar ki kalau me yake damunki me yasa kikeyin irin waddannan abubuwan kinsan kwa wa kika rike, ko kallon inda fulani batayi ba ta sa hannun ta kwace wukar hannun sa tare da yin cilli da ita gefe guda inda ba mutane shidai sarki saboda mamaki yama kasa motsawa dan kamar ma baya cikin hayyacin sa har ta samu damar kwacewa daga hannun sa, cilli tayi da hannun nasa data rike idon ta sun canza kala sunyi ja saboda bacin ran da ta shiga yanzu, cike da daga murya, muryarta har rawa take saida ta kalli fulani sannan ta kalli inda ake kallon ta suna hada ido aka zazzare mata ido alamar gargadi kar tace komai, kawar da kanta tayi ta kalli sarki da fuskar sa ta canza idon sa shima yayi jajur, saida ta kalli kowa nagurin sannan tace nagaji nagaji bazan iya cigaba da jurewa ba wannan abun naku yayi yawa ina zaku kai rashin imani ne bazan iya ganin anyi kisan kai agaba na bazan iya ba wallahi kuji tsoron Allah me yasa me yasa tafada tana kara daga muryar ta sama, sarki da yagama kaiwa karshe ya juyo afusace bai duba girmanta ba kawai ya ware ya tsunsa biyar tana huyowa ya kwashe ta da wani gigitaccen mari da saida taga ster atake kwa yatsun hannun sa suka fito, da sauri hamza yayi kukan kura yakarasa kunce igiyar da aka daure sa daman tun dazu yake ta kokarin kuncewa sai yanzu yakarasa kunceta kansa yayo da nufin yaramawa mahaifiyar sa marin da yayi mata, hajiya sarah tayi saurin dakatar dashi tace "rabu dashi kar ka karaso nan gurin, kamar yanda ta umarceshi haka yaja yatsaya cak daga inda yake, har yanzu hannun ta na dafe akan fuskarta inda ya mareta ta karasa gaban sa ta kalle sa ido cikin ido sannan cikin sanyin murya saboda hawayen da yake fitowa daga idon ta, tace "ni kamara ko? akan ina kokarin yi maka gata, ina kokarin dakatar da kai daga aikata da nasani, ina kokarin dakatar dakai daga aikata laifi irin na yan wuta, ina kokarin dakatar dakai daga fushin ubangiji, shiru ta danyi sannan ta canza murya cikin daga murya tace ina kokarin dakatar dakai daga aikata mummunan laifi da yafi komai muni awajen uabngiji, "kasan waye shi? kasan wa kake so kakashe da hannun ka to inbaka sani ba bari insanar dakai ko shi waye agere ka, to shidin MAHAIFINKANE.....!!! NACE SHIDIN MAHAIFINKANE, MAHAIFINKA KAKE SON KASHEWA DA HANNUN KA...............!!!!!!!!! 🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️🙆‍♀️ More comment more tying,🧏🏻🧏🏻 inba comment ba tying🙅‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️🤷‍♀️                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent)  [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 91 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     "kasan waye shi? kasan wa kake so kakashe da hannun ka to inbaka sani ba bari insanar dakai ko shi waye agere ka, to shidin MAHAIFINKANE.....!!! NACE SHIDIN MAHAIFINKANE, MAHAIFINKA KAKE SON KASHEWA DA HANNUN KA...............!!!!!!!!!!! shiru gurin yaɗauka kowa ka kalli fuskarsa kasan tsantsan mamaki ne akanta wasu sun zaro ido waje saboda tsantsan mamaki kowa yayi shiru yakasa magana, Hajiya Sarah ce ta cigaba da cewa "wannan dai da kake gani shi ya haifeka nan gidan ba gidan kubane kai ba ɗan sarki bane ɗan wannan mutumin ne da kake son kashewa da hannun ka  '"idan kuma ka ƙaryata ko baka yarda da abun da nake faɗa maka ba  ga hujja ina da ita saboda haka daman na ajiyeta zaro wani abu tayi ajakarta kamar plash ta miƙa masa sannan tace zaka iya zuwa ka kalla ko kuma ka tambayi wacce kake gani amatsayin mahaifiya kace tagaya maka waye ya haifeka idan ita ta haifeka in ta isa ta ƙaryatani anan wajen, amugun furgice fulani tace ƙarya kike na ƙarya taki ɗin wannan wacce irin banzar magana ce naga alamar kinsha ƙwaya hauɗin nan ni zakuce bani na haifeshi ba idan ba ni na haifeshiba uwarki ce ta haifeshi kai kuzo kufitar min da wannan mahaukaciyar daga gurin nan, tafaɗa tana kallon fadawan wajen, da sauri fadawan sukayi kan hajiya sarah dan aiwatar da abun da uwar masarauta ta umarce su dashi saidai sun karasowa gurin zasu kai mata cafka sarki salahuddeen yayi saurin daga musu hannu tare da dakatar dasu daga shirin kama tan dasuke, fulani na ganin haka ta zaro ido tare sa hadeye wani katoton bakin ciki da tashin hankali da suka rufar mata lokaci daya suka tsaya mata a makogaro, a kidime tayi tayi wajen sarkin tare da riko hannun sa tace wallahi karya take kar ka yarda da ita wannan matar da kake gani zararriya ce bata da hankali bata dade da dawowa dafa asibitin mahaukata ba kar ka yarda da ita taya ma za ayi ace kazama ba dana ba kaidin dana ne ni nahaifeka acikin muje ka tambayi mahaifinka kaji zai gaya maka gaskiya zo muje idan ni baka yarda dani ba muje idan kaji ta bakin sa zakafi yarda, tunda tafara magana yake binta da kallo kamar yasamu tv yakasa koda kwakkwaron motsi saboda gaba daya kansa ya kulle yarasa maganar wa zai dauka kuma tawa zai bari ga kansa da yaji yana yi masa wani rin mahaukacin ciwo, sanbatu fulani ta shigayi tana ta faman jansa amma ina ko motsasa takasa yi, kwace hannun sa yayi daga nata yana kallon ta saboda yanaso yagano gaskiyar zancen sai kawai yadaka mata tsawa tare da cewa ki fada min gaskiya kece uwata ko ba ke bace abu daya nake so naji daga gare ki "eh" ko "a'a"??? yayi maganar yana zazzare mata ido kamar zasu da fado waje gashi sun canza kala daga fari sun kima ja ran maza ya baci, "Fulani kam ba karamin tsorata tayi da yanayin saba dan tunda take dashi baitaba nuna mata irin haka duk da tunyana yaro tasanshi da saurin fushi abu kadanne yake bata masa rai, atake kwa jikin ta yadau bari sai karkarwa take amma duk da haka ta kara daurewa bata karaya ba itama cikin daga masa murya tace masa "EH, nice na haifeka idan kuma baka yarda ba nace kaje ka tambayi uban ka, hajiya sarah ce ta tako zuwa gaban su sai ta tsaya saitin fulani cike da dakiya tace haba maryama ko kifadi gaskiya ko baki fada idon ki da jikin ki sun bayyana ma kowa gaskiya domin kwa ga tsoronan karara akan fuskarki da kika kasa boyesa duk da son hakan da kikeyi amma kin kasa malama ba wani boye boye yanzu ki fito kigaya masa ko ke wacece agaresa kigaya masa a inda kika dauko sa inkuma kin bani wuka da nama yanzu zan yankasa in soya kuma in rabasa afaranti ko yagani kuma yaci ki daina wahalar da kanki daman ance rana dubu ta barawo raba daya tak ta mai kaya to yau gaki barauniya kuma gamai kaya azaune agabanki yakamaki kuru kuru dan haka bake ba wani yin kwana kwana da kike cewa yaji ya tambayi mahaifinsa ke atunanin ki yanzu zai kara yarda dake ko kinmanta saradin bokan naki ai ba sarki kadai ba daga yanzu bakin kowa zai bude akan wannan yaron saboda duk wanda yake cikin hayyacin da hankalin sa ya kalle sa yasan baiyi kala da yan gidan nan ba ba jinin sarauta kamannin sa sun bambam ta da kowa dake cikin gidan nan dan haka ko baki fadi gaskiya ba da bakin kiba idanun mutane zai gane musu hakan dan haka daga yau zuwa gobe sai ki nemo mafita ni daga yau baza ki kara ganin naba abun da hadamu ya rabamu zan dauki dana mu koma inda muka fito shawarata agare ki kinemi makaman kare kanki, tana gama fada mata haka ta juya kan sarki shima tace masa zanso intsaya har zuwa gobe dan innemi yafirya ka domin harda saka hannun akan rabaka da iyayen ka na asali wannan da kake gani zaune shine mahaifinka waccen kuma kanwarka ce uwa daya uba daya gashi Allah ya hadaku guri daya da kanka kaje ka shigo dashi itama kuma sanadin shigowarta Allah yayi shine sanadin haduwarku saboda badan itaba bana jin asirin nan zaitonu kuma ita ma sanadin dana hakan ta kasance, kuma ka.... sarki yayi saurin da katar da ita sanadin daga mata hannu hakan yasa tayi shiru, ahankali yashiga buda bakin sa sannan yace "ke duk taya kikasan ba itace ta haifeni ba kuma taya kika san wannan shine mahaifina alhalin ita bata san da hakan ba, dan murmushi hajiya sarah tayi sannan tace "kar kadamu da wannan duk ka tambayeta zatayi maka bayani komai dalla dalla amma dai bari inbaka amsa daya ni da kaina naje na daukoka akan gadon asibiti agaban mahaifiyar ka wannan duk shirin mune aka gaya musu cewar dansu ya mutu sannan aka kawo musu wata gawar yayan wata mata da yan biyu da suka mutu sai aka nunawa matar daya sannan aka nunawa mahaifiyar ka daya akace mata abun da ta haifa ya mutu ni da kaina kuma na sanar da mahaifinka mutuwar ka, kaji ta inda nasan shine mahaifinka amma ita bata sanda hakan ba shiyasa amma da tun ranar da ka kawosa da kanka da tun ranar zatasa yabar gidan amma bata saniba kuma aranar da na fara karo dashi nagaya mata ta koresa taki, kin yin hakan kuma gashi nan zai jawo mata da nasani, "Umma Hamza ya kira sunan ta cike da mamakin labarin da ta bayar dan shi baitaba sanin abun da ta aikata ba kenan wannan ai ita kanta zalinci ta aikata kuma kanta ta tonawa asiri ba wani ba, tunda ya kirata ta juya tana kallon sa tare da amsa kiran da yayi masa, kafeta yayi da ido tare da takowa ahankali har yakaraso gabanta bai dauke idon sa ba daga kanta, sunan ta yakara kira still dai idonsa akanta ko kiftashi bayayi kuma ya hade fuska tamau kamar baisan wani abu aduniya ba wai shi murmushi ko kuma farin ciki haka ya koma mata, cikin bacin rai yace "kina sane kika aikata wannan abun kuma kinsan da zaman sa meyasa baki taba gaya min ba daman duk abun da kike fada min ba gaskiya bane me yasa me yasa kika aikata haka da hannun ki kika raba da mahaifan sa kika kawosa nan aka dorasa akan zalintar mutane da cutar dasu yanzu da ban kiraki ba yakashe mahaifinsa da kansa kina tunanin iya shikadai za ayankewa hukun ci ke da kika rabasa dasu kuma kika sani baki sanar dashi ba hukuncin ki awajen ubangiji sai yafi nakowa kinsan gaskiya kuma kin take wannan wace irin rayuwa ce kika dorawa kanki nayi da nasanin kasancewa ta da agareki me yasa me yasa zaki aikata hakan amatsayin ki na musulma wannan wane irin mugunta ce wallahi bana ganin laifin kowa sama da naki kinfi kowa laifi aciki ahaka kuma kike cewa wai zaki tafi ki tafi ko ni da nake da awajen ki bazan bari kibar gurin nan ba batare da an hukuntaki daidai da abun da kika aikata ba yanda za a hukunta kowa kema dole ki tsaya ki karbi sakamakon ki duk da ke kika fallasa abun hakan bazai hana a hukun takiba, wallahi bantaba tunanin zaki iya aikata haka ba nawa ake biyanki da har kikayi wannan danyen aikin umma? yayi maganar cike da bacin rai yana tsatstsareta da ido, tunda yafara maganar hajiya sarah take zubar da hawaye yau wai yau dan cikinta ne yake gaya mata magana, tasan tabbas ta aikata kuskure amma shima baisan dalilin ta nayin hakan ba itama bada son ranta tayi ba dan ba yanda ta iyane shiyasa ta aikata hakan, kamo hannun sa tayi tana kallon sa yayin da hawaye suka gama wanke mata fuska suna hada ido yajanye idon sa gefe ta budi bakima zatayi magana sai kawai ya dakatar da ita tare da kwace hannun sa daga nata hannun ya juya mata baya ya koma gurin baba tsugunnawa yayi ya kuncesa sannan yaje ya kunce Azeema ma sannan ya shiga basu hakuri, yaudai yan masarauta sunga abun mamaki kuma sunji abun da basu taba tunanin ba basu taba kawowa ba kowa yana tsaye agun yana jiran yaji karshen zancen amma ba wanda yasamu damar yin magana saboda suna tsoron aji bakin ka agun yanzu wasu su sauke haushin su akansu shiyasa kowa yake zancen sa shikadai daga shi sai zuciyar sa amma kowa munafurci cinsa yake so yake yayi da dan uwansa amma ba dama dole sukayi shiru kowa ya zuba ido yana bawa idonsa abin ci, abangaren fulani kam tunda hajiya sarah tayi magana takasa koda motsawa bare tasamu karfin halin yin magana agun saboda tasan karshen ta yazo tunda har ta riga ta fallasa shikenan komai ya karye kamar yanda bokan yace duk sanda aka samu wani ya fadawa akunne mutane da yawa sukaji tofa asirinta zai tonu kowa dawo gani daidai sannan papa ma bazai kara yarda da itama shima kuma zai dawo cikin hayyacin sa ta daina juyasa yanda take so ya daina yi mata biyyya kamar yanda yake mata abaya daga yanzu komai zai canza, baba bakaramin mamaki yayi ba yanaso ya gasgata abun da suke fada amma yakasa gani yake duk kamar mafarki yake yaza ayi ace wai dan sarki guda shine dansa kai gaskiya wannan matar ba gaskiya ta fada ba idan hakane me yasa shi bai gane taba kuma dansa sa hannun sa ya binne sa ya riga da ya mutu kuma kawai kwatsam lokaci daya tawani zo tace wai dansane gaskiya karya take shi baida wani da araye bayan saleem da Azeema shikadai shima yake ta faman saka da warwarar sa, abangaren Azeema kam tayi mamaki batayi mamaki ba domin tunda matar tace dan babane ta kura masa ido sosai taga kamannin sa da yan gidan su kuma ta yarda da yayan natane duk da ba ataba gaya mata suna da yayan da ya mutu ba amma aranar da ta fara ganin sa taga mugun kamar da suke da yayan ta saleem saida abun da yasa bata tada hankalin taba tayi tunani gizo yayi mata aranar ko kuma tsorone yasa taga kamar dasuke kuma tunda ga ranar bata kara ganin sa ba face to face kamar yanda ta gansa ranar shiyasa tayi watsi da maganar kamar da suke saboda bashi ya kawota ba daman khma basu kuma haduwa ta gansaba duk sanda zasu haduma kanta na kasa, sarki da jikin sa yayi mugun sanyi saboda yagama yarda da maganar matar nan gaba daya saboda ya fahimci mahaifiyar sa fulani bata da gaskiya amma duk da haka bai gama tabbatar wa ba sai yakara samun hujjoji aransa yana ayyana mudun hakan ta kasance gaskiya bazai bar duk wanda ya rabasa da iyayen sa na gaskiya ba gashi ya kamo mahaifin sa da hannun sa yasa kuma an hukuntasa agaban sa da Allah bai rufa asiri ba da tuni ya kashe mahaufinsa da kansa ji yayi kansa gaba daya yadau wani irin matsanan cin ciwo shi kadai yasan halin da yake ciki ayau din nan, ahankali yafara takawa har zuwa gaban baba ga mamakin mutane sai sukaga sarki sukutun da guda ya tsugunna agaban baba cikin kasa da murya yace "da gaske kaine mahaifina ? kawar da kai baba yayi sannan yace "a'a ni banda wani da dana ya dade da mutuwa kai ba dana bane domin indai kai jini nane baza kataba zalintar mutane ba irin yanda kake dan haka bani da hadi dakai, da sauri Azeema ta karaso wajen su sannan tace "baba wallahi da gaske ne wannan danka ne bakaga kamar da suke da yaya saleem ba Allah baba wannan matar da gaske take nifa tun ranar nafara ganin sa naga yana kama da yaya saleem kodai baka gane kamannin nasaba, ko kallon inda take baba baiyiba kuma bai kalli sarkin ba ya kawar da kansa gefe kawai, jin batunsa yasa sarki mikewa tsaye jikin sa babu kwari dan yaji ajikin sa duk yanda akayi da gaske shine mahaifinsa kuma ya tuna lokacin da yazo wucewa yarinya takira saleem da karfi sai yanzu da tafada ya tuna lokacin da ta taba fadadin hakan kuma yakara tabbatar masa da zancen da ake gaskiya ne ahankali ya dora hannu akansa zai fara warware rawani kansa yaji anyi saurin rike masa hannu, hannu ya shiga bi da kallo har zuwa fuskar me rike masa hannun idon sane suka sauka akan Ammah da zuwan ta cikin gurin kenan, zaiyi magana kenan ta kar kada masa kai ma'ana kar yayi magana kallon yan gurin tayi sannan ta daga murya tace "kowa yakama gabansa banason ganin kowa anan sum sum sum suka fara watsewa daga gurin har suka tafi gaba daya amma wasu ba haka suka so ba sunso har sai sunga karshen komai anyi agaban su, cikin bacin rai Ammah tace "yanzu meye hakan kukazo kukeyi agaban mutane koma me yafaru ai baikamata ace kun tsaya gaban mutane bayi kuna kace nace agaban su suna jin sirrinku wannan abun da kukayi babu abun zai jawo sai zubewar mutuncin masarauta da rage mata kima da martaba da mutunci wannan abun da kukayi kwata kwata bai dace ba bai kamata ba da girman ku sai kace wasu kana nun yara kuna kallon sa amatsayin sa na sariki yana niyar kunce sarautar sa abainar jama'a koma meye ai a kunceta cikin mutunta da martaba wallahi kun batan rai kun ban kunya ni duk bansan meke faruwa ba sai yanzu aka sanar dani da ban bari hakan ta faru ba da tun wuri na dakatar da komai haba dan Allah sai kace wadanda basa tunani,, maida dubanta tayi ga fulani da ta sunkuyar da kai sannan tace "wlh ni duk laifinki ma nafi gani da kika kasa dakatar da abun har takai ga haka ya kuke abu kamar ba manya agidan me yasa ba asanar da papa ba tun wuri ko waziri ko galadima idan kin kasa su ai duk zasu iya ji da komai tunda su mazane idan ke abun yafi karfin ki duk da kina da ikon fada aji amma kika kasa yin hakan, sosai Ammah ta rufe ido ta hausu da fada babu wanda batayiwa fada ba acikin su sannan tace kowa ya tafi makoncin sa gobe da safe za ahadu afada kuma kada wanda yayi gangancin tafiya daga cikwa harda hajiya sarah, sannan Ammah tace baba shima ya koma dakin sa shi da hamza gobe za anemesu Azeema kuma ta koma part dinta kartaje part din fulani inyaso ita kuma fulani su tafi da hajiya sarah tunda kawar tace suje su cinye kansu ko kuma su san yanda zasuyu su samowa kansu mafita kafin safiya ba yanda suka iya yau Ammah ita ta koma mai juya kowa har fulani yau bata da wani ikon fada aji dole tabi yanda akace saboda gudun abun da ka iya faruwa nan gaba ji take dama idan ta koma part dinta Allah ya dauki ranta shikenan basai anyi zaman da ita ba da wane idon zata kalli sauran mutane idan maganar nan tagama karade ko ina tasan da kyar idan baza akoreta daga masarautar ba korar ta da za ayi shine babban abun da yafi daga mata hankali ahaka tana tunani bata iya cewa komai ba ta juya tafara tafiya dan bata da bakin magana ahalin yanzu tana tafiya hajiya sarah tabi bayanta da sake sake itama fal acikin ta,, baba shima saida taimakon hamza ya iya mikewa daga gurin sannan yatai makasa suka tafi nasu wajen, Ammah da kanta taja sarki takaisa har part dinsa sannan ta gargadi matansa da su bashi kulawa, sannan ta juya zatabar falon ita da Azeema yayi saurin dakatar da ita, tsayawa tayi tare da juyawa ta kalle sa da kyar ya iya budar baki yace "ki barta awajena, Azeema dake gefen ta ta kalla da har zatace a'a sai kuma kawai tace ba damuwa tana fadar haka kuma ta fice daga falon, Azeema tsaye tayi agurin takasa gaba ta kasa baya daya daga cikin matasane tayi mata magana da ta dawo kan kujera ta zauna jiki babu dadi duk atakure take jinta haka ta dawo zata zauna akan wata kujera sarki yace mata " dawo nan yafada yana nuna mata gefen sa da hannun duk kallon sa suka shigayi saboda su basu san me yake faruwa ba kuma sunga yana cewa wai tazo ta zauna kusa dashi shi da ko su da suke amatsayin matansa ba kasafai yake sakar musu fuska ba bare har yace suzo su zauna akusa dashi haka yaransa ma baifiya jansu ajiki ba, sai yaga dama ko kuma idan yan mulkin basa kusa shine zakaga wataran yadan yi musu wasa, kamar yanda yace haka taje ta zauna kusa dashi kallon yake sosai yakai wajen minti biyar yana kallon yakasa magana saidaga bisani sannan yace "tashi ki kunce min wannan abun kannawa ba musu kam ta tashi tashiga ware masa rawanin kansa saida ta kunce masa gaba daya sannan ta nannadai abun ta ajiye gefe sudai matan sa suna zaune suna kallon ikon Allah da abun mamaki, saida ta kunce masa ta kara ganin kamannin sa da saleem sosai suke kama kamar yan biyu saidai kawai bambancin su manyan ta kuma wannan yama fi kama da mama akan saleem bayan kamar da yake da saleem kana ganin sa zakaga kamannin mama afuskar sa, kura masa ido tayi shima ita yake kallo yana so yayi mata magana amma yakasa sai kallo kawai ji yayi son yarinyar na shigar sa dukan sa akayi mata dazu yafara tunawa da sauri ya rufe idon sa ji yayi bama yason tunawa gaba daya yanzu idan hakan ta kasance da wane ido zai ringa kallon su dan ya cuci mahaifinsa duk da ba asanin sa yayi hakan ba kuma ba laifin sa bane dorashi akayi akai dan idan yayi tunanin abubuwan da yayi sai yaji ya tsani kansa, duk son yayi mata magana amma yakasa sai kawai ya mike tsaye ya nuna dayar matar sa yace akaita ta kwanta sannan shima ya nufi dakin da zai kwanta yana shiga ya cire duka kayan jikin sa da niyar ban kwana da su dan bazai kara sakawa ba yasan da hakan kuma idan magana zama gaskiya daga gobe bazai kara zaman gidan ba dan jin sa yake gaba daya kamar akan kaya yake duk zaman gidan ya isheshi kuma ya tsani kowa dake gidan so yake gobe tayi kawai yabar gidan matar sace ta shigo dakin cikin lallami da kulawa take tambayar sa abun dake faruwa amma sai yace mata ba komai duk yanda taso ta shawo kansa abun ya gagara haka taita fama da shi daga karshe dai da ta gaji ta rabu dashi ko abinci ma kin ci yayi aranar, rana daya duk yabi ya canza yana abu kamar ba shi ba, Azeema tunda aka kaita wani daki takasa sakin jikinta haka tayi kwance agadon da aka nuna mata ta hau tayi shiru tana tunane tunane, aɓangaren fulani kam suna shiga falon ta kaiwa hajiya sarah shaƙa ta haɗa ta da bango tana zazzare ido tare da cewa ni zaki cuta ni zaki ciwa amana duk irin yarjejeniyar da mukayi dake akan sirrin nan shine yau zaki tona min asiri me yasa zaki min haka haka mukayi da ke to kafin kowa yagama sani bari in kasheki kowa ya huta sai inga ta yanda zaki bada sheda gobe wallahi da nasan haka zaki min da tuni na san yanda zanyi dake tun wuri ban taɓa tunanin haka daga gare kiba kin cucune wallahi nima bazan barki ba sai kin ɗanɗani kuɗar ki tana maganar taba zazzaro mata idanuwa, idanun hajiya sarah sunyi ja sun kaɗa gashi sun firfito waje saboda tsabar zafin shaƙar da take ji saida tabari ta gama tata maganar sannan ta buɗi baki da ƙyar tace to kikashe ni mana sai mai nace kikashe ni mana idan kin cika ƴar halak angaya miki idan kika kashe ni kin tsira kisani idan kika kasheni ne ma zaki jefa kanki cikin babban hatsari domin asirin ki yariga da yagama tonuwa kuma kin manta da shadar da na basa ko bana raye zai gani bare ma kuma daman kinsan boka yace daga ranar da akafaɗi maganar kowa yaji shine makarin asirin ki babu wanda zai ƙara yarda dake dan haka kikashe ni kiƙara jawowa kanki babbar masifa ni kin hutar dani ma bala'in da zan shiga kinga saiki haɗa da nawa laifin a hukun taki tun anan duniya kuma a hukuntaki alahira ki kwashe min duka zunu baina kinga naci riba biyu ke kuma kin tashi da tutar babu dan haka sai kiyi abun da kikayi niya kar ki fasa kiyi kishiga wutar jahannama, da ƙarfi fulani ta sake ta tare da turata gefe saida ta bugu da bango aikwa tana jin zafi tayo kanta itama cike da masifa da kuma jin zafin abun da tayi mata ta fara zazzagin ta ta uwa ta uba harda su gorin haihuwar da bata taɓa yiba tun abaya yanzu saida ta tuna mata tayi mata tass itama bata barta ta fara mayar mata da ai gwanda ita tayi auren ma ita da take yawon ta zubar fa tana zaman karuwan ci ba uwa ba uba ba dangi sai yawon bari kanci daga nan sai can tazo duniya abanza zata koma abanza jin hakan da hajiya sarah tayi bata san loƙacin da ta daddage ba ta kwashe fulani da maruka har guda uku sannan ta nunata da yatsa tace wallahi ki iya bakin ki san maganar da zaki ringa ni kike cewa karuwa kin taɓa ganina kwance gado ɗaya da ubanki idan ma karuwancinne to da ubanki nayi ubanki nake ɗaga ƙafa ya shiga ai bari in baki labari idan baki saniba agadon uwarki muke aikata zina da ubanki tunda uwarki tayi masa kaɗan ai dole ya haɗa da mai maiƙo irin mu kinga kwa karuwar ma tana da rana tunda ta taimakawa ubanki abun da uwarki takasa basa, ke idan karuwancinne ma har kyayi magana bayan ga babban kwartooo ubanki ubanki ai shine ɗan iskan me yawon ta zuba ba wani ba tunda dashi nake yawon ta zubar ɗin shi kuma ya kwasa da....... bata ƙarasa maganar da take son yiba fulani tayi wani kukan kura tayi kanta zata shaƙo ta taji anyi saurin riƙeta gaba ɗayan ta anyi baya da ita, hajiya sarah tace rabu da ita idan ita ta isa ƴar halak tazo ta taɓa ni wallahi sai na koya mata hankali, itama fulani murya cikin kuka tace kasake ni kasake ni nace wallahi yau sai tagaya min uban da yake karuwaci da ita kirasa wanda zaki gar min sai ubana da yake ƙarƙashin ƙasa duk abun da zakiyi meyasa bazakiyi shi tsakanin dake ba meyasa zaki saka mahaifina aciki da yariga da yabar duniya me yayi miki laifi bani nayi miki meyasa zaki huce akan sa ME YASA...!!! ta ƙarasa maganar da ƙarfi tare da fashewa da wani irin matsanan cin kuka wanda kana jinsa kasan daga ƙasan zuciyar ra yake fitowa dan maganar hajiya sarah ba ƙaramin ƙona mata rai tayi ba ta sosa mata rai matuƙa duk acikin abubuwan da suka faru babu wanda yafi ƙona mata rai irin maganganun ta na yanzu, kuka take sosai duk wanda yaganta awannan loƙacin sai ya tausaya mata dan kuka ne dake fitowa daga can ƙasan zuciya kana jin kasan ba ƙaramin abune zai saka mutum irin wannan kukan ba, Sam dake riƙe da ita shi kansa baiji daɗin zagin da hajiya sarah tayi mata ba duk da yaji wasu maganganun da tayi mata itama amma bai kamata ta rama ta wannan hanyar ba tun shigowar su ciki yake tsaye yana kallon su sai yanzu da yaji suna neman wuce gona da iri shiyasa ya ƙaraso wajen dan dakatar da su daga abun dasukeyi kar suje suyiwa kansu illa, janta yafara yi zuwa ɗaki zai kai ta ɗakin ita kuma tana fusfusgewa tana cewa yasaketa amma yaƙi sakin ta gashi kuma ya riƙeta ƙam ba yanda za ayi ta iya ƙwacewa daga hannun sa haka yajata saida yakaita har kan gadon ta ya ajiye ta sannan yafuto tare da ƙulleta aɗakin ta waje sannan yadawo falon itama hajiya sarah ya nuna mata wani ɗaki kuma ya gargaɗeta kar tasake ta fito komai zataji daga har safiya kar ta fito sannan itam saboda gudun matsala ya ƙulleta aɗakin sannan yafita daga part ɗin gaba ɗaya ma part ɗin Ammah ya nufa yana shiga yaga bata falo dan haka ɗaki ya nufa direct yana zuwa yayi nocking Ammah "tace waye? yace "nine jin muryar sace amma sai kawai tace "kai wa? ba ƙaramin mamaki yayi ba jin tambayar da tayi masa bai taɓa jin haka daga gare ta ba yasan dai tasan muryar sa kuma ya tabbatar ba bacci take ba bare tace bata gane muryar saba saboda da baccin da takeyi, da kamar bazai bata amsaba amma sai kawai ta daure yace "sameer Abdallah sameer, yana faɗar haka ga mamakin sai ji yayi tace "ya akai mai kake nema me za abaka? ƙofar ɗakin ya shiga bi da kallo kamar tana gurin kansa ya ƙulle yama rasa amsar da zai bata tunda take da ita hakan bata taɓa faruwa ba ba ƙaramin mamaki yayi ba yau abun da baitaɓa gani ba bai taɓajiba ko amafarki akace Ammah zatayi masa wannan tambayar dan yazo gurin ta bazai taɓa yarda ba, yama rasa me zaice mata dan haka sai kawai yafara ƙoƙarin barin wajen dan baisan me zaice mata ba saidai yana juyawa zai bar wajen aka buɗe ƙofar tsayawa yayi tare sa saurin juyawa yana kallon fuskar ta yaga alamun ba lafiya ba dan baitaɓa ganin hakan daga gare taba to me yake faruwa takawa yafara yi har yaje gaban ta tun kan ya buɗi bakima yayi mata magana ta dakatar dashi tare da cewa kayi haƙuri koma me zakace kabari sai gobe yanzu banda loƙacin yin wata magana duk ka adana tambayoyin ka sai kayi su gobe, gobe da safe zamu haɗu a fada kaji duk abun dake faruwa ina fatan ka gane, kai kawai ya kada mata alamar ya gane,, tana gama faɗa masa haka daman bata jira cewar saba ta juya ta koma ɗakin tare maida ƙofar ta rufe, ƙofar yaƙara kalla yadaɗai agurin tsaye mamaki yagama cikasa saida ga baya sannan jiki babu ƙwari ya juya ya fita daga part ɗin ransa duk babu ɗaɗi kansa neman yi masa bunduga yake yau me yake faruwa dashine daga wannan sai wancan abubuwan da suke faruwa dashi suna neman sufi ƙarfin tunanin sa suna neman tarwatsa masa tunani tafita kawai yake shi kansa baisan inda yake ɗora ƙafarsa tafiya kawai yake ahaka har ya ƙarasa part ɗin fulani ya wuce ɗakin sa yana shiga ya faɗa kan gado tare da kifa kansa yayi ruf da ciki shikaɗai hasan halin da yake ciki yarasa wane irin tunani zaiyi yaji daɗi abubuwa sunyi masa yawa yakasa samun mafitar tunanin sa daga yafafa wannan tunanin sai wani ya faɗo masa haka yayi tayi yana faman juyi akan gadon kansa sai sara masa yake kamar zai tsage gida biyu da ƙyar ga iya tashi ya ɗauko maganin ciwon kai da na bacci ya ɓalla ya sha sannan ya koma kan gadon ya kwanta bai jima da kwanciya ba sosai ba bacci ya ɗauke sa...... *********************** ______*Rasheeda & Meer* tana ƙarasawa gabansa tasamu kujera kusa dashi tare da zama tana wani karkaɗa ƙafafu tana jiran ya ɗago, amma baiɗago ba ko gefen tama bai kalla ba, aɓangaren sa kam tunda ta taho yake kule da ita har ta ƙaraso yasan da da ƙarasowar ta har zamanta duk yana sane da ita saidai baiɗago ya kalli taba dan ko kalar kayan jikin ta baisan waɗanda tasaka ba yadai san dole macece tazo wajen ba namiji ba yadai tsaya kawai yaga iya gudun ruwan ta koma wacece, cikin kasalalliyar murya me kashe jikin duk wani namiji me rai da lafiya tayi ƙasa da ita cike da kisisina da iya barikan ci da kuma ƙwaraiwa ta ɗaga hannun ta tare da ɗora sa akan gefen fuskarsa ta shafo gefe tana cewa Hyyy the beautiful of the world and nice to meet you baby tayi maganar tana wani kashe ido tare da ƙanƙantar dasu suka koma sexy tana kallon fuskar sa tana so ya ɗago ya kalle ta, yaci gaba da danna wayar sa da yakeyi gama cin abincin sa kenan yana shirin barin wajen sai kuma ya ɗauko wayar sa yana dannawa dalilin da yahana sa fita tun ɗazu kenan har tazo ta tarar dashi agun, amma da tuni ya tafi, ganin yaƙi ɗagowa ya kalle fa yasa tasaka ɗayan hannuta ta ɗora ta ɗayan ɓarin tana shirin juyo da fuskar sa gareta yanda zata samu damar kallon sa da kyau, saidai da juyo da fuskar tasa da ɗaga hannun sa duk atare tana juyo da fuskar shikuma ya wanke ta da wani ƙyaƙƙyawan mari saboda tsabar jin zafi da tsorata saida ta faɗi daga kan kujerar da take kai azaune, baijira wata wata ba daman zuciyar sa akusa take a zafafe yayi kanta kamar mayunwacin zaki haka yayo kanta gadan gadan hannu ɗaya yasa ya ɗagota tare da kaiwa fuskar ta naushi take adaidai kan hancin ta bata gama tantancewa ba ya ƙara kaimata wani awajen bakin ta take bakin yafashe yafara fidda jini ihun da tasaki ne yafara jawo hankalin wasu mutanen dake gurin suka fara kallon su ƙawayen ta da duk abun da yafaru akan idon su suka fara ƴar kallon kallo a tsakanin su kowa yakasa magana sai su kalli juna sai suci gaba da kallon yanda ake jibgar ƙawarsu sun kasa zuwa su taimake ta, saida suka ga yazaro belt yafara zuba mata ita ajiki tana ihu sannan suka tafi zasu taimaka mata daman gurin ba wasu mutane da yawa agun kuma daman gurin na ƴanji da kansune kowa yana ganin yafi ƙarfin zuwa wajen su yatambayi ba'asi dan haka kawai sai kowa yabasar dasu yaci gaba da abun da yakawo sa wasuma jin ƙarar ta ishesu yasa suka tashi daga gurin suka fitama gaba ɗaya, ƙawayen ta na ƙarasawa suka fara ƙoƙarin shiga tsakiyar su zee ce tafara shiga rai aɓace tace malam dakata bafa jaka kasamu ba kazo kana dukan ta sai kace an aiko ka, uban me tayi maka, baibata amsar baki ba sai ta duka kanta yakoma itama yafara zuba mata ai sauran basu jira sunce wani abun ba suka kwashi ƙafafunsu suka kwasa da gudu zasu bar wajen gurin dan sunga alamar mutumin baida hankali wataƙil, dan sunma manta da batun da momy tayi musu kashedi suka ƙi ji, ai basukai ga bakin ƙofar ba ya jefo musu belt ɗin tashiga gaban su suka harɗe duk sansu dake karsu faɗi amma saida suka faɗi ƙasa suna ƙoƙarin miƙewa kenan yariga su zuwa wajen da hannu yafara dukan su kafin daga baya ya ɗauki belt ɗin suma ya zane su da hannu ya jawo su ya haɗe su guri ɗaya kamar wanda ya sha maganin ƙarfi haka ya ringa dukan su sai yayi tunanin ya rabu dasu sai kuma yaƙarajin wani haushin nasu da kuma ƙarfi sai kawai yaci gaba da dukan su..... wacce ta taɓasa Rasheeda kenan ita yafi duka da ƙyar ta samu baki tafara basa haƙuri amma yaƙi rabuwa da ita, yana cikin dukan nata yaji an riƙe masa bulalar ta baya afusace ya juyo dan ganin me gigin da tsautsayi yasa yariƙe masa abun duka, yana juyowa idon sa yasauka akanta haɗe rai yayi tare da zaro mata idanu zai ƙwace belt ɗin dan itama ya sauke mata nata rabon ƙin saki tayi tasa hannu biyu ta riƙe sosai tana girgiza masa kai mamaki ta bashi sosai cikin kara jin haushi yaja belt ɗin da ƙarfin gaske ya kwace ta daga hannun ta ya ɗaga zai sauke mata abaya tayi saurin haɗawa da bulalar ta faɗa jikin sa ta tariƙe belt ɗin a hannun ta ɗayan hannun kuma tariƙeshi ƙam tare da fashewa da kuka tana cewa dan Allah kayi haƙuri kayi haƙuri.......!!!!!