An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BAYAN MUTUWA BAYAN MUTUWA Abdul-aziz Madakin Gini 1 BAYAN MUTUWA HAKKIN MALLAKA 2022 BUGU NA BIYU 2023 Bugu na uku 2024 2 BAYAN MUTUWA Bayan mutuwa K wance take akan luntsumeman gado irin na su na sarakuna tana ta faman sharar barci tamkar wata gawa, ko alamar tashi bata da niya, kallo xaya za ka yi mata a cikin rigar barcin da take sanye kasan Allah ya yi baiwarsa domin indai batu na kyau ne bata da tsara a nahiyar gaba xaya. Gimbiya lashmin ta kasance doguwar mace mai matsakaicin kaurin jiki,qirjinta a cike yake kuma tana da tudun baya, wuyanta dogo ne, tana da daradaran idanuwa gami da siririn dogon hanci, bakinta xan qarami ne kamar an yanka da wuqa mai xauke da lava masu tashin gaske. A yanzu haka da take kwance tana barci fuskarta cike take da annuri gamida wani irin murmushi irin wanda ka iya sabauta duk xa namiji daya haxa idanu da ita. 3 BAYAN MUTUWA A wannan lokacin gari yaw aye har hasken rana ya hudo ta cikin tagar xakin, gaba xaya kuyanginta na tsaitsaye zagaye da gadon da take kwance suna son su tasheta daga barci amma tsoro ya hanasu duk da cewar kuwa mahaifiyar Lashmin xince ta bayar da umarnin a rinka tashinta daga barcin a daidai irin wannan lokacin. Ba komai ne yasa kuyangin suke tsoron Gimbiya Lashmin ba face ita a rayuwarta ta tsani ayi mata bauta tafi son tayi komai da kanta. Sarauta da kuma daular data ke ciki ko kaxan bata dameta ba, inda son ranta ne tafi son tayi rayuwa irin ta sauran talakawan gari, kai inda za a qyaleta zata iya barin birinsu na Basra ta tafi can wani garin inda ba a santa ba tayi sabuwar rayuwa cikin qasqanci ba tare da wani yasan matsayinta ba. Kuyangin na tsaitsaye cikin halin tsananin tsoro da damuwa saboda gudun kada su yi laifi biyu. Laifin na farko shi ne basu bi umarnin mahaifiyar Lashmin ba sun tashe ta daga barci. Laifi na biyu kuma suna tsoron karya dokar Gimbiya Lashmin ta cewar kada wanda ya sake tashinta daga barci har sai ta farka da kanta. 4 BAYAN MUTUWA Kwatsam sai suka ga Gimbiya Lashmin ta yi juyi akan gadon kuma ta miqe zaune zumbur daga kwance kamar wadda ta farka daga mugun mafarki. Koda taga kuyanginta a tsaitsaiye kewaye da ita sai ya qyalqyale da dariya tace. “Na tashi da kaina ko? Babu wanda ya tashe ni daga barci ko?” koda jin wannan tambayar sai shugaban kuyangin nata mai suna Ilela ta dubeta cikin murmushi da girmamawa tace. “Ya shugabata babu wanda ya tasheki daga barci kece kika farka da kanki” koda jin haka sai farin ciki ya lulluve Gimbiya Lashmin tace. “Yauwa haka nake so ya kasance ina iya yin komai da kaina ba sai kunyi min ba,yanzu kuma zanje kewaye na yi wa kaina wanka” Koda jin haka sai hankalin ilela dana sauran kuyangin ya duguzunma ainun. Ilela ta dubi Gimbiya Lashmin a lokacin da idanunta suka zazzaro, fuskarta na nuna alamun tsananin tsoro tace. “Gimbiya ki rufa mana asiri kiyi sani cewa idan mahaifiyarki ta samu labarin cewar yau kinyi wanka da kanki sai tasa anyi mana horo mai tsanani...” Kafin Ilela ta gama rufe bakinta tuni Gimbiya 5 BAYAN MUTUWA Lashmin ta tari numfashinta tana mai doka mata tsawa tace. “Yanzu shi kenan ni har abada bazan tava samun ‘yancina ba? Tun ina jaririya ake yi min komai ba’a tava barina na yi wani abu ba, hatta goge haqora das a takalmi. Ni kam na tsani gidannan na tsani komai da kowa dake cikinsa”. Koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai kawai ta ji muryar mahaifiyarta tana mai cewa. “Qwarai kuwa duk abinda kike faxa gaskiya ne, kuma kisani bama ke ba hatta mahaifinki ma sau xaya ya tava sa takalmi da hannunsa wannan itace al’adar gidannan kuma wannan al’adae ba zata tava sauyawa ba har abada muddin ire-iren gidan na raye a doron qasa” Cikin matuqar damuwa Gimbiya Lashmin ta waiga bayanta ta dubi mahaifiyarta a lokacin da ta shigo cikin turakar kuma ta durfafo inda take da isowarta gareta sai ta kama hannunta ta jata izuwa cikin kewaye kuma ta yafito kuyangin da hannun suka biyo bayansu. Haka dai taci gaba da lallava Gimbiya Lashmin tana faxa mata kalmomi masu taushi gami da kwantar da hankali har suka iso gaban bahon wankanta wanda aka yi shi da zinare cike da ruwan 6 BAYAN MUTUWA xumi ga qamshin turaren miski na tashi a cikinsa kuma ga waxansu ganyayen fure ruwan xorawa a kansa. Ba tare da vata wani lokaci ba kuyangi huxu suka kwavewa Gimbiya Lashmin rigarta ta barci suka shigar da ita cikin bahon wanka suka shiga yi mata wanka suna cuxa sassan jikinta a lokacin da mahaifiyarta ta koma gefe xaya ta zuba musu idanu kawai. Nan take Gimbiya Lashmin ta ji wani irin mugun baqin ciki yayi mata katutu a cikin ranta don haka bata san sa’adda idanunta suka ciko da qwalla ba har hawaye ya suvuce mata. Haka dai ta haqura bisa dole har aka gama yi mata wanka. Bayan an gama wanka wankanne aka fito da ita daga ciki aka tsane dukkan danshin dake jikinta sannan aka shafe duka jikinta da man zaitun. Daganan kuma sai aka kawo tufafi irin nasu na ‘ya ‘yan sarakuna mai tsananin kyau da tsada aka sanya mata. Koda aka kawo Gimbiya Lashmin gaban madubi ta kalli kanta taga irin tsananin kyau da Allah ya bata da kuma yadda tufafin jikinta ya dace da kyawun nata bata san sanda ta saki murmushi ba. 7 BAYAN MUTUWA Tace a cikin ranta haqiqa duk ‘xa namijin daya sameni a matsayin abokiyar rayuwarsa ba qaramin dace ya yi ba”. Bayan Gimbiya Lashmin ta gama duba kyawunta a gaban madubi sai kuma aka tafi da iya izuwa cikin wani dogon xaki wanda ananne suke cin abinci ita da iyayenta. Babu komai a cikin wannan xakin face wani dogon teburi wanda tsawonsa yakai kamu saba’in faxinsa kuma kamu ashirin ne kacal. Duk girman wannan tebur kujeru uku ne kacal a qarqashinsa. Biyuu na can qarshensa a jere, xaya kuma na farkonsa, bisa teburin an zuba kwanukan abinci sama da kala xari biyu kowane kwanon na xauke da abinci iri daban-daban. A gaban kowane kwanon akwai kuyanga guda xaya wacce ta ruqe falan da cokali, kawai jira take a bata umarni ta zubo abinci ta kawo. Da shigowar Gimbiya Lashmin cikin wannan xakin cin abinci sai ta iske iyayenta zaune akan waxannan kujerun guda biyu dake can qarshen teburin, tuni sun rigata halattar xakin koda suma suka yi arba da ita sai sarki Sairan ya dubi matarsa Gimbiya Marita yace. 8 BAYAN MUTUWA ‘Yau kuma me aka yiwa Gimbiya Lashmin naga ko kaxan babu annuri akan fuskarta?” koda jin wannan tambayar sai Marita ta yi xan guntun murmushi tace. “Babu abinda aka yi mata, halin natane dai wanda kasanta da shi. Har yanzu taki karvar ni’imar da Allah ya bata, kullum so take a barta ta yi komai da kanta” Koda jin wannan batun sai nan da nan fuskar sarki Sairan ta sauya yanayi daga annuri zuwa fushi, bai san sanda ya doki teburin ba da tafin hannunsa al’amarin daya razana Marita. Gimbiya Lashmin da gaba xaya kuyangin dake tsaitsaye a gabansu, kawai sai ya miqe tsaye ya taho izuwa ga Gimbiya Lashmin ya tareta tun gabanin ta zauna akan kujerarta, take jikin Gimbiya Lashmin ya kama karkarwa saboda tsananin tsoron mahaifinta data ji ya kamata. Koda sarki sairan ya iso daf da lashmin yadda suna iya jin numfashin juna sai ya dubi gaba xaya kuyangin dake cikin xakin yayi musu wata inkiya. Take kuyangin suka fice suka barsu su uku kacal. Fitarsu ke da wuya sai sarki Sairan ya dakawa Lashmin tsawa ta sake firgita ainun taji kamar hantar cikinta zata faso cikinta ta faxo qasa yace. 9 BAYAN MUTUWA “Sau nawa zan gaya miki cewar kada ki qara nunawa kuyanginki cewar bakya son ayi miki hidima? Sau nawa zan gaya miki cewar ki zamo mai izza,girman kai da nuna isa?” koda jin waxannan tambayoyin sai Lashmin ta sunkuyar da kanta ta kas tayi shiru kamar wadda ruwa ya ci kuma jikinta ya ci gaba da karkarwa fiye da farko. Cikin xaga murya sarki sairan yace “Wannan shi ne cikar mulki da iko, idan baki da su ba za ki iya hawa kan karagata ba, dole mai mulki ya zama yafi kowa tausayi da rashin imani, domin ya iya zarta da mulkinsa daidai, ke kuma tausayi gareki zallah ba ki da rashin imani, dole mai mulki ya zama mai girman kai gami da izza, ke kuma sauqin kai ne dake tamkar ruwan sanyi. Dole ne ki zamo mai zafi ga talakawanki kuma ki zamo mai jin qansu da taimakonsu. Babu irin horon da bansa an baki ba akan haka amma ba kya amfani da su. To ki sani cewa daga yau na kafa miki doka ba zaki sake fita ko ina ba daga cikin gidannan har sai kin fara aiwatar da horon da nasa aka baki a aikace saboda haka zan baki riqon karagata na tsawon kwana bakwai, idan kika tsalake wannan jarrabawa za ki ci gaba da fita rangwadinki 10 BAYAN MUTUWA zuwa duk inda kike so, idan kuma kika kasa hayewa wannan jarrabawar har abada kin daina fita koda daga cikin turakarki har zuwa ranar da zan bar wannan duniyar”. Koda gama faxin hakan sai sarki sairan ya juya ya koma can inda matarsa marita ke zaune ya zauna yana mai tafa hannayensa biyu. Nan take kuyangin suka dawo cikin xakin kowacce ta tsaya a inda take da, a sannan ne itama Gimbiya Lashmin ta zauna akan kujera jikinta a matuqar sanyaye kuma hankalinta ya dugunzuma saboda tasan halin mahaifinta, indai ya furta zai yi abu tofa sai ya aiwatar da shi. Ba tare da vata wani lokaci ba suka fara cin abinci duka su uku. Nan take Gimbiya Lashmin ta yi abinda basu tava ganin tayi ba domin kuyangar dake kusa da ita ta duba ta daka mata tsawa tace. ‘Maza ki xebo min abinci da na saba faraway da shi mana, ko kuma sai na hamvareki da qafata tukunna” Jikin kuyangar yana rawa tayi sauri ta zuba mata abinci akan falan ta ajiye a gabanta. Koda ganin haka sai farin ciki ya lulluve sarki saihan ya dubi marita yace. 11 BAYAN MUTUWA “Ta fara sauyawa fa” Koda jin haka sai marita ta yi dariya tace. “Ai kasan duk duniya babu abinda Gimbiya Lashmin take so sama da zuwa cikin jeji kuma ta yawata izuwa sauran birane da qauyukan qasar nan” Sa’adda sarki saihan ya ji haka sai ya yi murmushi yace. “Ai duk wannan mai sauqi ne muddin zata zama kamar ni” Koda jin haka sai marita tayi sauri ta ajiye cokalin da take cin abinci da shi ta dubi sarki saihan cikin alamun razani tace. “Ta yaya ‘yarta zata zama kamar ka? Alhalin ta kasance ‘ya mace kuma bata kasance jaruma ba?” Da jin haka sai sarki saihan ya bushe da dariya sannan yace. “Ai ba ina nufin ta zama jaruma ba, ko mayaqiya ina nufin zuciyarta ta zamo dakakkiya irin ta sarakai wadanxa za su iya tafiyar da mulkinsu” Marita tayi ajiyar zuciya tace. “Da sannu ‘yarta zata kai wannan matsayin da kake so ammafa dolene sai kayi haquri kuma ka jira lokacin, ni yanzu babban abinda yake damuna batun auren wannan yarinya. A gaba xaya qasar nan babu wata ‘ya mace mai kyau da farin jininta ‘ya ‘yan 12 BAYAN MUTUWA sarakai da ‘ya ‘yan manya attajirai da yawa sun nemi auren Gimbiya amma kaqi basu. Shin kamanta cewa itace kaxai ‘ya a garemu? Shin ka manta cewa girma ya fara kamamu? Me yasa baka son muga jikokin mu? Kasani cewa ko Lashmin ta zama sarauniyar qasar nan dole ne tayi aure. Zaifi kyau tun yanzu ma ka sauka daga kan karagarta ka bata kuma ka zava mata mijin daya dace da ita. Koda jin wannan batu sai sarki saihan ya gyaxa kai sanan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye yace. “Ina nan ina tunani da aiki akan haka kuma nan bada daxewa ba komai zai kammala. Kinsani cewa dolene nayi wa ‘yarmu zave mai kyau kuma mafi alheri a gareta domin bayanmu ta yi kyau kuma ta xore” Haka dai sarki sairan da marita suka yi ta tattaunawa akan gimbiya Lashmin ita kuma lashmin sai ta ci gaba da cin abincinta kawai tunda bata jin abinda suke tattauna saboda nisan dake tsakaninsu amman kuma ta tsargu cewa akanta suke magana bisa ganin yadda suke yawan kallonta. Bayan sun kammala cin abinci kowanne su an wanke hannunsa an goge maiqon dake bakinsa sai suka miqe tsaye tare, sarki ya fito Lashmin da hannu ta taho garesu. Da zuwanta sai ta faxa kan qirjinsa 13 BAYAN MUTUWA suka rungume juna sannan ya janye jikinsa daga cikin nata ya sumbaci goshinta yace. “Kamar yanda na gaya miki xazu yaune za ki fara yin jarrabawar don haka nan da cikar rabin sa’a kije ki gama shiri ina son ki shammaci kowa kawai sai dai fadawa na da sauran jama’ar gari su ganki akan karagata, bayanin farko da za ki soma yi musu ina kwance bana jin daxi shi yasa kika wakilceni, daga nan sai kici gaba da gudanar da al’amuranki na mulki kamar yadda kika ga ina yi kullum” koda gama faxin haka sai sarki ya kama hannun marita ya jata suka fice daga cikin xakin cin abinci suka bar Gimbiya Lashmin a tsaye cikin fargaba, tunani gami da mamakin dalilin da yasa yau rana xaya sarki ya yanke wannan hukuncin na yi mata wannan jarrabawa. Babban tashin hankalita shi ne yadda zata gabatar da shari’a a fada tayi hukunci ga wanda aka zallunta kowa wanda ya aikata laifi. Duk abin da ya shafi sai an zubar da jini ko an musgunawa wani Lashmin bata son shi, saboda tsananin tausayinta amma kuma yanzu bata da wani zavi wanda yafi tayi wannan hukunci bisa dole don kada sarki ya kafa mata takunkumi fita rangadi da koma katse mata burinta na son yawantawa a cikin kasar. 14 BAYAN MUTUWA Lashmin na tsaye a cikin xakin cin abinci tana ta tunani har izuwa tsawon daqiqu masu xan yawa har sai da shugabar kuyanginta ta shigo ta dafa kafaxarta sannan ta dawo cikin haiyacinta ta dubeta a razane kamar wacce ta farka daga mafarkin ban tsoro, shugabar kuyangan tace. “Ranki ya daxe shin kin manta ne cewa za mu yi miki shirin zuwa fada?” koda jin haka sai Lashmin ta saukar da ajiyar zuciya tace. “Haka ne fa muje mana” Nan take shugabar kuyanginta ta wuce gaba Lashmin na biye da ita sannan sauran kuyangin suka take musu baya. Cikin qanqanin lokaci aka sauyawa Gimbiya Lashmin tufafi aka sanya mata irin tufafin shiga dafa. Aka kawo mata alkyabba irin ta mata mai darajar gaske aka yafa mata kuma aka xora mata hular mulki ta lu’u lu’u akanta. Hakan ne ita kanta Lashmin da ta dubi kanta a cikin madubi taga yadda wannan shigar tayi mata kyau sai ta dubi shugabar kuyanginta tace. “Tabbas mulki yana da daxi, amman bana son shi saboda har naji wani irin girman kai ya fara shiga jikina saboda kawai na sanya wannan tufafin na alfarma. To idan kuma na shiga fada fa naga 15 BAYAN MUTUWA fadawa,bayi da hadimai sun fara gaisheni suna girmamani? Ni kam idan na gama wannan jarrabawar da sarki zai yi min bazan sake yarda na sanya irin wannan tufafin ba har abada, maza mu wuce zuwa fada. Saboda sarki ya bani umarnin lallai na riga fadawansa zuwa fada” Nan take shugaban kunyangi ta sake yiwa Gimbiya Lashmin jagora suka fice daga cikin turakarta suna fita sai dakarun dake tsaron lafiyarta su arba’in suka rufa mata baya, tun a qofar turakarta Lashmin taga sabon sauyi, domin gaba xaya hadiman da suke binta sarki duk wajen da zai je ta gani tsaye suna jiranta. Ai kuwa tana fitowa sai dukkansu suka zube qasa gabanta suka kwashi gaisuwa sannan kowannen su ya kama aikinsa kamar yadda suka saba. Duk inda suka wuce a cikin gidan sarautar sai taga ana girmamata ainun fiye da yadda aka saba yiwa sarki shi ake yi mata domin nan take aka fara buga mata tambura ana busa kakaki da algaita, kuma gaba xaya jama’ar gidan suka rinqa zuwa suna zubewa qasa suna kwasar gaisuwa. 