===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 1 ==>Sauri take tagama watsa ruwan domin bugun da akema qofar palon su yafara bata haushi, tasan cewa ba kowa bane illa sumayya da Rufayda iyayen yawo, taja tsaki.mtsww! Ta bude murya afusace tace wai dalla cire qofar zakuyine? Walh Nazo gurin duk zakuci ubanku.,taga dai alamun bama jinta suke ba, adaddafe tagama wankan tai saurin daukar towel dinta wanda kadan yawuce rabin cinyarta. ko gama daurawa batayiba saboda tsabar Haushi ta bude qofar bayin ta fito tana fada. Gashin nan nata yayi kwance agadon bayanta gashi baqi sutuf ya kwanto har a fuskarta abinka ga farin fata sai tayi gwanin sha'awa ga sajen dake qarama fuskar nata kyau, ta nufi palon tana qara goge fuskarta da towel din jikinta,. kunfita tin dazu kunbarni agida ni daya kamar mayya alhalin kunsan su momy basa nan, kuma yanxu kun dawo ne zaku isheni da nocking. yau sai kunsha ranqwashi tafada tana kokuwan bude qofar da izzarta domin sotake da tabude ta cafko daya dan tasan zasu iya tserewa, Tofa mezai faru!?ji kake tasss! Sun gabza karo.,ta fasa wani uban qara don tsabar firgitan datayi ga zafin buguwa, ruqota yayi da hannu daya dayan hannun kuma yana qoqarin mulmula mata goshinta Inda sukai karo.cike da alamun tausayi Yake fadin oh sorry sister kinji tsoro ko, ita kuwa har yanzu jikinta karkarwa yake sbd irin ruqon dayayi mata gashi daga ita sai towel .hannayenta suna dunqule akan qirjinsa ta matse hammatarta sosai don tana gudun towel dinta karya fadi, shi kuma hannunsa yana tsakiyar bayanta inda ya tallabota lokacin datake qoqarin faduwa, daqyar ta iya daga hannu daya ta riqe hannun nasa dayaketa faman mulmula mata inda ta buge, cikin rawar murya kamar Wanda take shirin yin kuka tace. Yaya afnan daman kaine? Yace eh sannu kinji, tace dan Allah yaya afnan kayi haquri walh bansan kai bane nazaci su rufy ne, duk wannan maganar datake shidai kawai ya zuba mata ido ne yana kallon bakinta wanda yake qara daukar hankalinshi ga sweet voice dinta daya tirsasashi lumshe ido alokacinda ta idar da maganarnata,. Kawai saitaga yaqara hogging dinta da dayan hannun nasa yana qara matseta jikinshi, qirjinta yai wani mugun bugawa rasss!!!,ya dubeta cikin wani irin yanayi data kasa fahimtarsa yace sis su momy fa?,hankalinta atashe tace suntafi gaisheda INNA ne tare da cewa yaya AFNAN sakeni mana hawaye suka gangaro a bisa kyakkyawar fusakarta. Hankalinshi yatashi amemakon yasaketa saiya qara hogging dinta sosai tare da sassauta murya yana kiran sunanta daidai kunnenta ahankali salma!salma!salma kitaimakeni dan Allah salma nah., >BUTULCI KO SO!!!.? Part 2 ==>Arazane take kallonsa taga yadda idonsa ya kada yai jajur wani irin masifaffen tsorone yakamata gashi sai qara matseta yake aqirjinsa yana wani irin numfashi sama! sama! Cikin tsoro da fargaba taqara fadin ya afnan kasakeni mana dan Allah muryarta na rawa saiga hawaye sharrr! Haba tuni afnan yafara kai halshensa yana lashe hawayen nata tareda rugumeta Sosai har saida tai wata yar qara tace na shiga uku yaya kayi haquri, tafara ja dabaya kozai saketa tasamu ta ruga daki amma inaaa inda tadaga qafa nan yake mayarda tashi., yaya..yaya dan...wani irin kallo da yake mata yasanyata daburcewa takasa qarasa maganar, cikin wata irin murya mai tada hankali yake fadin salma salma kintashi hankali na. salma bazan iya rabuwa dake ba, afusace tace to kasakeni man yaya. Ya watso mata wani irin kallo Wanda saida tai qasa da kanta sannan cikin rawar murya yace bazan iyaba my dia, .tuni afnan yayo palo da ita tana tutse tutse ga towel dinta yana neman zamewa ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 3 ==>Har kiran ya katse be dauka ba.,tab da wanne zaiji da kiran abbanshi ko da tashin kankalin dayake ciki.,yana cikin wannan tunanin ne kiran Abba yasake shigowa qin dauka yayi domin hankalinshi kusan baya jikinshi,.salma! Salma!yake fadi ahankali yana rugume da ita,.wani irin jiri yaji yafara dibarshi da tsabar ciwon kai!.ahankali ya dauko wayarshi daqyar ya iya nemo numbern aunty sadiya ya danna kira.,tai ringing harta yenke ba'a dauka ba.,yaqara danna kira bugu biyu aka dauka tareda sallama.,ko amsawa beyi ba.,yace aunty kina gida ne? Eh ina gida afnan lapia kuwa naji muryarka haka?!aunty ba lapia ba.innalillahi tace meya faru kuma afnan bakada lapia ne.,uhm yace aunty dan Allah kizo gidansu salma yanxu dan Allah amma karki gayama su umma nan zakixo kawai kitaho ne karki fadama kowa kinji pls aunty ki taimakeni dan Allah,.wai...kafin taqarasa maganan yakashe. Taqara kira yaqi dauka.,afirgice tayo palo da nufin fadama momy halinda afnan ke ciki.,koda taxo saita tuna yace kawai tazo ne karta bari kowa yasani.,juyawa kawai tayi da sauri dn dauko hijabinta. Tai maza ta sanya hijab ta nufi qofa ahankali take tafiya dan bataso momy taga fitarta tace ina zataje.,tasamu ta fice tafara sauri har zuwa bakin titi inda tatare me keke nafef nahau.,har yanxu kiran afnan take amma yaqi dauka.nan da nan suka isa gidan tasauka tabiya me keke,tashige gidan cikin tashin hankali ko sallama babu. Gogan naka yana rige da salma jin dayayi an buga qofa GAM!!!.ya miqe afurgice domin atunaninsa ko yan gidan ne suka dawo.,nan yaga aunty ta fado palon a 60.,shikanshi saida yaqara rudewa.abin ka da mare gaskiya ko aruwa tsuma yake.,ganinshi tayi dagashi sai dogon wando da singlet.,ta bude baki zatayi magana ta hango salma sharbe sharbe kan kujera an dan rufeta da towel ga jini dayaketa bin qafafunta.,, innalillahi wa inna ilaihirraju'un tafada tareda daura hannu akai., afnan me kuma yasameta tareda qarasawa gurin.tadafe qirji na shiga uku afnan waya kasheta!?nan danan hawayen afnan suka qara kwararowa tareda durqusawa yasa gwaiwowinsa biyu aqasa aunty walh nina kasheta.nine nakasheta da kaina ,aunty na shiga uku walh fyade nai mata har said a ta mutu.,wa iyazubillahi.,fyade afnan?meya kaiga wannan aiki? afnan shikenan ka bata mana suna ta fashe da kuka tareda dago salman shimadai kukan yakeyi.,ta kalleshi cikin tsawa da kuka tace katashi kaje yanxu kasamo me nafef mu kaita asibity .,yace anty da sauran ranta ne.,ta daga murya nace maka kaje ka kira ko.wai ma su momy suna ina kayi wannan aikin,.walh aunty nazo gaisheda su momy ne Ashe wai suna gidan inna.,oh shine ka ida nufika akanta ko.,walh ba da gangan nayi ba aunty ki yarda dani kinfi kowa sanin wayeni kuma kinsan matsayin Salma awajena,.mtsww tayi tsaki zaka tafi din kosai ta mutun?da sauri yamiqe yasanya rigarshi ya fice, miqewa tayi tacire hijab tadauki salma tai toilet da ita tadinga wanketa tana kuka don gani take kamar ta mutu ne,. Haka dazo ta dakko riga tasa mata tashiga gara gurin,.sai gashi yadawo da kanshi ya dauketa yai waje da ita sadiya tana biye dashi abaya.,sai Horeb Hospital. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 4 ==>suna isa akayi Emergency da ita,.nan danan aka karbesu dan ganin yanda jikin nata yake .,Dr da nurse ne tsaotsaye akanta sunata qoqarin ganin numfashinta yadawo domin kuwa ba mutuwa tayi ba doguwar suma ne.,wasu na kan HQ dinta da har yanzu be danai jini ba.suka gano anyi mata rauni ne sosai awajen nanfa saida akai mata dinki akai mata allurori akasa mata drift.,sannan aka akace akirawo Wanda suka kawo ta dan tana buqatar qarin jini yanxxun nan,.dan jininta yayi qasa sanadiyar ciwon da akaji mata da kuma tashin hankalin data shiga shima yataimaka wajen saukar da BP dinta.,.nurse tafito suna ganinta suka miqe dikkansu dan Allah ya ake ciki ta tashi kuwa? tace kune kuka kawo Salma.eh suka fada atare.,tace OK kuyi haquri taji sauqi sosai kuma zata tashi insha Allahu saidai likita yace tana buqatar jini yanxunnan.,da sauri yace muje agwada nawa idan zaiyi adiba,sadiya tace muje idan nashi beba aduba nawa,.suka wuce tare da nurse aka gwada jinin afnan akaga zai iya bata jini aka diba shima akace yadan kwanta ya huta., ai ina yakasa kwanciyan suna fita shima yatashi yabisu.,saidai ganinshi sukayi adakin aunty dai tinda sukazo ko magana bata qarayimishi ba saidai harara,.yaqarasa bakin gadon yana fadin anty ya jikin nata. Ko kallonshi batayiba,jiyayi yana Neman fadi saiyanemi wata farar kujera datake bakin gadon yazauna,.yayi wani ajiyar zuciya dayaga salman tanata numfashi da alamun bacci takeyi.,nurse tagama abinda take tace to dan Allah tana buqatar Hutu karku yawaita surutu munyi mata duk abinda ya kamata da allurori yadda zata samu tadan huta dan ta wahala sosai kuma munyi mata dinki a HQ dinta .,tafice abinta.,gabanshi yai wani mummunan faduwa itama aunty haka.yanxu har yayi mata lahaninda saida akai mata dinki.,innalillahi kawai yake nanatawa azuciyarsa,. aunty sadiya tana zaune a bakin gadon tataba jikin salma tajishi kamar garwashi. Sai hawaye kawai take shima dai afnan kukan yake ba Wanda yacema wani uffan.,idan muka koma bangaren gida kuwa.momy CE riqe da hannun kahlid suka shigo gida sumayya da rufayda suna biye da ita.suka ruga cikin gida da gudu anty! anty!anty ina kike walh munyi miki wayau kina bacci muka gudu mukabi su momy gidan INNa kuma tuwon dawa mukaci da miyan ayayo me dadi!..sumayya tace dallah kinata zuba qilama har yanxu baccin takeyi kinsanta da baccin tsiya.suka banko dakinta aguje suna dariya.,adaidai lokacin momy tashigo palo riqe da hannun Khalid.! kai ina antyn inji rufy sumayya tace ko tana toilet ne.,aunty! aunty suka hau qwala mata kira.,momy CE tace lapia ina auntyn naku tashigane kuketa qwala mata kira haka.,.sukace momy bamu ganta bane ai adakin.,,,kamarya baku ganta ba bata toilet?. Momy tataso da sauri tana salma!salma!.wani irin iskancine haka ina taje tabar mana gida ba kowa. Tafada tareda bude qofar toilet din,.,cub mezata gani towel din salma ne yashe aqasa duk jini. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 5 ==>Da sauri tadauki towel din tabude wannan yafi qarfin ace jinin al'ada.su Sumy da rufy kam anyi tsuru tsuru,.ta juyo tareda daka musu tsaya dan ubanku ina salman take? duk saida suka tsorata.walh momy bamusani ba mudai mun fita mun barta tana bacci.,innalillahi wa inna ilaihirraju'un momy tahau salati tana tafa hannu.,da sauri tayo palo tana rasa abinda zatayi tafara zagaye gidan ita da yara sunata leqe leqe.,su rufy kam baki yamutu tinda ran momy yabaci daman gashi saida tace karsu biyo ta..,bangaren su afnan kam sadiyace taciro waya dantasan za a nemi salma bari takira tun kafin hankali yatashi.,ta lalubo number momyn salma takira harta yenke ba a dagaba don suna cen suna zagaye tsakar gida har saida tai 3 miss call.momy tace ai banga tazamaba bari inje inkira yayanku nagaya mishi halinda ake ciki.nanfa sukayo palo daidai sadiya tasake kira ahanzarce momy taqarasa tai saurin daukar wayan tareda sallama ina wuni momy lapia sa'adiyya ko salma tazo gidanku?.shiru tayi wasu hawaye suka zubo mata.momy taqara cewa kinajina kuwa? Sadiya cikin kuka tace momy muna nan tare da salma a horeb hospital ankwantar da ita a emergency word taqara fashewa da kuka.,,kuttt.kar kuso kuga gigicewa agun momy subhanallahi sa'adiyya meya sameta kifadamun dan Allah kota mutu ne?a a momy bata mutu ba taqara fashewa da kuka ta katse wayan,.momy kuwa jiki na bari tana fadin to meya sameta yanxu ina salman take?sannan ta lura ashe sdiya ta kashe..,ai tuni ta figo hijabinta sai asibityn,.nan tabar yara tsuru tsuru suma kukan suka kama,.Khalid ma haka yaketa tsala ihu wai zai bita ko kulashi batayiba,.shiko afnan tinda yaga sadiya tana waya qirjinshi ke bugawa,daqyar ya iya cewa aunty wa kika kira ne?ko kallonshi batayiba bare tabashi amsa., bangaren ummansu sadiya kuwa ummace tafito plo tana kiran sdiya sadiya!.tashiga har dakinta amma shiru,lallai yarinyarnan yanxu ficewa tayi nida nabarta tadaura mana girki dan iskanci saita fita babu ko tambaya daidai nan alhaji yashigo da lapia hjy kiketa fada kedawa haka? walh yarinyar nanne sadiya tafice tabar gida ni inacen ina bacci ko tambaya batayiba,kuma nabartane akan bari taje tai sallah ta daura girki yanxu nafito naleqa kicin babu alamun girki Ashe gaba daya ma gidan tabari sbd tamaidani shakatafi.yanxu jibi qarfe 6 0pm duk inda taje ai yaci ace tadawo,. ga gidan ba abinda aka dafa metakeso muci?!.alhj yai ajiyar zuciya.yace qyaleta hjy zata dawo taimin bayanin inda taje. Sannan yace afnan fa?.tace afnan ai tinda yafice yace zaije ya gaisheda INNA daganan sai yawuce office wajenka yace wai kanason ganinshi.ko beje office din bane?.uhmm alhj yace walh beje ba kuma nakira wayanshi yaqi dauka daga bisani ma kashe wayar yayi.tareda fadin zasu dawo su sameni dukkansu.,momy tace allah ya shirya.,barin daura mana ko taliya ne muci ko?.alhj yace aa sha zamanki nayo mana shopping saimu cinye sun tinda basuda kirki saisuci ubansu idan sun dawo.,gaba daya sukasa dariya tace kai alhj shikenan,.bari naje nai wanka natafi masallaci to alhj saika fito,. Momyce taqaraso afurgice tana tambaya kuwa aka nuna mata word din dasuke,.tabude qofa tashige afnan ne ya waygo dan ganin Wanda yashigo yana ganin momy gabanshi yafadi yai saurin sadda kanshi qasa!;taqaraso bakin gadon tana fadin innallahi sadiya afnan meya sami salman ne?!dan allah kufadamin mana:kuka tasa musu gaba daya suka hau kuka ba Wanda yace da ita uffan daga afnan har sadiya'. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 6 ==>Qarasawa tayi bakin qadon ta zauna tare da cewa sadiya harda qarin jini? Dn allah kufadamun abinda yasameta gaba dayansu kuka suke gani tayi babu me shirin bata amsa cikinsu,.dan haka ta kama dube dube jikin Salma ta duba nan ta duba cen.,itadai bataga ciwo ba jikin salma saidai tsabar zafin jiki dataji.,ahankali tajuya ta kalla afnan tace afnan wai meya faru ne da ita!?.jiyayi kamar ta soka mishi mashe a qirjinsa tsabar razanan dayayi da tambayan nata.shjru yayi yai qasa da kanshi kawai kamar muna fuki.,waya ta dakko tamiqawa sadiya tareda cewa kiramun Ahmad.,takarba ta kira sannan tamiqa mata.,bugu daya yadauka kamar Wanda yake jira,sannan yace momy nadawo gida naga yara sunata kuka wai kintafi asibity salma ba lapia?.tace eh daman nakira nafada maka ne ,.wani asibity ne momy?.nan horeb hospital ne yace OK,.yana gamawa yafice tareda cema sumayya ku rufe gidan yanxu zan dawo.,yafice sai asibityn yakira momy taimai kwatancen word din yaqarasa da Sauri.,.idan muka koma cen gidansu afnan kuwa.,momyce ta kalli agogo tareda cewa alhj anya yarinyar nan tanada hankali kuwa kallafa qarfe bakwai ake nema yarinyar nan bata dawo ba bayan fitarda tayi bada iziniba!.alhj yace to bakiga afnan dinba shima shiru shida yake dawowa qarfe 6, hjy tace lallai yaran nan yau zasu gamu da bacin raina musamman sadiya,.Yanxun haka qila gidan inna ta nufa ko wajen salma dan nasan duk iya yawonta kenan.,alhj yabata rai wato bataji abinda nagayamata ba har yanxu tana nan tana zuwa gidan kamar mayya ko.to zata dawo tasameni ai ke kika daure mata gindin taringa zuwa din..hjy jitayi dama bata ambata gidansu salma ba dan har ran alhj yabaci sosai.,nandai suka tashi danyin sallah.,,Ahmad ne yabude qofa yashiga word dinda salma take duk arude yaqarasa yana subhanallah momy meya sameta ne haka?.tace gasunan su suka kawota nayi nayi sufadamun mu sabbabin abin amma sunqi magana saidai kuka kawai suketayi.,asanyaye Ahmad ya kallesu sannan yace sadiya kuyi magana mana don allah shima kamar zaiyi kukan.,cikin kuka tace momy ku tambayeshi yafi kowa sanin abinda yafaru nikam bakina bazai iya fadi ba taqara fashewa da kuka mai sauti..,nanfa afnan yafara dan Allah momy kiyafeni momy kitaimakeni kiyafemin walh banida burin cutar da salma arayuwa na.momy bada gangan nayi ba kiyimin aikin gafara momy.,daga momyn har Ahmad sototo sukayi suna kallonshi yadda ya kofa gwaiwowin aqasa yana kuka sosai.,Ahmad yace kufada mana abinda ke faruwa mana kunsakamu acikin duhu.,nanfa sadiya tace momy afnan ya lalatawa salma rayuwa afnan yayima salma fy....kawai ta fashe da kuka.,momy afurgice tamiqe sadiya meyai ma salma din fadamun dan Allah., momy ya keta mata mutuncinta har saida akai mata dinki momy mun shiga uku., innalillahi wa inna ilaihirraju'un suka fada daga momy har Ahmad afnan kam jiyayi yayi mutuwar zaune.,Ahmad ne yajuyo tareda cafko afnan ya miqar dashi yana fadin afnan meya kaika meyasa zakai haka afnan?gaba dayansu kuka suke wiwi,.ya kuyi haquri Ku yafeni walh bada gangan nayi ba ya duk hukuncin da kayimin daidai ne domin nayiwa salma abinda yafi haka.,amma dan Allah ya kaimin adalci .,momy tada tallabo kan salma tanata kallonta tana Hawaye.,tace Ahmad sakeshi.; kasakeshi nace.,ahankali yasakeshi wasu hawayen takaici suka zuba masa.,nan tace zauna afnan kafadamun yadda akayi ni nasan d'ana bazai aikata abinda akace yayi ba.koma zaiyi bazai taba kwatantashi wa salmanshi ba.;kuttt..,momy batasan abinda yagani bane yau ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 7 ==>Momy tai salati tare da cewa Ahmad riqeta da sauri dan Allah.,Ahmad yai saurin cafko ta ai tuni takaimai wani fizga sai gashi cen yayi gefe guda yana tangal tangal.,ta cafko afnan dayake malale aqasa jini yanabin fuskarsa .momy kam salati kawai take tana fadin shikenan ta kasheshi.,Ahmad dake baya yai saurin fizgo sadiya ta baya har saida kanta yabuga bango amma tana riqe da wuyan rigar afnan tam!!.daqyar Ahmad yasamu ya matseta jikin bango sosai.sannan ya fixge afnan daga hannunta tuni momy tataso tariqe afnan tareda kwantar dashi agurin tayo gun sadiya da Ahmad yaketa faman turka turka da ita.,suka matseta sosai suka fara tofeta da addu'o'i.,ahankali tafara dawowa hayyacinta Ahmad yabarta da momy tanata faman yimata addu'a.,yafice da sauri yasamo ruwa yazo yafara yayyafama afnan. Cikin ikon allah yafarfado saidai yaji ciwo sosai akanshi wajen sai jini yake fiddawa kamashi yayi sukayi waje dan asamu atsaida jinin,.take aka karbeshi akai mishi treatment din wajen aka rufe da bandage akaimai alluri domin jikinsa yayi zafi sosai gashi yanata numfashi sama sama!,nan aka daura mai drift aka bashi gado.,.Ahmad yadawo bangaren su momy nan yaga sadiya tana kwance kamar me bacci"yafadama momy abinda ake ciki.',wayar sadiya CE tai qara Ahmad yamaida dubansa gun wayar sannan yasa hannu yadauka wayar yace momy dadynsu sadiya ne yakira'momy tace to dauka mana kuyi magana,.dauka yayi yakara akunnenshi tareda sallama,.cikin fushi abbansu sadiya yace waye kai!ina me wayar take?;Ahmad ya sassauta murya yace abba nine fa"Ahmad ne:yasake daka tsawa wani Ahmad din?;jiki asanyaye yace Abba Ahmad yayan salma fa-bata rai yayi to ina sadiyan!ahmad yace gata nan muna tare a horeb hospital salma ne ba lapia taxo dubata itama jikin nata yamotsa yanxu mun samu tayi bacci ne kuma saiga kiranka_abba yace subhanallah kuma shine bata fada mana ba tayi tafiyarta.aida sun taho tare da hjy,yanxu yame jikin!da sauqi Abba Ahmad yaqara dacewa ai muna nan tare da Afnan shima anbashi gado ya........momy tai saurin fixge wayar takashe kiran sannan tace kana hauka ne!?me kake shirin fada mishi to ina me gargadinka karda kasace naji wannan maganar abakin kowa hatta yayanka Habibullah ban yarda yaji wannan maganar ba nagaya maka!;cikin rashin faminta Ahmad yadubeta tare da cewa to momy ai wannan maganar bazata boyu ba dole ne kowa yasan abinda afnan ya aikata kuma koma me akai mishi ai shiyaja makanshi wannan maganar ai tafi qarfin a boyeta momy:'cikin sanyin jiki momy ta kama hannun d'an nata hawaye suka zubo afuskarta sannan tace Ahmad kataimakeni da wanne kakeso naji so kuke baqin ciki ya kasheni Ahmad kasan halin yayanka habibu yanxu idan yaji wannan maganar me kake tunanin zai faru ko so kake a haifi danda ba ido;yanxu ga salma rai ahannun Allah ga sadiya kwance afnan kwance so kake kafada yayanka yaxo yaita hauka yanemi hanyar salwantar da rayuwar wannan yaron ko kamanta zai iyayin komai akan duk Wanda ya cutar da salma?! yanxu abinda kakeso yafaru Keenan baqin ciki yakasheni- taqarasa maganar tareda fashewa da kuka,.shima Ahmad kukan yafarayi'nan yazaunar da mahaifiyar tashi kan kujera sannan ya durqusa aganta yana kuka'yace momy na yanxu ya kikeso ayi!?dan allah karki tada hankalinki walh momy duk abinda kikace zanyi,.gani sukayi sadiya tatashi ta zauna itama hawaye ne keta faman sintiri a fuskarta da alamun ta jima tana sauraronsu,.momy tamaida dubanta garesu sannan tace Ahmad yace na'am.sadiya tace na'am momy!,inaso kuyimin wata alfarma. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 8 ==>momy tace ina roqonku dan Allah karbu fadama kowa abinda yafaru kar wannan maganar taje bakin kowa kubarta anan dagamu sai allah,dan Allah kuyimin wannan qoqarin idan ba haka ba abinda zai biyo baya me girma ne kuma kanku saikunce mema yasa kuka bayyana,.Ahmad yai wata ajiyar zuciya..,sannan yace yanxu momy kina ganin wannan maganar zata boyu!? wannan fa ba qaramar magana bace yanxu idan an boyeta ya salma zata kasance wajen mijinda zata aura yanxu idan aka boye wannan maganar anyi mata adalci kenan momy?!momy tace Ahmad ba shawararka nake nema ba umarni nake baka abinda nakeso kuyimin kenan duk wani abinda zai biyo baya me sauqi ne akan idan aka bayyana maganar nan.,sannan ai dole ne ma afnan ya aura salma domin ayanxu babu Wanda yadace da auranta idan bashi ba'.dan haka kuyi abinda nace kuma kubar komai a wajena ni nasan mezan fada musu!!sadiya taja wani numfashi ta dubi momy tace momy be kamata a quntatawa rayuwar salma haka ba momy walh gwara ma a qyaleshi da babib din yai masa duk abinda yaga dama domin ya cutar masa da abinda yake matuqar tattalinta da rashin son bacin ranta.dan haka yadace ya fuskanta hukunci momy walh bana goyon bayan a rufa masa asiri.,ta qarasa maganar tana kuka!,momy ta dubeta sadiya hannunka baya rubewa kayanke kayar kome yaronnan yayi yakamata muyi masa adalci idan muka duba tsakaninshi da salma bedace mujuya masa baya ba dan ya aikata kuskure irin wannan danni na tabbata ba halinshi bane,.dan haka sadiya kuyi haquri kawai kubi abinda nace.,sadiya dai shiru tayi Ahmad ne yai qoqarin cewa insha allahu zamuyi yadda kikeso momy kuma babu Wanda zaiji wannan maganar abakinmu dayardar Allah munyi miki alqawari;momy tadan saki fuska tace yauwa Ahmad allah yaimuku albarka yanxu kiramin habibu nagaya masa muna asibiti.,kuma inaso idan zaka tafi kuwuce tareda sadiya domin su kwana da yaran nan.yakarba wayan yakira yamiqa mata.,bugu 3 yayi taga an danna busy bata damu ba tinda daman tasan baya daukar kiranta saidai yakashe yakirata.,jim kdan kuwa saiga kiran Habib tadau ka yagaisheta cikin ladabi.ta amsa muryarta babu annashuwa.,sannan tace habibu muna nan fa a asibity salma ba lapia yanxu haka dai gatanan sai abinda allah yaso,.what?momy meya sameta wani asibity ne momy ina fatan dai tana nan da ranta momy bani ita dan allah ko bata magana ne gaba daya Habib yarikice momy tama rasa amsar dazata bashi ajiyar zuciya kawai tayi sannan tace muna horeb hospital ne saikazo kawai takashe wayarta.,afurgice Habib ya nufi daki fadeela tamiqe a tsorace tana fadin sweetheart lapia kuwa?waye ba lapia.ko sauraronta beyiba yaje yasaka farar jallabiyyarsa yafito da sauri yana fadin asibity zanje yanxu momy takirani take fadamun salma ba lapia yanafadi yana qoqarin ficewa,.batayi mamaki ba dan tasan yadda yakeson qanwar tashi aranta taji haushi amma afili cewa tayi subhanallah allah yabata lapia saika dawo kafin tarufe baki shiyariga ma yayi waje,aranta kuwacewa tayi allah yasa ta mutu inga qaryar iskanci.,taja tsaki ciki ciki tajuyo ta rufe qofarta ta wuce dyning ta zquna cike da haushi.,shiko gogan naka tuni yafigi motarsa sai asibity,.a bangaren su abban afnan kuwa Abba yakira yakira wayan sadiya amma anqi dagawa tuni yafadama hjy abinda ke faruwa sannan yace tai maza ta dauko hijjabinta dan basuga tazama ba dan yaji ance afnan dinshi ba lapia kome yasameshi oho.,hankulansu duk atashe suka kama hanyan asibity mu samman ma Abba da ko kadan bayason yaji abinda zai cutar masa da dansa.,suna isa saiga Habib ya iso nan suka hadu a harabar asibityn daidai nan kuma Ahmad da sadiya sun fito da nufin tafiya gida.,nan suka hadu babu Wanda yatsaya wata gaisuwa Habib yadubi Ahmad yace ina ne word din?!Ahmad yace kuxo muje suka dunguma gaba daya suka nufi inda salma take.,nan suka tadda doctor a tsaye kan salma yana mata allura sannan ya cire ledan ruwan daya qare yasa mata wani. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 9 ==>Habib yai saurin qarasawa wajen jikinsa na rawa yana fadin doctor ya jikin nata da sauqi kuwa!?Dr yace yp zazzabine me zafi yanxu ya rufeta nayi mata allurori yanxu yanada kyau kubarta ta huta domin gaskiya taji jiki tana buqatar Hutu bamason ana yawaita surutu kubarta ta huta pls!Habib yace insha Allahu za a kula amma Dr menene matsalar nata abinciken da kukayi meyake damunta ne pls walh bata saba ciwo irin wannan ba naga harda qarin jini akai mata,.Dr yace eh abin ya danganta ne daga irin mijin da kuka aura mata wata qila yafi qarfinta kuma kaga qaramar yarinya CE gaskiya kunyi mata auren wuri gashi kun hadata da ba qauye marar tausayi yayi muku kaca kaca da yarinya gsskia ina iya cewa harda laifinku.,amma insha Allahu zata samu lapia karku damu.yafada tare da bude qofa yai ficewarsa inda yabar Habib atsaye yasaki baki hannunsa na rawa bakinsa na motsi amma yakasa magana gashi kuma yanada tambayoyi domin shidai be fahimci zantuttukan likitannan ba shin meyake nufi ne menene yasamu salman!;momy kuwa da Ahmad da sadiya tinda likira yafara zancen nan a furgice suke tsananin tashin hankali yaqara ziyartar zukatansu kuttt.!! hjy da Abba suma dai sun kasa fahimtar maganganun Dr dan duk yasasu a duhu.,amma shidai Abba hankalinsa be kwanta ba dan kuwa bega afnan ba.,babban burinsa kawai a nuna masa dan autan nashi,.Habib ne ya katse kowa daga saqe saqen zuci jiki a sanyaye yace momy nifa ban gane maganar Dr ba wai meya faru da salma!?.momy ta maida numfashi sannan tace Habibu wannan ba maganar nan bane.,yqnzudai yakamata kuje kuduba afnan din ko ta maida dubanta gun Abba tace alhj kuje kuduba afnan din ko,. Habib yai saurin cewa haba momy kifada mana abinda ya sameta mana mu fita daga cikin rudaninda Dr yajefamu yanxu ga salma a kwance afnan din shikuma meya sameshi??!yaqara sa bakin gadon yataba jikin salma agigice yajuyo yana fadin momy kinji jikinta kuwa,.dan allah meya sameta ne idonsa duk sun ciko da qwalla.,ta dubesu gaba daya tace alhj muje wajen afnan din inyaso mayi maganar a waje kaga Dr yace kar a yawaita surutu!,alhj kan daman ya qosa yaga afnan dan haka shiya fara bude qofa hjy tabi bayanshi dukansu zuciyarsu cike da saqe saqe,.momy ta kalla habib sanna tace kataso muje cen zakaji qaddarar data afko mana yau.,amma inaso kazamo me yadda da qaddara kuma karka tashi hankalinka domin haka allah yaso sannan itama ta fice sadiya da Ahmad sukabi bayanta.,da sauri yamiqe shima yabisu yna nanata maganarda momyn nashi tai masa yanxu a zuciyarsa!yasan lallai akwai wani Abu me girma,.suna shiga suka cimma afnan kwance sai rawar sanyi yake hatta gadon dayake kwance girgizawa yake.,Abba yaqarasa a furgice yana fadin afnan mega sameka ne haka!,dan allah kuyi mana bayanin abinda yasamu yaran nan.nan danan masu saurin kuka suka fara musamman ma wa Inda suka San abinda yafaru,.momy tai ajiyar zuciya sannan tace tabbas abin kuka ne yasamemu kuma dole muyi kuka bazan hanaku kuka ba,.taqara da cewa an tsutsemu an tsutsi salma yau anci mutuncin mu anci mana zarafi anje har gida anyima salma fyade na rashin tausayi.!!ta fashe da kuka ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 10 ==>Dukkansu saida suka razana da jin maganarda momy tayi.,Habib ne yameqe hankali tashe yace what momy fyade fa kikace salma din akaiwa fyade!;momy tace tabbas kuwa anyi mata fyade na rashin tausayi.dan dalilin dayasa kukaga afnan anan wajen kenan domin kuwa sanda abin yafaru da ita afnan yaje gidan da nufin yagaisheni yanata sallama yaji shiru gashi kuma yaga qofa abude sai yace bari ya leqa falon ko muna bacci ne aiko gana shiga yaga salma cikin wani hali juyowanda zaiyi saidai yaji an buga mai qarfe akanshi nan take shima ya fadi qasa sumamme,.yakai wani lokaci sannan yafarka jini sai binshi yace domin anfasa mishi kai daqyar ya iya qoqarin daukar wayanshi shine yakira sadiya yafada mata ita kuma tai maza taxo da mota aka kwasosu sai asibity nanne ma aka gane Ashe fyade akai mata.,innalillahi wa inna ilaihirraju'un gaba daya suka sa salati sadiya kuwa da Ahmad suna mamakin abinda momy ta shirya amma babu yadda suka iya dole suyi shiru,.afnan dake kwance yana fama da matsanancin zazzabi da ciwon kai.zuciyarsa ta qara daukar zafi.tabbas shidai beji dadin yadda momy ta rufa masa asiri ba,yazatai mishi haka,wata qila data bayyana gaskiya hakan ze iyasa ya mallaki salma amatsayin matarshi.ji yayi kawai zuciyarsa tana qara masa quna da zugi,shin kodai ya bayyana gaskia ne!?.,Habib ne yataso jikinshi yana karkarwa yaqaraso yazauna a bakin gadon da afnan yake.'ya dafa qafarsa zuciyarsa kamar zata buga yana fadin afnan ko kaga fuskar wanda yaima salma wannan mugunta?pls idan kaganshi zaka iya ganeshi!?nayi alqawari ko dan gidan uban waye sainaga bayanshi tinda ya cutarmin da salma!kuka ne ya kubuce masa tare da cewa na shiga uku shikenan an lalatama sister na rayuwa.innalillahi wa inna ilaihirraju'un",momy ta dubi aljh tace dashi inaso sadiya taje ta taya yara zama kafin mu koma gida yanxuma nace tabi Ahmad su tafi,aljh yace ba matsala,ta dubi Ahmad tace yakamata kutafi dan dare yayi sosai anbar yara a gida,tashi kawai sukayi suka fice ba tareda sun CE komai ba.,momy ta biyo bayansu sukai sallama ta wuce wajen salma,.Habib yasake maida dubansa kan afnan yana qoqarin sake yimishi magana,.sai gani sukayi yana wani miqewa yana nadewa jikinsa yasake dafewa kamar wuta gaba daya sukayo kanshi kar kuso kuga rudewa wajen Abba da ummanshi.Habib ma yadan tsorata da ganin yadda yakeyi.,dan haka da sauri ya miqe yace Abba bari akira Dr.dasauri yafice sai gashi tare da Dr umma dukta rude gani take kamar dan nata mutuwa zeyi.harta fara kuka,Dr yayi masa wata allura sannan yace su samu towel da ruwa su dinga jiqawa suna goge mishi jikinshi ahankali zazzabin ze sauka,.sannan akula kar ana yawan surutu akanshi,.dan jininsa ya hau saisun kula Dr ya fice,nanfa hankali yaqara tashi!!,Habib ficewa yayi abinsa ya nufi gun salma,yana zuwa yaga momy tana sallah yazauna bakin gadon ya tallabo salma tanata bacci saidai jikin nata har yanxu da zafi,.addu'a yafarayi cikin ransa ya allah ka nunamin Wanda ya keta haddin yar uwata.lallai an cutar mai da yar lelenshi,umma ta idar race dashi yakamata kaxo katafi gida ko,ya kalleta momy kije gida kawai ki huta zan zauna da ita.,momy so nake da zarar ta farka ta kwatantamun fuskar wannan azzalumin;.momy ta girgiza kai tace habibullahi abinda yafaru yariga yafaru,kaje gida abinka nizan kwana da ita kuma Dr yace da wuya ida zata farka yau,kuma kota farka ba lallai ne ta iya wata magana me tsawo ba.dan haka katashi kawai kaje gida abinka.,,haka momy ta matsa masa yatashi yatafi badon ransa yaso ba ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 11 ==>Gari