✍️✍️ _plss kuyi haƙuri da jina kwana biyu shiru wayata ce ta samu matsala ta lalace saida nakai aka gyara duk da ƴan group ɗin WhatsApp sun riga da sun sani nasa ansanar daku tun loƙacin da ta samu matsalar amma nasan ƴan Facebook basu sani ba todai da wanda yasani da wanda baisani ba duk ina ƙara bada haƙuri,_🙏🏻 *sannan kuma naji daɗin kulawar wasu ina godiya da ƙoƙarin taimakon da kukayi nacewa ahaɗa kuɗi aturo min duk da ba aturo ba ina godiya da hakan Allah yasaka muku da Alkhairi nasamu kuɗi na gyara yanzu zamu cigaba daga inda muka tsaya* _ina ƙara baku haƙuri dai nima bada son raina hakan ta faruba har nakai tsawon wannan loƙacin bangyara ta ba sai yanzu ina fatan zaku fahimce ni nagodai.......🙏🏻,_                    💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 92 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️     "Sosai ta riƙesa ƙam yakasa motsawa saida sukai wajen minti biyu ahaka jin bai motsaba yasa ta ɗago da jikin ta daga nasa batare da ta kalle saba ta ƙara cewa dan Allah kayi hakuri ka rabu dasu kazo mu tafi Ummy na kiranka tayi maganar tare da ƙara sunkuyar da kai dan tana ɗan tsoron kar taji saukar duka yanda kasan tayi magana da gini haka yayi ko motsawa baiyi ba kuma baida na kallon taba, ɗan ɗagowa tayi takalle sa aikwa caraf suka haɗa ido dashi da sauri ta sunkuyar da kai gaban ta na dukan uku uku ganin yanda idon sa yayi ja kamar gwarashin wuta, Su Rasheeda ta shiga kalla yanda suke malelekuwa aƙasa da ɗaya bayan ɗaya tashiga kallon su har ta saukesu akan Rasheeda kallo ɗaya ta gane ta zaro ido tayi cike da mamakin ganin ta tayi saurin zuwa gurin ta tana cewa aunty aunty ta faɗa tana ƙarasa tsugunnawa agaban ta tana ƙara kiranta duk ganin ta yasa tabi ta rikice sai ƙoƙarin ɗagota takeyi, duk da halin da Rasheeda take ciki hakan bai hanata gane Ameesha ba tayi mamakin ganin ta amma ba halin yin magana ko ta tambaye ta wani abun azabar jikin tama kaɗai ta isheta so take ta zaro wayar ta ajaka ta kira dadyn ta azo aɗauke ta amma ta kasa ganin Ameesha yasa ta buɗi baki da ƙyar tace ɗauko min wayata ajaka, da sauri Ameesha ta jawo jakar tare da buɗewa zata zaro wayar Meer yayi ball da wayar da jakar tare da hannun Ameesha a tsorace taja baya tana yarfe hannun ta saboda zafin da taji ƙafar yaƙara ɗagawa zai buga kan Rasheeda da ita Ameesha tayi saurin shiga tsakiyar su aikwa ya sauketa akan ta wata gigitaciyar ƙara tasaki tare da ɗora hannun wanta akan, dafe kansa yayi tare da cewa oh God this girl is very trouble tsaki yaja tare da ɗan ranƙwafawa kanta zai taɓata tayi saurin ja da baya tana karkarwar jiki sai hawaye dake zirya a kumatun ta, mamaki ne yakama sa ganin yanda ta wani matsa haushi ma ya hanasa motsawa wallahi badan ƴar uwar sa bace da sai yayi maganin ta, hannu yasa ya fincikota ya ɗago da ita tsaye sannan ya riƙe hannun ta yafarajanta tana ta kuka tana cewa ta saketa tana kiran aunty Rasheeda sai turjewa take tana jan hannun ta amma ko gizau ɗin alamun zai saketa baiyi ba har suka fice daga gurin bata daina kukan ba tana juyawa baya tana waiwayon gurin, saida sukaje wajen motar sannan ya sake ta ummy ce tayi saurin fitowa daga motar ta kama hannun ta tana kallon meer tace me yafaru da ita badai dukanta kayi ba daga shiga kiranka sai yarinya ta fito da kuka me kayi mata shiru yayi yana huci tare da kawar da kansa gefe baida biyar bata amsa kenan, maida dubanta tayi ga Ameesha sannan tace ƴata me yafaru me yayi miki itama kasa bata amsa tayi saboda kukan da take, ganin duk basu da niyara bada amsa tasa ummy ta shigar da ita motar tace sai kazo mutafi kazo ka shanya mutane mun kai wajen 30 minutes muna zaune muna jiran ka saboda ka raina mutane kuma kafito anayi maka magana ka saka yarinya kuka kuma kayi shiru kaƙi magana ta ƙarasa maganar cike da ta ƙaicin abun da yayi sannan ta shiga itama, maama dake jinsu tayi shiru abayan mota ta ɗanyi murmushi sannan tace banda abunki tunda kika gansu haka ai ba lfy sai kibari muƙara sa sannan kowa yafara saukowa sai muji me yafaru ko kiyi masa uzuri muƙara sa, kallon ta Ummy tayi tace Allah maama yaron ne ya iya abun haushi kafito da yarinya tana kuka kuma anyi masa magana yamaida mutane ƴan iska wallahi bana son wannan halayyar tasa da kullum gaba take mutum kullum sai baƙar zuciya da baƙin hali, Murmushi dai maama ta ƙara yimata batace mata komai ba, Abu ma da ransa ya ɓaci ya ɗan ɗaga murya yace ba magana ake maka bane in kuma baza katafi ba bani key ɗin ni sai inyi driving ɗin tunda kai ba a isa dakai ba idan kaga dama ka dawwama anan gurin atsaye har ranar da zaka mutu dan iskanci da wulaƙanci daga cewa bari ka shiga ka fito shine ka shiga kayi zaman ka ai da kasani baka fito ba kai zamanka acan shima dai faɗa ya rufe sa da shi, ashe duk wannan tsawon loƙacin da ya ɗauka aciki yana lugudar su Rasheeda suna nan suna jiran sa, duk da faɗan da abu yayi masa amma ba aloƙacin ya shiga ba saida ya ƙara ɓata loƙaci yana tunanin su Rasheeda ji yake kamar ya koma ya cigaba da dukan su har sai yaga sundaina motsawa sannan ya rabu dasu dan gani yake su suka ƙara sakawa akayi masa faɗa yanzu abundai biyu ne ya haɗar masa ga ɓata masa ran da sukayi ga kuma faɗan Abu da ummy cike da ɓacin rai sai huci yake fitar wa kamar dafaffan abinci da ƙarfi yaja murfin motar kamar zai ɓallesa haka yajawo sa ya buɗe sannan ya shiga fuskar nan tasa tamau babu ɗigon annuri akanta idon sa har ƙanƙancewa suke saboda tsabar baƙin cikin da yake cin zuciyar sa gashi sai ta farfasa take, yana tayar da motar yaja wani mugun reavers aguje ya kwashi motar kamar zai tashi sama haka gafara janta tunkan ya hau kan titin ma, maama na ganin haka tayi saurin cewa ɗan gwaggo ina da magana ɗan tsayar da motar minti ɗaya baiji abun da tace ba yana shirin hawa titi abu yadaka masa tsawa tare da cewa ba magana ake maka ba wallahi idan baka shiga hankalin ka ba sai nayi maganin ka agunnan, burkin ma da ƙarfi yataka sa duk saida sukayi gaba suka dawo Allah ma ya tsare babu wanda ya bugu, cike da masifa Abu ya sauko zai sauke masa maama tayi saurin dakatar dashi tace yi shiru kar kace komai banni dashi badan Abu yaso ba ya rabu dashi amma shima zuciyar tasa akusa take yakaisa ƙarshe, shiru motar ta ɗauka kowa yayi shiru dan Ameesha dake kuka dataga abun yafi ƙarfin tayi saurin yin shiru, maama duk wannan halayyar tasu da suke babu abun da yabata haushi hakan ma da sukeyi ita daɗi yake mata tayi musu hakane dan aɗan samu loƙaci kowa zuciyar sa ta ɗan lafa, bayan kamar minti goma duk suna jiran suji ta bakin amma tayi shiru, saidaga bisani ta kalli ummy tace "kin iya tuƙi ko? ummy ta kalle ta sannan tace "eh, Maama tace "zakiya mayar damu gida, ummy ta girgiza kai tace gaskiya maama ba lalle ba saboda bansan kan hanya ba ga kuma dare yayi ki barshi yakaimu kawai sai yatafi ahankali bari inyi masa magana, maama tace "a'a rabu dashi ai ko kinyi masa bazai taɓa yin yanda akeso ba adai wannan halin da yake ciki kuma idan yayi tuƙin nan komai ma zai iya faruwa dan haka kiyi haƙuri kiyi sai in ringa nuna maki inda zaki bi, ummy tace to maama tafaɗa tana niyar buɗe motar Abu yace "maama kawai dan ransa ya ɓaci kuma sai aringa rabuwa dashi waye ba ayi masa laifi kuma ka gansa nml idan rai yaɓaci hankali ai ba ya gushewa idan shi mahaukaci ne yayi tuƙin da zai kashemu kowama sai huta tunda shikaɗai Allah yayiwa zuciya, maama tayi murmushi sosai sannan tace bashi kaɗai bane hardakai kaima ai kana da ita shiyasa bance kayi driving ɗin ba saboda kaima ranka yanzu aɓace yake koda ka karɓa kai kanka bazaka iya yin driving ɗin cikin hayyacin kaba shiyasa nace ita tayi dan haka nagama yankewa kar wanda yaƙara magana, babana ɗan albarka dawo kusa dani kagaya min damuwar ka kaji tafaɗa tare da dafa kafaɗar meer, ganin ko motsawa baiyiba yasa ta fito daga cikin motar ta zagayo wajen sa sannan ta buɗe masa ƙofar ta kamo hannun sa bai musa mataba ya fito daga ciki basu shiga tace to fito kishiga fitowa ummy tayi ta koma driver seat sannan maama tace Ameesha ta shige ciki matsawa tayi sai ta fara saka meer aciki sannan itama ta shiga yazamana shine a tsakiyar maama da Ameesha, tayar da motar ummy tayi tafara tuƙawa ahankali har suka hau kan titi suka fara tafiya cike da nutsuwa takeyi ba gudu kuma baiyi slow da yawa ba, Abu ne dake gaba yafara kwatan ta mata inda zatabi..., maama ce ta jawo meer ta kwantar da kansa akan kafaɗar ta tace ɗan albarka waye ya taɓa min kai nasan wannan fushin naka ba abanza ba da kwai ƙwaƙƙwaran dalili ko har yanzu zuciyar bata fara sanyi ba, shiru yayi baice da ita komai, ganin hakan yasa ta ɗago da kansa tana kallon fuskar sa idon sa har yanzu yana nan ajansa bai raguba hakan da tagani kuma ya tabbatar mata da bazata taɓa samun amsa yanzu ba daga gare sa dan haka sai kawai tace kwanta anan ta nuna masa kan cinyar ta ko kunya baiji ba ƙato dashi ya kwantawa ƴar tsohuwa akan cinya, Ameesha bata san loƙacin da bakin ta ya suɓice ba tace kai  babba ne fa tana faɗa kuma tayi sauri tasa hannu ta toshe bakin ta, dariya maama tayi tana kallon ta tace to ina ruwanki da girman sa bama son sa ido, tana gama faɗa mata haka tasa hannu tana shafa masa kai tana cewa idan bai kwanta ba waye zai kwanta kinga ke kina da daddar ki ni kuma ga nawa shalelen nafi ji dashi akan kowa duk wanda ya taɓasa ma sai inda ƙarfina ya ƙare, ummy dake tuƙi tace wallahi maama wannan dakike gani ba ayi masa gwanin ta idan ya tashi rashin mutun cinsa har ke zai haɗa kar ƙiƙara lalata sa yaci gaba da abun da yake ya lafiyar kura bare ta ƴaƴan ta, Maama tace au ashe ƴan baƙin cikin da yawa to kwa ƙwalelan ku cinya ce ya kwanta saidai ɗan baƙin ciki ya mutu, Ameesha tayi dariya tace tabb wallahi abun ma ko kyan gani ma babu dan Allah maama kice ya tashi, duk abun da suke yana jin su bai tankawa kowa ba saida yaji abun da Ameesha tace sannan ya girgiza kai tare da ɗaga ƙafafuwan sa gaba ɗaya biyun ya saukesu akan cinyar ta itama tare da matseta da jikin kujera yanda zaiyi blance ya miƙar da ƙafarsa, Wayyo maama kinyi masa magana wallahi da nauyi ƙafata zata karye daman kuma zafi take mun tayi maganar cike da shagwaɓa kamar zatayi kuka, dariya sosai maama tayi mata tace "haka yake so yaji sa daman idan yabar ƙafar sa aƙasa bazaiji daɗin kwanciyar ba amma kinga idan yayi haka sai yafi jin daidai, miƙa hannu tayi ta ƙara gyara masa ƙafafun ya miƙar dasu da kyau sannan taci gaba da shafa masa gashin kansa tana ɗan bubbuga wa tace maza kayi yanda kake so a inda kake so kaji daɗi babban jikana, tayi maganar tana satan kallon Ameesha dan taji me zatace tana ɗan murmusawa, hawaye Ameesha tafara zubarawa tace wallahi da nasan hakane da ban biyo kiba kinsa haka zaki min kika rabani da dadda ta, to ko asaukeki koma maama tace da ita, goge hawayen tayi tana haɗe rai tana turo baki tace "nidai wallahi kice masa ya ɗaga ni ƙafara zafi zata karye, maama tace baki da baki bagaki gashi ba ke kigaya masa mana, turo baki ta ƙara yi tace "ni ba ruwana dashi bazan ƙara yi masa magana ba mugu ne ba abun da ya iya sai cin zalin mutane yanzu mafa wasu mata yakama aciki ya ringa dukan su yanzu hakama suna can akwance wataƙil ma wasu sun mutu kuma daga cikin su harda Aunty na nasan babu abun da sukayi mishi saboda mugunta da fin ƙarfi nima dannaje na bashi haƙuri shine yakama ya haɗa dani daga cewa yayi haƙuri yazo ummy na kiransa ya dawo kaina taƙarasa maganar tare da wurga masa harara ta ƙasan ido harda murguɗa masa baki hda ɗan tsaki ƙasa ƙasa yanda tasan bazaiji ba, maama tace au abun naki kuma yanzu harda sharri to nidai ko jikina duka kunnuwa ne bazan yarda ba, ummy ce tayi saurin cewa inna lillahi hayatee daman baka daina dukan mata ba wlh maama da gaske ne haka kwanaki yayiwa wata yarinya wai kawai dan ta shiga office ɗin sa shine bakiga irin dukan da yayi mata harda su cire mata kaya saboda tsabar iya shege irin nasa da rashin haƙuri, maama tace kofa me zakuce saidai kuce amma bazan goyi bayan kuba duk abun da yayi yayi daidai wallahi sai kace mahaukaci hakan nan zai gansu ahanya yakama duka sai kace taɓaɓɓe duk halin sa nasan bazai taɓa yin haka duk yanda akayi su suka jawowa kansu suka shiga harkar sa bana raba ɗayan biyu ma ko irin ƴan iskan matannanne suka gwada masa halinsu shikuma ya koya musu hankali gwanda da yayi maganin su wallahi, ɗan gidan gwaggo ƴan iska ne ko tayi maganar tana leƙan fuskar sa kai ya ɗaga mata alamar "eh, yauwa nidai nasani da dalili to wallahi ina bayan ka kamar doro kacigaba da yanda kakeyi duk ƴar iskar da ta kawo ma wurgi kaci uban ta ka koya mata hankali kai ko alama ma kagani ka saita mata tunanin ta daga kanka bazasu ƙara ba, Tabb gaskiya maama baza kuringa zama guri ɗaya ba duk yanda zanyi inga baku zauna guri ɗaya ba zanyi tundadai ke zigashi zaki ringa yi ba ƙya ganin laifin sa idan yaga haka ai cigaba dayi zaiyi maimakon ki hanasa amma sai kifara taya ɓera ɓari to wallahi da sake, maama tace "aikwa dai ba yanda zakiyi nidashi mutu karaba ke nan gabama ɗaki ɗaya zamu ringa kwana kuma duk inda zashi tare zamuje duk wanda yayi mana ba daidai ba kuma mu haɗu mucimar uwa zanma ƙara gayyato mana gwaggo tafiyar sai tafi daɗi, duk wanda yashiga sabgar mu sai ya gane bashi da wayo ko ɗan gidan gwaggo yanzu ma saida ta leƙa fuskar sa kuma tasamu haɗin kansa yanzu harda buɗar baki yace "eh, tace "yauwa ɗan gari na gidan gwaggo bani biyar inbaka goma ta miƙa masa hannu su tafa baisan me take nufi da hakan ba amma ganin ta miƙo hannu sa yagane nufin ta dan haka sai kawai ya ɗago hannun sa suka tafa hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba daman haka take so yafara sakin jikin sa shiyasa take yin haka tana goyen bayansa dan ta jawo hankalin sa zuciyar sa tayi sanyi kuma taga alama tasan zuciyar sa yanzu tafara dawowa normal, itadai Ameesha shiru tayi saboda haushi da taƙaicin su gaba ɗayan su haushi suka bata dataga bata ita suke ba suna ta surutun sa ta ɗan saci kallon tare da hararar sa ta janye idon ta tana kallon ƙafar sa tana ayyana abun da zatai masa ta rama kafin asauka gashi har anshigo layin gidan sun kusan ƙarasawa, sarai yaganta loƙacin da ta harare sa rabuwa yayi da ita kawai dan tara ta yake duk abun da tayi masa, tana cikin kalla tana wani abu ya faɗo mata rai karkaɗa kai tayi harda cije baki da ta ɗaga kai taga har sunzo me gadi ya buɗe musu gate sun shiga sai kawai ta tsugunna kamar zata ɗauko abu aƙasa sai kawai ta saisaita daidai wajen ya tsan sa tasaka abaki ta gasa masa cizo awajen, bazato ba tsammani yaji azaba baisan loƙacin da yasaki wani ɗan ƙaramin ihu ba da sauri ya janye ƙafar tare da miƙewa zaune ya riƙe ƙafar yana kalla, fashewa da dariya Ameesha tayi sosai ta shiga yin dariya harda riƙe ciki bata taɓa tunani zaiji zafin cizon ba wai sai gashi harda ihu idan ta kalle sa taga yanda yake zaro ido yana kallon ƙafar sai ta sake fashewa da dariya, Maama dai da take goyen bayan sa saida tasaka masa dariya tunda komai agaban idon ta akayi komai taga abun da Ameesha tayi masa dan haka itama saida ta dara sosai, ummy tana gama daidaita parking ɗin jin dariyar su tayi yawa ta juya tana tambayar dariyar ne akeyi duk sun kasa bata amsa sai dariya suke, wani abune yaso masa wuya ya tokare masa a wuya na taƙaici ga tayi masa laifi kuma tazo tana masa dariya hannu ya ɗaga zai maketa maama ta riƙe hannun sa da sauri tana so tayi masa magana amma dariya ta hanata, Abu ne yafito kuma yana fitowa yayi wucewar sa bai tsaya wajen su ba dan har yanzu bai dawo daidai ba cike yake da haushin Meer, ita kuma Ameesha gani hakan yasa tayi sauri ta buɗe motar ta fita saida ta fita ta ƙara kwashewa da dariya ta zagaya wajen ummy da ta fito daga ciki itama ta maƙale abayan ta, ummy tace ke kikayi masa laifi kenan to matsa daga bayana ke dashi ummy wallahi rama abun da yayi nayi ɗora min ƙafa fa yayi kuma nace da zafi ya ɗaga min yaƙi nikuma da na gaji shine na cijeshi, ummy tace kinyi daidai kam gwanda da kika rama amma da ba ruwa na idan bai haƙuraba zan riƙeki ya rama tunda shi ba cizon ki yayi ba, kai ummy kema goyon bayan sa zakiyi kenan shikenan tafaɗa tana matsawa daga kusa da ita da sauri ummy ta riƙota tana dariya tace da wasa nake miki zo mutafi murigasa shiga, suna juyawa zasu tafi maama da shi suka fito tare yana ta jan hannun sa tasake shi amma taƙi sakin sa saida suka fito har sun fara tafiya sai maama ta sakeshi dan taga me zaiyi tana sakin sa kwa da sauri yayi wajen su Ameesha, daman Ameesha tana tafiya tana juyowa ganin ya taho wajen ta da sauri yasa taja hannun ta zata gudu ummy ta riƙeta ƙam tace zo gata na riƙema ita, wayyo ummy dan Allah kisake ni wallahi dukana zaiyi mugune fa shi dan Allah kisake ni saura kiris ta fashe da kuka, yana daf da ƙarasawa kusa dasu sai ummy tasake ta tare da shan gaban meer tana dariya itama, Ameesha tunda taji ansake ta bata ƙara tsayiwar rabin second ba ta kwasa aguje tayi cikin gidan saida taje bakin ƙofar dakin sannna ta tsaya ta juyo tana kallon su tana dariya harda ɗaga masa hannu tace aidai baka kamani ba tana faɗa ta kuma shigewa ciki ɗakin da ummy ta kaita da safe nan ta shige tare da sakawa ɗakin key, cike da ɓacin rai ya kalli ummy yace "ummy kinga fa abun da take min ta rainani ta maidani ma abokin wasan kenan ni sa'an tane da zata ringa min irin waɗannan abubuwan wallahi na kamata sai karya nata ƙafa har ni zata ciza saboda ita mayya ce to wallahi sai tasan wanda ta ciza yafaɗa yana bin ta gefen Ummu ya nufi cikin gidan shima, da kallo suka bishi ita da maama da ƙarasowa ta gurin kenan, ummy tace "maama wannan faɗan nakine sai kisan yanda zaki rabashi tunda daman ke kika haɗa abunki sai kiraba, maama tace "zan kwa raba muje kedai kiga ai nasan bazata zauna a falo ba ayau dai ba yanda zaiyi da ita saidai kuma yabarwa gobe dan bazanma bari su haɗu ba, ahaka suka ƙarasa cikin falon suka gama ba kowa aciki shi har ga hau sama ɗakunan ƙasa suka fara dubawa har suka gano inda take ciki maama tace to buɗe mune ta can ɗakin Ameesha tace Allah bazan buɗe ba sai gobe ina nan so kike in fito ku haɗu kuyi min duka ko to bazan fito ba duk yanda suka so ta buɗe ƙin buɗewa tayi dole suka rabu da ita ummy ta wuce ɗakin ta gurin Abu, ita kuma maama Saida ta ƙara zuwa gurin meer ta lallaɓa sa har saida yayi sallah agaban ta yagama duk abun da zaiyi ya kwanta sannan ta fito daga ɗakin itama ta tafi nata bayan tayi wanka tayi sallah da addu'o'i sannan ta kwanta itama, *************************** *Rasheeda* da taimakon securities ɗin wajen aka taimaka suka shiga motar su amma babu wanda zai iya jan motar acikin su wanine daga cikin su yajasu yakai su har gidan su Rasheeda, bayan ya shigar dasu ciki da ƙyar duk suke iya takawa suka fito suka nufi cikin gidan suna shiga suka tadda su momy a falon suna zaune suna jiran dawowar su harda mom ɗin Rasheeda itama tana falon, gaba ɗayan su miƙe sukayi tsaye mom tayi saurin kamo Rasheeda cike da tashin hankali ta shiga tambayar ta abun dake faruwa taga shatin duka ajikin ta bata basa amsaba saima fashewa da kuka datayi zaunar da ita tayi kan kuke ta suma sauran duk guri suka samu suka zauna suna jinyar jikin su, itadai momy dariya take tayi aciki ciki bata bari ta fito ba daman abun da take gudar musu kenan suka ƙi ji, sosai mom ta rarrashin ta ta samu ta ɗan tsagaita kukan sannan mom ta shiga tambayar su gaba ɗayan su amma har yanzu babu wanda ya iya bata amsa, momy ce ta miƙe tace mom bari inbaki labarin abun da yafaru nan ta zayyano mata abun da yafaru tundaga farko har ƙarshe sannan ta ɗora da cewa mom wallahi yayi musu da sauƙi saida nagaya musu suka ƙi ji abun da yayi min babu wanda aka taɓa yiwa haka su ai amutun ce ya dake su nifa saida yayi min tsirara haihuwar uwata sannan ya dake ni kuma ya koro ni ahaka bainar jama'a ahaka, babu wanda baiyi mamakin abun da ta faɗa mom tace ɗan gidan uban waye shi agarin nan a ina yake waye uban sa, momy tace mom ba ɗan garin nan bane a Abuja yake ni banma san me yakawo sa nan ba, mom ta miƙe tsaye tana zagaya falon tace aikwa ya taɓo tsuliyar dodo sai yasan bai daki banza ba dan bazan barsa ba koɗan gidan uban waye agarin nan sai na nemosa akan me zaisa hannu yadakar min ƴa to wallahi daga kanta bazai ƙara dukan wata ba tunda shi jaki ne da zai ringa kama ƴaƴan mutane yadaka kuma yazauna lafiya to yo ya taɓo me gata dan sai an rama mata abun da yayi mata wallahi bai daki banza ba sai yayi da nasanin dukan ta, tana magana tana faman huci wai ita ala dole taji haushi an dakar ƴa (to masu ƴa kizo wajena yaseen zan baki address ɗin sa idan kanki wuta yake nasa gobara yake hajiya halima shirgigeya) momy najin maganganun da take aranta tace sai kin dawo Allah yabaki Sa'a wallahi bazana hanaki zuwa ba afili kuma tace wallahi mom yakamata dai anuna masa ya daki ƴar gidan gata yasan ko wa ya daka arama mata a wulaƙan tasa ya gane kuren sa, tace "kar ki damu ai harke sai na ramawa yanda yayi miki tsirara sai anyi masa haka yaji inda daɗi sainasa ya kusan zagaye garin nan babu kaya ajikin sa sai anyi masa dukan mutuwa yanda sai yadawo jin tsoron duk wata mace bama kuba ke har uwar sama sai tagane kuren ta tunda yanayi bata dakatar dashi ba tabari yake wulaƙan ta ƴaƴan mutane sai sun gane kuren su gaba ɗaya sai na koya musu hankali...... sosai momy ta nuna jin daɗin ta harda murmushi amma fa murmushin da biyu take na mugun tane kawai take mata dan harta hasko yanda za ayi facali da ita da wannan ƙaton jikin nata, cigaba tayi da koɗata tana zugata akan kar ta rabu dashi gobe gobe zasu koma gurin ma zasu fara binciken inda yake za anemo har gidan da ya sauka, da waɗannan maganganun suka sa su Rasheeda suka ɗanji dama dama har suka tashi da ƙwarin gwiwar su da taimakon su momy duk suka tashi suka kaisu ɗaki gaba ɗayan su.......✍️✍️ _🤣Woo gobe fa kowa ya shirya zamu taya su mom ɗin Rasheeda neman meer zamu ɗauki fansa🤣🤣🤣_ _gashi kuma gobe zamu tafi masarauta kai gobe dai da kallo da yawa_ I can't wait to see 💃💃💃💃💃💃                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 93 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                    *_WASHE GARI_* tunda sukayi sallar asuba babu wanda ya koma amma basu fito ba saida gari yafara yin haske sannan ummy ta fito tayi musu abun da zasu karya wajejen ƙarfe ta tara ta gama shirya musu komai akan dinning ɗin sannan taje tafara kiran maama tafito sannan ta haura sama taje ta kirawo meer da ƙyar ya fito acewar sa shi ta ƙoshi bayajin yunwa saida tayi masa dole sannan ya yarda ya fito, saida taga fitowar sa sannan ta nufi ɗakin da Ameesha take, tana zuwa ta ƙwanƙwasa mata ƙofar tare da kiran ta tace zo kibuɗe ni kaɗai ce, da sanɗa Ameesha tazo wajen ƙofar sannan tace Ummy dan Allah baya nan yana ɗakin sa dai ko? "Eh, Ummu tace mata sannan ta buɗai ƙofar ta ɗan leƙo ta tabbatar da ita kaɗai sannan ta karasa buɗe ƙofar gaba ɗaya, ummy ta kalle ta da towel aji kinta  sai tace mata "yanaga baki saka kaya ba ko bakiyi wanka bane naganki ahaka, ummy nayi kayan da zancanza ai suna motar banɗakko ba shi yasa danayi wankan na zauna ahaka saboda daman nifa ayau bazan fita ba ko abinci ma saidai inci anan indai ba barin gidan nan yayi ba bani fitowa wallahi, ɗan murmushi ummy tayi sannan tace "da kinsan kina jin tsoron sa har haka shine kika cije sa, bari insashi ya ɗauko miki kayan kisaka kifito babu abun da zai miki tunda har aka kwana baimiki komai ba to wataƙil ya manta ma shi bazai miki komai kidaina ɓuya ki kwantar da hankalin ki kifito muci abinci ke kaɗai muke jira kiyi sauri yanzu zan saka shi yakawo miki , a'a ummy wallahi indai shine bazan yarda in buɗe kofar nan ba nidai kawai dan Allah ummy akawo min abinci na nan ba sai na fito ba, Ummy tace "Allah kar kidamu yariga da ya manta saboda shi baida riƙo kwata kwata indai kayi masa abu aloƙacin zai rama idan kwa ya wuce bai ramaba to ya barsa kenan, dan haka kima daina wannan tunani bari inje idan ya ɗauko su amota sai ni in kawo miki nan sai kisaka mufita tare ina tare dake babu abun da zaimiki, Ameesha tace "yauwa ummy to gwanda haka dai kikawo min da kanki sai mufata ɗin, Ummu tace to shikenan bari inje sannan ta juya ita kuma ta koma ɗakin, ta rufe ƙofar bata saka muƙulli ba amma, " tunda meer ya fito kuwa yake baza ido yaga ta inda yarinyar nan zata fito dan yayi alƙawarin sai ya rama abun da tayi masa tunjiya abun ya tsaya masa arai inbai rama ba bazai taɓa jin zuciyar sa daidai ba, yana fitowa maama ta kalle sa sarai tagane kallon da yake yi dan haka tayi saurin kiran shi ta nuna masa gefen ta yazo ya zauna nan tafara jansa da hira suka gaisa da ita sannan ya juya ya gaida Abu banza Abu yayi dashi bai amsa ba dan har yanzu shima baisauko ba haushin shi yake jiki, shikam ko ajikin sa sai ya ɗauko wayar sama yafara dannawa, maama da ta lura da haka sai ta ɗan taɓasa da hannu yana ɗagowa ta nuna masa abu sa ido alamar abun da yayi bai kyauta ba shiru yayi baice komai ba, ƙasa ƙasa tace kabashi haƙuri kayi laifi kallon ta yayi da mamaki haƙurin me kuma zai basa alhalin bai masa komai ba rashin amsa gaisuwar sa kuma ganin dama yayi shiyasa yaƙi amsawa kuma shidai yariga ya fita tunda ya gaidashi shine baiga damar amsawa ba to akan me zai basa haƙuri kuma, girgiza masa kai tayi tace kayi abun da nace maka kawai inkanaso muzauna lafiya, saida ya ɗauki loƙaci yana tunani ta inda zai fara bashi haƙuri batare da yayi masa komai ba saida ta ƙara taɓasa sannan dai ya daure batare da ya kalli inda Abu ɗin yake ba yace sorry shima can ƙasa ƙasa ya faɗa saboda bada son ransa yayi ba, Abu yajisa amma yanzuma sai ya nuna baima san sunayi ba daga shi har maama, maama zata ƙara magana kenan ummy ta ƙaraso wajen tana ɗan murmushi tace maama mutuniyar kifa taƙi fitowa saida ƙyar ta yarda zata fito amma ta manta kayan ta amota jiya tsokana tahanata ɗauko su saidai hayatee yaje ya ɗauko mata saboda har ta riga ta cire waɗan can tayi wanka nasauyawa take buƙata kawai ta fito, dariya maama tayi tace ai nasan daman da ƙyar zata fito ai ya haƙura babu abun da zaiyi mata je ka ɗauko mata ka kai mata, da sauri ummy tace a'a maama tace saidai ya ɗauko nikuma sai inkai mata idan tasaka sai mufito atare amma idan ba hakaba bazata fito ba dan haka yaje ya ɗauko yakawo min sai in kai mata, Maama tace "to Shikenan hakan ma yayi yaje ya ɗauko ɗin yi sauri ka ɗauko danni ƴaƴan hanjina sun fara motsawa yunwa nake ji, da farko ƙin yarda ya tashi yayi saboda yana ganin ta gama rainasa shine ma zaije ya ɗauko mata kayan da zata saka tabb tayi kaɗan kuwa  saidaga baya kuma ko me ya tuna oho sai ya tashi ya nufi hanyar fita, umm 87y kuma sai tafara saving ɗin maama ta zuba mata duk abun da take buƙata sannan ta koma wajen Abu da yaƙi kula kowa agun sai faman haɗe rai yake, zuba mishi ta shigayi, Meer na fita yaje ya buɗe motar yashiga duddubawa yagano jakar kayan nata ya ɗauko yana wani ya mutsa fuska kamar ya taɓa kashi ahaka ya riƙo jakar har ya ƙaraso wajen falon dake da ɗan tazara tsakanin falon da wajen dinning ɗin sai ya kalle su ya tabbatar da hankalin su baya wajen sai kawai yabi tagefe ya nufi ɗakin da yake da tabbacin tana ciki har yaƙarasa bakin ƙofar babu wanda yaga shigowar sa, tunani ya ƙwanƙwa sa yayi sai kuma yafasa ya gwada murɗa hannun ƙofar yaji ko ba muƙilli aikam yana murɗawa yaji ta buɗu turawa yayi ya shiga tare da saka ƙafar sa guɗaya aciki sai kuma ya shiga gaba ɗayan sa dake ƙofar bata da ƙara kwata kwata bataji shigowar saba har ya rufe ƙofar bataji ba tana kwance akan gadon ɗakin tayi rigingine tanajiran shigowar ummy, tsaye yayi a bakin ƙofar ya jingina jikin sa da ita yana kallon ta ganin har yanzu batasan da shigowar sa ba, sai ya ɗaga jakar hannun sa ya wulla mata ajiki azabure ta tashi zaune bata gama tsorata ba saida tayi ido huɗu dashi azubure ta miƙe tsaye tana muƙewa bata tsaya wata wataba ta kwasa aguje tayi hanyar banɗaki kafin yayi yunƙurin binta harta shige ciki ta saka muƙulli, jinjina kai kawai yayi tare da yin ƙwafa yafice daga ɗakin dan shi ba ƙaramin yaro bane bazai biye mata suna guje guje ba zai rabu da ita har sai ranar da zatakawo kanta har inda yake zata gane kuren ta, yana fita yasamu waje ya zauna inda ya tashi maama tace ina kayan, "nakai mata kawai yace da ita sannan ya ɗauki tea 🍵 ɗin da ummy ta haɗa masa yafara sha, kallon kallo ummy da maama sukayiwa juna ba wanda yace komai sai kawai ummy ta miƙe ta nufi hanyar ɗakin tana zuwa taga ƙofar abuɗe shiga tayi taga ɗakin wayam ba kowa aciki kiran ta tashi ga yi, tana ƙarasa shiga cikin tsakiyar ɗakin, daga cikin bathroom ɗn Ameesha ta amsa tare da buɗe ƙofar ta leƙo saida taga ita kaɗai ce sannan ta fito daga ciki tace ummy shine kika aiko sa badan nayi hanzarin ganin saba da tuni yayi min dukan mutuwa, ummy tace "wallahi banma san yazo haka nace kawai yakawo min in kawo miki shine ya taho dan bansan ma loƙacin da yashigo ba har yashigo nan baidai yi miki komai ba ko, "eh ummy Allah ya taimakeni bai kamani ba ai, to yanzu yi sauri kisaka muje sai ɓata mana loƙaci kike tun ɗazu ke muke jira, da ƙyar dai ta yarda ta shirya sannan suka fito tare, tana ta ɓuya abayan ummy har suka ƙaraso gurin can kusa da abu ta zauna tunda tasan idan tana kusa dashi ba lalle yayi mata wani abun ba, saida ta zauna sannan duk ta gaida su amma bata gaida meer ba kuma babu wanda yayi mata magana dan basu lura bama amma shi yana sane da ƙin gaidashi ɗin da tayi, ba ɓata loƙaci suka shiga cin abinci batare da kowa ya ƙara magana ba, suna cikin ci wayar ummy tayi kara dubawa tayi sai taga number Ammi ce da ta karɓa jiya take kiran ra da sauri ta ɗaga tare da saka wayar a speaker tace hello daga can ma Ammi tace hello ina kwana  dafatan kun tashi lafiya, ummy ta amsa mata da lafiya lau, sannan Ammi tace daman yanzu yaron gidan masarautar nan ya kira  yace baida Number ku yace ku hanzarta kushir ya nan da ƙarfe goma za ayi wani taro acan kuma yanaso ayi agabanku saboda ansamu wata gagarumar matsala acan kuma yanaso ayi komai agaban ku dan haka yace kuyi gaggawar halattar taron, ummy ta ɗago ta kalli maama sannan tace to shikenan gamunan sai kuma kushirya muna zuwa sai mu wuce yanzu zamu fito, Ammi tace "to shikenan sai kun ƙaraso,  daga nan sukayi sallama, maama tace tofa me kuma yafaru haka da sassafe za ayi taro, ummy tace nimadai nayi mamakin hakan amma dai muyi sauri muje sai muji abun dake