16 BAYAN MUTUWA BAYAN MUTUWA 2 oda ganin wannan al’amari sai hankalin lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi, babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarta Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta gidan sarautar. Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake K 17 BAYAN MUTUWA zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki, aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana tafiyar qasaita kamar wani toron giwa. Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce. Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba. Da isar gimbiya Lashmin kan karagar mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba alhalin sarki yana raye. okacin da Gimbiya Lashmin ta lura da gaba xaya fadawa da ‘yan majalisu sun hallara sai ta yi gyaran murya take fadar tayi tsit aka saurara domin aji abinda zai fito daga bakinta. Duk wanda ta kalla sai taga yana muzurai L 18 BAYAN MUTUWA gami da haxiyar miyau kamar su tashi su matse bakinta tayi bayanin dole. A zuciyarta sai tace oh kaga miyagun banza kawai so suke suji wata maganar ta sharri bata alheri ba, domin su san yadda za su qula wani mugun makircin. Kawai sai aka ga Lashmin ta fara da yin murmushi sannan tace. “Yaku jama’ar wannan birni na sham kuyi sani cewar mahaifina bashi da lafiya amma duba ba wani ciwo mai tsanani bane don haka zan ci gaba da wakiltarsa har izuwa tsawon xan lokaci kafin ya warware, ina mai yi muku alqawari da cewar zan tafiyar da mulki bisa adalci kamar yadda mahaifina ke zarta da shi. Saboda haka ina fatan cewar ‘yan majalisa da dukkan dakaru da sauran shugabanni na birni da qauye za su bani haxin kai kamar yadda suka saba baiwa mahaifina. Yanzu take ina son a ci gaba da zarta da komai kamar yadda aka saba kuma zan saurari qara guda uku kacal a zaman da za mu yi yanzu, ina masu gabatar da qara?” Koda jin wannan tambayar sai wani dattijo daga cikin fadawan ya matso gaba kusa da 19 BAYAN MUTUWA karagar mulkinta a vangaren hannun dama ya zube qasa ya kwashi gaisuwa sannan yace. “Ya shugabata ni ne mai gabatar da qara a wannan fadar tsawon shekara talatin baya kamar yadda kika sani” Koda jin haka sai Lashmin ta yi murmushi tace. “Gaskiya ya kai Safwan bin ma’aruf bin kananata, tun kafin a auri mahafiyata kake wannan aikin. Kai ne ka gabatar da qarar waziri Dulnur wanda ya kashe amininsa ya aure matarsa kuma ya mallake dukiyarsa kimanin shekara talatin da shida baya anan fadar, da taimakon ka ne gaskiya ta bayyana har ka saka sarki kan’an ya yankewa waziri Dainur hukuncin kisa aka tsireshi a tsakiyar kasuwa ko ba haka abin ya faru ba?” Safwan ya risina yace. “Haka yake ranki ya daxe” Nan take jama’ar da suke cikin fadar suka kamu da tsananin mamaki bisa jin yadda Gimbiya Lashmin ta riqe wannan tsohon tarihin domin lokacin da al’amarin ya faru ba a ma san zata zo duniya ba. Lashmin ta dubi Safwan bin ma’aruf tace. “Karanto mini shari’ar farko na ji a kuma shigo da wanda ya kawo qarar da kuma wanda ake qara” koda jin wannan umarni sai Safwan ya miqe 20 BAYAN MUTUWA tsaye yaje bakin qofar da ake shigowa da masu shari’a yace. “Ina attajiri Huzulu da kuma saurayi Amzad a shigo da su”. Nan take sai ga wani dogon mutum ma’abocin kwarjini a cikin suture masu tsada ya shigo cikin fadar fuskarsa cike da annuri. Kallo xaya zaka yi masa kasan cewar babu wani abu da yake damunsa a rayuwa, yana tafe yana murmushi. Wanda ke biye da shi kuwa wani matashin kyakkyawan saurayine wanda kana yi masa kallo xaya zaka gane cewa in ba don talauci ba da bai kasance ramamme ba kuma da kyawunsa ya ninka hakan sau uku. Kai da ganinsa kasan yana fama da aikin wahala kafin ya samu abinda zai kai bakinsa, biye da waxannan mutane biyu dakarun fada ne. Koda Gimbiya da wannan matashin saurayin mai suna Amzad suka haxa idanuwa karon farko sai kowannensu yaji zuciyarsa ta buga da qarfi. Cikin hanzari Amzad ya sunkuyar da kansa qas don kada qurawa Lashmin idanu ya zama laifi ayi masa wani hukunci akan haka. 21 BAYAN MUTUWA Batare da vata wani lokaci ba aka gurfana da attajiri Huzulu da Saurayi Amzad a gaban Gimbiya Lashmin. Nanfa fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta sai da Lashmin ta qarewa attajirin Huzulu da Amzad kallo, tayi nazarinsu sosai sannan ta dubi Safwan bin ma’aruf tace. “Kafin a gabatar da wannan qarar ina son ayi mini bayani akan matsayin wanda ake qarar da wanda ya kawo qarar, ina son nasan sana’o’insu, mu’amalarsu da mutane da koma inda kowannensu ke da zama” koda jin haka sai mamaki ya kama gaba xayan jama’ar dake cikin fadar hatta manyan alqalai kuma na dukan kotunan qasar saboda wannan wani sabon salone bisa tsarin shari’ar qasar, Lashmin tazo da shi. Mai gabatar da qara Safwan bin mu’aruf ya juya ya fuskanci Gimbiya Lashmin yace. “Da farko dais hi wannan attajiri wanda kowa a garinnan ya sani da suna Huzulu yana zaune ne a unguwar sarakai kuma bashi da wata sana’a wacce ta wuce siye da siyar da gidaje da kuma bayar da hayar gida ko gona ko rumfar kasuwa. A cikin wannan birnin namu na Misra an tabbatar da cewa yafi kowa yawon gidaje da gonakai da kuma rumfunan kasuwa 22 BAYAN MUTUWA don haka ko sauran attajirai masu yin harkokin fatauci kalilan ne suka fishi yawan tsabar kuxi a hannu a qasar nan gaba xaya. Shi kuma wannan saurayi mai suna Amzad bashi da wata sana’a wacce tafi dakon tubalin gini ya kanje ya nemi aikin dakon tubali yana kaiwa inda ake gini abiyashi, wannan ita kaxai ce mu’amalar data haxashi da mutane. A kullum idan ya tashi daga aiki da yamma da zarar ya wanke jikinshi zai tafi ne izuwa can gidansu wanda ke kusa da gidan attajiri Huzulu a unguwar sarakai ya kaiwa mahaifiyarsa abincin da zata ci. Ita dai wannan mahaifiya tasu ta kasance tsohuwa tukuf, saboda tsufan ma bata gani da idanunta kuma bata iya taka qafafunta, ko kewaye zata shiga sai dai Amzad ya xauketa a hannunsa ya kaita” koda Safwan ya zo daidai nan a bayaninsa sai Gimbiya Lashmin ta xaga masa hannu kuma ta tari numfashinsa tana mai cewa. “Me yasa kake wuce gona da iri akan bayanin Amzad, amma sa’adda kake bayanin attajiri Huzulu sai ka taqaita komai yasa?” Koda jin wannan tambayar sai idanun Safwan suka zazzaro gaba xayan jama’ar dake cikin fadarma sai suka kama muzurai. 23 BAYAN MUTUWA Shi kansa attajiri Huzulu sai yayi fiqi-fiqi da shi ya kama muzurai yana mai qus-qus. Gimbiya Lashmin ta gyara zama kuma tayi gyaran murya sannan ta dubi Safwan tace. “Tsakanin attajiri Huzulu da Saurayi Amzad waye ya kawo qarar wani?” Safwan yace. “Ubangiji Dullas ya taimakeki Gimbiya ai yaro Amzad ne ya kawo qarar attajiri Huzulu” Koda jin haka sai Lashmin tayi murmushi sannan tace. “Ai dama abune mayuwanci attajiri ya kawo qarar talaka sai dai talakan ya kawo qarar attajiri saboda har kullum talaka ba zai iya danne haqqin attajiri ba tunda anfishi sanin komai da kowa kuma an fishi qima da daraja, maza a karantomin wannan qarar doming a dukkan alamu zan yanke hukuncinta a cikin qanqanin lokaci”. Koda jin wannan batu sai hankalin attajiri Huzulu ya dugunzuma ainun ya buxe baki kamar zaice wani abu amma sai Gimbiya Lashmin tayi masa nini da yayi shiru tace. “Kai ba’a magana a gaban kotu face an baka izinin yi” cikin alamun kunya da rashin gaskiya attajiri Huzulu ya yi shiru yana mai sunkuyar da kansa qas. Mai gabatar da qara Safwan bin ma’aruf yayi gyaran murya a lokacin da fadar ta suka yi tsit tamkar 24 BAYAN MUTUWA ruwa ya ci kowa sannan yace saurayi Amzad yana qarar attajiri Huzulu akan cewa ya kwace masa gidansa nag ado wanda mahaifinsa ya mutu ya bari a matsayin bashin da yake bin mahaifinsa, bayan mahaifinsa ya mutu, baya ga wannan gidan akwai rumfunan kasuwa guda uku wadanda yace tun kafin mahaifin Amzad ya mutu ya bashi su jingina kuma bai dawo da kuxin da ya araba har ajalinsa ya cika. Bayan rumfuna uku akwai babbar gona guda xaya wacce ke can kusa da kogin Luzim a bayan gari. A yanzu haka duk faxin garinnan babu inda ake noman kayan lambu sama da wannan gona kuma a tsawon shekaru ashirin da biyar da mutuwar mahaifin Amzad daidai da rana xaya ba a tava daina noma a cikin gonar ba kuma duk amfanin da aka samu Attajiri Huzulu ne yake riqewa. Bai tava baiwa mahaifiyar Amzad koda sisin kwabo ba, tun kafin ma ta haifi Amzad saboda tana xauke da junan biyun Amzad da watanni shida Allah ya yi wa mahaifinsa rasuwa” Koda Safwan ya zo nan a bayaninsa sai Gimbiya Lashmin tayi sauri ta xaga masa hannu tace. “Dakata haka haba ai wannan shari’ar ta wuce duk yadda nake zato, ina mai tabbatar muku za 25 BAYAN MUTUWA mu iya shafe wata guda muna yinta bamu qare ba duk da cewar za mu iya gano mai gaskiya a tsakanin attajirin da saurayin a cikin sa’a xaya jal” koda jin wannan batun sai kowa ya kamu da tsananin mamaki a cikin fadar. Su kansu manyan alqalai na qasar sai suka kasa gano manufar Gimbiya Lashmin da kuma yadda zata yi ta iya warware wannan qara da kuma dalilin da yasa tace za a iya gano mai gaskiya a cikin sa a xaya saboda basuga hujjojin da zata iya amfani da su ba. Kamar Lashmin tasan abin dake zukatan jama’a da sauran alqalan qasar sai kawai aka ga ta miqe tsaye daga kan karagar mulki ta tako kafafunta ta zo har gaban attajiri Huzulu ta dubeshi a cikin nutsuwa tace. “Shin gaskiya ne kana bin mahaifin Amzad bashin da darajarsa ta kai ta gidansa, rumfunan kasuwarsa guda uku da kuma babbar gonarsa dake can bayan gari, gonar da babu kamarta a duk faxin qasar nan?” koda jin wannan tambayar sai attajiri Huzulu ya gyaxa kai yace. “Wannan gaskiya ne kuma ina da shaidu akan haka gami da rubutacciyar takarda mai xauke da saka hannunsa da kuma saka hannuna akan duk kuxaxen 26 BAYAN MUTUWA da ya zo ya karva a hannuna da zumar zai biyanio kafin cikar wani wa’adi na kwanaki har ajalinsa ya riske shi bai gama biyana waxannan kuxaxen ba shi dalilin daya saka na riqe gidajensa, gonarsa da rumfunansa na kasuwa” Koda jin wannan batun sai Gimbiya Lashmin ta gyaxa kai kuma tayi murmushi sannan ta sake duban attajiri Huzulu tace. “Shin kuxaxen da mahaifin Amzad ya karva a hannunka duka ya karve su ne a rana guda ko kuma ya karve sune daban-daban akan ko wacce kadara tasa?” Hazalu yace. “Ai ya karve sune daban-daban, misali lokacin da yake so zai gina waxannan rumfuna na kasuwa guda uku bashi da kuxin aikin sai ya zo wurina na bashi rancen dinare dubu xari biyu da arba’in bisa sharaxin cewa idan ya kammala ginin zai bayar da hayar rumfar duk wata zai riqa bani dinare dubu hamsin har tsawon wata shida a sananne zai kammala biyana, a watan farko da zai fara biyana wannan kuxin ajalinsa ya same shi, tsawon shekara guda ba a bani ko kwabo ba. Duk sanda naje wajen matarsa na nemi haqqina sai tace dani itama ba a bata ko sisi ba ta ma san a hannun wa rumfunan suke ba, ya shugabata 27 BAYAN MUTUWA kinga kenan na tafka asara na tsawon watanni shida kuma inda kuxina a hannuna suke da sun ninka kansu, bisa wannan dalilin na riqe duk kadarorinsa a maimakon kuxaxena daya karva na fitar da matarsa daga cikin gidan na zuba ‘yan haya a ciki. Dangane da yadda aka yi na mallake rumfunan kasuwarsa kuwa guda uku shi ne bayan ya karvi wannan kuxin na farko dinare dubu xari biyu da arba’in, a tsakiyar watan da zai biyani ya sake dawowa ya ranci dinare dubu xari biyar ya sayi irin da zai shuka a wannan gona tasa wadda ya gada a wajen ubansa kuma ya biya ma’aikata suka nomata bisa sharaxin cewar bayan yayi girbi zai biyani dunare dubu xari takwas. Har bayan shekara biyu da mutuwarsa ba a bani kuxina ba, bisa wannan dalilin na riqe takardun rumfuna guda uku. Ana I gobe zai rasu Mahaifin Amzad ya sake dawowa gareni ya ranci dinare miliyan xaya ya sayi raquma,alfadarai da jakuna waxanda za su riqa safarar amfanin gonarsa izuwa qauyuka da birane dake cikin qasar nan kuma ya biya ma’aikata da za su yi masa wannan aikin rabin wahalarsu tun ma kafin kaka ta zo, da sharaxin wata biyu da shuxewar kaka zai biyani dinare miliyan xaya da rabi, sai da aka yi kaka uku ba 28 BAYAN MUTUWA a bani ko dinare xaya ba, bisa wannan dalilin na riqe gonarsa ta zama tawa”. Lokacin da attajiri Huzulu ya zo nan ciki dogon jawabinsa sai kawai aka ga hawaye yana zubowa daga idanuwan Gimbiya Lashmin nan take ta dubi Attajiri Huzulu cikin alamun tsananin fushi tana mai daka masa tsawa tace. “Tabbas ka cika shugaban azzaluman duniya, da farko dai na yarda cewar mahaifin Amzad ya ranci duk kuxaxen da ka faxa a hannunka bisa amincewar zai biyaka kuxin ruwa to amma idan aka yi la’akari da irin kuxaxen da aka samu a rumfunansa na kasuwa da kuma gonarsa a wannan tsawon shekaru ashirin da xaya ai kaci ribar data ninka kuxin daka bashi sau dubunnai. Kawai don kana binsa bashin kuxaxen da gaba xaya adadinsu bai haura dinare miliyan biyu ba sai ka cinye masa gaba xayan dukiyarsa wacce a halin yanzu idan idan qiyasta darajarta za a yi darajarta tafi dinare miliyan xari biyar sannan kuma dukiyar ta haura miliyan dubu goma. Sannan kuma kowa a garin nan ya sa ni kafin ka mallaki rumfunan kasuwa da waxan nan gonakin baka da jarin daya fi dinare miliyan biyar amma yau 29 BAYAN MUTUWA an wayi gari babu mai cinikin gidaje da gonakai wanda ya fika qarfin jari. To idan baka sani ba yanzu ka sani cewar wannan matsala taku kai da Amzad tun ina yarinya qarama na san da ita. Ansha kawo wannan qarar gaban mahaifina amma sai wasu daga cikin ‘yan majalisarsa su sa a kori qarar a baka gaskiya, badan komai ba sai don kana binsu izuwa gidajen su a sirrance xaya bayan xaya kana shaka musu cin hanci na maqudan kuxaxe. Na daxe ina jiran wannan ranar da zan samu damar cikakken bincike akan wannan qarar na qwatowa Amzad da mahaifiyarsa haqqinsu amma ban samu ba sai yau, ka sani babu cuta babu cutarwa, kaje ka zo da duk takardu da kuma shaidun bashin daka baiwa Mahaifin Amzad, shima Amzad zai zo da irinsu waxanda mahaifinsa ya mutu ya bari, bayan an zo da su kotu zata saka a yi lissafi na iya adadin hakkinka daya kamata a biyaka a cikin dukiyar da mahaifin Amzad ya bari sannan ayi lisafin a gani, tsakanin kai da shi wane zai yiwa wani ciko a tsawon waxannan shekaru ashirin da xaya” Koda jin wannan batu sai Attajiri Huzulu ya taqarqare ya kwarara uban ihu tamkar mahaukaci sabon shiga. 