[8/19, 10:54 AM] Zarahh: 👮🏻 *COLONEL UBAIDULLAH*👮🏻 ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon farawa lpy na kuma gama lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°1&2* *9JA,BARRACKS ABUJA* Tsaye yake daga shi sai 3quarter mai ratsin tambarin sojoji a jiki, sai farar T-shart and p-cap shi ma na sojoji. Dogo ne amma baza kace masa dogo sosai ba ,yana da ɗan fadin fuska daidai wa daida ,sannan baza kace masa fari ba, za dai ka iya saka shi a layin chocolate color Yana da gashin baki wanda ya kewaye masa baki wanda hakan ba ƙaramin kyau ya qara masa ba, duk da idonsa sanye yake da black shadow,but yana da ƙananan ido kmr na yan'chinese , yana da faɗaɗɗan ƙirji irin na gwarazan maza jarumai saɗaukai. Duk ya zuba hannayen sa a aljihu, yana tsaye fuskar sa babu alamun fara'a domin shi ko da smiling ne bai cika yiba infact baya ma yi balle kuma dariya bcox baya daukar raini a *barracks*, bama iyakar barracks ba ,a koma ina ne baya daukar raini, duk da sojoji ne amma da yawan ana shakkar sa. Iska ne ke ƙadawa awajan domin a garden din barracks din yake tsaye. Bakin sa ne ke moving ahankali saika Lura da kyau kafin ka fahimce ashe waya yakeyi but da airpieces a kunnan sa. Bisa alama kuma da mahaifiyarsa yake wayar domin yadda yake wayar cike da natsuwa. Mama tace. "*UBAIDULLAH* ina fatan dai komai lafiya?" Sai da ya numfasa ya hura iska kafin ya ce " eh mama lafiya lau fatan kuma kuna nan lafiya? Ina su sister's ?" Mama tace. " lafiyarmu lau hafiza ta je gidan yayarku ummu,na aiketa ,ita kuma na'ila wai taje karban aron littafi agidan su kawarta." "Mtsww!!! wlh mama na'ila bata jin magana at oll,na hanata zuwa yawo amma bataji, wani irin littafi da rana haka?" Mama tace. " indai na'ila ce sai dai mu dinga taya ta da adduah Allah ubangiji ya shiryeta." Ya amsa da ameen Hira suke dan tabawa na tsakanin uwa da ɗanta. mama tace. "Ubaidullah yaushe zaka zo ka gan mu ne kam munyi, kewarka sosai wlh." " Karki damu mama zanzo a next week weekend In sha Allah." mama tace. " Allah ya kaimu" suka ci gaba da hira, Ji yayi anyi hugging dinsa ta baya azafafe ya juyo domin yaji kamshin turarenta Kashe wayar yayi yana cewa I will call u back mama luv you!! Sa ke fuskantar ta yayi yana tamke fuska , ita kuma tana murmushi sanye take da kakin sojoji itama sai murmushi take masa, tasa hannu zata shafi fuskarsa ya buge hannun, sannan ahankali ya bude mouth dinsa lyk mai koyan mgn yace. "waike *RUMAISA* how many times zan fada miki ki dai na haɗa jikin ki da nawa?" Smiling tayi tace. " first lieutenant Ubaidullah I will never tried to say I love u duk fadin barracks din nan oll ladies din DA suke rububin suna sonka karya su keyi! ni ce masoyiyar ka Wanda nake maka true love, plss I beg u Ubaidullah ka so ni ko da kaɗan ne " ta ƙarasa tana so ta shige jikinsa ya bankaɗe ta ya wuce yana jan dogon tsaki ,rumaisa kuma tayi kwafa ta juya domin indai wannan wulaƙancin Ubaidullah din nan ta saba shan sa. Ahanya kafin ya isa dakinsa ya hadu da close friend dinsa infact garinsu daya tare suka taso burinsu ɗaya arean su ma ɗaya. *ZAIDU* yace. " Ubaidullah tun dazu nake neman ka ban ganka ba ina ka shiga?" A kasalance yace. " ina garden barrack ne menene?. " No dama stall sergeant David ne yazo neman ka akan mgnr meeting din da za a gudanar anjima a babbar filin taro na *murtala barracks* shine lieutenant general yace. A fada maka kai da commander Ku shirya domin taron ma yana da nasaba da mu dan gsky naji ƙishin ƙishin akan cewa zabe za ayi domin tura jama'ai izuwa bordern Niger domin kama yan'ta'adda." "To kai Zaidu a bakin wa kaji ?" "Na dai fara ji a bakin sergeant first class A,M kasan halinsa maybe shima ji yayi." Ubaidullah yace . "ok amma K,B yasan da mgnr ?. Zaidu yace. " eh dazu ma mun hadu dashi na fada masa kaine kawai baka sani ba." Ba tare yayi mgn ba ya jinjina kai kawai. Duk inda ya gitta sai an kallesa amma ya tsare gida dan Ubaidullahi akwai tsare gida, su na tafiya suna dan taba hira har suka isa part dinsu. Suna shiga parlour suka sa mu Raihana kwance a 3seter sanye take da wandon sojoji da black T-shart kanta ko p-cap din ma babu, balle kuma dan kwalli ko veil" Ubaidullah yayi tsaki yace. " ke kuma fa? oya tashi ki fita kafin raina yabaci ya fada yana mata nuni da kofar waje." ahankali Raihana ta miƙe tana taku harta zo daf dashi domin numfashin su har yana sarkewa waje daya tace. " i will,but ina so kasani wlh wlh bazan taba barin ka ba Ubaidullah, ta juya ta fice." Zaidu ya kwashe da dry yace. " wlh ladies din yanzu duk sun gama kwarkwancewa kalli fa yadda suke rushing akan ka?" Tsaki Ubaidullah yayi ya shige bathroom domin yayi fresh'up. Bayan ya fito ya shirya, ya ɗauki doguwar jallabiyya ya saka, yadan kwanta. Ya lumshe ido yana tuno rayuwar baya , haƙiƙa yanzu komai yana so ya zamo masa tarihi,sai kuma babban burin sa, na gaba. Bacci ma yake ji amma bazai iyaba dan haka ya tashi zaune. Kallon sa. " Zaidu yayi,lafiya kuwa Ubaidullah?. "Mtsww wlh Zaidu ina yawan tuno baya ne." "Bai kamata ka dinga tuna baya ba Ubaidullah,ka fuskanci gaba kawai,a rayuwar ka komai ya wuce, tunda a karshe Allah ya cika maka burin ka na zama jami'in soja, wanda kuma ake alfahari dashi." Numfasawa yayi. " Zaidu kasan ina da buri sosai a rayuwa ta, but bana so na dawo dasu mama barracks din nan,cox ka kalli abinda ladies ke min mama ba za ta ji dadi ba, ba ma zata jure ba." "Haka ne kuma ,to amma ya zakayi?" "Abinda nima ban gama yanke shawara ba kenan." Tattaunawa suka cigaba dayi. K,B ne yayi sallama ya shigo da sauri har yana tuntube, Zaidu yace lafiya kuwa K,B? "Ina kuwa lafiya, ga Raihana da Zeey can su na dambe wlh ina tausayawa Raihana dan babu abun da zata ɗauka, a jikin Zeey, yarinyar da ko wasu mazan tsoronta sukeyi, balle kuma Raihana." Dryn mugunta Zaidu ya hauyi, yace. "Ubaidullah tashi muje mu gani,kai Zeey bata da hakuri,am sure Raihana ce bata da gaskiya, cewar Zaidu." Duba agogon sa Ubaidullah yayi,yaga har to 4, yace. " i don't have time for this stupid ladies, Ku shirya mu tafi meeting." Shiryawa sukayi cikin kakin su na sojoji ,suka fito su na taku a hankali, wanda na Ubaidullah ya sha banban da nasu. Commander suka sa mu sannan suka ɗun guma *murtala barracks*. ••••••••••••••••••• Duk inda ka wulla idon ka baza ka iya banbance waye da waye awajan ba. Sojoji ne birjik ta ko ina da ina. Nan aka nemi da a buɗe, taro da adduah ,major usman shine wanda ya buɗewa musulmai nasu,sai major jonh shine ya buɗewa christian nasu, Kafin, aka fara gabatar da meeting. yayin da major general yake jawabi cikin harshen turanci, akan jaruman da barracks ke ji dasu za a tura ,amma kafin nan za,ayi ƙarin girma ga wa'inda suka je yaƙin maiduguri, Lieutenant general ne ya karbi jawabin daga hannun major general ya ɗora,da nasa akai. Mutum na farko daya lashe takwabin girma mai tambari shine...!!ehem ehem! *first lieutenant Ubaidullah* wanda a yanzu zai karbi matsayin, *CAPTAIN UBAIDULLAH*,nan jami'ai, aka hau tafa masa ji kake rab! rab! bayan anyi wa Ubaidullah ƙarin girma, shima Zaidu matsayin captain aka bashi, K,B kuma a tym din aka basa ,matsayin first lieutenant ,daga nan aka cigaba da rabon muƙamai. Ba a watse ba kuwa, sai da aka kira sallar magriba tukunna musulmai sukayi masallaci sai da suka idar, yan'9ja barracks suka koma. A gajiye suka shiga part dinsu. " Zaidu yace oh Allah ƙarin girma babu gayyata sai dai kawai gayyar sojoji? ai da an bari iyayen mu da yan uwanmu sunzo kafin ayi mana ko dan bamu da mata ne? Ko kuma,mu bamu kawo iyalan mu barracks ba?" K,B ya kwashe da dry yace "Zaidu kenan yanzu kai a tunanin ka, ka kai aure ?" " ai abun ne yazo ba shiri shiyasa kuma kaga nan da wata daya ne zamu tafi border gashi naji major general yace gobe zamu fara sabon training,amma kusan Allah commander victor bai so wannan ƙarin girma da a kayi ba, daka kalli kwayar idonsa zaka hango baƙin ciki da hassada ƙarara." "Wlh K,B ka kiyaye ni! Cewar Zaidu, ni zaka kalla kace ban isa aure ba?" Wani dry Ubaidullah ya kwashe dashi,sai da suka dan tsorata su na kallon sa. "Ubaidullah wannan dry haka?" cewar Zaidu. K,B yace "ina kuwa lafiya mutum sai kace mai iskokai." "No wlh hirar taku ce ta ban dry ,kunsan ai ni dry bata cikin manner dina " Zaidu yace "dama kai kam dryr ka ,sai dai kana gida,ko kuma kana tare damu." "But nifa wlh hassadar commander victor bai dame ni ba,tunda hassada a barracks ba yau farau ba,and bazai zama karshe ba, so just 4get about this matter,mu fuskanci yin gaban kanmu dan yanzu mun sake zama manya, captain ai ba wasa ba,muna tafiya yaran mu su na bin mu a baya." Ubaidullah yace "b4 mu tafi i need to go home,I want to see my momma and my lovely sister's." Zaidu yace " ok when are u going?" A takaice Ubaidullah yace, "next week In'sha Allah." "When did u come back?" Sai da ya ɗauki som minute kafin yace "5days." Zaidu yace " zan bika mu tafi tare sai mu dawo, but kasan fa, sai mun samu permission daga wajan, *GENERAL OF THE ARMY*." Ubaidullah yace "eh nasani." K,B ne yace. " kenan ni kadai zaku barni?" "Hahaha my guy kaima ka shirya kawai kaje ganin gida,amma seriously da mun dawo aure nake so wlh." Girgiza kai Ubaidullah yayi, yace mayan aure kawai,ku tashi muje sallah, tashi sukayi suka fito atare,sukayi hanyar ma sallaci *WANENE UBAIDULLAH*? ××××××××××××× Sharhin ku ne zai sa mu cigaba ko mu dakata......!!!! Domin fahimtar littafin ya muku ko bai muku ba COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAN YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah! ina qara godewa Allah a ko da yaushe, salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W, da iyalan gidansa da sahabban sa, da ma goya baya har izuwa ranar sakamako._🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy.🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°3&4* *UBAIDULLAH ABDULLAHI GALADIMA.* Shine asalin cikakken sunansa, haifaffen garin Bauchi ne, ya kasance maraya Mahaifinsa tsohon Soja ne." Ubaidullah tun yana yaro yake sha'awan aikin soja, sakamakon ganin yanda mahaifinsa yake ɗebi ba ɗaɗi da yan ta'adda. Su hudu ne rak awajan Mama mahaifiyarsu, Ubaidullah shi ka ɗai ne namiji, shi ne na biyu, Anty Ummu ita ce babba, sai ,Ubaidullah,Hafiza,Na'ila. "Tun Ubaidullah yana da shekara goma a duniya Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa, a wani yaƙin garin jos da a kayi, aka kashe mahaifinsu, sunyi kukan rashi a lokacin da aka shigo musu da gawar Baba, wanda a lokacin yake riƙe da matsayin commander na sojoji, Baba ya taka muƙamai da dama a aikin soja, bayan rasuwar Baba komai ya dagule musu, domin a lokacin sun ga jarabawan rayuwa. Abinci ma gagararsu yake yi, Mama tayi kuka harta godewa Allah, a lokacin kuma su hafiza su na yara, dan Hafiza shekararta biyar Na'ila kuma tana da shekara hudu, Ummu kuma tana da shekara goma sha takwas. Dan tsakanin Ubaidullah da Ummu ratan shekara takwas ne, Ubaidullah kuma yana bawa Hafiza shekara biyar harda rabi, tsakanin Hafiza da Na'ila kuma ratan shekara daya ne, shiyasa suka taso kansu daya. Sun sha matukar wahala kafin Mama data ga zaman ba zai yuwu ba, ta koma toya kosai a bakin kofar gida, domin a cikin dangin Ubansu Ubaidullah babu mai taimaka musu, a lokacin da Baba yake raye kuma kullum zaka gansu sunzo suna bin su, su na jan su a jiki kamar da gaske, amma tun da ƙasa ya rufewa baba ido shikenan suka ɗauke kafarsu, babu wanda ya sake tako kafarsa izuwa cikin gidan balle ya kawo musu ko da ƙwayar marasa ce. Mama tasha wuya ba ka ɗan ba wajan kula da yaranta, Ubaidullah ganin burinsa bazai cika bane ya sa shi zuwa wajan ƙanin mahaifinsa domin ya taimaka masa, amma abun mamaki sai ya koreshi, Ubaidullah yana da matuƙar zuciya tun a lokacin yaci Alwashi akan burinsa, sannan ko zasu mutu bazai sake taka kafarsa ba izuwa wajan dangin mahaifinsa ba. Da wannan Alwashin Ubaidullah ya ba zama neman aiki, yana ɗan shekara goma a lokacin amma ba labari, dan haka ya fara aikin cire yashi sai ya siyar, da haka ya koma makaranta, a wajen ne kuma suka hadu da amininsa Zaidu. Ya na da shekara goma shabiyu ya koma aikin karfi wato buga block, tun Ubaidullah yana ƙarami amma ɗamtsensa duk sun fito sakamakon aikin karfin da yake yi. Rayuwa kenan har Ubaidullah ya zo ya hana Mama toya Kosai, har ya fara biyawa ƙannansa kudin makaranta, ya biya nasa ya biya nasu. A lokacin da aka tashi bikin Anty Ummu, Mama tayi kuka kamar ranta zai fita, saboda ba kudin da zata yiwa 'yarta kayan ɗaki, inda a karshe Mama taci bashin kudi har dubu ishirin awajan wata mata, ashe kudin nan zai zama tashin hankali. Bayan biki mata ta dinga rashin kirki wa Mama tana gaya mata baƙaƙen maganganu, ran Ubaidullah ya baci dan ya tsani abun da zai batawa mahaifiyarsa rai, dan tun bayan rayuwar Baba Mama ta kamu da cutar hawan jini. Kudinsa daya tara zai biya kudin makaranta ya ɗauka ya bayar,dan bazai jure ganin hakan ba. "Ubaidullah yana da shekara sha biyar a lokacin kuma yana ɗan zuwa training jikinsa duk ya murɗe, wata ranar laraba suka buga ma wani babban mutum block sannan suka masa aiki, nan ya mai dasu kamar yaransa, sosai kuma yake jindadin aiki dasu. Kamar a wasa yake tambayarsu aikin da suke sha'awa domin aikin karfi bazai kaisu ko ina ba. Ubaidullah ya ce ," *Aikin Soja.*" Alhaji Adamu ya ce. "Da gaske aikin soja ku ke so?" Suka jinjina kai gami da cewa "eh" Alhaji Adamu da yake babban mutum ne ya ce, "ai kuwa major Hamza aboki na ne yana garin Abuja, sannan da ma naji wani sanarwa akan cewa yara matasa masu jarumtaza'ayi zabe wanda suke sha'awar aikin soja, za'a turasu ƙasar libya domin su samu ingantacciyar training, ina da aboki ma a ƙasar libyan wanda shine mataimakin mai bada horo, idan kuna so sai na tsaya muku na nema muku takarda ku tafi, shekara uku kacal za kuyi ku dawo da cikakkun tambarin ku na sojoji." Abun nema ya samu, nan Ubaidullah da Zaidu sukayi na'am Ko da Ubaidullah yake fadawa Mama fatan Alkhairi tayi masa, sannan ta saka masa albarka. Abu kamar wasa, bayan su Ubaidullah sunyi wannan maganar da Alhaji Adamu da sati biyu ya kira su yake shaida musu akan cewa sun samu shiga, murna kamar miye, suka dinga zuba godiya tare da yima Alhaji Adamu adduar gamawa da duniya lafiya. Alhaji Adamu ya ce,"kun zama tamkar yarana saboda ni ban da ƴaƴa maza, mata ne su biyu kuma duka duka shekararsu goma sha biyu ne, babbar sha uku, ai kun san su ko?" suka ce "eh" ,Alhaji Adamu ya ce "ina jinku tamƙar yarana, dan haka ku daina min godiya, nan da wata daya zaku tafi kuje ku fara shiri." Ai kuwa nan da wata daya su Ubaidullah sukayi sallama da gida, Mama,Anty Ummu,su Hafiza ,sunyi kuka dan gani suke idan ya tafi bazai dawo ba, shekara uku ba wata uku bane ba sati uku bane, ba kuma kwana uku bane. Sai da suka fara zuwa Abuja tukunna aka ajiye su a *Abacha barracks,* nan suka karbi wani horo na sati daya, kuma jirginsu ya ɗaga izuwa libya. Sosai Ubaidullah yake nuna jarumtarsa da baiwarsa a fagen training, a cikin wata shidda Ubaidullah ya iya riƙe bindiga tare da kwarewa a wajan saiti, shi a karan kansa mai koyar dasu sai da ya sallamawa Ubaidullah. Su na waya dasu Mama lokaci zuwa lokaci su na jin lafiyarsa shi ma yana jin nasu. A cikin shekara biyu Ubaidullah ya zama kwararre, idan ka kalleshi sai ka rantse ya kai shekara ashirin amma bai kai ba, shekarunsa sha bakwai ne, kawai jikin ne ya horu da horo ya saka shi zama babba, fuskarsa dama tun asalinsa ba mai ƙaunar dariya bane, sai dai idan yana tare da yan uwansa ko abokansa. Lokacin da su Ubaidullah suka yi shekara uku a kasar libya sai da aka tura su yaƙi a maƙotar ƙasar ,inda suka yi nasaran lashe yaƙin. Kafin Ubaidullah su dawo Nigeria sai da ya karbi matsayin *master sergeant.*" Ranar da suka dawo kuma aka shirya musu liyafa agarin Abuja na taya su murna. Alhaji Adamu yaji dadi sosai ganin su Ubaidullah basu watsa masa ƙasa a ido ba, su ma sosai suke basa girma tamƙar mahaifinsu, dan sun mai dashi Babansu. Ranar da Ubaidullah ya sauka agarin Bauchi wayyo zo kuga murna awajan yan uwansa, inda suka rungumesa sannan suka saka kukan farinciki sakamakon ganinsa da sukayi da kakin sojoji, tare da nasarori tun da ga takardansa wanda zai fara aiki a *MURTALA BARRACKS ABUJA.* Tun daga wannan lokacin Rayuwa ta canza ga ahalin margayi tsohon Soja Abdullahi galadima. "Hakan ne ya sa Ubaidullah ya fiye zama a garin Abuja, sai dai ya zo weekend 2days ya koma Abuja bakin aikinsa, dan basu son Ubaidullah yana nesa dasu. Duk yaƙi ,ko kuma kama yan' ta'adda su Ubaidullah ake turawa. Shekararsu daya da dawowa daga libya suka sake komawa wani yaƙin, inda aka dinga ɗauki ba'daɗi, da kyar su ka sha kamar ba zasuyi rai ba, amma da ikon Allah suka ci yaƙin, yayin da Ubaidullah shi da Zaidu suka ƙarasa wannan yaƙi a ƙasar. Bayan sun dawo aka gayyatoAlhaji Adamu, inda ya tsaya amatsayin Uba, aka musu ƙarin girma, inda suka lashe muƙaman *first lieutenant* sannan suka samu kudi. Ubaidullah ya kawo shawara suka haɗa kudi suka canzawa Alhaji Adamu mota. Ya ce "a'a yarana kun fini bukatar kudi ,dan haka wallahi na yafe." Su ka ce "ai ba dan yana da bukata bane kawai dan su faranta masa ne amatsayinsu na 'ya'yansa, dan haka ya karba ya saka musu albarka." A lokacin ne kuma aka mai dasu *9JA BARRACKS* bayan sun dawo nigeria kenan. Nan suka hadu da KB kuma suka zama abokai. Tun da Ubaidullah ya tako kafarsa izuwa 9ja barracks to'fa nan ladies suka sakosa a gaba, amma ko kadan baya ɗaga ido ya kallesu balle yasan dasu. Gida Ubaidullah ya gina wa mahaifiyarsa mai kyan gaske, inda yanzu a nan suke rayuwa, dan yanzu kudi yana shigo masa, dan first lieutenant ba wasa ba, da ma ance bayan wuya sai dad i,babu wanda yake fata ya mutu a wuya ko a talauci. Wannan kenan shi ne taƙaicaccan tarihin *First Lieutenant Ubaidullah* wanda a yanzu akayi masa ƙarin girma ya koma *CAPTAIN UBAIDULLAH*saboda yaƙin da sukaje agarin maiguduri, yayin da da yawan Sojoji sun gudu wasu kuma an kashe su, hatta su Ubaidullah sai da suka sha harbi kafin suka tsira. Dawowar su da wata biyu shine aka musu ƙarin girma, sannan za'a sake tura su border nan da wata daya, wannan kenan." ___________ *Wasa farin girki* Gaskiya ba kullum zaku dinga samun littafin nan ba, Ina barar adduar ku Ngd ngd ina ƙaunar ku masoya a duk inda ku ke.💖 COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻🤗 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 _dedicated to my *Fans*_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°5&6* Da washe gari suka fara fita ƙarin training a wajan commander Victor. A cikin 2weeks Ubaidullah ya sauke nashi, dan shi baya wasa barin ma a wajan aikinsa na soja. Ya fito zaije office dinsa suka hadu da Zeey. sanye take da 3quarter na sojoji da black t-shart tana ganinsa ta taho da gudu tayi tsalle ta ɗaga kafarta,ta kai masa naushi amma ko gizau Ubaidullah bai yiba, yadan gota kadan ,a madadin ta fadi, sai tayi wani juyi ta ɗirko akan kafafunta tana kallonsa tana smiling, tahau bubbuge hannayenta tana cewa wow nyc, that's very good my hero, that's why I love u always bcox u ar the best, ta karasa maganar tana kashe masa ido daya tana shirin hugging nasa. Hannu ya ɗaga mata ciƙe da bacin rai ya ce. Enough Zeey i said enough! Don't even touch me! ya fada a tsawance rai bace idonsa har sun kaɗa sun kara zama ƙanana. Ko a jikinta ta ce. Oh my boo common kai meyasa har yau kaƙi ka waye ne kam? Mtswwww Zeey u are very stupid oya get out of my way b4 nayi football dake. Maƙe kafaɗa tayi alamun ko a jikina sannan ta ce. "Anywhere I don't care about ur manner Ubaidullah , i just know 1 something, ta sake matsosa sosai ta ce kasan miye shi kuwa?"I love you" U are always in my heart Ubaidullah, bansan adadin son da nake maka ba. Ta, Gefenta yabi zai wuce yaji an kira sunansa, lumshe ido yayi a hankali ya ce. "Ya salam" Juyowa yayi yana watsa mata harara ita ma, ba kowa bace fa ce Rumaisa. A hankali take taku har tazo gabansa , ta ce. "My luv ina zaka je"? A dan hasale ya ce. "In'da kika aikeni jiyan nan da banje miki ba shine yanzu nake so naje miki Ma." Turo baki Rumaisa tayi ta bude baki za tayi magana taji muryan Zeey tana cewa. "Keeeee! Dan ubanki waye sa'anki a nan wajan"? A hankali Rumaisa ta waigo gefenta tana kallonta,kafin ta ce "eh gaskiya banga mate dina a nan ba infact mutane biyu ne a nan wajan" " Rumaisa and her lover Captain Ubaidullah." Ji kake Tass!tass!tass! Zeey ta faskawa Rumaisa maruka uku a gefe daya. Kafin kace me dambe ya ƙaraɗe waje. Ladies barracks ana bawa hammata iska. Kowacce fada ta keyi cike da kwarewa a salon training din da aka yi mata. Tsaki Ubaidullah yayi ya wuce gaba yana cewa karnuka kawai. Yana gaf da shiga office dinsa yaji ana kiransa a baya. Sir!Sir!Sir. A hankali ya juyo ya ce. What's wrong sergeant? Sergeant ya ce. Sir, "Major Usman ne ya ce na ce maka kaje , guardroom domin tambayar wani mai laifi an tambayesa yaƙi fadi." Okay, ina Captain Zaidu? and First lieutenant K,B? Sergeant ya ce Sir, "Major General ya aikesu Murtala Barracks." Okay kawai Ubaidullah ya ce sannan ya juya,ya dauki hanyar guardroom. Yana isa guadroom ya samu wanda ake tuhuma da laifin yiwa yarinya yar 8yrs old fyade ana tuhumarsa amma ya kafe ya ce ba shi bane,ya aikata ,bayan shaidu sun tabbatar shi din ne. Yana ganin Ubaidullah yaji gabansa ya fadi ganin fuskarsa babu alamun dariya Ubaidullah ya ce. Private first class? Ya amsa ya shigo da sauri yana cewa "yes Sir" Ubaidullah ya ce. "Jeka kawo min kayan aikina" Da sauri ya fita ko 4mnts bai yiba yadawo da sauri hannunsa dauke da ruwa jikin bucket da wayar wuta, ya a jiye, ya juya zai fita Ubaidullah ya ce. "Make sure ka rufe kofar nan da kyau." Private first class ya ce "ok sir" Kallonsa Ubaidullah keyi na yan wasu lokaci kafin ya sake rikiɗewa,alluran sojarsa ta miƙe dan shi a rayuwa idan akwai abin da yafi tsana a duniya,to ace anyiwa yarinya ko budurwa fyade. Ba tare da bata lokaci ba,ko yin magana, ya dauki ruwan bucket din nan ya watsa masa rabi,sannan ya ɗauki wayar wutan ya fizge bakin ya jona masa shocking ,yaja table ya zauna yana kallonsa. Nan mai laifi ya fara diskon dole ,yayinda babu in'da bata jijjiga a jikinsa Sai da yaga ya kusan sumewa kafin ya ɗauki babbar maduki ya bugesa dashi ya fadi bakinsa harta koma gefe. Captain Ubaidullah ya durƙusa a gabansa fuskarsa tamƙe tamau( wai soja mala'ikun duniya) naushi daya ya kai masa a baki take haƙorin mutumin guda biyu suka faɗi ƙasa,Ubaidullah yasa hannu ya ɗauka , ya damƙa masa a hannunsa,idanunsa sun ƙara ƙanƙancewa. Ya ce. "Ka faɗa min gaskiya kaine kayiwa yarinyar nan fyaɗe"! a tsawance yayi maganar. "Idan kuma kasan ba gaskiya zaka fada min ba, to ina baka shawara daka ja min tsummar bakin ka kayi shuru if not wallahi humm zaka sake ganin ainihin true color din Ubaidullah." Cikin sarƙewar murya ya ce. "Yallabai kayi hakuri ni ne na aikata." Ran Ubaidullah ya sake baci ya rufesa da duka, sai da yayi masa jina-jina, kafin ya fita yana huci. Direct office din Major Usman ya wuce ransa bace, ƙananun Sojoji sai sara masa su keyi. Ya shiga ya ƙame yana sara masa "Sir mai laifi yayi jawabi ya amsa laifinsa." "Nyc job Ubaidullah keep it up Ina alfahari da kai, you can go." Ubaidullah ya sake sara masa kafin ya juya ya fice. ya tafi office dinsa yana zama kamar da 10mints sai ga su Zaidu, da K,B sunyi sallama ya basu damar shigowa, hannu suka bawa juna su kayi musabaha. Zaidu ya ce. Captain Ubaidu how is work? Smiling yayi " we tnk god Captain Zaidu and u? Zaidu ya ce. "Alhamdulillah" K,B ya ce. "To abun kuma ƙi dangi ne"? Ubaidullah ya ce. "Menene kuma ƙi dangi"? "Ah to ba dole na ce ƙi dangi ba, naga ni yau ba ayi niyyar yimin magana ba, ba'a kulani ba" Gaba'ɗaya suka kwashe da dariya,Ubaidullah ya ce. "Wallahi Allah ya shiryeka K,B yau kuma sharri kake ji dashi zaka ce na ƙi kulaka"? K,B yana dariya ya ce. "Ah to ba gashi yanzu na saka ka dariya ba, dama bana so naga ka haɗe rai sosai din nan." Ubaidullah ya ce. " ai ba a san soja da dariya ba" Zaidu ya ce. "Yes of course , ba'asan soja da dariya ba but today you look very sad what's wrong my dude"? Ubaidullah ya numfasa yana jan iska mai zafin gaske yana fuzarwa,zuciyarsa yana masa soya. Ya ce. "Wallahi a rayuwata na tsani naji kalmar an'yiwa mace yarinya ko budurwa fyade, dazu an saka wani yaro matashi a gurdroom ana tuhumarsa da laifin yiwa yarinya, yar' 8yrs old fyade, dan rashin kunya ana tambayarsa ya kafe ya ce ba shi ya aikata ba, shine Major yasa naje na tambayesa, ina zuwa na jona masa shocking nan take yake gayamin akan cewa shi ya aikata, wallahi har yan zu abin yaƙi fita raina." Zaidu ya numfasa ya ce. "Naji case din tun jiya ake zarginsa yaƙi magana, ashe kai kana zuwa ya ƙoro maka jawabi"? Ubaidullah yayi tsaki ba tare da ya kuma yin magana ba, illa Zaidu da K,B da suke jajinta lamarin, amma shi kam tunani ya keyi yanda za'abi a magance yiwa yan'mata da yara fyade a wannan zamanin ,dan yanzu abun ya zama ruwan dare, bata ya'ya' mata ta hanyar rabasu da budurcinsu, yana ta faman thinking about this matter, har su Zaidu suka yi masa sallama suka tafi office dinsu. Da washe gari Ubaidullah da Zaidu, suka shirya zuwa office din General Of The Army domin neman permission, zasu tafi ganin gida b4 suje in'da aka turasu kama yan'ta'adda, wato border. Har office suka je amma yau general of the army bai zo office ba,nan ake shaida musu yau bai fito gida ba, dan haka suka juya suka fita. Zaidu ya ce. "Ubaidu muje gidansa kaga lokaci yana ƙure mana kuma kasan halin general, amma ya kace."? Tsaki Ubaidullah yayi sannan ya ce."okay muje amma gaskiya ba son zuwa nake yiba" Zaidu ya ce. "Na sani ai" Sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin su ƙaraso,gate din gidan General Of The Army,wanda duk inda ka wulla idanunka sojoji ne, ana ganinsu Ubaidullah aka ware musu gate ana sara musu, *CAPTAIN UBAIDULLAH & CAPTAIN ZAIDU*. har suka karasa bakin kofa wani soja ya bude musu yana sara musu gami da cewa " wlcm sir Ubaidullah and sir Zaidu" Zaidu ne ka dai yake amsawa , amma Ubaidullah sai dai ya jinjina kai da kar yake kallon kowa a barracks yasan wa inda suke sonsa da wanda basu sonsa. A parlour sukayi sallama Wata haɗaɗdiyar mata ce ta sauko daga kan step tana taku cike da izza da nuna isa da gadara ,kayan dake jikinta ma abun kallo ne, daka ganta kasan iyayi ya zauna ko ba a fada maka ba. Humm, *HAJIYA JAMILA KENAN MATAR GENERAL OF THE ARMY ABDULKARIM*. mata mai jida kanta gami da alfahari da nuna ita watace. Tana karasowa su Ubaidullah suka sara mata su na gaisheta , sai da ta dauki som minutes kafin ta amsa. Ubaidullah bai ce komai ba, Zaidu ne ya ce. "Madam Oga sir muke nema" A hankali ta kira sunan yar'ta cike da yanga. Hanan!Hanan!Hanan! Wata yar budurwar yarinya mai ƙarancin shekaru dan ba zata gasa 17yrs ba ta fito tana yatsine fuska tana binsu Ubaidullah da kallon banza. Hajiya Jamila ta ce. "Hanan je ki cewa dadynki yaransa su na nemansa, turo baki tayi tana ƙunƙuni ta juya ta haura upstairs din daddynta, kamar da minti bakwai suka sauƙo tare. Yana ganinsu yayi murmushi ya ce. "Ah Captain Ubaidullah and Captain Zaidullah I hope dai everything is fyn,na ganku at this tym"? Sara masa suka yi kafin suka haɗa baki wajan cewa "yes sir everything is fyn Alhamdulillah mun zo neman permission ne, b4 mu tafi border muna so muje gida." General ya ce. "Okay no problem kuna iya tafiya next 2morrow" Godiya suka yi sannan suka miƙe zasu tafi har sun kai bakin kofa ,general ya ce. Hope ba daɗewa zakuyi ba? Zaidu ya ce. "Eh sir 5days ne kawai" Jinjina musu kai yayi sannan suka fice ,Hanan sai kallon Ubaidullah takeyi tasan tana da ji da kai da girman kai amma bisa alama Ubaidullah zai fita zafi ,duk da ta yi musu kallon banza amma taji wani abu aranta akan Ubaidullah. ******agurguje Yau ne su Ubaidullah zasu je ganin gida sun shirya tsaf K,B ya ce. "Wallahi da nasani dana tambaya na biku amma nasan halin general yanzu kam ba zai barni ba" Zaidu ya kwashe da dariya ya ce. "Sunan ka sorry kawai" bye bye sai mun dawo, K,B ya kai masa dukan wasa ya kauce yana dariya ,a tare suka fito ya rakosu har mota suka shiga yana ɗaga musu hannu suka fice daga barracks , suka ɗauki hanyar garin *BAUCHI STATE*..... ~~~~~~~~ SAI FA HAKURI😢 MY FANS INA BUKATAR ADDUARKU AKAN WANNAN LITTAFIN DAN WLH TYPING ...YANA BANI WUYA COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀ [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ *MARUBUCIYAR* ( *HALITTA DAGA ALLAH NE*) ( *GUDU A JEJI*) ( *SHUHADA*) ( *NIDA ƘANNAN MIJINA*) TYPING...( *WA'YA KASHE ZAHRA'U?*) *#200* _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°7&8* Su na shiga garin Bauchi Ubaidullah ya jinginu da sit ya lumshe ido yana shaƙar ƙamshin garinsa, da shike yanzu Zaidu ne ke driving din motar, dan bayan sun tsaya a jos suka yi sallah Zaidu ya karbi driving din kasancewar Ubaidullah ne ya ja su daga Abuja to jos, shi kuma Zaidu ya ja su har garin Bauchi. Dukkan su sun yi shuru babu mai magana wa dan uwansa, ko wannen su da abun da yake tunani. Ubaidullah sai cool smiling yake saukewa a beautiful face dinsa , ga wani happiness da yake ciki. Zaidu ne ya ƙatse shurun ta hanyar cewa. "Ubaidullah dan Allah zan fara sauƙa a gida" "Okay Captain Zaidu tun da kasan ni ai ban yi missing din gida ba, kai ne kayi missing,mtsww" "Oh Allah, Ubaidu Allah ya shirye ka, ni fa ba wani abu nake nufi ba, kaga motar ka ce, ni kuma wallahi a gajiye nake ba zan iya mu fara zuwa gidanku ba, ka bar ni da wangale baki" "Kai dai kasani," cewar Ubaidullah. Har suka shiga sabon unguwarsu mai suna jahun, sai da Zaidu ya sauƙa tukunna Ubaidullah ya koma mazaunin driver yana shirin yiwa motar wuta, Zaidu ya ce. "Ba za ka shigo ku gaisa da su Umma da Inna ba? iwarhaka na san baba ba ya gida." Ba tare da yabawa Zaidu amsa ba ya fito yayi gaba Zaidu yana binsa a baya da jakarsa da ya rataya ta a kafadarsa. Tura kofar suka yi su na sallama Umma (mahaifiyar Zaidu) ta ce ."ah maraban ku oyoyo mazan fama" Kakarsu Zaidu (ta wajen Uba)ta miƙe da sauri har tana tuntube zaninta ya kunce amma ba ta bi ta kansa ba tana cewa . "Oyoyo, oyoyo mugun mai gida sannu da zuwa mugu oyoyo mugu,ta zo za ta rungumesa, sai kuma ta fasa,Zaidu ya ce. "Ah Inna me ya faru kuma, kin fasa oyoyo din ne"? "Mtsww oho maka kuma ban sani ba sau nawa zan fada maka idan zaka zo ka daina zuwa da wannan kayan naku ( *kakin sojoji*) haba idan mutum ya kallesu sai zuciyarsa ta tsinke ai wannnan mugunta ne da rashin imani,ga shi yanzu kasa ina jin zawo, ta fada ta juya tana kan mita ,ai gwanda ma kai kana dariya akan wannan abokin naka mai fuskar zaki " ta shige daki. Ubaidullah ya yi murmushi ya duƙa ya gaishe da Umma ta amsa cike da kulawa ƙannan Zaidu suka gaishesa tare da yi musu sannu da zuwa, Ubaidullah ya miƙe yana yiwa Umma sallama a kan cewa zai wuce gida. Umma ta ce. "Ah Ubaidu har za ka tafi gida ka tsaya kaci abinci mana " " a'a Umma na gode na gaji ne ba na so na zauna ne kar na kasa tashi a kan lokaci ,dan wallahi bacci nake ji" Umma ta ce. Ai dole ku ji bacci kullum ana abu daya Allah dai ya kare mana ku" Suka amsa da ameen Ya juya zai fita, Zaidu ya bi bayansa ,ya ce" to kai kuma ina zaka je da ka wani rakoni a baya "? Dariya Zaidu yayi "Wallahi Ubaidu kai dai ba'a yi maka gwaninta wai fa zan dan taka maka ne"? "No I don't needed tnx," ya fada yana wucewa gaba. Zaidu ya ce. "Ok ka gaishe min da mama kafin na shigo an jima" "Ok za ta ji sai ka zo" Zaidu ya juya ya koma cikin gida, daidai nan Inna ta fito tana yarfe zani tana riƙe ciki, Zaidu ya ce. "Subhanallah matar meya faru"! "Uwarka ce ta faru mugu kawai idan kana so na kula ka , ka je ka cire wannan kayan naka sai ka zo mu yi gaisuwa, " ta fada tana murguda baki Zaidu ya kwashe da dariya,Umma ta hararesa ta ce. "Ka fa dawo kenan ko? za ka fara saka Inna ciwon baki? to wallahi ba zan lamunta ba ka shige bangarenka." Zaidu yana dariya ya ce. "To shikenan Inna kwantar da hankalin ki na tafi" "Eh din na ji je ka mana, kar Allah ya sa ka dawo idan kaga dama, kafi ruwa tafiya" ~~~~~~~ Ta bangaren Ubaidullah ,parking din motarsa yayi a bakin madaidaicin gate din gidansu, black shadow din dake face dinsa ya cire,yana smiling. Turo ƙaramin kofa na jikin gate ya yi gami da sallama, amma shuru bai ga kowa ba, abun har mamaki ya basa, ko ina mai gadin da ya a jiye oho. Har ya kai kofar parlour kafin ya hau kwaɗa sallama, amma ya ji shuru ,har ya juya zai tafi part dinsa, sai ga Hafiza ta fito da hijabi, tana ganinsa ta saki dariya ta taho da gudu tana cewa. "Oyoyoo Yaya, rungumeta yayi sannan ya saketa tana ta murmushi (Allah sarki dan uwa gudan jiki) ya ce."ina Na'ila"? "Wani faduwar gaba ne yazo ma Hafiza ta hau tsilli-tsilli da ido dan Na'ila dazu kawarta ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar, kawarta. Ba ta kai ga ba shi amsa ba, sai ga mama ta fito, da sauri Ubaidullah ya mai da hankalinsa gareta,cikin murna da farin ciki ya je ta rungumeta, mama ta ce. "Oyoyo ɗana na kaina , barka da zuwa, bana kai kadai ka zo ne ,ina Zaidu"? Murmushi yayi kafin ya ce. "Zaidu na a jiyesa a gida amma ya ce na gaishe ki kafin an jima ya zo" "Ayya dan albarka Allah ya kawosa lafiya,ya amsa da amin kafin ya ce. Mama ina Na'ila ? Mama ta ce. "Hafiza ina Na'ila dan dazu tare na bar ku"? Cikin in-ina Hafiza ta ce. "Dazu bayan kin shiga daki kawarta Munira ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar Munira" Mama ta hau salati tana tafa hannuwa," Oh Allah na me Na'ila take son zama ne ? shi ne ta kama hanya ta fice baza ta iya zuwa ta fadamin ba? ko dan ta san ba zan barta bane?" Ita dai Hafiza ban da zare ido Babu abin da take yi,ga wani uban tsoron da ya lullubeta ganin yanda fuskar yayansu ya rikid'e ya canza kala jijiyar wuyarsa duk sun tashi da ka kalle sa ka ga bacin rai k'arara, jinjina kai yayi sannan ya hau wurgawa Hafiza harara ,ai nan Hafiza ta k'ara tsurewa. Ta kanta ya fara "A kan me kina kallo za ki bar Na'ila ta fita iye? Hafiza tayi shuru sai zare ido take yi ta kasa bada amsa, sai ja da baya ta keyi yana binta, ganin yana shirin cafkota ne ya sa ta ɗiba a guje ta yi bayan Mama ta saki kuka. Mama ta ce. " a'a wallahi karka taba Hafiza in dai Na'ila ce ba jin magana take yi ba, dan da tana jin magana to wallahi ba za ta fita a gidan nan ba,tun da nice nan na hanata fita da kuma kai, to ba ta ji maganata da taka ba, har za ta ji maganar Hafiza?" "Kuma na tabbata bata san za ka zo yau ba, da ba za ta fita ba." Ba tare da Ubaidullah ya yi magana ba ya juya ya fice ransa ɓace. Har yayi wanka ya shirya ya kwanta, Hafiza ta kawo masa abinci amma ko kallon abincin bai yi ba har aka yi sallar magriba, Na'ila ba ta dawo ba hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba. Ya je daki ya samu Hafiza tana karatun Alƙu'ani kasancewar sun kusan yin sauka, tana ganinsa ta dasa aya. Tambayarta yayi, ya ce. "A ina ne suka walimar"? Jikin Hafiza na kyarma ta ce. "Nima ban sani ba yaya." Ba tare da yayi doguwar magana ba ya juya ya fice. Yana fitowa ya samu,Mama a parlour ta kasa zaune ta kasa tsaye. Nan suka zauna jingum-jingum Har akayi sallar isha'i, su Na'ila basu dawo ba. Kafin wannan lokacin, Captain Ubaidullah ya fara tunanin kalar salihin dukar da zai yiwa ƙanwarsa. Sai wajan karfe tara suka shigo gidan. Ubaidullah,Mama,Hafiza duk suna zaune a parlour. Na'ila da kawayenta su biyar suka shigo Sun fara sallama kenan. Assalamu alay.....!! Sallamar ta tsaya a maƙogaron Na'ila sakamakon tozali da yayanta, yana mata kallon za ki ci Ubanki yau!! ============== *GASKIYA ZAN AJIYE TYPING DIN LITTAFIN NAN, ZUWA WANI LOKACIN DA NI KARAN KAINA BAN SANI BA,* *GA MASU ƘORAFI AKAN ABUN DA NA FADI DUK INA SAURARONKU........* COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ *MARUBUCIYAR* *HALITTA DAGA ALLAH NE* *GUDU A JEJI* *SHUHADA* *NIDA ƘANNAN MIJINA* TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°9&10* A hankali Ubaidullah ya tashi yana ci gaba da yi mata kallon yau na lahira sai ya fiki jin dadi. Ba iyakar Na'ila wacce ta yi laifi ba har ta Hafiza sai da hantar cikinta ya kaɗe ganin yanayin Yayan nasu. Juyawa yayi ya kalli Hafiza murya a daƙile ya ce. "Go and close the door" Jikin Hafiza na kyarma ta wuce a sabule, ta je ta kulle kofar, har ta juya ya ce. "ciro keys din, ki kawo min" Hafiza ta cire keys ta kawo masa, ta miƙa masa jikinta na rawa. Na'ila da kawayenta Allah ne kadai ya san kalar tashin hankalin da suka shiga, Na'ila har ta fara zikiri a cikin zuciyarta dan ta san ba makawa sai taci ubanta yau, yanda ya sa aka kulle da kawayenta ta san su ma yau sun kawo kansu, dan yanda zai jibgeta, haka zai jibgesu. A hankali ya kalli Mama wanda ta buga tagumi tana kallonsu dukkan'su, tana hararan Na'ila ,wacce ta kama hanya ta fice tun rana sai yanzu karfe taran dare ta dawo da sunan wai sunje walima. Durƙusawa Ubaidu yayi a gaban mahaifiyarsa hannun da ta sa a kumatunta ya cire sannan ya ce. "Mama pls ki shiga daki" ya fada ya kamo kafadarta ya miƙar da ita. Har cikin daki ya kaita ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya juya ya fita ya kulleta da waje. Yana fitowa parlour ya samu Hafiza har ta fara kuka ganin ya kai Mama daki ta san yau babu mai taimakon su Na'ila sai Allah. Wani harara ya galla mata da wani irin kalar ido wanda ba ta taba gani ba, kafin a tsawance ya ce. "Keee!!! Dan ubanki!! shiga daki idan kuma kina so na haɗa dake to bilmillah!" Ai da gudu Hafiza da ta yi daki har tana tuntube kafin ya juya ga Na'ila wacce ta fara kuka wiwi tun ba a kai ga dukarta ba. "Dan Allah Yaya ka yi hakuri na tuba ba zan sake ba wallahi ba zan kara ba Yaya ka yi hakuri kar ka dake ni" Nan Na'ila ta hau magiya kamar ranta zai fita, ganin ya ciro belt ya sakata fara kiran sunan Mama da Hafiza. Ya ce. "Wato tun baki tafasa ba kina so ki ƙone ko? tun baki kai ko ina ba kina so ki ƙarawa Mama hawan jini a kan wanda take dashi? Na'ila tun baki kai ko ina ba kina so ki gwada kamar kin fi karfinmu ko?" Yana maganar yana matso su , su na ja da baya. Na'ila ta ce. " a'a Yaya wallahi ba zan ƙara ba,am really sorry" Shut up!! Ya fada da karfi. Kawayenta suka haɗa baki su na cewa . "dan Allah kayi hakuri mu dai a barmu mu je gida" Su na gama fadin haka Ubaidullah ya rufesu da duka. Shata musu belt din kawai yake yi, ta ko ina ya samu dan idonsa a rufe yake, ba'a son ransa yake dukan Na'ila ba, zai so Na'ila ta zama kamar yar'uwarta Hafiza amma ya ga alama sai ya mata dukar da zata yi jinya tukunna. ya gwammace ya karyata idan ya so ya kaita asibiti ya yarda, ya kashe kudi akan wani abu ya sameta wannan rayuwar da bata da tabbas din. Tun su Na'ila da kawayenta su na kuka su na ihu, har ya zamto basu iya katabus. sosai Captain Ubaidullah ya musu rugu-rugu. Sai da ya ga ba su motsi sosai tukunna ya dakata yana huci. Mama tun tana kiran sunansa tana bugun kofa, domin jin yanda yaran mutane ke ihu su na cewa zasu mutu,da ta ji abun nasa ba na ƙarewa ba ne ,ta hakura ta koma ta zauna, ta zubawa sarautar Allah ido. Bayan ya gama jibgarsu ya ga sun kasa ihu da kuka basu motsi tukuna,ya kwashe su ya saka su a mota, sai RIMI HOSPITAL. Su na isa a ka basu taimako tare da yi musu,treatment saboda ya faffasa musu jiki da belt. Gado a ka basu, sai karfe uku na dare Ubaidullah ya koma gida, bayan ya tabbatar an yi wa su Na'ila allurar bacci sunyi bacci. Yana zuwa ya je ya bude Mama ya sameta zaune ta buga tagumi, har wannan lokacin ta kasa bacci, (ALLAH SARKI UWA). Da sauri ya isa gareta, ya cire hannunta daga kumatun'ta, kafin ya ce. "Ki yi hakuri idan na bata miki Mama, I don't mean to hurt you pls, but Na'ila tana bukatar hakan, bcox duk abun da ya same ta, ya same mu ne, amma ba za ta gane haka ba, ba zata iya hango tsananin son da muke mata ba, Mama har nawa Na'ila take duka-duka shekarunta goma fa Mama, amma take neman fin karfin mu?" Mama ta share hawaye ta ce. "Haka ne yanzu su na ina" Na kai su asibiti" Mama ta dafe ƙirgi ta ce. "Ubaidu asibiti dai, asibiti fa kace? har da ƴaƴan mutane ka daka fa? shi ne duk ka kai su asibiti?" "To Mama ai hakan shi ne daidai, baki ga ba saboda rashin kula irin na iyayensu akwai wanda ya zo nemansu ne? ba su zo ba ,ni a tunani na hakkin iyaye ne idan ba su ga y'ay'an su ba ko min dare ya kamata su je nemansu, amma ba su zo ba." Shuru Mama tayi kafin ta ce. "Ni fa wallahi bana son tashin hankali da ka bar yara sun tafi gidan iyayensu, bana son abun magana da ƙanwarka kaɗai ka hukunta." Wani murmushi ya saki kafin ya miƙe ganin har karfe hudu ta gauta ,ya ce. "Mama ba ki jin dadi ,ba ishashshiyar lafiya gare ki ba, yanzu ki kwanta ki huta gobe sai mu koma asibitin mu dubo su" Mama ta ce. "Yaran mutane kuma fa?" Ya ce. "Mama sai magana kike yi a kan yaran mutane , na ga fa harda Na'ila" Girgiza kai tayi ta ce. "Je ka huta, yau ka zo amma ko hutawa baka yi ba, Allah dai ya sa ka ci abincin ma" Dan sosa ƙeya yayi. "Wallahi Mama banci ba, zan ci idan Allah ya kai mu anjima", yana fadi ya sa kai ya fice a dakin,Mama ta bi bayansa da kallo kana ta ce. "Allah ya daɗa shirya min ku" ~~~~~~~ ta ban garen Hafiza ma ba ta yi bacci ba, tana jin yadda y'ar uwarta ta dinga ihu tana kuka, ita ma haka ta dinga kukan a daki, ko da taji shuru tsoron fitowa take yi karya haɗa da ita. ~~~~~~~~~ Da washe gari. Da safe misali karfe tara. Ubaidullah ya dan koma bacci bayan yayi sallar asuba kafin zuwa sha biyu su je asibiti" ana tunanin kenan. Cikin bacci yake jin kamar hayaniya na tashi, amma sai ya danganta hakan da mafarki, jin abun bana ƙarewa ba ne ya saka shi tashi ya dauki jallabiyyarsa ya saka ya fito, can wajan gate ya hango Mama da Hafiza tsaye gefe daya mai gadi da wasu samari su uku da yan mata biyu. Cike da takun isa da izzan jarumtaka na ƙarfeffen soja ya ƙaraso mai gadi na ganinsa ya sara masa ya koma gefe. Hafiza tana ganin Yayan nasu tayi saurin matsawa gefen Mama. Cike da ɗaure fuska ya ce. "lafiya kuwa meke faruwa?" Daya daga cikin samarin ne ya nuna Ubaidullah da yatsa yana cewa. "Kai dalla malam, ma su waye zaka fito kana ciccin magani, idan kana gadara kai namiji ne ai muma ba ka ganmu da jan baki ko dan'kwali ba, ina ƙannan mu?su muka zo nema, kuma ance sun zo nan tare da ƙanwarka, yanzu kuma mun zo muna jin wata zance da bamu ganeta ba." Ran Ubaidullah ya baci sosai ya tsaya yana masa wani kallon raini, Kafin ya kalli Hafiza ya ce. "Wuce ki shiga ciki" Da gudu ta juya tayi abin da ya umarceta kafin ya kamo kafadar Mama ya juya da niyyar ya shige da ita ciki ita ma, sai ya ji daya daga cikin samarin yana cewa. "Kaiiiiiii! ina ga baka san su waye ake kira da yan'bakaro ba, babu unguwar da ta kai mu sara suka a cikin garin Bauchi, idan baka fito mana da ƙannan mu ba, to wallahi sai mun yi gunduwa-gunduwa da kai." Cak Ubaidullah ya ja ya tsaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur jikinsa ya ɗauki b'ari. ============== MANAGER PLS COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀ [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ *MARUBUCIYAR* *HALITTA DAGA ALLAH NE* *GUDU A JEJI* *SHUHADA* *NIDA ƘANNAN MIJINA* TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°13&14* A hanya su na tafiya Mama sai mita take a ina Ubaidullah ya tsaya. Zaidu ya ce. "Mama maybe akwai abun da ya tsai dashi ne shiyasa a yiwa abokina uzuri" Mama ta girgiza kai kawai, ta ce. "Mu fara biyawa mu a jiye ƴaƴan mutane kafin mu wuce gida" "To Mama" abun da Zaidu ya furta kenan. Sai da suka a jiye yaran mutane a gidan iyayensu, Mama da kanta ta shiga tayi musu jawabi, wanda zasu fahimta sun fahimta, masu toshewar kwakwalwa kuma sun kasa fahimta, suka rufe Mama da ruwan bala'i, ganin yanda jikinsa ƴaƴansu ya kumbura da shatin belt, bisa alamu duka ba bana wasa ya musu ba. Mama har sai da ta ji dadi da Ubaidullah bai zo ba,dan tasan wani abun kam sai dai a kunna ƙaramin yaƙi. Zaidu ya ce. "Mama wai mai ya faru ne kam haka na kasa fahimtar komai fa?" Mama ta ce. "Ai gata nan a gabanka sai tsilli-tsilli take yiwa mutane da ido, na rashin gaskiya, ai tukunna ma sai mun koma gida ki sake haduwa dashi" Na'ila tayi rau-rau da ido alamun zata yi kuka. Zaidu ya ce. "No no my lovely kar kiyi kuka kinji ai gani nan ina nan bazan bari ya sake dukan ki ba." Da haka har suka koma gida. Mama tana tambayar mai gadi akan cewa "Ubaidullah bai dawo gida ba?" Ya ce. "Eh Mama ai tun da ku ka fita shi ma yaja mota wanda ya sakani tsinkewar zuciya ya fice bai dawo ba." Girgiza kai Mama tayi sannan ta ce. "Allah ya kyauta" Suka shige cikin gida, Zaidu ya ce. "Mama ni zan koma part dinsa na zauna kafin ya dawo" "To Zaidu ka huta kafin ya zo ma na gama muku girki, tun da yanzu kam sai dai abincin rana." ~~~~~~~~~~ Ta bangaren Ubaidullah ko da ya je hospital din aka tabbatar masa da an sallamesu, sun tafi tun dazu. Wayarsa ya dauka ya bugawa Zaidu, a lokacin Zaidu na zaune a 2sitter yana latsa systerm dinsa. Daukar wayar yayi yasa kunne. Ubaidullah ya ce. "ya ne, kun koma gida ne" "Ah no Captain Ubaidullah muna hospital muna jiranka." "Mtswwwww, Zaidu bana son raini fa" Wani dariya Zaidu ya kwashe dashi wanda yasa Ubaidullah rumtse ido, kuma da gangan Zaidu yayi dan kawai ya sake ƙular dashi. "Oh Allah, Yayana Ubaidu baka son raini, ni kuma kasan ai ina son raini, ka ga idan zaka dawo gida ka dawo, dan mu kam har mun manta da wai munje hospital yaran jama'a kuma mun kai su gida." Ubaidu bai sake magana ba illa tsakin da ya ja, ya katse wayar. Zaidu ma dariya yake yi, ya a jiye wayarsa a gefensa ya ci gaba da aikin da yake yi a systerm dinsa. Sallaman samarin yayi gami da cewa su tafi gida, ƙannan su an kai su gida,kafin shi ma ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida. ~~~~~~~~~ Wajan Mama ya fara wuce wa,tana ganinsa ta hau mita. "Tun dazu muka fita tare da kai Ubaidu,amma kai sai yanzu ake ganinka, ina ka tsaya ko kuma nace ina ka wuce?" Dan sosa gefen wuyarsa yayi dan shi bai cika son yiwa Mama karya ba amma yanzu ya zama dole ya suturta maganarsa. ya kafin ya ce. "Am so sorry my Momma, ina fita wani kiran ya taso min shiyasa dole na je nayi wancan aiki tun da nasan kun fita da Zaidu zai yi abun da ya kamata." "Oh Allah to da Zaidun bai zo ba kuma fa?" "Kiyi hakuri Mama tun da ya zo ai shikenan, yanzu ina Zaidun ya ke?" Mama ta juya ta shiga kitchen tana ba sa amsa tana kiran sunan Hafiza. Fita yayi ya je ya samu Zaidu zaune a kujera ya duƙufa akan systerm, sallama Ubaidullah yayi, Zaidu ya ɗago ya kallesa ya amsa, ganin sai wani cin magani yake yi yasa Zaidu ɗauke kansa shi ma ya ci gaba da abun da yake yi. Can zuwa anjima Hafiza ta shigo da sallama, suka amsa kafin ta ce. "Mama ce ta aiko ni na zo na tambaye ku, a kawo muku abincin nan ne ko zaku zo ku ci?" Zaidu ya kashe systerm din dake cinyarsa ya tashi yana cewa. "No my sister nikam a wajan Mama zanje na ci amma bansan wannan Yayan naku dan zafin kan ba" Tsaki Ubaidullah yayi shi ma ya tashi suka fito a tare, har izuwa parlour, Mama ta shinfiɗa musu babbar lade na cin abinci, suka zazzauna. Hafiza ta zauna can nesa dasu tana jiran fitowar Na'ila amma shuru ba Na'ila, ita kuma Hafiza ba zata iya cin abincin ba matukar y'ar uwarta ba ta fito ba. Zaidu ya kula da haka ya juya yana kallon Mama ya ce. "Mama meya faru ne kam, me aka yiwa my lovely aka faffasa mata jiki gashi yanzu taƙi fitowa ta ci abinci?" "Zaidu wannan lovelyn dinka bata jin magana kwata-kwata jiya wai sun tafi walima yaran nan tun rana amma sai karfe tara na dare suka dawo, sai ka ce basu da mafaɗi, shiyasa Yayansu ya jibgesu har da kawayen nata ai kaga gobe ba zata sake zuwa ba, na rasa dalilin da yasa Na'ila bata jin magana tun dana iyanzunta take son tuburewa ai gwanda ya mai dota saiti." Zaidu ya ce. "Haba Mama yanzu a gabanki ya musu wannan dukar sai kace ya kama b'arawo a guardroom? abokina nan fa ba barracks ba ne, gida ne bai ka mata ka dakesu da belt din sojoji ba ,gaskiya ban ji dadin haka ba, yes punishment din da ka musu shi ne dai-dai kuma naji dadi da ka haɗa har da friends din gobe ba zasu ƙara zuwa su ja ta ba, amma dukan yayi worst gaskiya ka dinga sassautawa." Mama dai bata sake cewa komai ba illa ma tashi da tayi ta shiga daki tabarsu a wajan. Ubaidullah ma ko uhum bai cewa aminin nasa ba. Zaidu ya kalli Hafiza wacce ta raƙube a gefe ya ce. "My sister oya tashi ki je ki kira min my lovely" Hafiza ta amsa da to , ta tashi tayi hanyar dakinsu. Da sallama ta shiga ta samu Na'ila zaune ta zuba tagumi har yanzu fuskarta a kumbure yake, wani tausayin yar uwarta ne ya kamata, tazo ta zauna kusa da ita ta ce. "Sister ki taso ki zo muje muci abinci mana?" Girgiza kai Na'ila tayi ta ce. "Na ƙoshi bana jin yunwa jikina ne yake min ciwo" "To ki sha paracetamol sai ki zo muje Yaya Zaidu ya ce na zo na kira ki ,kuma na tabbatar mun zo tare ki taso muje kinji siaterna" "Yaya yana parlourn?" Ta tambayi Hafiza. Hafiza ta ce. "Eh mana yana parlor ina so idan mun je ki basa hakuri kinga Yaya yana sonmu amma ke baki jin magana ,Na'ila ba kyau Mama ta ce kibar abu amma ki ƙi ji Yaya ya hanaki yawo Anty Ummu ma ta hanaki amma duk baki ji, ki ga fa idan har Anty Ummu ta saka Yaya abu yana yi fa, to ke meyasa idan ya sakaki ba zaki ji ba ko kinga ni haka nake yi ne iyee?" Girgiza kai Na'ila tayi alamun a'a. Kafin Hafiza ta ce. "To ki natsu kin ga dai yanzu Yaya, ya zama mugu amma bana mugunta ba dan haka mu bisa a hankali mu dinga jin magana, gashi karba ki sha muje" Karban maganin Na'ila tayi tasha da kyar, kafin suka fito sai rakub'e-rakub'e suke yi dukkansu. Su na fitowa Ubaidullah ya musu kallo daya yaga yanda jikinsu ke rawa alamun tsoronsa suke ji ,shi kuma ba haka bane burinsa ace ya zama dodo a wajan ƙannansa. Dan haka su na fitowa ya tashi ya fice yayi hanyar part dinsa. Zaidu ma fada yayiwa Na'ila sannan ya bi bayan amininsa. Kwance ya samesa a 3sitter ya lumshe ido. Zaidu yayi murmushi ya ce. "Na ga kalar soyayyar yan uwa, amma shine duk da haka ka shirgiɗa musu na jaki?" "Mtsww Zaidu ba zaka gane bane izuwa yanzu yaci ace ka gama karantar halina" "Eh na fahimce ka my man addua zamu dinga musu, ni fa kasan wani abu kuwa?" Ubaidullah ya girgiza kai yana kallonsa. Zaidu ya ce. "Ni wallahi da zaka ban Na'ila ita nake so wallahi zan jirata nan da shekaru biyar na aureta dan ina sonta." "Hahahah Zaidu kenan ko dai ka fara shaye-shaye ne? Na'ila fa ka ce ina zaka kai wannan gagaran,dama Hafiza ka ce yauwa amma Na'ila sai a hankali" ya karasa maganar yana dariya sai ka ce ba shi ba. Abun