na wayewa sadiya ta kimtsa komai daya kamata ta hada musu,.Ahmad yaxo yace idan tashirya taxo suwuce shima zaije yaga yadda suka kwana kafin ya wuce wajen aiki.sumayya tasa kuka itama sai anje da ita taga salma,.daqyar Ahmad ya lallabeta tareda alqawarin anjima zai dawo ya kaisu idan anty sadiya ta dawo sannan ta haqura,.suka kama hanya sai asibity,suna shiga sukaga momy tsaye akan salma suka qarasa da sauri,wai Ashe taga tana motsi da qafarta ne shine duk ta rude wai ko farkawa zatayi,.nan suka gaisa momy tace suje su duba afnan rai abace sukaje badon sunso ba,shima dai baccin yaketayi kamar matacce,suka gaisa da umma sama sama Ahmed yai sallama ya wuce abinsa,.sadiya taje ta kawoma momynta abinci.sukaci sannan tatashi taje ta duba salma ta dawo.,fitarta keda wuya saiga Habib yaxo ya nufi qanwar tashi yna tambayar momy ta farka kuwa,tace tadai dan motsa yau da safennan,inaga da alamun sauqi,likita yace babu wata damuwa zata tashi cikin ikon Allah.yace ya afnan dinfa.tace shima ba laipi kaje kadubashi mana.momy tayi tayi yace shidai agaisheshi koyaje tinda ba magana zai masa ba ai ba anfani,.ranar dai daqyar momy tamatsa masa yatafi office yana maqale da qanwarsa ko zaiga farkawanta amma shiru hakadai yadaure ya wuce.,duk wannan abin da ake inna bata sani ba.,aiko rufayda ta fakaici idon sumayya ta salale sai gidan inna, tana zuwa ta tadd inna a Palo taruga aguje ta fada jikin inna tana haki,,inna tace yau naga arziki yannan karyani zakiyi,daga ina kike haka kamar an jefoki kodai kinyo tsokana ne aka biyoki.,tace a a inna gudowa nayi sumayya bata sani ba nasan zata iya biyoni shiyasa naketa gudu nasan zataina nemana na barta ita kaidai.inna tace oh kudai Baku rabo da shiririta.to ai yanxu zakiga tabiyoki., ta dago kai a a inna ai bata isaba tinda momy batanan kuma Khalid yana bacci bazata fito tabarshi ba.,inna tace ina Maman taku taje bayan jiya tabar nan!?rufy tace ai tinjiya damuka koma gida bamuga anty salma muna shiga dakinta mukaga jini a towel dinta Ashe an yankata ne da bamanan shine momy ta fita itama taqi dawowa aunty ne ma tatayamu kwana shine....ai tuni inna ta hankadeta daga jikinta takai mata duka ban gane an yankata ba dan ubanki wani irin magana ne wannan ni zaki kawoma shashanci.,rufy ta zumbura baki tace to shine zaki dukeni ni gidama zan tafi abuna"inna ta ruqota yanxu ina salman take?! Taqara turo baki toba nace miki an yankata ba;,gaban inna ya yanke ya fadi lallaima yarinyannan da gaske take ko kuwa,.dan haka taqara jefo mata tambaya! to ina mamanku tace ai tin jiya bata dawo ba!,inna tasa salati innalillahi wa inna ilaihirraju'un. Inna tayo waje tna qwalawa husna kira!husna husna ta nufi sashensu,.momyn husna ne tace ke bakyaji inna na kiranki husna tace ni walh momy kinsan kiran inna yanzu haka ba wani abin azo aji bane.,saiga inna tashigo agigice ta miqa mata waya tace kirawomin abubakar yanxu rafida tazo take cemin wai an yanka salma wai mamansu ma bata kwana a gida ba.,safiya tace wani irin an ynkata kuma.husna ta kwashe da dariya tace umma kinji ko yanxu shirmen rufy zaki kama,.inna tace atafaf sai ankira mata abubakar.,husna ta kira ta miqa mata, yana dauka inna bata bari sun gaisa ba tace bukar meyafaru da salma ne?!shiru yayi yana tunanin waye yafadama ina abindake faruwa.tace kayi shiru ina sauraronka kafadamun abinda yafaru da salma.kame kame yafara inna..walh..inna wayace miki.tsawa taimasa taredacewa zaka fadamun kosaika rainamin wayau kodai salman ta mutu ne da gaske.,yace a a inna bata mutuba walh suna asibity tamaji sauqi inna ki kwantar da hankalinki. Kuka inna tasa da salati shikenan Ashe gaskiyane an kashe salma ba ason fadamunne magana yake mata amma kojinsa batayi duk. ya birkice gashi akan hanya yake zaitafi asibity ba shiri ya jiyo yayo gidan Inna., husna da mamanta sunyi tsarko tsarko suna kallon inna cike da mamaki. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 12 ==>Zama tayi dirshan tana tafa hannuwa tana cewa kungani ko yrinyar nan nasan haka nan kawai bazatazo ta fada wannan maganar a banza ba. Nasan ba hakanan ba akwai wani abinda ake boyemin.,husna tace inna wani Abu yafaru da salman ne?!tace gashi kuwa abubakar yacemin suna asibity to da wuya idan salma tana Raye., hjy safiyya tahau salati tace inna barida asake kiranshi aji!;sai sukaji sallama abubakar ne yashigo da sauri yayogun inna yana fadin inna bata mutu ba tashi muje nakaiki ki ganta .,tamiqe da saurinta tayo waje yabiyota abaya,.husna tafito a guje tana fadin Abba nima zanje kujirani Abba wai salman batada lapia ne?! yace wai waye yaxo yafadama inna ne,.husna tace rufy CE taxo tace mata wai an yanka salma., murmushi kawai yayi yace allah ya shirya jeki dakko hijabinki mutafi.,dasauri taje da dakko suka fice akabar hjy safiyya a gida.,ita kuwa rufy tuni ta sulale tai gida abinta., basu tsaya ko inaba sai asibity.,suna shiga momy saida ta tsorata da ganin inna amma ta dake tace inna waye fada miki muna nan?!tace ban sani ba an bari saita mutu sannan agayamun ko.tace yi haquri inna walh tin jiya hankalinmu be natsu bane,. Inna taqarasa gun salma tana fadin oh ni zuwaira meya samarmin salma ne!alhj kam juyawa yayi yanufi gun afnan yana shiga yaga dakin ba kowa mamaki ya kamashi yawo waje sai suka hadu da hjy tafito daga toilet tayo alwala.,yace ina afnan din?!tace ai yana ciki baka shiga bane yace yanxu nashiga banga kowaba tace wani irin bakaga kowa ba muje nabarshifa yana bacci,suka shiga tare hjy taga wayem tasaka salati tace alhj ina yanufa ne?! sukayo waje arude tai hanyan word dinda salma take yace dawo karkije tare mukaxo da inna yanxu kinazuwa hankali zai qara tashi murasa yadda zamuyi da ita,.tace saida nace ma sadiya tazo tazauna dashi amma ashe bata xoba,.yace yanxu taho muje inyaso daga baya saimu kirasu awaya mugaya musu abinda ke faruwa. Da sauri sukai mota suna tafe suna duba hanya, nan bangaren salma kuwa motsawa tafarayi gaba daya sukayo kanta suna tsatstsaye.Salma kuwa jitake kamar awani duniyar take jikinta duk inda tai qoqarin juyawa saitaji wani masifar ciwo kamar anyi mata shegen duka., momy ta zauna tana fadin salma salma sannu kinji!"ahankali abubuwa suka fara dawo mata tafara tuno abubuwanda suka faru tsakaninta da yaya afnan. Tuni tafara shure shure da qafa tana fadin yaya dan Allah kayi haquri bazan sake ba yaya kataimakeni nace baxan sake ba yaya.,kasakeni tuni momy ta tallabota ta rufe mata baki tana mata addu'oi inna tace oh wani yayan take kira ne momydai batace komai ba saida taga salma tadaina shure shure sannan tasake mata baki!"ahankali salma tabude idonta taqara lumshewa dan tarasa ina tace gashi hankalinta be gama dawowa jikinta ba., ta sake cewa yaya! yayana!kazo ka ceceni dan gani take kamar har yanxu a hannun afnan take.,momy tace salma bude idonki mana kiganmu ga inna tazo dubaki ga antynki sadiya ga sisternki husna kubude idonki kinji ba abinda zai sameki!"jin maganar su kawai take sama!sama kamar wani almara!. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 13 ==>Tasake bude idonta tafara ganinsu dishi dishi!.ta qara bude idonta sosai tana kalle kalle dan batasan a ina take bama. Wajen yayi mata wani kala ta kalli momynta tafara magana da murya qasa qasa kamar haka"momy nan ina ne?! momy tace asibity ne bakida lapia shine aka kawoki,!tai shiru jim kadan tasake cewa momy ina yaya Afnan!?momy tace yana nan zuwa..zakici abinci?ta girgiza kai tafara kuka a a momy dan allah kice masa karyaxo dan allah momy walh kasheni zeyi.,momy tai saurin cewa to kwantar da hankalinki zan gaya mishi dena kuka kinji"inna ta bude baki tare da cewa kaji wani shirme duk zafin ciwonne haka!inbada zafin ciwo afnan dinne zai kasheki!ta kalli momy tace Aisha anya kuwa yarinyar nan tana cikin hankalinta? kijifa surutanda taketayi tinda ta farka;momy tace inna zafin ciwo ne kawai zata warware insha Allahu,.inna sai qara shashshafata take itako tanata zare ido tana kalle kalle sai lokacin ta kula da qarin ruwanda ake mata.,sadiya da husna suka dubeta sukace sannu ya jikin batace komaiba tafara qoqarin tashi ta zaina nanfa taji qugunta yariqe gam ga wani masifaffen ciwon jiki.,anty sqdiya tace ko adagaki ne ta daga kai alamar eh., sadiyaa tazo da sauri ta dagota ahankali,.amma Ina jitayi bazata iya zama ba haka takoma ta kwanta;sai hawaye suka fara gararowa afuskarta da sauri anty sadiya tafara lallashinta tana goge mata ita kuwa husna tsaye tayi tana kallon ikon allah yadda taga salma lokaci guda ta rame manya manyan idanunta sun qara bayyana fuskarta yazama wani siriri lebenta ya bushe aranta tace lallai wannan ciwo yabama sis dinta wahala.,.alhaji abubakar kuwa haka suka dinga Neman afnan ko zasu ganshi akan titi amma babu shi babu labarinshi haka suka figi mota sai gida.,suna shiga palo wazasu gani afnan ne kwance ya daura hannuwansa akan qirjinsa ya miqe qafa daya ya daga daya fuskarshi na kallon sama!hawaye nata faman kwarara daga idonshi., sunyi tsarko tsarko suna kallonshi cikeda takaici ta wani bangaren kuma sunyi hamdala da ganinshi Abba yaqarasa yana fadin afnan wannan wani irin rashin hankali ne zaka gudo gida kazauna ciwo na cinka!hjy ta nemi waje tazauna tare da cewa kaimadai kafada.,yaxo ya kwanta ne yanata kuka kamar wani qaramin yaro to dukanka akayi taja tsaki..mtsww tindazu mukebin kwararo kwararo muna nemanka Ashe kai gida ka nufo kabar yan iska acen KO., Abba shikam harya karaya..yace haba kibarshi hakanan mana bakya ganin halinda yake cikine.! tace to mu kuma ai soyayi yajefamu atashin hankalinda yafi haka.yanxu daya fadi ahanya mota ta takeshi aimu yabari da baqin ciki., Abba ya dafa kan afnan yace my son me kakema kuka ko jikinne!?nan yaji jikin Afnan zafi kamar garwashi. Yace kinji jikinshi kuwa tashi mu koma asibity,.shigo dake kwance duk maganar da suke be tankaba saida yaji ance yatashi akoma asibity.,da Sauri yatashi ya zauna yana cewa Abba dan allah kabarni walh naji sauqi baxan koma ba,.Abba da umma sukace atafaf saiya tashi sun koma bazasu zauna suna kallo ciwo yakasheshi ba; fashewa yayi da kuka kamar wani qaramin yaro walh Abba idan kuka mayar dani mutuwa zanyi ni bazan koma ba,duk sai sukaji ya kashe musu jiki. Alhaji yace abarshi tinda bayaso zaije ya karbo masa magungunan sallama nan hjy ta kira momyn salma take fada mata afnan ya gudo gida,. Salma kuwa tananan tana masu kuka ita akira mata yaya Habib da yaya Ahmad suzo su kaita gida.,bashiri momy tasa aka kirashi! saigashi yaxo kamar Wanda yahawo jirgin sama.yana aikinshi a office daman hanklinshi yana wajenta saikuma yaji kira"momy dai tarasa yazatayi kar ahaifa danda ba ido!yaxo dasauri ya dagota murya a shagwabe tace wash yaya bayana ciwo da cikina yaya harda kaina ciwo yake'.saiga hawaye sun sake kwararowa: hankalinshi yatashi yace sorry sisterna waye yatabamin kene!;pls zaki iya gane fuskarsa dia kidaina kuka saina daukar miki fansa!;gayamin kinji zaki iya ganeshi?,!kuka ta sakar masa tare da cewa ba yaya bane..... ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 14 ==>momy tai saurin cewa aina gayama yayan naki karyaxo ba shikenan ba/Habib yai shiru daga bisani yace momy wani yayan take magana?tace uhm walh tinda tatashi taketa shirme nima narasa mezan mata ma;salma kuwa kallon maman nata kawai takeyi wai itace za ace tana shirme/kodai basu San abinda yaya afnan yai mata bane!;to amma idan basu saniba meyasa tagansu a asibity?kodai daman sun tafi sun barta ne dan yazo yai mata wannan Abu?! duk acikin zuciyarta take wannan tunanin"ya Habib ne ya katseta da cewa..qanwata kin ganeni kuwa?ta daga mishi kai alamar eh"ya na shirin jefo mata wata tambayar nan yakula Ashefa inna tana dakin kuma ya tabbata batasan halinda ake cikiba dan yasan baza a gaya mata wannan mummunan labarin ba!shiru kawai yayi ya dubi inna yace ke tsohuwa meran qarfe meya kawoki nan?'ta turo baki tace abinda ya kawoka/ ai natsayane naga iyakar gudun ruwanka tinda kashigo ko kallona bakayiba balantana ka gaisheni kana nan gurin qanwarka kaime qanwa ko"gaba daya sukasa dariya momy kuwa taji dadi da aka cenja fira dan duk hankalinta yatashi da irin tambayoyinda Habib kema salma!hararanda Habib yajefoma sadiya ne bashiri ta shanye dariyarta sanadiyyar faduwar da gabanta yayi. Tuni ta miqe tsaye takama hanya sumi sumi tai waje momy tace ina zakije?tace momy..zan.danje waje ne zafi ke damuna, momy tace zafi kuma AC akunne yake fa. Qara daburcewa tayi tace oh sanyi nakeso nace,momy tace eyya to dawo abinki bari akashe nima sanyin ya dameni.haka tadawo tazauna jiki ba qwari/tana daga kai suka qara hada ido da ya Habib yasake balla mata harara bashiri ta miqe zumbur harsaida momy ta kalleta sai cewa tayi momy zanje bayi ne yanxu zan dawo'/inna tai karab tace kinsan bayin zakije shine kikasa aka kashe mana AC dan gulma ko/ uhm kawai tace tafice abinda.momy tace inna kenan sarkin son AC,.sadiya kam zuwa tayi ta nemi guri tazauna akan wata farar kujera da aka tanadesu dan masu zuwa ganin Dr! Ta jingina kanta da bango hawaye suka ciko idanunta aranta tace meyasa yaya Habib yatsane ni?!wai yayshe ne zanyi abinda ze burge ya Habib"itadai tanason yaya Habib amma batasan laifinda tai mishi ba bayason ganinta;tabbas tana matuqar qaunarshi amma gashi tarasashi amatsayin mijin aurenta;hawaye zafafa suka dinga bin kumatunta wai yaushene zataga dariyar ya Habib?! Salma kuwa zamewa tayi daga jikin yayan nata ta hade rai ===>BUTULCI KO SOSO!!!,? Part 15 ==>yayi yayi inna kam tace ai dole saiya kaisu gida itada jikar tata husna'momy ma tace yayi haquri ya kqita sannan yawuce duk inda zashi"hakanan ya haqura suna shirin fita saiga Ahmad tare da sumayya sunxo aiko Habib yace shikenan maza kazo kakai inna gida allah ya ceceni. Yanxu office zan koma ana jirana kuma tace saina kaita gida.maza kakaita saika dawo.ko shiga beyiba yasashi yajuya sumayya kam shigewa ciki tayi abinta., inna dai tace oho dai koma menene.nidai akaini gida.,sadiya kam tagama cin kukanta taje toilet ta wanke fuskarta tace bari tadan leqa taga mamanta !tana bude daki taga wayam tace umma kuma tafiya sukayi an sallamesu ne amma bako sallama.ta juyo dukda tanajin tsoro taje taga ya Habib amma hakanan tadaure tace bari tashiga tagayama momy. Topa ana wata ga wata ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 16 ==>Salma tsce yaya kayima Dr mgana mutafi gida gobe yace to iyarigima zangaya masa! ammafa sai in kinacin Abinci sosai;ta tabe tabi tace yaya bakaga abincin danaci ba"yace nagani amma ki qara"mudai zamu wuce saida sfe! Momy tace Ku gaida gida suka fice abinsu, Abba yace salma anji sauqi sosai momy tace aikuwa alhmdlh!/yace to Allah ya kiyaye gaba kuma allah ya tona asirin duk Wanda yai mata wannan cutar ita kuma allah yasaka mata/momy da ya Ahmad sukace Ameen summa Ameen! Yace toni zanje nasami Dr arubutama afnan magungunan daya dace tinda yaqi zaman asibityn kuma ga ciwo nacinsa/ Momy tace oh haryanxu jikin ko",yace eh walh yanacen zazzabi yaqi sauka saidai yaita hawaye_momy tace to Allah yabashi lapia, Ameen Abba yace yafice abinsa.Salma tanata nazari cikin zuciyarta kome Abba yake nufi oho., to mema yasamu afnan din?! tambayar data kasa bama kanta amsa kenan.wato bayan yakusa kasheta shima ciwon yakamayi kenan! Wata qila ma da hadin bakin su momy. To amma yaza ai su momy suyi mata haka?!kuma meyasa idan tanaso tayi maganarshi momy ke tattarewa! gaskia akwai wani abu a qasa Ahmad ma yace momy zantafi sister allah yabaki lapia sai yaga ta fashe da kuka. Hankalinsu yatashi Ahmad yace sister lapia yaqarasa yace wani abunne ke miki ciwo?! cikin shagwaba da shashshekar kuka tace yaya daman da gangan su momy suka gudu suka barni yaya afnan yaxo yakusa kasheni..taqara fashewa da kuka ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 17 ==>Asuba nayi momy tatashi tai sallah nima tatasheni nayi sallah ta hadamin tie me kauri tabani nasha na qoshi 6 0 daidai Dr yashigo dubani ya cimmani inashan tie yanataimin dariya wai na warware haka yace to ya nakejin jikina nace mishi komai normal babu sauran wani ciwo nace mishi saidai banajin qarfi ajikina yace ba damuwa ahankali zanji daidai. Dr yace anjima da yamma zai sallamemu nan nafara murna nace mezai hana a sallameni yanxu yace sbd inada sauran allura yanxu zeyimin anjima zaimin sai a sallamemu momy ma tanata murna yaimin allura yafice abinsa. nan wani baccin yasake kwasheni. Wajen qarfe 8 0 saiga yaya Habib yaxo muryanshi ne ma yatasheni daga baccin danaketayi.sunata hira da momy ta fadamishi cewa anjima za a sallamemu. Ina tashi yaya Habib ya kalleni yace sister yau sai gida ko. Nadanyi murmushi na CE yaya yaushe kaxo? Yace tin daxu mana ke kinata bacci gashi mun tasheki ko. Na girgiza kai nace daman ngaji da baccin! Yace to nima yanxu zan wuce office anjima sai Ahmad yaxo yamaidaku gida idan nadawo daga office zanxo muyi magana kinji!.nace to yaya saikaxo. Yatashi yai sallama ya wuce abinsa. Momy taqara hadamin tie me kauri nasha nasha magani taje toilet tahadamin ruwan wanka tace nazo taimin Niko nace ban yarda ba saidai inyi dakai na. Tayi tayi haka ta haqura ta qyaleni. Naje nai wanka na yadda takemin gashin haka nima na daddage. Nayi inayi ina kuka idan natina yadda yaya afnan yaimin abin yanamin ciwo arai. Ina fitowa daga toilet momy ta gyara ko ina.nazauna bakin gado nafara shafa mai saiga aunty sadiya ta shigo tanata yimin dariya nima inayi mata tace rigimammiya harkin warke ko murmushi kawai nayi. suka gaisa da momy saika yaya Ahmad shima ya shigo ashe tare suke. Aka gaisa Momy nata tambayan dan autan NATA dan tayi missing dinshi gashi asibityn basa bari ana zuwa da yara da anxo mata da Khalid ta ganshi. Sadiya taxomin da wata doguwar rigana tace na cenja kaya daman wancen ta isheni momy tace Aida tabarshi ma dan yau za a sallamemu sunyi murna dajin hakan.momy tafadama yaya Ahmad yadawo anjima yadaukemu .wayar momy tai qara ta dauka tareda sallama Abba ne yakirata suka gaisa ya tambayi jikina mum tace ta sauqi anjima ma za'a sallamemu yace to alhmdllh daman innace tace dole saina kirawo mata salma taji muryarta yanxudai gata..yamiqama inna waya suka gaisa tace abani. Na karba nace hello inna tace me sunan mamana yajikin naki?nace naji sauqi Inna Dr ma yace anjima zai sallamemu inna yanxu aina fiki qarfima Tace rufaman baki kawai saiki kama ciwo yanxu dakin tafi kinbarfa. To zanxo gidan naku anjiman saikin fadamun dalili. Nai dariya nace shikenan inna saikinxo.namiqa ma momy wayarta suka qarashe firansu sukai sallama . Ahmad yai murmushi yace inna iyayen rigima. Yace amma momy yau dai kinsan dole yaya Habib zaixo yatambayi salma yadda abinnan ya kasance ko?! Tace tabbas kuwa nima tunaninda naketayi kenan.amma aiba wata matsala bane kawai cemishi zatayi ita batasan fuskar wanda ya aikata mata hakanba.yaya Ahmad furka a yamutse yace momy wai meyasa kikeson a boye maganar nan ne bayan abune me girma kuma kinsandai halin Abba ada ma baibari afnan ya auri salma ba bare yanxun dayake ganin an riga an dauke mutuncinta kuma baisan cewa afnan din bane toya abin zai kasance. Momy tai wani taqaitaccen murmushi tace Ahmad kenan kana manta wanene Habib ko to duk wani tashin hankali zaixo da sauqi akan yaji cewa afnan ne yataba mishi salma.dan haka dolefa sai anyi haquri amma idan mun koma gida akwai shawarar dana yanke insha allahu komai zaidaidaita. Ya Ahmed yace shikenan momy. Nida aunty sadiya kuwa bamuce affan ba illa dana sanya rigata na kishingida akan gado inajinsu harsuka gama.Ahmad yace Toni zanwuce sai anjiman zandawo nadaukeku.yafece abinsa Cen wajen yaya afnan kuwa daqyar umma tamatsa mishi ya karya yasha magani sannan yace zaixo yadubani umma tace ba inda zashi ai yanxu nafishi lapia shida aka kusa kasheshi sbd ni to ba inda zaije idanma zaixo din toyabari yaqarajin sauqi. Haka nan dai afnan ya haqura dukda ma dai yana tunanin da wuya zai iya tunkarata da nufin gaisuwan. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 18 ==>Qarfe 6 0pm likita yaxo yaimin allura dan harna fidda rai da sallama. Saida naganshi sannan naji sanyi amma saiyacemin wai yanxu yamma tayi sosai saidai gobe aiko nafara shirin kuka shine yace ai wasa yakemin ya bamu takardar sallama yanataimin dariya wai baby salm akwai rigima. Tsalle ne kawai banyi ba don murna dandai bazan iya tsllen bane amma da sainayi dan naqosa naganni a gida.aunty sadiya kam tin wajen qarfe 4 tawuce gida yaya Ahmad ma yaxo yaga ba a sallamemuba yawuce abinsa. Dan haka nace momy kawo wayarki nakira yaya yaxo ya daukemu tamiqomin na lalabo number dinsa nakira yana dauka nace yaya kaxo an sallamemu yadda nai maganar harsaida yabashi dariya yace to ganinan zuwa Ku kimtsa kafin na qaraso, Momy tafara shirya duk wani Abu damukaxo dashi. Jim kadan saiga ya Ahmad na miqe da izzana da danufin in ruga da gudu in riga momy shiga motar amma sai akasin hakan dan jinayi baxan iyaba tafiyarma da yaya aka qare dan banajin wani qarfi ajikina.dan haka nabi ahankali.nace momy nidai Ku sameni a mota ya Ahmad yace meyasa kika fasa gudun nace sbd kar mutane suyita kallona ne, yace kokuma bazaki iyaba ba kedin kinajin kunyan gudu ne. Nai murmushi na fice abuna. Ahmad yataimaka ma momy suka kwaso komai suka saka a both. Suka shigo mota muka kamo hanyan gida. nikam gani nayi ko ina yacenjamun. Muna isa gida su rufy da sumeey sai murna suka rugo da gudu suna oyoyo aunty tadawo. Khalid ya rugo ya rungumemun qafafu saida mukai kamar zamu fadi nidashi momy ta riqeshi tace gafara cen zaka kayarmin da yarinya wato ni inacen ina tunaninka amma kai ba tani kakeba ko.ta auntynka kake. Duk mukasa dariya gaba daya muka dunguma sai Palo tindaga qofa nakejin gabana yana faduwa muna shiga Palo qirjina yai wani mugun bugawa take zufa ya ketomin naji jikina yasaki idan ban nemi guri na zaunaba zan iya faduwa sbd ina ganin wajenda afnan ya danneni sai nakejin kamar yanxu abinke faruwa sai kallon wajen nake zuciyata fal da baqin ciki da qyar naja jiki dayan kujeran 3 setter na zauna momy ta kalleni tace lapia naga kinyi wani iri! Nace momy walh nagaji ne duk naji banajin dadi kuma kamarma bacci nakeji kinsan alluran nan tanasa bacci.tace eh gaskiya ne yanxu kiyi sallama tukuna saikici Abinci kisha magani saiki kwanta ko. To kawai nace su rufy duksun kewayeni wannan yace kaza wancen yace kaza. Aunty sadiya ta hada mana komai na Abinci mukai sallah mukaci Abinci nasha magani natashi nace ni yanxu zanyi sllahn isha'i. Dan bacci nakeji momy tce to Anty sadiya tatayani kwana inyaso gobe saita wuce gida.daman mamanta nata kira wai taqi dawowa kuma tasan afnan baida lapia kotaxo ta gaisheshi. Nidai ina sallah na sanya kayan baccina na kwanta.inna taso taxo a Daren saidai babu me kawota dan dole ta haqura. Ya Habib koda yaxo ina bacci dan haka ya bayyana momy buqatarsa nason in koma wajenshi. Momy kam tace batasan da wannan maganar ba babu inda zani.yayi yayi momy takafe akan babu inda zanje dan haka yace to shikenan amma gaskiya zaisa mana bodyguard dan bazai yiwu adinga abinmu agida ana zuwa ana lalata rayuwarmu ba. Shima dai daqyar momy tayarda dan saida Ahmad yasa baki a maganar. Haka yatashi yawuce jiki ba qwari domin kuwa shi yafison ya tafi dani wajenshi. Gari na wayewa saiga inna tareda husna tin duku duku dan mu bamu tashi bacci bama su suka tashemu. Muryar momy najiyo tana cewa inna kece da sassafen nan sannu da zuwa. Ina tashi toilet nashige nai wanka inna ta shigo dakin tana cewa ina me sunan mama saigani nafito ina dariya nace inna gani tace ah lllai sauqi yasamu nace ai daman na gaya miki yanxu zan iya karawa dake. Tazauna bakin gado nida nazauna surutunmu yatashi Anty sadiya tana tashi kuwa suka gaisa Kicin tanufa tafara shirya mana kayan breakfast. Inna tace ahada damu bamu karya ba idan mun karya zamu wuce gidan bukar dan Jiya yake gayamun Ashe afnan ma beji dadi ba zanje na dubashi.saida qirjina yabuga data ambaceshi nikam yanxu ina matuqar jin tsoron ya afnan. Sadiya ta kammala komai muna cikin break saiga ya Habib nan yasamu inna tanatamai surutun bashida kirki baya xuwa ya gaisheta nandai sukaita yan wasannin da suka saba. Suka gaisa da momy bai samu damar magana dani ba dai sbd ganin inna hakanan yawuce yace zai dawo da yamma.muna gama break inna tace husna taxo su wuce dan harmun shige daki nida ita munata hira dan haka inna tace to idan an gama meeting din afito mu wuce, momy tace inna kujira Anty sadiya mana Ku wuce tare. Inna tace bayan ko wanka batayi ba nibazan jirataba Aunty sadiya kuwa daman bason tafiya yanxu take ba.anma momy saida ta lallabi inna TAce anty sadiya tai maza ta shirya. Dan haka adaddafe tasamu ta shirya suka wuce Suna isaa.... ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 19 ==>Suna isa suka cimma su abba da umma a palo suna breakfast hjy ta miqe taqaraso da Sauri tana inna sannu da zuwa kune da safe haka Ku zauna. Suka zauna kan kujera inna Abba da umma sunata kwasan gaisuwa aunty sadiya tagaisheda momynta da abbanta. Husna ma cikin kunya ta dubi su umma da Abba tace ina kwana.sukadanyi murmushi tareda cewa lapia lau. Ya Maman naki?tace lapia lau. Inna tace ni banga afnan dinba ina yashige ne. Hjy tai dariya tace ai yana dakinshi nyi nayi ma yafito yaci Abinci amma yaqi sai abbanshi yaje tukun danni an rainani.inna tace toni barinje na ganshi daganan inyi lallashi. Sukai dariya inna ta miqe tace taso husna muje kinsan niba gane dakin nashi nake ba sosai. Akunyace husna ta miqe dukda dai itama tanason ganinshi amma tanajin kunyan su Abba. Haka suka kama hanya inatada inna sadiya kam tashi tayi tashige dakinta. Sun shiga dakin amma basuga kowa ba ga dakin duk ahargitse alamun andan jima ba a gyarashi ba. saidai sunji alamun watsa ruwa a toilet dan haka husna tace inna inaga yashiga wanka Ne ki zauna kan wancen kujeran mirror din nikuma indan gyara mishi dakin kafin yafito.yanadaga toilet yajiyo murya Amman yarasa gane ko waye.dan haka yaketa sauri yagama wankan. husna kam tanata faman gyara ko ina saidata ta kimtsa mishi tana cikin linke bargo sai gashi yafito dagashi sai dan gajeran wando da farar singlet gashi kwance a jikinshi kota ina. Tsayawa yayi bakin koqar yana kallonta kamar me shirin dukanta wani irin haushi yacikashi aranshi yace kya gama haukanki danni walh ko za'a kasheni ne bazan aureki ba saidai duk abinda zai faru ya faru tinda ga inna ma yanxu za'ayita ta qare. Yaqaraso bakin gadon ya zauna.ya kalleta ido cikin ido ta Sauri tai qasa da kanta batasan sanda ta saki bargon ba sbd tsabar kunyan dataji. Tsigar cikinta duk suka tashi. hannunta har karkarwa yake. Inna ta kalli afnan tace wannan wanka naka kamar ana cenja fata tin daxufa muke nan azaune.yai wani dan malalacin murmushi yace to Inna wama yabaku izinin shigomin daki duk kun hargiysamin daki. Husna tai dukta tsargu dan tasan da ita yake daqyar ta jawo jiki tadawo kusada inna Inna tace oh abinda zakace kenan dan an gyara maka dakin.to ai gobe ma rana ne. Husna tace yaya ina kwana?ko kallonta beyi ba saida inna tace bakajiba qanwarka tana gaisheka yace oh lfy.tace ya jikin?ya harareta yace wai cemiki akai banda lapia ne!? Inna tace oh Ashema lapia kake kasa muka taso tindaga gida mukazo gaisheka to aiko kaizaka maidamu gida.afnan yace inna ni daman inason ganinki dan akwai magananda zamuyi Tace to ina jinka.afnan ya kalli husna yace pls abamu waje ko. Sumui sumui tafice tai palo su momy sukace lfy harzaku wuce ne? husna tce a a inna suna magana da yaya ne. Afnan ya dubi inna yace inna dan allah ki taimakeni kisa Abba ya auramin Salma. Walh ni salma nakeso ba husna ba kuma salma tana sona kitaimaka kisa baki Abba yabarni na aura salma walh inna salma itace rayuwata yaqarasa maganar hawaye kamar zasu zubo a idanunsa. Inna tai ajiyar zuciya tace to afnan kasandai halin mahaifinka ba'a iya kaudashi akan abinda yai niyya indai ba wani ikon allah ba. Amma zanyi maka qoqari afnan nima nafisonka da Maman kasha kuruminka zanyima Baban naka magana kaji ko Afnan ya sauke numfashi ya dafa qafar inna yace kai inna dakin gamamin komai walh. Dan allah ki qoqarta dan walh idan ba'a auramun salma ba akwai matsala inna., Tace to kaita addu'a idan Allah yasa matarka ne saikaga anyi. Yanxu bari naje nasamu Baban naku muyi magana.. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 20 ==>Afnan yai saurin cewa a a Inna ba yanxu ba kobari saikin tafi gida saikisa akira miki shi yazo kuyi maganan.tace to shikenan zan kirashi.yanxu ya jikin naka?yace alhmdllh. Inna tace to ai saikaxo kamaidamu gida ko tinda kawarware. Yce to inna daman walh inaso nafita su Abba sun boyeni agida sun hanani fita. Yanzu bari nashirya na kaiki ammapa wancen qazamar bazata shigarmin mota ba.inna tace wacece qazamar afnan yace yar rakonki mana. Inna tace lallaima yaron nan husna dince qazama to aiko baka isaba saita shiga. Yai murmushi yanata shirinshi.inna tamiqe tace ina jiranka a palo tayo waje.shiko yahau shirye shirye yana gamawa yayo palo duk suna zaune hardasu aunty sadiya anata fira da Inna. Yana shigowa palon umma ta dubeshi tace maza kaje dining ga abincinka cen kuma kasha magani. Inna tace kaisauri kagama kakaimu gida inaso inyi bacci.,qarasawa yayi dining din yazauna Abba ko yace haba inna ai bashida lapia kibari idan zan wuce office saina saukeku.inna tace shikenan ma kaizakafi lallabani dan wancen be iya tuqi ba.yace to aini daman yanxu zan wuce kutashi kawai muwuce., Suka tashi itada husna suka bishi abaya Afnan kam jiyayi kamar ya hadiye ransa don bacin rai da takaicin rashin fitanda beyi ba.amma aranshi yace yau donene yafita kota halin qaqa saiyaje yaga salmanshi. Sadiya ta miqe zata wuce daki momy ta kirawo sunanta tsayawa tayi ba tareda ta waigo ba.momyn nata tace kinyima afnan din ya jiki kuwa?!juyowa tayi tace oh sry fa ya jiki afnan? Ji yayi wani dum kamar ta buga mishi dutsi akai.yace da sauqi aunty amma be iya hada ido da ita ba.ta juya abinta ta wuce dakinta. Kadan ya iyacin abincin yasha magani sannan unmansu tace nizan shiga inyi wanka kaima yakamata kakoma daki ka kwanta. Dasauri yace to umma.daman so yake tabar palon dan yasamu ya fice.tawuce abinta Shima yatashi yafice da saurinsa bema tsaya daukar mota ba yanufi get dasauri me gadi yataso yana gaisheshi tare da tambayanshi ya jiki..dan ko ba a gaya maka ba dazarar ka kalli afnan zaka tabbatarda yaji jiki dan yayi rama sosai.afnan yana fita ya samu me adaidaita sahu be sauka a ko inaba sai qofar gidansu salma.uhm afnan kenan baya ko tunanin me zaije ya tarar. Said a ya isa ne yasauka ya biya me adaidaita sahun sannan wani irin fargaba da tsoro ya fado masa yarasa ma yazaiyi ya shiga gidan kuma idan yashiga da wani ido zai kalli momy da salma. Shin meye mafita juyawa zaiyi ko kuwa dai Shiga zaiyi?! Su momy kuwa tinda gari yawaye gidansu cikin baqi yake yan uwa da abokan arxiki masu zuwa gaisheda salma., suna zaune a palo momy da salma sai Khalid sai hjy safiyya Maman husna sai qawarta sameera sunata fira salma tadan kashin gida akan kujera 2 setter Wanda yake person din qofar palon. su rufy da sumayyakuwa duk sun tafi school. Salma ta dube baki zatayi magana muryar data jiyo ana sallama ne ya datseta daga maganar da take shirin yi.tareda tsantsar fargaban muryar data ji. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 21 ==>Momy ne ta amsa sallamar tare da cewa wanene shigo mana.,afnan kam tsoro yahanashi shigowa sai wani dan maqe maqe yaketayi kamar mara gaskiya.koda yake daman Mara gaskiyar ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 22 ==>Momy ta juya da Sauri tafara buga qofar tana fadin salma lapia.!ki bude qofar mana! Qara lafewa tayi akan gadon momyn nata tana wani irin kuka me tsuma zuciya.! Suna jiyo sautin kukanta har palo. Momy ta juyo jiki a sanyaye ta kalli afnan tace masa afnan kayi haquri tinda tai ciwon nan abu kadan yake sata firgici nikaina narasa gane kanta kwata kwata. Yanxu katashi kaje gida kahuta dan kaima nasan bakajin dadin jikinka kawai qoqari kayi kaxo gashi kuma ansamu akasi yar uwantaka afirgice tace. Katashi ka lallaba kaje gida kaji! Hannu yasa a aljuhu ya ciro handkerchiefs ya goge hawayenda ke fuskarshi sannan ya miqi yace to momy barin koma Allah yabata lapia jiyawanda yayi ne ya kula Ashe ma basu kadaine a palon ba hjy safiyya da sameera sunyi jigum jigum sai kallon ikon Allah suke. Afnan ya sauri yakoma ya zauna sai yanxu yatuna Ashe be gaisheda kowa ba! Sannan ya sanda kanshi qasa yace momy na manta bamu gaisaba ina yini. Tace lapia qalau yajinka ya sadiya da gajiya. Yace lapia lau sannan ya juya yagaisheda hjy safiyya suka gaisa da sameera yai musu sallama ya tashi yafice cikeda jimamin abinda ya faru! , yana fita momy ta juyo ta cigabada kiran salma dan ta bude qofa amma shiru taqi budewa. Da Sauri momy ta nufi dakin salma ta dakko spare key din yakaye wajen salman taxo ta bude qofar tashiga. Su hjy da sameera duk suka biyo bayanta., salma na qwance ta kifa kanta a pillow momy ta zauna kusa da ita ta janyota jikinta taji jikin tana yadau zafi sosai tace subhanAllah salma zazzabin kuma dawowa yayi itakam ta runtse idonta kamar wata me barci.hjy safiyya ne tace nifa wannan Abu ya dauremin kai.ana cikin firq lapia kawai yarinya daga ganin mutum saita firgice kamar taga mutuwa?!momy tace kedai ganemin hanyan nima narasa gane kanta amma inaga kawai zafin tsiwonnan ne har yanxu be saketa ba. Momy ta dubi sameera tace dan Allah sameera taimaka ki miqomin place dincen da Kofi na hada mata tie,.sameera tace to momy bari zan hada mata dandanan aka hada mata tie daqyar momy tasamu ta bata sannan tabata magani bacci ya kwaaheta. Nan su hjy sukaima momy sallama kowa ya watse ,zuwa cen saiga su rufy driver ya dakkosu daga school! Suna zuwa sukai dakin salma momy ta dakatar dasu da cewa kar Wanda yasake yashiga batajin dadi tasamu bacci kuma zakuje kutasheta. Haka suka tsaya duk basuji dadi ba sudai kwanan nan duk gidan be musu dadi abokiyar firansu ba lapia..suka nufi dakinsu suka cire uniform dinsu sumayya tashiga kitchen ta debo musu Abinci suka baje suka kama ci., Afnan kam daqyar ya iya kaiwa gida yashiga palonsu yana dangadi kamar Wanda yasha ya bugu.yana buga qofar palo yai sa'a kuwa aunty sadiya tana zaune tana kallo tataso tabude batace mishi qala ba ya wuce sashensa yana zuwa yafada kan gado kamar Wanda akaiwa duka! Umma tafito daga daki tace ma aunty sadiyA wai har yanxu yaronnan bedawo ba kuma anata kiranshi yaqi dagawa. Anty sadiya tace umma yanxu yashigo daman yanzu zanza nafada miki yadawo. Umma batace komaiba tanufi sashensa ranta a bace. Tana zuwa ta fada dakinshi yai saurin juyowa danganin Wanda yashigo tazaun ta dubeshi rai ahade tace ina kaje baka iya gayamun zaka FIta ba?inace ma wai ba abbanku yace karkaje ko inaba!? Afnan yace to umma yanxu shikenan ni bazan fitaba saidai naita zama agida kamar mace yaqarasa maganarashi ashagwabe.harsaida yabama Umma tausayi tace to ai kozaka fitan saika bari kaqara samun sauqi ko!yanxu dai bari akawo maka abinci kaci kasha magani. Tamiqe tai kicking ta kamo masa abinci daqyar tasamu yaci haka taita lallashisa kamar qaramin yaro. Ranar dai haka ya yini daga tunani sai kuka rayuwa ta juya masa baya. Misalin qarfe 6:30mp saiga yaya Habib yaxo yasamu salma tanata bacci nan yai sallah sukaita fira da momy rufy da Khalid duk sun baibayeshi sunatamai surutu. Sumayya kuwa tana gefen momy. Sai ganin salma sukai ta shigo dakin sumui sumui ta nemi waje ta zauna akan kafet dinda Habib ke zaune ta lafe jikin kafadarshi kamar me shirin yin kuka. Ya kalleta cikeda kulawa yace sister lapia kuwa waya tabamin ke duk naganki wani iri ne!? Tai wani irin gajeran murmushi Wanda zamu iya kiranshi da yaqe tace yaya ba komai. Yace haba sister kifadamun gaskia mana! kinsan banason naga kina damuwa naso na daukeki ki koma gurina momy ta hana amma ba komai yanxu haka nasamar muku bodyguard gobe insha allahu zai fara zuwa dan haka ki kwantar da hankalinki insha allahu babu abinda zaisake zuwa ya cutarda rayuwarki ki natsu ki manta da komai kinji my dia sister kinga kunkusa fara exams dan haka ki maida hankali akan karatunki Allah shizai saka miki kuma shizai tona asirin duk wani me nufin cutar mana dake kinji KO!, Runtse idonta kawai tayi sbd hawayenda ke qoqarin gangaro mata bata iya cedashi qala ba. Momy tai ajiyar zuciya tace ai inaga exam dinnan ma da wuya idan zata iya har yanxu jikinta be wani qwari ba gashi kuma batason cin abinci. Ya Habib yace to kingani ko sister keda kiketa murna zaki shiga ss3 amma bazaki dage kidinga cin Abinci kisamu lapia ba. Yanxu yaushe ne exam din naku?! Sai lokacin ne ta iya bude baki tai magana tace ranar Monday ne"yace to kinga ashema jibi ne lallai kuwa idan kika tsaya sanya za a tafi abarki idan kuwa kin dage dakun gama exam zan cenja miki makaranta zan maidaki Turkish kuma zan samar miki driver dazai dinga kaiki yana dawo dake. Da sauri tamiqe daga jikinsa tana murmushi harta manta da damuwarda take ciki tace momy ina abinci nah!?.kafin momy tace wani abu Sumy tai tsalam tace to yaya ni kuma pa?"tareda turo baki kamar alade ya hangi kashi....! x ===>BUTULCI KO SO!!!? Part 23 ==>Gaba dayansu suka kwashe da dariya salma ta dubeta tace kedai kishi kike to saidai ki mutu dan yarinya bazanyi makaranta daya dake ba. Yaya Habib yace to duk ya isa haka kema idan har kika dage sosai zan kaiki duk mkarantar da kikeso kinji yar autan mama! Ta tabe baki cikin shagwaba tace yaya nima Turkish din nakeso asani"kafin tagama rufe baki salma tace aiko baki isaba walh yaya saidai asamar mata wani".ya dubesu yace to duk Ku kwantar da hankalinku kowa za'a sashi a inda yadace banason rikici kunji"rufy tace Dady muma axenja mana! Murmushi yayi yace wato abin naku yazama qasa kenan ko;to duk an fasa tinda abin hakane kowa ya zauna a inda yake!.ya dubi salma ya daga maya gira alamun karta damu sannan yace kije kici abinci kisha magani kinji ko.ni yanxu zan wuce gida"yasa hannu a aljuhu ya ciro kudi ya miqama kowa nashi sannan yaba momy nata Wanda itama batasan ko nawa bane sannan yatashi yai musu sallama ya wuce. Salma tatashi tai dakinta taje tai sallah sannan ta tashi tawuce dining taga an shirya komai kowa yaci iya cinsa.!aranta tace lallaima anraina komai saida akaci aka rage me makon atasheni duk an barmin kwantai" Haka nan dai ta tuttura tinda tanajin yunwa kuma ga abinda yayanta yace mata. Tana gamawa momy tazo tabata magani tasha sannan tace bari taje tai wanka ta kwanta. Tashiga toilet ta watso ruwa sanna ta nemi wani riga da wandonta na bacci tasa ta haye gado. Sai lokacin tunanin wayarta ta fado mata. To inama ta jefa wayar?! Saita tuna Ashe fa lokacinda tatashi daga bacci taga bataga su sumayyaba wayarta ta janyo ta kunna data ta hau WhatsApp tana cikin chatin taji jikinta duk babu dadi sbd tagama period kuma batai wanka ba dan haka tace bari taje tai wanka Wanda shine sanadin fadawanta hannun afnan. Kuma tindaga nan batasake ganin wayar nata ba.itadai tasan akan gado ta ajiye to kowaye yadaukar mata waya oho!? Tambayar da takasa samun amsarta kenan. Dan haka ta diro daga kan gadon ta nufi dakin momy tana zuwa kafin tace wani abu sumayya tace dama kin koma dan yau bazan kwana a dakinki ba"tsaki kawai salma tayi tace angaya miki ke nazo kira to dakixo da karkixo duk daya yarinya! Sannan ta kalli momy tace momy wayanafa waya daukarmin.? Tai murmushi tace sai yanxu aka tuna da wayar kenan"to aiko nima bansan inda take ba. Ta marairaice tace haba momy pls ina aka kaimin walh nayi missing frnd dina kuma data na a kunne yake za aitamin magana pls momy kibani. Momy tace to aini ban dauka wayarki ba. Amma ki tambayi auntynki sadiya dan naji tace tagani kuma ta adana miki.amma bansan yadda ta ajeba saidai kibari saitaxo., Tab!tai shiru tana yan waige waige saita hango wayar momynta akan wardrobe da Sauri ta dauka tahau lalubo numbern Anty sadiya" Momy tace mezakiyi.? Tace zan kiratne mana inji yadda ta ajemin., Momy tace ohh lallai kura tayi lapia. Tana kira kuwa taci sa'a tana kusa. Tce hello aunty ina yini' Lapia tafadi tana dariya tare dacewa lallai qanwata lapia yasamu"salma tadanyi dariya tare da cewa Anty daman zan tambayeki ne ko kinga wayana! Tace aiko lokacinda na kwana dakinki na ganta kasan pillow kuma na dauka nasa cikin handbag dina da safe na manta ban baki ba sbd tafiyar danayi ba shiri su inna na jirana shiyasa na manta ban baki ba kuma na taho dashi gida. Amma daman ina shirin gobe zanxo naqara dubaki saina taho miki dashi., Salma bataji dadi ba Amma saitace shikenan Anty saikinxo din"sukai sallama ta kashe ta dubi momy tace toni zanje na kwanta.,momy tace sumayya maza kitashi kibita kuje Ku kwanta sumayya ta turo baki zatai magana momy tace ba magana nake miki ba'haka nan tatashi badan taso ba salma kam hartayi gaba tare da cewa dolenki dakixo ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 24 ==>Asuba nayi hjy taxo ta bugama Abba qofa ya bude tace alhj kayi sallah kuwa. Yace eh nayi shigo daman inason magana dake. Taqaraso suka zauna bakin gado, Sannan ta gaisheshi. Abba ya dubeta yace hjy jiya kinsan Inna takirani tace eh. Yace to bayan naje shine inna take gayamun wai lokaci yayi dazan hada yaran nan Afnan da salma aure. Bayn na nuna mata qin amincewan hakan inna tasa kuka da sauran maganganu wanda bakai ba tushe tatayarmin da hankali intaqaice miki zance bandawo gida ba harsaida nai mata alqawarin hadasu aure. Yaci gaba da cewa To kuma kinsan wannan lamari bamai yiwuwa bane shiyasa tindaga jiya hankalina atashe yake narasa mafita. Da nayanke shawarar fada mata abinda yafaru da salma! To amma nayi tunanin halinda inna zata qara saka kanta aciki shiyasa nace bari dai ngaya miki yanxu mene ne mafita!? Hjy tai ajiyar zuciya daga bisani ta dubi Abba tareda cewa. Toh nidai alhj dazakaji shawarata anawa tunanin wannan ai abin farin ciki ne kuma rufama juna asirine. Yanxu idan akace salma wani bare zata Aura kaga dole ne sai an fada mishi abunda yafaru da ita kuma wannan kamar cin zarafine da kuma tonan silili. Idan ba tayi dace da miji me sonta bane yadinga mata gori kenan., akan abinda itama bada sonranta bane tsautsayine kawai ya hau kanta. To Amma yanxu kaga afnan shi yasan abinda yafaru da ita kuma har yanxu yana sonta ahakan. To alhj kaga zaifi mana rufin asiri sai ayi tuwo na maina kenan. Ammapa ni anawa tunanin kenan. Wani irin kallon rashin fahimta alhj yake mata. Yace wato ke har yanxu kina nan akan bakanki kenan. Yaci gaba da cewa Daman nasan abinda zakice kenan.sbd daman cen abinda kikeso kenan. To Amma idan da kinson wannan hadin yanxu yakamata ki cenja ra'ayi sbd bakisan qatonda yai mata fyade ba. Yanada cutar qanjamau ko bayidashi. Wannan duk be dameki ba. Ke baruwanki da lafiyar danki. To idanke kina ganin wannan hadin me yiwuwane gwara ma ki cenja tunani. Ke ko tunanin yadda aka wulaqanta miki yarinya ba kyayi. To kisani bazan taba bari a kashemin yaro ba. Shi kadai Allah ya bani na miji kuma nabari azo a goga mishi cuta. Towai shiyace miki ma har yanxu yana sonta. Ai shidinma ba mahaukaci bane. Juya kanshi yayi yai wani dan gajeran tsaki... Mtsw...tare da cewa keda akace kibada shawara kinxo kina wani fadin abinda bazai yiwuba. Sadda kanta tayi qasa tace Allah ya huci zuciyarka..Amma alhj ai shawaran na bada bawai nace ayi dole bane. Kuma kace kayima inna alqawari akan zaka aura mishi salma. Sannan na tabbata afnan shiyasamu inna yace tai maka magana domin Jiya bayan fitanka shima yafita. Na tabbata hakanan inna bazata taso da wannan maganarba saida izinin afnan. Kaga kenan har yanxu yanason salma!. Taci gaba da cewa. Ni nasan daman soyayyarsu da salma bazai iya gudunta akan wannan abun daya sameta ba. Kuma ya burgeni. Sannan Wannan shine lokacinda yakamata ya nuna mata shi masoyin gaskiya ne. Kuma zai iya kasancewa tare da ita a kowani hali. Yanxu sai kayi tunani. Danka dai yanason salma! Kai kuma kayima Inna alqawarin hadasu aure! Sannan wannan abun alfaharine agaremu. Kuma rufin asirin zuri'armu ne. Sai kaje kayi tunani ni iyakan abunda zan iya fada kenan. Amma ka gafarceni idan na bata maka rai. Gaba daya jikin Abba yai sanyi da irin maganganun umma. Saidai har yanxu yanajin bazai iya bari Afnan ya auri salma ba" To amma ya zaiyi da inna!?yakasa samun wannan amsar.dan haka ya dubi umma yace shikenan na gode! Ni yanxu zanshiga wanka ayi qoqari agama hada break kafin na fito. Umma tamiqe tace to alhj saika fito. Bata zame ko inaba sai kicking nan taga aunty sadiya tanata hada abincin break. Ta gaisheda momyn nata sannan tace umma ai nashiga dakinki zan gisheki ban ganki ba.nace ko kina dakin Abba ne shine kawai nataho kicking nakama aiki dan yau inaso ne naje gidansu salma. Umma tace eyya aiko yakamata kije kidubata kam, Nima yau naso tambayan Abbanku zuwan .to amma banga fuska bane dan yau ranshi abace yake kuma hankalinshi a tashe yake. Jiya inna tatayar masa da hankali. Aunty sadiya ta ware ido tace topa wani abun yai mata ne!? Umma ta yamutsa Fuska tace kinsan dai halin abban naku. Wai tataso mishi da maganar auren salma da afnan ne wai dole saiya hadasu Aure. Shine ya nuna mata beyarda ba. Shine ta dinga mishi kuka hankalinshi yatashi har saida yai mata alqawarin hadasu aure. Shine yau yatashi da bacin rai wai yaza'ai ya aura mishi yarinyarda aikaima fyade be sani ba kota kamu da wata cutar. To shiyasama nakasa tambayarshi nabari saiya huce. Gaban anty sadiya saida yai wani mugun bugawa. Amma ta wani bngaren kuma taji dadin wannan maganar. Dan kuwa shiyafi kowa dacewa da aurenta. Bai cuceta a banza ba. Dan haka tace tohpa yanxu momy yaza'ayi kenan" Tace oho nidai nabashi shawara idan yaji shikenan. Aunty sadiya tace to umma Alllah yazaba abinda yafi alkairi! Tace Ameen dai. Yi Sauri kigama kimtsawa dan yanxu zai fito yayi break ya fita. Umma ta fito tazo palo tadan kashin gid'a akan kujera. Abba kam yana gama kimtsawa beyi wani jinkiriba ya nufo palo anty sadiya tana tsaye tana shirya abinci akan dining ta duqa ta gaisheshi ciki ciki ya amsa da ganinsa kasan yana cikin damuwa. Yace sadiya maza kije ki kirawomin afnan yataso yanxu inason magana dashi. Tace to abba. Ta nufi sashen Afnan tafara buga qofa. Shima lokacin ne yasamu dan bacci ya kwasheshi, kamar a mafarki yaji ana buga qofa. Ahankali ya bude ido yana sauraron ko Zaiji an qara. Yaji anci gaba da bugawa. Daqyar ya iya tashi jikinsa ko ina ciwo yake haka yaqaraso bakin qofar ya bude. Aunty sadiya yagani ta jefo mai wani harara shiko yace ina kwana. Bata amsa ba tace Abba na nemanka yanxu kuma. Ta juya abinta bata saurari me zaice ba. Tana zuwa tace Abba yana zuwa. Abba na zaune akan dining umma ta zuba mishi abinci Amma ba abinda ya iya ci. Saiga Afnan ya fito jiki a sanyaye yaxo ya zauna akan Capet Ya dubesu yace umma ina kwana. Tace lapia lau ya jiki.? Yace da sauqi. Sannan yace abba ina kwana. Wani irin kallo yajefo masa me cike da alamun tambayoyi!.ba tare da ya amsa gaisuwanba. Cikin zafin murya yace AFNAN..! Firgicinda yayi saida qwaqwalwarshi da ruwan jikinshi duk suka dena aiki. Tsoro da fargaba suka ziyarci zuciyarsa.! Muryarshi na kyarma yace Na'am Abba. Abba yasake jefo masa wani hararan daga bisani yace. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 25 ==>Afnan kabani kunya. Ban taba tunanin zaka watsamin qasa a ido ba. Wai harkayi girmanda zakaje kahadani da inna akan salma ko?.to kasamu yadda kakeso. Domin kuwa tayi abinda kasakata. Kuma zan Aura maka salma! Amma kasani duk abinda yafaru dakai kai kaja ma kanka tinda kai bakasan ciwon kanka ba. Baka kishin abinda akaima yar uwanka . Dan haka zan Aura maka salma!kuma babu saki atsakaninku har abada. Sannan nacire hannuna akanka kaje kai duk abinda kaga dama. Afnan kansa na qasa ya dago kannshi ahankali idonsa sunyi jawur ya kalli Abba kabinsa na karkarwa yace Abba..walh..ni...kafin yaqarasa tuni Abba ya daka mishi tsawa..get out kabacemin da gani. Banason ganika agabana. Agigice ya miqe kamar zai kifa sbd Sauri. Umma ne ta kira sunan Afnan"tsayawa yayi cak! batare da ya waygo ba. Sannan taci gaba da cewa haba alhj dan Allah ka sassauta mishi mana., baka ganin shima ba lapia ne dashi ba. Abba bece mata komai ba ya miqe yadauki jakarsa da keys din mota yai waje fuuuu! Batareda yaci komai da aka Zuba mishi ba. Ganin Abba ya fice afnan ya juyo ahankali ya iso dining din yadda umma ke zaune yaja kujera ya zauna idanuwanshi cike fam da qwalla. Umma ta dubeshi tace Haba afnan kakwantar da hankalinka kariga kasan halin babanku. Fushi yayi kuma zai huce nan bana jimawa ba. Kuma ni ina bayanka 100 bisa 100. Naji dadin abinda ka yanke na taimakon yar uwanka. Kuma karka sake kace zaka kalli abinda akaima naka yar uwan domin kasamu hanyan musgunama salma. Dan kuwa ita babu laifinta aciki. Inamai farin ciki da wannan lamari domin rufin aairinmu ne gaba daya. Dan haka ka kwantar da hankalinka ka qyale alhj. Yanxu dai kaci Abinci kasha magani kaga sai rama kakeyi duk kabi ka lalace. Nan dai taita lallashinsa har saida yaci ya qoshi. Daman shi babban damuwarshi shine abba yaqi amincewa. Amma tunda sai ya amince komai zai faru me sauqi ne. Suna cikin firansu. Saiga aunty sadiya tafito ta fesa kwalliya tayi masifar kyau. Doguwar riga tasa na atanfa ya zauna daram ajikinta taqaraso gunsu cikin takunta irin na qasaita. Sannan taja kujera ta zauna gamida janyo kulan Abinci tana qoqarin zubawa tace umma Abba harya fita ne. Ta gefen ido kuwa wata irin harara ta dinga aikawa afnan din.umma tace eh yanxu yafita ko break dinma beyi ba. tace to umma nima na shirya yanzu zanci abinci ne na wuce. Umma tace to idan kinje dai kice ina gaisheda me jiki kuma insha Allahu nima gobe ina nan zuwa dubata. Afnan zai kawoni shima daganan ya dubata. Saida suka kalli juna aunty sadiya da afnan. Sannan yai qasa da kanshi cike da kunya da fargaban abinda Umma tafada. Sadiya taci gaba da cewa toh umma zasuji insha allahu,. Afnan ya miqe yace to aunty ki gaisheta. Tai kamar batajishi ba. Yakama hanya yai dakinsa. Aunty sadiya ma tatashi taje daki ta dakko jakarta da takalminta Wanda sukai macing da kayan gamida sa hijjab dinta taima momy sallama ta fice. Salma kuwa yau tatashi ta qarfinta domin tanajin qarfi ajikinta sosai. Sauqi dai yasamu da izinin Allah. Kwalliya kuma yadawo sabo!!.Tsaye take gaban mirror tana taje gashinta yadda ta sakeshi abaya, gamida dakko wani siririn hula Wanda macing color ne da kayan datasa tsakiyarshi a bude yake. Ta gaban hulan kuma an rubuta (love is life!) Riga da sket ne ajikinta Wanda yaya Habib yayo mata tsaraba daga Dubai. Sunyi matukar amsar jikinta. Tayi masifar kyau Wanda ba'a magana. Ta sanya wannan hular gamida fito da gashin ta tsakiyar hulan. Ta qara duba mirror sannan tasaki wani murmushi Wanda yasake bayyana tsantsar kyawunta gamida lumshe ido domin it a kanta ta burge kanta. Palo tayo tana tafiyarta a nutse tana isowa palo kafin takaga zama tajiyo sallamar aunty sadiya nan tatsaya cak! Aunty sadiya tana shigowa ta aika mata da wani irin qayataccen murmushi tuni Anty sadiya ta ware idanu gamida fadin. Woww!!! Sister irin wannan kyau haka ai saikisa inyi rangaji in fadi aqasa. Taqara sakin mata murmushi sannan ta ruga ta rungumeta tana fadin kai aunty ai kinfini hadewa. Taqara dubanta tace kai!!waneni da had a kaina da matar manya. Wannan ai dole kidinga furgita maza irin wannan kyau haka"Ammapa kar karki ya fashe kidauka wai kinfini kyaune. Kin wani zabga jan baki kamar yar hayin kogi. Gaba daya suka kwashe da dariya. Salma tace to aunty ni duk ba wannan ba ina wayana!toce kwantarda hankalinki gata a jaka. Ta karbi jakar tana kokuwan budewa. Saiga momy tafito tana dariya tace kudai bakwa rabo da barkwanci Indai kuka hadu. Dariya kawai sukayi salma ta ciro wayarta tayo daki tafada kan gado aunty sadiya kuwa nanta baje suna gaisawa da momy. Tin kafi tacire wayar a key take ganin saqonni daban daban messages miss call WhatsApp.!dan haka tarasa ina zata fara dubawa. Saita yanke shawarar bari tafara shiga whatsapp tana shiga saqonwa zata fara gani..uhmn..saida gabanta yafadi dan jitayi kamar yana kusa da itane zai kamata. Afnan ne yai mata sqo har gashi biyu..hannunta na rawa ta danna ta shiga ga abinda saqon farko ke dauke dashi...Amincin Allah shi tabbata agareki yake yar uwata kuma abar begena a kullum. Na kirawayarki baki pecking ba bansani ba ko kina bacci ne. Daman ba komai bane inaso na fada miki ne daman zanxo anjima in kawo muku ziyara kigaya momy kuma ki shiryamun kayan dadi kinji my dear sister!! Lallai fa afnan an shirya maka kayan dadi irin Wanda baka zata ba kuma kaci ka qoshi..!! x ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 26 ==>Da wani dogon tsuka. Mtswwwwwww!!!.gami da cewa...!Allah shi kyauta in Auri mugu! Ai ko maza zasu qare aduniya bazan taba aurenka ba sbd na tsaneka tsana mafi girma.!mugu kawai"! Tana turawa tai blocking dinsa. Amma mezai biyo baya!? Tunanin baya ne ya fado mata! Kalmomin da tafada masa abaya suka dinga dawo mata kamar anyi recording dinsu. Tabbas ta fada masa wasu kalmomi. a gurin da take zaune. Kuma a irin wannan yanayin na baqin ciki,. Lokacinda take zubarda hawaye. Zuciyarsu ke tsananin azabtuwa da son juna!. take masa iqirarin cewa....Haba yayana walh hannuwa na bazasu taba iya yin blocking dinka ba. Kayi hquri bazan iya aikatawa ba. Kamar yadda bazan iya guje maka ba. Haka baxan iya daina sauraronka ba. Idan kai zaka iya yin blocking dina to ina me baka daman yin hakan. To amma kasani Kunnuwana bazasu taba gajiya da sauraronka ba. Zuciyata bazata taba daina azabtuwa da sonka ba. Sannan a kullum zan kasance cikin baqin cikin rabuwa dakai. Idanuwana bazasu taba daina son ganinka ba akoda yaushe. Alqawari ne na dauka bazan taba auren wani namiji ba aduniya idan bakai ba. Ashirye nake dana rayu dakai ako wani irin hali ni bazan taba guje maka ba. Ina qaunarka yayana qauna irinta har abada.! Kayi haquri yayana walh bazan iyaba"hannuwana bazasu iya blocking dinka ba. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 28 ==>INNA..ki..taima..keni muryarta na rawa! Shi kanshi afnan yai matuwar rudewa da furgita tsoronshi daya karta fadi ta sume kamar yadda tayi lokacinda yaje gidansu. Dan haka yai miqe shima akidime yake fadin SALMA!SALMA Dan Allah ki natsu ki natsu kinji pls SALMA! Yana qara matsowa shima jikinshi barin yakeyi,. Haka take qara Ja da baya tana fadin INNA..kin ganshin.. KO.. Daidai nan ta tokare da qofa tai wani irin qara yayinda yaqaraso a guje ya ruqota alokacinda take qoqarin kifawa. A daidai lokacin daya ruqota taqara sakin wasu tagwayen ihu gamida kuccewa ta fada cinyar inna ta qanqameta sosai tana tsusa kanta a tsakankanin Inna,! Gaba daya mamaki ya hana inna cewa komai ganin jikokin NATA sun afka wani irin yanayi na rudu Wanda takasa fahimgarsu., batasan sanda tafara fadin."LAPIA!LAPIA meyake faruwa ne!? Salma kuwa qara qanqameta take tana fadin Inna kaina ne kaina inna! Cikina..ke..inna ta katseta da cewa meya samu kan naki? Afnan yanajin haka be tsaya yayi wata wata ba ya zari takalmarsa yabar gidan da saurinsa. Dan yasan idan yazauna abin saiyafi haka. Inna ta daqo tana qwala masa kira amma inaaa dan talikin yayi nisa! Dawo wa tayi kan salma taci gaba da cewa wai me kuke nufi ne daganinsa kin fara kuka shi kuma ya gudu gudu. Kin sakani cikin wasu wasi. Wani irin sanyi salma taji aranta alokacinda ta waigo ta tabbatar da cewa afnan baya palon. Miqewa tayi batare da taceda inna komai ba ta kwanta kan kujera domin har kanta ya fara ciki ga wani zazzabi dayke niman kamata. Inna tai juyin duniyar NaN akan salma tafada mata gaskiya amma ta dake akan ita kanta ne da cikinta kawai yake mata ciwo.! Haka ta gaji ta rabu da ita tace ai idan tai tsami maji . idan kuma Auren ne bakwaso ai sai inji. Salma tai saurin tashi ta zauna gamida cewa wani rin aure kuma.! Inna ta galla mata harara tace irin na uwaki! Dole takama bakinta tai cit! Tadan huta nawasu yan daqiqu tatashi tace zata wuce. Domin ita kam yau bataji dadin zuwanba ma. Daqyar tasamu ta isa gida tana tangadi jiri take gani sosai dan haka tana zuwa ta zube akan kujera jikin nan NATA ya dafe yayi zafi rauu! wasu zafafan hawaye ne keta sulalo mata. Momyce tafito daga sashenta gaqaraso wajenta da Sauri tana fadin salma lapia kuwa!meya sameki?!. Tana kai hannu jikinta taji zafi rau!tace subhanallah zazzabi kikeji haka kuma shine baki gayamun ba"bari nakawo miki Abinci kici nakira driver muje asibity. Momy ta qwalama sumayya kira saigasu sun fito dukkansu aguje suna dariya. Ganin salma a kwance yasa sukai tsuru tsuru momy tace ma sumayya maza kije ki zuboma auntynku abinci batajin dadi ne. Ba musu ta wuce kicking sai gata dauke da pleat din kuskus taxo ta dire ma momy sannan taje firji ta dakko robar faro daya ta kawo momy tace to tashi kici.! Taqarayin wani narai narai da ido tace momy cikina ciwo yake. Momy tace kiyi haquri kici koda kadanne. Haka tatashi momy tafara bta abaki. Bai wuce cokali 4 tayi ba kawai sai amai momy ta tallabota da sauri haka ta dinga kwara amai duk jikinta yai yaushi. Momy kam duk ta rude tasamu ta kwantar da ita sannan tamiqe dasauri taje ta kira habib tafada masa halinda suke ciki sannan taxo tafara gyara wajen.!ba a dauki lokaci ba habib ya turo da driver. Aka kwashesu sai asibity. Suna zuwa aka karbesu cikin kulawa kasancewar habib yayi waya tun kafin su iso..Dr ya dubata sosai tareda wasu yan tambayoyi itakam tadinga jera mashi amsa. Tagaya mishi cewa takai 2weaks tana fama da ciwon ciki kadan kadan. Sannan takanji tashin zuciya lokaci lokaci ga yawan ciwan kai. Dan hak Dr yasa aka debi jininta da fitsarinta sannan yahada musu wasu yan magunguna dazai taimaka mata yace suje gida tafara sha kafin su dawo gobe a tabbatar da result din da aka samu.! Momy bata kawo komai aranta ba"sabanin ni da harna fara wani tunani! Kaji iyayen katslandan ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 29 ==>A dimauce momy ta miqe tana Innalillahi wa inna ilaihirraju'un Dr karufamun Asiri jikinta ko ina fari yake. Yayinda ni da Dr muka saki baki da hanci da ido duk muna kallonta.! Mamakin Dr shine shin meyasa momy ta furgice haka shin bata bataraba da qaruwanda suka samu ne ko kuwa" Mamakin salma kuwa shine.. Wani irin ciwo ne juna biyu dahar momy ta furgice haka take Neman faduwa.! A tsorace ta kalli Dr tana qoqarin yimishi tambayar wani irin ciwo ne take dauke dashi.! Kafin ta kaiga cewa komai sai ganin momy sukayi ta sulele aqasa sumammiya!. A haukace salma tai kanta tana kwarma ihu tana fadin Dr wani irin cutane nake dauke dashi har baqin cikinshi yake Neman ya kashemin mahaifiya" Shima gaba daya yagama kidimewa yayo kan momy yana fadin kawai nace mata ne kinada ciki shine tashiga tashin hankali haka!? Ko bakida Aure ne dai! Allah dai yasa ba abun kunya kika daukoma iyayen naki ba. Cikin wata irin murya salma ke cewa Dr cikin baby nakedashi!? Yanxu baby ne acikina taqarasa maganar tareda shafa cikin! Dr yace qwarai kuwa kina dauke da juna biyu har na tsawon wata uku babu yan kwanaki!" Ai kafin yagama rufe bakinshi sai ganin salma yayi ta kife a qasa da alamun itama suman tayi.! Topa Dr yaqara rudewa matuqa da Sauri ya fice yana kiran nurse kamar wani zararre. Dan Danna akaxo aka kwashesu gaba daya aka basu gado. Duk iya qoqarinda zasuyi akansu sunyi Wajen 2 hours Amma basu farfado ba Dr duk ya gama rudewa da al'amarinsu. momy ce ma tadinga tafarfadowa tana sake sumewa."dan Haka Dr ya kira Habib ya fada masa abinda ke faruwa. Karkuso kuga daburcewa wajen Habib dan shima kadan yarage ya sume. Dan Haka numfashinsa ke fita wani kan wani. Baccin yayi ta maza da shima kwasarshi zq'ayi. A kidime ya suri motarshi ya kama hanyar asibityn yana rafka gudu kamar wanda ze tashi sama.! Allah ne dai ya kiyayeshi harya isa lapia. Yana isa ya kira Dr. Dadauri yazo suka qarasa yanda su momy suke daidai lokacin momy ta farfado sukayi ido hudu da Habib kawai saita fashe ta kuka. Yaya Habib yaqarasa gabanta shima idonshi sun kada sunyi jawur. Yace momy dan Allah ki kwantar da hankalinki ki natsu kar hawan jininki ya tashi. Pls momy komai ze wuce. Murya a sarqe momy take magana tayaya hankali na zai kwanta wannan balq'i ya afko mana ta Ina zan samu kwanciyar hankali. Kawai tasake fashewa da kuka shima kifa kanshi kawai yayi yana zubda hawaye. Saida sukayi mai isarsu sannan momy ta juyo tace ina salman take!? A hankali ya dago da idonsa jawur yace momy tana nan ita bata farfado ba Drs sunacen suna qoqari akanta. Gashi kema kinsa damuwa sosai aranki momy ta wanne kikeso muji. Momy ki dauka wannan Abu kawai hukunci ne daga Allah kuma babu yadda muka iya saidai haquri mu rungumi qaddara. Momy tafara qoqarin tashi yaji bazata iyaba haka ta koma tana zubda wasu zafafan hawaye. Nan Dr yaxo yafra duba momy. Jininta har ya hau sosai akai mata allura tasamu bacci. Habib yakira Ahmad yafada mishi abinda ke faruwa. Tab! Haka ya tawo asibityn a fusace da nufin komai ma zai faru to saidai yafaru dan yau saiya fadama yaya Habib Wanda yaima salma fyade. Cen bangaren su hjy safiyya kuwa gidan yacika da murna domin yaune ranar da yaya Aliyu zai dawo. An tanadar mishi girki kala kala. Husna ma datake kwance batada lapia yau daida ta gyagije sbd murnan dawowar yayan nata. An tura driver yaje ya daukoshi a airport tare suka wuce da husna akabar momy da inna A gida. Basu wani Dade da zuwaba jirgin nasu ya sauka. Ya kira wayar husnan tace yaya gamu nan a waje nida driver kai muke jira .yace OK to ganinan fitowa. Cen husna ta hangoshi yanata faman waige waige itako sai washe baki take tadaga waya ta kirawoshi yana dagawa tana yaya gashinan INA kallonka yace to ai ni.... Kawai daiya hangota tanata dariya da saurinsa ya karaso shima fuskarsa dauke da murmushi. Tace ya ya Aliyu kaga yadda ka qara kyau kuwa gaskiya garin nan ya karbeka. Yasaki kyakkyawan murmushi Wanda yaqara bayyana tsantsar kyawunsa gamida cewa yar Autar mama kenan. ai ni naga duk kin cenja munne gaba daya ma. Nida na barki yar qarama kina 8years. Yanxu ko shekarunki nawa ma oho. Ta murguda baki tareda rangaji dakai tace kai yaya shrkarun nawa ne ma zaka manta KO. Yai dariya yace to yar rigima wasa nake miki. Amma ga dukkan alamu kinyi ciwo dan naga kamar akwai rama a jikinki. Tandan murmusa tace yaya kenan ya akai ka gane. Yce ko Wanda be taba ganinki ba idan ya ganki yanzu yasan kinyi ciwo. Tace gaskiyarka ne yaya walh yanxu ma zuwanka ne yasa na warware sbd murnar ganinka. Yace wayyo yar Autar umma meyake damunki. Uhm kawai tace labarin me tsawo ne yaya yanxu dai muje gida ka huta Suka qarasa mota suka shiga suka dau hanya. Sun fara tafiya Amma gaba daya yakasa daure Abinda yakeso ya tambaya dan Haka yace yar Autar mama wai ina qawarki ne na dauka tare ma zakuxo tarbana sai kikazo ke daya!. Tadan jiyo ta kalleshi tareda cewa wa kenan! Yadanyi farii da idonsa gamida cewa Salma mana!. Tace oh kacemin Amarya! Dandanan dariyarsa ta tsaya ya daure muska yana mata wani irin kallon rashin fahimta cikin sassarqewar murya Wanda bemasan yayi ba yace ban gane Amarya ba!?. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 30 ==>Husna tace Eh mana! Yaqara hade rai yace Wato Aure akai mata ban sani ba.! Husna tadanyi murmushi tace kai yaya maida wuqar ai ba'a riga anyi bikinba ma daman ance saika dawo!. Yadanji sanyi kadan aransa sannan ya sake cewa to waima salman ne za'aima aure tun yanxu! Wayema ya fada miki haka!? Tace kaidai yaya kanada qosawa kabari idan munje gida zakaji komai. Yace kinyi alqawari tace eh yayana na kaina.! Haka yahaqura badan ranshi yaso ba dan yaqosa yaji gaskiyar abinda husna tafada. Ya qosa yaga ankai gida. Sun isa gida cikin qoshin lapia murna kota ina. Inna kam bakinta ko rufuwa bayayi. Ya Aliyu yaje yai wanka yaxo dining amma duk cin abincin ya gagareshi inna dasu momy da husna duk sun kewayeshi. Cikin hikima yace Inna wai mamanki batasan zan dawo bane?! Inna tace oh Mamana Amarya ai rabona da ita tun ranarda sukaxo nan da afnan sunataimin sakarci! Yana qoqarin kai cokalin abinci bakinsa baisan lokacin daya aje ba yana fadin Wani irin Amarya kuma Inna! Tace kaidai ci abinci koma wani iri ne ai zakaji. Gaba daya yaji ya qoshi dan haka yamiqe tareda sakin wata yar tsaki mtsw..saiku cinye abincinku ai.! Gaba daya suka bishi da ido dan sun gaza fahimtarsa. Momy tace A a inazakaje bakaci abincinba yace nifa nama qoshi tin a jirgi. Tace abincin jirgin wani abun kirkine! To dawo kazauna ko zakayi amai ne saikaci abincin nan bazamuyi wahalar banza ba. Murmushi kawai yayi me kama da yaqe yakoma yazauna yacigaba da tsakurar abincin. Ya kalli husna yace wai meya samu wayar salma ne baya shiga! Tace walh nima bansani ba tinda tai ciwo ba'q samunta awaya bansani ba ko wayar baya hannunta ne.! Oh tai ciwo amma ko agayamun KO! Gaba daya sukasa dariya sbd yadda yai maganar kamar wani qaramin yaro! Inna tace kaji shirme banda abinka idan an gaya maka zuwq zakayi. Yace amma ai nakira waya nai mata sannu ko! Anandai suka gama yan ciye ciyensu da firarsu kowa yanufi makwancinsa domin dare ya tsala" Wajensu momy kuwa Habib ne yadawo gida ya kwashe su rufy yakaisu gidanshi.!fadila tayi tayi yafada mata meke faruwa Amma yace mata kawai momy ne batajin dadi; sannan yakoma asibity cen suka kwana shida Ahmad. Yaya Ahmad tinda yaje yaga halinda momy ke ciki yakasa gayama Habib gaskiyar lamari dan gudun qarya hurama abin wuta.! Momy tadan samu sauqi dan qin zama tayima agunda aka ajeta takoma gun salma saidai takasa daina kuka duk in ta kalleta. Salma ta farka amma batasan inda take ba har yanxu likitoci ne ke zarya akanta. Sai fizge gizge take. Hakan yaqarasa jinin momy ya hau sosai haka suka kwana ba barci. Habib ne zaune akan darduma bayan ya idar da sallah yayi jugum yana tunanin abinda Dr yafada!. Idan har kunason tayuwar yarinyar nan to mafita daya CE! Kodai azubda cikin nan kokuma a nuna mata cewar kuskure akayi wajen fadar sakamakon!sannan kuje kucigaba da lallashinta kuna nuna mata mahimmancin yarda da qaddara! Sbd idan ba haka ba. duk ranarda ta fahimci da gaske ne"zata iya shiga halinda yafi na yanxu. Domin kuwa me ciki ba'asonta da damuwa hawan jini zai iya kamata tun tana yar qaramarta. Dan Haka ko wanne daga cikin abinda kuka zaba me hadarin gaske ne! Wasu hawayen baqin ciki suka gangaro masa. Aransa yace Tabbas dazaiga Wanda yaci mutuncin qanwarshi da babu abinda zai hana ya shaqeshi harsai ya mutu" Wayarshi tai qara ta katseshi daga tunaninta ya fada. Aliyu ya gani da numbernshi ta Nigeria ya dauka da Sauri gamida yin sallama! Ya aliyu ya gaisheshi cikin ladabi sannan yace yaya.. Hafin yagama fadi ya Habib yace yaushe ga dawo ne babu kodan sanarwa! Yadanyi murmushi gamida cewa walh jiya nadawo aina dauka mama ta fada muku zan dawo! Yace kai baka fada mana ba sai ita" yace to babban yaya afwan yanxu dai ya madam yasu momy! Y Habib yai shiru yama rasa abinda zaice.! Daga bisani yace uhmm Aliyu walh gamu nan ma A asibity salma da momy duk basuda lapia! Cikin tashin hankali yace subhanallah meya samesu!? Cikin rawar murya yaya Habib ke magana. Zan gaya maka Amma gidanku babu Wanda yasani Inna bata saniba momynku ba bata sani ba! Dan Allah karka fadama kowa dan kasan inna zata iya tada hankalinta hawan jininta yazo yatashi! A rude ya Aliyu yaci gaba da cewa fadamun nayi alqawari bazan fadamasu ba! Ya Habib yacigaba da cewa fyade akaima salma kusan wata uku dasuka wuce. Sanadiyyar barinta da akayi ita kadai agida wani mugun yasamu damar zuwa ya aikata lalata da ita! A wannan lokacin salma tasha wahala sosai kwananta 3 a asibity aka sallameta! Shine yanxu akai gwaji akaga tana dauke da ciki sanadiyyar haka ne Itada momy suke kwance yanxu haka salma batasan yadda kanta yake ba!" Tinda aliyu yake bai taba shiga tashin hankali irinna yau ba! Daga lokacinda yaji kalmar fyade yayi tsananin gigicewa Wanda bai ma iya fahimtar me Habib din yaci gaba da fadi ba"wani irin juwa yafara dibarsa Allah yasa akan gadonsa yake! Shin wai mafarki ne yake! Ko kuwa gaske ne abinda kunnuwansa ke jiyo masa! Masoyiyarshi"abin qaunarshi" wacce yadade yana tarairayar soyayyarta" Wacce yarayu da tsananin qaunarta tun kafin tasan kanta! Wacce yake burin tazamo uwar yayansa" Jinin jikinshi Salmat ita akaiwa fyade harma tana dauke da ciki!?" innalillahi wa inna ilaihirraju'un. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 31 ==>Cikakken labari...! Alhaji Suleiman shine Babban d'a awajen inna sai Alhaji Abdullahi sannan Alhaji Abubakar Wanda a yanxu suke kira da Abba! Haifaffun yar Kaduna ne. su uku Allah yaba Inna kuma duk maza. Bayan rasuwar mahaifinsu wato malam sani. Inna ta koma wajen babban 'd'anta da zama wato alhaji sulaiman. Shine yacigaba da daukar nauyinsu" bayan rasuwar malam sani da shekara1 Allah yadauki rayuwar alhji sulaiman wajen tafiya tafiyan neman halak da abinda zasuci a hanyar tafiyarsa lagos ne yai Accident Allah yakarbi rayuwarsa! Lokacin yanada matarshi daya hajiya Safiyya da 'ya'yansu biyu" wato Aliyu da husna. Tsakanin aliyu da husna akwai tazara sosai dan harsun fidda rai dasake samun haihuwa dan shima aliyu sun jima basu sameshi ba!.cikin ikon Allah saiga cikin husna anyi murna sosai!" Husna tanada shekara 5 aduniya mahaifinsu yarasu. Daga nan alhji abdullahi shiyacigaba da daukar nauyin gidan harda dawainiyar makarantar Abubakar har yakammala karatunsa'! alhj abdullahi yanada matarshi me suna hjy Aisha wacce suke kira da momy sunada yaransu hudu4 Habibullah Ahmad salma sumayya! Habib shike gaba da aliyu Dan yabashi wajen 6years sun taso tare jininsu ya hadu sosai! Alhaji Abdullahi shiyaci gaba da qoqari har Abubakar yasamu aiki" lokacin ne yasamu matarshi mai suna zainab" cikin ikon Allah tasamu ciki ta haifi santaleliyar yarinyarta wacce aka rada ma suna sadiya! Lokacin habib nada shekara 10 a duniya aliyu kuma Nada shekara 4". Bayan 2years aka haifi afnan aka sa mishi sunan mahaifinsu aliyu!..wato Suleiman. Shine ake kiransa da afnan.! Cikin ikon Allah habib kammala secondary school dinshi aka turashi maleshia acen yayi degree dinsa yadda yadawo amatsayin Cikakken engineer.! Lokacinda yadawo ne yayi daidai da lokacinda sadiya ta kammala secondary school tanada shekara 17" afnan kuma yana Ss1 shekaransa 15. An haifi salma da husna yanda shekarau8 aduniya! Kwana 4 salma tabama husna domin a jejjere aka haifesu" salma tun tana qaramarta sun shaqu sosai da afnan idan yaxo gidansu dagyar ake banbareta daga jikinsa!. Yaya aliyu ne ma basu wani saba ba hasali ma tsoronshi takeji danshi yanada fada kuma bayason yawan rigima. Saidai yana masifar tattalinta bayason yaga wani Abu dazai bata mata rai"baya sati baixo yaganta ba tareda tsarabar kayan ciye ciye, Ranar wata Saturday Abba da dadynsu salma suna zaune a palo yadda yakirashi domin tattauna wani muhimmiyar magana.! Dady ne ya dubi Abb yaci gaba da cewa..!. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 32 ==>Ba komai yasa na kira ka ba illa wata alfarma danake nema kuma nake ganin yadace mu qara qulla danqon zumunci! Ina nema ma Dan wajena Habibu auren yarka sadiya domin na yaba da nutsuwarta kuma na tambayi yaron nan yafitomin da wacce yakeso Amma ya nunamun shi babu wacce yakeso shiyasa nace toni zan duba mishi wacce tadace kuma naga babu wacce tadace dashi kamar sadiya. Dan haka ina nema mishi Aurenta idan har babu Wanda takeso! Murmushi kawai Abba yayi Wanda zamu iya kiranta da yaqe gamida cewa Gaskiya yaya naji dadin wannan maganar ai wannan basai kanemi shawarata ba dan kuwa sadiya yarka CE kana da damar zaba mata mijinda yadace da ita ballantana kuma wannan yaro me hankali kuma dan uwanta" Ai kaima me bashi ne basai ka nemi shawarata ba! Dady yai murmushi cike da jin dadi yace a a wannan ai haqqinka ne yazama dole na nemi amincewarka kuma naji dadin yadda kakarbi maganarnan yanxu saika sanarma iyalinka kuma a tambayi sadiya idan ta amince. Nima zan sanarda iyalina kaga idan komai ya daidaita ma basai ankai abin da nisa ba" yaqarasa maganar tareda qurama Abba ido! Abba yadan sosa qeya yace gaskiyane yaya ai dama ka yanke ranar Auren kawai tunda babu wata matsala nidai daga gareni." Dady yace a a baza'ai haka ba a duki kakkin yarinya gwara anemi amincewarta dan Bazanso arakura mata ba. Abba yace shikenan yaya za'ayi yadda kace amma nasanma babu wata matsala" Nizan koma yaya duk yadda mukayi zakaji". Dady yace to yayi kyau nagode sosai Allah yabar zumunci. Abba yace nikeda godiya yaya. Tareda miqewa sukai sallama ya nufi gida zuciyarsa cike da wasuwasi! Lokacinda Abba yasanarma umma maganar tayi farin ciki sosai haka ma bangaren su dady momy tayi farin ciki matuqa kuma tabada goyon baya Dari bisa dari! Saidai kuma a bangaren gwaskayen babu komai sai tarin damuwa Dan Kuwa habib hankalinshi yayi matuqat tashi a lokacin da yaji za'a hadashi da sadiya! Danshi gani yake an rainashi da wannan yar tsigigiyar yarinyarne za'a hadashi. Saidai kuma haka nan ya daure ya amince da zabin iyayensa batareda ya nuna qin amincewarshi ba. A bangaren sadiya ma haka. Dan tayi kuka kamar ranta zai fita dan ita bawai sonshi ne batayi ba Amma tana matuqar jin tsoronshi dan bata cika ganin dariyarsa ba, Tunaninta kawai ta yaya zata zauna da yaya Habib!" Ba'a jima ba aka tsayar da biki sati2 tunda aka sa ranar bakin bata sashi a idonta ba sai ana sauran kwana3 yazo shima a daddafe yake tambayarta nawa take buqata Wanda zatai hidima. Tace mishi bata buqatar komai. Besake cemata komai ba ya Ciro check din dubu dari biyar ya miqa mata.! Ta Amsa tareda dubawa ta ware ido gamida cewa yaya ai wannan kudin sunyi yawa babu abinda zanyi dasu! Shiko gogan naka harya juya baya yana shirin barin wajen yatsaya cak batareda ya juyo ya kalleta ba. Sannan yace..! ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 33 ==>Sannan yace idan kinyi Abinda zakiyi ki zubar da sauran.! Ya wuce abinsa yana qoqarin Ciro keys din mota a aljihun wandonsa! Yaqarasa cikin nutsuwa ya bude motarshi yacika rigarsa da iska. Inda yabarta nan tsaye a Gardine riqe da check din daya bata! Wasu zafafan hawaye ne suka cika idonta fal! Suna qoqarin gangarowa. A zuciyarta tace yanxu A haka ne zamu zauna toya zanyi kenan idan aka kaini gidanshi?! Tasa mayafinta ta goge hawayenda suka wanke mata fuska. Sannan ta shige cikin gida cikeda tunani iri iri. Ranar Saturday aka daura auren sadiya da habib . yan uwa da abokan arziki an taru sai murna ake! Kasancewar shine Wanda yafara yin Aure a gidan.; shiko Habib ba wata gayya yayi ba dan dayawa abokansa ma be sanar musu ba. Dan shidai a tunaninsa wannan ba Aure yake ba nan gaba dai zaiyi Aure. Ankai amarya dakinta. Gida yayi kyau sosai ba yabo ba fallasa. 4bedrooms ne akwai babbar Palo ga fadin tsakar gida. Daga cen wani bangare kuma Swimming poll ne da dan bukka wajen shan iska !. Bayan biki da 1month Aliyu yafara shirin barin qasar zai tafi qasar waje a cen zai kammala karatunsa! Dady shiya dauka nauyin komai"lokacin su salma da husna zasu shiga Primary1. A lokacin da zai tafi ne ana gobe yaxo gidan su salma yima momy sallama. Yana Zaune a palo suna gaisawa da momy salma tadawo daga school ta shigo da gudu da fada jikin momy tana fadin wash momy nagaji INA abincina" Kafin momy tace wani abu muryar yaya aliyu taji ya daka mata tsawa.. Ke bakyajin magana karyata zakiyi ne!? Shiyasa nakeson Sumayya da tafiki sanin yakamata. Da Sauri ta zame daga jikin momy gamida juyowa ta bata rai ta dasa mishi manya manyan idanuwanta masu kwantar da zuciya. Ko qiftawa batayi. Tana turo baki. Saida yadanyi murmushi acen cikin ransa! tabbas yana tsananin son wannan kyakkyawar yarinyar Allah dai yabashi ita yafada a cikin zuciyarshi!. A zahiri kuwa qara hade rai yayi gamida dubanta yace. Ke bakida kunya ni kike murgudama baki ko? Momy dai sai dariya take musu daman sun saba wannan diramar . aiko yana tafiya ta fara surutai. Walh ni momy yaya Aliyun nan haushi yake bani sai yaita ma mutane fada. Da yaya afnan ne yaxo baya maun fada! Momy tace to ai kece ba kyaji shiyasa yake miki fada. Tace to kawai dan nahau jikinki shikenan seyace in sauka. Ni gara ma yatafi yaba mutane waje yaje Cen taita musu fadan. Momy tace tafi cen rufemun baki. Wato har ma so kike yatafi ko. To bazai tafi dinba. Tashi kibani waje marar kunya kawai ba yayanki bane.! Wucewa tafi tana kumbura baki. Shiko yaya Aliyu daga nan gidan ya Habib ya nufa .saidai be sameshi ba dan Haka ya yanke shawarar kiranshi a waya ko kuma ya tura mishi text dan kuwa akwai muhimmiyar maganan dayakeso yafada mishi. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 34 ==>Haka kuwa akayi yana isa gida ya kirashi a waya suka gaisa yace Babba yaya naje gidan ka bansameka ba. Daman naje ne nai maka sallama. Nandai sukasha fira suna shirin yin sallama ne ya aliyu yadan Sosa qeya yace yaya daman... Sai kuma yafara uhm..uhm.. Daman.. Yaya Habib yace mene ne kuma kaketa wani uhm.uhm. kafadamun mana. Yadan fara kame kame sannan yace daman.. Yaya..wata alfarma nake nema.! To fadamun mana mene ne inji ya Habib kenan! Yaci gaba da magana yana sassarqewa kamar wani marar gaskiya. Daman..yaya..so So... nake ka kulamun..da salma.sosai. kafin nadawo pls! Ya idasa maganar yana shafa qeyarsa!. Yaya Habib ya fashe da dariyar da be shirya yinta ba. Cikin dariya yaci gaba da cewa shine kaketa wani inda inda kamar wani me koyon magana! Kawai dai kacemin kana ciki." To ka kwantar da hankalinka kamar kayi baquwa ta mutu! Zan kula maka da salma Kana dawowa zan baka abunka!. Sanda kansa qasa yayi kawai jikeda jin kunya kamar yana gabanshi. Tabbas yaji dadin yadda yayan nashi yayi saurin fahimtarshi. Nan yaya Habib yaita tsokanarshi harsukai sallama. Washe gari jirginsu ya daga. Yatafi da tsananin farin ciki Dan yasan cewa a yanxu salma tazama tashi duk sanda yadawo Za'a aura mishi ita. Bangaren Amarya sadiya kam zaman babu dadi dan yaya Habib gasata yake kamar waina. Kullum cikin kuka take Amma takasa gayama kowa abunda ke faruwa! Babban abunda yake qara qona mata rai idan ta tuna shine.. Ranar Daren farkonta yadda Yaya Habib yaxo mata a bushe babu ko dan kazar nan da ake kawoma amare Babba abin baqin cikin ma yadda yaxo bako kunya ya tumurmusheta yai mata hawan qawara babu wani alamun tausayi haka yai mata jage jage saida yaga bata numfashi. Sannan washe gari ma haka yasake yimata akan raunin jiya. Haka ya jera kwana7 be daga mata qafaba HQ ya kumbura yai sasul gashi batasan yadda zatayiba ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 35 ==>A kwanakin da salma tayi gidan aunty sadiya ita kanta ta fahimci ba dadin yayan nata takeji ba. Dan kuwa wata zubin a gabanta yake balbaleta da fada kokuma tayi abu ya gwasaleta. Tun aunty sadiya tana boye mata har yakai abin yawuce a boyeshi dan salma tagama fahimtar komai. Hakn yasa sadiiya tadena wani boye boye ta kirata daki ta lallabata tace kota koma gida karta sake tagayama wani cewa basa zaman lapia da yaya habib. Salma dai ranta baiso ba dan taso taje tabaiwa momy labari. Kwanan ta 4 a gidan tace ita gida zata koma ta gaji. Aunty sadiya bata so hakan ba dan tana rage mata damuwa sosai! Haka taci gaba da zama cikin kadaici ta takura da rashin samun kulawa wajen yaya Habib. Tana shirye shirye komawa karatu dan ita dama harta qosa tafara zuwa makaranta ko zata huta da jarabar yaya Habib. Kawai saita fara laulayi. Yaya Habib ne yakaita asibity akai treatment dinta aka tabbatar mishi tana dauke da ciki wata2. Murna wajen yaya Habib ba'a magana" dan shi Allah ya jarabceshi dason yara. Dahar yafara tunanin ko juya ya auro sbd ya qosa yaga jininsa! Tun daga ranar ya Habib yafara tattalinta aiki ma yahanata yi. Idan yaxo yaga tana wani abun shizai karba yacigaba dayi ko kuma suyi tare.! Ita kam harga Allah taji dadin wannan cikin dan ya gyara zaman takewar Auren su. Itace har take ganin dariyar yaya Habib. Ta kwanta jikinshi tayi bacci yana tarairayarta tai amai ya wanke. Tai mishi shawaba ya rarrasheta. Wannan abu yana mata matuqar dadi.! Dan ita harji take kamar ta zauna da cikin" dan haka taita addu'a Allah yasa suci gaba da kasancewa cikin farin ciki haka."dan a yanxu ji take tana tsananin qaunar mijinta. Wani irin soyayyace me qarfi ta dasu a tsakaninsu. Lokacin da cikinta ya cika wata7 ya hanata aikin komai abinci ma saidai a kawo mata daga gida! Idan yadawo wajen aiki qarfe6 bashida aiki saidai ya zauna ya kwantar da ita a yalwataccen qirjinsa yaita shafa cikinta yana rada mata kalamai masu kwantarda zuciya. Cen bangaren su salma kuwa duk in akai Hutu gidan aunty sadiya take zuwa har akoma makaranta. Saidai takan qosa tadawo wata lokacin sbd afnan yana zuwa musu firan dare Gashi tanajin dadin fira dashi Shiyasa idan bata ganshi ba kwana2 batajin dadi. Shima kanshi wata lokacin binta yake cen wajen aunty sadiya idan sukasha firarsu sai ya wuce gida. cikin sadiya nada wata8 su Afnan suka fara shirye shiryen tafiya school shida ya Ahmad. Inda Ahmad ya wuce sokoto. Afnan kuma ya wuce Libya. Salma tasha kuka sosai tafiyarsu. Shima kanshi afnan daurewa yayi. Haka ya rungumeta yanata rarrashinta tareda yimata alqawarin zai dunga kira kullum suna gaisawa ta wayar momy. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part 36 ==>Bayan wasu kwanakai da tafiyarsu afnan aunty sadiya ta haifi santaleleyar yarinyarta kyakkyawa yar blackbeauty yarinya son barka kamarsu daya da babanta saidai shi fari ne ita kuma black beauty ce irin mamarta. Murna kuwa wajen yaya Habib kamar ze hadiye babyn. Haka akasha shagulgulan suna inda yarinya taci suna Rufayda suna kiranta da rufy. Inna ce tazo ta zauna da ita. Su aliyu Ahmad afnan duk an kirasu an fadamusu sunata murna. Ranar suna akaima rufy wani hadadden hoto aka tura musu. Tunda aunty sadiya ta haihu salma ta dawo gidan ta tare satinta2 ta saba da Rufy sosai gashi yau zata koma gida dan haka taketajin ba dadi. Sanda yaya Habib zai mayar da ita gida ne bayan sun shiga mota fuskar nan tata a hade. Ya Habib ya dubeta yace yayadai yar rigima! Za'a fara rigimar ko" ta tabe dan madaidaicin bakinta ashagwabe tace yaya nidai banason tafiya nabar rufy. Yace to ai momy ne tace a mayar dake"nace tabarki tace a a! Tace to yaya dan Allah ka sayamun waya kullum na dinga kira inajin kukanta kaga momy bazata bani wayarta ba. Muguwa wato so kike tadinga kuka kenan ko. Yafada tareda jefa mata harara cikin sigar wasa" Murmushi tayi wanda bata shirya yiba ta dora da cewa to yaya nidai inason inji kuma idan inason abu zan kiraka nafada maka basai nataba wayar momy ba" To shikenan zan saya miki hankali ya kwanta!? Dariya ta saki gamida lafewa a kafadarsa wayyo yaya naji dadi Babba zaka siyamun KO. Ya Habib yace eh Ammapa idan naga zai hanaki kara2 qwacewa zanyi. Tace naji. Suka kama hanya saida ya tsaya a wani blazer yasai mata galleliyar wayarta HTC! Sai murna take kamar ta lashe yayan nata. Suna isa gida da gudu ta shige tana kiran Sumy..!Sumy..!Sumy..!momy CE ta fito tana Haba wanan kira haka kin fado ma mutane.cikin gida babu sallama. Saiga sumayya ta fito tana mammatse ido da alamun itama bacci take. Nan suka baje a palo salma ta fitoda waya. Momy tace Sam bata yarda ba za'ayi aba salma waya yar shekara11 nandai Habib yaita lallaba momy harta amince Amma tace baxata dinga tafiya dashi school ba. Nan Sumy tafara gungunai wai itama sai ansaya mata. Salma kam sai gwalo take mata. Habib ya lallasheta yace qyaleta naki ma sai yafi nata kyau sabon fitowa zan saya miki. Nata kuwa tsohon yayi ne. Nandai tasaki jikinta harda dariyA. Tun daga ranar kullum sai salma takira aunty sadiya taji kukan rufy daman yaya Habib ya sai mata layi ya cika mata da kudi Wanda ze Dade mata. Sannan ana bada hutu cen take zuwa taita raino! Suyita fada da inna daman itake zaman jego. Haka kuma su yaya Ahmad da yaya afnan sukeshan kira sukansu sunsan salma tayi waya.! Ya aliyu ne kawai bata kira saitace shi yacika fada. Koya kira yace abata su gaisa qin karba take. Tana zuwa school ta labartama qawarta sameera ai yaya Habib yasai mata waya. Itama nan tace aiko zataje gida sai babanta ya siya mata waya. a bangaren zaman takewar sadiya da habib kuwa. wani abun mamakin shine.. UTULCI KO SO!!!.? Part 37 ==>Tunda aunty sadiya ta haihu yaya Habib ya daina tattalinta idan kaga yana rawar jiki to babynshi ne ke kuka. Wani abun ma dan inna tana gidanne yake raga mata. Dan har marinta yatabayi akan wai tabar rufy tana kuka. Tsangwama dai iri iri. Dan kyawun jegon nan ma bata wani yi ba. Kullum cikin zullimi take. Ashe daman ya habib ba ita yake tattaliba babynshi yake tattali. Tunda tazo duniya kuma shikenan ita tazama shara. Saidai tai kukanta tagaji tashare hawayenta. Suna yin 40 inna ta tattara inata inata ta koma gida. Yanxu kam kowa yafara fahimtar sadiya ba tajin dadin ya habib .momy ta kirasu tare tai mishi fada sosai kasancewar tayitayi sadiya tafada mata gaskiyar abinda ke faruwa amma taqi. Dan haka taita mishi nasiha akan yariqe yar uwanshi amana idan ya cutar da ita kanshi ya cutar domin shima nan gaba za'aima nashi. Yadan rage mata wasu abubuwan Amman dai babu wata soyayya da yake nuna mata. Idan kaga yana dan lallabata to wani Abun yakeso a wajenta. Rufy Nada shekara1 ya habib ya hadu da wata yarinya me suna fadeela acen qasar India suka hadu lokacinda yaje gudanar da wasu harkokinsa. Ita kuma a cen take karatu. Fadeela tunda ta qyalla ido ta ganshi taji tana matuqar qaunarsa dan haka ta jajurce harsaida tasamu zuciyarsa. Fadeela fara ce me matsakaicin tsayi yar siririya tanada manyan idanu. Cikin dan qanqanin lokaci ta samu zuciyar yaya Habib. Daman shi irin matar da yakeso kenan wayayyiya yar boko wacce ta iya karairaya da lanqwasa. Asalinta yar Adamawa CE iyayenta Fulani ne. Babanta me kudin gaske ne tanaji da kanta sosai gashi an shagwabata. Komai takeso shi iyayenta ke mata. Rayuwarta gaba daya a qasar waje tayishi. In taqaice muku dai ya Habib shida yajeyin sati2 saida yai 1month acen sannan da qyar tabarshi ya dawo gida. Dan tagama yau dararshi da kisisinarta. Dzai wuce tabashi address din gidansu. Sukai exchange number". inda tai mishi alqawarin itama tana nan da dawo Nigeria nanda 2Weeks. Ya Ahmad ya kanxo Hutu lokaci lokaci. Ya afnan ne yaxo so daya ansha murna yaqara zama kyakkyawan saurayi gaba daya yaga salma ta cenja mishi dan rabonshi da ganinta ya juma. Haka salma ta dinga murna. Tunda yadawo yini suke a gidan inna wani irin shaquwane yacigaba da qulluwa a tsakaninsu. Lokacinda zai koma makaranta kuka salma taita yi hankalinshi yatashi sosai! Haka ya xauna yaita lallashinta. Tana kashingide a qafadarsa murya cen qasa take fadin =>BUTULCI KO SO!!!.? Part 38 ==>Yaya yanxu tafiya zakayi kabarni! Hawaye ne suka malalo daga kuncinta" Hankalinshi ya qara matuqar tashi ya Sauri ya Ciro handkerchief dinshi yafara goge mata hawaye yana Haba salma na banason kukan nan. So kike ki tayarmun da hankali ko. Intafi cikin bacin rai KO! Pls kibar kukan nan kinji qanwata ta kaina" cikin yanayin shagwaba tace. To nidai yaya saidai katafi dani.! Yace haba salma na makaranta fa zanje ya za'ai natafi dake kiyi haquri kinji zamu dinga magana ta waya. Ta daga kafada uhm..uhm..nidai saika tafi dani.! Duk ya rasa yadda zaiyi da shawabar salma. Sai faman rarrashinta yake yi. Sannan ya samu tai shiru har bacci ya dauketa yasamu ya sulala ya tafi. Yashe gari ya wuce makaranta. Fadeela kam tuni tadawo Nigeria ya Habib har gidansu yaje iyayenta kam duk sunsan dashi. Wani irin sabon wulaqanci aunty sadiya tafara gani. Wanda ya wuce tunaninta tarasa me tai mishi harsaida yakai abin yafi qarfinta taje takai qararshi wajen momy. Domin a yanxu babu ruwanshi ma da ita saidai ya kwanta a gabanta yaita waya da fadeela cikin dare. Basu zasu gama waya ba sai wajen 04:am na asuba. Su hanata bacci ga tarin takaici dayake cusa mata saida taga sunata soyayyarsu ko shakkarta bayayi. Ita kuwa saidai taita kuka ga wani matsanancin kishin mijinta dayake damunta. Wata lokacin ma idan yaga tana kukan sai yace ta fice tabashi guri zata takura mishi. Haka zata dauki rufayda sukoma palo su kwanta.gashi ya hanata ta koma kara2 'Dan kulawan dayake nuna ma rufy din ma yanxu babu! Wannan dalilaine yasa aunty sadiya takai qararshi wasu abubuwanma bata fada ba. Momy da dady suka zaunar dashi sukaimai kaca kaca abun yayi matuqar qona masa rai wato kamr shi har wannan tatsitsiyar yarinyarne zata kawo kararsa gun iyayenshi. Ba qaramin target ya shirya mata ba Amma sai yayi tunanin kada yataso da maganar Auren fadeela kuma ahanashi. Dan haka yadan sassauta mata musgunawar dayake mata amma dai bai fasa waya agabanta ba. Tana shirye shiryen yaye rufy ne tafara laulayi wani cikin. Nanfa Habib dukya rukice yafara Neman yadda zeyi ya kawo maganar auren fadeela dan yana gudun kar ace saita haihu shikuma ya qosa yaganta a gidanshi. Itadai sadiya batasan bidirin da ake yiba.tanada fama da kanta. Tanata fama da laulayi. Ya Habib Yaje yasamu dady yai mishi bayani yanason yaqara Aure. Da farko dady yaqi amincewa amma dayai tai masa magiya ya nuna shi mata daya tai mishi kadan. Dady yace to shikenan yanxu kabari zamu zauna da momynka abunda muka tattauna zakaji. Ku kasan tare dani danjin abinda suka tattauna. UTULCI KO SO!!!.? Part 38 ==>Yaya yanxu tafiya zakayi kabarni! Hawaye ne suka malalo daga kuncinta" Hankalinshi ya qara matuqar tashi ya Sauri ya Ciro handkerchief dinshi yafara goge mata hawaye yana Haba salma na banason kukan nan. So kike ki tayarmun da hankali ko. Intafi cikin bacin rai KO! Pls kibar kukan nan kinji qanwata ta kaina" cikin yanayin shagwaba tace. To nidai yaya saidai katafi dani.! Yace haba salma na makaranta fa zanje ya za'ai natafi dake kiyi haquri kinji zamu dinga magana ta waya. Ta daga kafada uhm..uhm..nidai saika tafi dani.! Duk ya rasa yadda zaiyi da shawabar salma. Sai faman rarrashinta yake yi. Sannan ya samu tai shiru har bacci ya dauketa yasamu ya sulala ya tafi. Yashe gari ya wuce makaranta. Fadeela kam tuni tadawo Nigeria ya Habib har gidansu yaje iyayenta kam duk sunsan dashi. Wani irin sabon wulaqanci aunty sadiya tafara gani. Wanda ya wuce tunaninta tarasa me tai mishi harsaida yakai abin yafi qarfinta taje takai qararshi wajen momy. Domin a yanxu babu ruwanshi ma da ita saidai ya kwanta a gabanta yaita waya da fadeela cikin dare. Basu zasu gama waya ba sai wajen 04:am na asuba. Su hanata bacci ga tarin takaici dayake cusa mata saida taga sunata soyayyarsu ko shakkarta bayayi. Ita kuwa saidai taita kuka ga wani matsanancin kishin mijinta dayake damunta. Wata lokacin ma idan yaga tana kukan sai yace ta fice tabashi guri zata takura mishi. Haka zata dauki rufayda sukoma palo su kwanta.gashi ya hanata ta koma kara2 'Dan kulawan dayake nuna ma rufy din ma yanxu babu! Wannan dalilaine yasa aunty sadiya takai qararshi wasu abubuwanma bata fada ba. Momy da dady suka zaunar dashi sukaimai kaca kaca abun yayi matuqar qona masa rai wato kamr shi har wannan tatsitsiyar yarinyarne zata kawo kararsa gun iyayenshi. Ba qaramin target ya shirya mata ba Amma sai yayi tunanin kada yataso da maganar Auren fadeela kuma ahanashi. Dan haka yadan sassauta mata musgunawar dayake mata amma dai bai fasa waya agabanta ba. Tana shirye shiryen yaye rufy ne tafara laulayi wani cikin. Nanfa Habib dukya rukice yafara Neman yadda zeyi ya kawo maganar auren fadeela dan yana gudun kar ace saita haihu shikuma ya qosa yaganta a gidanshi. Itadai sadiya batasan bidirin da ake yiba.tanada fama da kanta. Tanata fama da laulayi. Ya Habib Yaje yasamu dady yai mishi bayani yanason yaqara Aure. Da farko dady yaqi amincewa amma dayai tai masa magiya ya nuna shi mata daya tai mishi kadan. Dady yace to shikenan yanxu kabari zamu zauna da momynka abunda muka tattauna zakaji. Ku kasan tare dani danjin abinda suka tattauna. ===>BUTULCI KO SO!!!.? Part. 40 ==>Saiki gayamun inda Aka haramta Aure dan matarka nada ciki! Shiru kawai tayi taci gaba da kukanta! Cikinta na cikin wata na5 aka daura auren fadeela da yaya Habib. Lokacinda momy ta fahimci aunty sadiya nada ciki taso adaga bikin saita haihu Amma Abba yace ayi haquri kawai abarshi. Haka akasha biki na gani na fada"many a manyan mutane duk sun halacci bikin. Amarya ta tare a gidanta nanfa sadiya tafara ganin wula qanci kala kala domin ya Habib ma babu ruwanshi da ita komai saidai amarya. Rayuwa gaba daya taimata zafi duniya kam a yanxu ta fahimci Habib baya kyautata ma sadiya su dady sunyi fadar sunyi jan idon harsun gaji. Abu sai qara cigaba yake. Su Kansu ma kulawar da suke samu wajenshi ada! Yanxu kafin suganshi ma aiki ne. Wata lokacin ma sai idan sun nemeshi" baqin ciki kam sun rasa yadda zasuyi dashi. Akwai sanda yaya Ahmad ya sameshi yake nunamishi abinda yakeyi baya kyautawa dan Allah ya gyara. Saida suka kusa fada. Domin duk Wanda yace zai zagi fadeela to zai iya masa abinda baya zato. A Ban garen salma da afnan kuwa, Muna iya cewa wata alaqace me girma ta qullu Wanda su Kansu suka Gaza fahimtarshi. Matuqar basa tare basajin dadin rayuwa. A rana sai suyi waya sama da 10 sannan suraba dare suna fira. Sumy CE kadai tasan wannan shaquwar dayake tsakaninsu Wata lokacin ma har fada suke cikin dare tace ita duk sun hanata bacci. Wata rana suna waya da daddare kamar yadda suka saba. Ya afnan yana kashin gide kan gadonsa yana rungume da Teddy. Ya marairaice kamar yana gabanta yace.