30 BAYAN MUTUWA Sannan ya kalli Gimbiya Lashmin cikin tsananin fushi da qiyayya yace. BAYAN MUTUWA 3 ‘K e yarinya ce abinda mahaifinki yabarshi a rufe baki isa ki tona shi ba...” Kafin Huzulu ya gama rufe bakinsa tuni Gimbiya Lashmin ta sharara masa mari, ta dubi wasu dakaru uku dake tsaye kusa da shi tace musu. Koda ganin wannan al’amari sai hankalin lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi, babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da 31 BAYAN MUTUWA za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarta Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta gidan sarautar. Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki, aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana tafiyar qasaita kamar wani toron giwa. Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce. Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba. Da isar gimbiya Lashmin kan karagar mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya 32 BAYAN MUTUWA zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba alhalin sarki yana raye. Koda ganin wannan al’amari sai hankalin lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi, babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar hankali a rayuwarta Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta gidan sarautar. 33 BAYAN MUTUWA Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki, aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana tafiyar qasaita kamar wani toron giwa. Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce. Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba. Da isar gimbiya Lashmin kan karagar mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba alhalin sarki yana raye. 34 BAYAN MUTUWA K awai sai sarkin yaqi ya miqe ya qwalawa dakarunsa kira, nan take sai ga Dakaru sama da mutum xari uku sun rugo izuwa gabansa Lashmin ta sake duban sarkin yaqi tace. “Idan kuka kai shi can kurkuku ku sanar da cewar kar abar kowa ya kawo masa ziyara koda kuwa iyalansa ne kuma koda mai kawo masa abinci kada ya shiga wajensa shi kaxai kuma sai an tabbatar da cewar an cajeshi yayin shigarsa da fitowarsa. Sarkin yaqi ya risina yace “Angama ya shugabata” Nan take aka tusa qeyar attajiri Huzulu aka fice da shi daga cikin fadar a wulaqance abin da ko a mafarki ba a tava zaton cewar zai tava faruwa ba. Bayan an fice da attajiri Huzulu sai Gimbiya Lashmin tasa aka sallami kowa a fadar har da saurayi Amzad kuwa amman kafin ya tafi sai ya faxi qasa a 35 BAYAN MUTUWA gaban Lashmin ya fashe da kukan farin ciki kuma ya kama yi mata godiya kamar bazai daina ba har sai da ta daka masa tsawa a gaban Dakaru da kuyanginta sannan ya shiga taitayinsa sannan ta dubeshi tace. “Ban taimakeka domin komai ba sai domin na kawo sauyi a wannan qasar tamu na kawar da zalunci na shimfixa adalci, ko kai na kama da rashin gaskiya sai na hukunta ka, ka sani cewar kaima yanzu rayuwarka na cikin hatsari saboda haka dolene na haxaka da Dakaru waxanda za su baka kariya kuma ba zaka ci gaba da zama a wannan gidan hayan ba” Koda jin haka sai Amzad ya dubi Gimbiya Lashmin cikin alamun tsananin damuwa yace. “To mahaifiyata fa? Wacce yanzu haka tana can gidan tana jiran dawowata? Kin san cewa ta tsufa ainun bata gani kuma bata iya tafiya” Koda jin haka sai Lashmin tayi murmushi tace. “Kada ka damu tuni tun kafin ma a fara yin wannan shari’a taku nasa an xauketa an akita can gidan sarki dake bayan gari, kuma yanzu can za a kaika wajenta. Na tabbatar da cewar can za ku sami cikakken tsaro har izuwa ranar da za a kammala wannan shari’a taku” Koda gama faxin haka sai Lashmin ta dubi mataimakin sarkin yaqi tace. 36 BAYAN MUTUWA “Yakai muzainu wannan aikin kane, ka jagoranci Dakaru xari ku raka Amzad izuwa can gidan sarki na bayan gari kuma ka zauna tare da shi acan har izuwa tsawon lokacin dana neme ku” koda jin haka sai Muzainu ya dubeta cikin tsananin damuwa yace mata. “Ya shugabata idan sarkin yaqi baya nan nima bana nan akwai matsala ta tsaro a gidanna fa” Gimbiya Lashmin tace. “Ai nasan da haka amman kada ka manta cewa kafin kafin ma ka isa can inda na aikeka tuni sarkin yaqi ya dawo daga can kurkuku ko kuma kana zaton cewa za a kawo mana harin sumame a cikin wannan xan tsukukun lokacin?” Muzainu ya yi murmushi yace. “Aa bah aka bane kawai dai bana son ni da sarkin yaqi muyi laifi ne a wajen mahaifinki” koda jin haka sai Lashmin ta yi murmushi tace. “Ai yanzu ni ce akan karagar mulki ba mahaifina ba, saboda haka idan ma laifi ne ni za kuyiwa bashi ba, indai kana tsoron tuggun attajiri Huzulu ne to ka kwantar da hankalinka domin na xauki matakan tsaro tsaurara akan hakan”. Nan take Muzainu ya kama hannun Amzad ya jashi suka nufi qofar fita daga fadar dakaru na take 37 BAYAN MUTUWA musu baya. Sauran qiris Amzad ya fice ta cikin qofar fadar sai ya juyo suka haxa idanu shi da Gimbiya Lashmin take yaga ta yi masa wani irin kallo wanda ya ximataushi ya jefashi ciki tsananin, mamaki,wasuwasu, fargaba da rashin fahimta lokaci guda duk su biyun suka juyawa junansu baya ta nufi hanyar da zata kaita cikin gidan sarautar shi kuma ya fice daga fadar yana mai bin Muzainu a baya. Da sauri, dakaru sun kewaye shi suna gudugudu sauri-sauri. Lokacin da Gimbiya Lashmin ta shiga cikin gidan sarauta sai ta nufi turakar mahaifinta sarki Salhan kai tsaye tana isa babban falonsa sai ta iske shi a zaune tare da mahaifiyarta a cikin nishaxi suna ciyeciye da shaye-shaye har suna yin soyayya irin tasu ta manya. Al’amarin day a yi matuqar bata mamaki kenan domin a zatonta zata zo ta riskeshi ne a cikin tsananin fushi bisa abinda ta aikata yau a fada domin ta tabbatar da cewar tuni labari ya riskeshi. Koda sarki Salhan yaga Gimbiya Lashmin ta durfafo inda suke zaune sai ya miqe tsaye zumbur cikin matuqar farin ciki ya tarbeta yana mai rungumeta gami da sumbatar goshinta sannan yace. 38 BAYAN MUTUWA “Yake ‘yarta kiyi sani cewar yaune nayi alfahari dake a matsayin ‘yarta wacce zata iya gadata. Sai yaune na tabbatar da cewar ke jinina ce. Domin kin cire min qaton dutsen daya danne ni tsawon shekaru ashirin da biyar, na daxe ina son hukunta attajiri Huzulu amma na kasa amma ke gashi cikin daqiqu kaxan kin hukunta shi kuma a lokacin da ya dace ya karvi irin hukuncin da kika yi masa. A iya tunanina duk wanda ya mutu shi kenan komai na shi ya tafi kenan. Nazmir mahaifin Amzad ya mutu da tsawon shakaru ashirin da biyar dukiyarsa ta tafi ga hannun azzalumi Huzulu amma yau gashi za ki dawo da wannan dukiyar izuwa hannun tsatsonsa, wannan fa shi ne RAYUWA BAYAN MUTUWA sai yanzu a bayan mutuwar Nazmir sannan iyalansa za su yi sabuwar rayuwa irin wacce basu tava yinta ba, domin idan wannan dukiyar ta koma hannun su, babu sa’ansu a tarin dukiya a gaba xaya wannan nahiyar tamu. Lallai kuwa idan kika samu wannan nasara kinyi abinda har abada ba za a manta da ke ba a tarihin qasar nan, shi kuma Amzad ba shi da abinda zai iya biyanki da shi har izuwa qarshen rayuwarsa” Koda jin 39 BAYAN MUTUWA wannan batu sai gimbiya Lashmin tayi murmushi sannan tace. “Akwai abinda Amzad zai iya biyana da shi, ba komai bane face zuciyarsa da soyayyarsa, burina kawai ya so ni kuma ya qauna ce ni qaunar da babu algus a cikinta, ya riqe min alqawari na soyayya har izuwa ranar da zamu zamo abokan rayuwar juna domin mu samu zuri’a ta gari” koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a jawabinta sai mamaki ya turniqe sarki da mahaifiyar Lashmin suka zazzaro idanuwa suka kasa cewa komai. Daga can sai sarki ya dubeta yace mata “Yaushe kika fara ganin Amzad hard a za ki ce kin kamu da son sa haka?” Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubo wa gimbiya Lashmin sannan tace. ‘Na fara son Amzad tun ina da shekara bakwai a duniya, yakai Abbana shin zaka iya tunawa da wata rana da yammaci sakaliya sa’adda ka fita wani rangadi tare da ni” Koda jin wannan batu sai sarki salhan ya xaga kansa sama ya faxa kogin tunani. Kimanin shekaru goma sha xaya da suka gabata sarki salhan ya fita rangaxi a cikin keken dokinsa tare da ‘yarsa Gimbiya Lashmin a lokacin 40 BAYAN MUTUWA tana da shekara bakwai kacal a duniya. Dakaru kimanin xari uku ne ke kwaye da su suna tafiya a gefen wani daji dake daf da birnin nasu na misra sai kawai suka ji ana harbor musu kibiyoyi. Ashe Dakarun sumame ne suka kawo wa sarki hari. Nan take cikin gaggawa dakaru suka yanyame keken dokin sarki suka kareshi da manyan garkuwoyinsu don kada wata kibiyar ta zo ta sameshi ko ta soki Gimbiya Lashmin. Ana cikin hakanne sarkin yaqi ya leqo cikin keken dokin ya dube shi cikin alamun tsananin tashin hankali yace. “Ya shugabana maqiyane suka kawo mana harin bazato, duk yadda aka yi suna da xan leqen asiri a cikin fadarmu ta haka ne suka samu labarin wannan fitowar ta mu” Koda jin haka sai sarki salham ya girgiza kai yace. “Tabbas zancenka gaskiya ne amma sai bayan mun tsira sannan za mu yi bincike mu gano ko wanene wannan munafikin,wai shin adadin dakarun sumamen zai kai nawa?” Sarkin yaqi yace. “Ya shugabana sun ninkamu sau uku idan muka bari suka iso nan suka riskeka bani da tabbacin kai da Gimbiya za ku tsira, abu mafi kyau shi ne 41 BAYAN MUTUWA yanzu ku fito mu ruga izuwa cikin daji mu da tsirarun dakaru inyaso sauran Dakarun mu suyi kamar kana cikin wannan keken dokin su ci gaba da tsoronsa. Kafin a cim masu munyi nisa a cikin dajin mun zagaya tacan mun koma cikin birnin mu” Koda jin wannan batu sai sarki salham ya dubi sarkin yaqi cikin fushi yace. “Yanzu kana nufin mu gudu mubar sauran jama’ar mu anan a kashe su a banza kenan?” Sarkin yaqi yace. “Ai tun tuni sun siyar da rayukan su domin kare naka dana iyalinka don tsare darajar qasarmu, ka tuna cewar idan aka kasheka anan cikin dajin tamkar anci birnin mu da yaqine. Idan waxan nan abokan gabar suka san cewar sun gama da kai ai kuwa komawa za su yi suyi gaggarumin shirin yaqi su zo su baje birnin namu gaba xaya, jinin mutanen mu nawa ne zai zuba anan? Adadin dukiya nawa ne zata salwanta, kaga kenan ashe rayuwarka zata kuvutar da miliyoyin mutane da miliyoyin dukiya”. Koda jin wannan batun sai sarki salhim ya yi wuf ya xauki Gimbiya Lashmin ya goyata a bayansa ya xaureta tamau sannan ya zare takobinsa 42 BAYAN MUTUWA kuma ya xauki garkuwarsa ya fito daga cikin keken dokin. Nan yake shi da sarkin yaqi da tsirarun dakarun waxanda basufi su arba’inba suka ruga izuwa cikin daji suka bar sauran dakarun tsaye a gaban keken dokin suna gadinsa. Tafiyar su sarki ke da wuya sai ga dakarun sumamen sun iso bisa dawakansu da yawa. Koda suka hango keken dokin sarki sai dukkaninsu suka zare takubbansu suka afkawa dakarun dake tsaron keken dokin aka ruguntsime da yaqi. Duk da cewar dakarun sumamen sun ninka dakarun sarki salhan sau uku sai da aka shafe sa a guda cif ana baqin gumurzu sannan aka qarar da dakarun sarki.koda aka gama karkashe su aka leqa cikin keken dokin sai aka ga wayam. Nan take shugaban dakarun sumamen ya kurma ihu! Yace. “Tabbas waxannan mutanen yaudarar mu suka yi, tun xa zu sarkin misra ya fice daga cikin keken dokinnan ya gudu ku zo mu bi sawun su” Yana gama faxin hakan sai ya zaburi dokinsa yabi hanyar da su sarki salhan suka bi. 43 BAYAN MUTUWA Suma saran dakarun sai suka rufa musu baya suka rinka tsala gudu tamkar dawakan nasu za su tashi sama. ** Al’amarin sarki salhan da sarkin yaqi da tsirarun dakaru kuwa tunda suka fara gudu basu tsaya ba, cikin sa a kuwa suka hango qofar birnin misra daga can nesa tazarar kimanin zango xari. Nan take farin ciki ya lulluve su suka qara gudun su, sai daya kasance bai fi sauran taku baifi saba’in ba tsakaninsu da bakin qofar garin sai kawai suka hango dakarun sumame acan bayan su kaxan sun durfafo inda suke a guje bisa dawakai. A daidai wannan lokacin Nazmin mahaifin Amzad ya dawo daga gona yana save da fatanya a kafaxarsa kuma yana riqe da hannun xansa Amzad yaron da bai wuce shekara tara ba a duniya. Lokacin da su sarki salhan suka waiga bayansu yana goye da Gimbiya Lashmin suka hango dakarun sumame a bayansu sai suka qara qarfin gudunsu, koda ganin haka sai dakarun sumamen suka soma xana kibiyoyi akan baka suna harbinsu kuma suna daxa kusanto su. Nan fa suka soma yiwa dakarun 44 BAYAN MUTUWA sarki salhan xauki xai-xai suka riqa faxuwa qasa matattu. Har ya kasance sauran sarkin yaqi da sarki salhan kaxai suka rage a raye suna ta gudu. Tun daga nesa sarkin yaqi ya riqa qwalawa masu gadin qofar gari kira yana basu umarnin su buxe qofar amma da yake masu gadin basu shaida ko su wayeba sai sukaqi buxe qofar. A wannan lokacin Nazmir da xansa Amzad kuwa na daf da isa bakin qofar birnin Misra.koda suka jiyo gudun mutane biyu a bayansu sai suka waiwaya a firgice, take Nazmir yaga ashe sarki ne da sarkin yaqi suke wannan gudun na ceton ransu, kuma ga dakarun sumame can a bayansu sun durfafo sauran qiris su cimmasu, kawai sai Nazmir ya juya yana dakawa masu gadin tsawa yana musu ishira cewar sarki ne fa, nan take masu gadin suka yi sauri suka buxe qofar. Amman kuma sai masu gadin suka kasa fitowa domin kawowa sarki xauki saboda ganin yawan abokan gaba domin idan suka fito za a samu galabar shiga cikin birnin. 45 BAYAN MUTUWA BAYAN MUTUWA 4 Kawai sai gani aka yi kibiya ta soki sarki a cinya ya kife qasa, Lashmin dake goye a bayanshi sai ta faxi qasa ta riqa mirginawa izuwa baya can wajen da maqiya ke tahowa tana ihu, shima sarkin yaqi sai kibiya ta soke shi a gadon baya ya kife qasa. Koda ganin abinda ya faru sai Nazmir ya saki hannun xansa Amzad ya ruga da gudu izuwa inda sarki yake kwance ya sunkuceshi ya azashi a kaxarsa ya ruga da gudu dashi izuwa cikin birnin misra ko tunawa da batun xansa bai yi ba. Shima yaro Amzad sai ya ruga da gudu ya xauko Gimbiya Lashmin a kafaxarsa ya nufi qofar birnin misra, yana gudu ana harbor masa kibiyoyi har kibiya guda ta soke shi a hannu sai ya yi matuqar dauriya yaci gaba da gudu a haka jini na zuba a hannunsa ga lashmin a kafaxarsa yana layi jiri na xibansa amma sai daya shige cikin qofar birnin. 