da Zaidu ya fahimta shine Ubaidullah ya dauki maganarsa a matsayin wasa shi kuma da gaske yake yi ,amma ba komai zai basa mamaki. Zaidu zai sake yin magana ,Ubaidullah ya ce. "Ka ga tashi muje na gano y'ar uwata Yayata Anty Ummu naje naga lafiyarta daga nan naje na gaishe da Umma, mu zagaye gari tun da 5days kawai zamu yi." Zaidu ya ce. "Ok mu je" Fitowa suka yi a tare sai da suka yiwa Mama magana kafin suka shiga mota suka bar gidan. ~~~~~~~~ COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻👮🏻‍♀ [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ *MARUBUCIYAR* *HALITTA DAGA ALLAH NE* *GUDU A JEJI* *SHUHADA* *NIDA ƘANNAN MIJINA* TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°11&12* Ganin haka yasa Mama hankalinta tashi, dan tasan ba ƙaramin aikinsa ba ne yan zun nan ya musu lahani. Ubaidullah dake riƙe da kafaɗun Mama jin abun da dayan saurayin nan ke fadi ya saka shi sakin Mama ya juya a fusace cike da zafin nama, cikin hanzari Mama ta riƙosa gam kafin ta ce. "Kul Ubaidullah ban yarda ba ban amince ba karka taba daya daga cikinsu ka kyalesu muje, mu shirya, mu wuce asibiti a duba yaran sannan a basu ƙannan su, dan ni gaskiya banji dadin haɗawa da yaran mutane da kayi ba, danni ban son damuwa da hayaniya ko tashin hankali basu da dadi." Mama ,tana ta mita riƙe da hannun Ubaidullah wanda gabakid'aya jijiyoyin jikinsa sun fito raɗa-raɗa, tsantsan bacin rai, domin maganar saurayin yayi mugun bata mishi rai har gadara yake yi cewa shi dan sara suka ne kuma har yake fada masa ko dan bai san shi waye ba ne"? ya tambayi kansa. Da kyar Mama ta janye Ubaidullah ,suka shige cikin gida. Mama ta zaunar dashi ganin yanda jijiyoyin jikinsa ya fito ya bayyana, idanunsa suka sake ƙanƙancewa ,suka yi jajur dasu. Mama ta buɗe baki ta kwalawa Hafiza kira. Da sauri Hafiza ta fito ta ce. "Mama gani" "Je ki kawo min ruwa mai sanyi" Hafiza ta amsa da "to" sannan ta juya da sauri,ta dawo dauke da ruwa a glass cup ta miƙawa Mama. Karba Mama tayi sai da ta gurb'a tukunna ta miƙawa Captain Ubaidullah, amma sam ya ƙi karba balle yasha, dan har izuwa yanzu jikinsa kyarma yake yi burinsa bai wuce ya ladabtar da y'an iskan samarin bakaro ba, masu ikirarin su yan sara suka ne. Mama ganin fa tabbas Ubaidunta ransa ya baci ne ,ta sake kurban ruwan a bakinta, tukunna ta kamo kansa ta danna cup din ruwan bakinsa, da kyar ya iya karfin hali buɗe bakinsa, ya kurbi ruwan sannan ya sauke a jiyar zuciya mai karfin gaske, bakinsa yana fitar da tururi tare da hayaki. Mamaki ne ya kama Mama sosai a zuciyarta ta ce. "Tabdijam ni Salamatu gani ga ɗa, saboda bacin rai bakinsa harda hayaki? lallai kam da ake cewa soja marmari daga nesa." Da kyar Ubaidullah ya dawo hayyacinsa,ya ɗan sassaita natsuwarsa, ya miƙe tsaye ya ce. "Mama ki shirya mu tafi hospital din" Mama ta ce. "Dama wani hospital ka kai su?" "Rimi hospital, naga yafi kusa that's why" Mama ta ce. "Ok to, ka shirya kayi sauri kaji?" Ɗaga kai yayi, ya fice. Mama ta bi bayansa da kallo, a fili ta ce. "Ubaidu Allah ya kawo zuciyarka sassauci dama tun da ya kake balle yanzu da ake ɗirka maka alluran sojoji ai sai ta Allah. Mama ta ce. "Hafiza ki shirya yanzu kafin ya gama, nima kaya kawai zan canza dan nayi wanka tun dazu,dan hankalina yana kan yaran mutane wallahi" Hafiza ta ce. "Mama nima fa nayi wanka tun tuni" "To ki saka hijab dinki dan nasan ba jimawa zanyi ba zai fito" Mama ta fada tana shigewa dakinta. Hafiza ma ɗaki ta shiga ta saka hijab dinta, ta dawo parlour ta zauna, bata jima da zama sosai ba, Mama ita ma ta fito. Bayan zaman Mama kamar da minti biyar haka, sai ga Ubaidullah ya shigo parlour'n bakinsa dauke da sallama. Amsawa Mama da Hafiza suka yi. Mama ta ɗago ido tana kallon ɗan nata, sanye yake da wandon jeans and brown t-shart, mai ratsin tambarin sojoji a jiki, yayi matuƙar kyau amma fuskar nan jiya iyau. A hankali ya buɗe bakinsa, cikin sanyin murya kamar ba shi ba ya ce. "Mama muje" Tashi Mama tayi sai da ya ga tayi gaba tukunna ya bita a baya kafin Hafiza ita ma ta dauki basket din abinci ta bi bayansa ita ma. Har yanzu samarin su na tsaye a gate, Ubaidullah yana musu kallo daya,ya saki dariyar mugunta wanda shi ka ɗai ya barwa kansa sanin manufar dariyarsa. Ya buɗe mota zai shiga kenan sai ga Zaidu, wani farinciki ya sake mamaye Ubaidullah wanda shi kadai yasan hakan. Mama tana ganin Zaidu ta faɗaɗa murmushin fuskarta, da sauri Zaidu ya ƙaraso ya duƙa a gaban Mama yana kwasar gaisuwa, cike da fara'a da sakin fuska tare da kulawa Mama ta amsa, gami da cewa. "yasu Umma dasu Inna fatan kowa lafiya ko?" Zaidu ya sosa ƙeya yana russuna kai ƙasa dan shi kunyar Mama yake ji. "Kowa lafiya kalau yake,Umma ma ta ce na gaisheki sosai" "Ayya Allah sarki ina amsawa" Zaidu ya miƙe yana kallon abokin nasa, sannan ya juya yana kallon samarin da suke tsaye cike da neman tada zaune tsaye. Zaidu ya buɗe baki zai yi magana Hafiza ta gaishesa ya amsa yana cewa. "Lafiya kalau my dear sister Hafiza, where is my lovely sister Na'ila?. kafin Hafiza ta basa amsa ya juya ga Ubaidullah ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce. "My man wasu guys ne wa innan haka a bakin gate kuma ina zaku je?" ya tambaya yana kallon Mama da Ubaidullah tare da wa'innan samarin da yan matan. Mama ta ce. "Humm yanzu dai ba lokaci Zaidu muje asibiti." Zaidu ya waro ido waje ya riƙe baki yana cewa. "asibiti dai waye ba lafiya?" Mama tace . "Ƙanwarka Na'ila" Zaidu, zai kuma yin wata maganar Ubaidullah ya buga tsaki gami da cewa. "Oh my god dalla! malam ka wuce mu tafi kai ba ɗan jarida ba, but sai shegen uban questions din tsiya, idan muka je ai zaka ga abun da ya faru da idanunka. Mama ta riƙe baki tana kallon Ubaidu. Zaidu ya sa dariya ya ce. "Wallahi Ubaidu zaka ji dashi" Zaidu ya juya Ubaidu ya ce. "Zaidu pls dauki Mama da Hafiza da wa'incan ladies din, ni kuma zan ɗauki guys din nan ne." Zaidu ya ce. "Okay Mama and my sister let's go." Har zasu shiga mota Ubaidullah ya kira Hafiza tadawo jikinta na b'ari dan wani bala'in tsoron Yayan nasu take yi yanzu, dan gabaki'ɗaya ya sake burkice musu. Hannunta ya kamo ya mata raɗa a kunne, ɗaga kai kawai tayi sannan ta juya da gudu tayi cikin gida. Duk akan idon Mama, tana so ta fahimci wani abu amma ta kasa, dan haka ta saka zuciyarta salama, ta danganta hakan da yayi mantuwa ne, ya aiketa. Hafiza ko cikakkiyar minti biyu bata yi ba, ta fito ta miƙa masa abu ya karba ya shige mota, sai da Zaidu ya tada motar suka fita sannan Ubaidullah ya juyo da motarsa yana kallon gefe, ba tare da yayi magana ba. Daya daga cikin samarin yayi tsaki sannan ya shige gaban mota, sauran biyun kuma suka shiga bayan mota. Tun daga gate Captain Ubaidullah da yawani fizgi motar sai ka rantse da Allah duniyar taurari zasu. Wanda hakan yayi sanadiyyar faɗuwar gaban wa'innan samari, Ubaidullah da gayya yayi hakan ,dan sai ya ci ubansu hankalinsa zai kwanta, dan bai dauki raini a barracks ba ma, balle kuma ba a barracks ba. Cikin kaɗuwa na gaban ya kamo sitbelt zai ɗaura, saboda wani uban gudun da Ubaidullah yake sharan titi dashi yana tada ƙura. Har ya sa hannu zai jone Ubaidullah ya janyo yar ƙaramar wuƙa a gefen takalminsa wanda ake musu ikirari da boost ya datse sitbelt din. Sannan yayi wata smiling na gefen baki wanda zaka iya yi masa inkiya da mugutar soja. A madadin Ubaidullah yayi Rimi Hospital, amma sai ya juya kan mota ya ɗauki hanyar filin unguwar rafin zurfi. Da ɗan nisa a tsakani ,amma kasancewar gudun da yake bana wasa bane kamar giftawar ido da bismillah, sai gasu a filin rafin zurfi. Sosai Ubaidullah ke juya mota, yana shatale'tale, dasu. Ba ƙaramin jijjiga suka yi ba. Kafin Ubaidu ya tsaida motar ya fito yana huci. A hasale ya ce. "Duk ku fito." A galabaisa suka fito su na sauke wahalalliyar numfashi tare da ajiyar zuciya da kyar. Ruwa Ubaidu ya ɗauko ya basu, da sauri suka karba, ko wannen su sai da yasha 2bottle. Sannan Ubaidullah ya ɗane bayan motarsa ya zauna yana kaɗa kafarsa ɗaya. Murya a sheƙe ya ce. "Ku maimaita abun da ku ka ce dazu, ina so na tabbatar da cewa eh tabbas maza ne a gaba na idan kuma ba haka ba to ina muku albishir da cewa dole ku shafawa bakin ku wannan lipstick din, wasa za a buga tsakanin haziƙi gawurtaccen soja, da haziƙan tantiran y'an sara suka." Ya fada yana jujjuyawa jan bakin da ya aike Hafiza ta ɗauko masa, a hannunsa ya wulla sama sannan ya cafke. Tsoro ne ya gama mamaye zukatan maza uku, su har ga Allah basu yi tunanin soja ba ne. Gashi yanzu sun taro wa kansu jafa'i. Kallon-kallo suka hau yiwa juna options daya ne garesu shine su basa hakuri. Ai kuwa nan suka shiga koro ruwan hakuri. Ubaidullah ya ce. "Haba maza ya ku ka yi saurin yin sanyi haka tun ba a kafta wasan ba?" "Dan Allah yallabai kayi hakuri wallahi bamu san kai soja ba ne." Ubaidu ya numfasa kafin ya fara magana "Haƙiƙa na ɗaki ƙannan ku wanda a halin yanzu su na gadon asibiti tare da ƙanwata wanda ina mutuwar sonsu da kaunarsu, amma ni bana sake da ƙanne na saboda sha'anin rayuwa, ace yara ko shekara sha biyar basu kai ba amma wai sun tafi walima tun rana har karfe taran dare!" ya fada a tsawance zuciyarsa na sake yi masa zafi. "To ni bana daukar nonsense any moment and bana careless akan watsewar tarbiyyan ƙanne na, ba ma iyakar su ka ɗai ba ,dukkan mace, yarinya, babba , budurwa, ni haka tsarina yake ni Ubaidullah!" Ya karasa maganar cike da izza da jin ƙai. Sai da ya shiga mota sannan ya ce. "Sa'arku daya tak baku gwadamin iskancin samarin bakaro ba, dan wallahi da kun min taurin kai kun kawo min raini da ko wani ƙaramin dan iska ya kwashi kashinsa a tafin hannunsa, idan ku na da ra'ayi ku shiga mota mu tafi ko wallahi nayi tafiyata." Ai tun bai karasa ba suka miƙe har su na rige-rige, da sun ga alama idan har zasu yi faɗa da Ubaidullah babu abin da zasu ɗauka a jikinsa. ~~~~~~~~~ Ta bangaren su Zaidu kuwa sun isa asibiti sun samu jikinsu Na'ila da sauki, har ma likita yana maganar sallamarsu. Zaidu ya ce. "Bari Ubaidullah ya zo" Hafiza da gudu ta rungumi yar uwarta, suka saka kuka a tare. Zaidu ya ce. "Wai meya faru ne kam?" Mama ta ce. "kai dai bari kawai Zaidu kanwarka bata jin magana, idan munje gida sai ta fada maka da bakinta" Zaidu yayi murmushi ba tare da yayi magana ba Suka zauna jiran Ubaidullah yau ne gobe ne shuru. Mama ta ce. "Zaidu kawai kayi abun da ya kamata mu tafi gida wannan Abokin naka sai kai ." Zaidu yana dariya yaje sa hannu aka basu sallama sai gida . ~~~~~~~~~ COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻👮🏻‍♀ [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°15&16* Basu zarce ko ina ba sai gidan Anty Ummu, sallama suka yi, Anty Ummu ta fito da sauri daga kitchen sakamakon jin murya ɗan uwa gudan jiki. Tana ganinsa kuwa annurin fuskarta ta ƙaru, shi ma Ubaidullah dariya yake yi wanda har ya bayyana hakwaransa. Hannu Anty Ummu ta miƙa masa cike da murna, tana cewa. "Ɗan uwa kai ne ko kuma dai idona ne yake min gizo?" Cike da zolaya Zaidu ya ce. "Anty Ummu abu daya zai sa ki tantance ko shi ne, ko ba shi ba ne, bari na miƙo miki wancan tabaryar, ki shemesa da ita daga nan za ki gane gaskiyar tambayarki." Anty Ummu ta kwashe da dariya, ta ce. "Daga haka ma na tabbatar ƙanne na ne a gabana ku shigo daga ciki." Su na shiga Anty Ummu ta cike musu gabansu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,sai nan nan take yi dasu. Sai da ta tabbatar basu buƙatar wani abu tukunna tazo ta zauna kusa da kaninta suka gaisheta ta amsa,su na hira su na dariya. Anty Ummu ta ce. "Amma dai ina fatan bana zaku kwana biyu kafin ku koma ko?" Zaidu ya ce. "Ina kuwa jimawa Anty babba, wallahi 5days General Of Army ya bamu dan kwanan nan zamu tafi bakin bordern nijar domin kamo wasu y'an ta'adda." "Oh Allah ni Ummu kenan yanzu shikenan ku haka rayuwarku zata ƙara a fagen da ga?" Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki yayi magana. "To big sister ya zamu yi ai ya zama dole tun da munyi alƙawari tare da rantsuwar gare kasarmu ta gado wato nigeria, gashi mune jami'ai wanda aka fi ji dasu bana gaya miki a waya an yi mana ƙarin girma ba, to ai yanzu kam bamu ga wani hutu ko zama waje daya ba, kawai ku dinga tayamu da addua." Anty Ummu ta numfasa ta shaƙi iska, sai ga hawaye yana zuba daga idonta wanda yayi sanadiyyar hankalin Ubaidullah tashi nan ya shiga jero mata tambayoyi ba ƙaƙƙautawa. Girgiza kai Anty Ummu tayi ta ce. "Ba komai dan uwa ka kwantar da hankalinka,Allah ya taimake ku Allah yasa ku gama da duniya lafiya,Allah ya ƙare ku da ga sharrin masu sharri." Sosai Anty Ummu take ta zuba musu adduoi su na amsawa da amin. Daga baya kuma suka hau hiran yaushe gamo har yaran Anty Ummu su biyu suka dawo suka samu kawun su, suka hau murna su na cewa. "Oyoyo kawu" Ubaidullah ya na dariya sai kace ba shi bane mai cin magani a barracks, amma in dai a cikin familynsa ne yana dariya har haƙorinsa ya bayyana , sai dai idan y'an halin ne suka tashi,dan a kwaisa da miskilancin magana wasu lokutan, ga zafin rai, wa in da basu san shi ba kuma suke cewa yana da girman kai. Kallon yaran Anty Ummu yayi yana dariya ,Haidar da Sakina, ya ce. "Yarana ya kuke? fatan lafiya kalau kuke ko?" Suka amsa da eh, nan ya dan taba wasa da yaran kafin Anty Ummu ta korasu gidan kakarsu ta wajen uba. Bayan sun fita Anty Ummu ta ce. "Wai ni yaushe ne kam za a kawo min surka? gaskiya ina so naga matan ƙannena." Zaidu ya kwashe da dariya ya ce. "To Ubaidullah gareka fa ,big Anty tana son ganin in'law " Hararan wasa Anty Ummu ta yiwa Zaidu kafin ta ce. "Ai ba da shi kadai nake yi ba har da kai, ko sai na ba da sadakar ku ne?" Zaidu ya zare ido ya ce. "Big Anty ai wallahi my man yafi karfin sadaka dan baki ga yanda ladies a barracks suke haukan sonsa bane abun har tsoro yake bani wallahi." Anty Ummu tana dariya tana kallon ƙaninta lokaci guda ya haɗe rai da fuska sai ka ce ba shi bane mai dariya yanzu-yanzun nan. Zaidu ya ce. "Ka ga Malam Ubaidu duk wannan haɗe ran naka bai taso ba, kai soja ne nima kuma soja ne, kawai fina kayi da zafin rai miye to ma na hade rai din danna faɗawa Big Anty gaskiya?" "Mtswwww Zaid ka fa kiyayeni, kasan fa halina, Allah na tuba in ban da tsautsayi mai zanyi da y'an matan barracks? duk babu wacce take gabana, kai ne dai kake sha'awar aure yanzu, amma ni Captain Ubaidullah ba yanzu ba, dan har kwanan gobe ban ga yarinyar da tamin ba wanda zan buɗe bakina na ce ina sonta ba" Riƙe baki Anty Ummu tayi tana kallon ƙanin nata cike da mamaki da al'ajabi, shi fa haka yake, idan ya rikiɗe sai ka kasa gane kansa, dan wani lokacin ma yafi hawainiya. "To yanzu kai Dan Uwa idan baka yi aure yanzu ba sai yaushe zaka yi? karka manta fa kai Jarumin Soja ne, kuma Sojoji sai da mata a kusa"cewar Anty Ummu. Zaidu ya ce. "Kyalesa kawai big Anty, shi ma fa yana so kawai basarwa yake yi yana nunawa kamar baya so, kuma wallahi ranar da muka je gidan General naga y'arsa tana satan kallonsa duk yanda aka yi itama ta ƙyasa ne" ya ƙarasa managar yana dariya. Iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya gama tunzura, sai huci yake fitarwa yana hararan Zaidu. Dariya Zaidu ya kwashe da shi kafin ya ce. "Ai dama nikam sai dai na ƙare a harara amma babu abin da za a min aha" Anty Ummu abun dariya ya bata ta ce. "To shikenan naji ƙanina baya son aure yanzu, amma kai Zaid naji ya ce kana so dan haka wacece surkar tawa, tun da yallabai ya ce ba yanzu ba ina jira faɗamin ita yanzu?" Sun kuyar da kai ƙasa Zaidu yayi yana sosa ƙeya ba tare da yayi magana ba. "To ban gane ba na tambayeka ka hau sun kuyar da kai me hakan ke nufi?" Anty Ummu ta tambayi Zaidu cike da rashin fahimta. Ubaidullah ya ce. "Amma dai ba shirmen da ka fada min dazu bane kake wannan gulman sun kuyar da kan wa big Anty ba?" Kallonsu Anty Ummu tayi ta ce. "Kai ban fahimta ba me kuke nufi,kun sakani a duhu fa wace magana ce?" ta juya ga Ubaidullah. Ubaidullah ya ce. "Nifa wallahi har na manta ashe shi bai manta ba, kinsan jiya da nazo na yiwa su Na'ila duka har sai da na kaisu hospital" Cikin firgici Anty Ummu ta ce. "Me kuma su Na'ila suka yi da ka dakesu ,kuma har da Hafiza, ita da bata da hayaniya?" "A'a Big Anty ba fa Hafiza ba ce, Na'ila dai da kawayenta,wallahi Big Anty bansan me yake damun Na'ila da yawo ba wai jiya sun je walima tun rana amma yaran nan basu dawo ba sai 9 ni kuma raina ya b'aci nayi musu duka ita da kawayen nata sannan na kaisu asibiti"nan ya dinga bawa Anty Ummu labari. Anty Ummu ta ce. "Na'ila kam ai sai dai Addua Allah ya shirya mana ita, amma Na'ila kam bata ji, to miye kuma Zaidu yake sun kuyar da kai din?" Ubaidullah ya ce . "Wai cewa yayi yana son Na'ila zai jirata nan da shekara biyar ya aureta" Anty Ummu ta hau dariya tana kallon Zaidu. Ubaidullah ya kuma cewa. "Ina ma laifi ya ce Hafiza ita ma din tayi masa yarinya yanda yake b'ab'atun auren nan kam" Sosai Zaidu yaji haushi yana hararar amininsa ganin yana so yaja ra'ayin Anty Ummu ita ma ta mai da maganar wasa yasa Zaidu tasowa yazo kusa da Anty Ummu fuskarsa babu alamun wasa, ya ce. "My Big Anty plss karki biyewa Ubaidu ba zai gane bane amma Antyna ki yarda dani wallahi da gaske nake ina son Na'ila, kuma ko yanzu aka bani ita zan riketa ba tare da nayi mata komai ba har ta kai shekara sha shidda, zan ci gaba da kula da ita na raineta,amma bazan so na rabasu da ƴar uwarta ba saboda akwai shaƙuwa mai karfi a tsakaninsu, Anty karku duba cewa Na'ila tayi ƙanƙanta nima ai yaro ne, a wani kauyen ma wallahi Antyna karki yi mamaki kiga yarinya sa'ar Na'ila tana da yaronta a hannu, pls Antyna ki shige mun gaba ki bani kwarin gwiwa, am serious wallahi" ya ƙarasa cike da fuskar tausayi. Sosai Anty Ummu ta natsu tana sauraron maganar Zaidu kafin ta numfasa ta ce. "Karka damu ƙanina in dai har da gasken gaske kake yi, ni kuma nayi maka Alƙawari Na'ila matar ka ce" Zaro ido Ubaidullah yayi kafin ya kalli Anty Ummu ya ce. " What! Big Anty matarsa fa kika ce? ina wallahi Na'ila ba zata iya da kai ba, ka nemi wata mata" ya faɗa cike da sigar jin baki. Anty Ummu tana dariya ta tashi tana cewa. "ku kam halinku sai ku ,ba a iya muku ,yanzu dai idan naje gida zan faɗawa Mama ɗanta yana son ƴarta" Sake sosa kai Zaidu yayi ya ce. "Pls Antyna ki bari sai mun koma tukunna" Dariya Anty Ummu tayi ta ce. "Naƙi na bari ai gwanda Mama ta sani tun yanzu, kai kuma Dan Uwa zan ga ranar da zaka zo kace min ga zab'inka ina nan ina jira." Tabe baki Ubaidullah yayi ba tare da yayi magana ba, haka suka ci gaba da hira cike da nishaɗi, sai da akayi sallarh la'asar kafin suka yiwa Anty Ummu sallama suka nufi gidan su Zaidu. ~~~~~~~~ Da sallama suka shiga Inna ce kawai a tsakar gida tana ta faman sababi. "Haba ace ayi yara basu jin magana kwata-kwata sai kace ƴaƴan jinnu to wallahi nikam ƙaniyarku zanci ƴan buhun uba, yara sai rainin tsiya wallahi mai sunan ifrituwa zaki dawo ki sameni ne ha." Zaidu ya ce. "Oh Allah matar wa ya tabamin ke ne kam haka kike ta faman mita?" "Kai dai bari kawai soja mugun mutum ni da ƙannanka mana masu kai kamar giginya, ai yau babu abin da zai hanani ban b'allawa yarinyar nan kafa ba mai sunan jinnu ifrituwa" Zaidu ya ce. "Yanzu dan Allah Inna ba zaki dai na kiranta da sunan ifritu ba, ba fa haka sunanta yake ba, sunanta (Afnan) ne" "Mtswww dalla tafi can ka bani waje yara gaku nan duk suna babu tsari ba kan gado balle kan kujera, yanzu miye wani suna wai afirina?" Dafe kai Zaidu yayi sannan ya ce. "Ni dai Inna baza ki saka min ciwon kai ba, my man muje ciki" "Au ka ce min tare kuke kai da aminin naka mai fuska kullum babu rahma,wallahi na tabbata idan na rantse bazan kaffara ba, wannan a alluran da ake yi muku shi nashi na musamman ne,dan ana yi masa ƙari da na rashin dariya, haba mutum kullum sai kace ana masa bishara da mutuwa?" Girgiza kai Ubaidullah yayi sannan ya gaisheta ya wuce yayi gaba Zaidu ya bisa a baya nan Inna ta sake tasa wata sabuwar mita tare da zage-zage. "Zaku ji dashi wato ina magana shine ku ka yi gaba, ku ka barni ina magana ni ka daina wato na ɗaɗe ban yi ba ko, da abokin kan nan da idonsa ƙifi-ƙifi kamar ta soyu gyada." Su dai basu kulata ba parlour suka wuce suka gaida Umma ta amsa tana cewa. "Me yasa kuke son tab'o Inna ne kam? Kuma nasan kai ne Zaid,dan baka jin dadi in dai baka tsokani Inna ba, to wallahi ku kiyayeni yanzu suka gama dasu afnan kafin su fita" Zaidu ya ce. "Wallahi Umma nikam ban tsokaneta ba ai kinsan halin Inna" Umma ta ce. "To naji bar maganar haka kafin tazo ta sake fata-fata damu baki ɗaya" Tashi suka yi, Umma ta ce. "Ku huta kafin na gama abinci," Suka ce a'a sunci abinci a wajan Mama da kuma gidan Anty Ummu. Umma ta ce . "To yayi kyau ai haka ake so sun taimaka muku gauraye" Su na dariya suka wuce gaba. Sai yamma lilis gafen magriba kafin suka fita yawon zaga gari, basu koma gida ba sai bayan sallarh isha'i wajan tara zuwa goma, kowa gidan su ya wuce. ~~~~~~~~~ Da washe gari ma haka suka dinga zagaye gari, Ubaidullah har gidan dangin Baba yaje ya musu alƙairi wanda ya saka su jin kunya suka dinga kame-kame, amma yayi kamar bai san suna yiba. Yau kwanarsu hudu sun fara shirin komawa Abuja bakin aikinsu, kafin nan kuma, Anty Ummu ta fadawa Mama yadda suka yi da Zaidu dariya Mama tayi ta ce, Allah ya zab'a abin da yafi alƙairi aka bar maganar a haka. A kwanaki hudun da Ubaidullah yayi sam baya shga hidiman ƙannansa , wanda hakan ya saka su damuwa, Hafiza ce ta kawo shawara su masa girki da kansu sannan suje su basa hakuri karya tafi yana fushi dasu, hakan kuwa aka yi. Suka shiga kitchen, Mama take tambayarsu, me zasu yi, suka ce zasu yiwa Yayan su girki ne, Mama ta ce. " to Allah ya taimaka ta fita ta barsu" Da misalin goma na safe, Ubaidullah yana tsaya a dress mirror yana shiryawa, waya ne a kunnensa, su na waya da K,B. Sallama suka yi a hankali, jikinsu na kyarma saboda tsoro. Amsa sallamar tasu yayi kafin ya ci gaba da wayarsa da K,B yana tabbatar masa akan cewa zasu dawo gobe, kafin suka yi sallama ya a jiye wayar ba tare da ya kallesu ba. Na'ila ce tayi karfin halin cewa. "Yaya mun shirya maka breakfast" "Get out!! ya faɗa a tsawance, ba ƙaramin tsorata suka yi ba, a madadin su fitan kamar yanda ya bukata sai kawai suka ruga da gudu suka rungumesa sannan suka saki kuka a tare. Nan take jikin Ubaidullah yayi sanyi dan yana da raunin zuciya wajan tausayi, ɗaure zuciyarsa yayi,daƙile ya kuma cewa. "Ku sake ni!" Amma sun ki sai kukan su dake ƙaruwa cikin ,Kuka Na'ila ta hau magana. "Pls 4give me Yaya I promise u bazan sake ba, pls Yaya karka tafi kana fushi dani bazan sake ba na tuba pls Yaya trust me Yaya" ta ci gaba da kuka. Ita ma Hafiza hakurin ta hau basa cikin sanyin muryarta. "Yaya kayi hakuri mun san kana yine saboda son da kake mana but pls Yaya ka daina fushi damu" Na'ila ta kuma cewa. "Yaya idan ma duka ne na yarda ka sake min in dai zaka huce ka daina fushi, kwata-kwata wannan zuwan kan Yaya baka kulamu ba, Yaya nasan nice na jawo saboda bana jin magana, Yaya ka dakeni ka huce amma ka daina fushi kayi hakuri" ta faɗa ta hau wanke fuskarta da mari. Da sauri Ubaidullah ya rike hannunta,sannan ya rungumesu idonsa har sun kaɗa sunyi ja. A hankali ya ce. "Is ok, but karki sake, muje na ga abincin da my flowers sister's dina suka min" ya fada yana smiling. Sosai suka ji dadi. Har parlour suka jera yana riƙe da hannun su, Mama tana ganinsu ta girgiza kai ba tare da ta kulasu ba. Nan ya zauna ya fara ci su na hira kamar ba shi ba,yana santin abinci ya ce. "Yanzu ku, ku ka girki wannan abinci mai dadi haka?" Su na dariya cike da jin dadi suka amsa da eh, dan ba karamin dadi suka ji ba ganin Yayansu ya hakura. Ko da ya gama cin abinci ya kwashesu suka yiwa Mama magana sun fita Mama ta ce, a dawo lafiya. Gidan Anty Ummu yaje ya dauki Haidar da Sakina, sannan yaje gidan su Zaidu ya dauki Afnan da Manal da Nawaz (ƙannen Zaidu) yawo suka fita ya musu siyayya sannan suka koma gidan Anty Ummu, sai dare suka koma gida. Da daddare suka gama shirin su dan gobe da safe zasu koma Abuja dan har General Of The Army yayi kira a waya. ~~~~~~~ Ina mai baku hakuri, kuma ku kara hakuri na rashin samun posting akan tym Zazzabi ne ta sakoni gaba wallahi COMMENTS & SHARE BY MRS IS OK MOMYN AHLAN✍🏻 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________ Kawata @⁨Nana Aisha⁩ Tawan @⁨Maman Twins⁩ My luv @⁨Khadija Jounalist⁩ Inayinku over Allah yabar ƙauna. Dole na fara sa koku masoyan asali, Doter @⁨Surayyah Dan Ango⁩ Antyn Ahlan @⁨6 Naphersarh⁩ Habibty @⁨احلم فطمة⁩ @⁨Samira Bint Abdallah🌹🌺⁩ @⁨Maryam Mrs M Lawal⁩ Doter @⁨Doter Fareesat⁩ Dear @⁨Fatima Bintu Sagir⁩ @⁨👩‍⚕Dr,Herpsert👩‍⚕⁩ @⁨Mrs M,j (Fans)⁩ @⁨Mrs Faruq💃⁩ @⁨MAMAN ZAHRA⁩ @⁨Mummy jidda⁩ @⁨Maman Basma⁩ @⁨Aisha Ibrahim Ummi😊⁩ @⁨Firdausi Hussain Namad💝🔐⁩ _~IYAKAR WA INDA NA GANI KENAN~_ *WANNAN PAGE DIN TAKU CE MY PPLS*❣ *_~KO BA WUYA ANA TSABTAR TARE~_*💔 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°17&18* Washe gari da safe suka shirya tsaf cikin kakin su na sojoji, sosai suka yi ɗamara, yayinda kakin ya karb'esu, barin ma Ubaidullah yayi masa kyau sai kace a jikinsa aka halicci kakin. Fitowa suka yi a tare da Mama, da Anty Ummu, Hafiza,Na'ila. Ubaidullah yana tsakiyar su, Mama da Anty Ummu su na ta kwararo masa addua, sai amsawa yake yi da amin, yana so ya mai dasu barracks amma Mama ba zata yarda ta koma Abuja ba, duk ma ba wannan ba,da kunya ya ɗauki Mama ya kaita barracks saboda kajinan da suke bibiyar rayuwarsa ,ko wacce take kawo masa hari. Su na isowa bakin mota Zaidu ya fito ya duƙa ya gaishe da Mama ta amsa, sannan ya gaishe da Anty Ummu ta amsa tana dariya, su Hafiza da Na'ila suka gaishesa ya amsa, Anty Ummu ta ce. "To surkina dan Allah a kula sosai, Allah ya kaiku lafiya Allah yabaku sa'a a tafiyar da zaku yi, Allah ya ɗaura ku akan maƙiya tare da mahassada" "Amin ya Rabbi Allah, Big Anty mun gode da wannan adduar taki Allah ya saka da Alkairi" Anty Ummu tayi murmushi ta ce. "Ba komai ƙannena a kula dai da kyau dan Allah" Zaidu ya ce. "In sha Allah Big Anty zamu kula" Kallon su Mama tayi a lokacin da suka iso gaban mota ta ce. "Duk abun da ya kamata ace Uwa tana gayawa ɗanta a lokacin da zai fita neman halak dinsa Ubaidullahi ban rage ko guda daga ciki ba, na faɗa maka yanzu ma kuma zan ƙara nanata maka wasu daga cikin kalaman masu hatsirin gaske, Ubaidullah Zaidullah?" Mama ta kira sunan su a tare, suka amsa kansu duƙe su na kallon ƙasa. "Zan ƙara yi muku tuni akan cewa ku gujewa haram, karku yi tunani da cewa ai kadan ce sam Allah ba ruwansa da wannan ,kuna samun rufin asirinku dai-dai gwargwado, na tabbata da ace baku riƙe gaskiya ba, da ba zaku taka matsayin da kuke dashi a yanzu ba, dan haka ku guji abun haram karku fito a cikin hadisin Manzon Allah sallallahu alayhi wa'sallam da yake cewa ( لايدخل اجانةجسدغذي بااحارام) Wato dukkan gangar jikin da aka ginasa da haramun bazai shiga Aljanna ba, amma abun da zai baku mamaki a wannan zamanin da muke ciki bamu dauki haram a bakin komai ba,mun maida haram abincin mu, ruwan shan mu, gadon baccin mu, wajan zaman mu,komai namu, gabaki daya shagalar tai mana yawa, mun bar koyarwar Allah da Manzon S,A,W, mun bar hadisai mun bi ruɗin duniya da son zuciya da kyale-kyalen banza, wanda zata kai mu ga halaka, jin dadi duniya ƙadan ne wato (ADDUNYA MATA'UN ƘALILAN) dan haka Ubaidullah Zaidullah kuji tsoron Allah a duk in da ku ka kasance, karku biyewa neman mata kamar yadda aka yiwa sojoji ittifaƙin neman matan banza, ku ɗauke idanun ku ,ku yiwa idonku hijabi wajan kallon haram, abin da nake nufi shine abun da bai zama halaliyarku ba, idan kuma aure ne ga mata a gari da yaran yan uwa da abokan arziƙi, sai ku duba a ciki mu sha biki, maganganun basu kare ba, amma karna saka ku makara kuje Allah ya kaiku lafiya Allah yaba da sa'a Allah ya ƙare ku, gabanku da bayanku dama da hagunku, Allah yasa kuje aikin da aka tura ku lafiya ku dawo lafiya tare da manyan nasarori, Allah ya muku Albarka gaba'ɗayan ku" Sosai jikinsu ya sake yin sanyi duk da sun saba da nasihan iyayen nasu, amsawa su Ubaidullah suka yi da amin, sannan suka ƙara da cewa. "In sha Allah zamu kiyaye Mama, mun gade Allah ya ƙara girma da nisan kwana" Mama ta amsa da amin tana murmushin karfin hali dan hawaye ne ya cika tam a idonta, juyawa tayi zata koma cikin gida, ta ji muryan Ubaidullah, "MAMA" ya kira sunanta, tsak Mama ta tsaye amma bata juyo ba. Takowa Ubaidullah yayi yazo gabanta sannan ya rungumeta idonsa yayi ja sosai,baya so ya kashe mata jiki gashi dama tana fama da hawan jini so yake ya ce mata, ta yafesa idan har yayi mata wani laifi amma yaga alamunta ma hawaye take son yi dan haka ya canza akalar maganar ta hanyar cewa. "I gonna miss Mama" Nan ma murmushi tayi ta shafo fuskarsa, "miss u more son Allah ya maka albarka kuje yanzu kam, karku makara uhum?" Ɗaga kai Ubaidullah yayi, sannan ya saki Mama ya juya ya koma wajan su Anty Ummu da suke tsaye, Anty Ummu tana yiwa Zaidu tsiya , sai dariya yake yi yana sun kuyar da kai ƙasa yana satar kallon Na'ila, wacce suka takure waja daya ita da yar uwarta wanda da kaga alamun su kasan ƙiris suke jira su saka kuka, dama sun saba duk zuwan Yayan nasu idan zai koma sai sun masa kuka tun da yana shafe watanni kafin yazo idan kuma yazo baya wani jimawa zai koma ,idan har ya jima shine yayi 1week ya koma. Kallon su Ubaidullah yayi sannan ya bude bakinsa ya hankalin ya kira sunan su. "My flowers" sannan ya bude musu hannayensa da gudu suka rungumesa suka sa kuka, ita ma Anty Ummu bata san lokacin da hawaye ya wanke mata fuska ba, hawaye ta hau yi, Ubaidullah ya sake su Hafiza ya juya yana kallon Anty Ummu girgiza mata kai yayi alamun tayi shuru, sannan yasa hannu ya goge mata hawayen,da sauri ya shige mota Zaidu ma ya shiga yaja su Anty Ummu dasu Hafiza su na ɗaga musu hannu , mai gadi ya bude musu gate suka bar gidan suka ɗauki hanyar birnin tarayya Abuja. ~~~~~~~~~ Sallah ce kaɗai ya tsaida su Ubaidullah a hanya. Sai karfe 4:30pm su Ubaidullah motar su tayi parking a *9JA BARRACKS ABUJA*. da K,B suka fara haduwa nan Zaidu ya fito da sauri suka rungumi juna,amma kafin Ubaidullah ya fito sai da ya gama shan kamshinsa tukunna har K,B yana cewa. "wai ina guy din nan yake ne,ko bai dawo bane shi?" Murmushi Zaidu yayi sannan ya ce. "Amma dai inaji K,B ka manta da waye Ubaidullah ko? shiyasa bai fito a mota ba kake tambaya idan bai shaƙi kamshi ba kafin ya fito taya za a gane cewa Captain Ubaidullah Abdullahi ya dawo?" Suka sa dariya su na tafawa, dai dai nan Ubaidullah ya zuro kafafunsa ƙasa ,fuskar nan tamau ba annuri, K,B yazo suka rungumi juna Ubaidullah yayi wani miskilin murmushi sannan suka jera har part dinsu. Bathroom Ubaidullah ya wuce direct domin yayi fresh up bcox a gajiye yake, ya kwashi kusan 30mnts kafin ya fito daure da towel a kugunsa, juyawa yayi ya kalli Zaidu wanda ya baje a bisa katifa ya ce. "Hey guy oya get'up kaje kayi fresh up ka samu relief, dan ni yanzu ji nake babu wanda ya fini jin dadi da nayi wanka." Dariya K,B yayi ya ce. "To nifa na kasa ganewa, Abokina ai na ɗauka zaka dawo da mata amma kuma sai na ganka daga kai sai jakarka, ya haka to?" "Mtssww hummm don't wast u tym , ashe duk karyan banza ce da yake cewa zai yi aure yanzu" Cike da rashin fahimta K,B yake bin su da kallo daga Ubaidun har Zaidu. "My guy ban gane ba, fahimtar dani kamar ya karyan banza?" "Ba gashi nan a gabanka ba, kuma yana da baki ya fada maka da kansa" Juyawa K,B yayi yana kallon Zaidu wanda yake kwance yana aikawa da Ubaidullah harara. K,B ya ce. "Ni dai yanzu ka bar wannan hararan nasa ka bani labari hararan kayi masa anjima, meya faru?" A hasale Zaidu ya miƙe zaune ya ce. "Wallahi Yaya Captain ka kiyayeni dan ma ka samu yanzu zan dinga kiranka da suna Yaya shine kake min tsiya?" "To ƙanina Captain Zaidu yanzu hakuri kake so na baka ko miye?" Tashi Zaidu yayi ya nufi hanyar toilet ba tare da ya kula Ubaidullah ko K,B ba. K,B ya ce. "Ni fa tambaya nake yi." Juyowa Zaidu yayi ya ce. "Subhanallahi wai miye haka ne kam K,B mun dawo ko gaisuwa bamu yi ba, baka je ka nemo mana abinci ba balle ruwan sha, amma zaka wani tsareni da tambayar gulma kana soja,a sojan ma first lieutenant, gaskiya na yarda da batun nan da ake cewa gulma ya koma kan maza" ya fada yana shigewa toilet, tashi K,B yayi yana dariya yana cewa. "Ah haba dai Captain kace min yunwa ka kwaso, ai dole naje nemo muku abinci tun da Allah yasa baka dawo da matar ba balle ta girka mana muci duka kaga daga nan ma idan ka koshi kaban labari" Murmushi Ubaidullah yayi ganin sun haɗa kansu abotan su yana birgesa, ba bakin ciki ba hassada balle kuma ƙyashi. K,B na fita da yan mintina ƙalilan sai ga Rumaisa kamar an jefota daga sama, kafin Ubaidullah yayi wani yunkuri ta shige jikinsa tana sauke a jiyar zuciya, wani dadi ne ya ratsata a duk wani sansa na gangar jikinta, a hankalin ta hau furta kalman. "I miss u i miss u over my lyf, pls say u miss me too?" Da iyakacin karfinsa Ubaidullah ya ban gaje Rumaisa ta fadi kasa, sai huci yake yi shikenan ai yanzu kam ya dawo, zasu ɗaura daga inda suka tsaya. "Oya get out!of this room Rumaisa b4 i open my eyes leave now!" Smiling tayi kafin ta miƙe tsaye ta ce. " never" ta sake shigewa jikinsa tana ƙokarin haɗe bakinta da nasa, sosai suka shiga kacaniya ita dashi harta kaisu ga zubewa bisa gado sannan ta kashe masa ido daya ta ce. "Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne ka zuba idonsa ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa..." ~~~~~~~~ To fa mai Rumaisa take nufi da kalamanta masu zafi ga Ubaidullah? *MAH FANS ALLAH YABAKU IKON GYARAWA IDAN KUMA BA HAKA BA WANNAN SHINE LAST POSTING DINA*🙌🏻 COMMENTS & SHARE BY MOMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻👯🏻 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: I just published "part 19&20" of my story "COLONEL UBAIDULLAH". https://my.w.tt/jFpvO64SS4 follow me on my wattpad pls *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~~•~~ TYPING... *WA'YA KASHE ZAHRA'U?* *#200*(My No ga masu bukatar siya 08165550116) _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_💘 ____________________ _Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako_🤲🏻 __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *page°°°°19&20* Zaka ga yanda ake makirci Captain zaka sake tabbatarwa da cewa tabbas mata makirai ne,ka zuba idonka ka gani, ai duk wanda yaƙi sharan masallaci ba shakka zaiyi ta kasuwa..." Maganar da Ubaidullah yake ta nanatawa kenan a cikin ransa zuciyarsa tana masa suya, yana tunanin me Rumaisa ta shirya masa, da har take masa bazarana da kalamanta?" tambayar da yake ta yiwa kansa kenan amma ya rasa amsarta ,wani ban gare na zuciyarsa ya ce masa. "Haba Captain Ubaidullah jarumin soja abin alfahari, karka tsorata, tsoro baya cikin ɗabi'unka, duk wata sharrinta zai koma kanta ne." Da wannan karfin guiwar Ubaidullah ya sake ture Rumaisa kasa wacce take kwance a jikinsa tana faman shafa masa jiki. Ko da ya tureta bata saduda ba, ta sake tsalle ta haye jikinsa, zip din rigarta ta gaba, ta zugesa kasa take ƙirjinta ta bayyana, da karfi Ubaidullah ya rintse idonsa gami da cewa. "Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Subhnallahi! A'zubillahi Minash'shaiɗanirrajim! Allah ka shiga tsakani da wa innan bayin naka" A zafafe ya mike ya ware hannayensa, a lokacin Rumaisa tana shirin rungumarsa, da iya karfin ya taska mata marin da sai da ta kifu da baki ,dai-dai nan Zaidu ya fito yana fadin. "Subhanallah My Man me zan gani haka meya faru wannan mari haka?lafiya me Rumaisan ta maka?" Mikewa Rumaisa tayi taja zip din rigarta. Da kyau Zaidu yake dubanta yana son gano wani abu, sannan ya juya yana kallon Abokinsa wanda ilahirin jijiyoyin jikinsa sun miƙe sun fito raɗa-raɗa, kunnensa yayi ja, saboda bacin rai da tashin hankalin. Rumaisa ta shafo bakinta wanda yake fitar da jini tayi wata killer smiling, gefen idonta kuwa ya taro da jini, ta kallesa a fakaice ta ce. " Captain Ubaidullah , you slap me?" "Rumaisa get out right now!" "Humm Captain Ubaidullah, i wiil, but u will pay for this" sannan ta dauki wayarta akan dress'mirror tasa kai ta fice. Kallonsa Zaidu yayi yace. "wai meya faru ne kam Ubaidullah? Meya haɗaka da Rumaisa kuma?" Kasa magana Ubaidullah yayi ban da jikinsa dake rawa kamar mazari, a haka KB ya dawo ya same su, Ubaidullah zaune bakin gado ,Zaidu na tsaye daure da towel a kugunsa, da kallon tuhuma KB ya bisu dashi , ya ce. "Lafiya kuwa meya faru?" "Rumaisa" Zaidu ya bawa KB amsa da haka. KB ya ce. "Rumaisa dai? To meya hada su da Ubaidun?" "Nima wallahi ban sani ba, kuma kasan yanzu ko sama da kasa zasu haɗe Ubaidullah bazai yi magana ba, mu bari ya sauko tukunna" Cike da mamaki KB ya ce. "Kamar ya bazai yi magana ba?" Murmushi Zaidu yayi ya ce. "Nasan Ubaidullah fiya da yanda nasan gadon bacci na, mutum daya ce zata iya sa Ubaidullah ya sauko *MAMA* ita ma sai tayi da kyar kafin ya huce" Nan KB ya ajiye abinci tare da lemon da ya kawo musu, ya nemi guri gefe daya ya zauna, Zaidu kuma ya hau shafa mai, bayan ya gama ya saka jallabiyya shima ya zauna suka zubawa Ubaidullah ido. har yanzu idanunsa bai washe yayi haske ba, jijjiyoyin jikinsa ma basu koma ba, babu abun da yake masa gizo sama da kirjin da Rumaisa ta bude masa, nan ya sake rintsa idonsa da karfi cike da takaicin kallon haramun da Rumaisa ta saka shi yi. Zaidu gajiya yayi da jiran Ubaidullah ya dawo normal dan haka a sab'ule ya mike ya dauki ruwa mai kankara a karamin freezer din dake dakin nasu, ya shiga toilet ya dau karamin bowl tare da karamin towel yazo gaban Ubaidullah ya watsa masa ruwan, amma ko gizau Ubaidullah bai yiba sai kace ba ma shi bama aka watsa wa ruwan. Sai da Zaidu ya watsa wa Ubaidullah kusan sau uku kafin ya bude baki ya saki ajiyar zuciya bakinsa yana fitar da hayaki, cike da tsoro da mamaki KB ya ware idanunsa yana kallon Ubaidullah ya ce. "Tabɗijam tashin hankali Captain Ubaidullah anya akwai macen da zata iya zama da kai kuwa? Irin wannan zuciya haka ,harta maza na firgita inaga mata?" Murmushi Zaidu yayi ya ce. "Wallahi mace kadarace mai tsadar gaske duk zafin zuciyar namijin zaki da yazo gaban mace zai koma ɗan tsaƙo, kuma zaka ce na gaya maka,ai su mata matsayin su da darajar su daban yake domin su hijabai ne kuma rufin asiri garemu wawayen maza ne kawai basu san da haka ba, suka mai da mata bayi marasa daraja da galihu, to wannan idan ka duba rayuwar su bata wani albarka" Jinjina kai KB yayi, ya ce. "Haka ne wallahi maganar ka, gashi maza yanzu sun ƙaro wulakanci da an tabasu Sai su ce matan sunyi yawa yo ai su ma mazan sunyi yawa tunda dayawar su su na so suyi aure amma babu halin yi" Dariya suka kwashe dashi yayinda Ubaidullah ya buga tsaki ya tashi ya shige toilet, kusan 20mnts ya fito jikansa sharkaf da ruwa, towel ya dauka ya koma toilet din, da kallon Zaid da KB suka bi bayansa, Zaid ya girgiza kai a ransa ya ce. "Allah ya kyauta ya sauƙaƙa maka wannan zafin zuciyar" Bayan 5mnts ya sake fitowa ,jallabiyya shima ya saka ya kwanta ba tare da ya kulasu ba. Zama Zaid yayi ya ce. " am very very hungry wallahi" KB ya ce. "Yo to ba ga abinci a gabanka ba ai saika sunkuya" murmushi yayi ya juya yana kallon Ubaidulllah wanda idonsa yake rufe gam kamar mai baccin wuya, amma ba baccin yake yiba kalaman Rumaisa ne yake masa guɗa a kunne, haka kawai yaji kalaman sun samu matsuguni a zuciyarsa. Zaidu ganin yana cikin yanayin wani irin hali ne sai ya sa jikinsa sanyi, tashi yayi ya matso kusa da shi cikin sanyin murya ya fara magana. "Haba My Man bai kamata ace mace ta firgita ka haka ba duk abin da Rumaisa ta maka zaka iya hukuntata a matsayinka na ɗa namiji, duk da bansan me ya haɗaku ba" Sosai Zaidu ya dinga dannar Ubaidullah har ya sake,amma ba sosai ba, sai da aka kira sallar magriba tukunna suka fita izuwa masallaci bayan sun dawo suka saka kakin su na sojoji suka dauki hanyar Office din General Of The Army, da sallama suka shiga bayan sara musu da sojoji suka dinga yi. Bayan sunyi sallama ne, Ubaidullah shine a gaba, ba zato zaji sunyi karo da wata, tayi baya baya zata fadi da sauri ya tarota da ta faɗo faffaɗen ƙirjinsa take ta sauke ajiyar zuciya ba kowa bace face *Hanan* yar gidan *Ganeral of the army* Da sauri Ubaidullah ya matsar da ita daga kirjinsa ya gyara mata tsayuwarta bisa kafafunta, sannan ya haɗe ran nan tamau, gefe ta koma Ubaidullah da Zaidu suka ƙame su na sarawa Shugaban su, sosai General yaji dadin ya hau tambayarsu ya hanya da mutanen gida suka amsa da lafiya lau, nan ya sake musu ban gajiya gami da tuna musu yau saura 1wk kacal suyi tafiya suka amsa masa da cewa eh su na sane, kafin suka yi masa sallama har sunje bakin kofa, General of the army ya ce. "Captain Ubaidullah zan aikeka Abacha Barracks gobe wajan major Salihu" Da ok sir Ubaidullah ya amsa suka fita da Zaidu a hanya suka haɗu da Raihana ita ma sai da ta ƙunsawa Ubaidullah haushi kafin ta kama gabanta. Kafin su Ubaidullah su koma part dinsu sai da suka yi sallar isha'i kafin suka koma part dinsu, wayarsa ya dauka ya kira Mama suka sha hira kafin ya kira Anty Ummu suka dan taba hira sama -sama sannan sukayi sallama. Duk yanda Zaidu da KB suka so yin hira Ubaidullah yaki dan haka suka kyalesa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Washe gari da safe bayan Ubaidullah ya shirya cikin kakinsa wanda suke matukar yiwa jikinsa kyau, ya fito ya nufi office din Ganeral ya karba sakon a hanya suka hadu da wani shi da Rumaisa bisa alamu kuma sabon Ma'aikaci ne, kuma ba musulmi bane, dan a jikin rigarsa an rubuta *Sergeant Ema* kallo daya Ubaidullah ya musu ya dauke kai, yayinda S Ema ya ga Ubaidullah duk sai ya sake masa kwarjini, tabbas yanda ake fadinsa yafi haka, haka kawai yaji baya kaunar Ubaidulllah. Aiken da aka yiwa Ubaidullah Abacha Barracks direct ya wuce sai yamma ya dawo suka ci gaba da aikin su. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ After 6days da dawowar su Ubaidullah gobe ne kuma suke shirin tafiyar su, a wannan kwana shidda Ubaidullah yayi mari yafi a ƙirga, barin ma Rumaisa, da Raihana, ita kuma Zeey bata nan sun tafi wani Course a America, gashi yanzu yan matan sun kara yawa harda wa inda ba musulmai ba duk hari suke kawo masa, a daren ana gobe zasu tafi Rumaisa ta cewa Ubaidullah. "You know what Captain? Humm ina so ka tara hankalinka waje guda domin dawowarka daga tafiyan nan babu alƙairi a ciki za kuma ka gani" Kasa magana Ubaidullah yayi banda uwar kallon da yake bin Rumaisa dashi har ta fice daga parlourn. Tambayar kansa yayi wai me Rumaisa take nufi dashi ne kam.? @@@@@ Daga wannan page din na tsaida littafin nan zuwa nan da sati biyu. CMMENTS & Share By MAMYN AHLAN MRS IS OK✍🏻 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafinmu na Bakandamiya, danne nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°21&25* "Wai me kike nufi dani ne kam Rumaisa? Mena tare miki? Ya Allah ka kawo min sauki cikin lamarina, Allah ka shiga tsakanina da wa innan bayin naka,Ya Allah na kawo ƙaransu gareka,Duk abun da kike nufi ya koma kanki Rumaisa, aniyarki ta biki" cewar Ubaidullah, ya zube a kujeran parlour yana sauke ajiyar zuciya, KB da Zaidu ne suka shigo da sallama, a haka suka samu Ubaidullah cikin damuwa, zama sukayi kusa dashi Zaidu ya ce. "My Man what's wrong with you?" Dogon numfashi Ubaidullah ya sauke gami da sauke ajiyar zuciya ya ce. "Nothing ! am just feeling bad, that's why" Girgiza kai Zaidu yayi gami da cewa. "No ba halin soja bane,ina lura da kai tun abun da ya shiga tsakaninka da Rumaisa na fahimci kana cikin damuwa, Ubaidullah ka sha faɗamin akan cewa duk wanda zai saka tsoro da fargaba a cikin zuciyarsa baya zama gwani haka ne?" Lumshe ido Ubaidullah yayi gami da cewa. "Eh hakane matsoraci baya zama gwani, Amma kaidin mata yafi kaidin shaiɗan ina yawan faɗuwan gaba wanda nima bansan dalilin hakan ba Zaidu" numfasawa Zaidu ya yi, a tare suka dafa kafadarsa shi da KB ya ce. "Kaƙi ka faɗa mana meya haɗaku da Rumaisa" Sai da Ubaidullah ya gama shaƙar iska kafin ya fara basu labarin yanda sukayi da Rumaisa, riƙe baki KB yayi ya ce. "Dole kaji ɗari-ɗari a cikin ranka amma inaso ka sani duk ba zata haifa maka ɗa mai ido ba, Ubaidullah kana tare da Albarkan Mama, Rumaisa bata isa tayi maka abun da Allah bai maka ba, sai dai idan ya fito a cikin littafin kaddaranka, to wannan babu yanda ka iya dole ka karbi kaddararka hannu bibbiyu, amma zamu tayaka da addua In sha Allahu ma babu abin da zai faru" Jinjina kai Ubaidullah ya yi, ba tare da ya sake furta ko da kalma daya bane, KB da Zaidu ne suke hiransu amma babu bakin Ubaidullah a ciki, dan shi haka yake magana bata damesa ba, karshe ma da suka ishesa tashi yayi ya basu waje ya shige bedroom. Zaidu ya bisa da kallo ya girgiza kai ya ce. "Mutum sai kace mai iskokai, ga uban canza kala sai kace hawainiya, nidai bazan fasa fadi ba zanga kalar macen da zata iya zama da kai" KB ya kwashe da dariya ya ce. "Kai fa kace min tsab mace zata gyara Ubaidullah ya dawo saiti shine kuma yanzu kake wannan maganar? Ko kamanta kace min mace kadara ce mai tsada?" Dariya shi ma Zaidu yayi ya ce. "Ban manta ba, amma lamarin Abokina sai shi wallahi" nan dai suka ci gaba da hirarsu. Ko da Ubaidullah ya shiga ya kwanta ba jimawa bacci ya kwashesa ba tare da yasani ba, su ma da suka gama abun da sukeyi suka wuce bedroom dinsu kasancewar gobe asubanci zasuyi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Tun kiran sallar farko suka farka, wa inda basu sallah har sun shirya, nan ma sai da akayi daru da Ubaidullah shi da commander Victor wai sai dai su Ubaidullah su tafi ba tare da sunyi Sallan asuba ba sai suyi a hanya, Ubaidullah ya ce. "Sam bai jiba bai gani ba, ko da General Of The Army ne yazo akan cewa su tafi ba tare da yayi sallah ba, wallahi sai dai a tafi abarsa, a fasa tafiyar nan dashi. Haka kuwa suka hakura bayan sun gama shiryawa, ga barracks bus yayinda sojoji suke tsaye sun ƙame waje guda General Of The Army yana musu addua tare da tuni abun da zai kaisu kwana uku kacal ake bukata suyi su dawo, sara masa sukayi sannan suka shiga bus, General ya ce musu. "Goodlock." ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Tafiya suke ana hira amma ban da Ubaidullah, wanda fuskarsa jiya iyau, karshe ma wayarsa ya ɗaga ya kira Mama a lokacin karfe 9:00am sun ɗanyi nisa tun da sun fita daga garin Abuja, airpiece ya saka Mama da ta idar da Sallan walha tana lazimi taji wayarta na neman agaji, a hankali ta janyo wayar dan tasan bazai wuce ɗanta Ubaidullah bane, tana dubawa taga shine, ɗagawa tayi, tun kafin tayi magana ya ce. "Assalamu alaykum My Momma fatan kin tashi cikin koshin lafiya? Yasu Sister's?" "Lafiyar mu kalau Alhamdulillah Yaya Babba Soja mazan fama, har kun kama hanya ko?" Lumshe idonsa yayi domin idan yana waya da mahaifiyarsa, har wani farin ciki da Annushuwa yake tsintar kansa a ciki, yakan manta da damuwar da take damunsa ya fuskanci mahaifiyarsa su sha hiransu abun sha'awa da birgewa. "Eh My Momma dan har ma munyi ɗan nisa tun da gamu nan a jos yanzu haka" "To masha Allah Ubaidullah ya Zaidu da wanda muke gaisawa dashi din nan ma? Ubaidullah ya ce. "KB" "Yauwa Eh shi fatan su na lafiya ko?" "Eh lafiyar kalau Mama ba kiji, suturun su ba?" Mama ta ce. "Aifa dai kam akwai surutai kala-kala dan bana ma jin maganarka sosai saboda hawaniya" Dogon tsaki Ubaidullah yaja gami da juyawa ya kalli KB da Zaidu wanda suke zaune kusa dashi, a hasale ya ce. "Malamai ku sararamin dan Allah, surutunku yayi over, waya nake amma saboda maganganunku yasa bana jin abun da Mama take cewa"ya karasa maganar yana mai kara jan tsaki. Girgiza kai Mama tayi ta ce. "Ubaidullah Allah ya shiryeka, dan Allah ka dinga sassautawa zuciyarka kana saka mata salama kaji?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce. "To Mama In Sha Allahu ki dinga tayani da Addua" "Addua Ubaidullah kullum a cikin yi muku nake,Allah ya shirya min ku ya muku Albarka" da ameen ya amsa yana tambayarta su Hafiza da Na'ila, Mama ta ce. "Sunje makaranta" hira suka dan taba kafin sukayi sallama. Anty Ummu ya kira suka sha hira, bayan sun gama ya kira Umma (mahaifiyar Zaidu) nan yaji muryan Inna sai sababi take ita dasu Afnan wanda basu gida su na makaranta abun da suka mata tun kafin su tafi shine take ta mitansa har yanzu, Girgiza kai Ubaidullah yayi a cikin zuciyarsa yace wannan tsohuwa ba dai jaraba ba, ita kullum masifa ko gajiya bata yi. Addua Umma tayi musu dan Ubaidullah ya faɗa mata gasu a hanya, kuma dama tasan da tafiyar tasu, tun da Zaidu ya sanar da ita, bayan sun gama wayar ne Ubaidullah ya lumshe idonsa gami da jinginuwa da sit, Zaidu kallon Ubaidullah yake saboda kirkinsa, duk ji da kai irin na Ubaidullah yana son jama'a amma miskilancinsa ne yake hanasa sakin fuska, Uwa Uba zafin rai, da haka kowa ya ci gaba da hidimarsa a cikin bus babu mai kula wani, tun bayan da Ubaidullah ya daka tsawa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ba su Ubaidullah da isa bordern Niger ba sai karfe tara na dare, su na isa ba tare da bata lokaci ba suka kai wa yan ta'addan da suka zo kamawa farmaki, yayinda suke kokarin guduwa su kuma ,amma cikin ikon Allah suka kamasu sannan suka damƙasu a hannun jami'an tsoron bakin border din. Rundunar sojojin bakin bordern Niger sunji dadi sosai ganin aikin da suka kasa tsawon wata daya amma a ɗan kankanin lokacin da bai wuce awa biyu ba rundunar sojojin Murtala barracks na garin Abuja suka kamasu, sannan suka damƙa musu masu laifin, hakan ne yasa shugaban rundunar sojojin Niger ya bawa su Ubaidullah masauki mai rai da kuma lafiya. Kwanansu Ubaidullah biyu a Niger sannan suka kama hanyar dawowa Abuja. Asubanci sukayi, dan haka ana sallan isha'i suka shigo Abuja saboda gudun da suka dinga shararawa akan titi. Masha Allah sun iso lafiya, yayinda sojoji aka taro domin tarbansu, daga ciki kuwa harda General Of The Army da matarsa da Yarsa Hanan. San da su Ubaidullah suke fitowa a mota daya bayan ɗaya kowa sai ya sara musu, Ubaidullah shine karshen fitowa a mota, da kyar yake iya ɗaga kafarsa fuskar nan babu walwala. Yana fitowa yayi tozali da Zeey ta sakar masa murmushi, a zuciyarsa ya ce. "Another trouble don come back,Oh Allah ni Ubaidullah" Sai da yazo gaban General Tukunna ya dan sakin murmushin gefen baki, hajiya Jamila matar General sai yamutsa fuska take, Hanan kuwa ta gama mutuwa akan Ubaidullah bata san ta inda zata fara tunkarar mahaifinta ko Ubaidullah ba, ta rasa ya zatayi da Soyayyar Ubaidullah wanda kullum kara ruruwa yake a cikin Zuciyarta, gashi ta fuskanci Ubaidullah dan ji da kai da shan kamshi ne, dan duk yanda take da ji da kai Ubaidullah ubanta ne. Nan General Of The Army ya jinjinawa kwazo da jarumta irin na su Ubaidullah sannan suka mika masa lambar yabon da suka samu daga shugaban rundunar sojojin Niger. Sosai jama'a aka tayasu murna, masu tayasu bakin ciki ma duk sun musu,kafin suka wuce part dinsu, Zeey taso tayiwa Ubaidullah magana amma ina bata samu damar hakan ba. Sai da suka watsa ruwa sukayi sallan Isha'i, kafin KB da Zaidu suka nemi waje suka kwanta,a lokacin Ubaidullah na tsaye jikin mirror juyowa ya yi ya kallesu yaja tsaki. "Nifa lokaci ya yi da zaku barmin part dina ku koma naku especially kai Zaidu Mijin yarinya" ya fada maganar yana nuna Zaidu da yatsa. Zaidu dake kwance ya tashi ya zauna yana zubawa Ubaidullah harara ya ce. "Bazan koma ba Yaya Captain sai kazo ka mai dani" Me KB zaiyi in ba dariya ba yana kallon draman su. "Mtswwww! To nikam na gaji da ajiye ku a part dina, haba kowanne ku fa da nashi part din amma duk kunbi kun tare a nawa,abun haushin ma, ku kama, ku wani haye min bed dina ku barni akan kujera, tun da kunsan ni bana iya kwanciya da mutane bana son naji motsi kusa dani" Miƙewa tsaye KB ya yi yana cewa. "Gaskiya Ubaidu halinka akwai gyara baka son kaji motsi kusa da kai, idan kayi aure kuma fa,ko me kake nufi?" Zaidu ya ce. "Tambaye shi kam" "To sai aka ce muku ni mayen mata ne kamar ku?" "To mu ma kuma sai aka ce maka mayun matan ne?" cewar Zaidu yana haɗa rai. Murmushin gefen baki Ubaidullah ya yi ya ce. "Yes of course especially ma kai Dan kafi kowa son aure da maganar aure" Duk haɗa ran Zaidu sai da ya dara, dan maganar Ubaidullah ya basa dariya, ba kadan ba, kallonsa ya yi ya ce. "To wa ka taba ganina da ita a barrack din nan uhum? Da sauki ai tun da aure naso kaga kuwa alamun ni lafiyayye ne"ya karasa maganar da sakin dariya shi da KB, iyakar ƙuluwa Ubaidullah ya ƙulu, da haka ya fatantake su a bedroom din ya kulle yana cewa. "Wallahi sai dai ku kwana a parlour" Su na dariya suka wuce part dinsu, amma duk ƙura dole ce tasa suka dawo suka kwanta a parlourn Ubaidullah da niyyar gobe zasu sa a gyara nasu. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari misalin karfe tara na safe Ubaidullah bayan ya dawo daga training, dan ya zame masa jiki da yayi sallan Asuba zai fita judging shiyasa jikinsa duk ya murmuɗe da ka gansa sai kayi tunani wani ɗan shekara 30 ne, amma bai kai ba. Yana isowa kofar part dinsa ya ga su Zaidu tsaye cirko-cirko da wasu sojoji fuskar su dauke da tashin hankali, shi ma Ubaidullah a kiɗime yake tambayar su. "Meya faru?" da kyar Zaidu ya yi karfin halin cewa. " Ubaidullah muje ana nemanka a filin taro, barracks meeting yanzun nan" Duk faduwar da gaban Ubaidullah keyi ba shi ya hanasa juyawa cike da karfin hali da kwarin guiwa ba, dan shi dai yasan bai aikata komai ba. Jiki a sanyaye KB da Zaidu suka rufa musu baya. Yana isa ya samu General Of The Army tsaye fuskarsa ba annuri ya haɗe rai ,ya rikiɗe ya koma asalin sojan, a gefensa kuwa Major Shehu ne shima ransa bace,a takaice dai dik manyan sojoji fuskar su ba walwala. Gefe ya kalla ya ga sergeant first class Ƙasimu, (mahaifin Rumaisa) a ɗayan gefen Rumaisa ce zaune sai kuka take kanta a sun kuye, cike da Jarumta Ubaidulllah ya sara musu amma babu wanda ya kallesa, dama mahaifin Rumaisa haushin Ubaidullah yake ji saboda daga zuwansa Allah ya daukaka shi, yanzu kuma ga abun da ya faru ga abun da yayiwa ƴarsa, ai dole ya wulakanta Ubaidullah ya tozarta shi. Cikin Tsawa da ɗaga Murya General Of The Army ya juya ga Ubaidullah yana masifa yana nunasa da yatsa. "Kaban Mamaki Captain Ubaidullah! Kayi mugun bani Mamaki! Ban taba tunanin haka daga gareka ba, kai da kake yaƙi da wanda suke yiwa Yan mata fyaɗe amma ace yau kaine kayiwa Rumaisa fyaɗe har ka mata ciki!!!" Maganar General sai da ya girgiza duniyar Ubaidullah, ya kasa tantance a wace duniyar yake, shi yaushe ya taba kama mace ya runguma balle har ya kusanceta har ya mata ciki? Macen ma kuma Rumaisa wanda ko ɗaura masa ita akayi a kafa zai kunceta ya jefar balle har wata tarayya ya shiga tsakaninsu ya mata ciki? Innalillahi wainna ilayhirrajiun!" shine kalman da Ubaidullah yake iya nanatawa kenan ya kasa magana. Kallonsa Lieutenant General Musbahu ya yi gami da cewa. "Captain Ubaidullah shin da gaske kaine kayiwa Yar gidan Sergeant first class Ƙasimu ciki? Dan tace kaine Saurayinta kuma da kai take mu'amala. Ban da juyin da kwakwalwar Ubaidullah keyi, amma ya kasa katabus, juyawa yayi yaga sojojin da suke tsaye da zaune ga Rumaisa dake kukan munafurci har yanzu, kafin kace mai Idon Ubaidullah ya rikiɗe ya koma jajur ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe tsantsaye. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *_YA ALLAH MUN TUBA ALLAH KA YAFE MANA ZUNUBANMU ALLAH KA YAYE MANA CUTAT COVID19 ALLAH KASA MU GAMA DA WANNAN DUNIYAR LAFIYA AMEEN🤲🏻🤲🏻_* *MASOYA BOOK DIN COLONEL UBAIDULLAH,INA MAI BAKU HAKURI NA RASHIN JINA TSAWON SATITTIKA, NGD DA KAUNAR DA KUKE NUNAWA WNN BUK DIN NAWA*👏🏻👏🏻 COMMENTS AND SHARE MOMYN AHLAN✍🏻 [8/19, 10:56 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°26&30* Jikinsa sai kyarma yake yi, Alluran Soja ya miƙe dama ya lafiyar giwa balle tayi hauka, gadan-gadan yayi kan Rumaisa yana shirin kai mata cafka, da sauri Babanta ya tare Ubaidullah ya kai masa naushi a baki nan take bakinsa ya fashe sai ga jini tare da haƙorinsa biyu sun faɗo. Hannu Ubaidullah ya kuma kaiwa zai kamo Rumaisa Commander Victor ya sha gabansa gami da kaiwa Ubaidullah duka a ciki, zafi sosai Ubaidullah yaji amadadin ya duƙa sai ya rufe Commander Victor da duka, nan fa fili ya rikiɗe tamƙar filin yaƙi nan aka shiga kokarin riƙe Ubaidullah amma duk wanda ya tabasa zai zubar dashi kasa, hakanne ma yasa wasu sojojin suka samawa kansu lafiya ta hanyar komawa gefe suyi kallo,cakwakiya tayi cakwakiya dan Ubaidullah ya zubar da sojoji sun kai ɗari da wani abu a kasa sai kace yaje filin yaƙi, cikin zafin rai ya fara magana. "Ni za kiyi wa Sharri! Rumaisa? Ni za kice nayi miki ciki ? Ni zaki tozarta Rumaisa? Mena tare maki da zaki min ƙazafi? Nace mai na tare miki!" yana maganar yana kai duka yana tunkarota tana ja da baya. General ganin fa idan ba da gaske akayi ba wajan tare Ubaidullah idan ya kama Rumaisa to sai dai wata amma ba ita ba, da sauri General da Major suka riƙo Ubaidulllah ta baya, har Ubaidullah ya juyo zai kai duka sukayi ido hudu da General Of The Army nan ya sauke hannunsa da sauri sannan ya sara masa,jikinsa sai b'ari yake yi jijiyoyin jikinsa sun sake fitowa raɗa-raɗa, cikin tsananin bacin rai General Of The Army ya ce. "Aje a kulle Ubaidullah a saka shi a guardroom" da sauri Hanan ta ce. "No pls Daddy kar a a saka shi a guardroom sai kace wanda yayi sata ko yayi wani babban laifi, daddy da muƙamin shi da komai dinshi a saka shi a guardroom?" Tsawa General Of The Army ya dagawa ƴarsa wanda ya sakata firgita har sai da taja da baya tana zare ido, Major ya ce. " Captain Ubaidullah yayi babban kuskure na dukan da yayiwa Sojoji dan bai kamata ace ya dakesu ba, dan ya fisu muƙami,sannan ba a yarda da maganar da Rumaisa ta faɗa ba sai da ta gabatar mana da hujjar wani video recording wanda suke mu'amala tare, dan haka a tafi dashi" da karfi Raihana da wata yarinya christen mai suna Doratie suka mike gami da cewa. "Na lie! Ubaidullah he can't do this" amma babu wanda ya saurare su, Zeey kuwa mikewa tayi idonta jajur ta bar wajan, tashin hankalin da Zaidu da KB suka shiga kuwa bazai misaltu ba, dan suman tsaye suka yi,duk wannan budirin sun kasa yin katabus, Sai da suka ji General yana umarta kama Ubaidullah a tafi dashi guardroom tukunna suka fara roƙon General amma ina bai saurare su ba, sojojin da zasu kama Ubaidullah cikin tsoro da shakkarsa suka kamasa, dan Ogansu ne, uwa uba kuma mai karfi ne,dan su na jin tsoro karya zubar dasu ya ja musu kwanciyar asibiti. Rumaisa hankalinta ne ya tashi dan ita ba haka ta so ba, taso ace General dasu Major su bawa Ubaidullah Umarnin ya aureta ne, amma bawai a kullesa ba, tunani ta shiga yi, yanzu ya za tayi,Da sauri ta miƙe tabar filin wajan ta dauki wani hanya,tana tafiya hankalinta baya gabanta, batayi auni ba ta ji saukar naushi a bayanta take ta faɗi kasa, dagowar da zatayi taga Zeey tsaye a saman kanta fuskarta tayi ja. Cikin zafin rai Rumaisa ta miƙe zata rama naushin da Zeey ta mata, dan dama sun saba in dai dambatuwa ne,ta kaiwa Zeey naushi Zeey ta riƙe hannunta ta murɗeshi ta baya ta shaƙo wuyanta, ta fara magana cikin bacin rai, da tsawa. "Makaryaciya! ashe son da kike ikirari kina masa duk karya ne! Wallahi Rumaisa baki son Captain tun da har zaki iya zubar masa da mutunci a filin jama'ar da sun kai Fiye da dubu, Rumaisa karya kike kice son shi kike,tun da gashi kinci zarafinsa kinsa an kullesa a guardroom" "Rumaisa me Captain ya miki da zaki saka masa da ƙazafin *ZINA*? Haba Rumaisa! Haba Rumaisa! Wallahi ko rantsuwa dubu zanyi idan na karyata ki ba zanyi kaffara ba,saboda nasan halin Captain kema kuma kinsan halinsa, Rumaisa idan ma karya kike akan cewa kina da ciki alhalin babu, to saina miki la'anannan duka ta yanda sai ciki ya shiga jikinki, idan kuma akwaita na wani dan iskan ne a cikin barracks din nan kikeso ki liƙawa Captain to sai na miki kafurin duka ta yanda sai kin haifi cikin nan baki shirya ba" Nan Zeey ta rufe Rumaisa da ƙazamin duka dan ranta yayi mugun baci, tana cikin jibgarta kenan sai ga Hanan yar gidan General Of The Army da Doratie da Raihana, su ma sun biyo bayan Rumaisa su lakaɗa mata duka ne, amma me nan suka ci karo da Zeey dake jibgar Rumaisa kamar zata kasheta dan Zeey mugun karfi gareta, dan harta mazan barracks wasu shakkar Zeey suke saboda ba ƙaramin abu ne a wajanta duk dan iskan da ya taƙaleta ta nuƙuskushesa, ta ƙara gaba abunta. Hanan ganin Zeey tana shirin kai Rumaisa lahira nan suka shiga kokuwar kwatar Rumaisa daga hannun Zeey, da kyar da suɗin goshi suka kwaceta amma kafin nan sai da su ma sukaci duka. Gefe Zeey ta koma tana huci, yatsar hannunta manuniya ta nuna Rumaisa dashi gami da cewa. "Wallahi!Wallahi!Wallahi! Rumaisa kinji na miki rantsuwa uku ko, idan har baki je kin warware kullin da kika yiwa Captain ba, sai na miki *LAHANI* sai na miki *ILLA* sai dai duk abun da zai faru ya faru" tana gama faɗi tayi gaba kamar zata tashi sama. Cirko-cirko su Hanan suka Tsaya su na kallon juna, ga Rumaisa kwance a kasa tana sauke numfashi da kyar, Doratie ce ta kalli Rumaisa cikin hausarta da bata iya sosai ba ta ce. "Shame! Kinji kunya! Rumaisa, kince kina son Captain Ubaidullah for what reason zaki masa sharri? Sanin kowa ne a barracks din nan Captain Ubaidullah baya kula mata, infact har mazan ma baya shiga Hidimar su amma zaki masa wannan sharri! Walahi kinci sa'a amma kinga zugan mun nan, dama mun zo ne mu lallasaki sai kuma muka samu maiyi da gaske ta tumurmusheki, dan haka ki kiyayi gaba. ********** Da sauri KB da Zaidu suka bi General su na magayi, amma ya dakatar dasu, dan shima ya shiga cikin zullumi. Haka suka juya ba dan sun so ba, wajan Major suka je Zaidu ya ce. "Sir a duba lamarin Ubaidullah na miskilanci da rashin magana da kula mutane, ta ya wani mu'amala zai shiga tsakanin su da Rumaisa har ya mata ciki? Sir, idan mafaɗin magana wawa ne ai majiyinta mai hankali ne, pls Sir a duba lamarin" Zaidu ya karasa maganar kamar zaiyi kuka saboda tashin hankali. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da babu gwara ba dadi ko my ppls?😁 COMMENTE AND SHARE BY MOMYN AHLAN✍🏻 [8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_HAHAHA MASHA ALLAHU, IDAN KAJI WANE KO WANCE BA BANZA BA, KUNA INA MASOYAN KUNGIYAR NAN ƊAYA TAMƘAR DA DUBU, WATO KAINUWA WRITERS ASSOCIATION? WANDA SUKA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI DAƊA ƊA, MAZA MAZA KU MATSO KUSA GA DAMA TA SAMU, A YAU KUNGIYAR TAYI SURFE DA DAKA, TA TANKAƊE TA RAIRAYE, TA REGE TA BUSHAR, TA ZAƘULO MUKU JIGA-JIGAI HAZIƘAI NAGARTATTU MASHAHURAI,BASIRARRU, A YAYINDA ZASU GWANGWAJE KU DA FASAHAR SU, DAMA SUN SABA ILMANTAR DAKU NISHAƊANTAR DA KU GAMI DA FAƊAKAR DAKU, KU DAI KU KASANCE DA WAINNAN FASIHAN MARUBUTAN GUDA BAKWAI DUK A CIKIN LITATTAFANSU MAI TAKEN SUNA ( 𝕊ℍ𝔸ℍ𝔸ℝ𝔸ℝℝ𝕌 𝔹𝔸𝕂𝕎𝔸𝕀 ) AKAN FARASHI MAI SAUKI DA RAHUSA #500 KACAL YAN UWA, KU DAI KARKU BARI A BARKU A BAYA, NI UWAR AHLAN INA GAYA MUKU NE DAN KU HANZARTO KU GARZAYO, KU NEMI NAKU, KU SHA KARATU, A ISO LAFIA._* 💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞 *page°°°°°31&36* Major ya ce. "Ok Captain Zaidu kuje zanyi magana da General Of The Army idan yaso a tara meeting sai asan abunyi" Zaidu ya ce. "Tnk u Sir Allah ya kara girma, but pls kar abar Captain Ubaidullah ya kwana a guardroom "ya karasa maganar cikin roƙo da kasa da murya gamj da kwantar da kai. Major ya ce. "Kuje zan san yanda za ayi" sara masa sukayi, sannan suka sa kai suka fice daga office din Major. Su na barin office din Major hanyar guardroom suka nufa kai tsaye, su na tafiya su na tattauna lamarin, KB ya ce. "Amma dai gaskiya wallahi Rumaisa ta cika babbar makira, ban taba tsammanin zata yiwa Ubaidullah wannan ɗanyen aikin ba" "Hummm KB kenan wasu matan kam ai sai a hankali, kai a tsammaninka Ubaidullah zai kyaleta ne? Tab Ubaidullah bazai barta ba, sai ya koya mata hankali, shiyasa dazu da yake kokarin cafkota banyi tunanin katse masa hanzari ba, so nayi yayi mata shegiyar duka, amma sai wannan tsautsayin ta gitta, ko ba komai naji dadi da Ubaidullah ya fasawa Ubanta baki har yayiwa hakorinsa biyu sanadin zubewa kasa a cikin jama'a, kuma kasan sergeant first class Ƙasimu(mahaifin Rumaisa) ba kaunar Ubaidullah yake ba" KB ya ce. "Yes i know, ai naji dadi da Ubaidullah ya jibgi Commander Victor, dan kasan ba kaunarsa yake ba shima, ni na rasa me Ubaidullah ya tare musu" "Ai na lura wa inda basu son Ubaidullah a barracks din nan su na da yawa, gashi da mahassada kuma shi ba ɗan siyasa ba, da sunan shi Soja, kai gaskiya abun yana damuna" KB ya ce. "Hummm Zaidu kenan sai kace baka san halin *RAYUWAR BARRACKS* ba? Duk nan ne fa ma tattarin *HASSADA, KYASHI NUNA FIFFIKO* barin ma idan mutum ya fika muƙami, ga *SHARRI* ga *GA BA*" Zaidu ya ce. "In dai sharri ne kam na shaida tun da ga Abokina a kulle" ya faɗa maganar su na shiga wajan Ubaidullah dake tsaye ƙiƙam sai kace bishiyar itace, sallama suka masa amma da kyar ya iya amsa sallamar a cikin zuciyarsa. Rungumansa Zaidu yayi yana buga bayansa,Ubaidullah ya fizge jikinsa,dan ransa yayi ƙololuwar wajan baci, dan ko a mafarki bai taba tunanin zai shiga halin da ya shiga a halin yanzu ba, wai yau Ubaidullah shine a guardroom? Bama zaman guardroom din bane ya harzuƙa shi ba, ƙazafin zinan da Rumaisa ta ɗora masa shine yake sake ingiza zuciyarsa ta sake dulmiyawa cikin tashin hankalin da bai misaltuwa, dan shi ya tsani zina a rayuwarsa, hawaye ne maƙale a cikin idonsa amma fir yaƙi yarda su zubo kasa, rimtse idanunsa yayi mutanen da suke filin barracks yake tunawa a gaban su Rumaisa taci mutuncinsa. Mama zaune a bakin Gado ta ga yau Ubaidullah bai kirata ba kamar yanda ya saba kullum, dan ya kan kira mahaifiyarsa kusan sau goma a rana,hakan ma idan yana busy ne,dan shi baya haɗa Mama da kowa, dan ita ce haske kuma farin cikin rayuwarsa. Sosai gaban Mama yake faɗuwa wanda ta rasa dalilin hakan, ga kuma wayar a hannunta tana so ta kirasa amma kuma ta kasa, saboda faduwar da gaban ƙirjinta ke yi, sai jujjuya wayar take a hannunta tana kallon wayar, zuwa can anjima tayi jahadi ta dannawa layin Ubaidullah din kira,a lokacin su Zaidu su na tsaye su na kan bawa Ubaidullah baki amma ko gizau bai yiba. Kiran Mama ne ya shigo, wayar yana hannun Zaidu yana dubawa ya ga Mama ne,Ubaidullah kuwa daga ringingtone ya fahimci mahaifiyarsa ce, dan yasa mata ringing daban na waƙar larabawa, wanda ake cewa, *HAYATI YA MAMA*. Gaban Zaidu ne faɗi ganin Mama tana kiran Ubaidullah dan bai san me zai cewa Mama ba, gashi ita ba lafiya gareta ba, yanzu ciwonta zai tashi idan tasan halin da Ubaidullah yake ciki, kallon-kallo aka shiga yi tsakanin Zaidu da KB, wannan ya kalli wannan. Har sai da Mama ta yiwa Ubaidullah 3 miss call, ana 4 ne Zaidu yayi karfin halin ɗagawa kafin nan kuma hankalin Mama ya tashi ganin Ubaidullah bai kirata ba ita tana ta kiransa bai ɗaga ba, ta shiga zullumin meya samu ɗanta. Zaidu na ɗagawa Mama ta sauke ajiyar zuciya wanda har sai da Ubaidullah yaji, dan Zaidu ya saka wayar a hands'free ne. Ubaidullah jin yanda mahaifiyarsa ta sauke a jiyar zuciya, yasan hankalinta a tashe yake, dan haka ya wafce wayarsa daga hannun Zaidu yasa a kunne cikin sanyin Murya Mama ta ce. "Assalamu Alaykum, Ubaidullah fatan dai kana lafiya ko? Lafiyarka kalau?" Hawayen da Ubaidullah yake maƙale su nan take suka zubo da yaji muryan Mama. "Ubaidullah wai meya same ka ne kam? Ka faɗamin mana? Yanzu Ubaidu idan baka faɗamin damuwarka ba kana da wanda zaka faɗa mata sama da nine? " duk wannan maganar cikin damuwa Mama tayi su kasancewar tasan halin ɗanta. Kusan 10mnts su na tsaye a haka ban da Ajiyar zuciyar da yake saukewa, karban wayar Zaidu yayi yasa a kunnensa yayi sallama, Mama ta amsa suka gaisa,nan Mama ta shiga tambayar Zaidu me ya faru da Ubaidullah, cikin in'ina da inda-inda Zaidu ya ce. "Amm Uhum humm dama Mama ba wani abu bane, matsala aka samu shiyasa,amma ba komai ki tayamu da addua komai zai zo mana da sauki" "Adduata kullum kuna tare da ita Zaidu,sannan dan Allah ka dinga tausasan Abokinka kasan dai halinsa" "In sha Allahu Mama, karki damu, a gaida Na'ila da Hafiza" Mama ta amsa da "zasu ji" da ga haka sukayi sallama. Hannu Ubaidullah ya miƙawa Zaidu alamun ya basa wayarsa, ba musu Zaidu ya miƙa masa wayar ya karba,KB ya ce. Zaid muje musan abunyi dan gaskiya bai kamata Ubaidu ya kwana a nan wajan ba shi ba mai laifi ba" Zaidu ya jinjina kai alamun eh haka ne, juyawa sukayi zasu fita KB ya waigo ya ce. "Am Ubaidullah kawo wayarka Mu tafi dashi kasan ba a zama da waya a guardroom" Sai yanzu Ubaidullah ya bude baki da kyar yayi magana cikin kakkausar muryarsa wanda yake a dashe cikin tsawa. "Duk Uban da ya isa yazo ya karbe min wayata daga hannuna!" ai da gudu KB ya fice yana sauke ajiyar zuciya, shima Zaidu fita yayi yana dariya ganin yanda KB ya arce da gudu. Waje ya samesa yana tsaye dariya sosai Zaidu ke yi har yana riƙe ciki, cikin dariya ya ce. "Haba Soja kana matsayin First Lieutenant Amma shine dan Captain ya maka muzurai shine ka fece da gudu sai kace walƙiya?" "Uhm uhm Zaidu Ubaidullah ba kamar sauran mutane bane, ko hawainiya ba zata gwadawa Ubaidullah canza kala ba" Nan ma Zaidu ya sake fashewa da dariya ya ce. "Muje ko?" "Ina yanzu zamu je to?" "Eh to nima dai yanzu ban san inda muka nufa ba,amma inaji kawai muje Abacha Barracks wajen Major Usman muyi magana dashi ko ya kace?" KB ya ce. "Eh hakan ma yayi ka kawo shawara muje din kawai" Wajan da motar su yake suka nufa zasu shiga daga bayan su suka ji kira, juyowa suka yi a tare, Raihana Hanan da Doratie ne ,tsayawa Zaidu da KB sukayi har suka iso. Hanan yar gidan Shugaban sojoji ita ce ta fara magana. "Captain Zaidu yanzu ya za'ayi da case din Captain Ubaidulllah? Naje na samu dadyna amma ya ƙi ya saurareni at oll,now I don't know what can do to protect Ubaidullah" ta karasa maganar tana hawaye dan soyayyar Ubaidullah ya mata mugun kamu. Zaidu ya ce. "Don't worry Hanan everything will be better OK?" ta jinjina kai, Raihana ta ce. "Yanzu Zeey ta gama dukan Rumaisa har bata iya motsi da kyau. KB ne ya kwashe da dariya ya ce. "Kai Dan Allah fa? da gaske?" Doratie ta ce. "Seriously Rumaisa ta daku a hannun Zeey, u know Zeey She's very strong woman" Cikin dariya KB ya ce. "Yes I know She's very strong, wow gaskiya Zeey bata taba burgeni irin ta yau ba,ya zama dole nayi mata kyauta" Doratie ta ce. "gaskiya kam ta cancanci kyauta daga wajan Captain and First Lieutenant" Murmushi Zaidu da KB sukayi kana suka bude mota KB na cewa. "Bari muje Abacha barracks zamuyi magana da Major Usman ne" da ok suka amsa sannan su ma suka ci gaba da neman solution ta yadda Captain Ubaidullah zai fita a guardroom. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️ Ta bangaren Rumaisa kuwa hankalinta ya tash da maganganun da Zeey ta faɗa mata, kuma tasan halin Zeey zata iya sarai, kuma ko a muƙami mahaifin Zeey yafi mahaifin Rumaisa Muƙami dan shi matsayin Second Lieutenant ne, gashi ita kuma Zeey CBI ce ita wato jami'ar bincike, shiyasa Rumaisa tasha jinin jikinta gashi taci mugun duka, dan ba karamin horo Zeey ta samu ba daga wajan margayi commander Shafi'u, Uncle dinta ne kuma, Commander Shafi'u ya bawa Jami'an Sojoji ingantacciyar horo ta yanda zasu zama na kwarai su kare kansu da kasar su, dan sai mutum yasan matakin kare kansa kafin ya kare wani, a wajan wani yaƙi aka kashesa lokacin da sukaje yaƙin maiduguri nan yan boko haram suka yi masa kisan wulakanci, tun daga lokacin ba a sake samu wani jarumin Commander ba kamar shi, kuma ba a sake samun cikakken mai tsayuwa da kafarsa da zuciyarsa yayi yaƙi ba har sai da Ubaidullah yazo shi barracks din, da wannan tunanin Rumaisa ta rarrafa da kyar ta tashi tana jan kafafunta da gangar jikinta wanda suke mata tsami. Wajan Babanta ta wuce ta same shi a office dinsa,tasa masa kuka ita ba so take a kulle Ubaidullah ba, ita so take a saka shi ya aureta idan kuma ya ƙi asan abun da za ayi masa amma a buɗesa daga guardroom. Baban Rumaisa duk da yaga jikin ƴar tasa duk a fashe amma bai damu ya tambayeta ba, dan yasan ba zata faɗa masa ba, ya ce. "To shaleleta je ki abunki bari naje na samu General"ya faɗa yana mai ficewa daga office din yabarta tsaye a wajan. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️ Ta bangaren su Zaidu kuwa sun samu Major Usman sunyi masa bayani abun da ya faru dalla-dalla kuma sosai ya fahimta ya ce. "Gaskiya banji dadin abun General ya aikata ba, duk da Captain shi ma yayi ba dai-dai ba,but ba komai ku tashi muje can din" Fitowa sukayi yana gaba su ba binsa a baya, kafin suje kuma an sake kirawo Ubaidullah, a secret meeting room,wanda manya ne kawai a wajan kamar su General Of The Army, General, Major General, sai Brigadier da Colonel da Lieutenant Colonel, ga Uban Rumaisa a gefe da ita Rumaisan, ga Kuma Ubaidullah Zaune a gefe. Ko da su Zaidu suka iso bayan Major Usman ya kira General Of The Army yake gaya masa akan cewa gashi nan yazo ganinsa ne akan case din Ubaidullah,General Of The Army yake cewa Major ai gasu nan yanzu suka shiga secret meeting room su same su acan. Su na zuwa Sojoji suka saka musu gami da bude musu kofa suka shige,sara musu Major da su Zaidu suka yi kafin suka samu wajan zama suka zauna. General Ayuba shine wanda ya fara gyaran murya alaman zaiyi magana. "Amm Ubaidullah am not happy with ur action,dan takanka zan fara, da hankalinka taya ka bari har hakan ta faru tsakaninka da Rumaisa,ni nasan ba akan ka aka fara wannan abun ba, but am very surprised ta yanda naka ya baza barracks din nan, yau aka fara yiwa yara fyade ne? Ko kuma yau ne mace ta fara yin ciki a barracks iye? this is the not the first time da hakan take faruwa, wasu ma basu kai Captain Ubaidullah stars ba, amma ba'a saka su a guardroom ba,duk da ba'a barsu haka ba an hukunta su, gaskiya Sir banji dadi da kuma faruwan hakan ba" Nan Major Usman shima ya karbe maganar daga wajan General Ayuba. "Eh tabbas maganarka haka ne Sir Ayuba bai kamat ayiwa Captain haka ba,domin shi mutum ne mai matukar amfani a wajan mu" Brigadier Rashid ya ce. "Duk wa innan maganganun ma basu taso ba, ya kamata muji ta bakin Ubaidullah shin da gaske ne shi yayi mata ciki ko ba shi ya mata ba, na biyu idan ma shi ya mata cikin fyaɗe ya mata ko kuma ason ranta ya kusanceta, ya kamata a dinga bawa kowa hakkinsa, dazu da abun ua faru bana nan ne da duk bata kai ga haka ba" Lieutenant Colonel Aliyu ya ce. "Captain Ubaidullah akwai wata alaƙa ko mu'amala tsakaninka da Rumaisa ne?" Ubaidullah wanda tun zamansa kansa yake duƙe yana jin maganar kowa yana shiga kansa a hankalin, idonsa kamar anyi b'arin jini,ko ɗigon fari babu a idanunsa, ya ma kasa magana sai girgiza kai kawai da yake yi, ganin haka yasa Zaidu riƙe hannunsa gam ba tare da wani ya gani ba. Tattaunawa akeyi yayinda kowa yake tofa albarkacin bakinsa,duk wata tambayar da za ayiwa Ubaidullah da kai yake amsawa,Rumasa kuwa da an tambayeta zaia karkata baki ta shankaɗa karya da ƙarairaki dan duk abun da take faɗi babu gaskiya ko ɗigo a ciki. A karshe dai hukuncin da aka yanke shiya girgiza Ubaidullah bama shi kadai ba, harta Abokansa na Amana sun girgiza, hukuncin kuwa shine wai Ubaidullah *YA AURI RUMAISA* maganar da ta doki dodon kunnensa,a zabure ya miƙe yana girgiza kai gami da cewa. "Noooo! Naverrrrr! and Everrrrr! Impossible na aureki Rumaisa wallahi bazan aureki ba!" Nan Baban Rumaisa ya fashe da kukan munafurci yana cewa. "To me kake Sir Captain? Kana nufin shikenan kaci banza kenan? Ka kyatawa yarinyata budurcinta kaƙi aurenta? Dan kaga ka fini muƙami? Sai ka zalunceni" ya ci gama da kukan gulma,ran Ubaidullah ya gama baci matuƙar baci, wani wawan camuƙa ya kaiwa Uban Rumaisa. "Ni zaka yiwa Sharri !!! Yaushe nake mu'amala da yarka da har zan mata ciki!?" da kyar su Major da General da Brigadier suka banbare Baban Rumaisa daga hannun Ubaidullah. A fusace General Of The Army ya miƙe dan Abun da yake haɗa shi da Ubaidullah kenan saurin zuciya duk da hakan shine dai-dai a matsayinsa na Soja magana yake cikin bacin rai, kuma yawancin mutane an yarda da Baban Rumaisa da ƴarsa ga kuma wani Video wanda aka haɗa Ubaidullah da Rumaisan da wanda tayi ranar da ya wanketa da mari,shi har ga Allah bai san lokacin da tayi wannan video ba. " Captain Ubaidullah ya zama dole ka auri Rumaisa, idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci mai tsanani gobe idan Allah ya kaimu" General Of The Army yana gama fadi ya fice, yayinda Brigadier ya bada Umarnin kar a sake a mai da Captain guardroom, da haka kowa ya watse, tashi Ubaidullah yayi da Sauri Zaidu da KB suka bi bayansa. Bai tsaya a ko ina ba sai part dinsa, gashi duk inda yasa kafarsa sai an nunasa da tsaya ana gulmarsa, da ya juyo kuma kowa zai kama bakinsa,wannan ne ya saka hassala shi,ganin yanda lokaci ɗaya mutuncinsa ta zube. Zubewa yayi akan gadonsa ya kifa kansa da pilo ya lumshe ido sai hawaye shar-shar, tabbas army shine burinsa amma ya zama dole ya ajiyeta idan ba haka ba Allah ne kadai yasan kalar abun da za a masa gobe, a haka Zaidu suka shigo suka samesa su ma hankalinsu a matuƙar tashe. Zama sukayi gami fa dafasa amma sai ya miƙe ya nufi toilet ya watsa ruwa yayi alwala sukayi jam'in sallar la'asar bayan sun idar ya ɗaga wayarsa ya dannawa Mama kira, cikin sanyin jiki Mama ta ɗaga wayar saboda haka yau ta wuni bata jin dadi ga mummunar faduwan da gabanta keyi, gashi bata saba baccin rana ba, amma sai da tayisa yau, tare da mummunar mafarki. Sallama Ubaidullah ya mata ta amsa lokacin Hafiza da Na'ila su na zaune a gefenta, Mama ta ce. "Ubaidullah fatan lafiya kake ko?" Da kyar ya tattaro jarumta yayi murmushi mai sauti ya ce. "Eh My Momma am fyn,ina nan dawowa gida gobe idan Allah ya kaimu" Dam!dam! Gaban Mama da Zaidu da KB suka bada ware ido sukayi su na kallon Ubaidullahi. "Lafiya kuwa zaka dawo gida Ubaidullah?" "Eh My Momma lafiya sai nazo" ya katse wayar. Yana katse wayar suka hau rige-rigen tambayarsa. "Ubaidullah me kake nufi da zaka koma gida gobe? Aikin naka kuma fa? Dan Allah karkayi haka,hakika al'umma su na bukatarka a cikin jami'an Sojoji ,dan Allah Ubaidullah karka aikata abun da kake shirin aikatawa, barracks tana bukatarka" A hasale Ubaidullah ya ce. "Karya ne! Barracks bata bukatata Zaidu KB karku yaudari kanku, dukkanmu abun da muka sanine a fili zai biyo baya gobe dan ko sama da kasa zasu hade ne na rantse da Allah bazan auri Rumaisa ba, idan kuwa haka ne,gwanda tun da sauran ɗan guntun mutunci ne na ajiye aikin da kaina kafin amin koran kare, wanda idan hakan ta faru zan tsani aikin soja, kuma ni bazan so na tsani aikin soja ba, saboda burinane tun ina ɗan karamin yaro na gaji mahaifina, ko ba komai alhamdulillah na cika burina na aikin soja, nayi yaƙi da jinina da lafiyata , hakan ma na godewa Allah, wannan jarabawatace ina adduar Allah ya bani ikon cinyeta, ku tayani da Addua Allah ya baiyanar da gaskiya dan bana so na mutu da tabon zargi a idon mutanen dake wannan nahiyar" Kawai Ubaidullah ya fashe da kuka,nan take shima KB ya fashe da kuka,cikin ɗauriya Zaidu ya ce. "Ubaidullah u mean gobe zaka tafi bauchi?" Ubaidullah ya jinjina kai alamun eh,a zabure Zaidu ya miƙe kamar wanda aka tsikara da allura, nan suka bisa da ido wardrope Zaidu ya bude yaja akwatinsa ya hau zuba kayansa a ciki, da sauri, Ubaidullah ya mike yana riko gami da tambayarsa me yake shirin aikatawa, me zaiyi yake tattare kayansa,amma sam Zaidu ya ƙi sauraron Ubaidullah tamƙar mahaukaci haka Zaidu ya koma yana kwashe kayansa. Da karfi Ubaidullah ya fizgosa gami da daka masa tsawa. "What's wrong with you Zaidu!!?" Ɗago idonsa Zaidu yayi wanda yake cike da kwalla ya kaɗa yayi ja ya ce. "Tafiya zamuyi Ubaidullah, ba zaka tafi kabarni ni kaɗaina ba anan, yanda muka zo tare haka zamu koma tare"ya karasa maganar yana shirin fizge hannunsa daga na Ubaidulllah zai ci gaba da kwasar kayansa, Ubaidullah ya sake fizgosa gami da cewa. "No Zaidu karkayi haka,tabbas na san tare muka zo,amma ita aiki tamƙar rai ce ,bai zama lallai dole mu mutu tare ko lokaci ɗaya ba, dan haka ni kwanan nawa aikin ne ya kare, nasan kai din amininane na gasken-gaske, amma bazan tabbatar da kana sona tsakani da Allah ba, har sai kamin alƙawarin bazaka taba kabar aikinka ba Aminina" nan take suka fashe da kuka suka rungumi juna, Shima KB kuka yakeyi yazo ya rungumesu duka. "Kafi gaban haka Abokina, nayi maka Alkawarin babu inda zani tunda haka kakeso amma inaso kasani rayuwar aikin soja wajan Zaidu ba zatayi dadi ba indai ba Ubaidu a tare dashi domin Ubaidu shine garkuwan Zaidu" Murmushin Ubaidullah yayi ya ce. "Karka damu aboki ne komai zaiyi Normal zaka saba In sha Allah, kuma ma ai ga KB ne" ya fada yana kaiwa KB naushin wasa a kafaɗa, KB ya share hawaye dan ya kasa magana, haka ranar suka zauna a bedroom su ja jimami. Ta bangaren Mama kuwa faɗawa su Hafiza da Na'ila tayi akan cewa Yayansu Zaizo gobe, Murna suka hauyi su na tsalle,Na'ila ta ce. "Mama ki bamu kuɗi muje nan Jahun muyi siyayyar kayan abun da zamu girkawa Yaya gobe" Hafiza ta ce. "Eh kuma hakane Sismie kin kawo shawara Mama bamu kuɗin muje" Murmushi Mama tayi ta ce. "Wannan yara, to kuje ku buɗe jakata ku ɗauki kuɗin yadda zai muku" suka amsa da to suka miƙe da sauri,Hafiza taje ɗauko kudin, Na'ila kuma taje ɗauko musu hijabansu. Mama ta ce. "Karku jima fa kunga yamma tayi, dama kun bari sai gobe ne tun da babu makaranta" " a'a Mama tun da mun ɗauko kudi bari muje mu dawo kawai" cewar Hafiza. Mama ta ce . "to a dawo lafiya driver ne zai kai ku?" "A'a nan da Jahun din da zamu ɗan taka kawai" "To ai Hafiza naga yamma tayi ne ai" "Karki damu Mama yanzu zamu dawo In sha Allahu" "To Allahu yasha adawi lafiya" suka amsa da ameen suka fice. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️ Tsaye take akan titi fara ce amma ba zaka ce mata sol ba domin kuwa boyeyyan haske gareta,tana da ƙaramin jiki sosai bata da tsayi kuma ba zaka ce mata gajera ba,gashi bata da ƙiba kuma ba zaka sakata alayin ramanmu ba, idan ka kalli fuskata zaka ita karantar yanayin fuskarta,tana da son fara'a dan ko a yanzu fuskarta dauke yake da murmushi ga wani farin tabarau da ta saka a idonta tamƙar doctor. Su Hafiza ne suka zo wucewa, handbag din hannun Hafiza wani Almajiri ya fizge yana shirin ya zunduma da gudu yazo giftawa ta gaban wannan budurwan take ta saka masa kafa ya fadi sannan tayi hanzarin ɗaukar jakar yayinda Hafiza da Naila suka saka kururuwa a cikin jama'a nan aka taro akan wannan almajiri ana shirin a masa rufdugu, kuka ya fara yana bada hakuri akan cewa ba halinsa bane sata yunwace ta saka shi haka. Nan Hafiza ta hana a dakesa sannan ta ciro dubu 2 a cikin jakar tata ta miƙawa almajirin ya karba ya mata godiya,wannan budurwan ta ce. "Kai gaskiya kasarmu ta lalace , innalillahi wainna ilayhirrajiun! Ba dole yara kanana su fara sata ba saboda wahala Allah ya kyauta amma dole nayi rubutu na buga akan hakan" jama'ar wajan suka amsa da ameen, kafin ta mai da kallonta kan su Hafiza nan ta hango tsananin kamannin da suke da juna,murmushi ta sakar musu,haɗa baki sukayi gami da cewa. "Mun gode Anty" Dariya tayi ta ce. "Sunana *ABI'ATU*" Su ma dariyar sukayi. "To Anty Abi'atu" Ta ce. "No ku daina cemin Anty kawai ku kirani da Sunana, baku ga tsawon mu daya ba?" Murmushi Hafiza tayi ta ce. "Eh hakane amma ai kin girme mu" Ita dai murmushin tayi dan ɗabiar fuskarta ce murmushi ta ce. "To shikenan baku faɗamin sunayen ku ba?" ta fada maganar tana kallon Hafiza. Hafiza ta ce. "Sunana Hafiza sismie kuma sunanta Na'ila" Murmushi tayi ta ce. "Nyc to meet urs, ni bakuwa ce a wannan unguwar gidan mu yana can wajan bayan masallacin sallar Jumma'a yanzu kuma na fito siyayya ne amma fa kun burgeni ku twins ne?" "Aa mu ba twins bane ,amma ratan dake tsakaninmu ba yawa, muma gidanmu yana can wajan masallacin" Ta ce. "Da gaske?" suka jinjina mata kai, nan ta ce. "To muje mu gama sai naje naga gidan ku kuma ku ga namu ko za'adinga gaisawa ko?" suka amsa da to. Bayan sun gama siyayyar tasu sai da suka fara biyawa gidan su Abi'atun wanda gida hudu ne ma kawai a tsakaninsu kafin suka wuce gida daf da magriba. Da sallama suka shiga parlorn Mama ta rufe su da faɗa kan cewa sai yanzu suka dawo, Abi'atu kuwa tun da ta ga Mama taji wani bala'in kunyar Mama ya kamata wanda bata san dalilin hakan ba, ga kwarniji da Mama ta mata. Hakuri suka bata sannan suka bata labarin abun da ya faru da suka fita ,har haduwar su da Abi'atu da zuwa gidan su da sukayi yanzu. Sai a lokacin tukunna Mama ta lura da Abi'atu wacce ra rakub'e a gefen kofar parlour, Mama ta ce. "Sannu ko ƴata ya kike da Mamar taki?" Zubewa kasa Abi'atu tayi tana dukar da kai kasa ta gaishe da Mama. Take Mama taji yarinyar ta kwanta mata a rai. Na'ila ta ce. "Mama wannan gidan da aka ginasa kwanan nan, wanda gida hudu ne a tsakanin mu na wancan kwanar shine fa ashe gidansu" Mama ta ce. "Ayyo ai kuwa ranar da zanje gidan su Umma mun haɗu da Mamanki mun gaisa"ita dai Abi'atu kanta a sun kuye ta kasa sakewa. Mama ta ce. " ku tashi ku shiga ciki kuyi sallar magriba, sai ku kawo mata abinci da abun sha, ku kwashe wannan kayan kuma ku kaisu kitchen" suka amsa da to,sannan suka ɗibi kayan sukayi kitchen, sai da Abi'atu ta ga Mama ta shiga bedroom kafin ta sauke ajiyar zuciya, kamar ance ɗaga kanki nan ta hango ɗan wani lungu tsakiyar TV wanda lungu anyisa dan ajiye pictures, pic din da ta fara tozali dashi wanda ya haifar mata da faduwar gaba wanda harta miƙe taja gaban pic din tana kallo tana shafawa a hankali. Pic din Ubaidullah ne da kakinsa na sojoji yayi matuƙar kyau duk da fuskarsa a pic din babu murmushi, dan guntun tsaki tayi dan ta tsani mutum wanda baya murmushi ya fiye haɗe rai ita ana zubin kenan. Sake ɗaga kai tayi ta ga wanda sukayi ga Mama da Anty Ummu dasu Hafiza nan ta ga yayi murmushi sai da fararen teeth dinsa suka bayyana, itama murmushin tayi ta ce. "Yauwa jarumin maza ko kai fa anan kafi kyau" Gefe ta sake kalla ta gansu su biyu da kaki, a zuciyarta ta ce to wannan kuma fa ko shi da waye, bata san a fili ta faɗa ba sai ji tayi Na'ila ta ce. "Shi da Babban amininsa ne dukkan su Sojoji ne" da sauri Abiatu ta juyo ta kallesu su na mata dariya taji kunya ya kamata ta ce. "Lah kuyi hakuri " ta juya da sauri Na'ila ta riƙota ta ce. "A'a Anty tsaya ki gani, kinga wancan pic din" tayi mata nuni da wani pic a sama wanda bata ma gansa ba sai yanzu, a gefen pic din ta ƙasa anyi rubutu da jan alkalami *R,I,P FATHER*, gaban Abi'atu ya bada dam! Ta juya tana kallon su, taga su na share hawaye, Na'ila ta ci gaba da magana. "Baban mu ne, shi ma kuma soja ne Allah ya masa rasuwa a bakin aikinsa na soja, kinga wannan pic din kuma, da Mama da Babbar Yayarmu Sunanta Anty Ummu, sai Yayanmu sunansa Ubaidullah sai Sismie sai ni, yanzu haka Yayan namu yana aikin sojansa a garin Abuja, wannan pic din kuma shi da Abokinsa ne wanda suka taso tare, gobe kuma idan Allah ya kaimu zaizo" Sosai Abi'atu taji familyn ya burgeta taji kuma tana son ganin Ubaidullah ido da ido amma daga ganinsa za ayi ji da kai da miskilanci. Hafiza ta ce. "Muje muyi sallah fa kar Mama ta fito" Bedroom suka shiga bayan sunyi Sallah Hafiza ta fita domin kawowa Abiatu abinci. Abiatu ta kalli Naila ta ce. "Sis amma Yayan kun nan yana da ji da kai ko naga baya dariya?" Murmushi Naila tayi ta gyara zama gami da cewa. "Yayanmu baya da ji da kai, amma ya kasance baya son hayaniya da magana, kuma yana da miskilanci, ga zuciya, amma yana da saukin kai ga wa inda suka fahimcesa suka san halinsa, yana da dadin zama domin kuwa yafi karfin Yaya shi ɗin Ubana a wajanmu har ma ga Mama dan itama da bakinta take fadi, Yayanmu yana yaƙi da abubuwa dayawa a rayuwarsa,duk yanda muka zama nagari da taimakonsa ne" Dan murmushi Abi'atu tayi kafin ta tabe baki zata yi magana taji Hafiza na magana a bayansu wanda ta shigo dakin yanzu hannunta da tray din abinci. "Tabbas haka ne duk abun da Naila ta faɗa miki akan Yayanmu,ba shi da girman kai, amma kuma duk wanda basu fahimcesa ba kallon mai girman kai suke masa kamar yanda ke ma yanzu na tabbata haka kike masa" "Aa to kuyi hakuri karku min taron dangi dan da alama kuna son Yayan kun nan sosai" ta fada ta ciro wayarta ta danna video recording. Murmushi Na'ila tayi ta ce. "Idan har muna son shi sosai to shi kaunar mu yake, kuma ba da zuciyarsa yake sonmu ba, da ranshi yake sonmu, to idan har ya so mu da ranshi mu da me zamu so shi?" Dariya Abi'atu tayi ta ce. "To ai na bada hakuri, nace ayi hakuri kar a mun taron dangi a dakeni" A tare suka sa dariya. "Ah haba dai Anty Abi'atu taya zamu miki taron dangi mu da muke so ma idan yazo gobe ku dai-daita ayi yar gida, ko ba haka bane Hafiza?" Hafiza wacce take dariya itama ta ce. "Hakane kam wallahi dan sun dace" Na'ila tana dariya ta ce. "Allah yasa zanga bikin wayyo ni a ranar zan sha rawa bikin Yayana" Nan dai suka ci gaba da hira kamar wanda sun jima da sanin juna, sai da akayi sallar isha'i kafin Yayan Abi'atu mai sunan Safwan yazo suka tafi gida. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️ A bangaren Ubaidullah da Zaidu da KB kuka suka sha ba kaɗan ba suka taya Ubaidullah haɗa kayansa,tun a daren ya sa kayansa a booth. Da washe gari misalin karfi goma A babban filin taro na barracks, dandazon Sojoji ne birjik yayinda, da ka ɗaga kai kaki ne ke kashe maka ido. Ubaidullah tsaye akan Munbarin taro sanye yake da Baƙin wandon jeans da farin t-shart, fuskarsa fayau ba zaka iya gano me fuskarsa da zuciyarsa suka kunsa ba,cike da natsuwa da izza da jarumta ya fara magana cikin harshen turanci. " _Assalamu alaykum da farko ina gaida manya na, tare da abokan aiki ina yiwa kowa fatan Alkhairi, sannan ina neman gafarar wa inda na batawa a barracks din nan, ni na yafewa kowa daga ciki kuwa har wa inda suka kulla min sharri, mahaifina yasha faɗamun lokacin ina yaro kafin yabar duniya,cewa duk wanda ya min sharri na saka masa da alkairi, da babu wanda ya isa yayiwa wani abun da Allah bai masa ba, sai dai idan ya fito acikin littafin kaddararsa, dan haka na dauki kaddarata, kuma na yankewa kaina hukunci, ba lallai dole sai kun yarda dani ba, idan na faɗa kukaji ma ya biya bukata, *BAZAN AURI RUMAISA BA, SABODA BANCI NANIN BA, NANIN BA ZATA CINI BA, A YAU KUMA NA AJIYE AIKINA NA SOJA*._ Maganar da ya gigita su General kenan wanda ya saka su kallon Ubaidullah yayinda hankalin jami'ai sama da dubu ya tashi dan Ubaidullah garkuwa ne a barracks ba za a fahimci hakan ba sai baya nan. Juyawa Ubaidullah yayi ya ajiye takardan a gaban General Of The Army gami da sara masa, sannan ya sarawa su Major, wa inda suke kasa dashi suka sara masa bai jira cewar kowa ba ya wuce da sauri ya bar filin taron take wasu suka fashe da kuka wasu kuma suka shiga ruɗani, wasu kuwa zuciyarsu fes. Cikin ɗimauta Rumaisa ta miƙe da kuka, kamar ta faɗi gaskiya amma wani zuciyar ya haneta. Zeey kuwa suman tsaye tayi na wucin gadi kafin ta juya da gudu tabi bayan Ubaidullah har ya shiga mota su Zaidu su na tsaye, da sauri ta sun kuyar da kanta ta glass tana hawaye ta ce. "Captain am very very sorry for what happen,don't worry i will try my best to find out true i promise, u will come back this barracks very soon" Ta karasa, maganar tana hawaye, ta juya, Ubaidullah ya ce. "Tnk u very much Zeey, but I don't want to come back, don't mind" DA karfi ya figi Motar Sai ga Hawaye na bin fuskar Zaidu, Zeey ta ce. "Captain Zaidu shin kuna tare dani? Zaku taimaka min mu haɗa guiwa mu gano gaskiya ko da Ubaidullah ba zai dawo ba, amma tabon da Rumaisa ta masa ya goge, shin zaku tayani?" Zaidu ya ce. "Muna tare dake Zeey, nasan ma karya ne Ubaidullah yace bazai dawo ba dan yana son aikin soja, amma gaskiya bana tunanin ko zai dawo wannan barracks din, idan kuwa hakan ta kasance tabbas zan bar barrack din nan nima" ya na gama fadi ya juya da sauri KB ya bi bayansa Zeey ta kama gabanta domin ta fara bincike akan lamarin. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Ta bangaren Ubaidullah kuwa yana fita ya kira Mama ya shaida mata cewa gashi nan ya taso Adduar Allah ya tsare hanya ta masa sannan sukayi sallama, ya kira Anty Ummu ya fada mata,itama ta mishi Allah ya kiyaye hanya. ⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️⬇️ Fitowa Mama tayi ta samu Hafiza zaune a Parlour ta ce. "Hafiza wai nikam ina Na'ila ne kam tun safe ban ganta ba?" "Wallahi nima Mama ban ganta ba ,dan tun da mukayi sallar asuba ta fice" Salati Mama ta hauyi tana tafa hannu. "Wato ita dai Naila ba zata taba shiryuwa ba kenan yanzu ina taje da safe dan Allah?" Hafiza ta ce. "Kiyi hakuri Mama bari naje gidansu Anty Abiatu na dubota" Hafiza ta saka hijab dinta ya fice. Ko da taje Ummin Abiatu ta ce mata Naila tazo dazu amma ta tafi dan ko da tazo bata zauna ba, gida Hafiza ta dawo ta fadawa Mama, Mama ta kira Anty Ummu ko taje gidanta ne, Anty Ummu ta cewa Mama tazo amma bata jima ba ta tafi, Mama ta ce. "To ai shikenan zanga ta inda zaki dawo ga Yayanku yana hanya idan da rabon ki sake cin wani na jakin a hannunsa ne to" Naila bata dawo gida ba sai shabiyun Rana da dariyarta da shiga da sallama, Mama da Hafiza su na zaune jigum-jigum, Mama ɗago ta rufe Naila da faɗa. "Yanzu ke Naila ba zaki yi hankali ba? Da za adinga miki magana amma ba zaki ji ba? Ace kullum a tayiwa mutum magana akan abu daya? Naila so kike sai kin kasheni da rashin jin maganarki ko? Ko maganar da kika daukowa Yayanki dani kwanaki ne bai isheki ba? Naila ina miki faɗa ne dan ki gyaru tun ina da raina kafin na mutu ki rasa wanda zai miki, kum...." maganar da Mama bata karasa ba kenan Naila ta rungumeta ta fashe da Kuka. "Dan Allah Mama kiyi hakuri, wallahi ba yawo naje ba tun da nayiwa Yaya Alƙawari na daina ai ban sake ba, Mama ban fita a gidan nan ba fa sai wajan karfe tara, ina part din Yaya ne ina gyara masa,Idan ma baki yarda ba muje ki gani, ko kuma ki tambayi mai gadi, ko da na fita gidansu Umma naje na fada mata yau Yayanmu zaizo take tambayata akan cewa bata san da zancan zuwansu ba, nan muka sha hira dasu afnan, dana tashi shine naje gidansu Anty Abi'atu na fada mata Yayana zaizo yau, daga nan na wuce gidan Big Anty na gaya mata take cemin ta sani, to shine fa naje yelwa tsohuwar unguwarmu na fadawa Gwaggo Ladi Yaya Ubaidulllah zaizo, amma dan Allah Mama kiyi hakuri bazan sake ba" tana maganar tana kuka harda sheshsheƙ. Mama ta ce. "To naji kukan ya isa haka, ni dai so nake ki zama ta kwarai Naila kinga yau ace na mutu bana raye idan ba Ummu da sauran mutanen kwarai ba, babu wanda zai zaunar dake ya faɗa miki gaskiya" "Mama dan Allah ki daina fadin zaki mutu, baba ya mutu kema kina zancan mutuwa to ina zamu saka kanmu?" Murmushi Mama tayi ta ce. "Ai mutuwa ta zama dole Naila ki saka hakan aranki, kullu nafsin za'ikatil maut" Naila ta share hawayenta ta ce. "To In sha Allahu ma zan rigaki Mutuwa Mama,dan ba zaki mutu kibarni ba" ta karasa maganar tana shiga kitchen Hafiza tabi bayanta, Mama kuwa tabisu da kallo duk tana hawaye ga faduwar gaba tana fama dashi. Hafiza ta ce. "Sismie yanzu dame -dame zamu fara yi?" Juyowa Naila tayi ta kalleta sai kuma ta fashe da dariya ta rungumeta tana cewa. "Wallahi ina sonki yar uwata Anty Hafizata" tureta Hafiza tayi tana dariya ta ce. "Allah ya shiryeki Ke kam Naila" aikin suka fara su kwaba wannan su ajiye su hada wancan su ajiye, su na cikin yi Abiatu tazo ta hau tayasu, suka gama haɗa komai nasu, sauran kuma suka ce saiya kusan isowa tukunna sai su haɗa. Wanka sukayi kafin suka yi sallar azahar suka fito parlour, Abiatu tayi musu sallama ta wuce gida su kuma suka zauna su na kallo Mama ta fito ta kallesu ta ce. "Naila gashi wannan karba ki kaiwa Babanku( kanin Baban wanda unguwarsu ɗaya) Hafiza kuje ku dawo,har sun mike a tare Naila ta ce. "Sismiena shanyawa Yayana ƙananan kayansa wa inda na wanke ki kwashe ki goge masa sannan ki shiga masa da shoes dinsa wa inda na goge bari na kai sakon na dawo yanzu saina tayaki muyi a tare" Hafiza ta amsa da to. Hijab dinta ta saka harta kai kofar parlour ta juyo ta kalli Mama tana dariya ta ce. "Mamana ina sonki ki yafemin kinji? Hafiza ke ma ki yafemin" Hafiza ta ce. "Ke kam sai kinyi kamar zakiyi hankali sai ki sake karkacewa, ni bani hanya na wuce" Mama ma girgiza kai tana, Naila kuwa dariya ta tuntsire dashi har sai da hakorinta suka bayyana duka sannan ta fice da gudu, Mama ta ce. "Allahu ya shirya min ke Naila" ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ Ubaidullah a hanya motarsa ta lalace da kyar aka gyara masa, yau ga wani Uban goslow a hanya sai kace haɗin baki. Haka dai yake ta fama ya lallaba ya samu ya isa bauchi amma ina har wajan karfe uku kafin ya fita daga cikin garin jos da kyar. A gida kuwa tun fitar Naila har izuwa yanzu bata dawo ba,Mama ta hau mita tana cewa. "Tun karfe daya da minti ashrin na aiki yarinyar nan amma gashi yanzu har uku bata dawo ba,nan nan da gidan Baban ku?" Hafiza tace bari taje ta duba dan ita har ta gama aikin dakin Yayan nasu wanda Naila tace bari taje ta dawo suyi tare. Ko da Hafiza taje gidan Baban nasu nan ya shaida mata da cewa shi ko mai kama da Naila bai gani ba, kafin Hafiza ta dawo sai da ta biya gidan kawayen Naila, amma wasu ma kam cewa sukayi rabon da su ganta sun kai sati, ita kuma Hafiza bata so Yayansu ya dawo ya samu Naila bata nan shiyasa ta dage da nemanta. Gajiya da nemanta Hafiza tayi dan har gidan Anty Ummu taje da gidansu Umma(gidansu Zaidu) amma maganar ɗaya ne Naila bata zo ba,amma tazo da safe nan hankalin Hafiza ya tashi ta hau kuka. Da kuka ta dawo gida zata shiga gate sai ga Abiatu tana tambayarta. " ina Nailan" cikin kuka ta ce. "Ban ganta ba duk inda ya kamata ace na duba ta ban ganta ba" Dafe ƙirji Abiatu tayi tace muje mu faɗawa Mama asan abunyi. Ko da suka faɗawa Mama cewa tayi. "Naila ce fa ko kin manta halinta ne Hafiza" Cikin kuka Hafiza ta hau girgiza kai. "Aa Mama wallahi Naila ta canza,Duk gidansu kawayenta naje amma bata nan wasu ma kam wai sun kai sati basu ganta ba, Mama Naila ba zataje wani waje ba, bayan tasan yau Yaya zai dawo" shuru Mama tayi tana nazarin maganar Hafiza kafin taji ƙirjinta ya bada dam!dam!dam!. Ai nan Mama ta dauki hijab suka fita neman Naila har kasuwa amma basu ganta ba, har akayi sallar la'asar amma ba Naila, nan su Afnan dasu Umma da Inna suka zo domin su ji ko Naila ta dawo amma bata dawo ba,kafin wannan lokacin Mama ta fara fita hayyacinta, ta kira Ummu ta ce tazo yanzu, nan aka sake bazama neman Naila amma shuru har da yan gidan su Abi'atu. Ubaidullah bai shigo bauchi ba, sai karfe shidda saura,a lokacin su na tsaye jingum-jingum Ummi mahaifiyar Abi'atu tana tambayarsa shin yaga lokacin da Naila ta fita, mai gami ya ce shi bai gani ba, zata sake yi masa tambaya sukaji ihun Safwan a wajen gate, da gudu suka fito har su na tutture juna, me zasu gani.? Wata motace baƙaƙirim ta juya da mugun gudu tabar layin motar tana shan kwana ta Ubaidullah ta yanko kwana. A kasa kuwa Naila ce kwance jikinta ya baci da jini ko motsi batayi wani razanarniyar ƙara Hafiza ta sake, yayinda Mama tayi baya-baya tangal-tangal zata fadi ko ka ba aduba ba Naila kam fyaɗe aka yi mata, da sauri itama Anty Ummu ta saki Ihu nan unguwa ta rikice, Su Umma(mahaifiyar Zaidu) da Inna sukayi kan Naila wacce take yashe akasa wanwar. Hannunta Inna ta kama ta ɗaga ta saki hannun ya koma nan take Inna ta fashe da kuka tana cewa. "INNALILLAHI WAINNA ILAYHIRRAJIUN! ai babu ita ta rasu" Jin haka ya sanya Hafiza ihun da sai da Ubaidullah yaji, shi da bai kai ga ƙarasowa gate din ba,dan shi hankalinsa yana can akan abun da ya barota a barrack ashe zaizo ya ci karo da wanda ya fita ɗimauta, da sauri ya ɗago kai yana kallo jama'a akan layin nasu, bai karaso ba ya samu gefe yayi parking, dan babu inda zai wuce da mota saboda mutane, kuma ko ba a fada masa ba ihun kanwarsa yaji Hafiza. Cikin hanzari da tashin hankali ya parka motar ya fito. Hafiza kuwa ihun da ta sake ta zube kasa sumammiya, Mama zubewa ƙasa tayi sharab dan ji take komai na jikinta ya daina aiki. Abi'atu itama kan gawar Naila tayi tana ihu tana kuka yayinda Anty Ummu ta rumgume Naila gam a kirjinta tana cewa ki tashi kanwata. Faduwan gaban Ubaidullah ne ya tsananta jin muryoyin yan uwansa gashi kuma jama'ar da suke tsaye a kofar gidan su ne, haka ya dinga kotsa kai har ya samu ya shige, turus ya tsaya yana kallon Mama tana zaune sharab jingine da gate ga Hafiza sume a ƙasa ga Naila rungume a hannun Anty Ummu da wata yarinyar da bai san taba (ABI'ATU) su na Kuka. ji yake kafarsa da gangar jikinsa su na neman gaza ɗaukarsa, murje idonsa yayi ya bude sannan ya wanka wa kansa mari har sau uku amma har yanzu abu ɗaya yake gani a gabansa, durƙusawa yayi, da rarrafe yazo gaban Ummu yasa Hannu yana so ya karbi Naila. Sai a lokacin Anty Ummu ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta kuma fashewa da kuka, a hankali Ubaidullah ya jawo Naila jikinsa yana girgiza ta yaga dilim, ya sa hannu ya bude idonsa ya ga duk sun kafe, dubansa ya kai kasar farin siket din less din dake jikin, wanda yasha yaga ta gefe da gefe ga jini kamar an yanka zakara,wani razanarniya kara Ubaidullahi ya saki tare da furta. "INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!!!!! Noooooo! Innalillahi wainna Ilayhirrajiun!!! Ya Allah karka ɗoramin abun da bazan iya ɗauka ba" ya fashe da kukan rashin hankalin da ba asa masa rana. "Su wayeeeeeeee!!!!! Su wayeeee!!!! Suka aikata min wannan. Ɗanyen aiki?" Ya sake ɗago Naila yana jijjigata. "Kanwata! Kanwata !kanwata! Ki..kki..ki tashi kinji gani nazo!.. Tashi ki faɗamin su waye suka aikata maki hakan kinji Nailata ki tashi..!" Anty Ummu ta rungumesa tana kuka, jama'a da yawa a wajan kuka suke yi, da rarrafe Ubaidullah ya rarrafa da Naila a ƙirjinsa yaje gaban Mama wanda ke zaune kamar babu Ita. "Mama dan Allah ki ce ta tashi Mama wai me ke faruwa ne!? Su waye suka aikata?" MAMA kallon Naila tayi babu abun da ya faɗo mata rai sai dazu da zata fita, ta juya ta fashe da dariya ta ce. "Mama ina sonki ki yafe min" sai kuma lokacin da take mata fada ta ke cewa. "In sha Allahu ni zan rigaki Mutuwa Mama" Kuka bai ban tausayi da tsuma zuciya gami da tashar da hankali Mama ta sa ta rungume gawar Naila. ➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰ 💲To🅿️ *STOP* _A YAU NA DAKATAR DA RUBUTA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH SABODA WASU DALILAI NA MASU KARFI._ NA FARKO. _KAFIN NA FARA RUBUTA BUK DIN NAN SAI DA NA FUSKANCI KALU BALE MAI TARIN YAWA, WANDA NAYI HAKURI NA SHANYE NA CI GABA DA RUBUTAWA, A INA RUBUTUN MA ZUCIYATA BA ADAINA BATA MIN ITA BA_ _BAN CIKA SON INA BABATU AKAN MAGANA DAYA BA , GASKIA DAN NIMA INA DA ABUNYI_ NA BIYU. _YANDA NASHA KALUBALE WAJAN RUBUTA LITTAFIN NAN KAMATA YAYI ACE KU FANS DINA KU KARAMIN KARFIN GUIWA HAR MUJE KARSHR KAMAR YANDA KUKA FARA A FARKO AMMA SAI KUKA SA JIKINA YAYI SANYI, A HAKAN BAWAI NA GAMA DA KALUBALEN DANA FUSKANTA BANE_ _KARFIN GUIWAR KUWA TA HANYAR YIMIN DOGON SHARHI NE A LITTAFIN, SANNAN KU DINGA TATTAUNA ABUN DA KUKA FAHIMTA A LITTAFIN DA ABUNDA KUKA KARO DA WANDA YA BAKU HAUSHI DA WANDA YA BAKU DARIYA, DOMIN NA GANE SAKON DA NAKE SON ISARWA YANA ISA YADDA YA KAMATA, AMMA BUN TAKAICI WAI NA TURO LITTAFI WASU MA KAM SAI DAI SU KARANTA SUYI SHURU ABUN HAUSHI KUMA BANYI TYPING BA A ISHENI DA WAI CI GABA, TO YAYA ZAN CI GABA KUWA? BAYAN BAKU BANI GOYON BAYA 100%BA, ZAN ZAUNA NA KASHE AIKIN GIDANA DA KULA DA YARANA, NA ZAUNA NA ZUBA MUKU TYPING KUSAN 4TO5 READMORE AMMA KU 1READMORE JUST FOR DOGON SHARHIN DA ZAI FARANTA MIN YA GAGAREKU._ _KWANAKI DA NAYI MAGANA, WATA MARAR KUNYA TA BINI PC TANA GAYA MIN CANZAN BANZA, NAN MA KYALETA KAWAI NAYI WLH DAN BANA SON DOGON TURANCI_ *_DAN HAKA BAZAN CI GABA DA RUBUTA LITTAFIN NAN BA KO DA KUWA, ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH NE_* _INA GODIYA GA DUK MASOYANA WA INDA NA SANI DA WAINDA BAN SANI BA,INA MIKO MUKU GAISUWA TARE DA FATAN ALKAIRI_ ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE A DUK GARIN DA KUKE INA ALFAHARI DAKU. SANNAN INA NEMAN AFUWAR WA INDA NA BATA MUSU TARE DA NEMAN GAFARA KU YAFEMIN NIMA NA YAFEWA KOWA,ALLAH KUMA YA YAFE MANA GABAKI ƊAYAN MU. DAGA KARSHE INA ROKON MANA GAFARAR UBANGIJI,ALLAH YA YAFE MANA ZUNUBANMU YA GAFARTA MANA, YA YAYE MANA WANNAN ANNO BA TA CUTAR CORONAVIRUS(COVID19)ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN. SADUWAR ALƘAIRI DAGA. ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN. BISSALAM. [8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°37&40* Ta rungume gawar Na'ila a jikinta, tama kasa magana banda kukan da take yi tana girgiza kai tare da jijjiga Na'ila, da kyar Mama ta iya fizgar magana a bakinta muryarta harta canza kala tsananin tashin hankali. "Ƴata! Yarinyata Na'ila! Dan Allah ki tashi!" Cike da ɗimauta Mama take magana, Ubaidullah ji yake duniyar tayi masa zafi har wani duhu-duhu yake gani, ga kansa dake juya masa, komai ya cakuɗe masa, yanzu sam yaji baya gane komai. Jama'ar dake tsaye a wajan banda kukan tausayi babu abinda sukeyi dan tausayi iya tausayi sunji ma wa innan familyn yarinya da aka zo har kofar gate din gidan su, aka cilla gawarta. Ana nan a tsaye cirko-cirko kowa ya rasa abun yi, an rasa mai lallashin wa innan bayin Allah, har kuma yanzu Hafiza bata farka daga sumar da tayi ba, itama tana nan a kwance a kasa. Mahaifin su Abi'atu ne ya dawo yaga mutane rututu akan layin nasu, gabansa ne ya fadi ya ce. "To meke faruwa ne haka a arean tamu ko dai mutuwa akayi ne?" yana tambayar kansa yayinda ya samu waje yayi parking din motarsa ya fito. Cikin ikon Allah kuwa ya hango babban ɗansa Safwan a cikin mutanen yana tsaye a gefe yana share hawaye. Karasowa Baban su Safwan yayi ya dafa kafaɗar dan nasa yake tambayarsa kan meya faru, nan Safwan ya kwashe komai ya fadawa Mahaifin nasu. Baban su Safwan shine wanda yaje ya dafa Ubaidullah wanda da kayi masa kallo ɗaya zaka gane babu hankalin da natsuwa a tare dashi duk ya fice daga hayyacinsa. Kallonsa da kyau Baban su Safwan yayi kafin yayi karfin hali irin nasu na manya ya ce. "Haba ɗana kana namiji da kai, kuma daga ganinka kai din jarumin maza ne taya zaka saka mata a gaba kana kuka? Bai dace da kai ba plss, kayi hakuri, ku tashi mu kai yarinyar Asibiti a dubata, a tabbatar da abun da ya sameta watakila ma ba mutuwa tayi ba" Ya juya ya ce. "Am Safwan ɗauko mota, ku kuma dan Allah ku ɗan matsa a wuce" Kamar mahaukaci haka Ubaidullah ya suri Na'ila, yayinda Safwan ya juya da gudu domin yaja mota, jama'ar dake wajan suka matsa. Safwan yana kawo mota Ubaidullah ya shige gidan baya rungume da Na'ila a ƙirjinsa, Inna ta cire mayafinta ta miƙawa Ubaidullah ta ce ya rufewa Na'ilan jiki dashi. Karba kawai yayi ba tare da yayi magana ba, Umma (mahaifiyar su Zaidu) da Inna da Mama su ne suka ɗauki Hafiza wacce tayi shame-shame a kasa tamƙar itama babu rai a tattare da ita, suka sakata a motar. Baban su Safwan ya shige gidan gaba, Ubaidullah a baya shi da Na'ila ga Hafiza a gefensa itama. Ta window Baban Safwan ya leƙo ya kira Ummin su Abi'atun akan ta shigo gidan baya su zauna tare da Ubaidullah da Na'ilan idan yaso saita rungume Hafiza, tun da Abi'atu ta iya mota sai su taho dasu Mama da Umma da Inna, da kuma Anty Ummu. Hakan kuwa akayi Ubaidullah ya juya ya kalli Abi'atu dake tsaye wacce itama kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin hayyacinta, ya ce. "Idan har zaki iya driving motata tana can gefe akwai key a jiki, ki tuƙa kuzo dashi" ba ta iya ta amsa masa ba illa gyaɗa masa kai da tayi alamun to, sannan Safwan ya figi motar da karfin tsiya suka dauki hanyar Specialist hospital. Da kyar itama Abi'atu taje suka shiga taja motar Ubaidullah suka mara musu baya, amma me kafin su bisu sun bace musu Abi'atu ta ce. "Ban san fa wani asibiti suka nufa ba gashi sun bace mana" Inna ta ce. "To banda abunki ƴarnan ba bature ya kawo mana sauki ba, ina salularki, maza ki kira Umminki ki tambayeta kiji, haka kuwa akayi, ta kira Mamanta ta faɗa mata asibitin da suka nufa. Cikin gaggawa aka fara karban Na'ila, kafin akazo itama aka karbi Hafiza duk akayi emergency dasu. Ban da zirya babu abun da Ubaidullah yake yi, Adduarsa ɗaya Allah yasa kanwarsa tana raye bata mutu ba, sannan ta faɗa masa suwaye suka aikata wannan ɗanyen aiki. Baban su Safwan ne ya dafa Ubaidullah dan a lokacin har kusan karfe takwass da wani abu ya ce. "Ɗana ba muyi Sallar magriba bafa ga kuma Isha'i, Safwan kuzo muje muyi Sallah" ya juya ga su Umma Ummi(mahaifiyar su Abi'atu) da Inna da Mama ya ce. "Ku ma ku tashi ku kai farali sannan muyi wa yaran nan addua tun da har yanzu likitoci basu fito ba, balle mu san halin da yaran suke ciki" da to suka amsa sannan suka fita dan yin sallah mazan kuma sukayi masallacin dake cikin hospital din. Bayan sun idar da Sallah Ubaidullah ya jima yana kwararo addua inda a karshe ya sake fashewa da kuka dan ya kasa control din zuciyarsa. Har ila yau dai Baban su Safwan ne ya ci gaba da lallashinsa, ɗago kai Ubaidullah yayi ya kallesa ya ce. "Alhaji ban sanka ba amma naji dadin kulawarka a garemu Allah ya saka da alkhairi" Ɗan Murmushi yayi ya ce. "Ba komai ɗana amma karka sake kirana da Alhaji ka kirani da Abba dan haka yarana suke kirana, kuma ina ganinka naji ka shiga raina, ba lokacin da zaka san ko ni waye bane, bari komai ya dawo dai-dai, but still ya kamata ka sani, ni maƙocine gare ku, ban jima da dawowa unguwar ba" jinjina kai kawai Ubaidullah yayi, dan ko ba komai da yayi sallah yayi addua sai yaji sauki a ransa. Da haka suka tashi suka koma cikin asibitin har yanzu su Mama su na zaune jingum-jingum, Mama Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki gashi itama ba lafiyar gareta sosai ba, tunda hawan jini gareta. Sai wajan karfe goma kafin wani likita ya fito ya cire marks din face dinsa yana sharbe gumi ya ce. "Alhamdulillah mun samu damar ceto rayuwar dayan yarinyar kuma munyi mata allura, za a fito da ita nan da wani ƙanƙanin lokaci zata farka In sha Allah, amma ɗayar gaski......" sai yayi shuru bai karasa maganarsa ba yayinda Mama ta rintse idanunta gam zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Abba( mahaifin su Safwan) ya ce. "Likita ka faɗamin halin da ƴata take ciki dan Allah?" Ubaidullah tamƙar shuka haka ya tsaya ya kasa katabus, Anty Ummu kuwa ta fashe da kuka tana cewa. "Dan Allah likita karka ce min kanwata rasuwa tayi na roƙe ka!" cike da tashin hankali ta karasa maganar Umma itama hawaye take yi tana lallashin Anty Ummu yayinda Inna take dannar Mama, Abi'atu kuwa can gefe ta rakub'e tana kuka mai cin zuciya. Likita yayi gyaran murya cike da tausayin ganin halin da suke ciki ya ce. "Kuyi hakuri ku kwantar da hankalin ku, bata mutu ba, tana raye adduar ku take bukata pls ba kuka ba, amm Alhaji ina son ganinka a office dina kai da wannan" ya nuna Ubaidullah da Safwan tun da yaga sune maza. Da sauri kuwa suka bi likita office dinsa, cikin harzari Ubaidullah ya ce. " na roƙeka doctor ka fadamin gaskia a wani halin kanwata take ciki karka boye min?" yana magana hawaye na ambaliya a fuskarsa dan bai san adadin kaunar da yake yiwa yan uwansa ba. Cike da damuwa likita ya fara koro jawabi. "A gaskiya sai dai kuyi hakuri, dan yarinyar nan fyaɗe aka yi mata, dan gaskiya idan zata rayu to sai dai wani ikon Allah ,dan gabaki ɗayan gabanta yayi damager, and a iyakar binciken mu ba Namiji ɗaya bane ya danneta mazan da suka hau kanta zasu kai biyar and she's to young ace maza biyar sun danneta a lokaci ɗaya gata virgin ce, babbar mace ko a first nyt tana shan wahala tun da ranar da aka fara buɗata kenan, namiji ɗaya, to balle ita wannan yarinya ce karama, kuma da karfi suka shigeta, duk sun dagargaza mat....." maganar da Ubaidullah bai jira likita ya karasa ba ya saki ihu ya kwanta kasa yana birgima. Da sauri Abba da Safwan suka yo kansa, kuka yake yana toshe kunnuwansa dan ji yake sun gaza daukar jawabin likita. Da kyar Abba da Safwan da likita suka ɗago Ubaidullah wanda duk ilahirin jikinsa rawa take ga jijiyoyin jikinsa da suka miƙe a tsaye kiƙam kana ganin su zara-zara, Abba ya share hawaye ya ce. "Doctor yanzu miye abun yi" Girgiza kai yayi ya ce. "Gaskiya bazan boye muku ba, mu munyi iya yinmu sai kuma ta Allah" doctor yana gama fadi ya fice. Haka suka tashi Abba yana riƙe da Ubaidullah, room din suka shiga tana kwance an rufeta da farin yadin asibiti fuskarta ce kawai a buɗe, wajan kasanta kuma an saka mata wani abu an rufe wajan dashi, kasa jurewa Mama tayi ta juya ta fice tana kuka. Ubaidullah ne ya karasa jikin gadon ya kamo hannunta ya fara magana da muryarsa da bata fita. "Na roƙe ki kanwata ki tashi ki faɗamin suwaye suka miki! " wata norse ce ta shigo ta ce musu. "Pls ban da hayaniya dan anyi mata alluran hutu" tana gama faɗi ta fice abunta. Umma da Inna da Ummi suka fice, suka yi dakin da aka kwantar da Hafiza, itama an ɗaura mata ruwa, anan suka zauna aka bar Ubaidullah da Abi'atu Anty Ummu da Abba da Safwan, Abba ya ce. "Ɗana ku zo muje gida idan yaso mu kawo abun bukata" girgiza kai Yayi alamun A'a baza shi ba, babu yanda Abba bai yiba amma Ubaidullah ya ƙi sam, Abi'atu ma tazo suje ita ma tace sam ba zata je ba, haka Abba da Safwan suka baro asibitin da sunan zasu dawo da asuba. Haka suka zauna cirko-cirko abinci kuwa babu wanda yayi tunaninta ko ya bi ta kanta. Da asuba da kyar Ubaidullah ya tashi ya tafi masallaci, itama Abi'atu da Anty Ummu suka nufi dakin da aka kwantar da Hafiza nan sukayi Sallar asuba aka ɗan gaggaisa sama-sama. Ubaidullah ya dawo kenan daga masallaci zai shiga ya duba Hafiza sai yaji yo ihun Na'ila da karfi take furta kalmar. "Innalillahi wainna ilayhirrajiun!innalillahi wainna ilayhirrajun! Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Yayana!! Mamana!! Hafizata!! Anty Ummuna!! zasu kashe! zan mutu! Wayyoo Anty Abi'atu! Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!"" Da mugun gudu Ubaidullah yayi dakin da Na'ila ke zunduma ihu , Duk da ihun muryarta a dashe yake, ga wani baƙin azaban da take ji yana tashi a kasanta tamƙar ana hura mata wutar dalma. A ɗari da saba'in Ubaidullah ya shigo ɗakin ya ɗagota cikin ɗimauta ya hau mata magana. "Kan..kanwata! Gani gani! Gani a kusa dake" Mama da Anty Ummu matsowa sukayi suka kama hannunta gam. Sai juyin azaba take a jikin Yayanta, tambayarta ya kuma akan cewa su waye suka aikata mata haka, amma azaban da take ji ya hanata magana. Cikin dauriya da fizgar magana ta fara magana. "Mam..Mamana..ina Hafizata?" kasa bata amsa akayi ta ci gaba da magana, tana fizge-fizgen azaba. "Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na miki Anty Ummu kema ki yafe min, Yayana kaima ka yafe min, Yaya su bakwai ne suka kamani suk....."maganar da Na'ila bata karasa ba kenan ta koma fizgan kalman shahada a bakinta. Gabaki ɗayan su sun ruɗe da gudu Anty Ummu da Abi'atu suka fita neman likita, zuwa wani lokaci kuma tayi ɗiff ta daina murkususu da fizge-fizgen kamar cutar ya lafa mata. A kiɗime likita dasu Anty Ummu suka shigo, nan doctor ya hau dubata ya gama tattabata sannan ya jawo farin yadin ya rufe mata fuska ya ce. "Sai dai fa kuyi hakuri amma yanzu kam ta cika, ta amsa kiran mahaliccinta" Mama ta kalli hannunta wanda suke sarƙame dana Na'ila ta riƙe gam, doctor yasa hannu ya raba hannun Mama da na Na'ila, tangal-tangal Mama tayi baya ta zube sharab a kasa Umma tayi kanta da sauri, yayinda Abi'atu ta kwalla karan da yayi dai-dai da isowarsu Abba da Safwan. Ubaidullah tamkar almara yake ganin Abun,ihu ya saka gami da cewa. "Haba Na'ila!! Haba Na'ila! Ya zaki min haka? Baki fa fadamin suwaye ba? Dan Allah ki tashi Kanwata!?Kanwata!?Kanwata!? Ki tashi kince su bakwai ne suwaye bakwai din!?" Da karfi yake magana yana jijjigata, su Abba da Safwan da kyar suka b'anb'are Ubaidullah daga jikin gawar Na'ila nan ya hau buge-buge, wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba a sa masa rana, mutuwa kuwa bata sallama da lokaci yayi sai tafiya. 💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖 ALHAMDULILLAH AM BACK MY FANS PLS KARKU BANI KUNYA, YADDA KUKAYI ALKAWARI TO KARKU KARYATA. LATE COMER INA TAYAMU MURNAR ZAGAYOWAR SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN AMMA BA IRINTA 2020 BA. ALLAH KUMA YASA IDAN KUKA KARANTA KUNA MIN SHARING DINSA. ALLAH YABAR SO DA KAUNA MY PPLS ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN TAKU CE😁 [8/19, 10:57 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°41&45* Da kyar Abba ya jawo Ubaidullah suka fita haraban wajen asibitin, Abba ya ɗaga waya ya kira Malam Liman, na unguwar tasu yake sanar dashi akan cewa yarinyar ta cika,Allah ya mata rasuwa, Abba yana gama faɗawa Malam Liman ya kira wasu Aminansa ya ce dan Allah su zo da mota babbar asibitin Specialist za a dauki gawa ne. Ubaidullah na tsaye lokaci guda ya nemi hawayen dake zuba a idonsa ya rasa, idonsa ya ƙafe babu ruwan hawaye, ajiyar zuciya ya koma saukewa ba ƙaƙƙautawa. A can ciki kuwa Inna da Ummi sune suka kamo Mama sukayi waje da ita, yayinda Umma ta kama Anty Ummu da Abi'atu tayi waje dasu su ma. Abokan Abba sun zo su uku da manyan motaci guda Uku da mutane biyar, nan aka tsaya maganar sa hannu a bada gawar Na'ila dan aje gida a mata sutura a kaita gidanta na gaskiya. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da misalin karfe bakwai da rabi na safe. Tsaye suke sanye da kakin sojoji a jikin su, Zaidu sai jeka ka dawo yake yi ya kasa zama sai trying din numbern Ubaidullah yake amma yanzu kwata-kwata wayar bata shiga switch up ake ce masa, cike da damuwa gami da faduwar gaba ya ɗago suka hada ido da KB ya ce. "KB har yanzu fa Ubaidullah shuru anya lafiya kuwa? Gaskiya ni jikina baya bani lafiya, rabon da muyi magana dashi tun da ya ce min ya kusan shiga bauchi I told he will call me so that ya sanar dani cewa ya isa lafiya, but shuru fa" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, KB ya ce. "Gaskiya nima jikina yana bani ba lafiya ba, jiya na dauka gajiyar hanya ce ta sashi mantawa damu shiyasa bai kira mu ba, amma kuma Ubaidullah baya makara wajan sallarh asuba,kuma baya rabuwa da wayarsa a kusa dashi, kuma da asuba din nida kai duk mun kirasa bai ɗaga ba, gaskiya ya kamata ka kira Umma ka tambayeta tunda itama Mama ka kira bata ɗaga ba, gaskiya bana tunanin akwai lafiya" Zaidu ya ce. "To taya Umma zata sani? Ko da yake bari na kiranta idan yaso saita aiki Afnan da Manal su je su gani ko lafiya" Zaidu ya hau dealing din Numbern Mamansa, cikin sa'a kuwa a lokacin ita wayar yana hannnunta su na tsaye a waja ana jira Doctor yazo yasa hannu a bada gawar Na'ila, ta ji wayarta na neman agaji, tana dubawa ta ga Zaidu ne ke kiranta, ita tama manta da kiransa shakaf ta fada masa abun da ke faruwa, inama aka ga natsuwar kiraye-kirayen. A lokacin Anty Ummu tana rungume a jikin Umma ita da Abi'atu su na Kuka mai ban tausayi, Umma ta dan ɗaga kansu ta tashi ta koma gefe tana sharbe hawaye da hijabinta kafin tayi karfin halin ɗaga wayar Zaidu. Sallama ya mata ta amsa, a yanda yaji muryarta nan take ƙirjinsa ya bada dam!dam!dam, cikin damuwa ya ce. "Umma lafiya kuwa? Ya naji muryarki kamar kina kuka meya faru? Dan Allah Umma ki fada min meke faruwa,haka kawai naji jikina yana bani gida ba lafiya ba, jiya Ubaidullah ya taho bauchi inata kiran wayarsa bai ɗaga ba yanzu kuma bata shiga, harta Mama na kirata bata ɗaga ba, yanzu kuma na kira ki naji muryarki kamar kina kuka dan Allah Umma meke faruwa?" ya karasa maganar kamar zaiyi kuka. Duk yadda Umma taso ta daure karta yi abun da zaisa Zaidu ya gane amma ta kasa, bata san lokacin da wani sabon kuka ya b'arke mata ba, cikin kuka ta ce. "Zaidu, duk abun da kakeyi ka ajiyeta ka taho bauchi yau din nan kuma a yanzu, Zaidu babu lafiya,Zaidu ba kalau ba, Zaidu Mama ba zata iya daga waya ba, na tabbata bata san ma inda wayar take ba, Zaidu Abokinka yana cikin babbar damuwa da tashin hankali,Zaidu *NA'ILA TA RASU!! NA'ILA TA RASU!!* Zaidu" Umma ta sake fashewa da kuka. Zaidu bai san lokacin da wayar dake kunnnansa ta fado kasa ba, ya zube a kasa ji yake kamar mafarki yake yi, gabaki ɗaya wani duhu ne ya ziyarci kwakwalwarsa da idanunsa, ganin haka yasa KB saurin ɗaukar wayar yasa a kunnansa, banda shashshekar kuka babu abin da yake ji na tashi, cikin tashin hankali KB ya ce. "Umma lafiya kuwa me yake faruwa ne?" Cikin kuka Umma ta ce. "Rasuwa aka yi ƙanwar abokin ku ce ta rasu, yau da safen nan ta cika a asibiti yanzu haka ma muna asibitin muna jira Likita yazo yasa hannu abamu gawarta muje gida, idan da hali dan Allah ɗana ku taho yanzun nan ku samu jana'izarta , ka taimakawa Zaidu dan nasan yanzu ba zai iya wani ƙwakƙwarar motsi ba" tana gama fadi ta ajiye wayar dan tasan da maganar Zaidu na cewa yana son Na'ila zai jirata ya aureta. Kallon tausayi KB ya hau bin Zaidu dashi ganin yadda ya zube a kasa kamar ba shi ba, tunani KB ya hauyi yanzu ace zasu tafi a mota ai ba zasu samu jana'izar ba, "yanzu miye abun yi?" ya tambayi kansa, nan take ya fice da sauri har yana tuntube. KB bai zarce ko ina ba sai gidan General of the army, dan ma shine yasa aka barsa ya shiga. Nan ya samu ganin General Of The Army yake faɗa masa abun da ya faru, duk da yana jin haushin abun da Ubaidullah yayi na barin aiki amma bashi ya hana General jajantawa ba, KB ya ce. "Sir, nazo neman permission ne zamu tafi bauchi yanzu saboda mu samu jana'izar" "Taya zaku ce zaku tafi bayan kunsan yau akwai meeting ? Wanda ya mutu ai ya mutu Allah ya jikanta, but babu inda zaku je, ina shi Zaidun yake?" Wani kallon rashin imani KB ya bi General dashi kafin ya ce. "Zaidu yana can a ɗaki baya cikin hayyacinsa" General zai sake magana yaji muryar matarsa Hajiya Jameela tana cewa. "Allah ya jikanta amma dole sai kun bisa ne, wai ma ba jiya shi yabar aikin ba?" Kafin General yayi magana sai suka ji muryar ƴarsu Hanan. "Haba Daddy!? Haba Daddy!? Anya Daddy akwai imani kuwa a ranka?" ta fashe da kuka lokaci ɗaya, ta ci gaba da magana. "Daddy ka sha yabon Captain Ubaidullah a lokacin da yake saɗaukar da rayuwarsa domin ya ɗaga darajarka, dan kaddarar sharri ta gitta masa? Wanda duk idanuwan ku suka rufe ku ka kasa fahimtarsa? Na ɗauka kowa a barracks din nan ya fahimci halin Ubaidullah ashe duk ba haka bane, shi da ko maza baya kulawa taya zai kula wannan kuchakar kauyen Rumaisa? Yarinyar da ko class bata dashi,gudun wulakanci ya saka shi ajiye aikinsa duk da so da kaunar da yake yiwa aikinsa, yanzu kuma ance kanwarsa ta rasu zasu je Daddy kace ba zasu je ba, to wlh sai sunje idan kuma kana neman daƙushewar wannan barracks din nan Daddy bismillah ga hanya nan, amma tafiya dole sai sunje ni ma kuma zan bisu!" Tana gama faɗi ta haura sama aka bar General da matarsa baki sake su na kallon yarinyar tasu, juyowa General yayi ya kalli KB, KB ya sara masa ya juya ya fice ,komai ta fanjama fanjam, dan yaji zuciyarsa ta ƙiƙashe shima. Part dinsu ya koma ya samu Zaidu zube a kasa yanda ya barshi. Basu wani tsaya daukar kaya ba, KB ne dai ya sauya kayansa daga kaki zuwa kayan gida riga da wando, amma Zaidu ya kasa wannan, sun fito kenan sai ga wani sergeant da sako daga wajan ɗiyar General Of The Army. Karban Sakon KB yayi ya duba yaga ashe latter ne tayi rubutu kamar haka. " _KB Daddy ya hanani fita karshe ma yasa sojoji tare ni, amma kuje filin jirgi yanzu na siya mana sit mu uku jirgin zata tashi nan da 1hr, tsakanin Abuja da Bauchi indai a jirgi ne 2hrs ne kawai dan haka ku tafi yanzu na bawa Zeey tawa kujerar In sha Allah zaku samu jana'izar na kira Zeey na faɗa mata, yanzu Sergeant Montie zai kai Ku airport ku hanzarta pls_" KB yana gama karanta sakon yayi murmushi gami da cewa. "Allah ya biya ki Hanan, harka da ƴaƴan manya akwai dadi, komai nasu a saukake" KB ya juya zai yiwa Zaidu magana sai ga Zeey kamar an wullota, cikin tashin hankali ta ce. "Yanzu Hanan take faɗa min mummunar labari" KB ya ce. " muje dai yanzu tukunna kar mu makara" Mota suka shiga Sergeant Montie ya dauki hanyar airport. Zaidu tun da Umma ta ce masa *NA'ILA TA RASU* ya kasa banbance yana duniya ne ko akasin haka, burinsa kawai yaje yaga karya ne Lovely dinsa tana nan. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Sai wajan karfe tara kafin aka samu Doctor ya zo yasa hannu aka bada gawar Na'ila. Ubaidullah na tsaye aka fito ana tura gawarta, ganin abun yake kamar shirin film, har aka sakata a daya daga cikin motar Abokan Abba wasu mutum biyu daga cikin mutanen da suka zo, sune zasu ja motar Ubaidullah da wanda Abba da Safwan suka taho dashi. Bayan an gama komai Inna ta ce ita zata zauna da Hafiza, su wuce kawai, haka kuwa akayi har sun fita sun fara jan Mota Hafiza ta farka a haukace drip din da aka daura mata ta fizge shi ta diro daga kan gadon. Da mugun gudu ta dauki hanyar wajan asibiti tana ihu tana cewa. "Wayyo Allah na Na'ilata!! Wayyoo Allah yar Uwata! Ina Yar Uwata!? Wayyo zan mutu!" Da gudu Inna ta bi bayanta a lokacin motar su Ubaidullah ne bai kai ga barin asibitin ba, amma har sun bata wuta, yana cikin motar yaji ihun kanwarsa da sauri ya fito. Can ya hangota kuwa tana gudu tana ihu bata ma san inda zata je ba. Inna tana cewa. "Dan Allah yan uwa ku taimaka min ku riƙe min ita" wasu kuma sun ƙi riƙeta ne dan sun dauka mahaukaciya ce. Da mugu Ubaidullah ya taro kanwarsa tana ganinsa ta sake rushewa da Kuka, jawota jikinsa yayi yana bubbuga bayanta sannan suka jira Inna ta karaso wajan suka shiga mota sai gida. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Unguwar su Ubaidullah kamar an buga tambari haka jama'a suka cika har ba matsaka tsinke, saboda lokacin da Abba ya kira Malam Liman ya faɗa masa yarinyar ta rasu, shi kuma ya fadawa Jama'ar unguwa shiyasa kafin su iso unguwar ta cika da mutane, barin ma Na'ila da take da jama'a saboda gagararta ta shiga nan ta fita can, ga hidima da jama'a shiyasa nan da nan jama'a suka cika layin unguwar tasu. Da kyar aka samu aka wuce bayan an wangale gate din gidan gabaki ɗaya. Direct aka wuce da gawar Na'ila ɗakin Mama domin ayi mata wanka. Lokaci ɗaya Mama ta nemi kukan da ke idonta ta rasasu ,ji take idon ya bushe ƙamas, tana zaune a gefen gawar , su Umma da Ummi(mahaifiyar su Abi'atu) suka shigo da ruwan zafi wanda za'ayiwa Na'ila wanka dashi suka ajiye, suka dubi Mama wacce ta kafe Na'ila da ido ko giftawa bata yi, Umma tazo ta zauna kusa da Mama ta dafata ta ce. "Mama dan Allah kiyi hakuri, ki tashi ki fita, zamu wanketa nida Maman Safwan" Girgiza kai Mama ta shiga yi gami da cewa. " A'a Umma zan tsaya na yiwa ƴata wanka dan muyi sallamar karshe, ku zo muyi mata kawai, zan wanke ƴata, kin gani ko Umma jiya iwarhaka ina tare da ƴata wasa da dariya amma wai yau gata nan kwance a gabana ina so nace mata ina sonki ƴata ko da sau ɗaya ne ta bani amsa amma ina hakan ba zai yu ba, jiya har faɗa sai da nayi mata ashe duniyar ma gabaki ɗaya zata tafi ta bar min, Umma kin ganta kalli fa ki gani kamar bata mutu ba ko zamu koma asibitin ne a sake duba min ita?" Mama ta karasa maganar tana duban Umma. Duk yadda Umma ta so daurewa amma ina ta kasa, sai da Mama ta bata tausayi ta fashe da kuka, itama Ummi hawayen take yi kafin tayi karfin halin cewa. "Dan Allah kuzo mu suturta yarinyar nan a kaita makwancinta,Dan Allah Mama kisawa zuciyarki salama, kiyi dangana, kiyi tawakkali, ki dauki wannan kaddarar,ki ta nanata kalmar INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN! a cikin zuciyarki Dan Allah!" ita ma ta karasa maganar tana sake share hawayen da suka kasa tsayuwa a idonta, Mama ta ce. "To" a sanyaye. Nan suka yiwa Na'ila wanka amma Mama ta kasa tsayawa a shirya Na'ila, dan haka Ummi tayi waje da ita, wani bedroom wanda yake kusa da nasu Na'ilan nan aka saka Mama a ciki ,Mutane sai dannarta suke suna bata hakuri, amma sai dai ta ce. "Uhummm" Dan ji take Numfashinta ya fara Of and down. Hafiza kuwa bayan sun iso gida Inna tana tare da Ita a dakin su, dasu Anty Ummu, Abi'atu, Afnan Manal, sai kuka suke yi, Anty Ummu na zaune bata um bata um um,Hafiza kuwa ta raku'be a jikin Inna jikinta sai rawa yake yi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Karfe goma da rabi jirgin su ya sauka a airport din Bauchi State, ba tare da bata lokaci ba, suka nemi tazi sai a lokacin Zaidu yayi magana. Maganar kuwa unguwar da za akai su ne. Tun da Zaidu ya sauka a Bauchi faduwar gabansa ya tsananta, idonsa kuwa ya zubata kachokar a hanya. Zuciyarsa bai sake tsinkewa ba sai da suka doso unguwar su Ubaidullah tun daga farkon layi yaga jama'a, nan yaji ya fara yaƙi da numfashinsa, drivern ne ya ce sai dai su sauka in ba haka ba, idan ya shiga ba zai iya fitowa da wuri ba. Haka kuwa suka fito, KB ganin yanayin Zaidu yasa shi riƙe Zaidu wanda yake tangali kamar zai ci kasa. Lokacin da su Zaidu suka iso an gama shirya Na'ila tsaf tana kwance a cikin Makara(gadon mulkin kowa kenan Allah kasa mudace Allah kasa mu gama lafiya) parlour aka fito da ita domin yan uwa da abokan arziƙi su mata addua. Mama Anty Ummu Hafiza Ummi Umma Inna har da su Manal da Afnan, wanda tsoro ya gama kamasu. Mama durkushewa tayi a gaban gawar tama rasa wani Addua ne zata fara karantowa, jikinta sai kyarma yake yi, cikin dauriya bakinta na b'ari ta ce. "ALLAH YA YAFE MIKI NA'ILAH, NA YAFE MIKI DUNIYA DA LAHIRA, ALLAH YA SADAKI DA ANNABIN RAHMA S,A,W, ALLAH YA SAKA MIKI ƳATA!" daga haka Mama ta nemi maganar dake bakinta ta rasa abu ɗaya zuciyarta ke nanatawa shine kalmar Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!. Anty Ummu cikin kuka ta yiwa Na'ila Addua tare da kalamai masu ban tausayi da karya zuciyar duk wani mai imani, haka ma su Afnan ba abarsu a baya ba sun yiwa kawarsu addua, su Umma da kowa da kowa anyiwa Na'ila Addua amma banda Hafiza da take bin mutanen wajan ido. Ubaidullah da su Safwan suka shigo ya duƙa a gaban gawar Na'ila, Hannunsa ya ɗaga sama yana kwararo addua in da a karshe ya fashe da kuka mai tsuma zuciya, kukan da Ubaidullah ya saka yayi dai-dai da shigowar su Zaidu KB da Zeey. Turus Zaidu yaja ya tsaya yana kallon jama'ar dake wajan, da karfin ya ce. "INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN!" Take Ubaidullah da sauran mutane wajan suka ɗago suna kallon Zaidu. Da rarrafe Zaidu ya karaso gaban gawar yana binta da kallo kafin ya kalli Amininsa cikin fitar hayyaci ya ce. "My Man !pls karka ce min Lovely ne kwance anan zuciyata ba zata iya dauka ba, pls Mama Umma ku bani amsa mana, dan Allah ina my lovely take" ya juya yana kallon Hafiza wacce ta kurawa mutane wajan ido tana bin su da kallo tamƙar tab'abb'iya, tun fitowar su bata ce komai ba, dan bata yarda yar uwarta bace kwance a gabanta ba. "My sister ina lovely take nasan ke ba zaki min karya ba?" Umma ta ce. "Zaid ban son shashanci!" Ummi ta ce. "A'a bari a buɗe mata fuska su gani" Nan Ummi da wata mata makwabciyar su Mama suka warware likafanin fuskar Na'ila ya bayyana, Zaidu kusan haukacewa yayi ganin abun bana kare bane yasa su Umma sake rufe fuskar Na'ila sannan suka yiwa mazan dake waje magana azo a dauke ta, ganin haka yasa Hafiza sakin ihu gami da riƙe makaran gam, tana cewa. "Wayyo Allah na! Wayyo na shiga ukuna! Ina zaku kai min yar uwata! Dan Allah ku ajiye min ita, ba mutuwa tayi ba bacci fa take dan Allah ku ajiye min yar uwata! Wayyo Allah zan mutu, Na'ilata! Wayyo Allah Na'ilata! Yar uwata! Dan Allah karku tafi min da yar uwata! Ina zaku kai min ita mugaye azzalumai! Mama kina gani ko? Yaya zasu tafi min da Yar Uwata! Anty Ummu kice su ajiye min yar uwata!" Da kyar aka b'anb'ari Hafiza daga gawar Na'ila aka fice, ana fita da gawar Mama ta yanki jiki ta fadi, Anty Ummu itama tayi baya-baya ta zube kasa aka bar Hafiza tana ta kururuwa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Comments Share Momyn Ahlan Taku ce😟 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_jinjina da dubun gaisuwa gareku masoyana dan Allah ku ce min kun amsa 🙋🏻 Alkhairin Allah ya kai muku har garin da kuke har cikin ɗakunar ku, masu cmmnts ina yi muku sonso domin Allah, marasa cmmnts kuma na gaisheku 🙋🏻, babbar kyauta ga wa inda suke following dina a wattpad, jinjina gareku masu min cmmnts a wattpad 🙋🏻, kar de ku manta da cewa Momyn Ahlan TAKU CE 😁_* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°46&50* Da sauri jama'ar da suke wajen suka yo kan Mama aka hau jijjigata amma shuru, cikin Kuka Ummi ta ce. "Ina ga fa asibiti zamu kai su, ina Abi'at..." maganar da Ummi bata karasa ba kenan ta ga Abi'atu shame-shame ita ma a kasa, salati Ummi ta saka tana share hawaye, nan dai matan da suke wajan suka taimaka aka ɗaga Mama aka kwantar da ita akan dogon kujera aka cire hijabin dake jikinta aka hau mata fifita ana yayyafa mata ruwa. Haka ma Anty Ummu da Abi'atu ruwa aka yayyafa musu suka farfaɗo,tukunna aka maida hankali kan Mama sosai ake yayyafa mata ruwa ana mata fifita, amma ina kamar ba a yi mata komai, wata mata ce a cikin yan gaisuwa ta ce. "Gaskiya ni a nawa shawaran ya kamata ace a kira Likita yazo gida ya dubata, dan gaskiya bai kamata a kaita asibiti ba, hankali ne zai rabu ko ya ku ka ce?" Umma ta ce. "Eh haka ne akwai wata kawata Likita ce tana aiki a Rimi Hospital bari na kirata" Umma ta ɗaga waya ta kira kawarta cikin sa'a kuwa ya shiga ta shaida mata cewa zata zo kafin suka yi Sallama. A daki kuwa Hafiza ta gama haukacewa Inna da wata tsohuwa su ne suketa kokarin lallashin Hafiza amma ina kamar ba da ita suke ba, ihu kawai take yi tana cewa a dawo mata da yar uwarta. Inna ta kamo fuskarta ta ce. "Hafiza!HafizaHafiza! Kalleni nan kalli fuskata, ina so na tambayeki ki jini da kyau, kina jina?" ta gyaɗa kai alamun eh tana fizge-fizge. Inna ta ce. "Hafiza kin yarda da Allah?" ta gyada kai. "Kin yarda kullu nafsin za'ikatil maut ne?" ta sake gyaɗa kai. "Kin yarda da kaddara mai kyau da marar kyau?" Nan ma sake gyaɗa kai tayi. Inna ta ce. "To Hafiza tun da kin yarda da Allah kin yarda da akwai mutuwa kuma kowa zai mutu babu wanda yazo zama a wannan duniyar, kuma kin yarda da kaddara ina so ki daina yiwa yar uwarki kuka kina ihu, itama ba zata so haka ba, ki dinga mata addua Allah ya jikanta da rahma Allah yasa can yafi mata nan kinji? Barin ma Na'ila baki ga yadda tayi jama'a bane, ko ba kiji ance mutanen da suka yi mata sallah sun kai kusan dari da wani abu bane? Ai abun farin cikin mu ne, uwa uba kuma wasu azzalumai ne suka yi sanadiyar barinta duniya kinga kuwa da yardan Allah ita kam ta dace kinji? Ki daina ihu da kukan nan ki tayi mata addua kina yawan fadin kalman Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Kinji Hafiza?" Ta ce. "To Inna na bari" shuru tayi na wasu lokaci kafin zuwa anjima da ta ɗaga kanta ta hango hoton su wanda suka yi da Sallah sun rungume Juna su na dariya, nan Hafiza ta sake birkicewa ta sake sakin wani ihun. "Wayyo Allah Yar Uwata!! Wayyo Na'ilata dan Allah ki dawo!" Inna hakurinta da dauriyarta ya kare dan haka suka fice tana share hawaye aka kulle Hafiza da su Afnan a daki su na kuka babu mai ce ma dan uwansa yi hakuri. Parlour wajan karban gaisuwa Inna suka koma suka zauna wata makwabciyar su take tambayar Inna akan cewa Hafizan tayi shuru kuwa, Inna ta ce. "Ina kuwa , da kamar tayi shuru da muka lallasheta amma tana ganin hotonta da yar uwar ta sake birkicewa" Matar ta girgiza kai gami da cewa. " Allah Sarki! Dole ta fita hayyacinta, kullum zaki gansu tare, idan makaranta ne ko aiken su aka yi, ko wani waje ne tare zaki gansu, gashi itama Hafizan yarinya ce bata saba da mutuwar ba, tun da ko lokacin da Mahaifinsu ya rasu su na yara ne, Na'ila kuma basu taba rabuwa ba, ko wani garin zasu je indai kwana ne tare suke tafiya, amma lokaci daya mai yanke kauna ta yanke a tsakaninsu dole sai an haɗa mata da rubutu, gashi irin wannan mutuwa na farat ɗaya tafi shiga jiki, Allah na tuba gwanda ace mutum ka ganshi yasha jinya a gabanka,amma ka rabu da yaro lami lafiya adawo maka da gawa, abun akwai tashin hankali gaskiya, Allah dai ya karawa yan uwanta hakuri da juriyar rashinta" aka amsa da Amin. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Bayan an yiwa Na'ila Sallah a kofar Masallacin Jumma'ar dake unguwarsu kafin suka wuce maƙabarta. Aka siya kabari aka yi komai,amma kafin nan sai da aka faɗi sunanta aka rubuta da date din da ta rasu da cutar da ya yi sanadiyar mutuwar tata da shekarunta. Ubaidullah da Zaidu da KB Safwan da wasu samari Uku tsaye a gefe, wani Malami ya ce. "Ita mai rasuwar tana da miji ne?" Malam Liman ya amsa da. "A'a" "To ina Mahaifinta?" Ubaidullah ya rintse ido yana karanto "Innalillah wa inna ilayhirrajiun!" Wani ƙanin Baban su ne ya ce. "Mahaifin su ya rasu da ɗaɗewa" Malamin ya ce. "To ina wani ɗan uwa makusancinta ya matso kusa ya sakata a kabarinta" Jikin Ubaidullah ya dauki kyarma, sai da Abba da Baba (Yayan Baban su) suka dafa Ubaidullah kafin ya wuce ya kamo kanwarsa yana yi mata kallon karshe a cikin likafani, zuciyarsa ce ke cewa. "Yanzu Na'ilata kece wannan? Kece zan shinfiɗaki a karkashin kasa?" nan hawaye ya shiga wanke masa fuska har yana ɗiga akan likafaninta, babu abun da ya faɗo masa sai ranar da suka fita ya jibgesu ita da kawayenta, kuka sosai Ubaidulllah ke yi yana kwantar da ita a cikin kasa, yana gama shinfiɗeta ya ce. "Allah yasa Annabi S,A,W, yasan da zuwanki Kanwata Allah yasa Annabin Rahma S,A,W, ya karbi baƙuntarki, ki yafe min Kanwata nima na yafe miki!" ya karasa yana kuka har da sheshsheƙa. Zaidu ma Kuka yake yi kamar ranshi zai fita ya duƙa yana cewa. "Allah ya haskaka ki My Lovely, Allah ya yafe miki..!" kasa karasa sauran adduar yayi kuka yaci karfinsa nan aka hau mai da kasa akan Na'ila yayinda Ubaidullah da Zaidu suka koma gefe suka rungume juna gam su na kuka mai ban tausayi. Tun su na kallon likafanin Na'ila har aka gama tula mata kasa a kai ya yi tsini. ( _Hummm Rayuwar kenan fa, ta bakin hausawa suka ce karshen alewa kasa, duk kudinka duk mulkinka dun kyawunka, duk kasaitar ka, duk izzarka, da zarar ance wannan ran ya fita a gangar jikinka nan ne madakatar ka, Allah kasa mu gama da duniya lafiya Ameen_) An juma ana yi mata addua kusan awa daya kafin jama'a suka fara watsewa. Sai da kowa ya watse aka bar Ubaidullah Zaidu KB Safwan Abba da Abokan Abba mutum biyu. Da kyar aka lallashi Ubaidullah da Zaidu suka tashi suka baro maƙabartan, su na tafiya su na kallon maƙabarta har suka daina ganinta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A gida kuwa Likita tazo ta duba Mama har anyi mata karin ruwa, ta farfado amma bata um bare um um, saboda hawan jininta ya tashi sosai. Hafiza kuwa sai da aka yi mata alluran bacci kusan biyar kafin bacci ya dauketa. Su Ubaidullah su na dawowa daga maƙabarta nan fa sabon kuka ya tashi. Anty Ummu ta shiga dakin su Na'ilan tana kallon pic dinsu da Hafiza, kuka Anty Ummu keyi kamar ranta zai fita tana cewa. "Yanzu shi kenan fa kin tafi kenan, Allah sarki kanwata ashe ban kwana kika zo min jiya da safe, Allah sarki Na'ila Allah ya gafarta maki kanwata" ta ci gaba da kuka. Ubaidullah part dinsa ya wuce kai tsaye bayan an dawo daga maƙabarta ana parking din mota ya fice, Zaidu da KB suka bi bayansa. Yana shiga parlour ya fara fashe-fashe yana ihu, ba mutuwar bane abun da yafi ɗaga masa hankali da ɗimauta shi ba, a'a yadda mutuwar kanwar tasa ta kasance yasan mutuwa dole ce, baƙin ciki ne ke cin zuciyarsa idan ya tuno sanadiyar abun da ya kai kanwarsa kasa yau. A rayuwarsa ya tsani yaji kalma mai kaman ceceniya da *FYAƊE* idan aka kawo case akan fyaɗe sai inda karfinsa a kare amma sai gashi kanwarsa sanadin fyaɗe ta mutu ta rasa ranta,sunyi sanadiyar kaita cikin kasa, taya zai yafe? taya zai daina yaƙi da masu fyaɗe? taya ba zai kara tsanar fyaɗe ba? Taya zai gansu? Gashi bai san su ba, bai san ina zai samu mutane bakwai din nan ba, idan ma yace bincike zai yi ta ina zai fara? Ita ce ya kamata ta gaya masa suwaye amma Ubangiji ya karb'i abunsa hannunsa biyu ya zuba a kansa yana kuka mai ciwo, babu abun da ya sake faɗo masa rai sai lokacin da take fizge-fizgen azabar fitar rai take ce masa. "Yaya su bakwai ne!" Ihu Ubaidullah ya sake gami da dauƙar glass din table din da ya fara nan take ya farke hannunsa dashi, kuka yake ina faɗin. "Ina zan gan kuuuuu!! Wayyo Allah ni Ubaidullah! Ya Allah kabani ikon cin wannan jarabawar da ka ɗaura min! Lokaci ɗaya na rasa abu biyu masu mahimmanci a gareni mafi soyuwa wanda ka karb'eta a gareni itace kanwata, Ya Allah hakika ina son yar uwata amma ka fimu sonta, Allah kai ne ka halicce mu, kuma dole zamu koma gareka, ya Allah nasan kanwata daka ɗauketa yanzu bata yi sauri ba, mu kuma daga barmu ba muyi jinkiri ba, Ya Allah ka sassauta mana raɗaɗin rashin baiwarka Kanwata Na'ila, ya Allah ka bayyana min ta inda zan ga azzaluman bayinka, hakika bazan gushe ba, bazan gajiya ba wajan nemo wanda suka aikata min haka na hukuntasu da hannuna ko da kuwa shine abun da zanyi na karshe a rayuwata, Ya Allah ka nuna min suuuu!!" ya zube kasa gami da kifa kansa akan kujera ya ci gaba da kuka. Tun da Ubaidullah ya fara magana Zaidu da KB suke tsaye su na jin maganar tasa tana shiga kansu ɗaya bayan ɗaya, Zaidu ne ya matso kusa da Ubaidullah idonsa jajur ya duƙa gaban Ubaidullah cikin dasheshshiyar muryarsa wanda yasha kuka ya ce. "My Man, ban fahimci maganganunka ba, ina bukatar karin haske, meya samu lovely? Me aka yiwa lovely? Kashe! Lovely aka yi!? Sannan suwaye suka kasheta? Duk tambayar da na yi maka ina bukatar amsar su!?" Shima Ubaidullah ɗaga rinannun idanuwansa yayi wanda idan ya kalleka dasu zaka iya rantsewa idanunsa basu taba fari ba, miƙewa tsaye yayi cikin ƙaƙƙausar murya ya ce. "Zaidu Kasheta suka yi!" Shima Zaidu mikewa yayi jikinsa har na b'ari cikin zaƙuwa ya ce. "Su waye?" Hannu Ubaidullah ya ware. "Nima abun da nake tambaya kenan, SU WAYE!? Zaidu abun da na fi tsana a rayuwata wai yau shine ya faɗo akan kanwata, Zaidu FYADE FA AKA YIWA KANWATA! FYAƊE!FYAƊE!FYAƊE!" Saurin toshe kunnuwansa Zaidu yayi take ya ji jiri na ɗibarsa maƙogoronsa ya ji har wani ɗaci-ɗaci take masa, kishi haushi baƙin ciki duk suka haɗe masa waje guɗa har wani duhu-duhu yake gani. "Whattt! Fyaɗe!? Fyaɗe!? Fyaɗe!? Wa matar da na zauna jira zan aura din? Yanzu lovely fyaɗe aka mata?" yayi maganar hawaye na sake wanke masa fuska yana kallon Ubaidullah. Jinjina kai Ubaidullah yayi ya ce. "Ta ce mutum bakwai, amma bata faɗa min su waye mutum bakwai din ba, amma abu ɗaya na sani shine zan bazama neman mutum bakwai din nan na kashesu da hannuna duk da yanzu ni ba jami'i bane" KB ya ce. "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Hakika wa inda suka aikata abun nan basu san su wa suka tab'o ba, basu san sun taba yar gidan soja kanwar soja wanda yake sa ran auranta soja ba, amma komai muyi hakuri mu kuma dage da addua Allah ba azzalumin bawansa bane sai dai bawa ya zalunci kansa amma zasu gane basu da wayo, ni dai abu ɗaya na sani shine duk rintsin rayuwa duk tsanani duk wuya muna tare da kai Ubaidullah" Kuka suka saka a tare gami da rungumar Juna. Sallama aka yi, wanda ya saka su sakin junansu suna share hawaye, Abba ya girgiza kai ya ce. "Haba Ubaidullah, zaman gaisuwar kanwarka fa akeyi amma ka dawo ciki kana kuka kayi hakuri dan Allah mu dauki kaddara kowa lokaci yake jira Allah yasa Na'ila ta huta" Suka amsa da ameen, kafin Abba ya saka su a gaba suka koma kofar gida ana karban gaisuwa amma kallo ɗaya zaka yiwa Ubaidullah shi da Zaidu ka fahimci kalar tsananin tashin hankali da damuwar da suke ciki. Sai bayan sun fita ne KB ke sanar da Ubaidullah ai da Zeey suka taho nan KB ya basu labarin yanda sukayi da General Of The Army, girgiza kai Ubaidullah yayi gami da cewa. "Dan Adam kenan, ba komai rayuwa ce, ta ishe kowa ishara, Hanan kuma Allah ya saka mata da alkhairi. Tun da suka dawo daga maƙabarta basu koma cikin gidan ba,dan haka Ubaidullah bai san halin da Mama take ciki ba, sai da aka yi sallar la'asar tukunna suka shiga cikin gidan dan su gaisa da Zeey, nan Ubaidullah ya ga Mama tamƙar ba ita ba harta canza kamanni, nan hankalinsa ya sake tashi fiye da na da. Hafiza ma haka ta koma bata um bata um um sai illa rungume pic dinsu da tayi a ƙirjinta duk wanda ya ganta sai ya zubar da hawayen tausayinta, harta Anty Ummu ta koma tausayin Hafiza. Da dare kuwa ta shiga Kitchen dan ta dauko ruwa ma wata mata nan ta ci karo da tashin hankali. ba komai bane illa girkin da suka fara shiryawa Yayansu babu wanda ya taba abinci yadda suka ajiye haka yake, da gudu da kuka ta fice tayi hanyar part dinsa. Suna zaune jingum-jingum shi dasu Zaidu, sai ga Hafiza da Kuka kamar an wullota, tana zuwa ta faɗa jikinsa, ta ƙanƙame shi tana kuka mai mutukar tashin hankali. Ɗauriya iya ɗauriya Ubaidullah ya ɗaure kafin ya ɗaga Hafiza daga jikinsa yana share mata hawaye yana girgiza mata kai alamun tayi shuru, tama kasa magana illa hannu da take masa nuni dashi akan zo, tashi kuwa yayi ta kamo hannunsa suka fice, sukayi cikin gida har izuwa kitchen, suna shiga suka samu Abi'atu a kitchen din tana kuka. Nan Hafiza ta hau nunnunawa Yayansu abun da suka harhaɗa masa, dan kamar kurma haka Hafiza ta koma, Abi'atu ce tayi karfin halin fara magana. "Haƙika da nasan alaƙata da kanwarka ba zata jima ba dana roƙi Allah bai haɗani da su ba, kwana ɗaya ne kawai yasa muka yi sabon da ko shekara biyu albarka, bansan me Ubangiji ya tanadar ba na haduwar mu dasu,amma ka gani duk wannan girkin sun shirya shi ne domin kai, ashe abincin da ba za aci ba kenan" "Ƙannanka su na sonka tamƙar yadda kake son su, mun sha hira dasu shekaran jiya, jiya su na haɗa maka abinci har nazo na tayasu ashe duk aikin ban kwana muke yi da Na'ilah " ta karasa maganar da sabon kuka. Duk da Ubaidullah baya jin dadi amma haka ya zauna ya dauki abincin da suka dafa masa ya hau ci yana kuka, nan itama Abi'atu da Hafiza suka hau tayasa ci su na kuka har suka ci wanda zasu iya ci, kafin Ubaidullah ya koma part dinsa. Wannan family yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya rintsa Ubaidullah da Zaidu kwana sukayi su na sallah, Ubaidullah ma fita ya dinga roƙon Allah a cikin lamarinsa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A daddafe har aka samu akayi sadakar ukun Na'ila. Babu laifi jikin Mama da sauki amma har yau bata magana, amma idan aka zo mata gaisuwa tana amsawa da kai. Bayan jama'a an watse saura yan uwa na jiki wanda su na nan sai anyi adduar bakwai kafin su tafi su ma. Bayan mutane an ragu Ubaidullah Zaidu KB Zeey nan suka shiga bincike da iyakacin basirar da Allah ya basu akan gano wa inda suka yiwa Na'ila fyaɗe, barin ma Zeey da take jami'ar bincike (CBI) ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ _DAN ALLAH MY PPL'S SU KARA HAKURI WLH INA BUSY NE SHIYASA BAKU SAMUN POSTING AKAN LOKACI NGD DA KULAWARKU A GARENI._ _GA MASU KORAFI AKAN MUTUWAR NA'ILAH KUYI HAKURI HAKA LABARIN YAZO KU DAINA GANIN LAIFINA FATAN ZAKU FAHIMCENI KU FAHIMCI INDA LABARIN YA DOSA NGD._ Nasan za a samu kuskure ayi hkr banyi editing ba. COMMENTS AND SHARE MOMYN AHLAN TA KU CE👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *WALLAHI NA CI WUYA SAU BIYU INA TYPING YANA GOGEWA* 😰🥵 *page°°°°°51&55* Babu kalar binciken dasu Ubaidullah ba su yi ba dan ganin sun gano wa inda suka aikata wannan danyen aikin,amma babu wani information da suka samu. Da haka har aka yi sadakan bakwai din Na'ila sauran jama'a aka watse, amma babu wani hasken da suka samu, sosai Ubaidullah da Zaidu suka shiga damuwa akan hakan. Zeey bincikenta ne ya kasu kashi biyu, ga wanda ta ke yi a barracks ta barosa ga kuma wannan, ita ma ta shiga damuwa, babban burinta ta taimaki Ubaidullah ya koma bakin aikinsa idan yaso bayan ya koma sai su dage da neman wa inda suka yi raped din kanwarsa ya hukuntasu da kakinsa. Kwanar su Zaidu goma cif a bauchi su na gudanar da bincike kullum basu zama a gida, tun safe zasu fice ba zasu dawo ba sai dare, har wani rama Ubaidullah da Zaidu suka yi, saboda tsananin damuwa da tashin hankali. A kwana goman nan kuwa da dare General Of The Army ya kirawo su Zaidu akan su dawo gobe idan kuma basu dawo ba, to a bakin aikin su. Nan take Zaidu ya ce ba zai koma ba yabar aikin, sai da Ubaidullah ya yi da gaske kafin Zaidu ya amince zai koma a goben, a daren ranar ba su yi wani bacci ba. Da washe gari Ubaidullah ya nemo driver ya ba shi mota ya mai dasu Zaidu Abuja, idan ya so sai ya dawo masa da motarsa. Sosai Ubaidullah ya din ga yiwa Zeey godiya yana mata fatan alkhairi, murmushi kawai tayi ta ce. "See u soon" Da rashin fahimta ya kalleta, ta sake murmushi ta ce. "A barracks nake nufi" Girgiza kai kawai Ubaidulllah yayi sannan ya kalli Zaidu wanda ke tsaye har yanzu babu walwala a tattare dashi, kafaɗarsa Ubaidullah ya nausa cikin wasa, sai ga hawaye a idon Zaidu, da sauri Ubaidullah ya rungumesa shima ya fara hawaye, cikin dauriya Ubaidullah ya ce. "Sai Hakuri sirkina, Allah ya kara mana hakuri, Na'ila ba zata dawo ba ,da ace zata dawo tun kafin mu kaita maƙabarta ta tashi ko dan saboda kukan da muka din ga mata , ta ri ga da ta tafi ta barmu da kewa, kana gani dai har yanzu Hafiza bata dawo dai-dai ba tun da har gobe bata magana, Mama ita ma gata-gata nan ne, yanzu idan ka bar aikinka abun zai yiwa iyayenmu yawa, ni na ajiye kai ma ka ajiye me aka yi kenan? Kayi hakuri duk inda ka ke na tabbata kai din masoyin kanwata ne na hakika, abu daya na sani shine bazan taba barin wannan abun ya tafi a banza ba, wa inda suka aikata min wannan abun ba su san waye ake kira da Ubaidullahi bane, amma zasu sani ranar da suka shiga hannuna." "Za su yi nadama marar amfani a rayuwar su, dan duk randa nayi tozali dasu sunan su *GAWAWWAKI*." Yana gama fadi ya saki Zaidu sannan suka rungumi juna da KB, Sosai Ubaidullah yake zuba musu godiya tare da adduar Allah ya barsu tare har abada. Har cikin dakin Mama su Zaidu suka shiga mata Sallama. Mama kasa hada ido tayi da Zaidu ,dan gani take kamar zata ga Na'ila a gefensa shima Zaidun hawayena tab a cikin idonsa, cikin rawar murya ya ce. "Mama zamu koma bakin aiki, ki sa mana Albarka" duk dauriyar Mama sai da tayi hawaye ta ce. "Allah ya muku albarka Zaidu Allah ya kai ku lafiya, Allah ya kara mana hakuri ka ji?" Zaidu ya jinjina kai, KB da Zeey ma Sallama suka mata, Mama ta musu godiya tana sa musu albarka, dan ba laifi yanzu Mama ta dan sake tana magana, duk kuma saboda Hafiza ne, duk ta zama wata iri da ita, wani lokacin ma idan tayi abu kamar mai matsalar kwakwalwa. Ko da su Zeey suke yiwa Hafiza sallama da ido kawai take bin su dashi, kamar bata taba ganin su ba. Har waje Ubaidullah ya rako su, a tare su ukun suka rungume juna cike da kewa da bakin ciki, suka shiga mota Ubaidullah yana ɗaga musu hannu har suka fita gate din gidan. Su na fita ya koma part dinsa ya kwanta a parlour kan doguwar kujera yana tunanin da ya zame masa jiki kullum. Mama kullum cikin addua take Allah ya sassauta mata, dan wani lokacin idan tana tunanin Na'ilah ganin abun take tamƙar ta saka film ne ya kare. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ba su suka isa Abuja ba sai gefen magriba su na isowa Hanan ce farkon wacce ta fara taro su, tana tambayar su lafiyar Ubaidullah da kuma karin hakuri. KB da Zeey ne kadai suka iya tsayawa bata amsa amma har yanzu Zaidu baya cikin hayyacinsa dan ji yake yanzu son Na'ilah yake sake shiga zuciyarsa, babu yadda ya iya dole ya yi hakuri ya roƙi Allah ya masa sassauci. Sun yi waya da Ubaidullah sun isa lafiya, Allah huta gajiya Ubaidullah ya musu. Zeey kuwa wa inda ta saka su din ga bibiyar Rumaisa da wani shiga da ficenta, direct ta wuce take tambayar su yayinda suke bata jawabi dalla-dalla. Murmushin Nasara Zeey tayi ta ce. "Rumaisa kin kusan ki shigo hannuna, dadin abun ma shi ciki ba a karyarsa idan tana nan dole ta bayyana idan kuma babu duk zamu gani, Captain ka kusan dawowa soon In sha Allahu" ta fada tana murmushi dan idan Zeey ta saka abu a gabanta sai ta ga karshensa. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Zaune suke su biyu a parlour sun yi jigum babu mai yiwa dan uwansa Magana, Ubaidullah ne ya yi sallama ya shigo amma Abi'atu ce kawai ta amsa, sab'anin Hafiza da ta bisa da ido. Zama ya zo ya yi kusa da ita ya ce. "Kanwata tashi mu fita muje mu ga gari ko? Kema ki zo muje" ya fada yana dan kallon gefen da Abi'atu take zaune. Tashi tayi ba tare da tayi magana ba, ta shiga ɗaki domin ta ɗauko musu hijab din su, shi kuma Ubaidullah dakin Mama ya wuce ya same ta zaune a bakin gado, ga carbi a hannunta tana lazimi tana kallon kasan dakin. A hankali Ubaidullah yayi sallama yazo ya duƙa a gaban mahaifiyarsa ya kamo hannunta ya ce. "My Momma ki zo mu fita." "Mu fita kuma? Muje ina.?" "Momma mu dan fita shan iska ne kawai." Murmushin yaƙe Mama tayi wanda yafi Kuka ciwo, ta lura Ubaidullah yana so ne ya kwantar musu da hankali ko da kuwa shi zai kasance cikin tashin hankali, ko ba komai Ubaidullah ɗana wanda kowace uwa zata yi fatan samunsa a matsayin ɗanta domin ya zama garkuwa ga familynsa. " a'a Yaya Babba idan kuna so ku fita ne kawai kuje abun ku " Shagwabe fuska Ubaidullah ya yi sai kace karamin yaro duk saboda Mama ta saki jiki ta zo su fita. "Ni dai ni dai Mommana ki zo mu tafi kawai Hafiza da wannan yarinyar miye ma sunanta? Su na parlour har sun shirya dan Allah Momma karki ce a'a kizo mu fita yau kawai plssss!" Riƙe baki Mama tayi ta dan dungure keyarsa ta ce. "Kai Ubaidullah mai hali dai baya fasa halinsa wallahi, yanzu ƴar tawa ce baka ma san sunanta ba? Ai da a gabanta ka faɗa da naji kunya, to sunanta *ABI'ATU* saura kuma ka ce ka manta, duk irin kokarin da take yi a gidan nan kace baka san sunanta ba, kullum fa anan gidan take wuni tare da Hafiza." Dan tabe baki Ubaidullah ya yi, ya mike tsaye ya ce. "To Mama bazan manta ba ki fito muje" yana gama fadi ya fice daga dakin ya koma parlour ya same su duk sun saka hijab su na zaman jiransa. Fitowarsa da mintu biyu Mama ta fito itama nan suka yi waje, Ubaidullah ya kira mai gadi ya shaida masa zasu fita. Abi'atu ta bude bayan mota zata shiga Mama ta dakatar da ita da cewa. "A'a ƴata ki shiga gaba da Yayan ku ni da Hafiza zamu zauna a baya" ba dan Abi'atu ta so ba tayi abun da Mama ta ce dan ta lura Ubaidullah din nan dan rainin wayo ne. Shi ma Ubaidullah din wani kallo ya aika mata da gefen ido ta tabe baki. Mama kuwa burin da yake ranta shi ne Ubaidullah ya auri Abi'atu dan duk wanda ya samu Abi'atu a matsayin sirka yayi sa'a. Ita kuma Abi'atu a rayuwarta ta tsani mutum mai fadin rai da daure fuska sai kace wanda ake masa wahayi da mutuwa kullum, duk da yanzu mutuwar aka yi musu, amma tun can da daga ganinsa haka yake. Shi kuma Ubaidullah a nasa ban garen, ya tsani yarinya karama da iyayin tsiya dan a ɗan zaman da suka yi ya fahimci kamar tana da iyayi, dan shi kallon yar shekara sha uku yake mata, Abi'atu kuwa shakararta 19 ne ,kawai karamin jiki gareta sosai. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️ _KUNAAAA INAAAA NEEEE 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ MASOYANA NA HAKIKA WANDA SUKE SONA DA ZUCIYARSU BA DA BAKIN SU BA 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ MAZA-MAZA KU HANZARTO KU GARZAYO KU NUNA MIN KAUNA, A WANNAN KARON ZAN TANTANCE MASU SONA DA GASKIYA DA KUMA SON LITATTAFAINA, GA WATA SABUWA MAI TAKEN *ITA CE ZUCIYATA* DAN ALLAH KARKU BANI KUNYA KU NUNA MIN KAUNA TA HANYAR SIYAN WANNAN BUK DIN NAWA KU MIN KARA, AKAN FARASHI MAI SAUKI #200 HAKIKA WANNAN KARON ZAN FAHIMCI MASU SO NA DA GASKIYA 👯🏻‍♀️👯🏻‍♀️ KARKU MANCE NICE DAI TAKU UWAR AHLAN DA NA KAWO MUKU FITATTUN BUKS DINA KAMAR *GUDU A JEJI* DA KUMA *SHUHADA* GA KUMA WANDA KUKE KAUNA INA KAN TYPA MUKU SHI *COLONEL UBAIDULLAH* MASOYANA KARKU BANI KUNYA 🗣️🗣️🗣️ GA MAI BUKATA SAI YA TUNTUBENI TA NUMB WAYATA KAMAR HAKA 08165550116 MOMYN AHLAN KIRA KO WHATSAPP, SAI NA JIKI MASOYA NA HAKIKA👯🏻‍♀️ Comments & Share MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *KYAUTAR PAGE GAREKU, MY DOTER MA'EESHART AND MMN SON FADEELARH, WITH ANTYN AHLAN BLOODY SISMIETA INA YINKU SIS'S*💗 INSHA ALLAH MY COLONEL UBAIDULLAH FANS ZAKU JI SUNAN KU A PAGE NA GAMA IDAN NA SAMU NATSUWA KOMAI YA DAIDAITA MIN, KYAUTA CE GARE KU MASOYANA INAYINKU DAMA SAURAN WASU GRPS DIN.😘 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°56&60* Buɗe gaban motar tayi ta shiga ta dauke kanta ta juya masa ƙeya tana kallon window mota. Ubaidullah ji ya yi kamar ya dungure ƙeyar tata amma sai ya fuske ya ja motar suka bar gidan. Wajan shakawata ya kai su yana riƙe da hannun Hafiza yana nunnuna mata abubuwa, wani lokaci kuma ya tambayeta kina son wannan, amma sai dai kawai ta kallesa, dan fitar da suka yin ma sake tuna mata da yar uwarta ya yi, tun da yawancin fita irin haka tare suke yi. Yawo sosai Ubaidullah yake yi da Mama da Hafiza Abi'atu, sai wajan karfe uku ya wuce dasu gidan Anty Ummu. Sosai Anty Ummu taji dadin ganin su sai murna take yi, Mama da Anty Ummu sun sha hira sosai yayinda Mama take faɗawa Ummu ƙudirinta na son haɗa Ubaidullah da Abi'atu aure, nan take Anty Ummu ta bada goyon bayanta ɗari bisa ɗari dan kuwa itama ta yaba da hankalin Abi'atu. Sai bayan la'asar suka baro gidan Anty Ummu daga nan suka wuce gidan su Umma( gidan su Zaidu) sosai Umma taji dadin ganin su Mama, nan aka gaisa aka sake yiwa juna ta'aziyya. Abi'atu Hafiza Afnan Manal suka koma gefe su na dan taba hira wanda hiran Afnan da Manal sai Abi'atu dake jefa baki sama-sama amma ban da Hafiza. Inna ta ce. "Yauwa yarinyar nan, shekaran jiya dana kunna radio naji labarin mutuwar Na'ila a DUNIYAR MAMAKI RADIO, kuma naji muryar mai gabatarwar kamar ke?" Inna ta faɗa tana kallon Abi'atu. Abi'atu ta buɗe baki zata yi magana bata kai ga yi ba, kamar daga sama taji muryan Ubaidullah yana faɗin. "What! Labarin mutuwar kanwata a duniyar mamaki radio? Taya hakan zata kasance tun da ni dai ban yi hira da yan gidan radio ba?" Abi'atu ta ce. "Ni ce na kai kuma nayi magana akai, sannan nayi dogon rubutu akan fyaɗe, wanda ranar alhamis jaridar zata fito idan Allah ya kaimu, yan jarida zasu zo domin su tattauna da Mama da kuma kai, sannan...." maganar da Abi'atu bata karasa ba kenan Ubaidullah ya katseta da kakkausar murya. Ya kalli Mama ya ce. "Mama tashi mu tafi gida, Umma Inna sai an jiman ku, Hafiza ta so mu tafi" ya fada yana kama hannun Hafiza, itama Abi'atu tashi tayi jikinta duk ba kwari. Su na fita Inna tayi tsaki gami da cewa. "Iskancin banza kawai, ba ga irinta ba halin nasu, wai soja, soja ko mala'ikun duniya, dan Allah ki gani fa yarinya tana jawabi cike da natsuwa da ladabi amma ya katseta da kakkausar murya, ya figi hannun Hafizatu kamar wanda yake shirin zuwa sama jannati wai su tafi, yaro kullum fuska sai kace hadiri haba" nan Inna ta dasa mita tana yi tana karawa, ita dai Umma bata ce komai ba. @@@@@@ Ubaidullah bai tsaya a ko ina ba sai a gate din gidan'su ,su na isowa ana kiran sallar magriba, dan haka ya yi masallaci su kuma suka shiga gida. Mama tana dakinta Abi'atu da Hafiza su na zaune a daki sai ga Ubaidullah ya shigo ransa a b'ace ya damƙi hannun Abi'atu yayi hanyar fita da ita. Tana so tayi magana amma bata so Mama taji kuma ta fito ta ga Ubaidullah ya riƙo hannunta, dan haka tayi shuru sai da suka fito daga parlour ta fara magana. "Malam! Lafiya kuwa? Ina zaka kaini? Me nayi maka zaka min irin wannan rikon? Karka karyani mana ka sake min hannu" ko sauraronta bai yi ba ya yi hanyar part dinsa da ita. Bai tsaya ba sai da suka shiga parlourn'sa ya cillata kan kujera yana kallonta yana huci. "Akan me zaki kai labarin mutuwar kanwata gidan radio?" a masifance yake maganar. Miƙewa tsaye Abi'atu tayi ta ce. "To miye aibu? Dan na kai labarin mutuwar Na'ila radion mamaki? Naga kai soja ne, a sojan ma Captain na tabbata ba zaka taba barin wa inda suka kashe Na'ila ba, ni na kai labarin ne saboda idan ka kama su kayi musu hukunci ya zama izna ga yan baya masu sha'awar aikata hakan da su hankaltu, dan hausawa sun ce ana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, to miye laifina dan na kai labarin gidan radio? Eh tabbas nayi dogon rubutu akai wanda ranar alhamis zai fito kuma ma ai..." "Pls malama! Ya isheki haka! Ni na faɗa miki cewa ni soja ne yanzu? Duk ba bukatar kiyi haka sai ki nemi izinina, wai shin ma miye sunanki wacece ke?" Ran Abi'atu ba karamin sosuwa yayi ba da maganganun Ubaidullah. "Sunana Abi'atu Abdul'Maleek shehu journalist, ni yar jarida ce kuma ni writer ce a gidan radio ina rubuta abubuwan da suka shafi mata." Da mamaki Ubaidullah ke binta da ido, a ransa yake cewa. "Wannan yarinyar ce yar jarida kuma har da rubuta abun da ya shafi mata wannan yar abun?" yake tambayar kansa amma a fili ya ce. "Duk wannan ba damuwata bane, kuma karki kuskura wasu su zo mana gida da sunan wai yan jarida sun zo yi mana tambayoyi bamu da bukatar haka" nan ya gaggaya mata maganganu. Kwalla ne ya cika a idonta ta kallesa bakinta na bari ta ce. "Nakan yi shige-shige dan ganin na binciko wasu abubuwa dan na yi rubutu akai a samu mafita, bansan cewa nayi shishshigi bane, kayi hakuri idan ka sake ganina a gidan ku na yarda kayi min duk abun da ka gadama" tana gama fadi ta fice da gudu. Duk wannan draman da suke yi Hafiza tana tsaye a bakin kofa tana jin su, har san da Abi'atu ta fice da kuka. Rimtse ido Ubaidullah yayi wani bangare na zuciyarsa bai ji dadin kuma yanda ya mata ba. Yana tsaye hannunsa ɗaya a kugunsa daya kuma a fuskarsa ya ji sautin muryan da yau kusan kwana nawa bai jita ba, a hankali ta furta. "Yayana" Da sauri Ubaidullah ya juyo yana kallonta da sauri yazo ya rungumeta yana hawaye ya dago fuskarta ya ce. "Kanwata ke ce? Ke ce kikayi magana? Faɗa min?" Jinjina kai Hafiza tayi ta ce. "Yaya baka kyauta ba abun da kayiwa Anty Abi'atu, shin kasan kalar kokarin da take yi kuwa, wajan taya ka gano wa inda suka kashe min sismieta? Ita da Yaya Safwan kullum su na fadi tashi ,su na iyakar kokarin'su, Yaya, Anty Abi'atu tana da matukar kirki fiye da tunaninka bata da matsala ko kadan, ya kamata ka bata hakuri akan abun da ka mata." Ubaidullah ya ce. "Kina so na bata hakuri?" Hafiza ta gyaɗa kai alamun eh, ya ce. "To shikenan idan tazo gobe zan bata hakuri kin ji?" Hafiza ta sake gyaɗa masa kai sannan suka fito a tare suka shiga dakin Mama. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da sallama ta shiga parlourn gidan su Abba da Ummi su na zaune duk da fuskarta babu walwala amma sai da ta danyi fara'a tazo kusa da Ummi ta zauna, kafin ta gaishe da iyayenta, suka amsa Abba ya kara da cewa. "Ah ai na dauka zamu bi ki da kayanki ne ai yau kusan kwana uku ina tambaya kina ina wai kina gidan'su Mama" dan murmushi tayi ta ce. "Haba dai Abbana gani na dawo ai" Ummi ta ce. "Ya jikin Mama da Hafizan?" "Alhamdulillah Mama da sauki, itama Hafizan Alhamdulillah amma har yanzu bata magana" "Allah sarki! Zata ware a hankali Allah ya basu lafiya" cewar Ummi suka amsa da ameen, Yaya Safwan ya yi sallama ya shigo ya ce. "Ah journalist yau an dawo kenan" hararan wasa ta masa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta bata kula Yayan nata ba, kwanciya tayi tana tunanin maganganun Ubaidullah, sake rimtse ido tayi ,ta dauko wayarta ta shiga wajan video nan ta ci karo da videon Na'ila, kukanta tasha kafin ta tashi tayi sallar isha'i ta kwanta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari Ubaidullah ya yi shirin faɗawa mahaifiyarsa cewa yabar aiki. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *DA BABU GWARA BA DADI, KU LALLABA DA WANNAN KARKU ZAUNA SHURU PLS WLH YANZU BANI DA LOKACIN TYPING BUK BIYU, BAZAN IYA CE MUKU GA LOKACIN DA ZAKU DINGA SAMUN UPDATE BA, SABODA SABON BUK DIN DA NAKE TYPING, FATAN ZAKU FAHIMCENI, NGD* GA MASU BUKATAR SABON NOVEL DINA NA KUDI MAI TAKEN SUNA *_ITA CE ZUCIYATA_* SAI KU NEME NI TA NUMB TA KAMAR HAKA, 08165550116 KIRA KO WHATSAPP NGD. COMMENTS AN SHARE. MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻, [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 _QAUNAR KU DABAN YAKE_ *ANTY HAUWA MMN USWAD* *&* *ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA* _ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY'S_ __________________ Ya Allah kabani ikon gamawa lpy🤲🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°61&65* Da misalin karfe tara da rabi na safe. Da sallama ya shiga dakin, Mama tana zaune akan sallaya da carbi a hannunta tana lazimi da alama ta idar da sallarh walha ne. Amsa sallamar tasa tayi, ta shafa adduar kafin ta fuskancesa dan kuwa kallo ɗaya ta masa ta ga akwai magana shinfiɗe a fuskarsa. "Lafiya kuwa Yaya Babba? Daga ganin fuskarka akwai damuwa haka ne?" Gyaɗa kai Ubadullah ya yi, ya matso kusa da Mama ya kama hannunta sosai gabansa sai faduwa yake yi cikin sanyin murya ya ce. "My Momma, akwai abubuwan da suka faru a wajan aikina, wanda shi ya yi sanadiyyar dawowata gida, ina dawowa dan naji da ciwo ɗaya , sai kuma na iso na tarar da babban miƙin da har na mutu ba zata taba warkewa ba, Mama bansan ya zaki dauki labarin da zan ba ki ba, amma ni dai nasan mahaifiyata ta yarda dani, kuma tasan bazan taba aikata abun da ba shi da kyau ba, Mama ke da bakinki kin sha faɗamin cewa samu da rashi duk na Allah ne, idan Allah yaso zai baka abu sannan ya kwace a duk lokacin da yake so, inajin tsoron faɗa miki amma kuma duk daren ɗaɗewa dole ki sani, ban son ki sake shiga damuwa a ta sanadin hakan mahaifiyata" ya karasa maganar hawaye na zuba a idonsa. Sosai jikin Mama ya yi sanyi, hakika Ubaidullah wani abun na damunsa amma daurewa yake yi kawai, kallonsa tayi ta ce. "Yaya Babba, karka ji shakku akan abun da zaka fadamin, a yanzu yadda nake jin kaina, babu abun da za a fadamin wanda zai tayar min da hankali, domin kuwa idan tashin hankaline na gansu sau biyu a gabana, na gansu kwance su biyu a gabana, ba komai bane fa ce gawar mahaifin ku da kuma gawar yar uwar ku, dan haka naga gawar mijina naga na ƴata wanda ko wata ba tayi ba kwance a cikin kasa, ka faɗamin abun da kake son faɗa min." Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke kafin ya sun kuyar da kansa kasa ya ce. "Mama na ajiye aikina na soja, yanzu ni ba ma'aikaci bane" nan Ubaidullah ya shiga bawa Mama labari tun abun da ya fara shiga tsakaninsa da Rumaisa bai boye mata komai ba harda yan matan da suke bibiyarsa a barracks din ,duk ya faɗa mata, daga karshe ya kara da cewa. "Mama iyakar gaskiya ta na fada miki, na ajiye aikin ne saboda gudun a min wulakanci a ci zarafina, ni kuma ba zan dauka ba, kar nazo nayi abun da zai jawo a kasheni saboda zuciyar da nake dashi, shi yasa na ajiye aikina. Sosai Mama ta fahimci maganar Ubaidullah, duk da zuciyarta sai ƙuna take yi, a hankali cikin dauriya Mama ta kalli Ubaidullah wanda kallo ɗaya tayi masa ta hango tsananin damuwa da tashin hankali a tattare da shi. Kasa magana Mama tayi sai da Ubaidullah ya sake cewa. "Mommana ke ma baki yarda dani bane? Naji baki ce komai ba, wallahi Momma da gaske nake fada miki idan ma baki yarda ba ki kira abokaina Zaidu da KB su zasu faɗa maki gaskiya , da wannan yarinyar da suka zo ta'aziyyar Kanwata. Share hawaye Mama tayi dan kuwa ba karamin sake shiga damuwa tayi ba , da Ubaidulllah ya fada mata da cewa yabar aiki, a hankali Mama ta ce. "Allah yana tare da mai gaskiya ni nasan hali ɗana a matsayina ta mahaifiyarsa, kuma na yarda da ɗana, karka damu Ubaidullah dukkan mumini sai Allah ya jarrabesa dan a gwada imaninsa, Allah yabamu ikon tawakkali da rungumar kaddarar'mu hannu biyu" shi ma Ubaidullah hawaye yake yi ya kifa kansa akan cinyar Mama yana kuka tamƙar karamin yaro, zai yi magana suka ji Hafiza na shashsheƙar kuka a bakin kofar Mama. Ubaidullah ya ce. "Kanwata!?" da gudu ta bude kofar daki ta shigo da alama taji duk abun da Ubaidullah da Mama suke magana a kai ne, rarrashinta Ubaidullah da Mama suka shiga yi Amma taƙi tayi shuru, sosai hankalin'su ya tashi, da kyar Hafiza ta taƙaita kukanta , tana jan zuciya ta ce. "Yaya shi kenan kai ba Soja bane yanzu? Wa in da suka kashe min yar uwata suka barni ina rayuwata ni kadai sun kasheta a banza kenan? Yanzu Yaya ba zaka daukarwa Yar Uwata FANSA ba, yanzu Yaya kai ba soja bane ba zaka nemo wa inda suka kashemin Sismieta suka rabani da ita ka kashe su ba yanzu Yaya b...." bai bari Hafiza ta karasa ba ya rufe mata baki da hannunsa gami da cewa. "Kul! Wa ya gaya maki cewa bazan nemo su na hukunta su ba?ai kullum cikin neman su nake, Dole na, na nemo wa innan azzaluman bayin na kashe su da hannuna nayi alkawari sai na ɗanɗana musu azabata, duk abun da na koya na training soja sai na sauke musu shi, ki daina wannan maganar kinji ko?" ya karasa yana rungumeta, tashi Mama tayi ta fice tana share hawaye, ta bar Ubaidullah da kanwarsa a daki su na kuka ita ta koma parlour tana nata kukan. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da yamma Ubaidullah ya shirya zai fita, har ya shiga mota dan kuwa ya sanar da Mama cewa zai fita, da gudu Hafiza ta fito ta tsaya tana kallonsa. Fitowa ya yi a motar yana tambayarta akan menene ko tana son wani abu ne,amma ta tsaya sai tura baki take yi kamar zata yi kuka. Da sauri ya karaso gabanta ya kama hannunta ya ce. "Wa ya taba min ke?" dan kuwa Mama da Ubaidullah da Anty Ummu basu son su ga Hafiza a damuwa dan tafi basu tausayi. "Yaya, ya muka yi da kai?" Daga kai Ubaidullah ya yi, alamun tunani amma ya kasa tunawa, dan shi gaskiya har ga Allah ya manta da wani magana. "Am sorry Lil'Sis wace magana ce? Namanta tuna min pls." "Na hakurin da zamu je mu bawa Anty Abi'atu mana, tun abun nan da ya hadaku bata sake shigowa ba fa, amma kullum tare muke wuni kuma tana ɗebemin kewar sismieta duk da ba zata taba zama kamar ita ba, amma Yaya ina son Anty Abi'atu sosai, Mama tana sonta idan taji abun da ka mata kasan Mama ba zata ji dadi ba, kuma idan aka yi kwana biyu bata zo ba Mama zata fara zargin kayi mata wani abu ne tun da agabanta ka fara yiwa Anty Abi'atu magana da ihu tun a gidansu Yaya Zaidu" ta karasa maganar tana dukar da kanta kasa. Ubaidullah yasan duk abun da Hafiza ta faɗa gaskiya ne dan haka ya ce. "To shi kenan, shiga mota muje" girgiza kai tayi ta ce. "Yaya, nan da nan shine sai mun je a mota? ni kam kawai ka zo mu taka mu shiga." "Ohh Allah na, Hafiza kin koya rigima wallahi, anya ba wannan yarinyar mai iyayin ba ce ta koya maki rigima?" duk a cikin zuciyarsa yake faɗin wannan maganar, a fili kuma ya ce. "Haba Hafiza baki ga zan fita bane?" " ni dai Yaya muje da kafa" ba tare da ya sake magana ba ya kulle mota suka fita a tare. Tun da Hafiza suka fito daga gate dinsu ita da Yayanta ake bin su da kallo, ga kamannin da suke yi wasu yan matan unguwa ma ba su san Ubaidullah ba tun da ba zaman garin yake yi ba idan yazo ya jima da yawa shine ya yi sati ɗaya ya koma, kuma idan ya zo fitar su kullum a mota ne shi da Amininsa Zaidu. Wasu ma idan suka ga Hafiza sai su dauka Na'ilah ce dan ita ce mai jama'a, sai ka matso kusa tukunna zaka gane ba Na'ilah bace dan kuwa Na'ilah tafi Hafiza fadin Fuska, sai sake yi musu ta'aziyya ake yi su na amsawa, wasu ma yan mata da gayya suka zo yiwa Ubaidullah ta'aziyya dan kawai ya yi musu magana saboda yau ne karo na farko da suka fara ganinsa, basu taba ganinsa ba sai dai su ji labarinsa, ba yabo ba fallasa yake amsa gaisuwar ta su, da haka ya ja hannun kanwarsa suka wuce dan sauri yake akwai inda za shi. A gate din gidansu Abi'atu Hafiza ta kwankwasa karamin kofa, rabonta da fita tun rasuwar yar uwarta, sai kuma fitan da suka yi a mota da Yayanta, shi yasa take ganin komai daban yake mata. Mai gadi yana ganinta ya saki murmushi, nan suka gaisa shima ya sake yi musu ta'aziyya. Sai da Hafiza ta shiga tayi sallama Ummi ta fito daga bedroom dinta zata shiga kitchen ta ga Hafiza na Sallama, tsantsan farin ciki Ummi kasa amsa sallamar tayi da saurin tazo ta rungumi Hafiza tana cewa. "Hafiza ke ce?" gyaɗa kai Hafiza tayi ta duka ta gaisheta, Ummi ta amsa cike da farin ciki da jin dadi. "Ummi ni da Yayana ne mu ka zo, yace na rakosa wajan Anty Abi'atu zasu yi magana." Da mamaki Ummi take kallon Hafiza ta ce. "Tooo! Ina Yayan naki yake ,shine bai shigo ba? Sai kace wani bako ai da nan da gidanku duk ɗaya ne" Murmushi gefen baki Hafiza tayi tana kashe ido ɗaya ita kadai tasan plan din da tayi, yar uwarta ce ta fado mata a rai ana gobe zata rasu da suke hira akan cewa idan Yayansu yazo sai sun san yanda suka yi suka haɗa shi aure da Anty Abi'atu dan kuwa sun dace. "Allah sarki! Rayuwa baki da tabbas, Sismieta nayi alƙawari ko babu ke ni saina cika wannan burin In'sha Allahu" duk wannan maganar a zuciyarta take fadi a fili kuma ta ce. "Am uhum Ummi wai kunyarki yake ji" rike baki Ummi tayi gami da cewa. "Lallai kam ai sai ki ce masa ya shiga ƙaramin parlour, sannan ki zo ki kira Abi'atu tana daki, dan tun jiya na kasa gane mata bansan meke damunta ba" Hafiza ta amsa da to, sannan ta fita ta kai Yayanta karamin parlour, ta dawo da sallama ta shiga bedroom din Abi'atu. Abi'atu kwance ta lumshe ido kamar wata mai bacci, kamar a mafarki ta ji muryar Hafiza da sauri ta bude ido ta ga Hafiza a gabanta tana tsaye tana dan murmushi kaɗan-kaɗan, sake mutsintsike idonta Abi'atu tayi ta ce. "Ko dai gizo take min ne?" Hafiza ta ce. "A'a My Anty In-law ba gizo bane ni ce Hafiza ce" wani ihu Abi'atu ta saka wanda harta Ummi dake kitchen sai da ta tsorata, dirowa a gadon Abi'atu tayi ta zo ta rungume Hafiza har da kwallanta na farin ciki, Ummi ta shigo da sauri tana cewa. "Abi'atu lafiya kuwa? wannan wani irin ihu ne haka? Duk kin cika gida?" "Ummi wallahi ita ce ta fara magana." "Mtsww! Amma dai ke kam Allah ya shiryeki maimakon kiyi hamdala sai ki saki wannan kara haka, ai mun fara gaisawa da ita kafin ta shigo wajanki, hamdala za ki yi ba ihu ba" "Wallahi Ummi bansan nayi ihun ba, murna ce ta saka ni yi" Ummi tayi murmushi ta fice tana cewa idan kun gama dai karku manta kun bar mutum a parlour. Zama suka yi Hafiza ta ce. "Shine kika gudu ko?" Shuru Abi'atu tayi ta ce. "Aa ba guduwa nayi ba , akwai aikin da nake yi ne shiyasa baki ganni nazo ba" "To tashi muje Yayana ne yace na rakosa wajanki." Zare ido Abi'atu tayi da mugun Mamaki take kallon Hafiza, ganin haka yasa Hafiza ta miƙe ta ce. "Ki kawo masa abun sha ki same mu a ƙaramin parlour" tana gama fadi ta fice, Abi'atu jiki ba kwari ta tashi ita ma tayi hanyar kitchen. Da sauri Hafiza tayi wajan Yayanta, dan karya kwafsa mata dan tasan zai aika, a yau kuma bata son tayi missing din plan dinta. "Am Yaya ga Anty Abi'atun zuwa, Yaya karka bani kunya, karka bawa Mama kunya ka ji?" guntun tsaki Ubaidullah ya ja ba tare da Hafiza ta ji ba ya ce. "To na ji" ya fada a takaice dan yan halin sun fara tashi. "Am Yaya idan tazo zan tashi na baku waje sai ka bata hakurin a sirrince" da mamaki yake kallon Hafiza, shi kenan ta koyawa Hafiza kisisina. "Um" shine abun da ya iya fadi, Hafiza zata sake magana Abi'atu tayi sallama cikin zazzaƙar muryarta wanda sai da ya daki dodon kunnen Ubaidullah, wani kamshi yaji na tashi wanda sai da ya sanya idanunsa kaɗawa suka koma ja, da sauri ya tamƙe idonsa, yana so su washe dan yanda ya ji sunyi masa ya tabbata yanzu kam sun yi ja. Abi'atu tana shigowa Hafiza ta mike da sauri ta fice dan kar ma Abi'atu ta tsaidata. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *kun matsa ne amma banyi niyyar sakin page din ba, saboda page din baya na samu korafi ta pc akan cewa yy kadan na kara, kuma na fada muku cewa bani da tym din typing buk biyu lokaci daya* Momyn Ahlan Taku Ce👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_CIKIYA CIKIYA CIKIYA, DAN ALLAH WANDA YAKE DA BUK DINA (HALITTA DAGA ALLAH NE) PLS A TAIMAKA MIN A TURO TA MY NUMBER WLH NA RASA SHI NE SABIDA WAYATA DA TA SAMU MATSALA KWANAKI, 08165550116 PLS._* *Kacokar wannan page din na mallaka muku shi halak malak, yan COLONEL UBAIDULLAH FANS, idan kun so ku hana wasu grps din karantawa 🤪🤪 ni dai ba ruwana har da yan Wattpad ma* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°66&70* Fitan Hafiza da yan mintuna su na zaune babu wanda ya cewa kowa komai, Abi'atu ganin darajan Mama tayi a idonta sannan ta ga girman Anty Ummu, sai kuma Ubaidullah din da ta gansa kamar Yayanta Safwan dan haka ta daure a takaice tana kau da kanta gefe tana tabe baki ta ce. "Ina wuni?" Yadda tayi masa gaisuwan ne ya tsaya kallonta yana jinjina iyayinta, sai da ya ɗibi kusan minti sha'biyar,har ta fidda ran zai amsa, kafin ya amsa a takaice shi ma. "Lafiya" Daga haka ko wanne yaja baki ya yi shuru, Ubaidullah wayarsa ya ci gaba da dannawa Abi'atu tana zaune tana jira ta ji meya kawosa, har tsawon minti talatin su na zaune ba tare da sunyi wata magana ba tun bayan gaisawar da suka yi. @@@@@ Hafiza kuwa parlour ta koma ta zauna tana addua Allah yasa haƙanta ya cimma ruwa, tun da burin Mama, fatan Anty Ummu ne. Ko da Ummi ta fito daga kitchen ta ga Hafiza zaune ta ce. "Ah Hafiza ya na ganki anan kuma? Ina Abi'atu da Ubaidullah din?" "Su na karamin parlour Ummi, cewa ya yi na tashi na fita magana mai mahimmanci zasu yi shiyasa na dawo nan na zauna" Jinjina kai Ummi tayi tana tunanin dama akwai abu tsakanin Abi'atu da Ubaidullah ne. Hafiza tana nan zaune har Safwan ya shigo ya ganta ya yi mata magana, ga mamakinsa sai ya ji ta amsa ta gaishesa, shi ma farin ciki ya yi, daga haka ya zauna yana dan janta da hira tana amsa shi sama-sama har Abba ya dawo ya gan su a haka, har kasa Hafiza ta sauko ta gaishesa dan kuwa Abba maƙoci ne na gari dan ya musu halacci da rasuwar Na'ilah. Cike da fara'a Abba ya amsa gaisuwar yana tambayarta ya jikinta ta amsa da sauki ya ce. "ina Abi'atun taki?" "Su na tare da Yayana a ƙaramin parlour shi ya ce na rakosa wajanta" Safwan yasa dariya cikin wasa ya ce. "Ah Alhamdulillah! Ashe dai maganata zata zama gaskiya kenan, ga Journalist ga Army" itama Hafiza murmushi tayi Abba ya ce. "To Allah ya sanya alkairi mu bamu da ta cewa" Ummi ta ce. "Wallahi kam, ameen" daga haka Ummi suka wuce ita da Abba, shi ma Safwan mikewa ya yi ya ce. "Hafiza nima zan shiga ciki na watsa ruwa." "To Yaya Safwan a fito lafiya" daga haka Safwan ya shige part dinsa. Hafiza ta juya tana kalle-kalle a ranta ta ce. "To yana ji su shuru haka? Ba dai Yaya tafiya ya yi ba? Dan zai aika, to ko naje na duba ne? Kai A'a bari na kara musu lokaci kadan mu gani tun da, da ya tafi dole Anty Abi'atu ta dawo" da wannan tunanin Hafiza ta koma ta zauna. @@@@ Kusan awa ɗaya, Abi'atu tana zaune Ubaidullah bai ce da ita ƙala ba, tun gaisawar da suka yi. Guntun tsaki taja ba tare da ya ji ba, a ranta ta ce. "Ni Abi'atu yau na ga salon wulakanci har gidan Ubana, mutum ka zo, ka sa a kirani amma ka mai da ni tamkar wata poster? To wallahi baka isa ba, idan baka da abun yi ni ina dashi" tana gama faɗin haka a zuciyarta ta miƙe zata fita har ta kai kofar fita ya ɗago shi bai ma san ta tashi ba, da sauri ya ce. "Amm keee! ABI'AH." Cak Abi'atu ta tsaya saboda yanda ya kira sunan nata wai Abi'ah take tsiƙar jikinta ya tashi ga wani kasala da ya sauke mata. "Subhanallahi! Wannan bawan Allah akwaisa da fi'ili" duk maganar zuci take yi. Tasowa Ubaidullah ya yi ganin yanda ta tsaya bata da alaman juyowa balle ta sa niyyar dawowa,gabanta ya zo yana dan kallonta sama-sama dan bai son ya cika kallon mace saboda kar zuciyarsa ta ƙitsa masa abun da ba shi kenan ba. "Uhum amm dama na zo ne na baki hakuri akan maganar da kika fadi akan cewa ba zaki sake zuwa gidanmu ba, ko ba komai saboda ke Hafiza ta fara magana, na yi farin cikin haka sosai, ga shi Mama tana yabonki sosai ko ma ba danni ba ya kamata ki janye maganar ba zaki sake zuwa ba, tun da naga alama duk kin sace zukatan yan gidanmu, fatan kin fahimci abun da nake nufi?" Tun da Ubaidullah ya fara magana dodon kunnen Abi'atu yake mata guɗa, yanda yake furta magana ɗaya bayan ɗaya abun ba karamin burgeta yayi ba, barin ma sexy voice dinsa wanda taji yana shirin sakata bacci, a fili kuma, motsa dan ƙaramin bakinta tayi ta fara magana, zubawa bakinta idon Ubaidullah ya yi, a cikin ransa ya furta. "ya salam! Yarinya yar ƙanƙanuwa amma sai kisisinar tsiya" "Dama ai ba dan kai din bane zan koma, fatan kai ma ka fahimceni?" ta fada gami da juyawa zata fita a ranta ta ce. "Ka ji fa, wai ya zo bani hakuri amma bai furta min yi hakurin ba" juyawar da ta yi suka yi karo da Hafiza zata shigo ita kuma, tsayawa Hafiza tayi tana musu kallon tuhuma, daga masa gira Hafiza tayi ya kau da kansa gefe ya ce. "Hafiza muje ko?" Caraf ta ce. "Yaya, muje ka gaishe da Ummin, Abba ma ya dawo, Anty Abi'atu dan Allah karasa sai na biku a baya" da mamaki suka kalli Hafiza ta tura baki, dukkan'su basu ce komai ba, Abi'atu tayi gaba Ubaidullah ya bi ta a baya, har cikin parlourn su. Abba da Ummi su na zaune, su Abi'atu su na shigowa Safwan yana fitowa, nan suka yi musabaha da Ubaidullah ya yinda Ubaidullah ya dukar da kansa kasa sosai ya russuna ya gaishe da Abba da Ummi tamkar ya je gaisuwan surkai. Amsawa Abba da Ummi suka yi cike da fara'a, sannan Ubaidullah ya mike da sauri ya fice Hafiza tayi musu sallama tabi bayansa, Abi'atu ta zauna Ummi ta ce. "Ke Abi'atu wannan wani irin shirme ne? Mutane su zo wajanki zasu tafi ba zaki taka musu ba?" Ba dan Abi'atu ta so ba, ta miƙe ta fito wajan gate ta ga har sun dan yi nisa, tsayawa tayi na wasu lokaci kafin ta koma cikin gida. Ubaidullah su na zuwa sai da ya ga Hafiza Ta shige kofar parlour kafin ya shiga motarsa yabar gida, dan kuwa sauri yake yi akwai aikin da zai je mai muhimmanci. Ubaidullah bai dawo ba sai tsakar dare wajan sha biyu da rabi, amma duk da haka sai da ya fara shiga ciki dan ya ga lafiyar Mahaifiyarsa da Kanwarsa, Hafiza a dakin Mama ta yi bacci, Mama kuwa idonta biyu,har sai da ta ga Ubaidullah kafin ta ji karfin guiwar samun damar kwanciya. @@@@@ Da washe gari bayan Ubaidullah ya shigo sun gaisa da Mama yake faɗa mata in da ya je jiya, akan cewa ya samu wasu manyan shaguna ne a kasuwar wunti guda hudu ya siya, har ya bada other za a kawo kayayyaki yau za a zuba, sabida ya san yana da wani sana'ar da zata din ga kawo masa kudi, dan kar kudin hannunsa ya kare su rasa yadda zasu yi. Adduar Allah ya sanya alkhairi da Allah ya rufa asiri ya kara buɗi Mama ta yi masa, ya amsa da ameen, har ya tashi zai fita Mama ta ce. "Ubaidullah, shin Alhaji Adamu yasan da cewa kabar aiki?" "A'a Mama, bai sani ba, yanzu kusan shekaransa ɗaya da rabi kenan baya ƙasar, shi da iyalansa,su na Cairo" "Ayya, sai yau she kuma zasu dawo?" "Wallahi, Mama ban sani ba, duk da muna waya dashi lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, amma ban faɗa masa abun da ya faru ba." "To shi kenan, Allah ya zaba abun da yafi alkhairi a rayuwa" "Ameeen Mama, ina Hafiza ne?" "Ba su jima da tashi anan ba ita da Abi'atu" jinjina kai ya yi, ya fice. @@@@@ Masha Allah kwana hudu aka dauka ana gyaran shagunan Ubaidullah ya yinda aka zuba kaya masu kyau da tsada da arahar kudi, wanda ana ta neman sunan da za a sa wa shagon amma an rasa, Hafiza ta tambayi Abi'atu sunan da ya dace a sawa Shagunan. Nan Abi'atu ta ce, a sawa Shagunan suna, ABDULLAHI'S FAMILY, sosai kuma sunan ya burge Ubaidullah dan ya ji dadin sunan sosai. Cikin ɗan ƙankanin lokaci Allah ya sakawa shagunan albarka, nan da nan Abdullahi's Family Shop jama'a aka san da zamansa a garin bauchi, barin ma yan mata, dan kuwa an zuba su kyale-kyale, jakukkuna ne takalma atampopi shaddadu materials su cosmetics, babu abun da babu a shaguna guda hudun ne. Haka rayuwa ke tafiya da sauri-sauri duniya tana gudu, yau shagunar Ubaidullah watansa ɗaya da budewa kuma Alhamdulillah yana samun kudi sosai kudi su na shigo masa masha Allah, dan har mota ya siyawa MAMA da Hafiza, duk da shi ba zaman shagon yake yi ba ya samu masu zama masa dan shi har kwanar gobe baya da sha'awar wani aiki ko kasuwanci wanda ya wuce aikin soja, duk abun da ke faruwa Ubaidullah su na magana da amininsa Zaidu, ba laifi Zaidu ya fara warewa amma ba sosai, ta bangare daya su na kan bincike akan wa inda suka yiwa Na'ila fyaɗe, yanzu tsawon wata hudu kenan, da rasuwar Na'ila amma babu wani haske, Ubaidullah ya yi kukan baƙin ciki dan kuwa ya fara cire rai, a wannan wata hudun ne kuma Mama ta je ta samu ƙanin mahaifin su Ubaidullah akan ya je ya nemawa Ubaidullah auren Abi'atu, hakan kuwa aka yi, inda Ƙanin Baba ya je nemawa Ubaidullah auren Abi'atu ba tare da sanin Abi'atu ko Ubaidullah ba, amma kowa ya sani daga ciki kuwa har da Hafiza duk da Mama tace babu wani gayyar da za'ayi daura aure ne kawai, Hafiza kuwa ita ce ma a kan gaba wajan ganin auren ya tabbata. Abba cewa ya yi, ai Ubaidullah tamƙar Safwan yake dan haka ba komai ai, ya basa Abi'atu, har aka tsaida ranar biki ba mai tsayi ba, wata daya kacal. Mama tasa Ubaidullah ya haɗa akwati a shagonsa kayan lefe masu rai da lafiya, amma ba tare da ya tambayeta nawaye bane, dan ko da kayan shagon duka Mama tace tana so, zai kwaso ya kawo mata balle ta ce ya hado lefe ya kawo, har biki ya rage sati daya Ubaidullah bai sani ba tun da bai cika zaman gida , Abi'atu ma bata sani ba, tun da ba shale aka yi ba, yan uwa ma da suka ji suka ce tun da ba taro za'ayi ba, wasu ba sai sun zo ba. Ko da aka tashi ranar daurin Aure Ubaidullah baya nan tun da ba wani jama'a aka tara ba, sai su Umma dasu Inna da sauran yan uwa da abokan arziki haka ma gidan su Abi'atu. Ranar da aka daura aure Ubaidullah ba a gida ya kwana ba, sai da ya yi kwana biyu baya gida har yan uwa wa in da suka ɗan leko suka fara watsewa, tun da Mama ta ce babu wani shagali da za'ayi yanzu sai ta tashi tarewa. @@@@@ Ko da Ubaidullah ya dawo gida babu wanda ya gaya masa cewa anyi aurensa, Hafiza ce dai ta kira su Zaidu ta fada musu amma ta ce kar su fada masa dan shi ma bai sani ba auren yazo a baibai ne, ai kuwa Zaidu ya din ga yiwa Ubaidullah tsiya shi da Hafiza da KB su na dariya. @@@@@ Yau sati daya da auren Ubaidullah da Abi'atu, yau kuma ta kama jumma'a, an daura ranar jumma'a ne, sauri take yi zata fita aiki dan akwai labarin da take son yaɗawa sannan tasa a buga a jarida, labarin wani da yasa aka shiga aka yiwa matar makwabcisa fyaɗe. Har ta gama shirinta ta fito ta samu Ummi na zaune a parlour tana cin abinci, durkusawa Abi'atu ta yi ta gaida mahaifiyarta, da kallo Ummi ta bita da shi ta ga tasa hijab dinta, murmushi Ummi ta yi ta ce. "Yar gidan Abba sai ina kuma?" "Wallahi Ummi sauri nake yi zan je aiki akwai labarin da nake son yaɗawa yanzu ne, shi yasa nake sauri na je." "Ayya Abi'atu kiyi hakuri kar ki fita, ki kirawo Shafa'atu (cousin sistern Abi'atu ce wanda suka yi skull tare, kuma waje daya suke aiki, Shafa'atu bata cika zuwa gidan su Abi'atu bane yanzu, saboda kunyar Ummi da take ji, tun sadda Safwan ya ce yana sonta har aka musu baiko) sai ki bata ta je ta yaɗa." Gaban Abi'atu ne ya fadi ta ce. "Haba Ummi me ya sa, kwana biyun nan na lura kina son hanani fita meyasa to?" "Akwai dalili ne Yar Abbanta,yanzu dai yi hakuri ki koma ki kirawo Shafa'atu" tashi Abi'atu ta yi kwalla taf a idonta. "Ko dai su Ummi su na so na bar aiki ne?" take tambayar kanta bayan ta koma daki tayi wulli da takardun hannunta ta zube a gefen gado, sai da ta gama tunaninta kafin ta kira Shafa. Su Ummi kuma so suke su bata mamaki dan sun dauka akwai soyayya mai karfi tsakanin Abi'atu da Ubaidullah ne, ba su san da cewa kullum idan suka hadu sai an kai ruwa rana ba. @@@@@@ Yawancin kullum Hafiza idan Yayanta na gida to fa, sai ta ja shi izuwa gidan su Abi'atu, kuma idan sun je sai sun jima, duk da Ubaidullah yanzu baya zaman gida sosai, sabida binciken da yake zuwa yi yana sa ana kama miyagun mutane, dan ya ce ko ta haka Allah zai sa ya kama wa inda suka yiwa kanwarsa fyaɗe. Ko da Ubaidullah ya je gidan su Abi'atu ba wani shiri suke yi ba, akwai ranar da Hafiza ta ja shi bayan sallar isha'i suka je gidan, tana ƙirawo masa Abi'atun ta saffe ta koma gida ta kwanta ta hau baccinta abunta. Ranar har wajan karfe sha'biyu Ubaidullah su na zaune da Abi'atu ba tare da sun san dare ya yi haka ba duk da ba magana suke ba zaman kurame ne, su Abba da Ummi kuma basu damu ba tun da mata da miji ne, sai da Ubaidullah ya duba agogo ya ga sha biyu kuma ya ji shuru din Hafiza ya yi, yawa yau bata leƙo tace Yaya muje gida ba, sai da ya yatsine fuska kafin ya mike ya cewa Abi'atu ta je ta dubo masa Hafiza su tafi gida. Ba tare da Abi'atu ta amsa va ta je ta gama dube dubenta bata ga Hafiza ba, dawowa tayi ta fada masa, hankalinsa ta shi ya yi, da zai kira Mama sai ya fasa ya kira mai gadi nan yake shaida masa Hafiza ta dawo tuntuni. Tafiya Ubaidullah ya yi,ba tare da ya ce mata sai da safe ba, itama tabe baki tayi ta ce. "Allah ya raka taki gona" tana shiga sukayi karo da Ummi gabanta ya fadi ta dauka Ummi zata mata faɗa ne harta fara tunanin kalar abun da za ta yiwa Ubaidullah idan Ummi ta yi mata faɗa sai ta ji ta ce. "Ahh yar gidan Abba sai yanzu, ina Ubaidullah din sai yanzu ya tafi?" Sosa keya Abi'atu tayi saboda kunya ta ce. "Eh Ummi" daga haka ta shige dakinta da gudu Ummi tayi murmushi, itama ta fito daukowa Abba ruwa ne. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ko da Ubaidullah ya koma gida sai da ya fara shiga duba Mama dan hakan har ya zame masa jiki, Mama ta ce. "Daga Ina kake ne Yaya Babba?" Ba tare da tunanin komai ba ya ce. "Daga gidansu Abi'ah nake" ya fada yana masa sai da safe,Allah ya kaimu Mama ta ce dashi. Tana tunanin ai gwanda matarsa ta tare kawai, ya fi wannan sintirin da yake yi kullum kar su jawo kansu abun magana tun da dai har an daura aure ai babu abun da ya yi saura. @@@@@ Da washe gari Mama ta kirawo Ubaidullah ta ce ta ba shi nan da sati ɗaya ya gyara part dinsa *Matar shi zata tare*, cike da rashin fahimta ya kalli Mama ya ce. "Mama ni da banyi aure ba wace mata ce gareni da har zata tare?" "Ka ji shashancin banza, in ji waye yace baka da mata, to auren yau kwana goma kenan, kuma har fada musu zata tare nan da sati daya yau din nan, idan ma akwai wani abun da zaku shirya kuyi gwanda kuyi sirkata ta dawo gareni gabaki'daya" Ka sa fahimtar maganar da Mama take fadi Ubaidullah ya yi, ya ce. "Mama kina ta maganar ina da aure wacece matar kam?" " *ABI'ATU*" dum!dum!dum gaban Ubaidullah ya fadi sai kace mace, zai kuma yin magana Hafiza wacce take maƙale tana jin maganar da Mama da Ubaidullah ke yi ita kuma su na waya da Zaidu tana fada masa abun dake faruwa saurin katse wayar ta yi ta ce. "Yaya zo ka ji" ta ja hannunsa suka fita waje nan ta kwashe komai ta fada masa yanda auren nasa ya kasance, kwafa Ubaidullah ya yi, ya fice dan shi baya da ra'ayin aure yanzu amma yarinya ta mayince sai da ta aure shi, to zata gane kuranta ne. Ta bangaren Abi'atu itama drama aka yi da ita sosai da aka fada mata cewa tana da aure zata tare nan da sati daya nan ta dinga musu bori ,abun har mamaki ya din ga bawa su Ummi, suka hau tantama ko da ma ba soyayya suke yi ba, sunyi kuskure ne da basu tambayeta ba, wai su a nufin su zasu bata Mamaki dan tayi farin ciki ashe comedy ne za a kwasa. Ana saura kwana uku babu yanda su Afnan ƙannan Zaidu ba su yi ba, akan zasu yi party amma Ubaidullah da Abi'atu sun ƙi ƙememe, an dai samu anyi walima ƙayatacciya wannan ma Anty Ummu ce ta hada Inna kuwa sai cewa take yiwa Abi'atu. " Yarinya kin shiga uku an haɗaki da mala'ikan duniya." Mama da kanta ta kai Abi'atu ɗaki tayi mata nasiha sosai, tace kuma karta dauke ta a matsayin surka dan tana auren ɗanta har kwanan gobe ita tamkar mahaifiyarta ce wacce ta haifeta a cikinta. Abi'atu tasha kuka Anty Ummu sai tsiya take mata tana cewa bayan ko ihu kikayi Ummi zata ji ki, ai ke kam auren dadi kikayi, dan ma za ki ji ki kamar ma ba aure bane duk da aure ya wuci wasa ayi hakuri da juna, sosai Anty Ummu ta yiwa Ƙaninta da Matarsa fadan su zauna lafiya, su Zaidu basu samu damar zuwa ba. Hummm ango shi ka dansa ya zo ko kallon dakin amarya baiyi ba, itama amarya ana watsewa ta rangaɗa wankanta tabi lafiyar gado. Tun da aka kawo Abi'atu a matsayin matar Ubaidullah rashin shirinsu ya sake bunƙasa, dan kuwa zaman doya da manja suke yi. A badadi su na gara juna har aka ɗibi wata uku. Mama kuwa da Hafiza da Anty Ummu sosai suke jin dadin zama da Abi'atu, duk lokacin da taso zuwa gida kuwa zata zari hijabinta suje ita da Hafiza, yanda Hafiza take mu'alama da yar uwarta Na'ilah haka Abi'atu ta zama dan ta farantawa Hafiza rai, hakan kuwa Abi'atu ta kara samun daraja a idonsu Mama. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Tsaye suke sun ƙame waje guda, daga kansu kasan meeting ake yi, yayinda General Murtala ke jawabi. Ban da kakin sojoji babu abun da yake kashe maka ido. Cikin tashin hankali General Murtala ke magana akan yan matan nigeria kwantena uku da aka yi garkuwa dasu a kasar india a yankin bangalo, ana neman jami'ai wanda zasu je domin su dawo da wa in nan yan mata, nan aka shiga lissafo wa inda zasu je, amma abun takaici yawancinsu sun ce ba zasu iya zuwa ba, saboda mutanen da suka yi garkuwar su na da mugayen makamai. Ran General Of The Army ya baci sosai, nan ya hau masifa, har yana cewa, tun da Ubaidullah yabar barracks komai ya daina tafiya yanda ake so. Muryar Zeey aka ji tana cewa. "Taya kuwa komai zai tafi yadda akeso tinda akwai munafukai da yan hassada da makirai, yau ranar tonan asiri ne, a barracks din nan domin ance karshen alewa kasa, rana dubu ta b'arawo rana daya tak ta me kaya" gaba daya aka zubawa Zeey ido ta tsuƙe cikin kakinta fuskarta babu walwala hannunta dauke da wasu takardu. Ta ce. "Hakika ita karya fure take bata ƴaƴa, kuma kowa yasan gaskiya, dan haka zan tona asiri koya ya kasa kunnuwansa da kyau, sannan dole wanda aka zalunta idan ya ce bazai yafe ba, masu laifi su shiga kotu." ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *TO HAR AN ZUBA IDO DA KUNNUWA DAN AJI TONAN ASIRIN DA ZEEY ZATAYI KO? L😉LZ TO BA ZA KU JIN BA SAI A NEXT PAGE* A CI GABA DA KAFCE 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️DAN AKWAI ƘURA MOMYN AHLAN TA KU CE👍🏻😉🤾🏻‍♀️👯🏻‍♀️🏃🏻‍♀️[8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_DAN ALLAH YAN UWA, A DIN GA SA HAKURI DA UZURI 👏🏻 WLH NI IDAN NAYI POSTING BANA SAKE BUDE GRP IN DAI BA GRP DINA BANE, AKWAI WASU GRPS DIN MA BANA BUDEWA IN DAI BA POSTING ZANYI BA, KO ZAN SHARE SAKONNIN, TUN BA YAU BA NAKE SON YIN MAGANA ALLAH BAI BANI IKO BA, IDAN NAYI POSTING KINA SO DAGA FARKO KI BINI PC NA TURA MAKI, KARKI JI HAUSHI KIN MIN MAGANA A GRP BAN GANI BA KI JI,HAUSHI HAR GA ALLAH BAN JI DADIN WANI MAGANA DA AKA GAYA MIN BA, IDAN KUMA BANI NAYI POSTING DIN BA, WANDA SUKA YI KI MUSU MAGANA TA PC SU BAKI, ALLAH KA KARA MANA HAKURI DA UZURI GAMI DA FAHIMTAR JUNA, AMEEEN_* ( _GASKIYA YANZU YAN WATTPAD BAKU COMMENTS NA KUSA NA DAINA MUKU POSTING TUN YANZU BAKU SON BUK DIN_🤒🤒) ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *_YAU FA PAGE DIN NA KU NE 💃🏻 MASU COMMENTS GASKIYA KUN SAKANI NISHADI A PAGE DIN DA YA GABATA DAN HAKA KU WATAYA DA WANNAN, GA KU NAN KAMAR HAKA_*👇🏻💃🏻 *princess* *Surayya usman* *Farhat mrs mj* *Amina yayaji* *Dr,herpsert* *Ma'eeshatii twinkle* *Fadheelatii* *Asamau umar gajam* *fareesatii* *nafeesat* *Mom ayman* *Faeexetion* *firdausi mrs mubarak* *Maman zarah* *Maman abdul* *Bilkisu sulaiman* *Maman yan 2* *Kcubraah* *Ummi suraj* *Ummu imam* *ummi* *Mrs Faruq* *Maryam abdullah* *maman afreen* _________________ *@⁨I LOVE MY FAMILY* 🥰⁩ *@⁨Hassana Suleiman⁩* DUBAI FANS _______________ 😍 aha a fa duba da kyau, duk wacce bata ga sunanta ba, ban ga sharhinta bane, sai ta tareni a page na gama,a kara dagewa da sharhi, 😍 ni kuma zan din ga kyautar page gareku masoyana, a kafta. 🤾🏻‍♀️ ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°71&75* "What do u want to say Zeey?" cewar General Of The Army, rai bace Zeey ta fara magana. "Abubuwa dayawa sun faru, but babu wanda ya bada mahimmanci ganin an yi bincike an gano sahihin gaskiyar abun da ya faru, kowa ya yi watsi da case din Captain Ubaidullah tun da yabar barracks din nan, duk da kuwa ya yi aikin tuƙuru" Wajan shuru ya dauka sai ka ce ba mutane ana sauraron Zeey, ya yinda zuciyar Rumaisa ji take kamar ana daka, dan tana tsaye a wajan itama, kuma Zeey da ta shigo ta watse mata wani kallo wanda ta kasa fahimtar me kallon yake nufi, dan haka ta miƙe subul zata bar filin taron, Hanan da Raihana da Doratie suka tare ta, Zeey ta ce. "Hamshaƙiyar munafuka! Ina za ki? Tun ba ki jira kin ji abun da zan zayyano ba, kina neman haryar guduwa?" "Duk da bincikena ya daukeni tsawon lokaci, amma alhamdulillah sai hakan ya zama alkhairi, dan yau ba ƙaramin yagaki zan yi ba." "Idan lissafina ya yi dai-dai yau tsawon kimanin 9 to 10 months, da barin Ubaidullah aiki, and Rumaisa kin ce ya miki ciki, 4now i think ya ci ace kin haihu, kin haife abun da yake cikinki hakane?" zazzare ido Rumaisa ke yi ta kasa bada amsa, Zeey ta ce. "Hanan, ku hauro da ita gaban kowa ya ganta yadda suka wulakanta Captain a bainar jama'a, haka su ma yau karyarsu zata kare, dan kare fure take bata ƴaƴa" ai kuwa su Hanan suka cafko Rumaisa suka daura ta saman mumbari sai zufa ne ke keto mata ta ko ina, a sassar jikinta. Zaidu duk abun da ake yi yana video recording, dan kuwa tare suka haɗa baki yau za ayi tonon asiri. KB kuwa ya sakawa S Ema Ido dan shi ma duk ya daburce tun ba a je ko ina ba, dama hausawa su na cewa marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Gaban Rumaisa Zeey ta tako ta zo, fuskarta tamau, ta ce. "Ki bamu amsa Rumaisa, and ko da sau daya ne da Captain ya bar barracks din nan ban ga kinyi wani laulayi irin wanda masu ciki ke yi ba, idan ta samu ciki, akasari ma ban da iskancinki da kike sheƙawa a barracks din nan, wanda nan gaba zan ambato sunan abokin cin mushen naki! Rumaisa ko da sau ɗaya ne ban ga ciki ya girma a jikinki ba, shi kuwa ciki, ko da ka boyesa baka faɗeta ba, ita zata bayyana kanta dan ciki bata b'uya, ko wani anan ya ga Rumaisa da katon ciki tsawon wannan watannin?" nan jama'a aka hau girgiza kai masu cewa a'a su na fadi, sai yanzu suke bin abun daki-daki, da hankali da basira, ya yinda manya suka shiga ruɗu na ganin babbar kuskuren da suka tafka, in dai Ubaidullah na da laifi su sun fi sa laifi a matsayinsu na manya da basu bada mahimmancin bincike ba. "Rumaisa!!" Zeey ta ambata da karfi, wanda sai da hanjin cikin Rumaisa ya kaɗa sabida tashin hankali, nan mahaifin Rumaisa ya fito yana yiwa Zeey katsa'landan, Zeey ta ɗaga masa hannu. "Dakata! min tsohon najadu, kowa tarrr nake kallonsa a barracks din nan, ban zo kanka ba tukunna , karka katsemin hanzari, dan yau ko da General ne ba zai dakatar dani wajan fadin gaskiya ba balle kai stall sergeant" shuru Baban Rumaisa ya yi yana wulli-wulli da ido. "Rumaisa da ke nake yi, ina labarin cikin da kika ce Captain ya miki?" cikin in'ina Rumaisa ta ce. "Ai cikin ya zube ne" "Au haba? Da gaske cikin ya zube? Tun da zubar ciki tamƙar fitowar fitsari ne da har zai zube baki kwanta a gadon asibiti ba? Amma fa ba wai ina nufin na karyata ki bane, yaushe cikin ya b'are?" "Ammm uhumm hummm eh wata biyar da suka wuce" "Au da gaske? Shi kuma cikin da yake jikinki kimani wata biyu yanzu na waye ne!?" Dum!dum!dum!dum! Gaban Rumaisa ke bugawa, zazzare ido take yi, ya yinda zufa bai fasa tsatstsafo mata ba, hannu Zeey tasa ta shafo zufar fuskar Rumaisa ta ce. "Rumaisa, wannan zufar duk na menene uhum?, mai gaskiya fa hankalinsa baya tashi, kuma fa naga ba tsareki akayi da bindiga a kai ba, yo ni ko tsareki akayi da bindiga ai ba zakiyi wannan zufar ba in dai kina da gaskiya, da ga tambaya? Cikin da yake jikinki yanzu watan shi biyu shi kuma na wanene? Ko shi ma na Captain din ne?" "Kee! Ya isheki haka Zeey! ba fa tsoronki nake ji ba!, da zaki wani sakani a gaba kina min tambaya sai kace wata Uwata! Uban waye ya ce ina da ciki, babu wani cik...." maganar da Rumaisa bata samu damar karasawa ba kenan, sakamakon wata gawurtacciyar marin da Zeey ta ɗauketa da shi sai da ta kifu ta buga baki sai ga jini. "Ke har kin isa ki daga min murya Rumaisa? Da kika cewa ni ba uwarki bace bana fata Idan nayi aure Allah ya bani ƴa kamarki mashanranciya munafuka!, sannan a ta wani fanni ni nafi karfin uwarki! ko ubanki!, dan kinsan duk matan barracks din nan babu wacce ta kaini zafi, idan kuma akwaita ta ɗaga min hannu, tambayarki nake yi dan musan gaskiyar lamari, kuma ni ban daga miki murya ba, me yasa ni za ki daga min murya? Ko ni mate dinki ce?" Filin taro kamar ba kowa, dan kuwa rashin gaskiya ya bayyana ƙuru-ƙuru a fuskar Rumaisa, dan haka su General Of The Army, General, Major General, General, Colonel, Brigadier lieutenant Colonel duk manyan wajan babu wanda ya dakatar da Zeey ko kuma ya katseta ko ya ce abun da take yi bai dace ba, sabida yanzu mafita suke nema, dan nadama ta fara kamasu, su na so su san gaskiyar lamari dan a samu a ba wa Captain hakuri ya dawo bakin aikinsa dan a samu a ceto rayuwar yan matan da aka yi garkuwa dasu, sabida rayuwarsu tana cikin hatsari. Marin da Zeey ta kifawa Rumaisa sai da ta ga gittawar wasu taurari a idanuwanta da fuskarta, network din kanta sai da ya je hutun wucin gadi, kafin da kyar ta miƙe tsaye tana dafe mararta wanda ya murɗa mata lokaci guda. Kuka Baban Rumaisa ya saka gami da cewa ana so a tozarta sa shi da ƴarsa, amma babu wanda ya sauraresa. Ganin badaƙalar tana yin yawa ne, kuma ga shi asiri yana gaf da tonuwa ya sa, S Ema neman hanyar da zai fece daga filin taron, amma me tuni KB yasa masa kafa ya fadi gami da cewa. "To Almirin'jaki, baƙin munafuki algungumi, ina zaka je?" nan aka juyo ana kallon S Ema, Zeey ta ce. "Shi ma wai guduwa zai yi ko? Hahaha ina son irin haka, KB riƙesa da kyau ban zo kansa ba tukunna" "Rumaisa ke muke saurara?" Cikin rawar murya Rumaisa ta ce. "Ni kam sharri! Kike so ki min, amma ni kam bani da wani ciki." "Au haba? To shi kenan, Dr Mark!?" Zeey ta kwalawa Dr kira wanda dama yana kusa, babban likita ne a cikin asibitin dake barracks yawanci idan ciwo ya yi tsanani shi yake duba marasa lafiya masani ne sosai ta fannin aikinsa, kuma babban mutum ne dan a kalla shekarunsa zai iya kai wa 69 yawanci ana girmamasa a barracks din sosai. Tun da Zeey ta ambaci sunan Dr Mark, hankalin Rumaisa ya sake tashi, fitowa Dr Mark ya yi, dan shi ma Ubaidullah mutuminsa ne sosai, kuma yana son Ubaidullah, sabida kamun kai din Ubaidullah yasa yake birgesa,duk da yana barracks din amma bai san abun da ya faru da Ubaidullah din ba, tun da baya shiga hidimar fannin aikinsu yafi zama wajan fannin aikinsa, hawa kan mumbari Dr Mark ya yi, sannan cikin girmamawa Zeey ta zo gabansa da takardun hannunta ta ce. "Baba Mark, kai ne ka gwada Rumaisa shekaran jiya har result ya fito jiya,a in da ka gano tana da jaririn ciki na tsawon wata biyu haka ne?" cikin harafin turanci suke magana. "Shakka babu, nine nan na au'na ta kuma ga result din a hannunki, tana da jaririn ciki na wata biyu" "Good! Ko Rumaisa ta taba yin b'ari wata biyar da suka wuce? Tun da dai nasan babu wani asibitin da zata kwanta in dai bana cikin barracks ba?" "No, bata kwanta ba, cox 2years kenan yanzu ban yi tafiya ba, ina nan, balle ace ko bani nan wani Dr ya dubata." "Tnk u sir" cewar Zeey, kafin ta juyo ga Rumaisa, wacce hankalinta ya kai ƙoluluwa wajan tashi, dan tasan karyarta ya kare yau. "Rumaisa lokaci ya yi, da za ki bude baki kiyi magana, shawara ce nake baki,tun kafin na bayyana wani video kuma idan har na bayyana videon nan ba kiyi magana ba hummm! Rumaisa ni a karan kaina bansan abun da zan iya aikata maki ba, gwanda ki bude baki kiyi magana, First Lieutenant KB ka hauro da S Ema." Nan KB ya hauro da S Ema wanda shi ma yake zare ido, Zeey kallonsa take yi ranta bace ta ce. "Zaku yi bayani ne ko kuma sai na saki videon? Kunsan halina wajan bincike bana sanya barin ma wanda na saka kaina, akan Captain zan iya muku komai, dan haka zaku faɗi gaskiya ne ko har yanzu zaku ci gaba da kauce-kauce da neman hanyar guduwa, ko kuma kokarin shirya drama, kai za kayi bayani ne, ko kuma karya za ka yi kamar yadda ita...b sai na karasa ba dan ka fi ni sani abun da nake nufi ko?" Shuru S Ema ya yi gabansa na faduwa suka haɗa ido da Rumaisa, sai zufa suke yi, Zeey ce ta ce. "Bana son aiki da bata lokacin dan hak..." "No! Pls!" cewar Sergeant Ema. "Zan fadi gaskiya duk abun da na sani." "Yauwa dan gari, muna sauraron ka?" "Lokacin da nazo barracks din nan Captain baya nan amma ina jin labarinsa, kasancewar ni mutum ne mai ƙyashi da hassada, da haka har alaƙa ta shiga tsakani na da Rumaisa, har take bani labarin Captain Ubaidullah da yanda take son sa take sha'awarsa, ko da Captain Ubaidullah ya dawo daga tafiyar da su kayi na ganin gida, na ga yanda ake ba da labarinsa yana da kyau da gwarniji kamala, haiba, nasaba, kamun kai, ji da kai, jarumta, gwarzon maza, ƙi gudu sa maza gudu, dana gansa sai na ga duk yafi yadda ake bada labarinsa, da haka ne Rumaisa ta zo ta sameni wata rana da wani video karami wanda ta rungume Ubaidullah har ya wanka mata mari, to wannan videon ne muka haɗa lokacin ne muka kwanta da Rumaisa a karo na farko sabida ta ce tayi alwashi sai ta muzguna masa, fuskata ne muka yi amfani da shi muka saka fuskar Captain, wanda da shi ne aka samu madafan dafawa domin a tozarta shi ya aureta, shi kuma ya ƙi, ko bayan faruwar hakan da ya bar aiki bamu daina mu'amala da Rumaisa ba, kuma babu wani ciki a tare da ita lokacin, munyi wannan videon ne dan mu kawar da tunanin manya dan kar ace aje a au'nata, kuma munyi nasara a wancan lokaci, kuma ko yanzu cikin da yake jikin Rumaisa nawa ne, wannan shi ne gaskiya abun da ya faru wanda na sani amma dan Allah ayi hakuri bazan sake b..." "Shut up!!'' Cewar Zeey ta katse sergeant Ema idanunta sunyi ja, juyawa ta yi ta kalli manya ta ce. "Kun gani ko? Kun gani ko? Abun da muka ta fama ku fahimta kenan tun kwanaki amma kun kasa fahimta, ba iyakar binciken da nayi akan Rumaisa ba kenan, domin tun lokacin da Captain ya bar barracks na fara bibiyar rayuwar Rumaisa da duk wani shige da ficenta, ko da muka je bauchi nice kawai bani nan amma duk abun da ke faruwa ina sane dashi, idan wannan hujjar bai isheku ba, sai na sake muku wasu wanda zaku gansu ƙuru-ƙuru, kuma Wallahi Rumaisa idan har ba ki buɗe baki kinyi magana ba ko, Rumaisa idan na rufeki da duka sai na kaiki lahira kuma na kashe banza! Idan kince wasa ne to mu zuba mu gani!" Nan Rumaisa ta zube kasa tana kuka, tana cewa ta tuba a yafe mata, Major Usman ya ce. "A tafi da Rumaisa da S Ema a saka su a guardroom, kafin a san abun yi" nan Rumaisa ta hau ihu tana kuka tana magiya, Babanta ma yanayi, amma ina babu wanda ya saurare su, nan fa aka ce an kira secret meeting a secret room wanda manya ne kawai zasu yi wannan meeting din, dasu Zaidu da KB, amma daga ciki har da Zeey. Ko bayan da aka shiga secret meeting magana ce ake yi akan ya za ayi aje a bawa Ubaidullah hakuri ya dawo bakin aikinsa. Zeey ta ce. "Captain Zaidu ka kira mana Captain Ubaidullah" Murmushi Zaidu ya yi, ya ce. "Nasan halin Ubaidullah sarai, ba zai taba yarda ya dawo ta dadi ba, but let me try my best" Zaidu ya faɗa yana kokarin kiran Ubaidullah. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Tsaye take a gaban dress'mirror ta fito wanka ranta bace, rigimar da suka yi da Ubaidullah ne idan ta tuno yake bata mata rai, sabida maganar da ya gaya mata duk da a gabansa bata nuna taji haushi ba. Towel ne a jikinta ta sincesa ya fadi kasa, tunowa da maganarsa ta karshe tayi in da yake ce mata. "Kwaila, yo ke miye kike rufewa? Yaushe kika girman? Me kike dashi wanda za ki burgeni ko ki tafi da hankalina,miye a kirjin naki abu fili, yarinya yar firit dake sai baƙar jaraba da iyayi, ji be ki fa, yar abu dake!" Rintse ido tayi ta ce. "Hummm! Ni ce ka kira da yar abu? Zaka gane shayi ruwa ne, wallahi sai kayi yaren garinku in dai akwaita" ta dauki towel dinta ta daura ta bude wardrobe ta dauki english'wears dinta wando da riga, duka-duka wandon da kaɗan ya wuce mazaunanta, sai kuma wata yar fingilar riga marar hannu, wanda ko saman shafefen cikinta bai sauƙa ba, ta sharce gashinta ta zubo da wasu ta gaba, ta hada sauran ta tufke a tsakiyar kanta, ta shafa lipstick ta goge fuskarta, nan ta juyo ta kalli kanta a madubi tasan fa ta gama kyau ne, murmushi ta yi ta saka flat'shoe ta dauki humra wanda Ummi ta bata, ta mulkawa jikinta nan ta hau wani tashin ƙamshi wanda duk namiji mai lafiya idan ya ji sai tsuminsa ya tashi, wayarta ta dauka ta dauki earpiece ta saka, ga shi dai ba waƙa ta saka ba, a'a kawai zata je neman rigima ne tun da yanzu tasan ya shigo. Ubaidullah na kwance a dogon kujerar parlour, ya baya tv baya, haka kawai yake jinsa wani iri, bai yi auni ba ya ji wani kamshi ya daki hancinsa wanda ta haifar masa da kasala gami da sha'awa, kamshin ya dakesa ne a lokacin da ta bude kofar ta fito, tana taku tana jijjiga, ga shi dama bata sa bra ba, ga wandon da ta saka sunan shi yaka muna wando ne. Tsakiyar parlourn ta zo tana dan taka rawa tana lumshe ido tana satar kallonsa,a hankali Ubaidullah ya juyo ta yi saurin juyawa tana ci gaba da rawar tana jujjuyawa. Dum!dum!dum! Gaban Ubaidullah ya buga sadda ya yi tozali da sintima'sintiman cinyoyin Abi'atu, a ransa ya ce. "Wallahi wannan yarinyar ba za ki kasheni lokaci na bai yi ba." "Keeeeeeee!" ya buga mata tsawa, amma ko gizau Abi'atu ba ta yi ba, balle ta gwada masa alaman ta ji, a fusace Ubaidullah ya miƙe ya fizgota, ya fincike earpiece din ya jefar gefe yana aika mata da harara. "Keee! Wannan wani irin iskancin shiga ne!? Na ce wani sabon iskanci ne!? Da za ki kama ki fito tsirara!?" "Au yanzu kai dama tsirara ka ganni saboda filin yaƙi ya cinye maka idanu?" ta faɗi tana murguda masa baki. "Ki wuce ki je ki sa kaya bana cike da iskanci!" "Ni babu kayan da zanje na saka bayan wa inda suke jikina, to wai ma ina ruwanka ne kam? Da shigar da nayi, idan na gadama na fito ma tsiraran miye damuwarka,balle ma ba tsarara na fito ba da kaya a jikina, ni da nake ƴar abu kuma yarinyar yar firit barni nayi shigan da raina yake so, kuma wallahi idan na....." maganar Abi'atu ne ya tsaya mata a maƙogoro bai karasa fitowa ba, sakamakon murɗe mata hannu da Ubaidullah ya yi, ta saki kara "wayyo Allah Mama hannuna, wayyo Mama zai karyani." "Eh ba dole ki ambaci sunan Mama ba, tun da kin lashe mata zuciya, duk babu wanda yake ganin laifinki,ai basu san marar kunya suka ɗaura min ba." Duk da zafin murɗe mata hannu da ya yi, ba shi yasa bakinta mutuwa ba. "Dama INNA ta fada an hadani da mugu, ga shi yana shirin naƙasani, yo da kake maganar na lashe zuciyar Mama idan ma hakan ne alhamdulillah naji dadi, su Mama basu ga munina ba ehe." "Dama taya zasu gani tun da ba zama suke yi dake ba?" "Ai kuwa sun fika zama dani, mutum dai marar godiyar Allah dama shi ai ba a taba masa abun....." cak maganar ta tsaya sakamakon bakinta da Ubaidullah ya cafka yana aika mata da wasu zafafa kiss, sumar tsaye Abi'atu tayi jikinta ya dauki rawa, kafafunta suka gaza daukarta nan tayi yunkurin sulalewa kasa ya bi ta,kokarin turesa take yi amma ance karfin mace da na namiji ba ɗaya bane, kuma ya mata haka ne dan ya yi maganin rashin kunyar da take masa, dan wani lokacin idan su na cacan baki da ita har mamakin kansa ya ke yi, amma yana cafkar bakinta wani dadi ne ya ziyarce shi har ya manta da in da yake da wacce yake tare, ga humra da ta mulka a jikinta mai fizgar hankali. Tun tana turesa tana kai masa duka har ta fara kuka. Ubaidullah baya cikin hayyacinsa, karar wayarsa ce ta dawo da shi hankalinsa dan kuwa ita ce ta katse masa hanzari, da kyar ya saki bakin Abi'atu ya mirgina gefe idonsa lumshe yana sauke ajiyar zuciya, yana ɗagata ta mike da gudu ta yi bedroom har da saka key, dariya ce ta kwace masa ya ce. "Ashe ke ƙaramar marar kunya ce, nan gaba abun da zan din ga miki kenan idan har zan faɗa ki fada" daga bedroom din ta ce. "Mugu an gaya maka tsoranka naji? Kawai dai na ga kana shirin aikata abun kunya ne da yar abu, kuma wallahi kaci bashi abun da ka min" Ubaidullah zai kuma yin magana wayarsa ta kuma yin kara, a hankali ya saka hannu ya janyo wayar dan jikinsa a mace yake murus, da jajayen idonsa na jaraba ya kalli screen din ya ga sunan My Man na yawo, da kyar ya dauki wayar ya saka a kunne ya kasa magana, cikin zolaya Zaidu ya fara gyaran murya mai cike da tsokana, Ubaidullah ya fahimci abun da yake nufi dan haka ya ja tsaki, cikin dasheshshiyar murya ya ce. "Ka ga bana son iskanci, fadi abun da ke ranka ko na kashe wayata" "Dama tun da na kiraka kam ai dole na fadi amma dai ina Madam bata kusa ko? Ko tana kusan ma ai abun farin'ciki ne" cikin tsokana Zaidu ke magana, shuru Ubaidullah ya yi, bai bawa Zaidu amsa ba, Zaidu ma baya da lokacin tsayawa su yi shirme tun da ga su General a wajan, nan ya shiga zayyano masa abun da ya faru tun daga AtoZ amma abun mamaki Zaidu na gama basa labari sai cewa ya yi. "To sai aka yi me?" "Sai aka yi ana so ka dawo bakin aiki mana" "Bazan dawo ba! Na ri ga da na hakura da aikin soja!" "Karya kake yi Ubaidullah! Sai dai ka fada ma wani amma ba dai ni ba, na san ka, ka sanni!" "Ko da zan ci gaba da aikin soja ba dai a garin abuja ba, ba zan dawo barracks din abuja ba Zaidu pls ka kyaleni" "Pls Ubaidullah ana bukatar taimakonka" nan Zaidu ya ba wa Ubaidullah labarin yan matan da aka yi garkuwa dasu, murmushin takaici Ubaidullah ya yi, ya ce. "Sai da amfanina yazo kafin za a nemeni ko?" "No, Ubaid.." "Bana son jin komai Zaidu, magana ɗaya ce, bazan dawo ba!" ya katse wayarsa, ya cillar da ita ya rasa me ke masa dadi, tunanin yan matan da aka yi garkuwa dasu ya shiga yi, yanzu ace akwai kanwarsa a ciki ya zai ji? Kuma yasan dole fasikanci za a din ga yi dasu ana bata musu rayuwa ta hanyar yi musu fyaɗe, rintse ido ya yi, take a ransa ya ji babu dadi saboda tuno halin da kanwarsa ta rasa rayuwarta, kwalla ne ya cika a idonsa, dan Ubaidullah duk fadin ransa yana da rauni sosai ta wannan fannin, ya shiga tunanin mafita, kuma baya son komawa barracks din nan, tashi ya yi ya fice ya bar gidan gabaki daya, dan zafi uku ne suka hadu masa waje guda. Duk yanda Zaidu suka yi da Ubaidullah su General sunji,ya yinda Major Usman ya ce. "Kunsan dole ne ya ji babu dadi, dama kuma ga shi yana da mugun zuciya, ni a ganina ya kamata mu shirya tafiya gobe ko jibi muje har Bauchi mu basa hakuri a matsayinmu na manya wanda kuma basu kyauta ba, idan ba haka ba rayuwar yan matan nan su na cikin hatsari, kuma da an rasasu durkushewar barracks din nan yazo" kowa ya yi na'am da shawarar Major Usman, in da aka ce su General da brigadier lieutenant colonel da Major General zasu je har gidan su Ubaidullah,da haka meeting din ta watse in da Zaidu da KB suka din ga godewa Zeey su na jinjina mata, duk inda ka wulga zancan Ubaidullah ake yi yau a barracks, sai Allah yawadaran masu hali irin na Rumaisa da S Ema ake yi, masu son shi su na fatan sake ganinsa a barracks very soon. Ko ba komai yau Ubaidullah an wanke shi da ga zargi, kuma ana jira ya dawo ya maka su a kotu. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Sai dare Ubaidullah ya dawo, part din Mama ya wuce ya sameta zaune a dakinta, nan ya shiga ya zayyano mata komai bai boye mata komai ba, Mama ta ce. "Duk hukuncin da ka yanke dai-dai ne, amma ina so ka je kayi tunani da kyau, idan zaka koma fyn idan ba zaka koma ba duk daya, Allah dai ya zaba mana abun da yafi alkhairi" ya amsa da ameeen sannan ya mata sallama ya wuce part dinsa Mama murmushi kawai tayi ta bi bayansa da kallo dan tasan har kwanan gobe yana son aikinsa na soja. Ko da ya shiga yau bai ga abokiyar tawayen tasa ba, kuma shi ma bai bi ta kanta ba, dan yana bukatar hutu da tunani. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari ma bayan sun gama cakwakiyarsu ya fice dan yau yana so ya je ya dubo shagunarsa ne. Da yamma ya dawo yana dawowa ta tashi da gudu ta yi bedroom, kuma kayan da take sakawa kenan yanzu guntun wando da yar fingilar riga. Bai jima da shigowa ba ya sake fita, bayan ya sake fita tana daki ta ji ana zabga mata sallama da gudu ta fito da ta ji muryar mai mata sallamar ba kowa ba ce face Shafa'atu rungume juna suka yi cike da murna kafin Abi'atu ta saketa tana harararta. "Wallahi Anty baki da kirki inace sai yau kikayi niyyar zuwa inda nake? Wata na nawa da aure?" "Kai mitau, ai wata ba shekara bane, balle ki sakani a gaba da mita, tun da yanzu nazo ai shi kenan, bikin da ba muyi shiri ba kawai sai ji muka yi anyi wuff da ke" suka kwashe da dariya nan suka hau hiran yaushe gamo, sai dare Safwan yazo ya dauki Shafa'atu ya kai ta gida. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari misalin karfe goma na safe, Ubaidullah yana shirin fita ya ji, jiniyar motar sojoji na tashi a gate dinsu, abun ba karamin mamaki ya ba shi ba, ba zato ya ga shigowarsu Zaidu da KB kafin nan sai ga Manyan sojoji, da sauri Ubaidullah ya karaso gabansu ya kame yana sara musu dan Ubaidullah yana da ladabi. Nan ya musu jagora har parlourn Mama, kafin kace me an cike musu gaba da kayan motsa baki Abi'atu da Hafiza. Bayan an gaisa suka ɗan taba kayayyakin motsa baki aka kawo musu, Mama zata mike nan Major Usman ya dakatar da Mama, sannan suka zayyano wa Mama da Ubaidullah abun dake tafe dasu, sannan suka hau ba wa Ubaidullah hakuri su na masa magiya, ji yayi duk sun dauresa da jijiyoyin jikinsa, harta Mama sai da ta sa baki da kyar Ubaidullah ya ce ya hakura nan ma sai da Zaidu ya saka baki, nan take aka miƙawa Ubaidullah takardan komawa bakin aikinsa tare da bindigarsa da sabbin kakinsa sannan aka ce masa jirgi na jiransa gobe sojoji zasu zo su dauko sa, sun jima a gidan kafin suka je gidansu Zaidu aka gaisa sama-sama dan sun bata lokaci gidan su Ubaidullah dan yau zasu sake komawa Abuja tunda a jirgi ne ba bata lokaci. Har airport Ubaidullah ya rakasu sannan aka bar masa wasu sojoji wanda zasu daukesa su kaisa airport gobe, rungume juna suka yi shi da abokansa sannan suka daga masa hannu alamum sai sun gan shi a barracks gobe, murmushi kawai ya yi, sai da jirginsu ya daga kafin ya dawo gida ya ba wa sojojin da aka bar masa umarnin su tafi barrack din bauchi gobe idan ya shirya zai neme su,suka amsa cike da girmamawa. Ba karamin dadi Ubaidullah yaji ba, har sai da ya yi hawaye, Mama da Hafiza Anty Ummu Matarsa Abi'atu da iyayenta da iyayen Zaidu babu wanda bai masa murna ba. Da dare yana kwance Abi'atu tazo ta same shi ta zauna kusa dashi yau ba kamar kullum ba ,cikin sanyin murya ta ce. "Hakika nayi farin'ciki da komawar ka aiki Allah ya taimaka ya bada sa'a, Allah ya daɗa daga darajanka" sosai ta din ga kwararo masa addua, wani sanyi ne ya ziyarci zuciyar shi, har da yi mata murmushi ya amsa da ameen gami da cewa ya gode, murmushin itama ta yi ta tashi ta koma dakinta. Da washe da safe Abi'atu ta roƙi Ubaidullah tana son komawa aikinta, nan ya amince mata tayi masa godiya, jirginsa karfe uku zai tashi, Abi'atu ta shirya har ta je aiki abun ta. A safen ranar Hafiza ta fita ta kai sako gidansu Abi'atu wa Ummi. In da wasu samari mutum bakwai a baƙar mota sun shigo layin sukayi arba da Hafiza tana tafiya ta fito daga gate din gidansu zata koma gidansu Abi'atu Mama ta aiketa, wani daga cikin samarin da suke motar yace. "Kai Bahba kalli wancan yar flawern" Wani ya ce. "Kai daga ganinta zata yi dadi, zata kai yanda ake so" wani ma ya ce. "Amma fa kamar mun taba operation a wannan gidan fa?" "Anya kuwa?" cewar wani daga cikin su. "Eh mana Bahba ka tuna mana , nidai ban manta ba wata yarinya tasa farin less muka sunkuceta a nan kofar gate din, kuma na ga su na kama ko dai yar uwarta ce?" "To kai Bangis yaushe ka fara tuna yaran da muka farke?" magana suke yi irinta yan iska b'ata gari. "Nima dai ban sani ba, amma dai nasan na tuna yarinyar." "To dai ku bar wannan maganar mu san yanda zamu dauke wannan yarinyar ko yau ko gobe in dai tana fita" haka kuwa suka zauna suka tsara plan. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Karfe sha biyu Abi'ah ta dawo daga aiki, gidansu kuma ta wuce dan an fara shirye shiyen bikin Yayanta, sai karfe biyu da rabi ta koma gida ita da kanta ta hadawa Ubaidullah kaya suka yi sallama, da kuka suka rabu da Hafiza, har Abi'atun ma sai da tayi kuka a boye, ba tare da ya gani ba, shima duk sai ya ji ba dadi, da haka dai ya shiga mota sojoji suka ja shi suka dauki hanyar airport. Da Ubaidullah ya tafi Abi'atu ma, magana ta yiwa Mama zata je su gaisa da wasu y Yayun Babanta Mama tace babu damuwa sai ta dawo itama zata shigo anjima. Abi'atu tana tafiya tayi gidansu ba jimawa Hafiza tacewa Mama itama zata bi Abi'atun gidansu dan gidan ya mata Shuru Mama ta amsa da to Hafiza sai nazo. Fitowa Hafiza ta yi, dai-dai lokacin da wannan samari su bakwai motar su tasha kwana, nan suka hango Hafiza tana tafiya, da sauri suka fara dan jan motar tasu, itama kuma har ta sha kwana wajan gate din gidansu Abi'atu, daidainan Abi'atu da Safwan suka fito a mota an bude musu gate zasu karbo sako me zasu gani? Wasu kartin maza ne suka finciki Hafiza suka ɗurata a mota ihu Hafiza ke yi tana tirjewa tana neman taimako suka toshe mata baki suka turata a motar da karfi. Cikin ɗimauta Abi'atu da Safwan suka saki ihu, da mugun gudu Safwan ya take mota ya bi bayansu sannan ya cewa Abi'atu ta kira Ubaidullah idan jirginsu bai tashi ba ya dawo, duba wayarta tayi taga ashe ma bata da lambarsa, ta ce. "Yaya babu lambarsa anan" Wayarsa Safwan ya wulla mata ya ce kira shi da nawa, nertwork din wayar Safwan ce ta dauke, da sauri ta dauki lambar a wayar Safwan ta shiga kiransa lokacin har ya fara taka matattakalar bene ya ji wayarsa na ringing ya dubawa ya ga bakuwar lamba ya yi tsaki bai daga ba. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️ Cakwakiya. Momyn Ahlan taku ce👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~~•~~•~~•~~~• *_Tun daga wannan page din har izuwa karshen wannan book din na ku ne my 5 stars._*✨ *My Doter Samira bint Abdallah*✨💋 *Dear Fatima Bintu Sagir*✨💋 *Sisina Farhat Mrs M'J*✨💋 *Antyn Ahlan Princess (Nafeesat)*✨💋 *Habibty احلام فاطمة*✨💋 💞💞 Naji dadin karar'ku a gareni son so domin Rabbi, Allahu ya taya muku.💞💋🙌🏻 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_Na so na kira sunayenku wa inda suka min sharhi a page din da ya gabata kafin wannan amma Allah bai yi ba, dan haka duk wacce ta min sharhi ta saka a ranta wannan page din kyauta ce gareta, kuyi yadda ku ke so da page din dan naku my ppl's ina so ku sani ni Zahra Abdul Momyn Ahlan taku ce inayinku._*💋 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°76&80* Kira Abi'atu ke yi ba ƙaƙƙautawa, sai da ta yi masa kira wajan takwas amma bai daga ba, dan lokacin da ta yi masa kiran farko da ya gani yayi tsaki sai ya mai da wayar cikin aljihun wandonsa, ya juya yana ba wa sojojinsa umarni. Kukan tashin hankali Abi'atu ta saka gami da cewa. "Yaya Safwa bai ɗaga ba fa, wayarka kuma netwrk ya dauke ya ƙi kawowa kwata-kwata!" A fusace Safwan yana jan mota yana kan bin wa inda suka kwamushe Hafiza ya hau saukewa Abi'atu ruwan bala'i yana mata masifa dan hankalinsa a tashe yake ,domin ko da ya iskesu ance sarkin yawa ya fi sarkin karfi, su bakwai, shi ɗaya ai ba zai iya ba, idan aka taki rashin sa'a suka kashesa suka jinkiɗar da Hafiza da Abi'atun ai an bata goma ɗaya bata gyaru ba, sannan ace zai fara biyawa kiran yan sanda ai kafin su iskesu sun yiwa Hafiza Illa idan ma an kamasun kenan, dan yasan by tym da zasu iso idan aka ta ƙarƙare sun gudu. "Iskancin banza da hauka! Numbern Mijinki amma ba ki da shi?Mijinki fa!? Da ace kuna da number juna har za ki din ga yi masa wannan kiran bai ɗaga bane, da ace kuna da numbern juna ya ga wannan kiran da kike masa yasan babu lafiya, ai sai ki ci gaba da kira, ko kuma ki nemi nerwrk a wayana ki ci gaba da kira, in kuwa ba haka ba, muna karasawa sai su kashemu duka a huta, mtswwww!" Kira Abi'atu ta ci gaba da yi tana kan kuka. Ubaidullah jirgi ya shige ya zauna, ana jiran jama'a su gama shiga jirgi ya tashi da zarar lokacin tashinsa ya yi, dabara ce ta faɗowa Abi'atu da sauri ta tura masa saƙo da cewa. " _*KAYI WA ALLAH DA ANNABI S,A,W) KA DAUKI WAYAR NAN, IDAN HAR BA KA ƊAGA BA, ZA A RASA RAYUKA (ABI'ATU CE)*_" ta tura masa, Ubaidullah ya ciro wayarsa yana shirin kasheta gaba ɗaya ya ga tarin miss calls da numbern dazu, mamakinsa bai gushe ba sai ga shigowar saƙo buɗe sakon ya yi, ya karanta sannan ya shiga wajan history yana shirin kiranta sai ga kiran nata na sake shigowa, ɗagawa ya yi, muryar kukan ne ya fara kaiwa dodon kunnensa naushi, gabansa ne ya shiga bugawa a kiɗime ya ce. "Abi'ah! Meya faru? Meya sameki? Wa ya taba miki?" cikin sheshsheƙar kuka ta ce. " *DAN ALLAH! DAN ALLAH! IDAN HAR JIRGIN'KU BAI ƊAGA BA KA DAWO AKWAI BABBAR MATSALA AN DAUKE HAFIZA!*" wani wawan zabura Ubaidullah ya yi ya miƙe da gudu yana buge mutane, yana sauƙowa daga step din jirgin Sojojinsa ne suka kallesa "Mota" shi ne kawai abun da ya iya furtawa, nan aka miƙa masa Mota ya shige ya bata wuta, cikin tashin hankali Ubaidullah ya ce. " *SU NA INAAAAA! INA ZASU KAI MIN ƘANWATA!?*" "gamu nan mu na kan bin su ni da Yaya Safwan, kayi amfani da location, Dan Allah kayi sauri kar su cutar da ita, ga mu nan dai sun dauki hanyar fita daga cikin gari" da sauri Ubaidullah ya yi connecting yana bin su da gudu, sai ka ce zai ta shi sama jikinsa sai bari yake yi, hankalinsa idan ya kai dubu to a tashe yake. Su na ta binsu har suka yanki kwanar bayan gari, sun dan yi tafiya kaɗan cikin wata yar jeji, kafin suka iso wani kangon gida, daga nesa Safwan ya parkar motarsa suka fito da Abi'atu, ya kamo hannunta su na tafiya a hankali su na labewa, maƙalewa suka yi, in da suka hango samarin sun fito da Hafiza sai fizgarta suke kamar kaza suka yi cikin babban kangon nan da ita, ganin sun shige da Ita yasa su Safwan mara musu baya, tuni Abi'atu ta hau video recording da ɗayar babbar wayar Safwan, wayarta kuma Ubaidullah yana amfani da location, a hankali suke bin ta bayan kangon su na duƙawa dan kangon mai girma ne, shiga ciki suka yi su na duddubawa, ga uban daƙuna a kangon, duk in da suke tunanin zasu ga Hafiza basu ganta ba, hankalinsu ne ya sake tashi, kafin nan wayar Safwan netwrk ya dawo, nan ya sake kiran Ubaidullah, yana ɗagawa ya ce. "Safwan! Ina Hafiza!?" "Kayi sauri kazo kawai Ubaidullah dan gamu nan a cikin kangon da suka shige da ita, sai dubawa muke yi amma bamu ganta ba dan kangon yana da girma" a hankali Safwan ke magana gudun kar su jiyo su, tun da su mafakar su ce sun san kan abun su. "Ina Abi'ah!?" cewar Ubaidullah Safwan ya ce. "Gata nan a gefena muna kan shiga ciki" "Pls Safwan karka bari ta yi nesa da kai, ka kula da ita dan taurin kai gareta irin na yan jarida ba ko da yaushe take jin magana ba, gani nan na kusan isowa wajan, ku ci gaba da duba kangon a hankali, kar su muku illa na kusan isowa!" "Eh muna kan dubawa, ina tunanin....." Safwan bai karasa maganarsa ba ya jiyo ihun Hafiza, wanda ya yi sanadiyyar sakin wayar daga kunnensa karar da Hafiza ta saka harta Ubaidullah sai da yaja wawan burki a tsakiyar hanya, ya yinda ya haɗa motoci garuwa, jikinsa ya dauƙi bari idanuwansa suka zazzago suka yi waje, hawayen ma ya ji sun ƙafe daga idanunsa, take jijiyoyin jikinsa suka fito raɗa-raɗa barin ma na kansa da wuyarsa kamar zasu tsinke, dan ihun da Hafiza ta saka kamar wacce aka farke mata gaba ne, kamar namiji ya shigeta, Mutanen da Ubaidullah ya saka su gwarene suka fara masifa ba tare da Ubaidullah ya bi ta kansu ba, ya wani figi motar sai da wuta ta fi daga salansa, ya ci gaba da sharara gudu, Safwan kuwa ihun Hafiza ne ya saka su juyowa saitin wani windown da suke a nan ne suka ɗaure Hafiza, ihun da ta saka kuma na matse mata nono da daya daga cikinsu ya yi ne, dan tun da take babu wanda ya taba yi mata abu makamarciyar wannan, ihu kuma sun kunci mata bakin da suka ɗaure mata ne, dan idan sun kawo yarinya sukan kunci mata baki dan duk ihun da zata yi babu mai jinta balle ya kawo mata taimako, kasancewar bayan gari ne, kuma cikin jeji, a nan ne suke sheƙe ayarsu da yaran jama'a, Abi'atu ta buɗe baki zata kwallara kara da sauri Safwa ya toshe mata baki, ya jata suka duƙa kasa, bakinsa yasa a saitin kunnenta cikin raɗa ya ce. "Karki yi ihun da zai sa su ganmu dan za ki bata mana plan, ki ci gaba da video din ni kuma zan san yadda zanyi, ke yar jarida ce kinsan kan bincike baya son tonon asiri dan haka ki kula sosai, ki sa a ranki kece kika fito yaƙi da miyagu, kin fahimceni?" ta gya ɗa masa kai ta goge hawayenta, suka miƙe a tare ya sake cewa. "Duk abun da za ki ga sunyi min karki sake kiyi ihu ko ki shigo har sai Ubaidullah ya shigo kinji? Dan ina so ne na dauke hankalinsu kar su cutar da ita" tana hawaye ta jinjina masa kai ta cigaba da video din, ya zo zai wuce ya shiga ta ji gabanta ya fadi da sauri ta riƙo hannunsa tana girgiza masa kai, a hankalin ya zare hannunta ya lumshe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta ,sannan ya shige yana neman kofar da zata sadashi da windown da suka ga Hafiza, ga dai kofofi amma ya rasa wace kofa ce, shawara a yanke kawai ya din ga bin ko wacce yana dubawa Adduarsa daya Allah ya kawo Ubaidullah yanzu karsu cutar da Hafiza. Abi'atu na kan video ta ga su ma sun kunna video camera ,dan kuwa basu banɗare yarinya ba tare da sunyi video din badala da barnan da suka yi ba, riƙe baki Abi'atu ta yi ganin mutane biyu da suka rufu akan Hafiza wacce ta fara ihu da kuka abun tausayi tana kiran sunan Allah da Yayanta. "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun! Ya Allah ka ceceni! Allah ka ceceni! Allah ka turo mai cutona! Yayanaaaaaa!!! Wayyo Allah Mamana! Wayyo Anty Ummuna! Wayyo Anty Abi'atu!" Abi'atu jin Hafiza ta ambaci sunanta ya sata kara riƙe bakinta gagam a ranta tana fadin. "Wai Ubaidullah ina ka tsaye ne!? Yaya Safwan kai ma ka kasa shiga ko dai sun gan ka ne!? Anya zan iya hakuri kuwa?" tana kan tunani ta sake tsinkayo ihu Hafiza da kukanta har tana tari, da sauri Abi'atu ta sake saita waya tana kan ɗaukarsu, ihu Hafiza ta sake sakawa da salati a lokacin da ta ji an farke mata riga duk da tana da vest, wani na shafata ta baya wani kuma yana lailaya yan nonuwanta da suka fara tasowa,ihu take tana fadin. "Ya Allah ka ceceni! Wayyo Allah Yayana! Yayana nima zasu kasheni! Wayyo Allah Yaya Ubaidullah!" ɗayan jin ta ambaci sunan Ubaidullah ya ce. "Kai guys kamar fa nima na so na tuna yarinyar da muka kawo, dan yadda wannan ke ihun kiran Yaya Yaya itama wancan kun manta haka ta din ga ihu tana salati tana kiran sunayensu" Bangis ya ce. "Ai BahBa na gaya muku, mu duba system din nan ai ba zamu rasa ba" nan kuwa suka shiga bincike a cikin system yaran da suka yiwa fyaɗe sama da dari duk su na da videon yanda suka yi lalata dasu, bincikensu kuwa har ta fado kan videon Margayiya Na'ilah, suka kalli Hafiza suka sake kallon Na'ilah, suka hada baki wajan cewa. "Wallahi su na mugun kama" juyo da system din suka yi suka nunawa Hafiza dake kuka kamar ranta rai fita suka daka mata tsaw. "Keeeeeeee! Kinsan wannan!?" kuka Hafiza ne ya tsaya cak ganin Yar Uwarta Na'ilah, ta ce. "Innalillah! Sismietaaaa! Dan Allah tana ina karku mata komai nasan tana nan dama bata mutu ba" tsawa suka sake daka mata da cewa ta rufa musu baki ta kalla, gani ta yi su na yagewa Na'ilah kaya duka su bakwai din suka rufu akanta babu wanda baya murzata, sai ihu take yi tana ambatar sunan Ubangiji tana kiran sunan Mama da Yaya Ubaidullah da Anty Ummu da ita Hafizan har da Abi'atu da Yaya Zaidu, kuka Hafiza ke yi tana miƙa hannu abun tausayi kamar zata kamo Na'ilah dan yau mutuwar ta zamo mata sabuwa, tun Na'ilah tana ihu har ta zo ta yi dif, Abi'atu dake rusan kuka a windown hankalinta tashe, idon Hafiza ya kaɗa ya yi jaaa jikinta sai kyarma yake yi da jan idon ta bi su da kallo ɗaya bayan ɗaya ta ce. " *Daman ashe kuneee!? Kune kuka kashe min sismieta!? ku ka saka ni a baƙin ciki da ka daici kuneeee!?" ta fada da karfi.* *"Haƙika idan Yayanmu ya kamaku gawar kare sai ya fi ku darajaaaa na rantseeeeee!!!*" ta fada da karfi take wani ya wanketa da marin da sai da bakinta ya fashe, ko kadan Hafiza bata ji marin ba dan kuwa gobarar da zuciyarta ke yi yafi karfin marin da aka mata, dayan ya ce. "To shi din Yayan naku waye shi!?" Murmushin kuka Hafiza ta yi ta dukar da kanta kasa ta ce. " *Shi din wani tauraro⭐ ne mai tsananin haske daga zuciya, a fuska mutum ne mai sassauci ga mutane masu rahama, ta wani bangaren kuma shi mutum ne mai zafi wanda zafinsa da azabarsa tafi karfin narkakkiyar dalma ga mutane azzalumai mugaye maha'inta, shi din DODON AZZALUMA NEEE! YAYANA DUK YANDA ZAN GAYA MUKU SHI BA ZAKU TABA FAHIMTARSA BA, DAN KU ALLAH BAI HALICCIKU DA FAHIMTA BA, DAN KUWA DUK YANDA ZAN FADA MUKU SHI YA FI HAKA, KU JIRA RANAR DA ZAKU HAƊE DA SHI GANGAR JIKI DA ZUCIYOYIN KU SUNE ZASU GAYA MUKU, KO SHI DIN WAYE, JARUMIN MAZA,WANDA SHI NE ƘI GUDU MAI SA A GUDU, KU JIRAAA! NA CE KU JIRAAA!!."* Tabbas maganganun Hafiza ya ɗan razana su amma da shi ke babu Allah da imani a ransu nan ɗayan ya ce. "Wai mun kawo yarinyar nan ne dan muyi juyen baƙin man mu ko dan ta gaya mana maganganu?" wani ma ya ce. "Kuma hakane fa? Mu afka mata kawai wannan shagen bakin nata zai yi shuru" Abi'atu ganinsu ta yi gadan-gadan sun rufu akan Hafiza, Hafiza na ihu da kuka kamar yanda ke yi Na'ilah har sun kwantar da ita daya na shirin b'urma ta zai shigeta, sai ga Safwan ya shigo da gudu ya ture wanda yake kan Hafiza ya banbangaje wanda suka danne mata hannu sannan ya ɗagata, bai ankara ba ji kake kwassssss! Take Hafiza ta sake razananniyar kara tare da furta. "Yaya Safwannnn!" a tare suka saki ihu da Abi'atu, dan karfe wani ya kwaɗawa Safwan a bayan wuya ne ko a ƙeya ne oho dan bata san taƙamemen in da aka buga masa karfen ba, dan kuwa karfe ne mai kacha irin wanda ake naɗa kachar a jiki ga karfen Babba ne, nan take jini ya balle Safwan ya zube kasa babu alamun numfashi bare ayi tunanin akwai rai a tare da shi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Kuyi hakuri masoya masu kirana ngd da masu jaje wai ko na bar book dinne, ban bari ba amma na gaya muku uzurina, ga wannan ku dan wataya da shi, aha fans ana tare 🙌🏻🙌🏻🙌🏻🙌🏻 Uwar Ahlan Taku Ce 👍🏻🙌🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°81&85* Ihun da Abi'atu ta yi, ita da Hafiza ya sa suka ji ta, suka wai go suka ganta, da gudu Abi'atu ta bar jikin windown ta zo ta hau neman kofar da zai sadata da in da suke ,amma ta rasa, muryan Ubaidullah ne ta ji ya daki dodon kunnenta yana kiran sunayensu, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarta amma ta can kasa tashin hankali ne, sunansa itama ta kira kafin ta juyo da gudu kenan suka yi karo, sai da suka haɗa ido da shi ta sake fashewa da kuka, a kiɗime yake tambayarta ina Safwan da Hafiza? Tama kasa magana sabida kukan da ya ci karfinta da kyar take yi masa nuni da window da kofofi, zai yi magana ya ji motsin mutane da sauri ya fizgota izuwa jikinsa suka maƙale ya rungumeta sosai ya mata rumfa ya ɗaura hannunsa a saman bakinta sabida kukan da ta ke yi, wasu maza uku ne suka fito dayan na cewa. "Ina yarinyar da ta yi ihun nan?" dayan ya ce. "Ko dai ta gudu ne?" "Ai kuwa bata isa ba mu bi ta, dan itama ta kawo kanta" nan suka fita yuuu dasu, su na wucewa Ubaidullah ya saketa ya ce. "Abi'ah, ki tsaya a nan ki jirani, karki fito ina zuwa bari na shiga kinji?" girgiza masa kai ta shiga yi alamun ba zata tsaya ba, ya santa sarai tun da ta ce ba zata tsaya ba, to fa ba zata tsayan ba, dan haka ya yi gaba ta bi shi a baya, kofar da ya ga maza ukun nan sun fito nan ya shiga, yana shiga tun daga farkon kofar jini ne ya fara karo da shi gabansa ya fadi, ga ihun Hafiza wacce maza uku suka da baibayeta, ga daya a tsaye yana video yana dariya, basu ankara ba suka ji kukan zaki wanda ya sakasu tsorata lokaci guda, daya daga cikin wa inda suka danne Hafiza wanda yake kokarin danna mata abarsa suka mike ba shiri, dago fuskarta ta yi da kyar a wahala take bude idonta dan kuwa tasha nauyin kartin banza, da kyar take iya juya idanunta ta kalli Yayanta, murmushin farin ciki ta yi ta fara hada kalmomi. "Y...ya...na." daga nan ta sume, Ubaidullah gabaki daya ilahirin jijiyoyin jikinsa ne suka miƙe ya yinda idanuwansa suka rine lokaci daya wanda idan ya kalleka dasu sai ka gigita, dan daga gani babu komai a cikin wa innan idanuwa ban da tartsatsin wuta, bakinsa har wani hayaƙi yake fitarwa tamkar ya zuga shisha, hakika tsoro ya dabaibaye wa innan samarin yayinda dayansu ya ce. "Ko dai wannan shi ne Yayan nasu? Ga shi kuma na gansa da wandon sojoji ko dai soja ne? ya akayi yasan nan wajan? Ko dai lokacin da muke dauke wannan yarinyar wannan guy din da wancan budurwar ne suka sanar da shi? In ko haka ne yadda ta faɗe sa tabbas yafi hakan!" a tsorace suke magana su na ba wa junansu amsa, wani ma ya ce. "Kai baka ji kukan zakin da ya yi bane?" "Ka ji banza! To ni kurma ne, na ji mana!." Ubaidullah juyawa ya yi, ya kalli jinin da kafafunsa suka taka ya kalli Safwan kwance babu rai babu alamun rai Abi'atu ta ɗago shi tana kuka mai cike da tashin hankali ta ɗora kansa bisa cinyoyinta ga Hafiza a yashe a kasa itama sumammiya. Wani kujera Ubaidullah ya ja tsakiya sannan ya dauki Hafiza ya shinfiɗeta a gefe, ya ɗaga Abi'atu wacce take durkushe da Yayanta wanda ta kifa kansa saman cinyoyinta ya miƙar da ita tsaye riƙe kafadunta, sannan yasa hannu ɗauki Safwan tamkar ba namiji ya ɗauka ba, ganin yadda ya dauki Safwan abun ya sake firgita su matuƙa, kwantar da Safwan ya yi a gefe shi ma, sannan ya dauki wayar Abi'atu wacce ta sakesa ya faɗi ya jawo hannunta, damƙa mata wayar ya yi, ya sa hannunsa yana goge mata hawaye cikin murya wanda Abi'atu bata taba jin Ubaidullah da shi ba, bata taba tsammanin yana da ita ba, wanda da ya yi mata magana da shi itama sai da ta ji tsoron murya, wai a hakan ma ita ya sassauta mata. "Abi'ah just give me 10mins only, zamu kai Safwan Asibiti In sha Allah babu abun da zai faru da shi" ta jinjina masa kai ta sake ɗaga Safwan ta ɗorasa a saman kafarta, tana tare jinin dake malala daga kansa da mayafinta, duk mayafin nata ya b'aci da jini. Kujerar da Ubaidullah ya ja tsakiyar wajan zama ya yi a kai ya duƙar da kansa kasa, kafin ya ɗago jan idonsa yana kallonsu da shi, jira yake yi wa inda suka fita su dawo, bai jima da zama ba kuwa sai gasu sun shigo su na ganin Ubaidullah suka firgita, ɗaya daga cikin wa inda suka shigon ne ya ce. "Wanene kuma wann....." maganar da bai samu damar karasawa ba kenan sakamakon haɗa ido da ya yi da *Soja Namijin Duniya Ubaidullah!* juya idon da Ubaidullah ya yi ya hango wata igiya kakkaura, duba agogon hannunsa ya yi ya ga har yaja mintuna hudu a cikin goman da ya ambata, yana tashi idonsa a rufe da ya yi wani kukan kura ya shaƙi wuyar yan iska ya dinga gwara su da bango, ji yake yi ma gabaki ɗaya baya hucewa, dan ya rasa kalar dukan da zai yi musu, ta ko ina ya shiga kai musu zafafan naushi, suka fara ihu su na neman agaji igiyar da ya gani ya ɗauka ya hadasu waje guda ya ɗauresu tamƙar yadda ake daura bayi marasa galihu da yanci a zamanin da can baya, haka ya ɗaure su ƙwaƙƙwaran motsi basu iyawa dan kuwa ɗauri ba na wasa Ubaidullah ya musu ba, ya juya ya ga su koken da sauran wasu kayan maye, ɗaukar koken din ya yi ya tura musu a hanci da baki ya ɗaure musu bakin tamkar yadda suke ɗaure na ƴaƴan mutane, sannan ya tattara komai nasu a kangon ya ajiye gefe daya, ajiya mai kyau ya musu, da sauri ya ɗaga Safwan ya fita da shi ya saka shi a mota sannan ya dawo ya tattara wayar Safwan din ya dauki Hafiza ya fice da ita da gudu Abi'atu tana binsa a baya, ya sa Hafiza a mota itama, gudu yake shararawa sosai yayinda ya dauki hanyar Specialist Hospital, yana zuwa emergency ya bukaci a shiga da Safwan amma suka ce ba zasu karbesa ba sai yan sanda sun zo sun sa hannu Ubaidullah ya sa hannu a aljihun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya nuna musu card dinsa ya ce. "I'm Captain Ubaidullah Abdullahi Nigerian Army, wannan kuma Ɗan Uwana ne ya samu hatsari da miyagu ne" nan kuwa suka karbi Safwan suka ce Ubaidullah din yasa hannu ya saka, sai da aka shiga da shi emergency sannan ya miƙa Hafiza ma wata Dr mace, ya ce. "Pls Dr ki bincika min ita sosai idan babu abun da aka mata" Dr ta amsa da "ok sir", kafin Ubaidullah ya hau jeka ka dawo ya kasa zaune ya kasa tsaye wai ga wa ya yi bai ga Abi'atu ba, da sauri ya fita yana nemanta yana kiran sunanta a hankali, can wajan bayan asibiti ta zauna ta haɗe kai da guiwa tana rusar kuka dan gani take yi kawai ta rasa Yayanta dan bai yi kama da rayayye ba. Ba karami sanyi jikin Ubaidullah ya yi ba, ganin yadda Abi'atu ke dirzan kuka, tabbas Abi'atu masoyiyarsa ce ta hakika, dan duk abun da ya samu Safwan ta sanadin ceton kanwarsa ce, shi kuwa me zai yi wanda zai saka ma wa innan bayin Allah masu matukar mutunci da karamci gami da halacci da kyautatawa? Wani tausayin Abi'atu ne ya kama shi da fargaba yana addua Allah yasa Safwan na raye, dan kuwa har ya fara hango kalar tashin hankalin dasu Abba da Ummi zasu shiga, da sanyin jiki ya karaso yasa hannunsa ya kamo kafaɗunta, jikinsa a matuƙar sanyaye ya ɗagota, still kukan da ta ke yi ta kasa dainawa, fuskarta ya tallabo da hannunsa biyu hawayenta na zuba a tafin hannunsa, ji yake tamkar shima ya sa kukan suyi tare amma idan ya yi haka abu ya b'aci, cikin murya mai cike da taushi gami da lallashi ya ambaci sunanta, dan ba zai iya jurar kukan da take yi ba. "ABI'AH!" yana kiran sunan nata ta ji kukan nata ya ƙaru, sake ɗago fuskarta ya yi, ya sake ambatar sunan nata kafin ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta sake fashewa da sabon kuka dan kuwa ta kasa daina kukan, ga uban faduwar gaba, kuka take har tana shiɗewa ga shi yanzu ta kafesa da ido sabida fuskarta da ya tallabo da ambatar sunanta da ya yi, Ubaidullah idanunsa suka sake rinewa ganin yadda take kukan tana karawa, a hankali ya jawota ya haɗeta da kirjinsa yasa hannuwansa duka ya zagayeta da shi gabansa na faduwa, jinta a jikinsa yasa sautin kukanta sake canza kala, dan kuka take mai cike da ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, da kyar ta fara magana mai cike da ajiyar zuciya da shesheƙa. "Shi ke nan! Zan rasa Yayana, mutuwa zai yi shi ma ko? Zan ras....." da sauri ya sake matse fuskarta a ƙirjinsa sai ga hawaye na zubowa daga idon Ubaidullah kuma ya ƙi yarda ya ɗago da fuskarta, sosai Abi'atu tasha kuka lokaci ɗaya wani azabebben ciwon kai ya dirar mata, sai da ya tabbatar ta yi shuru kafin yana rungume da ita suka koma cikin asibitin. @@@@@ Sai wajan gaf da magriba Likitar da Ubaidullah ya sakata bincika masa lafiyar Hafiza ta fito, da sauri Ubaidullah ya yi wajanta yana tambayarta ya lafiyar Hafiza, nan take shaida masa lafiyarta kalau basu yi bata komai ba, wani wahalalliyar Ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke, ya juya ya sake rungume Abi'atu wanda idanuwanta suka ƙanƙance sabida kuka da ciwon kai. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A dayan bangaren kuwa. Ko da Mama ta zo gidansu Ummi take cewa ina Abi'atu da Hafiza, Ummi take cewa ita bata ga Hafiza ba, amma ba mamaki da zata zo sun hadu dasu Safwan da Abi'atu a gate sun fita tare, dan Safwan da Abi'atu sun tafi karb'o sako, da haka ne suka shiririce da zancan, har can yamma lilis ba Safwan ba Abi'atu balle a saka ran gani Hafiza tana tare dasu, abun bai damu Ummi ba, sai ana kusan sallar magriba tukunna wanda za a karba sako a hannunsa ya kira waya ya ce fa ga shi ba a zo an karbi sako ba, Ummi ta fara mita tana yiwa Safwan faɗa sai kace yana gabanta, har tana cewa, ya kama sun tafi da Abi'atu da shike itama mai kafar yawo ce da auranta sai da nace mata zauna ta ƙi, waya Ummi ta ɗauka ta fara kiran layin Safwan a lokacin ita kuma Mama ta koma gida ta ce gidan ba kowa sai mai gadi idan su Abi'atu da Hafizan sun dawo sa sameta a gida, lokacin da kiran Ummi ya shigo wayar tana aljihun wandon Ubaidullah yana zaune Abi'atu tana kwance a kafadarsa, ɗan ɗagata ya yi kaɗan, sannan ya duba wayar ya ga sunan Ummi na yawo a screen din, gabansa ne ya fadi dan baya so ya kirasu ya gaya musu halin da ake ciki sai likitoci sun fito an faɗi a wani mataki Safwan yake, babu yanda Ubaidullah ya iya haka ya ɗaga wayar Ummi jikinsa a matuƙar sanyaye, tun kafin Ubaidullah ya yi magana Ummi ta ri ga sa da cewa. "Haba Safwan! Wani irin rashin hankaline haka!? Tun wajan karfe uku saura ku ka fita amma har yanzu baku dawo ba fisabilillah!? Kuma kasan Abi'atu matar aurece yanzu ko!? Ba kamar da ba ce, wai ma tukunna ba ku je kun amso min sako ba, sannan ku baku dawo gida ba, ina ku ka biya ne kam? Hafiza tana tare da ku ne!? Dan Mama ta zo nace mata banga Hafiza ba, amma watakila kun hadu da ita a gate ku ka tafi tare" duk a lokaci daya Ummi ta jero magana da tambaya, jin shuru ba amsa ne ya sata kara faɗin. "Hlo Safwan ba ka ji nane?" "Ummi mu na asibiti!" cewar Ubaidullah muryarsa kamar zai sa kuka, jin muryan Ubaidullah yasa gaban Ummi bugawa da karfi,a kiɗime ta ce. "UBAIDULLAH!? meya faru!? Baka tafin bane!? Waye kuma a asibiti!?" shuru Ubaidullah ya yi ya kasa ba wa Ummi amsa, ya kalli ido Abi'atu wacce take shirin sake saka masa kuka, girgiza mata kai ya yi alamun kar ta yi sannan ya sake kifa kanta a gefen kirjinsa, da kyar Ubaidullah ya ce. "Ummi, ku taho Specialist Hospital yanzu pls da Abba da Mama" yana gama faɗi ya ajiye wayar, a kiɗime Ummi ta hau neman layin Abba Allah ya so bugu biyu ya daga nan ta shaida masa Ubaidullah ya ce yanzun nan su taho Specialist Hospital, shi ma Abba a zabure ya ce dama Ubaidullah din bai koma aikin bane, waye ba lafiya, Ummi tace itama bata sani ba, Abba yace dama yana kusa da gida ga shi nan zuwa, Ummi ta ce ya dauke su kawai ita da Mama a bakin gate din gidansu Ubaidullah din, Abba ya amsa da to, ko da Ummi ta yi Mama magana hankalin Mama ya tashi in da take cewa dazu da ta shigo gida Zaidu ya kirata akan ina Ubaidullah ta ce masa tun karfe biyu da yan mintoci yabar gida ya tafi airport yake ce mata yana ta kiransa baya dagawa, Mama tace masa, ba mamaki yana jirgi da haka suka yi sallama da Zaidu, yanzu kuma ance ana asibiti to waye ba lafiya? nan dai cike da zullumi suka fito gate suka tsaya su na tunanin waye ba lafiya da har su ka je asibiti, sannan ya akayi Ubaidullah shi da ya kama hanyar airport ya bige da zuwa asibiti, to ma ya akayi suka hadu dasu Safwan har wayar Safwan ta shiga hannun Ubaidullah? Wannan shi ne tambayoyin da Ummi da Mama da Abba suke yiwa Zuciyoyinsa amma babu mai basu amsa sai sun isa asibitin, basu fi minti bakwai da fitowa ba Abba ya iso nan suka burma motar su na jimamin meya faru, a cikin da kankanin lokaci suka iso asibiti Abba ya kira wayar Safwan dan ya kira na Ubaidullah bai daga ba, nan Ubaidullah ya ɗaga ya gaya musu inda suke gami da yi musu kwatance, tafiya sukeyi da sauri-sauri kamar zasu tashi sama, su na shigowa suka hango Ubaidullah da Abi'atu, ga jikinsu duk jini da sauri Abba ya karaso yana kiran sunayensu Abi'atu tana kallon Ummi ta sake barkewa da kuka ta tashi da gudu ta rungume Ummi, sosai jikin Ummi ta yi sanyi, kallon Ubaidullah Mama ta yi wanda ya dukar da kansa kasa, Mama ta ce. "Ubaidullah meya faru!? Hatsari aka yi ne!? Ina Safwan da Hafiza!? Wai meke faruwa ne!?" Abba ya kama Ubaidullah ya ce. "Mama kiyi masa tambaya a hankali, Ubaidullah meya faru, karka ji komai faɗa mana?" ganin Ubaidullah ya kasa magana yasa Mama dago Abi'atu daga jikin Ummi ta ce. "Abi'atu meya faru!? Hatsari ku ka yi ne? Ina Safwan!? Kun fita da Hafiza!?" cikin sheshsheƙar kuka Abi'atu ta gya ɗa kai ta fara basu labari da dasheshshiyar muryarta wacce tasha kuka ta godewa Allah, tana gaba basu labari Ummi ta yi baya-baya zata faɗi da sauri Abba ya tarota ya yinda Mama ta zube kasa sharab irin zaman yan bori sabida tsananin tashin hankali, Abba ya kalli Ubaidullah ya ce. "Yanzu ina Hafizan!?" da kyar Ubaidullah ya ce. "Tana ciki, likita ta ce basu yi mata komai ba" "Safwan din fa!!!!? Cewar Mama da jikinta ya ɗauki b'ari, a sanyaye Ubaidullah ya ce. "Tun da suka shiga da shi har yanzu basu fito ba, balle mu ji ya yana yin jikinsan yake" Abba ya ce. "To su yan iskan su na ina!? Ba dai barinsu ka yi ba!?" murmushin baƙin ciki Ubaidullah ya yi ya ce. "Abba taya zan barsu!? Mutanen da na dauki tsawon lokaci ina nemansu *RUWA A JALLO* sunyi sanadiyyar mutuwar kanwata, abun bai ishesu ba, sun sake zuwa suka dauke dayar, ga shi yanzu a garin taimakonta ga Ɗan Uwana yana cikin emergency ban san a wani hali yake ba, taya zan barsu Abba!? Su na can na daure su, so nake na san halin da Ɗan Uwana yake ciki kafin na koma garesu" Abba ya yi ajiyar zuciya gami da cewa. "Bari na kira Police" ya fada yana kokarin kiran waya, da saurin Ubaidullah ya rikosa ya ce. "Abba wani police kuma zaka nema bayan ga Soldier a gabanka? Mai mukamin Captain? Ba bukatar police Abba, nine nan zan hukuntasu da kakina, na godewa Allah da aikina ya dawo ababen farauta ne suka bayyana, sai na dandana musu azaba kafin na kashesu!!!!" ya faɗa bakinsa na hayaki,jinjina kai Abba ya yi, babu wanda ya sake magana a cikinsu illa fargaban da suke ciki, nan suka koma suka tsaya cirko-cirko, kafin likita ta fito ta ce Hafiza ta farka, su na shiga suka sameta tana kuka tana shirin wafce drip din da aka ɗora mata tana ambatar sunan Yaya Safwan, Abba ne ya dakatar da ita akan cewa karta cire Safwan yana lafiya, kallon Abi'atu ta yi wacce itama ke layi sabida matsanacin kanta dake mata ciwo kamar zai rabe gida biyu, Hafiza ta ambaci sunanta, Abi'atu ta zo ta rungumeta su na kuka tare abun tausayi, matukar tashin hankalin haƙiƙa hankalinsu a tashe yake, sai wajan karfe sha ɗaya kafin wasu Doctors su biyu ne suka fito su na sharce gumi, da sauri Ubaidullah ya tare su yana tambayar jikin Safwan, ganin yadda hankalinsa yake tashe ne suka dafasa sannan suka ce shi da Abba su biyo su office, hakan kuwa aka yi, ko da Abba da Ubaidullah suka zauna Dr ya ce. "Alhamdulillah! Aiki muka yi masa but mun sha wahala sosai, sabida da kyar jinin da ke zuba ya tsaya, dan bayan wajan ƙeyar kusa da wujan wuyarsa gurin ne Ya fashe dan kuwa abun da aka buga masa mai karfi ne gaskiya, saukinta ma bata wajan kwakwalwarsa bane da ya mutu ko ya samu tabin hankali, a gaskiya ya zubar da jini sosai, yanzu jini muke bukata dan da kyar muka samu muka tsaida jinin kafin muka yi masa aiki" da sauri Ubaidullah ya mika hannunsa yana cewa. "Dr ku auna nawa idan zai masa ku ɗiba a saka masa!" murmushi Dr ya yi ya ce. "Ka kwantar da hankalinka, Nan da 2days Dan Uwanka zai iya farkawa da zarar mun saka masa jini, dan mun ga ka damu sosai In sha Allah he will be fyn very soon" gauron ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke yana hamdala, nan aka auna jinin Ubaidullah amma bai zo dai-dai dana Safwan ba, dan haka Abba ya ce a dibi nasa, nan kuwa aka ɗibi na Abba aka jonewa Safwan, ranar babu wanda ya rintse haka suka tsaya a asibitin, kuma likitoci sun hanasu ganin Safwan din. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *A BARRACKS.* ko da sojojin da aka bar wa Ubaidullah suka ga har jirgi ya ɗaga basu ga dawowarsa ba, nan suka kira Major Usman suka shaida masa ga yadda Captain ya bar airport, Major Usman kasancewar yasan halin Ubaidullah ya saka shi basu umarni akan su bar airport din su koma barracks, bai damu da ya kira Ubaidullah dan yasan shi baya wasa da aiki, barin ma idan abu ya shafi ceton rai, duk abun da zaisa ya bar airport to hakiƙa babban abu ne, sabida haka ya bada lokaci zai kirasa ko da zuwa yamma ne ko dare, tun da tafiyar ma sai nan da 2wks but su na bukatar ganinsa a barrack ne, babu wanda Major Usman ya sama da maganar sai Captain Zaidu da first Lieutenant KB,nan yake shaida musu kamar yadda shi ma aka shaida masa, dan haka ko da Zaidu ya yi waya da Mama ya bar amsar da ta ba shi kawai dan yasan yanzu sai Mama ta tashi hankalinta, dan haka tun yamma ake neman Captain Ubaidullah amma shuru, Major Usman ne ya bada excuse wa Ubaidullah a barracks kowa kuma ya karba, ko bayan da Dr ya yiwa su Ubaidullah bayanin Safwan zai ji sauki soon sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga tarin miss call na manya manya sojoji, ga na Aminansa, sai da ya fara kiran Major Usman bai boye wa Major Usman komai ba, nan take Major Usman ya ce zai yi magana da General Of The Army amma kafin nan Ubaidullah ya kira Lieutenant Genaral ya masa bayani, hakan kuwa aka yi bayan sun gama magana da Major Usman ya kira L.G, nan ya nemi afuwa na rashin dawowarsa yau sannan ya karo uzurinsa, nan kuwa L-General ransa ya b'aci ya ce wa Ubaidullah ya ba shi permit ya taho dasu barracks ya hukunta yan iska, gobe zai ba wa sojoji umarni a taho dasu shi kuma ya sake bin flight, Ubaidullah ya amsa da ok sir gami da cewa ayi masa uzuri nan da kwana biyu idan Brothernsa ya farka, L-General ya ce ba komai zai yi magana da General da kuma General Of da Army, Ubaidullah ya yi masa godiya, kafin ya kira Zaidu ya basa labarin duk abun da ya faru, Zaidu kamar zai yi hauka, haka ya dinga buge-buge yana Allah Allah a kawosu barracks su ci kwal ubansu dan kuwa sun tanadar musu azaba da gwale-gwale dan kuwa basu son wa suka tabo bane, dama ance kwana dubu ta barawo kwana ɗaya tak ta mai kaya. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari da safe aka kira Ubaidullah, ya ga bakuwar number yana dagawa aka sara masa cikin girmamawa kamar yana gaban mai sara masan, nan yake cewa. "Sir Captain Ubaidullah, Sir L-General ne ya ce mu kiraka, zamu tafi da masu laifi, ka fada mana in da kake mu zo mu dauke ka" a takaice Ubaidullah ya gaya musu, cikin ɗan lokaci sai ga su sun zo, nan Ubaidullah ya yiwa su Ummi, Abba, Mama Abi'atu da Hafiza wacce take zaune, sallama ya musu gami da yi musu bayanin yadda suka yi da manyansa Abba ya jinjina kai ya ce. "To ba komai, nima yanzu gida zan wuce tun da sun ki yarda mu ga Safwan din kuma ku zo muje sai muyi wanka ayi girki a taho da shi, ga shi mun bar baƙi a gida, ina ga dai bikin nan ɗagawa za ayi tun da ga angon a kwance" Ummi ta jinjina kai, kafin Ubaidullah ya kalli Abi'atu da gefen ido ya ganta itama kamar wata marar lafiya so yake ya yi mata magana amma ba zai iya ba a gaban iyayensu dan haka suka fito a tare har da Hafizan, su na fita ya ga sojoji da wata babbar mota da kuma wata madaidaiciya duka kuma barracks car ne,yana fitowa suka ƙame su na sara masa, sannan suka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, suka tada motar suka fice daga asibitin, su ma su Abba mota suka shiga suka dauki hanyar gida. A hankali suke tafiya hakan yasa Ubaidullah gaya musu su ƙara gudu, su na tafiya yana musu kwatance har suka iso,bude masa kofa sukayi, ya yi gaba suka take masa baya, ko da ya shiga ya gansu a galabaice, nan ya kunce musu baki yana binsu da wulakantaccen kallo, da kyar suke iya bude idanunsu, su ga sojoji tsaye a bayansa, ɗaya ne wanda yake ɗan dama-dama ya fara magana cike da tsoro. "Dan Allah! Yallabai kayi mana rai kayi hakuri, wallahi bamu san kai soja bane, ba zamu sake ba mun tu ba, Dan Allah ka......" wani wawan naushin da Ubaidullah ya dunƙula hannu ya kai masa shine ya yi sanadiyar rashin karasa maganarsa wanda take jini ya taho da haƙorinsa uku, dan hannun Ubaidullah bai da kyau, ko ya ya ne ya taba mutum da shi sai ya fito ga hannunsa da mugun zafi, to balle wannan da ya kai masa naushin azafafe, kallon sojojinsa ya yi ya basu umarni da su tafi dasu, sannan duk wanda ya yi musu abun da bai musu ba a hanya su parker motar su ci Ubansa! Nan suka sake sara masa sannan suka dauki samarin suka fita dasu, wasu kuma ya sakasu kwashe masa lapton din yace a sama a mota ,amma kafin nan sai da suka yi ma abubuwan hoto har da kayan shaye-shayen, duk wasu kayan maye yace su tafi dasu but lapton da wasu memories ya ce a kaisa gida dasu,nan suka babbar motar ta dauki hanyar Abuja, wasu sojoji mutum biyu suka ja Ubaidullah izuwa gida. Horn suka danna mai gadi ya bude musu gate, part dinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga ua watsa lapton din akan kujerar parlour, bedroom din Abi'atu ya shige ya kwankwasa ya tura kofar bai ganta ba, nasa bedroom din ya wuce ya watsa ruwa shap-shap, ya sake saka kaya matasa nauyi ya fito ya yi part din Mama, a parlour ya samu Hafiza tana zaune Mama tana gefenta Abi'atu kuma tana zaune a kasa ta takure ga abinci a gabanta ta kasa ci, zama Ubaidullah ya yi kusa da Hafiza Mama ta ce. "Har ka dawo? An tafi dasun?" "Eh sai da suka wuce kafin aka maido ni gida" Mama ta jinjina kai ta miƙe ta yi kitchen,Ubaidullah ya sake sacin kallo Abi'atu wacce ta yi kamar bata san ya shigo ba, mai da idonsa kan Hafiza ya yi, ya shafo kanta a hankali ya ce. "Are u feeling much better?" ta jinjina masa kai kanta a sunkuye dan videon da aka nuna mata na yar Uwarta yayi mugun ɗaga mata hankali dan har yanzu ba wai ta koma nml bane, a hankali Hafiza ta kama hannun Yayanta ta yi masa nuni da Abi'atu sannan ta miƙe ta shiga daki tasa kuka, Hafiza na shiga daki Ubaidullah ya miƙe ya zo gabanta ya kamo hannunta bata yi masa gardaman ba zata tashi ba,ya dauki abinci ya jata suka fita ya yi hanyar part dinsu, yana shiga parlourn ya zaunar da ita, yaja stool gabansu ya ajiye abinci, gamin yadda idonsa duk sunyi luhu-luhu ta lumshe da bude, dafe kanta ya yi ya ji da zafi raɗau, abinci ya fara mata amma ta ki bude baki ta ci, da kyar ya samu ta bude bakin amma tana shirin saka masa kuka ya yi saurin toshe mata bakin ta hanyar haɗewa da nasa yana tsotsa cike da salon kauna wanda bata taba tsammanin hakan daga garesa ba, take ta nemi kukan ta rasa, sai wani bakon yanayi da ya ji ya ziyarceta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 😭😭😭😭😭😭😭 *DAN ALLAH MASOYA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH KUYI HAKURI, WLH ABU NE KAMAR WASA YANA SHIRIN ZAMA GASKIYA 😭😭😭 KWATA KWATA LITTAFIN YA FITA A RAINA SAI KACE WACCE AKA MIN ASIRI, BA WAI LOKACI NE BAN DASHI DA ZAN GAMA KAFIN SALLAH BA AA 😭😭😭 BUK DIN NE KAWAI NAJI YA FICE MIN FITTTT!!!! DAN ALLAH KU TAYANI ADDUA NA GAMA MU HUTU, KU KU HUTA NIMA NA HUTA 😭😭😭 ALLAH YASA MU DACE AMEEN.* ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ 😡😡😡😡😡😡😡😡😡😡😡 *_WANNAN JAN FUSKAN SHIMA BANGARENSA DABAN, A WAN CAN PAGE DIN NACE KUBAN SUNAYENKU NA BAKU KYAUTAR PAGE KUKAYI KAMAR BAKU SANNI BA KO 😡😡😡 AI KUN HUTA SAI DE KU NEXT PAGE, ZAKU JI SUNAYENKU HAR DA MASU MIN SHARHI A WATTPAD, UMMU AHLAN TANA GODIYA GAREKU MASOYA ABUN ALFAHARI_*💃🏻💃🏻 Anya kuwa ma kuna sharing din buk din idan kuka karanta? 🙄 Sorry 4 d typing..error ycn bazan iya editing ba 😪😪🥺🥺 Momyn Ahlan Taku Ce👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_HAPPY HAPPY HAPPY💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻, HAPPY ANNIVERSARY KAINUWA WRITERS ASSOCIATION, 3YRS ALHAMDULILLAH, YA ALLAH KA KARAWA KAINUWA DARAJA DA DAUKAKA, ALHAMDULILLAH KAINUWA DASHEN ALLAH MAHASSADANKI FADAWANKI 💪🏻💪🏻 KOMAI SU KAI KI BARSU DA ALLAH, YA ALLAH KA KARA BAMU IKON TSARKAKE ALKALUMANMU WAJAN RUBUTA DAI-DAI, ALLAH KA TSARE ALKALUMANMU DAGA RUBUTA SHIRME ABUN DA BA ZAI AMFANE ALUMMA ANNABI MUHAMMAD S,A,W BA, INA MIKO MIKI JINJINA DA DUBUN GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRI SHUGABA JA GABA ANTY FAUZA YAR AMANAR KAINUWA, ALLAH YA IYA MIKI, INA GAISHE DA KOWA DA KOWA NA KUNGIYATA, ALLAH YA KARA HAƊA KAWUNANMU YA KAƊE FITINA A TSAKANINMU, ALLAH YA KARA MANA HAKURI DA FAHIMTAR JUNA, (ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN INA YI MANA FATAN ALKHAIRI) UP UP UP UP UP KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA_*💓💓💞 *_YAU PAGE DIN FA NA KU NE_* 💃🏻 @💞💞 MEMCY💞💞 and........😟 yasin sis bansan asalin sunanki ba 😢 (Oriflime ne ko miye ne uhum 😢) sonso fisabilillahi. 💞👏🏻 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°96&100* Duk yaƙin da zasu je,da ya ga an kashe wani soja,ya kan shiga damuwa da tausayin iyalansu halin da zasu shiga, har misali yake yi da kansa yanzu ace gawarsa ce za a dauka a kai gida ya Mama za ta ji? Gaskiya sojoji su na matuƙar bakin kokarinsu, da zarar ka shiga aikin soja, to fa ka din ga rayuwa da sanin cewa za a iya farmaka ko wani lokaci,shi yasa da yawan wasu mata basu cika son auren soja ba, dan zaka yi sallama lafiya lafiya da Iyayenka da matarka amma ka je yaƙi a dawo da gawarka. @@@@ Kwanarsu uku a kasan babbar rafin kashmeer ba ci, sai dai sha, haka suka sake komawa aka ci gaba da takaddama, ya yinda sojoji sun kashe yan ta'adda da yawa, kuma rundunar sojojin india na yankin kashmeer sunji labarin sojojin nigeria sun kawo farmaki dan anyi garkuwa da yan matan kasarsu, amadadin su kawo musu dauki tunda su ma yan ta'addan sun addabesu amma sai suka labe dan tsoron makaman da yan ta'addan suke dauke dasu, sunji labarin wani jami'in soja wanda ke zubar dasu miyagu izuwa kasa wanda shine ja ragamar yaƙi,wa hakan ne suke son ganin wanene wannan jarumin. Nan fa sai dai suka sake share sati daya ana yaƙi, nan da kwana goma an kashe sojojin Nigeria guda goma sha uku, in da mutane ishirin suka ce su kam guduwa za su yi, Ubaidullah yace shi kam ko zai mutu babu inda zai je dan ya ɗau alkawari sai ya kubutar da mata da yardan Allah. Sojoji 20 da suka koma gida su ne suka bada labarin tashin hankalin da sojojinsu suke ciki, tare da sunaye da hotunan wa inda aka kashe, sosai hankalin General Of The Army da sauran manya ya tashi, dan kuwa sojoji masu nagarta aka zaba aka tura, Major Usman ne ya ce. "Su Captain Ubaidullah fa?" nan wani soja ya ƙame yana bawa Major Usman amsa da cewa. "Haƙiƙa Captain Ubaidullah jarumi ne yawancin yan ta'addan da aka kashe shine ya kashesu, kuma yace ba zai dawo ba ko da kuwa zai mutu sai ya karbo yan matan da aka yi garkuwa dasu, gaskiya shi din jarumi ne gagara gasa" murmushi Major Usman ya yi, nan aka fara shawarar ƙara tura wasu jami'ai amma kowa saffewa yake yi, dan ga shi nan wasu sun gudu, su kuma sai su kai kansu. Tun basu dawo ba, labari ta baza duniya na mutanen da aka kashe a india, wanda suka yi jarumta suka mutu a fagen yaƙi. @@@@ Zaune take gabaki ɗaya ta rame tayi duhu, da ka ganta kasan bata cikin walwala da kwanciyar hankali, hayaniya ke tashi bisa alamu dai shagali ake yi, dago ido tayi ta kalli Mama wacce take ta murmushi a cikin jama'a amma a zahirin gaskiya idan ka kalli cikin kwayar idonta kasan itama ba bata tare da natsuwarta, yan uwana ake ta shige da fice, ana shirin zuwa lunching na Safwan da Shafa'atu, Ummi ce ta ratsa cikin mutane ta zo gaban Abi'atu tana kallonta, ita kam ma Ummi kallon mai ciki take yiwa Abi'atu, "Ke Abi'atu ba za ki je lunch din bane? Kin zauna da kayan bacci kin kasa wanka? Ga jama'a da yawa a gida, ki tashi kije kiyi wanka ki cire wannan kayan bacci da hijabin ki zo, idan ma ba zakije lunch din ba kiyi wanka ki zama mutum a cikin mutane, ke ma Hafiza kin zo kin zauna a nan tashi kije ki shirya kema, tun da babu igiyar kowa a kanki, ita da take da igiya a kanta take fama da guntayen ciwuka sai ta zauna a gida" mikewa Hafiza ta yi ta amsa da "to Ummi" ta fice daga parlour tana fitowa gate wani soja ya rakata har izuwa bakin gate din gidansu kafin ya tsaya a gate din, Abi'atu kuwa haɗe rai tayi sosai ko kallon Ummi ba ta yi ba, Mama ta yi dariya ta ce. "Ummi , ki fa bar min yarinya tasha iska" "Haba Mama wani irin shan iska dan Allah, gida da mutane amma ta zauna da kayan bacci da hijabi?" Mama ta sake murmushi dan itama ta dauka Abi'atu ciki ne da ita, amadadin Abi'atu ta tashi sai ma gyara kwanciyarta da tayi dan wani irin haushin yan shagalin bikin take ji, Mijinta na can yau kusan wata ba ta ji lafiyarsa ba, amma wai su na shagalin biki, shagalin banza shagalin wofi, to wallahi ba zata yi wankan ba ma yau gaba ɗaya, har wa inda zasu tafi lunch suka gama shirinsu suka tafi abun su Abi'atu tana kwance bata saka lahadin tashi ba, rintse ido tayi tana taro dukkan moment dinsu da Ubaidullah har izuwa ranar da zai tafi ya furta mata kalmar yana sonta, wasu zafafan hawayen ƙauna ne suka wanke masa fuska, ta yi saurin gogewa ta jawo wayarta ta shiga cikin galary, pics dinsa ta hau kalla tana murmushi dan abun da yake iya sanyaya mata zuciya kenan, pic dinsa ta saka a wallpaper na screen din ta da kuma na WhatsApp dinta, kunna data ta yi ta shiga media, abun da ta fara karo dashi shine yayi matukar gigita mata hankalinta da natsuwarta Facebook twitter Instagram yawancin kafofin sada zumunta hotunan sojojin da aka kashe a india ne, Abi'atu tana gani ta saki wani kururuwan da sai da gidan gaba ɗaya ya amsa,a kiɗime aka yi kanta, ihu take tana " wayyo Allah Mijina!" Ummi ce ta zo da sauri ta rirriƙeta tana tambayarta menene, nan ta nuna musu abun da ta gani, Ummi ta ce. "Haba Abi'atu sai kace ba musulma ba?za ki saki wannan kururuwa haka, su yan uwansu da suka ga gawarsu su kuma su yi yaya kenan? Ko kin ga Ubaidullah a cikinsu ne?, ki ci gaba da masa addua a matsayinki ta matarsa, Allah ya basu narasa su dawo a sa'a, su kuma wa inda suka mutu Allah ya gafarta musu, sosai Ummi ke lallashin Abi'atu dan hankalinta ya kwanta duk da itama Ummi hankalinta a tashe yake bata so ta nunawa Abi'atu hakan ne, dan Abi'atu bata iya tsorata ba, yanzu sai ta ri ga Ubaidullah din ma mutuwa idan shi bai mutu a yaƙi ba, to Abi'atu sai ta mutu a fargaba, ga shi tana tsoro kar wani abu ya sami abun da yake cikinta, a cewar Ummi, bata san babu abun da ya taba shiga tsakaninsu ba balle aje ga ciki, lallashi iya lallashi babu wanda ba ayi wa Abi'atu ba amma sam kamar ba da ita ake yi ba, tace ita tana so ne ta ga mijinta, har yan lunching aka dawo aka saka Abi'atu a gaba, dasu Mama, nan dai aka nemi number ta barracks din su Ubaidullah aka kira, Safwan ne ya yi magana akan cewa ko akwai hanyar da zasuyi magana da Ubaidullah? Da taimakon Major Usman aka tura dan sako zuwa ga Ubaidullah ana so aji lafiyarsa, su na tsaka da yaƙi sako ta iskesa, dama shima yayi missing dinsu amma baya da halin zaman da zaiyi waya dasu, abun da ya sani shine kullum su na zuciyarsa, da kyar ya koma gefe ya samu nertwork ya kira gida, Mama ce ta fara ɗagawa tana jin muryarsa ta kasa magana, da kyar ta iya bude baki ta ce. "Babban Yaya kana lafiya?" murmushin karfin hali ya yi ya amsa da ina lafiya Mommana, fatan kuna lafiya dukkanku?" Mama ta amsa da eh sannan ta mikawa Abi'atu, tana karba ta saka masa kuka, ya rintse ido a hankali ya ce. "My Muahh, menene abun kukan?" kasa magana ta yi, jin ba zata yi shuru ta daina kukan da tayi masa magana ba ya ce. "Idan ba ki min magana ba, zan ajiye wayata, me kikeso?" cikin sheshsheƙa ta ce. "Ina so ka dawo" "Bayan wannan fa?" ya tambayeta cike da damuwa. "Ina so na ganka" "Okay bari na kiraku video call" ya fada ya tsinke wayar ya kira ta video call da suka gansa da ace a hanya suka hadu zasu rantse ba shi bane, dan wani baƙin da ya yi ga wani uban rama, Mama bata san lokacin da kuka ya kubuce mata ba ta tashi da sauri ta fice, Ummi ma sai da suka share hawaye, nan kukan Abi'atu ya tsananta ganin yadda mijinta ya koma duna baƙin wake, nan ta shiga yi masa magiya ya dawo, da kyar ya kwantar musu da hankali, su na kan magana nertwork ya dauke, Zaidu ma ya samu ya yi waya dasu Umma, Inna kuwa itama harda kukanta dan basu taba tafiya yaƙi mai azaba irin wannan ba. @@@@ Abu kamar wasa yau watansu Ubaidullah uku, idan ka ga yadda suka koma abun ba a cewa komai, an kashe sojoji ashirin da uku, yayinda da yawansu suka gudu suka koma gida, acikin su dari da saba'in da bakwai, saura mutum sittin da tara, kuma yanzu alhamdulillah sun gano inda yan matan suke kwacosu suke son yi, su yan ta'addan sun kashe sojoji 23 amma su an kashesu ta yadda ba zasu kirgu ba, kuma ogansu ya gane Ubaidullah dan a cikin kashi dari na wa inda aka kashe musu Ubaidullah shi ya kashe kashi tamanin, dan haka suke son kashe shi amma abun ba mai sauki bane. Cikin dare su Ubaidullah suka dirƙa musu ya yinda suka sake kashe wasu daga cikinsu, da kyar da gumurzu Ubaidullah ya fidda yan mata kwantena daya, wanda a daren suka baro kashmeer, inda Commender Isa Bala ya sanar da L-General nan kuwa da washe gari aka kwashi yan mata aka mai dasu kasarsu, inda wasu ke kukan murna da farin ciki dan har sun fidda ran zasu dawo mahaifarsu, a 9ja barracks aka ajiyesu inda ake musu tambayoyi su na kuka suke bada amsa, kafin su fara bada bayani sai da suka ta zubawa Ubaidullah addua, inda suke jawabi akan cewa siyar dasu ake yi a matsayin ƙaruwai, ko a siyar dasu bayi marasa galihu, su ma kuma idan bukatarsu ta tashi su na zuwa su zaba wacce suke so su keta mata haddi idan kuma ta ƙi amincewa su kasheta, sosai aka dinga naɗan rahotanninsu, inda a kwana biyu labarai ya karaɗe media, aka haɗa wasu da iyayensu. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Ubaidullah sai da suka sake diban kwana shaɗaya kafin da kyar da suɗin goshi suka sake kubutar da kwantena daya saura daya, inda sun sha baƙar wahala kafin su fidda na biyun, inda da yawan sojoji suka ce wlh ba zasu iya ba sunyi wa inda zasu iya yi, nan kuwa da yawa aka koma gida, su Ubaidullah wanda suka rage basu fi su ashirin da bakwai ba, Ubaidullah ya ce In sha Allah sai sun kubutar dasu, a wannan yanayi fa yan ta'adda sun ragu ba kaɗan ba, abun farautarsu kuma wanda suke nema ido buɗe ba ido rufe ba, shine Ubaidullah, wannan kwantena ɗayan da ya rage su Ubaidullah sun ji jiki matuƙar jin jiki, inda mutane goma suka sake mutuwa, nan suka rage su goma sha bakwai inda mutane goman su ma suka ce wlh su ma sun gaji suka gudu, su Ubaidullah suka rage su bakwai. A ranar da Ubaidullah ya ballo kwantenar karshe su na kokarin guduwa ne ogan yan ta'addan ya harbi Ubaidullah yana kan gudu bayan yasa sojoji hudu sun gudu daga kashmeer da yan matan, sannan tun kafin ya fiddosu sai da ya kira rundunar sojojin yankin kashmeer akan azo a tafi da sauran yan ta'addan sun yi musu aiki mai wahalan, kafin sojojin su karaso shine ogan yan ta'addan wanda ake kira Zaffar ya harbi Ubaidullah a kafaɗa, dama su uku suka rage daga shi sai Zaidu da KB, dai-dai nan sojojin indian suka karaso, kafin su yi wani yunkuri Zaffar ya sake harbin Ubaidullah a damtsen hannu, da karfi Zaidu ya kira sunan Ubaidullah, ganin haka yasa Zaffar saita bindigarsa a saitin Zaidu zai harbi Zaidu ganin haka Ubaidullah cikin ɗauriya yasha gaban Zaidu aka sake harbinsa inda bullet din ya shige wajan gefen ƙirjinsa wanda yasa numfashinsa tsayawa cak!!, Zaffar na shirin sake harbi da gudu KB ya shaƙosa, kafin sojoji suka kamasa da sauran yaransa, Ubaidullah na tsaye sai zufar dake keto masa ta ko ina sabida azaba, sai da ya kalli Zaidu ya saki murmushi gami da cewa, *"ALHAMDULILLAH!"* sannan idanuwansa suka ƙisfe nan ya zube kasa wanwar. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A lallaba 😪 UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻 Nayi nan sai kuma gobe in Allah ya kaimu 👏🏻🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_SAKON BARKA DA SALLAH GA DAUKACIN YAN KUNGIYATA ABUN ALFAHARINA, TUN DAGA IYAYENA YAYUNA, ƘANNENA, KAWAYENA ANA TSAFTAR TARE KO BA WUYA, ALLAH YA KARAWA KAINUWA BASIRA DA DAUKAKA_* 👇🏻 Anty Fauna ƴar amana Batul Adam Jattako Ummy On top Kadija Usman Ta me gari Maryam Umar (mmn Yusuf) Ummu Fatima Hauwa'u Salisu Haupha Real Nana Aisha Manab ƴar baba Rasheedat Usman (Ummu Nasmah) Fauziya Auwal Alin Baba Jingau Nabilancylv Fiddausi S.bak'i (Smart Feenat) Haleemat Hassan Leemat Jamila Sumaila Yusufa Zahra Faruk Hussy Sani Amina Fistlady Pretty Mardy Maryam Marsad Deeja Alkali Maman Noor Nimcylv *_INA YINKU, ALLAH YA KARA HADA KAWUNAN MU_* 💞💞💞 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°91&95* Azaba iya azaba, sun sha ta a wajan Ubaidullah da Zaidu, har wajan kwana uku, a yau ne kuma zasu bakunci lahira, videos din fyaɗe Ubaidullah ya kira Abi'atu ya bata aikin yaɗawa a ƙafofin sada zumunta, sannan ta yaɗa labarin masu ta'addanci da b'arna a doron ƙasa, masu lalata ƴaƴan jama'a, wanda yake sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu, da yawan mutane anyi commemts inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa, yayinda mutane da yawa suke bawa sojoji goyon baya akan idan an kama masu laifin a kashesu kawai ko za a samu a rage mugayen iri a cikin jama'a, dan har yau bamu ji wani hukunci mai tsanani da ƙasarmu nigeria ta dauka ba akan masu fyaɗe, yayinda rundunar sojojin su Ubaidullah ta samu ƙwarin guiwa dari bisa dari, mota suka shiga dasu, sannan suka dauki hanyar jejin nasarawa, tafiyar awa daya ce da yan mintoci ta dauke su, ya yinda suka isa jeji suka fito dasu, jera su suka yi, Ubaidullah yana binsu da kallo yana kallon videon yaran mutane masu ihu su na neman akawo musu dauki, daga cikin har da na kanwarsa NA'ILAH, abun da yake kara tunzura shi, da aka tambayesu wai tsautsayi ne da sha'awa, to idan sha'awa ne why not ka je gidan karuwai ka dauko karuwa ka biyata kayi da ita da son ranta? Amma sai ku din ga bin yaran mutane ƙanana kuna keta musu haddi, a kalla wa inda suka mutu sun kai hamsin, dan ko wata babbar mace ba lallai bane ta iya dauke bukatun Namiji balle yara kanana wanda babu wa inda suka haura shekara sha hudu ƙasa da haka a cikin yaran da suka yi wa fyaɗe, Ubaidullah ne ya saita bindigarsa akan saitin goshin daya daga cikinsu, har yaja kunnaman bindigar zai saki ya ji wayarsa ta dauki ruri, da kamar ba zai duba ba, sai kuma ya duba ya ga bakuwar number, nan zuciyarsa ta shiga waswasi ya ɗaga ne ko kar ya ɗaga, nan dai wata zuciyar tace masa ya ɗauka, yana dagawa yaji ana gargaɗa masa kasheɗi da kakkausar murya. "Hloo!!! Da Captain Ubaidullahi nake magana!?" sai da Ubaidullah ya shaƙi iska kafin ya amsa cike da izza ya ce. "Wanene kai!? Me kake neman Ubaidullah din zaka masa!?" "Kaiii!! Yaro!! Dama ance min kana da ji da kai, sabida kana fama da yarinta, abun da nake so da kai shine kayi gaggawar sako min yarona ya dawo gida, zan biyaka koma nawa ne, amma Ɗana daya tilo ya dawo gareni, karka sake ka cutar min da yaro, idan ba haka ba ko hummmmmm!!!!" wani ƙalulun baƙin ciki ne ya taso ya tokarewa Ubaidullah maƙoshi, ya ce. "Wanene kai!?ya sunanka!? kuma ya sunan Ɗan naka!?" "Ni ne *ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI* sannan UBAN *BANGIS* ina so ka sako min yarona, dan shi kadai na mallaka zan iya sadaukar da dukkan dukiyata a kansa, duk abun da yarona ke so shi nake so, dan ina da kudi, ina so ka kai case dinsa kotu, karka sake wani abu ya samu Ɗana!!" ya fada cike da tsawa, b'acin ran da Ubaidullah ya shiga baya misaltuwa, wai gargaɗi yake masa kar wani abu ya samu Ɗansa, shi kuma Ɗan nasa da ya cutar da yaran mutane su ba da jini aka yi su ba kenan?, kallon Zaidu ya yi da jan ido sannan ya yiwa Zaidu alamu da hannu ya matso sannan ya matso kusa da samarin yana kallonsu, bude handsfree ya yi ya ce. "A cikinku waye Bangis!?" a wahalce Bangis ya ɗago da sauri da kyar yake iya bude baki ya amsa da shi ne, dan fuskokinsu a kumbure suke dan Ubaidullah sun canza musu tsarin zubin halitta, Ubaidullah ya ce. "Alhaji Madugu kake ko wa ma? ga Ɗanka nan, tabbas zan baka Ɗanka, ba ma sai anje kotu ba, amma *GAWARSA ZAN BAKA* ka zo jejin narasawa ka ɗauki gawar yaronka!!!" "Kada ka sake kayi wannan gangancin Captain Ubaidullah!! Ina gargaɗinka!! kar wani abu ya samu yarona!! Za ka jefa kanka cikin masifa da bala'i, dan baka san waye ake kira da *ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI BANE!!*" "Tirrrrr!! Da masu hali irin naka, kai ma baka san waye aka kira da *CAPTAIN UBAIDULLAH BANE!! ALHAJI MADUGU!!! BANA TSORONKA, YARONKA KUMA NA GAYA MAKA KAZO KA DAUKI GAWARSU SHI DA ABOKANSA A JEJIN NASARAWA!!*" "Captain, kar yarinta ta jefaka aikin danasani!!! Kar wani abu ya samu yarona!!!" kallon Bangis Ubaidullah ya yi ya ga ma shine wanda ya fara yiwa Na'ilah fyaɗe a cikin su bakwai din nan, idonsa jajayen hawaye ne kwance, cikin ƙunar zuciya Ubaidullah ya ce. "Alhaji Madugu!!, yadda na rungumi Gawar Ƙanwata na sakata a karkashin ƙasa a sanadiyyar bata garin ƴaƴanku, kaima ina mai farin cikin sanar da kai da cewa za ka rungumi gawar Ɗanka ka saka shi a karkashin ƙasa, bari ma na fara maka alama yanzu ka jiiii!!" Ubaidullah ya faɗa gami da harbin Bangis a kafa, ihu Bangis ya saka gami da ya kwalawa mahaifinsa kira, ya yinda hankalin Alhaji Madugu ya yi muguwar tashi jin karar bindiga da ihun ɗansa, nan Ubaidullah da Zaidu suka buɗe musu wutaa!! Nan suka shinfiɗe su matattu( INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN, YA ALLAH KA RABAMU DA MUMMUNAR KADDARAR RAYUWA, BIJAHI NABIYYUL RAHMATI AMEEN) ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke sannan yasa wayar a kunnensa ya ce. "Alhaji Madugu ya ka ji Kururuwar Ɗanka? Shin abun ya maka dadi? Nima haka na ji na Ƙanwata, har lokacin da take ihun azaban fitar rai, dan haka kaima ka ji ƙunar da muka ji, ina kara gaya maka, ka zo jejin nasarawa ka dauki gawar danka da abokansa" Ubaidullah ya faɗa yana shirin ajiye waya ya tsinkayo muryan Alhaji Madugu yana cewa. " *UBAIDULLAH!!! HAƘIKA KA TAROWA KANKA YAƘIN DA BA ZAKA IYA DA ITA BA, NA RANTSE DA ALLAH!! NA RANTSE DA ALLAH!! NIMA SAI NA DAUKE ABU MAFI SOYUWA A GAREKA, SAI NA RABAKA DA FARIN CIKI NA HAR ABADA, TUN DA KA KASHE MIN ƊANA, KA RUBUTA KA AJIYE, ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI BAYA YAFIYA BAYA MANTUWA, ZA KA SAN CEWA KA KASHE GUƊAN JININA!!!"* Murmushi Ubaidullah ya yi ya ce. "Game over Alhaji Magudu, duk wanda ya kashe a kashesa, ko ba komai watakila zamu samu sa'idan fyaɗe, karkayi yunkurin shiga rayuwata Alhaji madugu, dan kuwa zaka ƙare rayuwarka a gidan mazaa!! Ubaidullah ba kamar sauran mutane bane wanda ka sani, dan haka kai ma ka kiyaye!!" sannan ya katse wayar ya durkusa akan guiyoyinsa gami da fashewa da kuka, dan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake ciki, Zaidu ne ya dagosa shima kukan yake, da kyar Zaidu da KB da wasu sojoji mutum uku aka kamo Ubaidullah aka saka shi a mota suka koma barracks, sun yiwa Lieutenant colonel bayanin komai sannan ya ce su bar case din kawai an rufe an gama da shi, aiki na gaba da zasu faɗa shine wanda zasu tafi india, Ubaidullah an yi masa magana akan su Rumaisa ya ce baya da lokacinsu, dan haka Zeey ne da kanta ta sa aka kori su Rumaisa daga barrack, duk abun da ya faru Ubaidullah yana waya da gida kuma yana sanar dasu duk halin da ake ciki, Mama hankalinta ya tashi jin yadda Ubaidullah suka yi da Alhaji Madugu, cikin tsoro Mama ta ce. "Yaya Babba kana ganin babu wata matsala kuwa? Dan gaskiya naji hankalina bai kwanta ba, karka manta fa, ba kasan wanene shi Alhaji Madugun nan ba fa!?" Murmushin takaici Ubaidullah ya yi ya ce. "Mama, shi ma bai san wanene Ubaidullahi ba, ki kwantar da hankalinki, ko ba komai yanzu zuciyata ta yi lafiya na hukunta wa inda suka kashemin Ƙanwata da kakina, adduarki kawai nake bukata, yau saura kwana uku mu tafi aiki, ban sani ba Mama ko zan dawo a raye" jikin Mama ne ya yi mugun sanyi ta ce. "Karo na farko kenan daga fara karya min guiwa, karkasa zuciyata ta tsinke, nina san wanene yarona kuma na yarda da shi,kamar yadda shi ma ya yarda da kan shi, a ko da yaushe kana tare da nasara Ubaidullah, Allah ya muku albarka" ya amsa da ameen, Mama ta kuma cewa. "Dazu fa naje na samu su Umma da Inna, mun jima muna magana, gani nayi me zai hana Zaidu ya auri Hafiza? Tun da na ga ya so Yar Uwarta amma Allah bai yi da rabon aure a tsakaninsu ba, kuma da Hafiza da Na'ilah tsantsa ɗaya suka fito, su Umma da Inna dai sunyi na'am da shawarata, kuma na gayawa Ummu itama tayi na'am, ban san kai ya zaku dauki abun ba kai da Zaidu, amma idan Hafiza tayi aure ta zauna a gidan Zaidu hankalina zai fi kwanciya dan nasan Zaidu zai kula da ita tamƙar Yar Uwarta, amma kai ya ka gani?" gauron numfashi Ubaidullah ya ja gami da cewa. "To shi kenan Mama, zan yiwa Zaid din magana, nasan ba zai ƙi Hafiza ba, amma dudu fa Hafiza she's 14 ne fa kawai yanzu take kokarin shiga 15yrs Mama ba ta yi ƙarama ba kuwa wa Zaidu?" murmushin Manya Mama ta yi ta ce. "Ubaidullah kenan! To idan kana ganin ta yi karama zata karasa girman a gidansa" ya sake yin ajiyar zuciya, nan dai suka ci gaba da tattaunawa a karshe suka yi sallama, ko da Ubaidullah ya samu Zaid da maganar bai damu ba, ya nunawa Ubaidullah amincewarsa dan da kunya yace masa aa , amma a can kasar zuciyarsa har ga Allah Na'ilah ce dan yarinyar ta kasa fita a ransa, dama yara masu kiriniya shiga rai ne dasu, dan haka Ubaidullah ya sanar dasu Mama Zaid ya amince idan Allah ya yi dawowarsu sai asha biki, ko da Hafiza ta ji labarin za a hadata aure da Yaya Zaid hankalinta ya tashi dan tasan irin son da Yaya Zaid ke yiwa Sismie dinta, su Afnan kuwa murna suka hau yi Hafiza zata dawo gidansu da zama. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau kam duk sun gama shirinsu na tafiya kasar india, sun kara training na tsawon kwana biyu ne kacal, zaune suke a airport su na jiran tashin jirgi sojoji su dari da saba'in da bakwai ne zasu tafi, manya ja gaba a wannan tafiya mutum na farko shine Commander Isa Bala, sai kuma ja ragamar yaƙi wato Captain Ubaidullah, da kuma mai taka masa baya Captain Zaidu da Mataimakinsa first lieutenant KB da dai sauran rundunar sojojin 9ja barracks, wayarsa ya ciro ya yi waya dasu Mama, Anty Ummu, Hafiza, Ummi, Abba da Safwan wanda a halin yanzu an sallamosa izuwa gida ya ji sauki sosai Ma sha Allah, alhamdulillah, an ci gaba da shirin yin shagalin bikinsa, dasu Umma,Inna, sai da ya gama waya dasu kafin ya kira Matarsa, ji ya yi gabansa na faduwa, sai da ya mata kira kusan uku kafin ta ɗaga,a tare suka sauke ajiyar zuciya, sun kai kusan mintuna shabiyar kafin ya fara mata magana kamar mai raɗa. "Madam, gamu a airport zamu wuce, ayi mana addua, Allah ya kaddara saduwarmu, sharrin karfe ma kadai wani ishara ne, kuma kin ga....." bai karasa ba ta saki kuka har da sheshsheƙa, sosai hankalin Ubaidullah ya tashi, gefe ya koma yana shirin ya lallasheta amma kashh!! Nan aka fara kiraye kirayen sunaye jirginsu zai tashi dan haka bai samu damar lallashinta ba, a hankali ya ce. "Ki kula min da kanki, In sha Allah zan dawo, idan na samu sarari kuma zan din ga kira dan ku ji lafiyata nima naji ta ku, *I LOVE U MY ABI'AH* goodbye" ya tsinke wayar ihu Abi'atu ta saka wanda yasa Hafiza dake kusan shigowa parlorn ta karaso da gudu, Hafiza ta san kukan da Abi'atu take yi, dan itama yanzu ta gama tata kukan, shine Mama ta ce mata taje ta dubo Abi'atu ta kirawota ta daina zama a part din ita kadai, rungume Hafiza Abi'atu ta yi tana cewa. "Hafiza ya tafi fa!! Ya tafi ya barni wayyo mijina" cikin kuka Hafiza ta ce. "Anty ba fa mutuwa ya yi ba, mu tayasa da addua, barin ma ke da Mama, dan Allah ki bar wannan kukan Anty, kar ya jawo miki ciwo" ta rungumeta tana lallashinta itama tana kuka, a hankali Abi'atu ta ce. " *I LOUVE U TOO MORE MY UBAID, SO MUCH LUV MIJINA, ALLAH YA DAWO MIN DA KAI LAFIYA YA BAKA SA'A*" ta ci gaba da kuka, haka ranar Abi'atu ta wuni sakoko ba guzari a jikinta har ta wani fige dan tafiyarsa da ya yi, dama gata ba wani auki ba. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A bangaren Alhaji Madugu sunje sun kwashi gawawwakin ƴaƴansu, yayinda Alhaji Madugu ya yi matukar tunzura da ya ga gawar dansa a wulakance, nan ya ci alwashi gami da lashen takwabin ganin bayan farin cikin Ubaidullah na har abada. (Wannan kenan mu ci gaba da kaftawa Mah ppls 🤾🏻‍♀️🏃🏻‍♀️) ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Alhamdulillah su Ubaidullah sun sauka a kasar india lafiya, ya yinda suka duƙufa aikin abun da ya kawosu izuwa kasar, sunje yankin bangaladash amma sam babu wani information da suka samu dan gane da yan matan da aka yi garkuwa dasu, basu yi kasa a guiwa ba suka sake zuwa yankin bangalour amma duk abu ɗaya ne, sosai hankalinsu ya tashi, sun kwashe wajan sati biyu su na faman ƙetara yanki yanki dake india, wanda ta'addanci yake bunƙasa, amma basu samu komai na labari da ya danganci yan matan nigeria ba, tun da su Ubaidullah suka zo india babu wanda ya rintsa a cikinsu, idan kuma musulmai zasu yi sallah sai dai suyi taimama idan sun risƙi wajan da ba ruwa, abinci kuwa duk abun da ya samu ci kawai Suke yi, da haka a wahale su Ubaidullah suka share wata daya a india, kuma tun da suka zo sau biyu kacal suka samu damar yin magana da yan gida, wasu daga cikinsu har sun fara fidda ran nasara ga wannan aikin amma sai Ubaidullah ya kara musu karfin guiwa, yau ma kamar kullum su na zazzaune a jejin Naidu wani sergeant ya ce. "Sir, a gaskiya na fara karaya, yau fa watanmu daya har da kwana biyar a jeji,amma babu wani information anya ba gida zamu koma ba kuwa? Mun je yanki yanki yafi sama da talatin a kasar nan amma shuru, sai kace maye yaci shirwa" shuru gaba dayansu suka yi, Commander Isa Bala ya kalli Ubaidullah ya ce. "Captain me ka ce akan wannan batun?" Ubaidullah ya kai kusan minti goma kafin ya miƙe tsaye da sauri ya ce. "Bamu je yankin Kashmeer ba" Zaidu ya ce. "Yes of course bamu je ba kam tabbas" Ubaidullah ya ce. "Da asuba zamu wuce Kashmeer" addua suka yi Allah ya basu sa a. @@@@ Da asuba suka gama shirinsu tsaf zasu shiga yankin Kashmeer da ga in da suke 100km ne, dan haka da zasu shiga yanki mutanen da suke haduwa dasu a hanya idan suka ce musu zasu shiga yankin kashmeer wasu har gargaɗansu sukeyi domin kuwa yan ta'addane da suka gagari rundunar hukumar ƙasar india baki ɗaya, nan su Ubaidullah suka sake shiga, amma da ta ka tsantsan sabida su na dauke dasu mugayen makamai, tun daga farkon sassaninsu aka fara tarbo su Ubaidullah da ruwan alburushi, nan fa yaƙi ta barke yayinda sojojin nigeria aka rarraba kafa nan su ma suka shiga mai da martani, yaƙi ne wanda ake kira *KO KA KASHE!! KO A KASHEKA!!* a dan ƙanƙanin lokaci Ubaidullah ya zubar da mutane kusan dari a kasa, yawancin yaƙin shi ya fi kowa kokari, dama shine karfin guiwar yaƙi, Zaidu ma ya yi kokarin dan ya zubar da hamsin, KB ma haka, kowa yana iyakar kokarinsa wajan cuto rayuka, taƙaddama kamar wasa amma inaa yaƙi sai kace ana karawa wuta fetur dan kuwa yan ta'addan su na da mugun yawa, Commander Isa Bala ganin an fara zubar da sojojin nigeria dan ga shabiyar kwance a cikin jini nan ya bada Umarnin su gudu, haka aka fara ja da baya, yayinda Ubaidullah yake kara tura kansa cikinsu, kwala masa kira Commander Isa Bala ya yi ya ce. "Captain!!!!! Kazo mu gudu tukunna!!" juyowa Ubaidullah ya yi, ya girgiza kai alamun ba gudu ba ja da baya, da kyar fa Zaidu da KB da wasu sojoji goma suka yanje Ubaidullah suka gudu can wajan kasar babbar rafin kashmeer suka maƙale, ga shi dare har ta yi, wa inda suka ji rauni ne aka fara yi musu magani ta hanyar hura wuta da wuƙa aka cire musu bullet yayinda mutum uku suka rasa rayukansu, sosai hankalin Ubaidullah ya tashi dan har ya fara tausayin iyalansu. ✨✨✨✨✨✨✨✨ MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *_SAKON BARKA DA SALLAH GA ADMINS DIN (COLONEL UBAIDULLAH FANS 1 GRP_* 👇🏻 @⁨💕mhiss precious🌺🤾🏻‍♀️⁩ @⁨Kulsuum Muhd Sadeeq⁩ @⁨Sahra👸🏻⁩ @⁨JOURNALIST💃🏼⁩ @⁨Mrs....... Ce😜⁩ @⁨Mrs. Meenad⁩ @⁨Mu'az⁩ @⁨Rashida Usman⁩ @⁨Be smart💅🏻⁩ @⁨fateema bintu sagir⁩ @⁨احلام فاطمة⁩ @⁨Afnan❤️ *_SAKON BARKA DA SALLAH ZUWA GA DAUKACIN MEMBERS DINA MASOYANA YAN (COLONEL UBAIDULLAH FANS 1 GRP)_* 👇🏻 @⁨Mme Manga⁩ @⁨Ummujabir...🧕🏻⁩ @⁨Mme⁩ @⁨Mme Hadi⁩ @⁨Nafisat M Auwal⁩ @⁨Maimuna Dauda⁩ @⁨Mrs Faruq💃⁩ @⁨Fadeelarh💞💕💗💖⁩ @⁨Firdausi Mrs' Mubarak 💖 😍⁩ @⁨+234 703 230 4446⁩ @⁨Aisha Muhammad⁩ @⁨Nafeesarh⁩ @⁨sadiqaadamumuhd57⁩ @⁨+234 703 747 6207⁩ @⁨Rabee'ah⁩ @⁨+234 703 761 0120⁩ @⁨Aishaabubakar⁩ @⁨Ummun Ameer⁩ @⁨Mrs N Tumah⁩ @⁨+234 704 262 0663⁩ @⁨mrs. babale⁩ @⁨Allah Kajikan Mamana🤲⁩ @⁨Maman Jafar⁩ @⁨Murja Bala⁩ @⁨Maman Kids😍😘🥰👩‍👧‍👧💝💗💞💕❣⁩ @⁨Fateemah Bello⁩ @⁨Maman Zarah⁩ @⁨Zulaitahu Umar⁩ @⁨+234 706 429 2426⁩ @⁨+234 706 442 6394⁩ @⁨neenee⁩ @⁨Aisha Yanusa Jg⁩ @⁨Khadeejah Journalist😘⁩ @⁨balarabakabirumar1122⁩ @⁨Masha Allah⁩ @⁨+234 907 957 0354⁩ @⁨Fatima Garba Musa⁩ @⁨FHR⁩ @⁨Momy Aryaaan😍😍😍⁩ @⁨Khadeejah M Murtala⁩ @⁨Ummee Waxeeri🤝⁩ @⁨Fatee Mk⁩ @⁨umm Ameer⁩ @⁨Faeezeetion⁩ @⁨Hauwa Mohd Aliyu⁩ @⁨Ummi Sagir⁩ @⁨Mommy Hadiza⁩ @⁨ANNABIN DAI ARUHINA🤲🤲⁩ @⁨+234 708 367 1848⁩ @⁨💃 pharteema ldrees yunusa⁩ @⁨+234 708 672 3772⁩ @⁨Jameela Y⁩ @⁨MUMSYN AMRAH⁩ @⁨Binta⁩ @⁨Amina Yayaji⁩ @⁨Maman Hamra⁩ @⁨Ummu Usman⁩ @⁨+234 803 317 2544⁩ @⁨Zainab Aliyu⁩ @⁨Zeenat⁩ @⁨Rukayya Hamisu⁩ @⁨Mom Ayman⁩ @⁨RM Amina Hussaini Abdulla⁩ @⁨Ummu Zarah⁩ @⁨Ummu Herbeber🥰💃🏻😁⁩ @⁨+234 803 534 2401⁩ @⁨Samira Bint Abdallah⁩ @⁨HAJJOH🥰⁩ @⁨Ameena dan larabawa 💃🏼💃🏼⁩ @⁨Rukayya Abdulmumin⁩ @⁨+234 803 797 1219⁩ @⁨+234 803 828 1358⁩ @⁨Maman Sameer⁩ @⁨M A KWR⁩@⁨+234 803 971 9586⁩ @⁨Rabiu Suleman Bradara Shi⁩ @⁨+234 805 842 8211⁩ @⁨Maman Ihsan⁩ @⁨Maryam⁩ @⁨Balkisu Sulaiman⁩ @⁨Zulaihat⁩ @⁨Sis Binta⁩ @⁨Oriflame⁩ @⁨+234 806 415 2288⁩ @⁨+234 806 564 0282⁩ @⁨Maman Abul⁩ @⁨Mmn Ameer⁩ @⁨My Love My Life⁩ @⁨M@M@N ASMEE💃👯‍♂️⁩ @⁨+234 806 701 6862⁩ @⁨Safeeyat⁩ @⁨+234 806 729 1780⁩ @⁨Ummu Haydar⁩ @⁨Alhamdlah⁩ @⁨Maman Fateema⁩ @⁨👩‍🔬Dr,herpsert👩‍🔬⁩ @⁨Maman Dija⁩ @⁨Zainab⁩ @⁨Ruky⁩ @⁨+234 806 966 7345⁩ @⁨+234 806 984 5563⁩ @⁨+234 807 234 0909⁩ @⁨+234 808 133 6510⁩ @⁨Heartbeat❤️💙❤️⁩ @⁨Ameerah⁩ @⁨💄💄Smile M@keup💄💄⁩ @⁨halimasuleimana@gmail⁩ @⁨Maman Noor⁩ @⁨Prince_s_square⁩ @⁨Rashida Aliyu Shehu⁩ @⁨Teemah⁩ @⁨Ummun Sultan⁩ @⁨Aisha Ibrahim⁩ @⁨ummu bilal⁩ @⁨Baiwar Allah 🌹🌹🌹⁩ @⁨🥰Shi'eetawa🥰⁩ @⁨Fauxy cool🥀⁩ @⁨Fatima Zahra⁩ @⁨Hibbaty⁩ @⁨Surayyah Usman Salis⁩ @⁨Uwani Bello✨⁩ @⁨Mummy jidda⁩ @⁨Jannat⁩ @⁨Momyn Noor⁩ @⁨M Yasmin⁩ @⁨Shamsiya⁩ @⁨Ummu Muslim⁩ @⁨Maman Khadija⁩ @⁨Faiza Yusuf Ibrahim⁩ @⁨Maman Alyasa,u⁩ @⁨Khadeejerh⁩ @⁨Halima Aisami😇⁩ @⁨abubakarzainabsoje✨⁩ @⁨~ummu Ilham⁩ @⁨Rukayya Rumah⁩ @⁨Ma'eeshart Twinkle Khan💞💞⁩ @⁨Eeshart Ahmad⁩ @⁨Farhat Mrs mj⁩ @⁨Merry Queen⁩ @⁨+234 907 073 1358⁩ @⁨Zainab⁩ @⁨Meemert💞💞⁩ @⁨Mrs. Meenad⁩ @⁨Ummita Ana Tare🤝🤝🤝⁩ @⁨Ummu Amal⁩ @⁨momyn abeeda⁩ @⁨Ummuaisha👩‍👧⁩ @⁨Maman Khadija Bishir⁩ @⁨Ummi⁩ @⁨+234 905 540 3671⁩ @⁨Ummu Khady⁩ @⁨Ummulsalama Ibrahim🔥🔥🔥🌎🌙🌍⁩ @⁨MMN ISMAEEL 💅💅💄⁩ @⁨Baby Sokoto✈️✈️⁩ @⁨waman yatawakal allah lah⁩ @⁨maman Maryam 💖⁩ @⁨Daddy's Princess👸🏻🥰😘⁩ @⁨Mom Abdallah😘😘⁩ @Bint Muhammad sani❤️❤️ *_SAKON BARKA DA SALLAH ZUWA GA MASOYANA MEMBERS DINA, YAN (COLONEL UBAIDULLAH FANS 2 GRP)_* Badiyya@ (mrs Moh)@hafsat@ummu adnan@amina Abbas abdulkadir@unknw@unknw@dr muhammad@nafisa m bello@mmn yanbiyu@ Maman alameen @ummeen pj@ummy @jamila ibrahim@maman mahseen @Allah akbar@maman affan @ayshat Ibrahim umar @unknw@shafaatu@mrs babale@unknw@unknw@maman khaleel@maman kausar@65799707a@halima Ummi shafa@ummu fteemah@saadatu ahmad@binta adamu @ameera Omar@abubakarhabiba@mariya adamu@unknw@umu imam@maman yan2@mommy ihsan@unknw@unknw@zulaha @ummieter@mimmy@ halimatumusa@aishababagana@mmm@unknw@maman jidda@ Khadijah Musa idris@ Meenal mohammad@ayshertumar73@anty maryam@princess hanal@hadizabalarabe30@mail.com@zainab abdullahi@fatima@khadija mustapha@ameerah@fatima khalil@fatima ibrahimmohammad@aishaibrahimali@maman saddeq@maman mohammad@ unknw@maryam Musa muhammad@bilkisuusman sani7@unknw@aishatu abubakar usman@hm @⁨+227 84 37 10 90⁩ @⁨+227 88 17 19 71⁩ @⁨+234 701 923 4584⁩ @⁨Amina abbas Abdulkadir⁩ @⁨+234 703 116 1097⁩ @⁨🇩 🇷—🇲 🇺 🇭 🇦 🇲 🇲 🇦 🇩⁩ @⁨Nafisa M Bello⁩ @⁨Mmn Yan Biyu👫🏻👫🏻⁩ @⁨Maman Al Ameen⁩ @⁨+234 703 547 9340⁩ @⁨Ummy⁩ @⁨Jamila Ibrahim❤️⁩ @⁨Maman mahseen⁩ @⁨+234 704 328 6999⁩ @⁨Maman Affan🥰🥰⁩ @⁨Ayshat Ibrahim umar⁩ @⁨+234 705 529 2976⁩ @⁨Shafa Átú😘⁩ @⁨mrs. babale⁩ @⁨+234 706 086 4622⁩ @⁨+234 706 347 9271⁩ @⁨+234 706 434 1892⁩ @⁨Maman Kausar⁩ @⁨+234 706 579 9707⁩ @⁨💃💃Halima💃💃⁩ @⁨+234 708 180 7994⁩ @⁨Ummu Shafa⁩ @⁨ummu fteemah⁩ @⁨Saadatu Ahmad⁩ @⁨binta Adamu⁩ @⁨Ameera Omar⁩ @⁨Abubakar Habiba⁩ @⁨Mariya Adam⁩ @⁨+234 803 658 4929⁩ @⁨UMMU IMAM!⁩ @⁨Maman 'Yan 2.⁩ @⁨Mmn Salma⁩ @⁨mmn maryam⁩ @⁨Mommy Ihsan⁩ @⁨Ameerah⁩ @⁨+234 803 941 7780⁩ @⁨+234 806 006 3668⁩ @⁨Zulaihat⁩ @⁨Ummieter🌹🌹⁩ @⁨Momy⁩ @⁨Halimatu Musa⁩ @⁨+234 806 468 8272⁩ @⁨+234 806 576 3898⁩ @⁨+234 806 605 9181⁩ @⁨Maman Jidda⁩ @⁨Khadija Muhd Idris⁩ @⁨+234 806 677 1959⁩ @⁨Halimatu Musa⁩ @⁨+234 806 696 1303⁩ @⁨Anty Maryam⁩ @⁨Princess Hanal👑👸⁩ @⁨hadizabalarabe30@mailcom⁩ @⁨Dr Zainab Abdullahi💊💊🩺🩺💉💉⁩ @⁨Fatima⁩ @⁨Khadija Mustapha⁩ @⁨Fatima Ibrahim Muhammad⁩ @⁨Ameerah⁩ @⁨Phartiemarh Khavier⁩ @⁨Fatima Ibrahim Muhammad⁩ @⁨+234 810 518 2303⁩ @⁨+234 810 589 0170⁩ @⁨Maman Muhammad⁩ @⁨+234 810 758 6356⁩ @⁨bilkisuusmansani7⁩ @⁨Maryam Musa Muhammad⁩ @⁨AISHATU ABUBAKAR USMAN🦋⁩ @⁨Ideal Midwife⁩ @⁨Ummu Salma⁩ @⁨HM⁩ @⁨Ummi suraj ❤️ ❤️⁩ @⁨+234 812 312 3728⁩ @⁨Shaawanatu Umar⁩ @⁨Salmatee✨🖤(👁️👃👁️)⁩ @⁨+234 813 384 5059⁩ @⁨+234 813 454 9958⁩ @⁨Fatima Y Umar⁩ @⁨+234 813 759 9429⁩ @⁨Maryam Danmalam⁩ @⁨aisha⁩ @⁨Mum Hanan⁩ @⁨Kcubraah🧕🏽⁩ @⁨😘🥰Aunty kh@leel@h🤎🤎⁩ @⁨Haseena⁩ @⁨Hassana⁩ @⁨aisha⁩ @⁨am7600652⁩ @⁨+234 814 081 7417⁩ @⁨Hadiza Abdullahi⁩ @⁨+234 814 442 0460⁩ @⁨+234 814 502 0695⁩ @⁨Kunyah⁩ @⁨+234 814 655 5970⁩ @⁨Ummu Ramlat⁩ @⁨+234 814 682 5749⁩ @⁨Deejaa⁩ @⁨Maman Amir⁩ @⁨+234 814 852 6181⁩ @⁨Eyshert Sule⁩ @⁨Eyshert Sule⁩ @⁨Zainab Saidu Sintali⁩ @⁨Aeesh⁩ @⁨Maryam Abdullahi💔💔⁩ @⁨بلقيس أحمد😍😍⁩ @⁨Maman Maryam⁩ @⁨Phareedah⁩ @⁨+234 816 379 0110⁩ @⁨Jeeddat⁩ @⁨Ummu Affan S⁩ @⁨+234 906 715 6932⁩ @⁨Ummu Ahmad💞💕❣️⁩ @⁨Maman Affan🥰🥰⁩ @⁨+234 906 574 8204⁩ @⁨Meenal⁩ @⁨Zainab Zee⁩ @⁨+234 906 323 2991⁩ @⁨Maman mahseen⁩ @⁨Maman Abdulmajid⁩ @⁨MAMAN JAFAR⁩ @⁨+234 906 001 2549⁩ @⁨Momy Ummee⁩ @⁨Khadeejat A.b.d.⁩ @⁨بلقيس أحمد😍😍⁩ @⁨Badiyya⁩ @⁨+234 703 547 9340⁩ @⁨Ummi⁩ @⁨Ummu Sulafah⁩ @⁨MRS MASHKUR⁩ @⁨+234 816 530 4790⁩ @⁨Hansa'u Haliru Iro⁩ @⁨+234 816 613 9834⁩ @⁨Ittakinnara Bilobishikin⁩ @⁨MAMAN HANEEF⁩ @⁨+234 816 881 4664⁩ @⁨karimataliyusani⁩ @⁨+234 901 277 7302⁩ @⁨😍😍😍😍⁩ @⁨+234 903 358 1796⁩ @⁨Khadija Abdullahi⁩ @⁨mmn maryam⁩ @⁨+234 903 733 3752⁩ @⁨Nafeesat Feesat👩🏻‍⚕️👗👑👛🤹🏽‍♀️⁩ @⁨+234 903 668 5864⁩ @⁨+234 903 496 0646⁩ @⁨Maman Musty⁩ @⁨+234 903 609 5250⁩ *_INA ALFAHARI DAKU_* 💞💞 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *_MY WATTPAD FANS KU MA BAN MANTA DAKU BA, INAYINKU SONSO DOMIN ALLAH, BARKANMU DA SALLAH_* 👏🏻👏🏻 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *page°°°°°86&90* Sun jima a haka kafin daga bisani ya zare bakinsa daga nata, idonsa sun kaɗa sunyi jajur dan jaraba da ta taso masa lokaci guda, cikin dauriya ya fara bata abinci, kaɗan ta ci, ta kauda kanta gefe tana yatsine fuska ta ce. "Am ok", Ubaidullah ganin bata ci abincin sosai bane ya saka shi haɗe rai sosai ya yi kamar bai ji me tace ba, ya ci gaba da ɗura mata abinci har sai da ta fara kakarin amai kafin ya kyaleta, tashi tayi ta wuce bedroom dinta ba tare da ta kallesa ba, ruwa ta watsa, sannan ta canza kaya itama, ta fito ta same shi, kama hannunta ya yi suka fita, nan suka tarar dasu Ummi, har dasu Umma da Inna a parking space, nan suka shiga mota suka koma asibitin. Su na shiga Abi'atu ta hango Shafa'atu zaune a jikin wata Addanta tana ta faman kuka, da gudu Abi'atu ta karaso ta rungumeta ta hau lallashinta, yawancin yan uwa da aka zo domin fara shirin biki duk sunzo asibitin, nan Ummi take shaida musu cewa Abba yace za a daga bikin, nan wata Gwaggonsu tace sam, lokacin bikin ma za a rage a daura aure tayi jinyar mijinta, bayan ya warke yaji sauki sai ayi shagalin biki, kasancewar Gwaggo itace babba haka kowa ya amince za a daura auren Safwan da Shafa'atu gobe da ya ji sauki kuma sai ayi shagalin biki, sai dare tukunna Safwan ya farfado kuma Alhamdulillah ya gane kowa, nan suka shiga hamdala su na godewa Ubangiji, da dare da suka koma gida bayan Ubaidullah ya yi wanka ya kwanta ya tuno dasu memories da lapton din da yasa aka kawosa gida dasu, kamar an zaburesa haka ya mike ya fito, yana fitowa itama tana fitowa,karo suka yi zata fadi ya riƙeta gami da jefo mata tambaya. "Ina zakije?" "Kitchen" "Me za ki yi?'' haɗe rai tayi dan bata ga dalilin tambayar da yake mata ba, ganin ta hau turo masa baki ta ƙi basa amsa ya sa shi matseta ta yi yar kara tana harararsa. "Au zasu tashi ne?" Ya tambayeta yana kafeta da ido" "Su wa?" "Ƴan rashin kunyan mana, yanzu nayi maganinki" kwace jikinta ta yi tana cewa. "Ai ban ga amfanin tambayarka bane" ta fada ta wuce kitchen, murmushi ya yi, ya fuskaci Abi'atu akwaita da gautsi, zama ya yi ya dauki lapton din ya bude ya hau bincike a ciki, fitowa ta yi daga kitchen din ganin system din a hannunsa yasata zuwa wajansa da sauri ta zauna, sai kuma ta fashe da kuka, da sauri ya kalleta ya ce. "Lafiya?" cikin kuka ta ce. "Na'ilah" "Na'ilah,a ina?" bata tsaya basa amsa ba illa system din ta karba ta shiga in da ta ga samarin nan sun shiga, nan videos suka watso, zaro ido Ubaidullah ya yi, yana kallon tashin hankali, bincikawa Abi'atu ta ci gaba da yi har aka zo kan na margayiya, da sauri Ubaidullah ya karba yana gani, wasu zafafan hawaye ne suka wanke masa fuska ganin yadda ƙanwarsa ke neman taimako har wa innan azzaluman suka farmata, cikin gaggawa Ubaidullah ya dannawa Zaidu kira sannan ya ce ya duba email dinsa ya turo masa da sakonni, ko da Zaidu ya duba sai da ya yi danasanin meyasa ma ya kalla, kuka sosai Zaidu ke yi tamkar ba soja ba, Ubaidullah ya sake kiransa akan cewa, ina an kawo masu laifin barracks, Zaidu ya amsa da cewa ba a kawosu 9ja barracks ba, abacha barracks aka kai su, sai gobe za a shigo dasu 9ja barracks, Ubaidullah ya ce gobe idan jikin Safwan da sauki sosai zai bi jirgin yamma ya dawo abuja, da haka suka yi sallama da Zaidu, su na kiyasta kalar azaban da zasu gana musu kafin su kashesu, videos din ya turawa Zeey sannan ya kirata ya mata bayanin abun da zata yi, nan ta amsa masa cike da girmamawa, a ranar Ubaidullah bai rintsa ba, ko da washe gari da safe misalin karfe shaɗaya da rabi aka daura aure, kuma jikin Safwan din da sauki sosai, nan Ubaidullah ya musu sallama a asibitin gami da cewa zai wuce, Allah ya kiyaye hanya su Abba da Ummi da Safwan din da sauran wa inda suke wajan suka masa tare da fatan Allah ya ba shi sa'a, gida ya dawo dasu Mama, Hafiza da kuma matarsa Abi'atu, bayan ya gama shirinsa cikin kakinsa wa inda a ko da yaushe suke masa kyau, fitowa ya yi, a parlour ya sameta tana tsaye, cikin sanyin jiki ya zo gabanta ya kama hannunta ya ce. "Zan wuce, kafin na tafi sai na tabbatar hukunci ta hau kan wa inda suka yi sanadiyyar ƙanwata da yaran jama'a, zamu tafi india kuma aiki ne mai hatsarin gaske, ban sani ba ko zan dawo ko bazan dawo ba, idan na mutu ki yafe m....." sauri toshe masa baki ta yi ta fashe da kuka ta rungumesa, dan murmushi ya yi, ya ce. "My Abi'ah, ki jirani! Ki jira dawowata, zan ba ki mamaki" yana gama faɗi ya bata light kiss a gaba daya fuskarta, sannan yasa kai ya fice, ita kuma ta zube a wajan tana kuka dan ba zata iya jurar ganin tafiyarsa ba, dan ko ba komai fadan da sukeyi ba karamin sabo bane ya shiga tsakaninsu, kuma ko ba komai zaman da suka yi ta fara son mijinta, itama kuma ta ga alamun hakan a wajansa, addua ta hau masa tana durƙushe a wajan, ko da ya fito sallama ya yi da Mama da Hafiza, sannan ya ce, bai yarda su dinga fita ba, zai aiko musu sojoji mutum uku masu kula dasu, addua Mama ta yi masa da fatan alkhairi gami da ƙarfafa masa guiwa, ya yi murmushi ya amsa da ameen gami da yi mata godiya, da haka aka bude masa mota ya shige, basu tsaya ko ina ba sai airport, ko da suka isa mintinsa shabiyar jirginsu ya daga izuwa birnin tarayya, karfe huɗu dai-dai a barracks ta yi masa, ya yinda dubbannin sojoji aka zo tarban Ubaidullah abun har mamaki ya ba shi, da masu sara masa da masu miƙa masa hannu,shima ƙamewa ya yi yana sarawa manyansa, kafin daga bisani suka rungumi juna da aminansa, Zeey ce ta taho da murnarta tana sanye da kaki a jikinta murmushi ta yi masa sannan ta sara masa gami da cewa. "Wlcm back Sir, Captain Ubaidullah Abdullahi" karo na farko da Zeey ta fara ganin dariyan Ubaidullah,dan kuwa dariya ya mata gami da cewa. "Tnk u Zeey, a gaskiya ke din ta dabance,kuma kin zama ta musamman a wajana" itama dariyar ta yi ta ce. "Kamar yadda kai ma kake na musamman awajan kowa ko? ya Madam? Fatan ka barota lafiya,dasu Mama da Ƙanwarmu Hafiza?" "Duk su na lafiya Alhamdulillah" "Ya mai jikin fatan yana samun lafiya?" "Eh jikinsa da sauki sosai, dan yau ma aka daura aurensa, sabida dole akwai abun da zai bukata wanda dole sai muharramarsa ce zata iya yi masa hakan" jinjina kai suka yi, sannan Zeey ta kuma cewa. "Ba a kawo masu laifin wannan barracks din ba fa, har yanzu su na Abacha Barracks, amma ka je ka huta, tun da ka iso, idan ka gama dasu, Rumaisa da mahaifinta da Ema duk su na kulle" girgiza kai Ubaidullah ya yi ya ce. "No Zeey ban ga ta hutu ba, in dai wa innan azzuluman su na numfashi a doron duniya, bari naje na gana da General Of The Army, sannan na zo na wuce Abacha Barracks din" KB ya ce. "Gaskiya kam, dan tun jiya nake cikin zaƙuwa a kawosu, jiya fa Zaidu kwana ya yi yana kuka, dama baka turo masa ba wallahi" Zeey ta girgiza kai cike da tausayawa ta ce. "Ka je ku gama da General din, Captain, nima na gama aikin da ka sakani jiya" murmushi ya yi ya ce. "Ina alfahari dake Zeey, just keep it up" itama murmushin ta yi sannan ta wuce. Duk in da Ubaidullah ya ratsa sai an kallesa, masu sara masa su na sara masa, har ya isa office din General ba tare da bata lokaci ba, General Of The Army ya bawa Ubaidullah Umarnin shigowa, bayan Ubaidullah ya shigo ya sara masa suka gaisa, General ya sake ba shi hakuri, Ubaidullah ya nuna masa komai ya wuce sannan ya yi gyaran murya ya fara magana. "Sir, akan yaran da aka kamasu da laifin aikata fyaɗe, gasu videos din b'arnan da suke aikatawa, daga cikin yaran da suka yiwa fyaɗe har da kanwata wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta har lahira, Sir! A ko da yaushe sai munji cases din fyaɗe sama da dari a garurruwa daban daban, Sir! Abun da yake daure min kai a matsayinmu na jami'an tsaro ban taba jin wanda aka kai shi kotu aka yanke masa hukunci, ko naji an hukunta masu aikata hakan ba, wanda zai zama izna ga masu aikatawa ko masu burin aikatawa dasu tsarota su hankaltu,dan masu iya magana su na cewa ana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, Sir! Ina neman alfarma, a barni na hukuntasu da hannuna ba tare da an kaisu kotu ba, dan naga alama akwai yaran masu kudi a cikinsu wanda suke da daurin gindin manyan ƴan ƙasa, hakika idan za a dinga zalunta bayin Allah marasa karfi sannan a danne musu hakkinsu, hakika duniya ba zata taba zama lafiya ba, dan yanzu an mai da ran muninai ba a bakin komai ba, taya ma duniya za a zauna lafiya bayan jinin bayin Allah da ake wanke kasa dasu sir? Lokaci ya yi da ya kamata ace an samu wani ci gaba a ƙasarmu ta nigeria, Sir! Dama nake so ka bani a karin farko, kafin muje yaƙin karbo yan matan ƙasata wanda aka yi garkuwa dasu" sosai General Of The Army yake kallon Ubaidullah, dan kuwa ba karamin burgesa Ubaidullah ya yi ba, a take ya ce. "Captain Ubaidullah na baka go ahead, wish u oll the best" murmushi Ubaidullah ya yi, ya sarawa General Of The Army gami da cewa. "Tnk u sir, Allah ya ɗaga ƙasata nigeria" sannan ya juya ya fice, yana fitowa suka hadu da Hanan, wani dadi ne ya ziyarci zuciyarta, da sauri tazo tana yi masa wlcm back, Ubaidullah ya amsa ba yabo ba fallasa, nan suka dan gaisa sama-sama, sannan suka yi sallama, wajan su Zaidu ya wuce nan suka shiga mota har da Zeey, Abacha Barracks suka wuce, sai da ya je suka gaisa da Major Usman, rungume Ubaidullah Major Usman ya yi, dan yana son Ubaidullah sosai, sannan Ubaidullah ya ce sun zo tafiya da masu laifi ne, nan Major Usman ya bada Umarni akawo su, su tafi dasu, hakan kuwa aka yi, tun akan hanya suke cin duka wajan Zaidu, har suka iso 9ja barracks, direct suka wuce guardroom dasu, inda suka rufesu da duka, tun su na ihu har suka kasa ihu, sai da suka musu lilis, kafin da kyar KB ya janye Ubaidullah da Zaidu, suka koma gefe suka zauna, Ubaidullah ne ya jawo kujera ya matso su sosai, sannan yasa aka kawo masa ruwa, nan KB ya sheƙa musu ruwan, wayar wuta Ubaidullah ya jawo, wanda daga gani kasan shocking zai jona musu ko ba a fada maka ba, a matukar galabaice wani ya ce. "Yallabai! Dan Allah kayi mana rai, ka yafe mana, ba zamu sake ba, bamu san cewa kai din soja bane, da mun san cewa kai soja ne da bamu fara ɗau....." saukar naushi ne ya hanasa karasa maganar da yake yi, wanda Zaidu ne ya kai wannan naushin, a matukar tunzure zuciyarsa na ƙuna ya ce. "Shut'up!!! Mutanen banza!! Allah yana arawa mugayen mutane irinku lokaci dan su aikata barna son ransu, kafin Allah ya dakatar daku a madakata, shin kusan wacece *NA'ILAH!!!!?