faruwa, nandai sukayi shiru sukayi sauri suka ƙarasa cin abincin daman kowa yayi wanka dan haka basu wani ɓata loƙaci ba suka gama shiryawa suka fita daga gidan, Meer da Abu agaba sai su maama abaya, yanzudai bayi wannan mahaukacin gudun ba yana tafiya ahankali har suka iso gidan su bossay, loƙacin da suka shiga suma duk sungama shiryawa su kaɗai suke jira, Hajiyar shettima ma da shi kansa shettiman duk suna cikin gidan  sun daɗe da zuwa saboda su  zasuyi musu jagoran ci zuwa cikin gidan batare sa an tsayar dasu tamabayar su waye ba ko daga ina suke, saboda kiran da sam yake tayi musu yasa basu wani tsaya gaisuwa mai yawa ba suka ƙara fitowa gaba ɗayan su harda dadyn bossay sai Ammi da bossay shettiman da hajiyar sa sai kuma dadda gaba ɗayan sudai haka sukayi mota mota wajen motoci haɗu sukayi suka nufi masarautar........., ******************************* ________*masarauta*_________      :A daren jiya dai babu wanda yayi bacci me daɗi kowa ya kwana zuciyar sa  babu daɗi wasuma basu samun damar  rintsawa ba yanda suka ga rana haka suka ga dare kowa na tunanin me zai faru ba iya waɗan da abun ya shafa ba har sauran ma'aikatan gidan da akayi komai agaban idon su tun adaren kuwa labari ya karaɗe lungu da saƙon cikin masarautar babu wanda baiji ba dan magana ma harta fara fita waje kan cewar sarkin gari ba ɗan masarauta bane baida alaƙama da masarauta haka dai sukai ta yamaɗiɗi tare da ƙara gishiri da magi akan maganar dan tafi armashi saboda ba iya abun da yafarau ake faɗa ba sai anyi ƙari, aranar yau kuma papa shima yadawo cikin hayyacin sa kuma shima Ammah tagaya masa abun dake faruwa ba ƙaramin ɓaci ransa yayi ba dan haka dan da nan yasa akafara sanar da duk wani wanda yake da alaƙa da masarauta akan ahallara ƙarfe goma daidai acikin fadar da kuma ƴan cikin fadar manya manya amma banda yara ƴan ƙananu iya iyaye da samarin gidan waɗanda suka mallaki hankalin kansu irin su sam kenan....., tun wajen ƙarfe tara akafara hallara acikin fada ɗaiɗai kune basu zoba kawai,     *_10:am_* kowa ya hallara daga ciki sarki Salahudden ne karshen shigowa shi da Azeema suka shigo normal kayane ajikin sa dan ko hula baisakaba haka yataho kamar bashi ba tunda ya shigo papa dake zaune kan kujera ya ke binsa da kallo tunda ga sama har ƙasa ya kafe sa da ido bashi kaɗai ba sauran mutanen gurin ma duk kallon sa akeyi can ƙasa daga gefe babu kowa agun nan ya nufa ya zai zauna aƙasa papa yayi saurin dakatar dashi tare da cewa me yasa zaka zauna aƙasa kuma ina kayanka ka saka waɗannan kayan kuma ko hula baka saka  ba akan wane dalili? sunkuyar da kansa yayi tare da cewa aimin afuwa amma bazan iya kara saka kayan ba saboda badani yadace ba kujera ma kuma nagama zamanta koda ace hakan ba gaskiya bane bare ma kuma na tabbatar da bani da alaƙa da ita tuba nake mai martaba amma bazan iya bin umarnin ka ba akan sai nahau kujera koma nasaka wani abu da ya shafi sarauta yana gama faɗar haka ya zauna a inda yayi niya tun farko Azeema agefen sa ya zauna tare da hade gwiwowin sa ya kifa kansa akai bai ƙara kallon kowa ba har mahaifin sa dake gurin, fulani kam yau itama ba kan kujera tana ƙasa kamar yanda kowa yake mutum biyu ne kawai akan kujera daga papa sai Ammah amma kowa na ƙasa, kujerar sarki kuma tana gurin itakaɗai ba kowa akanta, wayar Azeema ce tayi ringing da sauri tasaka ta a silent tare da miƙewa tsaye ɗan ɗaga murya tayi tace agafar ceni zanje in shigo da mamana sun ƙaraso, Ammah ce tace "to ki hanzarta ana ta ƙara ɓata loƙaci kowa ya hallara daman su muke jira, da sauri ta fita daga cikin fadar, papa ne yace "wai banga gwaggo ba ko ba asanar da itaba ne najita shiru har yanzu ko sai an ƙara kiranta, Ammah tace " inagadai ko wani abunne ya riƙeta Ammar je ka kaƙara kiran ta, da sauri ya miƙe tare da cewa to sannan ya fita, yanama fita suka haɗu da ita tana daf da shigowa dan haka sai suka dawo atare suka shiga suna shiga ko sallama gwaggo batayi ba tace "nashiga uku ni ƴar nan me nake gani haka daman abun da ake faɗa min gaskiya ne suwa nake gani aƙasa sarki naga kanka haka ko hula kuma aƙasa azaune lalacewae har takai haka  ina munafukar take hatsabibiyar almura  amma dai kedai bakida imani tunda nake bantaɓa jin irin wannan ɗanyaen aikin ba ke naki watakon yafi na kowa nidaman tun farko banyarda dake ba saboda daman zubinki zubin munafukai duk wanda yaga ƙwayar idonki yasan ƙungurumar munafukace da kanta kamar ƙullin maganin bokaye, har gabanta taje tare da ɗago kanta da hannu ta fara duddun gure nata kai tana cewa "Allah ya toni asirin ki yau wai mema akejira ba ayiwa yara tsira taba  tunda ga hujja an samu kuma me yarage ai naso inzo inga an sauya mata kamanni amma sai inzo inganta ras da ita babu wani tabo to ni wallahi bari infara yi mata dan idan naganta haka zaune lafiya ƙalau raina bazai min daɗi ba amma idan naga ana magana tana cikin wani halin sai nafi jin daɗi tana gama faɗar haka ta ɗaga wani ɗan katako da tazo dashi daman saboda dukan ta ta taho dashi ƙwala mata tayi akai zata ƙara sauke mata wani papa yayi saurin riƙeta yace haba gwaggo kiɗan dakata mana afara yin magana dan Allah ki rabu da ita ki samu waje ki zauna yanzu ba wannan loƙacin bane, kasan Allah bazan rabuda ita hakannan ba sai na tsiyayer mata da ido, daƙyar papa yajata amma duk da haka saida ta ƙara ziro katakon ta gefen sa ta bugawa fulani akafaɗa sannan tabar wajen, Allah sarki fulani tana zaune ta sunkuyar da kai takasa ɗaga ido ta kalle kowa ranta duk yabi ya dagule ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse ciki saboda jin kunya da taƙaicin abun da ake mata gashi kuma batasan ma me zai faru ba wane irin hukunci za a yanke mata ba, zama gwaggo tayi amma duk da haka bakinta yaƙi yin shiru da ƙyar aka samu tayi shiru sai kuma ta koma hararar ta tana girgiza kai sai karkarwa take jikin ta tsima yake kawai so take taga jikin fulani jaga jaga da jini an kunkunbura mata wani gurin sannan hankalin ta zai kwanta amma yanzu gaba ɗaya hankalin ta baya jikin ta, suna cikin haka saiga su Azeema sun shigo ita da mana da saleem, bakin su ɗauke da sallama suka shiga, amsa musu akayi  tunda suka shigo kallo yadawo kansu kowa su yake kallo yamaida hankalin sa gare su musamman ma ma mama da kana ganin ta kaga sarki Salahudden kuma suna kama da saleem ma sosai, dan haka tun kan ace komai ma kowa ya tabbatar da cewa lalle waɗannan jinin sane sune ƴan uwansa ba ƴan cikin masarauta ba, itadai mama batasan komai ba game da maganar saboda ba asanar da itaba kawai Azeema haka tace mata suzo ana nemansu masarautar saboda angano ta kuma gata ga baba komai lafiya babu wani abu da yasame ta dan ta kwantar musu da hankali har suzo shiyasa tayi musu haka, amma ganin kowa yana ta kallon su sai yasa duk suka tsargu dan haka ababakin ƙofar suka samu waje zasu zauna, gwaggo ta miƙe zunbur tace ina ku ina zama anan ai taron nakune ku matso daga gaba gaba kuji abun da wannan tsinanniyar da tagama kwashe kayan ta daga gaban ma'aiki ta tsula wannan gagarumin zunubin ko kunyar Allah bataji ba ta raba ɗa da mahaifiyar sa tazo ta koya masa mugayen ɗabi'un irin nata, papa ne yaƙara dakatar da ita tare da bata haƙuri kuma ya roƙeta dan Allah tayi shiru kar ta ƙara cewa komai tayi shiru da bakin ta, da ƙyar dai ta koma ta zauna ammafa bakin nan bazai taɓa yin shiruba taci gaba da kwashewa fulani albarka da zagi da ba'a da cin mutuncin babu wanda batayi mata ko tayi shiru na ƴan mintina zata cigaba daga inda ta tsaya, sudai su mama kansu ya ɗaure sun kasa gane inda maganar gwaggo ta dosa tsabar mamaki ma baisa sun kalli baba ba basu san ma inda yake ba kawaidai sun matsa gaba kaɗan sun zauna suna jiran ƙarin bayani game da wannan maganganun da matar nan take yi musu da basu gane kai da gindin sa ba, saida Ammah ma taƙara bawa gwaggo haƙuri akan tayi shiru su fara magana sannan suka samu tayi shiru, shiru gurin ya ɗauka bakajin motsin komai sai ƙarar Ac dake tashi acikin fadar kowa yayi shiru yaji ta bakin sarki me murabus (papa) saboda  ayanzu dai kusan shine sarki shine mai faɗa aji kowa hukuncin sa yake jira, gyara zama papa yayi tare da bin kowa da ido ɗaya bayan ɗaya kafin yayi gyaran murya zai fara magana Sam ya miƙe tsaye zunbur sannan ya ƙarasa gaban papa ya tsugunna sai yace kaka na nakaina dan Allah ina buƙatar wata alfarma agurin nan kafin afara magana inaso aɗan bani 10 minutes ko 15 wasu zasu ƙaraso nan ina ganin idan dasu maganar sai tafi tafiya yana da ƙyau ayi agaban su dan Allah ayi min wannan alfarmar, duk da halin da papa yake ciki hakan bai hanasa yin murmushi ba sannan ya dafa kan sam yace "SU WAYE SU? Sam yaɗan shafa ƙyeyarsa sannan yace "gaskiya bazan iya faɗar ko SU WAYE SU ba shiyasa nace amin alfarma saboda nafi son kawai ku gansu suna hanya yanzu zasu ƙaraso, wani murmushin papa yaƙara saki sannan yace to babana baka da matsala anyi maka wannan alfarmar ko cewa kayi aɗaga wanann taron sai an ɗaga saboda darajar me sunan ka duk abun da ka nema za ayi maka shi dan haka muna jiran ƙarasuwar su, sosai sam yaji daɗi daman tun zuwan sa yake ta duba wayar sa yana jiran yaji kiransu amma baiji ba gashi kuma yaga ana niyar afara shiyasa ya daure ya nemi alfarma awajen papa yasan daman za ayi masa dan haka yana gurin bai tashiba ya ƙara ciro wayar sa ya danna Number bossay yana ɗagawa yace wai har yanzu baku ƙaraso ba bansan me akace masa ba daga can kawai sai yace "ok kuyi sauri to dan Allah ku kaɗai ake jira daga nan kuma ya kashe wayar sannan ya kalli papa yace sun kusa zuwa, kai kawai papa ya ɗaga masa, gwaggo tace "kai kuma su uban wa kaje ka jajibo mana ince dai masu kama mutane kakirawo masu ladaftar da mutum su koyawa waccen figargiyar hankali dan nasan halinka kaima bada ganan ba akwai iya mugunta duk dade haushin ka nakeji saboda baka da mutunci bakasan shiba kuma akaina rashin mutuncin ka yake ƙarewa saboda ka rainani fiya da kowa agidannan to wallahi bari masu dukan mutanen suzo saina shuna musu kai sun maka duka kaima daga nan sai kadain rainani, hararar ta sam yayi sannan yace "ke matsala ta dake wallahi wataran baki san daidai ba sai ana wata maganar sai kisako wata maganar da ban ai ke Yakamata ma su zane idan sunzo saboda bakinki bashida saiti gigin tsufa yayi miki yawa shiyasa bana zuwa wajen ki dan nasan daf kike da mutuwa kar nazo ki shafa min dan nasan duk wanda yake raɓar ki da yawa kina mutuwa zai mutu ni kuma banshirya mutuwa yanzu ba yanzu ma nazo duniya ke kuma nasan ayanzu ma zaki iya mutuwa domi mutuwa ta ratayu awuyan ki da ita kike yawo duk inda kikaje tana tare dake shiyasa nake gudun haɗa hanya dake, gwaggo da sauri ta miƙe tsaye tare da riƙe  tace "kajimu da ɗan banzan yaro niɗin ce nake yawo da mutuwa to wallahi saidai idan munubiya da Abdallah ne suke yawo da ita dan jakar ubanka kai bakada zance saina mutuwa to duk baƙin cikin ka dani dai nan gani nan bari ɗumaman uwar mayya ba wanda ya isa yakashe ni loƙacina baiyi ba ni nasan duk sai naga gawawwakin ku kafin in mutu duk sai kun tafi kunbarni ɗan baƙin ciki wai ni ubanka me ka tsaya yi aƙasar nan baka koma ba can gurin ya hudawan ba  masu baƙin hali irin ka nifa wallahi bana ƙaunar ganin ka agidan nan yanzu ma bansan kana ciki ba da banzo ba, "to zo ki ɗauken kifitar dani mana idan kina da ƙarfi ko ke kifita daman kin ishemu kin cika mu da surutu bakin ki ko gajiya bayayi sai magana da masifa kamar wacce ta ƙone akai, Hannu ta ɗaga zata makesa yayi saurin tashi daga gurin yana tashi kuma wayar sa tayi kara da sauri yazaro wayar tare da ɗagawa yace kun iso, "ok" bari inzo, fita yayi daga cikin fadar cikin sauri, yana fita yagan su abakin gurin hannun ya miƙawa su bossay suka gaisa sannan yagaida sauran sannan yayi gaba suka shiga binsa abaya sallama yayi yafara shiga sai su shettima da hajiyar sa sai bossay da Ammi da dadda suma atare suka shiga kowa dai kallon su yake da mamaki, bayan sun shiga sai ummy riƙe da hannu Ameesha suka shigo bayan su kuma gimbiya SABREENA da ɗan ta daga baya kuma oga fata fata MEER na take musu baya fuskar nan ya ƙara haɗeta tamau gashi ya wani naɗe hannun riga kamar me shirin yin dambe jira yake kawai yaje ance casss ...... yabada warrrrrr💃💃💃💃💃💃💃                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 94 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                         'bayan sun shiga sai ummy riƙe da hannu Ameesha suka shigo bayan su kuma gimbiya SABREENA da ɗan ta daga baya kuma oga fata fata MEER na take musu baya fuskar nan ya ƙara haɗeta tamau gashi ya wani naɗe hannun riga kamar me shirin yin dambe jira yake kawai yaji ance casss ...... yabada warrrrrr........   :Akusan tare gaba ɗaya ilahirin fadar waɗanda suka san sabreena   suka miƙe tsaye suna kallon cike da mamaki da al'ajabi da ya kusan kashe su da rayuwakan su, kowa yakasa magana saida ƙyar bakunan  wasu ya buɗu ahankali suka fara furta gimbiya sabreena gimbiya sabreena dan sun kasa tantance abun da idanun su sukagane musu suna ganin abun kamar mafarki, wasu kuma da baya da baya suka fara ja saboda tsabar mamaki da rikiɗewar da sukayi abun yazo musu bazato ba tsammani wasu kuma sun tsorata da ganin ta suna ganin kamar ba itabace fatalwar tace, Ammah ma da ƙarfi tace Sabreena kuma kai wannan ba ita bace sabreena da ta daɗe da mutuwa shekarar ta nawa da mutuwa wallahi wannan sai dai inajin aljanune suke son buɗe mana ido da ita amma ni nasan ba itabace tafaɗa tana kallon sabreena kuma tana girgiza kai tare da yin baya da baya kamar zata faɗi idanunta duk sun firfito waje saboda tsabar mamaki da al'ajabi da suka gama kasheta da ranta, fulani kam saida ƴan kusa da ita suka dafeta sannan ta iya tsayawa da ƙafafun ta dan magana ma ta gagare ta sai wani uban gumi da yake tsatstsafo mata ta kowacce gaba dake jikin ta loƙaci ɗaya yagama wanke mata jiki idon kyam akan maama takasa janyewa ga jikin dake faman karkarwar sanyi atake dai wani irin mugun zazzaɓi ya kawo mata ziyara loƙaci ɗaya tare da ciwon kai hannu biyu tasaka ta riƙe kan danjin sa take kamar zai rabe gida biyu yabar jikin ta, papa ne yafara takowa zuwa inda suke jikin sa na karkarwa kamar zai faɗi ya ɗaga hannu sa yana tafiya  nuna ta dashi tafiya kawai yaka Bama yasanin inda yake saka ƙafar sa saidai idan yabiyo ta wajen mutane suyi gaggawar bashi hanya ya wuce bakin sa sai motsi yake yana yayi magana amma maganar taƙi fitowa ya kasa cewa komai, yana daf da zuwa kusa da ita yaja burki ya tsaya sakamakon jin nauyin da ƙafarsa tayi masa, da ƙyar ya iya buɗar bakin sa dake faman karkarwa kamar maijin sanyin sannan ya iya cewa maa..ta..tattt...taga...ri.... yayi maganar cikin in ina da rarraba ta kamar me koyon magana, ganin sa kuma sai yasa take taji idon  ta ya cika da ƙwalla taf ba shiri ta  fara zubar da hawaye take taji zuciyar ta ta karaya batasan loƙacin da wani irin kuka ya taho mataba cikin kukan itama tace "mai martabanaaa....tana faɗa sai kawai ta fashe da wani  kukan tare da ɗaga ƙafar ta da tayi mata wani irin nauyi ta manta ita wace kuma a ina take haka tayi taku da basu wuce uku ba taƙarasa gabansa  tana zuwa daf da shi kawai ta faɗa jikin sa ta rungume sa tana ƙara sakin wani kukan kuka kawai take takasa magana kuma takasa sakin sa, gwaggo dai da tayi suman wucin gadi tayi ba asaniba hakanne ya hanata magana dan tafi kowa tsorata da ganin ta matar da ta mutu me kuma ya dawo da ita indai ba fatalwar tabace ta dawo, dan haka tunanin fatalwar da tayi ne yasata tayi saurin komawa bayan kujerar ta takure waje ɗaya ta ɓuya saboda kar fatalwar ta ganta ta kamata, runtsi idon sa papa yayi tare da ɗagota tabbasa jikin sa ya tabbatar masa da ita ɗince matar shice ta dawo gare sa zuciyar sa tagaya masa haka domin kuwa daman duk acikin matan sa yafi sonta itace wacce ya aura da soyayya kuma haryanzu son da yake mata bai raguba yana nan yanda yake duk da ya tsufa shidaman tun aloƙacin bai yarda ta mutuba dan kusan hauka yayi loƙacin da akace masa ta mutu kuma aka hanasa kallon gawarta saboda maganganun da yake aloƙacin yana cewa bata mutu ba shiyasa aka rirriƙeshi har aka gama komai akakaita ba tare da yaganta ba, yana ɗagota ya kafe ta da ido yana mata kallon ƙirulla itama shi take masa sun tsaya batare da sun ƙara wani ƙwaƙƙwaran motsi ba kuma basu sake yin wata maganar ba,   ganin ana ta ɓata loƙaci kuma batare da amfahimci komai gaba kuma yanayin da suka tsinci kansu bisa ga dukkan alamuma sun manta da mutane agurin kowa yazuba musu ido wasu na jiran ƙarin bayani game da ita waɗanda basu santa ba kenan waɗanda ma suka santan suna jiran suji taya tadawo duniya bayan ta mutu hakanne yasa waziri (Alƙasim ƙanin papa kuma kakan sam) daman shima zuciyar sa adake take bai wani tsorata da ganin taba dan haka sai ya ƙarasa gabansu tare da kamo papa yace "yakamata ka arowa kanka nutsuwa yaya nanfa cike yake da yara da manya kamata yayi ayi abun da yadace a wayarwa da mutane kai dannaga harda masu ɓuya dan tsoron ganin ta amma sai ai gaggawar sanar dasu ainahin abun dake faruwa saboda kowa yana cikin duhu, "juyawa yayi gurin sabreena daman mutuniyar sace dake wayayyene ɗan boko kuma yanada ilimi addini shiyasa bai wani tada hankalin sa kamar kowa ba yasan hakan zata iya faruwa daman duk da yayi mamaki shima amma ba sosai ba kamar na sauran yana da saurin fahimta, na damar sabreena ne tunda tana gidan kallon ta yay sannan yace "gimbiyar mu U are welcome barka da zuwa dafatan kin iso lafiya muna miki fatan alkairi da dawowar ki cikin mu akan gaba loƙacin da ake buƙatar ki lalle wannan babbar ranace tafarin ciki agaremu gabaki ɗayanmu, da kansa yayi musu iso suka zauna sannan ya kalli ƴan cikin fadar da wasu sunfara maganganu ƙasaƙasa fadar na neman rikicewa da surutun wasu dan haka ya ɗan ɗaga murya  yace "pls kowa yayi shiru sannan ku koma gurinku ku zauna sannan ya nuna wani keɓattacen guri aka nunawa su ummy da su dadda suka zauna suma, yazamana kowa yana zaune amma banda shi kunsan me hali baya fasa halin sa yana tsaye inda yake bai motsaba daga inda yake yana kallon kowa dake ciki 1 by 1 yana nazartar su dan a iya yanzu ya riga da yagama selacting ɗin mutane da zai sawa ido dan duk wani wanda ya nuna alamar rashin  gaskiya yagama ware sa gefe  shiyasama ya tsaya saboda yafi ƙara ganin kowa da kyau yakuma bambance su da kamannin su, shidai papa hankalinsa gaba ɗaya yana kan sabreena yakasa ɗauke idon sa akanta bare ma yaga sauran da suka shigo tare, waziri da sai yanzu ya lura da rashin zaman Meer yace, kai yanaga ƙa tsaya anan ka ƙaraso kazauna mana, wani irin kallo Meer ya watsa masa mai kama da harara harara gargaɗi gargaɗi gadai shine ta ƙamaimai dai bansan irin wannan kallon na Meer ba bangane masa ba, sannan ya janye kansa daga gurin sa yaci gaba da abun da yakeyi ya tsaya ƙyam akansu kamar wanda akaturo shi akace yabawa kowa kariya, zaro idon waziri yayi tare da haɗiye yawu  ya karkaɗa kai bai ƙara gigin ƙara yi masa magana ba amma aransa yana jinjina abun da yayi masa ba ƙaramin mamaki abun yabasa ba daga magana sai yayi masa kallon banza, yadai rabu dashi saboda  ko ba afaɗaba bazai wuce ɗayan biyu ba yaron nan da jininsu yake kama tsayuwar da yayi kuma sai tayi masa kama da ta sarakai saboda tsayiwace ta girma wacce kana gani kasan ba raini da sarauta ajikin sa ma'anadai ɗan gidanne shima shi abunma burgesa yayi wani tunanine yafaɗo masa rai sai kawai yasaki murmushi tare da jinjina kai duk dadai baisan kowaye shiba amma dai ransa yabasa wani abu  saurin kawar da maganar yaron yayi aransa sai ya mayar da hankalinsa ga ƴan gurin, kowa da magana abakin sa amma yakasa saboda halin da suka tsinci kansu babu mai walwala ko sukuni acinkin su Ammah bakin ta ya ƙulle takasa magana amma dai ita har ranta iyaka gaskiyar ta bata yarda da cewa sabreena mutun ce ba amma dai tayi shiru taji ko zata yarda nan gaba amma fa ko ta yarda bazata ta taɓa bari ta raɓeta ba dan kallon fatalwa zata koma yi mata, kujerar da ta zauna ma saida ta takure kanta guri ɗaya ga zufa dake zubo mata itama na tsorata da ganin  gimbiya sabreena, shiru fadar ta ɗauka ana sauraron su, ɗayan kanin papa ne yataso yazo kusa dasu shima yana kallon gimbiya sabreena saidai baice komai ba yazauna akusa dasu yana ɗan satar kallon ta tunda ga kan ƙafarta har fuskarta dan duk ya tabbatar wa kansa dai itaɗin ce ba aljana ba, waziri ne yafara magana,  yace "to da farko dai zamu fara godiya ga Ubangijin mu da ya nuna mana wannan rana da bamu taɓa zaton zuwan taba acikin rayuwar mu ko amafarki bamu taɓa tunani zatazo ba sai kuma gashi Allah cikin ikon sa tazo ta riske mu da ranmu bamu mutuba, ɗan dakatawa yayi sannan yaci gaba dacewa, "nasan kowa yana mamakin ganin ta kowa yazata ta mutu tun loƙacin baya daɗewa  sai kuma gashi kunganta da ranta dole kowa ya tsorata to amma inason ku kwantar da hankalin ku wannan ba mai kama da ita bace kuma ba aljanna bace ba kuma fatalwa bace dan naga Hajiya gwaggo abayan kukera to kifito Iran ce dai da kuka sani matar yaya sarki kuma gimbiya sabreena matar sarki zahiri gaskiya kuke gani anan ba mutum mutumi ba wannan ta gaskiyar ce ina fatan kowa zai kwantar da hankalin sa yadawo cikin nutswar sa ,nima bawai banyi mamaki bane ko ban tsorata ba  nayi amma ina da dalilin da yasa nayi saurin ganeta kuma na yarda da ita aɗan ƙanƙanen loƙaci saidai kuma nima bansan ya akai hakan ta faruba saidai mujira jin ta bakin ta ita zata sanar damu abun dake faruwa, maida kallon sa yayi ga gimbiya sabreena sannan yace "to gimbiyar mu muna sauraron ki ko zamu iya sanin abun dake faruwa domin mu anan kinriga da kin mutu tun abaya dan anan akayi miki wanka mu da kanmu mukayi jana'izar ki muka kaiki gidan gaskiya sai kuma gashi mungani ki ba zato ba tsammani nima abun da yasa nasamu damar magana da ƙwarin gwiwa da tabbacin kece tun loƙacin mutuwar taki nagane bakece kika mutuba saidai nayi shirune kawai saboda aloƙacin banda ƙwaƙƙwarar hujja kuma koda na faɗa babu wanda zai taɓa yarda dani daga bayama kuma ni saina manta da zancen gaba ɗaya amma yanzu ganin ki ya tunasar dani komai, amma inason infara jin ta bakin ki kafin in gaya muku abun da nagani ranar mutuwar taki.....shiru yayi yana fuskantar ta yana jiran amsa daga gare ta, shiru tayi tana nazarin maganar sa hasashen ta zai zama gaakiya kenan wani irin baƙin ciki da haushi ne yazo mata wuya ya tokare mata maƙoshi tama kasa magana saidaga baya hawayen da take ta riƙewa saboda kartabari aga rashin dakiyar ta su suka shiga zubowa kan kuncin ta gefen mayafin ta takama tayi saurin goge hawayen sannan murya cikin rauni da taƙaici tace "ban taɓa tunani hakan zata taɓa faruwa dani ba tun barina gidann nan ko ince tun fitar dani da akayi daga cikin gidan nan ni kaina banƙara sanin inda kaina yake ba sai aɗan kwanakin da akayi min magani na warke daga cutar dani ɗin da akayi duk wani abu da yafaru anƙulasa ne daga cikin gidan saida akayi duk abun da akayi aka fitar dani sannan kuma aka sanar muku da mutuwa ta alhalin ina nan da raina duk ma wanda yake tunanin na mutu wanda yasan ya shirya tuggun sa to Allah yafi ƙarfin sa burin sa bai cika ba gani da raina da lafiya ta tare da zuri'ata abun da ba aso agani to gashi an rabamu kuma Allah ya haɗamu....ɗan dakatawa tayi da maganar tare da ƙara goge hawayen dake ƙara tarar mata duk son ta da ta nuna jarumtar ta da dakewar ta hakan ya gagare ta hawaye ne kawai take jin suna taho mata jin zasubo ne yasa tayi saurin dakatawa da maganar da take.... tsullum sai ga gwaggo ta fito daga bayan kujerar da ta ɓuya tazo gaban su kamar wata zararriya haka ta zube agaban sabreena ta riƙo hannun ta sai kuma ta ƙara tashi daga zaunen ta tsugunna tashiga goge mata hawayen........✍️✍️ _Dan Allah kuyi haƙuri da wannan, sannan kuma ka ƙara haƙuri da ni nasan bakwajin daɗin hakan nima kaina ba ason raina nakeson inringayin fashin rana ba naso ƙarahen watannan ingama littafin ma gabaɗaya wallahi amma hakan bata samuba kana takane Allah na tasa abubuwan sai ahankali wallahi,_ sannan ina godiya da addu'o'in ku jikina Alahamdullillh naji sauƙi saida kuma bansamu damar yi muku typing dayawa ba kawai Bama naso yauma yazamana banyi ba shiyasa nayi muku hakan da babu gwanda ba yawa ina me ƙara baku haƙuri dai akan rashin update kullum kuyi haƙuri, kuyi haƙuri, kuyi haƙuri 🙏🙏🙏 nasan ma idan wasu sun idan sun fahimce ni wasu bazasu fahimce ni amma suma suƙara haƙuri...........                                   💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 95 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️                        tsullum sai ga gwaggo ta fito daga bayan kujerar da ta ɓuya tazo gaban su kamar wata zararriya haka ta zube agaban sabreena ta riƙo hannun ta sai kuma ta ƙara tashi daga zaunen ta tsugunna tashiga goge mata hawayen.. tana ta faman tattaɓata da kyua dan taƙara tabbatar wa kanta itaɗin ce, sai kawai itama ta fashe da kuka harda su majina sannan ta koma ƙasa tayi zaman dirshen ta fara cewa "daman nasani nima Saida nace bata mutuba akace min kin mutu shiyasa aka hanani ganin gawarki ai duk wani wanda ke cikin gidan banajin yaga gawarki saidai a lulluɓe  an hana kowa gani ki, miƙewa tsaye taƙarayi  sannan tace gaba da cewa,  "ashe ƙullalliya aka ƙula shiyasa akayi haka tokwa Allah ya kwashewa tanbaɗaɗɗu albarka tsinuwar Allah ta tabbata agare su wannan wane irin mugunta ce ashirya mutum arabasa da iyalin sa da mijin sa kuma ace ya mutu wai wane ɗan iskanne ma yafara sanar mana da mutuwar ta wallahi shi za akama aci uwar uban sa kowaye shi tsinanne marar albarka tana maganar tana ɗaga hannu harda su sakin mayafi  ya faɗi ƙasa masifa kawai take zazzago musu  kamar wanda yayi laifin yana gaban ta sai da ƙyar aka samu aka rarrashe ta ɗan dakata da abun da take cewa, sannan waziri yacewa maama taci gaba da basu labarin abun daya faru da ita, kuma sosai gimbiya sabreena take saboda jin yanda akace ta mutu bayan kuma da ranta hakan ba ƙaramin sosa mata rai yayi ba, saida papa ya rarrasheta sanan tayi shiru ta samu bakin magana amma duk da haka sai tace "abubuwa da dama sun faru waɗanda ni kaina ban san faruwar su ba  saidai zan wakilta wanda zai baku labarin abun dake faruwa tunda barina gidan, ummy ta kalla sannan tace ga wacce suka tsince ni itace zata baku labarin abun da tasani kowa maida kallon da hankalinsa yayi kan ummy da maama ta nuna musu, daga inda take ummy ta fara basu labarin ta yanda suka haɗu da ita tun loƙacin da aka kawo su asibitin su da abun da waɗanda suka kawota sukace nandai ta kwashe komai tagaya musu har zuwa loƙacin da tadawo cikin hankalin ta bayan malam yayi mata magani saidai bata gaya musu alaƙara dake tsakanin su ba na ɗa da uwa harda jika kawai ta tsaya musu zuwa inda suka baro garin abuja suka dawo kano suka kama gida anan ta tsaya da basu labarin tace ga iya abun da nasani yanzu wannan baiwar Allahn zata cigaba da baku labarin ta nuna musu dadda, gyara zamanta dadda tayi sannan itama ta shiga basu labarin abun da tasani tunda ga loƙacin da aka bugeta a motar har baba yakai ɗanta gidan suka ci gaba da riƙesa hardai zuwa giraman sa da kuma waɗanda suka kawo masa farmaki............komaidai tagaya musu da yanda suka haɗu da su sam har suka fara taimaka mata akan zasu fara bincike sai kuma ga su maama sunzo suma loƙacin da Ameesha ta ɓata sai ta faɗa hannun ɗansu ya taimake ta daga maama ta gane cewar jikarta ce......., itama kuma bata gaya musu cewar Abu ɗan maama bane tadai sanar dasu Ameesha jikarta ce kuma ɗanta ma ana sa ran yana raye saidai ba a san inda yake ba abun da ake ƙoƙarin ganowa kenan tun kafin ma zuwan su Sameer Allah kuma baiyi ba sai yanzu da Allah yayi wannan haɗin cikin ikonsa na haɗasu guri ɗaya har sukazo nan yanzu suke bada labarin abun da yafaru,, Kalamar inna lillahi wa inna lillahi raji'un kawai papa yake iya faɗa saboda ba ƙaramin shock ya shiga ba jin yanda ahalin sa suka kasance cikin ƙunci da wahalar rayuwa suna raye awani wajen batare da sanin saba, bashi kaɗai ba gaba ɗaya ilahirin gurin babu wanda bai jinjinawa faruwar wannan abun ba kowa cike yake da ɗunbum mamaki tunda suke atarihin masarauta ba ataɓa aikata abu makamancin haka ba ba ataɓa mugunta irin wannan ba babu matar da aka taɓa yiwa irin wannan cin zalinci aka koreta daga gidan sarauta duk dade daman gidan sarauta yagaji irin waɗannan makirce makircen na asiri da makamancin su amma dai ba ataɓa aikata irin hakan ba, hayaniya gurin ya ɗauka wasu na sharar hawaye wasu kuma na zufa saboda yanda hankalin su ya tashi da bayyanar ta wasu kuma na farin cikin wasu na baƙin ciki wasu kuma nayin nadama wasu kuma suna ƙara wani tunanin aransu yanda zasu ƙara tarwatsasu dan bazasu bari farin ciki yaci gaba da zama agurin su ahaka suke so su ƙare rayuwar dan haka dole su ƙarayin wani ƙyaƙƙyawan shirin akansu dan bazasu taɓa lamuntar zaman su aciki gidan fa duk da sun tsorata amma hakan baisa sun karaya ba sun saduda ba saima wani tunanin ma suke daban, papa ne da idon sa yakaɗa yayi ja dashi saboda tsabar baƙin cikin da ya tsinci kansa ya kamo gimbiya dake kusa dashi yashiga bata haƙuri kamar shi yayi mata laifin, shi sai yanzu ma da aka bada labarin ya tuna ashe harda ɗa loƙacin da ta mutu tunawa yayi bai wanda yayi zancen ɗan tunda ta mutu kuma itama kanta aka manta da zancen ta bare kuma ɗanta kwata kwata babu wanda yayi zancen Sameer sai yanzu da aka bada labari kowa yatuna dashi anmantar dasu gaba ɗaya sai yanzu tunanin wasu yadawo,   gwaggo cikin share ƴar ƙwallarta ta matso kusa da ita tace "Allah yasaka muku duk wanda yayi miki wannan mugunta Allah yasaka muku gaba ɗayan ku Allah ya toni asiri tsinannu wallahi duk wanda aka kama da sa hannu sa aciki Ni da kaina zan binne sa da ransa bayan angasa masa azaba in Allah ya yarda Duk dai an kama maku mugaye tsinannu waɗanda basu da imani shine bayan kunfitar da ita daga gidan hakan bai ishekuba shine kuka bi ta bayanta kuka bugeta da mota sannan kuka rabata da ɗanta shima baku barsaba kukabishi kuke azabatar dashi da ƴarsa saboda tsabar mugunta da ha'inci da son zuciya irin naku maitayi muku mai tsare muku tunda muke da sabreena bantaɓa jin kanta da wani ba kowa nata ne tana mutunta mutane kukayi mata haka dan cin amanar zama ko dan saboda kunga ɗanta shine sarki to ai bata ɓaci ba asirin ku zai tonu kuma gashi Allah ya nuna muku ishararku gasu sun dawo sai kukashe kanku dan baƙin ciki, kallon ta tamayar kan Ammah da fulani sannan tace wallahi wannan mugun zama irin naku ai ba wani ɓoye ɓoye ko rufa rufa da za a ɓata loƙacin gurin gano wanda ya koreta dole acikin kune dan haka wallahi ku za akama musamman ke ɗin nan ta nuna fulani sannan tace "ko rantsuwa ma nayi bazataci ni ba wallahi ni nasan kece ummul aba isin faruwar komai tunda gashi kinkawo mana wani ɗan kince nakine anɗau sarauta ambasa saboda ke baƙya haihuwa shiyasa kika kori mai haihuwar kika kawo wani daban akan cewar ɗankine saboda tsabar ƙwarewa da son kai da mugun ta to wallahi zakici ƙundugurin buhun ubanki sai an karkarya ki gunduwa gunduwa anbawa karnuka suncinye ki ahaka dan nasan ƙasama bazata karɓeki ba saboda mugun halinki shegiya ƴar kutumar uba mai kama tukunyar giya 🤣(oh ni ƴasu daman a tukunya ake dafa giya) tana faɗa ta