46 BAYAN MUTUWA Sarkin yaqi ne ya qaraso da qyar da gudu yana faxuwa yana tashi har ya shiga cikin qofar, ai kuwa yana shiga sai dakarun dake tsaron qofar garin suka yi sauri suka mayar da qofar suka rufeta kuma suka hau kan ganuwa suka xana kwari da bakansu. Koda ganin haka sai dakarun sumamen suka yi tirjiya, bisa dole suka kaxa dawakansu suka juya da baya cikin baqin cikin rashin samun nasarar kashe sarki salhan. A cikin birni kuwa ranga-ranga aka xauki sarki da sarkin yaqi aka tafi da su izuwa gidan sarauta. A lokacin wani bafaxe ya zo ya fizge Gimbiya Lashmin daga kan kafaxar Amzad sai tayi wuf ta fizge wata qaramar sarqa dake wuyan Amzad ta dubeshi cikin murmushi tace. “Har abada ba zan mance da kai ba, ka zo gidan sarki ka amshi sarqarka a hannuna, ni kuma zan saka maka da abinda yafi komai daraja a wajena”. Tana gama faxin haka sai ta riqa xagawa Amzad hannu shima sai ya rinqa xaga mata hannu har aka hau kan doki da ita aka ruga da gudu suka qule ya daina hangota, a sannan ne mahaifin Amzad ya kama hannunsa ya jashi suka nausa cikin birni. 47 BAYAN MUTUWA A lokacin da sarki salhan ya zo nan a tunaninsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi Gimbiya Lashmin yace. “Yanzu ashe tun daga wannan ranar da Amzad ya ceci rayuwarki kika kamu da son shi?” koda jin wannan tambayar sai itama Gimbiya Lashmin ta zubar da hawaye sannan ta zura hannu aljihun rigarta ta fiddo wannan sarqa ta Amzad ta nunawa sarki tace. “Qwarai kuwa tsawon waxannan shekarun ina ajiye da sarqa Amzad kuma ina begensa a cikin zuciyata dare da rana. Tambayar da nake son na yi maka mene ne ya hana Amzad zuwa wajen da nake ya karvi sarqarsa dake hannuna? Mene ne dalilin daya saka duk sa’adda nace kasa aje a nemo Amzad da mahaifinsa sai kace har izuwa tsawon waxannan shekarun kace an halaka shi, nima kuma ka saka aka tsare ni a cikin gidan sarauta baka barina na fita sai da sharaxin wajen da zani nan xin zanje, ka hanani samun sakewa da zan yi bincike akan sa har zuwa girmana. Tabbas ka jefani a cikin kurkukun soyayya wanda yafi rijiya gaba dubu, ka sanya min xaci a zuciya wanda yafi azabar fitar rai, kuma ka dusashe 48 BAYAN MUTUWA min hasken idanu da baqin ciki da yafi dare duhu, tsawon shekaru sha xaya kenan ban ga masoyina ba Amzad rabona da shi tun ina da shekaru bakwai a duniya sai yau da aka gurfanar dashi a gabana domin na yi masa shari’a da azzalumin attajiri Huzulu. To ka sani ko ka bani amsar tambayoyina ko kaqi a yau xinnan sai naje na baiwa Amzad sarqarsa wacce na cire a wuyansa tun muna yara a ranar day a ceci rayuwata. Ko kana so ko baka so yakai Abbana sai na cika alqawarina a gareshi na bashi abin da yafi komai daraja a wajena kuma ba komaibane face soyayyata da kuma aurena”. Lokacin da Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai shima sarki sairan ya ji hawaye sun suvuce masa don haka sai ya kamo Gimbiya Lashmin ya rungumeta a qirjinsa yana kuka yace. “Ki gafarta min yake ‘yarta kiyi sani cewa akwai dalili mai qarfi wanda yasa na raba rayuwarki da Amzad xan Nazmir waxanda suka ceto rayuwarmu a tare kuma a lokaci guda, dalili kuwa shi ne bayan anyi mana magani ni da sarkin yaqi wato an cire kibiyoyin dake jikinmu an sa mana magani don kashe dafin kibiyar sai kawai muka ga bokana wato Darzas ya baiyana tsulum a gabanmu. 49 BAYAN MUTUWA Boka Darzas ya dubeni cikin damuwa yace “Ya shugabana kayi sani cewar ba wani bane ya turo dakarun sumame su kasheka ba face sarki zardar na birnin mailus, kuma munafikin da ya sanar da su cewar zaka fita yawon rangaxi ba wani bane face bawanka yunus mai kula da dawakanka na hawa, musamman sarki mailas ya siyar da shi izuwa fa farakenku suka zo dashi nan qasar,kai kuma ka siye shi a matsayin bawa har ka aminta da shi, saboda qwazon shi a wajen aiki da qwarewarsa wajen kiwon dawakai.ban gano wannan sirrin ba sai yanzu da zan zo wajenka na yi bincike akan kawo wannan harin. Abu na gaba da zan sanar maka kar ka sake kabar wata alaqa ta soyayya ta qulu a tsakanin Gimbiya Lashmin da Amzad xan Nazmir waxanda suka ceci rayuwarka xa zu a qofar birninnan daga hannun dakarun sumame, domin bincike ya nuna ba za su tava zama abokan rayuwar juna ba, kuma qarshen soyayyar tasu tana qunshe da baqin ciki a gare su da duk masoyansu” Boka Darzas yana gama faxin haka sai ya vace vat. 50 BAYAN MUTUWA S arki Salhan ya dubi Gimbiya Lashmin ya ci gaba da magana “Bisa wannan dalilin tun daga wannan ranar na sanya hijabi a tsakaninki da Amzad har mahaifinsa ya rasu ban bari kun sake ganin junaba. Ki yafe min yake ‘yarta, lallai ki yafe min na yi miki babban laifi amma son da nake miki ne gami da son ganin kyakkyawar rayuwarki a gaba yasa na yanke wannan hukunci”. koda sarki salhan ya zo nan a zancensa sai Gimbiya Lashmin ta fashe da matsanancin kuka, al’amarin daya karya zukatan iyayenta kenan suka kamu da tsananin tausayinta. Don haka sai mahaifiyarta ta janyota ta rungumeta a kan qirjinta tana mai rarrashinta tana bata baki har izuwa tsawon ‘yan daqiqai amma bata daina kukan ba, daga can sai Lashmin ta janye jikinta daga cikin na mahaifiyarta ta miqe tsaye ta dubi sarqa tace. “Ya kai Abbana kayi sani cewar babu wani qarfi wanda ya isa ya dates so na gaskiya a tsakanin masoya,addini ko sihiri, dukiya ko talauci,wuya da daxi basa raba masoya sai dai mutuwa da qaddara. ni banyi imani da dukkan abinda bokayen ku ke faxaba muddin ya shafi soyayyata, idan kuma har abinda suka faxa ya zama gaskiya to na yarda na mutu akan qirjin 51 BAYAN MUTUWA masoyina domin shi ne abinda ya fiye min komai farin ciki a rayuwata” koda gama faxin haka sai Gimbiya Lashmin ta miqe tsaye da sauri ta juya ta fice daga cikin turakar mahaifiyarta na kwala mata kira amman ko waigowa ba. Koda ganin haka sai mahaifiyar tata ta miqe da sauri da nufin taje ta ruqo ta amman sai sarki ya yi wuf ya runqota ya dakatar da ita yace mata. “Kar ki kuskura ki dakatar da zuciyarta da take ruruwa da wutar soyayya, domin daidai take da mahaukacin zakin da ya fusata a cikin daji a lokacin da yake fama da tsananin yunwa,kinsa cewa idanunta a rufe suke zai iya banke kowa” Koda jin wannan batun sai mahaifiyar Lashmin ta koma ta zauna kusa dashi ta xora kanta akan qirjinsa a lokacin da hawaye ya zubo mata shi kuma ya qanqameta a jikinsa tana mai cewa. “Haqiqa ‘ya tayi gadon ubanta akan zafin soyayya ko kuwa ka mance ne da yadda muka mallaki junanmu, mun sha baqar wahala da gwagwarmaya?” koda jin wannan batu sai hawaye ya suvutowa sarki salhan yace. “Zan iya mancewa da komai na rayuwata amma ba zan iya mancewa da tarihin soyayyata ba 52 BAYAN MUTUWA yake matata, a duniya banga abin da yafi soyayya daxi da haxari ba, kuma babban kuskure da mutum zai yi a rayuwarsa shi ne yace zai shiga tsakanin masoya” Koda jin wannan batun sai hankalin mahaifiyar Lashmin ya dugunzuma ainun ta janye jikinta daga na sarki suka fuskanci juna ta dubeshi cikin alamun tsananin damuwa tace. “Wai shin yanzu kana nufin kenan zaka kyale Lashmin ta yi soyayya da Amzad xan Nazmir alhalin kasan cewar qarshen soyayyar tasu mummun qarshe ne da mugun baqin ciki?” Koda jin wannan tambayar sai hawaye ya sake suvuce wa sarki sairan yace. “Y azan yi da qaddara? ko na bar Gimbiya ko na hanata saduwa da Amzad ba zan iya cire son sa ba daga zuciyarta, idan kuwa akwai sonsa a ranta idan muka matsa akan rabu su za mu iya rasata gaba xaya, wanne za mu zava a ciki yanzu? Ni dake muna son farin cikinta a yanzu idan muka hanata kuma a qarshe mu rasata ko kuwa mu barta ta mutu a cikin farin ciki. Shi kansa mahaifin Amzad yasan da wannan matsalar tun kafin ya rasu kuma mahaifiyarsa ma ta sani,bisa wannan dalilin suka nemi taimakon boka marigayi zardash ya saka Amzad ya mance da duk 53 BAYAN MUTUWA abinda ya faru tsakaninsa da Lashmin a wannan lokacin da suke yara amman ya tabbatar mana da cewa duk ranar da yaga wannan sarqa tasa wacce Lashmin ta cire a wuyansa to sai ya tuna da komai” Koda jin wannan batu sai hankalin mahaifiyar Lashmin ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ta kamu da tsananin baqin ciki kuma ta fashe da matsanancin kuka tana mai cewa. “Mene ne dalilin daya sa tuntuni baka sanar da ni wannan sirrinba, lallai inda nasan dashi da sai nasan hanyar da na bi nasa Gimbiya ta manta da Amzad kuma da sai nasa ta yi aure domin mu ga jikan mu da idanuwa kafin mutuwarmu amma yanzu baqin alwalami ya gama bushewa domin wannan burin na mu ba zai tava cika ba” Koda jin wannan batun sai sarki salhan ya sake kamo matar tasa ya rungumeta a kan qirjinsa suka fashe da kuka a tare. Komai rashin tausayin zuciyar mutum idan ya dubi waxannan ma’aurata a wannan lokacin da suke yin wannan kuka na takaici da baqin ciki dolene ya kamu da tsananin tausayinsu ba zai san sa’adda shima zai zubar da hawaye ba. Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin Gimbiya Lashmin da iyayenta a can gidan sarauta. 54 BAYAN MUTUWA Al’amarin Amzad kuwa lokacin da mataimakin sarkin yaqi tare da dakarunsa suka tafi das hi izuwa can gidan sarki na bayan gari sai kansa ya xaure kuma mamaki da wasi-wasi suka turnuqeshi, abu na farko daya fara tambayar kansa shi ne wai shin mene ne dalilin da yasa sarki ya sauka daga kan karagarsa ya baiwa ‘yarsa Gimbiya Lashmin hart a kwato masa ‘yancinsa alhalin a tsawon shekaru baya sarki ya kasa yi masa wannan taimakon. Amzad ya sani cewa mahaifinsa gagarumin attajirine domin ya mutu ya bar dukiya mai tsananin yawan da babu mai kamarta a gaba xaya birnin misra amma bayan mutuwar tasa ne shi da mahaifiyarsa suka faxa cikin tarkon attajiri Huzulu har ya zamana cewa sun rasa komai nasu suka zama talakawan da suka fi kowa babu domin da qyar da sixin goshi Amzad ya tsira da jaki guda xaya wanda yake sana’ar dakon tubalin gini dashi. Da hakane yake samo abinda za su ci abinci shi da mahaifiyarsa, sai dai ta kai basu da gidan kwana kuma basu da komai basu da kowa face jakin nasa guda xaya. 55 BAYAN MUTUWA Komai zafi komai sanyi sai dai su rakave a kangwaye ko rusashen gida su kwana, sau tari idan zai tafi sana’arsa ta dako sai dai yakai mahaifiyarsa ajiya izuwa maqotansu,inya dawo sai ya zo ya xauketa akan jakinsa su tafi inda za su kwana. Kullum haka suke yin wannan rayuwa cikin qunci, talauci da matsanancin baqin ciki, a duk sa’adda mahaifiyarsa ta tuno da irin daular da suke ciki sa’adda mahaifinsa ke raye sai tayi ta kuka tana tsinnewa attajiri Huzulu. Da qyar Amzad ke rarashinta yana gaya mata maganganu masu daxi domin hankalinta ya kwanta. Abu na biyu daya jefa Amzad cikin tsananin mamaki shi ne wannan kallon da Gimbiya Lashmin ta yi masa a lokacin da zai fita daga cikin fada. Shi dai a rayuwarsa babu waya ‘ya mace data tava yi masa irinsa face Gimbiya Lashmin. Kallo ne wanda indai aka yiwa mutum sai ya tabbatar da cewa akwai qauna ga wanda yayi masa akan wane dalili Gimbiya zata so ni ina matsayin talaka fitik wanda bai shafi jinin sarauta ba. Ai ko a mafarki soyayya ba zata qullu a tsakanin mu ba, domin qwarya sai dai tabi qwarya, 56 BAYAN MUTUWA dan tabi akwashi kuwa fashewa zata yi. Haka dai Amzad ya yi ta wannan tunanin gami da saukar da ajiyar zuciya, a haka har suka iso wannan gidan na sarki salhan dake can bayan gari. Kai tsaye mataimakin sarkin yaqi ya shige dashi har can cikin gidan. Suna isa babban falo na gidan sai Amzad ya hango mahaifiyarsa zaune bisa teburin cin abinci an cava mata ado da tufafi na isa sannan ga abinci kalakala irin na manyan attajirai da sarakai a gabanta, kuyangi na zuba mata dukanin kalar abinci da take so tana ci cikin tsananin farin ciki. Yanayin tafiyar Amzad kawai mahaifiyar tasa taji sai ta miqe tsaye cikin murna ta buxe hannayenta tana mai cewa. “Taho gareni ya kai xana, zo ka bani labari wane gaggarumin aiki ka yi ga sarki wanda ya saka har aka bamu wannan daular?” Cikin tsananin farin ciki Amzad ya qarasa wajen mahaifiyar tasa ya rungumeta sannan ya zaunar da ita akan kujerar da take zaune da. A sannan ne mataimakin sarkin yaqi ya sallami gaba xaya kuyangin dake wajen suka fice daga falon suka barsu su uku kacal. Kafin Amzad ya buxe 57 BAYAN MUTUWA baki ya baiwa mahaifiyar tasa amsar tambayarta sai mataimakin sarkin yaqin ya tari numfashinsa yace. “Yake ummul Amzad kiyi sani cewa Allah ne ya dube ku ya yi muku rahama bisa tsohon zalluncin da aka yi muku na tsawon shekaru, a yau ne ‘yar sarki Gimbiya Lashmin ta karvi aro karagar sarki saboda shi bashi da lafiya, a yau xin ta saka aka fito da duk takardun shari’oin da ake kawowa fada ta dubasu amma sai ya zavo taku shari’ar kacal ta saka aka kirawo attajiri Huzulu tare da xanki Amzad aka gabatar da shari’ar a gaban mutanen fada. A yanzu haka maganar da nake yi miki Gimbiya tasa an aika da attajiri Huzulu kurkuku an tsareshi kuma za a ci gaba da bincike har a gano gaskiyarku a karve duk dukiyar ku dake hannunsa a dawo muku da ita” Koda mataimakin sarkin yaqi ya zo nan a jawabinsa sai mahaifiyar Amzad ta kamu da tsananin farin ciki bata san sa’adda ta fashe da kuka ba, kuma tayi suvutar baki tace. “Yanzu ashe dama akwai ranar da ‘yar sarki zata tuno da halaccin da muka yi mata?” koda jin wannan batu sai mamaki ya turniqe Amzad ya dubi mahaifiyar tasa yace. 58 BAYAN MUTUWA “Yake Umma wane irin halacci ne muka yiwa Gimbiya Lashmin?” koda jin wannan tambayar sai tayi saurin ta wayance tace. “Aa ina nufin nace dama sarki zai tuno da irin biyayyar da mahaifinka yayi masa a rayuwa, ai a lokacin da mahaifinka yana raye yayi hidima da dukiyarsa a gidan sarauta sosai don haka na yi mamakin yadda aka yi sarki ya mance da bayansa yaqi ya neme mu ya taimaka mana” Koda jin wannan batu sai Amzad ya yi murmushi yace. “Haba yake umma, in banda abinki kuma ai su masu mulki suna da yawan mantuwa, sannan kuma kinsan ance ba a mugun sarki sai mugun bafade ai makusantansu ne suke hanasu yin aikin alheri. Wata qila yana son ya taimaka mana koma yana aiko mana da taimakon fadawansa na dannewa bamu sani ba”. Koda jin haka sai mataimakin sarkin yaqi yace. “Qwarai kuwa ai abin dake faruwa kenan” Amzad yace. 59 BAYAN MUTUWA BAYAN MUTUWA 5 ‘To amma mene ne dalilin dayasa duk a tsawon shekarunnan ko sau xaya sarki bai tuno da shari’armu bad a attajiri Huzulu sai a yau rana xaya da ‘yarsa ta hau karagar mulki ta tuno damu kuma har tayi mana wannan gagarumin taimako tamkar muna binta bashin wani abu a rayuwa? Alhalin bata ma san mahaifina ba bata irin gudumawar daya basu” Koda jin wannan tambayar sai mataimakin sarkin yaqi ya yi caraf yace. “Ai kasan babu mamaki shi sarki baya son ya vatawa fadawansa shi yasa ya kasa yin komai akan wannan shari’a taku tsawon shekarun da aka xiba musamman tunda duk manya fadawansa yaran attajiri Huzulu ne amma ai ita Gimbiya Lashmin babu ruwanta da fadawan sarki tunda yarinyace, duk abinda ya zo mata a cikin rai shi zata aiwatar”. Koda jin haka sai mahaifiyar Amzad ta gyaxa kai tace. “Na yarda da maganar ka” Nan take mataimakin sarkin yaqi ya miqe tsaye ya dubi Amzad yace masa. 60 BAYAN MUTUWA “Ni zan koma wajen dakaru domin na daxa tabbatar da tsaro kamar yadda aka uwarceni, ina son ku saki jikinku kuji daxinku duk abinda kuke buqata akwaishi a cikin gidannan kawai ku tambayi kuyangi” Amzad ya yi murmushi gami da godiya ga mataimakin sarkin yaqi shi kuma sai yace. “Ai bani za ka yiwa godiya ba face Gimbiya Lashmin kuma kusani cewa a koyaushe zata iya kawo muku ziyara ba zato” Koda jin haka sai Amzad ya dube shi cike da mamaki yace. “Haba ya za a yi Gimbiya Lashmin ta zo nan saboda mu kawai” Mataimakin sarkin yaqi ya yi xan guntun murmushi yace. “Baka yi mamakin yanda ta wulaqanta attajiri Huzulu ba saboda kai sai zuwanta nan? Ina yi muku sallama kuyi barci mai daxi sai da safe” Koda gama faxin hakan sai mataimakin sarkin yaqi ya juya ya fice daga cikin falon ya bar Amzad da mahaifiyarsa nan dai suka qarasa cin abinci nasu. Suna gamawa sai kuyangi suka kawo musu ruwa da qyalle mai kyau suka wanke hannayensu suka goge danshin hannunsu. A sannan ne xaya daga cikin kuyangin ta dubesu tace. 61 BAYAN MUTUWA “Yanzu zan sa a raka ku izuwa xakin barcin kowannanku” Koda jin haka sai Amzad yace. “Aa kada ku rabani da mahaifiyata, ban tava kwana ba tare da ita ba” Koda jin haka sai gaba xaya kuyangin suka bushe da dariya, babbar cikin su wacce ta fara magana da farko ta dubeshi cikin mamaki tace. “Yanzu kai da girma nan naka kana cikakken saurayi amma baka tava rabuwa da shimfixar mahaifiyar ka ba, sai kace wani qaramin yaro?” Amzad ya gyaxa kai cikin murmushi yace. “Qwarai kuwa domin bani da kowa a cikin wannan duniya face wannan mahaifiyar tawa, bani da uwa bani da uba maraya na taso, bani da damuwa ko ‘yar uwa kuma ban tava yin aboki ba ko qawa. Bani da budurwa ta yaya kike tsammanin zan iya rabuwa da uwata a dare xaya alhalin tun sa’adda take dauke da cikina muke tare kawo i yanzu?” koda Amzad ya zo nan a zancensa sai jikin gaba xayan kuyangin ya yi sanyi suka kamu da tsananin mamakinsa gami da tausayinsa cikin qaramar murya shugabar kuyangin ta dubi wata daga cikinsu tace. “Maza ki kai su babban xakin barci na gidannan, haqiqa raba wannan uwa da xanta ba qaramin aiki bane” Nan take aka yiwa Amzad da 62 BAYAN MUTUWA mahaifiyarsa jagora izuwa cikin wani qaton xakin barci maixauke da wani shimfixexen luntsumemen gado wanda yasha shimfixu masu taushi gami da qaton bargo da kuma matasan kai guda huxu. Da yake lokaci ne na sanyi sai Amzad ya kama mahaifiyarsa ya kwantar da ita akan gadon sannan shima ya kwanta a kusa da ita ya janyo qaton bargon ya lulluve jikinsu gaba xaya. Koda mahaifiyar tasa taji tsananin taushin katifar da suke kwance akai kuma taji xumin qaton bargon da suke lulluve das hi sai ta kama kuka tace. “Yakai xana ka yi sani cewa a rayuwata ban tava zaton cewa za mu sake tsintar kanmu a cikin irin wannan daular ba wacce rabon mu da ita tsawon shekaru ashirin da biyar kenan tun kafin ka zo wannan duniya lokacin da mahaifinka ke raye” koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Amzad yace. ‘Yake Ummina na so ace kina gani da idanunki domin kiga irin hawayen farincikin dake zubo akan kumatuna kuma kiga irin kayan alatun dake cikin gidannan, ki tuna cewa munsha kwana a kasa bisa tabarma kuma a filin Allah inda ruwa da iska ke qarewa a kan mu amman yau gamu a cikin qereren 63 BAYAN MUTUWA gida na kwatance bisa gado na alfarma kuma munci irin abinci da sai mai isane ke cinsa. Wai shin da me za mu iya sakawa wannan ‘yar sarki?” koda jin wannan tambayar sai hankalin Mahaifiyar tasa ya dugunzuma ta rasa abinda za ta ce masa, kawai sai tace ai. “ Kawai sai dai muce Allah ya saka masa da alheri” ta xan yi shiru taci gaba da cewa da shi. ‘Kai kar ka cikani da tambaya ka hanani barci akan wannan daddaxan gado sai da safe” Tana gama faxin hakan sai ta sake jan bargo ta lulluve fuskarta gaba xaua ko da ganin haka sai shima Amzad ya lulluve fuskarsa nan danan kawai barci ya sacesu ba tare da sun sani ba. Al’amarin sarkin yaqi kuwa lokacin da ya tafi da attajiri Huzulu izuwa can babban kurkuku na birnin Misra basu fuskanci wata matsala ba babu wani hari da aka kai musu har suka isa kurkuku. Da zuwan su sai sarkin yaqi ya isar da saqon gimbiya Lashmin izuwa ga shugaban masu gadin kurkukun cikin biyayya shugaban wani narkeken qato mai qirar mutanen farko ya risina ga sarkin yaqi cikin biyayya yace, 64 BAYAN MUTUWA ‘An gama ya shugabana” Nan take aka saka wasu masu gadin kurkukun subiyo suka karvi attajiri Huzulu daga hannun dakarun sarkin yaqi aka zuba masa sarqi a hannunsa da kafafunsa kawai sai suka ji attajiri Hauzulu ya taqarqare ya bushe da dariyar mugunta, al’amarin da ya yi matuqar baiwa sarkin yaqi tsoro da mamaki kenan. Daga can attajiri Huzulu ya murtuke fuska ya dubi sarkin yaqi yace masa. “Wannan gidan da kuka kawoni ji nake kamar a cikin gidana kuka kawoni, na rantse da darajar iyayena da kuma darajar abin bautarmu kana barin nan da tazarar sa’a xaya jal za a zo a fitar da ni daga cikin wannan kurkukun”. D aga can sai attajiri Huzulu ya murtuke fuskarsa ya dubi sarkin yaqi yace “Wannan gidan da kuka kawoni ji nake kamar a cikin gidana nake. Na rantse da darajar iyayena da kuma darajar abin bautarmu kana barin nan da tazarar sa’a xaya jal za’a zo a fitar da ni daga cikin wannan kurkuku” Ya xan yi 65 BAYAN MUTUWA shiru na wani xan lokaci yana kallonsa sannan ya ci gaba da magana cikin izza. “Ga saqo kaje ka gayawa Gimbiya kace da ita ni attajiri Huzulu na rantse da jinin uwata da ubana ita bata isa ta iya tozartani ba a cikin wannan duniyar, ka yaga mata cewa na gaba ya yi gaba na baya sai labari. Sannan ka shaida mata cewa lallai ta tabbatar da cewar ta mori jin daxin wannan mulki da take kai a iya tsawon ‘yan kwanakin da sarki ya ara mata domin kwanakin na qarewa zata zama baiwata, domin misra gaba xaya zata zama tawa. Saqo na qarshe a gareta ka gaya mata cewa wannan wulaqancin da tayi mini saboda tsohon masoyinta tun quruciya ta yi shi a banza domin bazata iya karve dukiyarsa dake hannuna ba ta damqa masa, kuma har abada ita da shi ba za su tava zama abokan rayuwa ba” Koda attajiri Huzulu ya zo nan a zancensa sai sarkin yaqi ya fusata ainun ya gabza masa naushi a fuska. Saboda qarfin naushin sai da attajiri Huzulu ya faxi qasa jini ya furzo waje daga bakinsa. Attajiri Huzulu ya miqe tsaye ya shafa bakinsa yaga jini kawai sai ya sake bushewa da dariya sannan yace. 66 BAYAN MUTUWA “Kayi babbar nasara hard a ka samu ka naushi babban maqiyinka. Yau zan sanar dakai babban sirrin da baka sani ba, ni ne na kashe ubanka domin na sauya tsarin gidan sarauta mu saboda shi ne kaxai baya bani haxin kai a cikin ‘yan majalisar sarki” Koda jin wannan batu sai sarkin yaqi ya daddage ya kurma ihu kuma ya zare takobinsa ya xagata sama ya kaiwa attajiri Huzulu sara amma sai shugaban kurkukun ya yi wuf ya zare tasa takobin ya kare saran ya dube shi a fusace yace. “Ai yanzu baka da sauran iko akan wannan fursuna face mun sami umarni daga wajen sarki ko Gimbiya” Koda jin wannan batu sai sarkin yaqi ya kamu da tsananin baqin ciki gami da takaici domin inda yasan cewa attajiri Huzulu ne ya kashe masa mahaifinsa da tun xa zu akan hanya zai kashe shi sai dai ya fuskanci kowane irin hukunci daga wajen sarki. Cikin tsananin fushi sarkin yaqi ya dakawa shugaban dakarun gidan kurkukun tsawa yace. “Ka bani attajiri Huzulu na kashe shi yanzu take anan ko kuma kai na yaqeqa na kasheka” Koda jin haka sai gaba xaya Dakarun dake tsaron kurkukun suka rugo da gudu izuwa bayan shugaban nasu suka 67 BAYAN MUTUWA zazzare takubbansu sai gashi sarkin yaqi da dukkan dakarunsa sun zama ‘yan kaxan a cikinsu. Attajiri Huzulu ya sake bushewa da dariyar mugunta a karo na biyu ya dubi sarkin yaqi yace masa. “Kai yaro ni murucin kan dutse ne ban fito ba sai dana shirya. Bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane. Kaje ka rungumi qaddara ka qarasa rayuwarka a matsayin bawan sarki idan kuwa kace zaka tavo tsuliyar dodo wanda a halin yanzu barci ya keyi, tofa idan ya farka sunanka gawa” koda gama faxin hakan sai attajiri Huzulu ya dubi wannan narkeken qato wato shugaban Dakarun kurkukun yace. “Yakai mandazi maza kasa a kaini xakina” Ba tare da wata gardama ba kuwa mandazi yasa aka kwance sarqoqin dake jikin hannun attajiri Huzulu da qafafunsa aka ruke hannayensa aka tafi dashi, su kuwa su sarkin yaqi sai aka ritsasu da makamai har sai da aka ga sun juya sun fice daga cikin kurkukun gaba xaya sannan aka rabu dasu aka maida qofa aka rufe. Nan fa baqin ciki ya turnuke sarkin yaqi ya dubi gaba xaya yaransa yace “Haqiqa birnin misra bata sarki bace, ta attajiri Huzulu ce, Gimbiya ba zata iya yaqi da attajiri Huzulu ba tunda sarki ya kasa, mu qalilan ne a cikin wannan masarautar bama tare da 68 BAYAN MUTUWA Huzulu, duk abinda ya faxa sai ya faru, tabbas nan da cikar sa’a guda za a fitar da shi daga cikin wannan kurkuku” Koda jin wannan batun sai xaya daga cikin yaran nasa ya dube shi yace. “Haba ya shugabana ta yaya za a iya zuwa a fitar da attajiri Huzulu daga cikin wannan kurkuku mai tsananin tsaro haka alhalin sama da shekaru xari baya ba a tava samun fursunan daya tava guduwa ba daga cikinsa?” Koda jin wannan batun sai sarkin yaqi ya jinjina kai yace. “Ai kuwa yau za ka ga abin mamaki da idanunka, lallai abinda bai tava faruwa ba a qasarnan yau zai faru, yanzu abinda zai faru za mu samu waje mu voye mu zuba idanu muyi kallo kawai” Koda gama faxin haka sai sarkin yaqi yaja gaba xayan dakarunsa suka ruga izuwa can saman wani tsauni dake can nesa kaxan da inda kurkukun yake suka kwanta. Da yake akwai tarin bishiyoyi masu duhuwa akan tsaunin kuma gashi darene babu yadda za a iya mutum ya gane cewa akwai mutum a saman tsaunin. Haka dai su sarkin yaqi suka ci gaba da lamvo akan tsaunin har tsawon sa a guda basu ga wani abu ya faru ba, har sarkin yaqi ya yunqura zai tashi tsaye 69 BAYAN MUTUWA sai kawai ya hango wasu xaruruwan waxansu manya aljanu a can qololuwar sama sun tun karo wannan kurkukun tun da sarkin yaqi da dakarunsa suka zo duniya ba su tava ganin aljanu masu tsananin girma da muni irin su ba. Nan take wasu daga cikin yaran sarkin yaqi suka zube a sume,wasu suka haukace, shi kansa sarkin yaqi ba don yana da qarfin sihirin tsafiba da nan take zai haukace shima. 70 BAYAN MUTUWA ** Kai tsaye jibga-jibgan aljanun suka duro qasa bisa turba a tsakiyar kurkukun. Duk badakaren daya sha gabansu da nufin ya yaqesu sai dai aga naman jikinsa ya zagwanye ya zama kwarangwal,sutural jikinsa ce kaxai take ragewa zube a qasa. Al’amarin daya razana dukkanin dakarun kurkukun kenan suka rinqa rugawa da gudu suna vuya, kai bama dakarun kurkukun ba hatta fursunoni vuya suka rinqa yi duk da cewa sun sami damar guduwa saboda tsoron yin arba da waxannan mugayen aljanun. Ko bango aljanun suka dosa sai dai kaga yarushe ya zube qasa, qofar qarfe kuwa narkewa take ta zama ruwa. Shugaban Dakarun kurkukun kuwa wato mandazi da hannunsa ya buxe xakin da attajiri Huzulu ke ciki ya fito das hi ya damqawa aljanun. Ba tare da attajirin Huzulu ya yi wata razana ba kawai sai ya nufi xaya daga cikin aljanun yana qyaqyata dariyar farin ciki, take aljanin ya zube qasa a gaban sa shi kuma sai ya haye bayan aljanin ya tashi dashi sama. Gaba xaya sauran aljanun ma sai suka tashi saman suna masu rufa masa baya. Kafin cikar daqiqu sun luluqa izuwa qololuwar sararin samaniya. 71 BAYAN MUTUWA Suka vace vat! A cikin gajimare,a sannane sarkin yaqi ya miqe tsaye zumbur ya shiga karanta waxansu xalasiman tsafi yana tofawa yaransa waxanda suka haukace da waxanda suka suma sakamakon ganin waxannan mugayen aljanun. Da qyar da sixin goshi ya dawo da su cikin haiyacinsu sannan suka sauko daga kan wannan tsaunin suka koma izuwa cikin gari cikin tsananin fargaba da tashin hankali. Amzad yana cikin xakinsa a kwance ya yi shiru lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalli mahaifiyarsa dake kwance, tana barci cikin kwanciyar hankali ga mamakinsa sai ya ji wani daxi ya lulluve masa zuciya. Tun tsawon lokacin daya taso a duniya bai tava ganin mahaifiyarsa yana yin barci mai daxi da nutsuwa kamar daren wannan lokacin ba. Hakan yasa shi ya miqe a hankali ya komo tsakiyar xakin ya zauna yana dube-dube. A lokacin mamaki kuma ya kama shi, ba komai ne yasa yake wannan mamakin ba face har yanzu ya kasa gano dalilin daya saka Gimbiya 72 BAYAN MUTUWA Lashmin ta yi musu wannan taimakon, tabbas yasan ruwa baya tsami banza. Duk da haka kuma sai ya ji wani tsoro ya lulluve masa zuciya, ba komai ne yasa fargabar a zuciyarsa ba face tunano attajiri Huzulu da kuma tsananin hatsabibancinsa, tabbas yasan ba zai barsu a haka ba, saboda har yanzu yana tuna irin arangamar da suka yi da shi a farkon lokacin da aka kai masa samace akan Amzad ya kai qarasar gaban sarki domin kwato musu dukiyarsu. Sun haxu da attajiri Huzulu ne a kasuwa yana zaune a wata rumfarsa shi kuma Amzad ya koro jakunan xauke da qasa yana zagaya kasuwa da su, cikin sauri ya saka aka kirawo masa Amzad, bai yi wata-wata ba ya shiga rumfar ya same shi. A wulaqance ya dubi Amzad yace masa “Har girman wuyanka ya kai da zaka shigar da ni qara gaban sarki? To ka sani kai baka isa ka amshi ko sisi daga wajena ba, kuma duk duniyar nan babu wanda zai iya kwato maka koda sisin kwabo daga hannuna”. Jin haka sai Amzad yace masa. “Ai duk taqamarka baka fi qarfin hukuma ba” Jin haka sai attajiri Huzulu ya qyalqyale da dariya. 73 BAYAN MUTUWA “Yaro man kare, tabbas har yanzu baka san wane attajiri Huzulu ba, don haka idan kana cin qasa ka kiyayi ta shuri, na kara da mahaifinka ma bai samu nasara ba bare kuma kai, ai tsiya dai ka gamu da ita kuma haka za ka ci gaba da rayuwa a cikin tsananin talauci har zuwa qarshen rayuwarka, ni kuma attajiri Huzulu hasken rana ne idan na fito tafin hannu baya tava kare shi” Jin haka yasa Amzad ya juya cikin fushi yana faxin. “Ni kuma zan tabbatar maka sarki goma zamani goma, duk yadda ka kai ga samun nasara akan wasu to ni zan samu nasara akan ka” Ya fice daga rumfar yabar attajiri Huzulu zaune cikin vacin rai. Amzad ya sauke numfashi a hankali sannan ya soma girgiza kansa, tabbas yasan shu’umanci attajiri Huzulu kuma yasan ba zai tava barin su ba dole ya nemi kawo musu hari, don haka a daren yau ya kamata ya yi tunanin mafita tun kafin gari ya waye. ** Al’amarin gimbiya Lashmin kuwa lokacin da ta baro turakar mahaifinta sarki sairan cikin tsananin baqin ciki sai ta koma can tata turakar ta zauna tana 74 BAYAN MUTUWA tunani da nazari. Da farko sai ta miqe tsaye zumbur da nufin ta fito ta kirawo dakarun dake tsaron lafiyarta su rakata izuwa can gidan sarki dake bayan gari domin taje ta nunawa Amzad wanan sarqa tasa dake hannunta ta tuna masa da duk abinda ya faru sa’adda suna yara. Domin su qulla sabuwar soyayya a yanzu amma data tuno da batun attajiri Huzulu sai ta fasa fitar ta kama kai kawo a cikin turakarta kawai jira take taga dawowar sarkin yaqi domin ta ji abinda ya faru. BAYAN MUTUWA 6 Ai kuwa tana cikin wannan haline shugabar kuyanginta ta shigo cikin turakarta a ximauce da sarki tace. “Ya shugabata ga sarkin yaqi can ya shigo falonki da gudu yana ta faman haki”. 