[05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ya bugo mini waya ya ji ya jikina ma bai yi ba, watakila ma ya mance da ni. Duk yadda ya kyamaci Amrah ta dawo ita kadai. Na lura tunda ya fada soyayya da yarinyar nan haka yake bata umarnin ta dawo da kanta. A kullum sai na tuna Abida sama da sau ashirin. Don kuwa kullum sai na ci karo da abin da yake na gaskiya a cikin hasashen da ta dinga yi akan Sahal. Zamanmu na nisa matsaloli na sake girmama. Ya mike yana fadin "bari na yi wanka gabadaya na gaji." Bai jira abin da zance ba ya shige dakinsa da saurinsa domin kaucewa kallon da nake masa mai kaifi. Tsawon lokaci ina zaune ina ta sake saken zuciya. Duk da ban taba yi masa magana akan kudaden da yake fitarwa ba, wannan kam ba zan iya yin shiru ba. Kwanaki kadan da suka shude ya cire sama da 150 kuma shima store ne suka cire, tabbacin shopping suka je ya yi mata, yau ma ya cire kusan hakan duk a cikin sati guda bayan wanda ya fitar da ya je siyo mana kayan amfanin gida, yauma ya sake cirewa ban da kananun da yake cira yana yin alheri da su ga ahalinsa da duk wanda ya so. A sanyaye na nufi dakina na watsa ruwa dan na samu na sake wartsakewa. Na shafa lotion (coconut na oriflame). Wanda na farare ne irina Aisha lame ta zaba mini, sosai nake jin dadin amfani da shi mussaman yadda ya sanya na yi tas fatar ta yi mulmul. Na gasgata products din da lame take sayarwa na kuma gamsu an mata baiwar sanin dukkan rabe raben skins, tare da sanin naui'in man da zai dace da kowa. Don kallon ka kawai zata yi ta gane irin man da zai dace da fatarka. Tuntube ta a wannan layin dan samun kalar naki man da zai gyara miki fatarki ko da ta fara yamushewa saboda tsufa ko rashin samun kulawar da ta dace. *Lame Nig....07036662633.* Rol on kawai na saka na zura rigar barcina cotton wacce cikin siyayyar da na yi ne a wajen Umm Asalah +201121544627 +2349162662750 kamshin turarena ya kamata. Na sanya dogon hijab din gunis na fita. Na leka dakin Amrah na tarar da ita tana kallo a wayarta. Na mika mata hannu, ba ja in ja ta miko mini domin doka ce karfe goma zata kawo mini wayar ba dan makarantar da take zuwa sun màtsa kowanne dalibi sai an siya masa waya ba da ba zan amince ta rike waya ba sai ta kammala sakandire domin hadarin da yake cikin wayar a wajen yara masu shekaru irin nata yafi alkhairinsa yawa. Kana tarbiya kana ta boye musu abubuwan da basu kai su gane ba ashe su kam kallon fanko suke mana domin da wayar hannunsu babu iyashegen da basa ga ni ko ji. Na tsani na ga ta bude tiktok din nan tana ganin yaran mata suna sakin maganganun rashin da'a da kunya hadi da shigar banza tamkar dai basa tuna watarana zasu koma ga ubangiji ga kuma doguwar kwanciyar kabari da take gabansu. Na leka Farha da take kwance a kan gadonta da shine na farko. Barci take yi cike da nutsuwa. A duk sadda take barci ko ta yi murmushi sai na ga tamkar Abida ce. Duk da ba kammaninta a tare da ita. Na kalli Amrah na ce "kin sa ta yi addu'ar barci?" Tana daf da shigewa bayi ta ce "Ta yi Mahmah, sai da safe". Ta shige bayin ni kuma na ja musu kofar na nufi dakinsa. A kishingide na iske shi da waya a hannunsa. Na isa na zauna a gefen da nake kwanciya. Kafin na yi magana ya kashe wayar ya ajiye a kan durowar gefen gadon. Ya juyo ya kalle ni. Ya ce "Ya jikin dai?" Na amsa da ce wa "Na ji sauki Alhamdulillah! Muka kalli juna abin mamaki sai ban ji wannan dinbin soyayyar ta taso mini mai tsanani ba. Amma kuma duk haushinsa da nake ji bai saka na ji na tsane shi ba illa iyaka soyayyarsa ta fara samun tawaya. Ya janye idanuwansa dan kauce wa kallon da nake binsa da shi wanda ya kunshi al'amura masu nauyi. Ya numfasa ya ce "Wannan kallon fa? Tunda na dawo kike ta tsare ni da idanuwa, ya ya haka ne, gabadaya a kwanakin nan bana gane yadda kike mu'amala da ni fa! Na sake zuba masa ido kirr ban tanka ba. Ya kufulo ya ce "Oh yau ai Basma ta zo gidan. Komai kika yi babu laifi, sai dai na fada miki duk abin da kuke nufi nima na shirya masa." [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Na hadiye takaicinsa na ce "Ai na ga alamun hakan tun dazu". Na gyara zama na ce "Da na ga sako daga H.M.H. store sun cire kudi daga asusun ajiyarmu na zaci ma kayan dubiya ka siyo mini, na adana yunwata ina dakon ka sai kuma na ganka hannu na dukan cinya". Ya kadu kwarai da gaske da furucina. Ya ce Bilkisu ke nan. Dama an sha fada mini zan fuskanci haka, sai ga shi kuwa na fara ga ni. Ki fito ki ce kin gamsu da hudubar da take yawan fada miki na ce wa ki daina hada aljihunki da nawa saboda naki mai nauyi ne." Karon farko da ya fadi hakan ban ji gabana ya fadi ba, ban kuma ji fargabar bai fahimce ni daidai ba. Na yi gajeran murmushi tare da ce wa "Ba dan nawa yafi nauyi ba ne. Watakila tana jiye mini tsoron faɗawa yanayin nan na k'ato da shan bugu kura da cinye wa." Ya zuba mini ido sosai cikin son ya fahimci azancina. Nima din na zuba masa dukkan nawa idanuwan cikin rashin tsoro ko zullumim kada ya yi fishi. Ya ce "Kina nufin ina shanye romon wahalar ki ne Bilki?" Jin ya fadi Bilki nasan yana cikin rashin sukuni. Dan haka kaitsaye na ce "Kusan hakane domin kuwa kana yiwa wadanda basu cancanta ba hidima da wahalata. A tunanina baka da son zuciyar da zaka yi haka, sai dai da yake kai din dan Adam ne kuma jinsin namiji ba abin mamaki bane idan ka yi fiye da hakan." Ya fusata ya mik'e ya dauko walet dinsa ya fito da ATM dina ya jefo mini. Ya ce ",Ga shi nan matukar ina shakar numfashi ba zan sake taba abin da yake na ki ba ne. Mafi munin kuskurena shine yadda da na yi imanin zan yi yadda nake so da abinki kaitsaye domin na dauka mun riga mun zama abu guda. A sadda nake da dama ba abin da ban miki ba mai asalin tsada ba garabiti irin wanda kike yi mini ba." Na kada kai na ce "Tafi nono fari domin kuwa ban yi lalacewar da zaka yiwa budurwa hidima da abin da yake nawane ba alhalin ni tuni ka y'anta kanka da ga yi mini hidima kowacce iri tun shekaru masu nauyi da suka shud'e." Ya fusata ya ce "Tabdi jam! Wato halittar mace da gori take da kuma manta alheri take! Cikin nutsuwa na ce "Namiji kuma da son kai da zalunci yake ba.! Na fada a matukar zafafe. Ganin na fara fusata sai ya sassauta fishin ya ce "Dan na yi aure a yanzu ai na yi miki adalci. Shekaru sha biyar zuwa sha shida dan zan k'ara aure sai ya zama zalunci?" Na hadiye na ce ba zalunci bane. Amma a sanin da na yi maka baka da lafiyar da zaka iya gamsar da mace biyu. D'ayar ma ya ya ne? Sannan aljihunka ma bai cudi bayanka ba." Nan da nan ya muzanta ya ce "A da duk hasashe kike yi da tsananta bin diddigi a kaina. A yau kuma ina mai tabbatar miki ina neman aure, wanda zai tabbata a kusa kusa". Na kafe shi da kallo mai tsananin gaske murya babu amo na ce"Sai yanzu ne ya kamata na sani Sahal?" Kaitsaye ya ce "Tunda ban bari sai bayan na yi auren kika ji ba, ai kuwa na mutuntata ki" Gabana ya fadi sosai murya na rawa na ce "Tsakanin ka da Allah kana da lafiya da halin kara aure?" Ya murmusa ya ce "Ba ki da hurumin wannan tambayar. Domin ba matsalar da ta shafe ki bace " Murya babu amo na ce To ba zan lamince na cigaba da zama a gidana alhalin ka samu sukunin bani muhalli ban sani ba". Ya girgiza kai ya yi kwafa. Can ya numfasa ya ce "Kamar d'azu na na yi ta jaddada miki cewar duk abin da kuke nufi da ni na shirya masa. Kin sani Abida ma ta hak'ura ta bar ni da dukkan nak'asun da take jigina mini, bare kuma yar karere irin Basma! Na hassala na ce "A da ba Sahal, a lokacin ina sonka, ina ganin adalcinka". Ya rausayar da kai ya ce "Shike nan lokaci zai fayyace komai." Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa cikin nutsuwa. Yayin da ni kuma hawaye ya balle mini. Na kasa daina kukan nawa duk da marar sauti nake yi. Irin na sharbe mai sanya nauyin kirji. Ba'a dauki lokaci mai yawa ba, ya fara sakin munshari tabbacin yana cikin nutsuwar zuciya. Na zura masa ido sosai. Ina ayyana al'amura masu yawa a kansa, sashin zuciyata har ce mini yake yi na dauki filon na danne masa kansa har sai ya daina numfashi. Nan da nan na zabura na mike ina ta'a'uziya tare da istigifari. Ina neman a tsare mini zuciyata da hankalina mummunan kishi da tunzurin zuciya mai sawa a halaka a kuma kafirta. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Na doshi kofa na fice na doshi dakina. Na zauna a bakin gadon. Idona a bushe yayin da da zuciyata ta yi nauyi kwarai da gaske. So nake na yi kuka ko zan samu sassaucin yadda nake jin kishi na babbako mini tare da bin dukkan ilahirin jikina yana soke ni. A fili da kuma k'arfi nake ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun.! Duk yadda na kunna a c da fanka basu yi tasirin da zufa ta daina yanko mini ba. Na dinga safa da marwa a tsakiyar dakin. Ina ta kokarin karfafawa kaina guiwa ta hanyar yin tunani na gaskiya tare da son na tursasa zuciyata k'aranta mata damuwa. A fili na ce "Bai kamata na bari k'aramin tashin hankali ya sake tarwatsa zaman lafiyar zuciyata ba. Domin na yi amanna na shiga wanda ya wuce shi tsanani. Abin da ya faru a gidanmu ya fi k'arin aurensa firgici a gare ni. Ya kuma wuce, duk da ba'a samu daidaito ba har yanzu. Dan haka ba abin da zan ga ni na jarabawar rayuwa yafi wanccan al'amarin tashin hankali. Tunda kuma har zuciyata bata buga ba a wanccan lokacin, to kuwa ba abin da zai sa na bari ta buga a yanzu. Na fada bandaki na doro alwalla. Sallah nake yi ba tare da wata nutsuwa mai yawa ba. Amma a kalla na yi raka'a goma. Na kasa addu'ar komai. Kawai nasan ina ta ambaton Innalilahi wa inna ilaihir rajiun, Hasbinallahu wa niimal wakil. Har tsakiyar dare ina zaune kan sallaya ina ta lazimin da ya zo bakina. Yi nake yi domin na samu sukunin zuciyata domin na kasa rokon Ubangiji komai. Sai goshin asuba barci ya fara fizgata, na sanya jarumta na tashi na sake alwalla dan na wartsake sosai, ban zauna ba sai da na sallaci asubahi. Na samu saukin tunanin da ya yiwa kwakwalwata k'awanya. Amma gabadaya na sake tsunduma wajen son sanin inda zai ajiye amaryar da ya kudiri niyyar yi. Zuciyata ta harba da tsananin gaske a dalilin na tuna muna daf da kammala gini. Tabbas fili nasa ne sai dai kuma kaso casa'in na kudad'en da aka yi ginin daga lalita ta suka fito, filayena guda muka siyar aka fara aikin ginin, bayan kudin sun kare, kullum cikin zuba kudade masu nauyi nake har muka kai da fenti da k'ananun aiyuuka ne suka yi saura. Tirk'ashi na furta a fili tare da hasashen girman dabarwar da take gabana. Da na ga kaina ya dau caci sosai sai kawai na hau hailala a fili. Cikin ikon Allah sai nutsuwar zuciya ta same ni domin akan sallaya barci mai nauyi ya yi gaba da ni . Na ji dad'in barcin nan domin rabon da na yi barci mai nauyi kuma cikin nutsuwa na mance. Ban farka ba sai wajen tara saura na safe. Na yi matuk'ar mamakin yadda ko motsin shige da fice yara ban ji ba. Tabbas na tabbatar sun shigo, Amrah da Alti ne zasu hanasu tashina. Na sa ni kuma ba k'aramin lallaba Farha aka yi kafin ta yarda ta tafi ba tare da ta gan ni ba. Na yi salati na yunk'ura na fad'a bayi Kaitsaye wanka na yi. Na fito na shirya cikin riga marar nauyi. A haka Alti ta turo kofa a hankali ta leko, ganina a tsaye har na yi wanka ya sanya ta shigo dakin gabadaya. Da kuzari tare da walwala ta ce "Kin tashi Mahmah? Na ji dadin barcin nan da kika samu. Da kyar dai yarki ta yarda ta tafi makaranta". Na murmusa na ce "Farha duniya. Ni da kaina na tabbatar ba karamin wahalar da ku ya yi ba." Cike da kulawa ta ce "Na miki kunun gyada. Na soya miki awara ne? Na dafa miki tun dare na saka a firij". Na murmusa na ce "Sannu da kokari Alti. Allah ya taya ni gode miki". Walwalar fuskarta ta karu. Tare da ce wa "Ameen Hajiya Mamah. Allah ya ninka miki walwalar zuciya da ta fuska." Na amsa da fadin "ameen ameen, zan yi walaha yanzu, wajen goma saura sai ki fara soyawa". "To " Ta fada da azama sannan ta juya ta fice tana fadin "Alhamdulillah!. Bayan na kammala karyawa da kaina na kwashe kayan na kai kicin. Na zauna a falo yayin da Alawiyya ta shiga dakina dan ta tsabtace. Gabadaya tamkar wanda aka cire mini Sahal a raina domin ko ganinsa ban ji ina son yi ba. Na cigaba da zama a falo har ta kammala ta bazawa dakin daddan turaren air freshener. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Jimawa kadan na koma dakin, akan kafet din na zauna ba akan gado ba. Sai dai na dauko filo guda daya daga kan gado. Haka kawai nake na jin d'okin cigaba da hakaito rayuwarmu ta baya dan na sake nisanta kaina da tunanin Sahal da kudirinsa na karin aure wanda yake ganin zai iya muzanta ni matukar na ce zan yi adawa da hakan. Na numfasa na janye filo na jingina da shi. Na lumshe ido na sake kutsawa tiryan tiryan ina hakaito abubuwan da suke zaune daram a kwakwalawata da wanda bayyanasu zai zama darasi da gargadi. Tunda na ga Abida ta hau nazarin karatu ya sanya na mike na shiga kicin dan na dora mana abin da zamu ci domin ba zata sake yi mini magana na har sai ta kammala al'amuran gabanta. Washagari ta juya Katsina ta zarce kaitsaye. A lokacin goyon Yaya Faruok Sahal ya samu budi sosai. Dan har Umra ya biya mana ni da shi tare da yaranmu gabadaya. Haka ya biyawa iyayensa duk da sun je. Bayan shekara da zuwanmu kuma ya biyawa su Baban Zaria da matarsa takwarar Amrah. Gata da tattali ba wacce bai mini ba, komai zai ajiye mini tamkar ba da kudi yake siya ba. A haka na yaye Faruk tuni kuma Amrah ta shiga makaranta. Hankalina ya koma kan rubuce rubuce akan abubuwan da suke Gina ciki. Misali zan dauka Apple na yi rubutu akansa da irin alfanunsa a jikin Dan Adam da sinadarin da yake bayarwa da nauin mutanen da suka fi bukatarsa a jikinsu. Wani lokacin Kuma sai na yi bayani akan mangwaro. Duk Kuma a kafar sadarwa ta Facebook tunda itace a lokacin kawai. Kafin na ankara sai na sake tara mabiya. Ina kuma sake fadada business dina na snacks. . Gabadaya na zama babbar mace da ilimi da gayu suka ratsa tunda miji ya tsaya mini sana'a kuma ta yi k'arfi. Iyayenmu kuma masu hali don ko da suka aurar da mu hidima suke yi mana kan hidima basa saka ran mu yi musu. Sai dai muna yi don neman albarka. Na zama big madam mazaunai sun fito sosai Dan haka na bude ta kasa na bada shape mai daukar hankalin masu kallona. Fata tana samun mayuka da sabulan da suka dace da ita kwarai da gaske. Haka nan kamshina na mussaman ne domin kuwa turare designer nake amfani da shi. Wadannan dalilai suka sanya na sake makalewa a zuciyar Sahal yana al'amarin kasancewata matarsa, shi da kansa yasan nafi dacewa da manyan masu kudi da suka zarta shi komai da koami dan kuwa shi din gabadaya nai bani shekaru uku cikakke ba ta bakin Abida. Sai dai har wannan lokacin da muke shekaru biyar da aure ba zan ce ina cikin rashin nutsuwa a dalilin aurensa ba. Kawai matsalar daya ce. Tabbas bashi da sha'awa mai yawa, wannan ne kawai tasgado domin ina kwaruwa sosai. Amma ba yadda na iya dan haka na saka rashin samun biyan bukata shine jarabawar aurena. Kuma abin mamaki zaman namu na nisa al'amarin na sake yawa. Dan yanzu kam sai mu kwashe kwanakin wata bai nema ba. Sai dai idan ya ga mutsumutsuna ya yi yawa zai yi romancing d'ina har sai na samu na fitar abin da ta takura ni. Na fara tunanin ko lafiyar makarfafarsa ce ta yi kadan. Na fara nazarin abubuwan cima da zasu taimaka masa wajen motsa masa sha'awarsa. Kullum cikin nazari tare da gabatar masa duk wani nauin abinci ko kayan marmari da suke taimakawa amma babu wani sauyi. Na fara magana da likitoci ana rubuta masa magani amma kuma da ya sha daya biyu to ya bar mini su kenan. A wanccan lokacin da shekararuna basu da wani yawa sai nake jin tsoron irin na gagajiya wanda ake zubawa miji a lemu ko a shayi don ina jin tsoron kada ya gane ya ce asiri nake yi masa. Ga shi al'amarin mai matukar nauyin ka tattauna da wani ne. Kan dole na hakura nake ta kokarin na danne abin tunda haka kaddara ta zaba mini. ✏️ *Contact me 08032773332 what'sapp only* *For all your kayan mata gangariya* *Bridal package* *Maijego package* *Uwargida package* *Bazawara package* *Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego* *Ciccibin garari* *Tsumin saiwowi* *Hakkkn daka emergency* *Gumbar ridi* *Gumbar saiwowi* *Surayya ce da kanta take kawo muku su daga Chad da Sudan*. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har Yaya Faruk ya isa shiga makaranta aka saka shi wacce Amrah take yi. Har zuwa lokacin kuma Abida bata yi aure ba. Watanni uku da kammala resident dinta a jamiar kasa ta Lagos (Uni Lag). Burinta kuma ta wuce da karatunta har sai ta zama kwararriyar likitan mata. Ta fada mini ta riga ta gama cike ciken tafiya kasar Uk dan ta zama gynecologist, sai komai ya kankama kafin ta bari gida su sani dan kada ma a hana ta tafiya, domin matukar ta samu gurbin karatun to ba za'a hanata ba tabbas. Bayan haka kuma ta nemi gurbin karatun a jamiar Ahamadu Bello, ma'ana raba kafa ta yi, tsakanin guda Nigeria da Kasar England. A matukar sanyaye na yi mata murna da fatan alheri, tare da addu'ar Ubangiji ya zaba mata mafi alheri. Tana shirin shiga shekaru ashirin da bakwai amma bata maganar aure sai dai neman ilimi tamkar alhuda alhuda. Autar gidanmu gabadaya ta kammala sakandire a bana. Bata damuwa da yadda aka aurar da kannemu ita tana zaune. Da yammaci ina zaune a falo ya dawo, na tashi na karbi jakar hannunsa tare da yi masa barka da zuwa. Ya jani jikinsa yana shinshinar kamshina jikina tare da tab'a gashin kaina da ya sha gyara yake tufke cikin katon ribbon. Ya dan shafi mazaunan da suke tsole masa ido da tare da yin spanking dinsu. Maimakon na ji dadin hakan sai takaici ya nemi taso mini domin daga hakan shike nan. Ba komai zan samu da ya wuce hakan ba. Kaitsaye dakinsa muka wuce na adana masa jakar na ce "Wanka zaka fara ko abinci?" Ya ce "Bari na watsa ruwa tukun". Na juya tare da ce wa "To a fito lafiya". Na ja masa kofar na nufi kicin na shiga fito da abincin ina shirya masa a dining table. Tuni mun bar gidan da muka fara zama da muka dawo Kano. Gida mai kyau na bada labari ya kama haya, kuma na shekaru uku ma ya biya, bamu jima da tarewa ba. Shi kuma cikin kaddararsa ko maganar ya sayi gida ba ya yi, don na tabbatar zai iya siyan gida ko da ba irin wanda yake hari ba. Ko maganar ya sayi fili na yi masa sai ya ce "so yake ya samu kudin da zai saya a unguwa mai daraja. Tunda ya siya a katsina sannu a hankali ma zai siya a Kano. Ni kam jinsa nake yi, domin ban gamsu da dabararsa ba. Ni a tawa dabarar ya siya a koina mana, sannu a hankali idan ka sake samun wani kudin sai ya siyar ya hada ya sayi irin wanda yake so, domin na tabbatar samun irin wanda yake so a cikin manyan unguwannin birnin Kano zai yi masa wahalar gaske tashi guda. Ya fito sanye da jallabiya ruwan toka sai kamshin turaren() ke tashi. Cikin nutsuwa nake zuba masa. Na zauna yana ci yana yi mini hirar yadda ma'aikatarsu ta Nigerian airways kullum take fuskantar kalubalen rashin samun tallafin da ya dace daga gwamnatin tarayya. Na zuba masa ido na ce "Ni fa na dauka gwamnatin na bada kulawa ta mussaman ga ma'aikatar tunda harkar sufurice ta kasa da kasa " Ya ce "Hmm al'amarin dai sai kurum cin hanci da rashawa ta shiga ko ina. Ko muma da aka buda mana muke samu ai kinsan hanya ne tunda shugaban ma'aikatar gabadaya abokin Baban Mashi ne. Idan ba haka ba ai albashina bai isa komai ba. Duk wata ma'aikata ko kamfani mai muhimmaci gwamnatin nan sai ta yi shagulatin bangaro da shi har sai ya durkushe ko sai sun cefanarwa yan kasuwa sannan hankalinsu yake kwanciya." Na numfasa na ce "Baban Amra ya kamata ka yi himma ka mana gini ka kuma saka hannun jari a kamfononi domin tsaron ko ta kwana. Ranar da aka ce babu shugaban wajen fa?" Ya ce"Kin fini tsinkaye Billy! Zan fara dan gaskiya albashi kadai ba zai rike mutum ba". Yana kammalawa ya tafi dauko su Amrah tunda sai biyar da kwata suke tashi a dalilin har da islamiya a makarantar suke yi. A daren wannan ranar bana mantawa da kaina na ballo masa magani da ruwa ya karba ya sha bai yi musu ba. Sai dai kuma yana gama sha ya kwanta barci mai nauyi ya yi gaba da shi. Sai da asuba ya bukace ni, ya yi iya abin da zai yi, ya samu gamsuwa shike nan ya tsallake ya yi wankasa ya hau shirin tafiya ofis. Ya kalle ni ina kwance tamkar ruwa ya cinye ni domin ni gabadaya ban ma gane komai ba. Wani irin abu na mamayata tare da [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Yana kammalawa ya tafi dauko su Amrah tunda sai biyar da kwata suke tashi a dalilin har da islamiya a makarantar suke yi. A daren wannan ranar bana mantawa da kaina na ballo masa magani da ruwa ya karba ya sha bai yi musu ba. Sai dai kuma yana gama sha ya kwanta barci mai nauyi ya yi gaba da shi. Sai da asuba ya bukace ni, ya yi iya abin da zai yi, ya samu gamsuwa shike nan ya tsallake ya yi wankasa ya hau shirin tafiya ofis. Ya kalle ni ina kwance tamkar ruwa ya cinye ni domin ni gabadaya ban ma gane komai ba. Wani irin abu na mamayata tare da tambayar kaina shin ita mace bata da hakkine a wannan fagen? Komin bukatarta matukar namiji baya da muradin haduwar sai dai ta yi hakuri ta yi ta fama da ciwon zuciya da kukan cikin dare? Haka nan ita mace bata da hakkin idan an hadun a tabbatar an gamsar da ita? Namijine kadai yake da hakkin ya gamsu a cikin al'amarin?" Ba ni da mai warware mini wannan tambayoyin, amma kaina ya yi matukar daukar caji. Ya ce "Ba zaki tashi ki shirya yaran ba ne?" Cikin dabara na dauke hawayen idona. Cikin nauyin jiki na sauko na nufi bayi. A gurguje na yi wanka. Na fito na saka riga na fita kicin ganin har shida da rabi. Kaitsaye na dora doyar da na fere tun daren jiya. Kafin ta dahu na je na tashe su, na yi musu wanka. Na shirya Yaya. Yayin da Amrah take shiryawa da kanta. Na tafi kicin bayan na ce su yi sallah. Na fasa kwai na hau soyawa. Na zuba musu a lunch box dinsu yayin da na hada musu cornflakes suka sha. Shi kuma ganin zasu makara sai na shirya masa doyar da tea a basket, ya karya a ofis. Ya fito yana daura agogo ya ce "Da alamun idan na tsaya karyawa zamu yi latti da yawa. Ganin na fito masa da basket ya sanya ya yi murmushi ya matso kusa da ni ya karba ya jani jikinsa ya yi mini sumba a goshina da kumatuna. Ya ce "Allah ya yi miki albarka. Daga haka ya tisa yaran suka fice. Na bisu bakin kofar falon ina yi musu addu'ar dawowa lafiya. Ba wani kuzari na hau aikin gyara kicin, din, sannan na dawo falo na gyara. Yau kusan sati kenan da tafiyar yar aikina garinsu akan Babanta ba lafiya. Kafin karfe tara na gama komai na kintsa ko ina har dakin barci da na su Amrah. Sai da na yi wanka sannan na karya. Na yi wanka na shirya so nake na yi rubutu akan tasirin da garin k'irya take da shi da yadda ake sarrafata ta yiwa mata maganin dukkan naui'in cutar daji(kansa). Tunda kan kansar mama, ta mahaifa, ta fata da dukkan naui'in ciwon daji. Amma zuciyata babu sukunin yin rubutun domin matsalar da nake fuskanta kullum sake mikawa take yi, ba ni kuma da halin da zan yi korafi ko na tattauna da wani tunda a wanccan shekarun abin kunya ne mace ta bude baki ta yi irin wannan korafin sai idan tura ce ta kai bango. Kan dole na kwanta ina fatan na samu barci ko na huta da kunan rai. Na jima ban samu barcin ba, sai dai da ya sure ni ban farka ba sai wajen karfe uku. Da azama na duro daga kan gado bayan na kalli agogon bangon da ya fada mini karfe uku saura mintina takwas kacal. Da na idar da azahar lazimi na zarce da yi har sai da na sallaci la'asar. Sannan na shiga kicin dan yin abincin da zamu ci. Domin na riga da na saba girki daya nake yi. Kwanaki suka yi ta shudewa suna haifar da makwanni, da haka a samu kwanakin wata, watanni su haifar da shekaru. Rayuwar aurena da na yi a Kano itace rayuwa mafi dadi a gare ni, domin cikin nutsuwa na yi zaman. Miji na cikin wadata, shi kuma bai mini kwangen komai ba. Ba ruwansa da samun kudina, baya kuma taba sakar mini wahalar gidansa. Komai yi mana yake yi ni da yara a wadace, ko hidimar bikin dangina ne ya taso zai bani gudunmawa mai nauyi, shima kuma zai je ya bada nasa. Dan haka kowa yake mini kallon na taki sa'a. Don hatta Abida ta yi matukar mamakin yadda Sahal yake da halin girma. Gaskiya ba ni da matsalar zahiri da za'a iya nunawa. Domin ni kaina da ace yadda yake sauke nauyin ciyarwa da tufatarwa tare da kula da lafiya haka yake sauke hakkin auratayya da na ce ba ni da matsalar komai a aurena. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Amma da yake dukkan aure da irin nasa kalubalen ni cikas din nawa mai girmane, dan har rayawa nake yi inama a abinci nake da tasgado tunda ina da kudin da zan siya mana abinci. Kan dole na cire matsalar a raina tunda tana da nauyin a fayyaceta na mayar da hankalina kan abubuwan da nake samunsu. Na tara kudade sosai a asusna domin kwarai da gaske sana'ar bakery tana kawo mini kudi mussaman shekarun baya da sana'ar bata yi yawa irin yanzu ba. Mun yi murnar cikar aurenmu shekaru takwas (wedding anniversary). Kwanaki uku a tsakani muka tashi da wani tashin hankali na rushe kamfanin Nigerian airways aka kuma sallami ma'aikatan daga aiki babu garatutu bare a je ga batun fensho. Mun shiga rudani kwarai da gaske. Amma da yake yarda da kaddara wajibine a sharadin zama mumini. Muka hakurkurtar da zuciyarmu mu karbi wannan kaddara da hannu biyu. Na taka muhimmiyar tawa wajen kwntar masa da hankalinsa a wannan lokacin. Haka aka yi ta zuwa mana jaje tare da fatan Allah ya kawo masa wata mafitar mafi alheri. Bamu shiga matsalar a farko ba domin shi mutum ne mai tara kayan abinci da yawa sosai, sannan a duk sadda zan yi cefanen kayan su samosa, spring rolls, meat pie, pizza da sauransu, cefanen ne na sosai dan haka a ciki muke diba mu yi amfani a gida. Kudin hayar gidane ya nemi daga mana hankali domin mai tsadane sosai, amma dana runtse ido sai kawai na cire a asusuna na biya. Farinciki kan farinciki Sahal ya yi tare da yaba mini. A yanzu da yake zaman gida komai tare muke yi, sannan ya ninka soyayyarsa a gare ni tare da kulawa da yaranmu, zai kaisu makaranta, idan lokacin tashi ya yi zai je ya debo su. Baya wani fita ya jima sosai. A rubuce rubucen da nake yi a kafar sadarwa ta Facebook ya ja hankalin mahukuntan hukumar lafiya ta duniya(W.H.O.) Suka gayyace ni ofishinsu, suka tattauna da ni, suka bukaci sanin matakin ilimina. Na tabbatar musu na yi karatuna na firamare har zuwa matakin digiri. Sannan na karanci ilimin abincin da ya dace da kowanne rikunin Dan Adam. Suka ce washagari na koma tare da dukkan takarduna. Na fito na tarar da shi a mota. Na shiga ya ja muka tafi. A hanya ya kalle ni ya ce "Ya ake ciki?" Da walwala na ce "Sun bukaci na kawo credentials dina gobe". Ya fadada murmushinsa ya ce "Alhamdulillah! Ina ji a jikina Ubangiji zai sake kawo mana dauki" Na taya shi murna tare da ce wa "Allah ya biya bakinka". Washagari tare muka fita da yara. Sai da muka fara ajiye su sannan muka wuce. Cikin sa'a kuwa bayan mun shafe awanni biyu na fito dauke da takardar daukata aiki na tsawon shekaru uku. Abin burgewa sau biyu zan fito a sati, sai na yi musu rubutun da zasu dinga dorawa shafinsu cikin harshen Hausa da turanci sau daya a sati. Ba karamin murna muka yi ba domin albashina mai tsoka ne matuka da gaske. Dan haka bamu wani shiga zullumin rashin aikinsa ba. Ba wani abin da ta canja mana. Sai dai shi tunda mai son ya yi alherine sai ya takura, duk da ban shata masa layi da komai nawa ba. Ko biyan kudin makarantar yara na shekara na biya musu dan haka komai lafiya lau. Watanni takwas da rashin aikin Sahal. Mun je hutu gida Funtua ni da yara zamu yi sati guda, domin na kwana biyu ban je ba. Na tarar da Abida da su Baba ana artabu domin kuwa daga Baba babba har Baba karami sun hade mata kai sosai akan ba yadda za'a yi su bari ta tafi uwa duniya babu aure da sunan zurfafa ilimi. Dama ace digirin farkone da sauki, amma yanzu tana da aikinta tunda likitace a babban asibitin Funtua tun shekarar da gabata take aikin. To matukar sun isa da ita aure suke so ta yi idan tana da auren ta tafi birnin Sin ma ba Ingila ba. Ba Abida ba, ni kaina mamakin yadda Baba babba ya shafawa idonsa toka ya yi nake yi, domin kuwa kowa yasan baya iya takure ta. Watakila kuma ya yi hakane don Baba karami ya kafe ba zata tafi uwa duniya babu aure alhalin tana da shekaru ashirin da bakwai tana shirin cika da takwas. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Cikin fishi sosai na tarar da ita, bata shiga shirgin kowa, kullum tana dakinta, ruwan shayi kawai take sha. Amma ganin Amrah yasa ta dan sauko take hira da ita. Yanayin da take ciki sai ya sanya ban ji dadin hutun ba. Domin tun filazal ita da Yaya Munira sune cikon farincikina a gidan, nafi shakuwa da su akan yayan mahaifina. Tun Mami na mini sababi har ta hakura ta kame bakinta mussaman da a yanzu duk cikin yaranta babu wanda yake gatantata Irina. Yaya Sulaiman ne yafi ni dama a cikinmu shi kuma ba'a kasar yake ba, yana Germany. Tunda ya kammala karatunsa ya zama likitan ido gwamnatin Kasar Germany ta rike shi na shekaru uku dan ya yi mata aiki. Amma ya dawo sati hudu da suka shude, dan haka zuwan nawa ma har da yi masa barka da zuwa. Dan da ya kammala wa'adin shekaru ukun sun so ya sake zama amma ya bijire tunda ya nemi aiki a nan Nigeria. Ya kuma samu da gwamnatin jihar Katsina. Yana cikin likitocin asibitin cikin gidan gwamnatin Katsina. Haka nan Yana da ofis a cikin babban asibitin Katsina. Dan haka idan zai mata aike kudi yake turo mata. Ni kuwa komai take so yi mata nake yi, haka bana raba ta da kayan ciye ciye kala kala, domin a kai, akai akai nake yin samosa da da meat pie na aiko mata ta saka a firij tunda a wanccan lokacin babu matsalar rashin wuta a Funtua. Na dauke mata gudunmawa, haka nan ina mata dinkuna sosai. Ina hadawa na yi musu da Momi amma dai na Mami ne sha kundum, dan haka na samu sassauci sosai a wajenta, ta daina tsananta mini akan sha'anina da su Abida, ta daina mini shagube, ta daina bagarar da lamarina. Tunda ya gamsu lamarinta shine gaba a wajena har mahaifina kuwa. Daren ranar da muka je muna dakinmu na sashen Mami. Na kalli Abida na ce "Yanzu Abida menene abin fishine har haka? Ki huce ko kuma ki fitar da mijin tunda idan har mijinki zai barki ai kuma ba sauran ace za'a hanaki yin abunda kike so". Ta ja k'aramin tsaki ta ce ",Ban samu wanda nake so ba. Ni dai kawai su Baba sun takaice ni. A wannan marrar wanne namijine zai yarda da ga yin aure na tsallake na tafi na bar shi? Su sun kasa fahimtar aure fa ba wajibi bane matukar mutum zai kame akan me za'a mini dabaibayi irin hakane?" A tausashe na ce "Suna son ke ma ki yi naki iyalin, aure ai sutura ne, rufin asirine ta hanyarsa kadai zuria take yaduwa" . Ta kaurara murya ta ce "Kun haifa mini, naku sun ishe ni". Na ce "To tunda kin samu a A.B.U din ki yi anan din mana" A takaice ta ce "Nan din ma sun ce sai na tsayar da miji sannan zan yi. Ni kam gaskiya an takure ni, ni fa jina nake yi dakila ce don kuwa yana wahalar gaske na ji sha'awa bare har na gundura da zamana haka. Menene a cikin aure ne ban da jidali, haka kawai ina cikin zamana na jefa kaina a garari. Ba dama kuma ka zo gida a saurare ka sai dai ace ka yi hakuri, suma hakurin suke yi. " Dariya ta so subuce mini wai tana zaton ita dakila ce. Amma na maze domin a halin da take ciki idan na yi kuskuren yi mata dariya zamu hau sama mu fado ne. Na cije na ce "Ke ba dakila ba ce Abida! Dan dai kin kulle zuciyarki ne akan rijalu amma da zarar kin samu wanda ya yiwa zuciyarki kutse na ban mamaki zaki tabbatar ke din ba haka kike ba" Ta zuba mini ido ta ce "Sannu Maigado masaniyar komai akan mace da namiji". Na tuntsire da dariya domin gabadaya a kufule take, kuma so take sai na gasgata ita bata cikin jerin mata masu sha'awa. Washagari har azahar ban ga Yaya Sulaiman ba. Na kalli Mami da muke zaune a falo na ce "Yaushe zai zo na gan shi ne? Na kasa samun wayarsa". Mami ta muskuta ta ce "Ina ganin gobe alhamis su dawo tare da Babanku". Na ce "To Alla ya kaimu ya kuma kawosu lafiya". Ta amsa da "ameen". Washagari kuwa tare da Baba karami suka dawo. Na jima ina karewa Yaya Sulaiman kallo domin ya zama zabgegen saurayi na k'asaita .Kammanina da shi sun sake bayyana karara. A tsaye yake cak tamkar dai Yaya Asad, banbancin yafi Yaya Asad haske. Ba farine kamar ni ba, amma kuma ba za'a shi a sahun bakake irinsu Baban Bilkisu ba. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Hoton fuskata na ga ni a fuskarsa sai banbancin gemu da kuma hasken fatata da sauran abubuwan da zasu banbanta jikin mace da na namiji. Amma tabbas muna matukar kama da juna. Na tafi lissafin shekarunsa domin shekaru shida ya bamu. A lokacin shekarunsa talatin da uku. A wanccan lokacin gani ake yi ya zama tuzuru domin dukkan sa'aninsa da ma wanda ya girma sun yi aure har sun haihu. Tun filazal Yaya Sulaiman dan gaye ne kuma dan bokone na gaske. Amma da ya dawo na fahimci ya samu cigaba mai yawa, ya goge da ilimi da kuma wayewar rayuwa. Sadda suka iso ni da Abida muna farfajiyar harabar wajen adana motoci, gidan Yaya Faruk zamu je yini. Da girmamawa muka gaida Baba karami. Ya kalli Abida ya ce "Maryam kin huce, kin daina fishin?" Ta dauke kai i tana fishi fishi kunya kunya ba tare da tanka ba. Ya ce "Ato gara kisan matakin dauka dan kuwa tabbas babu maganar wata makaranta kuma sai a dakinki. Ke ko sha'awar yanuwanki da kike ganinsu da yaransu ba kya ji?" Da shagwaba ta ce "To Baba sun duk sun samu mazan ni kuwa fa?" Ya zabura ya mata dakuwa tare da yin kanta zai kai mata bugu. Ta yi maza ta goce ta falfaala bata tsaya ba sai da ta bada tazara, sannan ta tsaya tana dan haki. Ya ce "Mutane nawa suna zuwa wajenmu da sunan sun gan ki suna so, kina yin tsallen albarka kina fadin ba da yawunki suka zo ba?" Ta kasa amsa masa. Ya yi kwafa ya ce "wannan karon kam ko ni ko ke na gaji da iyashegen ki, inma jinnul ashuq ne akanki zasu ci iyayensu dan kuwa na shirya yin arangama mai zafi da su". ✏️ [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Daga ni har Yaya Sulaiman muka kwashe da dariya domin yadda Baba ya furta jinnul ashuq akwai ban dariya kwarai da gaske, yayin da ita kuma ta sha mur. Haka muka tafi gidan Yaya Faruk tana ta gungunin ita bata da mashanshani, don kuwa duk wanda ake lissafin sun zo da sunan suna sonta ba jarumai bane ba kuma mijinta a ciki. Don ta yi imani da akwai mijin da kaddara ta zaba mata a cikinsu da tuni ta yi auren ai. Muka isa gidan Yaya Faruk muka tarar yana shirin tafiya gidan gona. Ya dinga marabtarmu cikin barkwanci. Haka ma matarsa domin a yanzu kam gaisuwar girma da arziki muke yi ta daina tsananta mini. Ya zauna ya ce to ku gaisa da matar gidan ku sha ruwa sai mu tafi gidan gonar mu yini a can ko sarauniyar shaiba?" A duk sadda ya ce hakan har cikin raina nake jin sunan. Tare da tasowar al'amura masu yawa a kansa. A sanyaye na ce "To Yaya Faruk". Ya saka hannu ya dauki mai sunansa da ya yi barci tun a hanya. Yana fadin my name sake tashi ka ga Yaya Faruk senior." Na murmusa ba tare da na ce komai ba. Ya kalli Abida ya ce "Autar momi wai har yanzu ba ki huce ba ne?" Ta sake zumbura baki amma bata tanka ba. Ya sassauta ya ce "Indai kin san akwai wanda yake sonki ki ba shi dama mana, ba fa wacce su Baba suka daga mata kafa irin ki. Ina jiye miki kada ki yiwa kanki sanadin da zaki ji sun bada aurenki ga wanda suka ga ya dace" Ta murmusa ta ce "Ba maganar a mini auren dole Yaya Faruk. A wannan karnin? Da ilimina?" Ta girgiza kai tabbacin ba mai yiwuwa ba ne. Na zuba mata ido ba tare da na furta komai ba. Wato Abida asalin feminine ce. Ya Farook ya kalle mu ya ce "Rigunan jininku sun mini kyau. Ban cika ganin abayas irin haka ba anan". Abida ta ce "Bilki ta siya mana a wajen Umm Aslan &Asalah. Egyptian abayas ne kasan sune original. Ya ce gaskiya sun yi kyau sosai nima zan baki ki siyowa Jamila irinsu ". 201121544627 da +2349162662750 Kawai ta tuntube ta a WhatsAp sai ta zaba da kanta idan kun tura kudin, sai na karba muku a Kano tunda anan kayanta suke sauka. Haka muka rankaya muka nufi gonar ladi farms da kwandon abincinmu matarsa ta hado mu da shi. Yadda muka zo a motar Abida haka muka shiga ya ja muka yi gaba yayin da ya shiga tasa ya bimu a baya. Gabadaya gidan gonar ya sake habaka, dukiyar dabbobi kala daban daban a ciki iya ganinka. Haka nan an gyara ta gyra na mussaman domin har zuwa ake yi da sunan yawon bude ido. Sosai ake hada hadar kasuwanci a ciki. Madara da yogurt din da ake sarrafawa a ciki na manyan kudade ne masu matukar nauyin gaske. Hatta kwai a kullum ana diban sama da dubu talatin ban da wanda suka fashe, shiyasa ma'aikatan wajen suma yawane da su tamkar me, an samu cigaba ta hanyar samarwa matasa masu yawa aikin yi Yaya Faruk ya sake zama babban mutum kudi ya zauna masa duk da shi kadai ne a Funtua cikin yayyanmu. Amma yana cikin daula don idan kana gidansa ma sai ka zaci kana Abuja ne cikin rikunin uguwanni masu daraja. Duk yadda nasan ladi farms girmanta ya kai kurewa amma a wannan ranar da na shiga cikin shekaru na hankali, ina kuma cikin nutsuwa sosai, na tsorata da irin girmanta da tarin dabbobi da shuke shuke. Don yanzu har 'katon runbun abinci an gina ta yadda ake adana kayan amfanin da aka nomawa a ciki. Jikin mangwarori suka yi parking muka yi shimfida muka zauna. Gabadaya wajen yabanya ce ga danshin k'asa a dalilin duk safiya da maraice sai an jona tiyo a duk inda aka yi shuke shuke ko inda koriyar ciyawa take. Duk yadda shekarun nan suke tafiya Yaya Faruk bai canja ba. Zama yake cikinmu a rak'ashe duk mai matsala ta zano masa, shi kuma zai saurare ka da kunnen basira ya kwantar maka da hankali ya kuma baka shawara ta gaskiya. A yau kam Abida ce ta dinga jero masa laifukan Momi. Ashe duk yadda soyayyar Abida bata boyuwa a wajen Momi yanzu zaman nasu ya fara tsami bisa dalilai guda biyu. Ita Momi aure take so Abida ta yi, dan haka ta matsa lambar sai ta fito da miji, bayan haka mafi yawa bata bari ta yi dinkuna ko saka kayan alatu bisa hujjar wai maza zasu kasa dunfararta da sunan aure tunda suna ganin matsayin aikinta da matsayin gidansu, kaya masu tsadar gaske kuma zasu sake kaita kololuwar [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: matsayi. Ya yi dariya ya ce "Hakuri za ki kara yi, lamarin iyaye dole a bisu yadda suke so. Sannan ni kaina so nake ki yi auren Abida! Menene ya rage miki ne? Aure kuma shine suturar mace. Duk zurfin karatun da zaki yi, matukar ba ki da aure kin rasa wata kariya ta mutuntaka da aure kadai ke bawa mace shi. Ki nutsu ki sassauta burinki, ba yadda za'a yi ki samu irin teste din ki, domin no body is perfect a cikin wannan rayuwar." Ba walwala ta ce "Aure lokaci ne fa yaya Faruk. Kuma ni ba wani dogon buri ko wani tsatssauran ra'ayin na dauka ba. Kawai wanda zuciyata ta nutsu ne ban samu ba, amma ko yanzu idan na samu wanda na aminta da shi zan gabatar da shi. Akan me za'a matsa mini har sai na je na auri wanda ba mijina ba ne?. Muka kwashe da dariya. Na kasa ce wa komai domin yanzu zata sauke mini fishinta da take fama da shi, na sani. Yaya Faruk ne ya ce "Dama ana auren mijin da ba naka ba ne autar momi? Da dukkan zuciyarta ta ce "sosai ma domin idan na auri wrong person ai ban auri mijina ba domin na fada cikin garari da talajaurar duniya". Ya gintse dariyarsa ya ce "Da ikon Allah na gari za ki aura albarkacin adalcin da iyayenmu maza suke yiwa iyayenmu mata ba za ki yi aure inda za ki wulakanta ba. Fatana ki kwantar da hankalinki. Ki bude zuciyarki ki fahimci manufar iyayenmu ". Anan muka yi sallar la'asar. Wajen karfe biyar sai ga Yaya Sulaiman ya iso akan machine. Yaya Faruk ya kalle shi ya ce "Baka son yin tuki ne?" Da walwala ya ce "Da kafata na yi rabin tafiyar. Sai kuma na hau machine domin daga bakin gate din nan ma shigowa ciki ba karamin tafiya ba ce mikakkiya". Yaya Faruk ya ce "Ka yi kokari, ka kuma motsa jikinka. Na kalle shi na ce "Yaya Sulaiman sannu da zuwa dama na k'osa mu hadu". Ya zauna yana ce wa "Ga ni "Bilkisu sarauniyar shaiba in ji Yaya Faruk ". Muka murmusa gabadayanmu ban da Abida da dama ba wani jituwa suke yi ba tun filazal. Ya kalle!ta ya ce "Autar momi saboda Allah har yanzu ma da kika girma ba zamu shirya ba? Tunda na dawo sau uku kika bude baki kika mini magana fa". Yana rufe baki ta ce "To ai sau ukun muka hadu." Ya ce" yau fa?" *Gunis hijab ba na biyunta wajen kawo hijaban da suke da kyau da nagartar.