ɗaga ƙafa zatayi kanta aka riƙota da daga abun da take shirin yi dan sunan idan suka sake ta sai ta kusa kaita lahira alhalin ba a tabbatar ba da zargin da take mata ba dan ahalin da suka ganta sunan halin ta zata iya aikata komai ma dan gwaggo haka take akwai zuciya bata iya fushiba idan ranta ya ɓaci bata ji bata gani tun ƙuruciyar tama idan abu ya haɗasu da wani to idan bata ganta akanka tana maka mugun duka to bata samun nutsuwa har saitaga ta ladaftar dakai da duka gata da ƙarfi kamar me aljanu haka take komawa idan tana dukan mutum shiyasa haryanzu halinta na nan ba raguba ba saima ƙaruwa da yayi ga faɗa kuma ga tsufa sai abun yake neman fin nada kunsan mutum ko baida faɗa idan ya tsufa sai kuga ya canza hali abu kaɗan zakayi masa ya hauka da masifa da bala'i duk kusan tsofaffi haka suke da zarar sun tsufa, bare kuma ita da daman can mafaɗaciyar ce ga tsufa kuma shiyasa abun yayi worse da yawa idan ranta ya ɓaci bata iya controling ɗin kanta saita koma kamar wata zararriya, abun har mamaki yake bawa mutane yanda take adore ƙashin ta da ƙwari har yanzu dan idan ta ɗaga hannu ta makama sai kaji ajikin ka ƙarfi gare ta kamar doki shiyasa har yanzu da sauranta bai gama tafiya ba, Ammah nason yin magana amma takasa saboda tsoron gwaggo da yakamata tana tsoron tayi magana gwaggon ta dawo kanta dan haka ta ƙara jan jiki  ta takure gefe guda aƙasan kujerar san zaman kan kujerar ma ya gagareta tunda akace acikin su biyu sai sun fito da wanda ya koreta ta tsure dan bataso zargi yazo kanta dan tasan zasu iya wahalar da ita idan suka fara zarginta dole ko mai zasu ce bazasu yardaba kuma tasan Fulani ko da ita tayi bazata amsa ba nan kusa saitasa an wahalar dasu itakam ina zata tsoma ranta wannan tunanin ne yasata rawar jiki ta sauko daga kan kujerar ta koma ƙasa can lungu lungu ta zauna ta kama kanta guri ɗaya...., nandai aka samu aka lallaɓa gwaggo tayi shiru ta zauna sannan akadai cigaba da tattaunawa akan matsalar inda papa yake cewa ayanzu dai baza a zargi kowa daga cikiba saidai za afara bincike ne har a tabbatar kuma ta inda za afara doke a fito da wanda ya sanar da mutuwar ta ranar da akace ta mutu idan akayi haka tanan za agano ko waye saboda duk wanda ya fara sanar da mutuwar ta dole shine tunda Saida yayi yanda zaiyi ta fice daga gidan sannan aka sanar ta mutu saboda kar ayi wani bincike shiyasa aka rufe musu baki da cewar ta mutu dan kar kowa yaƙara yin maganar saboda, waziri ne yace "wannan maganar taka gaskiya ce yana da kyau afara da binciken kafin azargi wani saboda zargi bashi da kyau bamusan ta ƙamaimai mai waye da sa hannu acikiba dole sai anfara bincike dan akama mutum da hujja yanzu sai muyi tunanin wanda yasanar da mutuwar ta yanda za ayi mugano shine kowa zai tuna wanda yagaya masa shima sa a tambaye sa waye yagaya masa kunga dagana dole za aje ƙarshen inda maganar ta fito sai mukama koma waye.......,amma yakuka ce da shawarata? kowa na'am yayi da shawarar da yabayar kuma wasu har sun fara tunanin wanda yasanar da su ɗin Saida babu wanda ya fito ya faɗa saboda ba abada damar faɗan ba, surutunne ya ƙara yawa kowa da abun da yake fitowa daga bakinsa  sai hayaniya ta nemi ta kaure aciki akayi saurin dakatar dasu......    da ƙyar aka dakatar dasu daga hayaniyar da suke sannan kafin wani ya ƙara cewa wani abun gimbiya ta miƙe cike da ƙasaita dan ta tuna baya takun da take na matar sarki gimbiya shi tafara yi yanzu saida taga kowa yaɗan nutsu tashiga binsu da ido tana kallon kowa da kyau sannan ta maida kallon gun Meer dake tsaye har yanzu sai ta taka taje har gaban sa sannan ta kamo hannu sa baimata musu ba ya shiga binta sai da taje gaban papa sannan ta sakesa sai ta koma gun da Ameesha take itama ta taso da ita takawo ta gaban papa da hannu tayiwa Abu alama da yazo dan haka yataso cikin rashin ƙwarin jiki dan shifa har yanzu yakasa yarda da abun dake faruwa jin abun yake kamar amafar ki da sanyayyen jiki ya ƙaraso inda suke ya tsaya, maida duban ta tayi ga papa da ya kafesu da ido yana ta kallon su kamar yasamu T.V yasaki baki kawai, nuna masa abu tayi sannan tace "mai martaba dawa wanann yayi maka kama inaso ka faɗa da kanka basai anfaɗa maka ba, kallon ta papa yake cike da rashin fahimtar maganar da take sai kawai ya maida duban sa ga Abu ya kallesa sosai sai ya janye daga kallon sa yamayar kan maama sannan ya shiga girgiza mata kai tare dacewa bansani ba, kallon sa tayi tace "yakamata dai kagane dan idan nafaɗa bashi ba kai ka yarda? kai ya girgiza sannan yace "a'a, Meer ta nuna masa tace wannan ba shifa dawa yake kama nan ma cemata yayi bai sani ba cike da ƙaguwar jin ko SU WAYE SU  aransa yana fatan Allah yasa su kasance jinin sa duk dadai alabarin da aka bayar ba afaɗi wani abu da yashafesu ba, shiru tayi tana kallon sa taso yagano da kansa saidai daman da kamar wuya da ace dai babu gemu a fuskar Abu tasan zai ganesa gashin da ya rufe masa fuska ne yasa kamannin sa canzawa gaba ɗaya itama da bata gansa a hoton nan ba zai wuya ta gane sa loƙaci ɗaya, da fuskarta ba aɗan sake ba yabo ba fallasa ba fus as ta saketa loƙacin da take masa magana amma yanzu kuma sai ta ƙara canzata ta koma ta kala tare da shiga tsakanin Abu da Meer ta riƙo hannun ko wannen su sannan ya kalli kowa dake falon cike da dakiya tafara magana, duk alabarin da akabaku nasan bakuji wanda zai firgita kuba maƙiya yo ta Allah bataku ba yau gani da gudan jinina wanda kuka rabani dashi tun yana yaro yau gashi agaban ku harma da ɗa wannan da kuke ganin sa ɗana ne SAMEER yaron da na fara haifa aka sace min acikin gidan nan to gashi yau ya shigo gidan ubansa da ƙafar sa anfita dashi loƙacin da baisan shi waye ba yanzu kuma yadawo adaidai loƙacin da baku taɓa zato haka ba wannan kuma ɗansane kuma jika agare ni ɗaya tamkar da dubu dan kufara kuka da kanku kodashi kaɗai na barku ya isa ya tarwatsa kwakwalwar ku baki ɗaya ni kuka cuta kuka zalinta kuka musgunawa rayuwata tsawon loƙaci ina kwance batare da nasan inda kaina yake ba batare da naga koda mutum ɗayane da sunan naga mutum kuma nasansa ina ganin mutane tamkar dodanni bana bambamce baƙi da fari ni kaina bansan ko ni mutum ce ko ba ita bace kun mantar dani komai kunjuyar min da hankali na kun rabani da ƴaƴan kun rabani da mijina kun rabani da ƴan uwana saboda son zuciya irin taku to kusani bani zan rama abun da kukayi min ba kuma ba ɗana ne zai rama ba jikanane zai ɗaukar min fansa akanku sai nasa yayi rugu rugu daku sai rama min abun da kukayi min fiye da kallar abun da kukayi min sai yaga bayan ko wannen ku dan bazan taɓa yafewa kowanne kuba dan haifi wanda ya haifi wanda zai iya da kowannen ku babu wanda zai ƙale dan haka kukuka da kanku tun kafin kuyi arangama dashi ina gefe ina kallo hankalina kwance zaiyi duk abun da ya dace, kuma sarautar da bakuso suyi dole suyi da yardar Allah zuri'atace zatai ta yaɗuwa dagana ha ƙarshen rayuwakan mu baki ɗaya jinin zaicigaba da zama a sarauta duk wanda kuma ya ƙara gigin shiga abin da banasaba Allah ya tarwatsa rayuwar sa ko waye shi, tunda ta fara magana kowa ya sha jinin jikin sa tabbas tunda aka bada labari babu abun da yafi ɗagawa wasu hankali kamar wannan maganar tata ɗanta na farko da ransa bai mutuba gashi harda ɗa shima namiji ga kuma wancen ɗan nata da bai fito ba shima namiji dole kwa sarauta ta dawo hannun su gaba ɗaya kamar yanda tace, daga cikinsu babu wanda yayi yunkurin yin wata magana saboda tsoro da furgici da suka tsinci kansu fiye da na ɗazu, papa da gwaggo suman zaune sukayi saboda tsabar mamaki sunma kasa motsawa saida ƙyar gwaggo taje ta gaban Abu tana kallon sa kamar tasamu T.V sai ta kallesa sai ta kalli maama da ƙyar dai ta iya cewa dan Allah wai maganar da nakeji kina faɗa gaskiya ce kodai kunnu wanane suka jiyo saɓanin abun da kike faɗi jinayi fa kince kamar wannan ɗankine Sameer, Sameer dai wanda kika haifa aka sace shi, shine yanzu agabana nake kallon sa ko kuma dai ƙarya kunnuwa na suke faɗa min, maama ce ta kamo hannuta cike da kulawa tace gwaggo ba ƙarya kunnu wanki suke miki ba abun da kikaji gaskiya ne kuma zahiri ne ba mafarki ba ki kalle sa da kyau jikanki ne, nandai itama tabasu labarin ta yanda ta ganesa da kuma halayyar Meer da ta zama iri ɗaya da ta gwaggo harma kamannin su da suke shigen kama, hannu gwaggo tashiga tafawa tana sallallami akan wannan lamarin da abun yagama kasheta da mamaki daga wannan sai wancen komai sai faruwa yake loƙaci loƙacin da basu taɓa tunanin wannan ranar zatazo itakam wane irin farin ciki zatayi na wannan ranar da ta zamemata babbar rana, rana ta musamman, papa ma tasowa yayi yana ƙara kallon Abu yaudai Abu yazama abun kallo agun family ɗin sa, hannu papa ya buɗa masa suka rungume juna papa yana ta faman sakin murmushi sosai ya nuna farin cikin ganin ɗan nasa da yagama fitar da rai akansa sai gashi yau Allah ya dawo masa dashi kana ganin sa zaka fahimci tsantsar farin cikin da yake ciki marar misaltuwa, daga nan papa yasaki Abu ya koma wajen Meer da yayi wani kicin kicin da fuska kamar baya farin ciki da dangin mahaifin nasa rungume shi yayi shima yana ɗan tsokanar sa na kaka da jika sannan ya sake shi shima sai yakamo hannun Ameesha itama ya nuna farin cikin ganinta da tausaya mata yanda tasha wahala a rayuwar ta, gwaggo ma cike da farin cikin ta shiga rungume su tana share ƙwallar farin ciki da ta tarar mata saidai tana zuwa kan Meer zata rungume sa yayi saurin matsawa daga kusa da ita tsayawa tayi da mamaki tana kallon sa, maama ta ɗanyi murmushi sannan tace bazakaje gurin gwaggon taka ba gwaggo ai tun kan muzo ma nake bashi labarin ki saboda halin ku ɗaya ba inda ya barki kaje mana ka matsa itace gwaggon da nake gaya maka mai kamar ka tayi maganar tana ɗan turasa wajen gwaggo, gwaggo daɗi ya ishe ta ance suna kama kuma halin su ɗaya cike da ƙara wage baki ta ƙara nufar wajen sa zata taɓasa ya ƙara matsawa fuska a haɗe yace ni karki taɓani kin tsofa da yawa mai kike jira baki mutu ba, yanayin maganar ya maida bakin sa yanda yake sai ka rantse ma bashi yayi ba, kasaƙe gwaggo tayi tana kallon sa kafin daga baya maganar ta ƙara tsaya mata arai aranta tace da ina yabonka sallah zaka kasa alwala ashe baza muje dakai ba, a fili kuma sai ta kalle sa tace "ubanka nake jira yazo sai mumutu tare marar mutunci daga yimaka abun arziƙi shine zaka gaya min magana to ahir ɗinka harda wani cewa wai mai nake jira dake daman ni zankashe kaina kenan to Allah baiyi zan mutun ba kuma babu wanda ya isa ya kasheni loƙaci na baiyi ba tafaɗa tare da buga tsaki harda su harara, ko kallon inda take baiyi ba bare yasa ran zai kulata haka tagama bambamin ta ita kaɗai su maama nayi mata dariya, saida suka gama nunawa kansu farin ciki sannan kowa ya koma ya zauna dan aƙarasa maganar saida suka samu nutsuwa sannan papa ya gyara zama ya ƙara yiwa Allah godiya da bayyanar ahalin sa sannan suma su maama yabasu labarin abun da ya faru na halin fulani duk abun da ya faru tundaga A har Z yabasu labari, sannan ya ɗora da cewa Maryama muna sauraron ki muna buƙatar ƙarin bayani daga gare ki, ki matso kiyiwa kowa bayanin yanda hakan ta faru batare da sanin kowa ba kika yaudareni da ɗan da banaki ba koma ince kika yaudari duka masarauta, shiru gurin yayi ba wanda yayi magana Fulani kam ta sunkuyar da kanta ta kasa ɗagowa ta haɗa ido da kowa duk da idanun su nakanta suna jiran jin ta bakin ta, saida papa yaƙara yi mata magana cikin daka mata tsawa sannan tayi saurin ɗagowa da jajayen idon ta da suke ta zubar da hawaye ajere ajere ta kalle sa tare da kawar da kanta gefe saida ta ƙara ɗaukan loƙaci..., sannan ta rarrafo jiki ba ƙwari tazo gabansu saikawai ta fashe da wani kukan me sauti kowa cigaba yayi da kallon ta ganin taƙin yin shiru yasa Meer cewa Kee... kishiga hankalinki kin ishemu da haukan kuka in ba hakaba wallahi zanyi ball dakeeee... yayi maganar cikin daka mata wata gigitaciyar tsawa da saida fadar ta amsa gaba ɗaya wasu daga cikima da badasu akayi wa saida suka firgita bare kuma wacce akayi wa ai saura kaɗan ta sakin fitsari agun, ba shiri kuwa ta buɗi baki tafara magana....., "dan Allah kuyi haƙuri ku yafemin wallahi sharrin sheɗanne duk yasa na aikata hakan ba bada son raina ba ina mai baku haƙuri abisa cin amanar ku danayi amma wallahi wallahi bansan komai ba game da fitar gimbiya sabreena ba babu saka hannun aciki kamar yanda kuke tuhumata wallahi bani nace yanzu zan faɗi duk wani abu da nasan na taɓa aikatawa, shiru tayi na ƴan mituna sannan ta cigaba da cewa, "tabbas wannan ɗa da nake dashi bani na haifeshi ba kamar yanda hajiya sarah tafaɗa muku haka zancen yake, shekarun baya tun kafin gimbiya sabreena tabar gidan Hajiya sarah tazo min da wannan maganar daman ƙawatace tun kafin inyi aure maƙociyar muce muna shiri da ita, to bayan nayi aure ma tana yawan zuwa gidana ranar wata lahadi tazo gidana sai tace mushiga ɗaki tana da wata shawara da zata ban muna shiga tafara tuntuɓata akan rashin haihuwata nace mata nima abun yana damuna gashi munje wajen likita ance bazan taɓa haihuwa ba shine tace yanzu hakannan zan zauna bani da ɗa babu abun da zan samu idan sarki ya mutu shine tace to wallahi in tashi tsaye insan abunyi dan idan na zauna kallon kwaɗo zai miki ƙafa ga wata shawara da zan baki kiyi tunani akai ta hakan kawai zakibi kisamu wani abun koda bayan ran sarki, gyara zama nayi nace ina jinta tagaya min shine take cemin mai zai hana muje wajen malami yabani abun da zaisa kowa yaga ciki ajikina alhalin babu shi kawai za arufewa kowa ido yaringa ganin ciki ajikina har zuwa loƙacin da watan haihuwar zaiyi sai muje asibiti sai abiya likitocin kuɗi subamu wani ɗan sai anunuwa kowa cewar na haihu kuma yaron koda yayi wani kammanin da ban babu wanda zaiga hakan babu mecewa komai akai , da farko ƙin amincewa nayi haka taita jan ra"ayina har na amince washe gari mukaje wajen malam babu ɓata loƙaci muka gaya masa buƙatar mu nanda nan yabamu magungunan da zamuyi amfa ni dashi sannan yaban wata ƙwarya yace aɗakina akwai wani guri da yake kamar ɗaki inje insan yanda zanyi inyi haƙa in zura ƙwaryar akai sannan yaban wasu jajayen kaya yace kullum idan na tashi inshiga ciki inyi fitsari akai sannan duk sati idan zan shiga gurin in tafi da dubu ɗari in ajiye agun sannaan in fito, nace har sati nawa zanyi ina ajiye kuɗin agun yace haka zantayi har ƙarshen rayuwata nace masa a ina zan ringa samun kuɗin Ni da ba sana'a nake ba kuɗin gurina kuma ko shekara ɗaya bazaikai ba sai yace min kar in damu da wannan akwai inda mijina yake ajiye kuɗin sa aɗakina dan haka daga nawa sun ƙare inci gaba da ɗaukan nasa ina ajiyewa konawa na ɗauka bazai taɓa ganewa ba kuma ya sheda min inda nayi hakan ɗan da zan haifama zai iya kasancewa shine sarki idan mijina ya sauka shi zaibawa sarautar dan haka sarauta zata dawo hannun sai yanda nayi da kowa duk abun da nafaɗa shi za ayi, nikuma wannan zancen da yayi na sarautar zata dawo hannun gaba ɗaya yasa nayi saurin amince masa zanyi duk abun da yakeso daga nan nabiyasa kuɗin da yake buƙata aloƙacin sannan yayi mana bayanin duk yanda zamuyi komai muka baro gurin sa muka dawo gida tundaga nan kuma nafara duk abun da yace min inyi ba daɗewa kwa na sanar da sarki ina da ciki tun baifito ba mukaje wajen likita aka dubani aka tabbatar wa da sarki eh ina ɗauke da ciki wata ɗaya muka dawo gida aka sanar da kowa nan da nan aka fara tayani murna loƙacin kuma da nake da cikin gimbiya sabreena har ta haifi ɗan ta sameer kuma Ammah ma ta haifi ƴan biyun ta mata ni duk danaga gimbiya ta haifi namiji banji cewar wai ɗan ta zai iya zama sarki ba bare har inyi tunanin koren ta daga gidan, tunda malam yasanar min na yarda dashi ana haka kuma tun kafin in haihu muka wayi gari babu gimbiya ba ɗanta aka neme ta aka rasa, nikuma bayan watan haihuwa na yacika Hajiya sarah tazo mukaje asibiti tun kafinma muje tace angama komai tayi magana da likitan da zaibamu wani ɗan haka muka shirya komai kamar haihuwar gaske muka tafi asibitin mu biyu nandai tasan cuku cuku ɗin da tayi ta samo yaron ta kawo min shi ina zaune awani ɗaki dan bansan ma ta yanda ta samo shi ba anan muka sanar da dangi da ƴan uwa cewar na haihu ga mamakina sai naga abun da malam yace ya tabbata dan yaron kwara kwata baya kama da kowa amma babu wanda ya iya cewa wani abu game dashi har muka dawo gida akayi suna aka saka masa SALAHUDDEEN..., bayan girman sa kuma da sarki zaiyi murabus akace shi za aɗora akan karagar mulki ranar har kyuata nayiwa Hajiya sarah da malamin saboda farin ciki, har ranar naɗasa akai tayi aka basa sarauta Saida abun da bansani ba shine tunda ya hau sau halayen mu daga shi har ni suka sauya kawai sai jnringajin zuciyata na ingizani ina yawan samun kaina cikin ɓacin rai daga bayama sai kawai Masarautar ta sauya min gaba ɗaya aka dawo cutar mutane da zalintar su wasu basuji ba basugani ba haka zansa ayiwa mutum hukunci fiye da laifin da ya aikata ni kaina abun yana damuna idan na zauna ina tunani ammafa maimakon inji abun yaragu saima inji ƙaruwar sa araina har takamam hakannan mutum baiyi laifi ba hukunta shi daga bayama har zubar da jini nasa aka farayi amma ni bazan taɓa hukunta mutum da hannun naba saidai insa ayi idan akayi kuma zuwa dare sai abun yafara damuna amma zuwa safiya zan cigaba da abun da nake bana saurarawa kowa ko shi mijin nawa sai abun da nace masa yakeyi idan ya kwatanta yimin magana akan abun da nake ba daidai bane sai raina yaɓaci kuma shima sai inga yakwanta yakama bacci sannan nake jin daɗi har zuwa yanzu da asirina ya tonu amma wallahi wallahi iyaka abun da nasan nayi kenan banda saka hannun wajen cutar das.........,bata ƙara sa maganar ba taji tasssss taji saukar mari afuskar ta bata gama tantance zafin ba aka ƙara mata wani ta ɗayan ɓarin bai dakata ba saida yayi mata wajen mari biyar ajere sanann su waziri suka tashi suna rirriƙesa da hannu ya nunata cikin ɓacin rai yashiga nunata da yatsa cikin ɗaga murya yace ƙarya take mu zata rainawa hankali kusake ni in ɓaɓɓalla ta mai yasa zaku tsaya kunajin wannan banzan labarin ƙaryar kusake ni inyi nece yafaɗa yana ɗaga musu murya sama tare da yin watsi dasu ya ƙwace daga riƙon da sukayi masa cikin zafin nama yaƙara nufar inda take, a zafaffe cikin zafin nama shima Abu ya miƙe tsaye tare da ɗaga murya da ƙarfi yace "MEER.......!!!!!!                       '                      💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 96 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️      'Cak meer yaja burki yatsaya baiƙarasa  gurin taba sakamakon tsawar da Abu yayi masa hakan yasan yashi dakatawa bai ƙarasaba, maama ce ta taso ta matso kusa dashi tare da kamo hannun sa tajasa ta zaunar dashi kusa da ita tace "ya isa haka kowa ya zauna, sannan sauran ma da suka tashi tsaye suka koma suka  zauna papa dai yana gurin sa azaune ko motsawa baiyi ba, shiru gurin yaƙara ɗauka sannan gwaggo tace "nimadai bazan taɓa yarda bake bace tunda har kika  iya aikata haka babu abun da baza ki iya aikatawa ba bazamu yarda da wannan ƙazon kuregen labarin ba ke kika fitar da ita dan haka dole kifito kigaya mana ta yanda kika koreta daga gidan yanda kika faɗi wannan shima haka mujeso kigaya mana ki amsa laifinki tunwuri kar ki wahalar da mu da ki wahalar da kanki, duk yanda akaso fulani ta amsa laifin ƙin amsa tayi dan haka dole aka rabu da ita, sannan aka dawo kan Hajiya Sarah itama tazo tayi bayanin abun da yafaru yanda dai fulani ta faɗa bata ƙarya ta ko magana ɗaya ba, aka tambaye ta dalilin yin hakan tace sharrin sheɗanne ayi haƙuri a yafemata, atake aloƙacin papa yasa aka yanke musu hukunci gaba ɗayan su, yace akaisu ɗakin ƙasa aƙulle baci ba sha kuma baza afito dasu ba har sai angama binciko kowaye yayi sanadin barin gimbiya gidan, daga nan papa ya kira baba da mama da kuma sabon ɗansu da basusan dashi ba aka haɗasu aka basu haƙuri, ba ƙaramin kuka mama tasha ba jin yanda abun ya kasance aka rabata da ɗan ta batare da sanin taba yarda wane irin yana yi zata kasance shin zatayi farin cikine ko kuma baƙin ciki takasa tantance halin da take ciki babama dai saida ya zubda ƙwalla ahaka dai aka cigaba da rarrashin su da basu baki har sukayi haƙuri suka fawwalawa Allah suka karɓi ɗan su shima duk juriyar sa saida yayi kuka idan ya tuna irin zalinci da yasa akayiwa mahaifinsa shikam duk da arashin sanine yana jin bazai taɓa yafewa kansa ba akan wannan laifin da ya aikata da kansa yasa aka ringa azabatar da mahaifinsa harda ƙanwar sa ma da suka fito ciki ɗaya da ita yasa ancutar dasu cikin kukan da bai taɓa yiba tunda yake ya tsugunna har ƙasa ya bawa baba haƙuri tare da neman yafiyar sa saida ya ɗauki loƙaci mai yawa yana basu haƙuri har saida baba ya dakatar dashi tare da cewa ya yafe masa suniya da lahira yasan ai arashin sani yayi hakan shi kansa da ace yasani bazai taɓa aikata hakan ba dan haka yadain ganin kansa amai laifi, maama ce ta fara magana tare da ƙara basu haƙuri abisa cutar dasu ɗin da akayi aka rabasu da ɗan su da kuma abun da akayiwa baba suma suka nemi da su faɗi hukuncin da suke so ayiwa su fulani, ana tambayar su sukace su babu wani abu da zasuce ayi mata taje ita da Allah Allah ya saka musu, papa ya ɗora da cewa inason duk abun da kuke so kufaɗa tare da yi musu alƙawarin kulawar su ta dawo hannun su sannan kuma shi sarki Salahudden zaici gaba da zama agidan dan ya riga da yazama ɗan gida baza ataɓa korar sa ba saidai kawai yaga ma tashi daga matsayin sarki zai koma daidai da kowa part ɗin sama yana nan amatsayin nasa ba yaje yaci gaba da zama acan, fafur Salahudden yabasu haƙuri yace shi bazai iya zama anan ba subarshi kawai ya koma wajen iyayen sa suci gaba da zama tare, da ƙyar aka bashi baki akace yayi haƙuri ya zauna domin zaicigaba da zama amatsayin ɗa agidan idan yace zaitafi kamar ya watsa musu ƙasa a idone, nan ma dai ƙin Amincewa yayi saida maama ta saka baki amaganar sannan tace tana roƙon papa da tana so suma su dawo nan da zama sai aware musu part ɗin su sai yaringa ganin su kullum idan hakan yayi masa saidai ina suma su baba ƙin amincewa sukayi saidai sun saka baki akan sun yarda shi yaci gaba da zama anan ɗin in yaso yaringa zuwa can inda suke, da ƙyar dai akasamu ya amince shima saboda iyayen sa, saboda yanaso yafara yi musu biyayya tunda har suka nuna suna son ya zauna ɗin zaizauna kawai saboda su ammafa kusan kullum yana tare dasu acan bacci ne kawai zai ringa shigowa dashi gidan abun da yabarwa zuciyar sa kenan, ataƙaice👌........ daga nan aka gama duk wani abu da za'ayi mai magana yayi magana su fulani kuma aka fita dasu amma saida ƙyar dan meer bai barta hakannan ba saida yasan yanda zaiyi yayi mata wani dukan gwaggo ma ta ƙara da nata ba ita kaɗai bana har hajiya Sarah itama saida ta samu nata kason na dukan sannan aka kwace su da ƙyar aka fita dasu daga fadar, nan dai guri ya kacame da surutu kowa na fitar da abun dake bakin sa ga ɗan uwansa, can na hango su saleem da shettiman da bossay da kuma sam suma suna tattaunawa akan yanda wannan abun yakasance tare da jajantawa saleem bisa abun da akayiwa mahaifinsa da taya sa murnar samun yaya, Azeema ma suna tare da Ameesha suna taya juna murna, Hajiya dadda ma har tasaki jikin ta itama akan farko da gaba ɗaya tayi shiru kamar babu ita agun saboda jikin ta ba ƙaramin sanyi yayi ba da jin labarin nan da taga yafi ƙarfin kanta, sannan ta shiga taya jikarta murna da bayyanar ahalin ta har ƙwalla ta zubar na farin ciki da kuma ta tuna da mijin ta Malama da ƴarta da tamutu da Sameer da ta ɗaukesa tamkar ɗan cikin ta saitaji jikin ta yakuma yin sanyi, su ummy ma baki har kunne idan ta kalle ta taga wai yau itace cikin dangin mijin ta abun yana mata daɗi Musamman idan ta tuna zataje ƙasarta ta ta nunawa mahaifin ta dangin mijin ta kamar yanda yayi fushi da ita yace har sai ta kawo su to yanzu loƙaci yayi zasu shirya da mahaifin ta loƙacin da zata ringa nufar gidan su koda yaushe batare da taji farga bar haɗuwa da mahaifin ta ba gaskiya yau ta tsinci kanta cikin farin cikin da ta daɗe batayi irin saba, su Hajiyar shettiman ma da su Ammi kowa yayi mamaki yanda komai yakasance haka da kuma taya su farin cikin haɗuwa da junan su....., hakadai kowa yayi abun da yakeso agun anataya juna farin ciki wasu kuma baƙin ciki kowadai da kalar yanda ya fahimci maganganun wasu kuma hukuncin da akayiwa su fulani baiyi musu ba sam wasu kuma basuji daɗi ba masoyan ta kenan, Allah sarki bawan Allah hamza da babu wanda yake bi ta kansa yana zaune guri guda ya haɗa kai da gwiwa yana faman zubar da hawaye batare da kowa ya lura dashi ba shi kaɗai yasan halin da yake ciki na damuwa yayi da nasanin kasancewar sa ɗaya daga cikin masu iyaye masu halin mahaifiyar sa baitaɓa sanin haka mahaifiyar sa take ba anya ma kuwa ita ta haifeshi ahikaɗai sai tunanen tunanen yake bashi da wanda zai rarrashe shi sai yaji ya tsani kansa dama duniyar gaba ɗaya ji yake inama ya mutu agun ya hutawa ransa......, sam ne yafara lura dashi dan haka yayi saurin yi masa magana tare da sanar da papa shi dan ganin anmanta dashi, anan shima dai aka bashi haƙuri tare da jansa jiki da kwantar masa da hankali duk da mahaifiyar sace ta aikata hakan amma saboda halinsa na gari yasa babu wanda ya nuna masa hantara ko kuma nuna jin haushinsa akan abun da mahaifiyar sa tayi hasalima haka akace laifin wani ai ba ya shafar wani dan baka ya kwantar da hankalin sa daga yanzu shima yadawo ɗan gida ya zaɓi inda yake so ya zauna dan badan ta sanadin saba da baza ataɓa sanin sirrin dake ɓoye ba, haka sukai tayi masa basu rabu dashi ba har saida sukaga yaɗan saki jiki dasu kaɗan duk dade sunsan taci na ciki bazai taɓa mantawa ba amma dai yaɗan sake ba kamar ɗazu ba........, daga nan kuma suna cikin fadar papa ya bada umarnin aje agyarawa gimbiya sabreena ɓangaren ta saboda tunda ta mutu babu wanda akasaka aciki an ƙulle sa kawai amma wasu loƙutan akan shiga aduba sa sannan a gyarashi tsaf kamar da wanda yake kwana aciki, dan da nan kwa akaje aka rufar masa da masu gyara aka gyarashi tsaf aɗan ƙanƙanan loƙaci komai yazama ready me shigar sa kawai yake jira, su mamma da babama sukayi sallama da su suka tafi saida banda Azeema, Azeema tunda suka haɗu da Ameesha suka manne cike da kewar junan su hakan yasa su baba suka barta Salahudden ma zai bisu aka dakatar dashi akan yabari komai yaɗan fara daidaita kafin yayi shiri na musamman dashi da iyalen sa harma da su papa duk sai suje tare aƙara fahimtar juna, basu daɗe ba suka wuce gida tare da ƙyautar kuɗaɗe masu yawa da papa yasa aka basu, tare da bada mota da fadawa suyi musu rakiya har gida, daganan kuma zama yaƙare akan sai an ƙara yin zama nagaba an tattauna akan yanda za aɓullowa al'amari wajen zaƙulu mugayen, sannan akace gimbiya ta koma part ɗin ta tare da su dadda da Ameesha, Abu kuma shima aka gyara masa wani part ɗin inda zasu zauna kafin asan abunyi dan ba nan yakamata ya zauna ba dole abashi waje ƙawatacce amatsayin sa na ɗan sarki guda kuma ana tunanin zai zama sarki tunda yanzu kan kujerar babu kowa amma dai kafin ya hau sai anfara daidaita komai domin yanzu ba wannanne akan gaba ba, sannan anjinjinawa su bossay kan namijin ƙoƙarin da sukayi wajen taimakawa su Ameesha sananna akace ayau suje su ɗauko mutanen da suka kama su dawo dasu cikin masarautar sai aci gaba da tuhumar su anan, su Hajiya ma da Ammi tun agurin sukayi sallama dasu suka tafi gida saidai fa duk wannan abun da akayi babu wanda yace mahaifin bossay shi ya buge ta da motar sun rufe abu kuma daman maama ce ta gargaɗesu akan hakan tunkan ayi zaman dan haka har akayi aka tashi babu wanda yasan da wannan maganar har suka tafi, dagan nan kuma papa da su maama suka fito atare dan nufar part ɗin ta suna fitowa aka fara sakin saraiwa ana hurata ga kuma ganguna da wasu suke bubbugawa na murnar dawowar gimbiya sabreena saboda gaba ɗaya ilahirin Masarautar babu wanda baiji labarin da wowar ta ba kuma an fahimtar dasu cewar daman ba mutuwa tayi ba shiyasa suka haɗa wannan abun da su nuna farin cikinsu akan hakan suna waje amma babu labarin da bai riskesu ba daman na saukar sarki agaban su akayi basa buƙatar ƙarin bayani, kiɗa suke sosai wasu kuma ma rawa tsofaffin bayin da suka santa mata suma suka dawo ta bayanta suka fara take mata baya tare da kwararo mata kirari nan da nan maama tafara jin kanta asama tunawa da baya da tayi daman tafiyar ta ta daɗe da canzawa ta koma gimbiyoyin ita da papa ne agaba sai Meer da ta riƙo hannun sa badan yanaso ba kawai yake binta, sai su Abu da ummy da dadda baya su Ameesha kuma suna tsakiyar su ita da Azeema da ta riƙo hannun ta, harda gwaggo ma itama tana cikin tawagar su bata bari anbarta abaya ba, ahaka suka ringa tafiya anayi musu kiɗe kiɗe tare da kirari har aka rakasu part ɗin sannan suka dakata masu kiɗan matan kuma Saida suka rakasu har ciki sannan aka sallame su tare da yi musu godiya, Sam, bossay, shettiman, harda hamza ma da suka jawo shi ta ƙarfin tsiya saboda tausayin sa suke yi atare suka fita sai suka wuce part ɗin fulani gaba ɗayan su dan su samu su huta kuma su tattauna, su waziri ma da sarki Salahudden ahaka dai ɗaya bayan ɗaya dai ƴan cikin fadar suka ringa ficewa daga ciki Ammah ce ƙarshen fitowa daga ciki tana tafiya tana harhaɗa hanya saboda jirin da yake ɗawainiya da ita ganin yanda akayi watsi da ita anma manta da ita agun sunyi gaba sun barta hakan sai taji babu ɗaɗi aranta ga kanta da yake mata wani irin ciwo ahaka ta daddafa taƙarsa har part ɗin ta tashige ɗaki tare da faɗawa kan gado tana sauke numfashi, su papa ma bayan sun shiga wata hirar suka ƙara ɗorawa kiran sallah ne kawai ya tashe su shima kuma suna idar wa suke kara dawowa su ɗora daga inda suka tsaya abinci kwa mai rai da lafiya akayo musu daga part ɗin momma sukaci suka ƙoshi basu suka dakata da hirar ba sai dare sannan aka raka su Abu inda aka gyara musu Ameesha da dadda kuma suma aka basu ɗaki ɗaya harda Azeema, sai kuma wani ɗakin dake ciki maama tace jikantane zai zauna meer ya zauna tare da ita bataso yayi nesa da ita su zauna part ɗaya gwaggo madai da ƙyar ta iya tafiya makwancin ta, zuwa loƙacin kuma su sam har sunje sun dauko su baban sumy da wanda suka ɗauko a Abuja saida ba azauna dasu ba anbari sai zuwa gobe suma kuma su bossay duk gida suka tafi shi da shettiman yarage daga sam sai hamza da yakasa sakin jiki kwata kwata yanayi abu kamar marar lafiya......✍️✍️                               💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 97 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️      washe gari yanda aka kwanta da farin ciki haka suka tashi da farin ciki kowa ka tsinta acikin masarautar yana farin ciki da dawowar ahalin masarauta labaride ya karaɗe ko ina da ina har ƴan wajen gari ma sunji labarin abun dake faruwa shikenan yanzu za afara mulkin adalci, kowa yayi Allah wadaran da halin da  fulani ta tafka shekara da shekaru ana mulkin zalinci acikin masarautar yau gashi rana ɗaya Allah ya kawo ƙarshen abun, suna zaune a part ɗin maama gaba ɗayan su bayan sun gama yin breakfast suka dawo falo suka zauna har gwaggo ma har tazo falon yacika maƙil da mutane wannan yazo yafita wannan yazo fita ana ta zuwa tayasu murna wasu kuma gulma ke kawosu suzo su ganne wa idon su abun mamaki, basu suka daina karbar baƙi ba saidai aka kira sallar Azhar sannan aka dakatar da kowa bayan sunyi sallah sun dawo suka ƙara cin abinci rana sannan aka ƙara baje babin hira kafin daga bisani papa ya umarci su sam da suma duk ana falon tare dasu, yace "suje su ɗauko mishi mutanen da suka ɗauko jiya amma can cikin fada zasu kaisu zai zo ya samesu dan haka ba ɓata loƙaci sukaje suka kwaso su daga inda suka ajiyesu suka kaisu cikin fadar kamar yanda papa ya basu umarnin haka sukayi sannan suka dawo suka sanar dasu, da papa da gimbiya sabreena da dasu gwaggo kusan dai su duka suka ƙara fita suka nufi fadar tare da fadawansu dake taka musu baya, Ameesha kam tun asubar fari su Amra da sukaji labarin ƴar uwar su ce sukaje gurin ta suka ɗauko su ita da Azeema suka koma part ɗin momma sukaci gaba da shagalin su da taya juna murna, su papa na ƙarasawa cikin fada kowa yasamu wajen ya zauna saidai fa har yanzu kan karagar mulki babu wanda yake zama akai so ake sai angama komai sannan a nutsu ayi babban shagali a ɗora sabon sarki, yanzu dai kusan papa ne akan gaba shi zai ringa juya komai kafin nan gaba saboda acikin su babu wanda yasan kan mulkin dole sai yana nuna musu komai ahankali, bayan kowa ya zauna fadar ta ɗauki shiru aka umarci su baban Meer da su ma tso gaba su gabatar da kansu da kuma laifin da ake tuhumar su, Matsowa sukayi jikin su ba karkarwar tsoro duk sunyi zuru zuru da su ga wahalar zaman da sukayi su sukaɗai baci ba sha saboda sam yama manta dasu babun da ake basu, baban summy ne yafara ɗagowa cikin mawuyacin halin da yake ciki yace yace wallahi wallahi bansan komai ba kuma banda masaniya akan komai iya abun danasani kuma nagaya musu, yana maganar yana ɗan tsatstsorata yana kallon gefen sa sakamakon ganin Meer akan sa yana zagaye sa yana mishi wani irin kallo hakanne yasashi dakatawa da maganar da yake cike da tsoro da fargaba, Papa ne yatsareshi da ido yana nazarin maganarsa kafin daga bisani ya ɗan numfasa yace "katababar maganar da kafaɗa iyaka gaskiyar ka kenan....? kai abban sumy ya ɗaga masa tare da cewa "eh" jinjina kai papa yaƙara yi sannan yace "tom naji bayanin ka amma fa kasani idan bincike yayi bincike aka gano kasan wani abun bayan wannan to wallahi hukuncin ka sai yafi na kowa ka yarda? yace "eh" bayan yagama nasa bayanin aka koma wajen ɗayan da yake ta faman rarraba ido kamar ankama ɓera arami, papa yace muna sauraron ka kagaya mana inda ka mayar mana da ɗa kuma waye yake saka, cike da fargaba ya ɗago yana kallon papa sanna yace wallahi wallahi wallahi nayi muku rantsuwa har uku na rantse da mahallici na ni kaina bansan wannan mutumin da kuke magana akai ba hasalima ban taɓa ganin sab........, baikai karshen maganar ba meer dake gaban sa ya kwashe shi da wani irin gigitacen mari tare da kai masa naushi afuska Meer bai sake shiba yakuma jin wata uwar shaƙa daga gurin sam da ransa yagama ɓaci da jin rainin hankalin da yake neman yayi musu, dan haka shima ya tashi rai aɓace ya shaƙesa da ƙara masa wani naushin sannan cikin ɗaga murya sam yace "mu zaka rainawa hankali da wata banzar maganar ka ko ka mayar damu ƴan ƙwaya ne ka kiramu da kanka kayi mana wani gargaɗi da tsoratarwa kuma shine yanzu zaka zo mana da wata banzar magana how dare you ehhhh.....! ya ƙarasa maganar tare da buga masa wata iriyar gigitacciyar tsawa idon sa har ya canza kala saboda tsantsar ɓacin rab da yafara zuwan masa, jin haka yasa meer yaƙara karɓar sa daga hannun sam suka fara pacing pacing da shi suna neman kasheshi da duka, sannan su Abu saukayi saurin dakatar dasu da ƙyar aka iya rabasu aka kwace sa daga hannun su, ahakan ma saida papa yasa baki sannan suka dakata su ka koma gefe kowa jikin sa na tsuma duk wanda yagansu dole su furgita ka su baka tsoro ko basu ce da kai komai ba kallon yanayin su kaɗai zai sa ka shiga taitayin ka, shikam da aka gama luguda yana yashe aƙasa sai faman sauke ajiyar zuciya yake akai akai dan yaji ƙanshin mutuwa, maama ce tace masha Allah tun ba aje ko ina ba kenan kadai ji ajikin ka ko dan haka sai ka taso ka faɗa mana gaskiyar magana idan kuma kace kwana kwana ɗin zaka cigaba dayi bazaka faɗi gaskiya ba to kai zaka sha wahala gaka ga su zasu ɗora maka daga inda suka tsaya ne ba ruwan mu saboda haka katai maki kanka kayi abun da yakamata dan tsiratar da ranka in kuma zakaci gaba da rufawa wani asiri to kaine aruwa dan abanza zasu kashe ka kuma sun kashe banza sai ka zaɓa idan sirrin su yafi ranka to in kuma ranka yafi sirrin su yarage naka....., ai ba shiri ya tashi zaune yana gyara zaman sa yanda zaiji daɗi saboda jikin sa duk amace yake yayi tsami, saida ya taro nutsuwar sa sannan yafara magana cikin sunkuyar da kai yace "zan faɗi duk abun da nasani kuma iyaka gaskiya ta, amma dai kamar yanda nace muku bansan shiba ban taɓa ganin saba to hakanne saidai zan baku number wanda muke communication dashi ta waya dan koni yaƙi bari insan shi ko in haɗu dashi bamu taɓa haɗuwa ba saidai ya ɗorani ne akai duk ranar da wani abun yafaru insanar dashi......, maganar gaskiya office ɗin da kuka je bashine ainahin office ɗin ba wannan office ɗin kawai anyi shine saboda irin haka kuma an umarci kowa da kowa indai anzo neman office ɗin director ɗin to anuna masa wannan office ɗin shiyasa ma aka gyara sa kamar normal office ɗin wancen ɗin ma amma awajen directors ɗinma basu san da zaman wannan office ɗin ba shima kamar office ɗin kowa yake awajen su sai ka shiga cikine kawai zaka gane yana da bambam ci da sauran sannan kuma yawancin waɗanda ake ɗora akai basu da wani alaƙa da wajen kawai suyosu ake daga waje a ɗorasu akai..... ni kaɗaine kawai wanda ke da alaƙa da gurin nawane office ɗin, ina zaune aka kirani da sabuwar number akace ana son magana dani, nace "inaji na gyara kara zama, sai kuma aka kashe wayar sai kawai naji alart ina dubawa naga maƙudan kuɗi aciki da sukai matuƙar furgita ni dan aƙala kuɗin sunfi million ɗari aka turo min bangama mamaki ba aka ƙara kirana akace naga alart nace"eh" cike da furgice abakina sai mutumin kawai ya kwashe da dariya yace "ai wannan bakaga komai ba kada ɗan wannan kuɗin yaɗaga maka hankali, nan gaba zaka samu fiye da haka indai ka bamu haɗin kai kagama arziƙi dan ba abun da zaka nema karasa arayuwar nan duk abun da kakeso zan baka, sai na tambaye sa nace wane irin haɗin kai kuke buƙata daga gareni sai yace "akwai wani mutum zamu kawo sa nan gidan da zummar zai zauna muna so kasan yanda zakayi ka kaɓi case ɗin batare da kowa yasan da shigowar saba sannan kuma ko nima bazan gansaba zadai ayi komai a ɓoye kuma za ashigo dashi gidan amma na ƴan kwanaki za aɗauke sa kawaida ana buƙatar saka hannun na wajen shigo dashi gidan zanyi musu jagora har ashigo dashi, sai nace musu ai dole sai na kai file ɗin sa can wajen su sannan sai alƙalai sun saka hannu sai yace "kar in damu da wannan su zasuyi komai sudai ɗaki kawai suke buƙata in bar musu komai a hannun su...... duk da wannan batun nasa banyar da dashi ba kuma na nuna masa bana son kuɗin daga nan sai ya kashe wayar baiƙara nemana ba sai bayan kwana uku sanann yakirani da duk daha ban amin ce ba dan ina tunanin idan aka kamani dole asirina zai iya tonuwa duk ranar da akazo dubasu akaci karo dashifa za asamu matsala haka yaita kwantar min da hankali har yaja ra'ayina na yarda, bayan kwana biyu saiga wani daga cikin ma'aikatan gidan yakawon file ɗin sannan akace insaka hannu kuma kar inbar gurin aikin yau zuwa dare zasu shigo dashi na karɓa nayi signing na basu bansan dai inda suka kai file ɗin ba, haka naita zama har bayan sallar magariba sanann aka ƙara kirana akace in fito inyiwa mai gadi magana zasu shiga ina gurin me gadin ma bamu gama magana dashi ba naga har sun shigo sun wuce dake na gayawa wanda ya mawo min file ɗin inda zasu ajesa dan haka basu jira iso naba sukayi wucewar su ciki nabisu da kallo sannan nabi bayansu zanbi hanyar da suka bi sai wani yatare ni yace kar inje sunce ya jira yanzu zasu fito sai kawai nace masa "to" daga nanma ban tsayaba na koma office ɗina dan in harhaɗa kayana intafi gida fitowata ke da wuya na nemesu na rasa ban damu ba tunda daman nasan harkace ta rashin gaskiya sai kawai nayi tafiyata gida, washe gari da na dawo naje ɗakin da na kwantanta musu sukaishi dan inyi magana da mutumin, saidai ina zuwa naga ɗakin wayam babu kowa aciki da ba ƙaramin mamaki abun yaban ba nadaɗe aci ina alajabi ni kaɗai sannan nafito na koma office ɗina na ɗauki wayata nakira number da ake kirana da ita amma sai taƙi shiga haka nai ta gwanda wa bata shiga har na haƙura ina daf da tashi saiga kiransa yaƙara shigowa na ɗaga tun kafin ma inyi magana yayi saurin katse ni da cewa kar kace komai nasan kaje baka gansaba ko kar kasa kanka tunani ka gama yimana naka aikin dan ba anan muka ajiye saba mun canza masa guri saboda tsaro bamu san kowa yasan shi daga ciki kuma har dakai shiyasa muka canza masa waje batare da sanin kaba mungode da haɗin kanka yanzu zakaji alart mungama dakai...., daga nan ya kashe wayar baijira nace komai ba dan haka ya turo min wasu kuɗaɗen, daga nan kuma ban ƙara jin ɗuriyar sa ba tun ina mamakin abun har na daina naci gaba da sabgar gabana har na fara kashe kuɗaɗen da suka bani da kaɗan da kaɗan, saida akayi kwanaki da yawa dan nama manta da batunsu yaƙa kirana bayan na ɗaga mun gaisa......, sannan yaƙara bijiro min da buƙata office ɗina nace wannan kuma bazan iyaba suyi haƙuri su nema awani wajen tunda bani kaɗai nake da office ba, sai yace yasan da haka nawa kaɗai ake buƙara abun da suke so in kawai shine za abada kuɗi agyara office ɗin batare da sanin manyan mu ba, daga nan kuma zasu kawo wanda zai ringa kula dashi nikuma inje duk inda nake so sannan in ɗan ringa shigowa gurin ina ɗan zagayawa sai intafi aikina kawai inleƙo in koma su zasu ci gaba da kula da komai, nace masa hakan ai bazata taɓa yiyuwa ba abani office ɗin amatsayina na ma'aikaci kuma ace wai wanine daban zai ringa kula da gurin taya hakan zata taɓa faruwa batare da sanin kowa ba sai kace gidan yarin mahaukata a ina ya taɓa jin anyi irin haka inbanda shirme, sai kawai yace ba ataɓa yin haka ba kuma za ayi yanzu dole in amince ko ina so ko bana so idan kuma ba hakaba sai sunsa anyi min abun da bantaɓa tunani ba sai nayi da nasanin rashin amincewar da nayi dan sharrin da zasu ƙullamin bazan taɓa cire kaina daga ciki ba, na tsorata da maganar sa sai kawai nace masa na amin ce amma da sharaɗi yafara faɗa min daliin da yasa yake so sai wani ya shigo office ɗin sai yace basai naji ba sudai buƙatar su kenan akwai aikin da zasu sa ayi musune aciki duk yanda naso yagaya min yaƙi ba yanda zanyi dole na haƙura na amin ce, bayan na amin ce mungama magana sai washe gari yace yafasa kawo kowa nida kaina zanje in ɗauko wani in ɗora nidai na rasa gane kan wannan abun nasa nan ma nace masa na amice naje na lalubo musu wanda zasu ɗora akai sukayi magana dashi sannan muka fara aiki mu biyu aguri ɗaya batare da sanin kowa ba, ataƙaicedai munyi haka da wajen mutum biyar idan wani yazo sai suce ya tafi wani ma yaƙara zuwa na biyar ɗin shine wannan ya nuna baban sumy sannan yace loƙacin da zan kawo sa sai suka ce suna buƙatar idan na kawo sa inbar komai a hannun sa in haƙura da zaman office ɗin ma gaba ɗaya in faɗi duk abun da nake so zasuyi min bayan kuma kuɗaɗen da suke turo min akoda yaushe daman kuma gaskiyar magana inada son kuɗi su suka nake amince wa da duk wata buƙatar su haka na ƙara amincewa da wannan buƙatar tasa, dake ina da hanyoyi agurin sai kawai nace ni zanyi resigning daga aiki amma ina neman alfarma ga wani ɗan uwana da aɗora akai ban sha wahaba kuwa aka amince na kawo sa to shikaɗai ne dai yake zaune da sanin kowa ta baya kuma yana min aiki domin bama tare dashi amma kullum duk abun dake faruwa sai yakirani ya sanar dani, ranar kuma da kukaje wajen sa tun kafin ma ya kirani yagaya min, wancen mutumin yakirani yagaya min cewar za azo office ɗin kuma dan haka inkira wancen ince masa kar yasake yafaɗa musu inda nake saboda ni zasuzo nema yayi musu yawo da hankali kawai da haka har su tafi, sai kuma aka samu matsala basu tafi ba suka gano sa, duk maganar da sukayi najisu dan haka nayi saurin kiran wancen nagaya masa abun dake faruwa sai yace "in rabu dasu idan kungama komai inkira ku ingargaɗe ku akan maganar nemana da kuke indai tsoratar daku kuma innuna muku cewar nasan komai game da wanda kuke nema sannan kuma ince nasan inda kuke kucire hannunku daga cikin case ɗin in bahaka ba kuma zanyi maganin ku, shiyasa aranar na kiraku nayi muku barazana amma wallahi bansan kuba bansan komai ba baya ga wannan abun da nafaɗa muku wallahi tallahi iyakacin abun da nasani kenan, kowa shiru yayi yana nazarin tunanin da zaiyi game da wannan labarin da mutumin nan yabayar shin maganar sa gaskiya ce ko kuwa amma dai duba da yanda yake rantse rantse kamar da ƙanshin gaskiya aciki, sam ne ya tsugunna agaban sa sannan yace file ɗin kuma da akace kaje kana nema fa ido rufe har kana mishi barazanar cutar dashi idan baifito da shi ba yayi masa tambayar yana kakkafe sa da ido, dogon tunanin yashiga saida sam ya daka masa tsawa sannan yace ba magana nake maka ba, sai loƙacin ya dawo daga tunanin da yake sannan yace wannan ba file ɗinsa bane case ɗin wanine ya taso za ayi shari'a dashi kuma ni akabawa file ɗin loƙacin da abun ya taso aka kirani akace inbayar ko in faɗi indai yake ba agansa ba shine nakira nace masa ya laluboshi yace min baigansa ba nazo da kaina na duddu ba nima bangasaba shine hankali na ya tashi saboda nasan ƙarshen zancen idan nake nace ba agansa ba raina ne zai ɓaci shiyasa nace ya nemo sa amma ba abun da ya shafi wannan maganar bace, miƙewa sam yayi tare da yarfar da hannun yana dafe kansa dan wannan abubuwan da suke faruwa nema suke su tarwatsa masa ƙwaƙwalwa sai ana tunanin ansamu mafita za afara warwarewa sai kuma aga akasin haka wai sai yaushe komai zai zama normal ne abun yayi yawa daga wannan sai wancan, A fusace meer yazo gaban yana binsa da wani irin matsiyacin kallo sannan yace kawo number mutumin da yake kiran ka, dan Meer akwai karantar mutum yagama karantar sa kuma ya yarda da duk abun da yafaɗa shiyasa ma baiƙara kai masa mazgaba, kai mutumin ya girgiza yace watar tana can gidana na abuja basu bari nataho da ita ba, sam yace "mundauko ta ai tana office, saidai aje can aɗauko yanzu, Papa da tun ɗazu yakasa magana sa yanzu ya samu damar cewa "basai kunje yanzu ba kubari agama komai zuwa anjima sai kuje, da "to" sam ya amsa tare da samun guri yazauna, shiru gurin ya ɗauka kafin daga baya papa yace za a iya mayar da su inda aka ɗauko su sannan suje suyi sallar la'asr, kamar baban sumayya zaiyi kuka haka ya durƙusa aƙasa yace dan Allah tund dai banda laifi kutai maka ku barni intafi gida dan Allah kusake ni intafi yayi maganar sada kansa ƙasa hana addu'ar Allah yasa su barsa ya matsu yaje yaga ƴar sa, buɗar bakin papa kam yace ba matsala zaka iya tafiya amma koda yaushe idan wani abun yafaru da ya shafeshi zai iya jin kira ya zauna cikin shiri, cike da murna da farin ciki yace "ya amince koda yaushe ake buƙatar sa zaizo, saida aka ƙara gargaɗin sa da ja masa kunne haɗi da ƴar ƙaramar nashiha akan yaguji abun duniya komai zaiyi ya tsaya iya gaskiyar sa yanzu gashi yajawo kansa duka da kwana wani wajen batare da sanin iyalan saba ya kiyayi cin hanci ko nan gaba domin hakan ba inda zaikaisa saidai ya kaisa yabaro sa, sosai jikinsa yayi sanyj yayi da nasani daman tun ba yauba tun ranar da sam ya dake sa agaban ƴar sa yake nadama, dan haka yayi masu godiya yayi wa kowa sallama harda wanda aka kamosu tare da yake ji kamar ya bisa, bayan yayi musu sallama sannan ya miƙe tsaye yajuya zai fita har yakai bakin ƙofar zai buɗe sai kawai yaji ance RABI'U......cak yaja yatsaye sakamakon jin muryar wanda bai taɓa tunanin jintaba a irin wannan loƙacin batare da ya juyo ba yafara ko kwanton anya kuwa muryar da yaji daidai kunnuwan sa suka jiyo masa amma kuma yana da tabbacin ko amafarki yajita yasan ta wace dan bazai taɓa mance taba, ahankali yashiga juyowa har yagama juyiwa gaba ɗaya yanda ya zuba musu ido haka suma ƴan ciki suke kallon sa, ɗaya bayan ɗaya yafara binsu da kallo dan yaga ta inda mai muryar zai fito yaji muryar sa amma kuma gashi baigan sa, Abu ne ya miƙe tsaye sannan yafara takowa ahankali har zuwa gaban sa yakafe sa da ido kallon kallo suka shiga yiwa juna, saura kaɗan baban sumayya ya faɗi ƙasa yayi saurin dafa bango yana zaro ido tsawon minti biyar yakasa magana shima kuma abu bai masa magana, sai da ƙyar baban sumayya ya iya ɗaga hannun sa ya shiga nuna sa da yatsa yana mamar mamar da baki yanaso yayi magana amma yakasa da ƙyar dai ya daure bakin nasa ya buɗu yace "umaru ru......, na'am Abu ya amsa masa yana kallon sa tare da harɗe hannun sa aka ƙirjin sa, yana sake ƙare masa kallo, abun mamaki sai kawai hawaye suka fara sauka daga idon sa cikin hawaye yace "daman kana duniya daman zan sake ganin ka arayuwa ta babu irin neman da banmaka ba umaru nayi neman har nagaji har garin Lagos naje bansame kaba daga ƙar she nahaƙura ashe da rabon sake haɗuwar mu aduniya ashe bazan mutu da zunubin ka ba dan Allah ka yafe min abubuwan da nayi maka abaya da abun da mahaifiyata tayi maka na roƙeka ka yafe mata dan ta cutar dakai arayuwa yaƙara sa maganar yana zubewa aƙasa yana dafa ƙafar Abu hawayen sa har yana ɗiga kan ƙafar sa, Abu baisan loƙacin da shima yaji hawaye na zubowa da sauri yasaka hannu ya share hawayen tare da tsugunna yasa hannu biyu yaɗan bubbuga kafaɗun sa sannan ya ɗagosa ya miƙar dashi tsaye tare da rungume sa rungume juna sukayi, kowadai na falon sun zuba ido suna mamakin wannan sanayyar da tasu a ina suka san juna haka, har da su kuma, Abu ne yaraba su sannan ya kamo hannu sa suka dawo ciki, ba tare da ya zauna ba yakalli su Abu da suka tsare su da ido suna jiran ƙarin bayani, kallon su yayi sannan yace "wannan bawan Allahn da kuke gani ƙani nane koma ince kusan sa'ani muke dashi agidan da nafara tasowa na tsinci kaina kafin daga bisani kuma muka rabu sai yau Allah ya haɗa mu, bayan yagama gaya musu kafin ma yayi magana ya maida dubansa ga baban sumy sannan yace "Rabi'u ai kaman ta da komai yafiya kuma babu abun da kukayi min nima na daɗe ina cigiyar ku bansa meku ba tunda natafi da na dawo akacemin kun tashi haka na koma naci gaba da rayuwa ta ni kaɗai nakama kasuwan cina har Allah yayi min arziƙi nama bar ƙasar naje nayi aure har bayan na dawo ma na kuma bada cigiyar ku gidan radio amma shiru tun ina neman ku har na haƙura zan cen da nake maka yanzu haka bandaɗe da sanin ma ba mahaifin mu ɗaya ba dakai sai kwana biyu da suka wuce nasan hakan, sakamakon haɗuwa da mahaifiyata ta gaskiya da mahaifina ga kuma dangina babu abun da zance sai godiya ga mahallici na, yanzu waɗan nan dakake gani iyayena ne wannan itace mahaifiyata wannan kuma mahaifina ga ɗana kuma wanda kuma ake tuhumar ku akan ɓatansa kuma shima ɗan uwana ne ƙanine agare ni, dan haka ni banda wata damuwa yanzu daman damuwata ɗaya ce ta inda zan sameku dan innuna farin cikin riƙe nin da mahaifinka yayi sai gaka kuma Allah ya haɗa mu nayi murnar ganin ka sosai, domin ko mai kukayi min arayuwa bazan taɓa mantawa dakuba saboda kun gama yimin komai ko ince mahaifin ka yagama yimin komai arayuwa tunda har ya ɗauke ni aloƙacin da bansan kowaba banda komai har ya raineni na mallaki have ankalin kaina kafin ƙaddara tazo ta rabamu, idan ban yafewa iyalen aba ai bancika ɗan halak ba banyiwa kaina adalciba zan kasance ɗata daga cikin masu yin butulci nikuma ba butulu bane....ɗan dakatawa yayi da maganar sannan yaɗan yi murmushi tare da kara kamo hannun sa yace "Rabi'u ina so kamanta da komai kabar tuna baya kasa ma kamar babu wani abu da yataɓa faruwa tsakanina da kai na rashin jituwa da makaman cinsu komai ya wuce yanzu ka zauna anan idan muka gama komai zamu je dakai kaini wajen baffa inganshi harma da Inne itama inason ganin ta da sauran ƙanne na ina fatan duk kowa yana nan lafiya da ransa da lafiyar sa dai ko? yaƙarasa maganar tare da faɗaɗa fara'ar fuskar sa, shiru Rabi'u yayi yakasa cewa komai saboda abun al'ajabin da yagama kasheshi wai wanda suke ɗauka abanza suke wulaƙan tawa da cin mutuncin sa da zarafi ashe yafi su matsayi shiɗin wani ne yafisu zaiso kwa haɗuwar sa da mahaifiyar sa da har yanzu tana nan yanda take taƙi canza hali yasan idan tagansa zuciyar ta sai ta kusan bugawa, sosai ya tsunduma kogin tunanin saida Abu ya taɓosa sannan ya dawo daga duniyar tunanin da ya luluƙa, cike da raunin murya yace "saidai kayi haƙuri amma baffa tun bayan barinka gida ba jimawa Allah yayi masa rasuwa su Khadijah kuma duk suna nan ƙalau kowacce tayi aure da ƴaƴan ta, Allah sarki baffa Allah yajiƙan sa yayi masa rahama Allah yasa ya huta, da "Ameen" gaba ɗaya falon ya amsa Abu yaji mutuwar nan sosai mutuwar ta dake sa ba haka yaso ba yaso yasameshi da ransa dan ya rama masa halaccin da yayi masa amma haka Allah ya tsara dan haka yayi ƙudirin taimakawa ƴaƴansa daga yanzu bazasu sake shiga damu ko ƙunci ba zai taimaka musu fiye da tunanin me tunani, haka suka gama jimamin mutuwar sa akayi masa addu'a da gaba ɗaya mutanen dake ciki tun agurin baban sumy yafara kiran wasu yagaya musu bayyanar amma baigayawa mahaifiyar suba so yake ta gansa kawai, har wajen magariba suna tare basu rabu ba kuma tun aloƙacin Abu yace masa ya shirya gobe yaje gidan da suka siya idan yayi masa sai ya zauna yabashi kyauta inma wani zaibawa yabawa dan yagama dashi sosai yayi masa godiya sannan yatafi gida ransa tas cike da farin ciki da murnar ganin Abu da kuma yafe masa da yayi jinsa yake yau kamar a aljanna, mutumin da suka kamo kuma mayar dashi sukayi inda suka ɗauko su sanan kowa yakama gaban sa saboda dare yafara kusantowa, ana tashi daga gurin sam da hankalin sa gaba ɗaya yayi kan sumy da ya ɗauko yakaita wani wajen bai ƙara bibbiyar taba duk da yasan baban ta yatafi gida kuma zai tarar bata nan hakan bai damesa ba kuma baijin zai mayar da ita yanzu sai yagama garasu sannan zai nemi mahaifin nata yaji wai wane irin zama take agidan kuma ina mahaifiyar ta take sai yaji labarin kafin ya yanke hukunci ya mayar musu da ita, suna tashi kuwa ko takan su shettima baibi ba yaja Hamza suka fice daga cikin masarautar batare da su bossay sun lura da hakan ba, duk suna zaune afalon maama ta kalli Meer dake zaune yana cin kayan ciye ciyen sa da yasaba, ta kalle sa tace "ɗan gidan gwaggo wai baka gajiyane da waɗannan kayan zaƙin baza ka zauna kaci abinciba saidai kaita cika cikin ka da kayan banza wallahi ka canza wannan halin inbahaka ba zaka zama lusarin namiji kadai jini ko, ko kallon ta baiyi ba kuma bai daina cin abun saba, Ameesha dake gefe ita dasu Amra sunyi shiru saboda dakatar dasu ɗin da yayi yace ko suyi shiru ko su fita da har zasu fita Amra tace dan Allah su tsaya ita tanaso tai ta kallon sa dan haka suka zauna basu fita Amra na ta aikin kallon sa kamar ta samu tv idan taga zai ɗago sai tayi sauri ta kawar da kanta su Hamra suna yi mata dariya ƙasa ƙasa Azeema ma kam tafi so su zauan ɗin dan jirgi ɗayane ya ɗebo sa da Amra, Ummy ce ta shigo falon da sallamar gaba ɗayan su suka amsa mata, tana ƙarasa shigowa ta ƙaraso ta kalli Meer tace "hayatee gurin ka nazo dan Allah ka tashi kaje gidan can kadai ji abun da Abu yace ba sai na ƙara nanata maka ba dan haka tashi zakayi kaje ka kwaso min kayan da na bari aɗakina duk masu amfani ne, yanzu ma inada abun danake buƙata kayi sauri kaje, maama tace "gaskiya dai noma kashiga ɗakina ka duba idan da abun da namanta kataho min dasu, bashi da yanda ya iya tunda maama tasaka baki dole yaje dan baice komai ba ya miƙe tsaye tare da nufar hanyar ɗakin sa dan ɗauko key ɗin motar, yana shiga ya kuma fitowa ɗauke da key ɗin ahannun sa, yana fitowa maama tace bakaji ba juyowa yayi yana kallon ta, "ga ƙannen ka kuje tare mana su rakaka yanzufa ka kashigo cikin dangi dole ka canza Wannan ɗabi'ar taka ka sauko karinga magana da kowa, tsaye yana kallon ta kamar yasamu TV sannan daga baya yace suyi zaman su yana faɗar haka yaɗaga ƙafa zai tafi Ameesha tace "nima ka taho min da kayana suna nan ajakar ɗazu, wani irin kallo ya watsa mata tasan za arina dan haka tana faɗa takawar da kanta gefe bata yarda ma sun haɗa ido ba bare taga abun da zai mata girgiza kai yayi aransa yace zanyi maganin ki, ahankali yace "su taho yana faɗa yayi gaba, maama ta ɗanyi murmushi tace ko kaifa to kutashi kuje Amra ce tafara miƙewa sannan sauran ma suka tashi Ameesha ganin da sune yasa bataji wani tsoron saba ta tashi suka fita tare suna zuwa suka gansa har yaje wajen motar da zasu fita,, ƙarasawa sukayi sai duk suka tsaya suna jiran sa ya shiga sannan su shiga yana shiga kam suka buɗe baya gudan kar ace Ameesha ta shiga gaba yasa tafara shiga canbaya sannan Azeema sai sauran ma suka shiga, tsayawa yayi bayan sungama shiga sai yaƙi jan motar, sunkai wajen minti bakwai agun sai kawai suka ga ya buɗe motar ya fito sannan ya buɗe tasu Amra ce afarko yana buɗe yace fito tayi zaton ko gaba zata shiga duk da tana tsoransa amma da sauri ta fito saidai kuma tana fitowa yace da Hamra itama tafito ba musu kuwa dolen ta ta fito, suna jiran jin mai zaice sai yacewa ya nuna Azeema da hannu itama yace mata fito da sauri kam ta fito jikinta har yana ɓari dan hakan nan take tsoron sa bayama idan ta tuna da marin da yayi wa fulani take tsoron sa, ganin Azeema ta fita yasa Ameesha tun kan yace ta fito ma tayi saurn matsowa zata fito tana daf da zuwa wajen ƙofar yayi saurin datse ta ya rufe ta aciki sannan ya koma gaba ya shiga yana shiga yayi wa motar key duk da mamaki suka shiga bin motar suna ƙwalalo ido Ameesha kam tuni cikin ta ya ɗuri ruwa take ji take kamar ta saki fitsari a wando tagane sarai yana sane yayi mata haka dan yarama abubuwan da tayi masa, haƙuri ta fara bashi da magiya amma ko kallon ta baiyi ba ya tayar da motar tare da janta da mugun gudu ya ƙaraso gurin gate sarauka aka buɗe masa yaƙara kwasar aguje ya fice kamar zai tashi sama guri ɗata ta haɗe ta matse jikinta ta fara sakin kuma dan tun a iya nan ma tagama tsorata dashi tasan shikenan ƙamshinta ya bushe tunda tazo hannun sa ta kaɗe har ganyen ta bata da maitaimakon ta yau sai ta Allah wataƙil ma yau kwanan ta ta ƙare dan yasan idan yasaka hannun ajikin ta da niyar duka saidai ahaifi wata dan mutuwa zatayiii..............✍️✍️✍️                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innoc [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 98 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ _Na haɗe har wancen page ɗin danayi last posting saboda baida yawa kuma daman banbawa number ba shiyasa na haɗe su a wannan page ɗin ina fatan kun gane, wanda ya   karan ta sai ya wuce zuwa inda ya tsaya wanda kuma bai karanta ba sai ya ɗora kawai,_      "yanda yaja motar yatafi yabar su Amra agun har yanzu suna gurin sun kasa motsawa sunyi carko carko agun kamar nonuwan maza ko mamaki yagama cikasa da yakasa yiwa ɗan uwansa magana, Hamra ce tafara dawowa daidai da mamakin yagama sakin ta sannan tace to me muke jira sai kuzo mu kwashi ƴan matan ƙafar mu muƙara gaba daman ni basan zuwa nake ba dan wannan daman kana ganin sa kasan baza ayi abun arziƙi dashi ba, saida ta taɓasu sannan Amra da ba haka taso ba ta taɓe baki kamar zatayi kuka tace "to wai mema yake nufi da hakan kodan ita kaɗaice ƴar uwarsa shine zai tafi da ita yabar mu dan ƴan ubanci, da sauri Azeema ta dafata tace "haba Amra ba haka bane ba abun da kike tunani bane bazai taɓa yin hakan ba wai dan ƴar uwar sace kinga shi ba me son mutane bane wataƙil abun da yasa yatafi da ita dan ta ɗebo nata kayan itama da ta bari saboda bazai ɗebo mata ba shiyasa ya sauke mu ya tafi da ita amma kar kisaka wani abu aranki muje kawai mujira su yanzu zasu dawo ta faɗa tana riƙo hannun ta ta fara janta, Hamra tace "ai ni abun da nake tunani ma daban ina tunanin da ƙyar ne ma idan ba wani abun zaiyi mata ba bakuga kallon da yayi mata ba loƙacin da tace ya taho mata da nata kuma daman idan baku manta ba ai tace tsoran sa take ji tayi masa laifi bataso su haɗa, wataƙil wata muguntar tasa zaiyi mata  tunda tace mugune, Azeema tace "aikuwa dai hakanne ma maganar ki naga daman ta tsorata tanaso ta fito ya ƙulle ta aciki aikam yau ta shiga uku ita da banda abun ta ina ita ina tsokanar wannan mugun, baka yi masa bama ya ka ƙareda shi bare kuma kashiga gonar sa Allah dai ya kareta kar ya cutar da ita, "Ameen Hamra ta amsa mata dashi cike da jimamin tausawa halin da Ameesha zata shiga, haka sukai ta surutun su har suka ƙarasa part ɗin, kuma duk surutun da sukeyi Amra bata saka musu baki ba dan ita bata yarda da maganganun suba aganin ta kawai yayi hakane da ya ware su ya ɗauke ta dan tsabar rashin mutun cima saida yabari suka shiga cikin motar suka zauna zai wani buɗe yace su fito da tun can me yahanasa cewa kar subiyo sa saida ga baya zai wulaƙantasu ji take kamar tasaki kuka dan taƙaicin da yake cinta, da sallama suka shiga falon maama ce kaɗai aciki ta amsa musu Sallamar su tana dubansu da mamakin dawowar tasu, Saida tabari suka gama shigowa ciki suka zauna, ta ƙara kallon su da kyau tace "ƴan matana yana ganku haka kundawo lafiya dai ko koroko yayi? Azeema tace "eh" tafiya yayi yabarmu, maama tace "daman nasan zai aikata tunda daman bada son ransa yace kutaho ba amma saida yajaku waje kuma zaice ku dawo dan baida m to Allah ya shirye sa, ina ita Ameeshan take banganta ba, Amra tayi caraf tace "da ita kaɗai yazaɓa yatafi saboda itace ƴar...... Hamra tayi saurin rufe mata baki tace "maama bayan munfita har munshiga motar fa sai ya buɗe yace mu fito daman Ameesha ce tafara shiga ciki da tazo zata fito kuma sai ya rufe kafin ta fito ya shiga ya ƙulle motar suka tafi shine muka dawo mukuma, "kai kai kai la'ila ha illallahu Muhammadan ɗan Abdallah yanzu shi duk wannan abun bai haƙura ba saida yayi yanda zaiyi ya tafi da ita dan yaje yaci zalinta duk haƙurin dana basa bai haƙura ba sai ya rama sai kace wanda Allah yabawa zuciyar kuturu da bazai ringa yafita ba,  ashe da biyu yace kutaho daman ya shirya hakan dan ya kamatane yace kutafi sannan ya koroku aikwa ya taɓa min ƴar nan yau sai na ɓata masa rai zai dawo ya same ni, tayi maganar tana riƙe baki, Amra ce tace "wai maama me tayi masa zaiyi mata haka, tayi tambayar ne dan tadaina tunanin abun da take tunani so kawai take taji zunubin da ta aikata masa sannan hankalin ta zai kwanta, maama ta ɗanyi murmushi tunawa da abun da ya haɗasu sannan tace "cizon shi tayi, akusan tare suka haɗa baki wajen cewa "cizoo...!?" maama tayi dariya ganin yanda duk suka zaro ido suna mamakin maganar, Amra harda matsowa kusa da ita tace maama cizofa  garin ya akai takai haƙoranta jikin sa ta cijesa, maama ta kalleta itama sannan "tace muna hanya ne ya ɗora mata ƙafa ita kuma da taji zafi tace ya ɗaga ta yaƙi sai kawai ta cizjeshi a ƙafar shine yake ta so takamata ya rama shiyasa yayi mata wayo yau ya tafi da ita saidai Allah ya kiyaye kawai nasan sai yaci zalin ta wallahi bari insa uwarsa takira sa ta haɗani dashi inyi masa magana, dadda ce ta fito daga ɗaki tana cewa wallahi kiyi saurin kiransa kar ya kashe min jika dan bazan yarda ba sai nayi shari'a da mutum idan wani