75 BAYAN MUTUWA Koda jin haka sai Lashmin tayi murmushi tace ai nasan haka zata faru. “Bari naje naji daga bakinsa” Nan take Gimbiya Lashmin ta nufi babban falo na turakarta da sauri. Da zuwa sai ta iske sarkin yaqi a tsaye yana kai kawo cikin alamun tsananin damuwa. Koda sarkin yaqi yaga Gimbiya ta fito sai ya taho gareta da sauri ya zube qasa bisa gwiwoyinsa saboda biyayya sannan ya buxe baki da nufin ya yi mata bayanin abinda ya faru amma sai yaji ta tari numfashinsa tana mai cewa. ‘Kada ka vata miyan bakinka ya kai sarkin yaqi, na sani cewa attajiri Huzulu ya gudu daga kurkuku a halin yanzu, abin da nake so na sani kawai shi ne shin aljanune suka zo suka kuvutar das hi ko kuwa dakarune na mutane?” Cikin tsananin mamaki sarkin yaqi ya xago kai ya dubi Gimbiya Lashmin yace. “Ya shugabata yaya aka yi kika san duk wannan al’amarin?” Lashmin ta yi doguwar ajiyar zuciya tace. “Ai mutum baya fita yaqi sai ya yi tanadi gami da nazarin abokin gabansa, dole kasan maqiyinka ka kuma san qarfinsa da qarfin shirinsa 76 BAYAN MUTUWA kafin ka tunkare shi, ko ba haka bane?” Sarkin yaqi ya gyaxa kai yace. “Wannan haka yake ya shugabata” Gimbiya Lashmin ta zuba masa idanu tana kallon shugaban sarkin yaqi qasar cike da jimamin abinda ya faru kana kallonta kasan ranta ba qaramin vaci ya yi ba, musamman domin tun tsawon zamani babu wani mahaluki daya tava guduwa daga wannan kurkukun sai yau da attajiri Huzulu ya tsere. Suka yi shiru na wani lokaci kafin can ta furza da numfashi cikin vacin rai. 77 BAYAN MUTUWA G imbiya Lashmin taje ta zauna akan wata kujera sannan ta dubi sarkin yaqi ta yi masa umarnin shima ya zauna, ya miqe ya zauna akan kujerar ba tare da vata wani lokaci ba ko gardama ba sai ya miqe ya zauna akan kujerar dake fuskantar tata. Take sai wata kuyanga ta kawo musu shayi,kowannansu ya karva suka fara sha, sai da gimbiya Lashmin ta kurvi shayin sau uku sannan ta ajiye kofin akan teburin dake gabanta sannan ta dubi sarkin yaqi a cikin nutsuwa tace. “Tun ina yarinya qarama yar shekara bakwai na gane cewa attajiri Huzulu yafi qarfin kowa a qasarnan domin hatta mahaifina tsoronsa yake ji, tun a sannan na fara tunanin hanyoyin da zan bi na yaqe shi, bisa dole na riqa bincike cikin sirri akansa har sai dana gano iya qarfin arziqinsa. Iyakakar qarfin sihirinsa na tsafi da kuma dukkanin mutunen dake yi masa biyayya a cikin 78 BAYAN MUTUWA qasarnan da wajenta, hakan yasa na gano ba zan iya yaqarsa ba ko kawar da shi ba face na nuna masa kaidi irin na mu na mata, wato fanin siyasa da kuma gano babban lagonsa guda xaya. Ta hanyar siyasa na soma dakushe girmansa da kimarsa a idon mutane, bisa wannan daliline nasa aka kamashi aka kai shi kurkuku, ina sane zai iya guduwa daga kurkukun amma kuma bazai yi saurin xaukar mataki ba a kaina saboda ana kasheni yanzu kowa yasan shi ne,haka idan yace zai zo ya yi juyin mulki a qasar farat xaya mutane za su gane cewa bashi da gaskiya kuma har abada ba zai samu haxin kan sub a. Dole yanzu ya voya a wani wurin sannan ya fara tunanin hanyoyin da zai bi yaga bayana da mahaifina da kuma Amzad, kaga kenan a karon farko ya zama mai laifi ya gudu daga kurkuku, guduwarsa daga kurkukun zatasa jama’ar gari su fara zarginsa da rashin gaskiya a lokacin da ni kuma nake ci gaba da tafiyar da shari’arsa dake tsakaninsa da Amzad ina fitowa da dukkan tuggun daya shiryawa mahaifinsa qarara a baina jama’a kowa yana ji, hakan zai saka kowa yasan rashin imaninsa da rashin gaskiyarsa. 79 BAYAN MUTUWA Hakan zai sa jama’ar gari su tsane shi,tofa a daidai wannan lokaci ne zai harzuqa yace zai yi amfani da qarfin sa wajen ganin ya gama dani da kuma mahaifina ya yi juyin mulki. Ni kuma a sannan ne zan kawo qarshensa ta hanyar amfani da babban lagonsa dana gano, yakai sarkin yaqi kayi sa ni cewa bazan iya gaya maka komene ne wannan lagon na attajiri Huzulu har sai bayan n agama dashi sannan zaka ga lagon nasa da idanunka. Yanzu zaka iya tafiya izuwa gidanka domin kaje wajen iyalinka su ganka su sami nutsuwa, ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa babu abinda zai sake samun waninku har izuwa sa’adda zamu ga bayan wannan babban maqiyin na mu wanda ya kashe mahaifinka”. Koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai mamaki ya turnuke sarkin yaqi yace. “Yaya aka yi kika san cewa attajiri Huzulu ne ya kashe mahaifina alhalin ni kaina bansani ba sai a yau xinnan da ya faxa min da bakinsa acan kurkuku?” Sa’adda Lashmin taji wannan tambaya sai ta yi murmushi tace. 80 BAYAN MUTUWA “Shin ka mance na gaya maka cewa tun ina yarinya nake bincike akan duk abubuwan da attajiri Huzulu ke aikatawa? To kasani cewa tun a sannane ma na gano cewa hatta dakarun sumame da suka tava kawowa sarki hari sa’adda muka fita wani rangadi attajiri Huzulu ne ya aiko su, kuma a wannan ranar ne Nazmir mahaifin Amzad ya ceci rayuwar sarki shi kuma Amzad ya ceci rayuwata. Kaima da qyar ka tsira da rayuwarka bayan an harbeka da kibiya a gadon bayanka, mahaifin Amzad ya saka anyi wani sihiri ga Amzad wanda ya saka ya mance da duk abinda ya faru tsakanina dashi a wannan rana, kuskuren da mahaifina ya yikenan da nima bai sa anyi mini irin wannan sihirin ba domin daidai da rana xaya ban tava mantawa da Amzad ba a cikin zuciyata. Ina tuna kamannin fuskarsa bayan kowace daqiqa guda. Sarqar wuyansa kuwa wacce na fizgo a lokacin da aka rabamu har yau har gobe da ita nake kwana da ita nake tashi ban tava rabuwa da ita ba” Koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai hawaye ya zubo mata nan take ta zura hannunta izuwa cikin rigarta ta zaro wannan sarqa ta Amzad ta nunawa sarkin yaqi. 81 BAYAN MUTUWA Koda sarkin yaqi ya yi arba da sarqa sai ya kamu da tsananin mamakin gami da al’jabi kuma ya kamu da tsananin tausayin Gimbiya Lashmin. Nan take shima hawaye ya zubo masa yace “Ya shugabata tabbas qwaqwalwarki daban take data kowa a wannan zamani, basirarki da hangen nesanki sunfi gaban tunani. Tabbas a gaban idanuna kika cire wannan sarqa daga wuyan Amzad a lokacin kina da shekara bakwai a duniya shi kuma baifi shekara taraba. Ina kwance a qas jini yana zuba a gadon bayana na xago kain naga sa’adda Amzad ya savaki a kafaxarsa ya ruga dake izuwa cikin qofar birninmu, bazan tava mantawa ba a wannan lokaci ma said a kibiya ta sokeshi a hannu ya kwallara uban ihu amma duk da haka bai yarda ke qasa ba sai yaci gaba da gudu dake xauke har sai da ya tserar dake, shin yanzu saboda haka ne kema yanzu kike son ki qwato masa dukiyarsa daga hannun attajiri Huzulu?” koda jin wannan tambayar sai Gimbiya Lashmin ta share hawayenta sannan ta girgiza kanta tace. “A’a bawai don na yi masa sakaiya bane bisa ceton rayuwata da ya yi sai saboda tun a wannan ranar na kamu da tsananin son sa, ina mai tabbatar maka da cewar idan kaga ban auri Amzad ba to sai dai idan 82 BAYAN MUTUWA bana numfashi a doron qasa” Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaqi ya dugunzuma ainun hawaye ya sake zubo masa yace. ‘Babu yadda mahaifinki baiyi ba akan kada wannan ranar ta zo, bisa hakane ya nisantaki da Amzad ya toshe duk hanyoyin da za ku iya haxuwa muma ya gargaxemu akan kada mu kuskura mu yi zancen Amzad tare dake ko mu sanar dake inda yake, saboda bayanin da Bokansa ya yi masa na cewar indai kika yi soyayya da Amzad a qarshe babu ribar da za a samu face nadama da baqin ciki...” Caraf! Sai Gimbiya Lashmin tace. “Duk nasan da wannan al’amarin domin shi kansa sarki ya shaida mini hakan da bakinsa amma na zavi nadamar da baqin ciki kowane irine da dai a rabani da masoyina. Idan ma ba mu yi soyayya ba ta rayuwar aure a wannan rayuwa ta yanzu ba to lallai za mu yi ta a bayan Mutuwa saboda na yi imani cewa an halici ruhinmu da zukatan mu domin su so juna. Ina mai tabbatar maka da cewar idan ma mun mutu ba mu yi aure ba za a sake tashin mu a wani vangaren daban na duniya kuma sai mun haxu da juna mun yi aure kamar yadda Amzad ya mance da ni a yanzu, muna 83 BAYAN MUTUWA haxuwa ni ce zan shaida shi tunda ni ban tava mantawa da fuskarsa ba. Ruhina da ruhim Amzad ba za su tava rabuwa ba, lallai akwai RAYUWA BAYAN MUTUWA ni dashi” Ko da Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai ta fashe da kuka ta faxa akan qirjin sarkin yaqi ta rungume shi. Nan take tausayinta ya turnuqeshi shima ya qanqameta a jikinsa yana mai kuka gami da rarrashinta. Sai da suka shafe tsawon ‘yan daqiqu suna manned a juna sannan sarkin yaqi ya janyeta daga cikin jikinsa ya dubeta yace. “Ya shugabata yanzu yaushene za ki nunawa Amzad wannan sarqa tasa domin ya tuno da duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninki dashi ku kafa tubalin soyayyarku?” Koda jin wannan tambaya sai farin ciki ya lulluve Gimbiya Lashim ta qyalqyale da dariya daga can kuma sai ta nutsu tace. “Bazan nunawa Amzad wannan sarqaba sai bayan na kawar da babban maqiyinsa wato attajiri Huzulu, sai naga cewar duk dukiyar ta dawo hannunsa yana cikin daula da kwanciyar hankali a sannanne 84 BAYAN MUTUWA nima zan sami nutsuwa har na iya aza tubalin soyayyarmu na baiyana shi a fili kowa ya gani”. Koda jin wannan batun sai sarkin yaqi ya yi doguwar ajiyar zuciya sannan hawaye ya suvuce masa yace. ‘Na ji ajikina za ki iya samun nasara akan azzaluminnan attajiri Huzulu amma maganar Bokan mahaifinki tana yawo a cikin ruhina, zuciyata tana bugawa da qarfi tana tabbatar mini da cewar wannan tubalin soyayya naku ke da Amzad ba zai kai ga ginuwa ba, tabbas rushewa zai yi”. Koda jin haka sai Gimbiya Lashmin ta sake faxawa kan qirjin sarkin yaqi ta fashe da sabon matsanancin kuka sannan tace. “Ni ma na sha yin mugun mafarki akan haka, mummunan abinda nake gani a cikin mafarkin nawa bazan iya gaya maka shi ba, sai dai zan faxa maka wani daga cikinsa sauran kuma na barshi ya zama sirri a cikin zuciyata” Ta xan yi shiru na taqin lokaci tana kallon sarkin yaqi sannan ta ja numfashi tace masa. “Na tava yin wani mafarki bayan na kwanta barci na gani tare da ni da Amzad muna zaune a cikin wani lambu muna hira cikin tsananin soyayyar juna da kulawa, kwasam sai muka ga wani mahari ya kawo 85 BAYAN MUTUWA mana sumame ya na zuwa ya kawo wa Amzad sara da zumar cire masa kai amman bai samu nasarar yin haka ba sai ya kauce saran ya bi iska. Suka tsaya suka yi carko-carko kamar wasu zakaru suna kallon junansu, nima ganin haka ba qaramin xaga min hankali ya yi ba cikin sauri na miqe ina kallon wannan mahayin wanda ya rufe fuskarsa da qyale sai idanunsa kawai ake gani cikin tsawa nace masa. “Kai wane?” Ya xauke kai daga kaina yana kallon Amzad yace masa. “Ba ke na kawo wa hari ba, wannan baqin azzalumin masoyin na ki na kawo wa hari, kuma ba zan tava barinsa ba har sai na farauce rayuwarsa” Jin haka sai Amzad ya juyo a fusace yana kallonsa. “Kai wane?” Shima ya tambaye shi. “Masoyiyarka zata san ko ni wane bayan na halaka ka” Yana gama faxin haka sai ya sauko daga kan dokinsa ya yi xauki zuwa kan Amzad nan suka soma fafatawa ni kuma na tsana ina kallon yanda suke wannan faxan cikin tsananin fargaba da tsoron abinda ka iya faruwa akan masoyina. 86 BAYAN MUTUWA Ganin yadda wannan jarumin yake neman farauce rayuwar masoyina Amzad sai na suri wuqa nima na kai masa xauki, nan fa wani sabon gumurzu ya varke, shima mahayin ya zare wata takobi ya far mana da wani azababen faxan nasa mun xauki lokaci mai tsawo muna wannan azababen faxan kafin ya samu nasarar sarar Amzad a qirji nan take ya faxi qasa ganin haka ya xaga takobinsa sama da zumar suke shi, ina ganin haka na faxa kansa na bashi kariya nan take ya suka mini takobin ta huda qirjina ta volo ta shiga cikin jikin Amzad da wani murmushi na dubi Amzad nace mas. “Masoyina ba zan tava aminta ka riga ni mutuwa ba, zan so mu mutu a tare lokaci guda wannan shi ne cikar burin soyayya da qaunar juna” Shima ya yi murmushi. “Tabbas kin nuna min ke masoyiyace ta gaske wacce ba za a tava mancewa da ita ba, ina ma zan yi nisan kwana dana nuna wa duniya cewar mu masoyane waxanda ba a tava yin kamarsu ba, amman a yanzu hakan ma ina godiya ga abin bauta domin duk wanda ya samu tarihin wannan soyayyar tamu zai san lallai duk wajen da masoya suke mun kai”. 