* *Gunis hijab ado cikin wayewar addini da rayuwa* *08163761797* Kaitsaye ta ce "Dazu bamu gaisa ba? Yanzu kuma daga zuwanka sai na ce make me?" Ya girgiza kai tare da ce wa "Ho Abida! To sannu da yammaci ". Ta amsa da fadin"Sannunka dai Yaya Sulaiman". Daga haka ta tsuke bakinta yayin da ni nake ta fadin [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Baba karami kam sai da aka sare gaban motar sannan aka fito da shi sai dai Babu rai ya amsa kiran mahaliccinmu. Wannan mutuwar na tsaya hakaito muku yadda ta yi mana mugun bugu bata lokaci ne mai yawa. Amma mutuwar Baba ya zama tamkar tafiya da dukkan nutsuwa da walwalarmune gabadaya. Daidai nan kuka mai tsananin gaske ya k'wace mini, dama lallaba zuciyata nake yi sai kuma na zo inda duk dauriyata dole na koka, dole hankalina ya tashi domin an zo gabar da bana fatan masifar da ta sauko mana ta sauka kan kowanne ahali. Mutuwa da ciwo da tonon silili take. Allah ka jikan makabantanmu. Da yake dab da magariba aka yi hadarin labarin mutuwar sai bayan magariba ya riskemu. Cikin tashin hankali na isa gidan Abida. Kuka muke yi kan kuka ita kam ta tubure a lokacin zamu tafi tunda Yaya Sulaiman na asibiti rai a hannun Allah. Da k'yar da sudin goshi Yaya Asad ya dakatar damu akan gobe da asuba zai saka a zo a kaimu Funtua. Barci barawo a wannan ranar bai iya satarmu ba. Gabadaya ni da Abida a rikice muka ainun ba mai bawa wani hakuri. Sai dai na yi imanin Abida ta fini rikicewa. A fili cikin kuka take ce wa "Allah ka kaddara mini na ga Yaya Sulaiman da ransa, Allah na tuba kada a yi mana biyu innalillahi wa inna ilaihir raji'un! *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher n zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini later domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zata iya zuba kudi ta saro masu daraja irinsu ba*. *Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*. Kuka nake yi mai tayar da hankali sosai amma da zarar na kalli Abida sai na ji tashin hankalina na sake rub'anya mussaman idan tana gunji tana rokon Ubangiji kada ya k'addara mata yin takaba a yanzu. K'arfe shida na asuba motar y'ansanda ta zo ta kwashe mu. Muka isa muka tarar da kofar gidanmu tamkar zai stage da jama'a. Haka muka kutsa muka isa. Idanuwan kowa ya yi jajur tabbacin an sha kuka an gaji. Baba Babba kuwa gabad'aya ya rikice baya um baya umum ya zama wani iri k'arfin imani ya hana shi ya shiga cikinmu ya yi ta rafsa ihu, don tabbas an masa mutuwa mai gigitarwa. Mami kuwa sosai take sowa da k'yar aka samu ta koma yin na sharb'e. Hankalinmu bai dawo ba sai yamma aka tafi asibiti wajen Yaya Sulaiman. A can muka tarar da Abida tana zaune duk ta fige ta lalace. Kasancewarta likita kuma ta yi aiki a wajen ya sanya ba'a shata mana layi wajen shiga wajensa ba. Jikinmu ya sake yin sanyi a lokacin da muka halin da yake ciki. Yana kwance bai san inda kansa yake ba. Yanzu haka sun tura shi asibitin K'ashi na dala. Don ya bugu sosai. Tashin hankalin da muke cikinsa k'warai ya tsananta. Ranar da aka yi sadaka uku aka tafi da Yaya Sulaiman asibitinn Dala cikin Kano. Cikin k'ankanin lokaci gabadaya aka gigita mana nutsuwa da walwalarmu gabadaya, don Baba Babba ma a kwance yake ana ta kara masa ruwa. Dukkan ahalinmu kowa ya bar inda yake ya taho gida. Daga Funtua kuwa aka d'unguma Kano nemawa Yaya Sulaiman da har lokacin ba'a san matsayin lafiyarsa ba, tunda asibitin dala ma sun ce sai an hada masa da ganin likitan kwakwalwa don ya bugu a kai. Ganin hakan Yaya Asad ya ce Farouk da Abida su shirya zasu tafi Germany ya ga likitoci a can, tunda a can ya yi karatu ya kuma yi aiki na shekaru zai samu kulawa ta mussaman. Wata guda yana asibitin cikin coma sannnan aka samu visar tafiyarsu. Gabadaya bama cikin nutsuwa sai dai su Yaya Asad sun koma wajen aikinsu. Kan dole muka hakura muka bi Baba da adduar rahama, aka mayar da hankali wajen neman lafiyar Yaya Sulaiman da a yanzu muke cikin tashin hankali ganinsa tamkar gawa. *Dafatan zaku gyra zama don yanzu ne zamu kutsa cikin danbarwar labarin. Ku nutsu sosai, ku bi sannu a hankali har zuwa inda zn karkare don kuwa yanzune abin da labarin yake tafi da shi zai fara.* [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Su Abida sun isa ƙasar Germany tare da Yaya Sulaiman, sun dai yi waya damu sun sanar damu isar su amma tun bayan nan ba mu sake ji daga gare su ba, ni kaina idan na k'ira wayar Abida ba na samu, da man Yaya Faruku ne ya kira ni a lokacin da suka sauka a k'asar. Su suna can mu kuma muna nan amma zullumi bai bar mu ba, mun san ce wa mun rasa Baba ƙarami ya tafi in da har abada ba zai dawo ba, amma zullumin da fargaban halin da Yaya Sulaiman ke ciki ke nurƙurkusan dukkanmu, kowa ka yi waya da shi jikinsa a sanyayaye ba karsaashi ba farinciki. Mami kusan ko da yaushe muka yi waya da ita cikin kuka take, haka muke ta kwantar mata da hankalin ce wa ta cigaba da addua in sha Allahu Yaya Sulaiman zai warke. Amma ita ga ni take yi kamar shima ɗin kamar Baba karami ne rasa shi za mu yi, ni kaina karfin hali na ke yi amma a yadda aka tafi da Yaya Sulaiman bai san wanda ke kansa ba kowa ma ya sare amma saboda kar na zama raunin Mami ya sa na ke daure zuciyata ina nuna mata da ikon Allah Yaya Sulaiman zai tashi da ƙafafunsa. "Umh Bilki, shima rasa shi zan yi, rasa shi za mu yi kamar yadda muka rasa Babanku." Kalaman Mami ke nan a duk lokacin da muka yi waya da ita shi ya sa in muka gama waya sai na zauna na ci kukana na ƙoshi ba mai lallashina. Domin Har da tausayinta ke nuk'urk'usata, mutuwar miji da rashin sanin makomar rayuwar d'a tashi guda ba k'aramin alamari ba ne. Baban Amra lokacin farkon faruwan lamarin ya kula da ni, ya tausaya mini,amma tunda aka fara nisa da mutuwar shike nan ya janye tausayawar. Kullum sukuku na ke, ga ciwon mutuwar mahaifi ga zullimin makomar lafiyar Yaya Sulaiman. Amma sai ya kalle ni ya ce "Ki k'arantawa kanki wannan damuwar fa duk ba mafita ba ce, hakuri da addu'a shi ne mafita. Allah ya jiƙan Baba shi kuma Sulaiman Allah ya tashi kafaɗun sa." Na sani gaskiya ya fada, kuma shi zuciyarsa d'aya yake fadin hakan. Amma ni so nake ace cikin taushi da laushi tare da kulawa zai dinga fada mini, ba wai ya fada ya cigaba da uzzirinsa ba. Tun da na dawo ba na cikin sukuni da walwala, hakan bai hana shi kallo ko charting ba, har ga Allah na ji zafin sa ko dai bai taya ni kuka ba ai ya taya ni alhinin halin da na ke ciki ni da zuciyata amma bawan Allah nan da wuri ya wartsake. Alhalin lokacin da nasa tsohon ya kwanta dama mun shafe fiye da wata ko talabijin bamu kunna ba. Ba Shi da sukunin yin kallo dan haka nima na haramta mana ni da yara dan taya shi jimami, amma abu ya zo kaina, na ga daban. Matsanancin mamakinsa kullum k'ara ara yi mini tsamari yake yi tare da tunanin mene matsalar ne? Basmae kullum sai ta kira Ni a waya tana sake kwantar mini da hankali. Duk bayan kwana biyu sai ta zo ta debe mini kewa tare da ba ni hakuri tabbas ita ɗin ƙawar alheri ce. Baba Babba duk dakiyarsa wannan lamarin ya raunana shi ya gaza, ko a waya na k'ira shi yadda na ke jin sa wani sanyi sanyi ba na jin daɗi, yana gida ba ya zuwa ko'ina lalle mutuwar Baba karami ta raunana kuzarinsa sosai Momi ce ma in muka yi waya da ita na ke jin karfin gwiwa domin ƙwarin da tabbaci ta ke bamu da cewa Yaya Sulaiman zai warke, mu ma kuma muna fatan haka in sha Allahu. Tun tafiyar su ba a sake jin su Yaya Faruƙu ba, sai bayan kwana goma sannan Yaya Asad ya kira Baba Babba ya sanar da shi halin da suke ciki, ashe shi suna magana da shi, mune suka rufe hanyar sadarwa da mu, shi kuma da ya ke da aljihunsa ake yin komai, sannan a matsayinsa na babba suna k'iransa suna kuma sanar da shi halin da ake ciki. Alhamdulillah likitoci sun yi gwaje-gwaje akan ƙwakwalwar Yaya Sulaiman jini ne ya taru a wani gefe in da aka gode ma Allah bai taɓa ƙwaƙwalwarsa ba, tuni an yi masa aiki sannan in da ya ke da karaya sun ɗora shi sun kuma ba da tabbacin a kowani lokaci zai iya farfaɗowa, a bakin Yaya Muneera na fara jin labarin sosai n samu sassaucin zullimin da nake ciki ba ma ni kaɗai ba dukkan mu wannan labarin ya wanke kaso mafi girma daga cikin damuwarmu. Sai bayan kwana biyu na samu mgana da Abida yadda na ji muryanta cikin sukuni ya sa na samu tabbacin labarin da muka samu gaskiya ne. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Maigado an gano matsalar Yaya Sulaiman na masa aiki a kansa sannan an masa na k'afa dazu! Abin da ta fara faɗa mini ke nan ko gaisawa ma ba mu yi ba, farinciki ya cika ni na yi hamdala a fili da sarari, mun ɗan jima muna hira, tana tambayana ya su Mami da mutanen gida? Na ce "kowa lafiya da godiyar Ubangiji, a baya dai muna cikin zullimi amma yanzu sai godiya. Ta tambayi yara, na ce su suna nan lafiya, mun ɗan jima muna hira ta ce mini za ta ɗan kwanta tun zuwan su ba ta samu barci ba. Ranar yini na yi murna da farinciki na kira Basma na faɗa mata itama sai murnar farinciki take yi. Baban Amra ma da rawan jiki na tare shi da labarin har sai da ya ɗan rumgume ni yana faɗin" Alhamdulillah." Nima na riƙe shi ina mai bayyana farincikina har fararen haƙorana suna bayyana tsabar murna. Yara ranar kaf sun san Mahma na cikin farinciki saboda yadda na yini tare da su. Mutuwar Baba karami ta gigitamu k'warai da gaske mussaman da ba jinya ya yi ba. Sai kuam aka had'a mana da kila wa Kala na rayuwar Sulaiman dole dukan sai ya yi mana yawa, ace ba Baba ƙarami sannan ba Yaya Sulaiman, tabbas zukata za su raunana sai dai da ya ke Ubangiji ne mai yin abin da ya so, idan ma hakan ne ya so ya faru sai dai mu yi haƙuri ba mu isa mu ja da hukuncin Ubangijinmu ba. Labarin farfaɗowar Yaya Sulaiman ya zo mana da kwana ashirin da isar su ƙasar Germany. Yaya Faruku ne da kansa ya kira ni ya sanar da ni, bayan shi Abida ma ta sanar da Ni an kawo shi ɗakin hutu amma dai yana ta barci ne ba su samu shiga wajen nasa ba. amma tabbas ya dawo hayyacinsa. Na samu K'warin guiwar tafi ganin Mami tunda an samu cigaba sosai . Hakan ya sa na ce wa Baban Amra gobe ina son zuwa gida bai hana ni ba. Washegari na tattara yara muka zo Funtua kamar na sa ni gida cike da matansu Yaya Faruku da yara ana ta barka da arzikin da aka samu. Baba Babba kuwa kofar gida ya fito aka tara masa almajirai ya riƙa rabon kuɗi sadaka domin godiya ga Ubangiji, mu kam mu a cikin gida kowa ka ga ni ya d'an samu k'warin jiki har Mami na ga ta d'an samu kuzari. Yaya Asad daga can lagos ya nemi visa sai dai kawai da suka kira mu Video call suka haɗa mu da Yaya Sulaiman muka gan shi a can kwatsam ba tare da kowa ya san tafiyarsa ba. Allahu Akbar Allah mai gagara misali, sai ga Yaya Sulaimam zaune a kan gadon majinyata ga rigarsu ta asibitin kafafunsa da ya samu karaya an ɗora shi kansa da wani bandeji, amma yana zaune yana mgana kamar ba shi ne aka kai shi rai ƙwaƙwai ba, kowa ya gaishe shi kuma ya amsa sannan ya kira sunan kowa alamun dai ya dawo hayyacins sosai a Allah abin godiya. Ni ina ganinsa sai kawai na ji kuka ya zo mini. Farha na jikina ta lafe. Abida ta leƙo da kanta tana kallona ina ta sharan ƙwalla, sai kawai ta kaɗa kai kafin ta ce" Sola ke wai me ya sa ba kya girma ne? Gaban ɗiyar ta ki, kike b'are baki kina kuka? Ina jin ta ce haka sai na sake fashe wa da kuka don gabad'aya tausayinsa ya yi mini k'awanya Bai san mahaifinsa ya rasu ba. Baba Babba ne ya kalle ni kafin ya ce" Bar kuka Maigado yi magana da ɗant'uwanki kin ji! Na gyaɗa masa kai, kafin na yi magana Yaya Sulaiman ya murmusa kafin ya ce" Bilkkina ba ga ni kin ganni ba? Ki daina kuka kin j! Kar ki saka Farha ta fara gata nan idanuwanta ya kawo ruwa." Sai da ya faɗa na juya ina kallon Farha ta kusa kukan itama. "Ya jikin ka Ya Sulaiman? "Na ji sauƙi Bilkina. Alhamudulillah mun gode ma Allah" Kallonsa kawai nake yi duk ya rame ya yi baƙi sai na tuna dr rasuwar Baba ƙarami kawai sai na sake fashewa da kuka kamae wata ƙaramar yarinya na ɗauka bai sani ba ashe ya sani sai ji na yi yana ce mini "Maigado ya ƙarin haƙurinmu!? Allah ya jiƙan Baba da gafara Allah ya kyautata makwancinsa" Gabaɗaya muka amsa da Amin Yaya Usman ne na ji yana faɗa mini Yaya Asad ne ya sanar da shi bayan ya isa a jiya. Su Abida ba su samu wannan ƙarfin zuciyan sanar da shi rasuwar Baba ƙarami ba. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Har wayar ta gama zagayawa hannun kowa ban daina kuka ba, Mami da Momi suna ƙwalla amma na farinciki ne Baba Babba faɗi yake yi" Allah na gode maka da ka karɓi ɗan'uwana, sannan ka bar mini ɗana Ubangiji na gode maka." Muryarsa ta karye mutuwar Baba ƙarami ta sake dawo mana sabuwa dama tana jika, ba ta gama fita ba, kuma har abada ba za ta fita ba, ba za mu manta ba, don da yanzu ina tunano abubuwan da suka faru amma ina jin kamar a yau ne muka rasa Baba ƙarami. Mutuwa tana da d'açi, sannan mutuwa mai tonon asiri mutuwar Baba ƙarami ce ta yi sillar ta tarwatsewar gidanmu, kaina na saka a cikin tafukan hannayena duka biyu na sake fashe wa da kuka ina jin wani irin nauyi a samam k'irjin irin nauyin da na riƙa ji lokacin da gidanmu ya hirgitse, Ubangiji na ke fata da roƙo ya daidaita kan ahalina Na cigaba da hakaito rayuwarmu washegari muka koma gidajenmu cikin sukuni da salama, sannan yanzu muna mgana da su sosai, barin ma Yaya Faruƙu yana yawan kirana saboda har gobe Yaya Faruƙu nawa ne, ina girmama karamcinsa a gare ni. Abida ma muna waya sosai sannan Yaya Sulaiman ma suna haɗa mu da shi, kuma jikinsa sai godiya yana ta samun sauƙi. Ya Asad sati ɗaya ya yi ya juyo zuwa gida Nigeria. Abida da Yaya Faruƙu za su cigaba da zama tare da shi har sai an sallame shi, Abida ko an ce ta dawo ba za ta yarda ta dawo ba. Baba Babba ya ce a barta ta zauna ta samu ladan jinyar mijinta, ban ɗauka haka Abida ke son Yayana ba sai a wannan lokacin aikin ta ta ajiye ta ta tafi jinyar Yaya Sulaiman kuma da aknsa ya faɗa mini da jikinta da zuciyarta take wahala da shi, kusan ita ke yi masa komai sai na ji tausayinta ya kama ni, shi da man Yaya Faruƙu Ladi farm ne kuma ba matsala akwai masu kula da wajen shi ya sa ba shi da wata matsala. Gabaɗayanmu mun koma bakin aikinmu tunda hankula sun kwanta ni kuma a gida na cigaba da karɓan aikin snacks sannan a bangaren aikina na W.H.O, mun cigaba da wayar waa da mata kai wajen kula da cikin da raino da kuma muhimmancin yin rigakafi ga yara bayan haihuwa. Ba tare da shawara da kowa ba Baba Baaba ya fara tattara dukkan wata dukiyarsu shi da ɗan'uwansa idan a baya ba wanda ya san shiga da fitar dukiyarsu, yanzu mutuwa za ta yi sillar fallasar komai. Idan a baya dukiyarsu tana haɗe ne a waje ɗaya ba wanda yasan tsakaninsu yanzu dalilin mutuwa yasa dole komai ya bayyana, ya shiga har bangarenmu ya yi magana da Mami da Ansari tun da Yaya Sulaiman baya kusa. Ya ce 'an fara tattara dukan abin da Baba ƙarami ya mutu ya bari idan an gama tattarawa lokacin su Yaya Sulaiman sun dawo za a zauna a raba gado domin a sauke masa nauyi, wannan maganar rabon gado, wannan gadon shine silar dambarwan da ta faru a gidanmu dambarwar da ta yi silar da na rasa Abida na rasa Ya Munnera. Bansan da mganar ba Mami ta kira ni da kanta a waya tana faɗa mini abin da yake faruwa. Sai na ji hawaye ya goce mini, yanzu shike nan mun rasa Baba ƙarami, har ga shi ana mganar rabon gado Allah sarki rayuwa Allah ya kyautata makwancinsa ranar yini na yi kamar marar lafiya. Baban Amrah yana can bangaren Hajiyarsu sai da ya shigo ne ya ganni zaune a falo na shiga zurfin tunani ban san ya shigo ba sai da na ji hannunsa a saman kafaɗata sannan na dawo hayyacina. "Lafiyarki kuwa? Ya faɗa yana kallona cikin kulawa, na sauke ajiyar zuciya idanuwana suka kawo ƙwallah, gidan da ma ya yi mini shuru yara sun tafi islamiya, Basma ce ta ce mini za ta shigo to ta kira ni ta ce ta fasa zuwa Baban Abdul ya yi baƙi sai dai zuwa gobe. "Na sha faɗa miki ki daina zurfafawa kanki tunani. So kike na rasa ki na shiga uku? Kalamansa na ƙarshe yasa sai da na yi dariya, kusa da ni ya zauna ya ɗan rumgumo ni da sigan lallashi yana ɗan buga bayana. "Komai mai wuce wa ne, Allah ya jiƙan Baba,. Shi kuma Yaya Sulaiman da ikon Allah sun kusa dawowa" Na gyaɗa masa kai cikin gamsuwa domin na yi lamo a jikinsa na kuma karɓi lallashinsa, ban san me yasa ba sai gani ina bashi labarin wayar mu da Mami, ina ƙoƙarin mai da hawayen da suka cika mini ƙwarmin idanuwana, amma ga mamakina sai da ya ɗago ni cikin nuna murnarsa kamar na ba shi labarin wani abin daɗi. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Ma sha Allah." Ya faɗa yana kallona, na yi kasaƙe ina kallon sa, faɗa masa fa na ke yi mutuwar mahaifina ta dawo mini sabuwa saboda an yi maganar rabon gado, amma yana kallona da farinciki a muryansa har ya bayyana a saman fuskarsa. "Gaskiya Baba Babba ya yi tunani kuma ya cika ɗanuwa na gari, gwara a raba a bawa kowa haƙƙinsa haka addini ya tanadar" Ni dai har ya gama magana ya tashi, ban sake wani motsi ba me ya sa yake murna? Saboda na ce za a raba mana gado, a kullum al'amuran Baban Amrah mamaki yake ba ni, ba ya gyarawa kuskuransa sai ma ƙoƙarin sake wasu yake yi, ajiyar zuciya na sauke amma abin da ya yi ya tsaya mini cak a zuciyata sai dai ban iya faɗa wa kowa ba sai washegari da Maman Abdul ta zo, ban yi mata wata magana ba, saboda na san ko na faɗa mata sharhi da magana kawai zan jawowa kaina ita da Abida har gobe ba sa iya boye adawarsu akan Baban Amrah shi yasa na yi shuru da bakina amma dai na ji daɗin zuwan ta mun yini tare muna hira kuma ta saka ni na saki jikina har na manta damuwata. Tun daga lokacin da na yi ma Baban Amrah maganar rabon gado ya dame ni bini-bini sai ya tambaye ni wai ya ake ciki ne har yanzu ba a kiramu ba? Tun ina mamakinsa har na daina na gama fahimtarsa kuɗin kawai yake hange, tun da ranar ma muna karyawa a gaban yara yake ce mini." Kai gaskiya za ku sha kuɗi Balki, ko gidan gonar nan kaɗai ai sai ta yi miliyan dubu da doriya." Kawai sai na saki baki ina kallonsa, au shi da man ya kwanta ne da gidan gona yana lissafin zan samu kuɗi ya sake komawa ya naɗe hannu ni kuma na sakin masa kuɗi ina masa hidima shi da ƴaƴansa da iyayensa, tun da na riga na sabar masa, a lokacin ban ba shi amsa ba sai da ya sake yi mini zancen kai tsaye na faɗa masa gaskiya. "Gidan gonar da kake mgana ba ta Baba ƙarami ba ce shi kaɗai, duka dukiyar tare ne da na Baba Babba. Ko mu y'ayansu bamu san yadda dukiyar su take ba." Tun daga nan na kashe masa baki amma duk da haka bai daina tambayata har yanzu Baba Babba bai kiramu ba?Ranar da daddare har mun kwanta ya sake yi mini mganar na harzuƙa na miƙe ina faɗin" Bai kiramu ba, don Allah Baban Amrah ka ƙyaleni da wannan maganar. Mu fa ba gado ba ne a gabanmu mutuwar mahaifinmu ta fi yi mana ɗaci, sannan lafiyar Yaya Sulaiman ta fi damunmu fiye da tunanin wani gado." Ganin na buɗe masa wuta ina masifa sai ya yi ƙasa da murya yana faɗin" Sorry ni ma ai mutuwar tafi damuna amma ina so na ga an sauke ma Baba ƙarami nauyi, ai Allah ne ya ce a raba ko Bilkis? Kuma ke matata ce duk abin da ya shafe ki ai ya shafe ni." Saboda haushinsa da ya kama ni ko magana ban yi masa ba na koma na kwanta na juya baya ya san ya yi laifi shi ya sa ya mirgino ta gefena yana kiran sunana, ta gefen kunina da dama yana yi mini raɗa, da ya ke ya iya kalamai sanyaya zuciya Idan ya so, tuni ya shawo kaina da azama muka tallafi juna sai dai kamar ko yaushe bai wani daɗe ba, ya matsa gefe ya fara barci ni kuma ya bar ni kwance cikin hawaye, na daɗe ina kallon shi ina tunanin wai haka sauran maza suke? Ba su damu da damuwar matansu ba sai kan su? Ban gane komai ba amma ba ni da yadda zan yi haka na ja jikina na shiga tiolet na yi wanka na tsarkake jikina na zo na sauya rigar barci na raɓe ta gefensa na kwanta ina tunanin makomar rayuwata, shike nan ni a haka zan ƙare, ba zan iya ɗorar da komai akan jin daɗin aure ba, a wajen ana mini kallon mace a cikin sahun matan da suka yi dacen samun gwarzon miji, kyakkwa Kuma marar hayaniys, ni kuma a cikin gida ni kaɗai na san inda ɗakina yake yi mini yoyo, na daɗe kafin barci ya kwashe ni cikin tunani da zullumi. Tun da muka yi haka da Baban Amrah ya kiyaye ni da maganar rabon gado, nima jin Mami ba ta sake yi mini maganar ba, sai na cire abin a raina sai kwanaki biyu tsakani Ansari ya kira ni a waya yana faɗa mini wai Baba Babba shiru har yanzu bai ce komai ba? Takaici ya kama ni amma sanin da na yi Ansari da Mami bakinsu ɗaya [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Lokacin da Upper ɗin ta fito da kansa ya shirya ya zo gidana, na yi mamakin ganinsa amma sai murna ya danne mammakina, na yi ta rawar jiki da shi, na rasa ina zan saka shi na ji daɗi, ga shi yara ba sa gida baban Amra ma baya nan ya shiga cikin gari. Na share hawaye a ɓoye saboda shi kadai ya ke damuwa da lamarina a yanzu. Ya Hamida da gaske take ta yanke alak'a da ni, ba ta k:irana ko na k'ira ta sai ta ga dama take ɗauka. Su Saddiqa ba kasafai muke mgana da su ba, Duk ta zuge su. Ya Sulaiman ɗin ne kaɗai na ke gani na ji daɗi, lokacin da ya damƙa mini upper ɗina ta aiki bansan ya aka yi narumgume shi ina fashewa da kukan dan nake ta danne shi ba. Murna da tausayin kaina suka dabaibaye ni. Ina kuka ina faɗin" Na gode sosai Ya Sulaiman, na gode Ubangiji ya yiwa rayuwarka albarka, ya tsare ka ya sanya albarka a dukiyaka da ya'yanmu, Allah ya jiƙan iyayenmu." Ya amsa da Amin kafin ya ce" Ba komai Bilkina ni dai fatana ki nutsu, ki yi haƙuri, ki rungumi mijinki da ƴaƴan ki, ki koyi juriya da yadda za ki iya tsayawa kanki ko da ba ki kowa a duniyar to ya zama kina da Allah kina da kanki! Sai na ji maganganunsa masu kama da yana barin wasiyya ne. Hankalina ya tashi kar ya zo shima mu rasa shi kamar yadda muka rasa Mami da Baba ƙarami. "Yayw Sulaiman waɗanan mganganun fa? Ina za ka je?" Na faɗa cikin damuwa da tashin hankali Sai ya yi saurin ce wa" Ba komai Bilkina, wata yar tafiya zan yi amma kar ki tayar da hankalinki, idan da rabo za mu sake haɗuwa." In jin ya ce haka na fara kuka ina faɗin" Na shiga uku Ya Sulaiman kai ma barinmu za ka yi! Don Allah kar ka tafi ka bar ni." Hannayena ya riƙe cikin nasa kafin ya ce" Na ce ki kwantar da hankalinki ba zan daɗe ba, zan dawo, ke dai kawai ki koyi dauriya da jarumta, komai zai wuce, kina da ƴaƴa da mijin da wata rana za su iya zama garkuwa gare ki" Duk yadda na so Ya Sulaiman ya faɗa mini k'udurinsa bai yi ba, ban dauka ganin k'arshe na yi masa idan a ce na san haka da ko za a mutu bazan bari ya bar gidan nan ba. Ganin yadda nake ta kuka yasa ya ɓata lokaci wajen lallashina har sai da ya ga hankalina ya kwanta. Har abinci sai da na yi masa kuma ya ci mun d'ade muna hira yana ta mini nasihohi yana ce mini na kula da rayuwa, na kuma saka ido sosai akan yara. Ni kam na gama tsorata da jawabansa ya yi mini fatan alheri da fatan nasara sannan ya ce zai tafi. Na ce ya ɗan jira su Farha sun kusa dawowa. Ya kalleni kafin ya ce" Farha kaɗai sauran yaran fa? Na yi shuru ban yi mgana ba. Ya numfasa ya ce "Ki daina danganta Farha da ni Bilkina, d'aya take da su Amra a wajena, ba tawa bace ta kice tun kafin ta zo duniya kowa ya tabbatar da cewa Farha taki ce don kuwa na fi Abida cancantar na ba ki ita". Na ba shi haƙuri ganin ransa ya ɓaci sai da na tabbatar da ya hakura sannan na sakoasa batun Abida tare da fatan ya dauke ta Su tafi inda zashi don na tabbatar hakane kadai zaisa hankalinsa ya nutsu. Ya girgiza kai ya ce "Bilkina ban saki Abida ba, amma matukar sai na nemi ta dawo gare ni to la shakka na haramtawa kaina ita. Bamu samu matsala da ita ba, ban mata komai ba, Baba da Yaya Asad suka zuba mata ido take yin yadda ta so, saboda kawai ba ni da Baba k'arami. Muryarsa ta karye. Ni kuwa kuka nake yi sosai don na gane ba k'aramin ciwo lamarin yake yi masa ba jarumta kawia yasa ciwo Bai kada slazzphi ba saboda tsananin damuwowin da suka yi masa k'awanya. Ya hadiye kukan dan ya so k'wace masa ya ce "Da ikon Allah sai na samu damar da zan tozarta Abida fiye da tozarcin nan da ta yi mini. Sai Allah ya ba ni dama na nunawa Asad iyakarsa. Saboda Yana da kud'i shiyasa ya shake Baba a maimakon ya tsaya ya daidaita komai a matsayinsa na babban wanmu" Na yi shiru don ba ni da bakin magana don na lura Yaya Sulaiman'zfishinsa akan Yaya Asad fiye ma da Baba Babba akan batunsa da Abida. Na dinga ba shi hak'uri har ya d'an nutsu sannan muka yi sallama har harabar gidan na raka shi muka yi sallama cike da kewa. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ganin ya ruɗe yana ta wasu surutai yasa na s lalubo jarumta na yi ta masa nasihan da jan hankalin cewa tunda mutuwar Mami ta zame masa wa'azi ka da ya karaya, ya yi haƙuri ya cigaba da harkokinsa kowa iya kwanakinsa zai yi a duniya ya ɗauka ita Mami kwananta ne ya ƙare, da irin kalaman da na yi amfani kenan na lallashi Ansari ya bar kuka ya samu natsuwa. "Allah ya jikan Mami da Baba ƙarami Allah ya sa sun huta." Ya faɗa cikin karaya, na amsa mishi da Amin ina mai ɗauke hawayen da suka zubo mini da yatsun hannuna. "Ya Sulaiman har yanzu ba labarin shi Ansari?? "Wallahi babu, na bincika duk in da ya kamata da wajen abokansa da suka yi karatu tare a Germany amsar duk iri ɗaya ce basu san in da yake ba sannan suma ba ya magana da su." Ansari ya amsa mini cikin damuwa a muryansa. "Shike nan. Idan yana raye Allah ya tsare shi a duk in da yake. Idan da rabon mu gana Allah ya haɗa fuskokinmu da alheri." Na faɗa ina jin kamar na fashe da kuka Ansari ya amsa da Amin mun daɗe muna tattaunawa kafin mu yi sallama bayan mun gama wayar na zauna a ɗaki ni kaɗai na ci kuka na ƙoshi sannan na faɗa bayi na wanke idanuwana, haka nake yi idan na tuna da yau ba Mami ba Baba ƙarami, sannan ba iyalan Baba Babba. Ga Ya Sulaiman ya yi nesa damu sai na ji ina kuka wanda banma san ina yi ba, ƙarfin zuciya ne da tasirin musulunci ke rike da ni amma matuƙa zuciyata da gangar jikina sun raunana, ƙarfin hali ne kawai da karɓar kaddara tunda rubutattaciya ce daga littafan kaddarar rayuwarmu, kuma cikar kowani musulmi karɓan kaddara mai kyau ko akasin ta. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi haka nan bawa yake zirga-zirgarsa na yau da kullum tunda akwai rai har da lafiya mun godewa Allah. Ba laifi ina samun ƙudi sosai tunda gidajen da na samu duk haya na saka, sannan ga sana'ata ta snack ta karɓu sosai da dukkan zuciyata da jikina nake yin aiki tuƙuri domin idan tuna maganar Ya Sulaiman ta ƙarshe a gare ni akan na zama jarumace na tsaya akan ƙafafuwana saboda ni uwa ce domin zama garkuwan ƴayana wata rana. Bana ko tsayawa jiran Baban Amrah domin ɗaukan laluranmu ta riga ta zame mini jiki komai ni nake yi, mantawa ma nake yi nauyin hakan na kan Baban Amrah ne, tun kuma da hakan ta faru ban sake komawa Funtua ba, saboda ko na je wajen wa zan je? Gida na can a kulle babu kowa shi yasa ko marmarin zuwa ban taɓa yi ba. Ansari da ya dawo ya zo kwanaki da ya shigo garin kan harkokinsa duk ya rame amma ba laifi tun da ya kwantar da hankalinsa ya fara ɗaukan dangana, ya sanar mini ya samu aikin amma an tura shi Maiduguri babban birnin jihar Borno. Jikina ya yi sanyi tare da zullimin yadda Ansari zai yi nisa Ga shi a lokacin garin Maiduguri na fama da ta'adin yan tada k'yar baya. Amma na daure na yi masa kyakkwar adduar alheri. Ya mini sallama akan gobe zai tafi. Tafiyar Ansari ya sake kassara ni don gani nake yi tamkar shima ya tafi kenan. Da k'yar na hak'ura na cire al'amarin a raina amma bansan me yasa nake ji a jikina ƴaƴana kad'ai suka rage mini. Shi yasa na rike aikina da sana'ata da muhimmanci don duk ƙokarina da wahalata sabo da su ne, domin na ingata musu rayuwa ko da wata rana bana tare da su. *BAYAN WATA SHIDA* Bayan watanni shida da tafiyar Ya Sulaiman, ba wanda ya sake jin labarinsa, yana raye ko ba ya raye ba wanda ya sani sai Ubangiji. Ni dai addu'ata kullum shi ne idan yana raye ubangiji ya karkato da hankalinsa gida idan kuma ta Allah ta kasanance da shi Ubangiji ya haɗa mu a darussalam. Ashe Abida ta haihu ban sani ba, kuma ba na tunanin wani a cikinmu ya san da batun haihuwar nan, nima Ya Faruƙu ne ya k'ira ni kwana uku da haihuwar ya sanar da ni, sai na ji abin kamar a mafarki tambayar kaina na ke yi dama Abida na da ciki ne? Mamaki da al'ajabi suka sake mamaye ni da jin ikon Allah! Yafaɗa mini namiji ta haifa da uwar da abin da aka haifa duk suna lafiya. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Duk da C.S aka yi maa Abidan a dalilin ba zata iya haihuwa da kanta ba, ban sani ba, sam bansan Abida na da cikin Ya Sulaiman ba wato shi ya sa da rasuwar Mami na ganta wani iri ashe lokacin ma tana cikin laulayi ne? Allah sarki! Kwalla ta zubo mini a dalilin na Kara fahimtar ya'yan Baba Babba gabaɗayansu sun rufe ni daga ganin status dinsu koma share lambata suka yi oho! Ya Faruƙu da na ke ganin yana yiwa zumunci kara bana ganin status dinsa Sai dai ina masa zaton bai share lambata ba, amma na gode masa domin ba dan shi bazan ji labarin haihuwar ba. zumunci ya riga da ya lalace gyaruwarsa zai zama wani abu ne mai wahalan gaske. Amma na dinga mamakin yadda Baba Babba bai fada mini ba don kuwa ni ban daina gaishe shi ba, a kai akai ina k'iransa a waya na masa gaisuwar juma'a tare da tambayar jikinsa da iyalinsa gabad'aya. Ni na kira su Saddiqa na faɗa musu haihuwarAbida suna ta mamaki, Ya Hamida ce sai da ta dama ta ɗaga kirana da nafaɗa mata haihuwan Abida ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Ta baya ta rago kenan. Ta yi nasaran koran shi daga k'asar gabaɗaya, sai ta zama uba da uwar abin da ta haifa." Daga haka ta kashe wayarta sai na sake kiranta. A fusace ta ɗauka tana faɗin" Wai lafiya kike ta kirana Bilki?" N tausasa harshe na a ce" ko za ta shirya mu je Abuja mu ga Abida da abin da ta haifa?" Kawai haka na fad'a Ya Hamida ta fara zagina ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, ta ce ita kam ba in da za ta je idan ni zan je Allah ya raka taki gona tunda ban san kishin kaina da na y'anuwana ba. "Ba haka ba ne Ya Hamida, kar ki manta ba saboda ba Abida za mu je ba. Saboda Ya Sulaiman ne." Ko saurarena ba ta yi ba ta sake katse wayarta tana faɗin sai kuma na yi, tun da na ji haka sai na zare ta a ciki a raina na kudiri niyyar ni kaɗai ma ya isa zan je na duba ta saboda zumunci da kuma Ya Sulaiman. Na kira Ansari mun yi magana ya ce shi Wallahi nauyi yake ji da ya raka ni amma na fara zuwa shima daga baya zai je, ko dai bai je ba magana ma mai daɗi sadaka ne na ji daɗin mgana da shi. Baban Amrah na dawowa na tare shi da maganar haihuwar Abida. "Wace ce kuma Abida?" Ya tambaye ni yana kallona, bai wani ba ni mamaki ba sanin dama ba ya son duk wata magana da ta danganci Abida yake yi ba. "Abida dai tawa da ka sani y'aruwata" Na ba shi amsa a takaice kuma a dake. Ya jinjina kai kafin ya ce" ikon Allah, dama tana da ciki ne? Na amsa masa da ce wa "ni ma ban sani ba sai da ta haihu." Tabe baki ya yi bai yi magana ba, ni kuma ganin haka saboda bana son mu sake wata mgana daga baya da sauri na ce" Ina so ka yi mini izini na je Abuja na duba su." Ya ɗaure fuska kafin ya ce" Me yasa za ki je?" "Saboda ya kamata! Na amsa mishi kai tsaye, tuna Ya Sulaiman da na yi yasa kawai sai na fara hawaye ina faɗin" Baban Amra ka yi mini izini na tafi, zan je ganin abin da aka haifawa Yaya Sulaiman wanda ba mu san ko yana raye ba, ni ina ji a jikina wataƙila ba ya raye, domin idan yana raye ba zai kai wannan wattanin bai neme ni ba, k'ila ma a inda ya je ya haɗu da tsautsayi na ajali." Na ƙarisa faɗa ina mai fashewa da kuka. Jikinsa ya yi sanyi ya taso zuwa gare ni ya rumgume ni yana lallashina. "Daina kuka, in sha Allahu Sulaiman yana raye kuma cikin ƙoshin lafiya." Ya furta hakan murya babu amo. Na ɗago daga kan k'irjinsa ina faɗin" To idan yana raye yana ina. Me ya sa har tsawon wannan lokacin bai neme mu ba? Na faɗa hawaye na sake kece mini! Shi ya share mini hawayen yana sake rumgume ni, a daran ya yi ta lallashina da kalamai sai ga shi na saki jikina tun ballanta ma da ya ce ya amince na je amma shi ba zai samu zuwa ba, za su je Zaria shi da Amrah su duba mai sunanta. Na ce masa sai na tafi da Faruk da Farha. Ya ce to sai mu tafi gabaɗaya idan muka duba Maman Zaria ni da sauran yaran mu ƙarisa Abuja. Da wannan shawaran muka tsaya washegari kasuwa na shiga na yo siyayyar kayan jarirai da su pampers kamar za a bude shago. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Ni kaina sai da na ga kayan sun yi yawa Abida kuma na siya mata super wax da leshi mai tsada da mayafinsu masu tsadar gaske, ko ba za ta amsa ba ni dai na sauke haƙƙi da nauyi a matsayina na uba tunda ina makwafin yaya Sulaiman ne, tunda ba inuwarsa a wajen kuma babu wanda zai maye gurbinsa sai ni shi ya sa ban ji na sare ba. Da na koma gida shi kan shi Baban Amrah da ya ga yawan kayan sai da ya yi magana, ni kuma na sake ba shi amsa da fadin "Abida ce ta haihu sannan d'an Ya Sulaiman ne, komai zan yi musu ban biyasu girman ƙaunar da suka nuna mini ba". Jin na faɗi haka yasa sai ya yi shuru bai yi mini sharhin nasa ba". Washegari tun safe muka d'au hanya, azahar muna Zaria salla kawai muka yi sai abinci da muka ci, ya kai mu tasha muka shiga mota cikin sa'a gurbin mutum biyu ya rage dan haka muka biya wajen ni da yara. Nan da nan muka kama hanyar Abuja ni da su Faruk, muka bar Amra da Babanta a Zaria sai washegari za su koma Katsina. Ni kuma dama na ce masa zamu dan yi kwanaki, daɗin da na ji, jiya mun samu hutun mid semester. Sai da muka sauka a garin Abuja sannan na kira wayar Ya Faruku na ci sa'a ya daga k'iran ya sha mamaki da na ce masa ga ni a Abuja, addreshin gidan Baba Babba zai ba ni. Ya shanye mamakinsa, ya turo mini adreshin, mai taxi ɗin da na tare na nuna masa ya ce ya san wajen tunda fitattaciyar anguwace ta masu hali. Danƙareren gida Ya Asad ya saka iyayensa a ciki, har sai da na saki baki ina kallon gida. Ba kowa a gidan daga Baba Babba sai Momi sai Abida, sai ma'aikata. Kawai suka ganmu kwatsam kamar daga sama, tunda da na isa bakin gate din gidan Yaya Farouk na k'ira ya yiwa maigadin magana ya bude mana bayan ya kinkimi kayana. Ya ce mu shigo zai dawo ya shigo mini da sauran kayan. Momi ce a falo tare da Baba Babba. Dukkansu bakinsu ya kasa rufuwa na murna da mamaki. Momi ta miƙe tana faɗin" Lale marhaban Maigado ke ce tafe?" Ina murmushin jin daɗi na ce" Ni ce Momi." Su Farha suka nufe ta ta tarbesu cikin farinciki. Ni kuwa gaban Baba Babba na ƙarisa na rusuna ina gaishe shi. "Barka da zuwa, lale da Bilkisu yayar Abida! Nan da nan idanuwana suka kawo ruwa domin na tuna shekarun da suka shud'e a lokacin da muke hade, muke rayuwa cikin jin dadi da kaunar juna. Kaina na kasa da rawar murya na ce " Sannu Baba mun same ku lafiya?" Ya amsa da lafiya k'alau yana tambayata sauran yaran da sauran ƴan uwana duk na amsa mishi da muna nan lafiya. 'To Alhamdulillah sannu mai gado. Allah ya yiwa rayuwarki albarka.' Na amsa da "Amin" K'wallah na taruwa a kwarmin idanuwana farinciki da alhini sun kewaye ni kamar na fashe da kuka haka nake ji. 'Sai kika ji yar uwar taki ta haihu ko?' Baba Babba ya katse mini tunani. "Ban ji ba Baba. Sai shekaranjiya ne Ya Faruku ya kira ni ya faɗa mini." Ya jinjina kai kafin ya ce" Da ya ke sai jiya aka sallamo ta daga asibiti wataƙila ba ta samu natsuwar kiran ki ba ne maigado " Ina kallon Baba Babba a cikin zuciyata sai ayyana har yau Abida ce raunin Baba. "Maigado har yanzu baku samu labarin Sulaiman ba? "E, Baba bamu samu labarinsa ba har yanzu." Ya jinjina kai kafin ya ce" Ubangiji Allah ya bayyana shi cikin aminci" Na amsa da Amin kasa kasa sai falon ya yi shuru, tunda Momi ta ja yaran zuwa ciki, ta gefen ido nake k'arewa Baba Babba kallo ya warware sai dai bai mayar da jikinsa ba haka nan tsufa sosai a tare da shi alamun har lokacin zuciyarsa bata nutsu sosai ba. Mamakin Baba Babba nake yi a kullum shin wanne dalilin ne ya sanya ya zubawa Abida ido ta zauna a gida har hakan ya taimaka wajen b'acewar Yaya Sulaiman? Duk da dai nasan itace rauninsa, amma duk da haka ina mamakin yadda ya iya zuba ido Abida take zaune a gabansa, idan a lokacin ba shi da lafiya ai daga baya ya ji sauƙi ya kamata ya mayar da Abida d'akin mijinta tunda bai sake ta ba. Bai kuma yi laifin da za'a kashe masa aure ba. "Maigado tashi ki shiga wajen y'aruwar ta ki, ku gaisa ki yi salla ki ci abinci ki huta." [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Muryarsa ta katse mini tunanina, na amsa masa da to na tashi na shiga dama kayan da na zo da su tuni Momi ta shigar mini da su. A bedroom ɗin farko na iske Momi da yara ta zuba musu abinci suna ta mata hira tana dariya. Nan na fara shiga na duk'a har k'asa na sake gaishe ta. "Lafiya lau Maigado, ya mutanen gidan ina me gidanki da amaryar Alhaji?" Na amsa mata da duk suna lafiya, mun barta a Zaria tare da Babanta. Na daɗe a wajenta muna hira itama sai da ta tambaye ni labarin Ya Sulaiman na ce mata ba wani labari cikin damuwa ta ce "Oh Allah ka bayyana wannan yaron alfarmar Annabi." Na amsa mata da Amin. "Za ki fara yin salla ne ko sai kin ƙarisa wajen y'aruwar ta ki? Na ce bari na je can wajenta sai na yi, ita ta nuna mini dakin da Abida take ciki na shiga ciki na iske ta zaune a gefen gado tana shan tea ga Baby a cikin showel a gefenta yadda ta kalle ni na gane ba zan wani samu karbuwa daga gareta ba. Ba ta yi mini mgana ba tun bayan da na yi sallama ta amsa mayafin jikina na yaye ina faɗin" Sannu "Abida." Kai tsaye da muryata cikin dakewa ta ce" Yauwa Bilki" Na kalle ta itama ta kalle ni, hawaye suka kawo mini amma ban bari sun zubo ba, itama ina ganin rauni a cikin idanuwanta sai dai ta yi saurin kauda kanta daga barin kallona. Ganin haka yasa na ƙarisa wajen jariri na ɗauko shi zuwa jikina a gefen gadon na zauna, ina mai kallon yaron sai da na yi kabbara a cikin zuciyata yaron nan kamar ni ce na haife shi tsabar kammanina da ya debo, ni kuwa dama kaf ɗakinmu na fi kama da Ya Sulaiman hawayen da nake tarewa suka zubo har saman kumatun jaririn na saka hannu na share masa sai barci yake yi. "Kai ma mu ka biyo?" Na faɗa murya babu amo kamar shi da Farha a bayyane ba tantama, wannan jinin Ya Sulaiman ne! Da sauri na rungume jaririn ina mai fashewa da kuka har yana fidda sauti. Abida na gefe tana kallona amma ba ta yi mini magana ba sai da na sha kuka na k'oshi na share hawayena amma ina ƙankame da jaririn a hannuna zaman sama da mintina ashirin ba mu tanka ma juna ba sai ita Abidan ce da ta gaji da kanta ta kalle ni tana faɗin. "Ina yaran ko ke kaɗai kika zo?" Ina shirin bata amsa sai ga su Farha Momi ta kawo su Faruk ya nufi Abida yana ganinta, ta rike shi a jikinta tana faɗin" Yayanmu akwai ƙauna ashe baka manta da ni ba? Ta faɗa tana shafa kumatunsa shi kuma yana dariya. Jaririn da yake hannuna ta nuna masa tana faɗin" Je ka kaga k'aninka? Kana son shi? Da sauri ya ce" E Ammi ina son shi." Don kaf yarana Ammi suke kiran Abida, wajena ya nufo yana faɗin na ba shi jaririn na ce ba zan ba shi ba Momi ta ce ya zauna sai na rike masa haka ko aka yi jikin shi har rawa yake yi. "Mahmah da shi za mu tafi? Ina shafa kan shi na ce" A a Faruk a wajen Ammi za mu bar shi." Abida kuma na ta kallon Farha itama tana ta kallonta kamar ta gane ta, kamar ba ta gane ta ba, sai ta miƙa mata hannu tana faɗin"Farha zo mu gaisa." Ta mik'a mata hannu Farha ta tafi zuwa gare ta, ta riƙe ta ta daɗe tana kallonta kafin ta shafa kumatunta tana faɗin" Farhan Bilki ta girma! ✍️ [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: *Bojuwa herbs* *Oder your kayan mata for women of class* *Our products are healthy and original*. *Tested and trusted*. *Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta Ki*. *Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini later domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zata iya zuba kudi ta saro masu daraja irinsu ba*. *Duk wadda ta ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi* *Just DM for your order @08033773332*. Na kalle ta ina mai murmusawa, duk yadda soyayyar ɗa da uwa take Abida ta yi jarumtar bar mini abin da ta haifa shi yasa nake yi mata uzziri don ta nuna mini zahirin soyayyar da ta shafe dukkan iyashegenta a zuciyata. Nan duniya na shaida Abida na cikin jerin masoyana na haƙika. Duk da tana kawaici amma yanayin yadda take kallon Farha zaka san akwai soyayya irin ta uwa a idanuwan Abida. Ta sake tambayar Farha da 'Ina yayarku?' Farha ta ce "Mun barsu a Zaria tare da Dady". Ganin har biyar ta gota ya sa na mike na kwantar da jaririn a saman gado, ganin na mike yasa Farha ta saki hannun Abida ta nufo ni tana faɗin" Mahma ina za ki?" Ina kallonta na ce" Ba inda zan je Farha salla zan yi " Ta sake ni jin ba tafiya zan yi ba. "Je ki zauna wajen Ammmi ku k [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Bilki ta fara dariya a zuciyanta ta ce yaushe rabon duniya da ayyaraye? A fili kuma sai ta ce' Ai ni na gama, yanzu lokacin amarya ne ta yi ta zazzaga masa yara.". Domin ta fahimci ya fi ɗokin haihuwar daga bangaren amarya tun da yadda yake b'arin jiki kan cikin nan ko a lokacin da ta yi cikin Amrah ba ta ga ya yi wannan ba'rin jikin ba. A yanayin da ta ke ciki bata ma fatan ta sake haihuwa to ta ina ma ta ga mijin ballanta har ta sake samun ciki? Mutumin da yanzu sun fi wata biyu bai neme ta ba tun samuwar cikin matarsa, ranar kwanan ta ma yanzu ba ta ganewa domin a sati bai wuce sau biyu yake kwana a dakinta ba shima a tafe yake kwana haurawa sama yana duba yar gwal, asuba na yi idan ya fita ba ya sake dawowa. Gabadaya ta rasa ma ina tsarin gidan yake kawia tana cigaba da binsa da ido ne Amma akwai ranar kin dillanci. Yana ta karakaina a kanta, haka ƴan'uwansa ma kullun cikin zuwa gidan suke da sunan duba amarya. Haka nan itama Hawwan k'annenta biyu sun zo daga Kaduna sun fi sati sannan suka tafi, ita dai sai dai ta ga ana shiga ana fita. Wanda ya shigo wajenta su gaisa wanda bai neme ta ba, ta yi kamar bata san ma ya zo gidan ba cikin irin rayuwar da take ciki ke nan. Shi kan shi maigidan tamkar wanda aka yi musu farraku abin kullum hauhawa yake yi, ta kuma tabbatar ba wani farraku kawai sabbin bita yake mata cikin littafin kitabur ra'asi. Dan haka bata jin zafi domin ƴan'uwansa sun nuna rashin kulawa a kanta. Ba ta ɗorawa kanta damuwarsu a zuciyarta ba. Ta tabbatar wulak'ancin Baban Amra yafi jan kaso mai yawa na ciwon damuwar da ya kamata fiye da kason damuwar abin da ya faru cikin ahalinta. Tunda tun kafin ya yi aure yake nausa mata bak'in ciki, yanzu da ya yi aure tozarta ta yake yi ta hanyar fifita yarinyar da bata wuce ta zo a mai yi mata hidimar gida tana biyanta ba. Ana cikin haka semister ta yi nisa har an yi gwaji, sai ga Sahal ya zo yana yi mata magana, akan darasin da ta ke daukar su Amarya. Wai ta yi musu gwajin(test )kuma ya ga ta bata karamin maki 6 a cikin 20 me take nufi da hakan?" Ya fada yana wurga mata takardan gwajin a jikinta. Lokacin tana cikin ɗakinta tana duba wasu takardu ne na makaranta ya shigo yana yi mata wannan jawabin. Ko ɗagowa ma ba ta yi ba, ta cigaba da duba takardun hannunta. Idan shi ba adali ba ne to kar ya yi tunanin kowa ma irin sa ne, wato tunda tana matarsa ta bata maki 20/20 saboda shi, lalle Sahal ba shi da kunya to ai bai tsinana mata komai na abin arziki ba tun bayan auransa ballatana yarinyar ta ci darajarsa. "Magana fa na ke yi miki kin yi mini banza?" Ya fada a fusace Bilki ba ta son hayaniya shi ya sa ta dakata da abin da take yi ta dago tana kallon sa. "Akan me ka ke magana? Ta tambaya cikin nuna kamar ba ta gane in da ya dosa, duk bai sa ya fahimci ba ta da lokacinsa ba sai ma ya sunkuya k'asa ya dauko takardar yana nuna mata. "Kin kyauta ke nan abin da kika yi Bilkisu?" "Me na yi Baban Amrah? Itama ta tare shi da sauri. "Au ba ma kin san laifin da kika yi ba ko?" Ya fada cikin harzuƙa. "Ban sani ba, idan na sani ai ba zan tsaya ina tambaya ba." Ya mika mata takardan yana fadin" Duba ki ga ni." Ta karba ta duba sannan ta kalle shi tana fadin" Wannan kamar darasina a ina ka samu?" Ta fada har tana bayyana mamakinta. Baki ya saki yana kallon Bilki tana nufin ba ta san ko takardar wace ce ba? "Duba sunan? "Hawwa Hamza! Bilki ta karanta a bayyane sannan ta mayar da fuskarta gare shi ta ce "Wace ce ita? " Ta tambaya cikin mamakin. Sahal ya yi wani sororo, wuyansa ya lamgwabe kafin ya ce" Kina nufin ba ki ma san ta ba? "Ban gano wace ce ba, kasan daliban nawa suna da yawa ba zan iya rik'e sunan kowa ba." Ta fada tana mik'a masa takardar hannunta amma ya kasa karɓa saboda mamakinta. Ajiye masa ta yi a gefen gado ta d'au takardunta ta cigaba da dubawa. "Kina nufin ba ki san sunan matata ba Bilki? Amma dai ai kinsan kin fara daukarsu darasi?" [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Don Allah fa?" To ban ma taɓa lura ba, kuma ita ta fada maka ina daukarsu? Idan na shiga ajin bana tsayawa tantancesu abin da nake yi basu darasi da tabbatar da sun fahimcin darasin da kyau. Bayan haka bana sanin komai akansu illah zakwakuran cikinsu, Wanda hazakarsu ta wuce gigiggiwarsu. Bana ji itama ta dauke ni malamarta mai daraja don ban tab'a ganinta a aji ko a makaranta ta yi mini gaisuwar da zan shaida ina koyar da ita ba" Ta fada tana kallon sa. Kafin ta sake ce wa" Ka fada mata ta mai da hankali gaskiya, ta rage rawar kai a tsakanin kawaye if not , ba zata kai labari ba." Sahal ya kai k'ololuwar fusata wato da gangan Bilki ta yi wannan muguntar? "Ke nan da gangan kika kayar da ita a gwajin ko? "Allah ya tsare ni, abin da ta rubuta shi ta samu." Bilki ta amsa masa, a ɗan zafafe domin ita kam ta gaji da wannan ihun da ya ke yi mata a saman kanta. "Ko da ba ta ci ba ai darajata sai ki bata maki mai d'an dama Bili" Ya fada yana wani rage murya har da fadin sunan da rabon da ya ambace ta da shi ta manta. Ta kalle shi shekeke kafin ta ce" Ai ba na haka, duk inda na ke adalci na ke yi ba zalunci ba, bana k'arawa mutum hak'kin da ba na shi ba." Sai jikinsa ya yi sanyi domin sai ya ji kamar shagube Bilki ta yi masa. "To ki d'an k'ara mata ko zuwa goma ne ga ta can tana kuka." Haushi ya kama Bilki ta mike ko magana ba ta yi masa ba ta shige tiolet ta bar shi nan da ya gaji ne da tsayuwa ya fice sai da ta ji fitarsa sannan ta fito amma ta kwana cikin mamakin Baban Amrah, da ba ya jin kunyar aikata duk abin da ya ga dama. Ban da k'arfin hali har ya zo ya same ta da wannan maganar? A a ba kuka take yi ba, ta yi na jini ma, yarinyar sam bata mayar da hankali wajen karatu kwakwalwarta ba ta ja, sannan kusan kullum sai ta ga tana nunawa mutane ita suna zundenta. Bata taɓa nuna ta gane ba bare ta tanka a bata rashin gaskiya. Shine kuma ta k'i yin karatu, sai kuma ita dan tana tsoron kada ace ta yiwa kishiyarta mugunta sai ta k'ara mata makin din da bata cancance shi ba? Wato ta turo shi ne ya yi mata dole shi kuma ba tunanin komai ya zo zai yi mata tilas. Ta dade tana mamakinsa har Basma sai da ta bawa labari da suka yi waya. Basma ta buga wani zagin Katsinawa sai da Balki ta kashe waya tana dariya. Ashe zance bai k'are ba da aka yi jarabawa ma sai da ya zo ya same ta akan ta bawa yarinya sakamako mai kyau ta ce to babu musu illah iyaka ta kud'iri ajiyar ba zata taimake ta ba, haka nan ba zata danneta ba. Ai kuwa sakamako na fitowa Hawwah ta samu F a darussa biyu ciki har da wanda Bilki take daukarsu wato pharmacology. Sannan sauran ta haye ne irin da k'yar din nan dan haka gabad'aya GDP dinta ya yi k'asa matuƙa da gaske. Ta dinga kuka sosai tun a hanya yake rararrashinta tare da cewa yasan tana da kokari lififin cikine ya hanata hayewa dan haka ta kwantar da hankalinta yana tare da ita kuma zai yi kokari komai ya daidaita mata. Cikin rishin kuka ta ce "Ban ci na wacce kake da iko da ita ba sai na wani ne za'a gyara mini? Ni Wallahi ka bude mata k'wanji ta gyara mini sakamakona, na gane bak'inciki take yi da ni tunda ta ga ina da ciki shike nan ta daura aniyar sai ta kai ni k'asa. Duk ajin ni da kawayena kawai ta kayar har wanda muka fi su k'ok'ari duk ta ciccibasu sun haye amma ban da ni da duk wanda nake mu'amala da su." Suna dawowa gida kaitsaye wajen Bilki ya dira yana neman ba'asin kayar da Hawwa da ta yi. Bilki da bata son jan maganar ta mik'e ta ce "abin da ta yi ne ta ga ni". [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: Rikici har wajen Hajiya, itama wai Hajiya kamar ta manta da zaman da suka yi tana goyon bayan Sahal da matarsa. "Haba Balki abu duk na gida, ai ko don darajar Sahal kya bari ta wuce tunda kina da damar yin haka" Mamaki ya hana ta magana sai da Hajiya ta ce wai idan ta isa da ita to ta gyarawa abokiyar zamanta jarabawarta. "Kin ga ciki ne da ita har ya fara girma damuwa kadan zai saka a samu matsala." Bilki ta gyara zama tana kallon Hajiya ido cikin ido kafin ta ce" Ai ba ni da wannan ikon Hajiya na riga na bawa makaranta duka sakamakon jarabawar komai na hannunsu yanzu, ita ce za ta gyara carryover ɗin ta wata shekaran amma ni ba ni da wani taimakon da zan iya yi mata." Hajiya ba kunya tafara fadin" Haka za ki ce Bilki? Ashe ba kamar uwa kika dauke ni ba?" "Uwa kuwa mai k'ima na d'auke ki Hajiya. Amma hakan ba zai saka na ci amanar aikina ba. Ko shi Baban Amra nake koyarwa ya kin yi karatu to ba zan ba shi makin da bai cancance shi ba. Don a lahira ni kad'ai zan kwashi zunubin son zuciyata " Hajiya ta kasa magana Balki ta gama daure ta da maganganu da haka maganata da mutu mussaman da k'anin Sahal din ya ce wa Hajiya ba maganar suna auren miji d'aya wannan daban, bangaren malama da daliba daban idan ta yi abu mai kyau za ta ga ni. Babu adalci a tilastawa Bilki ta ci amanar aikinta, da haka zance ya k'are ba ta san yadda ya k'are da mai kuka ba. Kan dole Hawwa ta gaji ta hakura tunda ba ta samu mafit ba wato tunda suna auren miji daya bari ta kwanta a gida ta k'i karatu, tana jiran ta wuce a banza, ba mutuncinta take ga ni ba, bare ta taimaka ta cicciba ta, tana ganin yadda take hada kai da kawayenta suna gulmarta suna zundenta. Sai da ta zo making ta tarar duk yan group din nasu basa wani ja. Cikin Hawwa ya fito ana gani sosai, tuni ta fara zuwa awo a bakin Alti take ji domin akwai wata rana da Sahal ya sakata ta rakata shi zai kaita sai kuma aka kira shi daga wajen aiki. Ba domin Alti ba, ba ma za ta san wattanin cikin ba ta ga dai ya girma tun da har ya fara turowa a riga sosai. Ba ruwanta da harkar da ba a saka ta ba, shi yasa ta zauna lafiya in da ta sake godewa Allah warkewarta daga cutar damuwa yanzu ba ta shan magani, sai na hawan jini kawai domin ya kamata, shi ya sa take kiyayewa sannan tana shan mgani. Ta riga ta kama kanta da sha'anin gidan gabadaya ba ta maida kai akan wasu abubuwan, shi yasa ko wani abu ya faru a gidan sai dai ta ji a bakin yara ko bakin Alawiyya to yau ma tana dawowa daga aiki ta yi yamma a cikin makaranta. Amrah ke faɗa mata Abban su ya siyo su dankali da doya bai kawo musu ba duk an haura da kayan zuwa saman Anty. Dama tana son ta samu damar da zata bata labarin abin da ta jiyo kwanakin baya dan haka duk Amra sai ta had'a ta faɗawa uwarta abin da ta ji Anty na faɗawa Dady, akan batun cefane da mota da kuma super wax. Wato yanzu shine ya yo mata cefane irin nata da take ga ni tunda garar da aka kawota da ita ta k'are. Lamarin ya daurewa Bilki kai, har yana da kudin siyan su doya da dankali da kayan miya daga Jos shi ne ita bai taɓa yi siyo mata ba! Tunda ya yi aure ya ce kowa ta yi girkinta ba zata iya tuna abin naira biyar da Baban Amrah ya siya musu na kayan amfanin gida ba. Amma tasan ya kawo mata k'aramin buhun shinkafa da katon din taliya da man gyada 5litr, wanda cikin garar Hawwa ne. Ba zata iya tuna me ya kawo mata ba bayan wannan. Ba ta yadda da maganar Amrah ba sai da ta tambayi Alti itama ta bata tabbacin ta ga sadda yake hawa da su har da ledar kayan tea ta ga ni. Shi yake siyawa amaryarsa ita kuma bangarenta idan ba zata siya ba sai dai su hakura da shan tea din, shi yasa ba ta jiransa sannan ba ta tambayarsa idan tana da kudi siyan abin da take so kawai take yi. Abin ya dame ta amma ta kud'iri niyar sai ta yi masa magana, ranar ko ya shigo d'akinta zai kwana kamar yadda ya saba sai dare ya tsala ya yo shirin barcinsa daga can yake shigo mata. Har ya kwanta ta ce ya tashi zasu yi magana ya fara faɗan sai da ta ga zai kwanta sannan za ta ce za ta yi masa magana. Ta hakurkurtar da zuciyarta ta ce "maganar ba za ta daɗe ba sannan fa ya tashi ya zauna. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Baban Amrah kana yin wasu abubuwa da ban gane musu a cikin gidan nan ba.' A hassale ya ce" Kamar na me fa? " "Kamar na yadda kake tafiyar da mu tsakanin ni da yaranka da amaryarka mu ba ka yi mana cefane, tunda ka yi aure sisi na dawainiyar abincin bangarena ba ka bani ba, duk ni ce nake yi, yanzu fa ba da ba ne Allah ya rufa maka asiri dama saboda ba ka da shi ne nake yi, na dauka yanzu za ka yi tunanin karbar ragamar da Ubangiji ya dora maka, amma sai na ga ba haka ba. Ita kana yi mata cefane ni kuma ko oho ni da yaran ka. Ai ya kama ta ka daidaita bisa adalci na yadda ko wanne magidanci yake yi. Kuma ni dai a sanina a farkon aurenmu kai adali ne ba abin da baka yi a gidanka na bajinta ma amma yanzu ka sauya mini gabadaya Baban Amrah! Ta fada cikin taushin harshe ainun. Kai tsaye ya ce" Kin taɓa ce mini baku da wani abu ne kika ga ban kawo ba Bilki? Ya k'ura mata ido yana kallonta sosai. "Ban gane ban taba fada maka ba. A matsayin ka na megida ai ya dace kasan duka hakkin da yake rataye a wuyanka. Ba bukatar a tunasar da kai." Ta fada kaitsaye don ta fara harzuk'a. Ya jinjina kai kafin ya ce" To ai ganin ba kya magana shi ya sanya na dauka kina da komai ne. Hawwa kuma tana fada mini abu kaza ya kusa k'arewa tun ma kafin ya k'are shi yasa kika ga ina siya mata, ke ma idan kin koyi yin hakan zan siya miki ai hakan ba matsala ba ne " Baki bude Bilki take kallonsa kafin ta samu zarafin magana ya cigaba da fadin" Duk abubuwan da kike yi ke kika saka kan ki. Ni ban tab'a rokon ki alfarmar ki yi ba, saboda haka ba ki da ikon magana. Ko lokacin da ba ni da aiki, ke da kanki kika kika fara abubuwa kan ki tsaye ban roke ki ba, bayan na samu aiki na ga kin cigaba daga inda kika tsaya, kin ga ita ta tasan nine zan bata don bata da sana'ar da zata nuna mini bata buk'atar hidimata sannan ba ma'aikaciyar gwamnati ba ce. Ke kuwa fa?" Kalamansa sun daki Bilki k'warai da gaske ta kasa magana saboda mamaki. "So kar ki zargi kowa a kan wannan abun. Ki fara tuhumar kan ki." Daga haka ya juya ya yi kwanciyarsa ya bar ta, tana binsa da kallon mamaki da tu'ajjibi. Wato shi Sahal ya mayar da ita wata shashasha, kidahuma kuma sakarya, ba ta sani ba. Sake kiran sunan shi ta yi yana daga kwancen ya katse ta da fadin" iya gaskiyata na fada miki. Ki bar ni na yi barci don Allah." Hawaye suka kawo mata amma ba ta barsu sun zuba ba. Sai ta jinjina kai kafin ta ce" Shi ke nan na gode. Zan gyara a gaba." "Better." Ya amsa mata yana daga kwance, ranar kwana ta yi cikin takaici kuma tun daga ranar ta ce an yi an gama daidai da ruwan sha idan babu ba zata sake saka ko sisinta a cikin cefanen gidansa ba. Ko sati ba a yi ba indomie ɗin yara da kwai tare da lemun da suke tafiya makaranta suka rage sauara na kwanaki biyu su k'are. Tunda ya ce ba a sanar da shi, shiyasa baya siya. Sai ta fad'a masa ranar da ya waye a wajenta da safe, yana karyawa. "Ki ranta cikin kudinki, a siyo komai, zan ba ki anan gaba. Yanzu duka kudaden hannuna na bawa Hawwa zata fara rage siyayyar haihuwa tunda ana saka rai karshen next month ne haihuwar ". Bilki ta saki baki tana kallonsa saboda yanzu Sahal ya daina bata mamaki al ajabi da tsoro yake bata. "Ban gane ba?" "Yadda dai kika ji?" "Ban gane ka bata ta yi siyayyar kayan haihuwa ba! Haihuwar yau ne ko gobe? Saboda haka so kake yi mu zauna da yunwa saboda hidimar haihuwa?" Bilki ta tambaye shi cikin karaya da lamari. Daga faɗin haka ya juyo a fusace kamar zai kai mata mari. "Dakata Bilki ni fa na gaji da hallayarki a cikin gidan nan tunda kika ga na yi auren nan bakincikinki da hassadarki suka taso a kaina. Na fada miki gaskiyata ko so kike yi na zauna har sai an yi haihuwar sannan zan tanadi abin da ya kamata! Idan kina da adalci ai kema haka nake yi miki, amma saboda son zuciya har kina da bakin magana" Bilki ta saki baki da hanci amma ta kasa magana. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "Kin ce abu ya kare na ce ki ranta, ki siya zan baki shima duk bai yi miki ba, kina so ki tsiro da wata magana. Ina ce da ke kike siya? Me ya sa duk ba ki damu ba sai yanzu da aka kawo wata? Ki kiyaye ni kar ki kure ni na gaji da korafinki fa". Yana gama faɗin haka ya wuce fauu ya sauka kasa, ya bar Balki da ciwon zuciya da kyar ta iya rarrafawa ta sauko ta koma dakinta sai da ta yi kuka. Idan ta ce ba ta gaji da Sahalu da gidansa ba ta yi karya. Ta gaji tana bukatar natsuwar zuciya da na gangar jiki. Amma matukar tana gidan nan to ba za ta samu haka ba. Yini ta yi ranta a bace, ba ta da shiga makaranta kwance ta yini tana tunanin rayuwarta da ba komai cikinta sai bacin rai da takaici, ba ta dauka a daran Baban Amrah zai neme ta ba, tunda yadda suka rabu da safe sai ga shi ya zo yana rage mata murya. Shi kan shi bayan fitarsa da safe yana tafe a mota sai ya ji duk bai kyauta ba, bai kamata ya fadawa Bilki maganganu masu zafi haka ba, shi yasa yana dawowa ya sauka a wajenta yana ta Haba haba da ita, yara ma har kallo ya yi da su sai jan su da hira yake yi. Sai da daddare sun kwanta ya tausasa harshe yafara lallashintaa. "Bili ni fa na dauka mun wuce wannan k'adamin a tsakaninmu. Na dauka ni da ke mun zama d'aya . Abin da yake tayar mini da hankali na kasa nutsuwa da ke tunda kika yi mini gori akan kudin da nake cira a asusunki na fara baya dake, ba ki fa da tabbacin budurwa na ke kashewa kudin, a lokacin ma Hajiya ce ba ta da lafiya, amma kika rufe ido kika yi mini gori, shiyasa nake jin zafinki gaskiya tare da tsoron ki. Bana son gori nan duniya Bili ba wata macen da zan aura da zata fiki, ke ce farkona fa, me ya sa zan manta da mafari? Hausawa suka ce da tsohuwar zuma ake magani. Ke din rufin asirince, mai sonace da gaske, ki yi hakuri ki huce kada ki ga dan muna ta samun sabani wai bana sonki ko an sha gabanki ne a zuciyata. Lah har abada ke ta daban ce, ina tuna yadda kika k'i manyan mutane da suke sonki kika zabe ni duk da k'uruciyata da kuma rashin abin yi na. Ki yi hakuri da ni dan Allah! Tun Bilki na janyewa har ta saki jiki da zuciya ta karbi lallashinsa abin mamaki, tsawon lokaci suka yi suna raya daren a karo na farko bayan tsawon shekaru ta samu gamsuwar da ke bukata a wajensa shi ya sa ta tashi cikin farinciki da sukuni duk da shaidan sai ayyana mata yake yi albarkacin amarya ta samu don kuwa kafin wannan had'uwar bai taba yin jarumta akanta irin haka ba. Ke nan ya yi riveving kansa don ya dinga gamsar da amaryarsa. Tasan haka ne amma ta kore wannan zaton ta dinga addu'a da fatan karshen matsalarta ne ta zo. Da safe ya lallabe ta da daɗin bakinsa. "Bili ki siya duk abin da babu, ki rika rubutawa ni nasan abin da nake yi. Ki k'ara hakuri da ni idan Hawwa ta haihu komai zai sauya. Tunda ba batun hidimar haihuwa." Dama ai ta saba shi yasa bata damu ba ta ce masa to a ranar kuma ta shiga kasuwa ita da Alti ta siyo duk abin da ya kamata ba ta sake bin ta kan Baban Amrah ba tun da ko da yaushe hakuri yake bata akan cewa yana sane da abin da take yi. Sannan yanzu kam ba ya yarda ya wuce sati bai take ta ba tunda ya fahimci idan ya mata wannan harkar yana saurin dankwafe borinta. Bayan an yi haka ya wuce sai kuma ya tsiro da wani abu. A da iya makaranta yake kai amarya da daukota. Yanzu kuma duk inda zata je sai ya bar komai ya kai ta sannan ya jirata ko ya koma ya daukota. Yana kafa kafa da ita, kamar yar gwal Balki ta ga shiga hakkin ya yi yawa ita take fama da dawaniyar kai yara makaranta ko da ba da safe zata shiga makaranta ba. Haka nan kullum ita take kwasosu. Sai ta ce masa ya dinga kai yara makaranta da safe, duk da tana da mota, fitar na safe ne matsalarta. Amma Baban Amrah ya kafe ya tsare akan cewa ba shi da lokaci sai dai ita ta cigaba da kai su, Bilki kuwa ta ga abin na shi ba adalci. Yana da lokacin kai matarsa duk inda zata bayan makaranta amma ba shi da lokacin kai yaransa makaranta. Itama ta kafe ta ce ba za ta dinga kai su ba. [05/09, 12:49 pm] Maman shukhrah: "To Alawiyya ta dinga kai su a cikin napep." Ya fad'a da ya ga sun yi kwanaki biyu basu je ba. Bilki ta ce sai dai ka ba da kudin drop na wata amma Alawiyya ba za ta dinga wannan wahalar ba tunda da zata d'auke ta ban fad'a kai yara da daukosu na cikin ayyukanta ba" Kai tsaye ya ce" Ki dauki mai Napep din ba ni da wannan halin." Bak'inciki ya kama Bilki ta kasa magana kuma abin da ya fada ya tabbata ba ya kai su makaranta. Sai da ta ga fushin ba zai haifar mata da d'a mai ido kan yaranta ba ta sauko ta dawo tana kai su, ko tana cikin maka Sai dai ya tabbatar dukanta ba k'aramin bala'i zai rakitowa kansa ba domin duk yadda ya mata gorin ahalinsu sun dare sun tarwatse bata yi arahar da zai saka hannunsa a jikinta da sunan duka ya kwashe kalau a hannun ahalin nata ba. Duk tak'amarsa kuwa. Tana da yaya kwamishinan y'an sanda (Asad) wanda tun asali yasan bai so aka ba shi aurenta ba. Tana da Usman soja ne wanda shima matsayinsa ya fara nisa a gidan soji. Tana da tantiri irin Ansari kuma mai d'amara ne. Bayan haka ga Farouk da yake da kud'i a hannunsa ya tabbatar zai kashe ko nawane akan Bilki. Haka nan tana da darajarta ta daban kasancewarta tsohuwar ma'aikaciyar kungiyar lafiya ta duniya (W.H.O) Wanda suke had'akar ayyuka da hukumar kare hak'kin d'anadam(Human rights). Bayan haka Munira babbar Lauya ce da take aiki da kotun duniya reshen k'asar da take zaune, sannan jamiar kare hak'kin ya'ya mata ce. Ga uwar iya Abida. Ga Yaya Hamida mijinta babban alkali ne a kotun shari'ar musulunci. Ga Basma yar karare da zata yi zugar da dukkan ahalinsu Bilki zasu yi masa d'aurin talala. Dan haka a fusace cikin isgili ya ce "Don iyayenki masu son zuciya ki je na sake ki saki biyu, ba don uku tashi guda sakin jahilai ne ba, da na cike miki, shasha mai bak'ar zuciya da bakin k'ishi. Ki je, idan kin samu adalin da ya fini wanda ba azzalumi ba, sannan ba mai gadon abin kunya ba sai ki aura Hakima Bilkisu Isa Funtua! Yana gama fad'in haka ya fita ya bar mata falon. Ita kam sai ta ji kanta na juya mata kalaman Sahal na mata kuwwa a kunnenta har ma kwakwalwarwarta bakidaya. "Ki je dan iyayen ki na sake ki saki biyu" Tirk'ashi! Sahal ne ya sake ta? Zai iya sakinta ashe? Duk da ta fahimci ya gaji da ita amma ba ta taɓa tunanin gajiyar zata kaisu ga wannan gwadaben ba. Bata taɓa hakaito idan zasu rabu zasu yi rabuwa irin haka ba. Ta dauka zai yi mata alkunya ya rabu da ita cikin mutunci da fakewa bayan k'addara. Sai ga shi ya yi mata wani irin wulakantaccen saki tare da yi mata gori mai tayar da ciwon hawan jini. Sai dai ta godewa Allah da itama ta yi masa gori mai dasa ciwon zuciya. Idan baki yasan abin fad'a bai san abin mayarwa ba. End of book 2 Muje ga book 3