abu yasamar min shalelena wannan yaron da ba imanine dashi ba komai ma zai iya yi mata wallahi, maama tayi dariya tace to meye ai ita tafara tsokanar sa ni nama fasa kiran suci kansu tafara girmama sa daman na fuskanci ta rainasa gwanda ma ya koya mata hankali, tayi maganar cike da tsokanar dadda, dadda tace "da kwa ankwashi ƴan kallo agidan nan dankwa kowa sai abun ya shafeshi idan kuna son zaman lafiya to kar abari wani abu ya shafi shalele na ehe idan ba hakaba kuma kowa ya kuka da kansa bazamuga kowa da gashi zamu yage masa rigar mutunci ba, haka sukaci gaba da hirar su cikin raha daga ƙarshe dai su Amra sukaje suka sanar da ummy saƙon maama amma da takira wayar sa tana ta ringing ba aɗaga ba sai daga baya aka ganta a falo ashe baima fita da itaba, haka duk kowa yayi tagumi ana jiran dawowarsu......, da addu'ar Allah yasa kar yayi mata komai............,         ********************** tunda suka fita yake kwarara gudu, Ameesha ta rakuɓe agefe ita kuma sai faman raira masa kuka take zuwa yanzu ta fara fita hayyacin ta kuka take kamar ranta zai fita, duk kukan datake akan kunnen sa yanajin ta amma bai fasa gudun da yake ba, saida suka zo wajen danja da aka dakatar dasu sai loƙacin yasamu ya taka burki ya tsaya nadan ransa yaso ba, jin kukan nata ya isheshi yasashi juyo ya kalle ta tare da daka mata tsawa,yace  "ki rufewa min baki kafin in karkar yaki agunanna ubanki namiki na taɓaki da zakizo kina cikamin kunne da wata ƙatuwar muryar ki yakama ki adana kukan ki saboda gaba zai miki amfani ba yanzu ne loƙacin da yakamata kiyi saba kibari mu sauka saikiyi me dalili, wallahi naƙara jin muryar ki saina canza miki kamanni agunnan nonsense yafada tare da buka wani tsaki ya mayar da kansa bakin titi yana ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa, ɗif tayi bata ƙara bari sautin kukan nata ya fito ba hannu kawai tasaka ta toshi bakin ta tana yi ƙasa ƙasa jikin ta kuma sai faman ɓari yake ji tayi wata irin tsanar sa ta darar mata a zuciyar tsanama wacce inajin tunda take bata taɓa ji tayiwa wani ba haka takejin ta yanzu loƙaci ɗaya, ana basu hannu yaƙara kwasar motar kamar yanda yake yi yacigaba da gudu, dan gudun ma kamar yafi na farko, har wani ama"amai take ji na taso mata saboda gaba ɗaya hanjin cikin ta yagama kaɗawa cikinta ya ruɗe duk tabi ta furgita gashi kuma ya hanata kuka, duk yanda taso ta daure kar kukan yafito amma ina yafi ƙarfin ta saida yafito fili harda su tari da ya sarƙeta, da ƙarfi yataka burki da saida kanta ya bugu da kujera taƙara yin baya, ba ƙaramin faɗuwa gabanta yayi ba dan tayi tunanin ma motar ce take juyawa, bata gama tantance wannan azabarba yasa hannu yajawo gashin kanta daman mayafine ajikinta shima iya kai ko ɗan kwali babu, da ƙarfi yaja gashin tare da ɗagota dashi ahaka yajawo ta daga baya ta dawo gaba ya wurgata kan kujerar gefen sa, sai ya buɗe wani guri ajikin motar ya zaro wata ƴar ƙaramar wuƙa, yasaitata akan wuyan ta yace "wallahi idan baki min shiru ba sai yanka ki da ita, kiƙara cewa uffan kiga yanda zan gunduwa gunduwa da namanki acikin motar nan, inkashe ki na kashe banza dan ubanki mai kama da miyagu, atai miki magana ke bakijin magana kin raina mutane so kike ki fasa min kunne, to ni kafin kiyi min illa bari ni inmiki yana faɗar haka yadanna wuƙar awuyan ta kamar zai yanka ta sannan ya ɗauke, saura kaɗan Ameesha ta sume agun dan bata taɓa tunanin wannan muguntar tashi takai haka ba bata taɓa tunanin zai iya kisan kai ba ashe bayan dukan mutane da yake har kashesu yakeyi daman tare take da makashi bata sani ba, ai ba ƙaramin tsorata tayi ba ko kallon inda yake bata ƙara yiba ta matsa gefe ta rakuɓe jikin ta na kerma yake ga kanta da yafara yi mata wani irin ciwon azaba, tayar da motar yayi yaci gaba da tafiya har suka ƙarasa gidan, saida yazo dab da gate ďin sannan yayi parking ďin motar yafita ya zuge gate ďin ta sannan ya dawo ya kuma budewa ya shiga motar sannan yaja yashiga ciki. yana gama daidaita parking ya buďe ya fito baibi ta kanta ya koma ya rufe gate ďin, har yaje ya dawo bata fito ba, wajen motar ya koma ya buďe da kansa yana buďe wa tayi baya zata koma baya ya jawo ta ya fincikota ya fito da ita waje, gefen rigarta ya riqe ya fara janta ita kuma tana kwacewa da tagadai da gaske ciki zai kaita tafara basa haquri amma yaqe sauraron ta, ta manta da laifin da tayi masa tunfarko ta qara kai baki zata cijesa aikwa ya riqo bakin ha matse kamar zai fasa mata shi haka ya matse mata shi, tana kuka tasaka hannu tana qoqarin kwatar bakin  ya kuma  riqe ďayan hannun  nata ga murďe shi har sai yayi  qara sannan ya sake  ta yaci gaba da janta har yakaita cikin falon yana shiga ya jefata ciki ta faďi qasa saura kaďan kanta ya bugu da center table  dake tsakiyar falon Allah ya tsagaita mata wahala ya kareta bata kai ga buguwa ba yasa ka hannu ta dafesa, loqacin da suka shigo anfara kiraye kirayen sallahr isha'i  dan haka sai babi ta kanta ba ya juya zai fita har ya kai bakin qofa sai kuma ya tsaya haďe da juyowa ya wurga mata wani banzan kallo sannan yace "ko da wasa kikayi kuskuren fitowa na lahira sai yafiki jin daďi yana kaiwa nan yayi fice abunsa, ko kallon sa batayi ba saida ta tabbatar da yafita tayi saurin tashi zaune tinanin yanda zata samu mafita ta shiga yi yanda zata kare kanta daga haďuwa dashi, jitayi kamar tafiya tayi tunanin ko shine ya dawo aguje ta miqe har ra doshi ďakin da ta kwana tana zuwa tajisa arufe arikice ta juyo ta qara nufar ďayar kofar nanma takasa buďewa babu qofar da  bata gwada buďewa ba amma duk sunqi buďuwa, qofar shigowar taqara kalla tajidai har yanzu bai shigowa sai kai tayi sauri taqarasa gurin qofar taci sa'a kuwa kye ďin yana jikin qofar, sai kawai tayi sauri ta rufe qofar ta kulle harda su zira saqata ajiki sannan tabar muqullin ajiki saboda koda ya zira wani bazai buďu ba, duk da atsorace take da zaman itakaďai amma ta gwammace ta zauna ita kaďai akandai yadawo yasameta aciki, dan tunanin tama kawai wuqar ya tafi ya ďauko kasheta zaiyi shiyasa ta rufe ta koma kan kujera ta zauna cike da tsoro da fargaba jikin ta sai rawar sanyi yake abunne ma yahaďar mata biyu ga tsoro ga sanyin garin shiyasa take rawar ďari, tana zaune agun har tsawan loqaci bataji dawowar saba wani tunanin ne yafaďo mata kodai tafiya yayi yabar ta ita kaďai tunanin hakan yasa ta tashi da sauri ta taje wajen  window ta yaye labulen ta leqa waje sai ta hango motar agun ajiyar zuciya ta sauke ganin bai tafi ba tana niyar barin wajen kenan ta hango shigowar sa da sauri ta saki labulen ta koma inda tame ta zauna gabanta na qara faďuwa tafara addu'ar Allah kawo mata ďauki Allah yasa dadda tazo ta taimaketa.........., bugun zuciyar ta ne ya ƙaro loƙacin da tajisa kusa da ƙofar yana murɗawa alamar zai buɗe ƙara ƙanƙame jikinta tayi ajikin kujera jikin ta nacigaba da ɓari, ba ƙaramin mamaki yayi ba ganin ƙofar arufe da alama rufeta akayi ransa yaji yaƙara ɓaci ga sauran muƙullan suna cikin falon har muƙullin motar yana ciki ya ajiyesu loƙacin da zaiyi alwala, buga ƙofar ya shigayi da ƙarfi kamar zai ɓalle ta, cikin ɗaga murya yace "ki buɗe ƙofar nan wallahi kika bari na shigo sai ranki yayi mummunan ɓaci ki buɗe, tana jinsa amma ki motsawa batayi ba  haka yai ta bugun ƙofar nan taƙi buɗewa, haƙura yayi ya nufi wajen motar sa yajata ko zata buɗu amma yajita arufendai da yabar ta taƙaicine ya isheshi yarasa samun mafita, dawowa yaƙara gurin yaƙara bugawa bata buɗe ya koma wajen window ɗin suma arufe suke ta ciki tashin hankali wanda ba asamishi rana yau wannan ƴar kucililiyar yarinyar ce ta rufe masa ƙofa rainin har yakai yana mata magana tanajin sa tayi masa banza idan kwa yakamata ta shiga uku sai ya kusan karya ta wallahi abun da baiyi niyar yi mata ba tajawa kanta sai yayi mata abun da bata taɓa tunani ba aidai dole ta buɗe tunda ba aciki zata kwana ba, samun wani ɗan guri yayi ya zauna yana jiran buɗewar ta acewar sa idan tagaji da zama ita kaɗai zata buɗe, gugugu gari yaɗauki kukan hadari loƙaci ɗaya ya turniƙe da haɗowar wani gagarumin hadari, zunbur ya miƙe daga gurin cike da tashin hankali da fargaba da ruwan samane kawai yake haddasa masa tsoro da fargaba saboda ko ɗigon ruwa ba ya bari ya taɓasa indai ya taɓasa har suma yana iyayi baya son ruwan sama ya taɓasa saboda akwaisa da jin sanyin aɗan ƙanƙanan loƙaci sanyi yakesawa ya fita daga hayyacin sa inda kagansa hankali kwance ana ruwa to yana ɗaki aduƙunƙume aciki bargo yana bacci shine kaɗai kwanciyar hankalin sa, asukwane yaƙara zuwa kusa da ƙofar yayi mata wani irin mahaukacin bugu wai ko zataji tsoro ta buɗe amma taƙi buɗewa, cike da raunin murya da yasan bashida wata hanya da ta wuce wannan yace "pls ki buɗe I promise you bazan miki komai ba kibuɗe hadarine agarin kar ruwa ya sauko, kamar tana gabansa ta maƙe kafaɗa alamar bazata buɗe ba haka yayi tayi mata daɗin baki ta buɗe amma taƙi buɗewa acewar ta wayo zaiyi mata shiyasa yabiyo ta wannan hanyar dan ta buɗe yasamu damar cin uwar ta, daga ƙarshe ma da tagaji da bugun da take sai kawai ta tashi da ƙyar taje ta kunna T.V tare da ƙure vollum yanda bazataji saba kuma hakan zai rage mata tsoron da takeji saboda daman bataji ƙarar hadarin ba dan haka koda ruwan ma akafara ba lalle tajisa ba, dafa kansa yayi ajikin ƙofar yana ɗan mammatse jikinsa saboda sanyin da yafara kamasa tunani yayi kodai yafita daga gidan yaje koda wani restaurant ɗin ko kuma yatafi masallaci sai kuma ta tuna ai sun rufe masallacin yanzu saidai kawai ya fita ko zai samu wata mafakar awaje gashi ɗakin me gadi ma arufe yake bare ya shiga, har ya juya zai tafi sai kuma tunanin ta ya faɗo masa in bazai mantaba ranar da suka haɗu da aka fara ruwa wataƙil tsoro ne yasa ta dawo kusa dashi ta kwanta dan ya fahimci hakan to gashi kuma yanzu ita kaɗai aciki yasan bata yarda dashi ba da yace mata hadarine agarin tunda gashi yanajiyo sautin tvn da ta kunna alamaun batajin ma abun dake faruwa, to idan yatafi yabarta kuma ta ankare wane irin hali zata shiga wata zuciyar tayi saurin bashi amsa da cewa ta shigama duk halin da zata shiga tunda ita ta zaɓi hakan ta mutuma ina ruwanka, da wannan tunani yayi na'am dashi da hakan ya ɗage kafaɗa tare da ɗan taɓe bakin sa ya ɗaga ƙafa zatafi aikwa kamar ɗaga ƙafarsa ake jira ruwa ya fara saukowa da sauri yayi baya kusa da ƙofar saboda wajen gurin ya ɗan rankwafo amma ba sosaiba babu abun da zai hana ruwa ya taɓaka, saidai bakamar kana tsakiyar saba kunsa koya guri yake idan kaji ruwa neman ɓuya kake agun, shima haka ya koma jikin motar ya manne da ita yana ƙara buga ƙofar duk da yasan bazataji saba saboda ƙarar vollum ɗin, duk addu'ar da tazo bakinsa yinta yake tun ruwa na taɓasa kaɗan kaɗan har yadawo sauko masa da yawa take kwa yafara fita hayyacin sa nufashin sa nayin sama sama kamar zai ɗauke agun ya sulale ya tsugunna yana dafa ƙirjin sa loƙaci ɗaya idanun sa suka fara kakkafewa takurewa yayi guri ɗaya ya jingina da ƙofar jikinsa sai karkarwa yake haƙoransa har kaf kaf suke dana juna wajen rawar baki da yake, ƙafarsama nema take takasa ɗaukar sa haka yayi zaman dirshen agun ya haɗa kai da gwaiwa ya matse jikin sa, tun yana motsawa har yadaina motsi agun da alamun dai kamar ya ƙame agun sanyin ya ƙamar dashi ko numfashi ma bayayi, a kai wajen awa ɗaya ana keta ruwa yana sauka akan bawan Allahn nan da yana cikin wani yanayi matacce ko rayayye babu wanda yasan halin da yake ciki, aɓangaren Ameesha jinsa kamar ma baya bubbuga ƙofar yasa ta ɗan rage vollum ɗn tare da yin sanɗa ta matso kusa da ƙofar ta kara kunnen ta dan taji yana gurin ko ya tafi shiru taji alamun babu kowa agun gurin windown ta ƙara komawa ta buɗe labulen ta leƙa wajen motar sa taga tana nan, anan take ganin ruwan da yake sauka kaɗan kaɗan, mamaki ne yakamata daman da gaske yake hadarine agarin gashi ruwa har ya fara sauka to ina yayi Allah yasadai bata fiya yayi ba, da sauri ta dawo wajen ƙofar ta murɗa Kye ɗin tare da jan ƙofar dan ta duba inda yake, tana buɗewa taji abu me nauyi akan ƙafar ta kamar anjefosa cike da tashin hankali takai dubanta kan ƙafar idon ta sukayi mata tozali dashi, wata iriyar ƙara tasaki cike da firgici ta tsugunna agaban sa tare da fara taɓasa ganindai da gaske baya motsi  yasa ta janye ƙafar ta da ƙyar tafara jijjigashi tana taɓa saitin hancin sa taji babu numfashi, Inna lillahi wa inna illaihi raji'un, inna lillahi wa inna illaihi raji'un, inna lillahi wa inna illaihi raji'un, itace kalmar da take ta nanatawa cike da tashin hankali da bata taɓa tsintar kanta ba a ciki ba, da gudu taje wajen kitchen duk tabi ta duburbur ce ta rasa ina zatayi saitayi wajen kitchen ɗin sai tadawo da ƙyar dai ta iya buɗe ƙofar ta shiga ta ɗebo ruwa a kofi cikin sauri ta dawo wajen kafin tazo ma ruwan duk yagama zubewa baifi rabin kofi ba yarage saboda tsabar saurin da take, tana zuwa ta yayyafa masa a fuskar sa amma kamar ta watsawa bango, daga tsayen da take ta saki kofin ya faɗi ƙasa ya fashe, hankalin ta da jinta gaba ɗaya sungama gushewa bata son loƙacin da itama tabi kofin tayi daɓas aƙasa hawaye na rige rigen saukowa yayin da ta kafesa da ido tana kallon sa agaban ta tana yimasa kallon gawa, tashin hankalin ta shine idan ta tuna loƙacin da yake roƙon ta ta buɗe babu abun da zaiyi mata taƙi buɗewa gashi ta sanadin ta ya rasa ransa, yanzu kamar ita ta kasheshi kenan tunda itace sila, ahankali ta furta kisan kai ni na kasheshi sai kuma ta shiga girgiza kai tace "a'a, a'a, a'a bani bace wallahi bani bace bani na kashe shi ba, bai mutu ba ni nasan bai mutuba da ransa haka takama sanbatu awajen kamar zararriya sai kuma tayi saurin miƙewa taƙara natsawa kusa dashi, ta shiga girgiza sa da iya ƙarfin ta tana jijjigasa tana cewa ka tashi dan Allah katashi kar ka mutu ka tashi Inga baka mutuba kar wani yazo yaganka ahaka kayi haƙuri ka tashi dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan ƙara rufewa ba katashi kayi min duk abun da zakayi min na yarda ma ni ka kasheni da duka bazan ƙara guduwa ba,  tanayi tana jijjigasa amma ko motsi bayayi kuma bata fasa jijjigasa ba tana sanbatu wasu abubuwan ma batasan tana  faɗa ba saboda bata cikin hankalin ta gaba ɗaya, kuka kam harda su majina dataga dai da gaske baida niyar tashi sai ta fara jansa wai ta matsara dashi daga bakin ƙofar amma sai takasa, ɗaga ƙafar ta da zatayi saikwa ta sauketa akan kwalbar kofin da fasa take jini yafara zuba daga ƙafar ta sakin sa tayi, sannan tayi saurin zama agunta riƙo ƙafar tana kuka tanaso ta cire amma zafi ya hanata sai kuka take ga tsoron ta jinin da taga yana fita, kwance tayi agun tana sakin wani kukan azabar tana juyi zata tashi taƙara ɗora hannun ta akai shima kwalba tashiga da sauri ta tashi zaune tana yarfa hannu dake ta hannun bata kai ta ƙafarfa saita damƙe idonta ta zare kwalbar da ƙyar, gudun karta ƙara taɓawa yasa tasaka hannu again tafara tattare kwalbar waje ɗaya aikwa tasamu rabonta dan Saida wasu ƙana nun suka ƙara shige mata hannu haka ta zauna tana kuka tana ciresu hannun ta duk ya farfashe, kallon ta ta mayar kansa har yanzu yana nan yanda yake a sanƙame, wani tunanin ne ya faɗo mata bata san loƙacin da ta miƙe tsaye ba tana takawa kuma kwalbar ta ƙara shige mata runtse idon ta tayi sosai sannan ta ƙara buɗesu duk da azabar da takeji haka ta daure ta cije ta shiga takawa ahankali, ko ɗan kwali babu akanta haka ta fito daga cikin falon halin da take ciki yasa batabi takan kwalbar dake ƙafar taba duk da zafin kwa da takeji haka ta daure take ɗingisa ƙafar tana taka inda ba kwalbar, da ƙyar take takawa har ta ƙaraso bakin gate ɗin ga ruwa da akeyi amma ba mai yawaba yayyafi ne shima ba sosai ba, buɗe ƙofar tayi ta fito wajen titin tsayawa tayi tana duban garin yayi tsit bakajin motsin komai kuma kan titin ma babu kowa ba mota ko ɗaya, duk irin tsoron Ameesha yau ta dake batajin tsoron saboda zuciyar ta tabushe kawai burin ta ta haɗu da wani yakaita gida taje ta faɗi halin da ake ciki, da atunanin ta ko zata iya zuwa gida aƙasa amma sai ta tuna batama san hanyar da zata dosa ba, ta daɗe agun bataga giftawar kowa ba har tana tunanin ta juya kawai sai taji wata ƙara na ruɓeɓɓen mashin ta bayan ta da sauri ta juya tana kallon hanyar da yake tahowa ko fitila babu ajiki haka mashin ɗin yake tafiya matsawa tayi gefe tana jiran ƙarasowar sa gun, tun kan ya ƙaraso take ɗaga masa hannu tana cewa wait wait pls help me, amma mashin ɗin yana zuwa sai yayi wucewar sa, har ɗan binsa tayi tana kiran yatsaya ya taimake ta amma yaƙi kamar tayi kuka haka ta haƙura ta juya zata koma har taje wajen gate ɗin sai kuma taƙara jin ƙarar mashin ɗin..... ɗan juyowa kawai tayi tana kallon sa bata ƙara gigin tsaidashi ba tayi tunanin yanzuma wucewar sa zaiyi shiyasa batayi tunanin dakatar dashi ba, sai kawai taga ya nufo inda take, take taji wani irin daɗi ya ziyarce ta, agabanta yayi parking ɗin mashin ɗin nasa tare da kasheshi sannan ya sauko daga kai, tsoho ne sosai jikin sa kuma yana sanye da wasu irin kaya kamar na fata ga wata jakar arataye a wuyan sa kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci mafarauci ne, da tagama kallon sa tsorata tayi dan aduhune batagan sa sosai ba, ita bata taɓa ganin ma mutum da irin wannan shigar tasa ba tunani tafara kodai aljanine, ko kuma ɗan daba, tunanin hakan yasa tafara yin baya baya, kallon ta yayi tundaga sama har ƙasa sai kawai yasaki murmushi yace "da kinsan kina jin tsoron kika tsaida ni me yafito dake a cikin daren nan akuma rin wannan yanayin bakya tsoron wani abun ya cutar dake ko mugayen mutane? shiru tayi tana kallon sa takasa cewa komai saboda har yanzu a tsorace take dashi, wani murmushin tsohon yasaki yace yarinya karkiji tsoron komai sanar dani buƙatar ki yanzu nan inbiya miki ni ba macuci bane, saboda irinku nake zagayawa daman inda mai neman taimako in taimaka masa, sai yanzu ta ɗanji sanyi aranta ganin yanayin sa yasa taji kawai ta yarda dashi kuma tasan zai iya taimaka mata ɗin kamar yanda tace, ahankali ta shiga bashi labarin abun dake faruwa tundaga A har Z, yana gama jinta yace muje ciki to in dubasa, gaba ta fara yi yana binta abaya ganin tana ɗingisa ƙafar da ƙyar yayi saurin dakatar da ita tsayawa tayi tare da juyowa, tana kallon sa wata ƴar ƙaramar fitila ya ɗauko sannan ya tsugunnna agaban ƙafar ta yace muga ƙafar ɗan ɗaga masa tayi yagani sai yace ta zauna, ya cire mata, batayi musuba ta zauna ɗin, shi kuma ya kamo ƙafar saida tayi kuka wajen cire mata sannan yasaka mata wani magani da yazaro ajakar sa, bayan nan ya taimaka mata ta shi tsaye da ɗan ɗingishin suka karasa cikin gidan har sukazo ƙofar falon inda ta barsa haka tazo ta same sa, ita tafara shiga ciki sannan tsohon ya shiga idonsa aka Meer dake yashe aƙasa kamar gawa, ganin irin kallon da tsohon yake yiwa Meer yasa Ameesha ƙara tsorata murya cike da rauni da take shirin fashewa da wani kukan, ta kalli tsohon tace "ya mutu ko....? kallon sa yamayar kanta sosai ya zuba mata ido yana kallon ta kamar me son  gano wani abu ajikin hakan kuma harsaida ya haddasa mata faɗuwar  gaba tare da tsoro ganin irin kallon da yake mata ko ƙiftawa bayayi ga wani uban kwalli da yasaka da sai yanzu ta ankara dashi, bata gama furgitaba saida taga yana canza kalar fuskar sa ya haɗe ta tam ta koma wani iri tare da zaro mata idanu yafara nufar inda take, ganin hakan yasa tafara ja da baya tana karkarwa yayin da idanun ta suka cika taf da hawaye tana tafiya muryarta na rawa tace "dan Allah kayi haƙuri kar ka cutar dani dan Allah dan Annabi, duk magiyar da take masa baida na binta ba saida yakaita kusa da bango sai ya tsaya agaban yana sake kallon ta yanda take kuka kamar ranta zaifita, saida yaƙara ɗaure fuska sannan yace "me yasa kika kashe shi duk maganar da kikayi ban yarda dake ba ƙarya kike ke kika kashe shi. shine zakizo ki shirya min ƙarya ai na ganoki kuma yanzu zan kirawo miki ƴan sanda suzo su kamaki ko kuma ni inkamaki in tafi dake, wanne kika fiso ni ko ƴan sanda? da sauri ta shiga girgiza masa kai tare da haɗa hannu wanta guri guda tashiga yi masa rantse rantse wallahi ba ita bace, girgiza kai kawai yayi tare da sakar mata murmushi har haƙoransa na fitowa waje, baice mata komai ba kuma sai ya matsa daga kusa da ita ya koma wajen Meer jakar sa ya ciro daga wuyan sa sannan ya zauna akusa dashi yafara ɗan tattaɓa sa, juyawa yayi ya kalleta tana inda yabarta bata daina kukan ba, "zo ki ɗauko min roba ki zubo ruwa aciki sannan kidaina wannan kukan, da sauri tasa hannu ta goge hawayen saboda ba ƙaramin tsoron sa takeji ba, cikin sanɗa tafara tafiya ta nufi ƙofar kitchen da kallo yabi bayan ta yaga yanda take tafiya, sai kawai yayi murmushi yana ɗan kaɗa kai yana sane dan yaga ya zatayi ya ɗan canza murya tare da ɗaga murya da ƴar ƙaramar tsawa yace "kee...!! bazakiyi sauri ba ne., Allah sarki daman kwa a tsorace taken sai kawai ta kwasa aguje tama manta da ciwon dake ƙafar ta ta takesa saboda tsoro, tana shiga kitchen bata daɗe ba ta fito da wata ƴar babba babbar roba da ruwan aciki kamar yanda yace mata tana fitowa taga har ya maidashi tsakiyar falon ya ɗorasa akan Capet mamaki ne yakamata ganin har ya maida shi kafin ta shiga ta fito kuma abun da yafi ɗaure mata kaima shine taya yana tsoho dashi har yasamu ƙarfin da ya iya ɗaukan sa anya kuwa wannan mutumin mutum ɗin gaske ne baya tare da aljanu ko kuma shikansa ɗin aljanine yayi shigar mutane, ta manta da aiken ta yayi ta tsaya tana wani tunanin saida ya kuma yi mata magana sannan tayi sauri ta ƙarasa gurin hannun ta har yana karkarwa wajen miƙa masa robar saura kaɗan ma tasaki ruwan ya zube yayi saurin riƙe robar, baice mata komai ba ya warware wani abu a takadda ya zubasa aciki ruwan yasa hannu ya jujjuya sannan ya ɗauko wani ganye yaringa ɗiba dashi yana watsa masa aduka jikin sa har saida ruwan yaƙare sannan ya zaro wani abu me kamar mai a kwalba ya buɗe sa yace da ita  "matso, atsorace ta matso kusa dashi yace "kawo hannun ki miƙama sa tayi ya zuba mata aciki" yace "murtsuke shi a duka hannun ki, nan ma batayi masa musuba ta murtsuke shi yanzu bata da wani zaɓi ko jayayya dashi dole tabi duk abun da yace mata,  tana gama murzashi ahannun ta ɗan saci kallon sa tana jiran taji me zaice caraf kwa suka haɗa ido da sauri tayi ƙasa da nata, "matso ki shafa masa shi afuska zuwa wajen wuyan sa gaba ɗaya, kasaƙe tayi tana kallon sa kamar bazatayi ba, kallon ta yayi shima yace bazakiyi bane, idan bakiyi ba ke zakiyi asara dan sai kinfi kowa da nasani nan gaba, kiyi ki shafa masa in kuma sokike ya mutu to shi kenan intashi inyi tafiya ta, "a'a yi haƙuri zanyi tafaɗa tare da ɗora hannun akan fuskar sa tana shafa masa ahankali kamar me tsoron taɓasa, ahaka har tagama shafa masa aduk inda yace ta shafa masa sannan ta cire hannun ta, shi kuma yaƙarasa duk wani abu da yasan zai masa yasamu lafiya yagama komai ya mayar dasu cikin jakar yasaƙalata awuyan sa yamaidata mazaunin ta, "kallon ta yayi yace taso ki zauna anan ya nuna mata gefen sa., Ahankali ta tashi daga inda take ta koma kusa dashi ta zauna inda ya nuna mata ɗin ta zauna tare sa sunkuyar da kai aƙasan zuciyar ta kuma tana jin tsoron sa Allah Allah take kawai ya tafi, Hannun ta yakamo duka biyu ya riƙe anasa yana kallon ta, Itama  ɗagowa tayi tana kallon sa sai kawai ya ƙara sakar mata murmushi, da sauri ta kawar da kanta, Ganin hakan yasa yafara magana ahankali, kiyi haƙuri ni ba macuci bane ba kuma mugu bane dan haka ki kwantar da hankalin ki babu abun da zan miki duk abun da nake miki da wasa nake miki kawai tsokanar ki nake, Saboda naga kin tsorata ne da yawa shiyasa nayi miki haka. Kuma wannan bawan Allahn yana daf da tashi idan ya tashi kibashi kulawa sosai duk abun da ya buƙata kiyi ƙoƙari kiyi masa koda hakan zaimiki ba daɗi kinji ko? Kai ta iya ɗaga masa kawai. Sannan yaci gaba da cewa "bari ingaya miki wasu abubuwan da baki sani ba saboda ke yarinya ce ƙarama yakamata kiriƙe su tun yanzu kafin nan kafin zuwan wani loƙaci kina jina yayi maganar yana kallonta, yanzu ma ɗaga masa kan ta kumayi, Sai kawai ya girgiza kai ya ɗora da cewa... "nasan kinsha gwagwarmayar rayuwa tun kina ƙarama kuma har yanzu kina kanshan ta kuma bazaki daina shantaba nan kusa, akwai wasu ƙalubalen da zasu sameki nan gaba, to amma inaso kiɗauki ƙaddarar ki hannu bibbiyu kiriƙeta amatsayin jarabawar rayuwar ki, Nan gaba komai zai wuce zai zama kamar ba ayiba taurarin ki zasu cigaba da haskawa har bayan ranki keɗin watace anan gaba shiyasa zaki ringa ganin abubuwa kala kala na akasin farin ciki, ba tafa nake miki ba amma nasan akwai matsalolin da zaki fuskanta nan gaba fiya da waɗanda kika fuskanta abaya shawarar da zan baki itace kiriƙe addu'a safe da rana da dare ki yawaita ibada sosai fiye da wadda kike yi domin girma nazo miki ta nanne kaɗai zaki iya yaƙar maƙiyanku har kici nasara akansu, kiriƙe abu ukunnan da zan faɗa miki. Na ɗaya kinga wannan mutumin da yake kwance da shi kaɗai yakamata ki yarda shine kaɗai bazai taɓa cutar dake ba duk wani shawara idan zakiyi ko abu ya shige miki duhu kafin ki tunkari kowa da maganar kifara tunkarar sa koda bazai kulaki ba, Na biyu daga yanzu kar ki ƙara yarda da kowa kar kibari kowa yaƙara sanin abun dake cikin ki ki yakice kowa daga cikin ranki hakan zai miki amfani nan gaba, Na uku arayuwar nan kar kiga wai mutum yana miki wasa da dariya yana nuna so agareki akida yaushe kiyi tunanin shine masoyin ki to ba haka abun yake ba sai kiga wanda zai haɗe miki ran koda yaushe shine masoyin ki na haƙiƙa abun azuci yake wanda me iya fito da sirrin zuciya sai Allah sai kuma me ita idan yaso asani, Hmm nasan duk yanda zanmiki bayani bazaki gane komai yanzu ba amma nan gaba zaki tuna da magana ta kuma zatayi miki amfani, abu na ƙarshe kar kisanar  da kowa abun da ya faru yau daga ciki harda haɗuwar mu sau ɗaya nake haɗuwa da mutum idan na barsa na barsa kenan amma ke kin zamar min dole zan ƙara waiwayar ki ko badaɗe ko bajima bari ingaya miki abun da bakisani ba yanzuma zuwana nan bawai sa'a kikaci muka haɗu ba  a'a daman da shirin zuwan na fito saboda nadan halin da kike ciki shiyasa nazo dan na taimaka miki, itadai tunda yafara magana take sauraron sa takasa tanka masa sai dalla dalla takewa maganganun sa wasu tagane wasu kuma tarasa in da suka dosa, shima shiru yayi yana ƙara nazartar ta kafin daga bisani yace "KHADIJAH! Da sauri ta ɗago ta kalle sa ita duk a surutun sama datake jinsu kamar faɗar su kawai yake baisan me yake cewa ba babu wacce ta ɗaga mata hankali fiye da kiran ainahin sunan ta da yayi, Ganin yanda take kallon sa yasa shi sakin dariya harda sauti sannan yasakar mata hannu tare da miƙewa tsaye yace to ni loƙacin tafiya ta ya yi sai mun ƙara haɗuwa nayi farin cikin kasancewa dake yau ɗin nan sai nakejin dama kar natafi amma bazan iya kwana ako inaba batare da itaba da na zauna dake zuwa safiya, Duk dake ɗinma kin cancanci hakan kina buƙatar zamana tare da ku amma tafiki buƙatar hakan dake da ita duk ɗaya kuke aguna saidai kuma kinfita gata ahakan, da sauri itama Ameesha ta miƙe tana kallon sa, sai tace masa "wacece ita dan Allah kar katafi katsaya ka sanar dani waye kai kuma duk taya kasan abun da ya faru dani da kuma wanda zai faru dani kuma a ina kasan suna na dan Allah kar katafi kar barni da tunani kasanar dani waye kai? Ɗan murmusawa tsohon yayi sannan ya ce "waɗannan tambayoyi ai sunyi min yawa dan haka bazaki samu amsa ko ɗaya ba yanzu kidai bari akwai loƙacin da yakamata kisani ba yanzu ba, Na miki alƙawarin zan dawo na bada jimawa ba ki tanadi tamyoyin ki dana yanzu da waɗanda zaki samo nan gaba duk sai ki haɗasu waje ɗaya idan nadawo zan baki amsar ko wanne, kuka tasaka masa tace "dan Allah fa nace wallahi, zuciyata bazata taɓa kwanciya ba muddin baka gaya min ba, "Zata kwanta mana indai kinso hakan Hadizatul kubra kisa aranki baki ma taɓa ganin naba ki goge haɗuwar da mukayi arayuwar ki kafin nan kafin wani loƙaci ki manta dani ki fuskanci abun dake gaban ki, sannan abu da na manta bangaya miki ba kizama me dakakiyar zuciya duk wani abu dazai zo yafaru nan gaba kar kibari yayi tasiri a zuciyar bare har yayi miki illa akwai babban abun da zai taɓa miki zuciya nan gaba wanda baki taɓa jin irin taɓuwar ba to aduk loƙacin da hakan ta faru kituna da maganata ki saurin kawar dashi kar yayi tasiri a zuciyar ki in kwa bahaka ba ina mai tabbatar miki da zaki iya kamuwa da bugawar zuciya loƙaci ɗaya bari in baki wani abu... Jakar sa ya zuge ya zaro wani ɗan baƙin abu me kama da awarwaro amma na robane hannun ta yakamo ya ɗaura mata shi sannan ya ɗauko wanima yace "shima ki saka masa amma ba yanzu ba sai nan gaba kidai adana sa duk sanda kika samu damar naɗa masa sai ki naɗa masa, karɓa tayi tana jujjuya sa a hannu ta aranta tana tunanin ta ina zata iya saka masa a hannun wannan bauɗaɗɗan nutumin dandai baisan halin saba shiyasa yace haka, "Kar ki damu akwai ranar da zai yarda kidai adana sa kawai. Ɗagowa tayi ta kalle sa da mamaki ƙarara akan fuskar ta kardai yaji tunanin da takeyi anya kuwa wannan mutum ne to kodai bokane abun da take ta rayawa aranta kenan, Sarai yagane tunanin da take bayaso ya ƙara rikita tane shiyasa yayi shiru kawai bai tanka mata ba sai kawai yace "to ni natafi Allah haɗamu da alkhairin sa ki kula dashi sannan kar kiji tsoron komai babu abun da zai sameki daga nan har waye war gari da yardar Allah, Yana kaiwa ƙarshen zancen sa yayi gaba har yaje wajen ƙofa zai fita tayi saurin cewa bawan Allah baka gaya min sunan kaba saboda iringa tunawa dakai, juyowa yayi yasakar mata wannan murmushin nasa da yazame masa jiki, "Gashi nan kin faɗa shine sunana ai bawan Allah ne ni bani da kowa bani da komai dan haka sunan ma bandashi" ki kirani da bawan Allah ko kuma kice min mabaraci agurin Allah amma banda wani suna aduniyar nan ko kinga namiki kama da waɗan ake kiransu ni bana na haɗuwa da kowa bare aringa kirana idan naje kin gane? shikenan zan iya tafiya ko da kawai wata tambayar? Ahankali ta shiga girgiza masa kai tana binsa da kallo, hannu ya ɗaga mata yana murmushi ya fice daga gidan tare da jawo mata ƙofar falon...., Tunda ya fita take kallon ƙofar kamar shine awajen, Takai wajen mintina goma agun bata motsaba, Ahankali tafara maida duban ta ga Meer maganar da ta faɗo mata itace wai duk wata magana da zanyi inyi ta da wannan mutumin mutumin da ko kallo baka isheshi ba taya zata fara tunkarar sa tagaya masa abun dake damunta wannan impossible abun da bazata ta ɓa iyawa ba kenan, Kuma meyasa zai ce mata wanda yafi kusanci da ita bashine mutumin kirki ba agurin ta, Taya kuma wanda yake cin zalinta ya tsane ta ƙiriri ace wai shine ba muguba duk da ance mugu baida kama amma baza ta taɓa yarda da cewa Meer ba mugu bane shine abokin shawarar ta kai gaskiya wannan mutumin baifaɗi gaskiya ba, da sake,  A fili tace duk ƙarya yazo yake faɗa mun bazan yarda da maganar ka ba ko ɗaya inma bokane kai babu ruwana tana ayyana haka ta zare abun da yasaka mata a hannu ta haɗa da na hannun ta ta watsar dasu gefe, tana watsarwa ta samu kujerar kusa da Meer tayi zaman ta tana faman sakin tsaki aranta tana ayya na wa duk abun da yace tayi baza ta yi ba abun da kuma yace kar tayi to kwa sai  tayi baza ta ɗauki maganar saba ko guda ɗaya kamar yanda yace ta manta da shi to kwa zata manta dashi ɗin gaba ɗaya zatayi watsi da duk wasu ƙarairayin sa da ya yi mata, da sauri wata zuciyar tace to idan ƙarya yake taya akai yasan asalin sunan ki wata zuciyar tace to ba boka bane komai ma ai zai iya ganowa, da sauri wata kuma tace to koda bokanne ai zai iya gano koman ki na gaskiya shiyasa ya gano kuma ya faɗa miki dan haka yakamata kiduba maganar sa kar kiyi saurin yanke hukunci, da sauri ta miƙa tsaye tare da sakin tsaki tace ƙarya ne ƙarya yake ba zan taɓa yarda ba taya za ayi ma yace wai zan fuskan matsaloli nan gaba bayan kuma gashi yanzu ƙarshen komai yazo na samu dangina ina cikin su kuma meye zai zo yasame ne da ɗin ma dan banda kowa ne shiyasa na ɗan sha wahala amma yanzu komai yazo ƙarshe, zaka kawo min wata maganar banza, Wani tsakin ta ƙara ja a karo na biyu sannan ta ƙara miƙewa tsaye sai tana tashi sai taga kamar giftawar abu azubure ta juya sai kuma bataga komai ba maida dubanta tayi ga Meer ta ƙurawa fuskar sa ido sannan ta janye haka tayi zaune agaban sa tana jiran farka war sa, gaban ta taji yana tsanan ta faɗuwa ga kuma wani irin tsoron da tafara ji saboda ji take kamar da mutum acikin gidan, kusa da Meer ta koma sosai ta riƙo hannun sa tare da kifa kanta a kan damtsan hannun sa, so take tayi bacci ko zata dai na jin tsoron sa take ji, amma duk da haka kamar ma daɗuwa yake, Maganar tsohon ce ta ƙara faɗo mata loƙacin da yasaka mata abun hannun nan yace "kar ta cire zai taimake ta kuma babu abun da zai sameta daga nan har gobe da yardar Allah kar ta tsorata da zaman gidan da sauri ta tashi inda ta watsar dasu taje zata ɗauka sai taga baya gurin cike da mamaki ta shiga laliben inda ta jefar amma sama ko ƙasa ta rasa sa, Ba ƙaramin mamaki tayi ba na rasa shin da tayi a bun kuma ya fara bata tsoro sosai,  jiki a sanya ye ta tsugunna a gaban sa tama rasa wane irin tunani zatayi kwakwalwar ta, Ta kusan daina aiki gaba ɗaya koman ta ya tsaya tunda take bata taɓa haɗuwa da tashin hankali irin na yau ba, Ɗaga kan da zatayi ta hango abubuwan hannun a wajen ƙarƙashin kuje ra da sauri ta tashi taje wajen tare da sa hannu ta ɗauko su sai yanzu hankalin ta yaɗan kwanta da ta gansu sai tayi tunanin daman itace bata lura da kyau ba wajen da ta jefar,  Mayar dashi tayi hannun ta ɗayan kuma ta kama hannun Meer zata saka masa ta tuna yace kar ta saka masa yanzu dan haka sai kawai ta fasa saka masa,  Koma wa tayi  in da ta tashi ta kamo hannun sa ta kwanta akai tana kwanciya kuwa taji ta ɗan samu nutsuwa ta daina jin tsoron da take ji, bata daɗe da kwanciya ba wani nauyayyen bacci ya su lalo ya sureta....., Can cikin dare wajen ƙarfe huɗu da rabi Meer ya fara motsi da ƙafar sa daga can kuma sai ya fara  motsa idanun sa da sukayi masa nauyi, A hankali ya shiga buɗe su dishi dishi yafara gani kafin daga bisani suka idasa washe wa gaba ɗaya, Tar ya buɗesu akan fankar dake juyawa, ɗan lumshe ƙyawawan idanun sa yayi sannan ya buɗe su duk a loƙaci ɗaya jin kamar mutum akan sa yasa shi saurin maida idon sa gun da yaji nauyin,  A kan sumar kanta ya sauke idon sa tunanin ya shiga yi wai a ina ma yake da sauri kwakwalwar sa ta fara tariyo masa abun da yafaru tundaga farko har zuwa loƙacin da ya tuna sanadin tsayiwar sa a waje loƙacin ana ruwa da dukan da ruwa yayi masa har dai loƙacin da ya tsugunna agun yana karkarwa daga nan kuma bai ƙara sanin abun dake faruwa ba sai yanzu, tunanin ta ya a kai yazo nan ya shigayi bashi da mai basa amsa a halin yanzu dan haka ya kawar da tunanin ya ƙara kallon kanta  tunawa da roƙon da ya ringayi mata ta buɗe ƙofar taƙi ya shiga tunawa wani irin ƙato ton a bune yazo masa rai ya tsaya masa tare da jin haushin ta da tsanar yarinyar shi kaɗai yasan halin da ya shiga a loƙacin amma saboda bata da hankali taƙi buɗewa, da iya ƙarfin sa ya ɗaga hannun sa zai kai mata duka a kai sai yaji yakasa ɗaga sa hannun yayi masa wani irin nauyi da ya takurawa kansa ma wajen ɗagasa saida ƙashin sa ya bada sauti yace ƙas, saboda daɗewar da ya yi a kwance baya motsa su, Rufe idon sa ya ƙarayi tare da buɗe su jikin sa yaji gaba ɗaya yana yi masa ciwo so yake ya tashi amma bai san ta in da zai fara ba ga hannun sa da ta danne masa shima ciwo yake masa, ba yanda zai yi dole ya haƙura ya tsaya da ƙoƙarin tashin da yake son yi, Ahaka yaci gaba da zama loƙaci zuwa loƙaci yakan harare ta duk da baya kallon fuskar ta amma hakan bai hanasa ai ka mata da harara ba gashi ya manta sunan ta bare ma ya kirata ko zata tashi, kuma ya rasa da me zai kirata shiyasa kawai ya fasa yi mata magana, Yana zaune agun yajiyo kiraye kirayen sallah a Masallatai zaro manyan idanun sa yayi waje saboda tsabar mamakin da yayi kenan ahaka ya kwana ya akai haka ta faru yarinyar nan ta barsa ya kwana anan aƙasa, wani tunanin ne yayi saurin faɗo masa rai ya akai yaji sauƙi haka har ya iya tashi da kanshi kuma yagan sa ba a cikin asibiti ba alhalin duk ranar da ruwa ya taɓa sa baya dawowa cikin hayya cin sa da wuri sai yafi sati a kwance, Duk da bai fi sau biyar hakan ta taɓa faruwa dashi ba shima kuma tun yana yaro ne da girman sa kuma sau ɗata yataɓa ritsawa dashi ranar kuma yafi sati biyu bai samu lafiya ba to amma yanzu ace a rana guda ya dawo cikin hayyacin sa harma yana tunawa da abun da ya faru haka cikin sauƙi ba wata matsala, to ya akai hakan ta kasance waye kuma ya shigo dashi cikin gidan bayan a waje abun ya faru, yasan dai ba ta yanda za ayi wannan yarinyar ta iya jawo sa, a fili yace "hakan bazai taɓa yiyu wa ba zata min bayani, yana gama faɗar haka ya maida duban sa gare ta da ɗan ƙarfi ya ɗan ɗaga murya yace "keee....., shiru ba bata motsaba saboda yanayin da yake ciki yasa duk da ya ɗaga muryar amma ba ta fitowa sosai saida yayi mata wajen sau uku sannan ta ɗan motsa kanta ta gyara kwanciyar ta aƙasan capet ɗin ta ɗaga masa hannu, kamar tasan abun da yake so kenan ta ɗaga masa, Saidai kuma tana ɗagawar yaji hannun ma yafi da zafi ya sanƙame saboda daɗewar da tayi akai har yayi tsami sosai, Oh my God! Ya faɗa cike da gaji yawa da halin da yake ciki ya rasa yanda zaiyi da ƙyar ya iya motsa ƙafar sa, amma hannun dai har yanzu yakasa motsa sa, gashi har antayar da sallah amma yana kwance wannan shi kaɗai ne abun da yafi ci masa rai kenan, ba ƙaramin abu ne ba yake hana sa zuwa sallahr asuba amma yau gashi abun da yaɗauka ba komai ba ya zame masa komai tunawa da ya yi cewar halin da ya shiga jiya ma ai da tuni yanzu haka baisan ma duniyar da yake ba kamata yayi ma ya godewa Allah da yakawo masa sauƙi da wuri...., Haushi ne ya ishe shi ganin har yanzu tana kwance hankalin ta kwance yasa ya ƙara kiran ta da ƙarfi! juyi tayi fuskar ta ta dawo saitin sa suna facing ɗin juna saida ta fara yin miƙa saboda itama da ciwon jikin ta tashi saida ta gama miƙarta sannan ta shiga  buɗe idanun ta a hankali har ta idasa buɗesu gaba ɗaya.  Tana gama buɗewa suka sauka akan fuskar Meer maimakon ta janye idon ta, ta tashi sai kawai ta tsaya tana kallon shima itan yake kallo har saida yaga kallon nata yayi yawa sannan ya wurga mata harara tare da jan tsaki a hankali ya furta "mayya saidai kici kanki. Hakan da yayi mata yasa ta saurin janye idon ta akan sa sannan ta yunƙura da ƙyar ta tashi zaune tana hamma tare da yin wata miƙar azaune tana duban garin yanda ya ɗan fara yin haske hakan kuma ya tabbatar mata da safiya har tayi daɗi sosai taji saboda tunawa dole ya tashi su tafi da zarar tayi sallah, tunani ta shiga yi to shi ne yake agun akwance har yanzu da alamar ma ko sallah baiyi ba ko uban me yake jira da bai tashi ba oho masa, wani tsakin taji ya ƙara saki yana kawar da kansa gefe, da mamaki ta kalle sa a ranta tace masifaffe kayi ka gama kaci kanka ba kulaka zanyi ba, a fili kuma sai ta taɓi baki haɗi da miƙewa tsaye sanin bata da inda zata tayi alwala a ɗakunan yasa ta nufi kitchen direct taje can ta ɗibi ruwa sai ta fita ta ƙofar baya acan tayi fitsarin tayo alwalar ta dawo falon, Har yanzu yana inda ta barsa ko motsawa baiyi ba bata bi ta kansa ba ta fara tunanin  da hijabin da zatayi sallahr, Tsaye tayi taba ɗan dube dube ko zata samu amma bata ga komai ba sai mayafin da tazo dashi shi taje ta ɗauka akan kujera daman doguwar rigace a jikin ta kuma bata kamata sosai ba ga dogon hannu sai kawai ta yafa shi a kanta sannan ta hau kan Capet ɗin ta tayar da sallahr. Duk abun da take yana kallon ta yana jin taƙaici a ransa har ta idar tayi addu'ar ta ta ɗora da Azkar ɗin safiya ta ƙara yin wata addu'ar ta shafa, sai ta juya ta kalle sa tana juyawa suka haɗa ido maimakon yajanye saboda kamansan da tayi yana kallon ta sai kawai maze tare da harar irin ita yagani tana kallon sa, Ɗan jinjina kai tayi kawai sannan tace tace "ina kwana,  da sauri ya juyo yana kallon ta dan yayi mamakin wannan gaisuwar tata bai taɓa tunanin zata iya gaida shi ba, Itama anata ɓangaren batayi tunanin zai amsa ba sai taji yace "lfy daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba" So yake yace ta taimake sa amma ya kasa saboda yana gudun kar ta raina sa, da yayi mata maganar ta gwamma ce yaci gaba da zama a haka zuwa ɗan anjima ko zaiji sauƙin jikin sai ya tashi da kansa, Abunne yafara bawa Ameesha mamaki ganin dai har yanzu bai motsa ba sai ta ɗan tsorata da hakan ta fara tunanin kodai yakasa tashi ne tuna hakan yasa ta ƙara maida duban ta gare sa, sai tace "Kayi sallah kuwa? Ɗan juyowa yayi ya kalle ta baiyi magana ba har ta cire ran zai bata amsa ma sau taga ya girgiza mata kai alamar a'a, Ta ɗanyi mamaki kaɗan amma sai ta danne tare da miƙewa tsaye ta matsa kusa dashi daf dashi ta tsugunna sannan tace "me yasa, ko ka  kasa tashi ne? Yanzu ma kan ya kuma ɗaga mata kamar wani ƙaramin yaro, Sai taji ya bata tausayi abun da zai hanasa tashi kuwa ai ba ƙarami bane adain iya sanin da tayi masa namiji ne mai dauriya amma tunda ya faɗi haka kuma har takai ga ya kasa tashi to ba ƙaramin abu bane yake damun sa dole ka tausaya masa, Miƙewa ta tsaye ta kuma yi sai ta miƙa masa hannun ta, Hannun ya shiga bi da kallo har zuwa kan fuskar ta yana tunanin me take shirin yi taya zata iya ɗaga sa tama mayar dashi ƙaramin yaro janye idon sa yayi batare da yace mata komai ba kuma bai miƙa hannun na saba, Hannun tane ya fara ƙagewa da miƙa masan da take dan haka sai ta janye ta ƙara tsugunna wa a gaban sa tace katashi in taimaka ma kayi sallah, A hankali taji yana magana dan bata ma jin abun da yake cewa kunnen ta taƙara matsar wa kusa dashi tace me kace? "Baza ki iya ba nace" "Wallahi zan iya ta basa amsa" Shiru yayi baice da ita komai ba saida ya ɗauki loƙaci sannan yace "Bismillah ya faɗa tare da miƙa mata hannun riƙewa tayi tare da miƙewa tsaye ta shiga jansa amma ko motsi bayayi, in banda wata wahalar ma da take son ƙara masa babu abun da take da ta gaji sai ta saki hannun tana sauke numfashi kamar wacce tayi gudu, da yana dariya da babu abun da zai hanasa yi mata dariya yauɗin nan yanda take ta wani sauke numfashi ɗagasa kawai ɗaga warma da batayi ba amma wai ta gaji, Kamar wacce aka tsikara tayi sauri ta miƙi tare da nufar kitchen binta yayi da kallo yana mamakin ƙarfin hali irin nata yarinya ƴar ƙarama da ita sai tsaurin idon masifa ita yanzu kallon mutum take wa kanta, ta daɗe a kitchen ɗin baisan me take ba sai yaga ta fito ɗauke da roba a hannun ta yana kallon ta har ta ƙaraso inda yake ta ajiye robar da ke ta faman tiriri na ruwan zafin dake ciki, tana ajiyewa ta ƙara komawa sai ta fito da wani sabon towel da abayi amfani da shi ba, a gaban sa ta ƙara zama, Duk yana kallon ta baice mata komai ba dan yagane me take shirin yi kuma ya jinjinawa kaifin tunanin ta dan yana da buƙatar hakan, kamo hannun sa tayi ta ɗora akan cinyar ta sannan ta saka tsumman acikin ruwan zafin ta matse sai ta ɗaga hannun nasa tasaka shi akan tsinman ta fara ɗan mammatsa masa har zuwa wajen kafaɗar sa saida ta tabbatar da hannun ya gasu sannan ta koma ɗayan ma nan ma tayi masa ruwan yafara salan cewa dan haka ta ta shi taje ta ɗebo wani ta dawo taƙara yiwa ƙafafun su takan wandon jikin nasa take masa har wajen cinyo yin sa gaba ɗaya dai saida ta saka masa ruwan zafi a ko ina ta gasa masa  har wajen wuyan sa sai da ta ɗan daddanna masa, sannan tasaka hannu ta ta ƙara ɗan daddanna masa wasu guraren, saidai  kayan jikin sa duk sun jiƙi, Ba ƙaramin daɗin jikin nasa ba kwa yaji dan a cikin kaso ɗari kaso saba'in ya ragu dan har ya motsa hannun da ta gajiyar masa dashi, Hannun ta ya kamo da ɗayan hannun sa ɗayan kuma ya dafa kujerar da take gefen sa ya yun ƙura zai tashi amma sai yaji ya kasa, miƙewa tsaye tayi tasa iya ƙarfin ta da Allah yabata ga kuma shima yana ɗan ƙoƙarin tashin bai sakar mata duka nauyin saba a haka yasamu da ƙyar ya miƙe zaune, Sannu tayi masa, ya ɗaga mata kai yana ƙara gyara zaman sa da kyau sai ya jin gina kansa da jikin kujerar, 'Robar ta ɗauke tare da towel ɗin ta ƙara komawa kitchen ɗin, sai taƙara fito da robar ɗayan hannun ta kuma ɗauke da wani jug, ta ƙaraso gurin sa ta ajeye masa robar agaban sa tace "bari in zuba maka kayi alwala, hannun ya miƙa cikin robar ita kuma ta zuba masa ya fara wanke su kamar yanda akeyi dai idan za ayi alawala sannan ya wanke bakin sa hardai yagama duk wani abu da mutum zai yi idan zai yi alwala ya rage saura ƙafa sai ta dawo da robar wajen ƙafar tasa ta taimaka masa ya ɗaga ta wanke masa ƙafar sannan ta ajeye ta gefe ta ƙara ɗauko ɗayar ma tayi masa, "Bayan ta gama ta ajiye robar a gefe daga can baya sannan tace "ɗakin ka abuɗe yake ta tambaye sa tana kallon sa, batare da ya kalle taba ya ɗaga kansa, tashi tayi da sauri tafara hawa upstairs ɗin ta nufi ɗakin nasa, tana zuwa ta buɗe ta shiga ciki tafara duddu ba inda zata ga jakar kayan sa bata gani ba dan haka sai ta nufi drowar ɗin dake ciki ta fara bubbaɗe su har tayi karo da wata jallabiyar tare da wando aciki, hannun tasa ta ɗauko sannan ta fito waje loƙacin da tafito yana ta ƙoƙarin jajjan hannu wansa dan yaji sun ƙara saki ko yaƙara jin ƙarfin jin nasa, kusa dashi ta ƙaraso sannan ta ajiye masa agefen sa tace ka canza kayan jikin naka kar wani sanyin yaƙara shigar ka, 'kai kawai ya ƙara ɗaga mata ita kuma ta ɗauke robar da jug ɗin ta nufi hanyar kitchen dan tabasa damar shirya wa, tana tafiya yayi ƙoƙari yafara cire rigar sa ya saka jallabiyar sannan ya tashi ya zauna akan kujera ya cire wandon yasaka wanda ta kawo masa ya ajiye jiƙaƙƙun agefe, saboda ƙwarin jikin nasa da yaji  da azaune yayi niyar yin sallar amma da ya miƙe tsaye yaji shi ƙalau sai kawai ya tsaya da ƙafafun sa ya kalli gabasa ya tayar da sallahr, tana shiga kitchen ɗin ta ɗora masa  ruwan tea sannan ta fara tunanin abun da zata dafa musu, tunda akwai komai a kitchen ɗin gashi daman yunwa take ji jiya bata ci abinci ba ga kukan da tayi duk ya rarake mata ciki, da ta rasa abun yi sai kawai ta ɗebo dankalin turawa daidai wanda tasan zasu iya cinye wa tafara ferewa bayan ta gama ta sauke shayin ta ɗora mai akan wuta, ta juye musu tea ɗin a wani ɗan ƙaramin flask, kafin ta gama manta yayi zafi sai ta hau suyar dankalin tana bata daɗe ba ta gama saboda baida yawa, tana gamawa ta juye shi a flate sannan ta soya musu kwai shima ta ɗora akai ta ɗauko wani flate ɗin ta rufe ta samu babban faranti ta jerasu akai maimakon ta saka cup biyu sai tasaka ɗaya acewar ta idan yagama sai taci nata ita kaɗai, Yana zaune agun bayan ya idar da sallah har yayi Azkar baiga fitor ta ba yayi mamakin rashin fitowar tata da wuri duk da yana jin ɓurun ɓurun tunta kuma yana jin tashin ƙamshi amma haka baisa yayi tunanin ita take yin abun da yake ƙanshin ba yayi tunanin kodai na wani gidanne ya shigo ciki, saboda kallon da yake mata ko indome bazata iya dafawa ba, shiyasa baikawo abun da take a kitchen ɗin ba, Yana gun yana tunane tunanen sa ta fito ɗauke da farantin a hannun ta, tunda tafito yake kallon ta da mamaki har ta ƙaraso gurin ta ajiye agaban sa ta ƙara miƙewa ta nufi wajen dinning taje ta ɗauko kayan shayi ta dawo ta zauna a gaban sa bata ce dashi komai ba, shima kuma baice da ita komai ba kawai yana binta da kallon mamaki, Cup ɗin ta ɗago ta tsiyaya ruwan zafin aciki sannan tayi masa haɗi mai kauri bata cika masa siga da yawa ba saboda kartaje baya son zaƙi, Tana gama haɗa masa ta miƙa masa kallon ta ya tsaya yi batare da ya karɓa ba, da haka zaice mata bazai shaba sai kuma yayi tunanin idan yayi haka bai kyauta mata ba kuma daman yana jin yunwa dan haka yasa hannu ya karɓa yafara sha a hankali, buɗe masa dankalin tayi ta tura masa gaban sa, Ƙamshin da ya dake sane yasa sai yanzu ya yarda wai daman ƙamshin nan agidan yake, to ya akai yarinya ƙarama ta iya yin wannan aikin alhalin kuma inda ta taso ba wani babban gida bane bare ace ta koya anya kuwa zaiyi daɗi ba ƙazantar ta taje ta ƙwabo ba shayin ma dan a gaban sa ta haɗa masa amma da bazai shaba dan haka yanda ta turo masa haka shima ya tura mata shi gaban ta tare da cewa wannan ma ya isa kici kawai,  yayi hakane dan kar tayi tunanin wani abun, kallon sa tayi  cike da sanyin murya tace "me yasa baza kaci ba......, Ɗan ya tsuna fuska tayi yayi sannan yace "I'm not filling hungry" kasaƙe tayi tana kallon sa har ya idasa maganar sa bataji daɗi ba dan haka tace "ka daure kaci ko kaɗanne zai maka amfani da yunwa ajikin ka kana buƙatar sa, "Tom", yace kawai yaci gaba da shan shayin sa da baya jin zai iya ci kuma baya so su yi ta jan maganar shiyasa yace mata tom ɗin, sunkuyar da kai tayi tana jira yayi ya gama taja sauran taci saboda yunwar tafara damun ta, kuma ba bata iya ci dashi ba tasan ma hakan daman bazai yi yu ba, Har ya kusan shanye shayin bai kula dankalin ba da ta lura da hakan kuma tana kallon sa yana ɗan satar kallon dankalin amma bata san dalilin da ya hana sa ci ba ko bayar da da ita bane shiya sa bazai ci ba, A hankali ta ɗago dara daran idanun ta ta sauke sa akan sa murya ƙasa ƙasa tace baza kaci ba saboda kana tunani zan cutar dakai ne ko me, Batare da ya lalle ta yace "ko ɗaya" sai kuma yayi shiru,  Tashi tayi daga kusa dashi ta koma kan kujera ta zauna hakannan take jin haushin rashin cin da yaƙi yi kodan tana jiran sane yasa ta jin ba daɗi oho, Har ya shanye shayin tas ya ajiye cup ɗin ya gyara zaman sa ya miƙar da ƙafafun sa ya ɗan kishin gyaɗa ta ƙasan ido ya hango ta kan kujera ta haɗe rai sai faman turo ɗan kucililin bakin ta take, shi abun mamaki ma yabasa dan yaƙi ci shine take jin haushi, sun daɗe a haka babu wanda yaƙara cewa ƙala, tashi yayi daga kishin giɗar da yayi ya gyara zaman sa sannan ya jawo plate ɗin gaban sa yana kallo baya so tayi tunani marar kyau a kansa dan yaƙi ci kuma duba da yayi da ɗawainiyar da tayi dashi yau yakama yaci ko kaɗanne tunda har ta nuna son hakan, Hannu sa ya saka a ciki ya ɗauko ƙwalli ɗaya  tare da ɗan yagar dankalin yakai bakin sa, kamar me cin magani haka ya shiga tauna sa a hankali bayan ya cinye ya ƙara ɗauko wani maimakon ya ɗauki ɗaga yanzu sai ya ɗauko biyu saboda ya ɗan ji daɗin sa haka ya ringa ɗauka yana ci aransa niyar sa yaci ko guda biyar ne amma sai gashi ya ware yana ci yana taunasa cikin daɗin rai da kwanciyar hankali, Tunda ya fara ci take satar kallon sa ta gefen ido bata bari ta kalle sa ba gidan kar taje su haɗa ido ya daina ci, Shima kuma yana sane da ita yaƙi kallon ta yaci gaba da cin abun sa hankali kwance wasa wasa dai sai plate ya gani ya cinye tas batare da ya ankare da hakan ba, da yana cewa bazai ci ba gashi kuma ya cinye yanzu da wane idon zai kalle ta, Taɓe baki ya shiga yi yana ya tsina fuska kamar zai yi amai ɗagowa yayi da niyar yace mata me tasaka a ciki amai yake ji babu daɗi zuciyar sa sai tashi saboda kar tayi tunanin daɗi ne yasa ya cinye, saidai kuma yana ɗagowa da niyar faɗa mata sai kawai yaja burki da maganar tasa sakamakon hawayen da yagani kan fuskar ta ta sauko ƙasan kuje tare sai hawaye dake ziryar saukowa daga idon ta, Ƙame wa yayi yana kallon ta da mamakin me kuma yasa ta kuka haka harda su sauko wa ƙasa shi baima san loƙacin da ta sauko ƙasa ba, Badai haushin ta yaƙi cin abin ci ba yanzu kuma gashi ya ci kuma tana kuka, Tun tana hawaye kaɗai sai kuma ta fara fidda sauti harda su tura ƙafa gaba, mamaki bai gama kashe Meer ba saida yaga ta kifa kanta a ƙasa tana cigaba da kukan, Tunani ya fara to kodai aljanu take shirin tayar wa in ba aljanu ba mutum yana zaune kawai yasaka kuka batare da anyi masa komai ba shi baitaɓa ganin inda akayi haka ba, Daurewa yayi yace kee..! me ya same ki wani abunne ya cije ki komai, zaki sani a gaba kina min kuka ko na miki wani abu, tashi tayi zaune tana goge hawayen ta kalle sa da jajayen idanun ta da suka koma kalar na kuka ga majina da take taho mata tana mayar da ita, Hannu ya sa ya dafe gefen fuskar sa yana kallon ta shi har yanzu abun mamaki yake basa, ƙara nana ta mata tambayar da yayi mata a farko ya yi amma still bata basa amsa ba saida ta ɗauki loƙaci tana shashsheƙar kuka sannan cikin kuna tace "yunwa nake ji kuma nasha wahala nayi mana kazo ka cinye gaba ɗaya, tana gama faɗar haka ta ƙara sakin wani kukan saboda baƙin cikin da ga kuma taso mata taso taci tunda tayi take haɗiyar yawu daman arayuwar tana son dankalin turawa da ƙwai idan akayi agidan su Rasheeda har guziri take ta tafi dashi gida saboda son da take masa shiyasa ma da ta rasa abun yi ta yi musu shi  ko ɗanɗa nawa bata yiba saboda batason tajiyo daɗin sa tun kan tazo ci   saboda tasan bacci zaiyi da yawa idan yagama sai ta cinye gaba ɗaya to kuma gashi yanzu ya ɓata mata bojet  tana ji tana gani  a gaban ta ya cinye bai bar mata ko ɗaya ba, Tunda tayi maganar yakasa motsawa daga gun  ido kwa bai yarda sun haɗa ido ba saboda wata irin kunya ce ta kamasa wai abincin mutum biyu ya cinye shi kaɗai tabb akwai matsala yanzu bai san ma yanda zai yi da ita ba,  Sai yaji ta basa tausayi kuma ta basa dariya da tasan bata ciba ta kawo masa kuma harda jin haushi dan baici ba yanzu kuma yaci tazo tana masa tijara, kukan natane ya ishe shi sai ya kalle ta yace "me yasa baki gaya min ba, da kin gaya min ni ko ci ma ba zan yi ba, daman ni ai banyi niyar ci ba kece kika takura min naci abun ma da ko daɗi babu kinzo kinsa zuciya ta sai tashi take ni banyi kukan ba sai ke to wallahi ki min shiru tun kan ranki ya ɓaci a gunnan ni nace kibani, sai kiyi haƙuri kisha tea kawai ko kuma kije kiƙara yin wani bada akwai ba, yayi maganar yana haɗe rai waishi a dole kar ta kawo masa wani raini a ciki idan ba haka ya yi mata yasan baza su zauna lafiya ba dan ta fahimci yarinyar a kwai tijara yanzu sai tasaka masa ciwon kai, Jin maganar da yake mata kawai ta koma ta kwanta aƙasa taci gaba da kukan taƙaici biyu ya haɗar mata maimakon ya bata haƙuri amma shine zai rufe ta da faɗa duk abun da tayi masa bai gani ba ba sannu bare na gode saidai ma ya ƙara mata da wani laifin kuma ya hauta da masifa saboda shi ya kawo faɗa duniya, Duk yanda yaso ta tsoratar da ita tayi shiru amma taƙi yi, uzuri yayi mata saboda yarinya ce kuma yasan shine da laifi kowa akayi wa haka bazaiji daɗi duk da ba da sanan saba ya yi hakan, Abun da bai taɓa ba yau shi zaiyi tashi yayi da kansa ya nufi kitchen ɗin dan yi mata wani yasan duk abun da zai mata bazatayi shiru ba kuma yanzu halin da take ciki bazai iya dukan ta ba idan ma ya dake ta kukan sai yafi haka kuma babu yanda zai yi da ita ga bazai iya driven yanzu ba shiyasa amma da ɗaukan ta zaiyi su tafi gida shiyasa gwara ya bi da ita  a hankali su rabu lafiya, Tunda ya shiga kitchen ɗin yake faman sakin tsaki yake tunani yafara yi yama ake yin dankalin yasan tunawa yayi ashe fa sai an fere da sannan a soya tab zai iya kuwa, ji yayi ina bazai ɓatawa kansa loƙaci ba wajen yi juya yayi ya fice daga kitchen ɗin yana fita yaƙara hango ta har yanzu kukan take wani tsakin ya kuma ja sannan ya juya ya koma idan ma baiyi ba ransa zai ta ɓaci gwara yayi mata ya hutawa ransa, Da sauri yaje ya ɗebo dankalin tare knife ya fara fere sa yana ajiye wa akan drowar saida yafere wajen guda biyar da ya ajiye ya samu wani ɗan benci dake gefe ya zauna ya huta sannan ya tashi ya cigaba wajen guda ashirin ya fere sannan ya yayyan ka su yana yi yana zama ya huta agurin yankan kuwa saida ya ɗan yanke a hannun amma wuƙar bata shiga sosai ba, daman man da ta gama suyar dashi yana kan gas ɗin bata ɗauke ba dan haka sai ya kunna kawai baijira ya ɗau zafi ba ya antaya duka dankalin aciki ya koma kan bencin ya zauna yana jiran ya soyu ɗan jimawa kaɗan ya tashi yaje ya jujjuya sa yaga har yanzu bai fara soyuwa ba kuma baya tafasa, komawa yayi yaƙara zama bai daɗi ba ya ƙara dubawa still dai yana nan yanda yake, Wajen mituna goma yaga dai yagaji da zaman sai ya tashi ya leƙa ta yagan ta a zaune ta haɗa kai da gwiwa tana abun da take, komawa tayi gurin da yaga yana ta motsi sosai yana ta motsawa alamar zai soyu shikuma daman yaga ji da yaga haka sai kawai yayi tunanin ai yama gama soyuwa plate ya ɗauko ya fara kwaso shi daga cikin mai yana zuba shi direct akan plate ɗin ba wani jiran tsanewar sa kawai da man da komai yake zuba wa a kai, yana gama kwashe wa yakashe gas ɗin yaɗauki plate ɗin dankalin har zai fita sai kuma ya tuna ashe fa da egg ake cin sa a jiye wa yayi sannan ya nufi inda yaga crades ɗin suke yaje ya kwaso guda biyar yazo ya farfasa su ya zuba su a kwana nan da yaga ta yi amfani dashi, sai ya ɗauki maggi har guda uku ya zuba a ciki ya samu gishiri shima ya zuba da ɗan yawa ba laifi daidai misali amma a wajen sa albasa kuwa yama manta da batun ta ko ince ina jin baima san ana sakawa ba, ya kaɗa abun da gwanin kyau a ido yanda yake kaɗawa kai kace wani ƙwararren kukunne ga wani gumi da ya fara tsatstsafo masa na wahala, man da ya soya dankalin ko ince ya gasa dankalin baiyi tunanin ya juye saba ko kuma yarage a'a kawai shaka ya watsa kwan duka a ciki bayan ya zuba yayi kwance aƙasan man sannan ya kunna gas ɗin, ya zuba masa ido yana jiran ya fara tafasa ya soyu kamar dankalin abun da ya basa mamaki sai yaga wai har ya fara tafasa bai ba kamar yanda dankalin ya ɗauki loƙaci ba, daɗi ne yakama sa da yaga yana ta ƙara kunburowa mai na shirin zubowa yana ganin haka yayi saurin kashe gas ɗin sai da ya jira man ya ɗan lafa sannan yasaka ludayin ya fara ɗibo sa sai yayi mamaki gani duk ya dagar gaje bai haɗe jikin sa ba ba kamar yanda ta kawo masa ba, sai yabar hakan kawai azin soyuwa yayi da yawa shiyasa ya dagargaje tsamosa yayi tsaf gaba ɗaya ya ɗora sa akan dankalin sannan ya ɗauki plate ɗin ya nufi hanyar fita dashi, saida yaje bakin ƙofar sai ya tsaya yana ƙarewa abun kallo yadai san shidai a ido ba kamar haka yaci ba ɗazu amma yana da tabbacin dai haka ake, ƙara kallon sa yayi sai yaji wani irin daɗi ya ziyar ce sa wai shi yayi wannan gaskiya yayi namijin ƙoƙari saidai bayajin zai iya ci saboda ya dafa sai yaji duk ya haumasa kai(hmm daman idan ƙwaraiwa tayi ƙwaraiwa ai mutum baya iya cin abincin da ya girka musamman idan yayi kwaɓa irin taka, gaskiya Meer kaban kunya duk wannan iyayin ba a iya komai a kitchen ba daman,🤔😁😁) A hankali ya shiga takawa cikin falon ya doshi inda take har yaƙarasa gaban ta sannan ya tsaya, bata ɗago ba tana kan gwiwar ta bataji zuwan saba sai wani nannaɗaɗɗen ƙarni da ya nannaɗe yashiga ya lallaɓa ta ƙasa ƙafar ta ya dakar mata hanci da ƙarfi, hakanne yasaka ta ɗagowa da sauri ba shiri dan ganin abun da yake neman saka ta amai......, Ido biyu tayi da dankalin da yake miƙo mata, sannan tabi hannun sa da kallo har zuwa kan fuskar sa sannan ta ƙara mayar da kallon dankalin da a ido ma baida kyaun gani kana gani kaga ɗanyan abu babu alamar soyuwa ko ɗaya, Gajiya yayi da tsayiwar har yake jin kamar ya ajiye mata amma ganin kallon da takewa abun sai yayi tunani ko burgeta yayi tayi tunanin ƙoƙarin da yayi, Hannu tasa kamar zata karɓa sai kawai ta fasa ta miƙi tsaye tana kallon sa tace meye wannan? Da mamakin rainin hankalin tambayear da tayi masa haɗe rai yayi sosai sannan yace "Idon ki me yagane miki, Ta manta da kukan da take bata san loƙacin da ta tuntsure da dariya ba ai saikwa ta hau ƙyalƙyala dariya tana kallon sa waishi nan da gaske dankali ya soya tana kalla sai ta ƙara fashe wa da wata dariyar kamar sabon kamu, hannu takai zata karɓa ya janye haushi ya kamasa tama mayar dashi mahaukaci ya sha walaha yayi mata abu kuma tazo tasa shi agaba tana masa dariya ko taga wani abun na dariya ajikin sa, ko kuma abun da yayi ne yabata dariya oho mata, Ameeaha fa sai an kawo ɗauki ta tafi sai dariya take harda su riƙe ciki ita ƙwanne ma yafi bata dariya yanda yayi wani wara wara kuma tana kalla ta fahimci acikin mai ya zuba sa, shiyafi komai bata dariya ashe duk burgar tasa bai iya girki ba sai iya dukan mutane, Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska...........✍️✍️✍️ tofa team ɗin Meer a kawo taimakon gaggawa a koyawa Meer girki kar raini ya shiga tsakanin sa da Ameesha dan naga alamar bazata ɗaga masa ƙafa ba wajen dariyar nan tata, To fa ga kuma bawan Allah ko waye wannan tsohon da yazo gurin Ameesha taya akai yasan ta haka to kodai bokanne kamar yanda Ameesha take zato, Amma dai muje zuwa muji shi kuma dame yazo, *_to ya kuka ga wannan page ɗin da aringayin irin sa da kuma aringayi kullum duk ƙanƙantar sa wane kuka fi so???????