87 BAYAN MUTUWA Tana kawo nan ta yi shiru tana duban sarkin yaqi, wannan karon idanunta sun ciko da hawaye. Su duka suka yi shiru duk jikin sarkin yaqi ya gama yin sanyi a hankali Gimbiya Lashmin ta ce. “Idan har wannan mafarkin nawa ya faru da gaske to tabbas haka qaddararmu take ba za mu iya sauyawa ba, yakai sarkin yaqi ina neman alfarma guda a wajenka” Koda jin haka sai sarkin yaqi yai sauri ya janye jikinsa daga cikin na Gimbiya Lashmin ya dubet a cikin kaxuwa yace. ‘Ke kuwa wace irin alfarma kike nema a wajena?” Gimbiya Lashmin ta goge hawayenta sannan tace. ‘Idan har ni da masoyina Amzad mun mutu a lokaci guda to duk yadda za a yi kar ka bari a binne mu a kabari daban-daban, ka tabbatar da cewar an binnemu a cikin kabari guda kuma hannuna na daman a cikin hannunsa na dama wannan itace kaxai alfarmar da nake nema a wajenka. Ina son yanzu ka yi min alqawarin cika min wannan burin nawa” Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaqi yace. 88 BAYAN MUTUWA ‘Kamar yadda na rinqa tsaron lafiyar mahaifinki da taki tsawon shekaru na yi alqawarin zan cika miki wannan burin naki indai na kai wannan lokacin amma ina fatan cewa ke da masoyinki ba za ku mutu ba harsai kunyi aure kun bar zuri’a tagari”. Dajine fetal iya ganin mutum wanda ke xauke da tsaunika,bishiyoyi da duhuwoyi masu ban tsoro. Shi dai wannan daji tazararsa da birnin misira ya kai tafiyar kwana goma sha shida.kuma fatakema sai sun haxa babbar runduna sanna suke iya ketawa saboda mugun fashin da ake yi a wajen. Kai tsaye wani mahayin doki ya ratsa farkon wannnan daji ya nausa cikinsa ba tare da wani jin tsoro ba tamkar yana tafiya a cikin harabar gidansa, abin tambayar shi ne shin ya san dajin kuwa ko kuwa yana da wata alaka da yan fashi dake cikin dajin? Haka dai wannan mahayin yaci gaba da kutsawa cikin dajin ba tsayawa ba waige har sai daya shafe sa’a uku yana tafiya a cikinsa yana kallon tsiran dabbobin daji msu gifta masa da kuma tsintsaye da kai komo a cikin 89 BAYAN MUTUWA sararin samaniya. Kwatsam sai yaga waxansu mutane suna faxowa kasa daga saman bishiya waxanda adadinsu ya kai xari kuma suna sanye da wani koren tufafi wanda ya saje da ganyen bishiyar wajen babu ta yadda za a yi mutum ya gane cewar akwai mutum a wajen. Nan da nan waxannan mayaqa suka yiwa mahayin qawanya. Nan take rabinsu suka zare kebiyoyi suka xana akan baka suka ritsashi, wasu kuma suka zare takubba. Bisa dole mahayin ya ja linzami dokinsa ya tsaya cak. Shugaban dakarun ya dube shi da kyau yace masa. “Waye kai kuma ina zakaje?” Ba tare da nuna wata alamar firgita ko tsoro ba mahayin ya yi murmushi yace. “Ni manzo attajiri Huzulu ne shi ne ya bani umarni na zo nan darul uzut na same shi a yau xinnan” Ko da jin haka sai gaba xaya dakarun suka mayar da makamansu sannnan suka koma gefe da gefe 90 BAYAN MUTUWA suka tsaya. Shi kuma shugabansu sai ya mayarwa da mahayin martanin murmushi sannan yace. “Biyoni a baya na kaika wajensa”Take ya juya suka sake nausawa cikin daji shi kuma mahayin ya sakarwa dokinsa linzami ya bishi a baya. Sai da suka wuce rukuni-rukuni bakwai na ‘yan fashi waxanda adadinsu ya kai mutum dubu-dubu kuma dukkansu a cikin shigar yaqi suke ga tarin makamai na yaqi kala-kala har da irin wanda mahayin bai tava gani ba sannan suka qaraso darul uzut. Darul uzut wata fadace wacce aka ginata da zallar dutsen wuta, girmanta yafi na gidan sarautar sarki sairan haka ma kayan qawa dana alatun dake cikinta sun ninka na gidan sarautar sarki sairan sau goma. Suna shiga cikin fadar suka isketa cike da barori da kuyangi mata iri-iri baqaqe da farare kyawawan gaske tamkar zavosu aka yi daga cikin matan duniya suna ta hidima da kai kawo. Abin haushi shi ne 91 BAYAN MUTUWA mutum biyu ne rak a cikin fadar kuma suna zaune akan karagar mulki baabba guda xaya an tara musu kayan ciye-ciye dana shaye-shaye iri-iri na alfarma babu kalar da babu. Ba waxansu bane waxannan mutanen biyu face Attajiri Huzulu da kuma sarkin varayi nahiyar gaba xaya wanda ake kira da suna Ranzalar. Koda Attajiri huzulu ya hango wannan mahayin an tsaida shi a farkon qofar shigowa fadar, wanda ya rakoshi ya kama dokin ya sauka ya juya baya sai ya miqe yana murmushi ya buxe baki yace “Lalle marhabun da makanu lallai ina farin ciki da isowarka akan lokaci, maza ka qaraso nan gareni” Koda jin haka sai makanu ya saki fuska cikin sauri ya qarasa wajen su Huzulu, koda ya rage sauran taku huxu ya qarasa wajen sai ya zube qasa ya kwashi gaisuwa. Huzulu ya taso da sauri ya rungume shi, sanan ya janye jikinsa daga cikin nasa kafin ya kama hannunsa ya ja shi zuwa wata kujera dake kusa da shi suka zauna. 92 BAYAN MUTUWA Faruwar hake ke da wuya sai matarnan suka kawowa makanu abinci da abinsha sama da kala ashirin suka ajiye a teburin dake gabansa. Nan fa makanu ya shiga cin abinci da abin sha har sai daya qoshi sannan ya sha ruwan inbi ya yi gyatsa. Ko da Attajiri Huzulu yaga makanu ya samu nutsuwa sai ya bushe da dariya yace “Yauwa yanzu lokaci ya yi daya kamata ka bamu labarin duk abinda yake faruwa a cikin gidan sarautar birnin misira da wajenta” Makanu ya yi gyaran murya gami da gyara zama yace. “A halin yanzu Gimbiya lashmin tasa ranar yanke maka hukunci a bisa guduwa da ka yi daga gidan kurkuku amma har yanzu shi sarki Raihan baisan cewar ka gudu ba, ka sani idan wannan ranar ta yanke maka hukunci ta zo kuma aka zarta da hukunci a fada to alqadarinka ya karye saboda a wannan ranar Gimbiya lashmin zata tona maka asiri ta faxi dukan laifukan da ka aikata a garin na sirri, hakan zai matuqar zubar maka da mutunci da kuma darajarka” 93 BAYAN MUTUWA Koda makanu ya zo wajenan a maganarsa sai jikin Attajiri Huzulu ya soma tsuma, zuciyarsa ta rinqa tafarfasa kamar zata qone. Cikin tsananin fushi ya miqe tsaye zumbur ya dakawa makanu tsawa yace “Rufe bakinka ko yanzu na zare takobi na sare maka kai” Cikin hanzari makanu ya sunkuyar da kanshi qasa ya tsuke bakinsa. Da ganin abinda ya faru sai sarkin varayi ya miqe tsaye da sauri ya kama kafaxar Attajiri Huzulu ya riqe yace. “Haba Attajiri Huzulu uban ma su kuxi, duk wani attajiri da ma su mulki a qarqashinka suke, jarumai da matsafa duka yaranka ne, akan wane dalili wata ‘yar qaramar qwaruwa zata tayar maka da hankali alhalin kaine uba kuma uwa ga duk wani mahaluki a wannan nahiyar gaba xaya, ai tunda wannan labarin ya zo garemu ba za mu tava barin mutuncinka da qimarka su zube ba. Dole mu ruguza duka shirye-shiryen Gimbiya Lashmin kafin wannan ranar ta zo wacce take son kaika qasa”. 94 BAYAN MUTUWA Sarkin varayi ya juya ya dubi makanu a lokacin da zuciyar Attajiri Huzulu ta xanyi sanyi yace “Ya kai makanu ina son ka sanar da ni yau sauran kwana nawa gimbiya Lashmin ya rage ta yankewa mai girma Attajiri Huzulu hukuncin qarshe a fadarta?” Makanu ya xago ya dubi sarkin varayi yace “Yau sauran kwana ashirin da xaya” Jin haka sarkin varayi ya yi murmushi sannan ya juya ya koma kan karagar ya zauna kusa da Attajiri Huzulu ya dubeshi yana mai dafa hannunsa yace. “Ai tayi kuskure data xauki dogon lokaci, ina mai tabbatar maka, nan da cikar sati xaya rak za mu kawo qarshen mulkin wannan yarinyar sannan kuma zamu kama mahaifinta da hannunmu mu kawoshi cikin kurkukun gidanmu mu voyeshi kai kuma ka xare karagarsa ka zauna”. Lokacin da sarkin varayi ya zo nan a maganarsa sai Attajiri Huzulu ya xan yi murmushi mai kama da yaqe yace “Faxar wannan qudurin a baki yana da sauqi amma ka sani aikata shi a aikace ba abune mai 95 BAYAN MUTUWA sauqi ba, ina mai tabbatar maka cewar wannan yarinya Lashin ta daxe tana tanayi akaina ba tun yanzu ba tun tana yarinya qarama, ban san da haka ba sai da bokayena suka yi bincike akanta suka gano haka, duk faxin nahiyar nan babu wanda yasan sirrrina sama da ita kuma ita kaxai tasan lagona wanda idan ta riqeshi to ta gama da ni, amma riqe wannan lagon nawa daidai yake data faxa cikin wutar data shekara tana ruruwa? Nima kuma yanzu na gano lagonta da shi kuma zan yi amfani na hanata ci gaba da aiwatar da mugun nufi akaina?” Cikin hanzari sarki varayi yace. “Mene ne lagonta? Kuma kaima mene naka lagon?” Sa’ar da attajiri Huzulu ya ji wannan tambayar sai ya qyalqyale da dariya sannan lokaci guda ya turvune fuska yace “Ya kai sarkin varayi mai fadar Darul uzur kayi sani cewar babban lagon gimbiya lashmin shi ne wannan yaron Amzad wanda take son ta karve dukiyarsa daga hannuna. Tun suna yara ita da shi ta kamu da tsananin sonsa sa’adda ya ceci rayuwarta amma sai sarki ya shiga tsakaninsu ya 96 BAYAN MUTUWA yiwa Amzad sihirin da ya manta da ita gaba xaya, kuskuren da sarki ya yi shi ne bai yiwa gimbiya lashmin irin asirin da ya yiwa Amzad ba don haka ita bata manta da shi ba don haka kullum a cikin begensa take dare da rana,matakin daya kamata na xauka shi ne na saka a sato Amzad yanzu a kawo shi nan, sannan na saka a sato wata sarqa ta musamman dake wajen gimbiya lashmin, ita dai wannan sarqa ta Amzad ce kuma ita kaxai zata nuna masa ya tuna duka abinda ya faru a baya a tsakaninsu da ita. Ni na san sato Amzad daga cikin birnin misira abune mai sauqi a wajen mutanenka, ya kai sarkin varayi ya za ai a sato sarqar dake wajen gimbiya lashmin alhalin dare da rana tana wuyanta a xaure, kuma ko wanka zata shiga kewaye bata cireta? Ko sau xaya bata tava cireta ba tun sanda ta cire sarqa a wuyan Amzad sa’ar da suna yara a lokacin da aka rabasu. Idan na samu Amzad da sarqa na samu cikaken lagonta kuma duka umarnin dana bata dole ta bi saboda zata iya salwantar da rayuwarta da mulkinta saboda Amzad. 97 BAYAN MUTUWA Naji ka tambayi wai mene nawa lagon? Zan iya sanar da kai nawa lagon amman sai idan kaima ka sanar da ni naka lagon” Koda jin haka sai sarkin varayi ya bushe da dariya sannan ya risina gaban Attajiri Huzulu yace “Tuba nake ya shugabana haqiqa na yi kuskure kuma ba zan qara ba, yanzu ina neman izininka a yau xinan zan tura zaqaquran yarana guda biyu izuwa cikin birnin misira. Mace xaya namiji xaya su ne Inzal da Karimat. Imzal zai sato Amzad ita kuma Karimat zata sato wannan sarqa dake wuyan Gimbiya Lashmin” Lokacin da sarkin varayi ya zo nan a zancensa sai attajiri huzulu ya yi shiru yana tunani har izuwa tsawon ‘yan daqiqu sannan ya miqe tsaye ya yi xan taku uku ya juyo ya fuskanci sarkin varayi yace. “Ko shakka banayi Imzal zai iya sato Amzad amma karimat ba zata iya sato sarqa gimbiya lashmin ba, idan kuma ta samu nasara satota zan kuwa bata kyautar dukiyar da babu ita babu talauci har izuwa qarshen rayuwarta. Maza a kirawo Inzal sa Karimat su 98 BAYAN MUTUWA yi shiri su tafi izuwa birnin misira” Kafin Attajiri huzulu ya gama rufe bakinsa tuni an kirawo Inzal sa Karimat sun bayyana a gaban sarki varayi. Shi dai Inzal wani kyakkyawan saurayi ne mai kwarjinin gaske kuma ya cava ado kai da ganinsa kasan cewa xan sarkine ko wani xan babban attajiri kuma fuskarsa tana xauke na xauke da alamun mutum mai tausayi da jin qai sai dai kash akasin hakanne a cikin zuciyarsa domin mutune mai tsananin mugunta da rashin imani. Ita kuma karimat mace ce doguwa mai qirar kalangu kuma baqar fata. Ba za a kirata kyakkyawa ba kuma ba za a kirata mummuna ba. Tana da yalwar gashin kai domin ya zubo har qasan kwankwasonta, kaurin jikinta madaidaicine ba yabo ba falasa, duk da kasancewar karima a qarqashin sarkin varayi take ba zaman kanta take ba, amma jikinta luwai-luwai yake kamar na jarirai, hakane zai tabbatar maka tana samun jin daxi da hutu sosai. Karimat tana xaya daga cikin manya-manya hadiman sarkin varayi wanda ya aminta 99 BAYAN MUTUWA da su, kuma yana qaunarta yana son ma ya mallaketa a matsayin matarsa ta uku, amma saboda yana da wani buri guda xaya wanda ita kaxai zata iya cire masa shi don haka ya dakata da batun aurenta. Saboda gaba xaya hadiman sarkin varayi sun san yana sonta don haka ko kusantarta basa yi, shima sarkin varayin baya zuwa inda take idan ta zo fadarsa to zata je aiwatar da wani aiki na musamman. Lokacin da karimat da inzal suka tsaya a gaban su sarkin varayi, attajiri Huzulu ya yi arba da ita sai ya ji ya kamu da tsananin sha’awarta don haka bai san lokacin daya qura mata idanu ko qiftawa baya yi ba. Sai da sarkin varayi ya tava hannunsa ya yi firgigi kamar ya tashi daga bacci sannan ya basar sarkin varayi ya yi murmushin qarfin hali. “Amman wannan hadimar taka mai kyauce” Sarkin varayi ya murmushi yace “Ai wannan ne aiki na qarshe da zata yi ta zama matata”Koda jin haka sai jikin Attajiri Huzulu ya yi sanyi ya kauda kai ga barin 100 BAYAN MUTUWA kallonta, shima sarki varayi yace “Ya ka ganta? Zata iya wannan aikin ko ba zata iya ba?”. Attajiri Huzulu ya yi murmushi yace “Ai da ganin kura zata ci mutum” sarkin varayi yace “Ta qware wajen iya qissa da shirya makirci ga iya magana na turata izuwa qasashe saba’in da biyu ta jagoranci gagarumar sata a masarautun amma ko sau xaya ba a tava samun rashin nasara ba, karimat mace ce mai tsananin sa’a aduk abinda ta saka a gaba, wannan ce sata ta saba’in da uku na kuma yi mata alqawarin shi ne aikinta na qarshe wanda zan ‘yanta ta na aureta”Koda sarkin varayi ya zo qarshen maganarsa sai murmushi ya suvuce wa karimat ta kamu da tsananin farin ciki amma a farin cikinta babu batun aure da sarkin varayi domin shi ne mutum na qarshe data tsana a duniya, ba komai ya saka ta tsaneshi ba face tun tana da shekara shida a duniya ya xaukota daga qasarsu bayan ya kashe iyayenta ya kwshe dukiyarsu, ya tafi da ita ya baiwa matarsa ita ta riqeta ta riqa bata horo na koyon sata, yaqi da jarumta a haka 101 BAYAN MUTUWA ta girma ta cika shekara ashirin da xaya ta zama gagarumar varauniya mashahuriya. Abinda sarkin varayi bai sani ba ko yaushe da dare sai karimat ta yi mafarkin abinda ya faru ga iyayenta tun tana shekara shida, amafarki tana ganin lokacin da sarkin varayi ya zare takobi ya sare mahaifiyarta da mahaifinta ita kuma tana zaune tana kuka ya sureta ya fice da ita daga cikin gidan tana ihu tana kiran sunan iyayenta. A kan idanunta sarki varayi ya saka aka cinawa gidansu wuta ya qone qurmus. A qarqashin zuciyar karimat ta ci burin cewar komai daxewa sai ta xauki fansar ran iyayenta a kan sarkin varayi. Sarkin varayi ya dubi inzal da karimat yace “Za ku tafi izuwa birnin misira yanzu kai zaka sato Amzad wanda ake shari’arsa da maigirma Huzulu ita kuma karimat zaki sato mana sarqa wuyan Gimbiya lashmin, bana son ku shafe sama da kwanaki bakwai a cikin birni ba tare da kun kammala aikinku ba, maza kuje sarkin gida ya baku dawakai da guzuri yanzu ku tafi” 102 BAYAN MUTUWA Da jin haka sai Inzal da Karimat suka rusuna sannan suka juya tare ficewa daga cikin fadar. Fitarsu ke da wuya sai attajiri Huzulu da sarkin varayi suka dubi juna suka bushe da dariya farin ciki saboda ji suke kamar buqatarsu ta gama biya. Wannan shi ne abinda ya faru a fadar sarkin varayi, fadar da ake yiwa laqabi da darul uzur inda attajiri huzulu ya vuya bayan ya gudu daga babbar kurkuku na birnin misira. A can birnin misira kuma lokacin da sarki yaqi ya baro gidan sarauta bayan ya gana da gimbiya lashmin sai zuciyarsa ta cika maqil da wasi-wasi gami da 103 BAYAN MUTUWA firgici. Ba komai ne yasa ya tsinci kansa a cikin wasuwasu gami da fargaba. Ba komai ne yasa ya tsinci kansa ba face tunanin hanyar fa ya kamata yabi ya samu nasarar taimakon lashmin domin ta cika burinta. A wannan lokaci yana tafiyane yana ta sauri domin ya isa gidansa ya zauna yayi tunani mai zurfi domin samun mafita kwatsam sai yaga mutum tsaye akansa nan take zuciyar sarki yaqi ta buga da qarfi tsaya cak a inda yake suka fara kallon-kallo da mutumin dake tsaye a gabansa. Ba wani bane wannan mutum face sarki Raihan wato mahaifin gimbiya lashmin cikin alamun tsananin mamaki gami da tsoro sarki yaqi ya qaraso kusa da sarki Raihan ya zube qasa ya kwashi gaisuwa sannan ya miqe tsaye ya dubeshi kansa na sunkuye cikin biyayya yace “Ya shugabana mene ne ya fito da kai daga gidan sarauta ka shigo cikin gari a wannan lokacin? Sa’ar da sarki Raihan ya ji wannan tambayar sai ya yi ajiyar zuciya sai yace “Na xauki karagata na baiwa ‘yaarta a ranar data hau ta yi abinda na kasa yi a 104 BAYAN MUTUWA shekara ashirin da biyar tunda ta sami nasarar kawar da babban maqiyina daga cikin birnina amma kuma ta tsokano mana tsoliyar dodone, na samu labarin cewar atttajiri Husulu ya gudu daga kurkuku, tunda na samu wannan labarin na kasa ci da sha kuma na kasa bacci, saboda nasan cewar qarshen mulkinmu ya zo kuma adalci ga talakawa ya qare ni da duka zuri’arta da dukkan masu biyayya a gareni ta su ta qare domin attajiri Huzulu ba zai barmu muci gaba da rayuwa ba, ko dai a murqushe qasarmu gaba xaya ko muyu ragas mu da attajiri Huzulu da jama’arsa Yanzu dai kaine kaxai abin dogarot a shin zaka iya taimakon ‘yarta akan aiwatar da shirinta na daqile attajiri Huzulu? Abune na siyar da rai domin babu tabbacin nasara a cikinsa, abune mai matuqar wahala idan kana ganin ba zaka iya taimakonta ba to ina da zavi na biyu, shi ne dani da gimbiya da duk masoyana mu bi dare mu sulale mu gudu mu yi qaura daga garin”. 