* ita din Ƴa ce, ga tsohon *SOJA* wanda ya riƙe muƙamin Major kafin Allah ya ɗauki ransa a bakin aikinsa, sannan Ɗansa yake riƙe da mukamin Captain, *NA'ILAH! ƳA CE GA SOJA! ƘANWAR SOJA, MATAR SOJA!* amma ku ka yi sanadiyyar mutuwarta, tun da gaku yan iska ko!!! Shi ne ku ka kyetara ta gonawa kooo!!" ya faɗa gami da sa kafarsa mai dauke da boot army shoe ya take gaban ɗayansu ya saki ihun azaba, Ubaidullah ya jona musu shocking. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ *_SAKON BAN HAKURI GA MASOYANA 😪😪 A TAYANI DA ADDUA BUK YAZO GANGARA AMMA GAMAWA YA ZAMA AIKI, BUK DIN NAN ZAI KAMMALU NE A CIKIN SATIN NAN DA YARDAN ALLAH, AMMA DA TAIMAKONKU MASOYANA, TA HANYAR ZUBA MIN SHARHI WANDA ZAI SAKANI POSTING SAU UKU A RANA 😜🤪, INA KARA BAKU HAKURI, BARKANMU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN_* 👏🏻👏🏻👏🏻 MOMYN AHLAN TAKU CE👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* 🤔🤔🤔 *_OH ALLAH NA NI ZAHRA UWAR AHLAN, TUN BAN DAUKI MAGANAR DA WANI MAHIMMANCI BA DA ZANYI MAGANA AKAI, AMMA SAKON DA NA ISKE A PC DA KUMA KIRAN WAYA YA SA ZANYI MAGANA, AKAN PAGE DIN DA YA GABATA KAFIN WANNAN, WAI KAR NA KASHE UBAIDULLAH IDAN YA MUTU LABARI YA B'ACI, TO INA DA YAR TMBYA, "SHIN YA SUNAN BUK DIN NAN NE KAM? INA CE SUNAN SHI COLONEL UBAIDULLAH NE? KUMA HAR YANZU UBAIDULLAH YANA CAPTAIN NE BAI JE COLONEL BA, TO IDAN YA MUTU MA NI ZA A NAƊAWA COLONEL DIN? 🤔 ) DUK MA BA WANNAN BA, A RAYUWA BA KOMAI KAKESO YAKE ZUWA MAKA YADDA KAKESO BA, INA SO KU FAHIMCI HAKAN PLS, KAR MU DIN GA RAYUWA AKAN SON ABUN DA MUKE SO DAN ZA TA IYA KASANCEWA BA ALKHAIRI BANE, DA YAWA WASU BA WAI SU NA KARANTA NOVEL DAN SAKON DA YAKE CIKI BANE, WASU SU NA KARANTAWA NE DAN NISHADI KAWAI, PLS AND PLS, KAR MU DIN GA TAFIYA A NISHADI, A TAFIYA ANA SO A DIN GA WAIWAIYE( HAUSA CE) FATAN KUN FAHIMCENI, AHA MASOYANA MUJE DAI A CI GABA DA KAFTAWA_* 🤾🏻‍♀️🤾🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ *page°°°°°101&105* "Ubaidullahhhhhh!!!?" Zaidu ya furta da karfi ya dagosa yana jijjigasa cikin tashin hankali, da sauri shi ma KB yazo suka rungumi Ubaidullah su na ambatar sunansa cike da tashin hankali, cikin gaggawa sojojin india suka yo kan Ubaidullah, nan suka taimaka aka saka shi a mota sai asibiti ma fi kusa da Kashmeer, nan aka wuce emergency da Ubaidullah, faɗin halin da su Zaidu suke ciki abun baya misaltuwa, ko da suka sanar da barrack dinsu an harbi Ubaidullah nan barrack ta rikice, kafin kace me labari ya karaɗe barrack akan sojojin 9ja barrack sunyi nasara amma an harbi jarumi Ubaidullah. Likitoci su na ta faman kokarinsu wajan ganin sun cuto rayuwar Ubaidullah in da babu bata lokaci suka shiga yi masa aiki dan cire masa bullet din da yake jikinsa, kasancewar kasashen waje sun fi kasarmu bada attention akan marasa lafiya, kusan kwana suka yi su na aiki akan Ubaidullah dan harbin da aka masa wajan gefen ƙirjinsa kiris ya rage bai wuce ya huɗa masa zuciyarsa ba Allah ya taimaka, amma da ace Zaffar ya sake harbinsa wajan saitin wajan ba ma kawa da ya mutu, bayan sun gama yi masa aiki ne suka saka shi a cormer dan kuwa yana cikin mawuyacin hali. Satin Ubaidullah ɗaya a comer har yanzu bai san inda yake ba, dan ba fiddo shi aka yi ba, harta su Zaidu sai dai su hangosa ta glass, sosai yake samun kulawa wajan jami'ai da kuma hukumar sojojin india da na ƙasarsa nigeria, su ma su Zaidu sosai suke bawa Ubaidullah kulawa dan burinsu bai wuce su ga Ubaidullah ya samu lafiya ba. @@@@ Da yawa mutanen nigeria sunji labarin cewa jaruman sojojin sun kwato yan matan da akayi garkuwa dasu, kuma da ake zantawa dasu sun fadi wanda ya fiddosu amma abun daurewar kai din shine ina *CAPTAIN UBAIDULLAH* din yake ? Dan kuwa ance kar a faɗi abun da ya same shi ya zama sirri har sai ya ji sauki tukunna. A gida kuwa ganin labarai ya karaɗe yan mata sun dawo kasarsu da yawan sojojin ma sun dawo, daga ciki har da commender'n yaƙin amma babu Ubaidullah ba Zaidu ba KB, nan fa hankalinsu Mama ya tashi fiye da misali, nan suka din ga azalzalan yan barracks din su Ubaidullah inda a karshe Major Usman ya ce kawai a fadawa duniya gaskiya tun da Allah yasa Ubaidullah din bai mutu ba, nan kuwa aka yi kiran manema labarai inda Major Usman ya wakilci 9ja barracks da Abacha barracks ya yi jawabin akan mashahurin sojan nan wanda yake sadaukar da rayuwarsa wa kasarsa inda Major Usman yake cewa masoyan Ubaidullah su taya shi da Addua dan lokacin da ya kubutar da yan matan kwantenan karshe aka harbesa yanzu haka yana asibitin kasar india yana samun kulawa, a yankin kashmeer wajan kusa da inda suka yi yaƙin, kuma a halin yanzu yana cikin comer dan Allah masoya a taya shi da addua Allah ya tashi kafadunsa, domin ace an rasa mutane kamar su Ubaidullah ba karamin babbar asara aka yi ba, da haka jama'a suka gamsu yayinda kuma suke yiwa Ubaidullah fatan samun lafiya. @@@@ Ko da Abi'atu ta ji labarin an harbi mijinta yana cikin comer a take ta zube kasa sumammiya, ruwa-ruwa aka yi da ita asibiti, ko da ta farka kuka ta din ga yi tana kiran sunan mijinta, kwananta uku aka sallamota, nan suka koma gida amma hankalinsu ba a kwance yake ba. @@@@ Satin Ubaidullah biyu aka fito dashi daga comer inda ya farfado jikinsa da sauki amma da alama yasha wahala ya ji jiki, kwanarsa uku da fitowa ya fara shirin komawa kasarsa, kafin ya farka manyan sojojin nigeria duk sun zo duba shi, a daren ranar da zasu koma nigeria nan shugaban sojojin india yazo ya samu Ubaidullah da wani zancan, kallon marar hankali Ubaidullah ya masa kafin yayi wani murmushi mai wuyar fassara,ba wani abu bane illa su na so su siye Ubaidullah ya dawo kasarsu da zama ya shige cikin rundunarsu, dan sun yaba da jarumtarsa, ba yaudara ba boye-boye Ubaidullah ya ce. "A yawan kasashe na duniya, dukkan dan ƙasa yana kaunar ƙasarsa,amma babu wanda suke nuna fiffiko akan kasarsu sama daku, kun mai da kasarku uwa kamar yadda kuke furtawa, babu abun da ba zaku iya yi ba akan kasarku sabida kishinta da kukeyi, nima hakan take a wajena, ina aikine wa ƙasata ba dan albashin da nake dauka ba, illa alƙawari da rantsuwan da nayi na kare ƙasata da dukkun baiwar da Allah ya bani, dabadin gumi na halak da nake ci ba, da sai na bar karban albashi, sabida son ƙasata da nake yi nima, *ALLAH YA ƊAGA NIGERIA!!*" Ubaidullah ya fada yana sarawa shugaban sojojin india, ba karamin sanyi jikinsa ya yi ba, haka ya tashi ya fita yabar Ubaidullah, ko dasu Zaidu suka tambayesa wani magana ne sukavyi da shugaban sojojin india dariya kawai Ubaidullah yabyi kafin ya basu labari, zare ido KB ya yi jin makuɗan kudin da zasu biya Ubaidullah, Zaidu ya ce. "Su fa naga alama sun raine mutane wallahi" Ubaidullah ya ce. "Manta dasu kawai" nan suka ci gaba da shirinsu, ko da washe gari da zasu baro india a motar asibiti aka kai Ubaidullah airport, su Zaidu ne suka taimaka masa lokacin da zasu shiga jirgi, an saka masa bandage a wuyarsa wanda aka rataye masa hannunsa, bayan sun zauna Ubaidullah ya lumshe ido yau yana cikin farin ciki marar misaltuwa zai je ya ga iyalansa wata kusan biyar kenan rabon shi dasu, su Zaidu ma haka murna suke yi. @@@@ Sai dare su Ubaidullah suka sauka a airport din abuja, sojoji ne birjik aka zo tarbansu, da ɗima-ɗima motocin barrack, nan jama'a ake ta sarawa Ubaidullah masu mika masa hannu su na mika masu, Major Usman yana zuwa ya rungumesa Ubaidullah ya danyi kara kadan wanda Major Usman ne kawai ya ji, duk sun bi sun rame tamƙar basu ba tsantsar wahala da tashin hankali, nan aka shiga mota sai barrack, direct aka wuce da Ubaidullah part dinsa dan ya huta tun da baya da lafiya, bayan su Zaidu sun taimaka masa ya yi wanka ya fito yana dingisawa dan harta kafarsa na hagu a kumbure yake dan wajan faɗa akwai wanda ya buga masa ƙotan bindiga, zama ya yi a gefen gado ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a gida amma ba hali, muryan Zaidu ya ji yana tsokanarsa da cewa. "Alhamdulilah mun tsallake teku da baya, dan mu kam ba zamu ce rijiya ba, wannan yaƙi da tashin hankali, wlh ban sa ran zan dawo a raye ba, gaskiya Malam ka dawo da matarka ta karasa jinyarka dan Madam ce kawai zata iya yi maka wasu abubuwan, amma mu kam ba zamu iya ba" harara Ubaidullah ya gallawa Zaidu duk da na wasa ne dan rabon da Zaidu ya masa irin wannan wasa tun Na'ilah na raye, ga shi baya jin dadi balle ya biye masa su dan capta, dan haka maganinsa yasha ya kwanta. @@@@ Da washe gari bayan kananun sojojin sun zo sun yiwa Ubaidullah ya jiki, da misalin karfe biyu Major Usman ya zo shi ma, da sauri su Zaidu da KB suka miƙe su na sara masa, murmushi Major Usman ya yi ya kalli Ubaidullah, shi ma sara masa ya yi da gefen hannu da kyar ma yake iya motsa hannayen nasa, takardu Major Usman ya mika musu dukkansu, suka karba suka buɗe KB ne ya fara ihu da ya karanta, ya miƙe tsaye yana tsalle kamar karamin yaro, Zaidu ma haka murna ne ya cika shi, ticket Major Usman ya sake miƙa musu, nan Zaidu ya bude ya ga jirgin yamma na yau, bai san lokacin da ya kama kafar Major yana godiya ba, kallon Ubaidullah Zaidu ya yi ya ce. "My Man gida zamu tafi yau an bamu hutun wata daya da iyalanmu, muje su ganmu" murmushi ne ya bayyana a fuskar Ubaidullah ya kalli Major Usman ya ce. "Sir, nasan wannan dukka kokarinka ne,mun gode sosai" "Haba dai, ku daina godiya,ni ina amfani da abun da ya kamata ne, shiyasa kuna dawowa jiya na samu General Of The Army muka tattauna da shi, kuma kai Ubaidullah kana bukatar kulawa, kunyi matukar kokari, dan haka ku koma gida ku huta, Ubaidullah zaka fi samun kulawa, In sha Allah a wata daya jikinka yayi kyau, sai ku dawo da iyalanku dan kuzo ayi liyafan karramaku" sosai suka din ga zuba masa godiya ba shiri suka mike suka hau tattara kaya, Zaid ne ya taimaka ya hadawa Ubaidullah na shi nan suka yi sallama da barracks aka wuce dasu airport, mintinsu talatin jirginsu ya daga izuwa bauchi, shi kuwa KB dan Kaduna ne dan haka suka yiwa KB sallama su suka wuce abun su. Basu sauka da wuri ba sai wajan bakwai, tun kafin jirginsu ya sauka sojoji suka zo daukarsu, dan haka su na sauka sojoji suka sara musu sannan Zaidu ya ce zai raka Ubaidullah gida, amma sam Ubaidullah ya ƙi yace kawai ya wuce gida shi ma ya tabbata su Umma sunyi kewarsa su na son ganinsa, kawai su tafi idan yaso ya zo gobe, da haka suka yi sallama aka bude musu mota suka shiga Zaidu ya dagawa Ubaidullah hannu, shi kuma ya ɗaga masa kai, nan driver yaja su sai gida. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Kwance take a parlour akan 2sitter duk ta rame ta yi duhu itama, idonta a lumshe kamar mai jin bacci ta rufu da hijabinta, kamshin turaren da take kwana dashi ta tashi dashi, shine ya mata sallama wanda ya yi sanadiyyar zaburanta ta mike zaune, nan ta gansa tsaye a bakin kofar parlour wanda shi ma wa ita ya zubawa ido yana kallonta, murje idanunta ta yi ta rufe ta bude still dai ta ga ba gizo bane a hankali ta miƙe jiri na dibarta ga kyarman da jikinta ya ɗau lokaci guda, hannunsa daya Ubaidullah ya miƙa mata alamun tazo, a hankali take taku yayinda idanunta hawaye yake ambaliya har tazo gabansa tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, nan ta tabbatar da eh lallai shi ne, ihu ta saka tana kiran sunan Mama da Hafiza, dan dama a parlourn Maman take kwance, bata san lokacin da ta rungumesa da gefen da baya da rauni ba tana kuka mai tsuma zuciya, shi ma Ubaidullah din hawaye ne suka hau wanke masa fuska, Hafiza wacce take wanka ta ji Abi'atu na kwala kira haka bata gama wankan ba ta fito ta daura zani, ta saka hijabi, parlour ta fito ta tsaya turus ganin Yayanta, shima kallonta ya yi ya mika mata hannu da gudu tazo ta rungumesa gefe daya tana kuka itama, ɗaga kai Ubaidullah ya yi ya ga Mama tsaye kofar dakinta tana ta faman kuka, sake su Hafiza da Abi'atu Ubaidullah ya yi yaje gaban Mama yana kallonta yana murmushi tare da hawaye, bakin Mama na b'ari cikin raunin murya ta ce. "Yaya Babba?" da sauri Ubaidullah ya rungumi mahaifiyarsa yana hawaye. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ A lallaba bani da chaji 😢 UMMU AHLAN TAKU CE👍🏻 [8/19, 10:59 AM] Zarahh: *COLONEL UBAIDULLAH* ( _the story about a young gentle man_) *ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY*✍🏻 *Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢* (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ) ( *y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾*) 👸🏻 *SAHIBAR KAINUWA*👸🏻 _dedicated to my brother_ *~UBAIDULLAHI~* ~~•~~•~~•~•~•~ _my wattpab_@Fateemah0 ~~•~~•~~•~~•~~• *Special gift to my 5 ☆stars★* _Samira bint Abdallah_💋 _Fatima bintu Sagir_💋 _Farhat Mrs M'J_💋 _Princess (Nafeesat)_💋 _احلام فاطمة_💋 *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻 ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻 https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association *____________________________________* *page°°°°°106&110* Sun jima haka kafin daga bisani Mama ta dago tana shafa fuskar Ɗan nata, tana jin farin cikin sake ganinsa, Hafiza ce ta kira Anty Ummu ta sanar mata akan cewa Yaya Ubaidullah ya dawo, Anty Ummu ba shiri ta zari hijabi takalmi ma daban-daban ta saka ta fice, Hafiza ma ficewa tayi da gudu ta je ta kirawo su Ummi ta ce Yayanta ya dawo, kafin ka ce me maƙota an cika parlourn Mama ana yiwa Ubaidullah jaje da ya jiki tare da yi masa fatan alkhairi akan nasarar da suka samu, har Anty Ummu ta iso tana zuwa ita ma da kuka ta tari ƙanin nata, idan ka kalli fuskokinsu a yau kasan su na cikin farin ciki matuƙa, har wajan karfe goma gidan Mama ana hayaniya, har da yan mata, musamman suke zuwa ganin jarumi Ubaidullah ya yinda da yawa su na fatan su shiga zuciyarsa su samu matsuguni a gidansa, Ubaidullah gajiya ya yi da hayaniyar, nan ya miƙe yana musu sallama ya ce zaije ya yi sallah yasha magani ya kwanta, Mama ta ce. "Abi'atu tashi ki taimaka masa, idan kuma ba za ki iya ba ki fada min" a kunyace Abi'atu ta miƙe ta kama Ubaidullah suka fice, itama Anty Ummu sallama ta yiwa su Mama akan cewa zata zo gobe da safe daga nan aka fara watsewa, har gidan ta yi tsit, Ubaidullah kuwa su na shiga part dinsu bedroom dinsa kai tsaye suka wuce, bedroom din a gyare tsaf dashi, zaunar da shi tayi a bakin gado kanta a sunkuye dan haka kawai ta ji wani masifaffar kunyarsa take ji, a hankali ta yi magana ta ce. "Ka fara watsa ruwa kafin kayi sallahn" ta juya zata shiga toilet ya riƙo ta da hannunsa mai lafiya din ya ce. "Ina da magana" sake yin ƙasa da kanta ta yi. "Hummm, to wannan dukar da kan da kike yi na miye ne?" shuru ta yi bata ba shi amsa ba illa wasa da yar yatsar hannunta da take yi, da ya ga bata da niyyar magana ne ya saketa, yana saketa ta shige toilet da sauri har tana tuntube, tana shiga ta lumshe idanunta tana murmushi, daga Allah sai ita tasan irin kalar murnan da take ciki wanda baki ba wai iya furtawa ba, ruwan ta haɗa masa ta fito ta zo gabansa tana kallonsa ta ji gabanta na faduwa, dan da alama jikinsa bai yi ƙwari ba danyen ciwo ne, yanzu ya zata yi, ko ta je ta kira Mama ne? Take tambayar zuciyarta, bata gama tunaninta ba ta ji yana cewa. "Kin gama haɗa ruwan ne?" ta gya ɗa masa kai alaman eh, ya ce. "To zo ki cire min kaya ki min wanka" zaro idanu waje ta yi tana kallonsa ta ce. "Iyeeeee!?" ya ce. "Eh! Nace ki zo ki ciremin kaya ki min wanka" turo baki ta yi tana dan kunkuni ya ce. "Magana kike yi?" "Eh magana nake yi, taya zan maka wanka?, kafin kazo wa ke maka wanka? ni gaskiya sai dai naje na kira Mama ta maka wanka, amma ni kam ba zan iya maka wanka ba, babba da kai" "To ai ba hakkin Mama bane jinyata ko kula dani ba, hakkin ki ne, a matsayinki ta Matata" da sauri ta kallesa ya kashe mata ido daya tare da mika hannunsa ta cire masa riga. "Ni fa da gaske nake yi bazan iya maka wanka ba" "Ohh!! Abi'ah na fa faɗa maki banyi sallah ba gashi yanzu har sha ɗaya saura ki hanzarta" juyawa ta yi zata fice ta ji yana ce mata. "Au dan bani da lafiya shine za ki gujeni ba za ki iya kula dani ba ko? Ashe duk kukan da kike min na dawo kinyi kewata ashe duk yaudara ce? Wai ni an turoni gida matata ta yi jinyata ta kula dani ashe ma ba zata iya min komai ba,da na sani ma da ban dawo ba, da na zauna a barrack masu so na su kula dani su yi jinyata har na warke" jiki a sanyaye ta juyo ta kallesa ta ga ya haɗe rai yana faman kokarin cire riga amma ya kasa sabida dayan hannunsa dake sagale a wuyarsa gabaki daya baya iya amfani da bangaren hannun, tausayinsa ne ya kamata ta dawo jiki a sanyaye ta sa hannu zata cire masa rigar ya tureta gami da cewa. "I don't needed just leave me alone, ki tafi abunki" sake kai hannu ta yi zata kama shi ya daga mata tsawa wanda ya yi sanadiyyar fashewa da kukan da ta yi ta kama kunnenta ta durƙusa a gabansa ta ce. "I'm sorry, bazan sake ba, sorry plssss" still bai kalleta ba, ya ci gaba da kokarin cire rigarsa, ya daga hannun kenan yana so ya cire dayan hannunsa ya bugi ƙirjinsa da ɗan karfi ya furta "wasssshhhhhh Allah" da sauri ta tazo ta kama hannun nasa a wannan karon bai tureta ba, kuma bai mata magana ba, cikin dauriya ta cire masa rigan ya rage vest a jikinsa, jikinta na kyarma ta cire masa vest din, a hankalin ya miƙe tsaye ya dan dafa bango, kallon kafarsa ta yi taga kafar a kumbure ta dago ta kallesa taga har yanzu fuskar nan tasa tamau take Ubaidullah ko hawainiya ba zata gwada masa canza kala ba, ta faɗa a zuciyarta sannan ta shiga cikin waswasin cire masa wando, da kyar ta yi jahadi ta cire masa belt ta zare kafin ta hau balle masa aninin wando gabanta na dukan tara tara, haka ta gama ta ja masa wandon kasa, sannan ya ɗaga kafarsa, ya rage da ga shi sai boxers, kama shi ta yi suka yi hanyar toilet bayan sun shiga ta ja ta tsaya ki ƙam tamƙar gunki dan bata san me zata yi masa ba kuma, a dan fusace ya ce "ba ki san yadda ake yiwa mutane wanka bane? Idan ba ki sani ba pls fita min anan ki ban waje malama" kin fita ta yi illa ƙura masa ido da tayi tana kallon fuskarsa dan ta kasa kallon gangar jikinsa, hawaye ne ke zuba a idonta, tsaki Ubaidullah yaja da dan karfi kafin ya juya baya yasa hannunsa daya zai zare boxers dinsa, da sauri ta riko hannunsa ta ce "dan Allah karka cire zan maka wankan amma karka cire, ance haramun ne kallon tsiraici pls" a mugun mamakince Ubaidullah yake kallonta amma tama raina masa wayau, wallahi badadin baya da lafiya ba da taji maza yau din nan ba sai gobe ba, amma haka ya kyaleta, nan ta hau murza masa soso da sabulu tana wankesa cikin daraba, sun bata lokaci dan sai sha biyu suka fito daga wanka, zama ya yi kan stool dinsa ta goge mi shi jiki ta shafa masa mai,ta saka mi shi jallabiya sannan ya tada sallah, ganin yadda yake sallah duk sai tausayinsa ya kara kamata, bayan ya idar ne ta tambaye shi ko yana bukatar wani abu zata tafi, cikin daga murya ya ce. "Ki tashi ki tafi mana, na hanaki ne ko na riƙeki ne?" jiki a sabule ta miƙe ta fita, Ubaidullah ya rintse ido gabansa na faduwa aransa ya ce. "Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!! Ba dai Abi'atu bata sona bane? Da na shiga uku ji Ubaidu, da ace tana so na ba zata min wannan tarban ba, wata biyar fa bamu tare na dawo kuma da ciwo amma ba zata nuna min kulawa ba?" ya sake rintse ido "dole ne na fahimci kina so na ko baki so na" wayarsa ya jawo ya duba yaga su miss calls har da na Zaidu da KB dasu yan barracks, Mama ya kira yana tunanin ma ko sunyi bacci, ringing biyu Mama ta daga ta ce. "Yaya Babba, ya dai kana bukatar wani abu ne?" "A'a My Momma, bana bukatar komai, amma dan Allah turo min Hafiza" Mama ta amsa da to, ta kira Hafiza tace mata Yayanta na kiranta, ita kuma Abi'atu tana fita dakinta taje ta watsa ruwa tana tunanin rashin kyautawar da bata yi ba, dan haka bayan ta fito wanka ta shirya ta fita kitchen tana haɗa masa simple food bai dan ruwa ruwa wanda zai ji dadin ci, wanda ba zai damesa ba, tana girkin ne taci alwashin zata kula da shi zata cire kunya tayi jinyarsa tunda mijinta ne, jikinta ne ya yi sanyi tuno ce mata da ya yi, ta tashi ki tafi ai bai hanata ko ya riƙeta ba, a ranta ta ce "laifina ne, zan ba shi hakuri" baya ta gama ne ta haɗa masa coffee mai kauri da madara tasa a karamin trey ta yi hanyar dakinsa da sallama ta turo kofar ta ga Hafiza na ba shi magani, nan jikinta ya sake sanyi ta ajiye tray din hannunta akan karamin center table din dake dakin tana cewa. "Hafiza ba kiyi bacci ba?" "Eh wallahi Anty da har zan kwanta Mama tace Yaya na nemana" jinjina kai tayi ba tare da ta sake magana ba, Hafiza tana gama ba shi maganin tayi musu sai da safe ta fice abunta, ko kallonta bai yi ba ya fara shirin gyara kwanciyarsa ta ce. "Ga shi fa nayi maka girki ne shap-shap" ya ce. "Am ok, bana jin cin abinci" shuru ta yi kafin ta miƙe a hankali ta dauki tray din ta fice ta koma kitchen ta dau supboil ta zuba masa kadan sauran kuma ta juye a rabo ta sa a freezer dakin ta dawo ta haura gadon nasa ta kwanta, Ubaidullah da ya rufe ido kamar mai bacci ya ji shigowarta bai gama mamakin me ya dawo da ita ma ya ji ta hayo gado ta rungumesa cikin sanyin murya ta hau basa hakuri tare da alkawarin ba zata sake ba, da kyar ta shawo kansa ya kalleta ta dinga rokonsa ya ci abinci, kafin ya tashi yaci ta taimaka masa ya yi brush suka kwanta. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da washe gari sun makara sallah dan bacci ya musu dadi, rabon da su yi bacci kamar haka sun manta, sai karfe goma suka yi sallahn asuba, bayan sun idar suka sake komawa bacci basu da farkawa ba sai karfe biyu, nan ma sai da Anty Ummu ta aiko Hafiza ta duba ko su na lafiya, tukunna suka tashi, ta taimaka masa ya yi wanka ta shirya shi, itama ta yi ta shirya sannan ta kama shi suka yi part din Mama, tun daga kofar parlour hayaniya ke tashi, su na shiga kuwa suka iske mutane, su Ummi ne dasu Umma, Inna, Zaidu, Anty Ummu, Yaya Safwan da Matarsa Shafa'atu, da sauran maƙotan arziƙi, su na shiga aka hau gaishe-gaishe, Inna ganin Ubaidullah ta ce. "Ohh Allah Ubaidu? Sannu ansha fama,an wuce da kyar ko? Yanzu sabida rashin imani haka suka yi maka? Dan ma kana da taurin rai inaji da yanzu zaman makoki muke yi, ina dalili da wannan aikin soja, kun bar mu cikin firgici da tashin hankali, gaskiya ni kam abun ya isheni" ta karasa maganar tana haɗe rai, Ubaidullah suka yi dariya shi da Zaidu, ba tare da sun bawa Inna amsa ba, aka ci gaba da hira su na bada labarin tashin hankalin da suke gani kafin Zaidu ya fara bada labarin yan ta'addan da aka kashe da sojojinsu da aka kashe duk da sunji a labarai amma ance waka a bakin me shi yafi dadi, yawancin mutanen da suke wajan fatan Alkhairi suka din ga yiwa sojojin nigeria, tare da adduar Allah ya daga nigeria, su Safwan ne suka miƙe su na yiwa jama'ar dake wajan sallama dan Shafa'atu bata jin dadi tana faman da laulayin karamin ciki, tun da Ubaidullah ya fahimci Shafa'atu na da ciki ya ji shi ma fa a duniya yana son ya ga Jininsa kwanan nan, inda ya kudirta a ransa kafin ya koma barracks sai ya mai da Abi'atunsa cikakkiyar mace, hira aka sha da Ubaidullah kamar ba shi ba, duk da azaban ciwon da yake ji a jikinsa, sai dare kafin jama'a aka watse. Haka aka din ga yi har na tsawon sati daya ana cika a gidan Mama tamkar wanda ake shagalin biki, jikin Ubaidullah Ma sha Allah yana samun sauki kasancewar Hajiya Abi'atu an zage dantse wajan kula da miji, abun da yasa ta kara mai da hankali sabida yan matan da ta ga su na shigowa masu baki kamar na jab'a wai su na zuwa gaishe da mijinta ko wacce da kalar fari da idon da take masa, shi yasa ta sake ƙaimi wajan ba shi kulawa, da haka har ya yi sati biyu, kuma yanzu alhamdulillah yana iya daga dayar hannun nasa, wajan ciwon ya fara kamewa, yau ma kamar kullum ta fito daga kitchen shi kuma yana zaune kasar carpet, zama ta yi kusa da shi hannunta dauke da cup, fara ba shi kunun ta yi a baki yana sha, ya dan ja kumatunta, ya ce. "Abi'ah?" kallonsa ta yi ba tare da ta amsa ba, ya kuma cewa. "Abi'ah, *KINA SO NA?*" gabanta ne ya faɗi, tabbas tana son shi mana, amma sai ta tsinci kanta da kasa ba shi amsa, shi ma ganin ta yi shuru bai sake ce mata komai ba, illa zullumin da zuciyarsa ta shiga, tashi ta yi sabida ya gama shan kunun, tana tashi ya bita da wani kallo wanda ya haifar masa da kasala da jan ido, hakika Abi'atu tana da sirhitaccen kyau, jinginuwa ya yi da kujera ya lumshe ido yana taro yadda take tafiya halittar jikinta yana motsawa, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai sani ba, sai da ta da fa shi ta ce. "Lafiya kuwa?" bude ido ya yi, ta ga yadda idonsa ya rine, ta zaro ido ta sake jefo masa tambaya. "Ya salam! Me ya same ka ne? Ko wani waje na maka ciwo ne?" bai bata amsa ba ya sake lumshe idonsa, kamar da, 5mins haka ya ce. " *ABI'ATU*, nayi miki tambaya amma ba ki bani amsa ba, ko me yasa?" sake yin kasa ta yi da kanta tana wasa da fingers dinta, ji ta yi ta furta masa tana son shi ya mata tsauri a baki, fizgota Ubaidullah ya yi ta zube a kirjinsa wanda sai da ta bugi ciwonsa da sauri ta ce. "Ciwon ka fa?" zata sa hannu da hannunsa marar lafiyar ya ture hannunta kamar zai yi kuka ya ce. "Ban damu da wannan ba kawai ni ki bani amsata, do u luv me?" Shuru ta yi tana dan wani nazari kafin ta gya ɗa masa kai alaman eh, sake matseta ya yi a jikinsa dan farin ciki,duk da dai ya so ta furta ne a baki ba wai da kai ba, amma ya san ta da kafiyar tsiya kuma sai ta furta da kanta, magana ya fara mata ya ce. "Yauwa, ni dama magana nake so muyi dake ko nace ina so ne muyi yar wata shawara,kinsan matarka itace abokiyar shawararka hakane?" "Eh, haka ne, ina jin ka to" "Yauwa, ina so ne Zaidu ya yi aure kafin mu koma bakin aiki, dan kin ga ance za a karrama mu ne, zan so ace yana da mata shi ma, dan haka ina so ayi aurensa da Hafiza kafin mu koma, amma ke ya kika gani?" gyara zama ta yi ta riƙe hab'a ta ce. "Maganarka abun dubawa ne, amma kai kana ganin auren nan zai yu kafin ku koma? Yanzu fa saura sati biyu ne kawai, har za ayi shiri kafin ku koma?" murmushi ya yi, ya ce. "Me zai hana, sati biyu ai da lokaci, da kudinmu fa a hannu, kuma kin ga auren gida ne ba na waje ba, daga yau zamu fara shiri in dai kin bada shawarar ayi, to ki koma gefe kiyi kallo" dariya ta sa ta ce. "Na bada goyon baya dari bisa dari, na bada shawarar ayi, amma mijina bai ji sauki ba fa?" "Wa ya gaya miki Mijinki bai ji sauki ba?" "Au yanzu kai a ganinka ka ji sauki?" "Ke ba ki yarda da naji sauki ba?" "Taya zan yarda?" tashi ya yi ya kamo hannunta ya ce. "Zo muje bedroom dina na gwada miki naji sauki, za ki sha mamakina yau" ba tare da ta fahimci abun da yake nufi ba ta hau binsa, har sunje bakin kofa zasu shiga ta gane me yake nufi da sauri ta fizge hannunta tana dariya ta sa gudu tayi hanyar bedroom dinta har tana riƙe kirji, shi ma dariya ya yi ya ce. "Ai da kin tsaya na nuna miki yar nema kawai" kaya ya shiga ya canza ya fito ya kwankwasa mata kofa "matsoraciya, fito muje wajan Mama" da sanɗa ta fito su na haɗa ido suka saki murmushi a tare, kafin suka jera izuwa part din Mama, a dakinta suka sameta, nan Ubaidullah ya mata bayanin shawarar da suka yanke, Mama ta yi na'am da hakan, sannan ta ce ya nemi Zaid din su yi magana, yanzu ita ma zata nemi su Umma su yi magana sai asan abun yi, amma yana ganin jikinsa ya warke ne da zai bullo da maganar biki, ya amsata da shi baya jin komai ciwon ne kawai da basu gama hadewa ba, Hafiza dake tsaye kofar Mama ta ji shigowarsu Yayanta tazo ta gaishesu taji su na maganar da ya daga mata hankali, da gudu ta koma dakinta ta sawa kofar key ta dauki pic dinsu ta kifa a kirjinta ta hau rare kuka. "Anya zan iya kuwa? Zan iya auren wanda ya so auren yar uwata? Kuma har kwanan gobe yake sonta? Anya nayiwa kaina adalci nayiwa yar uwata adalci? Anya idan na yarda na aure sa banci amanar yar uwata ba? Kai inaaa!!! Gaskiya bazan iya auren Yaya Zaidu ba, zanje na sanarwa su Mama ba zan auresa ba" duk maganar zuci take yi tana kuka, har wani ciwon kai ya sauka mata nan bacci mai nauyi ya yi gaba da ita, tare da mafarkin Na'ilah tana ce mata. "Sismieta!! Yaya Zaidu yana da kirki karki kuskura kice ba za ki auresa ba, idan kika yi haka na yarda baki sona, ki auresa za ki ji dadi zakiyi farin ciki, idan ba ki auresa ba kinci amanata, kuma bamu ni babu ke dan haka kin ga tafiyata!!!" a bacci Hafiza ke mikawa Na'ilah hannu tana "sismieta ki tadawo na amince zan auresa dan Allah karki tafi ki barni" Na'ilah tana b'acewa Hafiza ta farka gami da kwala wa Na'ilah kira da karfi wanda Mama da tazo wucewa zata shiga kitchen ta ji, da sauri ta zo ta hau bugawa Hafiza kofa dan ta tura ta jita a garƙame, da kyar Hafiza ta rarrafa tazo ta budewa Mama kofa, jikinta sai kyarma yake yi gashi duk ta jiƙe da zufa, kuka Hafiza ta saka ta kwanta a jikin Mama tana yi, rarrashinta Mama take yi ba tare da tayi magana ba, dan ta sani har abada Na'ilah ba zata taba fice musu arai ba, Mama ta ce. "Dama kina daki kina bacci har magriba? Ba dole ki din ga mafarkai ba, idan kinyi mafarkin yar uwarki ki daina mata ihu ki din ga mata addua, yanzu ki tashi ki watsa ruwa kiyi sallar magriba kafin a kira isha'i, anya ma kinyi azahar da la'asar?" ta girgiza alamun aa, "to ki tashi ki yi yanzu ko?" ta amsa da "to" Mama ta fice jikinta a sanyaye dan har an gama maganar bikin Hafiza da Zaid, inda za ayisa nan da kwana goma, ko da Hafiza ta watsa ruwa a daddafe ta yi sallah sabida mugun zazzabin da ya sauko mata, tana kife a wajan akayi isha'i, tana yi ta kwanta ta shige bargo, wajan takwas da rabi ta ji an banko mata kofa ana dariya, ji tayi har da guɗa, cikin zazzabi ta daga ta bude idonta ta kalli su Afnan da Manal da Afrah da Iman, kawayen su Afnan din ne, Afnan ce ta zauna a bakin gadon ta yaye bargon ta ji jikin Hafiza da zafi radauu ta ce. "Subhanallahi!! Ba ki da lafiya ne? Manal je ki kirawo Mama" da sauri Manal ta fita, Afrah ta ce. "Tooo daga saka aurenki shine har kin kwanta ciwo?" cikin zafin ciwo da tsananin mamaki Hafiza ta dago tana kallon Afrah ta ce. "Aure kuma Afrah? Auren wa?" "Keee! Kina nufin kice bakin an tsaida ranar aurenki yau ba? Nan da kwana goma? Yoo mu fa abun da ya kawo mu kenan mu fara shirye shiryen abun da zamu yi, dan aradun Allah zamu cashe, babu mai faɗa mana muji sai manya" suka sa dariya su na tafawa, yayinda Hafiza ta ji zazzabinta ya ƙaru, da haka Mama ta shigo ta dubata ta ce ko a kaita asibiti ne,amma firrr Hafiza ta ƙi, dan haka aka bata magani, su Afnan suka mata sallama da cewa zasu dawo gobe Allah ya kara sauki, suka fice abun su, su na fita Hafiza ta koma cikin bargo ta ci gaba da rera kukanta, abu goma da ashirin ne suka haɗe mata waje daya. @@@@ Da washe gari ma haka ta wuni a daki ko parlour ta kasa fitowa ta bangare uku kuwa shirin biki aka fara ba kama kafar yaro, Ubaidullah ya kira KB ya sanar da shi auren Zaidu dan haka ya yi kokari ya ga ya halacci auren, KB ya fadawa Ubaidullah ai idan bai zo auren Zaidu ba, bai cika amini ba, Abba shine ya zama wa su Ubaidullah Uba a komai, ana biki saura kwana biyar KB ya sauka a bauchin yakubu, tun ranar da aka sa bikin Hafiza bata sake ganin Zaidu ba, bata yarda sun hadu ba, shi ma bai nemeta ba, dan ba a natsuwar shi yake ba, bayan KB ya iso nan ya saka Mama dasu Umma a gaba shi ma wallahi ayi masa mata a bauchi, yanzu fa shi kadai ne kawai baya da mata, wallahi zasu saka shi a gaba ne, Inna ta ce. "Zo nan dan Albarka" dan kuwa jinin KB ya zo daya da Inna, kasancewar KB akwai barkwanci "ina dai mata kake so ko?" KB ya ce. "Eh Innata, gaskiya nima mata nake so" "Ma sha Allahu! Nayi maka mata, amma sai kayi hakuri da ita, dan ba jin magana take yi ba" dariya KB ya yi ya ce. "To Inna wacece?" sai da Inna ta murguda baki ta ce. "Na baka Ifritu" Zaidu dake zaune kamar ba ya wajan ya ce. "Inna ki daina batawa ƙanwata suna" "Yoo to ni ina ruwana da iskancin banza da wofi, jama'a ba zaku dinga saka sunan mutane ba sai na aljanu,kai kam ma naga take takenka, tun da aka saka lokacin aurenka naga kana min wani jiji da kai, ita dai Hafizatun bata fini a komai ba, kuma duk arziki duk tsiya nicevta farko ehe" yawancin yan uwa da ake zaune a wajan dariya ake yi, Zaid ya mike a hankali yabar wajan Inna ta ce "Kabeeru, ina dai ka karbi zabina ko?" "Ahh sosai ma Inna na karba hannun bibbiyu" da haka shi ma ya tashi. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau ta kama alhamis gobe ne kuma za a daura aure, yau ana ta shirin zuwa Family and friends, Amarya Hafiza tasha kyau dan kuwa Ummi ce ta dauko mai gyaran jiki ta gyarata a kwana goman nan, yau ma kuma Ummin ce ta dauko mai makeup ta fentawa Hafiza fuska tasa kayanta golden color, kawayenta su Afnan kuma sun saka maroon, sunyi kyau sosai su ma, Tun da aka fara hidimar bikin Hafiza Ubaidullah da Abi'atu basu samu zama ba, basu nan basu can, har aka gama shiryawa aka tafi, ana ta neman su Ubaidullah da Abi'atu ba a gansu ba, sai bayan da duk jama'a ana can wajan taro, har an dibi awa daya tukunna ka ji wani kiɗa na musamman na tashi, yayinda maroƙi ke wasa Ubaidullah da Abi'atu, jama'a an zuba ido ana jira aga wasu taurari ne haka ake koɗasu, kamar daga sama sai gasu sun shigo su na dauke ido cikin shiga ta alfarma, farar shadda ce bugaggiya fara sol da ita anyi mata aiki da bakin zare, Ubaidullah ya saka bakin hula da bakin takalmi baƙin agogo kirar gucci, Abi'atu kuma ta yafa bakin gyale bakin takalmi da jaka, sakarta dasu abun hannu da zobe duk bakake ta saka, wayyo jama'a zo ku ga maching iya maching, ihu aka sa ana basu hannu, basu zarce ko ina ba sai wajan ango da amarya, su na isa Zaidu ya mike tsaye suka rungumi juna da Ubaidullah, sannan Abi'atu ta rungume Hafiza wacce kanta ke kasa tun zuwansu wajan ta kasa hada ido da Zaidu kamar yadda shi ma bai kulata ba ko a mota, nan aka ci gaba da event, yayinda hankalin KB ya tashi ya ji shi ma aure kawai yake so, haka akayi taro lafiya aka watse lafiya, da washe gari bayan an sauko daga masallacin jummaa aka daura auren Zaidu da Hafiza in da a yau wasu daga cikin manyan sojoji sun halaccin daurin auren, bayan an daura ne aka wuce reception da yamma aka yi walima, da washe gari kuma aka yi Soldier Day inda jama'a aka yi shigan sojojin har da harba bindiga, taro fa tayi kyau sai dai fatan Allah ya bawa ango da amarya zaman lafiya, Allah ya mai da kowa gida lafiya, haka aka watse da washe gari kuma suka fara shirin komawa barracks dan yau saura kwana biyu su koma, kuma da matan su a can zasu zauna dasu, kamar Hafiza ita ma kam ta tafi kenan. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Da dare da sallama ya shigo bedroom dinta, tana tsaye a jikin madubi ta fito wanka daure da towel tana tsane ruwan jikinta da wani karamin towel din dake hannunta, tana ganinsa ta tsorata ta hau rurrufe wani bangare na jikinta,dariya ma ta ba shi, ya tsaya yana ƙyaƙyatawa, cikin tunzura ta ce. "Me ya kawo ka bedroom dina har kake min dariya? Kuma ko excuse babu?" ta murguda masa baki, takowa gabanta ya fara yi yana cewa. "Gani nayi na warke naji sauki, shiyasa nazo dan a ramawa kura aniyarta" "Kamar ya?" ta tambayesa tana ja da baya yana sake matsota. "Matsalata da yarinya rashin kunya ga uban tsoro kamar farar kura, idan za ki cire wannan tsoron gwanda ki cire dan soja kike aure" "To sai aka gaya maka tsoronka nake ji ne?" "Ahh dama ni ai bance kina tsorona ba" ya fizgota jikinsa da karfi, towel dinta ya tsince zai fadi ta riƙe towel din gam ,ihu ta kurma tana kankame jikinta " to ke Madam miye amfanin ihun bayan ba tsorona kike ji ba? Kwantar da hankalinki jarumar mata" ya hau shinshina wuyarta tare da fara sauke mata zafafan kisa-kisai, tun tana mutsu-mutsu har ta hakura ta sake masa jiki, tsayuwar gagararsu tayi, suka zube bisa gado, zafafan sakonni Ubaidullah yake aika mata dasu masu wuyar fassara, tun tana dan biye masa tazo ta ji abun nasa ya fara zarce tunaninta, hankalinta bai gama tashi ba, sai lokacin da taji ya ja towel dinta ya yi jifa da shi, ya haye saman kanta tukunna ta shiga sambaɗa ihu da iyakacin karfinta tana ambatar sunan Mama dasu Ummi, Ubaidullah ya yi nisa dan kuwa yau a shirye yake da ya kashe arnan sama, ban da sambatu marasa kan gado babu abun da yake mata, wanda ita bata fahimtar me yake fadi, san da zai shigeta ta saki razananniyar kara ta shaƙo shi tana kai masa duka, naushi yaƙushi, cizo, amma Oga Captain ba shi da wannan labarin, sai da ya ji ya samu natsuwa kafin ya sauka a kanta ya koma gefe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa wanda bai taba jin kamar shi ba, a hankali yasa hannu ya jawota ya ɗaurata a bisa faffaɗen kirjinsa yana shafa bayanta a hankalin alamun lallashi, kasa katabus Abi'atu tayi dan ji take yi gangar jikinta tamkar ba nata ba, bakinsa ya kai satin kunnenta ya fara mata magana cikin tsigar lallashi da dukar da kai tamkar ba shi ba. "Am! Am! Am so sorry my everlasting, and i'm very happy today, Abi'ah kedin ta musammance a gareni, bansan me zan faɗa miki ba, kawai na gode, na gode, na gode, Allah ya miki albarka, farin cikin da kika sakani a yau, Allah ya dauwamar dake har gaban abada" ya sake rungumeta tsam a jikinsa, a hankali ya miƙe ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya zo ya dauketa cak ya shige da ita, sannan ya sakata a ruwan, ji tayi wani zafi ya sake ratsata da dasheshshen muryarta ta furta " wassshhhh Allah na, Ummina ya kashe! Ya kasheni, wayyo ya kasheni" tana yarfe hannu, saura kiris ya rage dariya ya sub'ucewa Ubaidullah, amma ya yi saurin hadiyewa dan idonta ya kalla ya ga tana jin zafinsa sosai, tana mugun jin haushin abun da ya mata dan haka ya maida hankali wajan gasata, sosai ya gasata kuwa, daga karshe ya fita ya barta ta yi wankan tsarki, yaje ya gyara bedroom din ya canza bedsheet, sannan ya koma toilet din ya sameta zaune a bakin bath ta daura towel sai gyangyadi take yi, ga zazzabin da yake shirin rufeta, kallon tausayi ya bita dashi kamar zaiyi kuka ya zo ya dauketa ya mai da ita bedroom ya zaunar da ita ya dauki rigar da tayi niyyar sakawa Allah baiyi ba a lokacin, ya saka mata sannan ya gyara mata kwanciya shi ma ya kwanta ya rungumeta, sai da ya ji ta yi bacci kafin ya mike ya zo ya yi wanka yayi alwala ya yi sallah raka'a biyu ya hau rokon Allah ya basu zaman lafiya da matarsa Allah kuma ya kaɗe musu fitina, Allah kuma ya sa musu albarka a wannan raya sunnar da sukayi Allah ya azurta su da haihuwa, bayan ya gama adduoinsa ne ya tashi ya hau gadon ya kwanta ya jawota jikinsa ya sumbaceta kafin ya lumshe ido, nan bacci mai dadi ya kwashesa, da asuba shi ya fara tashi ya yi alwala ya tafi masallaci sai karfe shidda ya dawo, bayan ya dawo a hankali ya fara tashinta daga bacci, da kyar ta bude ido, murmushi ya mata ta galla masa harara, tashi ya yi ya sake haɗa mata ruwan zafi ya sake gasata kafin ta yi wanka ya daukota ta zo ta yi sallar asuban da ba tayi akan lokaci ba, bayan ta idar a wajan bacci ya dauketa, sai sha biyu ta farka ta ga abinci kala kala a dakin, dama bakar yunwa take ji, nan ta zo ta hau bubbudewa nan taci karo da wata gasheshshiyar kaza wanda taji yaji, gasu drinks kala kala, yawu ta hadiye ta sauko ta hau cin kazan nan ido rufe, tana ci har lumshe ido take yi, dan kazar tayi mata dadi, har ta kusan inciye ta ji muryarsa yana cewa. "Kazar da dadi ko? Ta yi dadi sosai? Kuma kina jin dadinsa?" harara ta galla masa ta ci gaba da ci dan ya mata dadi, murmushi ya yi ya ce "gaskiya kam kazar nan da dadi, kuma dama haka nake so kiji dadinsa, dan nima naci dadi jiya da daddare, dan haka idan ma bai isheki ba a shirye nake na kara zuwa na siyo wasu ranki shi dade, dan kuwa kazar amarcinki kike ci" tofar da wanda yake bakinta tayi ta zo zata mike a masifance amma me kasawa ta yi ta zauna tana matsar kwalla. " ahh yi hakuri, na tuba, yanzu dai zo kisha magani" ya fada yana zama kusa da ita, maganin ya bude ya bata, ba gardama ta karba dan tana bukata, sha ta yi sannan ta hau hauma alamun bacci, a hankali ta mike ta koma ta kwanta a gado ba jimawa bacci ya sake kwasheta, wunin ranar Abi'atu bata leka ko parlour ba, da an tambaya tana ina kuma Ubaidullah zai ce bata da lafiya, su Mama da Hafiza sun zo dubata tana bacci, dan Hafiza bata tare ba, bayan an gama hidimar biki a gida ta zauna tun da gobe zasu wuce Abuja in da zata zauna dindindin, shiyasa Umma tace a barta kawai tunda duka za a wuce kuma ita ba zata dawo bauchi ba. Yau da daddare sun gama shirinsu tsaf sai tafiya kawai ya rage musu. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Jirgin safe suka bi dukkansu, MAMA, UMMA, INNA, UMMI, ABBA, UBAIDULLAH, ZAIDU,HAFIZA, ABI'ATU, Safwan bazai samu damar zuwa ba sabida matarsa ba lafiya, KB kuma dama ana gama shagalin bikin Zaidu ya koma, karfe shaɗaya su na airport din abuja, yayinda sojoji birjik aka zo tarbansu, amadadin a wuce dasu 9ja barracks sai aka wuce dasu Abachan barracks, basu zarce ko ina ba sai babbar filin taro na abacha barracks, inda an ƙa wa ta wajan ta yadda bakin ba zai iya faduwa ba, hotunan sojojin da suka je yaƙi ne a wajan,har wa inda suka mutu tare da iyalansu, murna a wajansu Ubaidullah abun sai wanda ya gani, nan Major Usman ya rungumesu yana saka musu albarka, Major General ya umarcesu da suje su canza kaya zuwa kaki, haka kuwa akayi nan aka shiga gabatar da abun da ya tarasu, inda aka shiga jinjinawa jarumai musamman Ubaidullah, inda aka shiga yiwa wa inda suka rasa rayukansu addua tare da bawa iyalansu abubuwa, inda a karshe lieutenant colonel ya karbi jawabin da cewa za a fara kiran sunan jarumi na farko wanda shine zaƙaƙuri a wannan yaƙin wato Ubaidullah wanda za ayiwa karin girma a halin yanzu, dan haka ana bukatar ganin Captain Ubaidullah a fili, nan Ubaidullah ya fito cike da zarra da jarumta yana taku mai dauke hankalin maza da mata, nan ya bayyana a fili, yayinda General Of The Army ya miƙe ya bawa Ubaidullah hannu, sannan Major General tare da wasu manyan kasa masu fada aji da yan gwamnati suka mike, nan aka yiwa Ubaidullah karin girma daga Captain Ubaidullah kai tsaye ya koma *COLONEL UBAIDULLAH* nan jama'a aka hau ba shi hannu jikake rab rab, inda aka bukaci matar Ubaidullah ta fito, nan Abi'atu ta miƙe da kyar dan har yanzu bata iya tafiya yadda ya kamata, har tazo kan mumbari Major Usman ya bata wasu stars yace ta daurawa mijinta, nan kuwa ta daura mi shi tana murmushin farin ciki, su Mama murna har da hawaye, Zaidu kuma nan aka ba shi mukamin major inda ya koma *MAJOR ZAIDU* Hafiza ce ta saka masa tambarin girma a matsayinta ta matarsa, KB kuma a lokacin ya karbi matsayin *CAPTAIN* baya da mata kanwarsa ce tayi masa jagora kamar zaiyi kuka Ubaidullah sai dariya yake masa, sauran sojoji kuma suka samu lambar yabo da jinjina, taro ta yi kyau sai son barka inda aka watse lafiya, ranar murna ta hana wa in nan family bacci, kwanarsu Mama biyu kafin suka baro Abuja, ranar da zasu koma Hafiza tasha kuka, kamar ranta zai fita, dan ta kasa gane kan Zaidu kwata-kwata sosai Mama ta danneta kafin su tafi, Abi'atu ma komawa gida bai yuba dan Ubaidullah yace sai dai a biyota da kayanta. Wannan kenan. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau kusan watansu daya da dawowa barrack komai na tafiya dai-dai, inda KB ya samu Zaidu da Ubaidullah akan shi fa da gaske yake yi yana son Afnan, Dan Allah su ba shi ita, Zaidu yace indai Ubaidullah ya amince shi kam baya da matsala dan Ƙanwar Ubaidullah ne, Ubaidullah cikin farin ciki ya ce ya amince kuma zai gayawa Abba, abu kamar wasa magana ta fara girma inda aka tambayi Afnan tana son KB cikin kunya irinta hausa fulani ta amsa ta hanyar rufe fuska, Inna ta ce ja'irar yarinya tasan cewa na iya zabe, magana ta yi magana in da aka tsaida auren KB da Afnan wata hudu masu zuwa, yau kuma watansu uku kenan da dawowa, Ubaidullah da Abi'atu soyayya ake zubawa kamar ba za a mutu ba, kaffa kaffa suke yi da juna basu son b'acin ran juna, ta bangaren Hafiza kuwa zata iya kirga sau nawa suka hadu da Yaya Zaidu bayan dawowarsu garin nan, inda yau ta sakawa ranta zata jira ta ga shigowarsa dan akwai maganar da take son masa, tana son ci gaba da zuwa makarantarta ne ko hakan zai rage mata kewa, dan ba zata iya wannan rayuwa ba, ko ina sojoji, da misalin karfe goma ya shigo babbar parlourn nasa kwata-kwata baya jin dadin jikinsa bai ma lura da ita ba sai ji yayi tace masa "sannu da dawowa Yaya Zaidu" cikin san sanyar muryarta, juyowa ya yi ya kalleta ta sun kuyar da kanta kasa, gabansa ne ya fadi, dan kuwa yasan bai kyauta ba, kuma idan har aka fahimci baya bawa Hafiza kulawa tabbas ya ci amanar Mama da Amininsa Ubaidullah, ganin ta ƙi kallonsa kanta a kasa ne yasa ya kamo hannunta suka zauna dan ya fahimci akwai magana a bakinta. "Hafiza kina son wani abu ne?" shuru ta danyi tana rausaya kanta da idanunta wanda suka ciko da kwalla, dan ita har ga Allah bata yi farin cikin wannan hadin ba, a hankali ta fara magana ta ce. "Yaya Zaidu, nasan bai kamata ace ni matarka bace, dan nasan irin son da kake yiwa Yar Uwata, ni kawai inaso ne muyi rayuwa da kai kamar da, har kwanan gobe ni kanwarka ce ba matarka ba, idan nayi girki kadin ga ci pls, ina so kuma dan Allah na ci gaba da zuwa skull amma bana son na cikin barracks" duk cikin sanyin murya take maganar, sosai jikin Zaidu ya yi sanyi ya ce. "To wa ya gaya miki ke bana sonki? Kema ina sonki sosai" murmushi tayi tace. "Wannan maganar ta wuce Yaya Zaidu" ganin yadda tayi maganar yasa shi kara shan jinin jikinsa. "To shi kenan, gobe zansa master sergeant ya duba min skull mai kyau, are u happy now?" ta jinjina kai tana murmushi " na gode Yaya Zaidu, sai da safe" ta tashi da gudunta ta haura sama, da kallo Zaidu ya bita dashi "wai ma miye banbancin Na'ilah da Hafiza ne kam? Me yasa a yanzu bazan karkato da hankalina akan Hafiza ba? Anya hanyar da na dauka zata b'ille min kuwa? Amma kuma taya zan fara rayuwar aure da Hafiza? Tayi yarinya da yawa, duka duka sai yanzu Hafiza take 15 anya zata iya dauke min bukatuna kuwa? Wayyo Allah ni Zaid" tunani yake yi kala-kala da kyar ya tashi ya haura sama ya wuce bedroom dinsa, da washe gari ya bawa master sergeant umarnin binciko masa skull mai kyau, haka kuwa akayi inda ya zakulo masa wata makaranta ta yaran manya, a sati daya aka yiwa Hafiza komai ta fara zuwa skull sojoji ke kai su dawo da ita, Ubaidullah ya ji dadin hakan sosai, tun daga ranar kuma Zaid ya canza mata idan ya dawo daga office zasu zauna suyi hira su yi wasa da dariya, kuma ya ƙi yarda ya fara jin feelings akanta dan wai kar ya jawowa kansa bala'i, sosai amince ya shiga tsakanin Ubaidullah da Zeey da Abi'atu dan ba karamin shiri sukeyi ba, Zeey ma kam ta kusa aure zata yi aure a America ta hakura da Ubaidullah duk da ta so shi tsakaninta da Allah, Hanan kuwa ta ƙi aure har kwanan gobe Ubaidullah ne a ranta shi take so. ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Bikin KB ya matso, abun ba wuya a wajan mai rai, inda aka fara shagalin bikin a garin abuja, Abi'atu bata samu damar yin komai ba, dan kuwa laulayin ciki take yi Ubaidullah ko kasa baya bari ta sauko wai karta bawa yaronsa wahala, da haka har aka yi bikin KB da Afnan inda nan ma aka sha shagali, ita ma ta dawo barrack da zama tare da mijinta, rayuwa sai dai ace alhamdulillah, Shafa'atu ta haifi Ƴa mace, duk yadda Abi'atu taso zuwa amma firrr Ubaidullah ba kunya ya hanata, har aka yi suna sai dai ta ga su pics, in da yarinya taci sunan Ummi su na kiranta da Amal, haka rayuwa ta ci gaba da tafiya duniya tana gudu, inda cikin Abi'atu ya girma ya shiga watan haihuwa, Mama ta matsawa Ubaidullah akan ya dawo da Abi'atu gida ta haihu, amma Ubaidullah ya murzawa idonsa attargu yace babu inda Matarsa zata je, Mama kam abun Ubaidullah har mamaki yake bata, wata ranar jumma'a da dare Abi'atu ta haifo santalelen ɗanta mai kama da mahaifinsa sak dan babu inda Ɗan ya baro Ubaidullah, sai bayan ta haihu ne suka je asibiti inda aka gyara Uwa da Ɗanta, kafin kace me gabaki daya barrack ya ɗauka matar *COLONEL UBAIDULLAH* ta haihu, da yamma aka sallamota daga asibitin da yake a cikin barrack din, da kwana biyu Mama tazo da kanta ta tattari Abi'atu tayi da ita bauchi, ihu ne kawai Ubaidullah bai yiba, amma babu yadda ya iya, haka akayi shagalin suna inda yan uwa da abokan arziki aka halitta, inda yaro yaci sunan Babansu Ubaidullah, wato ABDULLAHI, amma za a dinga kiransa da ABRAR yaro ya yi goshi inda ya samu kyaututtuka daga waje daban daban, sai da Abi'atu ta yi arba'in kafin ta dawo wajan mijinta, tasha gyara kam sosai kamar ba ita bace ta haihun a ranar ta gurzu a wajan ogan nata har sai da ta gane cewa Allah daya ne, komai yana tafiya yadda ya kamata sai dai ace Alhamdulillah Ma sha Allah, sosai suke rainon Ɗansu Abrar cike da so da kauna, ga kulawa. TAMMAT BI HAMDULILLAHI. TO BE BEGINNING👉🏻 ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ Alhamdulillah bayan dogon zango da wanga book ya ɗauka yau na kawo karshen wannan littafi nawa da yardan Allah, abun da na fada daidai, Allah yasa mu amfana kuskurena kuma Allah ya yafe min. Ina miko sakon gaisuwa ga masoyana wanda suka bibiye wanda littafi nawa, alherin Allah ya kai muku har garin da ku ke, na gode sosai. Ku tare ni a ci gaban littafin nan dan ba ayi komai ba ma tukunna wato👇🏻. *GAWURTACCEN SOJA* ci gaban _COLONEL UBAIDULLAH_ ga masu bukatar ci gaba zasu same shi akan farashin #300 VIP KUMA #500, SANNAN KARKU MANTA AKWAI WANI KUMA MAI TAKEN SUNA *AHLAN* WANDA SHI MA ZAKU SAME SHI A FARASHIN #200 VIP #500 ga masu bukata sai su tuntubeni a lambata (08165550116) sai na jiku masoyana, na gode sosai Allah ya sadamu da alkhairi 🙌🏻 UMMU AHLAN TAKU CE🤙🏻