_*                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                         🅿️ 99 ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ ____Haushi da taƙaici da ya ishe shi da dariyar da take masa yasa ya ɗaga plate ɗin hannun sa ya kifa mata shi gaba ɗaya a fuska..........., ___Ɗif tayi da dariyar da take masa ta fara ƙif ƙif da ido gudun kar ya shigar mata ido, take fuskar ta tayi dama dama da mai kamar a fuskar a ka soya ƙwan, duk da taji ƙarni kuma taji haushin kifa matan da yayi a fuska, amma itama dan ta ƙara masa wani baƙin cikin sai kawai tasake fashewa da dariyar ta ciga ba da yi masa dariyar, Hannu ya ɗaga zai kai mata duka tayi saurin gocewa ya daki iska, ƙwafa yayi cike da ta ƙaici yana hararar ta yana kallon dankalin dake zube a ƙasa yana ƙara jin wani irin haushi na taso masa yanzu yarinyar nan dan ta gama ci masa mutun ci ya sha wahala ya dage ya taƙaƙƙare ya zuba basirar sa yayi mata amma yanzu shine zube a ƙasa gashi kuma taso tasa shi gaba tana masa dariya, dan tagama rainasa to kwa wallahi bata isa ba sai ta cinye sa tas duk da ya zuɓe a ƙasa sai taci sa da haka dan bazai yi wahala aban za ba, Tana tsaye daga ɗan nesa dashi tana dariyar ta tana toshe baki bata ankara ba taji ya fisgota ta faɗa kansa saura kaɗan ta faɗi tayi saurin rirriƙe shi, hannu yasa ya ƙara riƙota da kyau kamar abun arziƙi a haka ya rungumo ta suka zauna a ƙasan gurin sannan ya rabata da jikin sa ya zaunar da ita agaban sa, Yunƙurin tashi ta fara yi yayi saurin riƙe ta ya miƙar da ƙafafun ta sannan ya ɗora nasa a kai ya danne su, sannan ya haɗa hannu wanta gaba ɗaya biyun ya riƙe su da hannu ɗaya ya matso da ita gaban sa sosai yanda ba yanda zata tayi ta tashi sannan yasa ɗayan hannun sa ya ɗebo dankalin tare da ƙwan ya matso dashi wajen bakin ta, Cike da zaro ido ta fara girgiza masa kai tare da rufe bakin ƙam yanda bazai iya saka mata, dodana mata shi ya shigayi a bakin amma yaƙi shiga saboda ta rufe bakin ƙam, haɗe rai yayi ya harare ta yace wallahi idan baki buɗe ba ranki zai ɓaci ba yunwa kike jiba nace kije kiyi kinƙi saurara ta kuma yanzu kinsa naje nasha wahala nayi kice bazaki ci ba wallahi baki isaba sai ki cinye sa, Kuka tafara yi tana girgiza kai aranta tana ayyana taya zata iya cin ɗanyan dankali ita bana rashin soyuwar ne ma yafi damun ta ba ƙarnin ƙwan shi yafi ɗaga mata hankali, gashi tana so ta buɗe baki ta bashi haƙuri kuma tana tsoron kar ta buɗe ya danna mata shi, Duk yanda yaso ya da tura mata taƙi buɗewa sai kokawa suke tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, da yaga dai abun nata ba easy sai kawai ya ajiye dankalin a ƙasa ya sakar mata hannu, Nan tasamu damar buɗe bakin ta ta shiga basa haƙuri da yi masa magiya amma ko kallon ta baiyi ba sai ya ɗauko mayafin ta ya ƙara haɗa hannun nata duka biyu ya ƙulle mata hannu wan dashi sosai ya ƙulle yanda bazata iya kuncewa ba, saboda zafin da taji harda hawaye, Ƙara jawo ta yayi yasa hannun sa ɗaya ga matsa mata bakin har saida ya buɗu sannan ya sa ɗayan hannun ya ɗebo dankalin dan mugun ta ciki hannun sa yayi dashi ya nufi bakin ta dashi, Duk yanda taso ya kwacewa shigar dankalin bakin amma hakan ya gagara saidaya danna mata shi abaki, ƙin taunawa tayi, yace wallahi ko ta tauna ko yasa ta haɗiye shi ta dole, Ba yanda ta iya haka tafara taunasa garas garas saikace ɗanye tana taunawa tana jera masa Allah ya isa tafi cikin kwando kuma tayi alwashin wallahi bashi yaci dan sai ta rama, inda Allah ya taimake ta ma bai haɗa mata da ƙwanba iya dankalin ne, tana hawaye saida ta gama taunesa tsaf, sannan yaƙara ɗebo mata wani yanzu kam har da ƙwan ga haɗo mata ƙwan ma kuma yafi yawa haka shima ya danna mata shi yace "oya cinyesa yanzu nan ai baima gama maganar sa ba tayi saurin furzar dashi tana kallon tace "wallahi bazan iya ciba dan Allah ka rabu dani ba cikina bane me yasa kake son yi min dole inci abun da kwata kwata babu daɗi kuma wanna kwan gishiri da maggi yayi yawa wallahi bazan iya ciba, kuma kaci gaji ga uban ƙarni da yake baka sa albasa ba Allah kuwa bazan iya ciba saidai ka kashe ni........, Bam taji a bakin ta yasa hannu ya buge mata baki, Saida tasaki ƴar karamar ƙara sakamakon zafin da taji ga ya ƙulle mata hannu bare ta shafa wajen, Bai dadda raba ya ƙara ɗebowa ya cusa mata shi a baki ta ƙarfin tsiya sannan ya toshe mata bakin ta yanda bazata iya fito dashi ba, Maggi ne da yaji suka zagaya mata baki take taji zuciyar ta ta hargitse amai ya taho mata duk yanda taso ta riƙe sa abun ya gagara saboda yazo mata wuya, yana sakin bakin kuwa tashiga kwarara amai, yanda yayi ɗaiɗai da ƙafarsa ya danne ta haka aman nan ya wanke masa jiki gaba ɗaya akan rigar sa ta kwararo sa agaba ɗaya rigar jikin sa, Damƙe idon sa yayi jin zubar amai ajikin, aransa kuwa nanata kalan man anan yake "amai amai ajiki na tabbb wannan yarinyar ta tagama dashi shida ko jin ana amai ma baya so yau shi akayiwa amai ajiki, tana gamawa ta fara maida numfashi bazato ba tsammani taji ya ɗauke ta da wani irin gigitaccen mari har guda biyu, take jinra da ganin ta suka ɗauke saboda aman da tayi da kuma ƙarnin da yaje samun ta taje taji wani irin zazzaɓi ya fara ziyar tatta da kwa yaƙara mata da mari take ta sume awajen, tayi gefe zata faɗi yayi saurin riƙo hannun ta sai kuma yaji tayi nauyi jikin ta ya saki gaba ɗaya, tsaki yana yasake ta saboda ya gane sume masa tayi, tashi yayi yana me ƙenƙamin jikin sa ji yake kamar ya cire duk jikin sa, haka yake ji duk ya tsani kansa, Tsaye ya miƙe yana so ya cire rigar amma yana tunanin ta inda zai fara saboda idan ya ɗaga ta zai taɓa masa fuska shikam bazai iya jurar hakan ba, da yarasa yanda zaiyi kawai sai ya ɓalle bottel ɗin jallabiyar ya kama tsakiyar ta da iya ƙarfin sa yajata Ya yaga  Tsakiyar ta tunda ga sama har ƙasa ya keta ta ya cire yayi wulli da ita gefe,sannan ya zare dogon wandon ma  ya rage daga shi sai gajeran wando shima na ciki skintight irin na maza da suke sakawa ta ciki kafin su ɗora gajeran wando, wajen fridge yaje ya ɗauko ruwa me sanyi, yazo ya yayyafa mata kaɗan bata motsaba, saida ya sharara matasa bakin robar sannan ta kawo numfashi me nauyi, a zabure ta miƙe zaune saidai idon ta nayin ido biyu da santaleliyar surar jikin sa ba kaya, take ta haɗiye wani yawu me zafi da ya haddasa mata wani suman batare da ta shirya hakan ba ta tafi luuuu ta koma inda ta taso, Mamaki ne ya kamasa ganin ta ƙara sumewa yana tunanin anya kuwa lafiyar ta ƙalau ita abun suma baya mata wahala, tsaki yaja tare da wucewa upstairs yaje ɗakin sa ya ɗauko wasu kayan ya saka ya fito yana tafiya yana sakin tsaki, saida yazo daf da ita ya ɓalla mata wata uwar harara yaje inda ya ajiye muƙllin motar ya nufi hanyar waje har yaje bakin ƙofa ya tuna idan ya koma gida ba ita yasan dole sai an tuhume sa akan hakan, tunanin hakan yasa shi dawowa da baya ya ƙara ɗaukan ruwan ya watsa mata a fuska wani sanyayyen numfashi ta sauke saidai taƙi buɗe idon ta dan tana farkawa taje surar jikin sa ta sake faɗo mata duk da ta rufe ido amma bata daina hango ta ba a idon ta ƙara ƙanƙame idon ta tayi tana so ta manta da abun da tagani amma hakan ya gagara,  Har ɗan leƙen fuskar ta yake yana mamakin abun da take shi tsoro ma ta ɗan basa har yafara tunanin to kodai aljanune da ita, ɗan dakewa yayi, sannan yayi gyaran murya, yace "ke meye haken kike kitashi mutafi ko inyi tafiya ta, "wallahi bazan buɗe ba bana son ganin ka ahaka Please dan Allah katafi ka matsa daga kusa dani, tana faɗa tana sake rufe ido tana girgiza kai, wani dogon tsaki yaja jin batun da take sai yanzu yagane dalilin suman nata tab aikwa tana ruwa zata mutu watarn kenan idan taga me duka lol 😂 injini fa ba inji saba ah to, Haushi da taƙaici yasa yarasa mema zai ce mata, dan ta bashi haushi, wani tunanin ne ya faɗo masa to kodai shatin alulun sane shiyasa ta tsorata saboda skintight ɗin babu abun da baya fito dashi, tuna hakan yasa yaji yafara jin haushin kansa me yasama tun wuri baiyi wannan tunanin ba bai saka kaya ba ya tashe ta, gashi yanzu taga girman sa shikenan wataƙil ta samu damar rainasa, ji yake kamar yayi hauka ya akai yabari haka ta faru, cije bakin sa yayi tare da furzar da iska me huci sannan ya sa hannun ya fara shafa sumar kansa yana me ƙara jin wani taƙaicin, tsaki ya kuma ja cikin sarsarfa ya juya mata baya sannan yace "idan kinga dama ki kwana anan banda loƙacin ki yana kaiwa nan ya ƙara gaba ya fice, A hankali ta buɗe idon ta suka sauka abayan sa loƙacin yana daf da fita daga cikin falon, da sauri ta miƙe zaune ganin da kaya ajikin sa yasa tayi saurin tashi tsaye, saida ta bari yagama fita daga ciki sannan ta biyo bayan sa loƙacin da ta fito har yaje bakin motar yana ƙoƙarin buɗewa, sauri ta ƙara gudan kar taje ya tafi ya barta shiyasa ta fara sauri harda ɗan gudu gudun ta, yana shiga ciki itama ta buɗe baya ta shiga, yana jinta amma bai ce mata komai ba kawai ya kaɗa kansa tare sa tayar da motar yajata zuwa bakin gate ɗin sannan ya fito, ya buɗe ya fitar da motar ya ƙara fitowa yaje ya zuge gate ɗin sannan ya shiga ya tayar suka ci gaba da tafiya...., Tunda suka fara tafiya ba wanda yayi magana acikin su kowa da abun da yake tunani, Sun ɗan fara nisa da tafiyar batare da ya juyo ya kalle ta ba, ta cikin madubi ya kalle ta yaga yanda fuskar ta take maiƙo gaba ɗaya tayi dama dama mamaki yayi ita ko damun tama bayayi, murya can ƙasa ƙasa yace "ki samu abu ki goge fuskar nan kuma wallahi idan mukaje kika faɗi abu ɗaya ma zaki yanda zanyi dake, tajisa sarai amma saita murguɗa baki tare da basarwa irin bataji me yace ba, jinta shirua yasashi ƙara maimai tawa yace "ko baki ji me nace, sai tayi sauri ta ɗago tace "wai magana kake, girgiza kai kawai yayi saida suka ɗan ƙara tafiya sannan ya ƙara maimaita mata, sai kawai tace ina ruwanka ko fuskar kace yanda ka watsa min ahaka zanje gida innunawa maama kuma ince kayi min dukan tsiya, sai tayi ƙasa da murya yanda bazai ji taba tace kuma ince baka iya girki ba kayi  kwaɓa da jagwalgwalon ka ka turamin shi abaki dan mugunta, Allah ya taimake ta baiji abun da tace ba da ya sassama ta amotar yadai ji tana magana amma baiji me take cewa ba, girgiza kai kawai yayi yaci gaba da yafiyar sa kamar ma bazai bata amsa ba sai can dai yace "mu zuba mugani dan kinga bantaɓa ki ba ko tara ki nake wallahi na kamaki sai kin gwanmmace dama baki san wanda yassanni ba bare kuma ni harkiyi min abun da kikaga dama yanzu dai kinci sa'a na ɗaga miki ƙafa amma ki kiyayi haɗuwar nan gaba, am telling you that kiriƙe wannan, tundaga nan yayi shiru bai ƙara magana ba, duk da yana jinta tana ƙara wasu maganganun ƙasa ƙasa amma bai kula taba suka ci gaba da tafiya, har suka ƙaraso masarauta, suka shiga ciki loƙacin da suka dawo gida goma na safe saura, dan haka yana tsayawa da motar ko parking bai gama daidai tawa ta buɗe motar ta fita tare da kwasa aguje ta nufi part ɗin maama, da kallo kawai yabita yana jinjina irin wannan halin nata na yarinta zallah, shima buɗewa yayi yabi bayanta cikin takun sa na kamala da kwarjini duk wanda ya haɗu dashi a hanya sai ya zube ƙasa ya gaida shi tare da yi masa kirari shikam baso yake ba dan haka babu wanda ya iya amsawa har ya ƙarasa cikin falon baiyi sallama ba ya faɗa ciki kansa tsaye, tundaga bakin ƙofa yake jiyo sautin kukan ta, yana shiga yaganta jikin ummy tana ta kuka, Ummy ce tace zo nan tafa ɗa tana kallon sa ƙarasawa yayi kujerar gefen ta ya zauna, yana hararar Ameesha ta ƙasan ido, Ummy tace "ka kyauta abun da kayi me kayi mata, kallon ummy yayi ya maƙe kafaɗa yace "babu" Ummy tace ƙarya kake ba abun da kayi mata naga fuskar ta haka gashi takasa magana sai kuka take meye ma dalilin ka na ɗaukar ta katafi da ita kuma kabar wayoyin ka anan sannan kuma kaƙi dawowa gidan, kuma yanzu ana tambayarka zaka wani ce ba komai, ransa ne ya fara ɓaci bare da ta kalli taɓa yace to idan nayi mata wani abun ai gata nan kitambaye ta mana, rashin dawowa kuma kinsan dai ana ruwa bazan taɓa fitowa a wannan loƙacin ba, yana faɗar ransa yana ƙara yi masa suya tunawa da halin da tasa ya shiga jiya har ruwa yayi masa duka awaje gashi kuma yazo gida ana neman yi masa faɗa ta ƙaicine ya ishe shi kawai ya miƙe daga gurin ya nufi ɗakin sa yana ji ummy tana yi masa magana amma yaƙi dakatawa saboda halin da yafara tsintar kansa komai ma zai iya faruwa idan bai nesa dasu ba, Ameesha ƙasa ƙasa ta fara yi da kukan nata jin abun da yace saitaji yabata tausayi gashi bai faɗi gaskiyar abun da ya faru ba idan hakane ma ai ita ya rufawa asiri ashe su baya a son ruwa ita da kuma ga abun da tayi masa tasana din tama da tuni ya rasa ransa badan ta wannan tsohon ya taimake shi ta ba, A hankali ta shiga goge hawayen ta sannan ta miƙe daga kan ummy tana shirin barin wajen ummy ta ƙara riƙo ta tana tambayar ta tagaya mata abun da yayi mata sai kawai itama tace mata ba komai, tana faɗar haka itama ta wuce ɗakin su ita da dadda, Da kallon mamaki ummy ta shiga binta tana tunani me take nufi to da ba komai tasan dole yayi mata wani abun tunda har tashigo tana kuka, gashi kuma taƙi faɗa to meke faruwa ne dasu gaba ɗayan su dan ta fahimci dole akwai wani abun da yafaru tunda taga shima ransa a ɓace har tana masa magana ya shareta tasan ba ƙaramin abu bane zaisa shi yi mata haka, tana zaune agun tana tunane tunane maama ta shigo falon da sauri, Miƙewa ummy tayi tana kallon ta tace maama lafiya dai ko an samu inda take, cike da damuwa maama tace a'a wallahi babu inda ba aduba ba kuma me gadi yace baiga fitar taba, abun ya mugun ban mamaki wallahi, ummy tace tofa gaskiya abun dole ayi mamaki kai kai abun yayi yafara yin yawa daga wannan matsalar ta lafa sai kuma wata ta kunno kai gaskiya da sake yakamata asan abunyi, ga waɗan can yaran ma sun shigo yanzu, Maama tace sai yanzu suka dawo lafiya dai ko ba abun da yayi mata, me ya hanasu dawowa? ummy ta ɗan kwaɓe fuska alamar damuwa atare da ita tace wallahi dai gasunan sun shigo shi ransa aɓace ita kuma tana kuka kuma duk na tambaye su me yafaru kowa yayi cemin ba komai sun shige sun barni a wajen, Maama tace to Allah ya kyauta Allah yasadai lafiya, yanzu dai kar ki bari yarinyar nan tasan kakar ta bata nan abari zuwa anjima idan ba aganta ba sai asanar da ita, ki bata kulawa yanzu dai mai martaba ya ƙara sawa a bincika, Da to ummy ta amsa mata sannan ta samu waje ta zauna tana me mamakin ɓatan dadda abu kamar almara lafiya suka tashi amma ace aɗan loƙaci ƙanƙani anrasa inda ta shiga sai kace allura, Fita maama ta ƙarayi waje dan takasa zaune takasa tsaye, Meer ne ya ƙaraso falon kusa da ummy yazo ya samu waje ya zauna murya can ƙasa yace ummy waye ya ɓata, Ummy ta kalle sa cike da damuwa tace wallahi dadda ce muna zaune anan gaba ɗayan mu tace bari ta ɗan shiga cikin gidan shiru shiru muka ga bata dawo ba shine fa aka hau neman ta tode yanzu zancen da nake maka anne me ta anrasa acikin gidan nan kuma me gadi yace baiga fitar ta ba, Ɗan taɓe baki yayi baice komai ba batare da yaji ɗigon damuwa aransa ba, ya daɗe agurin a zaune kafin daga baya ya tashi ya fice daga, cikin falon wajen masarautar ya fito tare da harɗe ƙafafun sa ya nade hannun sa akan ƙirjin sa tare da cije bakin sa leben ƙasa yana karkaɗa kai, ya daɗe agurin yana ta bin mutane gurin da kallo ɗaya bayan ɗaya, wani dogari ne yazo wucewa, sai ya ɗaga hannun ɗaya yayi masa alamar yazo, Da sauri dogarin ya ƙaraso gurin sa tare da zuɓewa agun yana gaida shi sai ya ɗaga masa hannu, batare da ya kalle saba yace inason kasamo min kujera ka kawo min nan gurin sannan kacewa kowa da kowa yazo ina son ganin sa, Da sauri ya miƙe yace angama ranka ya daɗe maganar ka kamar yankan raiza ce, ko mutanen garin kake son gani yanzu zaka gansu agaban ka..... Wani wawan kallo ya watsa masa da yasa yayi saurin haɗeye maganar sa yajuya ba jimawa sai gashi ya kawo masa wata kujerar ƙarfe me kyau, sannan ya ƙara komawa kan kace me gurin yafara cika da mutane wasu kodan su gansa sazo musamman matan gidan, dan da yawa ya tafi da imanin su, wasu tun daga nesa suka mayar dashi tvn su har suka karaso gaba suka zauna, Dai dai da me gadi ba abari ba saida aka kirasa kowa ya hallara agun, duk yawansu kuwa gurin ya yi tsit baka jin motsin komai kowa ya kama kansa gudun jawa kai bala'i dan sunji labarin sa baya ɗaukan raini, yanzu zai canza maka kamanni da duka, duk abun da ake yaje kunnen papa dake part ɗin Ammah dan haka bai dakatar dashi ba duk abun da zai yi yasan bazaiyi ba daidai ba, ba papa kaɗai bama har su ummy da maama ba wanda baiji ba kuma babu wanda yayi yunƙurin da katar da shi ko tambayar sa dalilin sa na haɗa wannan taron, su Amra ma anfito kallo Azeema taje ta kirawo Ameesha suka samu waje daga ɗan gefe suka zauna suna kallon sa musamman ma mutuniyar tasa Amra da har ta manta da haushin nasa da take ji na jiya, kowa dai yana gurin yara da manya maza da mata, su waziri ne da matayayen su kaɗai basa gun, manyan dai gidan, sune basa gun, Saida Meer yagama ƙare musu kallo gaba ɗayan su sannan ya gyara zama tare da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sannan yace tsofaffi su ware gefe tsofaffi mata da maza su ware gefe takan su zai fara, da sauri kowanne su ya tashi suka koma inda ta nuna musu kowanne zuciyar sa cike da zullumin abun da zaiyi musu suna tunanin laifin da suka aikata, Dorinar hannun wani dogari yace abasa har guda biyu ya karɓa ya haɗa su waje guda, Miƙewa tayi daga inda yake ya taka yake gaban tsofaffin ya shiga zagaye su yana karkaɗa bulalar a hannun sa sai ya yi kamar zai ɗagata ya sauke akan wani sai ya fasa, saida yagama ruɗasu duk suka sha jinin jikin su tunkan aje ko ina, ga mamakin su sai kawai ya shiga binsu da ita yana sauke ta akan kowa duk wanda ya samu zuba masa yake saidai ba wani dukan su yayi sosai ba ya dakata, sannan ya kalle su yace wannan ɗan tuni nayi muku ba wai hukunci ba, abun da nake so daku shine kafin inje indawo kowa yagama haɗo min labarin abun da yasani game da cikin gidan nan saboda kune manya nasan kundaɗe a cikin ta kuma kunsan komai dan haka nake gargaɗin kada wanda ya sake yayi min ƙarya kuma game da matar da ta ɓata ɗazuna nan shima inason jin wani abun daga gare ku, ina mai baku shawara mutum ya faɗi gaskiya ya zauna lafiya, yana gama faɗar haka ya juya gurin sauran, yace a rakani part ɗin waziri take kowa ya miƙe zai rakasa ya daka musu tsawa da cewa baku da hankali ne da zaku miƙe dukan ku, dukan su komawa sukayi suka zauna, Sai ya nuna wani namiji me ɗan jiki yace "muje, da sauri ya miƙe yayi gaba shikuma yabi bayan sa, har yafara tafiya ya juyo yace "kar wanda yabar gurin nan kuma kar wanda yayi magana daga nan har naje na dawo, yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya.........✍️✍️           ***********************                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent) [27/12, 7:53 pm] #yaya Azeema#:   ❤XEEMAT___LOVE❤ 💅SARKI SAMEER...💅              (wasa farin girki)                   💖*the talent troupe writer's*💖                  *Book 2*          *sarki sameer book two na kudine kabiya ka karanta cikin salama kar ka karantan littafi idan baka biyani hakkina ba dari biyu ne 200  bantsawwalaba, ga mai bukata ga account number 8124226526 AZIMA AMINU DAHIRU opay bank sai kuturo da shaidar biyan ta nan 08124226526*                      *The last of book 2* ✨الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر✨✨ ✨بسملله الراحمن الرحيم✨✨ Bismilah............✍️ Sai ya nuna wani namiji me ɗan jiki yace "muje, da sauri ya miƙe yayi gaba shikuma yabi bayan sa, har yafara tafiya ya juyo yace "kar wanda yabar gurin nan kuma kar wanda yayi magana daga nan har naje na dawo, yana kaiwa nan yaci gaba da tafiya........, Har part ɗin suka ƙarasa loƙacin da suka ƙarasa bai wani jira cewar abada izinin shigaba ya canza fuska ya haɗe girar sama da ta ƙasa sannan ya danna kai ciki direct, yana shiga babu manya a falon sai wata yarinya tana ganin sa ta shiga wage baki tana nufowa inda yake ba yanda ya iya dole ya ɗan sasauta fuskar sa ya miƙa mata hannu ya riƙe nata sannan yajata suka zauna akan kujera surutu ta shiga yi masa yana biye mata wani abunma baya gane me take cewa saidaga baya cikin wasa yace mata mamanta tace masa tana ɗaki yace to jeki kira min ita, da gudu ta sauka daga kan kujerar ta nufi ɗakin mahaifiyar tata bata wani jima ba suka fito tare yarinyar akwai surutu, mahaifiyar tata na fitowa tana ganin sa ta saki fuska fuskar ta ɗauke da murmushi ta ƙarasa kujerar gefen sa ta zauna tana kallon sa, shikam inbanda haɗe rai da ya ƙarayi babu wata alamar raha a fuskar sa, murya adake yace ina me gidan ki? mamaki ne yakamata sosai amma kuma ta wani fanni sai ta ajiye mamakin ta saboda itama taji labarin sa ance baida mutunci amma bata san har su rashin mutuncin nasa yake ba, sai gashi yayi mata ko girman ta bai duba ba ba gaisuwa ba komai sai tambayar me gida, katse mata tunanin ta yayi tare da cewa bana maimaita magana, Ɗan murmushin yaƙe tasaki tare da cewa ayya yi haƙuri baya nan amma nasan ba nisa yayi ba yana ɗayan part ɗin matar sa mu biyu ne, Kafin ma ta idasa maganar ta ya miƙe tsaye sannan ya kalle ido cikin ido yace waya gaya miki mutuwar Sabreena, gaban ta taji ya faɗi jin sunan da ya amta itafa koda akace ta dawo bataje ta ganta ba ganin take kamar fatalwa zataje ta gani dan bata gama gasgata hakan ba shiyasa taƙi fita taje ta ganta, Saurin daidaita nutsuwar ta tayi tare da kama kanta sannan ta shiga tunanin waye ma ya sanar da ita tabb nan ake yinta wallahi ta manta bazatace ga bakin da ta fara jin mutuwar nan ba, "Kin matane in tuna miki ta tsinkayi muryar sa, Ɗan kallon sa tayi da har zatace eh ta manta sai kuma loƙacin ya dawo mata a ƙwaƙwalwa ta tuna tabbas waziri ne yagaya matatake kwa ta sanar dashi, yana jin haka baice mata komai ba ya fice daga ciki, da kallon mamaki tabishi yanda taji labarin sa ashe ya wuce haka,karkata kai tayi aranta tana ƙissima abubuwa da dama sannan taja hannun yarinyar da take ta ƙoƙarin bin Meer da ko kulata bai ƙara yiba tunda suka fito har ya fice kuma yama manta da babanta, kamar tai kuka haka tabi ta suka koma ɗaki gaba ran matar waziri duk adagule babu daɗi...., Meer na fita yasanar da ɗan rakiyar tasa inda yake son zuwa nan suka juya akalar tafiyar tasu zuwa ɗayan ɓangaren, ba wani tafiya suka suka ƙarasa part ɗin kamar yanda yayi acan part ɗin haka yayi yanzu ma ya shiga kansa tsaye, ya kwa ci sa'a yana shiga ya tarar dasu gaba ɗayan su afalon waziri da matar sa saboda suma duk yaran sun fita kallo, Ido biyu da waziri sai yaji girmansa aransa dan haka sai kawai yaɗan maze yayi sallama ciki ciki, yana ƙarasa shiga ciki, Cike da murmushi shinfiɗe kan fuskar waziri dan har haƙoransa na bayya na yace "Ah ah ah kace banban baƙo ne yazo min to sannun ka da zuwa Bismillah ga guri zauna, ya nuna masa gefen sa, zama yayi tare da cewa "barka da safiya, waziri yace "barkan mudai magaji mun kwana Lafiya ya kwana baƙunta ai daman yanzu nima nake shirrin zuwa can wajen ku ashema kana tafe, Meer da duk yaji zaman gurin ya gundure sa ya gaji da surutun da yake masa, shiyasa yayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa "yauwa magana nazo muyi akan maganar maama Sabreena, gyara zama waziri yayi yana fuskan tarsa da kyau sannan yace "to to madallah hakan yayi, nima daman jira nake inji yaya yayi maganar shiyasa ma banƙara yinta ba nabari zuwa wani loƙaci amma tunda yanzu kazo shikenan sai muyi, Meer ya kalle sa sai kuma ya kawar da kai tare da mayar da fuskar sa yanda take tun farko sannan ya wani canza murya kamar bashine yanzu yagama magana cikin ruwan sanyi ba, "Abu daya zuwa biyu nake son ji daga gare ka sauran duk kabarsa idan kafaɗan hakama kaɗai ya isa an hutar  dakai kacire hannun ka zanji da komai, Wani busashen yawu waziri ya haɗiya dan maganar Meer ba ƙaramin sosa masa rai tayi ba amma sai yayi saurin kawar da duk wata damuwa da take shirin wanzuwa aransa yace "ina jinka magaji saidai kuma wani hanzari ba gudu ba bazaka iya ba gwanda de kabari ataimaka maka saboda baka san kowa ba kuma baka san kan gidan ba dan haka bincike kai kaɗai ba ƙaramin wahala zai baka ba tsintaiya ɗaya bata shara, wannan abun yana buƙatar tsintaiyoyi da yawa, dole sai an haɗa ƙarfi da ƙarfe kafin a cinma abun da ake so a cinma ina fatan ka fahimce ni, Tunda ya fara magana Meer yake yi masa wani irin kallo ta ƙasan ido batare da shi wazirin ya fahimci hakan ba, saida ya bari yayi shiru ga mamakin waziri sai kawai yaji Meer yace "No needa nagama magana kuma baza canza ba, baijira cewar waziri ba, ya ɗora da cewa "tambayata ta farko agare ka shine kagaya min agun wanda kafara jin mutuwar ta sannan kuma agurin nan kace kana da dalilin da yasa ka yarda cewar itace kana da hujja to hujjar nake son ji idan ka gaya min waɗannan abubuwan shikenan ya wadatar dani ina sauron ka......., shiru waziri yayi na wasu ƴan loƙuta kafin ya gyara zama yace, azahirin gaskiya taƙa maimai bazan ce maka ga abakin wanda nafara jiba, ranar da abun ya faru bana gida ina dawowa natarar ana zancen mutuwar tundaga bakin gate ɗin, ni kuma a loƙacin ban yarda ba saboda tun adaren washe garin kafin ace ta rasu ɗin naje part ɗin ta sai na tarar bata nan sai mai aikin ta kawai ita kuma take sanar dani cewa ai bata nan ta fita unguwa nayi mamakin jin hakan ya za ayi tafita unguwa a irin wannan loƙacin ita kaɗai saboda kafin inje in sameta muna tare da yaya(papa) muna magana bayan mun gamane nace masa zane wajen mutuniyata saboda muna shiri da ita sosai, shiyasa abun ya ƙara ban mamaki da yasan bata nan ai da zai sanar dani tunda tare muka taho dashi ni nayi ɓangaren ta shikuma ya tafi wajen ɗayar, a loƙacin nayi niyar inje insanar dashi sai kuma naga dare yayi sosai wataƙil ko ya sha'afane shiyasa bai sanar dani ba ko tayi tafiya me nisa ta kwana tunanin hakan shine yasa kawai na ɗan bar maganar zuwa safiya, da safe kuma sai kiran gaggawa ya same ni na fita daga gidan tun a subar fari ma nabar gidan, bandawo ba sai wajen ƙarfe sha ɗaya na safe ina dawowa kuma na riski mutuwar da na tambaya ya akai ta mutu kowa yake cewa hakannan aka tarar da ita ta mutu a ɗaki nace akaini wajen yaya akace ai baya cikin hayyacin sa yanzu haka yana ɗakin fulani a kwance, nan nashiga tashin hankali naje wajen mahaifiyar mu nace wai da gaske gimbiya sabreena ta mutu itama tana kuka tace min wai sunce da gaske ne amma itama bata yarda ba saboda loƙacin da za a fita da gawar hana kowa ganin ta akayi wasu ne suka yi mata wanka acewar fulani wai dangin tane sukazo tun asuba dan haka su sukayi mata wanka suka lullubeta kaf cikin gidan nan babu wanda yaga fuskar ta a haka aka fito da ita akayi mata sallah aka kaita maƙabar ta tunda nidai bana gidan aka kaita, da na tambayi ina dangin nata akace har sun koma ƙasar su nikuma a iya sanina nasan tunda aka kawota nan babu wani wanda ya taɓa takowa yazo nan daga cikin ƴan uwanta sai kuma ace ranar da ta mutu har suka zo kuma suka koma taya hankali zai ɗau wannan baya nin aloƙacin saida mukayi kaca kaca da fulani akan ƙarya ne babu wasu ƴan uwanta kuma banyarda ta mutu ba tadai faɗi inda ta kaita rigima mai ƙarfi taso ta tashi daga cikin gidan sai kuma daga baya aka samu masu yi mata aiki suka bada shaidar su sunga ta da idanun su kafin ayi mata wanka, duk da haka nace banyarda ba saida mahaifiyar mu(gwaggo)tace inbar zancen kar ta ƙara jin nayi wata magana haka inaji ina gani nayi shiru tun ba ake ko ina bama maganar ta watse aka manta da babun ta, ba a ƙara zancen taba kuma sai ranar da kuka zo aka ganta sannan kowa ya tuna da ita, yaro kam da ta tafi dashi daman ba zancen sa dan ko ni a loƙacin nama manta dashi banyi zancen sa ba, kuma wannan ba komai bane face asiri ina da tabbacin tun aloƙacin da abun ya faru an riga da an asirce kowa ne shiyasa babu wanda yayi jayayya akan maganar duk abun da aka faɗa sai mutum ya yarda saboda an batar wa da kowa tunanin su ta yanda ko maganar su ma babu wanda zaiyi, to kadai ji abun dake faruwa, sai an tashi tsaye gurin gano ko waye nasan yana cikin gidan nan abun dubawa ma shine idan akace baza a binciko su ba to dole zasu ci gaba da tayar mana da tozarma ba za ataɓa samun kwanciyar hankali ba sundun gayin dauki ɗaiɗai kenan tunda gashi naji labarin matar da kuka zo tare ba agan taba, kaga daga nan kuma ba asan kan wa zasu koma ba, bayama yanzu da suka ga dawowar ku cikin gidan dole suma su tashi tsaye saboda gudun kar akamasu, daka tawa yayi da maganar yana kallon Meer da yake taune bakin sa yana girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin waziri, miƙewa tsaye yayi ya ɗanyi taku biyu zuwa uku a tsakiyar falon sannan yace "ina masu aikin nata da suka bada shaidar sun ganta kuma wacece wacce tace ƴan uwanta ne suka yi mata wankan gawa, waɗan nan suka kaɗai ake nema daga zarar ansame su to kamar ankama wanda ya ɓatar da itane, Shima Waziri miƙewa yayi yace tabbas kamar ankama wanda yayi ne idan aka kamasa saidai kuma wani hanzari ba gudu ba tunda ga ranar banƙara ganin meye mata aikin ba tunda nasanta a fuska kuma hargidan su nasani saboda ni na kawota amma daga ƙarshe da na fara memanta hargidan nasu ma bansamu ba, sauran kuma bansan fuskokin suba amma ina da tabbacin suna cikin gidan nan sudai ba afita dasu ita kaɗai aka fita da ita da nayi bincike nagano hakan saidai kuma nakasa samun su kuma nayiwa fulani maganar loƙacin tana fushi dani taƙi tagaya min, amma yanzu dole mu ƙara tuntuɓar ta da maganar, Meer yace "muƙullin amsar mu yana gurin ta, zata fito da wanda yasata ko tana so ko bata so, zanje na fito da ita yanzu nan yana kaiwa nan yayi alamar kamar zai fice daga cikin falon, Waziri yayi saurin dakatar dashi, daman yana sane ba fita zaiyi ba dan yaji ta bakin sane dan haka sai ya tsaya cak batare da ya juyo ba, Waziri ya gyara tsayiwar sa da kyau tare da takowa zuwa gaban sa yana fuskan tarsa sannan yace "baka tunanin kuma bayan muƙullin amsar mu yana gurin ta itace ma amsar ina tunanin matar nan dole tasani inma bata saniba tasan wanda yasani saboda bata da gaskiya kwata kwata daga ita har ƙawar tata, gashi dukkan wani abu da zai fito daga gurin ta yake fitowa, bayan kuma ɗan da taje ta sato ta kawo sa amatsayin ɗa ai dole tasan shi zaizama sarkin shiyasa ta koreta ita kuma ta kawo nata in ba haka ba taya zata kawo wannan shawarar cewa tana da ciki ai sai tana da tabbacin barin waccen ɗin sannan zata ɗora nata akai, Shiru Meer yayi yana nazari sai daga bisani ya ɗan numfasa sannan yace, "bana tunanin hakan iyakacin gaskiyar ta ta faɗa anawa tunanin kawai kamar ana amfani da ita ne wajen nuna kamar ita take aikatawa yanda duk abun da yafaru ita za azarga dan haka ni SAMEER ɗan SAMEER jikan SAMEER nacire fulani daga zargi yanzu nan ma za afito da ita, daga inda take kuma wanda zai shiga ba kowa bane face kai dan haka sai kasake shiri, kajira kirana, yayi maganar yana nunasa da yatsa cike da gargaɗi yana kaiwa nan kuma yaja ƙafarsa ya fice daga falon tare da banko musu ƙofar....., Saura kaɗan Waziri ya faɗi aƙasa dan ba ƙaramin buguwa zuciyarsa tayi ba dan tana daf da tarwatsewa ta fito waje kana ganin cikin idon sa zaka ga zallar tsoro atattare dashi, Matar sa dake laɓe duk tagama jin maganganun su, ta fito daga inda take tana tafa hannu har ta ƙaraso inda yake bata daina tafawa ba saida ta tsaya agaban sa tana kallon sa ido cikin ido tace, "Bisa ga dukkan alamu zaki yazo farauta kuma ya farauci abun da yake so nidaman na daɗe da gane shirye shiryen ka idan nayi maka magana kace kar na dame ka to gashi nan yanzu ɗan cikin ka zai mayar dakai abun da yaga dama zai wulaƙan taka abainar jama'ar wallahi wallahi nayi da nasanin auren ka kaidai ba mutumin arziƙi bane munafuki mai fuska biyu Allah ya cigaba da tonar asirin ku acikin gidan nan ankama ka sai kasan ta yanda zaka kwaci kanka ai na godewa Allah da ya halicci wannan yaron a duniya dan yayi maganin irin ku gashi ka daɗe kana abu atunanin ka ba mai gane ka sai gashi a ɗan mintina yaro yayi wasa da tunanin ka ya nuna maka yafika iyawa, yanzu shawara ta rage game shiga rijiya ka kwana aciki kai ka ɗai ko kuma kajawo wasu ku kwana aciki kafi jin daɗin baccin domin mutuwar yawa kakace, wallahi idan baka faɗaba ma ni da kaina zanto na muku asiri dan masan duk abun da kuke shiryawa dakai da su........... Bata ƙarasa ba yakai mata wata uwar shaƙa awuya yana ta fitar da numfashi idonsa sun kaɗa sunyi ja yama kasa magana ya shaƙeta kawai, ita kuma tana ta faman kakari zatayi amai tana ƙoƙarin ƙwatar kanta, amma ina ƙarfin su ba ɗaya ba, bai sake taba saida yaga ta daina numfashi sannan yasake ta, tafi luuuu ta faɗi a ƙasa mataciyyyya........✍️✍️ *Tammat bi hamdulillahh anan nakawo ƙarshen littafin nan akaro na biyu saida kuma muyi fatan shiga babi na uku, SARKI SAMMER DA ZaFI ZAFI yanzu za a fara wasan har yanzu dai da saura rina a ragaya, mujee zuwa......💃💃💃💃*           ***********************           ***********************                         💖NEW TEAM💖 💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA*      👇👇👇👇 *1,DUK ƘARFIN IZZATA*        by(ster lady) *2,GIDAN AUNTY*        by(mss lee) *3,SARKI SAMEER*       by(xeemat....love) *4, JINI DAYA*       by(mrs bbk) *5,YA FITA ZAKKA*        by(mum Sayyid)   *6,BABY         by(mhiz innocent)