105 BAYAN MUTUWA Lokacin da sarki ya zo nan sai hankalin sarkin yaqi ya dugunzuma ainun fiye da kowanne lokaci ya rasa abinda ke masa daxi a duniya ya yi shiru suna kallon juna har izuwa tsawon daqiqa biyar daga bisani kuma sai sarki yaqi ya kalli sarki cikin nutsuwa yace. “Ya shugabana nan ba wajen da za mu yi wannan maganar bane, saboda babu sirri kuma ka yi ganganci da kake fitowa daga gida a irin wannan lokacin saboda maqiya za su iya sakawa a saceka” Sarki raihan ya yi murmushi yace “Babu wani maqiyi daya fini sanin birni misira da kuma mutanen da suke cikinsa, nasan hanyoyin da zanbi ba tare dana haxu da wani tsautsayi ba, duk wani baqo da zai shigo garinan ina ganinsa kuma ko da zai voye fuskarsa sai da na ganka yanzu sannan na buxe fuskarta koma na gama nazarin wannan wurin da muke tsaye. Yanzu mu wuce izuwa gidankaa domin mu zauna mu tattauna tabbas akwai shawarwari da zan baka za su yi matuqar taimaka maka”. 106 BAYAN MUTUWA Sarki Raihan yana gama faxar haka sai ya xauki mayafin dake kafaxarsa ya xora akan fuskarsa ya rufe fuskarsa da shi yadda idanunsa kaxai ake gani sannan ya kama hannun sarki yaqi ya jashi suka nausa cikin gari izuwa hanyar da zata kaisu gidan sarki yaqi. Al’amarin Gimbiya lashmin kuwa bayan sun rabu da sarki yaqi ta shiga turakarta sai ta shiga sabon tunani mai zurfi inda ta ji cewar babu abinda take so a cikin faxin duniya sama da mallakar Amzad a matsayin abokin rayuwarta. Nan take ta tambayi kanta a cikin zuciya tace ta yaya zan kwato dukanin dukiyar Amzad daga hannun Attajiri Huzulu a cikin kwanaki biyu kacal? Ta yaya zan gani inda attajiri Huzulu yaje ya voye na saka a kamoshi a gurfana da shi a gabana a tsakanin yau zuwa gobe? Yin haka abune mai wuya amma kuma ai mulki ba wasabane. Me mulki yana yin komai indai abun mai yiwuwane a doron qasa. Matakin da zan bi ya zama dole a gobe a zo da Amzad fada na ganshi ya ganni kuma na tuno masa da koni wacce a gareshi, mataki na biyu a daren yau dolene na 107 BAYAN MUTUWA gana da babban bokan attajiri Huzulu wato boka zallazi domin ziyara zan kai masa ta bazata tunda shima nasan lagonsa lallai zai taimakamin akan attajiri Huzulu koda gama aiyana wannan al’amarin sai gimbiya lashmin ta qwalawa ilela kira ta shigo turakar da gudu ta zube qasa a gabanta, lashmin ta dubeta tace. “Mike tsaye muyi magana ki kalleni ido cikin ido” Da jin haka sai Illela ta miqe ta dubeta cikin nutsuwa Gimbiya Lashmin tace. “Ina son a cikin darenan na kai ziyara can bayan gari wajen boka zillazi a sirrance ba tare da wani ya ganmu ba, kece kaxai zaki rakani, bana son a ga fitarmu daga cikin gidanan ko dawowarmu sannan kuma ina son mu tafi da akwatinan ta lu’u lu’un sarki ki riqe mu tafi da ita” Koda jin wannan maganar sai Ilela ta firgita ainun jikinta ya kama rawa a lokacin da idanunta suka zaro tamkar tayi arba da mutuwa tace. “Haba ya shugabata ki sani ya shugabata duka dukiyar sarki babu abu mai darajar wannan akwatin ta 108 BAYAN MUTUWA lu’u lu’u a duk nahiyar nan gaba xaya, shin saceta kike so muyi?” Gimbiya Lashmin ta girgiza kai alamar cewar ba haka ba tace. “Fansa zan bayar a matsayin raina dana Abbana da kuma amzadm ki sani ba domin komai boka zulazi yake taimakon attajiri Huzulu sai saboda ya yi masa alqawarin cewa da zarar ya karvi karagar gidannan zai bashi akwatin lu’u lu’un sarki. Ita kuma wannan akwatin babu mai tavashi da hannunsa ba tare da hannun ya guntule ba har sai ya zama sarki garinan duk wanda ya mallaki wannan akwatin zai zama duka nahiyar babu mai kuxinsa, kuma dole sai mai mikin garin ya xauketa da hannunsa ya damqa maka sannan zaka ci gajiyarta. An turo varayi sama da dubu ashirin izuwa gidan sarautar domin su sace wannan akwati amma dukansu da guntulallen hannu suke komawa, ki sani idan na xauketa na saka a cikin jakarnan ta akwati zan iya baki ki riqe, duk abinda nake buqata nasan zaki iya shi yasa na umarceki da ki ruga kije ki aiwatar da shirye-shirye na wannan fitar da za mu yi a 109 BAYAN MUTUWA cikin wannan dare” Ba tare da wata gardama ba Ilela ta risina tace. “Angama ya shugabata” Cikin hanzari Ilela ta juya ta fice, ita kuma Gimbiya lashmin sai ta juya ta shiga cikin turakarta ta soma shirin fita. Al’amarin Inzal da karimat da xan saqo makanu suka baro fadar Darul uzu amma da ya rage sauran baifi tafiyar rabin sa’aba a iso birni misira sai suka tsaya suka yada zango shi kuma makanu ya wuce gaba izuwa birni misira. Bayan tafiyar makanu ne Inzal da Karimat suka fara hira inda ya dubeta yace. “To ke yanzu ta yaya zaki sami damar sato sarqa dake wuyanta?” Koda jin wannan tambayar sai karimat ta sauke ajiyar zuciya cikin alamun karayar zuciya sannan ta dubi Inzal tace “Bani da wta dabara a cikin zuciyata amma kuma ka sani cewa ni ban tava karaya bisa kowane irin aiki da zanyi ba komai 110 BAYAN MUTUWA wahalarsa da haxarinsa, kai kuma fa? Shin kana ganin sato Amzad abune mai sauqi, alhalin dole Gimbiya lashmin ta saka cikaken tsaro tunda tasan dole attajiri Huzulu ya saka a farauceshi” Inzal ya numfasa yace. “Maganarki gaskiyace amma ki sani indai gari yayi duhu a lokacin da na shiga cikin birni misira to ko da gaba xaya dakarun qasar suka kewaye xakin to sai na shiga” Koda gama faxin haka sai suka ga wata gada ta giftasu cikin hanzari Inzal ya miqe tsaye zumbur yace. “Ke jirani anan ina zuwa” A guje ya bi wannan gadar izuwa cikin daji karimat ta bishi da kallo har sai daya qule ya vace mata da gani faruwar hakan ke da wuya sai taji motsin tafiya a can bayanta nesa kaxan da sauri ta juya ta ruga ta vuya a can bayan bishiya kawai sai taga wasu mutane sun nufi can hanyar da ta nufi wani qaton kogo, nan take zuciyarta ta cika da tambayoyi su wane waxannan mutanen kuma me su ka zo yi alhalin gari ya soma duhu kuma akan hanyar da babu mai binta domin hanya ce data nufi gidan 111 BAYAN MUTUWA boka zullazi tana gama faxin haka sai ta bi bayansu da sauri don kada su vace mata da gani amma da taga ta soma hangosu sai ta riqa binsu a hankali don kar suji motsinta su waigo su ganta. Haka suka ci gaba har suka iso bakin kogon tana ganin haka sai ta kuma voyewa a bayan wani dutse, ba wasu bane waxannan matan face Gimbiya lashmin da kuyangarta koda suka qarasa sai tace “Ya shugaban bokaye buxe mun qofa” Kafin Gimbiya Lashmin ta gama rufe bakinta sai ga tsaunin ya rabe gida biyu wata qofa ta bayyana, su Gimbiya Lashmin suka shiga bisa ga mamakin Karimat sai taga qofar bata rufe ba don haka sai ta nufi wajen da azama ta shige, ai kuwa tana shiga sai qofar ta koma ta rufe karimat ta juya a xan tsorace ta kalli qofar amma sai ta dake ta juya ta kunna kai cikin gidan. Wani falo ne qawatacce wanda komai na cikinsa anyisa da zallar zunare, wata karagace guda xaya jal wacce aka yita da shuxin zinare aka yita, zaune akan karagar wani dogon mutum ne mai matuqar kwarjini 112 BAYAN MUTUWA da cikar haiba, gashin kansa sajensa gami da gashin baki duk farare fat. Kallo xaya zaka yi masa kasan cewar ya haura shekara tamanin a duniya koda ya gango Gimbiya lashmin da Ilaila sun nufo shi hannun Ilaila xauke da akwatin lu’u lu’u sai fuskarshi ta faxaxa zuwa ga murmushi kafin su qaraso tuni ya miqe ya taresu fuskarsa cike da murmushi. Cikin girmamawa boka zillazi yace “Barka da zuwa ya sarauniyar duniya, ki sani cewar ya Gimbiya yau shekara sittin kenan ina zaune ina jiran wannan ranar da za ki zo ki damqa mun wannan akwatin ta zinare da hannunki, tabbas kin gama cika mun wannnan burin nawa na duniya ke ma ki sani cewar zuwa gobe da yamma naki burin zai cika” Da jin haka sai Gimbiya lashmin ta yi murmushi ta amshi akwatin lu’u lu’u daga hannun ilaila ta miqa masa koda ya amsa sai suka ji an zabga wata tsawa mai qarfi wacce ta tsorata Gimbiya lashmin amma sai suka ga boka zallazi ya qyalqyale da dariya ya juya ya nufi inda aka ajiye wata bishiyar qarfe ta zinare, yana zuwa ya xora 113 BAYAN MUTUWA akwatin akan bishiyar faruwar haka sai akwatin ta narke ta haxe da bishiyar kamar ba’a tava xorata a wajenba kuma sai aka sake zabga tsawa a karo na biyu wacce tasa gidan gaba xaya ya girgiza Gimbiya lashmin da ilaila sai da suka faxi suka yi saurin miqewa. A lokacin boka zallazi ya waigo ya dubi su Gimbiya ya yi murmushi sannan ya taho zuwa ya garesu yace mata “Yake gimbiya kiyi sani cewar yau ko raina kike so zan baki, domin kin cika mun burina daya gagari iyayena da kakanina, nasan cewar baki da buri daya wuce ki amso dukiyar Amzad daga hannun attajiri Huzulu kuma ki kawo qarshen zalluncinsa, kuma kina son mallakar amzad a matsayin abokin zamanki na dindin” Koda Gimbiya taji haka sai ta yi murmushi tace. “Duk abinda ka faxa gaskiya ka faxa”. “To nima dole na sallama komai nawa bisa sa’a kuma wanda zai miki jagora wajen cika wannan burin 114 BAYAN MUTUWA naki mutum xaya yana nan cikin kogon tare da mu”Jin haka sai su Gimbiya lashmin suka soma waige-waige amma ba su ga kowa ba sai tace masa. “Kace mu huxu ne amma ni banga kowa ba, sai mu uku” Jin haka sai ya qyalqyale da dariya kafin kuma ya murtuke fuska yace. “Ya karimat mai sa’a ya kamata ki fito haka ai ina sane na bar qofar a buxe kika shigo” Koda jin haka sai tabar bayan ginin data vuya ta fito su Gimbiya da Ilaila suka qare mata kallo suka ga basu tava ganin mace kamarta ba. Boka zallazi ya tako ya qaraso zuwa gareta ya zo ya tsaya yadda suna jin numfashin juna yace mata “Yau shekara goma sha shida kenan ina jiran rana da zaki xauki fansa iyayenki da sarki varayi ya kashe miki to yau ga dama ta samu mudin zaki yadda ki haxa kai da sarauniyata, shin za ki yi amfani da wannan damar ne ko za ki zavi xan abinda attajiri Huzulu yace zai baki? Ki sani idan kika taimaki 115 BAYAN MUTUWA sarauniya zata baki dukiyar ba zaki kasheta ba har qarshen rayuwari kuma ba zaki iya kasheta kuma zaki zama maxaukakiya wato za ki zauna a cikin ma su mulki riba biyu kenan kin jefi tsuntsu biyu da dutse xaya”Koda boka zullazi ya zo nan a maganarsa sai karimat ta yi murmushi tace. “Ya maxaukakin boka ai ka fini sanin kaina shin yanzu ta yaya zan bada gudumawa a cikin wannan maxaukakin aikin?” Koda ya ji haka sai ya yi murmushi yace. “Zan baku wani taimako yanzu nan yadda ku uku nan za ku tafi can fadar Darul uzur ku yaqi duka dakarun ku kamo sarki varayi da attajiri Huzulu ku kawo su cikin birnin misira a wulaqance ku yi masa hukunci da kuka ga dama” Ya dubi karimat yace “Yanzu zan baki amsar tambayarki” Yana rufe baki ya nufi wata qofa ya buxe ya shiga jim kaxan sai ya dawo xauke da kayan yaqi guda uku da takobi, mashi da kuma wata hular qarfe zalla ya miqawa lashmin takobin ita kuma karimat sai ya abata mashi sannan ya 116 BAYAN MUTUWA miqawa ilela hular qarfe duk su uku suna riqe da kayan yaqin sai suka ji wani irin qarfi na musamman ya shiga jikinsu cikin matuqar mamaki lashmin ta dubi boka zallazi tace. “Ya kai babban boka wannan wanne irin kayan yaqi ne haka na ma su qarfi sihiri. Na rantse da gemun mahaifina yanzu ina jin zan iya shafe kwana da yini ina yaqi” Ya bushe da dariya yace. “Ai kwana bakwai za ki yi batare da kin gaji ba, ki sani babu wani kaifi ko tsini da zai tava tasiri a tare dake, wannan takobin dana baiwa gimbiya sunanta saiful lujara, mashin dana baiwa karimat sunan shi galilil haras, ita kuma hular dana baiwa Ilaila sunanta Lamsara, ba a tava yin kayan yaqi da suka kai wannan daraja da kuma sihiri ba, kuma sunfi shekara dubu xaya da xari uku a hannun kakanin kakanina, yanzu na baku wannan kayan domin ku kawo qarshen zallunci attajiri Huzulu domin idan aka sake ya mallaki birnin misira to zai mallaki tsafina da kuma kayan yaqinan, ku sani kuma idan kun gama yaqi kun 117 BAYAN MUTUWA samu nasara waxannan kayan yaqi za su vace su koma can qasan teku su ci gaba da zamansu kuma har abada ba za a kuma samun wani mahaluki da zai xauko su ba har duniya ta gushe, maza ku tafi fadar darul uzur domin aiwatar da wannan babban aikin” Koda jin haka sai Gimbiya lashmin da karimat da Ilala suka juya suka nufi hanyar fita. Lashmin ta zare takobin saiful daga cikin kubeta, ilela ta saka hular lamsara, ita kuma karimat ta wulwula mashin galilin haras, bisa ga mamaki sai sukaga sun fice fit ta cikin garu sun nausa da gudu cikin daji wani irin gudu ban al’ajabi suke yi. Saboda qarfin gudun ya kai na tauraruwa mai wutsiya koma duk abinda suka riska a gabansu tsalleke shi suke su wuce komai faxinsa da tsawonsa maimakon su shafe rabin sa’a kafin su isa fadar Darul uzut sai gashi cikin daqiqa biyar kacal sun isa ai kuwa sai dakarun sarki varayi suka ta so musu aka ruguntsume da wani azababben yaqi, kamar mace ta saka tsintsiya ta share qofar xakinta haka Gimbiya 118 BAYAN MUTUWA lashmin da Ilela da karimat suka karkashe dakaru dubu uku da xoriya. Sai gasu a cikin fadar tsulum sun bayyana a gaban su attjiri Huzulu da sarkin varayi, cikin firgici sarkin varayi da attajiri Huzulu suka zare makamai suka yi xauki kansu lashmin da sara da suka, ko da takubbansu suka haxu da saiful lujara da galili haras sai suka narke suka zama ruwa abinda ya yi matuqar ranazana su ke nan, nan suka zube qasa kafin su taso tuni Ilela ya bayyana a gabansu ta gwara musu hular lamshara nan take suka baje a wajen sumammu. Lokacin da sarkin varayi da attajiri Huzulu suka farfaxo sai suka tsinci kansu a zube a qasa a tsakiyar fadar birnin misira, attajiri Huzulu na duba gabansa sai ya yi arba da Gimbiya Lashmin da Amzad a zaune akan karaga xaya yana kallonsa yana masa murmushin mugunta, nan take Amzad ya miqa wa gimbiya hannu ya ta saka masa sarqa a cikin hannunsa ya soma juyata akan fuskar attajiri Huzulu yace. 119 BAYAN MUTUWA “Wannan sarqa ta amso mun haqqina dake wajenka kuma ta samar mun matsayi da xaukaka, duka dukiyar daka tara yanzu ta zama tawa kai kuma tsireka za ai bisa laifin fashi da makami tare da abokinka sarkin varayi” Yana rufe baki sai ga sarki sairan ya shigo fuskarsa cike da murmushi yace. “Tabbas yanzu za a tsireka” Masha Allah. QARSHE. 120 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels