https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ *TSANTSAR BUTULCI* ⚱⚱⚱⚱ *NA* *BINTA UMAR ABBALE* *®BINTUBATULA👄* ```Marubuciyar``` ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING....``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ *NA FARA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN K'AI* _*Arashi*_ *WANNAN LITTAFIN K'AGAGGE NE DAGA NI MARUBUCIYAR BANYI DOMIN WANI KO WATA BA WANDA YAGA YAYI DAI-DAI DA RAYUWARSA TO A RASHIN SANI NE* *BAN YARDA WANI KO WATA BA YAYI AMFANI DA WANI B'ANGARE NA RUBUTU NA BA,BA TARE DA IZINA NA BA, AYI HATTARA* *WANNAN LITTAFIN NA KUD'I NE, NAIRA D'ARI BIYU IN MUTUM NA BUK'ATA SAI YA BI WANNAN NUMBAR KAMAR HAKA* 08089965176 07084653262 *UP* *UP* *UP* *KUNA RAINA, BINTA UMAR FAN'S HAK'IK'A BANI DA ABUNDA ZANCE DA KU SAI FATAN ALKAIRI* *GAISUWAR KU DABAN TAKE, DOMIN BAKWA GAJIYA DA YI MIN COMMENT* *UMMAHANI "YAR MUTAN BAUCI* *NANA AISHATU " YAR MUTAN KATSINAWA* *PREETY "YAR MUTAN BARNO* *ZAINAB " YAR MUTAN KATSINAWA* *MAMAN SUDAIS SAKWATTO* *HAJIYA INDO AMADU* *FAUZIYA MA'AWIYYA* *RAHAMA ALIYU* *MAHILLA UMAR* HAK'IKA BAZAN TAB'A MANCE KARAMCIN KU GAMI DA FATAN ALKAIRIN KU A GARE NI, NAGODE SOSAI DA ADDU'AR KU. KUYI HAKURI WANDA BAN FAD'A BA KUMA KUNA RAINA SOSAI ANA MUGUN TARE🤝🏻 _ZAMANI WRITERS ASSOCIATION_ _________________________ *KUN CANCANCI YABO DA GODIYA A GARE NI* *1 HUSAINI ATK 80k* *2 ZAINAB ABDULLAHI,SHAXXI* *3 NASMATU "YAR MUTAN ARKILLAH* HAK'IKA BANI DA BAKIN GODIYA A GARE KU SAI DAI IN CE ALLAH YA K'ARA MUKU LAFIYA DA NISAN KWANA, MUNA TARE IYA WUYA🤝🏻 _ALHAMDULILLAHI INAI WA D'AUKACIN AL'UMAR MUSULMI MURNAR BABBAR SALLAH UBANGIJI ALLAH YA MAIMAITA MANA YASA MUGA NA SHEKARU MASU YAWA, ALLAH KA SHAFE MANA ZUNUBAN MU, AMEEN_ _*WANNAN PEGE D'IN NAKI NE*_ *HAUWA S ZARI'A* (Maman Usuwan) *ALLAH YA K'ARA HIKIMA DA AZANCI* *BISIMILLAHIR-RAHAMANIR RAHIM* *🅿1&2* Wani babban gida ne me d'auke da d'akuna masu ciki da rumfa-rumfa za su kai bakwai, kana ganin gidan kasan gidan yawa ne kuma da ka gani me gidan me tsohuwar dukiya ne, a zamanin sa, bene uku ne a gidan d'aya a soro biyu a babban tsakar gidan, tsakar gida babban gaske ne ga wasu manyan bishiyu na dirimi a gidan har guda biyu, band'aki na futsari uku ne haka kuma na bayan gida uku ne,bayan na tsakar gidan a kwai wasu a bene guda bibbiyu. Kana ganin benen kasan na samari ne saboda yadda suka barbaza takalmansu da gajerun wandunansu, fulas din abuncin su, da kwalaben lemo gami da robobin ruwa da ledar pure watar duk ga sunan a watse a barandar benan me d'auke da d'akuna biyar. Kicin d'in na kalla naga wata k'atuwar tukunya a kan murhu ana ta da huwar abunci "yan matan gidan ne suke ta kai kawo tsakanin kcin d'in da d'akunansu, ko wacce da aikin da take banda mutum d'aya, Rabi'a kenan,tana kwance can k'arshen rumfar su tana karatun wani k'aton novel na turanci sai mutsu-mustu take tana lumshe ido ita kad'ai, k'anwarta ce tazo ta tsaya a kanta tana zumbura baki tace" Ke Rabi'a Mama tace"Kizo ki daka mata citta da kanin fari ki d'ora mata shayi kin San yau littinin tana azimi" A fusace Rabi'a ta aje novel d'in hannunta tace"Wallahi zanci uwarki Sumayya, kin raina ni ko? Ke me ya hana ki d'ora mata shayin da zakice dole sai ni" Buga cinya Sumayya tayi,tace"Yo ai bani bace Mama ce ta aiko ni, kuma wallahi bani kika zaga ba kanki kika zaga ehe! Da sauri Rab'ia ta mik'e zata kai mata duka, tayi waje da gudu tana dariya gami da tsalle-tsalle tana murgud'a mata mazaunanta, Ta kalmi Rabi'a ta d'auka ta jefe mata tace"Shegiya "yar lukuta kawai" Da gudu ta k'arasa kusa da Mamansu Hajiya Zulai kenan tana zaune kan dadduma tunda ta idar da sallahr la'asar take zaune tana lazimi, tayi saurin yin gyaran murya ganin yadda Rabi'a tayo kan Sumayya tana k'okarin dukanta da takalmi, rike'hannun Rabi'a tayi tana d'an hararata, Rabi'a ta gane hukuncin Mamansu ko da ido ma tana yi, girgiza kai tayi ta bar gurin tana fad'in za ki shigo hannu ne yarinya Allah sai na zane ki" Gwalo Sumayya tayi mata tana dariya ta d'ora kanta kan cinyar Maman nasu. Hajiya Gaji ce ta futo daga d'akinta da murmushi a fuskarta ta kalli Sumayya tace"Ke kam kinji kunya, kullum kina nad'e a cinya kin girma baki san kin girma ba wai ke "yar shagwaba'a" Bubbuga k'afa Sumayya tayi cikin shagwab'a tace" Ni Mama a k'yaleni inci lokacina nice fa duk "yar k'arama a gidanan, a k'yaleni in suburbud'a sha'anina" Dariya Hajiya Gaji tayi tace"Dube ta don Allah,da baki kamar gidan tsutsa ya iya fad'ar suburbud'a" Murmushi Hajiya Zulai tayi da carbi a hanunta k'okarinta taga ta kammala laziminta ta shigarwa Sumayya domin yanzu Hajiya Tabawa ma ta futo d'orawa zatayi kan abunda Hajiya Gaji take wa Sumayya suyi mata taron dangi wanda yake sata kuka. Zumbura baki Sumayya tayi tana kauda kanta. Hajiya Gaji ta wuce bakin rariya tana dariya. *TUSHEN LABARI* ALHAJI MADO GWADABE Shararran d'an kasuwa ne, me dukiya taban mamaki wanda yasha gwagwar maya a harkar kasuwanci inda ya tsaya da k'afafunsa a wancan lokacin da turawan ingila yake harkar atampah da yadika irin na maza da d'ankwali na mata, mutum ne shi me nasibi shiyasa ko wane gari kayansa suke zagawa idan yaje ya dawo zai rarraba kaya cikin sauk'i da rahusa kafin kace kwabo kaya sun k'are, kamfaninsa biyu a ingila wanda ake atampah d'aya a chana ana d'ankwali, sosai mutane suke ci a karkashinsa, mutum ne shi me k'arfin zuri'a, mutane da dama na cewa gado yayi saboda mahaifinsa Gwadabe ya haihu sosai da sosai wasu sun mutu wasu sunanan a raye shi Mado ya taso bai san ubansa ba domin ya kasance dan amaryasa ne, wanda ya kasance shine k'arami a cikinsu,yana a Da she kara d'aya a duniya mahaifin nasu ya rasu. _Tab'a ka lashe_ *ZAN CIGABA INSHA ALLAH SABODA MASU BUK'ATA KAFIN IN DA TURAWA GROUPS SAI WANDA YA BIYA* *200* [14/08, 13:13] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿3&4* A k'alla Gwadabe ya haifi "yaya arb'in da bakwai tare da mataye iri-iri kasancewar shi mutum ne me aure-aure shiyasa ya tara " yaya da yawa mace d'aya sai ka same ta da "yaya goma, ko goma sha biyu cikin mantan nasa guda hud'u harda me " yaya goma sha biyar, Mado ne kawai bashi da d'an uwa saboda da kan babarsa Gwadabe bai k'ara auran wata mata ba, gashi lokacin ya tsufa sosai,kuma mahaifiyarsa ta dad'e bata haihu ba. To mutane suna cewa Mado ai gado yayi saboda mahaifinsa yayi aure-aure shine shima yake yi saboda yaga yana da kud'i, lokacin da zaiyi auran fari ma da mata biyu ya fara, kuma suna haihuwar fari ya k'aro wani auran inda ya auri mace d'aya itama da tsohon ciki ya cikashe ta hud'un babu abunda ya dame shi. Yanzu haka yana da "yaya ashirn da bakwai mata da maza, wasu iyayensu ma basa gidan. Yana da " yaya maza goma sha hud'u inda mata suka kasance su goma sha uku, matayensa uku ne suka rage kasancewar amaryarsa ta futa ta dalilin babban d'ansa me suna Habib, wanda yanzu haka yana can ingila kan harkokin mahaifin nasu shi da k'aninsa Auwal me bi masa kenan, Fafur!Habib ya hana mahaifinsa k'ara wani auran tunda amaryarsa ta futa yace"Har indai yarinya zai je ya d'auko to gwara kawai ya hak'ura da auran domin yanaji yana gani ba zai yarda yaje ya d'auko musu yarinya k'arama ba tazo tana zagin iyayensu, waccen ma kafin ta futa sai da ya sumar da ita dalili ta zagi Hajiya Tabawa matar mahaifin nasu ta uku, sosai yaran gidan maza da mata suka taso da tarbiya da nutsuwa uwa uba ilimin addini da na boko dai-dai gwargwado kowa najin magana, banda Sumayya ta gagari kowa a gidan maza da mata, mussaman yanzu da ta samu sakewa Yaya Habibu bayanan sai tak'i zuwa makaranta haka duk za'a d'ad'e a gidan babba da yaro duk su tafi banda ita, daga taga lokacin makaranta yayi sai ta shige k'uryan d'akin su tayi kwanciyarta kan gadon k'arfen Mama ta shige loko sosai ta saki labule, haka za'a k'araci nemanta a hak'ura sai taji gidan yayi tsaitt! sai ta futo tana sharb'a gumi tana sosa soshe irin na rashin gaskiya. Nan Hjy Gaji zata kamata ta murd'e mata kunne tai ta fad'a tana cewa"Wallahi ko don wannan abun naki da kikeyi zan tursasa Yayanku ya dawo domin shine maganin ki,haka zaki zauna babu karatu,shashashar yarinya kawai" Zumb'ura baki take kawai taje ta d'ane karfen baranda tana sufa tana kyalkyala dariya sai kace wata shashasha, haka take yi ni tana wasa a gidan, babu ruwanta,da zuwa makaranta sai taga dama, har inda kaga tana himmar zuwa makaranta to tabbata Habibu yazo gida,nan ne zaka ga ta nutsu tana abu simi-simi kamar me gaskiya ko tsokanarta akayi a gidan bata ramawa Dan kar ya dake ta, saboda in yazo gurin baya tsayawa ya bi ba'asi zane ta yake ciki da bai yace"Ai itace bata da gaskiya,sai dai tayi kukanta ta gaji, Mama kuwa haushi duk ya isheta duk ranar da Habibu ya dake ta yini take bata kulashi ba,sai dai yazo ya karaci maganarsa ya tafi. Haka "yan matan zasu dawo gida kowa na bitar karatun da akai masa a makaranta amma banda Sumayya, magariba nayi zasu shirya su tafi makarantar magariba, nan ma sai ta tsiri baccin k'arya, Rabi'a tai ta tashinta tana ji tayi shiru mamansu tace tak'yale ta kawai tayi tafiyarta, haka zasu tafi Rab'ia na jin haushin yadda Sumayya ta maida kanta koma baya cikin " yan uwa, lafin su dawo kuwa ta fakaici idon matan gidan mussaman insun shiga sallah,sai taje ta bud'e miya ta tsamo nama ta tsuguna kchin din tana ci, sai taci me isarta sannan zata gudu gurin Babansu Alh Mado kenan d'akinsa na can benen soro dake d'akuna uku ne sai ya d'au d'aya Habibu ya d'auki d'aya shima Auwalu ya d'auki d'aya, to can gurinsa take guduwa tayi kwanciyarta har sai garin Allah ya waye sannan take sakkowa tana zumb'ure-zumb'uran baki. To duk me girki a ranar in taga an tab'a tukunya tasan Sumayya ce,haka zata k'araci fad'anta ta hak'ura saboda in tace zata bita saman tayi mata fad'a zasu iya b'atawa da me gidan domin ba'a tab'a masa shalelensa,ko kayan kasuwa ya siyo duk yawansu ita yake bawa yace ta raba musu, in ta sakko k'asa sai tasha na sha taci na ci sannan zata raba musu ragowar Rabi'a tai ta dukanta, ita kuma tana b'are baki tana kuka, babansu najin kukanta,zai lek'o ta taga yayi ta fad'a haka zasu hak'ura su k'yale ta. Babbar yarsu Zainab tana aure a Kaduna tana da yara bakwai, Ihisan ce babbar "yarta kuma duk itace mace sauran duk maza ne.Ihisan Aminiyar Sumayya ce sosai in tazo Hutu. haka zasuyi ta tsula siyarsu Sai Khadija ita kuma tana Aure a jibi'a can katsina kenan yaranta uku duk maza Sai Aisha ita kuma shekararta biyar da aure Allah bai bata haihuwa ba, tana can abuja can take aure *_Wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu kacal in mutum na buk'atar cigabansa ga numbar ta nan_* 08089965176 07084653262 [15/08, 15:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*Wannan littafin na kud'i ne, naira d'ari biyu in kana buk'atar sa ga numbar nan*_ 08089965176 07084653262 _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿5&6* Rabi'a da Suwaiba ne cikin k'uryan d'akin Hajiya Gaji, suna hira k'asa-k'asa Sumayya ta zo ta lab'e bayan labule ta kasa kunne tana jin abunda suke fad'a Rabi'a tace"Wallahi Suwaiba aure nake so, na gaji da zaman gidan nan gwara ayi min aure kawai in je in mori k'uruciyata,bakiji yadda nake ji ba in ina karanta novels duk sai in dunga jin tsigar jikina na tashi, humm kin san shekaran jiya a gidan k'awata Nusaiba na wuni wallahi baki ga yarda suke soyyaya da mijinta ba,a gabana fa naga yana tsotsar bakinta, wallahi ji nayi ina ma nice" Hannu Suwaiba tabata suka tafa suna dariya tace"Ba sai ki fad'awa babanmu aure kike so,nasan halin baba aure zai miki da Ansar d'in ki" "Humm nasan da haka ai,kin san babbar damuwa ta wacce tasa na hana Ansar zuwa gidanan shine, Wallahi ina bal'in jin tsoran masifar yayanmu, kin sam shi babu abunda yake so muyi a yanzu idan ba karatu ba,ni kuma wallahi aure nake so" Rabi'a ta k'are maganar tana sauke ajiyar zuciya kana kallon yanayin ta kasan da gaske take. Suwaiba tace"Bake kad'ai ba,Allah nima da zan samu tsayyayen miji aurena zanyi babu ruwana da wani karatu," Tafawa sukayi a karo na biyu suna k'yalkyala dariya. Motsi sukaji a falo gabansu ya fad'i a hankali Rab'ia tace"Allah yasa babu wanda yaji Suwaiba ce ta d'aga labule a hankali tana lek'owa,kawai sai ta hango k'afar Sumayya bayan labule, tana k'okarin guduwa Suwaiba ta rik'eta tam!tana janta tana turjewa, fad'i take"Wallahi naji abunda kuke fad'a sai na fad'awa yayanmu,ko in fad'awa Babanmu, tabd'ijam,wai aur....da sauri Rabi'a ta rufe mata baki suka jata da k'arfi suka kaita d'aki. Turje-turje take tana k'okarin kwantar kanta ta gudu sun rik'eta sosai, Rabi'a tace"Haba k'anwata ta kaina, bani ce fa nace ina son aure ba labarin k'awata Nusaiba nake bawa Suwaiba, don Allah kar ki fad'awa kowa kinji" Kamar zatayi kuka ta k'arashe maganar. "Oho miki,ni dai sai na fad'a ehe!ai naji sanda kike cewa wai mijin Nusaiba yana tsotsar bakinta, kema kina so,sai na fad'awa yayanmu in ya dawo wai kina so mijin ki ya tsotsi bakin ki" Cikin rawar murya Rabi'a tace"Ayya Sweet Sistar na, nace miki fa bani nace, labari ne kawai a novel irin Wanda nake karantawa don Allah kar ki fad'a kinji, na miki alk'awarin zan baki wannan mayafin nawa da kika CE kina so" "Oh"Oh to me yasa kike karanta novel d'in ai Mama ta hanaki,ni dai babu ruwana sai na fad'a" Sumayya tafad'a cike da kuruciya Suwaiba tace"Wai ke dan kinga ana lallab'a ki shine kikewa mutane botsare-botsare, wallahi dukan ki zanyi,yanzu kije ki fad'a d'in" Zumb'ura baki tayi tace"Tabd'ijam ni babu me dukana in kyaleshi sai ruwan sama" Hannu Suwaiba ta d'aga zata mare ta a fusace, Rabi'a tayi saurin rik'ewa tana girgiza mata kai. Ita kuwa Sumayya b'are baki tayi zatayi kuka,Sumayya tace"Ko in baki kud'i,nawa kike so" Sanin halin jarabban san kud'i irin na Sumayya yasa Rab'ia ta yanke wannan shawarar. Aiko da sauri tace"Na yarda ki bani Dari da hamsin, bazan fad'awa kowa ba" Da sauri Rab'ia ta d'auko jakar makarantar bokonta ta ciro naira hamsin a tsakiyar littafinta na engilis tace"Gashi nan itace dani,ranar Monday zan cika miki d'ari, shikkenan ko"? D'aga kai tayi ta karb'i hamsin d'in ta b'oye k'arkashin siket d'inta, tana kallon su tace" Yaya Suwaiba kece shaida ko, Allah idan bata cika min kud'ina ba sai na fad'a" Suwaiba tace"Eh nice shaida da kaina zan karb'a in baki in za muje makaranta" Zumb'ura baki tayi ta juya ta futa tana muskura mazaunai. Da kallo suka har ta futa, Rab'ia tace"Wannan yarinyar munafuka ce,wallahi ashe tana kallon sanda muka shigo d'akin shine ta biyo mu ta lab'e tana jin abunda muke cewa" Dariya kawai Suwaiba take,harda kwanciya k'asa tace"Ai tuntini na dawo daga rakiyar yarinyar nan wallahi, Sumayya,humm duk inda kika d'auke ta ta wuce nan" Itama Rabi'a dariyar take tace"Shegiya "Yar lukuta kawai tana fama du d'uwawu kamar an d'ora turmi" Kwanciya sukai d'akin suna ta shek'a dariya, Hajiya Gaji ta shigo d'akin ta gansu suna dariya tace"Ku kuma fa kuna dariya kamar wasu shashashai. _*Tab'a ka lashe*_ [16/08, 17:15] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿7* Had'a baki sukayi gurin cewa "Babu komai Hajiya"Girgiza kai tayi tana k'okarin sakko da samira dake kan kwabarta tace" Yanzu naga Sumayya ta futa Allah yasa ba tsokanarta kukayi ba,kun San halinta fad'anta baya rabuwa, haka kawai baza Ku jawo mana fad'an Alhaji ba, yana gida bai futa ba mutuk'ar yaji kukanta, to kuma sai kunyi kuka" "Laa Wallahi Hajiya ba ita muke tsokana ba, labarin wata " yar ajinmu nake bawa Suwaiba" Rabi'a ce tayi Wannan maganar cikin wayance wa. Hajiya Gaji tace"A to!ni dai na fad'a muku" Sumayya ce ta shigo d'akin da gudu,tana dariya hannuta rik'e da biscuit d'an hamsin tace"Hajiyarmu kizo ga Yaya Khamis yazo yanzu" Cikin fara'a tace"A'a lallai muna da babban b'ako a gidanan lale maraba, maza je ki ce ya shigo" Har ta juya zata futa,tayi saurin dakatar da ita,ta hanyar kiran sunan ta" Sumayya taja ta tsaya tana k'okarin bud'e ledar biscuit d'inta Had'e fuska Hajiya Gaji tayi tace"A'ina kika samu kud'i kika siyi biscuit ko rok'onsa kikayi daga zuwansa. Girgiza kai tayi,tana zare ido tace"Sama na hau gurin babanmu na karb'o kud'i" Hajiya Gaji tace"Mak'aryaciya kawai ba yanzu na sakko daga saman ba,bacci yake ko tashinsa kikayi"? D'aga kai tayi tana zumbura baki. "Wuce ki bani guri kuma ina fatan kin gaida Yaya Khamis d'in" D'aga kai tayi ta futa tana zumb'ura baki. Khamis na zaune kan dadduma dake falon, kansa a sunkuye, ya d'ago kansa yana kallon Summya da ta futo daga d'akin, ganin tana zumb'ura baki, yasa ya saki dariya, yace"To uwar shagwab'a zonan ke dawa kike toro baki gaba,sai kace shantu" Kuka tasa tana buga kafarta cikin sangarta tace" Ya Khamis bana so, ni bakina baya kama da shantu" Dariya yake kyalkyalawa yana binta da wani mayen kallo, bubbuga k'afarta da take yasa dukkanin sassan jikinta motsawa, mussaman mazaunanta,duk da take yarinya "yar shekara sha biyu hakan bai hana bayyanuwar hallitar ta,saboda macace mai girman jiki sosai ga shinan har tafara k'irgar dangi sunyi tsaye Carr!a cikin rigarta, gurin cikar k'afa da shara b'a ba'a magana a cike suke dam! Wani irin kallo yake mata me tattare da zallar sha'awa sosai yake son lafiyyan jikin yarinyar da alama za'a huta a jikinta" Hajiya Gaji ce ta futo fuskarta cike da fara'a tace"Lale maraba da Hamusu, sannu da zuwa" Gyara zama yayi yana me d'auke idonsa daga kan Sumayya,yace"Sannu Hajiyarmu fatan mun same Ku lafiya " Hajiya tace"Lafiya lau muke Hamusu ya harkokin?ya mutan gida,su Hajiya Laure" "Wallahi duk sunanan lafiya, ai jiya nima na dawo shine nace bari in shigo mu gaisa kafin mu fad'a kasuwa koma duk harkoki su da baibaye mu" "Ai kuwa ka Kyauta sosai da kazo muka gaisa Allah yayi maka albarka, Allah ya dafa muku,a dukkanin abunda kuka sa a gaba" "Ameeen" Ameeen Ai munyi Waya da Habibu yace" Yana kan hanya insha Allah a satin nan zai dawo" Hajiya Gaji tace"Ka rabu da shiriritar wannan, ko jiya sai da nasa Abdulsamad yayi masa waya abunda ya fad'a maka da ban da wanda ya fad'a mana" Dariya Khamis yayi yace"Wannan karon dai da gaske yake, insha Allahu mu tsammace shi a satinan,don haka ma bazan koma Maidugiri ba,sai ya dawo nan zan zauna" Hajiya Gaji tace"To Allah yasa da gaske yake,ai naga alama shi babu abunda yasa a gaba sai neman kud'i shikenan yawo daga wannan k'asa zuwa wannan k'asa" Cikin murmushi Khamis yace"Haka abun yake Hajiya fatanmu dai kuna yi mana addu'a su kud'i ai dole a neme su Ku dan su Ooo gatanan a tsaye" Ya k'arashe maganar yana dariya" Hajiya ta tayashi dariyar ,tana fad'in "Aikwa dai,wannan sarkin kashe kud'in, bata da aiki sai ciye-ciye" tafad'a tana mik'ewa da niyar futa,tace"Bari in sa a kawo maka abunci" Suwaiba ta kira tace"Kuna jin yayanku kun kasa futowa Ku gaidashi ko" Kusan a tare suka futo kai a k'asa suka gai dashi cikin girmamawa,suna mutuk'ar ganin girmansa,kamar yadda suke ganin girman Yaya Habibu saboda bashi da babban aboki kuma amini kamarsa" Hajiya tace"Ko zo muje Ku kawo masa abunci" Bayanta suka bi,duk su biyun suka bar Sumayya da Khamis d'in a falo. Tana can gaban tv tana k'okarin kunnawa,yace"Zonan Sumayya, barin abunda takeyi taje ta tsaya kansa, cinyarsa ya nuna mata wai ta zauna. Duk da yarintar ta tasan hakan ba dai-dai bane saboda haka sai ta mak'e kafad'a alamar tak'i. Karku manta wannan book d'in na kud'i ne naira 200 ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [17/08, 04:26] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿8* Kashe mata idonsa guda yayi cikin sigar yaudara yace"Zo ki sammin biscuit d'in naki,naji irinsa zan baki wani kud'in ki siyo" Jin zancan zai bata kud'i ta siyo wani yasa ta tafi gurinsa da sauri, rik'o hannuta guda yayi yana murzawa, yana lumshe idonsa ya zaunar da ita kan cinyarsa, yana lek'en cikin rigarta, Ita ko Sumayya sam bata san wace wainar yake toyawa ba,mik'a masa ledar biscuit d'in tayi,tana "yar dariya cike da k'uruciya tace" Yaya Khamis kalli fa na cinye duka saura dudduga,da gaske zaka bani kud'i in siyi wani" Gyad'a kai yayi yana d'an matsa mata mazaunai,yana lumshe ido,har ya soma futa daga hayyacinsa, ita kuma jin da tayi yana tattab'a mata jiki yasa tayi zumbur!ta mik'e daga jikinsa,tana kallon yanayin sa, tabbas ta tab'aji a makarantar magariba malaminsu ya fad'a cewar babu kyau namiji baligi ya kusanci mace,ko kuma ya tab'a mata jiki, Kallonsa take sosai taga duk ya zama soko kamaninsa duk sauya, bakinta na rawa tace"To bani hamsin d'in na siyo kaji,ai kaga wannan saura dudduga,idan na siyo wani sai in sammaka" Mik'ewa yayi tsaya,ya d'auki hularsa yasa yace"Ki kawo min abunci ina d'akin Habibu,idan yaso sai in baki kud'in biscuit din" Kafin tace komai ya fuce daga falon saboda baya son wani me hankali yazo ya fahimci halin da yake ciki na tsantsar sha'awa. Kicin ta wuce tana tafiya tana tattare siket d'in dake jikinta, Suwaiba ce tsugune a kchin d'in yayin da Hajiya Gaji take zuba abunci cikin fulas me kyau, tace"Hajiya Yaya Khamis yace"In kai masa abuncin" Da sauri Suwaiba tace"K'arya kike, babu wani yace ki kai masa abunci,Allah Hajiya kar kibata k'ila in taje rok'onsa zatayi ai kin san halinta" Mama Zulai dake zaune a kujera "yar tsugo,tana gurza kub'ewa d'anya, wacce za'suyi amfani da ita da daddare tace" Suwaiba bana son abunda kukewa yarinyar nan,fa wai me kuka mai da ita ne"? Suwaiba tace"Allah Mama Halin Sumayya sai ita,babu mai iyawa sai ke sai babanmu, ni har na k'ago Yayanmu ya dawo, ya suburbud'a mata jiki" Duka Sumayya ta kai mata a fusace!Tace"To yadawo mama meye ruwana,ai sai ya ganni a gurin da yake sannan zai dake ni, sai an kula kashi yake d'oyi" Dariya suka sa har Hajiya Gaji dake kicin tace"Lallai Sumayya kin iya cika baki, Allah ya dawo dashi, kin san dama babu ni a masu ceton ki" Shiru Sumayya tayi batace komai ba,Suwaiba ta karb'i tiren abunci ta futo daga kicin d'in, da sauri Sumayya taje ta tare hanya tana k'okarin k'arbar abuncin, fad'i take"Ai ni yace in kawo masa" Mama Zulai tace"Ke Sumayya saki mana kar kuyi b'arna mana" "To ai Mama nifa yace in kai masa shine zata wani ce ita zata kai" Ganin rigimar tak'i k'are wa yasa Hajiya Gaji tace da Suwaiba ta sakar mata tiran kar su zubar da abunci a banza, Dole babu yadda ta iya ta sakarwa Sumayya, Hajiya Gaji tace"Sai ki kula da kyau ai kada garin rawar kai kije ki zubar. A hankali take tafiya dan kar abuncin ya zube, tafara taka matattakalar bene a hankali har ta isa kofar d'akin Yayan nasu, tura k'ofar tayi ta shiga da sallama a bakinta kamar gaske. Khamis na zaune gefen k'atuwar katifar Yaya Habibu wacce tasha lafiyyan shimfid'a ke kyace yana d'akin kullum sai fidda k'amshi yake mai mugun d'adi,k'amshi da yakama jikinsa kenan,yaran gidan har sun gane k'amshinsa indai yazo guri kowa sai ya gane shine, saboda k'amshinsa na mussaman ne, to haka k'amshin d'akinsa ma ya kasance na mussaman, duk bayan kwana biyu Hajiya Gaji da kanta take hawa saman ta gyara masa d'akin ta feffesa turaran da yake amfani dashi na k'amshin d'aki,ta jawo d'akin ta rufe. Saboda sanin hali da tayi idan ya dawo yaga d'akin babu gyara,zai iya sawa duk a kwashe kayan d'akin a yi masa sabon fainti sannan a zuba komai sabo,wancan ayi gwanjonsu, shi futar kudi a gurin sa ba komai bane,saboda Allah yayi shi mutum mai son k'yale-k'yale d'an kwalisa,ne ajin k'arshe ga tsabta ko mace albarka, kaya kuwa ko mai tsadar yadi ko shadda zaka ganshi a jikinsa, sabbin takalma sau ciki masu gidan ya tsaya gasunan iri-iri sai idan ya gama amfani dasu ya futowa da k'annasa su mora,duk wata yake d'inka sabbin kaya,ya futar da tsoffafi,ya rabawa mabuk'ata. Babu abunda babu cikin d'akinsa na more rayuwa, Yanzu ma Khamis na zaune yana kallon tv plasma inda yake kallon wak'okin india,a sky movies, dake shi ma'abocin kallon raye-raye ne yana son yaga suna rungume-rungume suna burge shi. Sumayya ya ke kallo har ta shigo d'akin ta aje masa abuncin a gabansa,gurin durkusa wuyan rigarta ya zamo k'ananun nonowanta suka d'an futo babu dabara sam bata da niyyar gyarawa, Shi kuwa Khamis ji yayi kamar ya zura hannu ya cafko guda d'aya ranshi yana ta biyawa da yarinyar. Tsayuwa tayi tana kallon tv taga an nuno Preetyzeenta tana rawa tana dariya ga dimful d'inta na lob'awa,sai ta k'yalk'ale da dariya kamar wata sokuwa tace"Laaa Yaya Khamis ga me kama dani K'ungunta ya rik'o da hannusa yana so ya d'orata a jikinsa,ita kuma tana dagewa, yace"Waye yace miki Preety tana kama dake" Cikin k'uruciya tace"Su Yaya Abdul ne wai irin dariyarmu d'aya da ita"joyowa tayi tana fuskantarsa tace"Kaima kagani ko don Allah muna kamai,kai!gaskiya dani kyakykyawa ce in ina kama da ita" Tafad'a tana buga tsalle. Muryarsa tafara sauyawa yace"Zo ki zuba min abunci inci yunwa nake ji" Yayi hakane don ta k'ara sunkuyawa ya samu nasarar ganin k'irjinta a karo na biyu. Cike da k'uruciya da rashin sanin meye rayuwa ta sunkuya tana zuba masa abuncin shi kuma yana ta kallonta k'irji. " Yaya Khamis gash....Shiru tayi ganin ya k'orawa k'irjinta kallo,tayi saurin kallon inda yake kallo, taga abunda yake gani,sai ta mik'e tsaye da sauri tana zumb'ura baki, cikin zuciyarta tace"Lallai ma Yaya Khamis d'in nan ina ganinshi me kirki ashe shima d'an iska ne,dubi yadda yake kalle min k'irji, wata zuciyar tace,kiyi saurin futa kar yayi miki fyad'e, duk da batasan meye fyad'e ba,amma tanajin anacewa a labari ai namiji nayiwa mace fyad'e,da sauri ta nufi hanyar futa daga d'akin cikin tsoro, kiranta yake yana fad'in tazo ta karb'i hamsin d'in biscuit d'in,amma INA!!tuni ta ruga da gudu,bibbiyu ta dunga had'a matattakal benen ta sauka k'asa. _*Wai wanene Khamis ne?*_ Karku manta wannan littafin na siyarwa naira 200 ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [18/08, 05:28] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿9* Khamis Abokin Habibu ne tun na k'oruciya d'ane ga abokin Alh Mado Gwadabe, wanda suke harkar kasuwancinsu a wancan lokacin,shi mahaifin Khamis Alh Auwalu d'an jahar barno ne wato maiduguri kenan, Alh Auwalu ya kanzo kasuwar kano yayi sarin kaya kaya gurin Alh Madu, ya kai can garinsu ya tallata, cikin ikon Allah kasuwancin sai ya k'arbeshi, Alh Auwalu mutum me amana da gudun abun wani, shiyasa ma abotarsu da Alh Madu tayi tsayi saboda shima bayason mutum macinyin amana, ganin irin wahalar da Alh Auwalu ya kesha gurin zuwa sarin kaya,yasa kawai ya yanke shawarar bud'e masa shago a can garin nasu ya zuba masa dukkanin kayan da ake Nema, in yaso duk shekara sai ayi lissafi a futar da riba. Alh Auwalu na zuwa, Alh Madu ya fad'a masa shawarar da ya yanke, nan take yayi na'am da abun ya dinga godiya Alh Madu yace, ai duk anzama d'aya ya daina godiya,,, sosai suka k'ulla harkokin kasuwancin su komai yana kankama, yana bunk'asa, wani lokacin Alh Auwalu ya kanzo da d'an shi Khamis, in ya shigo Kano gurin abokinsa,nan Khamis suka saba da Habibu,saboda Habibu kullum yana kusa da mahaifinsa yana koyan dabarun kasuwanci lokacin yana d'an shekara goma sha uku. Sosai suka saba wanda har ta kai Khamis yake gudun Mahaifinsa in zai tafi, sai su gudu gida Habibi ya b'oye shi, ganin irin guje-gujen da Khamis yake in zasu tafi yasa Alh Madu ya rok'i alfarma gurin abokinsa kan ya bar masa Khamis d'in, in yaso sai tayi masa transifar na makarantun da yake, zuwa. To babu wata buk'ata da Alh Madu zai zowa da Alh Auwalu ita bai amunce ba, babu ja'inja ya amunce, yayi tafiyarsa ya bar Khamis a garin Kano. Habibu da Khamis sun shak'u iya Shak'uwa komai tare sukeyi hatta da suttura iri d'aya suke sanyawa takalma iri d'aya huluna iri d'aya abunci tare suke ci, tare sukayi karatunsu a babbar makarantar nan ta jahar Kano wato BAYARO UNIVASITIY in da suka karanci harkar kasuwanci, ta wani fanni sunyi tarayya gurin hali, ta wani fanni kuma halinsu ya banbanta, ta inda sukai tarayya shine gurin saka kaya iri d'aya duk wani abu d'aya ya siya sai d'an uwansa ya siyo irinsa shima ko da abunci ne, hatta da turare iri d'aya suke fesawa, in suna tafiya baka tab'a banbance waye a cikinsu,sai Wanda yayi musu farin sani, saboda d'aya yafi d'aya tsayi hakanan d'aya yafi d'aya k'iba, Habibu Dogo ne, sosai mai fad'in k'irji, yana tara suma a kansa,kuma yafi Khamis hasken fata, Khamis bai kai tsayin Habibu ba kuma yafi shi kauri kad'an,,, shi yana da san mutane da tsokana ko a cikin abokai ne, sab'anin Habibu da take mai muguwar a k'ida da tsattsauran ra'ayi, ga gaddama da kafiya, shiyasa abokansu basa su musu ya had'asu dashi, baya gajiya gurin tsari, lallai tsarinsa shine dai-dai, yana da mutukar surutu a cikin abokai gami da kwarjini da haiba,ta mutane babba da yaro,kowa nasa ne, bayason raini bayaso ka raina shi,mutum ne mai son girman tsiya shiyasa suke bugawa da Yayarshi Aisha wacce ta girmeshi da kwana uku, lallai sai yace ai ya girme ta sauri tayi ta rigashi zuwa duniyar,girman kwana uku ba girma bane, haka zasuyi ta k'wamawa dashi sai dai ta hak'ura ta kyaleahi domin yafita iya tsari! In yaga tayi shiru sai yai ta yi mata dariya yayi tafiyarsa. To duk wannan k'walisa da Wanka da wannan matasa sukeyi ba da dukiyar kowa suke ba,face da ta Alh Madu, shi ya sakar musu,bayan sun kammala makaranta, Alh Madu yace duk abunda zai yiwa d'ansa na cikinsa haka zai yiwa Khamis domin abotarsu da mahaifinsa ta mussaman ce,Sam!baya d'aukar zugar mutanan gari Gaba ki d'aya rayuwar Khamis ta dawo kano sai dai yaje Maiduguri ziyara, tare suke tafiya da Habibu su dawo a tare Sai da sukai kai shakara ashirin da bakwai ne, Alh Madu ya d'amkawa kowa makulli na shago cikin kasuwa ya zuba musu kaya, sosai yace, su fara zuwa domin su gina kansu,kuma kyauta ya basu,ba bashi ba, cikin sa'a suka fara harkar kasuwanci inda ta fara garawa da Habibu ba'ayi shekara ba ya fara futa kasashen waje,yana had'a hark'allarsa da turawa,kai harda Larabawa Habibu harka yake,mussaman na Dubai,nan sukai masa doyayen riguna na mata masu kyau da jallabiyoyi na maza gami da hula, zai auno kaya ya dawo ya rarraba take,zaka nemi kaya ka rasa, mutane sai suka fara surutu cewa taurarin arzik'i sun sauka daga kan mahaifinsa sun dawo kansa saboda haka shine zai gaji ubansa, ganin cece kucan da mutane keyi yasa kawai ya hana Alh Madu futa kasuwa sai jefi-jefi yake zuwa,tunda in yaje d'in ma sai dai ya zauna yana shige da fuce, shagonsa cike yake da yara masu neman su kafa Kansu,duk ya sakar musu kowa ya samu nashi . *Kai gaskiya da anyi dattawan arzik'i da kudi lo wani abun duniya bai rufe musu ido ba,masu maida d'an wani nasu* Sai yake zama a gida kawai tunda lokacin Auwalu ma ya kawo k'arfi shi yake zuwa ya kula da harkar cinikayyar duk ranar da bai futa ba. To yawon tafiye-tafiye da Habibu yake ne yasa Khamis yayi sabbin abokai cikin kasuwar irin,kullum suna shagonsa ana hira ana birni k'iri-k'iri costoms zasu shigo kasuwar a kan idonsa sai ya share kawai a cewarsa shi bazai wani damun kanshi ba kan kud'i kamar yadda Habibu yakeyi tunda yaga zai iya yayi tayi,bashi da matsalar komai in ya buk'aci kud'i zaije ya cire ne cikin Account din Habibu batare da damuwarsa ba,shima Habibun in ya gani baya damuwa,saboda wasu ne suke shigowa kullum, ganin arhar kud'i yasa Khamis d'iba iya son ransa ya tafi bariki yaje ya kashewa mata,ya shana sosai yayi watsi da kud'i, tuni idonsa ya bud'e da mata tare da had'in gwiwar sabon abokinsa Manniru, shima cikin kasuwar yake, kullum suka tashi daga kasuwa sai su wuce hotal suje su nemi matansu duk kalar da suke so. Khamis Mutum ne jarabbabe in yaga mace kamar yayi hauka haka yakeji,, kuma yakiyin aure,sai shanawarsa yake. Kwatsam A ka aiko Alh Auwalu babu lafiya,dama yana da Hawan jini,da sugar babu b'ata lokaci Alh Madu ya tattara iyalinsa suka nufi Maiduguri hankali a tashe! Alh Madu ya gigice da ya ga Abokinsa baya iya motsi ko ina na jikinsa ya shika komai sai dai ayi masa,babu shiri ya sa aje ayi vis domin futar dashi kawar waje a bunkici lafiyarsa, anyi komai an gama, a daran Alh Auwalu ya rasu,wannan mutuwa ta gigita alumar musulimi duk Wanda ya bud'i baki zai ce tare dashi yayi sallah juma'a da kayi jiya, ai dama mutuwa bata da kama in lokaci yayi dole a tafi, Alh Mado ya koka da rashin da yayi daga k'arashe ya barwa Allah yabi abokinsa da addu'a. Bayan sadakar bakwai, da kansa ya tara iyalin Alh Auwalu matarshi Hajiya Laure da "yayansa su bakwai namiji guda shine Khamis kenan,yace" Nine babban abokin Alh Auwalu, ni Alh Madu Gwadabe duk wata dukiyata da Alh Auwalu yake juyawa komai yawanta na barwa iyalinsa har abada ko bayan babu raina ban yarda a tada maganar ba, wannan magana nayi ta ne a gaban iyalina domin Ku zama sheda" Kuka iyalin Alh Auwalu suke,suna godiya ga Alh Madu suna jinjina nagartarsa, dukiya me tarin yawa wacce ba'asan kanta ba, anyi kyautarta lallai dole ayi wa Alh Madu jinjina. Wannan furucin da Alh Madu yayi ya mutuk'ar yiwa Khamis dad'i dama ta samu kenan yanzu zai famtama cikin dukiya shi kad'ai ne namiji kuma basu da "yan uba dole yayi yarda yake so da dukiya, Bai nuna komai ba, ya bar abun cikin ransa, yace" Baba mungode da wannan karamcin naka, Allah ya kara girma yaja kwana, da wannan nake Neman alfarma a barni in zauna nam domin in cigaba da kula da dukiyarnan ganin babu wani tsayyaye" Alh Madu yace"Wannan shawarar taka tayi kyau nima sai da nayi tunanin haka, dama dole yanzu ka tsaya ka kula da "yan uwanka gami da mahaifiyar ka, na amunce da maganar ka, saboda haka duk wani Abu da kake bukata kazo la tunkareni kar kaji fargabar komai har yanzu kanan a matsayin Habibu a gurina" Hajiya Laure taita godiya sauran "Yayanta suma sunayi. Haka Alh Madu ya tattara Iyalinsa suka tafi yana kewar Abokinsa Alh Auwalu Karku manta da cewar wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [19/08, 12:34] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿10* Wannan shine cikkaken tarihin Khamis. Yanzu ma ya dawo daga Aba ne,a cewarsa yaje sarin takalma sai ya fake da yawonsa ya biya b'ukatarsa da mata, shi mace ko arniya ce mutukar tayi masa sai ya kwanta da ita, duk wannan mugayen halayen nasa abokinsa bai sani ba, saboda sunyi nesa da juna yanzu,sai dai idan d'aye ne ya kai wa d'aya ziyara, haka ma Alh Moddobo kullum cikin ganin girman Khamis yake gami da nagartarsa. Sumayya ko tana sauka k'asa ta manta abunda ya faru tsakaninta da Khamis d'in ta cigaba da sabgoginta Kwanan Khamis uku da zuwa Habibu yayi Waya yace"A tareshi a airport misalin sha biyu na rana, gida ya rud'e da murna, yara da manya,hattaa da samarin gidan murna suke da dawowarsa, banda Sumayya duk ta b'ata rai tayi kicin-kincin da fuska duk inda taje ta zauna taji ana zancan dawowarsa gida sai ta bar gurin,k'arashe ma da taga ba'a ta ita,sai ta shig'e k'uryan d'akin Hajiya Tabawa babarsu Suwaiba kenan tayi kwanciyarta. Karkuce duk tsawon wannan kwana ki ukun Khamis be fasa tab'a jikin Sumayya ba,har indai yaga babu idanun jama'a a guri sai ya san yadda yayi ya tab'a wani b'angare na jikinta. Umulkairi ce ta shigo da gudu d'akinsu ta buga tsalle ta haye gado, sai murna take,a fili take cewa"Yayan mu zai dawo, nasan tunda naci jarrabawa inada kyauta ta mussaman,wayyo dad'i kashe ni in huta" Sumayya ta k'ulu iya k'uluwa,juya baya tayi taja tsaki gami da cewa"Aikin banza Aikin wofi kawai" Umulkairi ta juyo tana kallonta cikin mamaki tace"Dama kina cikin d'akin nan"? Banza Sumayya tayi mata, Umulkairi tace"Ni kike zagi ko Sumy,ai babu komai nagode Allah,watan cin ubanki ya kama,yaya ya dawo wallahi sai na fad'a masa irin rashin mutumcin da kikayi" A fusace!Tace"Ki fad'a masa mana don. Allah in kin fad'a masa kar ya barni da raina,ko an fad'a miki tsoransa nakeji kamar yadda kuke tsoronsa, k'arya kike" Sumayya ta k'arashe maganar cikin raini Umulkairi ta fidda hannu ta tsinka mata mari a fusace!tace yayan namu shine yake miki k'arya lallai Sumy baki da Hankali" Da hauka Sumayya tayi kan Umulkairi da duka,dama a fusace take,jin Umulkairin tana murna taci jarrabawa,ita bataci tasan dariya zasuyi mata suyi mata gwalo in yayi musu kyauta shiyasa ta fusata,takama Umulkairi da kokawa fad'a suke sosai,Umulkairi tafi Sumayya k'arfi kuma dama ta girme mata da shekaru hud'u,ita Sumayya mugun girman jiki ne da ita,gashi babu k'arfi, Umulkairi ta yar da ita k'asa, tana niyar gudu itama ta rik'e mata k'afa d'aya ta fad'i k'asa tayi saurin mik'ewa ta haye ruwan cikinta tana duka kamar wata "yar dambe, Umulkairi k'okarin kwatar kanta takeyi,Sumayya duk ta yakushe mata fuska,duk wasu dabaru na fad'a Sumayya ta sani, dak'ay Ummu ta cilar da Sumayya k'asa ta rugu da guda tana dariya,gami da haki!dad'i take shegiya sai kace mage duk ta ya kushe min fuska" Da gudu Sumayya ta biyo bayanta tana zaginta tana kuka,gashi dai itace taci galaba kan Ummu d'in amma kuka take,Mamansu ta tare ta tana tambayarta abunda ya faru,,k'okarin funcikewa take daga hannun Maman tana son kaiwa Ummu duka,Mama tace"Ke Ummu me ya had'a ku ne, wallahi na tsani tsokanar da kuke mata" Umulkairi tace"Wallahi Mama itace me tsokana haka kawai ta hau zagina tana zagin yayanmu" Cikin mamaki Mama ta kalli Sumayya tace"Hakane maganar ko kuwa " Shiru Sumayya tayi tana share hawaye. Hakan ya tabbatar wa da Mama gaskiya ne, b'ata fuska tayi tace"Kul! kinji na fad'a miki idan zaki rashin kunyar ki, ki tsaya idan kike, dan baki da hankali Habibun kike zagi, kar in k'araji,kinji ko baki jiba"? Kuka Sumayya ta fashe dashi,Mama ta shige d'aki abunta,Umulkairi ma tafiyarta tayi,ta cigaba da sabgoginta, Sumayya ko can saman babansu tayi tafiyarta ta kwanta tana kuka har bacci ya d'auketa. ******* K'arfe goma sha biyu da rabi na ranar Habibu ya sauka a gida, "Yan uwansa duk sun baibaye shi suna gaisawa cike da farin ciki, yake amsa musu, d'aya bayan d'aya ya shiga d'akin iyayen nasa suka gaisa,ya fito yana kallon " yan uwan nasa mata kowacce na zaune sunyi shiru, kallon Rab'ia yayi yace"Ina Sumayya take" Inda-inda ta farayi domin bata san inda take ba, Umulkairi tace"d'azu tana nan, inaji tana sama gurin Baba" Habibu yace"Baba,yana waje can na baroshi yana hutawa a waje" Hajiya Gaji tace"Tana sama tana bacci, d'azu da na hau na ganta,indai ba ta tashi ba" Shiru sukayi, Khamis ya mik'e da sauri ya nufi hanyar futa, shima Habibu mik'ewa yayi ya kalli "yan uwan nasa yace" Ku bari inje inyi Wanka in huta tukkuna zan zauna da kowacce a cikinku" Hajiya Gaji tasa dariya, tana fad'in lallai kuwa yau zamu sha kallo da dariya" Ya k'okarin tafiya yace"Duk wacce batayi abun arzik'i ba a makaranta ai ta san sauran, babu duka babu zagi sai dai taga anayi" Yana gama maganar ya futa daga falon d'akinsa ya nufa. Khamis kuwa da yayi saurin mik'ewa ya nufi sama,kai tsaye d'akin Baba ya bud'e ya shiga . aikuwa Sumayya ya gani kwance kan kafet din dake shimfid'e a kasa tana bacci sosai, dake dogon Wanda ne a jikinta da k'aramar riga me dogon hannu, duk sai hallitun jikinta suka bayyana, jikinta ya shika bacci take sosai, kura mata ido yayi yana mata kallon k'urulla wata irin sha'awarta tana bijoro masa, zuciyarsa na ingizashi kan yaje yayi mata abunda ya saba,yanzu tunda bacci take,ko ya samu ya rage rad'ad'in sha'awar da yake ji, motsi yaji alamun za'a hau sama, yayi saurin dawowa hankalinsa,jin ana tab'a kofar d'akin yasa ya wayance da zuwa gaban tv ya tsuguna yana duba kasa-kasai.Habibu ne ya shigo d'akin, suka had'a ido dashi, yace"Kai dama nan ka shigo" Cikin wayancewa Khamis yace"Eh mana ina duba kasat ne, yau kallon hausa film nake sha'awa" Tab'e baki Habibu yayi yace"kallo baya isarka kai kam,ina fata ba'anan zakayi ba,kar ka tashi Sumayya daga bacci" Khamis yace"Banan zanyi ba, yanzu zan shigo muci abunci ai" Futa Habibu yayi daga d'akin, Khamis ya mik'e shima yana waiwayen Sumayya, har ya futa yana cizon ya tsa. Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne, naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan. 08089965176 07084653262 [20/08, 16:54] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation e: ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿11* Habibu na shiga d'akinsa yayi shirin yin wanka, wani katon towol ya d'aura a jikinsa ya shiga toilet ya wanke jikinsa tas ya futo ya tsaya gaban dressing miroow yana taje sumarsa ya sanya mata mayu ka, dake yanayin zafi bai shafa mai ba, turare kawai ya fesa a jikinsa, ya sanya wasu Jesi kaya irin na "yan ball kayan sun masa kyau sosai, da yake yana bala'in son kwallon k'afa shiyasa yake yawan sanya kayansu, yana son " yan k'ungiyar arsenal in kaji ana musu dashi akan ball sai ka rik'e baki,kallo in ba na ball ba babu wanda yake tsayawa yana mayar da hankali a kansa,sai dai ko labarai. Khamis ya bishi da kallo lokacin da yake k'okarin zama kusa dashi,yace"Shikkenan an dawo fagen fama, za'a cigaba da fafatawa ko" Habibu yasa dariya gami da bashi hannu suka tafa yace" To me za'a fasa, ai yau sai na futa majalisa na buwaye su" Khamis yace"Kamar ka sani kuwa d'azu da safe da naje, Lurwanu yake tambayar ka" Habibu yace"Gani nadawo ai,zamu had'u da juna" Hira suka cigaba da yi irin ta abokain da suka yarda da junansu, sukaci suka sha suka k'oshi, Habibu ya mik'e kan doguwar kujera yana lumshe ido,bacci na fuzgarsa kad'an shi kuma Khamis kaset d'in da ya d'auko ya sa a DVD ya fara gani,yana cin dariyar d'an Rabilu musa d'an ibro, cikin kaset d'inshi na *Ka kiyayi me nema* ganin film d'in dan Ibro ne yasa Habibu mik'ewa zaune yayi yana dariya duk rashin son kallo irin nasa, indai film din Ibro ne, yana kalla,dan yaci dariya. Giftawar Sumayya ya gani tana kokarin sauka kasa sai faman sosa soshe take, saura kadan ta fadi saboda idanunta a rufe suke rike karfen barandan tayi ta bude idonta kadan tana kallon hanya, Ransa ne ya b'aci ganin irin kayan da suke jikinta riga da wando ne duk sun matse ta sun futo mata da shatin jikinta gashinan, shi kuwa Khamis kallonta yake kamar tsohon maye, Tsaki yaja ya had'e fuska tamau ya kira sunanta a kausashe! Gabanta ya fad'i jin muryar Yayarmu sai tayi bude idon nata gaba d'aya tana kokarin sauka kasa da sauri, Da k'arfi yace '' Sumayya mutukar kika sauka kasa baki kiran da nake miki ba sai na b'ata miki rai! Tsayawa tayi tana sosa kai kamar mara gaskiya ta koma da baya simi simi hannuta ta sa abaki tana cin farce taje ta tsuguna gabansa, baki na rawa tace'' Yayanmu ina wuni an dawo lafiya''? Harara ya banka mata. Batare da ya amsa mata gaisuwar taba yace, '' Dan ubanki ban hanaku sa kananun kaya ba? wato kece me kunan k'ashi ko'' Yafad'a yana murd'e mata kunne. Khamsi ya b'ata fuska yace'' Wanan cin zali ne kawai ka kama yarinya kana murd'e mata kunne duk abunda tayi k'uruciya ce in ta girma zata daina'' Babu abunda yace wa Khamis d'in ya cigaba da murde mata kunne. Yace '' Kika sake na sauko na same ki da wannan kayan a jikinki sai na zane ki wallahi kin san zan iya ko'' D'aga kai tayi cike da tsoro idanunsa ta kalla ta gansu jazur tasan bashi da imani dukanta zaiya. rank'washi ya buga mata a ka cikin tsawa yace'' Tashi ki bani guri munafuka kawai. Zan zo ai in tambayi duk abubuwan da kikayi da banan'' Da sauri ta mike daga kusa dashi ta ruga a guje, tana sauka matattakalar farko ta kurma ihu! sosai da gudu ta afka d'akin Hajiya Tabawa tana kuka kamar wacce a kaiwa dukan tsiya Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira d'ari ga me bukata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [20/08, 21:38] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿12* Hajiya Tabawa na tsaka da ninke kayanta na sawa taji ihun Sumayya, girgiza kai tayi kawai ta cigaba da nin ke kayanta tana fad'in, '' Ke kam Sumayya naga ranar da zaki daina shagwaba wallahi.ke kenan kuke-kuke bakya gajiya' Cikin kuka Sumayya tace' Hajiya yayanmu ne ya rank'washe ni akaina kin san kuma babanmu ya hana a tab'amin kai saboda ciwon kan da nakeyi wallahi yanzu ma kaina ya fara ciwo' Ta karashe maganar cike da shagwaba da sangarta. Tab'e baki Hajia tayi tace'Wannan ciwon kan naki ai na sangarta ne,haka kawai sai kice baza ai miki kitso ba in aka tab'a kan ko yaya ne sai kice kanki na ciwo sai kace wata mai iska' Kuka Sumayya take sosai cikin zuciyarta tana wa Habibu Allah ya isa domin babu hali ta zageshi gaban Hajia tasan halinta tana da zafi zata iya kai mata duka. Babansu ne ya shigo gidan yana sanye da wani yadi fari tas anyi masa d'inkin babbar riga kanshi da hula dara irin ta mutan da, hannushi rike da carbi fari tas dashi, tunda soran farko yake jiyo kukan shalelensa dan haka da sauri ya k'arasa shiga cikin gidan da sallama a bakinsa. Hajia Gaji na zaune kujera tana gyara kayan miya ta amsa masa. 'Alh Sannu da shigowa' Hajia Gaji tafad'a tana gyara zamanta Amsawa yayi yace'Kukan me Sumayya take ne, tun daga soro nake jin kukanta. Hajia Gaji tace' Yanzun nan ta sauko daga sama, bacci take tun d'azu amma inajin ita da Habibu ne, ai gwara da ya taso ta taci abunci ta tafi makaranta duk "yan uwanta sun tafi tun d'azu" Alh. yace"Shikkenan sarkin cinzali ya dawo zai tasa min yarinya a gaba da duka kamar wanda ya samu jaka, bari zai shigo y same ni ai" Hajia Gaji shiru tayi kawai tana d'an murmushi tasan halin fad'an mijinsu a kan Sumayya kwata-kwata baya son jin kukanta. D'akin Hajia Tabawa ya nufa inda yake jiyo kukan Sumayya. D'aga labule yayi ya shiga dakin cikin fad'a yace"Kina ji yarinyar nan tana kuka kinyi burus da ita ko" Hajia Tabawa tace"Nayi -nayi tayi shiru taki yi alh kasan kukan Sumayya babu mai rarrashinta sai kai" Da sauri Sumayya ta mike daga kan gadon taje ta rike hannun baban nasu tana fada masa irin cinzalin da Habibu yayi mata harda sharri ciki Hannuta ya rik'e suka futa daka dakin. Sama suka nufa suna tafe yana rarrashinta kamar k'wai Yace "Ki share hawaye ki zan samu Habibu in ja masa kunne kan kar ya k'ara dukanki" Shiru tayi tabar kukan suka haura sama, har yanzu d'akin Habibu a bud'e yake yana hango hawowar babansu da Sumayya ya mik'e zaune sosai yana me k'ara daure fuskarsa saboda yasan yanzu zai tuhume shi kan me yasa ya daki Sumayya, aikuwa dai-dai k'ofar d'akinsa ya tsaya yana ya mutse fuskarsa ya kalli Habibu da b'acin rai a fuskarsa yace" Kar ka kara dukan ta har ka koma inda ka futo.shikkenan kazo gida bata da kwanciyar hankali sai duka da kyara me ta tsare maka ne"? Gyaran murya yayi yana d'an sunkuyar da kai yace" Alh wannan yarinyar bata da tarbiya duba fa ka gani irin tufafin dake jikinta, tuntuni na hanasu sakawa sauran sun daina ita tak'i jin magana, saboda tana samun d'aurin gindi a gurin ka, tarbiyarta tana iya lalacewa" Cikin fad'a Alh. yace"kafi ni ido ne, da har zakace min in dubi tufafin dake jikinta yarinyar guda nawa take da gar kake min wannan zancan, na fad'a maka kar ka kara dukanta" Habibu ransa ya b'aci jin abunda mahaifin nasu yake cewa kan Sumayya wannan na nuna cewar gata zai yi sanadiyar lalacewar ta, wanda yana ganin haka ba gata bane abunda yake nunawa yarinyar tunda amanar Allah ce ita, Ubangiji yace " yayanku amanarku ne kuma amana ta ne,zan tambaye ku ranar lahira to balle kuma Sumayya da take marainiyya wacce bata san uwarta da ubanta ba bata san kowa nata ba a sali ma batasan wacece ita ba ita dai kawai ta so cikin gata da kulawa gami da soyayyar iyaye biyu wato Alh MADU da HAJIYA Zulai matarsa ta uku kenan. _*Wai shin wacece Sumayya?*_ SHEKARU GOMA SHA BIYU DA SUKA WUCE. ALH. Madu ne tare da matarsa Hajiya Zulai suna tafiya cikin mota hanyarsu ta zuwa abuja shekaru goma sha biyu da suka wuce. Akwai wani kamfani da k'warori suke bude a abuja ake har kar taklma a wancan lokacin. suka nemi sa hannun ALh MADU saboda shaharasa a duniya ta fannin kasuwanci ko wane iri ne, babu wani b'ata lokaci ya amunce musu ya zuba dukiyarsa aka fara aiki sosai ake samun albarka, ba sosai yake zuwa ba sai dai duk abunda yake faruwa yana da labarinsa. Kwatsam!ranan ya shirya tare da matarsa suka nufi abuja cikin motarsa kirar toyota wanda a lokacin sai wane da wane. Dake futar asuba sukai shiyasa suka yi sauri sun wuce kaduna kad'an dai-dai wani k'aramin gari motarsu ta tsaya taya tayi faci. Alh Madu ya futo da sauri yana dubawa lokacin shida da kwata na safe gari ya soma yin haske. d' agowar da zaiyi kawai ya hangi wata ba fulatana ta yanko daga wani daji da gudu jikinta sanye da kayan sak'i irin nasu hannuta nan nad'e da wani abu ta rungume sai gudu take. Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira dari biyu ne ga me bukata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [21/08, 17:37] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _Mu fad'i alkairi ko muyi shiru,mu kiyayi aibata wani ko cin zarafin wani,ba tare da hakkinsa ba, mu kintsa harshen mu,domin yana iya kaimu ya baro mu guji k'yashi da hassada ga jununmu, domin mu samu rabo a duniya da lahira, muyi wa kanmu kyakykyawan zato, mu giji fad'ar abunda ba,tayi ba, muce anyi, A kwai ranar tsayuwa ta ranar mahashar,ranar da kowa yake ta kansaUwa Uba Miji mata "yaya, K'awa Aboki kowa na takansa, mun sanyawa Harshenmu linzami_ *Allah kasa mu dace* _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿13* Kafin Alh Madu ya ankara matar tayi kan titi da gudu, bata kallon gabanta bare bayanta, wato mota k'irar marsandi tazo tayi gaba da ita,abunda yake hannunta ya gangara bakin hanya. Salati Alh Madu yayi ya nufi inda matar take kwance tana nishi cikin jini,me motar kuwa yayi nasa guri, Hajiya Zulai ta futo daga mota da sauri,bakinta d'auke da Kalmar innalillahi wa'inna ilahi raji'un. Kukan jariri taji da sauri ta nufi inda take jin kukan ta dauke jinjiri sabuwar haihuwa,bata tsaya dubawa mace ko namiji kawai ta nan nad'e shi,ganin babu ko wando a jikinsa, kusa da mijinta ta matsa tana nuna masa jaririn dake hannuta, shi hankalinsa na kan matar, gashi sai nishi take,tana k'okarin mutuwa babu mataimaki, da sauri ya mik'e yaje ya bud'e but d'in motarsa ya ciro tayar mota,yazo ya kwance wacce ta sace ya daura wacce ya d'auko, da kansa ya zo ya kinkimi matarnan cikin jini yaje ya sanyata a mota,Hajiya Zulai taje ta shiga tana rungume da jariri sabuwar haihuwa,gwanin tausayi sai kuka yake, cikin tausayi da tu'ajibi ya kunna motar suka bar gurin,sauri kawai yake ya isa abuja, domin ya kai matar asibiti a dubata ganin yadda jini yake ta zuba ta baki ta hancinta,ga kanta ta fashe duk jikinta ya kurje,da alama batasan inda kanta yake ba, wani babban asibiti suka isa, da sauri ya futo daga motar ya bude gidan baya inda take kwance rai a hannun Allah,ya ciccib'ota, fuskarta kawai ya kalla ya tabbatar da cewar rai yayi halinsa,amma domin ya kara tabbatarwa yasa ya shiga da ita asibitin, ma'aikaita sai kai kawo sukeyi, suna ganinshi, da sauri suka k'araso, suka karbeta daga hannusa, kai tsaye, Emagency aka nufa da ita. Duk wasu aune-aune sunyi sun duba ta sosai matar Allah yayi mata rasuwa mintuna talatin da suka wuce,haka suka futo suka sanar da Alh Madu, dama ya san haka, innalillahi ya furta a fili yace"Allah ya jikanki wannan baiwar Allah, wannan abunda kika bari kuma Allah ya rayashi ya albarkaci rayuwarsa,nan Alh Madu ya sanar da hukumar asubitin abunda ya faru dashi,da matar kuma ya nuna yana bukatar taimakonsu kan yadda za'ayi rayuwar wannan jaririyar da tabari ta inganta, shawarwari sosai suka bashi, kan abunda ya nema, suka d'ora baby kan madara irin wacce ta dace da ita, a takaice dai, wasu daga cikin ma'aikatan asubitin dasu akai jana'izar matar da ba'asan daga wace duniya take, Alh Madu yayi musu godiya sosai kuma ya sakar musu kud'i yadda ya kamata, sannan suka kama hanya suka bar asubitin, kai tsaye gida suka koma,domin ji yayi bazai iya zuwa wani guri ba, da jaririyar yarinyar domin wani irin so da tausayinta yakeji a zuciyarsa,yana tausayawa rayuwarta, *** Kaf ya tara matansa ya sanar musu halin da ake ciki,to suma dake sun san meye rayuwa sun tausawa rayuwar Sumayya, Alh Madu yace"Bayaso su tab'a nuna banbanci tsakanin Sumayya da yayansu, duk suka d'auki Wannan alk'awari, Masu hankali daga cikin yaran gidan sune suka fahimci abunda yake faruwa, amma sauran k'ananun yaran murna sukeyi wai Hajiya Zulai ta haihu,Rab'ia sai murna take, ta samu k'anwa. Alh Madu shine ya zab'a mata suna Sumayya, Hajiya Zaliha ta cigaba da rainonta cikin kulawa,itama haka kawai take jin tausayin Sumayya ita kuma haka zata taso batare da tasan suwaye iyayenta,menene tushenta wannan abu na d'aga mata hankali. *Wannan shine tarihin Sumayya* Shida da rabi na yamma "yan makaranta suka fara dawowa, Alh Madu na zaune kan wata kujerar k'arfe wacce yake zama yana shan iska a k'ofar gidansa yana kallon hanya, da yara " yan makaranta, Sumayya na zaune kusa dashi da goro ba,a hannuta tana ci, ko kishin kanta batayi,ganin yadda yara suke ta wucewa ko wanne sanye da uniporm na makaranta, can ya hango iyalinsa sun tawo reras da su abun sha'awa, ya kalli Sumayya, a tausashe yace" Yanzu Sumayya bakya yiwa kanki fad'a ba, dubi "yan uwanki fa,suna zuwa makaranta ke kink'i kin tsaya wasa, ko kinaso in had'aki da Yayanku ne"? Girgiza kai tayi,tana cigaba da cin gorobar ta,yace" To indai kina so mu shirya dake,kar in k'araji anyi rigima dake, gurin zuwa makaranta,lokaci na yi kiyi himma,kinji ko, in naga kina maida hankali ke zan fara kaiwa Umara" Dariya take sosai ta rik'e hannusa cike da k'uruciya tace"Don Allah da gaske kake Babanmu" Fuskarsa a sake yace"Kwarai kuwa ke dai ki maida hankalinki kan karatu ki gani" Tace"Insha Allahu zanyi,amma zaka bani kud'in makaranta wanda yafi nasu Ummu da Rabi'a ko"? "Ke zan bawa a hannuki ma,in zaku tafi, makarantar sai ki rarraba musu" Jin abunda yace ne yasa tai ta murna da dariya. Su Rab'ia duka k'araso tsugunawa sukai dukaninsu sukace"Babanmu Sannu da hutawa" "Yawwa sannu ku, Rabi'a kun dawo" Suka amsa da "Eh mun dawo Baba"? Yace" Allah yayi muku albarka,to ku shiga gida" Har sun wuce, Suwaiba ta dawo da baya,tana kallon Sumayya dake musu wani irin kallo,yace" Ke Sumayya malam Mubarak yace"Wallahi zaku gamu ne, yana lissafa iya adadin fashin da kikayi, sai ya zane miki jiki" Cikin tsiwa Sumayya tace" Eh ai dama kune masu zugashi ya dake ni, gobe zanje,kuma Babanmu ne zai kaini sai inga ta inda zai dake ni" Suwaiba tace"Oho miki dai!ke kika sani" Sumayya ta mik'e da sauri jikinta na b'ari tace"Babu ruwanki dani,tunda dai ni kinga ban kulaki ba,ko"? Alh Madu yace"Ke Suwaiba wuce gida,bana san tsokana" Suwaiba ta wuce gida,tana mamakin masifar Sumayya daga magana ta mik'e tana k'okarin kamata da kokawa" Bayan tafiyar Suwaiba Sumayya ta koma ta zauna,tana zumb'ura baki tace"Babanmu gobe ka kaini makarantar da kaina idan ba haka ba,nasan muguntar Malam Mubarak wallahi" Alh Madu Yace"Allah ya kaimu lafiya,ai dai kinyi min alk'warin baza ki k'ara fashi ba ko"? D'aga kai tayi Yace"Yawwa" Suwaiba kuwa Dai-dai soro na biyu suka had'u da Habibu shi da Khamis zasu futa,ta durk'usa har k'asa ta gaishe su, suka wuce,ita kuma ta mik'e ta shiga Gida. Abun mamaki suna futa ya ga Sumayya na gwagwuyar goroba sai kace wata akuya,babu kamun kai,a tare da ita, still haryanzu,Wannan kayan ne na jikinta Wanda yace ta cire, wato bata ciresu ba,saboda tana ji da taurin kai,lallai dole yayi maganinta. Tana ganinsu ta d'suke kanta,domin bata so su had'a ido da Habibu,shi kuwa Khamis sai wasa yake mata,ta sha kunu,tak'i kulasa Shima bai kalli inda take zaune ba. "Barka da yamma" Yafad'a yana mik'awa mahaifin nasu hannu" "Barka ka dai" Alh Madu ya fad'a,Khamis ma gaisawa sukayi cikin mutumci, suka wuce majalisar su. Karku manta da cewar Wannan book din na kud'i naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nab. 08089965176 07084653262 [22/08, 14:16] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿14* A na kiran sallahr magariba Alh Madu ya shiga gida domin d'aura al'wala, Sumayya na bayansa sai kace jela, Alwala ya d'aura ya futa zuwa masallaci, Ita Alwalar ta d'aura, ta shige d'akinsu babu wanda tayi wa magana a gidan. Bayan ta idar da sallah ne ta kwanta kan dadduma bacci na neman d'auke ta. Hajiya Zulai ta shigo d'akin, ganinta a kwance kan hanya tace"Ke ki tashi ki ci abunci sai ki kwanta, magariba nayi zaki hau bacci sai kace wata kaza" M'ikewa zaune tayi, tana mutsika ido, Hajiya Zulai ta d'auki abunda zata d'auka ta futa,Sumayya ta mik'e tabi bayanta. Habibu ne ya dawo gidan, yana rarraba ido neman Sumayya yake,da bai ganta ba, a tsakar gidan, sai ya nufi d'akin Hajiya Zulai sukayi kicib'us da ita, ta futo daga d'akin, Sumayya na bayanta. Babu abunda yace Kawai ya kamo hannu Sumayya, ido ta bud'e jin an mata rik'on tsauri, Yayanmu ta gani yana janta, bud'e baki tayi zata kurma ihu ya rik'e bakin. Hajiya Zulai tace"Wato da kaga Alh ya futa shine ka dawo domin kaci zali ko" Shiru yayi yaja Hannun Sumayya tana turjewa ya kaita d'akin. Girgiza kai Hajiya Zulai tayi kawai tai tafiyarta. "Wayyo Hajiya ta" Abunda Sumayya take fad'a kenan. "Babanmu kazo ka taimake ni" Tsawa! Ya buga mata, yace"Rufe min baki,ko in ci Ubanki" Tsitt!! Sumayya tayi tana zare ido,ga d'akin da duhu Hajiya bata kuna fitila ba. Zatinsa kawai, take gani a d'akin, cikin tsawa yace"Cire wannan kayan na jikin ki,kiyi shirin makaranta" Jikinta na kyarma ta fara cire kayan jikinta,dake da duhu a d'akin ba sosai yaga jikinta ba,yana tsaye da fuska a murtuke Ta bud'e sif d'in kayansu ta d'auko doguwar riga , ta zura da sauri ta d'ora hijabi a kai, yace"Wuce muje" Simi-simi tayi gaba yana bayanta suka, Tsayuwa yayi tsakar gidan, yana kallonsu Rabi'a suna cin abunci Yace" Ke Suwaiba da kungama cin abunci, ku tafi makaranta tare,in ta gudo ko tayi barci, a makarantar ku fad'a min" Suwaiba tace"To" fucewarsa yayi daga gidan,dama abunda ya dawo dashi kenan. Hajiya Gaji ta zuba mata abunci ta zauna tana ci tana gyangyad'i domin baccin ya hau kanta sosai. Kad'an taci ta cire hannuta, taje ta wanke, sai zumb'ura baki take. Babansu yaji dad'i da yaganta cikin a yari zasu tafi makaranta, ya basu kud'i duk da cewa ta magariba ce, in sun dawo hanya suna tsayawa siyi siye-siye irin nasu gyad'a me gishiri da Aya me sukari. Rab'ia na lure da Sumayya sai gyangyad'i take sam bata fuskanci, karatun da akai ba,haka aka tashi daga makaranta, Suwaiba ta rik'e mata hannu dan kar ta fad'i. Har yanzu Alh Madu na zaune a inda yake, yanzu suna tare da wani mak'ocinsa suna hira. Yaga ana rirrik'e Sumayya tun daga nesa,suka k'araso, inda yake, yace" Yaya kuke rik'eta ne" Ummulkairi tace"Bacci takeyi a hanya" Dariya Alh Madu yayi yace"Sumayya kenan, to maza ku shiga ciki kar ta fad'i" Ciki suka shiga, Alh Madu suka cigaba da hira da mak'ocinsa. Duk suna zaune tsakar Gida, suka shiga, Hajiya Zulai tace"Nasan za a rina dama,ai in bacci ya hau kanta, sai tayi ko a ina ne, Hajiya Tabawa tace" Ai kuwa dole ko zata dunga baccin a makaranta ta dunga zuwa sai ta saba" Dariya suke wa Sumayya sosai. K'asa ta kwanta,hijab d'in jikinta ma Rab'ia ce ta cire mata. Hajiya Gaji tace"Ai saboda baccin da take da wuri shiyasa take riga kowa tashi da wuri, gashi abunci da na zuba mata ma kad'an taci" Hajiya Zulai tace"Sai da safe kuma ta tashi da yunwa" Haka suka cigaba da hirarsu cikin fahimtar juna har wajan goma na dare, daga bisani sukayi sallama da junansu ko wacce ta shiga d'akinta domin shirin kwanciya. Karku manta da cewar wannan littafin na kud'i ne naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan. 08089965176 07084653262 [23/08, 13:00] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿15* Washe gari da wurwuri Sumayya ta tashi daga bacci ,domin ko irin baccin nan na bayan sallah Asuba bata koma ba, shirin makaranta takeyi, cikin walwala,yau za'abata kud'inta a hannuta ta siyi abunda ta ke so, yau me alawar madara za tayi cini ki a gurinta, tsaf ta shirya, hatta da takalmi da safa ta saka, su Suwaiba sai dariya suke mata, tana kallonsu tai musu banza,domin tasan tayi musu wani abun, Yaya Habibu dukanta zai yi, ba tare da ya bi ba'asin waye me tsokana a cikinsu ba,amma dole sai ta gayawa Babansu domin yaja musu kunne babu ruwansu da ita. Kai tsaye sama ta nufa gurin Babansu, tana taka matattakala ta uku, Habibu ya futo daga d'akinsa, yana sanye da riga da wando ga jere irin na "yan ball, wuyansa rataye da wani k'aramin towol, k'afarsa takalmi ne irin na " yan ball, da'alama motsa jiki zai futa. Kallo guda yayi mata ya kauda kansa, ya fara saukowa. Sai ta ja ta tsaya, tana jira ya sakko sai ta hau, hannunta ta zura a bakinta, as'usul ta fara cin farce kamar yanda ta saba in ta ganshi. Wannan d'abi'a da take in ta ganshi yana mugun b'ata masa rai,yana zuwa dab da ita,yasa hannu ya buge hannuta dake bakinta, fuskarshi babu walwala,yace"Wallahi duk sanda kika k'ara ganina ki ka saka hannu a baki kina cin farce, sai na sa, d'an Yaya me yankan farce, ya cire miki farcen gaba d'aya, sai inga ta iskanci, shashasha kawai" Wasu hawaye ne suke k'okarin zubo mata,taji haushin abunda yayi mata,k'okarin danne hawayen take tana son hanasu su zubo,bakinta na rawa tace"Yayanmu ina kwana" domin tasan wata masifar ce idan bata gaishe ba" A banza ce ya amsa ya wucewarsa yana wata tafiya irin ta "yan kwallo. Sai da ya futa, ta fara goge hawayen da ya ke ziraro mata,tana jin wata irin tsanar sa a zuciyarta, duk gidan babu wanda yake kyararta gami da hantararta sai shi,duk sauran " yan uwansa maza suna mata wasa ban dashi,Yaya Auwal har yawo yake tafiya da ita, a cewarsa,duk tafi sauran kyau ita ta shiga mutane ce. Babansu na ganinta ya saki fuskarsa sosai, yace"Lallai yarinyata me jin magana ce, Allah yayi miki albarka" Tsuguwa tayi kusa dashi tana gaida shi,ya amsa da fuska a sake. Nazarin ta yake, yaga fuskarta babu walwala yace"Waye ya tab'a min ke da safiyar nan"? Shiru tayi ta zumb'ura baki,domin babu halin tace"Yaya Habibu ne, tasan fad'a zai yi masa, shi kuma Yaya Habibu, zai iya dukanta a kan haka. Girgiza kai yayi yace"Rabo dasu kinji ko,kinga je ki d'auko jakar alawa,cikin wancan kwalin, ki tafi da ita makarantar,ki bawa duk wanda kike so." Da sauri ta mik'e taje ta bud'e kwalin da yake nuna mata,ta ciro jakar Alawa gudu,ta farke ta ciri biyu ta b'are, ta sa abakinta,tana tsotsa. Dariya Alhaji Madu yasa yace"Uwar shan zak'i kenan, nasan dai babu komai a cikin ki,tunda safiya ce,yanzu kije ki karya tukkuna,sai ki sha alawar amma kar ki k'ara sha yanzu kar ta k'ulle miki ciki." Gyad'a kai tayi, tace"Babanmu bani kud'in to" Wata durowa ya bud'e ya ciro gudar dari biyu,yace"Gashi ke ki d'auki naira Hamsin, d'ari da Hamsin d'in kuma sai su raba, sauran "yan uwan naki" Wannan magana da yayi, itace ta tuno mata da bashin, da take bin Rabi'a shaf! ta manta, Lallai kuwa yau zata bata kud'inta wallahi ko ta tona mata asiri,tunda itama dariya suke mata. Karb'ar kud'in tayi daga hannunsa ta mik'e tana godiya,shi kuma ya nai musu fatan dawowa lafiya, har ta bud'e k'ofar d'akin zata futa, sai ta tsaya, tana kallonsa tace"Babanmu "Za'ai min dukan fashi fa,kace zaka kaini da kanka,ka basu hak'uri" Girgiza kai yayi yace"Kije kawai, jiya na tura Yayanku Habibu yayi magana da malaman makarantar" Dariya tayi cike da farin ciki ta futa daga d'akin. Tana sauka k'asa ta zura jakar alawar da kud'in a jakarta, ta nufi kicin domin d'auko kayan karin kumallon ta. Wani irin kunun gyad'a ne fari tas dashi ya sha madara,sosai sai k'osai jazur dashi,yaji attaruhu da albasa,ta zauna babbar rumfarsu ta fara shan abunta. Sauri-Sauri ta kammala karyawa ganin duk sun shirya, ita kad'ai kawai suke jira. Sallama sukaiwa iyayen nasu suka tafi, Suwaiba zata hau sama domin karb'o kud'in makaranta, Sumayya tace"Ke Suwaiba ga kud'in nan" "Au! Ashe kin karb'o" Suwaiba ta fad'a. D'aga kai Sumayya tayi suka futa. Karku manta da cewar wannan littafin na kud'ine naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [23/08, 16:10] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿16* Sai da aka futo break, Sumayya ta fasa d'ari biyun ta d'auki naira hamsin d'inta,ta tafi ajin su Rabi'a, tana shiga ajin nasu,ta rik'e k'ugu ta tsaya tana neman inda suke da ido. Wata k'awarsu ce ta hangota, ta tab'o Suwaiba da hannunta "Suwaiba ga wannan k'anwar taku nan" Suwaiba ta hango Sumayya, bakin k'ofar ajinsu tana harare-harare, tasan halin tsokanar Rabi'a zata iya tsokanar wata cikin ajin ko tayi mata rashin kunya,kuma gashi duk ba sa'ointa ba ne, Mik'ewa tayi ta nufi inda take. Zumb'ura baki Sumayya tayi tana mik'a mata kud'in tana fad'in "Ga kud'inku nan, na d'auki cikon d'ari ta, wacce nake bin Rabi'a" Suwaiba ta karb'i naira Hamsin a hannuta tana juyawa cikin mamaki tace"Bafa na san neman rigima ke Sumayya,ai ba Rabi'a ce kad'ai me kud'in ba, da zakije kice kin d'auki kud'in ki" Sumayya na k'okarin futa daga ajin tace"Oho muku ni dai na d'auka, ai sai da na fad'a miki kece shaida,kina kallo bata bani kud'in ba, saboda na manta,to yanzu na tuna, kuma na d'auka" Sakin baki Suwaiba tayi kawai tana bin ta da kallo har ta futa daga ajin nasu, Malamin Hausa ne ya shigo, tayi saurin koma wa ta zauna. Bayan ya futa suka futa break, Suwaiba ta fad'awa Rabi'a abunda Sumayya tayi musu, haushi ne ya kama Rabi'a a fusace ta nufi ajinsu Sumayya. Tana zaune tsakiyar k'awayenta,suna hira irin tasu ta k'wailaye sai dariya sukeyi, Sumayya tace"Ke ikilima naji fa ranan Yaya Rabi'a na cewa wai da dad'i abunda kike fad'a, kuma ba iskanci ba ne" Ikilima tace"Meye ba iskanci ba? Sumayya ta mak'e murya tace"Tsotsar bakin juna,tsakanin mace da namiji" Ikilima tace"Wallahi iskanci ne kuma k'azanta ce, haka kawai sai in tsaya namiji na tsotsar bakina,tab d'ijam" Suka kwashe da dariya har da tafawa, Abashiyya tace"Wallahi naji dad'i da Malam Anas be shigo ba,sai shanawar mu muke" Hango shigowar Rabi'a tayi. Kicin-kicin tayi da fuska,tana jiranta ta k'araso kujerar zamansu Rabi'a tazo ta tsaya kusa da ita fuskarta a had'e tace"Dan uwarki ina kud'inmu yake"? "Na kashe su" Sumayya tafad'a kai tsaye! Cikin tsawa Rabi'a tace"Wallahi k'arya kikeyi idan baki futo min dasu ba yanzu nan zan je in had'aki da Malama Sakina" Jin abunda Rabi'a tace yasa jikinta yayi sanyi tasan halin Malama Sakina muguwa ce,ta iya duka, ita kuma tsoran bulala takeyi. Cikin tsiwa tace"Kud'ina na d'auka ai baki biyani cikon d'ari ta ba" Rabi'a tace "Dan ban biya ki ba, kuma sai ki d'auka anan dan baki da hankali, ai ba kud'ina ne duka ba, ki bari idan mun koma gida zan baki" Shiru tayi na minti biyu,ta zura hannu cikin jakarta ta d'auko d'arin ta mik'a mata. Rabi'a ta karb'a, ta fucewarta daga ajin, tasan da badan tayi mata jan ido ba, baza ta bata ba. Ita kuwa Sumayya, taci alwashin tonawa Rabi'a asiri tunda ta kasa cika mata alk'awari, sai yawo take mata da hankali. Ko da aka tashi daga makarantar tafiyar kowa daban-daban sab'anin yadda suka tafi da safe, Sumayya ta rigasu zuwa Gida, tana addu'ar Allah yasa yayansu bai futa ba, tana shiga soro taji sautin Tv ana kallo hamdala tayi w zuciyarta, da sauri ta haye sama, babu wata fargaba a zuciyarta ta tura k'ofar d'akinsa ta shiga da sallama. Khamis na zaune kam kujera me cin mutum d'aya daga shi sai gajeran Wando kallon wak'okin India yake yana kurb'ar lemo abunsa. Suka had'a ido da Sumayya, ya wani lumshe ido tsigar jikinsa na mik'ewa, zama ya gyara sosai yana sakar mata wani k'ayattacan murmushi, itama murmushi take ta k'arasa kusa dashi,gami da zama hannun kujerar da yake zaune,tana gaishe shi. Amsawa yayi yana bin ta da wani mayen kallo. Tace" Yaya Khamis ina yayamu"? Lumshe ido yayi yau k'asa da muryarsa yace"Yana toilet yana wanka, menene"? Sosa kai tayi cikin inda-inda tace"K'arar Rabi'a na kawo masa" K'aramin bakinta yake kallo yana jin kamar ya kamo ya tsotsa,yace"Me Rabi'ar tayi"? "Uhumm" ummm, Wani abu tayi" Tafad'a tana cin farcenta as'suel. Kallonta yake, kamar wani tsohon maye yace"Ki fad'a min mana" "Kaga fa Yaya Khamis dama Rabi'a da Suwaiba ne, naji suna wani zance irin na " yan iska, she karan jiya" Khamis yace"Fad'a min zancan da suke" "Ji nayi Rabi'a na cewa wai mijin k'awarta yana tsotsar bakinta,kuma itama tana so, wai dama ai mata aure, itama mijinta ya dunga tsotsar bakinta" Wani irin yarrrrrr! Khamis ya dunga ji a jikinsa, idanunsa ya fara sauyawa murya a dusashe yace"Da mugun dad'i hakan wataran zan yi miki kiji, kema zaki so hakan" Tab'e baki Sumayya tayi, tace"Allah ya sawak'e m......Habibu ne ya futo daga toilet daga shi sai gajeran wando hannusa rik'e da towol yana goge jikinsa,had'a Ido sukayi da Sumayya tana, ya buga mata wata irin tsaya, "Ke me kike min a d'aki dan Ubanki " A furgice ta mik'e tsaye jakarta ta makaranta ta fad'i k'asa ta sunkuya ta d'auka zata futa daga d'akin a guje! Wata tsawar ya k'ara buga mata a karo na biyu, yace"Dawo kar ki sake ki futa anan sai kin fad'a min gulmar da ta kawo ki" Khamas yace "Kayi mata a hankali mana" Hararasa Habibu yayi yace "Ai duk iskancin na gurinka,kasan ina toilet ina wanka,kuma kasan a yadda zan futo shine ka k'i korarta daga d'akin" Khamis yasa dariya yana fad'in"Nima gani nayi ta shigo, kuma nima dubi ni ka gani" Habibu yace"Kai kasa kanka zama a haka, dama ka saba zubar da girman ka" Yafad'a yana kallon Sumayya da tayi tsilli-tsilli jikinta sai karkarwa yake,ita fa ta tsorata da yadda taga jikin Habibu a murd'e sai kace wani d'an dambe,k'irjinsa cike da gashi linkif. "Ba magana nake miki ba" Ya fad'a a kausashe, ya cigaba da cewa"Waye ya baki izinin shigo min d'akina" Jarumta ta aro, leb'anta na rawa ta fara magana kamar haka. " Yaya Habibu dama, immm! Dama Rabi'a ce" Shiru tayi ta kasa k'arasawa. "Dama Rabi'a ce me"? Yafad'a yana kallonta da jan ido. " Dama abunda zan fad'a maka ne, jiya,au!!! Shekaran jiya ne, naji su ita da Suwaiba suna wani zance na "yan iska, wai! Umm.... " Zan ci ubanki Wallahi idan baki daina wannan wai-wai d'in da kike ba,ki fad'i magana kai tsaye kin tsaya kina wai-wai" Khamis ya had'e fuskarsa yana fad'in "Bafa na son wannan tsawar da kake mata". Banza yayi masa yw cigaba da sauraran Sumayya. Jikinta duk ya jik'e da gumi ta cigaba da cewa" Dama jinsu nayi suna cewa, wai aure suke so, Rabi'a tana cewa, ummm! Wai tana so mijinta ya tsotsi bakinta,saboda a kwai dad'i kuma tsigar jikinta tana tashi! Ta k'arashe maganar da jiki a sanyaye, tana jiran abunda zai biyo baya. Wani irin banbarakwai Habibu yaji lokacin da Sumayya ta k'are zancan ta. Mamaki yake sosai yaushe yaran nan suka san wannan abu,da har suke zaunawa suna zancan. Ranshi a mutuk'ar b'ace ya durfafi inda take tsaye wani irin mari, ya yarfa mata, wanda yasa taga limawar taurari, idonta yayi dishi-dishi, a zabure ta bud'e idonta ta k'wala ihu! Sam bata kallon gabanta take k'okarin futa daga d'akin. Ya jawo ta da k'arfi, yana fad'in "Wato wuyanki ya isa yanka kenan,tunda har kika iya Tara ta da wannan maganar Lallai yau kashin ku ya bushe a gidanan, yanzu ta kanki zan fara". ya k'arashe maganar yana k'okarin fuzge hijab d'in jikinta. Ihu! Sumayya take kurmawa na Neman d'auki sai kiran Yaya Khamis take, ya k'araso gurin yana K'okarin k'watarta daga hannun Habibu, ya bangaje shi yana fad'in kar ka tab'a ta Malam, babu ruwanka" Karku manta da cewar wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 [24/08, 21:29] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿17* K'afafun, Khamis ta rik'o tana kuka tana k'okarin, kwanciya a k'asa, shi kuma Habibu k'okarin cire hannuta yake daga rik'on da tayiwa K'afafun Khamis. Wani jin wani irin haushinta, saboda rashin kamun kanta, ko wane namiji ta tab'a masa jiki, sam! ba yason dukanta, yana tausayawa rayuwarta sosai,amma ya fuskaci yarinyar bata tausayin kanta, tayi bala'in bashi haushi ganin yadda ta rungume k'afafun Khamis a k'irjinta, shi kuma tana tsaye yana lumshe idonsa, jin tudun k'irjinta a jikinsa. Habibu ya funcikota, daga jikin Khamis d'in har sai da wuyan hijab d'inta ya yage ya sauka kafad'arta d'an kwalinta ya fad'i k'asa,yalwataccan gashin kanta ya bayyana, sam Sumayya bata wannan take ba,k'okarin kawai take ta gudu, Habibu ya rik'e hannuta tamau! da alama bata cikin nutuswar ta. Khamis kuwa zuwa yayi ya zauna cikin kujera jikinsa yayi mugun sanyi sha'awar Sumayya na k'ara d'ad'umoshi, dole yau ya futa ya rage dare domin bazai iya jurewa ba. Sumayya duk ta gigice tana kuka, tana bashi hakuri, babu sunan Wanda bata kira ba,a gidan domin yazo ya cece ta, sam ba zaci a bun zai juye kanta ba, ta zaci in yaji abunda su Rabi'a sukayi zai gode mata ne,sai taga abun ba haka ba. _Ni ko nace ai ke Sumayya k'uruciya ce take damunki_ Hannusa na rik'e da nata ya je ya ciro dugowar riga cikin kayansa, ya zura a jikinsa cikin dabara, yaja ta suka sauka k'asa, kana kallon fuskarsa zaka san yana cikin tashin hankali. Duk suna zazzaune k'aton tsakar gidansu, ana ta hada-hadar cin abuncin rana, kowa sai cigayar Sumayya yake,kawai suka ganta a hannun Habibu ya shigo da sallama. Hajiya Gaji tace"Ko da naji,ashe tana gurin ka, tuntuni "yan uwanta suka shigo gida,kuma sunce ta rigasu ta tawowa gida" Shiru yayi yana kallon Rabi'a da ta sunkuyar da kanta k'asa gabanta na mummunan fad'uwa. Cikin tsawa yace"Rabi'a yaushe kika zama "yar iska ke da Sumayya"? Hajiya Tabawa tace" Wannan wace irin magana ce Habibu?" Ranshi a b'ace yace"Hajiya yaran nan sun zama abunda suka zama a gidan nan, wato duk irin k'okarin da kuke yi muke yi a kansu, basa gani, suna futa suna b'ata mana tarbiyar gid... Hajiya Gaji ta katse shi ta hanyar cewa"Wai me sukayi ne,uhum? Shikkenan kai in kadawo basu da kwanciyar hankali a gida, kullum fad'a da tsawa" Har yanzu bai saki fuskarsa ba, yace" Duk gidan nan kunyi shaidar Sumayya a kan rashin k'arya, wannan magana da ta fad'a min, nasan gaskiya ce, yanzu zan sata ta k'ara fad'a a gabanku kuji" Rabi'a har ta fara kuka, ta fara tausayin kanta,ganin yadda Sumayya ta jigata a hannun Habibu. Cikin kuka Sumayya ta fara magana kamar haka. "Hajiyarmu rannan ne fa, naji Rabi'a da Suwaiba suna magana ta iskanci, nan Sumayya ta kwashe komai ta fad'a musu,har da alk'awarin kud'in da Rabi'a tace zata bata. Salati kawai suke suna sallallami, Hajiya Zulai ta kaiwa Rabi'a duka, tana fad'in " Yanzu dama wannan littafin da kike d'auka kullum kina karatu ashe na shirme ne,kika munafur ce ni, kika ce, na makaranta ne" Rabi'a kuka take tana girgiza kai, Habibu ya buga mata tsawa, yana fad'in " Jeki d'ebo min novels d'in ko inzo nan in ci ubanki, tunda aure kike so za'ai miki,dake da munafurka da ta tona miki asiri" Sumayya ta tsala ihu! Tana k'okarin b'anb'are hannusa daga nata,amma ko gezau hannusa yak'i motsi ihu take tana fad'in"Ni wallahi babu wanda zai min aure, domin na tsane shi,yaushe ma na isa aure da zace za'ayi min,wayyo na shiga uku na lalace,wayyo Babanmu kazo ka cece ni" Ihu take sosai wanda ya cika gidan,Hajiya Gaji tayi Hamdala ga Allah ganin Alhaji Madu baya gida,Sumayya take wannan ihun! da kashinsu ya bushe duk ransu sai ya b'aci har Habibu. Rabi'a ta futa daga d'akinsu. tana kuka Hannuta rik'e da novels manya-manya Guda uku,jikinta na rawa ta mik'a masa, ya k'araba, had'e da tsinka mata mari wanda bata zata ba. Zubewa tayi gabansa tana bashi hakuri, fad'a yake mata sosai, yace"Tunda aure kike so, shikkenan za'ayi miki,dan haka kicewa saurayin naki ya turo magabatansa, domin a tsaida magana, kafin ki jawo mana abun kunya nan gaba, tunda kika san wannan,to tabbas kin San meye aure" Rabi'a da Sumayya sun shiga halin ni "yasu domin Habibu yayi rantsuwar da cewar ko Alhaji yana ko baya so sai an musu aure, a cewarsa baza su lalace a waje ba gwara kawai ai musu auran a huta. Iyayen nasu suma sunyi na'am da wannan hukunci da Habibu ya yanke. Su Suwaiba kuwa duk sunyi tsuru-tsuru suna tausayawa su Sumayya. Karku manta da cewar wannan book d'in na kud'i ne naira d'ari biyu, game buk'ata ga numbar nan, na kusa daina yin post d'insa,a groups sai Wanda ya biya zai samu 08089965176 07084653262 [25/08, 22:02] 80k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿18* Fad'a sosai Hajiya Gaji takewa Rabi'a ta inda ta shiga ba tanan take futa ba,Rabi'a sai kuka take. Hajiya Tabawa tace"Ai ba ita kad'ai zaki wa fad'a ba harda Sumayya, kai dukkaninsu ma zaki had'asu domin su kiyayi gaba,ni kam wannan hukunci da Habibu ya yanke yayi min dai-dai wallahi,to amma ya cire maganar Sumayya a ciki, tunda bata kai shekarunsu ba,kuma bata dawo har yanzu" Hajiya Zulai tace"To in banda abun Habibu an tab'a aure babu miji,Sumayya ina taga saurayi ma,gwarasu suna dashi,rashin fuska ne yasa basu kawo shi ba,amma yanzu tunda sun nuna suna so ai shikkenan" Rabi'a tayi da tasani yafi cikin kwando, kuka take Suwaiba na taya ta, ita kuwa Sumayya shiru tayi tabar kukan jin abunda Hajiya Zulai tace, bands ita a Wanda za'ayi wa aure tunda bata da saurayi. Ranar gidan kwana sukayi zuciyoyinsu babu dad'i, domin Alhaji Madu ma, da yaji labarin abunda ya faru,yayi mamaki sosai kuma yayi fad'a ya kuma goyi bayan hukunci da Habibu ya yanke akansu Rabi'a dole su turo samarin nasu, su turo magabatansu domin a tsai da magana,amma ya cire Sumayya a ciki,a cewarsa yarinya ce, kamar yadda Hajiya Zulai tafad'a. Da safe,sukuku suka tashi sukayi shirin makaranta kamar ko da yaushe Sumayya ta hau sama, gurin Babansu,suka gaisa,ta karb'o kud'in makaranta,nan Alhaji Madu yayi mata fad'a sosai,kuma ta d'auka domin ta tsorata da hukuncin da akai wa su Rabi'a,in akwai abunda ta tsana a duniya bai wuce ace za ai mata aure ba. Tana k'okarin sauka k'asa , Habibu yana k'okarin hawa, tsayuwa tayi ya k'araso inda take,yana mata kallon sama da k'asa, fuskarsa a had'e, Da sauri tace" Yaya Habibu ina kwana"? "Lafiya lau" Yafad'a yana nazarinta, sunkuyar da kai tayi cike da tsoransa, yace" Wannan itace damar ki ta k'arshe,a gidanan, kiyi k'okari ki maida hankalin ki kan karatu,idan ba haka ba, zaki cuci kanki ,domin ko da miji ko babu miji aure za'ai miki domin shi kika nuna kina so, duk sanda kika kuskura, naga wani abu na, shashanci daga gare ki, to irin hukunci su Rabi'a zan yanke a kanki" Muryarta na rawa tace"Insha Allahu na daina zan nutsu sosai kuma zan maida hankalina kan karatuna" D'aga kafad'a yayi ya wuce yana fad'i "Wannan shine ya dace dake dama" Sumayya ta sauka k'asa jikinta a sanyaye,duk wannan rawar kan babu shi,ta nutsu sosai, tare suka tafi makarantar, ko a ji ma,Sumayya shiru tayi babu hayaniya da surutu har k'awayenta sukaita janta tayi shiru kawai tana d'aukar darasi. **** Sati hud'u da faruwar Al'amarin, maganar auransu Rabi'a ta kankama, domin Habibu ya zauna da iyayen Ansar saurayin Rabi'a an tsaida magana, hakanan iyayen Saifudden saurayin Suwaiba suma sun a munce, an sanya rana shekara me zuwa,lokacin sunyi candy, tunda basu dad'e da shiga ss3 ba, haka rayuwa take,Wannan karon Habibu Cotonou suka tafi,domin cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin su. Sumayya ta nutsu sosai,ta dage da karatu, a boko da isilamiyya,har da makarantar dare, yanzu isilamiyya an sata a layin"yan sauka,domin dama can tana gane karatu itace take maida kanta koma baya Makarantar boko kuwa dama da aji d'aya,su Rabi'a suka wuce ta, ta k'ara girma yanzu, k'irjinta a cika ta zama babbar mace yanzu ta daina sanya k'ananun kaya, kullum cikin hijabi ko a gidane ma cikin hijabi take,sai zata kwanta bacci Hajiya Zulai take matsa mata ta cire. Wannan sauyin da aka samu yasa Alhaji Madu yaji dad'i don haka ya kirata samansa, yayi mata albishir da cewar ta shirya ranar asabar zasu tafi saudiya domin suyi umara. Da murnar ta ta sauko k'asa tana fad'a,aikuwa da gudu "yan matan gidan, suka nufi saman gurin Alhaji Madu, kowa naso aje dashi,nan yace" Subari in sun dawo zasuje dab da bukinsu Rabi'a,haka suka hak'ura domin sun san halin Babansu,in yafad'a magana. ***** Watansu Habibu goma a Cotonou suka dawo gida, Khamis duk inda Habibu yaje k'afarsa,nan yake aje tasa,yak'i tafiya harkokinsa, shima, Habibu yana mamakin wannan lamari,amma da yake bashi da bin k'wak'wafi, kawai sai ya k'yaleshi, suka cigaba da sabgarsu. Tunda ya dawo gida ya hautsine ana ta murna,gami da rabon tsaraba, bayan k'ura ta lafa, d'aya bayan d'aya suka dunga hawa Sunai masa sannu da zuwa, Sumayya ce a k'arshe, Habibu yayi mamakin sauyin da aka samu,ta fanni Sumayya,kallon ta ya dunga yi a fakaice,idan ba idonsa ne yake masa k'arya ba,sai yaga ta k'ara girma,da kwarjini, lafiya lau ya amsa mata gaisuwar ta, babu kyara babu hantara, Khamis kuwa duk ya susuce sai mutsu-mutsu yake kan kujera,yana janta da wasa,yak'i sakar masa fuska kamar da, Habibu yace"Je ki d'auko min jakunkunan makarantar ki, in duba" Da k'warin jiki,Sumayya ta taje d'auko masa, ta makaranar boko ya fara dubawa, ya ga sauyi sosai, ya mayar da littatafan, ya fara duba ta isilamiyya, nan alhamdullahi, kallonta yayi,a nutse yace"Yanzu I zufinku nawa"? "Hamsin da biyu" Tafad'a kanta,a k'asa. Gyad'a kai yayi ya mayar da alk'uranin da sauran littatan addinin cikin jakar ya fara bud'e jakar makarantar dare, Khamis yace"Lallai Malama Sumayya an kusa sauka Ashe,gaskiya ranar zamu sha hidima" Murmushi Sumayya tayi kawai ta sunkuyar da kanta k'asa. Yana tsaka da duba littafin ishimawi,Wanda ya futo dashi daga jakar Sumayya,kawai wata takarda ninkakkiya ta fad'o k'asa. Hannusa na rawa,ya d'auka ya bud'e ya fara karantawa kamar haka. _Assalamu alaikum_ _Sumayya ma'abociyar kyau da kyawun zuciya,kyakykyawa, zinari mai d'auke,da sirika da ba ko wace mace,take dasu ba, Sumayya mai cikakkiyar sura,me cikkaken k'irji,me cikkaken mazaunai,wanda suke sakani sha'awarki, Sumayya kin cika mace,domin duk inda ake son mace kin kai,kin kawo,wallahi Sumayya ina son nonuwanki, ina zumud'in ranar da zanjisu a hannuna ina lailayasu, ranar nasan mutuwa kawai zanyi dan dad'i,Sumayya INA bala'in son inji zak'in miyau d'in bakinki, ina so ji gard'inki ma'aciyar kyawun sura, bazan tab'a daina sanki ba har k'arshen rayuwarta_ *Daga masoyin ki* *me k'aunar ki har abada* Karku manta da cewar wannan littafin naki na kud'ne naira d'ari biyu ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿19* Wani gumi ne ya tsinkewa Habibu,cikin tashin hankali! ya d'ago kansa,ya zubawa Sumayya idonsa,jajur, gabanta ya fad'i ganin yadda duk ya burkice lokaci guda, k'asa tayi da kanta, jikinta yana b'ari,mik'a mata wasik'ar cikin bada umarni yace"Karanta min abunda yake cikin takardar nan" cikin rashin fahimta Sumayya ta karb'i takardar ta fara karantawa. Wani gumi ne ya yanko mata lokacin da tagama karantawa,kuka tafashe dashi,tana gyad'a kai kamar d'an k'adangaruwa, bakinta sai motsi yake takasa cewa uffan. Cikin wata irin tsawa yace"Wane d'an iska ne wannan"? Shiru Sumayya tayi,tana kuka Habibu ya d'aga hannunsa ya kai mata duka a fusace! Zama tayi a gurin.ta d'ora hannunta a bakinta. Ba dake nake ba ne"? Yafad'a cikin b'acin rai! "Wallahi Yaya Habibu ban sanshi ba,asali ma ban san daga ina takardar ta fito ba,wallahi ban san wanda ya aje min ita ba" Wani dukan ya k'ara kai mata a karo na biyu,Khamis yayi saurin rik'e hannunsa,yace"Banda duka Habibu, ka bita a hankali mana" Fuzge hannusa yayi, yace"Ki fad'a min wanene shi"? "Wallahi ban san ko waye ba,don Allah kayi hak'uri" Tafad'a tana share hawaye. "Sumayya wannan rayuwar kika jefa kanki ko,wato ke kunnen ki na k'ashi ne ko,za'ai ta fad'a miki magana ki toshe kunnen ki,shikkenan, hukunci ya tabbata a kanki,kije ki turo min saurayin naki zamu zauna dashi,tunda ya matsu dake,kema kin matsu dashi,sai ai muku aure kawai" Ya k'arashe maganar yana had'iye wani mugun d'aci irin na b'acin rai. Kuka take sosai ta ririk'e masa hannu,tana fad'in"Ka yarda dani Yayanmu wallahi, bansan da wannan wasik'ar ba,asalima ni bana tsayawa da wani d'a namiji saboda fad'an da kake mana kullum,ka tambayi su Rabi'a ma kaji" "Babu Wanda zan tambaya ni,na riga na gama maganata, aure babu fashi,sai anyi miki,dama shine cikar duk wata " ya mace a duniya" Cikin kuka Sumayya tace"Yaya Khamis ka bashi hakuri don Allah kaji,wallahi nayi rantsuwar ban san daga inda wasik'ar ta futo ba" Khamis ya sosa kansa cike da farin ciki, tabbas burinsa ya kusa cika, akan Sumayya, yasan yana cewa zai aureta za'a bashi, don haka sai yace"Ki kwantar da hankalin ki, kin jiko Sumayya, zanyi bunkice akan hakan,nasan baza ki aikata ba, kije kawai zan rarrashe shi, ya janye maganar" Sumayya ta mik'e jiki a sanyaye ta futa daga,d'akin, Habibu ya bita da kallo yana girgiza kai cikin bak'in ciki da damuwa. Khamis yace"Ni fa ina ganin wannan abun ba na tada hankali bane, dama yarinyar ta isa aure saboda haka ana samun irin wannan, in suka kai wannan matakin saboda haka ka daina d'aga hankalinka, kamar yarda ka fad'a ta turo saurayin nata sai a tsaida magana idan kuma babu ni ina so sai ayi dani" Habibu ya girgiza kai cikin damuwa yace"Lamarin yaranan yana bani mamaki wallahi, wai har sun San aure da abunda akeyi a cikinsa,da gani wannan ma mugun d'an iska ne,duba don Allah yadda yake wasu maganganu na shashanci" Khamis yasa dariya yana fad'in d'an iska irinka ba, ni banga wani iskanci ba,anan gaskiya ce abunda ya fad'a" Habibu ya mik'e cikin b'acin rai yace"Ai halinka ne kaima baku kimtsa bakinku,gurin mata,sai Ku tsaya kuna zantukq da basu dace ba" Dariya sosai Khamis yakeyi. Kwanan damuwa da bak'in ciki Habibu yayi a ranar,da ya juya ya juya,wannan kalamai na cikin wasik'ar zasu fad'o masa a rai,wani irin kishi da damuwa su dame shi,wani abu ne yazo ya tsaya masa a mak'ogaro yaki ya fad'a masa, haka ya wayi gari cikin damuwa, shi kuwa Khamis cikin farin ciki ya tashi, kana ganinsa kasan bashi da damuwa, bayan sun futo daga masalaci ne, Habibu ya bi Babansu d'akin sa yana shakar fad'a masa abunda yake bakinsa,yasan ba lallai ne ya yarda ba,amma shi yana ganin Wannan itace maslaha. Ko da Habibu ya gama wassafa Babansu abunda yake faruwa,sai yaga babu wata damuwa a tare dashi, murmushi ma yake yi, shiru d'akin yayi na wajan minti biyar kana Alhaji Madu yace"Anzo gab'ar da zanyi magana akai, Habibu naji dad'in hukuncin nan,kuma ina alfahari da kai gurin ganin ka kare min Martaba da ta iyalina,tabbas kazama d'aya tamkar da dubu, a zahirin gaskiya akwai wani k'udiri a raina Wanda ya dad'e shekara da shekaru,kuma Wannan kudirina akanka yake ina fatan zaka yi min biyyaya kamar ko da yaushe" Habibu yace"Duk abunda ka umarce ni dashi zanyi mutukar bai sab'awa addinin Allah ba" Alhaji Madu yace"Alhamdulilahi, so nake ka auri Sumayya" Wani irin gingirim Habibu yaji a kansa,yayi masa nauyi sosai, yace"Alhaji anya wannan lamari zai yi wu" "Babu abunda zai hanashi yiwuwa Habibu babu haramci idan ka auri yarinyar nan, tunda baku sha nono d'aya ba" Habibu ya girgiza kai fuskarsa da damuwa yace"ina tunanin halin da yarinyar zata shiga mutuk'ar ta gane,cewar Ku ba iyayenta ba ne,kuma mu ba "yan uwantq na jini bane" Alhaji Madu yace"Nafi ka tunanin wannan Abu,domin ina tunanin zuwan wannan ranar,to amma ni akwai abunda nake hangowa a game fa rayuwarta,Habibu kaine nawa ina kyautata zaton zaka rik'e min ita da mutumci da amana" Shiru Habibu yayi yana share gumi, yace"Hakane Alhaji,bani da abun cewa a wannan al'amari sai dai in ce Allah ya sanya alkairi a ciki" Alhaji Madu yace"Ameeen ya rabbi nagode sosai, inayi maka fatan alkairi a rayuwarka,ina fatan Allah ya saka ka haifi "yaya masu albarka da biyayya" Habibu yace "Ameen Alhaji" Mik'ewa yayi zai futa, Alhaji Madu yace"Ai yanzu za'ayi ta ta k'are kaje ka kira min iyayenka,da ita Sumayya" Habibu ya sauka k'asa domin cika umarnin mahaifin nasa,a zuciyarsa yana ganin wannan abu da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa, A zuciyarsa baya jin son Sumayya kuma baya jin k'inta shidai gashi nan dai. Karku manda da cewar wannan book din na kud'i ne naira Dari biyu ga me buk'ata ga numbar nan 08089965176 07084653262 https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation ⚱⚱⚱⚱ _*TSANTSAR BUTULCI*_ ⚱⚱⚱⚱ _*NA*_ _BINTA UMAR ABBALE_ *®BINTUBATULA👄* _*MARUBUCIAR*_ ```NANA KHADIJA``` ```YARO DA KUDI``` ```GIMBIYA BALARABA``` ```LOODING......``` _*TSANTSAR BUTULCI*_ _*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*_ ____________________ _*We are here to educate,motivate and entertain aur Reades*_ _______________________ _*BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM*_ *🅿20* Dukaninsu, suna Zaune gaban Alhaji Madu, har da Sumayya,tana kusa dashi kanta a k'asa, gabanta yana wata irin fad'uwa. Alhaji Madu yayi gyaran murya, kana yace"Alhamdulilahi, Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar da raina da lafiyata, Hausawa sukace ranar wanka ba'a b'oyan cibi, babban abunda yasa na taraku anan shine,ina so in fad'awa Sumayya Wacece ita,saboda wani dalilina, Sumayya ta d'ago kai tana kallonsa,gabanta ya cigaba da fad'uwa duf-duf-duf. Hajiya Zulai ma jikinta sanyi k'alau yayi,tasan dama dole akwai zuwan wannan ranar. Alhaji Madu ya kalli Sumayya yace" Yake "yata ta ruwan sanyi, hak'ika kece mafi soyuwa a zuciya,Sumayya Allah ya d'ora min son ki da tausayin ki,duk cikin " yayan da na Haifa, inaso in warware miki wasu muhiman abubuwa da suka shafe ki,ina fatan, zaki d'auki k'addara ki rungume ta hannu bibbiyu, domin kin san da cewar ko wane bawa yana tafe ne,da tashi k'addarar me kyau ko mara kyau" Alhaji Madu ya ajiye maganar yana jan numfashi. Sumayya ta d'ago kanta tana kallonsa,idanunta suna zubar da wasu zafafen hawaye tun kafin taji maganar da Babansu zai fad'a mata,tasan ba mai dad'i bace. Kuka take sosai da sosai. D'akin yayi tsit! Alhaji Madu ya cigaba da cewa"Sumayya a zahirin gaskiya ni da kika d'auka a matsayin mahaifin ki,bani na haife ki ba,haka nan kuma Hajiya Zulai ba itace mahaifiyar ki ba" Nan Alhaji Madu ya warware Sumayya yadda akayi aka same ta har ta girma a hannusa, ba tasan Wacece ita ba. Suman zaune Sumayya tayi a gurin tana zazzare ido,in ta kalli wancan sai ta kalli wancan, a d'akin duk ta furgice! Manyansu sune suka san labarin Sumayya shiyasa basu gigita ba, irinsu Rabi'a da Ummu Suwaiba dana k'asa dasu sune suka gigita jin ashe Sumayya ba jininsu bace tsintar ta akayi. Mik'ewa tayi tana rangaji jiri na d'ibarta takama hanya zata futa,daga d'akin da alama bata cikin hayyacin ta,tsallake mutane kawai take,tana kallo suka bita dashi, tazo dai-dai gurin da Habibu yake zaune ta tsaya tana rik'e kanta, luuuuu! Ta afka jikinsa, yayi saurin rungume ta a gigice ya mik'e tsaye da ita a jikinsa,yana kallon Auwal yace"Maza kaje ka futo da mota. Tashin hankali, Sumayya ta sank'ame dafara na futowa daga bakinta,hankalin Alhaji Madu ya tashi ainun, addu'oi yake tofa mata. Hajiya Zulai tana kuka take cewa"Wannan magana Alhaji daka sani baka fad'a ta ba, amma ban san manufarka ba, ina tsoran halin da yarinyar nan zata shiga" Alhaji Madu yace"Ki kwantar da hankalin ki,komai zai zo da sauk'i Insha Allah ina da munufata a kan haka da nayi. Jikinsa na tsuma ya sungume ta ya sauka k'asa da ita,kai tsaye waje ya futa,inda motarsa take ya nufa,Auwal ya gyara parking ya shiga da ita a jikinsa,Auwal ya kunna mota,zasu tafi sai ga Khamis ya tawo a gigice yazo ya bud'e motar ya shiga,yana jin kamar ya k'wace Sumayya daga hannun Habibu amma babu fuska,wani mugun kishinsa ne yake damunsa. Haka sukayi tafiyar babu me cewa komai Habibu yana ta aikin goge mata kumfar da take futowa daga bakinta, Shi kuwa Khamis banda aukin kallonta babu abunda yake. Dogon suma Sumayya tayi Wanda har sai da aka sama ta abun zuk'u numfashi,awa uku sanam numfashin ta ya dawo dai-dai Tun kafin ta bud'e idonta wasu hawaye suka fara zubo mata,wannan ya tabbatar wa da Habibu cewar ta dawo cikin hayyacin ta,kiran sunanta yayi cikin taushin murya,ta bud'e idonta tana kallonsa, hawaye jage-jage! "Kiyi shiru ki bar kukan nan da kikeyi domin zai iya janyo miki wani ciwon ki d'auki k'adarar ki, wannan ba yana nufin cewar mun cire ki daga cikinmu ba, ko angano iyayen ki, ko ba'agano su ba,kina nan a matsayin " yar uwarmu,kuma "ya ga Alhaji Madu Gwadabe, saboda haka,babu wani banbanci da zaki gani ko wani sauyi in sha Allau ki rik'e a zuciyarki cewar badan a tozar taki aka fad'a miki wannan maganar ba, fad'in ta shine alkairi a gare ki" Shiru tayi tana zubar da hawaye, tarasa wane irin tunani zatayi k'wak'walwarta duk ta toshe, ita duniyar ma gaba d'aya batai mata dad'i, duk maganganun da Habibu yake wasu bata fahimtar su. Khamis ne ya zauna kusa da k'afafunta,ya rik'e hannuta yana murzawa cikin sigar rarrashi yace"Sumy kiyi hakuri kinji ko bana son kina kuka kinji ko,mutukar muna Raye bazaki wulakanta ba,Insha Allahu nayi miki alk'awarin duk inda iyayenki suke zan shiga in futa in nemo miki su" Wannan magana da Khamis yayi ta sanya Zuciyar Sumayya sanyi, tana kuka tace" Yaya Khamis kayi min alk'awari ko"? D'aga kansa yayi yana murza mata hannu. Habibu duk bai lura ba,yace "Ki goge hawayen ki, nima zan taya Khamis muje mu nemo miki su,amma sai kin kwantar da hankalin ki" Sumayya ta goge hawaye n ta tana sauke ajiyar zuciya. Habibu ya kalli Khamis yana fad'in bari inje in kira likata yazo ya duba jikin nata mu tafi gida" D'aga kai kawai Khamis yayi, domin bazai iya magana ba,muryarshi zata iya tuna masa asiri. Habibu yana futa,Khamis ya k'ara matsawa jikin Sumayya sosai,yana goge mata hawayen fuskarta a wayance ya d'ora hannunsa a k'irjinta wai yana gyara mata hijab, Sumayya ta ture hannusa tana k'okarin mik'ewa zaune,ya taimaka mata ta zauna, karyar da kai yayi yace"Sumy a kwai abunda nakeso in fad'a miki dama" Sumayya tace"Ina jinka Yaya Khamis. Lumshe ido yayi cikin sigar yaudara yace" Wallahi ina mutukar kaunar ki, ina mutuk'ar sonki da tausayin ki a rayuwata,ina so ki yarda dani ki aure ni" Wani irin kallo Sumayya tayi masa, tana girgiza kai,batayi mamaki ba,domin ta dad'e tana kallon so da k'aunarta a k'wayar idonsa,yayin da ita kuma bata jin son sa ko guda d'aya a cikin ranta Khamis yace"Idan kin amunce kawai zanyiwa Alhaji magana sai a tsada mana rana kamar tasu Rabi'a" Girgiza kai tayi kawai tace"Ka bari inyi shawara" Khamis yace"Shikkenan ina fata kiyi shawarta alkairi,amma akwai abunda nakeso in fad'a miki ki kula akai shine, Ki kula da Habibu domin baya k'aunar ki duk wannan maganganun da yake miki dad'in baki yake miki, cutar ki zaiyi, kar ki k'ara yadda dashi yana tab'a miki jiki,domin lokacin da kika suma ma, shine ta d'auko ki, a mota ya dunga tab'a miki nononki, nine na hana shi nace yaji tsoran Allah domin yana kallonsa. Sumayya ranta ya b'aci idan da akwai abunda ta tsana a duniya bai wuce a tab'a mata k'irji ba, ta tsani namiji ya kalle mata kirji shiyasa kullum cikin hijabi take,wato yanzu Yaya Habibu dan ya san ba su had'a dangata ta komai ba shine yake tab'a ta Lallai dole tayi taka tsan-tsan da samarin gidan kar su lalata mata rayuwa, Wannan shawar zuciyarta take bata. Habibu ya shigo tare da likita ya duba ta, sosai ya sallame ta,,,,, suka tafi gida Habibu shike tuk'a motar saboda Auwal ya tafi kasuwa an da meshi da waya,to shima Habibu yanzu haka jiransa ake a kasuwarsu, akwai wasu bak'i da zasu sallama kuma zasu fara raba kaya a shaguna, sai waya ake masa. Duk yana kallon irin shishshigewar da Khamis yakewa Sumayya girgiza kai yayi kawai,yana so ya fuskaci wani abu daga gurin Khamis din,murmushi kawai yayi a zuciyarsa har sukaje gida. Sumayya ta kasa sakewa a gidan sukuku kullum babu walwala, idan ta hau sama gurin Babansu nan ma bata dad'ewa take saukowa kowa ya fuskanci sauyi a gurin ta, haka dai suka cigaba da tafiya da ita,babu Wanda ya nuna mata sauyi ko banbanci matan gidan da yaran gidan,itace kawai takasa sakewa. **** Bayan sati uku da Faruwar al'amarin Sumayya ta saki jikinta har ta fara mantawa,sai dai idan ta tuno da cewar ita ba wata tsiya bace,kuma bata da iyaye sai ta shiga d'aki tayi ta kuka,ta gode Allah. Ranar Lahadi da safe,Alhaji Madu yasa aka kira masa ita, taje ta gaidashi ta zauna kusa dashi kanta a k'asa, kafin ya fad'a mata dalilin kiran sai da yaja ta da wasa,kamar yadda ya saba,sannan yace"Sumayya ina so in aurar dake kamar yadda zan aurar da su Rabi'a, ina fatan zaki zauna lafiya da mijin ki" Cikin fad'uwar gaba ta d'ago kanta tana kallonsa tace"Babanmu wanene mijin, ni da bani da tsayyayn saurayi,, ni kam bana son Khamis Babanmu" Murmushi yayi yace"Ashe akwai maganar Khamis A k'asa Sumayya" D'aga kai tayi tace"Kwana ki yace wai yana sona zai aure ni" Alhaji Madu yasa dariya yana fad'in shine baki fad'a min ba" Sumayya ta sunkuyar da kanta gabanta yana fad'uwa! Alhaji Madu yace"Na riga na d'ade da wani burina a raina da babu wannan burin da babu abunda zai hanani aurar dake ga Khamis domin nagartarsa,amma kash! Duk nagaratarsa bai kai Habibu ba, ina mutuk'ar so inga na aurar dake ga yaron kirki Habibu" Dafe k'irji tayi tana zazzare ido bakinta na karkarwa tace"Wane Habibu kake nufi Babanmu"? Murmushi yayi yace"Ina da wani Habibu ne bayan nawa" Sumayya ta gigice sosai tana fad'in don Allah Babanmu ka janye maganar nan, kayi min rai, Babanmu Yaya Habibu ba tsaran aure na bane, Yaya Habibu yaya na ne. Bazan iya rayuwar aure dashi ba" Ganin yadda ta gigice yasa Alhaji Madu kwantar mata da hankali gami da yi mata misalai, dawa amma Sumayya takasa fahimta komai kuka take, Lallab'ata yayi yace"Ta daina kuka zaiyi tunani janye maganar ta kwantar da hankalin ta. Sumayya tashiga k'unci da damuwa tana ganin kamar bata da gata shiyasa za'ayi mata auran dole, ita a ganinta da ta auri Habibu gwara ta auri Khamis sau dubu domin tana ganin shi yafi Habibu sakin fuska,kuma shi ya furta yana sonta da bakinsa,sab'anin Habibu da tunda suka dawo daga asibiti wata magana bata k'ara had'ata dashi ba, tsakaninta dashi gaisuwa CE kawai,wataran ma in ta gaidashi baya amsawa,tana ganin Habibu bazai iya kula da ita ba saboda shi babu abunda yasa agaba sai harkar kasuwancinsa. Jin Alhaji Madu bai k'ara tayar mata da maganar ba yasa ta kwantar da hankalinta,a ka cigaba da sabgogin bukin su Rabi'a da ita,wanda ya rage saura "yan kwana ki. ***** Yawan zurgar zurgar dasu ke ne yasa bai samu zama da mahaifin nasa ba sai ana saura kwana sati d'aya daurin aure suka zauna a d'akin Alhaji Madu suna tattaunawa maganar katin d'aurin auran ya d'auka yana dubawa, sunanshi ne a sama shi da Sumayya sai na Suwaiba da angontq sai na Rabi'a itama da angonta, nan ya sauko daga saman da katikan a hannusa Abdulsamadu ya baya yace yaje ya rarrabawa mutane, Hajiya Gaji takarb'a ta bawa su Hajiya Zulai kowa ya rabawa danginsa, nan Yaran gidan sukaga sunan Sumayya cikin katin ita yayansu, mamaki suka dunga yi sosai daga bisani sukayi shiru da bakinsu, Sumayya na makaranta lokacin tana dawowa suka had'u da Abdul samadu da katin a hannusa sai ta karb'a tana dubawa, abunda tagani ya gigitata, Zubewa tayi a gurin ta suma Wanda yayi dai-dai da shigowar Khamis soran ganin abunda yake faruwa yasa baiyi wata-wata ba,ya d'auki Sumayya Abdul ya bi bayansa suka hau dama,D'akin Habibu ya shiga da ita lokacin baya ciki Abdul yaje ya bud'e firji a d'auko ruwa me sanyi ya watsa mata, ta sauke ajiyar zuciya, ganin ta farfad'o Abdul ya sauka k'asa da saurin domin fad'awa Yaya Habibu abunda yake faruwa. Katin d'aurin Auran Sumayya ta nunawa Khamis tana wani irin kukan me ban tausayi. Khamis ya karanta yafi sai goma wani zazzafan gumi yana zubo masa, wato shi za'a munafurta kenan,tabbas shima akwai nasa shirin insun San wata basu San wata ba, rarrashin Sumayya yake sosai yace"Ki kwantar da hankalin ki wannan aure indai ina Raye baza'a daura miki shi da Wannan azalimin mutumin da baya k'aunar ki, zan tsaya miki tsayin daka gurin kwantar "yan ciki, zan gudu dake, in b'oye ki sai k'ura ta lafa sai in dawo dake,ko kuma muje a daura mana aure tare,in boye ki inda bazasu ganki ba, INA fatan iin yarda da wannan Shawarar tawa" Sumayya ta d'aga kai tana wa Khamis godiya ta amunce ya gudu da ita, idan anga bata nan ai dole a hakura da daurij auran. Habibu ne ya shigo yaga Khamis kusa da Sumayya yanai mata magana k'asa-k'asa kome yake cewa oho. Karku manta da cewar wannan littafin na siyarwa ne naira Dari biyu ga me bukatar cigabansa ga numbar nan 08089965176 07084653262