9/27/16, 7:56 PM - Messages you send to this chat and calls are now secured with end-to-end encryption. Tap for more info. 9/29/16, 2:11 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 1_A gaban mudubi take tana k'yali,ta shafa nan,ta shafa chan,ta mudubin kuma tana d'an k'allon ta cikin shi tana murmushi, ganin yadda mutuminta ya zuba mata ido ta ciki. Juyowa tayi,yai d'ai-d'ai akan gado yana k'allonta, d'uk rashin k'yau na abu,toh mud'in kana muradin shi mai k'yau ne a wajen ka. Babban mamakin shi yadda ya kasa ganin munin Matarshi a kullum, yakan shafe "seconds" dan gano ta inda "Prettyn"shi ta gaza, kai ya girgiza, dan shi baiga makusa ajikinta ba ko kad'an. D'uk a kullum dangin shi suna mishi gorin d'uk k'yawawan garin nan,amma ya rasa wacce zai jaju6o sai Fulera,ga ta "JUYA",ta bare suce ko dan haihuwa taci darajar so,,d'uk ta tare gaba,ta tare baya, ta hanashi ganin d'uk wani makusa tata a gare shi,balle yai tunanin gazawarta na zama "JUYA". Asalima shi in d'ai zai tozali da Fureran shi"Pretty" toh yakan manta komai. "Pillow" ya sake jawo wa,lokacin da ya g'yara k'wanciya yana cigaba da k'allonta, d'ai- d'ai da dak'ika d'aya baya fatan yaga "Pretty" ta barshi,yana matukar k'aunar ganinta kusa dashi. Bai aune ba ya ji ta hure mishi ido da bak'inta tana murmushin nan wanda ke sashi murmushi ko da bai shirya ba,, kamshin "lestrine" ya buge shi, had'i da kamshin alawarta ta kullum,"splash". Take ya sau ajiyar zuciya, kan ya k'allota. Hakika yana kara godiya ga Allah mad'aukakin sarki da ya bashi "Pretty" a matsayin "Matarshi" kuma "Sanyi ga Idanunshi". Tabbas yana daga cikin maza masu t'sant'sar sa'a a rayuwa na samun "mace ta gari'',wacce ganinta kad'ai, ya isa wanke maka bak'in cikin rayuwa,har yai hamdala da mahaliccin shi,dan ya mishi baiwa,irin wacce ba Kowanne namiji ke da ita ba, a ganin shi,dan ya hanashi "D'a" bazai zamu ya masa butulci ba. Murmushi ya sakar mata,kamar kullum ya fara yaba mata wankanta. "Kinyi k'yau sosai pretty, a kullum ranakun duniya kamar ana dad'a kawata min ke ne,kamar ki zauna nai ta k'allon ki kawai. "Ko zaki fasa zuwa sunan? Murmushin jin dad'i tai,gashi d'ai kullum irin kirarin nan tana shan su,amma baya hana taji dad'in jinsu. Zama tai, tare da ruko hannunshi ta kai baki tai"kissing" take k'wa ya sauke ajiyar zuciya,tare da d'aura d'ayan hannunshi kan nata.. Tsaf ta riga da ta gama samo abinta cikin ruwan sanyi, ta riga da ta gama sanin d'uk wani "week points" nashi akanta, mai lafazi mai k'yau ce ita da sanyin murya, takan ko'k'arin tauna zance,sannan ta ya6a mishi"gold" da "lu'u-lu'u kan ta bashi. Cikin salon ta da wata irin murya ta fara magana tana lumlumshe mishi ido da d'an lallashi. Ji yake mar rad'a take mishi a kullum. "Kar kaji kom "Nawan" ni taka ce ai,k'walliyar ma taka ce, zan rintse ta ga ganin kowa,sai d'ai in mata y'an uwa na, badan sanin mahimmancin sunan nan a gare ni ba,da zan ta zama,kai ta k'allo na,har sai kace na ishe ka.. Ta karasa tana fari da idonta, take k'wa ya sau ajiyar zuciya. Unguwa ko bai niyar barin prettyn shi ba,da kalam kawai zata sa ya firta "Toh". Kai ya girgiza kan ya tashi ya zira rigarshi. Ita kuma ta sa hijab da Nikaf dan rufe k'walliyar. Tafe suke a mota,suna ta faman firar duniya cikin nishadi,har ya faka a kofar gidan sunan,wanda matar K'aninshi take gare shi. Hannunshi na cikin nata,tambayarta yake sai yaushe zai zo d'aukan ta? Ganan wasu na shiga,wasu kuma na fita a gidan sunan,sai d'ai in sun fito,maimakon su tafi,sai suja su tsaya k'allon su prettyn. Tana shiga ta tsaya ta cire nikaf d'in, kan tai bangaren mai jego. Da sallama ta shiga d'akin fuska sake, fal cike da jama'a, kowa ya zuba mata ido, ta samu gefen gad'on ta d'an dosa na,tana kula da hararar da wasu ke sakar mata,"ina yinin ku.. Fuska mai jegon ta yamitsa,kan tace"sai yanzu? Dad'i Miji.. Murmushi tai,dan tasan da ta tofa yanzu za'a fad'a mata magana. Cigaba tai, "shidai cin tuwon kishiya ramako ne,ehee. Kai ta k'ada, lalle mutum. K'anwar mijin tace ta amshe,"ba Kowanne tuwan bane na ramako..kar ma kisa a ka,a yadda tai shirim d'in nan ne zaki sa rai? Baki ta ta6e,kan tace suna ga wata wai "JUYA" tashi tai "parlour'' tana hararar prettyn,wacce ke mata murmushi. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:12 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 3_Asalin su y'an Kaduna ne,a karamar hukumar Zaria,Baban ta Muhammad "mechanical engineer ne,Matar shi d'aya,Mama Dije,da yaran su takwas, tun samun aikin shi ya dawo cikin garin Kaduna da zama da iyalen shi,a lokacin yaran biyu ne rak!, Suleiman shine babban d'anshi,sun dan jima kan su samu Aisha,sai Furera,Maryam, Hassan da Husaini da k'annen su. Tun su Furera suna yara Abban su ya shiga "missed call" sai ya zamo baiya aikin Gomnati sai makanikanci, rumfa ya bud'e dan wannan harkar, ko dan burin shi na sai yaran shi sunyi karatu, da taimakon Allah,da taimakon dan uwanshi dake Zaria ya kafu,, sosai ya iya g'yara, dashi yake samu ya biya ma yaranshi karatu. Tun tashin yaran yai musu sa6on dad'i, sai kuma akazo ya rasa aiki,d'uk da haka yana iya kok'arin shi yaga ya wadata yaran shi da d'uk wani abin jin dad'i, ta yarda bama zasuyi kukan baida shi ba,d'uk an neme shi daga baya yace ya d'aina bautawa Government, g'wada yaci da gumin shi. Mama Dijee itama takan yi su su6o da sauran kayan sanyi. Sosai suna k'wata ma yaran su tarbiya,kuma sun taso ba laifi, d'uk dunsu ba masu son k'warafniya bane,in banda d'aya da ta fita zakka cikin su,wato "Fure". Tun tashin Fure sam bata d'aukar wargi,ita sha yanzu ce,magani yanzu,sam bata barin ta k'wana. Gidan haya na biyu kenan suna yi,yanzu su biyu ne aciki,sai d'ai shi baban su sai ya kewaye bangaren su da langa-langa, d'uk ba jin dad'in zaman suke,d'an fa d'ayar matar sam batta kirki, d'uk hakurin Mama Dijee sai da ta kaita bango,a kan yaranta t'saf sai taci damara. Ga yara zagi a bak'insu kamar ruwa. " Fure ki wuce mu tafi yanzun nan kan na had'a ki da Umma. Kara chakumar wuyan y'ar gidan matar tai, "wallahi bazan cikata ba,mey yasa zata zagi uwata? Sa'ar ta ce? Jin kok'awar fad'an ne ya fito da Larai daga daka, tuni Aisha tai gefe,dan tasan ba abinda zai hana ta rufar musu a ka. Zaune ta samu Furera akan y'ar tana nad'a kamar Allah ya aiko ta, sarai Umma naji, amma tai kamar bataji ba, Larai batai wata-wata ba ta rufar wa Fure,tana dukanta ita kuma tana narkar y'arta, wanda a zahiri ta fita girma da komai,amma ihu take a taimake ta a hannun Fure. Ganin zatai wa y'arta illah yasa ta bar dukan Furen ta hau ko'k'arin fincike ta akan y'ar. " uwata Sa'ar ta ne,ai dama na fad'a mata wataran sai na fasa mata baki agidan nan, shegu dangin maguzawa... Da gudu ta zuba, ganin larai taiwo kanta tai zaure, g'walo tai ma yarinyar, da tana kuka tana kuwa k'wararowa iyayen Fure wasu mugan zagi ba ko dad'in ji, tana daga zauren tace "oho d'ai, ko banza na koya miki hankali, kuma zamu had'u anjima. Umma dake d'aki suna jin ruwan ashar din da Larai da y'arta suke watso musu.. tai shiru ita da Aisha da sauran k'annen ta. D'a ne ka haife shi baka haifi halinshi ba,ko ta hana Fure kula Larai da yaranta sam bata jurewa,barin in suka zage ta,amma abin na yau yafi k'arfin ta,dan d'uk tsiya sai d'ai suyi chachar baki,amma yau Fure harda dam6e. Tana zaure har taga shigar Larai da y'arta d'aki kan ta arto da gudu tai kewansu. Harara Umman ta sakar mata, uffan bata ce ba tai shiru, amma dole yau asan nayi, dan sam zaman gidan nan ba nasu bane, dan tsaf Larai zata gur6ata musu tarbiyar yara, musamman Fure, zama da Larai bak'inta yai masifar kara bud'e wa,ga fad'ar magana kamar y'ar makafi. Da dare kuwa Abban su yana dawo wa ta kora mishi bayani, kamar kullum ci kanki bai cewa Fure ba,wanda ita Umman ta zata zai ja mata k'unne. Tun daga ranar jaraba ba kama hannun yaro tsakanin ya'yan Larai da Fure, sam bata ko shakkar girman su, haka zasu kamata su mata taran dangi har uwar amma uffan Umma bazata ce ba, kuma inda zasu k'wana dukanta sai ta rama kuma ba ko hawaye, tana zuwa d'aki Umma ta kara mata wani. Ba shiri Abba yasai fili ya kuma ta dasu a gidan Larai kan suka samu lafiya. Gidan su kad'ai ne a ciki,mai d'aki biyu da baranda, yanzu burin Abban su kawai ya tara kud'in gini, dan k'warai ya gaji da bin haya,in yaso ko na kasa ya gina musu. K'wance tashi su Fure har an shiga secondary, day d'uk yaran suke,yayinda Yayan su Suleiman ya kammala secondary sai jami'a. Sosai y'an gidan suna da K'wak'walwa, barin Fure uwar rawar kai, Kasuwa kam ta bunkasa wa Abban su, dan har ya bud'e wa Ya Suleiman shima wajen g'yaran kan ya samu g'urbi a A.B.U Zaria. Anyi hutu suka tarkata sukai Zaria ziyara, anan ta samo yaran kawunsu sa'aninta suma sun dawo a Queen Amina, yadda suke bata labarin makarantar da "boarding school" kawai tai sha'awar zuwa,, Uncle d'in nasu achan yake aiki d'ayan, tuni Fure ta tada bal'li ita sai Boarding. Da taimakon Kawun ta biyu da Abban su ta samu g'urbi a makarantar Queen Amina College. Haka Abba yake fafutukar nema kodan biyan makarantun yaran. Fure a Boarding, k'warai rayuwar ta mata,d'uk da tana k'ewar gida wataran, nan ido ya kara bud'ewa, daga "Furera" ta koma "Pretty". A d'uk dabi'ar ta bata nuna cewa ita y'ar wani ce,asalima ita irin k'aryar nan ta y'an boarding sam bata d'ad'a ta da kasa, dan sosai tana alfari da Abbanta, kuma bata 6oye mazaunin ta d'uk fafar ta. K'wance tashi ba wuya a gun Allah,ga nan su Fure har an shiga SS1, Cikakkiya ce Pretty,ta bun kasa,d'an ba ramammiya bace ita sam, t'sirinta da tsabar iyayinta su ke boye muninta, bata sahun farare, sai d'ai sahun bak'ak'e, sai d'ai a cikin bak'ak'en ma iya kiranta wankan tarwada, a fuska kam ba wata k'yak'yawa ta azo mu gani bace, d'an karamin k'yau gare ta, sai d'ai a jiki a dire take. Babban sirrin k'yaunta" gashi" dan ko a fuska "eye lashes" d'inta da girar ta sunfi d'aukar ta tazamo mai k'yau. Yadda k'wa take far-fara su in tana zance, kai kace da ga'iya take,dan tamkar tai "fixing". By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 10 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 4_A jiki "Full option" ce kam,abun da a yanzun tafi jin haushi a kira ta dashi kuwa shine "Fure". Yana d'aya daga dalilin da yasa a school suka k'ak'aba mata" Pretty " dan kam ita k'yau ce da wanka. D'uk yanzu y'an unguwa yawanci da Pretty suke kiranta, a gida ne kawai sunan ya gagara k'arbuwa gun su Umma,dama shi Abba bai san da sunan ba. Ak'wai lokacin da Abban ta da ya Suleiman suka je musu Visiting, shaf sai suka manto visiting card d'in a gida. Da alfarma aka kira wata mate d'in su Fureran kan su fad'a mata sunan ta kira ta da y'anuwanta. Sunan ta tsaya tana maimaita wa, halamar tama rasa mey shi, sai da yasa sunan uba da unguwa kan tace"au Pretty ce, bari na kira ta,, da d'an gudunta ta tafi tun daga wajen ta fara k'wala mata kira, Abba ya girgiza kai, kan ya k'alli yayan nasu,"yanzu wai kaji Fure har sunan k'arya ya shafe na gaskiya? Murmushi yai,kan yace"Abba makarantar kenan,sai a hankali. Tana hango su Abban da gudunta ta nufo su, har ta baro sauran a baya,"da gaske k'wa kaga ita d'in ce suleimanu, dariya yai, lokacin da ta karaso tak'wa tukuikuye Abban,kan ta koma kan Yayan nasu. Bayan sun gaisa yace, "Yanzu Fure ke ce kika koma pretty saboda Allah? Da sauri ta matso tana marairaita mawa baban kan ya d'aina cewa Fure,sai wai school ta d'auka. Yace" ungo naki, shi dai ya Suleiman dariya kawai yake musu. "yasu Umma? Yaya ya makaranta? Yai murmushi, "suna gaida ku, " yaya ka kusa gamawa ai? Kai ya k'ada mata,''InshaAll lah, murna take kan yayan ta shima zai zama engineer. Sunje hutu sun dawo,wanda a shine suka shiga ss2,anyi sabin coppers, yayin da iskancin su pretty ya motsa. Sun bala'in raina wa coppers hankali, d'an su kam mayun mata ne. Ranar d'aya ya shigo ajin,Hausa yake d'auka, sai fafa yake musu shi nan a dole yana gaban y'an mata. Bayan ya gama darasi ya k'allo su, dariya kawai suke mishi, amma shi ko a jikin shi, sai ma wage musu baki da yake. "If you hv questions queshh" or additional information... Haba wa,mai su Pretty zasuyi inba dariya ba. Har aka buga "next period" ya bar ajin ba wanda ya kula shi sai shakiyancin su suke. Yana fita su pretty ita da y'ar desk d'inta suka fito k'waik'wayar shi,, ta d'au alli"if u hv questions quashhhhh... Or additional information. Yadda kasan shine a gaban allon. Fad'i suke in banda malam,mey ya kai turanci kai da kake koyar da hausa? Tuni sai suka fara tariyo na d'ayan coppern da yai musu mathematics, dariya Fure take harda rike ciki,d'an yin irin in'inar da d'an NYSCn yake. Tsitt! Ka ke jin ajin sai dariyar Fure da Adama ke tashi. Zungurar ta Adama ta fara,lokacin da tai ar'ba da abinda yasa class y'in shiru. Hard'e yake da hannu a kirji,rike da "text book" an rubuta"chemistry" a jiki,sanye yake da fara sol d'in rigar NYSC da siririn farin glass a fuska,fuskar nan sam ba annuri,, tunda suke ko a malamai basa jin da wanda ya ta6a musu k'warjinin wannan, balle a wanda suka raina. Ajin ya shigo,har lokacin idon shi nakan Fure da ta kame a gun baki sake, tuni ita Adama tasan nayi. A gabanta ya tsaya tamkar wani soja rai a had'e. Takarda Adama ta nannad'e,sai ta seta Furen ta hulla mata, a tsorace tabar K'allonshi tai gun zamanta. A t'sanake ya karewa ajin k'allo, tabbas nan Garba ya shigo dazun,dan daga iskancin su yasan sune, yana jin lokacin da malamin Hausa yake sanar da sauran iskancin da suka masa. Ya kai a k'alla minti biyar yana karantar ajin su Furen,yana k'allo takadiran cikin d'aya na zungurar d'aya. Kai ya k'ada, kan ya ju ya kan allo ya fara rubutu. "Chemistry" Shine abinda ya rubuta. Fure ta ta6e baki. Juyowa yai,kan ya bud'e baki cikin murya mai sanyi. Cikin turanci yace sunan shi "Ahmad Abba Ahmad", shi zai na d'aukan su Chemistry daga yau. Bayani yake musu,wanda tsit ka ke ji kamar anyi ruwa an d'auke, dan d'uk iskancin su nasan kure Malami a turanci yau sun gamu da bokan turai. Class mastern su har zuwa yai leken ajin dan jin yau shirun su da yai yawa, a tunanin shi discipline master ne a ajin,da mamakin shi sai ya ga Ahmad. Kai ya k'ada, lalle wai gaba da gaban ta,Aljani ya taka wuta. Ko da aka tashi gulmar Uncle Ahmad suke ta yi,daga suce mai girman kai,sai su ce ya had'u amma. Suna hanyar tafiya "hostel" suna ta shakiyancin su, kasancewar ss3 suna "practical'' a "hall'' yau su suke cin karan su ba babbaka. Ko "lunch" basu tsaya k'ar6a ba suka taho. A bak'in "gate" suka tsaya, ganin Baba mai gadi na d'akin shi bai kuma gate d'in a datse da "key", maimakon suce ya bud'e musu su shiga,kawai sai suka hau mishi wakar su ta kullum,wanda har ya riga ya gane su Fure. " Baba a bud'e "gate" ko mu taru mu 6alla "gate"... Shima kamar mai wakar daga d'akin nashi ya basu amsa, "Ku taru ku 6alla,tunda gate d'in na uban ku ne... Dariya su Fure suka sa, lalle ashe mutumin su ne " on duty". Kawai sai suka bashi amsa dan kawai suyi ta deban shi,, "K'warai na uban mu ne,tunda Gomnati ta siya.. Da gora ya fito daga d'akin yana bam-bami," yau zan kawo karshen iskancin nan naku,, "au Fure? Nasan kece gandi lida, yau za kuyi bayani.. Dariya suka sa mishi," Baba namu,mukwa na Allah, muga Annabi... Da gudu suka zuba, ganin ya bud'e gate d'in yai Kansu da gora,, wuuu sukai "gate" d'in kamar zasu 6alla suna mishi dariya,tun daga nan aka fara yin d'ai-d'ai da kaya, daga su sai underwear suka isa hostel. Washegari kuwa da safe sai ga kira daga principal tana kiran Fure da y'an Eysla d'ukansu.. Principal kam tasu ce,ba ko shakka suka nufi office, sun san bazai wuce fad'a akan surutun aji ba. Masinja ne yai kiran Furen ita kad'ai zuwa ciki, yana zaune su biyu a kujerar da ke gaban principal d'in, da ladabi ta gaida principal, kan a ciki ta gaida su,d'ayan ne kawai ya amsa,yayin da d'ayan ya d'auke kai. Dagowa principal d'in tai,ganin Fure ce yasa ta k'ada kai,"Furera" kai sunkuye ya ta k'warai tace"Yes Mom, kai ta k'ada, kan tai murmushi, " Trouble marker" kenan,ai tunda naji SS2 ne nasan sunan ki sai ya fito ciki. "Wai zaku 6allawa Baba gate koh? Kai ta kara kasa dashi, "sorry Ma, kai ta k'ada, " ai kinfi kowa rashin ji, sannan kinfi kowa tsoro. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:13 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 5_Tuni tai narai-narai da ido kamar zatai kuka tana k'allon PCn, "Momy kiyi hakuri, kai momyn ta k'ada, " last warning " kar na sake jin haka daga gare ki "Fure" kai ta k'ada, kan tai godiya tai waje tana murnar ba ko "punishment". PC ta k'allo su Ahmad, wanda suke k'allon yadda momyn ta bi Fure da k'allo tana murmushi, " yaran sun matukar shiga raina, tun jss1 d'insu aka kawo ni, tun a sannan nasan dasu,fitina, tsokana,ilimi d'uk yan su ne. Kai su Ahmad suka k'ada, tare da mamakin saukin kan principal d'in. An dawo a break yake da su, d'ane wasu suke akan desk a zaune, wasu sun had'a group ana shewa, chan ya hango Fure a tsakiya tana ta zuba k'wainane, kofa ya buga,da sauri kowa ya nemi waje ya zauna. Kamar jiya,yau ma ya kare musu k'allo, magana principal ya fara tan tama na anya yaran suna da kok'ari? Akan Fure ya dire idon shi wace ke fito da irin "Text book" d'in shi a jaka. Ciki ya shiga,kan zasu gaida shi ya zaunar su. Daga inda ya tsaya jiya ya tashi,suna tsaka da karatu ya k'allo desk d'in su Fure, ture-ture suke kamar wasu yara kanana. Alli ya saita su dashi ya hulla musu, da hannu yace su mike, kan ya tambayi sunan su, "Fure" ya kira ta, da sauri ta daga tana k'allon Y'an aji da har sun fara kunshe dariyar su, tuni ta kicin- kicin da fuska kamar zatai kuka. Gaban allo yace ta fito. Hannu ya hard'e tare da zuba mata ido cikin glass,ita tuni hankalinta yai kan y'an ajin, bata zata ba ta tsinci tambayar shi gare ta. "can you name the first 20 elements of the periodic table pls?" Tsayuwa ta g'yara,dan yasan dak'yar in ma ta sansu bare ta rike su.. Sai d'ai kan ya karasa zancen zuci ya tsinci muryar ta cikin sauri-sauri tana jero su kamar ma ita wasan yara ta d'au ka. "Hydrogen,Helium,Lithium, Beryllium... Ba ko shan numfashi ta dire masa su tana du6en shi. Kai ya g'yada, kan ya sake jeho mata wata tambayar,kiris yake jira ya sata kneeling. " electronic configuration of firs.... Da sauri ta katse shi tare da karanto mishi, "Boron,carbon, Nitrogen... Suma ta dire cikin sauri ba tare da ta bari ya gama maganar ba,dariya y'an ajin suka fara,tun itama tana dake wa har suka sa ta yi, ajin ya k'alla, sai sukai tsit,itama ta kunshe tata, bak'in kofa ya nuna mata da hannu, da mamaki take k'allon kofar,wai tai "kneel down" ta daga hannu ta rufe ido, tuni kuma ido sai ya raina fata, dan taki jinin punishments,ga ya had'e rai ba damar bada hakuri. Daga yin minti 5 ta fara raki, shikam dalibai ya cigaba da koyarwa,jefi-jefi yana d'an k'allo ta. Hawaye ta fara,da gefen hannu take gogewa,gaba d'aya hannunta ya fara sage wa, sai motsa K'afa take halamun ta gaji, ya juyo da zummar kara k'allonta yaga tana kuka, sai ya d'auke kai, y'an aji tuni aka shiga taitayi,ganin Fure na kuka,dan sosai sunsan abin da zai sa Pretty kuka babba ne. Ba'a fi minti uku ba ya kara k'allo ta, ta cikin glass d'in ya d'an rufe ido,bai so ta kaishi bango ba,kawai ya ki jinin rawar kan nan na Fure ne. A hankali ya kira sunanta ta bud'e ido, tuni har sunyi ja, d'aurewa yai yace ta tashi taje ta zauna. A shag'wa6e ta tashi tana d'an dingisawa, koh zama bata gama ba aka k'ada, ya tattare kayan shi tare da d'an k'allon yadda ta d'aura kanta akan desk hawaye na zubowa. Da sauri ya d'auke kai dan kar su gane yai waje, ai kamar jira suke sukai kan Pretty suna lallashi. Har akazo k'wanciya in ta tuno sai tai k'wafa, ita sam bata ga mey tai ba da har ya sa ta kneeling. Shima d'ai Uncle Ahmad d'in yana a d'akinsu dake cikin "staff quarters" d'in, a ganin shi raini ne zaisa Fure yin hakan,sai d'ai shi mai tausayi ne, tuno da yadda take hawaye dazun d'uk sai ya ji ba dad'i. Ihun y'an makaranta ne da ke "hostel" yasa shi tashi da sauran y'an d'akin, tun zuwan shi wannan ne na farko da akai ihun gardi,waje suka fitu,ganin wasu malamai nayin hanyar hostel d'in yasa suka bisu,ba kad'an ba yara ke gudu,wasu na fad'uwa, d'uk anjijji ciwo wasu na kuka,kawai Fure ce ta fad'o mishi,sai d'ai bai isa fidda ta cikin yawan daliban ba. Washegari da safe a "area classis" sai zancen jiyan ake, yana jin lokacin da aka ce dayawa sunji ciwo,wasu na "dispensary ",kawai sai ya samu kanshi da leka ajin su Fure,suma d'ai maganar jiyan suke tayi,suna ganin shi suka nutsu tare da g'yara zama. Juyawa yai,dan ganin ba Fure a ajin,sai yai hanyar dispensaryn. D'ang'walolo,tana k'wance sai wash! take tana y'arfe hannu ana mata "dressing" d'in kafarta. Murmushi yai, ganin dan ciwan amma take wannan wash! d'in. Yana tsaye yaga an zaro allura,Furen ya k'alla, ai kam ido ta zaro,"Allurar mey za'a min? Tab! Baya ta ja kan ta mike tsaye, "nifa na warke malam, na d'aina ma zazzabin, mai allurar yace" kiyi hakuri kawai ki ju ya, dan fa sai na miki. Kawai da mamakin shi yaga ta 6are baki tana kuka,kuma ba koh hawaye, dayar y'ar "mate'' d'insu tace"haba Pretty,allurar? A masife ta k'allo ta," eh din ina ruwan ki. Murmushi yai,kan ya k'ada kai ya shiga cikin "dispensaryn". By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:15 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 6_Tana ganin shi ta juyar da kai tare da d'aina kukan, ya koma gefen da take, bata nufa ba taji yace "sannu Furera.. Da sauri ta dago,sam batai tsammanin bahaushe ne ba, yafi mata kama da y'an chan kudu,fari ne,dan sosai ya fita haske,mai sage siriri,da tsayin shi,dan ya kere ta da kusan kai uku,da gani mai hakuri ne, sai d'ai bai d'aukan raini. Sosai yake da k'warjini, musamman agun y'an mata. A hankali cikin sigar lallashi yace tai hakuri a mata,kai ya k'auda, sai ta samu kanta da d'an daga wa, gefen nashi yake take k'allo, halamar bai son ganin abin,ido ta lumshe,lokacin da taji tsinin allurar, "shikenan fa an gama, ido ta bud'e, tare da sauke rigarta tana k'allon Uncle Ahmad da har yanzu yaki k'allon ta, magani aka zuba mata,dispensarern yace gobe ta dawo, juyowa yai,lokacin da take k'ar6a. Tare suka fito,tana d'an dingisa K'afa, shi kuma rike da maganin da k'walin lemon da y'an k'wanarsu suka kawo mata, mamakin ta yadda ya zamu mai saukin kai,har aji ya rakata, a bak'in kofa ya tsaya,tare da kiran Adama tazo ta k'ar6i kayan, sudai y'an aji da ido suke binshi,sam ba wasa a fuskar shi bare su tanka,tana zama ta k'allo shi, hannu ya dago mata yana murmushi, itama sai ta murmusa,baki sake suke k'allon su har ya juya ya fita. Da sauri y'an class suka zo jin gulma,wasu na Sonta yake Allah,harara ta basu, "wani irin so? Ku fa baku kai. Ina,sukam y'an ajin har aka tashi suna pretty ta uncle Ahmad. Tun tana masifa har ta fara binsu da ido. Sai d'ai fa ana zuwa bacci ta kasa sukuni, dan har yamma sai da yazo duba ta,harda drinks d'inshi mai sanyi da cake. Takan yawaita murmushi in ta tuno shi,wanda ita kam a nata wayon bata san meye ba.m Sai ya zamo Uncle Ahmad sun d'inke da Fure sosai,d'uk da bai ce yana son nata ba,asalima in yana " teaching'' yi yake kamar bai san kowa ba a ajin,,dama kuma itace "class captain" ta y'an iska,d'an ita d'uk randa akace ai ''noise maker" ranar take cewa kowa yai surutu son rai,randa ba'a ce ai ba kuma zata chunkune kaji aji tsit,tari kai sunan ka ya shiga. "Records" na exams nasu suke su da uncle Ahmad, suna karanto mishi ita da Adama,ga nan wata na musu firfita,har Adama ta gama nata pretty ta fara. Yadda take fidda lafazin cikin murya mai dad'in sauraro kai kace tun daga "primary" ta samu "good foundation'', sosai yake jin muryar ta har tsakar kanshi, yakan rasa mey yake ji a game da " pretty" in dai zai tsinkayi muryar ta. Jim tai,yana jiran ta fad'i "next" tai murmushi, "Furera muh'd, murmushi yai kan ta fad'a mishi mark itama tana murmushin, Adama ta zunguri mai firfita suna gulmar su. A zahiri kowa na son kowa,amma sun kasa gano hakan,shi d'ai uncle yasan yana yawan tunanin Pretty, amma sam bai kawo so ba. K'wance tashi har sun kusa gama service d'in su,a dalilin uncle Ahmad Fure ta nutsu sosai,har d'aurin karatun addini yake musu ita da K'awayenta,da nusar su yanzu sun girma su daina kaza da kaza,,sosai kamar K'anwar shi haka yake ji da ita,randa yai k'wanan waje in bata ganshi ba d'uk sai taji kamar tana jin zazzabi, d'uk a tunanin ta ba d'an KD bane. Ana gobe zasu tafi lokacin su Fure na ss3,kuma " Head girl" Duk tabi tai laushi, a kofar aji suke a dandamalin a zaune, kowa ya zuba musu na mujiya,k'allonta yake ba ko kiftawa, ita kam kai d'uke kamar ta sau kuka, a dan karatun littafin soyayyarta ta zata sonta uncle d'in yake,ashe ba haka bane,gashi har yau zai tafi bai furta mata ba. In d'ai batai k'arya ba ita kan tasan ta rufta a son shi,murmushi yake,"Furera" kai ta dago,da dan murmushi a fuskar ta,''ki kula sosai,kinga kun fara "practical", kiyi karatu ko d'an ki fita da result mai k'yau. Kai ta k'ada mishi, wayan shi ne ya k'ada kirar" Blackberry" da murmushi ya daga kan ya ambaci sunan "Mama" sai ya d'an tashi ya matsa, sai da ya gama ya dawo fuskarshi d'auke da murmushi, "Mama na gaida Furera, murmushi tai kan ta k'ada kai," ina amsawa. Har address d'in Fure ya k'ar6a, da alkawarin zai kawo mata ziyara har gida in sun gama makaranta. K'warai ta d'aure ganin batai kuka a gaban shi ba, sai d'ai yana tafiya ta k'ar6i "pass" tai ''Hostel". Kuka take wanda da biyu,itama d'ai ta zurma d yawa, amma irin su Uncle Ahmad tasan ba ajin su bane,wai k'warya tabi k'warya, yadda yake da aji da k'yau tasan yafi k'arfin ta, zuciya kawai ke yaudarar ta. Tun tana damuwa da son Uncle Ahmad har ta jingine shi ta hau karatun ta. In har da rabon zasu gana kila ta ganshi. Sun gama "exams" kowa ya tafi gida da k'ewar juna da dunbin k'yaututtukan ta,sa6anin Adama da suke kusan unguwa d'aya da Pretty. K'allon Fure Umman su take,d'uk ta rame kibar nan ta dawo y'ar chas da ita,"har yau ina mamakin ramar nan taki Furera,ko A'i batai rabin ramarki ba data gama makaranta. Murmushi tai,kan tace"Umma karatu ne, zai maida kiba ta har da k'ari, kai ta k'ada, sai dai har yau tana mamakin yadda Fure ta nutsu gaba d'aya, ta zama wata irin sassanya,a zaton ta d'uk makarantar ne, sai d'ai gashi har sun shafe wata 1 da gama makaranta Fure na yadda take,kawai sai ta bada girma ne ya shigi Fure. Abu d'aya ke ci mata tuwo a k'warya yadda shiru ba labarin Uncle Ahmad, ga yadda tsabar tunanin shi ke hanata sukuni,takanji zuciyarta na wani iri in ta tuno shi, gashi ko numbern shi bata rike ba, dabara ce ta fad'o mata,fatan ta Allah sa Abban su yai saving numbern, dan tana yawaita kiran shi da ita. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 14 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 7_Da dare Abba ya dawo a wajen aiki ta d'au wayan da nufin zata kira k'awaye, d'akinsu ta kule,kan ta hau duba "contact" "Fure schl" taga sunan wani contact, tasan kenan numbern da take kiran Abba dashi ne a makaranta, gabanta na fad'uwa tasa numbern a "private" kan tai "dailing'' g'yara k'wanciya tai,tana sauraron yadda wayan ke "ringing" bugun zuciyarta na k'aruwa, sai da ta kusa yankewa har ta sadddak'ar ta sinkayi sallamar shi da muryar da ke sata cikin nutsuwa. Ido ta lumshe tana sauke numfashi da sauri, hannu tasa a d'ai-d'ai zuciyarta dake mata barazanar fitowa fili. "Da wa nake magana pls? Sai a sannan ta bud'e ido,tama manta da ya d'auka,sai da ya kara sallama kamin a hankali ta zare wayan a k'unnenta tana hawaye ta kashe. "Ashe ita kad'ai ma ta damu dashi? Kila ma shi ya manta kashin wata Fure a wani gu, zatan ta baya ma kasar, dan yasha sanarta "England" zai je masters, ashe yana kasar a garin amma bai ko neme ta ba har tsawan wannan lokacin... "Fure lafiya? Umma ce ta katse ta,da sauri ta goge hawayen tare da k'ak'alo murmushi, "ba komai Umma,, da mamaki Umman tace "ba komai ki ke kuka? Jin dad'i komai? Kai ta k'ada,tare da kawar da zancen da cewa "yaushe Aisha zata dawo Umma? Zama Umman tai,kan tace" a satin nan zaki ganta, ai tasha hutu kusan wata biyu kenan,amma Furera tun dawowar ki na fuskanci kin sauya, kin zama shiru-shiru, kodai ba ki lafiya ne? Kai ta k'ada kan a hankali ta zame ta k'wanta cinyar Umman, "Umma ba komai, makaranta make ma son shiga Umma. Kai ta k'ada mata," yana da k'yau, Allah shige gaba,amma sai kin tsaida tunaninki waje d'aya, gashi har yau kin kasa maida jikin ki,sai ma wata ramar da naga kina yi. Kai ta k'ada mata,kan tai ko'k'arin had'iye kukan ta. Gaba d'aya ta tattara Uncle Ahmad ta jingine shi gefe,har numbern shi ta ma goge,dan in d'ai ta motso mata in ba muryar shi taji ba bata samun sa'ida, yanzu kam Alhamdulillah, ta samu ta fara manta so,sai d'ai "memoryn' baya yana a K'wak'walwar ta. Yanzu karatun ta kawai tasa a gaba,a bangaren ''catering''. Yaya Suleiman ya kamalla karatun shi har an bashi aiki,yanzu burin shi aure,sai dai har yau bama budurwar,babban burinshi kamin na yanzu bai wuce ya tara kud'i ya tada ginin Abban shi ba,dan sosai yake da murad'in iyayenshi suyi nasu su huta da haya. InshaAllahu zaya hutar da Abba aikin makanikanci bada jimawa ba,yai alkawarin ji da iyayen su da y'an uwanshi dad'i na duniya in har Allah ya bud'a. Albashin shi na farko Abba da Umma ya direwa,a ganinshi su yafi kamata su fara ci kamin kanshi, musamman Abban su mai arzikin zuci,ya sani da Abban su mai jajircewa ne mai kuma nema da guminsa,shi yasa yake kara alfari dashi yake kuma neman koyi da dabi'un shi. Zaune suke da yamma,dawowar shi a aiki kenan suna zaune a katuwar darduma a tsakar gida shida Umma da sauran k'annen shi,yakan yi nishadi in ya ji shi cikin gida haka da d'uk Familyn shi,Abba kawai ya rage baya a cikin su,tad'in bikin Aisha suke da Umma, yayinda Fure ke zaune tana taya su Hassan da Hussaini "Assignment",sai d'ai jefi-jefi yayan nasu na sako ta cikin zancen. Ka gansu g'wanin ban sha'awa, gidan su ba k'yara bare hancini, kowa yana nan-nan da juna. Adama tai sallama, cike da murnar ganin K'awarta ta shigo gidan. Wani ihu da suka zuba kan Furen ta tashi suka ruk'unk'umo juna, daga Umma har yayan baki suka saka suna k'allon su,toh g'wara Umma dama tasan halin Adama da Fure,amma shi da mamaki kawai yake k'allon su musamman Adama, sai da suka gama rawar kansu tukun cikin kunya ta gaida Umma,kan ta sauke k'allonta akan Ya Suleiman,da halamun kowa d'ai yai katari da " soul mate " d'in shi, dan kasa tai da kai,lokacin da ta gano waye shi,shikam k'allonta kawai yake da murmushi,kai duk'e tace "ina yini Ya Suleiman, Fure ce ta katse shi," Adama ce fa Yaya,ta girma koh? Murmushi yai kan ya amsa,"ai sam ban gane Adama ba,"2years" d'uk sun kara girma,koh Umma? Murmushi ita d'ai Umma tai,da halamun ta gano bak'in zaren. By Feenat Ja'afar. Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 Apr 14 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 8_D'aki suka shige, suna firar yaushe gamo, "kawai ki kaje kikai zamanki a Abuja abinki? Murmushi tai, kan ta ware "pashminan" kanta, "k'awata Abuja tayi a rayuwa, ke! Bari kawai, Allah kamar kar na dawo, naci fa na k'wanta, hatta kayana wanken ake. Hannu ta bata suka tafa tana "shege Ada,kinyi k'yau ke kin ganki? " ke d'ai bari, zama ta g'yara, "kai k'awata yayan kun nan fa Allah sai had'uwa yake kara yi, d'uk yafi y'an gidan nan k'yau fa.. Dariya ta tuntsire mata dashi, kan ta bata suka tafa, " dad'ina da k'awata ba fulako,ki ce munyi kasuwa? Hannu ta kai bak'inta halamar tai a hankali,"Allah dama ranar yace nai mishi budurwa a unguwar nan,sai kuma naga shima kamar ya zurma. Wasa-wasa d'ai zance ya tabbata tsakanin Adama da Ya Suleiman, har magana taje gidan su Ada, sosai ba wanda yakai Fure son wannan had'i, sai kuma su da suka k'ulla abunsu. Biki kam ya karato, d'uk da yazo a lokacin da Fure ke shirin y'in Exams a school. Tafe suke ita da Aisha da k'awayenta su biyu daga saloon,ganan g'wagg'waran su a leda da aka nad'a musu, k'awayen suka tsaida 'Taxi" suna sanar da Aisha sai goben, sauri suke, ganan magriba ta wuce amma hanya d'uk "go slow", sai sunyi kamar zasu t'sallaka sai Fure ta r'unkumota har wata motar ta taho, t'saki Aisha tai," wallahi kamar tashin k'auye kekam, da tuni mun wuce sai wani rirrike ni kike. "A ke,rai d'aya ne, a yadda kowa yake saurin nan muje wucewa da garaje kawai sui ciki damu? Kai Aisha Amarya ta k'ada," toh ni kam zan t'sallaka, dan kinsan Abba in ya dawo ya tarar bamu dawo ba fad'a zai,in yaso randa mutane suka d'auke K'afa sai kizo. Hijab d'inta ta rike,"wallahi baki isa ba. Yanzun kam mota suna d'an nesa, hannun Furen ta kama"ki biyo ni toh yanzun. Da d'an gudunta Aisha tai gaba,sai jin Fure ta zame hannunta tai, "tsaya ledar mu, ina, A'i har ta wuce,da sauri ta ju ya da nifin ta t'sallaka t'saut'sayi, ashe wata jar CRV ta kuts'o,da gani kuma sauri su ma suke, gashi tazo t'sakiyar k'walta,ga ihun Aisha na tai gudu ta karaso. Ga ihun "horn" din motar,d'uk sai ta kasa gaba ta kasa baya,suka had'u da tsoron k'walta suka rikita Fure,ido ta rintse,tare da sakar ledar kayan a kasa ta rufe k'unnenta da hannunta d'uk biyu, tasan ba makawa sai motar nan tai ciki da ita. Jin shiru ba ai ciki da ita ba saima hasken motar da ya dalle mata ido da dan jin hayaniya yasa a hankali ta bud'e ido jiki na ka'r-ka'rwa. "Da ke! ke da asara wallahi bamu ba, so nai a yabimin ta kanki tunda kin gaji da duniyar shi kuma ya tsaya.. Babbar mace ce,sai d'ai da ka ganta zaka san isassiya ce mai ji da kanta, k'allo d'aya zaka mata kasan naira na inda take, fara ce mai kiba ba chan ba. Sam ita bama ta lafiyar Furen take ba. Masifa take ma Fure kamar ta rufeta da duka,gashi ita Furen ta tsaya kem! Kamar an dasata a gun,har yanzu jikinta na ka'r karwa, Aisha data karaso ita kad'ai ke bawa Hajiyan hakuri,tare da ko'k'arin janye Fure. Wasu da suka gaji suka zame bi ta gefe. Haka take ga wanda yake " driving ",tunda ya taka birki yake k'allon wacce yaso ya bige, kamar wani wawa ya sau baki yana k'allon Fure ba ko kiftawa, ganin suna neman tafiya yasa da sauri ya 6alle murfin mota yai gunsu, Hajiyan ta zata k'addamar musu zai yi sai taja baya,yace"Momy shiga mota in zo yanzu. Sai da yaga ta shiga mota yai gunsu Furen," Aisha. Da sauri Aisha ta dago,wanda Fure itama tai saurin dagowa lokacin da zata d'au ledar, "a pharmacy? Ba d'ai kai ne a motar ba? Idon shi akan Fure yake yana murmushi, yayin da itama Furen ta zuba mai ido ba koh kiftawa. Tabbas itace,ya fad'a a zuciyar shi,sai da Aisha ta kara magana kan ya juyo gare ta, "kuyi hakuri amaryar mu,sam ban zata ku bane, kan Fure ya dawo, " Furera da fatan bakiji ciwo ba?....Momy ce ta katse shi da cewa "Kai dare fa na kara mana a titi, kabar wannan yaran dama y'an titin ne daga gani mu tafi. Wai waya wa yai," toh Mom,coming. "Ku kara hakuri pls Amarya, ya dubi Fure,da itama shi take k'allo ba ko kiftawa, Aisha ma da mamakin ina yasan Fure take, sai kuma mamakin uwar shi bala'e'iya, Tana nan a haka har sukai sallama amma ita ta kasa furta komai. Har ya shiga mota shima yana waiwayen ta. Ko da suka je gida su Umma suna ta tambayar su ina suka tsaya har haka? Furen Aishan ta k'alla, "Umma amare ne sukai yawa a garin,ga gidan mai kunshi ma acike. ''Toh ita Furen mey ya same ta? Koh yunwar ce? Da sauri Aisha ta k'ada kai, dan tasan in d'ai ta sanar da Umma abinda ya faru yanzu zata rikice. Juyi kawai take a katifa, har yanzun ta kasa t'ant'ance murna take ko akasin haka? Ga Aisha ta dameta da tambayar ina Ahmad yasan ta? Kai kawai ta k'ada mata, kan tace itama bata sani ba. Juyi ta kara yi,sai ga hawayen da tun dazu take bidar su zubo sunki sai yanzun. "Dama uncle Ahmad na garin nan har yanzu? Lalle yanzu ta kara tabbatar da ihu kawai take bayan hari, tunda har address ta bashi in yaso zai neme ta. Haka ta lulluba tai mai isarta kan ta sa a ranta indai tana da zuciya toh tabar tuna uncle Ahmad. Suma chan su Momy tun a mota take ta kara zagin su Fure,shi d'ai yai shiru,tunani ne fal ranshi har suka zo gida. K'wance yake yana k'allon" A.Cn d'akin nashi, kawai yanayin Fure yake tuno wa, ashe Allah zai sa yaga Fure a fad'in garin nan bayan rasa address d'inta da wayar shi? Murmushi yai,a hankali ya furta"Pretty" sai kuma ya gintse. Tabbas Fure na matukar kama da Aisha,sannan sosai yasan yayan Aishan a A.B.U,toh meye had'in su da Fure? Dan tun dawowar Suleiman a dalilin auren Aisha sau biyu yana zuwa gidan su,amma bai ta6a ganin Fure ba... Gaban shi ne ya fad'i sakamakon tunawa da zanchan su na jiya da Suleiman d'in, kan wacce zai aura makarantar da yai service tayi,kuma shekarun d'aya.. Kar fa ace Furera ce wacca Suleiman zai aura? Kila koh y'an uwa ne shi yasa suke kama... Cewar wata zuciyar. Tashi yai zaune,dan tuno da g'yaran amaren da suka sha ga uban lalle da kayan g'wag'gwaro da suka fad'i kasa. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:17 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/16, 12:30 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 9_Washegari "10am" a kofar gidan su Aisha ta mai,a kofa ya same su, da halamun daga wani waje suka dawo,tsaye suke da Ya Suleiman suna ta nishadin su da dariya,tun a nesa kawai ya bada hasashen shi ya zama gaskiya,toh amma ita Furen wace tasu? Ina ne gidan su? Tun tsayuwar shi Fure ta tsagaita dariyarta tana dub'en motar,tabbas ta jiya ce, k'allonta Yayan nasu yai,kan ya k'alli inda take k'allo, tuni fara'ar shi ta karu tare da furta"A'a, AAA.. Kan yai wajen shi,Aisha ma ta fara fara'a, ita kam kasa tai da kai,dan ganin suna yin wajen su da Uncle Ahmad d'in. Idon shi na kanta,ganin yadda Yayan nasu ya shiga t'sakiyar su ita da Aisha,da fara'a suka gaisa da Aishan,kan itama tace"Uncle ina k'wana.. Damm! Ya ji zuciyar shi ta buga,a hankali ya amsa,tare da d'auke kai a kanta, shikenan Pretty ta fita a rabon shi? Ido ya dan rintse,"kai zurfin ciki bai ba a rayuwa, gashi yana k'allo k'wado zai mishi K'afa. Ya Suleiman ya k'allo shi, "nasan dama zaka sansu, sai ya k'allo Fure da murmushi, itama ta k'akalo murmushin dole. "she's my.. Da sauri ya tare mashi numfashi da fad'in" I know, sai yai murmushi a takaice, kan ya k'allo Furen, Ya Suleiman yace"ok,kun ta6a had'uwa a gidan ne hala? Kai ya k'ada, duk sai ya ji tsayuwar ta gundure shi,Aisha ce ta katse shi da fad'in "Ina Angon ka barmin shi? sai kuma ta rufe fuska ganin yadda Yayan su ya kafa mata ido, " iyee! Lalle fitsaru. Shikam murmushi yai kan yace"yana a masaukin shi,zai zo bada jumawa ba. "Zan wuce, dama Ilyass ne yace na tabbatar da lafiyar Madam d'in shi,sai mun had'u a " Dinner ". K'allo su Fure yai,"toh amare zan wuce,sai mun had'u anjima, kai Fure ta k'ada mishi, kan ta d'au ledar su ta shige gida,da tsabar takaici,ashe ma ba dan ita yazo ba? Ajiye dilkar tai da suka k'ar6o, tai ciki ta bar y'an biki a t'sakar gida. Shikam a mota d'uk ya rasa sukuni, Fure ita ce mace ta farko da ya fara jin " feeling'' akanta, hatta Maman shi tasan da zancen Furera,yau da ya sanarta yaga Furera k'warai ta tayashi murna,har yaje gida sukuku yake jin kanshi. Sam baida kuzari. D'akin Maman shi ya zu6e, wanda indai maganar mace ne toh dole sai wajen ta,amma sauran lamari Momy ce ja gaba sama da Maman tashi. Mata biyu ne ga Baban shi, Momy itace Uwar gida,yayinda Mama ke amarya, d'uk a zankuwa aka haife su, sai d'ai lokacin su Ahmad na yara, kamin suka dawo Kaduna da zama gaba d'aya. Baban su Alhaji Abba Ahmad "costom" ne kan yai "resining" ya zama d'an k'wangila. Sosai yana da kud'i, sannan da dattako, Momy nada fad'a, sam taki jinin talaka,dan baban ta babban "costom" ne lokacin da Alhaji Abba ya aure ta. Ga matukar dagawa da raina mutum,ga son fasa taro,komai ita ke ju ya shi son ranta a gidan,yaranta 3,Hauwa(Aunty Jidda), itace babba a gidan,sai Nasir,da Huwaila, sai y'ar K'anwar ta da take ruko Rukayya. Kan aka auro Mama, d'uk itama gidan su ba laifi,gata mace ce har mace,mai hakuri da t'sabar sanin ya kamata,tana da kawaici, kullum zaka samu fara'a k'wance kan fuskarta, da fari Momy ba taso zama da kishiya ba sam ita, sai d'ai kuma wani had'in Allah, kawai sai tasu tazo d'aya, dan komai ta sakar mata ta mallake,hatta yara in ta haifa toh sun koma zaman d'akin Momy,ita kam dake mai hakuri ce,d'uk sai ta sallama mata su, yaranta shida,Usman, wanda shine mijin Aunty A'i, sai Aunty Maryam,Ahmad,da Ummi autar ta rasu. Amma d'aya kawai ta rike wato Ummi. T'sakaninta da sauran sai gaisuwa koh in taje bangaren Momyn,sai ko randa ta motso musu suzo bangaren ta,dan ita k'wa6arsu take matuka, amma a d'akin Momy sunan ka"kai komai ba komai na". D'uk da mugun hali irin na Momy sam batai ma yaran Mama mugunta,batta da mitar ta,hakan ne yasa ita maman sam bata damuwa,sai d'ai abu d'aya, duk yaran kad'an ne basu kin talaka da raini,wannan dabi'ar ita kad'ai ke ciwa Mama tuwo a k'warya. Dan tamkar fad'an Allah d'uk yaran gidan sai mai kud'i, in maza ne sai ya'yan manya masu k'yau. Hudubar Momy kam tai aiki,Ahmad shine ya fita daban,wanda sam baiya burin auran y'ar masu dashi,sannan kuma k'yak'yawa. Asali ma tun tashin Rukayya Momy tace itace Matarshi, shikam fur yaki, dan ka'f ba abinda ta bari a halin Momy,tamkar ita ta haifo ta. Gadai k'yau har k'yau, amma sam ba hali. Shi yasa ko dariya Ahmad bayayi a gaban ta, asalima ita d'uk gidan shi tafi tsoro. Takanyi ma Momy kukan sam Ahmad bai kula ta,sannan ga hancinin tsiya. Momyn takance ta k'wantar da hankalinta,Ahmad kamar ya zama nata an gama. Haka kowa yana da burin fita kasar waje yai karatu a gidan amma banda Ahmad. Rayuwa mai sauki shi ya za6arwa kanshi, kuma a zahiri kowa a gidan naji da Ahmad, har sukan kira shi da mai "ra'ayin kanshi". Anan ya had'u da Ilyasa,yayinda shi Ilyass yake abokin Ya Suleiman. Nan suka k'ulla abota, duk da kowa bangaren shi daban,sannan ba yadda za ai ya nuna maka shi d'an wani ne,dan ko mota bai ya zuwa da ita cikin A.B.U. Ko Abban ne a yanzu d'ai da Ahmad yake yawo ko ina zashi,tunda sauran manyan yaran kowa ya kafu da K'afarshi. Sosai Abban su yake son yaran shi,haka bai son takura musu,yai musu sa6o da jin dadi,d'uk da shi d'ai bai kin talaka,sannan baida wulakanci. Mama ce ta k'allo Ahmad," ya d'ai? Har ka dawo a gun Fureran? Kawai sai ya k'wanto cinyarta "Mama aure zatai go6e.." Ya Salam! Shine kalmar da maman ta fad'a. Kamar ya k'urma ihu haka yake ji. "Ita ta fad'a maka? Kai ya girgiza, " A'a, Aboki na d'ai zata aura. Kanshi ta shafa cikin sigar lallashi, "kai hakuri toh,Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi, Amma sosai nima d'uk da banga Furan nan ba ta shiga raina. Nan tai ta bashi baki,kan matar mutum kabarin shi. By Feenat Ja'afar. [4/16, 1:44 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 10_Da k'yar ya iya shirya wa zuwa wajen "Dinner". Sosai yai k'yau cikin manyan kaya yau da ya shige su,dan shi ma'abocin kanana ne. Farar shaddar ta matukar k'ar6ar shi, ga hular nan ta kama,sai kamshi yake kamar Angon ba wai abokin Angon ba. Parlourn Momy ya shiga,don sanarta ya fita. Rukayya ce kawai a parlourn tai d'ai-d'ai a kujera tana " 2go". Tana ganin shi ta mike da rawar kai harda ce mishi yai k'yau, baki ya d'an ta6e kan ya had'e rai''ina Momy? Da dan harara ta nuna mishi d'aki ta koma ta k'wanta a ranta tana"ka'r- ka'ra a d'aura mana aure ne,zaka shigo hannu. Sukuku ta gama shiri tun jiya batta kuzari, hakanne ma yasa Y'an uwan suke d'an sata nishadi,amma da anjima zata dawo gidan jiya,su sun d'auka koh rabuwa da Aisha ke sata haka. Tsaye suke a gaban madubin su na katako a d'akin su,kanta kawai take k'allo, matuka tai k'yau tamkar wata k'yak'yawar. Tabbas in kana da k'yau ance ka kara da wanka. A d'uk k'walliyar k'ewayen idonta yafi ko'ina d'aukar hankali. Ma'abociyar ita gashin ido ce dana gira sune tushen k'yanta. Yau sunsha" Mascara'' da "eye liner''. G'yaran jikin da fatarta ta samu ita ta fidda ta zama " Black Beauty", net ne "gown" "combination" d'in fari da "pink" a jikin ta. Daga sama aka sa farin zuwa chan g'wiwa, kasan aka mishi tattara da "pink" d'in, da "head' na "pink" da k'yali-k'yallin "silver''. sosai tai k'yau ainun kamar itace amaryar. d'uk da su masu karamin k'arfi ne amma ak'wai zuciyar yi,dan sosai sun fitar da kansu kunya,d'ai-d'ai g'warg'wadon hali Abba da Ya Suleiman sun fitar su kunya. Kawun su na Zaria shi ya d'au nauyin gado da kujerun Aisha y'an zamani,sosai y'an uwa ma sun musu kara abin sai son barka. Adama ma tasha lefe Ya Suleiman kamar ba go6e,ranar albashi yai rana da taimakon makanikancin. Aisha ce ta shigo ita ma sanye da" net" "brown".. Sosai tafi Fure k'yau,amma a yau d'uk sun had'u sunyi k'yau sosai. Gaban madubin taje tana murmushi, kanta ta d'aura akan kafad'un Furen, " y'ar uwa tamkar kece amaryar kinyi k'yau ainun,, murmushi Fure tai d'uk tai laushi, "ku nake tayawa k'yau tunda kunyi k'yau kuma. Tai murmushi, "dan Allah Furare mey ke damun ki? Tun randa abin nan ya faru d'uk kin dawo wata iri, kinyi sanyi sosai, "dazun naji kince ma "pharmacy" Uncle, amma kince min baki sanshi ba,bayan Ya Suleiman yace anan yai "service'' a school d'inku,mey kike 6oye min ne? Murmushi tai kad'an kan ta juyo, gaskiya ta fad'a mata kan ta sanshi sosai. Ido kawai ya zubawa kofar " Hall" d'in dan jin ana sowar ga Amare nan, Asha da Angonta ne a gaba,sai gata ita da Ya Suleiman, sai dai shi ya ju ya waje lokacin da ya gane Adama ta tsaya. Ido ya rintse dan ganin lokacin da Ya Suleiman ya rad'a ma Furen wani abu tana d'an tushe baki da dariya. Tsayawa su Aishan sukai,har ta karaso bai daga kanshi ba. Tana daga kanta tai ar'ba dashi ido rufe,da sauri ta d'auke kanta jin wani abu na taso mata a zuciya wanda tuni ta rufe bab'in shi. Sowar daya kara ji ne yasa ya bud'e ido,sai ga Adama sun shigo da Ya Suleiman, da sauri ya k'alli wajen su Aisha yaga Furen na tsaye tana d'an murmushi tare da d'an had'a hannu tana musu tafi a hankali. Wata ajiyar zuciya ya saki tare da sakar murmushin farin ciki. "Dama Adama ce matar Eng.Suleiman? Kai amma ansha dashi k'warai. Tashi yai Shima yana d'an tafa musu da murmushi a fuska,kan a hankali ya ju ya ga Fure, wacce itama da sa'a ta k'allo shi,murmushi ta sakar mishi wanda kamar dak'yar ya fito,kan ta d'auke kai a hankali. Sosai ya famo mata wani ciwo,ga wani uban k'yau da ya mata cikin manyan kaya yau d'aya, dak'yar ta saita kanta. Chan inda aka warewa abokan Ango da na Amare ta nufa kai d'uke, kujerar da ke k'allon shi kawai ta rage" empty " shikam har yanzun k'allonta yake har ta zauna. Ana gabatar da abubuwa shikam Fure kawai ya zubawa na mujiya,sosai tai mishi k'yaun ban mamaki, ga wata nutsuwa da yaga tai bala'in mishi, kamar ba Fureran da ya sani ba. Kowa ya tashi,na taka rawa suna yi,na yawo nayi, sai ya rage daga Fure sai Uncle Ahmad. Kai duk'e ta gaida shi da sanyin murya,jin bai amsa ba yasa ta dago,murmushi yake yayin da idon shi ke k'anta. Sai ta samu kanta da kunyar shi. Da k'yar ta samu ta zame da wayyon Adama na kiranta. Binta yai da k'allo, yau d'aya Fure ta kara mamaye zuciyarshi, bazai kuma kara sakacin ta ku6uce mishi ba. Wa yaga "real Love'. Daga ita har shi har aka tashi fara'a suke, ita kam batasan tata ta meye ba. Maimakon yadda suka zo su koma tare ita da Amare,kawai sai mazajen su suka d'auke su,Ya Suleiman yace ya had'a mishi da y'ar K'anwar shi da wata cousin nasu. Ba dan taso ba suka shiga motar,wata "civic" baka mai k'yau. Baya Sadiya tai saurin shiga,wai ita ta shiga gaban. Haka tai sakare,kan ta bud'e ta shiga,ya ja su. A hankali yake tuki cikin nishad'i,ya kan d'an k'allota kad'an kan yai murmushi, itama takan d'an satar k'allon shi ta gefen ido, fuskarta sake,sai d'ai ba walwala,kowa y kasa ce wa kowa uffan. "A.C ya kara,kan ya hankali ya kai hannu ya k'unna wakar da in d'ai zai ji ta toh Fure ke fad'o mishi, sai d'ai yau gata gare shi, a hankali ya d'au "remote" ya d'anna "play" sai ga nan wakar "Nothing gonna change my love you ta shigo. Tsam ta nutsu, tare da sauraran b'aitin cikin wakar,sai ta samu kanta da lumshe ido kamar mai bacci,tare da jingina kai a kujerar motar. k'allo ta yai,kan shima ya jingina a kujerar yana tukin shi cikin nishad'i,tamkar ance an bashi Fure. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:18 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 11_Ido rufe kamar mai bacci taji sun tsaya,maganar sadiya ta tsinkaya tana mishi godiya,kan ta fita,k'allo shi tai,kan cikin sanyin murya tace"mun gode Uncle, ba ta jira mey zai ce ba ta fara ko'k'arin fita,sai dai gam, kofar a kule,tsam tai,kan a hankali ta juyo ta k'alleshi da halamar tambaya. Shima idon ya zuba ma ta,sai ita ta k'au da nata,kusan minti uku ya ki magana, ita kuma tsabar haushin shi ma take ji,wanda ita kanta bazata ce ga dalili ba. Chan yai ajiyar zuciya, kan cikin nutsuwa yace"Furera... Kanta na gefe ta amsa,sai kuma ya kasa ce mata komai,mota ce ta hasko su,su Aisha ne, gaba d'aya suka bisu da k'allo ganin yadda suke a nishad'i, kawai sai ya d'anna "unlock" kan yace"ki tsimaye ni gobe..dan K'allonshi tai kan ta k'ada kai tai waje,da k'allo ya bi ta, kan shima ya fito. Gun su Aisha tai,duk jikinta yai lak'was,ganin ba Adama tasan sun kaita gida. T'sakiyar su Ya Suleiman ta shiga da Aisha, yayansu mai saukin kai ne,ba ruwan shi da hantarar su ko k'yara, shi yasa k'warai ya zama abokinsu. Murmushi kawai Ilyas yake musu,ganin yadda Fure ke shag'wabe fuskarta. Uncle Ahmad ya karaso yaga Ya Suleiman ya kama hannun Fure,sai ya t'sinkayi maganar shi cikin lallami,"wai Aisha mey ya samu Furii ne tun jiya bata da walwala? Murmushi tai,kan ta k'alli Uncle Ahmad wanda idonshi ke kan Ya Suleiman a na Fure. "Na tambaye ta tace ba komai. Ilyas yai murmushi," hala bata son ku tafi ku batta ne? Gida su Aishan suka shiga,kan su kuma suka hau fira a kofar gidan. Kasa d'aurewa Ahmad yai,"wai ni Engnr. Meye had'in ku da Furera pls? Na kasa gane wa fa.. Dariya sosai Ya Suleiman shida Ilyass suka,kawai sai ya sa musu ido,shi d'ai amsa yake nema. "Amma tambayar ta ban mamaki "pharmacy", cos jiya ka ce min" you know'' I thought ko a makarantar su kasan ta ai. Kai ya k'ada, "Eh,amma bansan nan ne gidan sun ba. Ilyass ne ya dafa shi da d'an dariyar shi, "kana da abun dariya Aboki,hala neman iri ka ke ka fara bamu girma tun yanzun? Murmushi yai, tare da k'ada mishi kai, " toh abinda yai Aisha shi yai Fure yai kuma Engineer.." Same Ma, same Baba.. "Ko in ma ta d'an g'wari-g'wari? Kai ya k'ada murna fal cikin shi,kan ya k'allo Suleiman, wanda har yanzu yake dariya kasa- kasa. " a gaskiya na wahala a neman K'anwar ka Engr. Ashe tana a kusa ma ban sani ba? Murmushi yai, kan ya k'ada kai. "Pretty"..... "Furera''.... Kai, yanzu na gane, ashe ita ce wacce ake neman nan ido bud'e. Cewar Ilyass cikin shakiyanci. "Shegen kaya, kai yanzu ko kamar ai zaka d'akko hanya. Kai ya k'ada yana murmushi, kan yace "a bar zancen kawai, amma ni kam,naga gida. Dariya Ilyass ya sa mishi,shikam Suleiman k'ada kai yai, dan sosai yasan had'in yayi, lalle k'annen shi sun dace da mazajen aure na k'warai. Dan Ilyass abokinshi ne sosai,tun a Zaria, ta dalilin shi yaga Aisha, sannan yasan Ahmad, sosai ya yaba da yadda yaje gidan su Ahmad yasha k'allo, amma sam shi bai ta6a nuna musu shi d'an wani bane. Kai ya k'ada, yana mai adu'ar Allah sanya alkairi. Bak'in nan kamar gonar audiga ya shiga gida," direct " d'akin mama ya nufa,suna parlour ita da Ummi suna k'allo, yadda yake fara'a ne yasa mama K'allonshi itama d'auke da tata. "Ka dawo? Kai ya k'ada, kan ya k'alli Ummi wacce tai likwas cinyar Maman tana mishi sannu. Da murmushi yace "Je kice Momy na dawo a kai min abinci d'aki.. Kai ta kada kan ta d'au dank'wali ta yafa, kusan Ummi halinsu d'aya da Ahmad, shi yasa tasu tazo d'aya, dan rainon mama ce ita. Tana fita ya k'allo mama. "Mama pretty ashe K'anwar Suleiman ce uwa d'aya, ashe ni ne ban gane ba sai yau. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 18 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 12_"mashaAllah, ashe Furera na kusan mu ma. Kai yai kasa dashi yana dan sosa keya yana murmushi, mama tace"toh Allah sanya alkairin shi,sai d'ai bansan yadda zaka kaya da Momyn ku ba Ahmad? K'allota yai,kan yace"gaskiya mama Rukayya bata a matan aure na,cos ba lalle muyi zaman aminci da ita ba nasan. Kai ta k'ada, lalle tasan ak'wai rigima a kasa,dan sarai tasan yadda Momy ta d'aukaki had'in nan nasu Ahmad da Rukayya, ita d'ai tasan nata ido, sai kuma tabi su da adu'a. Washegari "10am" aka d'aura auren masoyan biyu,basu samu kansu ba sai dare bayan ankai amare gidajen su,d'uk anan suke. Shi yau ma ya d'akko ta daga gidan amarya,yau da ita da autar su,cikin nutsuwa yake sauraran surutun Amal,bata fi "4yrs" ba, kawai sai ya ji babyn ta shiga ranshi, sosai tana mishi kama da Furen shi. Kawai sai ya fara bata tad'in Fure a schl. K'allo ta yai,itama fara'ar take,sai yai murmushi, Amal tace "Uncle, kuma kana d'ukan Aunty Fure in tai surutu a class irin Uncle John? Harara Fure ta ju ya ta sau ma ta jin tace mata Fure. Murmushi yai lokacin da suka had'a ido da Furen. Kan yace wa Amal "nop,sai d'ai na sa ta " kneeling" dan kinga ai ta girma koh? Kai ta k'ada mishi tana ma Furen dariya. "Toh kuma tana kuka? Sai ya k'alli hanya yana tuno wani lokaci a baya.. Akan Fure ya sauke idon shi, wanda take k'allon titi ta kasa k'unne ta ji amsar shi. Sai yai murmushi, tare da k'ada ma Amal kai, "sosai,har tana kiran Umma tazo ta taimake ta.. Dariya suke mata, ita kam kai ta lang'wa6e mishi, " kai Uncle A,ni d'in? Gira ya daga mata,sai kuma ta d'auke kai. G'walo Amal ta mata tana "woo Aunty Fure.. A karo na biyu tace"wai waye Fure? Dariya yai har da d'ukan sititari,ganin yadda tai da baki gefe Amal ma ta mata. Yace!" No Amal,daga yau sunan ta"Aunty Pretty... Baki suka saka,ita na K'allonshi, Amal na k'allonta. Ido ya k'anne mata,da sauri sai ta d'auke kai tana murmushi,ya akai yasan Pretty? Ko a schl? Amal tace,"La! Uncle "Pretty Zinta ta Jaduu? Dariya suka sa mata d'uk, kai Amal. Haka har suka zo gida Amal na musu abin dariya. Tsaida mota yai,kan suka fito,ganan y'an kai amare wasu suna waje,sai Amal tai gida wai d'akko mishi "sweet". Da k'allo ya bita, har ta shige gida kan ya dawo kan Fure. " pretty"...Buguwar zuciyarta ne ya dawo take yau,dan jin ya ambaci sunan ta cikin sanyi, a hankali ta amsa, "Ashe Engr. Yayanki ne? Kai ta daga mishi,kan a hankali tace" Umm. "Sai ki ka ji ni shiru ba? Kai ta duk'ar, ba tare da tace kom ba. Tsayuwa ya g'yara, kan ya fara bata labarin bayan rabuwa. " A motar haya na gamu da mai yankan aljihu,waya na da "Address" naki da na sa d'uk ya de6e, k'warai na fi jin ciwan 6atan "address" d'inki sama da "phone'' na,karshe nai "losing" "contact " na Abba,ko da nai "swapping" still ban samu ba..kai ta dago,da mamaki ta k'alleshi. " kin san dalili? Kai ta k'ada. Amal ce ta dawo da alewa a leda tana bashi,sai yai murmushi, maganar da bai gama mata ba ya bari kan sai gobe sa had'u, ya kuma nemi number, ba musu ta fad'a mishi. Sukai sallama Amal na mishi "bye-bye. Tun da yazo k'wanciya zaro wayanshi yana duba pic d'in da mai " photo" ya tura mishi na pretty a waya. D'uk da halamun bata ma san an d'auka ba, dan sam ba ta da wal wala sosai,sai ya bada "style", sosai ranar ta mishi k'yau, shi yasa yace mai hoto d'uk motsinta ya d'aukar mishi ita. Murmushi yai tare da shafo wanda takewa Adama murmushi, a hankali ya furta "Furii pretty". Kawai sai ya raya ya kira ta ya ji muryarta ko zai samu na bacci. "Tea" take sha lokacin taga wayanta na d'an wal- wal. Kofin ta sauke,kan ta kai hannu ta daga, wayan ta kurawa ido, tasan numbern,sai d'ai ta k'wanta mata. Saura kad'an ta kat'se ta daga,shiru tai dan jin ko wacce take zargi ce.."Assalam Alaiki Furiii...Ido ta lumshe, tare da saita kanta da sauri,dan har ranta taji sunan,d'uk da ta gane mai maganar, sai ta basar,''walaikum salam.. Daga chan yai ajiyar zuciya, muryar Fure na daga abinda yake son ji a tare da ita.. "Hope kin gane mey magana? Kamar ta ce" eh, sai kum tace, "ban gane ba kam.. Murmushi yai, kan ya ju ya tare da rage karar *TV".Yace "coper Ahmad Abba Ahmad, (AAA) " Chemistry " "teacher''.. Murmushi tai mai sauti,wanda har ya ji, sosai yau tana a farin ciki,, cikin nutsuwa da wannan murya ta pretty kad'ai tace" am sorry Uncle AAA,I thought koh... Sai kuma tai shiru. Tashi yai zaune, kan yace"koh wa? Kai ta k'ada, tare da k'allon sadiya da tai mata kurii da ido. "Ba kowa. "ka je lafiya? Ajiyar zuciya yai,kan yace"lafiya lau,ina Amal? Ido ta lumshe, sautin shi na neman zarar ta,a hankali tace "tana gun Mama. Fira ya cigaba da mata,kan yai mata sallama kan ta tsimaye shi zai zo mata da batu in y'an biki sun watse har gida. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:20 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/19, 8:11 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� : "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 13_Wayan take k'allo, sai ta samu kanta da murmushi, ji tai gaba d'aya ya wanke kanshi a gunta,tuni taji wani sabon lamarin da yafi na da,a hankali ta zame ta d'aura kai kan "pillow" tare da tariyo had'uwar su zuwa yau, fatan yasa yazo mata da abu mai dad'i. Da tunanin juna suka k'wanta, shi kam harda mafarkin "FURIIN" shi. Washegari suna t'sakar gida da sauran bak'in da basu tafi Ang'waye sukai sallama,anzo gaisuwar sirikai. Amal aka ce ta leka,sai gata da gudu tana rad'a ma Fure"Aunty Furera Uncle... Murmushi tai,kan ta k'alli kofa, Ya Suleiman ne ya shigo, tare da sanar da su Umman,darduma suka sa musu,kan tace ya shigo dasu. Chan bak'in kofa ta zauna,har suka shigo, tana jin lokacin da suka gama gaisa wa Ilyass na tambayar ta. Leko da kai tai kad'an,d'uk sai wani sunne kai suke har mutumin ta,d'uk da yana d'an wayancen dagowa neman ta. A hankali tace musu "Ina k'wanan ku... Cikin nutsuwa ya dago kai zuwa bak'in kofar da ya jita, ido suka had'a, da murmushi tai kasa da kai suka amsa. Amal kam tana manne da Ahmad,wanda murmushi yake saka in sun had'a ido da Fure,cikin kunyar k'allon d yake mata ta buya d'aki. Har suka zo fita yana d'an leken ya ganta amma ba hali. A zaure ya tsaya bayan sun fito,dan gidan su Adama suka fara zuwa. Amal ya aika wai ta kira mishi Aunty Pretty, da d'an dariyar ta ta tafi kiran. Jim tai kad'an, kan tai murmushi ta tashi,zani ta sauya,ta cire hijab d'in jikinta,sai ta samu kanta da t'sayawa gaban mirror, gashinta ta g'yara, ta d'aure shi t'sakiya da k'yau kan ta sa hijab akai ba dank'wali. Gun Umma taje,tace ana kiranta. A zauren ta same su shi da Amal yana rike da hannunta tana mai wai karatun ta na islamiya" Asma'uillahi Husna". Kai ya dago da ya sauke su kanta lokacin da take musu sallama. Murmushi ya sakar mata kan ya amsa,yau kawai kunya ce tazo mata tashi. Shikam k'yau ta mishi a hakan ma da ba make- up, a chan kasa yake k'allonta, wanda tuni ya kara mata wata kunyar. Rabin tad'in nasu da Amal su ke,kan ya tambaye ta yaushe zata Aisha,tai jim,yau kam ta gaji,tun dazu take mata nacin tazo ta riga tace sai gobe, ga d'ai bak'i zasu zo, "gobe InshaAllah. Zauren ya k'alla, na kasa ne amma wata iska yake ji mai sanyin dad'i, ji yake kamar yace ta shimfida mishi taburma kawai ya zauna suyi ta tad'in su yana shan iskar zaure. Tabbas yana alfari da Suleiman da k'annen shi,har ma da iyayen su,rayuwa suke cikin sauki da rufin asiri,ga kowa ka gani a gidan mai fara'a ne. Sannan basu raina kansu wai dan wani ya fi su,shi yasa sosai ya fara abota da Suleiman a dalilin Ilyass abokin shi. Sai yaji ya kara son had'a jini dasu, Kai ya k'ada yace "Allah ta kaimu,,a hankali tace"Amin. Ya Suleiman ne ya shigo zauren shi da Ilyass yana ta dariyar keta, shi kam Ya Suleiman murmushi kawai yake, gaishe su ta kara yi,tana tambayar ina K'awar ta? Sai yai murmushi, kan yace tana gaishe ta. Sosai suke bawa su Ahmad sha'awa ganin yadda yake ji da y'an k'annen shi. Janshi Ilyass yai yana mishi tsiya sukai waje,sai ya juyo tare da kai hannu k'unnenshi a hankali ya furta"I will call you". Murmushi kawai ta mishi tare da sunne kai. By Feenat Ja'afar. [4/19, 9:28 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� : "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 14_Washegari gidan Adama ta fara zuwa, ba wata k'walliya tai ba,kawai "powder" ne da janbaki sai "mascara". Sanye take da "pink'' na doguwar riga kirar '"Dubai'' wanda Ya Suleiman ya sai musu kan biki, farin fashmina da ratsin pink ta faka gashin nan kan ta nad'e shi cikin g'yalen, ta hau "hill", matuka zaka zata y'ar wani mai kud'in ce,amma tsabar rufin asirin Allah ne da had'uwa da iyaye masu zuciyar yi. Harara ta kai mata, "ai nayi fushi K'awa, murmushi tai,a kiyi hakuri. Kai ta k'ada, "ya zanyi toh? Ina su Umma? Murmushi tai, kan tace" suna gaida amarya,jiya kad'ai har kin kara "shining " dariya tai kan tace"dan ma yayanki ne. Sai Bayan la'asar da k'yar Adama ta tabarta,dan sau biyu mutumin ta na tambayar ko taje?. A parlour ta same ta ita kad'ai, sai ta kara bin parlourn da k'allo, tabbas iyaye sunyi rawar gani,dan tsaf an fito da Aisha musamman parlourn. "Kai Allah sakawa iyayen mu da alkairi, Aisha tace "Amin kam, sam ban tunanin zan samu rabin kayan nan ba,Abba ga harkar gini shima yaya ga auren shi,Furera k'warai Abba abin alfarin mu ne wallahi... Kawai sai ta fara hawaye, tasowa tai ta dawo kusan ta, kan ta goge mata ido, "Adu'a zamu musu Allah ya kara musu bud'i,muma Allah sa su more mu haka. Kai ta k'ada tare fad'in "Amin. Nan ta hau kuma fad'in kamar ta koma gida take ji,gaba d'aya tai missing nasu. " Ga nan ce fane muje man ki d'an d'aura min daga inda kika t'saya y'ar K'anwata,,dan harara ta sau mata,kan tace"kima zage,dan ba zuwa zan nayi ba. Sai k'arfe biyar suka shigo lokacin suna kitchen,"Chief" tuni ta bud'ade gidan da kamshin girki,"kai Furera mijin ki zai k'washi gara fa, dariya tai kamin ta fara bawa Aisha shawarar itama ko"Grace so amazing catering creations" ta jona tunda "3month" ne. Tace zata tuntu6e shi kuwa,bari a d'an k'wana biyu. Da sallama suka shigo, sai d'ai ilahirin parlourn ya d'ebi kamshin abincin amare. Zama yai yayin da Ilyass yai hanyar "kitchen" yana zuba santin kamshi cikin zolaya. Shi kam gogan ido ya lumshe, sosai yana son macen da ta iya girki,yasan tunda Aisha ta iya toh prettyn shi ma ta iya. Ita kam ganin ana neman mata fitsara a gabanta yasa ta wanke hannu ta basu gu,a bak'in "kitchen" d'in ta makale,tare da k'allon mutumin ta yadda yake lumlumshe ido. Tsiyar Ilyass da yake wa Furen ne ya sa shi bud'e ido,sai warai a kanta,a hankali ya dago kai tare da zama d'ai- d'ai, kanta kasa tana musu murmushin kunya. Tabbas ance Wai ''in ka da k'yau, toh ka kara da wanka" toh shi kam pretty da tayi wankan ko batai ba tana burge shi matuka. Sosai yake son karamin k'yau irin na "Prettyn" shi,gashi ta iya dauk'ar wanka. Murmushi yai tare da k'ada kai, Ilyass bai bar kowa ba ashe? Hannunta Aisha ta rike tana fad'in "rabu dashi sis,kan suka zauna a kan kujera. Har suka gaisa da Aisha idon shi na kanta. Ilyass yace" madam, tashi mu basu gu su sarara,dariya tai kan ta k'ada mishi kai sukai d'aki. Tasowa yai ya dawo kusa da ita ya tsugune tare da d'aura yat'sanshi a kan le6en shi,ido kawai ya zuba mata,kamar wanda yaga sabuwar halitta. A hankali ta dago,tare da K'allonshi ido ciki- ciki,sai tai murmushi tare da kara kasa da kai. A k'alla ya kai kusan minti''5" kan tai magana,"ina yini Uncle... Sai yai shiru bai amsa ba, sai ta kara dagowa, kai ya k'ada mata,"Ba Uncle daga yau Furii,ki bar wannan a makaranta, K'allonshi tai, sai ya kara k'ada mata kai, "g'wara ki ce ma AAA, "I like it,, murmushi tai, kan ta k'ada kai. Zama yai akan "center carpet" d'in, tare da t'ang'washe kafarshi, kamar mai d'aukar karatu,shi kanshi yakan rasa ya ake yake rasa nutsuwar shi gun Furiin shi. ''Shin kina jin abinda nake ji a game da ke pretty? Kai ta dago,kan ta zuba mishi ido,halamar bata gane ba. Murmushi yai,kan ya sada kai kasa,yana mai fatan ta yarda dashi,d'uk da yasan mai wuya ne ma taki yarda d'in. "Pretty".. Ban san so ba sai a gare ki na samo, tun wani lokaci achan baya zamanin "school" nake jin irin " feeling " d'in nan, sai d'ai ban gane meye shi ba.. Kai ya dago, idon ta a kanshi,ba ko kiftawa, sai yai murmushi, "kar kiyi mamaki Furera Muh'd, Sai ya k'ada kai,kan ya tsare ta da ido,"I love you more than you will ever know.. And I can't never ever let you go again.. Ido ta rintse,tare da jin zuciyarta na tsanannta bugu, kan ta farga ta kara jin wani sautin wanda jinshi take tamkar waka yake raira mata dan sanyin muryar shi... Da sauri tai kasa da kanta kan tai ko'k'arin mai da kukanta. Ya Ilahii.. Da gaske ne abinda take ji kuwa? " ko d'ai yai batan kai ne? Kai anya? Toh ko wannan shine batun da yace zai zo mata dashi? A hankali ta sauke k'allonta a kanshi da shima yake k'allonta dan jin tai shiru,zuciyarshi ce ke faman buga mishi, tsoron shi d'aya kar dai Fure tace bata son shi. By Feenat Ja'afar. [4/19, 10:58 AM] Feenat Ja'afar 馃鉁嶐煆� : "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 15_"Ya ki kai shiru? Hope... Kai ta k'ada mishi, "zan yi shawara. Murmushi yai, " toh a son nawa za kiyi shawarar ko a aure na? Murmushi tai kan tace"d'uk Uncle..sorry. Kai ya k'ada, "zaki ji ni gobe toh,amini kara d'ai. Murmushi tai ganin ya ka'rkata kai. Firar su suka ci gaba da yi ya koma kujerar kusa da ita. Waya ya zaro,kan ya bud'e" gallery" "you gotta see this amazing pictures.. K'ar6a tai a kunya ce, ganin ta a ciki yai bala'in bata mamaki. Tana ina mey akai wannan photonan masu yawa? K'allonshi tai da halamar mamaki, gira ya daga mata tare da kafada,sai ta marairaice mishi. Sosai yake t'suma ta soyayyar shi,an ja aji kan ta k'arbi tayin ta, sosai ta kara burge shi, dan bai son budurwa mara kamun kai da aji, sai ya kara bata wani girma na daban. Gidan su yake mak'e kunya yaje,Amal kam kusan kullum ranarta ce," ice cream " cheese " komai ita,shi yasa sosai suka saba. Ko kad'an bai nuna mata shi masu dashi bane,asalima kusan kullum da mota d'aya yake zuwa mata,sam bai kaunar rayuwar fa-fa. Ba'a jima ba ya nemo k'anin Baban su da yayun Mama suka zo tambaya, sai da ya tace su kan yace su zasu,dan sarai yasan sauran yanzu sa raina mishi tushen su Furen shi,d'uk da d'an uwan Abban sai da ya tofa, sai d'ai ganin dattakon Abban su Suleiman d'in yasa ya gane d'an nasu gidan k'warai yabi ba wai dukiya ba. Ginin su Abba da ya Suleiman yake musu yai nisa sosai,har nashi a jiki yasa fili shima ya had'a, dan haya shima ya kama. Abba gidan shi na Zaria ya siyar wa yayan shi, tuni ya chake mishi kud'i hannu ya bashi,har da karin na bulo, d'uk da shi yana arzikin da zai iya rike iyalin gidan k'anin nashi amma yakanyi mamakin jajir cewa irin tashi,sam yafi son komai yai da gumin shi da k'arfinshi. Ahmad har gun aikin Abba yake zuwa in ya tashi a shago suyi ta fira,tuni sai ya k'wanta mishi a rai, dan ko motar da yake zuwa mishi da ita ka gani kasan d'an masu hali ne,sai d'ai bai da girman kai. Har aikin yakan ce zai taya Abba. Sai kawai yai mishi dariya,dan sosai dan gayu ne,ina shi ina aikin bak'in mai?. Umma take tambaya kan wai Ahmad yace gobe zasu gidan su gaida su Mama,tace ta bari Abban su ya dawo tukun,. Ko da Abban ya dawo Umma ta sanar shi yace ai ba damuwa,sai a had'ata da wani rakiya. A gado take suna waya kamar kullum, a hankali maganar ke fita wanda na d'aki ma sai ya kula kan yasan tana waya, idonta lumshe tana saurararon yadda AAAn ta yake zuba mata kalami masu sanyaya rai, tabbas yaci sunan shi da ta kira shi da"SAHIBUL KALAM". Takanji wani irin wutar sonshi na kara ruruwa cikin ranta,tun tana kunya har ta ware tana aika mishi da nata salon son. Tunda ta sanar shi ya fesa wa Mama cikin murna, tare da cewa Momy wai gobe zatai bakuwa. Sam bata kawo kom ba,sai tace mishi Allah ya kaimu,har abin dad'i tasa tai mishi,"Momy pls da hannun ki nake so,kai ta g'yada.. "Wannan k'wa wacece haka? Hala y'ar makarantar ku ce? Murmushi yai yace"eh kawai,dan yasan gobe da budiri a gidan nan. Washegari tana a gaban Amal tana g'yara mata g'yaran gashin ta,ta zira mata "gown" "cotton mai adon ja da yelo da ratsin fari,yana daga kayan da tai fitar biki. Tai k'yau sosai, tasa mata dan karamin hijab na yara fari da takalinta choge fari,ba laifi,ko a y'ar masu kud'i Amal ta fito,turare ta mika hannu ta bata wai ta fesa mata na "Lailatul sahrA", kan itama ta hau make-up, sosai tai k'yali iya k'yali, ga tasha filawar baki da jan Rani. Ak'wati ta bud'e tana neman kayan sawa, ta fidda wannan ta kara ta ajiye,idonta kan material ya kai wanda tama manta shi bata sa ba na fitar biki,guda uku yayan su ya siya musu da amaryar shi wai an kai office d'in su, dan " India " ne "Orange", da filawa mai hoton ganye green an gewaye shi da k'yallin"silver", murmushi tai dan ganin" favorite " na Ahmad "Orange" musamman a jikin mace. Zira su tai kan ta tsaya gaban mirror ganin yadda d'inkin ya zauna mata cif! Tuni ta hau d'auri, kai kace wata liyafar zata. Tana cikin d'aura "buckle" d'in takalmin ta "silver"data sa ranar "dinner" ta tsinkayi muryar shi Umma na ya shigo. Da gudu Amal tai waje. Tashi tai ta d'au g'yalen kayan da "poss" d'inta ta yafa,gashin nan yai tum-tum a keya. Sai taja g'yalen sama dan rufe gashin. Tasan ko ina zata shiga a kasar nan, dan d'ai- d'ai ruwa,d'ai-da'i t'saki. Umma ce ta leko,"gashi fa,kai ta k'ada, sai Umman ta karasa ciki d'uk. Lalle tana yabawa da ya'yanta,sosai kamar sunyi makarantar koyan k'walliya. "Kinyi k'yau kam,sai d'ai naso hijab,amma ba komai tunda an rufe kan, "ki gaida su sosai. Kai ta g'yada, kan ta fita,a zaure ta sameshi shi da mutuniyar,uwar magana,shi ko gajiya baya yi da surutun Amal. Sai d'ai suna ar'ba da ainashin madam d'in ya kame,d'aidan wani, wai ka'rkataccen wani, a fili ya furta "MashaAllah... Kai tai kasa dashi tana murmushi, bata nufa ba taji "flashes" a hankali ta dago,sai ya kara mata wani, kan ya d'auke wayan ya k'alleta, sai yasa a ajihu,ya rike hannun Amal suka jera, kamar wasu sabbin aure. By Feenat Ja'afar. 庐 NWA 9/29/16, 2:23 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 16_Shi ya bud'e mata, cike da y'ar kunya ta shiga,ya bud'ewa Amal baya. Cikin nut'suwa yake tuk'in, tamkar wanda baison su isa inda zasu da wuri, firar Amal kawai ke tashi, su kam murmushi kawai suke aika ma juna,yau kam, tamkar siriki haka shima take d'an kunyar shi, shi kam ganinta kawai yau na kara mishi farin ciki. "Prettyn Uncle.. Da mamaki ta ju ya,kan ta k'allo AAAn,sai ya daga mata gira, kai ta d'an girgiza tare murmushi, kan ta dan harari Amal wacce ke mata dariya," wa ya fad'a miki? Da hannu ta nuna Ahmad, wanda ke musu dariya,sai ta ju ya tare da d'aura kanta a kujerar tana K'allonshi cikin wata siga. Yana "driving" d'in ya ju yo kad'an, sai ya ga ta zuba mishi ido tana d'an murmushi. Sai ya daga idon shi halamun "ya akai? Kai ta d'an k'ada mishi tare da sauke ajiyar zuciya. Sai ta koma kan titi tana k'allo,wani irin farin ciki ta ji yana rat'sata. K'allo shi tai lokacin da ta ga ya tsaya a gaban wani waje kamar ''company" kato, sai yai murmushi, kan yace "mun zo,yau za kiga Mama da Momy da sauran k'anne na. Yake tai mishi, kan ta kara k'allon yanayin gidan tun kan ma a shiga," Ya ilahi!! Ina take shirin shiga? Mey ya sa Ahmad bai nuna mata shi d'in d'an masu dashi ba ne har haka?. " Gate" ne guda biyu a gidan,tafkeke ne sosai, dan zai kai g'wan-g'wani d'aya, ita kam ba mai shige-shige bace,sai d'ai gidan su k'awaye masu d'an hannu da shuni,karara k'auyencin ta ya so ya fito fili,bata tunanin ta ta6a shiga irin wannan gidan a rayuwar ta. "Horn" yai,sai taji an zuge ta ciki. "Subhanallah" shine kalmar da ta ambata a bak'inta,lalle duniya na inda take. "Flowers" d'in gidan su suka fara mata"welcome" wanda suke a t'sare an musu "decoration " masu ban sha'awa, d'uk gidan shimfid'e yake da "interlock" tsari hudu ne a gidan,wato "parts" tsaf sai ta karaya,da sauri tai kasa da kai gabanta na fad'uwa. Ba d'ai Uncle Ahmad d'an gidan "Alhaji Abba Ahmad" bane dan k'wangila? Sosai tana yawan jin sakon gaisuwar shi musamman a radio in Umman su ta kama, sannan ana yawan fira dashi in harkar k'wangilar da aka bashi ta kammalu musamman ta jaha. Kai ta dago,d'ai d'ai yana "parking" kusa da wasu "arnun" ubansu motoci,hankalinshi k'wance, sai ma murmushi da yake ma Amal da take tambayar shi nan ne gidan sun? Ummi yai ma waya,kan gasu kofa, k'allota yai lokacin da ya gama wayar,"muje koh? Kai ta k'ada mishi, sai ya fito ya bud'ewa Amal,kan ya karaso ta ma bud'e, sai ya karasa bud'e mata, d'an murmushi tai a takaice sai ga nan Ummi ta fito. "Sannun ku Bros, da fara'ar ta tai gun su, fara ce,kana ganinta ka ga Ahmad, har fara'ar su d'aya. Itama da fara'a ta k'alleta, sai ta k'alli Amal da tai wajen ta,dan fa d'uk surutun ta toh a bakon waje miskila ce, ummin ta d'an riko hannun Amal d'in sai ta make kafada,sai ta mata murmushi tare da shafo fuskarta da fad'in "fine girl". Murmushi yai,shi yasa yake son Ummi a d'uk k'annen shi, ita kad'ai ya yaba da nutsuwar ta,sannan yasan ba zata bashi kunya ba. Bangaren Momy suka fara shiga,kawai sai taji gabanta na fad'uwa tun da suka doshi ciki. Kana gani kasan gidan y'an boko ne,ko ina cikin tsari da k'yau, sosai yai k'yau, kasan naira ta daku. Rukayya kawai ke parlourn tana "chat" a "Facebook" shine a gaba,da sallama ya shigo, a chan ciki ta amsa,dan jiya tasu ta had'a su. Bai bi ta kanta ba yai d'akin Momy. A y'atsine ta k'alli su Ummi,daga sama har kasa ta ke k'allon Fure wacce Ummi take ce mata ta zauna. Sam a d'uk y'an gidan basa shiri da Ummi,dan ko k'allo suke ita ke damun su da su tashi suyi sallah,gata sam bata raga mata,shi yasa basa shiri,kai ta d'auke, da har zata tambayi Ummin wacece ita??? Da fara'a Momyn ta fito tare da shi, kai Furen ta duk'ar kasa,ita kam Momy har ta zauna tana neman inda ta ta6a ganin Fure. Sai ta amsa tare da k'allon Ahmad, "daga ina bakuwar taka tazo? Dan sam ita bata ga halamun wata hamshakiyar bakuwar da har ta shiga kitchen dominta ba, duka-duka kayanta basu wuce dubu 7 ba har g'yalen. Kai ya fara sosawa yana d'an k'allon Ummi, sai tai murmushi,kawai ba rufi tace" Momy budurwar bros ce fa.... Wayar hannun Rukayya ce ta fad'i kan tiles,wanda yasa d'uk suka zuba mata ido,banda Momy dake k'allon Fure,a dirare tai mata k'allon wulakanci,"ban gane budurwa ba AAA?? A d'an takaice Fure ta juyo,dan tambayar ta bata mamaki,sai d'ai mey,tabbas ta gane matar nan,ita ce wacce Ahmad ya d'akko ta har suka kusa maketa. Tabbas tai matukar tsorata da yanayin Momyn,toh amma ya akai ta manta da Momy uwar Ahmad ce har tazo gare su? Ido ta rufe,dan kam bata ga halamun sassauci a gun Momy ba tun wanchan karan bare yau. Dagowa tai a hankali ta k'alli Ahmad d'in, dai-dai yana rokon Momy da hannu kan tai hakuri kar ta bashi kunya. Baki ta ta6e,kan ta tashi tai d'akinta. Sai Rukayya ma ta tashi ta bita,tare da d'allawa Fure harara, koh ta kan wayarta da ta fad'i bata bi ba. Sanin hali, yasa Ummi tai saurin kat'se Fure da cewa"muje bangaren Mama Auntyn mu, murmushi ta k'ak'alo, wanda kana gani kaga na dole. Sai ta k'allo Ahmad,kamar tace bazata ba,dan a gun mahaifiyar shi ma bata samu k'ar6uwa ba bare kishiyar ta? Sai d'ai yadda ya marairaice mata yasa ta tashi,sai ya ruko hannun Amal. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 Apr 20 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 17_Kuka Rukayya ke ma Momy,ita kuma na aikn lallashi,"ki ma bar 6ata hawayen ki akan wannan mummunar, zai zo ya same ni ne, wato dan t'sabar yaso ci min fuska shine harda sani na zage a "kitchen" wajen girkawa wata shegiyar da koh a y'ar aiki bazan d'auke ta ba.. "Momy ki ganta fa,daga gani sam bata ma kama kafar dacewa dashi ba, amma ni ki dubi irin yadda ake kaiwa rana akan yaja soni yaki. Sai ta kara fashewa da kuka, tuni ta kara tunzuro Momy, "ai ni na miki alkawarin zama Matar Ahmad bah? Kai ta k'ada. "Toh kiyi kamar ma baki ga ba. A parlour suka tarar da Maman,rike da waya a hannunta, cikin nutsuwa da fara'a take k'allonsu tana cigaba da wayar,ita d'ai Fure a dirare ta zauna a bak'in kujerar,dan sam bata ma k'alli Maman ba. "A,sannun ku da zuwa, a d'an hankali ta dago ta k'alli Momyn,Ahmad na zaune kusan ta,kamar zai shige mata,kamarsu har ta 6aci da Maman sama da Ummi,da sauri ta sunkuyar da kai tana murmushi, kan a hankali tace"yauwa, sai ta zamo daga kujerar ta gaida ta. Ganin haka Amal dake kusan Ahmad ma ta gaida Maman. Da mamakin ta sai taji ta amsa cikin mutunci harda tambayar y'an gidan su. Amal Mama ta ruko," ya sunan y'an matan, da fara'a Ahmad yace"Amal mama, sai tai murmushi, "Aiya,ina ta samun labarin Pretty, yau gani ga ita. Kai ta kara kasa dashi cikin kunya. Lalle abin da mamaki,anya ba mama bace Maman Ahmad?.. Maganar ta ne ta kat'se tunanin Fure, "ki saki jikin ki fa, d'an kinzo gida ne, ita d'ai murmushi kawai take. Ummi tace ta kawo musu abin sha. Sosai mama ta ba ma Fure mamaki,dan mace ce wayeyya,ga saukin kai, sannan fara'arta ita tafi komai sa Fure nutsuwa. Dan har ta shiga ciki ita da Amal da ta yarda fuskarta sake,ta yiyu anan Ahmad da Ummi suka gadi sakin fuska. "Auntyn mu kisha fa, ga nan lodin abinci na jiran ku. Murmushi tai mata,bari naje na dawo,kila bros ni ma tana kunya ta ne. K'allon Furen yake da murmushi, sosai Ummi da mama sun wanke shi gun Fure. Tana fita ya dawo kusan ta ya zauna,tare da miko mata lemon, k'ar6a tai tana k'allon shi,fuskarta da abu biyu zuwa uku. Na farko mamaki,na biyu murmushi, na uku tsoro. A rayuwa taki jinin wulakanci, ta kuma tsani t'saki. Gashi d'uk ta gani a bangaren Momy. Sosai sun mata karamci,har bata ma san ta saki jiki dasu ba,musamman Ummi. Da zasu tafi mama ta cikata da sha tara ta arziki,har kofa ta rako ta,sai d'ai da yace suyi ma Momy sallama sai da taji dan dar! Suna zaune a parlour ita da Rukayya sun cika sun bat'se, sai harara Rukayya ke aika ma Fure,koh da yace zasu tafi, a wulance ba tare da ta k'allo Furen ba tace"ta gaida gida. Abinci ma bata samu ba bare sinkin mai. A mota tai kok'arin d'annne ranta, ko'k'arin shi kar ta sa abin Momy da Rukayya a rai,shi yasa yake ta d'auke hankalinta da fira. Har gida suka shiga dashi,yana rike da t'sarabar mama. Har suka rabu bai ko mata maganar su Momy ba, amma Allah- Allah yaje gida ya jima Ruky. Amal ke bawa Umma labarin gidan da abinda suka ci,har sai da g'wa6e mata baki, dan sosai Umma bata son yawan magana. Sai dai ita Fure d'uk jikinta yai sanyi tunda suka dawo. Ido kawai Umman ta zuba mata. Su Hassan ne suka bud'e kayan suna shigo wa,baki sake Umma ke bin kayan da k'allo, A hankali ta fara daga su, Atamfofi biyu ne da less, d'uk da batasan kud'in su ba amma taga ana daga irinta a na kayan Aisha, tasan masu uban t'sada ne. Ga wani uban Le's wanda zai kai ashirin zuwa 30,ga "cosmetics " har da kud'in da mama ta bawa Amal. D'uk sai jikin su yai sanyi,Umma ta k'alli Fure,Furen ta k'alli Umma,kowa ya kasa cewa komai. By Feenat Ja'afar. 庐NWA Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:24 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 18_Suna nan har Abba ya shigo ta tashi ta tafi d'aki, a dirare ta k'wanta, anya zata tila kanta a irin wannan gidan kuwa? Sam bata ga halamun samun k'wanciyar hankali a gidan ba sai gun mama,toh ya sauran y'an uwan nashi zasu t'ar6e ta? Tana tsoron wukanci,musamman a gun mai kud'i. Anya zata auri A A Ahmad?... Tuni wata zuciyar tace "Ya ya zakiyi da kaunar shi fa? Shi kike so ba wani abinshi ba, sannan dashi zaki zauna. Da wannan tunanin yau tai bacci. Washegari sukuku ta tashi,d'an ma wai bata fad'a wa Umma mey akai ba. Ya Suleiman Umma ke nuna wa kaya wanda ya shigo gaida su, d'uk yaga jikinta yai sanyi, sai yake tambayar ba'asi tace ita wulakancin masu kud'i take gudarma y'arta. Sannan tana gudun bak'in jama'a. Baki yai ta bama Umman,kan ba komai sai alkairi. Da mamakin ta da Abba yaga kaya sai bai ce komai ba sai fatan alkairi, hakan yasa itama Umman jan bak'inta tai shiru. Sosai take jin fad'uwar gaba in ta tuno su Momy, Anya kuwa? Sai d'ai so da kaunar AAA takan mantar ta d'uk wani abu da zai je ya kawo. Shikam yana komawa d'akinshi ya shige,dan yasan sarai idonshi yau,idon Momy. Sai d'ai ita da taji shiru da kanta tazo jin ba'asi. Dowawar shi daga masallacin isha'i kenan ya k'wanta tare da bud'e hoton Fure na dazun yana k'allo. Kofa ya ji an turo, ba ko sallama, sai ya dago,dan dabi'ar y'an gidan ce haka yasan,irin dabi'ar da ya t'sana, sai d'ai da mamakinshi yaga Momy,tashi yai tare da k'akalo mata murmushi, harara ta aika mishi kan ta nemi waje ta zauna. "Wato dan ka'rma nai magana shine ko abinci baka je ci ba? Toh ni na zo, sanin k'anka zancen Rukayya ne a gidan nan, ba wai na wata chan ba,amma abin mamaki,yanzu Abban ku wai yasan da zance,kenan har ina gidan nan aje maka tambaya ban sani ba koh? Kasa yai da kai, hakuri kawai yake bata, dan yasan Momy, in ta huce ya lalla6a kayarshi. "Ba ma wannan ba, tukun ka kula da k'yau kamin ka so yarinyar nan har kake neman shigo mana da ita gida? K'allonta yake, sai ya girgiza kai, "na sani ai.. "Momy ina sane fa,Furera mun juma, ni ne kawai ban fad'a ba... "Ka rufe min baki, in haka ne Rukayya ma kun juma ai,kuma ni ita na sani. Kai ya K'awar, kan yace"amma Momy tun ba yau ba na sanar ki Rukayya ba kala ta bace fa,dan Allah ki bar zancen ta,taje itama ta samu miji, ni na samu m... "Ahmad, cikin t'sawa Momyn ta kat'se shi, " ni zaka ciwa fuska? Kai yai kasa dashi, yau zazzagar arziki ta mishi,harda dan ba ita ta haifo shi ba.. sai ta tashi tai waje,yana ta kiranta ta doko kofa. Kai ya girgiza, a gaskiya bai son fushin Momy,amma akan Rukayya zai yi komai dan ganin ba'a manna mishi ita ba. K'wanciyar shi yai, yana mai tunanin iko irin na Momy, tabbas lokaci yayi da zaiyi "breaking" wannan t'sarin na shigo da y'ar talaka zuri'ar su, shi Pretty yake so, kuma ita zata zame mishi mata da ikon Allah, fatan shi Allah ya taya shi yakin nan,dan maganar Momy da ita ake gudanar da komai a gidan. Bangaren Mama yaje cin abinci,tasan yau kam za ai haka, amma ita y'ar k'allo ce a t'sakanin su. "Ya suka je gida? Baki ya wage,tuni sai ya ji ya ware,"Mama lafiya. Sai da ya gama ci kan ya k'allo Maman tashi, "Mama ai d'ai tayi koh? Murmushi tai,tare da ajiye waya, "tayi kam,sai d'ai ya zakai da Rukayya Ahmad? Maman yake k'allo da nazari,chan yace "Mama sam Rukayya bata min ba,Momy ce d'ai ta dage... Sai jim, "amma Mama ki taimaken wajen ka'rfafa Furera gun Abba,nasan Momy shi kad'ai zai iya hanata yi min dole. Kai ta k'ada, sosai take tausayin yaran ta,musamman yadda suka k'waso dabi'ar Momy goyon Momy, guda d'aya ya fita zakka ciki, akan Ahmad kam baza ta bari Momy tai nasara ba InshaAllah, a wajenta da talaka da mai kud'i d'uk d'aya ne. Sai d'ai tace ya lalla6a Momyn. Sosai ya ji dad'i, shi yasa yake kara kaunar Mama. Dan tana son abinda yake so. Washegari kamar kullum yazo gaida ta tai banza dashi tare da juyar da kai, sai yai murmushi, kan yaje inda ta juya, tsugunawa yai tare da dafa hannunshi a cinyarta, hakuri ya fara bata,kan ba yadda ta d'auka yake nufi ba. Da k'yar ya samu ta d'aina fushi,sai dai har yanzun tana kan bakarta na Rukayya ta sani,k'yaleta yai tare da lalla6a ta,dan a rabu lafiya. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:27 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 19_Tun daga wannan rana ya gama fito wa da Fure ainashin shi waye,tarihin su,fa komai,har hamdala tai a zuciyarta da taji ba Momy ce ta haifo shi ba,hakan yasa ta ware suka cigaba da fahimtar juna. Yanzu kam fachaka ya fara mata,sai d'ai kullum in ya bata sai sunyi fad'a, wataran ma sai d'ai ya kai wa Umma da kanshi. Sai dai sosai yana jin dad'in yadda take nuna abin duniya bai dameta ba. Chargy yasa a parlourn Momy yaje masallacin azahar,Rukayya ce ta shigo parlourn dan zaman charting. Sai ta kula da wayan shi,kawai sai ta raya mata bincike cikinta. Sunkuye take da kai tana murmushi ta d'an rike g'yale,"eye lashes" nata sunyi zara-zara, hoton ya manna a "screen" na wayar shi, "Mtsww,banza kawai, sai ta k'ada kai, kawai sai ta shiga cikin "gallery" ta hau "deleting" d'uk wani hoton Fure da yai "editing" yasa "pretty". Sai da ta goge d'uk "foldern'' kan ta shiga "contact". Bataga wani sunan mata ba sai na y'an gidan, ko numbern ta babu,sai ga "pretty" ya fito, wayarta ta d'akko ta k'wafi numbern tana surutu ita kad'ai, tana gama k'wafa tai "deleting", ta ajiye wayar kamar ba'a ta6a tai ta zauna. Bai shigo ba sai bayan la'asar, shima sai da ya tabbatar ya gama shirin zuwa gun Fure yazo cire chargy, "blank" ba komai kan screen d'in, sai yai tunanin "memory" ne ya goce,yana k'allonta yai kamar bai ganta ba,zama yai g'yara memory, ita kam dariya take kunshe wa, yanayin shi d'uk ya sauya,fuska had'e ya k'allo ta,da sauri ta gintse dariyarta ta d'aina K'allonshi. A masife yai yo kanta, "Kina hauka ne?...Yaushe na zama abin wasan ki? Tashi tai tana k'unk'uni, "mey na ma toh? Wayar ya k'alla,ji yake kamar ya rufe ta da duka,ihun da yake wa Rukayya ne ya fito da Momy, yana ganinta bai hana ya gama sauke komai ba, "lafiya? Kai kawai ya gad'a yai waje,yana fita ta hau dariya. Abinda y faru ta fad'awa Momyn,tace ta mata d'ai-d'ai. A mota t'saki kawai yake,Allah ya so shi ya tura su "system" nashi, a hakan zai yarda da auran Rukayya? Yarinya marar K'wak'walwa? Yai t'saki. Da k'yar ya seta kanshi kan yaje gun Fure. Ita kam Rukayya yana fita sai tai tunanin ba gun Fure za shi ba, cewa Momy tai tana zuwa, d'akinsu tai,ta k'wanta kan ta fara kiran layin Fure. A zaure suke,kamar kullum suna tad'in su cikin nishad'i,ga Amal a gefe tana mota. Wayan Furen ne tai kara,sai ta k'allo shi da murmushi, kai ya k'ada mata, dan ko shi aka kira in dai suna tare sai ya nemi izinin Pretty kan ya daga. Number ce, cikin nutsuwa tai sallama, sai d'ai ita daga chan da zagi ta bud'e taron. Yadda fuskarta ta sauya ne yasa yake k'allonta, sai ta k'ak'alo murmushin dole tana cigaba da sauraran Rukky,batasan speakern yana d'an ji kad'an ba. "Kina magana da Rukayya matar Ahmad bada jimawa ba.. "Y'ar matsiyata kawai, ai nasan kinsan ba ajinki bane shi, ki fita gona ta,dan Ya Ahmad nawa ne ni kad'ai... "Nice zabin y'an gidan nan, so tun wuri kisan inda dare ya miki.. Tashi tai,da hannu take nuna mishi tana zuwa,tana shiga d'aki tana jin yadda take aikawa iyayenta zagi. Murmushi tai, kan tace "Furera ikon Allah,toh a gaskiya bazan iya musayar yawu da wacce bata isa inda take tunanin ta isan ba... "AAA na Fure ne kad'ai, wallahi k'walelen ki,tunda anyi k'wantai a fad'i haka man... " uban wa yai k'wantai? T'saki Furen tai, kan tace"Allah kat'se miki wahala, dan kin haukace... Kit ta kashe wayarta. Kanta ta g'yara,kan tai zauren d'auke da murmushi, kawai Rukayya y bada,amma da mamakin shi sai tace wai "wrong number" ne,shi d'ai yaji sunan Rukayya a wayar,kawai sai ya share suka ci gaba da tad'in su. "Sai rowar hoton nan ake min,yau d'ai a d'akko min naga. Kai ta k'ada, kan ta tashi, dama dan ya d'au number ne, cikin sauri yai copying zuwa wayarshi yai dailing sai ya kashe da sauri. Har ya tafi bata fad'a mishi komai ba. Yana zuwa parlour ya zauna,lokacin Rukayyan tasa chargy, dailing ya fara,sai yaji a rufe,kawai sai yaje ya duba,a rufe take,dan ya tabbatar ya k'unna, sai k'wa ga kira ya shiga. Da gudunta ta fito,a zatan ta,murmushi kawai yayi,ya ajiye ya wuce. Sai d'ai a ranshi ya sa zai bawa Rukayya mamaki,dan ko zata mutu bazai aureta ba. T'sawan kusan wata 7 yanzu kenan da had'uwar su, biki saura wata d'aya dan tana exams, amma naira biyar bata ta6a rokarshi ba, shi yasa yake d'aukan Fure ta daban cikin mata. Hakan yasa yau yace zai g'wada ta, suna a zaure suna tad'in su cikin so ya k'allota. "Pretty, kai ta dago tare da amsawa, sai ya k'alli Amal da ta zuba musu ido,sai yai murmushi, " ga nan biki sai karato wa yake amma baki nemi komai ba. Murmushi tai, kan ta k'alli gefe, "Yanzun kam bana bukatar komai gaskiya, in ma za'a bukata su Ummi zasu ma magana. K'allonta yake, yasan in ya biye mata da gasken bazata tambaya ba, "toh ke da kanki ba ki bukatar komai? Nasan dasu Ummi, da pretty nake. Murmushi tai, kan ta k'ada kai, "eh,na sani. Kai ya k'ada, sai ya tashi yace ta d'an jira shi, ya nufi mota. Da babbar leda ya dawo,d'auke da k'wali a leda. Ita d'ai nata ido, "karan nan pretty ban son musu, kai ta daga, sai ya ajiye mata ledar kayan a gabanta kan ya zauna da dayar. Zaro k'walin yai,sai ga nan waya zankadediya ta fito, sai ya cire recit d'in kan ya mika mata. Idon shi take k'allo, sai yasha mur,dan yasan yanzu sai tai mai musu, k'ar6a tai kan ta tsaya neman ba'asi. "Ta ki ce,en bana son musu, wayar take juyawa,koh wata uku bai yi da siya mata ta hannunta ba,sai d'ai ba bak'in magana. Takalma ne kusan kala uku masu k'yau dad'in zuwa "dinner". Sai kud'i aciki masu yawa, text taji ya shigo wayan ta,wai ta amfani da kud'in. Sai tai murmushi, ta kaima Umma su,dan dama takalmi da sarka ne kawai bata siya ba. Ginin su Abba fenti kawai ya rage, Umma tafi kowa murnar su tare ko dan auren Fure. Ana saura k'wana goma biki ya sanarta y'an gidan su zasu suzo kawo kaya. Gidan Adama taje dan Aisha tana fama da kanta suka musu pepee chicken. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 20_Ganin kayan auren Ahmad ba karamin kuka Rukky tai ba, bori take na gaske,wannan karan kam anfi k'arfin Momy,dan Abba ya shiga zancen dumu dumu. Hakuri kawai take bata,kan ko ba yanzu ba kamar ta auri Ahmad an gama ne. Washegari mota hudu sukai dan zuwa kai lefen Fure,daga nan zasu kai na d'ayar amaryar k'anin Ahmad. Tunda aka t'saya a kofar suke tantama, "anya nan ne? Waya Aunty JIDDA ta d'auka, kan ta kira Ahmad d'in, "ka yi k'watancen nan d'ai-d'ai kuwa? Jim tai tana sauraran shi, kan ta k'alli sauran y'an uwan nasu da y'an uwan iyayen su. "wai fa nan ne,har nanata min yake wani gidan kasa mai zaure.. Tai k'wafa,tunda naji artabun da ake dashi nasan ba haka aka bar yaron nan ba,yanzu ki duba wai gidan da zamu kai wannan uban kayan? Wato shi yasa yake boye ta fir yaki kawo ta mu gaisa. T'saki Huwaila (Sa'adatu)tai, "Aunty shi fa ya jiwo, ku y'an aike ne, suma sauran d'uk jikin su yai sanyi,banda y'an uwan mama, wanda ta sanar su komai. Bai fi mutum uku bane sukai sallama,kowa fuska d'aure,sosai suka rainawa Ahmad, karewa gidan k'allo suke,Fure dake d'aki tana leken su ta window, daga mai ta6e baki,sai mai y'atsine fuska,kalilan ne aciki wanda fuskarsu a sake, zama tai a kan katifa, ganan abinda taki jini,raini,wato sun raina mazaunin ta? Zaman kirki basuyi ba aka basu tsarabar su da tukuici,y'an uwan mama ne suka k'ar6a harda godiya,sukam tuni sunyi waje. Allah ya so su makociya d'aya ce,sai y'an uwan su na Zaria, dasu Adama da Aisha, kowa jikin shi yai sanyi da dangin mijin da Fure zata aura,barin Umma. Kaya ne gasu kamar ba gobe Ahmad yasa aka tulo su,sai san barka. Da dare suna zaune har da Furen ana nunawa Abba kaya, ita d'ai Umma roko take ai ai fenti su tare ko a daina ma y'arsu gani gani. A ganinta wai Tuwan girma miyarshi nama. Murmushi Furen tai da d'an guntun hawayenta, kan ta k'allo su Umma, "Umma d'an guntun gatarinka wai yafi sari ka bani, ni d'ai ina alfari da tushe na... Hawaye ta goge, k'warai auran nan ya fice mata aka, ji take tamkar tace ta fasa. ''Abba dan Allah ko an gama komai kar ku tare sai bayan bikin nan, Umma nan ne asalinmu, dan Allah a min wannan alfarmar, mu zauna anan, ba ruwa na da zancen su, tunda d'ai shi ya ji ya gani. Murmushi Abba yai, shi yasa yake alfahari da Furen sa, d'uk D'a na k'warai mai kishin tushen shi ne k'warai. Kai ya jinjina, kan ya k'alli Umma da jikinta d'uk yai sanyi. "Nima nayi tunanin nan,kiyi hakuri Umman su,kiji kawai ki kiji, har a watse lafiya. Kai ta jinjina, sai Furen ta basu waje,bata jima da shiga ba sai ga kiran Ahmad d'in. Yadda take amsa wayar yasan tabbas tana a damuwa, wanda yasan bazai wuce na y'an gidan su ba. Dan yanzun barin cikin gidan suna ta kace nace akan gidan su Fure,su basu ga abin zagwadi a y'ar gidan ba da har zai ki Rukky. "Kiyi hakuri pretty, ni ne mai auren ki,InshaAllah zaki same ni mai rike amanar ki cikin aminci. Da mamaki take sauararen shi, da sannu sai da ya wanke laifin y'an uwanshi cikin lumuna, har taji zata iya ji ta gani wajen zama dasu. Haka k'wa akai,gini ya kammalu amma Abba yace sai bayan biki, y'an uwa wasu na neman ba'asi sai yace musu kawai ba dalili. Fatan shi Allah yasa alkairi cikin auren Furen shi,kodan mutuncin Ahmad a gun shi, ko da Ya Suleiman yace ma Adama su su tare sai tace mishi abari su tare dasu Umma. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 21_Gaban madubi take a gidan Aisha,kowa yana yaba yadda tai k'yau. Yake kawai take musu,sosai itama tasan tai k'yau, "net" ne "brown" da ratsin "golden" na doguwar riga yai mata cif-cif. An nada mata g'warg'waro shima "golden", a d'aya a takalmin Ahmad da ya bata kan biki ta d'au wani ubansu "golden" ta sa,kai kace da "gold" akayi shi,rike da "poss" irin takalmin. G'yaran jikin da ta samu ne yasa fatarta kara gogewa ta dawo ruwan itama "golden" d'in, sosai ta barar da k'yau a wannan rana, idon nan kad'ai ke fari kamar tai "fixing" na "lashes", ga yasha "Eye shadow" abin ba'a cewa komai, a gaskiya in kaga Fure a ranar bazaka d'auka ba bikin wata y'ar Attajirin bace,komai ya ji,an t'sat'so k'yau sosai. D'uk wani sukuku take jin ranta tunda aka d'aura auren. "Dinner " za su, wayan ta ke kara tsohuwarta ta da, sam a ganinta in ta rike sabuwar kowa yasan daga gun shi ne, sai ta bari sai ta shiga daga gidan shi ta fara amfani da ita. Cikin sanyin murya tai mishi sallama. Sai ya jingina a jikin kujera jin muryar har k'wanyar kanshi,Ilyass dake tuki yai murmushi. Har cikin gidan Ilyass ya shiga,kan amarya ta fito da sauran k'awaye. Kanta kasa suka fito ita da Aisha da Adama, da kanshi ya fito daga gaban motar ya bud'e mata gidan baya. Shima sai ya zaga d'aya bangaren, dariya suka hau mishi,sai Ilyass yace Aishan ta shiga gaba suje Adama ta jira mijinta, sauran suka shiga suma mota. Tafe suke Ilyass na ta musu shakiyanci sukam sai murmushi suke, a hankali ya k'allota,sai tai kasa da kai tana murmushi. Yasha riga malum-malum na farin shadda,an mishi aiki da zare brown, yai k'yau sosai,hular shi ma "brown" sai kamshi yake zubawa. Sosai yake k'allonta dan tun jiya rabon da ya ganta har aka d'aura Aure, wanda ita har kunya ya fara bata. Hannunta yake k'allo, wanda suka sha "bangles" manya kamar na gold da zobuna manya. Ga kunshin nan ya hau kasan su sai suka mishi k'yau. Bata aune ba taji shi rike da y'atsunta, tuni taji wani abu ya tsirga mata,yayinda gogan ajiyar zuciya ya saka, yasan ya kare iyakar Allah sosai,yau ne farin ta6a hannun macen da ba muharama sa ba, gashi yau ta zama mallakin shi halali. Shi ko wannan "pre- weeding" pic d'in da ake d'auka a rungumi juna sam bai mishi ba, dan a ganin shi duk abinda zai kai ka ga sa6on Allah sam bai burge shi. Yadda take lumshe ido d'ayan hannunta na kan bak'inta sai ta kara kawatuwa mishi, dole yace"D'ukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai, ya gode Allah da yau Prettyn shi ta zama tashi a yau. Har suka isa gun "dinner" yana rike da hannuntan. Suna tsayawa akazo bud'e musu kofa, sai ya daga musu hannu kan shi zai bud'e mata, hooo, kowa ya birgisu, hannu ya mika mata wai ta rike ta fito, ganin an d'aura yasa ba musu ta bashi, sai d'ai fir yaki cika mata hannu,a haka suka jera cikin "Hall" d'in kanta kasa d'auke da murmushi. Tuni su d'ayan Angon sun hallara da amaryar shi su kawai ake jira. "Flashes" ake basu ta ko'ina, Fure fa ta bada kala,dan ko y'ar masu kud'in bata fita da kom ba sai d'ai k'yau. Su kansu su Aunty JIDDAN sai suka ga shigarta tafi k'yau, amma haushinta ya hana su yaba. Barin Rukayya ganin su rike da hannun juna kamar ta kurma ihu. An fara program aka umarci ango da Amarya su fito su yanka "cake". Hannunshi na kan nata suka yanka, cikin jin kunya ta sa mishi a baki, da wasa shima yake kokarin sa mata ya dan shafi " lips " nata,kowa ya zuba musu ido,ba kunya ya kai hannu zai goge mata sai ta dan k'alleshi, mai hoto kuma ya d'auka a hakan. Sosai sunyi k'au, Ahmad yana ta barin SO a hall, yayinda masu t'saki nayi masu murmushi nayi,masu musu tafi sunai,su Rukky kam baki ta ta6e. Rawa aka ai bayan an cigaba da "program''. Kai ta girgiza mishi, sai ta burge shi, ita kam d'ayar amaryar sai taka rawa take ita a dole wayayya ba ko kunya. Ana tashi ya k'arbi "key" wai shi zai kai matar shi. Sukam su Ya Suleiman nasu dariya ce. Ba musu ya mika mishi mukulli. A hankali yake jan su a sabuwar motarshi da siya musu shi da Prettyn shi, ita kam yau d'uk kunya yake bata. Shi yasa kanta na k'allon glass d'in gefenta da murmushi. Ba tasan irin farin cikin da yau take ji ba. Ga wata kauna da taga Ahmad na nuna mata, wanda a ganinta koh ita ta isa sata tai zaman auren shi. Wakar shi ta kullum ya sauya, tuni ta fara taken "Nothing gonna change my love for you.. If I had to live my life without you near me The days would all be empty The nights would seem so long With you I see forever oh so clearly I might have been in love before But it never felt this strong Our dreams are young and we both know They'll take us where we want to go Hold me now Touch me now I don't want to live without you. Jingina tai tare da lumshe ido cikin murmushi, sosai baitin ke shigarta,sai ta tuno wani lokaci achan baya,kawai bata nufa ba taji ta dara,har hak'waranta suka baiyana, d'ai-d'ai taka burkin da gogan yaci. Da sauri ta bud'e ido jin sun tsaya,dan baici ace sunzo ba. Taga titin ba abinda ya faru, sai ta juyo da k'allonta gare shi,tagumi ya da hannu d'aya yake k'allonta, sai ta daga mishi gira halamar lafiya?... Kar ya fad'arsu yasa ya taka birki. Kai girgiza mata, tare da sauke ajiyar zuciya. Shi kanshi bazaice ga adadin son da yake ma Pretty ba,sannan wakar nan tana kara rura wutar Sonta ne a kullum. Matsowa yai da fuskar shi d'ai-d'ai tata har numfashin su na had'uwa da na juna, sai taja tata baya tare da K'awar da kai tana murmushin kunya. Hannu yasa ya juyo da ita,sai tai kasa da kai, a hankali ya rage "volume",tuni ya hau tsuma zuciyarta da kalamai wanda bata ma san ta dago tana k'allon shi ba. K'warai sakon aiken ido yafi isa cikin sauri, hakan da tai sai ya bashi damar aika sakon shi tanan. Gaba d'aya sai da ya gama kashe mata jiki da tad'in shi,wanda ita bata san ya iya irin shi ba,sosai yakance yana Sonta har ba iyaka, amma kalaman yau na daban ne. Karshe sai da ya sada ta da jikin shi ya samu sa'ida,ita kam lum tai kamar ta samu pillown ta. Chan kuma sai ta hau kiciniyar K'wacewa, d'uk da glass d'in baki ne. Dagowa yai da lumsassun ido yana duben ta," yanzu sai gobe za'a kai min ke? Kai ta lang'wa6e mishi, cikin marairaita. Sai ya zuba ma bak'inta ido wanda yasha janbaki mai k'yau "brown'' mai shekin golden, ganin ya kawo fuskarshi tata yasa ta saurin rufe ido. Sai ya tsaya k'allonta da murmushi, ganin yadda ta wani tamke ido,hannu ya kai kan idon sai ta bud'e a hankali,bata aune ba taji sabon al'amari, ba shiri ta kara rufe idon. Shikam kamshin strawberry ma kamar yake ji a bak'in,ga dan zakin "lips" d'in nata. Dan kanshi ya batta,kan ya hau cigaba da kallonta, idon nan a rufe... "Horn" d'in su Ilyass ne da har sun gama sa jama'a gashi har sun cimmusu suna nan. Take sai tai gefe da kanta ta boye cikin kunya,kai ya k'ada, kan yai murmushi ya tada mota. Yasan yau sai d'ai ya toshe k'unnenshi agun Ilyass,tunda har ya cimmasa. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 23 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 22_Har suka rabu taki bari ya ga fuskar, Ashe AAA haka yake? Hmm ita kuma ga kunya. Haka ya hakura sukai sallama yana fad'in "I Love you... Jim tai,kan ta shiga gida kamin ya k'ada kai shima ya wuce. Lekowa tai daga zauren da ta la6e , sai ta koma ganin ya wuce ta jingina da bango cikin murmushi ta dafe kirji tana maida numfashi,tamkar wacce tai wani tseren. A hankali ta kai hannunta kan "lips" nata tana tuno dazun, "Love you too AAA,wai kuma sai tasa tafin hannu ta rufe fuska ita a dole kunya, sai ta k'ada kai tai cikin gida. Tuki yake yana shafo "lips" nashi,harda dubawa a "mirror'' yana murmushi. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, " Furii" "Pretty"..sai ya sau murmushi, kan a hankali ya furta "I Love you" kamar tana k'allon shi. Biki anyi cikin aminci, sai d'ai har aka gama ba wanda ya kara leko kafarshi gidan su Fure sai y'an uwan mama da Abba, hatta d'aukar amarya basu zo ba,sai suka tafi d'aukar d'ayar amaryar. Haka Fure naji aka tafi da ita ta rabu dasu Umman ta. Sai d'ai fatan Allah kad'ai hau. Y'an mata aka kai,ba tare da tsayawa wani siyan baki ba,a ganin sun wuce ajin inji Ilyass. Wasu suka tsaya yiwa Ango da Amarya fad'a. Yana rakasu ta koma d'aki. A gaskiya iyaye sun mata ba zata, sam bazakai t'sammanin ba y'ar masu dashi bace,d'uk kamar wanchan karan karan nan ma kawunsu na Zaria ne ya mata gado da kujeru,shikam da zamani yake tafiya, shi yasa koman su tsaf-tsaf. K'wance take tana kara duben yanayin d'akin,sai ajiyar zuciya take na wacce taci kuka, sosai ya mata k'yau, ga wasu arnun labulaye, Allah sarki Abban ta da Ya Suleiman, Yanzu ta yarda da wadatar zuci tafi ta kud'i. Fatan ta Allah ya kaita lokacin da zata rama musu itama. A haka har ya cimmata a d'akin. Tsayawa yai yana k'allon ta, sai ta tashi ta takure kanta tare da jingina a jikin allon gadon. Sallama yai,sai ta duk'ar da kai ta amsa, zama yai kusa da ita yana k'allon yadda d'uk ta bata k'walliya da kuka,, shi a kullum yana da tambaya ga mata,wai shin mey ke sasu kuka in za'a kawo su gidan aure? A ganin shi farin ciki yafi kamata suyi su kuma gode wa Allah. Hmm.. Bazaka gane ba AAA. Ya ya iyah,aikin lallashi ya hau yi, sai d'ai dama bai ba,dan kuwa ya jang'wa6o ta. Kuma fa ta manne mishi,amma tana fad'in su Umma...Lol. Kamar wata yarinya ya hau hura mata k'unne. Tuni k'wa sai ta nemi kuka ta rasa,ya tafi garin su. Da dabara yai ta janta har ta ware tana murmushi k'eta. A haka har suka gabatar da da sallah kan ya d'akko komai a "parlour" da "plate'. Haka ba dan dad'i sai dan ya mat'sa mata taci kad'an. Ta tashi ta k'washe kayan,a kitchen ta t'saya k'allo, lalle duniya,wani abin ma bata san dashi ba. Ga nan "gas cooker" da halamun mai gidan yasa. Dan harda gidan ta. Ya shiga d'aki ta dawo parlourn, shima ba laifi an mata bajinta d'ai-d'ai k'arfi, kujerunta masu "Ledar" ne kalar 'Orange' da "milky" labulan ma haka, ga dan "center carpet" nata mai "grass" da "table" mai zanen "heart" a jiki. Sai TVn ta "plasma" manne, sun had'a mata "home theatre" dai,ga nan wata "flower" a tsaye kamar g'wada da da ya'yanta "Orange''. Ajiyar zuciya tai,jin an bud'e kofa. A hankali ta zauna a kasa,yayinda shi kuma yai wajen TV, ashe har sun had'a. Kujerar da take ya dawo da "remote" a hannunshi, sai ya tasa kanshi a cinyarta yana k'allon fuskarta da murmushi. Itama murmushin take,amma cike da kunya, sai ya juya kan TV ya d'anna "play". "Title" taga na "My heart will go on... Wani page ya fito da ire-iren pic din da yake d'aukan ta ta daga kai sama tana dariya har hak'waran ta sun fito, Sai ya rubuta. To my darling Furii.... Sai ga nan wakar "Celine Dion" na "every night in my dream tana yi cikin "slow motion" ta fara. Wani pic d'in ya shigo shima tai k'yau, a kasa yasa.. "I have been in love with you from the very moment I met you and every day I continue to fall deeper in love with you"..... K'allonshi tai, tama kasa magana,dan sam wasu ma bata san an d'auka ba,sukanyi dai fira wataran taga kamar yana d'aukar ta hoto. Har ya kare yana mai fallasa mata sirrin ranshi ne kawai a gare ta,sosai ta gamsu da ganin abin, ya kayatar ta.. K'allonshi kawai take tana tunanin da gaske tun had'uwar su ta farko ya fara Sonta? Ganin k'allon ba na karau bane yasa ya dawo fad'i da bak'in shi, ina Fure bazata iya d'auka ba, dan bataji ko ita tana mishi irin wannan son da yake ta k'wadata da shi. Kan su farga har dare ya ja sosai,tasan in zasu k'wana haka yana fad'a mata irin kalaman nan toh bazata gaji da sauraron shi ba. Ahmad kam karshe ne, ya kere ta a komai, sai d'ai ya zame mata dole tai ko'k'arin finshi iya kalami, a ganinta ita ya dace ta haddace. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. 9/29/16, 2:28 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 23_K'allon yaje ya kashe,dan jin TV na kukan a kashe ta ta kare, sai ya ajiye "remote" d'in tare da juyo wa gare ta, shi take k'allo, sai yai murmushi tare da zuwa da t'sugunawa a gabanta kamar mai neman tuba. Abin ba na magana bane a gare su, sai yasa hannu ya ware g'yalen da ta nad'a, ya cire d'ank'walin, sai ya ciro da ribbons d'in da ta tufke kanta da ya sha "relaxer'' d'ai-d'ai fankar "parlourn" ta k'ada gare su,tuni sai gashin ya fara tashi, ina gogan baki ya saka,ganin yalasha, tare da fad'in "SUBHANALLAH.... Hannu tasa ta rufe fuska,dan sai ya bata kunya ma, cikin ranshi kuwa,fad'i yake "Lalle t'sarki ya tabbata ga Ubangijin Sammai.. Ubangijin d'aya k'era mishi FURIIN shi mai saukin k'yau a baiyane, sannan mai t'sananin k'yau a ciki.. Ashe Allah idan ya hana k'yaun fuska,sai kaga ya baka k'yaun jiki... Yanzu ya yarda kowacce mace mai k'yau ce, ina ma Y'an uwan shi zasu d'aina zaban k'yalk'yal banza, suje su lalumo irin wanda basa so da yai imani su da auren mai k'yau sai d'ai-d'ai... Shidai yace "ALHAMDULILLAH.. Ganin irin "postern'' da yai yasa ta zamu itama tai yadda yai, sannan ta hau fad'in cewar ita ce fa,ba wai sabuwa ba. Sai yai murmushi kan ya tashi t'saye,sai ta bishi da k'allo, hannunta ya riko tare da tasarta t'saye suna fuskantar juna. Jin ba zaya jure ba yasa bata nufa ba taji ta asama ya d'auke ta kamar wata baby, sai ta sunne kai kamar marar lafiyar da aka d'akko ta kasa tafiya. Gun fanka suka je,sai ta mika hannu ta kashe, tare da sak'alo wuyan shi. A gado ya zaunarta, sai shima ya zauna tare da shafo kanta, halamun d'ai gashin ya mishi, sai tai murmushi tare da sadda kai kasa tana wasa da awarwaron ta. Sai shima ya kama hannun, a hankali ya kai shi d'ai-d'ai fuska yana k'allon filawar da ta fito da taimakon hasken "bed lamp",cikin nutsuwa ya fara zame su a hankali, babu magana sai d'ai murmushi. Sannu a hankali har d'an k'unne ya tayata cire wa,,kan ya cigaba da rera mata wakar dake mantar ta kanta ma, sosai in da so,toh komai ya kan tafi a sauki, sai d'ai fa Furii rakin nan daga baya yasha shi, tushe k'unne kawai yai, kan daga baya ya ji da lallashin. Asuba nayi ta bud'e ido, yana rike da hannunta ya durkusa gabanta,kamar mai neman ta inda zai fara tada yake, murmushi ya sau mata,tare da kai hannu ya g'yara mata gashin ta,sai ta k'au da fuska itama da murmushin,sai dai hawaye na k'waranya. Ganin har za'a tada sallah yaki tafiya yasa ta yunkura zata mike, sai ya taso dan taimako, kai ta girgiza, kan tace zata iya. Da k'yar ta lalla6a ya tafi,kan tai dabarar tashi. Yau d'uk sujjada sai Furii ta samu adu'a, har bazai ce ga adadi ba,fatan shi Allah ya basu zuri'a da Fure daiyiba masu t'sant'sar tarbiya irinta. Kan ya dawo ta kimt'sa komai har ta kara k'wanciya. Haka ya shigo da allura daga d'akin shi, macen dake kunyar shi sai gata ta hau waro ido... Sai ya hau lallashi,kan tai hakuri ba da zafi zai mata ba, kai ta k'ada, kan a hankali ta tashi, tsinin allurar kawai taga ta fara yarfe yat'sa. Hmm,tana kai miki Fure. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 24 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 24_Soyayya suke kam kamar babu gobe, a satin su Umma da Ya Suleiman suka tare a sabon gida, amma fur mutumin yace ya gano mata gida ita sai tai wata,sai dai satin ta biyu taje,gida kam yayi,d'uk da ba wani kato bane amma d'ai ya ninka nasu na Zaria ma na da,katon parlour yasa aka zana ma su Umman,ba wani kayan azo mu gani ba ne,amma tsarin yayi, y'ar TVn su "standard" da "dish" domin k'allo, kujerun su ma d'ai dai k'arfi,sai t'sakiya "Chinese carpet",da "tiles" sai "shining" yake,aciki yai musu "3 bedroom" Kowanne da bandaki a ciki,da kitchen din Umma, sai waje yai d'akin su Hassan guda biyu, da "public toilet" t'sakar gidan y'ar madaidaiciya, ya zuba musu "interlock". Sosai ajiya tai rana, filin makotan su Abban Ya Suleiman ya siya,katanga kawai ta had'a su,sai ya fidda kofar yadda zai iya zuwa ma kowa. Randa suka tare murna gunsu ba a cewa komai,dan kam ko yaya sabon waje ak'wai k'yau. Da ta cika sati biyu ya batta taje ganin sabon gida,d'uk da shi zuwanshi 2. Ana haka azumi ya kama, sosai yana taimakon ta ga kuma Maryam, dan "store" gare shi na delar magani babba, d'uk da yakan je asibiti jefi-jefi, amma zuwa shagon yafi,sannan yana da masu kullar mishi,yanzu burin shi su Hassan su gama secondary ya d'aura su kai, duk da ko ita FURIIN bai sanarta ba. An gama azumi lafiya yau ta kama sallah, t'saye yake gaban "mirror" ya daga kai tana 6alle mishi ma6allin rigan shi, tana gamawa ta wuyanshi da hannunta tana murmushi, sai ya dago jin ta gama, "kai k'yau sosai.. Ta karasa tana k'allon wuyan, juyarta yai gaban mirrorn suna k'allon Kansu aciki da murmushi, sai ta bashi sarka,cikin nutsuwa ya ke 6alla mata,sai ta shafo wuyan ta mudubi tace" thanks. Murmushi kawai yai tare da d'auro kanshi a kan kafadarta, fuskarshi ta shafo, "hala yau azumin magana kake? Murmushi yai tare da kara juyo ta, "kinyi k'yau ne shi yasa banson kat'se k'allon ki da magana,ki gane ke d'ai, ya ruko k'ugunta,sai tai kasa da kai tana murmushi, idonta ya manna "lips" nashi,yana son yaga tai d'an kasa da kannan tana murmushi, sai yaga kamar "eye lashes" nata na karu wa. Hoto yai musu,kan sukai shirin zuwa masallaci. Ana idar da sallah ana huduba ta ciro waya tana mishi "Happy Sallah" sai ga nan nashi, sai tai murmushi, tare da goge nata tai mishi mai sanyaya rai ta tura. Yau wanda bata ta6a gani bama a abokanshi sunzo k'wasar gara, Furiin shi abar alfaharin shi ce wajen girki,shi yasa ba musu ya barta ta cigaba da makarantar ta. Tana daga kitchen ita da Maryam,suna jiyo santin su,sai kara fasa mishi kai suke, bak'in nan har k'unne, Furii ta fitarshi kunyar Abincin sallah. Washegari tai ma su Mama da Umma lafiyayye su ma, "flask" daban tai wa Momy, Mama ma haka. Lokacin suna parlour Abba yana ta fad'an jiya basui abinci ba, yauma da yunwa zasu barshi? Sam ya t'sani abincin y'ar aiki,yar aiki mai girkin taje hutun sallah,ga Momyn ce da girki tun jiya,nufin shi tashi yai bangaren Mama sai ga nan flask daga Fure, shak'e da sinasir da wata hadaddiyar miya, taji kaji,da murmushi Abban ya k'alleshi, lokacin da yake gaida su, a gaban Momy ya ajiye k'wandon. Da fara'a Abban yace mishi "mey muka samu ne Abba na? Baki Momy ta ta6e, sai yai murmushi, "Abba abincin sallah akace na kawo muku.. Da fara'a ya k'alli Momy, "Maryam bani,zuban naci anan ma,dan fita zanyi, yai nufi kan "dining room'' d'inta. Ba dan ta so ba ta d'au k'wandon tai kan "table'' d'in, tana bud'e "flaks" kamshi ya doki hancin su,tuni Abba ya fara tattare hannun rigar shi, Ahmad dake gefe ya girgiza kai yana murmushi, sai yai "kitchen" d'in Momyn ya tarowa Abba ruwan wankin hannu. Zai fito sai ga nan momy,itama shi zata d'ebo,harara ta sau mishi kan tai hanyar d'aki dan jin haushin zag'wadin uba da d'an akan abincin Fure. A kusa da Abban ya zauna,sai wani lumshe ido Abban yake yana k'wararo santi. Shikam gogan abin nema ya samu, yasan ko waye in yaci abincin Fure sai yai santi. "Baba na, da murmushi Ahmad d'in yace "Na'am Abba, sai da ya kara yankar sinasir ya d'ang'wala a miya kan yace, "amma makarantar koyan girki iyalin ka take.... Haba wa,mai Ahmad zai in ba dariya ba, Abban yace"Allah kuwa,, dake Abba cikin yaran shi Aboki yake zamar musu. Kan ya farga yaci tayi biyar, kira yake abarnan kamar an sa mata madara. Shidai Ahmad baki yaki rufuwa. Tare suka fito da Abban, shi yai mota,shi kuma ya nufi bangaren su Mama. Yau ita kad'ai ce, Ummi d'uk sun fita dasu Rukayya. Kok'arin tashi take ta d'aura girki sai ga nan sallamar Ahmad d'in. Suna gaisawa yace ga nan abincin inji pretty, cike da jin dad'i ta bud'e tana godiya. Abinda sirikan gidan basu ta6a ba kenan, wai kawo abinci ko abincin sallah, su ganin su bata lokaci ne ma. Sai ga Fure da bata ma fi wata da sati biyu ba ta kawo sabon sauyi. Labarin santin Abba yake ba Mama suna dariya. Tace "nima dama ko'k'arin tashi nake na d'aura kan yaran nan su dawo. Sosai Mama ta yaba da zabin d'anta, ganan yaran nasu da suka taso cikin d'aular ba wacce zata ma abinci mai dad'i, su d'ai barsu a mai aiki sai ko dafa indomie. Ita kam Momy su Abba na fita ta dawo parlourn, d'uk kamshin miyar Fure ta karad'e mata "parlour", sai ta hau t'saki, da mamakin ta Alhaji yaci da yawa da ta bud'e, gashi fa itama ranta ya biya, amma sam taki koh ta6a miyar. Tana nan a parlourn taji hayaniyar su Rukayya, kana ganin su kaga sun k'waso gajiya da yunwa. A kan abincin Rukayya ta sauka,Huwaila ta zauna kusa da Momy, tana kai loma d'aya ta hau lumshe ido, taji abinci ba irin na Iyabo mai aiki ba. "Kai,"delicious".. Hannu baka hannu k'warya ta fara ci,sai ta k'allo Huwaila, "ka'r kiyi missing.. Da sauri itama tai kan table d'in, daga t'saye ta d'an dana, a zaton ta ko ba dad'i, ai tuni ta ja kujera.. Sai da sukai nak, kamin Rukayya ta k'allo momy wace ta sau baki tana k'allon su. "Momy yau kin mana mai dad'i, kai,yaushe rabon da na ci irin wannan abincin da yawa? T'saki Momyn tai,kan tace "abincin kishiyar ki toh kika ci, kuma wai dan iskanci suka hau k'ak'arin amai na gulma. "Amma d'ai Momy da kin fad'a tun farko wallahi bazan ci ba, cewar Huwaila, sai sukai kitchen suna ta bala'i, wai y'ar neman gindin zama,sai d'ai fa kan a wanke hannu har lashe wa akai bama su sani ba..y'an Kot'ar nan. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 24 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 25_Da ya je gida tai mamakin yadda taji wai y'an gidan na santin girkinta,sosai ya ji dad'i, dan murna sama yai da ita suna hajijiya da tuntsura dariya. Shi yasa yamma nayi tai wani abin,sannan tasa ya siyo mata Aya da kayan had'i. Washegari ma hadadden "meat pie'' da "doughnut" tai musu da kunun Aya mai sanyi da k'ankara cikin kula,ya ji K'wak'wa da kayan had'i da madara. Tun jiya da yamma tai "doughnut", ta nika ayar ta,dake suna da wuta "standard" ta samu k'ank'ara. Komai Fure tai tana burgeshi matuka, ga nan kullum cikin sabon t'sari take na girki. Fitowa tai daga kitchen jin yana kiranta, da mamakin shi sai yaga har ta gama shiri cikin "favorite" d'inshi wato "Orange color". Wani dak'akken "swiss" ne mai ruwan Orange da filawa fari, sai tai amfani da wata "fashion" na kalar kayan,shi bai son kit'so,sai ya had'u da mai son fakin,daga chan kasan d'aurin tumin nad'in gashinta ya fito,sai ta ja g'yale saman kan. Sosai tai mishi k'yau dan ta lakanci abinda yafi so, karasa yai tare da k'ar6ar abin hannun nata sai ya manne hannunta cikin k'wanon da nashi, in ta ja sai shima ya ja,sosai filawar tai k'yau ta hannun. Sai tai murmushi, ganin hakan sai ya sassauta ta cire hannunta tare da g'yara g'yalen, k'wanon ya ajiye sai ya hau tayata g'yaran g'yalen. Ita d'ai nata murmushi. Suna a mota hannunshi rike da lalle yana dan dubawa tare da k'allon hanya,ita dariya ma yake bata, dan tun safe da ya fita sauke kayan "storen" shi da aka kawo bai dawo ba sai dazun,shima yana wanka ya kara fita,sai waya da ya mata gashi nan zuwa.. Sai zuwa yai yaga lalle,mai yi har ta tafi, kuma ya kasa tambayar yaushe akayi. Har suka je gidan suna a farin ciki, sosai kamar wani rakumi,haka yake zama in yana gaban Prettyn shi. "Part" d'in Mama suka sauka. Ko jumawa batai ba tace taje wajen Momy,har ga Allah tafi kaunar ganinta da Mama. Nata "snacks" d'in ta ajiye Ummi ta d'au d'ayan sukai "part" d'in Momy Gomnati. Kusan ilahirin gidan da sirikansu a gidan ta same su,Aunty JIDDA ce kawai bata a cikin su,harda amarya Hassana da aka dawo daga "Honeymoon" ana ganinta aka hau fikara. Har kasa ta gaida Momy,a ciki-ciki ta amsa,daga nan kala bata kara ce mata ba tai d'aki. Wajen y'an parlourn tai yo,bayan ta zauna ta gaida su,d'uk sun amsa,amma biyu kam keya ma suka juya mata. Aunty A'i ce tai mata magana kan daga zuwa d'aya shiru, sai tai kasa da kai tana murmushi,kan ta dago, "zamu zo InshaAllah, Aunty Maryam ke harar su Sa'a,kan su saita k'allon sun, sai suka d'an basar. Har kusan azahar kan Momy ta dawo "parlourn'' samu tai suna alfari ma Fure, d'an t'sabar cin fuska wai tarihin kanshi kowa zai bayar tunda an hallara yau, kowa yasan juna, ita d'ai Aunty A'i ta hakimce K'afa d'aya kan d'aya a kujera tana d'anna waya,dan sam bata shiga haukar nan ta k'annen mijinta. Amma jin Bayanin da Huwaila take,kawai sai ta sau baki tana k'allon su da mamaki. A ranta tana"Oh,thank God, Allah ya gama su da sarakan dagawa da nuna su sune, sai ta k'alli Momy,ko ajikinta, asalima murmushi take musu ana k'wada arzikin gidan su. "Ni suna na Sa'adatu.. (Huwaila) in bracket. "Ina da aure,da yaro na d'aya, ta shafa ciki, "sannan ga nan na biyu. Har wani k'ada ido take, "Abban mu ya mallaki gida je har ba adadi,sannan kud'i a "accounts" bamu san adadin shi ba,ga motoci sai wanda ka kaga damar hawa, kowacce acikin mu yakan mallaka mata mota in zatai aure,da gidan ta na kanta,sannan mu fita kasar da muke so in hutu ya t'saya, kai,kud'i yayi a rayuwa. Ta fad'i tana k'allon Fure da ta sau baki. Sai ta k'allo Hassana, " ke fa Matar yaya? Hassana ta g'yara zama, tare da y'atsina, "ni baba na d'an Kasuwa ne,sannan d'an siyasa ne ajahar nan da ma Arewacin kasar nan,sannan yana aiki da "Government'' nima ban san adadin kud'in da ya tara ba,Abu d'aya na sani,shi sananne ne acikin masu kud'in jahar nan. "Ga nan kuma t'sarabar "Honeymoon" ta karasa magana tana wani k'ada kai da shafa ciki kamar wacce tai abin kirki. Ita d'ai Fure tai kasa da kai,abin har ya d'aina bata mamaki, ya dawo bata dariya. Huwaila ce ta k'allo ta, "Amarya ke fa? Dagowa tai tana k'allon irin y'atsinar da mai tambayar take mata. Sai tai murmushi, Ahmad da tun zuwanshi yai tsaye a "corridorn" Momyn, har zai shigo,sai ya t'sinkayi maganar Furen tana ce musu, "Ni? Sai suka daga Kansu wasu harda murmushin keta. Su a dole zasu tozarta ta. Sai tai murmushi kan ta k'alli wani gefe. "Furera muh'd suna na. Baki suka ta6e harda tafawa,wai "Furera"?? Sai tai murmushi tace "Baba na makanike ne shi,mai g'yaran mota ko babur.. "bai da kadara,sai rumfar aikin shi guda biyu. Sannan ba fittacce bane a garin nan balle ma akasar nan. "Tabbas! ban tunanin yana ma da "account" ma,balle kud'in shi har ya gaza kididdiga, sannan ko gidan kanmu bammu dashi,a haya muke zaune,sai dai Hamdala ga Rabba, abu d'aya na sani... "Baban mu zaki ne,mai nema da k'arfin shi da Allah ya bashi domin yaran shi, sannan ya bamu ilimi wanda zai taimake mu anan duniya da kiyama, ya bamu farin ciki, wanda har kullum in mun k'alleshi mukan ce Alhamdulillah. "Sannan ya bamu..... "Ke!!! ya ishe mu haka, kai ta dago, Momy ce ta kat'se ta, sai sauran y'an parlourn suka sa mata dariya,banda Aunty A'I da Aunty Maryam, wanda tunda ta fara suka nutsu sauraren ta jiki a sanyaye, tuni farad d'aya ta k'wanta musu a rai,ita kam Ummi d'an karamin t'saki tai ma su Rukaiyyan.. tana jin Rukayya tace "Rubbish" cikin y'atsina. Sai ta k'ada kai, tare da yin kasa da kai tana murmushi tare da wasa da y'atsunta. Kai ya jingina a jikin bango,t'sabar So da kaunar Furii ke kara shigar shi, tabbas ya t'sani fari'a, sosai ta kara kima a idon shi, d'an fed'e musu ainashin ita wacece... Ji yai an dafa shi, da sauri ya bud'e ido ya k'alli gun, Mama ce,har da d'an guntun hawayen ta dan tun t'sayuwar shi ta t'sinkayi komai, sai ta k'ada mishi kai, tare da ruko hannunshi suyi "part" d'inta. Zama sukai,sai yai jugum, itama d'ai shiru tai, chan ta kira shi ya dago,da mamakinta sai taga idonshi ya k'ada kamar zai kuka, sai ya marairaice mata, kafadarshi ta dafa, "Ahmad, kai hakuri,ni ina ji a jikina matarka alkairi ce gare mu a gidan nan, dole kaji ka toshe k'unne ka, dan nasan zata iya bawa kowa amasarshi d'ai d'ai shi tunda ta bada a wannan karan, ,kar ka fara tunanin cire ta a y'an uwan ka..kai hakuri, da sannu zasu gane nasan wataran. Kai ya k'ada mata. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:31 AM - Queen Safiyyert馃憫: Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 26_Ko minti biyar basui da dawowa ba sai gasu ita da Ummi da Aunty A'i. Fira suke cikin murmushi, sai Momyn ta dan ji dad'in yadda Aunty A'in ta sau ma Fure jiki. Aunty A'i tace, "dan d'aki ashe tare kuke da amarya? Kai ya k'ada mata yana k'allon Furen da murmushi. Sai mama tace Ummi ta zuba musu doughnut dasu kunnun Ayar, sai tai ciki dan basu gu,cikin murna tai kitchen da zamud'in zata kara cin abincin Fure. K'allota Aunty tai tana taunar "doughnut", "wai gaske ke ne ki kai ba aikatau ba? Murmushi tai kan ta dan k'alli wajen Ahmad,itama Aunty A'in sai ta k'alleshi. "Ok,kai kayi kenan? Kai ya k'ada, "ya kika ji toh? Kai ta k'ada tare da dauk'ar "meat pie", wannan ma ta hau k'ada kai cikin santi, sai d'ai Ummi na zuba mata kunun Aya ta hau g'yara zama, fad'i take "kai,wannan kuma mey ne? Dariya suka hau mata,ita kam ta dage da gaske take bata san kunnun Aya ba,ita d'ai Fure kawai murmushi take musu, dan tasan tsaf sai ta kasa sannin, dan y'an gayu sai da lemon k'wali. Suma achan ba ko kunya suna ganin Aunty Maryam ta fara ci suka zira hannu, barin Hassana,kamar wacce bata taba ganin filawa ba haka take narkar "snacks" d'in. Rukayya ce bata ta6a ba,tabi Momy suka zuba musu na mujiya kawai. Amma chan kasan ranta bata manta daddadan abincin Fure ba. Suna gamawa sukai bangaren mama,sai d'ai yadda Aunty A'i ta had'e rai,shine yasa suka gagara tankawa Fure. Sai da akazo sallah tukun ta yaye g'yale da nufin zuwa alwala, baki Ummi ta saka ita da sauran,ganin gashin Fure,ga nan ilahirin shape nata ya baiyana cikin les din. Sai tai murmushi, tana jiyo musun Huwaila da da Hassana kan wai "attachment" tasa. Kawai sai ta k'ada kai ta shige alwala. Har ta iddar ba wanda ya motsa sai Ummi, Aunty A'i tace tana fashi, Aunty Maryam kuma tana gun mama, kawai sai ta zuba musu ido, da mamakin ta har uku suna kan waya ana nuna kayan k'arya na d'aki wai Huwaila zata sauya. Mama ce ta fito,sanyin hali yasa ta tambaye su tukun sunyi sallah? Kansu na waya suka girgiza halamar A'a, sai ta had'e rai, ''toh maza ku bar min nan, ace d'an musulmi har uku bai sallah ba? Fure d'ai ikon Allah take gani,ba musu suka bar parlourn sukai na Momy,sai Hassana ce ke sinke kataje tai alwala. Sam basu kaunar zama kusa da Mama,ita sam bazata bar bawa ya wataya ba,ga nan Momy,suci karan su ba babbaka ma ba ruwanta dasu. Washegari kuma tai gidan su,sai dare ya d'akko ta suka dawo. Sai dai koh a fuska har yau bata nuna mishi abinda y'an uwanshi suka mata ba. Sai d'ai a ranta tana fad'in ta d'aina tanka musu,dan ta san rashin islamiya ke damun su. Sai d'ai Hassana tafi bata dariya,mai tunkaho da kud'in ubanta. Kud'in Tukudi, kud'in cizo,kusan unguwar su d'aya da Y'an uwan su Adama, ta bata sirrin komai ai, karya kuma ta kare. Tun daga wannan ranar d'uk "weekend" d'in duniya sai Fure ta aika ma Abba dasu Mama abinci,na satin nan sai ya ninka na satin gaba dad'i. Sai ya zama har Allah-Allah Abba yake ya ji ance "weekend " tayi yana gida,dan ya k'washi garar abincin sirikarshi mama na gefe tana mishi murmushi. Dan sam Momy ta d'aina k'ar6a koh an kawo mata. Ko ran girkin Momy ne kuwa indai ya fad'a a ranar kawo abincin Fure Abba shi zai ci. Bashi ba,hatta sauran mazan gidan irin su mijin Hassana nasan girkin Fure. Dan ak'wai lokacin da yazo ya samu Fure ta gama girki tana "serving" yayan shi shima ta zuba mishi, da hadd'en lemonta na kullum,tuni ya soma wa Ahmad santi, nan tana daga d'aki taji yana t'surkutawa Ahmad d'in wallahi ba abinda Hassana ta iya sai dafa indomie da k'wai,kai ranar Fure taci dariya ta gode Allah. Sosai zata gode ma Allah a bisa yadda ya sauya rayuwarta farad d'aya.. Babban farin cikin kuwa shine yadda ta zama fitilar haskawa ga mijinta, ta zama abar alfarin shi, ya zama abin nuna ma sa'a, domin ya bata d'ukkan farin cikin dake a gidan aure,ance zo mu zauna zo mu sa6a.. Toh a gaskiya Fure sai anyi kure,kan taga sun sa6a d'in, albarkacin mijinta ta leka garin manzo, ta leka kasar da ko a mafarki batai tunanin zuwa ba. Sai d'ai dake Allah ya kan jarrabi bawanshi a d'uk farin ciki toh dole ak'wai bak'in ciki, ba komai zaya had'a maka 100% ba a rayuwa,matuka yanzu burinta haihuwa. Ko dan ganin yadda har ta fara taka matakin gori daga y'in shekara agun dangin Ahmad. Yanzun kam ta kara samun matsayi, daga y'ar MATSIYATa ta koma JUYA. Bata jin da taron da za ai a watse lafiya ba tare da an wat'sa mata magana ba. Hakan yasa ta halarci ganin likita,ko d'an ganin mey matsalar. Duk da shi ta gun Ahmad d'in d'uk kaunar shi da yara bata ga chanji ba, asalima cewa yai yaushe ma akai auren? Kar ta tada hankalinta, "soon'' zasu samu baby. Tanan kawai takanji sanyi,har ta manta bakin cikin su Huwaila. Ranar sun fito ziyara sukai har gidan k'aninshi mijin Hassana, dak'yar ya yarda,shima sai da tace bai fa je ganin baby ba. Suna a "parlour" yana cin abinci, da murna ya tari d'an uwanshi, itama Hassana ba laifi, ganin Ahmad ta sau mutunci,dan sam bai bata fuska koh a gida suka had'u. Sai dai motsi kad'an ta ambaci sunan y'arta, ita a dole zata bawa mara D'a haushi. Murmushi kawai Furen ke mata,shikam Ahmad kamar an tsikare shi yace ta tashi su tafi. Direct gidan Aunty Jidda suka sauka, hakima isassa, Allah ya gani d'uk Familyn su Ahmad tafi ganin tsanarta karara akan Fuskar Aunty Jidda. Ba abinda ta bari na Momy,sosai in ka ganta sai ka d'auka K'anwar Momyn ce ma,dan sosai tafi Momyn tsufa. A kofa ya batta kan zai shigo Abba na neman shi. Kai ta k'ada mishi, sai d'ai tana jin jina shigarta gidan ita kad'ai. Rukayya da Huwaila k'wa suna gidan,uku ta had'u mata. Tun daga gaisuwa ta d'auke suka d'auke mata wuta,Aunty Jidda ta had'e ran nan. A walakance Aunty Jidda ta k'alleta ta wat'sar, sai k'alli su Rukayya, "nikam ku tambayi Matar Yayan naku naga har yanzu shiru,sai ban ruwa muke shuka na hau hawa.. Baki Huwaila ta ta6e, "bari dai kiji ta bak'inta Aunty, sai ta k'allo Fure wacce itama su take k'allo cike da mamaki. Sai tai kasa da kai tana murmushi. Tamkar wata Umman ta tace "Wai ke har yanzu shiru ne Fure? Sai Rukayya ta amshe, "Ki ka sani? Kila d'ai "JUYA" ce...Da sauri ta k'allosu fuska d'auke da mamaki,kan ta koma kan Aunty Jidda, baki ta ta6e,sai ta tashi ta basu gu, su kam ko ajikinsu, asalima dariya suka hau mata harda tafawa,, kamar kullum,yau ma ta kasa tanka komai a game da maganar da ake ya6a mata d'uk a rashin bata haihu ba cikin shekara d'aya. D'uk da tasan tana da damar ramawar a kansu, maimakon hakan ma,sai kawai ta kara kasa tare da k'adashi tana murmushi. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 25 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 27_Sosai tana mamakin d'uk bak'inta da iya bada amsa a zance, amma in an kira ta da "JUYA" sai tai shiru. Ba shak'ka kila wataran Allah zai ara mata rana ne acikin ranakun rayuwarta d'an zuwan hakan.. Ko kuma baya rasa nasaba da ganin darajar mijinta, wato Habeebinta Ahmad dake d'an uwan su. "Kinga ai tai shiru, anzo an bake gida,ana hura hanci anji sanyin AC,baki Huwaila ta ta6e, "wallahi nafi jin haushin Yaya da ya k'waso ma kanshi alakakai, k'alleki fa Rukky,wallahi ke ki kafi da cewa da wannan gidan ba ita ba,tuni suka hau zaginta cikin turanci kamar kullum a nufin y'ar talaka ina zata samu ma "foundation" mai k'yau bare ta iya turanci. Sosai take nuna musu dolancinta, sai tai tamkar bata jin mey suke fad'i, ko turanci aka mata azance sai ta nemi su fassara maata. A haka har Huwaila ta shigo ma da Rukky maganar mijinta,kan ta kasa gane inda ya dosa,har ta gaji da kai karar shi gun Abba. Fure na jin lokacin da tace ta fad'ashi da Ya Ahmad, tunda k'aninshi abokinshi ne. A ranta tai dariya har ta gode Allah, ace y'ar mai dashi ta rasa gane kan Miji?. Sannan k'warai in bata manta ba ta ta6a jin ance Aunty Jidda har suka rabu da mijinta bata haihu ba agun Ummi,toh wai shin g'wanau baya jin warin jikinsa shi sai na wani? Ko kuma ji nai batai ba yaran na gun Abban su? Da wannan tunanin har Ahmad yazo suka je gidan Aunty Maryam, ita kam maganar bak'inta ma gagarar ta take,bare Furen ta gane inda ta dosa. Wasa wasa Fure har ta k'ware a auna kanta da kanta da pt,ko k'wana d'aya "period" nata yai "due'' yanzun zata d'au "strip", dan tun yana kawo mata d'ai d'ai yanzu k'wali ya dire mata,shi d'ai kullum burin shi ta ma d'aina g'wadi, takan k'alleshi da mamaki,ita ya dace tai mishi lallashi,dan sosai tana ganin yadda yake son yara koda in su Adama sunzo mata. Tuni ta kammala makaranta tun wata uku da suka wuce,ba wanda yasan tana zuwa,daga Umma sai ummi,fatan ta "result'' ya fito,yaya yayi alkawarin kama mata shago kan ya tara kud'in bud'e mata karamin "Restaurant". Magana ta kara karuwa ne lokacin da Hassana ta kara samun ciki, sosai take d'anne ranta,har bata kaunar abu ya had'a su zama waje daya, a gun mama da Ummi kawai take samun sa'ida. Momy kuwa, shekara biyu na cika ta tada ballin dole Ahmad ya kara aure da Rukayya, tunda ga nan yadda Matarshin tazo. Ko kad'an bai fara gigin bari Fure taji zancen nan ba,shi yasa kawai yake bin Momyn da toh, dan ganin Abba ma baice komai ba. Ita d'ai taga fallin Rukky ya karu, sannan Momy ta rage mata wani abin, maimakon haka ma,sai ta t'siro da mata murmushi in tana gaida ta ko in ta ganta, wanda kai kana gani kasan mugunta ne. Allah sarki Fure baiwa ta Allah. ************************ Doguwar ajiyar zuciya ta sauke,lokacin da ta gama tuna baya, tuni sai ta tashi ganin lokacin sallar "Duha" yayi, yi take tana kai ku kanta gurin Allah, in har tana da rabo na alkairi toh Allah ya bata. Harda dan guntun hawayenta dan tuno da jiya a gun sunan Hassana. Sai ta samu kanta da daga hannu, tana mai rokon Allah indai tana da rabo na haihuwa a gaba,toh dan t'sarkin mulkinshi ya aramata rana, ya ara mata lokacin zata had'a kan kowa dan bashi sakamakon abinda ya tusa mata. Tana shafawa ta hau kuka, sai da tai mai isarta kamin tai shiru taje ta k'wanta. "Text" tai ma AAAn ta kamar yadda ta saba in tafiya shi da Abba sukai bata kira. Sai ta kashe waya kan ta juya dan rama baccin ta. Saukar su kenan ya kai Abba gun taron da suka je yaji shigowar "text". D'aki ya kama musu shida Abba "Hotel" kan yai wanka yai "ordern" abinci. Chokali yasa yana jujjuwa abincin yana tuna wa da "delicious" na Prettyn shi, sai yai murmushi k'ada kai, Furii kam "special" ce agun shi. Sai d'ai yana mamakin yau har ya sauka baiji "text message" nata na "safe journey" ba, hannu ya kai dan tunawa da sakon da ya shigo wayan shi dazun. Baki ya wage ganin ita d'in ce kuwa k'wace kan "screen'' an sa Pretty. Cikin zumudi ya bud'e sakon fuska d'auke da murmushi. Ajiyar zuciya ya sau, kawai sai tuno da ta jaka kamar kullum, da sauri ya tashi ya zuge jakar,sai ga nan abu cikin duguwar ruba marar kauri nad'e a "wrapping paper". Yana dago shi sai ga nan wani y'ar "paper", ajiye na hannun nashi yai, da "pencil" ta "heart" tai "shedding" nashi g'wanin k'yau, kan a ciki tai wasu mit'si- mit'sin rubutu. "Ticking beats my heart, and the desire to see the person that I love. I wish the best for you in this journey, and I wish you a speedy return.... Love you. Zame wa yai a hankali yai k'wanta a gadon, yana mai shafa jikin y'ar guntuwar takadar. A hankali ya mike,sai ya ware wannan bowl d'in, cikin sauri ya fara ci,tuni ya k'auda wanda yai "order" tare da jawo wayan shi da zummar kiranta ya ji "switch up",a haka yana ci yana kara k'allon heart d'in yaci kusan rabi,ya kora da lemo. Ji yake kamar yai fuffuke yaje ga FURIIN shi. A kullum ta duniya yana alfahari da zaman Pretty mata a gare shi, sosai ya sani ko a haka Allah ya barshi ya kaunace shi, balle zai so yaga yaran shi da Pretty kad'ai a duniya,badan bai san yadda hali zai yi ba,da sai yace daga kan Pretty ya dat'se aure, hmm,wa yaga "MIJIN MACE D'AYA na sis (Rufaida Omar). Sai d'ai yasan K'ADDARAR shi ba a hannunshi take ba,kawai d'ai "hope" ne. Lalle Fure kin ciri tutar zama "MAR'ATTUS SALIHA",, wace k'allonta ke sanya miji a farin ciki,wace rashin ta a kusan shi ke sashi k'ewar ina ma tana kusa.. Wace ya yabe ta g'wana ce gun iya girki, sannan k'wararriya gurin iya lafazi mai k'yau da ma'ana. Tuni shima ya hau t'sara mata nashi salon,yasan bacci kad'ai ke sa Pretty kashe waya,burin shi in ta tashi ta bud'e ido da "hot message" nashi gare ta. By Feenat 9/29/16, 2:36 AM - Queen Safiyyert馃憫: [4/26, 7:41 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 28_Sai kusan d'aya ta tashi,warai taji ta,a hankali ta sako kafarta kasan gadon ta zura ta kalmin sosonta na "bedroom"tai kitchen, mai sanyi tasha,kan ta dawo d'aki ta d'au waya,tana bud'ewa kuwa sai ga nan "text" nashi, sosai ya ware ta cikin nutsuwa, kamar yasan a "mood" d'in da take a ciki. Sai da akai azahar kan sai ganan kiranshi. Cike da murna ta d'auka tare da sallama. "Y'an mata na ta tashi lafiya? Dariya ta sau mishi cikin wata siga, tasan an so tsokana, kan taja numfashi ta sauke,tsaf a k'unnenshi, tuni ta kara narkar da murya, "lafiya d'an samari na,"hope" kun sauka lafiya? Shiru yai mata kan ya juyo, "lafiya,sai k'ewar ki,, mey kike yanzun? Numfashin ta kara ja,kan tace "k'ewar ka nake nima, sai kam ya ji dad'i, nan suka cigaba da lalacewa cikin birnin su na su kad'ai. Kan su farga kusan 1hr suna a manne da wayar juna. Gida yace ta d'akko koh Maryam ne,dan Abba har la'asar bai dawo ba,harda da d'an kukan shag'wabarta, tuni ya hau lallashi kan yau ne kawai. A gida ta samu su Aisha,Adama ma sai gata ita da yaronta kalil dan shekara 2,ganan tsohon ciki, sai ta hau mata tsiya, "A Yarinya,yi a hankali,in dai labor room ne tana jiranki, kai tai kasa dashi, an tabo mata inda ke mata kai kayi, Aisha ta k'allo ta," wai Furera ni har yau kina sa zancen mutanan nan a ranki? Baki Adama ta ta6e, "wallahi Aisha har mamakin Pretty nake, wannan kananan kadagarun wallahi in ni ce tuni an shani na warke,, dan ba wacce ta isa takani na k'yale. Murmushi tai, "bazaku gane ba ne ba Ada, ak'wai ranar tankawar, tana nan zuwa. K'wafa Adan tai, "amma kinsan nafi mamakin yadda kika bar Hassana nacin tuwo a kanki? Ke da kike da abin fad'i ahannu? Ki sau mata d'aya kiga yadda bak'inta zaya rufe malama, ita da miki gori wallahi har abada. "Y'ar gidan tsohon najadu kawai.. Dariya suka sau, "shege Adama,au Aunty,labari na tsoron ki, kai Adan ta k'ada, "ai ni tun ranar Dinnern ku naji komai gun Hanna. Yau sirrin da Fure bata sani bama na gidan su Hassana ta sani ka'f. Sai dare ta d'au Maryam Ya Suleiman ya sauke su. Waya suke da AAAn ta tana d'an k'allon Maryam itama dake waya tana d'an y'atsine wa kamar an mata dole. Data gama ta k'allota itama ta gama, "Oh ni kam, Maryam anya bakki Aljanu? Baki Maryam d'in ta ta6e, "Kila toh, sai Furen tai murmushi, ''ni d'ai ki rufawa kanki asiri ki bar ruwan ido,kowa yazo kice bai miki ba, tashi Maryam d'in tai tana rage kayanta, kan ta hawo gadon, "ni fa bakar k'arya ce ban so, wai fa in munyi aure d'uk bayan sati zaina fita dani waje,mota sai wacce na ga dama, hala k'aruna ne uban shin.. Dariya Fure ta hau,kan tace "Allah shirye ki,tace "yoo Allah kuwa,in gani a kasa man,ko katin dubu bai ta6a turan ba. Ita d'ai tana ta dariyar yadda Maryam ke zage samarinta, ka'f ciki babu g'wanin ta. Washegari da t'ar6ar Oga suka tashi, sosai take yaba zafin naman Maryam, d'uk da d'ai ita ke binta,t'sakanin su shekara biyu ne, Umma takance Maryam guntun Fure tasha,dan ita harda taso fin Fure a iyayi da rashin barin ta k'wana. Matsalar d'aya ita tafi zama a Zaria, dan da sosai zata k'ar6a ma Fure y'anci. Kusan biyar d'in yamma sai gasu sun shigo shida Mohammad mijin Hassana mey bin Ahmad, Fure na d'aki sai Maryam dake kan dining tana ajiye ruwan wanke hannu. Da fara'a tai mishi sannu da zuwa,kan ta dire kan mai cewa "Matar yaya mey aka mana ne? A dirare take K'allonshi, Ahmad na kula dasu,sai ya k'ada kai yai ciki. Shikam k'allonta yake ganin wannan tafi Fure fari,tsayi,jiki,da kuma k'yau. Ita kam ina wuni kawai tace,sai ga nan Fure da fara'ar ta, ganin irin k'allon da Moh'd kema Maryam yasa ta k'ada kai, "a Abban Jidda tare ku ke? Da d'an wayan ce yace eh,sai kuma ya d'an saci k'allon Maryam dake ko'k'arin cire chargy, "yau,nifa tafiya zanyi,ai ya dawo, Umm,sai ya ji har muryar su d'aya da Fure, " toh ki jirani, sai ta dawo kan Moh'd, "Abban Jidda zauna kan nazo,yau kam mutuminka ne. Sai ta koma d'aki gun mijinta tana mai ina ma ina ma.. Maryam na ganin haka ita tai d'akin bak'i dan kimtsa kayanta sannan da gujewa k'allon Moh'd. Sai da ta jiyo hayaniyar su ta fito rataye da jaka tana yafa g'yale, dan tsaf in ba haka tai ba yanzu zasu ce sai ta kara k'wana. Da murmushi Ahmad ya k'allota, "madam kenan,kamar muna koranki haka? Fure ta k'alla, kan tace"ai na muku, g'wara na tafi gun Umma ta. Ta sauke kan mutuminta,karan nan suna had'a ido sai yai kasa da kai da murmushi yana d'anna waya, sai ta d'auke kai tare da dan ta6e baki. Sudai su Fure na ganin ikon Allah. Dak'yar Ahmad yasa ta kara k'wana, harda d'an bubbuga kafa kan bata so hakan ba, "eh munji, kawo jakar, Fure ta k'ar6a takai d'aki. Ba sai ga mutuminka ya dawo Washegari ba, tun goma sai gashi sun shigo shida yayan nashi wai daga "jogging" yake bayan da mota yazo...Lol. Ita d'ai Fure sai dariyar ciki take,ta Allah Amin, wallahi zata so wannan "dramar" dan zatai dad'in k'allo t'sakanin ta Hassana. Anan yai break yana d'an k'allon d'akin da Maryam ta shiga jiya, d'uk Ahmad na kula dashi,zai so zargin shi ya tabbata,amma kawai sai ya basar dan ganin iya gudun ruwan shi. Sai k'wa gashi ya k'allo yayan nashi,"ni yaya bakuwar ku ta tafi ne? K'allon da Ahmad ke mishi ne yasa ya hau sosa keya, "no'' ba fa wani abin bane,,atoh, sai ya d'au tea ya kai baki,bai zata ba ya ji yayan nashi ya k'walo kiran Maryam,tuni sai ga Moh'd ya k'ware, dan fa Maryam ta bashi tsoro jiya da wannan k'allon nata. Fitowarta a wanka kenan ta sa kaya, hijab ta zira ta amsa da d'an k'arfi kan tai waje. Ganin Moh'd yasa ta d'an kama kai, "Na'am yaya,tashi Ahmad d'in yai yaja kujera, yana murmushi ya nuna Moh'd,"ga nan mai kiran ki,ruwan wankin hannu zaki bashi wai. Sai ta k'allo Moh'd d'in da yai tsuru tsuru yana k'allonta. Dariyar shi AAn ya kunshe, ganin zata tafi yace,"au,ma manta,k'ani na ne fa, mai bi min,yake tai musu,tace "ina k'wana. Bata jira mey zai ce ba tai kitchen debo ruwan. "Haba bros, wallah tsoron yarinyar nan nake fa, kuma.. Sai yai shiru yana sosa keya, kai yayan nashi ya k'ada. Sai ya bashi gu yana dariya jin motsin Maryam zata fito. Yanayin da yake ne yaso ya bata dariya,d'uk ya susuce, ruwan na hannunta ta mika mishi,kawai sai yai sakare! Yana k'allon ta,kai ta ka'rkatar tana dan mishi fari cikin murmushi tare da matsar da ruwan kusan dashi. Sai ta bashi dariya tare da kai hannu zai wanke ta d'ang'warar kan table d'in tare da yin gaba kamar ba ita ba. Kai ya k'ada, shi yasa yace tsoron ta yake. A gaskiya Maryam ta mishi,sosai ba k'arya sai d'ai taya zai fara tunkarar ta da tsoron? K'wada wa masu gidan kira yai kan shi zai wuce. Sai ga nan Fure ta fito tana d'an dariya jin mitar Maryam kan k'allon da Moh'd ke mata. "A,ka bari ya fito,yanzun,ina zuwa, sai ta nufi d'akin su. Kusan a tare suka fito da Maryam, masu gidan sai y'ar dariya suke,shi yana k'allon Moh'd ita na k'allon Maryam, "wai mintsinin ki ake ne maryam,? Baki ta turo, ''nifa tafiya ta zanyi, kawai ku barni, ta karasa tana dan magana kamar mai shirin kuka. Ahmad ya k'ada kai, "toh munji, amma gobe zaki zo? Kai k'ada,"nikam gobe zan bar garin,Zaria ma zan gudu. Yin duniya taki zama, suna k'allon yadda suke dan k'allon juna,ita Maryam na basar wa. Moh'd bai zata ba ya ji Ahmad yace "d'an sauke ta da Allah Bros, sai ya k'allo Maryam d'in da tai kicin kicin, sai Ahmad yace," koh zaki bari mu fita anjima? Da sauri ta k'ada kai, dan tasan yanzu sai su kara rike ta. Shikam kamar an mishi gafara yaji, da azama ba musu ya tashi yana musu sallama. A mota suna tafe yana murmushi shi d'aya, ji yake kamar ma ace man Maryam ta zama tashi ne zai kaita unguwa. Kanta duk'e ta ce mishi "left" k'allo ta yai, kanta na waya, sai yai yadda tace, suna dan kara gaba ta kat'se shi da "right". Sai yai murmushi, yana son mace mai aji. Da "left'' right" suka zo inda zai sauke ta. Da mamakin shi sai yaga ba gidan su Furen bane,dan rabon shi da gidan tun suna na kasa,da ta barshi chan zai kaita. Godiya ta mishi zata fita yace "Maryam, sai ta juyo tare da tsare shi da ido, sai ya kuma hau kame kame. "I thought ke K'anwar Matar yaya ce? Kai ta k'ada, "K'awarta ce. Zata kara fita yace, "OK, ok,nan ne gidan ku? Sai ta kara k'ada kai, "Umm Umm.. Sai ya marairaice mata, "dan k'watanta min, K'allonshi tai, kan ta k'ada kai, "a unguwar zana nake,layin y'an kara.. Ido ya waro, zata kara fita yai saurin tsayarta, "meye zana da kara? A takaice tace mishi "Unguwa ce. Bata jira ba tai waje ta barshi baki sake. Har ta shige gida yana k'allonta. Da yaje gida kuwa Allah-Allah yake yamma tayi. Yadda ya dinga k'waliya kai kace gun d'aurin aurenshi zashi, har Hassana dake K'allonshi ta kasa jurewa. "Wai Abban Jidda yau ina zuwa haka da wannan irin d'aukar wankan? Murmushi yai, ba tare da ya k'alleta ba yace "waje mai mahimmanci, sai ya juyo, "ke d'ai nayi k'yau? Baki ta ta6e, kan tai mai banza, shi ko kula da cikar da take bai ba,burin shi kawai ya isa ga unguwar Zana layin Y'an kara. By Feenat Ja'afar. [4/27, 12:10 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 29_Sukam su Fure tun fitar su tai gun tarairayar mijinta,sai d'ai tana ga kamar Maryam zata bata shirin, wallahi har ta gama hasko Maryam a matsayin kishiyar Hassana, ita d'ai kawai burinta Allah kai Damo ga Harawa. T'saye suke gaban madubi tana 6alle mishi ma6allin rigarshi suna cikin nishad'i. Sai kamshi yake zubawa. Hannu ta mika tare da d'akko hula tana kafa mishi, sai ta d'an mat'sa tana dubanshi tana rike ha6a, "ummm...MashaAllah.. Murmushi yai,kan ya tako gareta, "ke ne Mashaallah, sai kara k'yau kike kullum, ya rukota,''meye sirrin.. Baki ta kai k'unnenshi ta rad'a mishi a hankali "So da kaunar ka ne. Murmushi yai, kamar kar ya fita, kawai sai ya ruk'unk'umo ta yana d'an shinshina wuyanta tana dariya. Sallamar Moh'd ce tasa shi dagowa yana k'allon Furen, "Oh Allah,, waye wannan? Dariya ta sa, "bari na dubo, sai ya k'ada mata kai "no bari naga. A bak'in gado ta zauna tabi shi da k'allo har ya fita,sai ta sauke nauyayyen ajiyar zuciya, tana matukar son Uncle d'in ta, sam bata kaunar yai mata nisa. Da dariya ya dawo,yana "fito kiga abin mamaki, yafo g'yale. Cikin azama ta biyo shi. Muh'd ne yai k'ankane akan kujera. Yana ganinsu ya g'yara zama. A kujerar mai mutun d'aya suka zauna suna fuskantar shi,ita na kan hannun kujerar, haba,shi yasa suke ba shi sha'awa, sam shi ba'a g'wada mishi soyayya a gida, tuni ya ji ya kara zumudi akan K'awar Fure. "Kin ganshi wai Maryam ya karade nema wai bai same ta ba,shine yazo ki mai dalili..ya karasa suna dariya, k'allo su yai, gaba d'aya ya gaji neman wani unguwar zana layin Y'an kara. "Matar yaya ki taimake ni, da gaske K'awar ki ta wahalar ni, mai na har ya kare a neman Unguwar Zana Layin Y'an kara... Dariya sosai ya basu, har ya soma k'uluwa kuwa. Dak'yar Fure ta t'sagaita da ta ta, "kai amma tasha da kai fa, Ahmad ya k'ada kai, "Maryam ake fad'a maka, sosai "style" nata ke burgeni fa Allah, , sai suka kara sa dariya. K'wafa yai,kan ya tsiyaya ruwan dake roba a dining ya dawo, "Au,dariya ma na baku ina sanarku abinda K'awar ku ta min? Kai Fure ta k'ada mishi, tana d'an ta6a Ahmad kan yai shiru. Kawai sai ya sa musu ido. "Maryam K'anwata tace fa,UWA D'AYA(na Aunty YBK), "sannan ba wani layin zana ko kara da take, sai ta k'allo shi, "toh kai wane unguwa ka kaita? Ba zuciya kuwa ya fad'a mata cikin mamaki, sai ta kara kunshe dariya, "nan take da zama,iskancin Maryam ne kawai. Ahmad yace "toh mey ta ma irin wannan nema haka bros? Waya ya ciro,"ku ban numbern ta kawai, daga baya zaku ji komai. Wasa sukai ta mishi da hankali,har sai da ya fito 6aro 6aro yace shi fa Sonta yake. Tab,yau ake yinta inji Fure a ranta, lalle lokaci yayi dazata danawa Hassy Bom, fatan ta Allah yasa Maryam ta yadda da Moh'd kawai. Sam bata nuna ma Ahmad murnar ta a fili ba, sai ma shi ke nuna tashi, tunda muh'd ya biyo sahun shi. Wasa wasa kullum sai yazo ma su Fure, dan Washegari Maryam ta wuce Zaria da zummar karasa satin ta biyu. Sai d'ai kusan kullum sai ya kirata a waya kan wani bawan Allah ne mai kaunar ta Fisabilillahi. Binshi take a haka, dan Fure ta bata komai "in details". Kamar yadda suka saba shawara da Momy in abin su ya tashi yauma nan Muh'd yaje da kokon shi, dan mud'in yasan in Momy ta yarda toh kamar kowa ya yarda da batun karin auren shi. Sosai yai mamakin Amin cewar Momy a take,sai d'ai ya boye matar da zai aura jin Momyn na mishi fad'an kar ya kara jaju6o musu irin su Hassana. Dan tuni ta dawo a rakiyar ta, ganin uban Hassyn bai ya tabuka komai ko ta haihu,a ganinta da ita da y'ar matsiyata Fure d'uk d'aya. Sai d'ai yai shiru yana jinta, fad'i take "karan nan a ni koh AAA a gidan nan, sam ban ta6a cin ka'ro D'a mai taurin kan Ahmad ba, in banda haka ina gami t'sakanin waccan kod'dadiyar matar tashi da Rukky? Kai ya k'ada mata, "Momy babu kam, sai tai k'wafa, "atoh,ka d'ai za6a ka darje karan nan,kar ka kara bamu kunya. Kai ya k'ada, yana mai tunanin randa Momy zata san wa zai yayu6o musun. Gida ya koma cike da farin ciki,tana a parlour yara na ta tsula ihu, amma sam ita ko a jikinta, cikin fad'a ya fara mitar tabani bazata kula su ba? Sai ta ta6e baki tare da sau mar harar haushi, "tunda kace baza'a d'akko musu "Nanny" ba toh mey yai ruwanka acikin ihun su? Sunkuwa yai zai d'au mahma yana k'ada kai, a ranshi yana "kin kusa gama na kud'in ki. Sai d'ai yana daga babyn ya kawar da kai, kashi tai a "pampers" har ya fara fitowa. Kamar ya rufe ta da duka ya ji, "mey kike ji dashi ne Hassy? A y'atsine ta k'allo shi, "da akai mey? Kai ya jijjiga, kan ya komarta ya k'wantar, "kin kusa gama na kud'in ki, kiyi komai ba komai, amma ki tabbatar kan na fito kinsan nayi da y'ar nan. Da harara ta bishi har ya kule, kawai haushin shi take ji,dan tayi tayi ya sai mata mota fir yaki, ga nan Fure karamar d'angarta tana murza mota, shine fa k'wana biyu take sakar iskanci son rai, a ganinta hakan zai sa ya sai mata. Fure ce k'wance ta k'allon kofa lokaci-lokaci, da halama mai gidan take jira, ga ya manta wayanshi a gida. Hannu ta kai kan wayar jin ana kira, "Huwaila" taga an rubuta, sai ta ajiye taki d'auka har ta yanke, tunanin dabi'ar Huwailan take a gare ta, sai ga nan wani kiran ya sake shigowa. Kamar kar ta d'auka, sai d'ai ta share ta daga da zummar sanarta baya gidan. Ba ko sallama ta sau kuka cikin wayar, "Bros dan Allah ku dawo, gashi nan yana kara kirarin shi wallahi yara biyu yake son ya tara sai dai nai "abortion, daga magana har mari na yai.. Furen naji daga cikin wayar mijin Huwailan na fad'in ta sanarwa kowa ma, amma shi kam bai san da wani ciki ba, kuma in aka takurashi zaiyi rashin mutunci. Da sauri Huwailan tace "kaji koh Bros, kaji da k'unnenka... Da sauri Fure ta kat'seta da "za'a sanarshi in ya iso, sai ta kashe ta bar Huwaila da baki sake. Fure cike da mamaki tai t'sam da tunanin fad'an Huwaila da mijinta, chan AA ya nufa kenan tun dazun? Tab,yau ake yinta, yanzu dama irin mugun zaman da Huwaila take a gidan miji akan haihuwa? Wai bai son tara yara, kuma harda mari? Shin ina gatan nata da isar? Lalle ta kara gode Allah, wasu nan suna nema,gashi ita mai gorin tana haifa amma mijin bai so, mey kenan akai? Kai ta kara jinjina mata, kawai sai taji tausayin ta, dan sosai taci a tausaya,daga mari gaba ai sai duka. Tana haka sai ga nan mai gidan ya shigo shida Mohammad, har yanzun mita yake akan mijin Huwaila. Har suka zo k'wanciya yana na nata abu d'aya, dan tsaf ya nuna musu shifa ga ra'ayin shi. Ga nan wayar da sukai da Huwaila dazun har marin ta sanar shi. Dak'yar Fure ta samu ya dan lafa tana dan "massaging'' kanshi. "Allah Pretty mutum wani bai da godiyar Allah sam, tsam tai tana jinshi, "ki duba wani ya samu Allah ya k'wace au duk'a, wani koh d'aya bai samu ba nema yake amma lokaci bai zo ba, sai shi ne dan t'sabar butulci ma Allah ya bashi su,sannan yai mishi wadata sannan yace bai so? Wace iriyar rayuwa ce Furii? Tsam ta k'wanto kanshi cinyarta cikin nutsuwa take dan shafa kanshi, "kai hakuri, nasan da ciwo, amma ka d'auka wannan kad'an daga dabi'ar dan Adam, kawai adu'a yake nema Allah ya shirye shi Dear. Kai ya k'ada, "da k'yar ne,dan fa ra'ayinshi ne na rashin son tara yara, sam tun farko banso auren Huwaila da mutumin nan ba, amma fir ta dage ita sai shi,irin abinda nake hanga mata gaba kenan. Murmushi tai,kan tace "adu'a zaku mata,Allah kawo mata sauki. Kai ya k'ada,"toh Amin. Har suka k'wanta tunani ne fal a ranta. Hakan yasa ta kara gode ma Allah,dan ya bata Ni'ima sosai a rayuwa. Wanda in zata butulce dan Allah ya tauye mata d'aya batai ma kanta adalci ba. Dan tayi imani tafi Huwaila k'wanciyar hankali a gidan Miji. By Feenat Ja'afar. [4/27, 12:10 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 30_Abu kamar wasa maganar Muh'd da Maryam ta tabbata, dan ko gare ta bata ta6a jin wani saurayi a rayuwarta ba sai Moh'd, bayan dan jan ajinta daga baya ta yarde, tuni suka dinke. Sosai Fure tai matukar Farin ciki da wannan had'i, zata so ganin yadda Momy zataji wa Muh'd zai aura, sannan za taso sui ar'ba da Hassy ido da ido. Dan fa har anje tambaya, d'uk da Abba yaso da yaki yarda ganin yaushe ma yayi aure da zai kara mata? Sannan ga nan sauran yayunshi ba mai mata biyu. Yau ne ranar da likitan da take gani yace ta dawo,d'uk da tasa a ranta daga yau ta bar jelar asibiti, ga nan Ogan baya gari. Kamar kullum yau ma ya gama dubata yace komai "normal" lokaci ne d'ai bai yi ba. Sai ya bata kan taje tai "blood test", dan shi kam bai gane ba, gashi tace period nata ya wuce da k'wana yau goma. A "lab'' ta zauna rint'se da ido za'a d'au jikinta. Sosai ta t'sani ganin allura,amma dake abinda rai ke so ne shi yasa ta yarda. Auduga ya bata ta d'anne gun yace ta zauna a chan ta d'an jira. Kusa da wata mata ta zauna,a hankali taji kamar matar na shesshekar kuka kanta duk'e. Da mamaki ta zata ko batta lafiya ne, sai tace mata "sannu baiwar Allah, kiyi adu'a ki bar kuka. A hankali matar ta dago,zata fi Furen da shekaru kusan bak'wai, idonta ya k'ada yai jajir halamar tai kuka har ta gode Allah. Sai tai ma Furen murmushi kan ta goge hawaye wani na kara zubar mata. Kawai sai ta tashi ta fita da result na "urine test" a hannu. Ba'a jima ba ganin an sa ai da sauri suka fidda ma Furen result. Ido rufe ta fito, tana mai fatan in ta bud'e taga "positive". A d'an gefen "lab'' d'in ta t'saya,matar nan ce zaune tana cigaba da kukanta, sai ta juya mata baya tare da bud'e ido, sai ta ware "result", Da sauri ta rint'se ido sai ga hawaye. Bata nufa ba taji kuka ya su6uce mata wanda batasan ma na meye ba, ta kusa minti d'aya kan ta t'sagaita jin ta kusa da ita tai shiru, sai ta juyo ta k'alleta, itama Matar ita take k'allo hawaye na zuba, sai Furen tai mata murmushi tare da sa bayan hannunta tana goge ido, da mamakinta sai taga matar itama na murmushi tare da itama goge hawayenta. Sai ta taso tazo gun Furen, tare da ce mata "ina fatan ba matsalar mu d'aya ba y'ar uwa? Murmushi Furen tai tare da k'ada mata kai, dan batasan tata matsalar ba. Hannu matar tasa ta k'ar6i "result'' d'in hannun Fure ta duba. Da mamakinta sai taji tai murmushi mai sauti, wanda agun Fure wani hawayen ne ya kara saukar mata. k'allo Furen tai,kan tace, "hala kina gudun a kira ki da JUYA ne sister? Da sauri Fure ta dago tana k'allon matar, da mamaki tace "ya akai kika sani? Murmushi matar tai,kan tace "za kiga likita ne koh gida zaki? Kai ta girgiza mata, "yace in "Negative'' ne ba sai na dawo ba. Kai matar ta k'ada, tare da mika mata nata result d'in, "Pt=positive" taga, sai ta dago ta k'alli matar da mamakin toh mey yasa ta kuka bayan nata ya nuna "positive"? Hannun Furen ta kamo, "muje,nasan za kiyi tunanin mey ya sani kuka? Tafiya suke tana sanarta "nima irin kice da,kullum nazo asibiti naga "Capital Negative" sai nai hawaye, amma na yau na daban ne, rakani na kai mishi result d'in kiga. Ita d'ai Fure binta kawai take,dan sosai ta kosa taji meye dalilin kukan matar nan. Da mamakinta likita d'aya suke gani da ita, sai ya juyo ganin su tare da Fure, tuni sai fara'ar shi ta karu, zaton shi Furen ta samo "positive" ne. Sai d'ai yana k'ar6a ya girgiza kai, "madam kiyi hakuri,ki kara adu'a, kin ga nan y'ar uwarki, in kinji nata zaki gode Allah ne. K'allo matar, kawai dan ya hucer mata da zuciya yasa kullum tazo yake bata "pt'', amma shi yasan sai wani ikon Allah. Sai d'ai yana bud'e result da sauri ya d'au "glass" ya kara dubawa,sai ya k'allo matar fuska d'auke da mamaki, "madam, result d'in kine wannan? Kawai maimakon amsa sai ta kara sakar kuka. Ita Fure har matar ma ta fara bata haushi, dan a ganinta abin farin ciki ne wannan ba wai na kuka ba. Sai dai jin abin da likita yace yasa ta K'allonshi. Abin yai matukar d'aure mishi kai ne, har bai san sanda ya kara k'allon result d'in ba yace"how is this possible? Tashi yai, kawai yace su biyo shi, ita kam Fure sai ta bi su. D'akin"scanning" suka nufa, Fure zata t'saya yace ta shigo itama, taga ikon Allah. Ido yasa ma allon "machine d'in scan" d'in yana k'allo. A hankali ya furta"lalle d'ukkan ya6o ya kara tabbata ga shugaban halitta. Take ya tuno da kalmar shi ta "how is this possible, nan take ya Istigfari ga mahaliccin shi, take ya kara gaskata k'arfin iko na Allah,domin gareshi " everything is possible ", gashi cikin ikonshi yace "KUUm..sannan FAYA KUM d'in,matar da suka sanar da mijinta cewar bazata haihu ba gashi Allah gagara misali yai iko nashi kanta. Ajiyar zuciya ya sau, kan ya k'allo su, "madam kinga ikon Allah koh? Mai iko akan d'uk abinda yaso.. " a gaskiya "case" d'inki shine na biyu da ya ta6a bani mamaki tun fara aiki na. "Yanzu kam kuka ya kare miki, 4 good ten years yau Allah ya nuna ikon shi akan ki, kiyi murna da godiya ba wai kuka ba. Kai ta k'ada, ita d'ai Fure ta kasa gane inda suka suka dosa. Ta d'ai gane matar shekararta kamar goma ne bata samu haihuwa ba sai yanzun. Kan Furen ya dawo, "matar "pharmacy" ki dad'a hakuri, dan tabbas matar nan ta ishe ni ishara. "Kisa a ranki in har baki haihu ba Allah ne kawai bai nufa ba. Kai kawai ta k'ada mishi, tare da k'allon matar, sai yai rubuce-rubucen shi da taimakon tambayar da ya yai mata, da murmushi ya dago, "in har lissafin nan d'ai-d'ai ne toh cikin nan ya ma shiga wata na hudu fa,right? Kai ta k'ada mishi, dan wata hudun shine karshen y'in period nata,d'uk dama ba wai "regular" bane. By Feenat Ja'afar. [4/27, 1:59 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 31_Iyanzun ta d'aina kukan, sai d'ai takan k'alli Fure da itama kawai k'allon matar take cike da tambaya. Sai tai murmushi, d'ai-d'ai wata mota ta k'allo Fure, "zan so k'warai in kin yarda ki bini in dai ba mai d'aukar ki na baki labarina,nayi imani daga yau kin d'aina wahalar da kanki a asibiti, da daga yau kin d'aina kula zancen jama'a har yazo suna saki a bak'in ciki, da na zame miki Aya a rayuwar nan tamu. Kai Furen ta k'ada, kan ta d'au waya ta buga ma Ahmad dan neman yardar shi. Mota ta shiga,halamun ya barta,yayin da matar ma ta shiga tata, a hanya take binta,har suka t'saya a d'ai-d'ai wani gida, sai taga ma matar batta nisa da unguwar su Umma. "Horn" matar tai aka bud'e musu "gate". Gidan bai fi rabin nasu Fure a girma ba, suna "parking" matar ta fito, da murmushi tace ma Fure "Bissmillah. Kawai ta rasa dalilin da ya sa ta nacewa matar d'uk da bawai ta santa ba. Suna da rufin asiri d'ai d'ai g'warg'wado, ta kama Fure ruwa da lemo kan ta d'aura musu abinci. Nan da nan itama taji kawai ta aminta da Fure,sannan da taimakon jin likita yasanta. Zama tai kusa da Fure lokacin da ta fito a kitchen, sai tai mata murmushi, ganin tun dazun Fure na ta binta da ido,ita so take ta gano inda cikin ya makale har na wata uku, sam sai ka zata cikinta ne,dan d'uk yabi jikinta. "Da farko d'ai sunana Fatima,ina da shekara 29,ni y'ar Kano ce, aure ya kawo ni nan, k'anin Baban mu ne kawai na sani a garin nan, sannan a wani hutu nazo garin nan muka had'u da Salman,Allah d'ai yai ikon shi har na yarde wa auren shi, sosai ya nunan so tamkar ba gobe,har hakan yasa na mance da kad'aicin iyayena, abu d'aya na fara fuskanta shine sam y'an uwanshi basu son kular da yake nuna min, a hankali ya rage wasu abubuwan tun kan aje ko'ina, sai d'ai d'uk da haka ban nemi komai na rasa ba. "Abi na biyu da fara fuskanta shine jinkiri na ta gun haihuwa ta, dan tun ana min abu da kawaici har ya zamo kiri kiri ake min, wasa wasa har na shafe shekara uku shiru, dan ko 6ari ban ta6a ba. Duk da a bangaren Miji na ban samun matsala sam har na shekara uku. Mukan je ganin likita d'uk wata ni da Salman,ace mu g'wada na gargajiya,muyi na rubutun, amma sam babu cigaba. A wannan lokaci nayi iya hakuri na naga na fita harkar y'an bani na iya dangin Salman sai d'ai sun kaini bango. "Sai ya zama ina d'ari-d'arin shiga cikin su, dan d'uk wani zama bazai kare ba sai an gorata min kan ban haihu ba. In takaice miki sai da na shekara biyar muna jelar asibiti ni da Salman. A wata rana da bazan ta6a manta ta ba munje ganin likita kamar yadda muka saba,tare da "result" na "X-Ray" da aka min "HSG" a wajen mu, shima kuma Salman yazo da abinda za'a g'wada lafiyar k'wanshi, tashin farko farko likita ya tabbatar wa da Salman ai d'uk wai "tubes" sunyi ''blocking". Duk da banyi science ba, amma na gane maganar shi ta karshe wai "there was no chance of conceiving naturally Ever... Wai zai de had'a mu da Ogan shi. "A time likitan dake dubani yaje karin karatu, ranar naci kuka na gode Allah, yayin da Salman ke ta aikin lallashi, ya na iya, kinga d'ai ba wanda zai kaini damuwa, amma in sanar ki a satin har gida akazo aka wanke ni ciki da bai, kan na zama JUYA naki sakar ma mijina mara ya kara aure. Biyu sai tazo ta had'e min,bani inda zanji sauki sai agun Allah da gun Salman, dan ko gidan k'anin Baban mu naje sun dunga fad'in "Allah sarki Fati,shiru koh? Sai tai murmushi, hakan yasa suma na rage zuwa gidan sun, dan sosai suke kara min damuwa. Har ranar da likita ya dibar mana ta cika banji Salman yace na shirya muje ga likita ba. Sai da dare nai mishi magana, d'uk da naga yana ta cika da bat'sewa. Budar bak'inshi sai yace shi ba inda zashi. A lokacin nai mamaki, dan sam bai ta6a min haka ba, Washegari sai ni naje, da ikon Allah wannan likitan ya had'a ni da Ogan su, ni d'ai naji yana mai bayani da turanci kan wai ai min "laproscopy to "unblocked" my tubes. A lokacin da ido nake binsu,sai dai suna fad'in zasu dan min aiki kad'an na t'sure. Tun daga ranar ban kara bi takansu ba, shima kuma Salman bai tambaye ni ya akai ba. I yanzun kam na ma fidda rai ga haihuwa, tunda sun sanar ni in dai ba'a bud'e ba ba zancen haihuwa. Haka na cigaba da toshe kunne na,ranar ana biki gidan k'annin Baban mu naje, kusan d'uk y'an uwa sunzo, sosai nai farin ciki a ranar,muka rankaya gidan amarya, chan kusa da y'ar gidan k'anin Baban mu naje dan ganin kujerar da take kai ce kawai da waje. Da zuwa na dama ta fara ta6e baki, cikin wasa na kula take watsan magana musamman in naje gidan ta. Zama na kenan tai saurin mikewa tana fad'in "a Fatee kar ki min illah man, d'uk na k'alli y'an d'akin kowa na sabgar gaban shi, sai nace " mey kenan hakan yake nufi cikin wasa. Sai yamutsa fuska, "kinsan cikin ba irin naku bane.. Sai tai waje ta barni da k'allon bayan ta,sai a sannan ne na kula da karamin cikin jikinta. Ranar har nazo gida ina mamakin maganar Maryam y'ar k'anin Baban mu, tun daga ranar nasa a raina na dena jin haushin kowa dan ya kirani da JUYA, tunda ga nan y'ar uwata ma ta jini ta ya6an magana. Sosai abin ya t'saye min a rai,har na sanar ma makociya ta lokacin muna a tsohon gida. Sai ta sanar ni ak'wai wani Malami ya ta6a yiwa yayarta aiki irin nawa,a watan ta samu ciki. Jim nai,zuwa wani lokaci nace zanyi shawara. Ina fita naji sam abin bai k'wanta min ba,dan in da abinda da nat'sana bai wuce bin malamai ba. Wasa wasa har muka shiga shekara ta shida aure, sam Salman ya sauya, abu kad'an hanci ni, ba makawa ya fara d'aukar zigar y'an uwan shi kila. A satin ne kuma naje gidan su duba Umman shi, sam ban kawo zan sami y'an uwan shi a gidan ba. Kusan sai nace d'aya ce bama y'ar tsama da ita,sai ko Hajiyan shi. Tana a k'wance a gado suke ya6an magana, sam bata hana su, sai d'ai ma ta d'auke kai, shi yasa na kasa gane inda ta dosa. Da gan gan d'aya ta k'allo d'aya kamar yadda suka saba, sai d'aya tace ma d'ayar tana ta had'a kiba ina zata kai, duk ina kallon su, budar bak'in ta sai cewa tai "ai ni tawa kibar da dalili, ba kashi kawai take sau wa ba gidan Miji. A ranar na kasa hakuri,har na sanarwa d'an uwansu irin maganganun da suke ya6a min. Sai tai murmushi ta k'allo Fure tana hawaye. "Kin san mey yace min? Kai Fure ta k'ada, sai ta tashi tai kitchen tukun ta dawo. Har yanzun hawaye na binta, "budar bak'in Salman sai cewa yai waye bazai so ganin k'wanshi ba a rayuwa.. A ranar ya tabbatar min da cewar shekarun sa na ja, a gaskiya zai kara aure dan wai ya min kara... Kuka ta fara Fure na lallashi, "wallahi a yadda nake son Salman in ta gunshi ne wannan matsalar zan zauna dashi har karshen rayuwa. Ranar nayi kuka kamar nai mey,dan a fili ya nuna ya gaji da Gaza wata ta rashin haihuwa. "Zuciya batta kashi, Washegari na tambayi unguwa, ba musu ya barni,ban zame ko'ina ba sai wajen makociya ta, dama kamar tana jira,har da ita mu kaje gun malamin da yayarta. Zuwa na farko ya bani turare da layu kan in zan k'wanta na d'aura layar a mara ta na shafa turaren,in dai har mun kasance tare da salman zan samu ciki. Har yana fad'in wacce ta fini matsala ma ta haihu bare ni. Hawaye ta goge,halamar abin da ta tuno bai ba. By Feenat Ja'afar. [4/27, 3:30 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 31_Haka ina jin ina gani nai "shirka", dan na had'a Allah da wanin shi, sam ba yadda zaki ce wannan mutumin Malami ne ba boka ba. Ana nan ana nan,har wata na biyu ya kama shiru,ba ciki ba dalilin shi, har na hakura, sai d'ai in na tuna da gorin jama'a nakanji k'warin g'wiwa. Haka na nad'a muka koma wajen bokan nan chan bayan gari, tuni sai ya fara sirkulen shi, kan ya k'allo ni yana fad'in dole sai an min babban aiki, ba musu nace na yarda,duk ban san meye babban aikin ba,ni d'ai burina na fita sahun JUYA. Turare ya kaini wani d'aki ya banka min, d'uk sai da yasa na cire kaya na gaba d'aya, ganin na t'saya gardama yasa yace in cire g'yale na da dank'wali. Sannan yace lalle-lalle gobe na dawo in ina son haihuwa, sannan kar nai mishi gardama. Har muka fito makociya ta da yayarta suna min fad'an mey yasa na t'saya gardama? Kasa da kaza,kasance war mun gaji yasa muka sauka gidan yayar makociya ta. Muna a gidan zaune sai ga nan y'ar matar ta farko ta shigo tana masifar kan wai uwar bata bar musu abinci ba. Yarinya har murguda baki take, sai uwar taji kunyar gani zaune ta tashi ta jata waje tana nad'a. "Wato abinda naji yarinyar na fad'a wa uwar ba karamin tsorata nai ba, ina k'allon makociyata itama ta fita tana kumfar bak'in wai ta kara mata. Yarinya sai ashar take maka musu ita da uwar tana Allah ya isanta. Hakan ne yasa na leka dan ganin shin da uwar take wannan zagin ko wa? A inda nake ban mat'sa ba ina mai k'allon yadda ake dam6e t'sakanin matar nan da y'arta tana karo mata zagi da Allah ya isa, tuni nai d'aki na suri jakata na barsu nan,ina jin makociya na kira na gaba d'aya na rikice. Tabbas Allah ya soni da har ya nunan wannan abin da ido na, ba shakka wannan irin yaran su ne wanda naje nema na kusa 6atar da kaina wato " Y'AY'AN ALLAH BANI. Tun daga ranar gani nake na ma Allah butulci,na ci amanar Miji na dan na tu6e g'yale da dank'wali gaban wani kato, sai d'ai nasan rashin abokin shawara na gari ne ya ja min da son zuciya. Ranar nai kukan nadama har naji ba dad'i, cikin zafi na d'akko laya nasa mata kalanzir na kona, sannan na tittilar da turaten yabi shadda. Sam al'amarin haihuwa nama jingine ta gefe,na hau istigfari zuwa ga Allah,bisa had'a shi da nai da wanin shi. Ana haka Salman ya gama gininshi muka tare, sai d'ai da kaga gida kasan na zaman mata biyu ne. Anan ne na samu makociyar k'warai, mai nuna min komai nufi ne na Allah, ita kad'ai nake kaiwa kuka na naji dad'i. Sam na nisanci kowa, in kinganni a gun dangin Miji ko gidan k'anin Baban mu toh biki ake koh suna. Shima a tsatssaye zan shiga na fito, da wannan kawai na soma samun sa'ida, sai kuma aka dawo fad'in dan mijina yai kud'i shi yasa yanzu na fara dagun kai. Sai kawai na bisu a hakan. Har na shekara takwas da aure. Anan ne nake jin labarin dawowar likita gun makociya ta, kan yanzu ya karo karatu ana ji dashi. Zuwan farko yai mamakin jin har yau ban haihu ba, hakan ne yasa ya kara rubuta min ''HSG", sannan ya k'ar6i numbern Salman. Ran litinin sai naji yace na shirya muje asibiti yana dan 6ata rai. Kamar wanchan yauma na wahala gun wankin cikin, sai d'ai g'wajin da ya fito ne yasa daga ranar Salman ya d'aina zuwa asibitin, dan likita ya tabbatar mishi da a gaskiya ba wani "hope", wai k'allemun mahaifata d'uk sun ru6e,wato "tubal damage" a gaskiya likita bai sanar ni ga matsalar ba, amma na tsinkayi wayar Salman shi da wani abokin shi, Gaskiya karan nan ban "losing hope" ba,na sanarwa Umman mu tace nai ta adu'a dan tanaji ajikinta tabbas za naga dan kaina InshaAlllah k'wana kusa. Ana cikin haka Salman ya t'siri abin kirki,tashin farko mu kaje Umara, muna dawo wa ya fara koya min mota. Sosai naji dad'in yadda baya damuwa a rashin haihuwa ta yanzun, sannan in nace zani asibiti da kanshi zai kaini ko ya ban mukulli. Kullum abu d'aya ne in naje,sai likita ya rubuta min awun fitsari d'uk karshen wata. Sai ta karasa da d'an murmushi mai kamar kuka. "Ranar ina zaune parlour ni da makociya ta ina fad'a mata irin abinda Salman yake min na alkairi tana murmushi sai gashi ya shigo da murna. Wai nazo naga abin mamaki, a ranar salman ya mallaka min mota tawa ta kashin kai. Sosai nai murna,marar na baki misali, ana nan koh wata biyu ba ai da yin haka ba naji a gari wai Salman aure zai yi, har ma an kai sadaki. Hawaye ta goge wanda ya zu6o mata, kan tai murmushi, "kawai ni kuma sai na sa mishi ido naga iya gudun ruwan shi. A ranar wata laraba sai ga y'an gidan su nan kusan su biyar wai sunzo ganin d'akin amarya yadda yake tun kan tazo. Ina jinsu suna yadda magana wai alkadari na akan d'an uwansu ya karye tunda gashi da kanshi ya nemi aure. A ranar naji takaici, dan Salman ya nunan ni ba komai bace, abu tun inaji a gari gashi har ya tabbata. Ranar kamar kullum nai shiri na nai d'akinshi, yana a k'wance yana waya. Yana ganina sai ya fara kiran wai zai kira, zai kira, tuni na gane da amaryar yake waya. Sai nai murmushi na zauna a gefen shi, tare da d'aura kaina a kafadarshi, dak'yar na iya saita hawaye na basu zubo ba, wai yau har Honey Salman ke ce min? Dan takaici kawai sai na zame na k'wanta. Sai ya mat'so da tambayar koh lafiya? Kai kawai na K'ada mishi, "kai kad'ai za ka iya bani mutuncin da kowa zai ga d'auka Salman, kai ne kawai za ka bada kofar da wani zai k'alleni yace min ban isa ba... Sai na fara kuka. Nan ya hau wayan ce wa,kan wallahi kunyar fad'a min yake, sai nace mey fa? Sam sai na nuna ban ma san komai ba. Anan ya sanar ni komai ba ko kunya, kuma wai saura wata biyu tazo. Kai kawai na k'ada, tare da mai fatan alkairi. Sam tunda aka fara rad'a rad'en auren Salman na ma manta da zuwa asibiti na d'uk wata. Sai da jiya ta ciwo ni akazo wai za'a kai kayan amarya gobe ga nawa, harda fad'in fatan su ta cika musu gida yara. Sai nai murmushi kawai, a lokacin ne na tuno da asibiti. Fure ta k'allo tana goge hawayenta, itama Furen harda kuka, ashe nata nafila ne akan wasu? Hannunta Fatima ta ruko, "kinsan mey ya sani kuka da naga "positive" a result na? Kai Fure ta k'ada tana mai k'allonta. Sai ta juya gefe da fuskarta, "wallahi tunda nake ban ta6a jin kunya ta mahaliccina ba irinta yau, na sa6a mishi, nai kuka,har nakance Kila wani lefi nai wa Allah shi yasa bai ban haihuwa. "Nayi kuka ne saboda Allah ya nunan komai lokaci ne, gashi kuma na gani, cikin da ban ma san dashi ba,gashi a zuwa d'aya ya saukar da Ayarshi akaina. By Feenat Ja'afar. [4/27, 5:31 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 32_"Sam na manta da cewa bawai rashin so bane yasa Allah bai ban haihuwa ba,da So ne,da na tabbatar ya bawa Nana Aisha(R A), dan Allah na son d'uk wani abinda Manzon sa ke so, na kuma sani a d'uk duniya babu Wanda Annabi yafi So irin Nana Aisha,, tabbas wannan ma Aya ce da Allah yake son nuna ma dan Adam, amma na rasa ina "TA'UHIDI" na yaje a lokacin. "Gashi yanzu na rasa falala biyu a rayuwa, ta farko hakuri,na biyu mukami, dan nasha jin ana fad'in cewar ''Allah yana kunyar had'a ido ga wanda bai bawa haihuwa ba har ya koma gare shi ranar gobe kiyama.. Nayi imani ba abinda a duniya Allah zai hana ka ya kuma ji kunyar ka irin wannan, amma na manta,har sai da ya kure kan na hango shi, na rasa wannan falalar. Sai ta fashe da kuka. A gaskiya yau Fure ta kara samun tuni a game da rayuwa, har batasan itama ta fara kuka harda shassheka ba. Chan cikin kuka Fatee tace,"shi yasa nake son dan Allah ka'r kiyi ma Allah butulci irin nawa, ki k'ar6i K'ADDARA a d'uk yadda tazo miki, dan gudun irin wannan rana ta kunyar Allah. Kai Fure ta k'ada. "Idan anyi Duniya dan Manzon Allah daga rana irinta ta yau bazan kara da na sani akan ban haihu ba. "Zan d'au hakuri,na kuma juri jin yadda ake kirana da JUYA. "Tabbas yau na gane kuran kuka,sannan na tsorata da jin labarin D'an Allah banin waccan matar. Kai Fatin ta k'ada mata, kan tace. "Kawai na amince miki ne tafar d'aya a ganin ki, ubangiji ya baki damar cinye jarabawar ki sister, kar ki bi yewa mutane, za su kai ki ne kawai su baro. "Sannan ki d'aina sanya tunanin kowa a ranki sai Allah,InshaAllah za kiga d'ai d'ai... A takaice Furen ta sanarta itama tarihinta, sannan da address nata, suna cikin haka sai suka ji dirin mota a kofar gate, sannu a hankali sai ga nan mata na shigo wa da dangin mijinta su biyu. A wulakance y'an uwan su Salman d'in suka k'allo su,ba koh gaisuwa suka cewa dangin amarya su shiga ga nan "part" d'in amarya. Da ido Fure tace tai musu magana. Sai ta d'aure ta gaida su, sosai da ganin su tasan za'a buga da amaryar. Har suka gama dak'yar ta kai musu ruwa shima da sa bak'in Fure. D'uk dangin amarya sunyi waje,sai dangin Salman da suka t'saya karewa parlourn Fateen k'allo suna ta6e baki, ganin ya sauya mata kaya. Ci kanku bata ce musu ba, sai d'ai sukai kitchen, d'uk dan su takali fad'a. Wannan karan kam fatee kasa hakuri tai kitchen d'in Fure na kira amma sai sa ta karasa. A bak'in kitchen d'in ta t'saya, bud'e bud'e suke mata suna fad'in "haka d'ai, sai d'ai a ware ciki aci aka iya ai kashi, sai ta basu hanya, K'anwar Salman d'in sai da tazo d'ai d'ai kusanta ta sau mata t'saki. Batai wata wata ba ta sharara mata mari, tuni ta dafe kunci, "ni kika mara? Tass! Ta kara mata wani, wai sai tazo zata rama, ina, Fati da wa Allah ya had'a ta, tuni ta hau jibgarta kamar Allah ya aikota. Fure da d'ayar K'anwar tashi suna ko'k'arin bambare Fati, ganin taki dagata yasa tai waje, sai da ta huce d'uk wani haushi da suka zuba mata tukun ta bari Fure ta k'waceta tana haki. "Ihu yarinyar take dan sosai ta bugu gun Fati. Da gudu Salman ya shigo da K'anwar da dangin amarya. Tuni Fati ta sauya kama ta rike k'ugu, wallahi yau yadda take jinta tai imani ko Salman zata iya nad'a mai duk'a. A yadda yaga Fatin tabbas shima ya tsorata, dan Sam bai ta6a ganin ta burkice haka ba, "Fatima ya haka fisabilillahi? Abinda ba halinki ba shine yanzu zaki t'sira saboda zan kara aure? Wannan ai hauka ce.. Wata uwar harara ta sau mishi, kan ta k'allo k'annen yadda suke doka mata harara, data zabura tace "ku t'saya,ba akan ku na haukace ba? Sai tai kitchen,''yau wallahi za kaga d'anyen kai. Bai nufa yaga ta fito da gudu da muciya tai kan k'annen shi da dangin amarya, habawa,takai ta kai, kowa hanyar gudu yake nema, har gate ta bisu tana muka musu a d'uk inda hannunta ya kai. Fad'i take "ba haukatar ni kuke so kuyi ba? Bari toh na fara ta kanku, haki take tana "naga wata shegiyar da zata kara zuwa har gidana ta ci mutunci na d'an... Saukar Mari taji a fuska, da sauri ta y'ar da muciyar ta K'alloshi tare da dafe kunci. "Salman... Mari? Ni ka Mara? Cikin tunzura yace"an mare ki d'in.. Koh nima zaki dake nin? Kai ta girgiza,tai cikin parlourn, kawai sai ya bita yana kara sauke mata sababi, "Aure ba fashi, wallahi sai d'ai kiyi abinda zakiyi, dama tunda naga har yau baki tanka a auran nan ba nasan da abinda kike shirya wa. Da mamaki take K'allonshi.. Kan ta rint'se ido da murmushi ta furta "Na Miji?Namiji? Kawai sai tai k'wafa. " Ba laifinka bane, sai d'ai ka sani, wallahi na bazan zauna na jidi wannan rainin hankalin ba har wata ma ta shigo ta kawo min raini ba.. Hannu ya hard'e kan ya k'allota, "yanzu mey kike so ayi? Da sauri tace "saki.. Kai Fure ta hau girgiza mata, sai ya k'allo Furen yai Murmushi, "toh wallahi bazan saka ba,aure kuma kamar anyi an gama ne.. Cike da bala'i tai woo kanshi, "wannan ne kuma baka isa ba wallahi. kawai sai ta rufo kofar parlourn,"in har ka fita a gidan nan toh ka Sake ni, na tsane ka, ban son ka, koh kaunar ganinka yanzu bana yi. Kafada ya make, "kiyi komai amma wallahi bazan sake ki ba, sai d'ai zaki iya zuwa ko'ina ne in ma baki son ganin zuwan amarya bazan hanaki ba. A masife ta ta kutuntumawa Amaryar zagi, kawai sai ya hau mata dariya. Ganin tana neman fita a haiyacinta yasa Fure kamo ta. Sai sukai d'aki. Tuni ta hau tattare kaya. "A'a sis Fatee, jama'a za su miki k'allon kishiya ce ta kore ki fa... A masife tace"sumin.. In dai jama'a ne ai ko na zauna zasui komai, wallahi bazanyi kaffara ba sai na bar gidan nan. Yin duniya Fatee taki hakura. Sai da tai katuwar "trolley" kan ta janyo taiyo parlour kan ta koma d'akko hijab,, yana ganinta ya mike, dan sam bai zaci da gaske take ba. "Fatee kar muyi haka dake, a masife ta ja jakar har tana bi da ita ta kan kafarshi, har ta kusa kofa ta tuno da jakarta, ita d'ai Fure sai binta take a baya tana tai hakuri. Jakarta ta zuge, cikin masifa take birkito kayan ciki, "ga Fatee matsiyaciya, "cheque" dinshi ta hulla mishi, kan ta d'au mukullun mota, "duk ka jika kasha, ni ba masiyaciya bace, sannan ka sanarwa da dangin ka su zuba ruwa a kasa su sha, na barka har abada.. "And 2 hell with amaryar ma. Ganin gaske ta d'au zafi yasa kuma ya kid'ime, "Fati ka'r kuskura ki fita ba da izini na ba, Fateema, ko ta kanshi bata bi ba, burin ta kawai ta bar gidan, mukullin Fure ta k'ar6a ta bud'e mota, a baya ta sa jakar, sai gashi ya fito, "Fatee ki saurare ni pls? Yanayi yana k'allon Fure kamar mey nufin ta sa baki, ita kam Fateen ma sai ta fara bata tsoro,don d'uk ta firgice mishi. Shiga tai da zummar tada motar ya rike kofar gam, "Fatima pls, kira take "ka cikan murfi mota, ba kace naje ko'ina ba? Kai ya girgiza, "hakuri, wallahi da wasa nake.. A tunzure tace "wasa? Da sauri ya jijjiga kai, "eh, kiyi hakuri.. Wallahi ko na kira su Abba? Da tai wani kukan kura da k'arfi taja murfin motar, "Allah baka sa'a. "Reverse" ta fara yana kiran sunanta, amma ina, ga unguwa kamar ta mayu ba kowa layin, da sauri ya shiga dan d'akko waya yasan Abba kad'ai zai t'sayar mishi da Fatima. By Feenat Ja'afar. 庐NWA 9/29/16, 2:39 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 33_Sosai take kudu dan ma kar ya cimmasu tai ta k'wane-k'wane, sai da ta tabbatar da ta mishi nisa kan tai "parking" achan gefen titi tana k'allon gabanta ba koh kiftawa, haki take tana jawo numfashi tamkar da kafa tai gudun. Fure ta k'allo ta "Kiyi hakuri ki kori shedan sis Fatee... A "stirring" motar ta d'aura kanta ta sau wani kuka mai k'arfi, kawai sai Furen ta zuba mata ido dan ko zata huce ta hakan. Sosai tai tana mai kara t'sanar halin mutum. Sai da tai mai isarta kan ta share, a sannan Fure ta fara ce mata komai yai zafi maganinshi Allah, ta duba halin da take ciki kar ta jama kanta matsala. Ita d'ai uffan bata ce ba,sai ma hawaye dake k'waranya. Wayan ta taji yana kida, a hankali ta sa hannu a jakar ta ciro, "Abba" ta gani, tuni sai ta seta kanta kan ta d'auka. Ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sannan ya sanar mata kar ta fara dosar inda suke tunda akan kishiya zata sa6i mijinta. Har ya kashe in banda kuka ba abin da take, sai ta share idon, kawai sai ta raya mata tai yola dangin Ummanta kawai, Fure ta k'alla sai tace tazo ta tuka. Ba musu sukai musanye, "kaini tasha.. Kai ta k'ada mata ba musu, sai ta d'aura kai a gefen kujera tana k'allon gefe hawaye na t'silalowa. Kai ta daga ta k'alli Fure lokacin da taji tana "Horn" sai Furen ta d'auke kai. Har suka shiga gida bata k'allo ta ba. "Tasha nace ki kaini fa.. Fita Furen tai had'e da bud'e baya ta ciro kayan Fateen. Kawai sai ta bita taga iya gudun ruwanta. A parlour ta sauke, a takaice ta karewa ko'ina k'allo kan ta zauna, sai Furen taje "fridge" ta d'akko mata sassanya ta tsiyaya a cup tare da tsayawa a kanta ta bata. D'uk sai kuma ta fara kunyar Furen,ba musu ta k'ar6a tak'wa shanye tare da mikawa Fure,kara mata tai kan ta zauna, tuni sai ta sau ajiyar zuciya. Kai shedan mugune, nan da nan zai sa ka tafka tsiya zuwa anjima ka dawo kamar ba kai kai ba. "Koh kud'in mota baki taho dashi ba,hala zasu kai ki k'yauta? Sai a sannan ta tuna da ba ko sisi d'uk ta zube mishi t'siyarshi. Yanzu mui sallah,sai muci abinci,"I know babyn mu yau ya jigata, dan yau Momyn shi taji k'arfi... Dariya suka sa Fateen na goge hawaye. Sallah sukai ta d'akko mata dan "snacks" ta rage kan ta tafasa musu ko taliya ne. Zama tai lokacin da take dumama miya tana murmushi, "Ashe kin iya fad'a haka sis? Kai koni na tsorata fa, kai ta k'ada. "Mutane ke koya maka d'uk wani hali da ba naka ba. "Amma wallahi da gaske na t'sani Salman, ko ganinshi na t'sani yi, sam namiji bai da tabbas. Kai Furen ta k'ada, "kiyi hakuri, komai mai wuce wa ne. Ki zauna anan zuwa gobe AA ya dawo sai ya bamu shawarar yi.. Da sauri ta k'allota, "namiji ne zai bamu shawara? Da rashin fahimta Fure ta k'ada kai, sai ta girgiza kai,"toh a gaskiya bazan zauna ba, dan maza sun shani tuni na warke... Kiran Salman ne ya shigo tana ji taki d'auka, dan "ring tune'' nashi "special" ne. t'saki ta ja ta tashi ta d'au wayar ta d'anna "reject" kamar ta cire "buttun" d'in wayar. Ko ajiye ta batai ba ya kara kira. Kawai sai ta kashe wayar gaba d'aya. Shikam suna fita ya dawo d'aukar mukulli ya kira Abban Fateen, suna gamawa sai ga nan kiran likita, da mamakin shi ya ji yana mishi "congrats" wai ya zama Baba.. Kamewa yai gu d'aya lokacin da yace ma likita shi bai fahimta ba ya sanar shi. Sai ga nan takardar asibitin ya d'auka da ta bari. Kai ya dafe kai, har da k'wallarshi, wanda bai san ta meye ba. Abu d'aya ya sani yaso Fatee har yau d'in nan. Tuni ya bisu ko zai same su, shine har tasha amma ba Fatee ba kalarta. Dak'yar Fure ta shawo kanta ta zauna suka k'wana, kusan k'wanan zaune sukai suna firar duniya, fir taki ma k'unna waya bare a kira ta. Washegari Fure da taryar AA ta tashi, sai d'ai Fatee na tayata tana ta6e baki, dan gaba d'aya maza sun sane mata t'saf. Ita dai Fure murmushi kawai take binta da shi. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 28 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 34_Sai kusan magriba AA ya shigo, a gajiye yake, lokacin suna a d'akin baki ita da Fatee kan lalle ita sai ta tafi, suna cikin gardamar taji dirin motar shi, sai ta fita tare da kulle Fatee ta waje, sam bata so ta tafka kuskure. Kamar ba kowa ta t'ar6e shi da fara'ar ta, kamar kullum ya kimtsa kan yaci abinci, sai kawai suka hau soyewar su ta ma manta da Fatee. A zabure ta mike a cinyar shi a parlourn tai d'akin baki da gudu, da sauri shima ya mike yana "lafiya pretty? Tana bud'e ta tana zaune a gefen gado ta k'wando mata harara. Sai ta kara rufota kan ta kama hannun AAn sukai d'aki. A nutse ta sanar shi komai harda hawayenta, sai kai yake jinjina wa, lalle taga tasku, amma yafi ganin lefin mijin. Parlour suka dawo ta kara bud'e Fatee, kamar mey jira sai gata sanye da g'yale da Jaka a hannu, "dan Allah karki t'sayarni, ki barni na tafi nagode k'warai... Shiru tai ganin Ahmad, sai yai mata k'warjini har batasan ta gaida shi ba, hakuri ya fara bata kan tai hakuri yanzu magriba tayi, zuwa gobe sai su san abin yi, ba dan ta so ba ta hakura,kawai sai taga girman shi. Ita kanta Fure ganin AAn sai taji tana d'an dari dari dashi, dan kawai d'aurewa take, amma ace gaba haka ya faru da ita wai... Hmm sai Allah kawai. Fitowarshi a wanka kenan yaga ta had'a tagumi, sai ya k'ada kai, tabbas yasan maganar dazun ce. Yana k'allonta har ya gama shiryawa ta lula duniyar tunanin dabi'ar maza da mutanen duniya. Sai ya k'ada kai,a hankali ya tako ya iso gabanta ya tsuguna. Ajiyar zuciya ta saukar,kan ta d'an k'ak'alo murmushi, sai ya dafa cinyarta, "I love you pretty... En banson ki sanya shakku, ki cire tunanin komai a ranki, AAA naki ne... bazai ta6a miki haka ba InshaAllah.. Hawaye ne ke ko'k'arin zubo mata, so take ta gaskata shin gaske AAA nata ne? Sai kawai ta sau su suka zubo, hannunta ya ruko,har yanzun yana a tsugune, "Furii believe me, maza ba d'aya ne ba... Tuni ya hau tsumata da dad'in baki,Aiya,ita kam ta ziru t'saf, sai yasa hannu ya sunkuyo da kanta da take murmushi hawaye na k'waranya yasa ''lips" nashi yana tarar su. A hankali ya dago ta suna k'allon cikin idon Juna, tabbas ta aminta AAA na daban ne a sauran maza, a hankali ta zamo itama tai yadda yayin suna mai cigaba da karantar juna ta cikin ido, sai ya tadasu t'saye tare da lafar da kanta a gun zuciyar shi, a hankali tamkar wata baby yake dan jujjuyawa kad'an kamar mai rawa,ita kam Fure anyi luf..cikin nutsuwa ya kara karasa ta da wakar da indai yai mata take jin a sama. Takanji wani nishad'i, har ta manta da komai, sam in kaji yana wakar ka zata shine mawakin, amma kawai dan Furen shi baitin na "Nothing gonna change my love 4 you.... Yake burge shi. T'saf acikin daren ya ware Prettyn shi cikin sauki da lumana, har ya lalla6ata tai bacci fuskarta d'auke da murmushin son shi da jin dad'in baitikan, da yaso yin shiru, sai ya ji tana ya cigaba. Murmushi yai, Mata sai da lalla6a. Da safe suna kitchen yana tayata had'a ''break" ta fito da dan gudunta, a zaton ta ita kad'ai ce a kitchen, hannunta ta cire a wuyan AAn taiyo gun Fateen da ta juya. "Sis lafiya? Gaskiya a d'aina gudu da d'an mu.. kawai sai taji ta ruko hannunta da murna ta d'aura kan cikinta, "wallahi yau sai mot'si yake, cikin murna Furen ta kara d'aura d'ayan hannun tana murmushi, Allah sarki Fatee, fara'a take kamar mey, shi d'ai Ahmad daga bak'in kofa yana ta musu murmushi. Sai lokacin Fatee ta kula dashi, a dan kunya ce ta gaida shi, sai ya amsa yana ya Baby? Sai tai kasa da kai shi kuma ya shire "apron" nashi yai waje. Kitchen d'in suka wuce dan gama aiki, sai g'yada kai Fatee keyi ganin yadda Fure ta zama "Chief ". Bayan sun gama cin abinci ya shirya yace Fure ta kira Fateen. Sai gasu sun fito sanye da Hijab. Sanarta yai ya ji komai, sannan ta zauna anan zuwa yai ma su Abban ta magana, ya d'ai lalla6a ta har ta yarda. Cikin wayo yasa Fure tai mai "copying" numbern mijin Fateen. Sosai take jin dad'in zama da ita kamar sun saba a k'wana biyu. Iyanzu kam,ji take Fure tamkar y'ar uwa ce a gunta. Cikin dabara Fure tasa ta bud'e waya kan zasui "exchanging" number. Tana bud'ewa "texts" d'in Salman na shigowa, d'uk na ban hakuri ne zuwa wai ina take? Tai mishi rai ta dawo, tabbas itace ma had'in rayuwar shi, baki ta ta6e, "yau na gama yarda da dad'in bak'in maza... Ji ni zai rai nawa hankali? Wai mahad'in rayuwar shi? Fure tai murmushi, kawai sai tai k'wafa ta hau goge su tana mita. Ita d'ai Fure dariya take tana tai hakuri. Shikam yana d'akin Fatee ya tasa "result" yana k'allo, waya ake mishi kan yau za'a zo jeren amarya, sai yai jim, "ba yau ba. Kawai sai ya kashe waya. "Delivery report" ne ya fara shigo mishi, da halamu kenan Fatee ta bud'e waya. Da sauri ya fara dailing, da kamar bazata ta d'auka ba, sai d'ai ta waske, ''ya akai? Cikin magiya ya fara "Fatee, Fatima,Batool, haba Bintu na, dan Allah ina kike? Kiyi hakuri pls... T'saki tai, "kaga fa, ni wallahi wannan mayaudaran kalaman naka bazasu min kom ba, ka ma d'aina tambayar ina nake, dan wallahi bazan fad'a ba. " Haba Batula,gaba d'aya kinsa na fita hayaci na, auren ma d'uk ya ficen a ka, ga nan Umma ta tadan nata akanki itama... Da sauri tace "kar ka maida ni bi ta chan, ka zata fasa auren ka zai damen ne?.. Kawai sai taja t'saki ta kashe. Fure tace "a gaskiya yayi nadama fa man d'in nan.. Harara ta dan sau mata, "ke fa na fuskanci bakisan halin maza bane. Kai ta k'ada tana murmushi, sai ta ajiye waya zata kama ruwa, tuni Fure ta sace numbern Salman. Da yamma suna zaune suna wainar filawa sai santi Fatee take, wani abu na ciki, tunda taga positive Washegari ta t'siri t'surfa. Fure sai dariya take mata, "haba mom twins, Wa'ina ai sai Kano, kai ta g'yada tana d'ang'walar y'aji, "haka ne kam, amma ke komai naki ai "special" ne... T'sam Fure ta zuba mata ido tana k'allon ta, ita kam sai zuba santi take, "yajin ki ma na daban ne, a k'wana uku na koyi abubuwa... "Lafiya wannan k'allo? Kai ta k'ada, dan har ta Lula duniyar tunanin AAAn ta,tunda tace koman ki "special" kawai shi ta tuno. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 28 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 35_Bud'e gate suka ji, Fatee tace "d'an mikon g'yale na, hannu ta mika kan ta yafa mata. Shi kad'ai ya shigo yana murmushi, kai kasa Fatee tai mai sannu da zuwa. Sai ya nuna wa Fure waje da hannu, kan ya dawo kanshi,yana nufin ta d'akko mayafi, kai ta g'yada, sai yai waje, ta d'akko ta tarar Fatee zata shiga d'aki, tace "A'a. Mui zaman mu, zasu zauna taji Ahmad na fad'in"bissmillah man, shigo daga ciki. Juyawa Fatiman tai zata tafi d'aki, a tunanin ta ko bako yayi, sai ta ji yace "bissmillah Fatima, dawo kiyi zaman ki, tana juyo wa tai ar'ba da Ango. Tuni ta k'ank'ance ido tare da rike k'ugu, sai ya marairaice mata, kawai sai yaga ta kara mishi ma k'yau dafari. "Mey ya kawo ka?.. Cikin marairaita ya matso, ''haba Fati ta, kamshin masoyi ai baya buya koh AAA? Sudai dariya suke musu. Harara ta sakar mishi, "kar ka yaudari k'anka, dan ka d'auka ban sanka ba All... Shiru tai ganin ya zube mata g'wiwa biyu a gabanta. Sai ta k'allo su Fure, itama k'unne ta kama kan tai hakuri. Sai ta d'auke kai, "tashi malam,bani da matsayin nan, tashi, maza ka rufan asiri.. Ahmad ya k'allo, sai yai mishi da ido kan ya cigaba da gashi. "A'a Batool, wallahi kin girmi hakan, kinsan fa ina kaunar ki, believe me... Sai yasa hannu a wuya halamar ya rant'se, tuni sai ta fara hawaye, da zummar samun nasara ya kara k'allon Ahmad, da halamun d'ai shi ya kit'sa mishi komai. Sai Fure ta k'alleshi da tuhuma tana k'anne ido d'aya, da sauri ya daga kafada halamar ba ruwan shi. "A'a, g'wara ka auro mai haihuwa,, kaga k'wanka kaima a duniya koh? Ni kuma banni rai.. Kawai sai ta fashe da kuka. Da sauri ya matso ta kara ja da baya.. " A'a Fatee, gashi ai Allah ya bamu, kiyi hakuri nayi kuskure.. Sai ya k'allo Ahmad da ke girgiza kai halamar ya k'wafsa, bai aune ba ya ji ta doko kofar. Bugo ya fara akan ta bud'e dan Allah, tana kuka tace dan ciki yazo ba dan ita ba, kuma ciki nata ne ya tafi kawai. Yin duniya taki bud'ewa. Dak'yar yabar gun Ahmad ya jashi suka fita, "gaskiya kai su6ul d baka, sai da nace kar ka nuna mata kasan da cikin nan, za ta d'auka shi ya kawo ka. Kai ya dafe, "toh ya zanyi? Wallahi ni Fatiman ce d'uk ta ban tsoro,sam bamu ta6a haka da ita ba. Dak'yar yace ya dawo gobe kan sun shawo mishi kanta. Sai bayan isha'i ta bud'e dan yunwar cikinta. Fure na parlour, harara ta sau wa Furen, kan ta zauna, "yi hakuri, ga nan abincin ki kici, k'allota tai, "baga nan irin halin mazan da nake fad'a ba, sarakan san kan tsiya, Allah ya kaimu gobe da safe ku ga. Ita dai Fure murmushi kawai take. Washegari bak'wai da rabi a gidan ta mishi, Ahmad ya dawo a jogging ya tarar da mutum a kofa. Sai ya jinjina kai,lalle Fatee ta kunno wuta. Matar da ta gama shirin tafiya sai gata ta bingire da bacci,har d'akin Ahmad yace ya bita, ganan jaka ta had'a tai "ready". Gadon yaje ya zauna a kusan ta cikin sand'a, tana t'saka da bacci taji ana kamar shafa mata mara, da sauri ta bud'e ido, tana ganin shi ta sau kara tun k'arfinta, da sauri yasa hannu ya rufe mata baki,batai wata wata ba ta gant'sara mishi cizon da ba shiri ya cire hannun, "waya baka izinin shiga d'akin jama'a? Cikin jin zafin hannu yace "ban sani ba d'in,, kofa ta nuna, "toh fita, matsowa ya fara, "ba inda zan fita fa, mai gidan yace in shiga. Ganin yana kara matsowa yasa ta fara duben abin duka,kasa ta s'akko da filo a hannu,"kar ka matso nan, tsayawa yai, kan ya kara zubewa, "toh kiyi hakuri, wallahi na tuba, harara ta sakar mishi, "kai kasan wannan, ganin ta ki da lumana shima ya fara fad'a, "dole ki koma, a tunzure tai parlour tana "toh sai naga dolen, kawai sai yaja mata jakar chan, "haba Fati.. Ganin su Ahmad yasa yai shiru, "Dan Allah ku bata hakuri. "Fatima kiyi hakuri, d'uk dan Adam yana da hakan, amma ki duba yai nadama, Fure ta k'allo wace ke magiya,"bai ba wallahi, Ahmad yace"yayi man Fati, kawai sai ta sa musu kuka,nan suka had'u suna bata hakuri,komai sukace Salman sai yai kalar tausayi yace ''na daina. Sai ga Fatee ta fara kukan shag'wa6a, su Fure sukai d'aki suna leken su, tun in ya mat'so tana ture shi har ya runkomota t'sam, sai kuma yace mata yunwa yake ji, kai suka k'ada, "lalle Fatee matsala, cewar Ahmad. K'allonshi Fure tai, sai suka rufe d'aki suna dariya. A ranar suka d'inke t'saf da Salman d'inta. Da zasu tafi suka shige d'aki da Fure, dariya take mata kan ta g'wara bawan Allah, "Hmm,bazaki gane ba, ni nasan mey nasha a baya ai, sai d'ai wallahi har na haihu ba mai gani na a dangin shi, amarya yasan inda zai kaita ba a gida na ba. "Na haihu kuwa, in kika cire Umma.. Toh ba d'an uban da zai d'au d'ana wallahi, dariya Fure take, "a assasauta d'ai, tace "za ki gani ai. ************************ Sadakin Maryam aka kai, d'uk Wa'inar nan da ake toyawa sam Hassana bata ji ba. Anan yayan su Ahmad ya fallasa Momy taji wai K'anwar Fure aka kaiwa, nan ta tada tsiya. Kan wallahi in dai za'a auro Maryam toh Sai an auro Rukayya. Takanas Momy ta Wanki K'afa har gidan Fure ta kare mata tass! Wato wai so take ta gaje musu dangi da t'siya? Toh tasan da saninta, indai har ta yarda auren Muh'd ya faru da Maryam, toh wallahi itama Rukayya sai ta shigo mata.. Da sauri Fure ta rint'se ido hawaye ya zubo. Tab,ana wata ga wata. Tunda har Momy ta rant'se toh k'wa tasan Rukayya ta shigo ta gama... Hannu ta d'aura aka hawaye na zubar mata, a hankali ta furta "wayyo ni.. tama kasa koda ihu ne taji dad'i,kukan ma sai hawaye, koh wata biyu ba ai da kashe "case" d'in Fatee ba ga nata ya d'anno. By Feenat Ja'afar. 庐NWA Feenat.mywapblog.co 9/29/16, 2:41 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 36_Tamkar mara lafiya haka tai lamo akan kujera,har maigidan ya dawo, sam shima bai shigo da walwala ba, sai d'ai yana ganin Furiin ya rikice mata. Dan yanzun daga gidan yake Momy ta sanar shi tazo, ga yaje gun Abba,Abba yace tunda an nace abu kusan shekara nawa kawai ya hakura ya aure tan, dama bai bi takan mama ba, dan t'saf yasan abinda Momy tai agun ta ido ne. "Pretty... Ido kawai ta zuba mishi, sai ya dago ta,d'uk ta sau mishi jiki k'allo ne nata, tuni sai ya tsorata, da k'arfi ya jijjiga kafad'unta "Furera... A firgice ta k'alloshi,cikin sanyi tace "uhmm.. Suna had'a ido ta barke mishi da kuka. Juyin duniya Fure taki d'aina kuka, kawai sai ya sa mata ido shima kamar zai sau kukan. Jijjiga kafad'unta kawai yake halamar rarrashi yana share mata hawayen,sai d'ai yana goge wa wasu na zubowa, kawai sai ya d'auke ta tuni ta damke ido tana cigaba yai d'akinshi da ita, "bathroom" ya shiga,ya cika "bathtub" da ruwa, sai ya bar kofar a bud'e, tana t'saka da kuka ta jita cikin ruwa. Da azama ta bud'e idon,ya k'ada yai jajjajir tana k'allon shi, tuni shima ya fara ko'k'arin shiga ciki, kawai sai ta kara jiniya tana dan bubbuga ruwan da shura K'afa. Shiru kake ji Fure, kuka ya kare. Shi kad'ai yasan "week points" na prettyn shi, dan ka burkita mishi ita da kanshi zai samo kanta, gashi yanzu harda waka kamar ba ita ce dazun ba. Shi kam yana a bak'in gado yana k'allon yadda ta zubo da gashi ta gaba tana gogewa da "towel" daure da wani, tare da wakar "mayafi na bargo nah.. Sai murmushi yake. Da hannu tasa tai baya da gashin fuskarta ta baiyana,mutumin kawai ya zuba mata na mujiya. "Towel" d'in ta hulla mishi a fuska, tuni ya shaki kamshin "shampoon" jikin na "vatika" yana lumshe ido,cire wa yai da zummar hulla mata ta kawar da kai tana murmushi. Bata aune ba taji ya janyo ta gaba d'aya suka suka zube suna dariya. "Wallahi ki tada musu hauka na fad'a miki, tuni zance zaisha ban-ban, cewar Fatee da suke waya. "Hmm, sis Fatee bazan iya ba, in fa wani yaci riba,wallahi wani duka zai ci, kar ki manta a gidan su fa take? Babbar riba ta yanzu na samu Maryam ta shiga gidan Hassana, wallahi ko Rukayya tazo naci riba. "Bari banja da ikon Allah ba, amma in dai kece Furera Muh'd, Matar Ahmad AAA, wallahi Rukayya sai d'ai gani da ido t'sakaninta da Mijin ki. Ki rubuta ki ajiye, bana ke zakiyi "wining" a wannan "battle" d'in, InshaAllah daga wannan karan kin zamarwa Momy ciwan ido,kin zama k'arfen K'afa, InshaAllah ke da AAAn ki TAKALMIN KAZA ne. Ajiyar zuciya tai, sam ta ma sa a ranta Rukayya fa ita ta shigo ta gama, amma bata isa ja da Sis Fatima ba, yanzu sai ta hau mata. "Amin toh, yanzu ma haka ina gida gun shirye- shiryen bikin Maryam d'in, Fatee tace "ita Maryam taji zancen? Kai ta k'ada mata, "mutum d'aya yasan auren Maryam shine fansar zuwan Kishiya ta ba... "Sis wallahi ji nake kamar zuciya zata fashe in na tuno AAA za'a d'aura mishi aure da RUKAYYA. "Ina matukar son Mijina, shima yana sona, ance ba'a "BA'A YABON DAN KUTURU" wai sai ya girma da yat'sa.. "Believe me.. Na aminta da AA, dan shi ya so ni a yadda nake, gashi yanzu ya fiddo ni cikin jama'a. "Sis Teema ya zanyi na rage kishi pls... Buh ki d'aina k'wantar mun da hankalin kishiya bazata zo ba, ki barni na zama "ready'' dan t'ar6ar ta. Shiru Fateen tai, wallahi bata tara sani ga Allah ba, amma a jikinta take jin tabbas auren nan ba mai yuwa bane. Sai dai ya ta iya, kawai sai ta hau lallashinta kan tai hakuri tai ta adu'a in da alkairi toh. Kamar Yarinya haka ta sau kuka a d'akin su Maryam lokacin da suka kare wayar. Hawaye Maryam ta goge, wacce tazo d'aki d'an nuna wa Furen gadon da su Ada suka za6a achan t'sakar gida. Ba koh sallama ta shiga d'akin, da sauri Furen ta hau goge hawayenta. Zama tai tana k'allon fuskarta, sai Furen tai kasa da kai kamar marar gaskiya. "Ya Furera kishiya za'a miki amma ba wanda ya sani? Kai ta dago tana k'ada mata, "toh mey yasa zaki zabi ki muzgunawa kanki dan kawai jin dad'in kanki da nawa? Kai Furen tai kasa dashi, kawai sai Maryam d'in ta tashi tai waje, sai ta d'aura bayanta. "Umma! Umma!!.. Cikin shesshekar kuka take k'wala mata kira, tana zuwa ta wat'sar da hoton gadon kasa, d'ai-d'ai Fure ta taho, "Lafiyar ki kuke kuka? Kawai sai Maryam d'in ta k'ada kai da takaici, "ku zama sheda toh Umma, na fasa auren nan wall... Da sauri Fure ta rufe mata baki tana girgiza kai. Ture hannun tayi tana hararar Furen, "bari kiji Fure, wallahi nafi k'arfin ai "playing" wannan "game" d'in dani daga ke har har dangin Muh'd d'in.. Fad'i take ita kam sam bazata d'au wannan ba, tun wuri yazo ya debi sadakin shi ya ware, ita za'a rai nawa hankali? "Mai suka maida ki? Sakaryar da baki san abinda kike ba ko mai? da har za'a fanshi aure na da kishiyar ki? Kai ta k'ada tare da rike k'ugu. Da taga suna bata hakuri ma tai waje, ba ita ta dawo ba sai da taji kiran Muh'd yana sanarta yazo. Ba jima wa ta karaso, wankin babban bargo ta rufe ido tai mishi, sannan ta jaddada mishi ba ita ba auren shi, dan sunfi k'arfin cin zarafi. Gaba d'aya yai mutuwar t'saye jin masifar Maryam, har ta shige gida kamin ya farga fara t'sayarta. Wasa-wasa d'ai Maryam ko waya ta d'aina amsa nashi, ga a gidan kullum kuka, barin ma da taji irin cin kashin da dangin ke ma Fure, mamakinta d'aya "wai shin ina masifar Fure tayi? Ina wayonta? D'uk da tana matukar son Muh'd amma mutuncin y'an gidan su yafi k'arfin komai a gunta. Sai d'ai shi Abba yace sam bai san zance ba, tunda taki fad'a mishi dalilinta na fasa auren k'anin mijin Fure. Tanan kawai suka samu cikas. Biki saura sati uku, in kaga Fure d'uk zabge, amma k'arfin halinta yasa sai mai kula zai gane. Yauma tana gida, Umma sai tausarta take kan ta cire damuwa, tabar wa Allah komai, Maryam ta k'alla wace tun ranar ta d'auke mata kai, sai tai murmushi. "Maryam.. Banza ta mata, d'uk da tabar abinda take. Bata damu ba ta kara cewa "Maryam tun ranar chan naso son kisan k'in auren ki da Muh'd tamkar kin bawa Momy damar cin galabar mu ne, dan dama so take a fasa naki, wanda nai imani baza'a a fasa na Ahmad. "Maryam.. Kiyi hakuri kibi zuciyar ki, ni ki bar nawa gurin Allah, ki sani fasa auren ki, bazai sauya zani gun Momy ba. Matsowa tai ta dafa hannunta,d'uk Umma na k'allon su. "Maryam, kai ta dago tana hawaye, sai ta share mata. "Ki min alkawarin sauke gammon nak'in nan da kika d'aura, ki duba so,da kuma kaunar da bawan Allah nan yake miki, da naso auren ramako dake, ashe kana taka Allah na tashi, kar ki bawa Abba kunya, ki manta dani, ki fuskanci Moh'd, ina rokon ki... Dago wa tai ta k'alli Umma, sai Umman ta tashi ta basu gu, sai ta jijjiga wa Furen kai. "InshaAllah, amma fa ki sani, wallahi d'uk dan uban ni da ya nemi takani zan murje mutum.. Kai ta k'ada mata, "wannan ban hanaki ba, ba kuma zan fara hanaki ba. Da wannan ta samu suka d'inke da Muh'd d'in, aka cigaba da hidimar biki a gidan guda biyu. Dan sam ko kusa Ahmad bai ko mot'si, asalima Fure ke tambayar shi wataran kan abinda yake shirya wa, banza yake mata. Ita kam bangaren Momy koh a jikin su, d'an ko ita ta isa yiwa Rukayya lefe, yayinda a bangaren Mama tasa wa kowa ido, daga Ahmad d'in har Muh'd,dan ba mai ne manta cikin harkar kara auren shi. Ku tambayen ina labarin Hassana man?..Lol. Hassana d'ai sai ana saura sati wata d'aya biki kan taji labari, akanzo har gida ana tambayar ta da gaske mijinta wai zai aure? Wataran harda shewa zata bada amsar A'a, Yayanshi ne zai kara aure dan matar ba ta haihuwa. A ranar Momy ce ta tare ta da zancen ba koh rufi, haka ta dawo gida ta hauka cewa Muh'd, yayi lallabin duniya taki, a fafur sai ya fasa, sai d'ai a ranar da tasan wa zai auro mata tattare ta bar gidan. Sai dawo wa yai yaga gida a bud'e tayi gidan su, hakan ya bashi damar cigaba da shirin auren shi cikin nutsuwa da aminci, bai ma kara bi takanta ba. ************************ Ana saura k'wana d'aya aure har gida Momy tazo ta chake shi harda kukanta kan wai ya mayarta mahaukaciya, ita kad'ai take kid'anta a auren. Tuni yai shiru, Fure dake kitchen d'akko ruwa tana jin yana fad'in "nifa Momy kar a kaini bango nai ba d'ai d'ai ba, dan wallahi bazan auri Rukayya b... Mari ta sauke mishi, tuni Fure da akai akan idonta tasau "tambulan" din lemon ya fashe tana k'allon Momy. Haka ta taka ta durkushe gaban Momyn da g'wiwa biyu wacce ke kukan dan ba ita wai ta haife shi ba, amma ai wai ita taci kashinshi har ya zama mutum "dan Allah Momy kiyi hakuri, dole zai bi umarnin ki, zai auri Rukayya, dole ne wannan. Tun fitar Momy ya kasa ko mot'si daga inda yake, cikin d'auriya Furen ta fara lallashin shi da kalamai masu sanyaya rai, kan Momy kam Mama ce, dole yabi umarninta, kodan ta fita zargin ba sa hannunta a kin aurenshi ba, dan Allah, kuma domin ta... Har kuka tai mishi, shi d'ai kala bai ce ba. A t'saye yake gaban madubi kamar kullum tana shirya shi, sai d'ai yau shirin na daban ne, dan wai shirin d'aurin auren kishiyarta take mishi. D'uk inda tai K'allonta yake, sam tun jiya har yau baida walwala, sai yaga ma kamar shi kad'ai yake kin auren, dan har wani wasa ta d'au abun. Turare take fesa mishi, kamar kullum taja baya tana yaba mishi k'yaun da yayi, sai d'ai wannan karan ci kanki bai ce mata ba, d'uk yadda tai haka yake binta da ido. Muryar y'an gidan Angwayen ne a parlour kan wai sunzo tafiya dashi. Takalmin shi sabo da jiya tasa Muh'd ya siyo mata "half cover" takai gaban shi zata sa mishi, cikin zafin nama ya dagota cikin masifa, cikin t'sawa yace "Mey kika d'au abin ne? Wasa? K'arfa ki mayarni yaro... Gaba d'aya ya burkice mata. Murmushi ta k'ak'alo na dole, tare da d'an zame hannunshi tana fad'in, "relax", sai ta sa hannu kan maballin wuyar rigarshi, har yanzun yana mat'se da ita, "yau fa ba ranar fad'a bane Dear, muje ana jiran ka a parlour. Hankad'a ta yai kan gado,cikin fusata ya bud'e kofar ya doko mata ita. Da sauri ta tashi tasa sakata. Tuni ta zame kasa ta cire d'aurin dank'walin data sha, ihu zata kurma ta tuno basui nisa ba. "Wayyo! Shi kad'ai ta iya furtawa,kan tai ko'k'arin tashi, tuni ta fara ganin jiri,ba shiri ta koma ta zauna, sosai tai k'arfin halin kin nuna damuwar ta gaban Ahmad, da rarrafe ta hau gado, tuni wani irin kuka mai matukar daci yazo mata... "Shikenan ita, ta faru ta kare mata. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:47 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 37_Batta da mai lallashinta kusa,saboda haka sai da tai mai isarta tukun ta samu nutsuwa. A hankali ta daga kanta zuwa ga agogon dake manne a d'akin na hutansu suna k'allon juna. Sai tai lamo tare da kura ma agogon ido,(10:50am), tasan d'uk inda suke yanzu an d'aura na Maryam da Muh'd k'arfe goma, kenan saura minti goma a d'aura na mijinta? A hankali ta yunkura ta tashi,sai ta furzar da iskar bak'inta ta k'ada kai, kaya ta hau cire wa, d'uk k'walliyar ta goge da kuka. Bandaki taje,cikin sauri tai wanka ta fito ta hau shiri, sosai tai k'walliya kamar ma ita ce amaryar, sai ta bud'e "wardrobe" d'inta cikin kayan da ta tanada a fitar bikin ta hau zabi. Akan wata dakakkiyar shadda ta t'saya fara ce,tasha zubi da zare "Orange" da "blue" "gown". D'inkin yasha "stones work" mai k'yau da t'sada, Kai ta kama tattare achan kasan keyarta kan ta kamashi da "ribbon" ya had'u waje d'aya a bayanta. Cikin nutsuwa ta zira rigar kan ta t'saya gaban madubi rike da dank'wali, ta baya ta d'auroshi, yadda gashin zai shiga ya fito ta t'sakiyar d'aurin. Nan da nan komai ya ji, sarka da "bangles'' had'e da zobuna sun hau. Turare ta fara feshi, had'e da murmushi lokacin da ta k'alli kanta a madubi. K'warai ance in kana da k'yau, wai ka kara da wanka, ita d'ai Pretty tanaji da d'an k'yaun nan nata wajen kara k'wask'wareshi ta dawo mai k'yau. D'akin ta g'yara kan ta fito parlour ta kunna "burner", dirin mota taji, a hankali taji gabanta ya fara fad'uwa, kila har an d'aura an dawo... Da k'yar ta iya seta kanta ta had'iye kukanta. Har tai hanyar d'aki taji Fatee na k'wada sallama. Da fara'a ta juyo tana amsa mata. Baki Fateen ta rike, "inye, ka ga uwar gida a gidan AAA.. Kingan ki kuwa? Fuska ta K'awar tana murmushin k'arfin hali. Fatee ta karaso dak'yar tana tura ciki. "Allah ya kawo AAA yanzun, na tabbatar za kisha k'arin angwanci, kai! Ke ko a jikin ki koh? K'allon Fateen take, tamkar ta sau kukan bak'in ciki haka take ji, wai ko a jikinta? "Ki bari ka'r na huce tawa haukar akanki da cikin ki.. Dariya kawai ta hau mata tamkar taga shasha, kawai sai ta zuba mata ido, ji take kamar ta rufeta da duka. Sai ta juya kanta chan gefe kuka na shirin zubo mata, "wato ke da zaki taushi zuciyata, ke kike min dariya ma... Cikin dariyar keta Fateen tace "no,sorry, sorry,... Sai d'ai fa taki t'sagaita dariyar, harda k'walla, Fure na shirin fashewa da kuka ta t'sinkayi Fatee na fad'in "Angon Furera... Da sauri ta rint'se ido, gabanta ya cigaba da d'ukan tara-tara. Sai da ta tabbatar ta had'iye kukanta tukun ta juyo had'e da k'ak'alo musu murmushin dole. Shi da Salman ne, sai d'ai kamar su ma dariyar suke,gogan na ganin ta juyo ya g'imtse fuska, kawai sai taji wani rauni yazo mata. Tun yanzu har ya fara washe baki ni kuma yana had'en rai? K'wafa tai a ranta, da gaske ne kam Namiji ba d'an goyo bane ba. Ji fa yadda ya bar gida yana cin magani amma daga d'aura aure har ya ware,ita kad'ai ya dake wa. "Sannun ku da dawo wa, murmushi Salman yai, kan yace "kinga taso mu tafi kan wannan ''nuclear bom'' d'in ya tashi damu Batool. Harara ta dan sau musu kan ta d'auke kai, sai dai ko ita taga bala'in d'auriyar ta. Tashi Fateen tai tana dafa cinyoyin ta, har yanzun dariya take a ciki ciki, "toh K'awa, sai munzo d'anna kirji anjima. Yake tai mata, suna dariya suka fuce ita da mijin. Fure fa ta cika tai bamm! Kiris take jira ta fashe da kuka. Kan maigidan ta dawo, kawai sai taga yai d'aki ya barta, sam ba fara'a a fuskarshi. Kai ta k'ada, sai ga nan wasu hawaye masu d'umi sun zubo. "Wato ni AA zai manna ma? Dak'yar ta iya tashi tai d'akin cikin goge fuska, tana k'allon kiran Aisha da Adama taki d'auka, gani take yau kowa ya t'saneta, sai d'ai kana k'allonta kasan tai kuka. Jingina tai a jikin kofar tana k'allon yadda ya t'saya a gaban madubi yana kunce "link" d'in hannunshi. K'allo d'aya ya mata ya d'auke kai zuwa ga abinda ya ke, d'uk sai ta kara jin ta samu karaya. D'uk ta marairaice fuska. Karasa wa tai gun da yake kai a kasa taki duban shi, d'ayan hannun ta ruko tana tayashi cire wa,ido ya zuba ma fuskarta yana dan kunshe dariya ganin yadda ta marairaice. Jin burbushin kunshe dariya yasa ta d'an dago tana k'allon shi, suna had'a ido ya kasa jurewa,dariya yake irin ta ketar nan, kawai sai taga an ma mayarta mahaukaciya, cikin fushi ta y'ar6ar da hannun da ta rike ta ta turo baki tana shirin sakar kuka. Maimakon ya t'sagaita dariyar tashi kawai sai nunata da hannu harda rike ciki, tuni k'wa sai kuka ya k'wace mata, bai nufa ba kawai ya ji tana k'wada mishi pillow ta ko'ina ko zata huce takaicinta. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.co 9/29/16, 2:48 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 38_Karewa yake,yana mai cigaba da dariyar, ganin ba gajiya zatai ba yasa ya fara ko'k'arin kar6ewa ya rukota, tun tana tirjewa har tai lumm yana jijjiga ta tare fad'in sorry,sorry. Dak'yar ya samu tai shiru sai ajiyar zuciya take. Kanta ya dago, sai ta rint'se ido d'uk k'walliya ta baci, sai ya sa hannu yana goge mata hawayen sannan ya cigaba da jijjigata da mata kirarin da ke sa ta nutsuwa. Luff,kake ji,ba ko shesshekar, sai yai murmushi, shi kad'ai yasan lagon Prettyn shi. "Pretty"... Ido rufe ta dan mot'sa, sai yai murmushi, "you know.. "My destiny is taking me where my love is. "Kin riga da kin tare ko'ina nawa Furii..har ma ban iya k'allon wasu mata a mat'sayin sun isa balle su kamoki,cos I can see only one thing..hear one thing..and think about one thing... That you pretty.. Ido ta bud'e, sai ga nan hawaye ya zubo,k'allon cikin idon shin take,so take ta gano akasin zancen shin,amma ta kasa.. Ko haka ya barta tasan yai mata lallashi da son shi, sai d'ai kan ta farga taji dan hayaniya a kusan k'unnenta, kamar kuma na d'aurin aure a waya yai "recording". Sai ta mat'se ido,dan jin maroki na fad'in sadaki kamin yace "na auren Rukayya da Nasir.... Da azama ta bud'e ido tana k'allon shi, gira ya daga mata yana murmushi.. Da sauri ta karbi wayan ta kara taro wa, abu d'aya ta kara ji, sai ta k'alloshi wai kuma ta hau kukan dad'i. ******"""" MU D'ANNA BAYa.. Tun bayan fitar AAA da ang'waye dan halartar d'aurin aure suka sauka gida inda za'a taru a tafi nasu Muh'd. Gida ya shiga,"direct" yai d'akin Mama, ganan y'an biki wasu a "parlour", su Ummi yaga,ya tambaye ta Mama, sai tace tana bangaren Abba, sam itama haushin za ai ma y'ar d'akinta kishiya take. Da sallama ya t'saya bak'in kofa, daga ciki Abba ya bashi izinin shiga, suna a parlour Mama na had'a mishi "tea" d'uk yai wani iri, ji yake sam bai zatan samu nasara ba. Bayan ya gaida su yai shiru, Abba ya K'allonshi, "Har kun iso? Kai ya k'ada, kan ya dago kai, da sauri Abba ya ajiye kofin shayin, "Subhanallah, Abba na, kuka fa? Ido Mama ta zuba mishi, kawai sai ya goge yana kara zubo da wasu, tashi Abban yai, dan a duniya ya t'sani ganin ran kowa ya baci a yaran shi bare Ahmad t'dokarshi. "Haba Baba na.. Maza da kuka? Fad'an wa ya ta6a min kai? Mama ya k'alla, da mamaki itama take K'allonshi, kawai sai yace shi baison auren nan, sam baison Rukayya... "Abba yaushe akai auren namu da har za'a kosa na kara aure dan bata haihu ba, nan yai ta mishi, kan tana chan wai ya barta sai bori take ta rufe kanta a d'aki tana kuka. T'sam Abban yayi, sai yace Mama ta miko mishi wayarshi. Momy ya kira, cikin k'ank'anin lokaci tazo. Ganin Ahmad durkushe yasa tasan da wata a kasa. Waje ta samu ta zauna, sai Abba ya sanarta abinda Ahmad yace, tuni ta hau 90, kan aure ba fashi, wallahi tunda har yau d'aurin aure, yau ya nuna mata bata isa ba, yau harda Mama ta balbale, tuni ta bawa Abban haushi, "t'saya kiji Maryam, ki cire son rai, yaron nan kar mui mishi dole, in aure yake bida zai ne in lokaci yayi, sam ban zata ba had'in zumunci kike son kulawa ba, kiyi hakuri, suma zasu haihu ne, amma a bar auren nan... Kuka Momy ta sau, yau wai an nuna mata karshenta, sannan an nuna mata ba ita ta haifi Ahmad ba.. Shidai gogan yai kasa da kai, fatan shi komai ta fanjama fanjam, yai lallashi daga baya. "Momyn su kiyi hakuri, sam abin bai ba, ranar aure kace ka fasa... ''Rufan baki, ai da saninki a haka, kuma dad'inta na haifa, aure yau za'a d'aura da d'aya a wanda na isa... Sallamar Alhaji Nasir ce ta kat'se ta, "lafiya kuwa Abba? Hayaniya har t'sakar gida fa... "Yauwa Nasir, shigo, cewar Momy,shi d'ai Abba da ido kawai yake binta, "Momy kuka? Mey toh yai zafi haka? "Komai nace kawai kace toh Nasir,, hawaye ta goge, "ina son ka auri Rukayya, ka fanshen bak'in cikin da ake son dasa min akan Ahmad.. Da mamaki ya k'allo su Abba, suma shi suke k'allo, "haba Momy, aure fa? Ni? Kai za... "Ban san musu Nasir,in dai ba kana son ku hallakani bane.. Kawai sai Momy ta hau haki.. Asma ta mot'sa, da sauri suka rukota, Nasir dama ya sani yake bai shigo ba t'saut'sayi ya fad'a masa.. Haka yanaji yana gani ya yarda dan Momy na fad'in in wai bai yarda ba wallahi zata mutu...Lol Ko su Rukayya basu san zance ba sai da aka d'auro suka ji, dan chan gidan su akaje. Bori ta hau yiwa Momy kan ya za'a ta mata haka? Tana k'wance asmar ta d'an saketa take bata hakuri. Fur Rukayya tace batasan wannan ba, mey zatai da tsoho, dan farin gidan, tuni ta tattare tai gidan su tana kuka. ********************** Da sauri Fure ta ruk'unk'umo abinta tana kukan murna, sai kara kakank'ameshi take har tana shirin fad'arsu kasa sai sukai kan mai laushi. Karan nan bai hanata ba, dan yasan na murna ne, sai ma yahau tsokanarta da fad'in, "haba uwar gida, yau fa ba ranar kuka bace... Dariya ta hau yi kuma kuka kuka. Sai ya zame dank'walin tare da mirgina ta kasa suka zuba ma juna ido, mey zata ce da abun nan? Lalle Allah bai had'a maka zafi biyu, gashi an so a muzguna mata Allah bai yarda ba, sai ta hau matso hawaye. Kanshi ya d'aura a kafad'arta yana goge hawayen, sai ta hau kuma sunne kai cikin kunya. "Sosai bayan na fita zuwa kawai zanyi na auri Rukayya tunda naga ni kad'ai nake k'ida na, sai d'ai ina fita na t'saya a bak'in kofa, ina ji kika sa key kika zube, wai kuma harda kuka, kinyi dauriya fa, ko irin y'ar haukar k'aryar nan da mata suke ke baki ba.. Hakan ya nunan ta ciki yana cinki, kawai sai nai jahadi na tunkari yakin dake a gaba na... Kat'se shi tai ta hanyar d'aura "lips" nata cikin magand'ar sa tana jin kamar da haka zata biya shi. By Feenat Ja'afar. Like 路 Reply 路 Report 路 Apr 30 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 39_Lokaci sosai suka d'auka, kan a hankali ta fara ko'k'arin zame kanta ido rufe,shima nashi haka, "thanks" shine abinda ta furta, sai ya ware ido cikin nata, lalle yau ya biya ta ba kad'an ba. Tuni kuma ya hau tsukanarta tana dariya.. A mota suke,yau shi ma zai kaita gidan bikin, hannunshi d'aya na nata kawai ta juyo tana ta aika mishi murmushi yana k'ada kai. Lalle kishi masifa ce, sannan batasan haka son AAA ya kai ba cikin ranta sai yau da ake neman a k'ak'aba mishi auren dole. Hannu yasa yai tagumi yana k'allonta da murmushin yadda ta zuba mishi na mujiya. Kawai sai taje ta lafe tana d'an mishi dariyar kauna,t'sam ya rukota yana sauke ajiyar zuciya. Yau d'aya ya kara tabbatar da son da Pretty ke mishi. Dak'yar ta dago tare da d'aukar wayanta, hannu ta daga mishi, tare da fad'in ''Bye... Sai taji yai shiru yana k'allonta kawai. Ta kara fad'in "hello", a hankali yace "I love you.. Kai ta k'ada tana murmushi, sai ta k'arkata kai da fad'in "I know... Cikin shag'waba, bak'inshi ya nuno mata, ba gardama ma ta nashi mai zafin, tare da fad'in "bye" ta suri jakarta zuwa waje, dan tasan in ta biye mishi a motar nan zasui ta zama. Zagawa tai ta bangaren da yake, ta daga mishi hannu, kai ya leko, "Remember that...Nothing gonna change my love 4 you... Sai ta k'ada mishi ido tare da d'aura jaka a kafad'arta.. Tace "really? Kai ya k'ada, tare da jero Nothing..Nothing... Hannu tasa a bak'inta tare da d'an wata munafukar dariya, sai ta manna wa hannunta "long kiss'' Muahhh... ta nuno shi da hannun "love you... Da farin ciki suka rabe, har sai da ya kule kan ta k'ada kai ta shiga gidan su Umma. Da gudunta ta karasa tana kiran su Adda da Aisha. Tuni suka fara mata barka,reshe ya juye wai da mujiya. Fatee ce ta kira ta, kan itama gata a hanya bayan azahar, tana ta mata dariyar keta kan wai d ansha da ita, ai ta fad'a mata taji a jikinta auren nan babu shi, itade murmushi take kawai, amma tasan da k'yar ta t'sallaka rijiya da baya. Sai dai kuma ta tushe k'unnenta a gun su Momy. Lafiya aka gama biki, sosai sun ma Maryam bajinta har ta ninka Fure, kayan kitchen guda Fure ta d'au nauyi, Ga nan AAA ya ma su Umma gudunmawar kayan abinci da drinks, dan fur suka ki k'ar6ar kud'inshi, Abba d'ai ya zama d'an k'allo da Umma. Aisha Bedsheets, Ya Suleiman kam an kafu sosai, d'uk kayan parlour shi yai,sosai ya ka'r mata nera, kamar kullum yau ma kawu ya d'au nauyin gado, ganin haka yasa ya sai mata babba mai t'sada da k'yau. Koh y'ar gidan wani mai kud'in karshenta kenan. Amarci sukaci ba k'arya a gidan Hassana, yanzun ne Muh'd yasan yai auren so da tararaya, sai yanzu yasan sirrin dake cikin auren y'ar masu karamin k'arfi da suka rena. A gun Momy kuwa, kowa ta d'aina kula shi dan a ganinta an mata babban wulakanci. Kullum sai Ahmad yazo gabanta neman gafara, yau d'ai har da d'an guntun hawayenshi dak'yar ya shawo kan Momyn. Ta bangaren Rukky kuwa tuni babanta yace bazata zauna mishi gida da aure kanta ba, su Momy su ne iyayen ta,dole haka tanaji aka yayimeta aka kaita gidan Nasir. Hassana na gida, fur Muh'd yaki zuwa biko, yace ai ba shi yace ta fita ba,zata iya dawo a d'uk lokacin da taso, ganin ba sarki sai Allah yasa ana wata da bikinsu ta tattaro ta dawo,sai d'ai ganin Maryam a gidan ba karamin bala'i ta tayar ba, a fafur sai d'ai ya sauya mata gida. Shikam yace amarya tace had'i take bida. Komai yi suke a gaban Hassana,haka zai ta biye wa Maryam suna guje guje a parlour akan abu kad'an. Hassana sai a ta6e baki,"mahaukata kawai.. Sam Maryam bata bin ta kanta, sai d'ai da taga zata shiga gonarta zata taka mata birki. Sunan Huwaila ake yau, wannan ce rana tafarko tun bayan auren su Maryam da Fure suka had'u da Familyn gu d'aya. Murmushi kawai take, jin ana chakarta kamar kullum,ga rashin auren Rukayya ya dad'u,tasan batta bak'in komai. Muryar Hassana tafi ta kowa tashi a d'akin maijegon. D'ai-d'ai su Maryam da Ummi na shigowa suka t'sinkayi Hassana na fad'in "bar mat'siyaci, nima ana chan anga guri ana ta 6arkan hauka, cewar Hassana. Da sauri Maryam d'in ta karasa d'akin, sai da taje d'ai-d'ai kan Hassana tukun ta k'alli Fure,"sha kurumin ki sister, sai tai gefen Hassana da hannunta tukun tace "dan tuni t'siya ta kare kan t'sohon nan na gida mai kud'in LUKUD'I ... Wanda da iyalanshi su ci k'wada K'adangarun BARIKI suci... "Sannan t'siya ta kare ga uban yana da kud'in, amma in ya dire buhu masara, daga ranar ba sauyin abinci har sai ta kare. Sai ta k'allo Hassana, "toh indai kikazo nan, toh k'wa t'siya ta kare a gun ubale... A tunzure Hassana ta mike, zatai kanta, da sauri Maryam d'in taja baya tana k'allon Hassanan kamar taga kashi, ilahirin d'akin sun zubawa Maryam ido suna k'allo baki sake, ''ni fa t'siya ta da y'ar gidana akuyanci, yanzu sai fa kice zakiyi dambe dani? A kuma cikin taron jama'a.. "Toh wallahi ki iya bak'inki... Chan ta mat'sa kusa da Ummi ta zauna, tai banza da Hassana wacce ke nad'e tabarmar kunya cikin jama'a. Har dariya Aunty A'i yau tayi, lalle wai "GABA DA GANTA... Tun zuwanta gidan Maryam d'in ta tarar da fad'an su da Hassana tasan za'a buga da Maryam. Yayinda maijego ta ta6e baki, badan ta kanta take ba yau da ta takawa Maryam burki. D'uk da tabbas batai ma Hassana sharri ba, dan fa sai da ta ciwo maganin zama da ita ka'f kan ta yarda a had'a su zama tare, tai alkawarin d'uk d'an uban da baiji kunyar taka mata y'ar uwa ba, toh itama bazata ji kunyar take shi ba. Ita kam Fure kasa tai da kai tana murmushi, tabbas tasan wataran KARE na yawo, KURA na yawo tasan dole za'a a had'u. Batajin da wanda Maryam zata dagawa K'afa a ka'f Familyn su Huwaila. Lalle kam,dole ta zama y'ar k'allo, dan k'wa badai ita ta takawa Maryam burki ba sam. Fatee ta haihu babyn ta mace, da zumudi ta gama abinda zata kai mata tai gidan, dan ta ce an sallame su. "Drama" taje ta tarar, wanda sosai taci dariya. Fatee na band'aki taji sallamar y'an gidan su Salman, da sauri ta wat'sa jin sun shigo d'akin da ake shirya baby. Cike da murna suka zauna a gama su k'ar6i baby. Da d'aurin kirji ta fito, nad'e da towel a kanta, d'ai-d'ai za'a basu Baby da sauri ta karaso ta shiga t'sakani, "Wa? Ai wallahi na rant'se ba shegen da acikin ku zai d'au y'ar JUYA.. "Dallah mat'sa min daga nan, ta warce y'arta ta d'ane gado tana bala'i. Gaba d'aya sun kasa cewa uffan, Fure da tazo ganin ikon Allah yasa ta ma kasa sallama, Ashe da gaske FATEE take da tace ba mai d'aukar y'arta acikin k'annen Salman sai d'aya? "Ido ko kunya babu wai kunzo ganin Y'a? Toh g'wara ku d'au fagon wani gu ku barmin gida, tuni wasu suka fusata, har sun manta, ana haka y'ar k'anin Baban su tazo da y'an gidan, jin yadda Fatee ke ma dangin mijin wankin babban bargo yasa taja tai shiru, aikwa sai da ta wanke ta tas! Kan d'uk taji sanyi. Zuciya sukai suka fita suna ta jika y'ar tasha.. "Eh zan jika...aje d'ai, gaiyar na aiya. Salman sai da yazo bada hakuri,yana dari dari, ganin yadda take cika, ba shiri yai shiru. Suna zuwa suka sanar da Umman su Salman d'in, da mamakin su sai su ka ga tai dariya. Sosai Fatee ta burgeta, sai ta k'allo su, "kuna nufin kunji haushi? Kai suka k'ada mata, sai tai murmushi, "da zaku san adadin shekarun da na d'auka kan na haife ku da baku kara kiran wata JUYA wai dan bata haihu ba, na zuba muku ido ne, dan nasan dole wataran zaku d'au darasi. Kowa k'allon kowa yake, su d'ai tun ba yau ba suna mamakin yadda Umman su ta t'sufa kuma wai ya Salman ne d'anta na fari. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:49 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 40_Rayuwar tana tafiya ma Fure cikin godiyar Allah, domin a kullum ta Allah tana matukar samun cigaba a rayuwa. Bata da tawaya ta ko'ina ta bangaren jin dad'i ko zamanta da mijintan, sai d'ai har yanzun Allah bai nufi samun ciki ba, a kullum batta kalmar fad'i ga Allah da ya fice "ALHAMDULILLAH" domin ya bata d'ukkan farin cikin rayuwa... Tawaya ta rashin D'a, bazata tai ma Allah butulci ba..InshaAlllah, Abadan. Ga wani karin farin cikin budi da ya same ta,AAAn ta ya bud'e mata "Restaurant" nata na kanta. Jere suke, anyi rubutu cikin "bord" d'aya da symbols.. "AAA pharmacy & stores Ltd. Yayin da nata dake makotanshi yasa mata "Mr's AAA Restaurants" tamkar tag'waye abin g'wanin ban sha'awa. Toh mey zata ce da Allah? Sai Godiya. Ajiyar zuciya ta sau, lokacin da ta kara g'yara mak'wancinta tana mai zuba ma AAAn ido wanda ke murza mai a gaban "mirror" yana mai dan k'allonta. A zahiri shi take k'allo, amma sam hankalinta yayi kan dumbin Alkairin mijinta gare ta. A hankali ya tako zuwa gefenta ya zauna, tai kur'i da ido ba ko kiftawa. Ido ya zuba mata, ba t'sammani sai ga nan siririn hawaye ya zubo bisa kuncinta. Hannu taji a fuska ana goge hawayen, cikin nutsuwa ta waiwayo da duban ta gare shi, murmushi yai mata, kan cikin zancen karatun kurma ya tada kai halamar mey ne ne? Murmushi tai,kan ta k'ada kai halamar babu, sai ta matso tare da d'aura kanta kan kafafunshi tana k'allon fuskarshi,sai ya kai hannu yana mai tattare gashin da ya bazar mata, sai ta ruko hannun tare da rint'se su cikin nata tana k'allon shi. D'ayan hannun takai fuskanshi tare da murmushi tana shafo ta,shikam murmushi yake mata,cikin sanyin murya ta hau mishi godiya bisa ga k'yautatawar shi gare ta.... "Life is really not worth living without you! You make me feel so special and complete! I can鈥檛 find words to utter,but I just want to say 鈥淭hank you and I love you much more Dear... JazakALLAH. Ajiyar zuciya ya sau, tare da k'ada cikin da jin dad'in kalamanta, cikin salon shi dake sata taji tamkar ita d'in "Queen" ce a "Universe"... Tuni ta sa mishi ido kawai tana k'allo,ganin d'uk yadda tai taga tafi AAA iya lafazin a fagen kaunar shi,sai d'ai ina,tuni ya mata nisa. Dariyar suke,lokacin da ya bud'e mata''bott" tana d'aukan k'wandon abinci,sam bazaka ce su ne suka shekara 4 da aure a tare ba, sun fi kama da irin sab'bin auren nan dake ji da junan su. Mika mishi d'aya tayi, kamar kullum ta d'au na Momy. Chan ta fara yada zango kamar kullum, suna "parlour" ta tarar Huwaila na kuka tana fad'in ta gama aure.. Suna jin sallamarta sukai shiru, waje ta samu, sai ga nan Rukayya ta fito a kitchen da abu a hannu, kamar kullum cikin girmamawa ta gaida Momy, sai da ta k'au da kai tukun ta amsa da "lafiya, kan Aunty Jidda tazo, ita kam harara ma ta sakar mata, su kam sauran ba wanda ya tanka ta, shiru kake ji ba mai cewa uffan. Takan rasa a rayuwa mey ta t'sarewa bayin Allahn nan, sam yadda suka ki jininta ko Maryam da bata barinsu basu t'saneta haka ba. "Mtsww.... T'saki Rukkay taja,kan ta samu gefen Aunty Jidda ta zauna. "Gaba d'aya anyiwa mutum dabaibayi duk an hanashi rawar gaban hant'si. Ta karasa tana y'atsine fuska, murmushi ta mata,kan tai kasa da kai, Aunty Jidda tace "wai ni ba naji an bud'e Restaurant da zummar nata ba? Hala tun yanzu ya fara raba gado tunda ba D'a bare kwai? Baki Momy ta ta6e, "shi fa ya sani, ni ina ruwana, su had'u su talautashi ma shi ya sani. Kasa tai da kai kawai tana jin su, tana jin Rukky ta amshe.. "hmm, matsiyaci kuke ji,ai bai iya samun gu ba, sam yadda zaki san abin nan da agumau yadda yaya ke rawar kai akanta, wallahi shi yasa bazan ta6a harka da mat'siyacin mutum ba, sam. K'allonta take, sosai nata sai ido, Fure lalle Allah ya yarfa wa zuciyar ki hakuri, dama Maryam na gun. Tamkar masu huce haushin mijin Huwaila a kanta haka kowa ke mata, sai d'ai wai harda Huwailan a zaginta? Abinda da mamaki, indai har zata kirata da haka. Ita d'ai murmushi ne kawai a fuskarta, sai ta janyo "basket" d'in abincin ta mika gaban Momy tace ta tafi, ba wanda ya tanka,sai ma t'saki da Rukayya taja mata. Sai da ta t'saya a gefen "corridorn'' ta goge hawaye kan ta karasa gun Mama. Anan ne kawai ta samu farin ciki, mama tana ta sa mata albarka akan abincin "weekend" na kullum. Abba da yazo bangaren kamar kullum weekend sai ya tarar dasu Furen, shima yaba mata yake akan ko'k'arin iya girki dasu duk k'wana uku na weekend, sosai Fure ta shiga ranshi, gasu da ladabi ita y'ar uwarta.. Ka'f sirikan gidan daga kansu ne kawai masu sanin ya kamata. Da dare ta biya dubo Maryam da cikinta ya isa haihuwa. Ba ai k'wana uku ba k'wa ta haihu,ta samu babynta namiji. Da murna tai d'aki dan sanar da AAA, sai gashi shima yana shirin sanarta har suna g'ware, "Maryam ta sauka... Sai suka sa dariya jin sun had'a baki gun albishir. Sosai Muh'd ke d'aukin zuwan babyn nan, yayin da Hassana ke ta cika dan wai ita yara mata ta haifa har uku,gashi har an fara kiranta da "UWAR MATA.. Amma ga amaryar shi tana zuwa har ya bata namiji a wata goma.. Ranar Maryam tai dariya kamar ta mutu, kai rashin ilimin Addini ne ma masifa ce, sam yanzu ita gani take Hassana ta kunce. Suna a parlour ana g'yara baby Hassana ta fito,gobe suna fir taki zaman parlour, jin yadda ake ta shigo da abubuwa. Fatee da Fure suka bita da k'allo, sai kunshe dariya Fatee take,dan ganin yadda Hassana ke hararar baby da uwar shi. Da gan gan Fatee ta fara "Accountant" ba, yaro mai goshi, sosai kazo da azziki. Baki ta ta6e, kan cikin haukarta ta fara ma Jidda dake kusanta "Jidda y'ar gatan Abba koh? Sai Jidda ta k'ada kai, cikin zance ta kara da cewa, "Dad'in abin na haifa, ba o o bace, nasan yau da Jidda ta iya mota,nasan da dadyn Jidda ya mallaka mata ita... Fatee ta k'alli Maryam, kawai bata nufa ba sai ji tai sun sau mata dariya harda shewa da tafawa, kamar wanda suka had'a baki wajen fad'in "wa yaga takai takai,,cikin dariyar mugunta Maryam tace "uwar Jiddan ma tai ko'k'arin mallakar ta kamin nan ita Jiddan... "Wallahi ban so ba,da tuni na mallaka.. Baki Fatee ta ta6e,kan tace su shiga ciki kawai, ita d'ai Fure nata ido. By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 2:50 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 41_Suna ya kayatar, sosai maijego ta fito da yayarta, baby yaci sunan Abba,an ka'r naira sosai, da yamma kamar kowa aka kawo kayan maijego da baby na mey suna su Aunty Jidda. Har kasa Fure ta zamo ta gaida su, Maryam tana daga gado ta gaida su sam ba fuska. Cikin fara'a suka amsa, Ak'wati biyu Aka sheko musu, komai na k'arya da nuna su sune, ganan wata katuwar leda da tarikicen su pampers da da sauran su. Fure da Ada da Fatee na duba kaya Maryam tai waje gun amsa kira. Huwaila da ke kusan su Fure dake ganin kaya cike da izgili ta k'allo Fure, "tunda y'ar uwa ta kot'se sai a zuciya bana a diba.. Chak Maryam ta t'saya wacce shigowarta kenan da masu duba kaya, a fusace Maryam ta karaso, "Sa'a kike ko... Da azama Fure ta tashi ta toshe mata baki, sai ta girgiza mata kai. Sai d'ai kan ta farga har Fatee taja t'saki. "Haihuwa ai kai inda ake nemanta itace haihuwa a gani na.. In ta wuce wannan, wallahi na yarda a kiramu da JUYA... A wulakance Huwailan ta k'allo ta, "ke kuma a suwa? Wai kare da gudun layya.. Mtsww, "Allah ya fissheni zama JUYA. Dariya Fatee tai,kan tace ''oho d'ai, dan dake da babu agun mijin d'uk d'aya wai karuwa ta haifo shege. Tuni ta tunzura ta,har ta soma zagege su Aunty Maryam da Jidda suka shigo jin ba'asi. D'aya ta fad'a sai Fatee ta mayar mata goma, ita d'ai Fure ta damke bak'in Maryam gam,dan yanzu tasan sai ai baram barama ranar suna. "Ki taso toh mu tafi ke Huwaila, banga t'saran yinki agun nan ba. Cewar Aunty Jidda. Da t'saki Fatee ta bisu, tana fad'in "a sauka da nauyi. K'allonta Aunty Jidda tai,kan ta nuno, "ki shiga taitayinki dani,ba JUYAR bace ita? Ta fad'a... Fatee tace "oho d'ai, nima d'ai na fad'a, ka haihu inda ake mararin ta ba inda aka maishe ka JUYA tafi ka mukami ba... Janta Huwaila tai, tana "Aunty bar mahaukaciya, ba laifinta bane, da k'arfi Fatee tace "Dawan'au ce ma ni. Sai da ta tabbatar sun fita tukun ta sau bak'in Maryam, kusan kowa na parlour, sai su Ummi da kawayenta, suma ana farawa sukai waje,dan taki jinin taga ana ciwa Fure fuska a gabanta, dan d'uk yayunta ne. "Aunty Fatee kin mun d'ai-d'ai wallahi, cewar Maryam, "sam Ya Furera tamkar sun dat'se mata baki haka take, a kusa da Fatee Fure ta zauna,cikin marairaita tace"Fatee Aunty Jidda ce fa? Yayar su AAA.. Baki ta ta6e, "ke kika san wannan, ai d'uk tsohon da baiji kunyar hawa Jaki ba,toh k'wa Jaki ba ya ji kunyar nana shi kasa ba. Adama tace "sosai kuwa. Sai ga nan Hassana ansha d'auri tazo, "ina tajin hayaniya,da fatan lafiya? Harara Hassana da Maryam suka k'wad'a mata, kan Maryam tace "ba'a sani ba uwar gulma, Fatee tace "Shishiganatu ba. Jiki sali6e Hassana ta juya Allah sarki ta koma. Ita d'ai Fure sam bataji dad'i ba, ta kuma sanarsu in dan ma ita sukai toh wallahi basu burgeta ba, nan suka chake ta,kan wai tsoron su take, "shi yasa kowa ke cin kashi akan ki ai. Cewar Fatee. Aisha kam tai shiru, dan sam ta t'sani hayaniya. Sai ta kama hannun Fure suka fita su Fatee na kiran matsorata. Aisha ta k'allo Fure dake kuka acikin motar da suka shiga. "Ki kara hakuri Furera, wataran sai labari, ki d'aina barin k'ananan maganganun su suna miki tasiri, ak'wai Allah, ki sa ranki a inuwa, Allah yai alkawari ga d'uk bawanshi ba wa d'uk wani abu da ya tauye shi aka goranta mishi shi, mat'sawar k'wa baka samu ba, toh ka d'auka wannan abun ba alkairi bane gare ka da rayuwar ka. "Kar kisa a rai,g'wada ki rama da ki barshi a ciki yazo yai miki illah. Kai ta k'ada mata, "wallahi ban ta6a da na sani akan hukuncin Allah ba sis, abu d'aya na sani, d'uk ranar da hakan ta faru nakan ke6e nai ta kuka,in na gama na share, ban kuma ta6a fidda rai daga samun ra6o sam, sai d'ai bana iya d'aure gorin jama'a, musamman dangin su AAA. Sosai ta lallasheta, har sai da tace ta g'yara fuskarta kamar ma ba ai komai ba, sannan kar ta cewa su Maryam komai. Ko da suka koma k'ida suka ji yana tashi a d'akin Maryam, suna shiga Fatee da Adama na ta rawa suna bin kid'an Ladi mai kid'an k'warya kamar basu ba. Murmushi tai,sosai Fatee y'ar hau ce ita da Ada da Maryam, sam ba zaka d'auka ba y'an uwan juna bane. Suna ganinta Fatee ta kamo hannunta wai ta shigo fili, ga nan y'arta sai k'yak'yala mata dariya take daga zaune. Har gida karan nan ma Momy tazo ita da Aunty Jidda suka sauke mata ruwan bala'i. Lokacin AAA na d'aki yau tun safe yake k'wance ciwan kai. Sama-sama yake jin hayaniya, a hankali ya daga window, muryar Momy da Jidda yake ji suna sauke wa Prettyn shi tana ta fad'in suyi hakuri. T'sam yai bai ya koh k'wak'waran mot'si, ya dace ya kawo karshen kiyayyar da su Momy ke ma Furii,amma ta ina? Tas Ummi ke sanarshi d'ukkan abinda ake ma Fure kawo da gorin haihuwa. Lekawa ya karayi, ga nan FURIIN ta duk'ar da kai kasa,a ranshi yana kila ma kuka take... Sai ga nan shima idonshi ya cicciko jin Momy na fad'in "ki yi zuciya ki fita sahun JUYA toh.. Amma dole su fad'a miki. Itama fit'sarun Maryam zani har gidan tunda a dalilinta komai a afku,tun shigowar ku dangin mu aka fara t'siya,saboda an yayimo dangin t'siyar. Ya'yan makaniken mota.... Da sauri ya sau labulen, tare da komawa kan gado, bazai iya d'aukar jin wannan kalaman ga Furii ba,tuni ya ji ciwan kai ya karu, shin Ina wai Tauhidin su Momy yaje ne? Wannan tambayar yau ita tazo kanshi, sai d'ai har suka gama hayaniyar su bai samo amsa ba. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 2:51 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 42_Tamkar marainiya haka ta takure kanta a parlour tana kuka mara sauti,sai da tai mai isarta ta kad'e tai d'aki cikin sand'a, a zaton ta har yanzun bacci yake,dan tasan da idonshi biyu da yanzu ya taso gaida su Momy. A.c ta rage mishi, kan a hankali g'yara mishi bargo tare da ta6a kanshi, da dan sauri ta wanke fuska gudun ka'r ya gane tai kuka, sai ta fita kitchen. Da k'allo ya bita yana mai tausayin ta had'i da karin kaunarta. Tabbas Furii tai sanyi, sanyin ma na ban mamaki,dan shi zaya bada wace ce Fure? Amma yanzun tai hakuri tana ta cin jarabawar rayuwa. Har bazai tuna rana ta karshe da tai pt a gidan ba,gaba d'aya ta faiwalawa Allah, tai hakuri, amma ya rasa mey yasa mutane suka gaza hakurin da tai, wace irin zamani ne yanzu Allah ya kawo mu? Bargo kawai ya cire yai tagumi. Sai ana kiran Magriba tazo tashin shi, sai ta tarar ya ma tashin, sai ta koma kitchen. Yaga har anci abinci bata ce mishi kom ba, dare yai sosai, sai ma dan tad'in da take mishi tana "massaging'' d'in kanshi a hankali. Yasan kawai d'aurewa tai kamar kullum dan kwanciyar hankalin shi. "Furii...a hankali ta amsa,tana cigaba da abinda take, sai ya ruko hannun d'uka tare da zago da ita suna k'allon juna,tabbas yasan d'auriya take, amma har yanzun bata dawo d'ai-d'ai ba. Kasa tai da kai,ganin yadda ya zuba mata ido, hannayen su ya rint'se, tare da g'yara zama kan gadon. "Are you Ok?.. Kai ta dago tare da saurin k'ak'alo murmushi, sai ta k'ada kai, wato ba d'ai zata fad'a ba? Sai ya sau ajiyar zuciya, ya fara abin da yasan d'uk rashin walwalarta takan dawo farin ciki. Ido kawai ta zuba mishi dan jin kalaman kaunar shi gare ta. Bata nufa ba sai ga hawayen dad'i ya zubo, cikin sauri ta isa gareshi ta lafe tana murmushi, a hankali taji komai na warewa har ta dawo cikin nutsuwar ta. Tasan in da AAA, sam ba ita ba k'wanan bak'in ciki, Son shi kuwa,a ganinta zai iya mantar ta d'uk wani gi6i da ya tare mata gaba.. Fatan ta yasa kaunarshi ta d'aure, dan shi kad'ai ke samota ko ta k'auce. Zaune suke a parlour suna firar duniya, ta tasa kanta da cinyarshi a kasan lallausan darduma. Ag'waluma ke a hannunta d'aya, yayinda d'ayan ta rike lollypop,jin yai shiru tana ta zuba yanzun yasa ta k'allo fuskarshi. Kawai ya tasa ta gaba kamar wata TV da murmushi yana k'allon yadda take kai alawar tana zance. Sai kai alawar bak'in shi, ba musu ya k'ar6a. Da hannunta take bashi itama ya bata. Ta kawo hannu zata bashi taji ya rike, sai ta k'alleshi, y'atsunta yake dubawa cikin farcen,sai yai dan shiru. "Lafiya?.. Kai ya k'ada mata, sai ya tada zaune,duben ta ya fara, d'uk da ba bangaren shi bane, t'sam yai yana tunani, ita d'ai Fure sai K'allonshi take,ganin ya sauke idonshi kan rigarta. Sai ya k'ada kai, "yau period naki k'wana nawa ya wuce? Baki sake take K'allonshi, dan abinda bai ta6a mata ba kenan. "K'wana shida,lafiya? Murmushi yai, kan yace "yana kaiwa haka dama? Sai tai jim,kan ta k'ada kai, ''sai d'ai ya wuce da biyu ko uku. "K'wadayinki na k'wana niyun nan fa? Kai ta lang'wa6e, "dama ina yi ai,musamman in na kusa farawa. Hannun ya kai inda yake k'allo, "nan fa? Su ma haka suke? Sai ta dan harareshi, "sosai sukanyi suma in zanyi.. Lafiya? Tafin hannunta ya shafa yana k'allo, sai ya kai hannu gemunshi yana shafawa tare da mata wani k'allo.. "Ke ma fa kin sauya a um um... Bori ta fara,ganin yadda yake ta mata t'siya, dariya yai, sai yace "ina zuwa ke d'ai. Sai ya tashi yai d'akin kayanshi na tarkashen aikinshi. Tunani take, itama fa tana dan jin sauyi a tare da ita,d'uk abubuwan nan da take k'wadayi yanzun, ba su take ba in period ne, sannan... K'allonshi tai ganin yazo da pt da abin da wani abu, a dirare take K'allonshi, anya yau mutumin lafiyar shi kuwa? Duk sai wani fara'a yake,hannunta ya kamo,sai ta tsura mishi ido, "meye wanchan?.. Da sauri ta juya inda ya nuna, "ahh..tace da sauri,jin an soka mata wani abu a yat'sa,da sauri ta juyo dan jin zafi, tana ganin jini ta hau kukan baci,hakuri yake bata, kan ko yace ta t'saya yasan ba zatai ba. Baki ta zumbura, harda dan hawayen karya, yana sakar hannun ta hau yarfewa cikin lang'wai, sai yai murmushi ya k'ada kai, tukun ya hau abinda zai, da kamar minti biyar fara'ar fuskarshi ta karu, yayinda Fure take K'allonshi tana dan yarfe hannu. Bata nufa ba taji ya ruk'unk'umota har suna yin kasan carpet, "I knew it.. Ciki fa, Allah Pretty... K'wak'waran mot'si ta kasa,baki sake take K'allonshi, kan a hankali ta furta "ciki?.. Kai ya k'ada mata, "sosai, tashi muje lab, dagota yai, kawai d'uk sai ta zama wata doluwa, da ido kawai take binshi ganin irin bak'in da yake ta washe wa. A lab ana ta yi da Fure, da k'yar ta sa kanta a jikin shi kan aka sa syringe aka zuki jini, y'an wajen sai dariya suke musu, ganin yadda yasa cotton yana goge mata gun harda hurawa yana fad'in sorry,ya rasa meye a allura da Fure take kinta? Tuni sai ya tuna mishi da wani lokaci achan baya.. Basu jima ba aka fito da "result". Kad'an ya rage ya dagata sama ta ja baya tana k'allon y'an cikin "reception" d'in, d'uk sai taji kunya, Hannunta ya kama sukai waje,amma bai iya jurewa ba sai da rungumota cikin murna,tayashi kawai take, kan a hankali ta k'ar6i result d'in, ganin abin da ke jiki yasa ta kafawa papern ido ba ko kiftawa. A hankali ta dago da dub'enta gare shi, ta kasa furta komai, kai ya k'ada mata yana shafa cikin. Tuni hawaye ya cika idon ta, "ciki?... Bata nufa ba taji ta fara jika pepern da hawaye, janyota yai yana "oh no Furii...murna za kiyi,tana shiga jikin shi ta fashe da kukan dad'i, ikon Allah, Fure ta ciwo POSITIVE. By Feenat Ja'afar. Like 路 2 路 Reply 路 Report 路 May 2 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 43_Dak'yar ta saisaita ganin wasu za su nufi lab d'in, hawaye ya hau goge mata, tai kukanta yasan na dad'i ne, ko ba komai yasan farin cikin FURIIN shi yazo. Allah ya yi,Alhamdulillah itace kalmarta ta kullum a gun Allah,domin ya mata gata masu yawa,shi yasa zai g'wada imaninta gare shi. Tuni ta hau istigfar bisa kukanta da tai tayi a chan baya. Jiyan nan ta gama mishi maganar su d'akko Amal,kuma yai murna. Tafe suke yana ta d'an turo ciki da kama k'ugu tana mishi murmushi, sai ganan wata mata da tsohon cikinta, kawai sai ta maka mishi harara, da sauri ya d'ai d'ai ta, dariya Fure ta hau, sai tabi matar da k'allo,ko ta zata ta da ita yake ne oho. Suna zuwa gida ya d'akko ta a hannu kamar wata Baby, Baba mai gadi ya girgiza kai yai murmushi, sosai suke burge shi, dan gidan su babu hayaniya. A gado ya direta suna dariya,kawai sai ya t'saya k'allonta daga k'wancen, sai tai murmushi tare da miko mishi d'uk hannunta halamar yazo gare ta, ba musu kuwa ya taho,d'uk sai tai mishi dabaibayi cikin hawaye. Fatee ta fesawa, kan su Adda suka ji bayani, alkawari tace ya mata, kan dan Allah kar kowa ya ji in ya wuce Mama, tana son kawai ya fito ne,za su fi dauk'in shi. Kai ya k'ada, yasan tana son ma wa jama'a ba zata ne, kuma InshaAlllah ba mai ji sai d'ai in ya fito su ga. "Kai k'awata nai murna wallahi har ba iyaka, gani nai bazan iya k'wana ba sai nazo ganin ki. Murmushi tai kan tai gefe da kai. Hannunta Fatee ta kama, "ki min maganin t'sagerun dangin Ahmad d'in nan dan Allah... Ki rama abinda sukai miki,wallahi ki hana ko wacce t'sageriyar babyn ki ko k'ya huce takaicin baya. Kai ta k'ada tana k'allonta, "sis Fatee da k'yar ne, kowa yai nagari dan kansa, abu d'aya na sani,shine ba mai ji bare gani, sai d'ai dake kinsan d'an duma ne. "Hana su d'aukar D'ana bazai iya hucen takaici na ba, asalima Batool, nai alkawarin d'uk wanda baizo ya ga D'ana ba zan kai mishi har gida. Kai Fatee ta k'ada, "lalle kina da hakuri, tab, wallahi ba wanda ya isa nai mishi haka. Murmushi kawai tai. Sai d'ai a daren fure ciki ya shiga 5 weeks ta soma matsala,tamkar an jangamo ta. Washegari taje ganin likita,sai taya AAA murna yake,kan ya bata magunguna kan in ya cika 3 month tazo yai mata "scanning". Tun daga wannan rana Fure ta dage da godiya ga Allah da kuma gode mishi, sosai take wahala da cikin,d'uk ta rame tai fari abunta, dole wacce bata so aka kawo mata, wato y'ar aiki. D'ai-d'ai da abinci ta d'aina yi, sai d'ai kullum daga restaurant d'inta a kawo wa Baba maigadi da mai gidan,ita kam sai d'ai Umma ta dafo mata tuwan hat'si,shi kad'ai ke shiga, mama kawai ta sani, shi yasa bata rabo da aiko mata kayan makulashe, koh ta aiko Ummi tai mata k'wana biyu. Har gida Mama tazo ta duba ta,tare da mata adu'ar Allah inganta. Ba wanda yasan da jinyarta a gidan sai su biyu da Ummi,sai Abba da ya ga an d'aina kawo mishi "delicious" na Fure. Ita kam Momy ko rashin zuwan abincin bai dame ta ba, sai d'ai su Huwaila dake fad'in kila ta ware su ne yanzun cikin kason ta. Fir koh jajen rashin ganinta basui ba har yau. A haka har ta raka wata ukunta. Sunyi tafiya da Abba Abuja,yayinda yace taje kawai dan cika umarnin likita. Hawaye take sosai a kan gadon scan d'in, shikam likita ya ma kasa cewa komai, sai chan ya nisa, a gaskiya kuna da sa'a a rayuwa ke da Madam Fatima, haa'a.. Sai ya maida kanshi jikin allon machine d'in. "Malikul kuddus kenan, gaskiya ina da babban tukuici in na sanar da "pharmacy" wannan abin farin cikin. Da sauri ta girgiza kai, "A'a Doctor, dan Allah ka riken ya zama sirrin mu, dan Allah... ''Assistance" ta kusan su tace "amma wannan abin farin ciki ne, balle ga mijinki. Kai ta k'ada, "na sani, sosai ma kuwa. Murmushi likita yai, "na gane Madam, InshaAllah pharmacy bazai ji batun nan ba, I promise. Kai ta k'ada, harda godiyarta. Tana tafe a mota tana kara yabo ga godiya ga Allahu subhanahu wata'ala,lalle Allah gagara misali ne, ikon shi ya wuci komai, kuka ta fashe dashi sosai, sai ta nemi gu tai "parking", lalle hakuri wani abun ne a matakin rayuwa. Hannu takai kan cikin, sai ta rint'se ido, hawaye ya k'waranyo. Tuni ta fara ma wa Allah kirari, a cikin k'arfin mulkinshi da iko, tasan wannan k'yauta ba kowa ke samonta ba sai dan baiwa. Dak'yar ta d'ai- d'aita ta karasa gidan su. Dan d'uk ji take in bata dangana da Ummanta ba bazataji sa'ida ba. Ido cike da hawaye itama Umman ke k'allon Furen, "Kinga kad'an daga ikon Allah, ki bar kuka haka, kiyi adu'a, Allah ya inganta miki. Kai Furen ta k'ada tana goge hawaye a cinyar Umman. "Ki d'auka wannan tukuici ne ga Allah zuwa ga hakurin da kikai a jarabawar rayuwarki. Ki d'auka wannan su zasu zama silar yayewar d'ukkan kuncin rayuwar ki, nasan kin ari hakuri kin yafa, Ubangi yai miki albarka Furera... Hawaye ta goge tana fad'in "Amin Umma. "Umma amma mu rufeta daga ni sai ke, ko AAA bazai ji ba, in lokaci yai kowa ya gani, kai Umman ta k'ada, "ai wannan ba abun fad'a bane Furera, abu ne a 6oye, sai lokaci yayi in sun baiyana a sanar. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.my 9/29/16, 2:52 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 44_Koda AAA ya dawo maganin da aka rubuta mishi kawai ta bada, sannan ta sanarshi komai "normal". A haka tai ta rakawa har ta shiga "2nd tremiser", yanzu tana iya komai,har Abinci ta cigaba da yi ma su Abba. Iyaka d'ai ita intai ne bazata ci ba sai tuwan Umma har yau. Sannan t'sawan watannin bayan ga Aunty Maryam da Ummi da Mama ba wanda yazo ganin ko lafiya take a gidan. Sai yau da Aunty A'I tazo dan jin tunda ta dawo a Dubai ba waya ba zuwa. "Ga nan babyn Maryam har ya girma tufa. Murmushi tai,kan tace "eh ba,ai kunsha Dubai, zama ta g'yara, "amma d'uk fa kin rame Pretty, hope lafiya? Kai ta k'ada mata tana murmushi, "toh ko d'ai anzo gurin y'ar gida na? Dariya tai,sai tai kasa da kai, tabbas Aunty A'i mai Sonta ce, ba tajin zata iya boye mata wannan. "Allah sa hakan ne pretty,pls ki ban albishir. Kai ta daga mata tana d'an murmushin kasa kasa. "Kai,dan Allah ki ban labarin ya y'an gidan ki sukai da sukaji labari? K'allota tai, "kai banjin wani ya sani ma bayan mama... Kai Aunty A'in ta k'ada, "good,kun min d'ai d'ai, g'wara su gani tashin farko,in yaso sai hawan ruwan mutum ya hau muga inda zai mutu? Nan suka hau firar yaushe gamo, yawanci kan matsalar gidan mazajen nasu ne.. Sosai ta tayata murna har ba tasan sanda ta ruka musu ba su ma. "Wallahi Aunty A'i ina son naga kin haihu kema, d'uk da ina ga kamar... Sai d'ai tai shiru. Murmushi Aunty A'in tayi, kan tace "kina ga kamar bamu damu ba koh? Kai ta k'ada, "ba haka ba. Sai ta g'yara zama. "A da na damu sosai tunda na shekara hudu, d'uk sosai ban damu wani chan ba,toh g'wara nima akan maigidan, dan shi kam bai ma fiya son yara ba, boko ta sha mishi kai da burin tara kud'i, sam yaran basa a gabanshi. D'uk da gaskiya ni ban ta6a samun mat'sala a gun dangin shi ba, sai d'ai na damu daga baya sosai,dan ko ba komai ina son ganin d'an kaina ko d'aya ne. Ganin na mat'su ne yasa har da mukai wata tafiya Umara mukaje muka ga likita, ni kam ban da mat'sala, sai shi ne suke tunanin a gareshi take a bangaren "hormones" nashi, wato (Hormonal imbalance) sannan ga karancin shi kanshi spm. (Low sperm counts). ''An d'aura shi a magani, sannan da shawarwari, sai d'ai abin bai ba. Muna da shekara shida muka sauya kasa d'uk a dalilin na damun, sai likita ya bada shawarar ai min "IN VITRO FERTILIZATION" (IVF) wato a sanya k'wanshi da nawa bayan "eggs" d'in yai fertilizing. Anyi nasara, har ciki yakai wata 4 muka dawo gida, sai d'ai ko wata ba mai ba na samu "miscarriage". Sau uku ana k'wata haka,sai d'ai duk basa zama,da haka na hakura na sanya ma sarautar Allah ido. Sai na ma d'aina damun kaina da abin,gashi yanzu muna zaman mu lafiya. Sai dai ko in kad'aicin hakan ya ta6o ni wataran. Sannan har yau ka'f cikin gidan ban tunanin sun san haka ba in banda Mama. "Kawo iyanzu da muke kok'arin cika shekara ashirin da aure.. Kai Fure ta jinjina, tare da mata fatan alkairi. Bayan tafi Fure ta zurfafa tunanin rayuwa. Cikinta watan shi hudu kenan da sati biyu yau, sai yau ta je gidan su Momy. Kamar kullum chan ta fara nufa. Su Huwaila wacce ta aure ya mutu ana parlour. Tun daga kasa har sama ta take k'allonta. Doguwar Riga ne jikinta da babbar rigar sanyi fara wacce ta boye asirin cikin. Kau da kai tai,dan sosai tai k'yau, amma ganin kyashi su kullum muninta suke gani. "Sannu Huwaila,ina ta sallama ko baki ji ba? A wukance tace "eh. Sai tai murmushi. "Ina Momy toh? Harara ta wat'sa mata kan tace "tana kaina. Ita abin ma sai ya bata dariya. Har ta juya zata fita sai ga nan momyn ta fito. Har kasa ta gaida ta, da mamakinta sai taga tana k'allonta ta amsa. Da ta dago kai za taga ita momyn ke k'allo. Abincinta ta mat'sar. Yau d'ai anyi mutunci, dan har ta fita ba wanda ya tofa mata. Da sauri Momy ta k'alli Huwaila, "ni fa kamar ciki nake tunanin yarinyar nan take dashi, kai Huwailan ta k'ada, "haba d'ai ciki Momy? Wannan katuwar riga kamar tana a "swisszaland" ba dole ta mayarta mai ciki ba.. Kawai sai ta batar da Momy. Dariya Fure tai, ganin hakkarta ta cimma ruwa, dan tanajin su sarai. Dan ba wani sanyin azo muga ake ba a gari. Mama sosai tai murnar ganinta, bare taga jika har ya tasa. D'uk sai ta fara sinke kai da jin kunyar Maman. Momy ke da girki, Abba yai bangarenta don cin abinci. Wai sam ba tasan zai dawo da rana ba tunda yau ba weekend ba. Zai fara balbaleta tace ganan ai na gidan AAA, tuni ya hau washe baki, "a toh zuba min, sai ku jira y'ar aiki. D'auka tai suka tafi chan bangaren shi da k'wandon. Wa'ina ce tasha miyar Egusi da banda da jan nama. Tuni kamshin ya karad'e parlourn Abban, shi kam bai jira ba yaje da kanshi ya wanke hannu. Tuni ya fara kai gara. Ita kam a kullum mamakin yadda ake ya6on abincin Fure take,musamman Abba. "Maryam miyar nan kar ta barki, za kiji haushi.. Sosai sai had'iyar yawo take, amma isa ta hana ta ci kamar kullum. Shikam Abba da ya gut'suro sai ya mika mata, ta d'an y'atsine fuska kamar bata so. Abba yace "ci d'ai. Daga bata d'aya sai ga matarka ta t'soma hannu,d'uk loma d'aya sai ta y'atsine fuska tuni sai gashi har tafi Abban ci. Sai kam ya hau mata dariya kan ai wannan "Master Chief ce a cooking. Haka ta d'au ragowar ta kaima Huwaila, "gashi ku ci, kinga na sai an wahalar da kai ba,tunda y'ar wahalar ta kawo. Daga yau mun hutar da rose d'uk weekend. Tuni k'wa kamar mai jira ta hau ci ita da ya'yanta. Tun daga ranar su Momy ke cin abincin Fure y'ar wahala. Sosai ta gama da y'an gidan k'arfk'af da daddan abincinta. Sai ga nan Momy na Allah-Allah weekend tayi, sannan kullum cikin kushe abincin Rose mai aikinta take, wanda a da gani take tafi d'uk y'an gidan iya girki. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com Feenat Jaafar's Mobile Blog feenat.mywapblog.com Like 路 1 路 Reply 路 Report 路 May 2 Feenat Ja'afar Novel's "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 44_Koda AAA ya dawo maganin da aka rubuta mishi kawai ta bada, sannan ta sanarshi komai "normal". A haka tai ta rakawa har ta shiga "2nd tremiser", yanzu tana iya komai,har Abinci ta cigaba da yi ma su Abba. Iyaka d'ai ita intai ne bazata ci ba sai tuwan Umma har yau. Sannan t'sawan watannin bayan ga Aunty Maryam da Ummi da Mama ba wanda yazo ganin ko lafiya take a gidan. Sai yau da Aunty A'I tazo dan jin tunda ta dawo a Dubai ba waya ba zuwa. "Ga nan babyn Maryam har ya girma tufa. Murmushi tai,kan tace "eh ba,ai kunsha Dubai, zama ta g'yara, "amma d'uk fa kin rame Pretty, hope lafiya? Kai ta k'ada mata tana murmushi, "toh ko d'ai anzo gurin y'ar gida na? Dariya tai,sai tai kasa da kai, tabbas Aunty A'i mai Sonta ce, ba tajin zata iya boye mata wannan. "Allah sa hakan ne pretty,pls ki ban albishir. Kai ta daga mata tana d'an murmushin kasa kasa. "Kai,dan Allah ki ban labarin ya y'an gidan ki sukai da sukaji labari? K'allota tai, "kai banjin wani ya sani ma bayan mama... Kai Aunty A'in ta k'ada, "good,kun min d'ai d'ai, g'wara su gani tashin farko,in yaso sai hawan ruwan mutum ya hau muga inda zai mutu? Nan suka hau firar yaushe gamo, yawanci kan matsalar gidan mazajen nasu ne.. Sosai ta tayata murna har ba tasan sanda ta ruka musu ba su ma. "Wallahi Aunty A'i ina son naga kin haihu kema, d'uk da ina ga kamar... Sai d'ai tai shiru. Murmushi Aunty A'in tayi, kan tace "kina ga kamar bamu damu ba koh? Kai ta k'ada, "ba haka ba. Sai ta g'yara zama. "A da na damu sosai tunda na shekara hudu, d'uk sosai ban damu wani chan ba,toh g'wara nima akan maigidan, dan shi kam bai ma fiya son yara ba, boko ta sha mishi kai da burin tara kud'i, sam yaran basa a gabanshi. D'uk da gaskiya ni ban ta6a samun mat'sala a gun dangin shi ba, sai d'ai na damu daga baya sosai,dan ko ba komai ina son ganin d'an kaina ko d'aya ne. Ganin na mat'su ne yasa har da mukai wata tafiya Umara mukaje muka ga likita, ni kam ban da mat'sala, sai shi ne suke tunanin a gareshi take a bangaren "hormones" nashi, wato (Hormonal imbalance) sannan ga karancin shi kanshi spm. (Low sperm counts). ''An d'aura shi a magani, sannan da shawarwari, sai d'ai abin bai ba. Muna da shekara shida muka sauya kasa d'uk a dalilin na damun, sai likita ya bada shawarar ai min "IN VITRO FERTILIZATION" (IVF) wato a sanya k'wanshi da nawa bayan "eggs" d'in yai fertilizing. Anyi nasara, har ciki yakai wata 4 muka dawo gida, sai d'ai ko wata ba mai ba na samu "miscarriage". Sau uku ana k'wata haka,sai d'ai duk basa zama,da haka na hakura na sanya ma sarautar Allah ido. Sai na ma d'aina damun kaina da abin,gashi yanzu muna zaman mu lafiya. Sai dai ko in kad'aicin hakan ya ta6o ni wataran. Sannan har yau ka'f cikin gidan ban tunanin sun san haka ba in banda Mama. "Kawo iyanzu da muke kok'arin cika shekara ashirin da aure.. Kai Fure ta jinjina, tare da mata fatan alkairi. Bayan tafi Fure ta zurfafa tunanin rayuwa. Cikinta watan shi hudu kenan da sati biyu yau, sai yau ta je gidan su Momy. Kamar kullum chan ta fara nufa. Su Huwaila wacce ta aure ya mutu ana parlour. Tun daga kasa har sama ta take k'allonta. Doguwar Riga ne jikinta da babbar rigar sanyi fara wacce ta boye asirin cikin. Kau da kai tai,dan sosai tai k'yau, amma ganin kyashi su kullum muninta suke gani. "Sannu Huwaila,ina ta sallama ko baki ji ba? A wukance tace "eh. Sai tai murmushi. "Ina Momy toh? Harara ta wat'sa mata kan tace "tana kaina. Ita abin ma sai ya bata dariya. Har ta juya zata fita sai ga nan momyn ta fito. Har kasa ta gaida ta, da mamakinta sai taga tana k'allonta ta amsa. Da ta dago kai za taga ita momyn ke k'allo. Abincinta ta mat'sar. Yau d'ai anyi mutunci, dan har ta fita ba wanda ya tofa mata. Da sauri Momy ta k'alli Huwaila, "ni fa kamar ciki nake tunanin yarinyar nan take dashi, kai Huwailan ta k'ada, "haba d'ai ciki Momy? Wannan katuwar riga kamar tana a "swisszaland" ba dole ta mayarta mai ciki ba.. Kawai sai ta batar da Momy. Dariya Fure tai, ganin hakkarta ta cimma ruwa, dan tanajin su sarai. Dan ba wani sanyin azo muga ake ba a gari. Mama sosai tai murnar ganinta, bare taga jika har ya tasa. D'uk sai ta fara sinke kai da jin kunyar Maman. Momy ke da girki, Abba yai bangarenta don cin abinci. Wai sam ba tasan zai dawo da rana ba tunda yau ba weekend ba. Zai fara balbaleta tace ganan ai na gidan AAA, tuni ya hau washe baki, "a toh zuba min, sai ku jira y'ar aiki. D'auka tai suka tafi chan bangaren shi da k'wandon. Wa'ina ce tasha miyar Egusi da banda da jan nama. Tuni kamshin ya karad'e parlourn Abban, shi kam bai jira ba yaje da kanshi ya wanke hannu. Tuni ya fara kai gara. Ita kam a kullum mamakin yadda ake ya6on abincin Fure take,musamman Abba. "Maryam miyar nan kar ta barki, za kiji haushi.. Sosai sai had'iyar yawo take, amma isa ta hana ta ci kamar kullum. Shikam Abba da ya gut'suro sai ya mika mata, ta d'an y'atsine fuska kamar bata so. Abba yace "ci d'ai. Daga bata d'aya sai ga matarka ta t'soma hannu,d'uk loma d'aya sai ta y'atsine fuska tuni sai gashi har tafi Abban ci. Sai kam ya hau mata dariya kan ai wannan "Master Chief ce a cooking. Haka ta d'au ragowar ta kaima Huwaila, "gashi ku ci, kinga na sai an wahalar da kai ba,tunda y'ar wahalar ta kawo. Daga yau mun hutar da rose d'uk weekend. Tuni k'wa kamar mai jira ta hau ci ita da ya'yanta. Tun daga ranar su Momy ke cin abincin Fure y'ar wahala. Sosai ta gama da y'an gidan k'arfk'af da daddan abincinta. Sai ga nan Momy na Allah-Allah weekend tayi, sannan kullum cikin kushe abincin Rose mai aikinta take, wanda a da gani take tafi d'uk y'an gidan iya girki. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. 9/29/16, 2:53 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 46_"Hand golf " ya sa dan duba "CM" da mamaki ya k'allota, sai d'an nishi take tana zufa,sosai yai mamaki,da sauri ya fasa ruwan, ganin yaki, Waje yai gun AAAn, ina zaton zata iya, InshaAllah,kuyi mata adu'a kawai. Kai ya k'ada, "za mu iya shiga? Kai ya k'ada shima likitan, "sosai, musamman kai, za ta fi bukatar ka kusa. Maryam ya je bama abin g'wajin da doctorn ya bashi,tuni ta sanar da Umma da dasu Aisha. Tashi Umman tai kawai ta shiga bayi ta d'auro alwala. Tara da wani abin,sai ta zauna sallaya tana mai rokama y'ar tata sauki da Nabiyur Rahmati. Komawar likita har Nurse tai gunta, ganin yadda take ta ko'k'arin nishin fitar D'a. Gaskiya likita yana jinjina mata,ganin yadda ta dage sai ta haihu da kanta. Kawai sai ya hau had'a abubuwan taimakon labor. Tana t'saka da nishi sai ga nan AAA shida Maryam, nurse tace ya shiga man ganin ya t'saye kawai k'allon Furin yadda take nishi gumi na zuba tamkar wacce ta had'iyi kunama. Kai ta daga kamar ance k'alli kofa,suna had'a ido kamar zai sau mata kuka.. Ido ta rufe,cikin masifa tace "Fita.. Ka fita bana son ganin ka... Da sauri likita da su Maryam suka jiyo,ganin AAAn ne sai abin ya basu mamaki, cikin rawar murya AAAn yace "Pretty ni ne fa... Da sauri ta bud'e ido, kawai sai taji mugun haushi, "eh kai d'in.. Baki sake yake k'allonta.. Ganin yaki fita ta juyo gefe, k'walin "hand gulf'' ta d'au ta hulo mishi, cikin balbalin masifa ta rufe ido tana sai ya fita... "Ya fita kawai... Kawai sai ta farke da kuka... Cikin rawar murya yace "yi hakuri, na fita, sannu, kiyi hakuri, Allah sarki AAA. D'uk sai ya basu tausayi. Yana fita ya goge k'walla, tabbas yasan ba karamin wuya prettyn shi ke ci ba, tunda har zata iya t'sanar ganinshi. Da sauri ya d'au waya yana kiran Mama. "Ka k'wantar da hankalin ka,Muh'd ya sanar ni, zata haihu lafiya.. Ka d'aure. Dak'yar Maman ta d'ai d'ai ta shi. Sai d'ai Furi har goma shiru ana ta fama. Tuni Maryam har ta fara kuka. Abba karan nan ta kira, shima tuni ya taho gida d'uk sai ya ji kamar bazai iya ci gaba da aiki ba. Jin Maryam na kuka yasa ya d'au jarka ya hau karanta mata d'uk wata adu'a ta saukin haihuwa, "Umman su ko d'ai zaki je ne? Kai ta k'ada, "bana tunani, sai ta share k'walla. "Sai d'ai nasan d'uk inda Furera ta t'saya tana jin jiki.. Ganin tana hawaye yasa yai mamaki. "D'uk yaran nan sun haihu lafiya Umman su, itama zata haihu,in d'ai har tasha wannan adu'ar da yardar Allah. Kai ta k'ada, "Allah yasa, amma haihuwar Fure ba irin tasu bace... Komai ta sanar ma Abban, nan yai ta mamaki, sai ya fita makotan su, ak'wai dabino,ya samo danye fresh wanda aka jijjige a take mai bauri. Yasa Umman dakeshi cikin sauri, su basu rabo da zam-zam y'an Naira dari, dashi ya had'a da ruwan tofin, ana haka Ada ta shigo ajiye yara zata asibiti harda breakfast d'in ta. Nan Abba ya bata sako, tare da ce mata ta tabbatar tasha. G'wag'war maya ake da Fure da likita kan bazata iya ba tana musun zata iya, adu'a ce kawai fal bak'inta. Babu wanda ke a K'wak'walwar ta sai Allah. Lokacin zuwan Ada har Ummi ma tazo,tana zaune kusa da yayanta wanda yake ta sallar "Dhuha" baji ba gani, in ya hau "Sujjada" yakan jima yana rokar ma prettyn shi sauki gurin Allah. Maryam ta kira, sai gata tazo,idon nan ya k'ada, "Maryam ya akai? Kai ta k'ada, "ina zaton ba D'a d'aya ne ga Ya Furera ba, dan naji tun dazu likita na ambata mata "Babies" kan bazata iya ba ita kad'ai. "Ba komai,kiyi ko'k'arin ki bata wannan inji Abba,InshaAllah zata iya tunda ansa Allah. Kai ta k'ada, kan ta k'ar6a tai ciki. Sai d'ai fur likita yace zata t'sayar mata da labor wai ya koma baya,tace adu'a ce. "Zansha Doctor, adu'a ce, a bani dan Allah.. Kai ya k'ada, dan shi yanzu komai aka ce Allah kawai yinshi yake,dan yaga Aya.... Cikin Rahmar Ubangi, ko minti goma batai da sha ba taji wani nishi ya taho mata, da sauri likita ya k'alleta kan ya d'akko abin ka'ri yai mata. Baki Maryam ta toshe,take ta k'alli robar dake a hannunta. Da ikon Allah ya zaro baby,sai ga nan wani na biyo bayan d'aya. Tuni Furen tai baya tana mai jan numfashi sama. Da gudu maryam tai waje tana murnar taga yara biyu. "Yaya Ahmad!..Ya Ahmad, yana d'urkushe yai sujjada kusan minti biyu adu'a kawai yake ma Fure. Ganin haka ta ruko hannun Ummi da Ada, "wallahi twins ne, ta haihu naga... ''Assalamu Alaikum warahtullah... Yai k'waya d'aya hagu da dama. Cikin azama yace "Pretty fa? Sai ta zuba mishi ido, dan sam ita bata ma kula da halin da take ciki ba. Ganin ta zuba mishi ido yasa da sauri yai hanyar kofar room d'in. Samu yayi likita na fad'in zaki iya,ki kara nishi tana k'ada kai, gaba d'aya numfashin ta sama yake. Ganan yana ganin wani abu bak'i-bak'i likita na ko'k'arin fitar shi. Da gudu yai kanta tare da kiranta, dusu-dusu ta fara gani, tuni ta hau yunkuri kamar zatai amai, da sauri likita ya jawo babyn da Allah ya kara tunkudoshi. "Sir... Da sauri Nurse ta fara nuna mishi Furen dake ko'k'arin d'auke numfashi Ahmad na jijjiga ta. Cikin sauri ya bama d'ayar Nurse d'in babyn kan yace "oh no! Cikin zafin nama ya jona mata "Oxygen", tuni ta fara sama da kirji tana jan numfashi, ko dusu-dusu ta d'aina gani, cikin sauri ya zuke wata allura bai wata wata ba ya chuka ta jikin cinyar Fure. Numfashi mai k'arfi taja,wanda yai d'ai-d'ai da k'wala kiran da AAA yai mata "PRETTY.......................... By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywa 9/29/16, 2:55 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 47_Ina Pretty ta lula, Kanta yazo yana d'anna mata kirji yana k'allon numfashin, sai d'ai ita ko gizau, tuni Ahmad ya kafawa hannun likita ido ba ko kiftawa, ya ma kasa kok'arin hanashi ko sashi,hawaye kawai ke zubar masa, da sauri likita yace nurse ta nemo mishi likita guda biyu,ya sanarta sunan su,kan su zo ya kara mata wata allurar, ganin ba nasara yasa Ahmad kawai ya zame gun yana kuka kamar yaro, shi kenan shi, ya zama maraya. Kai da g'wiwa ya hada yana rusar kuka, yayinda likita yake ta aikin shi. Su Maryam da suka leko tuni sukai waje suka had'a kai suna kukan Fure,dan d'uk sun saddakar ta ma mutu. Wani numfashi Fure taja mai k'arfi, a hankali ta fara mutsu- mutsu d'ai-d'ai shigowar likita d'aya. "Pharmacy".. Cikin murna likita ya kira shi, da sauri ya daga jin tarin Furen,sai d'ayan likitan ya cire mata Oxygen d'in. Da gudunshi ya karaso yana kiranta, cikin hankali ta fara bud'e ido,komai ya fara dawo mata. Akan AAA ta dire,wanda har yanzun hawaye yake rike da hannunta a bak'inshi yana d'an dariyar murna tare da shafa gashin kanta, sai d'ai koh sannu ya kasa furta mata,a hankali ya d'aura kanshi a kirjinta kamar wani yaro. Cikin hankali ta d'aura hannunta a kanshi tana hawaye da sigar lallashi, tasan da ta mutu, da AAA shi zai fi kowa shiga a wani hali. Da taimakon manyan likitocin suka had'u suka temaki matar "pharmacy". Tuni su kuma Nurses suna chan a d'akin taimakama yaran. Sai da d'aya Nurse ta fita tace ma su Maryam toh su d'aina kuka karamin suma tai... Sai da ya tabbatar ta g'yaru da komai sannan yahau musu godiya. Har aka gara ta d'akin hutu na musamman suna a manne da hannun juna. Tuni kuma aka hau buge-buge su Ada su su Ummi kan Fure ta haifi y'an biyu, shikam suna a gado d'aya. Sai ga nan yaran su an garo musu cikin gadon yara. Wani ihu su Maryam suka buga da suka ga uku, tamkar yara harda dan t'sallen su,tuni suka bi Nurses d'in d'akin da Fure take suna murna, kam suka ce musu banda hayaniya, amma sun san ai ba abu ne mai wuya ba. Wai sai a sannan ya ma tuna da yaran, tuni kowa ya d'au d'aya, ummi tace "woow.. Adama tace "k'yau... Yayinda Maryam tace "MashaAllah, kawai sai nurses d'in suka sa dariya, dan ko su suna ta yaba kyaun yaran, gasu da dan girman su, kan suka had'a baki gun fad'in "Congratulations sir" kai ya k'ada musu, kan yace "yau ak'wai k'yautar magani a store. Na hannun Maryam suka ce "wannan ne Hassan, ga nan Hussain, na hannun Ummi kuma itace mace "Gambon su, kan suka fita. Wajen gadon su Fure sukai da yaran, harara ya kai musu cikin wasa, "ai munyi fad'a dasu, kad'an ya rage na rasa Momman su ya k'wanto kan Furen suna musu dariya har Furen, a hankali ta lallashe shi kamar gaske. Ido kawai suka zuba ma yaran da suka d'aura musu su. A hankali ya k'allo Furiin, tambayarta yake shin tasan dasu? Kai ta ka'rkace mishi tai kallar tausayi, ido kawai ya zuba mata, Furii ta mishi komai.. Ga ta bashi yara masu kamar shi, sai sumar(gashi)Furiin da suka d'akko da d'an bak'in nan. Kan kace wani abu sai ga nan y'an uwa sun fara diddikowa, harda Mama ta wanke ido tazo ganin twins, sai d'ai suna ganin uku sai su hau kabbara. Abba cikin sauri yai d'akin Momy da har yanzu d'aya saura bata bud'e d'aki ba tana bacci,wanda a zahiri in ta dad'e takai goma,amma ranar Allah ya k'wantar ta. Mut'seke ido take ta bud'e, ganin Abban sai wage baki yake yasa tace "Alhaji lafiya? Cike da murna yace "Maryam matar Babana ce fa ta haifi y'an uku.. Cikin rashin fahimta tace "waye hakan? Sai ta kai hannu kan dank'wali tana warewa, "a wanake dashi bayan Ahmad, Furera ce ta haifa ai..... Hannu kame a kai Momy tai poster, jin Bud'e kofar gefe yasa ya juya cikin murna, Huwaila ce, "Abba wa nake ji kana haihu? Cikin murna yace "Sa'a matar Ahmad, uku fa,ras, kuma da kanta... Waya aka mishi sai yace "bari ga nan Ummi. Cikin zakuwa yai waje yana amsa waya, baki sake suka bishi da k'allo, Momy na furta "Furera kuma?... Cikin kok'wanto. By Feenat Ja'afar. Feenat.mywapblo 9/29/16, 2:58 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/4, 10:09 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 48_"Kai Momy ina fa Abba bai ji da k'yau bane, wane irin Haihuwa? Kuma y'an uku?.. Kai "impossible".. K'allonta kawai Momy take, "tun ba yau ba na fuskanci yarinyar nan tana da ciki,amma fir kika karyata.. " no ba ma wannan ba, saboda rashin mutuncin ya mot'sa musu,kinji wai har akaita asibiti Ummi taje bamu sani ba?... Tuni ta hau kumfar baki, kan zasu ga ba inda zata toh. "Wallahi Momy kar kije, tunda an nuna baki isa ba kawai. Tuni ta hau zigata, kuma wai sai ta hau buga ma su Rukayya da Aunty Jidda waya, kowa ya ji sai ya na nata haihuwa kuma? Y'an uku?. Kamar k'wa yadda Momy tace d'in kin zuwa tai, sai Huwaila ce taje ta ga k'wak'waf. K'wanan su biyu yasa a sallame su, tare da d'aukar Nurse mai zuwa duban su, dan sosai jama'a sukai yawa.. Tun a asibiti Fure tasan tai haihuwa, dan Abba mota biyu sukai zuwa ganin yara shida Abokanshi, kowa yazo sai ya direma Fure y'an banki. A gidan ma haka, jama'a sosai, kusan kullum Aunty A'i na nan gidan kusa da yara, Fatee na jan nata tsohon cikin, shi yasa d'uk tai lum, amma d'uk da haka tana a hanya kullum, Hassana an zo, dak'yar aka d'anne zuciya ganin ikon Allah, sam AAA baida k'arya, amma akan yaran shi ya tada ta, d'uk wani kaya na ban sha'awa yara sun sha su, an k'awata d'akin su g'wanin ban sha'awa. Yara sunci Hassain,Hussein, da Hasna(pretty),t uni tun a asibiti yai ma yaranshi huduba, sam ba sunan kowa, dan kowa yazo yana son mai suna, Hasna kam wai ta mishi k'yau, shi yasa ya sa mata shi, dan ta chanchanci zama pretty 2 wai. Har sukai k'wana 5 ba Momy ba Aunty Jidda bare Rukayya, d'uk rashin shiga jama'a na kishiyar Rukayya amma tazo gidan Fure a karo na farko. "Anya mutanan nan zasu ga Annabi Ya Furera? Ace tunda haihu, ba wacce ta leko dubaki cikin Momy da Aunty Babba? Murmushi tai kan ta k'alli Maryam d'in, "mey kike so toh nace? Tunda kinsan yadda nake gunsu.. Baki ta ta6e Maryam d'in, Aisha tace "ki barsu ke d'ai Fure, kar ki fara komai, aciki har hudubar hanasu su Hasna da ake miki.. Murmushi tai ta k'ada kai, ita kad'ai tasan mey zatai. "Ba wanda zan hana yara,asalima nai alkawarin d'uk wacce ba tazo ba zan kai mata har gida ta goya. Karamin t'saki Maryam tai, "wallahi ba mahalukin da ya isa na haihu bai min barka ba na kai mishi D'a, wallahi ko zai mutu. Tab, karshen kyyaya kenan wannan... Shiru tai lokacin da Aisha ke zungurarta, su Momy ne t'saye bak'in kofa ita da su Aunty Jidda. "Momy shi yasa nace miki bazan zo gidan nan ba kika tilasa min, sam na ki jinin had'uwata da shegiyar yarinyar nan.. Ta nuno Maryam. Ciki momyn ta shigo, tana mai harar kowa na parlourn, kasa Fure ta s'akko cikin girmamawa, ita kam Maryam baki ta ta6e, tare da dan gunguni ciki ciki. "In bata nuna haka ba ina za kusan y'ar gidan mai waldar mashin ce ita... Da sauri Fure ta dago, Rukayya ce, tuni taji zuciyarta na tafasa, ga nan Huwaila, ga Aunty Jidda, ga kuma Momy. Wani murmushi tai, kan a hankali ta girgiza kai, Lalle Allah a yau ya ara mata ranar da ta jima tana neman zuwanta, ranar da har sallar t'sakar dare tai dan zuwanta. "Mtsww.. "Alhamdulillah, a ko ina zan bugi kirji sannan nai alfari, "of course, ita ce sana'ar uban mu, amma kamun nan sai ki fad'an sana'ar taki uban... "Maryam... Cikin t'sawa Fure ta kat'seta, "ki kama kanki, baki ta ta6e, Cikin fusata Rukayya ta mike, ''karya na fad'a, iyalan t'siya da t'siya, an zo aci aziki ai dole a haiho y'an uku, kinga ko ba komai an mamaye gida. Ido Maryam ta rint'se, a rufen tace "Ya Fure ba miyi dake zaki t'sayar ni a batun nan ba fa, saboda haka wallahi sai na furta. Ido ta bud'e, har da mat'sowa kusan Rukky, su Momy da Aunty Jidda ido ne kawai nasu, dan sosai sun yi mamakin fitsare idon Maryam, wai a gaban su take wannan rashin mutuncin? "Sana'a ba chacha bace, ba kuma satar kud'i bace a Ak'watin gwamnati, a jerin barayin g'wamnati dole uban ki ya fito ciki, ga chacha kamar ibada, ga neman mata kamar d'an taure, ga.... Mari Fure ta sakar mata, cikin t'sabar fusata ta fara mata fad'a, "wa ya fad'a miki wannan abin? Rike da kunci Maryam tace "sana'ar ubanta na fad'a, ko ke ba k'ya kishin naki uban?.... "A'a ki barta, ki barta ta kai Aya, tanan zamu san lalle an gaji t'siya da talauci, bak'in ciki take da dukiyar uba na, kuma wallahi yafi Ubanku Malam Muhamm... "Rukayya....cikin t'sawa Fure ta kat'seta, kan ta nuno ta da hannun cikin t'sananin fushi da "ki iya bak'in ki, ya zama ranar karshe da zaki kara wannan kuskuran na ambatan sunan mahaifin mu ciki. Kiyi komai, amma wallahi ki t'sallake wannan, ba zan d'auka ba... Ta karasa tana mai kawar da kai gefe, Ba wanda ba k'alleta ba lokacin da tai t'sawar, yayinda su Ahmad suka karaso bak'in kofar parlourn suka t'saya gefe. Harara Aunty Jidda ta k'wada mata, "dallah rufe mana baki a gun, ji ta, har wani abin tunkaho ne ga alfari ga d'an waldar, an fad'a muku ya'yan mai walda, matsiyata kawai... Ido Fure ta rint'se, kan ta dago ido ta sauke su kan Aunty Jidda. "A fad'an komai, amma uban mu daraja ne gareshi matuka a gun mu, a gaskiya yau hakurina zai kare akan hakan, kai ta girgiza, "dan Allah sam bazan d'auka ba, sam Allah. Sai ta sa bayan hannunta ta goge y'ar k'wallar da zata ta fad'o mata. "Momy kina jinsu ba kiyi magana ba? Sunci sun koshi wai har ita wannan tana da baki? Yaushe kika samu y'ancin kai dan kin tashi a JUYA? Shine har zaki wani hau fallin fararo budurci bayan haihuwa?... Cikin sauri Maryam tace "Dallah rufe mana baki, ki bari y'an gidan masu y'ancin magana suyi, dan yanzu sunan JUYA ya koma naki... Tunda gado ta zame muku sai ki haiho... Kanta suka yiwo ita da Huwaila, tuni Maryam taci damara,Fure na ganin haka ta shiga t'sakiya, yayin da Ahmad suke kuts'o kai dan jin abin na yawa, "d'uk wanda ya ta6a ta wallahi zan zage muci uwa a gidan nan dashi... Ido ta rufe tare da sauya musu kama "hakuri ba hauka ne ba, kar ku kaini bango Wallahi. "Kuma ki sani haihuwar ba gado bace, dan da tuni yaya Babba(Aunty Jidda) ta gada, ba gado bace, wallahi da tuni nima na gada, ba gado bace, dan da tuni kowa a duniya ya gadeta, dan ba dan uban da aka ta6a ruwan shi daga sama ya fad'o, kowa uwa ce t haiho Shi a duniya. By Feenat Ja'afar. [5/4, 11:53 PM] Feenat Ja'afar.: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 49_ If you feel so high? Then Stay away.. Or else.. K'yam suka t'saya, baki sake suke k'allon Fure tai turanci, "Wa? Da wacce ta isa ta dake ni ne ina k'allo? Ai wallahi da mutum ya debi hakoranshi a kasa, na rantse. "Toh ba anan ba, sai d'ai ku tafi gidan uban ku yau, ku tattare ku kara mai, aje inda aka fi k'wari. Baki Maryam ta ta6e tana since damara, yayinda da Fure ta rint'se ido. "A gaskiya bazan iya fita ba izinin mijina ba, kiyi hakuri Aunty Jidda... Cikin fusata ta tashi tana huci, "Are you challenging me?.. Murmushi Furen tai, kan ta girgiza kai, "No,am not, sai Aunty Jiddan tai murmushin mugunta, sai dai kan tai magana Fure ta karasa da "Amma "If it comes to that... Sai ta juya bayanta tare da rint'se ido. "Then i challenge you".... Su kam su Ahmad jin abin na yawa yasa sukai cikin parlourn. Aunty Jidda tace "Eyeee... Lalle kin koshi Fure... Uban waye gatanku a garin nan? Da sauri tace "Allah, da kuma... Marin da Momy ta sau mata mai mot'si ne yasa ta kasa karasa wa tare da yin baya zata fad'i taji an rukota da Hannu da yawa. Sanye yake cikin farar "suite" da "purple" d'in y'ar ciki, sosai yai k'yau, da ganinshi Naira ta zauna mishi, ganan fatar nan tai k'yau... "Ya Suleiman, cikata Ahmad d'in yai,dan Ya Suleiman yafi rukota, da gudu maryam ma tai yo wajen shi, kwai sai suka ruk'unk'umeshi tare da sakar mishi kuka. Hannu yasa d'uk ya zagaye kafad'un su, har wani ka'rkarwa jikinshi yake,tuni ran y'an maza ya tashi. Cikin Azama zai gun Momy Fure ta rike shi, kai take girgiza mishi hawaye na zuba,ganan kukan dan Maryam ya karad'e parlourn, kawai sai ya rint'se ido, tare da cije le6e. "Muje, kan na aikata kuskure Maryam, Furera d'akko shiga ki fito. Kai ta sunkuyar, kan ta dago su kan Ahmad, wanda idonshi rintse bazaka gane halin da yake ciki ba. "Ahmad, ka ban izinin fita dan Allah. Ido a rint'sen yace "ki bi umarnin su Momy, ki je gida Furera, kije... Kawai ya juya ya fice a parlourn cikin sauri. Ido ta rint'se, wato taje? Kawai sai ta k'ada kai. "Sai ai gaba ya sallama ki, Huwaila tace "kuma a bar mana yara.. Harara Maryam ta sakar mata, "ko baku fad'a ba, dan mu kad'ai aka kawo mu,babu su cikin garar auran mu. "Ku barsu Fure,ku saman a mota. Wajen Hasna Fure tai, tana a k'wance ta fara ko'k'arin goyata Rukayya tazo, "bakiji ki bar mana yara ba aka ce? Tana jin tana ko'k'arin d'auke ta ta dago a tunzure ta sau mata mari, "uwar kice tai min nakudar da zan bar muku yara na? Eh? Toh naga wanda zai t'sayarni in ya haifu. Jan Rukayyan Aunty Jidda tai, "ku k'yale su suje, mey za kici da yaran bare a huce a kanki? Ko ta kansu basu kara yi ba su Ada sukai waje da sauran, fure ta d'akko hijab, yayinda d'an gidan Maryam ke t'sala kukan ta d'auke shi, t'sawa ta daka mishi, "ai ba inda zaka bini yaro,tuni ta yakice shi tai waje,kasa yai yana bori da kara jiniyar kukan shi. A bak'in gate Fure ta dago tana k'allon Ahmad dake cikin motarshi a k'ulle, da sauri ta d'auke kai ganin zai k'allota ta shige mota. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. 9/29/16, 2:59 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 50_Suna ko'k'arin jan mota sai ga nan Muh'd yai sauri fita a tashi yazo, t'sayawa ya Suleiman yai tare da K'awar da kanshi, tuni Maryam ta k'ank'ance ido, kofar ya bud'e, "Ya Suleiman ka'r kai haka, "Maryam ka'r ki tafi, dan Allah Aunty Furera kuyi hakuri, yanzu AAA ya kira ni, mey yai zafi haka?... "Ka shiga daga ciki zasu kora maka bayani, sannan tafiya kam nayi na gama, wallahi ka ma biyo ni da takkadda ta.. Murfin motar ta ja, tuni Fure ta sau kuka lokacin da Ya Suleiman ya ja mota, shi kam Muh'd ya ma kasa komai. Da sauri ya juya jin an dafa kafad'arshi, AAA ne idonshi yai jajir, "ka shiga ka d'akko yaron ka ciki yana kuka, ka'r ka kula kowa,kawai ka fito mu tafi, kai ya k'ada mishi. Rukayya ya samu tana k'wadawa Abulkair t'sawa... "Dallah yi mana shiru agun... "Tunda ta barka kowa ma ba mai d'auka, irin t'siya da talauc.... Tass, da sauri suka jiyo,wanda ba shiru Rukayya ta dafe gun mari a ka'ro na biyu yau, tuni Abulkhair yai shiru. Ilahirin Parlourn sun zuba mishi ido, sam shi baida fad'a, asalima shi mai bark'wanci ne, sam zai wahala kaga bacin ranshi, tuni sai ya sauya musu kama. "Ashe rashin mutuncin ki ya kai haka? D'an nawa ne gadon t'siya? "Muh'd, mey nake gani? Matar Yayan naka ka mara?... "Ta Allah Aunty Jidda da mari ne kawai, da wallahi sai nai kasa kasa da ita a gidan nan.. Charaf Huwaila ta chafe, "Aunty Jiddan? Cikin fusata yau yo kanta, da sauri ta nufi bayan Momy, kawai sai ya sunkuci d'anshi yai hanyar Parlour, "Yau na tabbatar Mama Uwa ce Momy, kuma Maryam kamar ta dawo ta gama, dan ba mai raba min aure ban shirya ba. Zaune suke ya Suleiman na t'sara ma su Umma da Abba abinda ya je ya tarar, "G'wara da bakai hukunci ba Sule, Allah ya muku albarka, ki bar kuka uwata, d'uk na halili mai kishin iyaye ne, tabbas anzo gabar da bazan hana ku k'ar6ar y'ancinku ba, kuyi hakuri, Allah ya raya muku yaran ku,kema Maryam banso kin bar musu yaron ba sam, bari na koma gun aiki, ku kara hakuri. A gado Umma ta k'wantar da Hasna,kan ta d'akko Hussein da Hassein dake parlour. A hankali Fure ta zame kusan Hasna ta k'wanta,d'uk idonta yai mata nauyi dan kuka, k'allon yaran kawai take hawaye na zubar mata. A hankali ta kai hannun kan sumar kan Hasna. K'allonta Umma tai cikin tausayin y'artata, tana fatan wannan ya kasance cikin karshen kuncin rayuwar ta. A gefe Maryam ta zauna. "Kuka bazai miki magani ba Fure, kar kisa damuwar su har ta ja miki mat'sala, kinga kina da d'anyan jego, Allah zai bi ku hakkin ku ne kuna zaune.. Kai Maryam ta k'ada, "Allah Umma na hakura da auren nan, wallahi har Muh'd na t'sani ganinshi balle danginsu... Hawaye ta goge a karo na farko tun faruwar abin. Shiru Umman tai, tasan yanzun d'uk suna a cikin fushi ne, sai ta tashi ta basu waje tare da nufar kitchen dan d'aura ma Fure ruwa. A gaban Mama suke bayan sun t'sara mata abin da ya faru, dak'yar Ummi ta goya Abulkair sukai waje don rarrashi, tamkar yaro haka AAA ya d'aura kanshi kan kafar Mama yana hawaye bayan ya gama t'sara mata. Shikam Muh'd yana a gefe sai fad'in Allah kawo Abba yake. T'sam Mama tai,tabbas lokaci ya yi da zata takawa Momy birgi, ko Abba bai d'au mataki ba a wannan karan zata t'serar da mutuncin sirikanta, dole su zamto y'antattu cikin gidan nan.. Dole ne wannan. By Feenat Ja'afar. Assalam Alaikum warahtullah.. Ku diba wannan, sannan ai min affuwa, zan d'an yi tafiya,Kila ku jini inna samu time... In anji chilu toh sai na dawo... Luv you. Like 路 5 路 Reply 路 Report 路 Ma 9/29/16, 3:00 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 51_Dawowar su kenan sukai bangaren Mama, Muh'd na ganinsu ya mike yai waje,yayin da AAA yai saurin goge idonshi,kan ya d'aura bayan Muh'd, da k'allo Momyn ta bishi, bata ta6a ganin AAA cikin yanayin nan, sannan koh sannu da zuwa bai mata ba,asalima ko inda take bai k'alla ba, ita kam Mama kai ta kawar,da hannu Momy tai ma su Aunty Jidda suje bangarenta. Kamar kullum ta fara zazzage ma Mama kan wai Muh'd ya mata rashin kunya akan Matan su marasa mutunci... Sai balbali take,"in na zartar toh ta zaunu gidan nan, basu ba dawo mana sai sun san mutuncin mu tukun... Murmushi Mama tai,kan ta k'allota a ka'ro na farko tun t'sawan shekarun su kuma ta tanka. "Hajiya Maryam wane mutuncinku ne yai saura gunsu da gaba kike tunanin ya karu? Iya kok'ari yaran nan suna miki biyayya ka'r ma Matar Ahmad taji bayani, wanda nai imani koh manyan sirikan gidan nan basa miki, haihuwa tai har t'sawan k'wana biyar kan kukaje ganinta, d'uk ke ya kamata ace kin fara zuwa ganinta ko dan irin gorin da kuke mata dan bata haihu, bazan boye miki ba, a gaskiya banjin sam dad'in irin abinda Furera ke fuskanta a gunku sam... Cikin mamaki ta k'allo Maman,kan cikin fusata da isarta ta t'sayarta,tuni suka fara kace na ce,sabon lamari,wanda sam ba halinsu ba. "Sam ya isa ikon,dole a barsu su wala kamar d'uk sauran sirikan gidan nan.. Safiya tunda kina neman ja dani,toh naga wanda zai dawo mana dasu gidan nan, yara ni nake iko dasu ba ke ba, dan ni naci fitsarin su da kashinsu, dan haka ba mai nuna min isa kansu... "Hajiya Maryam kamar sun dawo sun gama ne, kuma kisa ido.. A fusace momyn ta tashi, "wa ya isa dawo dasu gidan? T'saye itama Maman ta tashi, "ni Safiya da kaina zan dawo da sirikaina gidan nan, karan nan kin kai ni karshe kiyi hakuri... ''Safiya sam,kar ki ma fara, ki bar Maryam tai son ranta... Abba da Muh'd da AAA ne t'saye bak'in parlourn. Murmushi momyn tai ma Mama lokacin da su Abban ke karasowa, ita kam Mama kai tai kasa dashi,tasan Momy ita ke da fad'a aji ko agun Abban su AAA, amma dole karan nan ta nuna itama mai iko ce, sai d'ai da mamakinta taji Abba na fad'in, "Wanda yace su tafi shi zai dawo dasu, Maryam da kafarki nake son ki dawo da yaran nan d'akin su... Cikin mamaki suka k'alleshi, barin Momy da ta cika da mamakin Abban,Muh'd harda g'yada kai da murmushi. "Sam banga aibun yarinyar nan ba Furera, tana kula damu,gata da kok'ari, amma tun ba yau ba nake mamakin yadda jininta bai gamu da naku ba. "Sosai zan bata ran d'uk wanda zai fara tarwatsa gidan ya'yana, ina umartarki da kije tun muna sheda juna ki dawo da yaran nan, Tashi yai kamin ya k'allo Momy, "kinji na fad'a miki...ya k'arkade rigarshi da bambami ya fita,yana mai kara sanar da Momy zancen shi. Da d'an harara ta k'allo su Mama, "Allah ya kiyashe ni biko wallahi, yau naga t'sant'sar butulcinki Safiya, kuma in nice ba ni ba yaran ki, ka'r in kara ganin keyar wani sashe na.. D'uk ki jijasu na bar miki... A fusace tai hanyar fita AAA yai saurin binta, "Momy abin bai kai haka ba pls.. A fusace tace "ka'r na kara ji ka kirani da Momy, ban haifeku ba, da harara tabi mama kan tai waje, binta zai kara yana k'allon Mama, kai ta k'ada mishi, hakuri ta basu kan sui hakuri, sannan ka'r su kuskura fara yi ma Momy rashin kunya kan Matan su, su bar komai hannunta, sannan in ta huce su lallasota,kai suka k'ada mata. Huci take tamkar asman ta zata tashi, da sauri sukai kanta, "Momy lafiya? Hannu take kaiwa baki,da sauri Huwaila ta d'akko mata ruwa ta bata,zuwa chan ta nutsu. "Yau Alhaji ya nunan karshe na,yai min tozarci... nan ta k'washe yadda sukai da Abban ta sanarsu, tuni suka hau zigata kan ka'r taje ko'ina, su d'in wa?? ~~~~~~~~~~~~~~~ "Allah takaddarmu zaku bamu, ka sanar da ya Ahmad ma tun wuri... K'allon Maryam d'in Furen kawai take yadda ta rufe ido tana y'arfawa Muh'd masifa cikin waya,Kai ta k'ada, ina ma zata iya yiwa AAA haka ko taji saukin zugin zuciyarta? kawai sai ga nan hawaye ya zubo mata,bayan hannunta tasa ta goge, tun jiya AAA yake aiko text amma ta kasa ma k'allon wayar bare ta d'auka ta gani. kamar had'in baki kuwa Maryam na gama waya sai ga nan call na AAA akaran farko tun jiya. Sautin "Ringtone" nashi na ("nothing gonna change my love 4 u") ne yasa ta k'alli wayar,maimakon taji sanyi kamar kullum in AAA na mata baitin koh kidan na tashi kawai sai taji wani haushi da t'sanar wakar ya rufe ta. Cikin zafin nama da masifa ta d'au wayar ta seta bango da niyar k'wad'a ta Umma ta shigo da Hussein na kuka... A hankali ta zame wayar ta fad'i kan gado, kawai sai ta sa ma wayar kuka, ga Kukan Hussein. Da k'allo Umma ta bita baki sake, tasan Fure bata huce ba, ita so ma take taji tai koh masifar irinta Maryam koh taji sa'ida,amma ina,tun jiya take kuka da tunani. Cikin nut'suwa Umma ta zauna a kusanta, sai ga nan Hasna ma an kawota, tuni sai suka karade gidan kuka, har sun ma rasa wa zasu lallasa. Sai da tai mai isarta Umma da K'anwarta na k'allonta kan tai shiru,sai ta hau goge ido kan ta mika ma su Umman hannu, ba musu suka d'aura Hussein, dan Hasna har ta gaji da kuka tasa hannu a baki. D'uk sai suka basu tausayi. Ajiyar zuciya tasau, tuni sai ta dan samu sa'ida ganin yaranta yayin shayarsu, tasan koh su zasu iya maye mata g'urbin AAA a farin ciki. Zuwa wani lokaci har ta ware,sai d'ai d'uk ta koma marar baki,ido kawai ne nata. Haka AAA yai ta kira ba d'auka, gun abincintq ma suna ta neman ta, daga karshe ta d'auka, sun hau mata lissafi kenan ta kat'sesu da cewa su rufe "restaurant" d'in su kaima AAA mukulli, bata jira su ba ta kashe ma wayar d'uk tana huci. Da yamma ta fito a wanka,d'uk kanta sai sara mata yake, har wani jiri-jiri ta fara ji,a hankali ta nemi gefen gado ta zauna tare da rintse ido, ji take tamkar kan zai rabe biyu. Kukan Abulkair ne da kamshin turaren AAA yasa ta d'an dago kai da sauri, yana t'saye rike da Hasna duk ya marairaice fuska. Gefe tai da kanta,sai kawai ya kut'so kai, wato tana wanka suka shigo?amma ba mai yinkurin fitarsu a gidan nan?... "Pretty"... A zabure ta mike ido rufe tana tuna mishi hanyar kofa,sai d'ai ta kasa furta komai sakamakon wani sarawa da kanta yayi. Cikin sanyin murya tace "fita.... Da azama ya k'wantar da Hasna ya yo gunta ganin ta fara layi hannu rike da kai, cikin k'arfin hali da ganin dusu-dusu tace"kar ka ra6e ni... Maganar ce ta sarke jin K'wak'walwarta ta bar aiki,dulum take gani ba koh dusu dusu, a chan nesa take jiyo AAAn na kiranta yana dan girgiza kafad'arta, sai d'ai ina,d'uk ta sake mishi jikinta tamkar wata macacc....... By Feenat Ja'afar. 9/29/16, 3:01 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 52_Da rige rige su Umma suka doshi d'akin jin irin kiran da AAAn ke ma Fure, turus sukai ganin yadda AA ke jijjiga ta amma bata koh mot'si, kawai sai Umma ta ju ya jiki a sanyaye,ta saddakar sunyi ajalin y'arta ta, Maryam tai saurin karasa wa tana kiranta,a yanayinda take yasa Muh'd fita a d'akin, tuni cikin kuka ta fara in sun kashe mata y'ar uwa wallah su kuka da kansu... Ganin ba nasara yasa AAA ya zame rike da Furen yana kuka tamkar wani yaro... Ya ma manta da wani asibiti, yasan harda sa hannunshi a mutuwar Fure.... Tamkar had'in baki su Hasna suma suka sau kuka, Hussein dake gado shima ya fara. Tamkar wani zautacce haka yake surutai rike da Furen yana kuka. Tamkar an hankad'o Ya Suleiman sai gashi cikin d'akin, shi bai fuskanci abin da Umma ke fad'a a waya ba,yasan d'ai tana ta ambaton Fure cikin kuka. "Subhanallah.. Mey ya samu Furera? Da sauri AAAn ya dago kai ido jajir, tuni Maryam ta amshe,"yaya sun kashe mana ita ne,sun huta... Cikin azama ya Suleiman ya kamo hannun Furen,sai ya k'allo su, "muje asibiti, ku kamata,, AAA ido kawai ya zira mishi,sai da ya kara fadi kan Maryam ta d'akko ma Furen doguwar riga suka zira mata.. Ya Suleiman zai d'auke ta AAAn ya rigashi, kamar Yarinya ya sunkuceta sukai waje,da ido Umma ta bisu,dan tasan sai wani ikon Allahn Fure, ga ihun yara na yunwa. Anyi sa'a likitoci sun k'ar6e ta taimakon gaggawa,tuni Muh'd ya sanar ma Mama halin da ake ciki,lallashi kawai Ya Suleiman ke mishi,dan ya gano a halin da yake ciki, ba'a jima ba sai ga nan Mama da Ummi. Sun samu ta farfado, sai d'ai har yanzun ido rufe amma tana numfashi, halamar an mata allurar bacci. A hankali ta fara juya kanta tana mot'si da ido halamar tana son bud'e su, cikin hankali ta bud'e idon ta sauke su kan sling,ba abinda take ji sai karar bugun agogo da d'an ajiyar zuciya a kusan kanta. Sai ta sauke idonta kan waje,AAA ke rike da hannunta mai allura ya d'aura kai a gefen gadon.. Tuni ta fara tuno abinda da ya wakana,kawai sai ta fashe da kuka tana ko'k'arin zame hannunta, a ka'ro na biyu ta t'sallake rijiya da baya. Da sauri ya dago cikin magagin bacci,ganin Furiin ta farfado yasa yai saurin tashi. "Pretty... "Sannu..."in ke miki ciwo?.. Ido ta rint'se tare da juyar da kanta,tuni sai ya rikice mata, burinshi ta bar kuka koh dan yadda Bpn ta ya hau.. "Ki yafe ni Pretty,ki taimaken ki bar kuka ko dan lafiyar ki,dan Allah... Shima sai ya sa mata, "kar ki maishe ni da yara na marayu please Furii...please. Chak kukan ya t'saya jin ya ambaci yaranta, tasan d'uk inda suke suna chan suna neman ta ko dan abincin su.. Tamkar an t'sikareta ta mike tare da k'allon agogo, sha biyu na dare,sai ta cije le6e tare da furta "Hasna... Ido ta sauke kan AAA, yadda ya kusanto ta yana hawaye yasa d'uk sai ya kashe mata jiki,t'sanin mace da mijinta sai Allah, tuni sai ta ji haushin shi ya ragu ranta,hannu takai kan kuncinshi da hawaye ke sauka tana girgiza mishi kai itama hawayen na zuba... SO HANA GANIN LEFI.... K'allon-k'allo kawai suke kowa na goge ma d'an uwanshi, yasan akan Furii komai zai indai zata d'aina fushi dashi,sai ta k'wanto shi kafad'arta kamar yaro ta hau lallashi,tuni sai ya kara samun k'warin g'wiwar sanarta sirrin ranshi a kullum har sai da ya tabbatar ta saki ajiyar zuciya ta gamsuwa da hasashen shi. Kanta ya dago,kan ya hau sanarta kan tai hakuri bisa fad'in da yai taje gida,yasan mey yake nufi da hakan ba wai rashin so bane. "Pretty ina son k'ar6a miki y'ancin ki gun su Aunty Jidda ne,su san darajarki su martabaki, ni nasan wataran zakiyi mamaki,dan da kansu zasu zo bikonki.... Murmushi tai tare da kara lafe mishi a jiki, tasan fad'i yake dan ta kara sanyaya, wannan bikon sai d'ai cikin mafarkinshi. "A jiki na ina jin su Hasna na chan suna kuka, ni kam da an kawo min su... Sai ta karasa da kalar tausayi,jijjiga ta ya fara halamar rarrashi, ("I know), amma dazun kusan takwas naje ni da Mama, an siya musu madara da taimakon Dr,gaskiya suna da wayo,barin Hussein, da ya ji an sa mishi (feeder) zai fara kuka, dak'yar d'ai muka samu suka sha kad'an da taimakon Umma da Mama sukai bacci. Ajiyar zuciya ta sau,kan tace "Aiya,ni nafi tausayin Hasna, mai rauni ce... Dak'yar ya lallaso ta ruwa ya kare ya fidda Mata ruwan kan ya bata abinci suka ci tare kan suka k'wanta. Washegari tun asuba yaje gidan su Umma. Da Abba sukai ka'ro ya dawo masallaci, sun gaisa yake tambayar Mai jiki yaga sai sunke kai yake,sai Abban yai murmushi, "Amadu shigo daga ciki, yau bamui bacci ba sam yaran nan masu wayo.. Ai kam suna shiga Muryar su Hussein ce ta fara amsa musu sallamar su,Abba yace "kaji ba? Fur sunki shan madarar sai karamar ke sha. Umma yai ma magana suka fito parlour,ba su ko jima ba Maryam da K'anwar Umma suka nufi gun Fure dasu. Tana ganin yaran ta ajiye kofin shayin, Hasna ta fara k'ar6a suna mata t'siyar tafi ji da ita,sai d'ai ita baccinta ma take, ana bata su Hussein tuni suka kama mikis kake jinsu ba kuka. Sai tai murmushi tare da k'allo AAA.. Idonshi na kanta yana jijjiga Hasna a hankali yana murmushi, sai itama tai mishi,Maryam dake k'allonsu ta ta6e baki. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 3:02 AM - Queen Safiyyert馃憫: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 53_D'uk da Mama ta sanar ma su Momy Fure na asibiti ba wanda yaje,d'uk Abba na hankalce dasu. K'wana biyu aka sallame su da sharadin ba taron suna. Kusan gidan Umma ya dawo wajen zaman AAA,dak'yar yake samun lekawa Store, d'uk ragamar ya barma su Hassan da wani dan K'anwar Mama, d'uk sai ya same su masu amana. Sannan ya danka ma masu kula da restuarant kan su cigaba da gashi. "Abbansu yau na tura banki ance account na ya d'aina aiki,sannan an sanarni da sa hannunka, shin zan iya sanin dalili?... Abincin shi kawai yake ci yaki tanka mata yana d'anna waya. "Alhaji magana nake fa?... Tuni ta fara kuluwa, dan yau k'wana biyu kenan ya d'auke mata wuta, wanda tasan d'uk bai rasa nasaba da kin bikon Fure da taki yi. Sannan bata tunanin yi ko da a gaba ne. Sai da ya cinye abincin shi tass kan ya k'allota fuska ba walwala. "Ince d'ai ni nan na bud'e miki shi? Kai ta k'ada mishi, "toh daga yau na rufe shi, kuma ya zama rana ta karshe da zaki min magana akan shi.. Tashi yai ya barta baki sake ya rufo d'akinshi, mey kenan hakan yake nufi? Ita Alhaji zai ma wannan wulakancin? Bayan ya hanata d'uk wasu mukullan motar gidan sai d'ai su Huwaila su kaisu a tasu shine ya bullo tanan? Kai ta k'ada, "mu zuba toh. Bangarenta ta koma, sosai take da bidar kud'i a wannan lokacin, tunaninta ina zata samu? Dan d'ai ita kam tafi k'arfin aro... Tanan parlour d'uk abun d'uniya ya isheta sai ga nan Huwaila ta shigo mata da kuka. "Momy kiji Abba ya sa an k'ulle gidan da ya ban ya kuma K'wace mukullin motata, ina haushin wannan na wuce cirar kud'i Momy chan ma yai blocking.. K'allonta kawai Momyn take,mey wai hakan yake nufi?.. "Momy daga zuwa jin ba'asi ya k'ar6e min mukulli,kuma wai wallahi kan gobe na tattare na koma gidan mijina.... Dan Allah Momy ki taimake ni, har mari yau nasha gun Abba... Da sauri momyn ta k'allo ta, ta ma kasa cewa komai, abinda Abba bai ta6a ba yau ta gani. Kan ai sati harta Y'an aikin gidan Abba ya koresu,Momy ita zatai girki,shara da wanke-wanke,dad'inta d'aya wanki inji ke mata sai shanyawa, tuni Huwaila ta koma gidan miji, nan ta tarar da wata t'siyar, dan fir yace aure zai kara ga mai bin t'sarinshi na rashin son yara. Ga Aunty Jidda itama ya tada mata wuta,har gida ya bita shida mijinta, kan ta tattara ta bashi mukullin gidanshi da mota tabi mijinta, dan ya sanarsu tun ba yau ba shi bai saki Jidda ba,ba kuma zai saki ba har abada... Ranar Aunty Jidda kuka tai taima Abba kan ita zamanta ita kad'ai yafi mata, Abba yace toh ba a gidan shi ba. Gaba d'aya Abba ya sasu a kasa mai wuya, an saba jin dad'i da fashaka yanzu komai ya yanke, tun Momy na fushi dashi har ta fara neman sulhu sai d'ai shi yace bai san wannan ba, ta cika sharadinshi akan su kawai. Zaune tai a kan dining tai tagumi da hannu d'aya, sai chakala abinci take,yanzu cin abinci ya zama sai d'ai taci dan yunwa, abinci in ba na gidan AAA ba jinshi take salam ko da kuwa nata ne... T'sawan sati uku kenan tai missing abincin Fure,wanda har in taga AAA a sashenta takan k'alli hannunshi, sai d'ai tasan Fure tai musu nisa.... Ajiyar zuciya ta saka,kan ta ture abincin gefe,komai ya t'saya musu chak ita da yaranta,musamman Huwaila da Miji ke shirin aure wannan satin, sam bai da mutunci shi,dan ko Momyn baiya ragarma sai d'ai Abba,dan in takamarsu kud'i shima yana dashi,amma yanzu fur ya rufe aljihunshi gun Huwaila... Kullum cikin yi ma Momy korafi take,gasu basu aro ko dan ka'r ace sun gaza. Dafata akai a cinyarta, da sauri ta k'allo gun, AAA ne d'uk ya marairaice fuska, d'uk tausayin ta ya fara ji,dan yasan Abba ya takureta da yawa... Kai ta k'auda, dan har yau fushi take dasu da Mama,a ganinta d'uk su suka ja mata Alhaji ya maisheta Talakar k'arfi da yaji.. D'uk da yasan ko ya gaidata kamar kullum ba zata amsa ba, hannunta ya ruko yana daga t'sugunne, "Momy nah... Cikin sanyin murya ya kirata, bata juyo ba,amma yasan tunda bata K'wace hannunta ba yau zata saurareshi. Cikin nut'suwa ya fara lallashinta kan bashi da uwa sama da ita ta yarda,yasan haifarshi ne kawai batai ba, ta tausaya ta d'aina fushi dashi koh ya samu komai ya tafi mishi cikin nasara... Sosai yau ya k'wada Momy har sai da ya tabbatar ta gamsu a gunshi baida kamarta ko da kuwa Mama ce... Kai ya d'aura cinyarta har da hawayenshi, "Sam bani kaunar ganin ki cikin wannan yanayin Momy na,nakan shiga wani hali in na ganki ba k'ya walwala.. Cikin siyasa yai ta nuna mata kan damuwarta tashi ce har kullum. "Momy ki ce komai kin isa,amma dan Allah ka'r ki rabani da yarana da Mamansu, ina neman ki yafe musu in sun sa6a miki,ki musu afuwa ki ce su dawo,nasan ke mai son farin ciki na ne a kullum Momy, amma in kinga basu dace dani ba Momy zan bi d'uk yadda kika ce,zanyi... Ya karasa yana saukar mata da hawayenshi bisa kafarta... Sassanya ne Ahmad, ko a yaranta batajin dan wanda bai kaunar ganin damuwarta sama da AAA, tasan ba wanda yake jin maganarta sama da AAA, sannan bazata ce ga abin da Fure tai mata ba har ta ji bata kaunarta,gashi tana mata ladabi iyakar iyawarta, koh dan duba ga yadda sirikarta kishiyar Rukayya ke yi a gidan, gata d'ai y'ar masu kud'in ce,kuma jinin sarauta,amma sam bata ganinsu da daraja bare mutunci, asalima ba gidan su take zuwa ba ko da abu ne kuwa ya faru, ga nan mijin Huwaila, arziki kamar suyi ihu amma ba k'wanciyar hankali, baya darajasu su iyayen Matarshi. In d'ai haka auren mai arziki yake toh tabbas tasan g'wara su Fure,masu karamin k'arfi amma suna k'yautata musu iyakar iyawarsu, sun san darajarsu, sannan bassu girman kai.. Sai yanzu ta banbance dabi'ar talaka da mai kud'i... A dalilin su Fure ta banbance t'sakanin t'saki da t'sakuwa... Ajiyar zuciya ta sau, kan ta kai dubanta kan AAA da har yanzun yake hawaye yana kuma nema musu gafara shi da Furiin shi, a hannu takai kan sumar kanshi tana shafawa halamar yai shiru,sai ya k'allota, murmushi tai mishi tana girgiza mishi kai tare da goge mishi hawaye.. "Momyn ka na kaunar ka da iyalanka Ahmad, tabbas nasan kai D'a ne,har da kari, na gode sosai sannan zaka sha mamaki. Murmushi yai wanda har hak'waranshi suka baiyana,sai ya kara k'wantar da kanshi yana k'wararo mata godiya tana murmushi. Bai tunanin zai samo Momy da y'ar guntuwar ban hakurin nan ba... Mama da tazo ban hakuri itama yau dan ta gaji da wannan gabar sai ta goge idonta, fatan ta Allah yasa Momy ta gane kuranta game da Fure. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. Feenat.mywapblog.com 9/29/16, 3:04 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/17, 10:20 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 54_"Ya zanyi Sis Fatee? Abinda hakuri bai baka ba,nasan rashin shi ma bazai baka shi ba, adu'a ta a kullum Allah ya shirye su su gane... Dan t'saki Fateen tai, "Ba komai kake ma hakuri ba Furii,mutum shi kad'ai ke nemawa kanshi y'anci, ace yau har sati uku ba ko kayan suna, toh mey suke nufi? Murmushi Furen tai, dan bata sa a ka ba,wai an T'sikari ka'rkausa.. Maryam dake gefe da sai hararar Fure take tace "ki barta Aunty Fatee,ki ma d'aina bata yawun bak'in ki, dan ni tun daga yadda ta sau jiki da mijinta nasan tabbas Ya Fure batta zuciya, tunda nan ya korota gidansu cikin bainar jama'a. K'allon Maryam d'in kawai take,yadda take ta kumfar baki, sai ta k'ada kai, "ba zaku gane inda na dosa bane Maryam.. Rayuwa y'ar hakuri ce, AAA na da dalilinshi na yin hakan, believe me... Har kusan magriba suna zaune tattauna mat'salar gidan su Momy, kukan su Hasna ne ya kat'se su suka fara aikin lallashi. K'allon yaran take,yadda sukai bul bul dasu,barin acici su Hussein. "K'allon yaran nan kad'ai ya isa mantarni d'uk wani bak'in cikin rayuwa Allah... Ku manta da zancen su Huwaila, kema Maryam ki kula mijinki fa yaron ki,sosai na kula har yau baki sakar ma Abulkair, ki sani basu laifi, haka Muh'd bai da laifi,ki fuskanci zahiri,mijinki na son ki, kar ki fara huce haushinki kansu.. Karan nan da halamar ta d'au zancen Furen, suna cikin haka suka ji a chan t'sakar gida Umma na fad'in Sannun ku da zuwa Hajiya Maryam... Da sauri Fure ta k'alli Maryam, tabbas muryar su Momy take ji, da sauri suka tashi kowa rike da d'aya suka leka waje, su d'in ne kuwa. Tuni Maryam ta had'a girar sama da ta kasa ta kama k'ugu da hannu d'aya tana girgiza ganin irin k'allon da su Huwaila ke ma gidan tasan ba zuwan mutunci sukai ba, "mey kuma aka biyo a ma ya'yan masu t'siya har gida?... Da sauri Momy da Umma suka k'allo Maryam. "Umma ki sanarsu su bar mana gida kan muyi ta'asa dasu wallahi... Da sauri Umma ta kat'seta "Maryam... Ban son shashancin banza... T'saki Huwaila tai,kan ta harari gun su Furen, "ba dan Momy ba wallahi da ba abinda zai kawo ni gidan nan... Har meye abin tinkaho a wannan akurkin? Cikin tunzara Maryam zatai kanta Fure ta rike ta,, Momy kai kasa bata hana ba, Umma ta sau baki, sam batasan yaran bassu tarbiya ba sai yau... Gaban Momy Fure tazo, har kasa ta tsuguna ta d'aura mata Hussein a cinya, ta juya ta k'ar6o Hasna da Hassain ta jere su kasan dardumar a gaban Momyn. Kowa k'allonta kawai yake, cikin nut'suwa ta fara fad'in "Momy, dan Allah yau ka'r ki kat'seni,ki barni at least na fad'i son raina, ki bari yau d'aya nai magana in yaso in na gama ki min hukunci koh da na marin ne, wallahi zan d'auka... Ta karasa kamar mai shirin kuka. "Huwaila.. A wulakance ta k'allota tana y'atsina,kai in ka ganta d'uk ta fita hankalinta ta fige, d'uk dan tashin hankalin gidanta. Murmushi Furen tai tare da girgiza kai, "kin san Allah d'aya? Toh wallahi mun fiki k'wanciyar hankali.. Baki ta Huwailan ta ta6e, "ina wata k'wanciyar hankali a talauci?.. Murmushi Furen ta sake, "haka ne, amma zai fi k'yau ki t'saya a talaka a yanzun da wannan halin da kike ciki.. Zai fi miki k'wanciyar hankali zaman ki a JUYA,sama da zama mai haihuwa gun miji... Kowa ya kalle ki yaga marar k'wanciyar hankali, ga dai daular, amma kin gamu da gamanki, kin gamu da wani irin Miji, wanda da ke mai hankali ce da kin gane Ayar da Allah ya saukar kanki... A tunzure ta k'allota,sannan ta k'alli Momy, kanta na kan su Hasna. Sai ta samu kanta da kasa fad'in kalma ko d'aya ga Furen.. Hakan ya bata damar cigaba da bayaninta. "Kasantuwa ta a JUYA a da a gunku,hakan bai hanani samun soyayyar Miji ba,naci takaicin ku,d'uk a ban haihu ba,na zata in na haihu gori zai kare ma d'an kada.. Ban san aibu na gare ku ba, ban san da mey na rage ku ba?..ban sani ba Momy. "Momy in har na ta6a sa6a miki dan Allah kimin afuwa... Bazan iya kankare asalina ba, bamu zama d'aya ba, ba kuma zamu zama ba.. T'sit kake jin su, tamkar wasu mummunai sun kafeta da ido,mamaki ne koh meye oho. By Feenat Ja'afar. [5/17, 11:31 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 55_Kan Aunty Jidda ta dawo,cikin aminci ta fara mata magana. "Aunty Jidda.. A gani na ke ce mutum ta farko da ya kamata ace kin min uziri yayin da ban samu haihuwa ba.. A gani na kalmar nan ta JUYA bai kamaci fita a bak'in ki ba ma. "Na sani da kila ke baki gano matsayi d'aya Allah ya bamu ba a da, wallahi sai nake ga kamar abin kunya ne kai ma mutum gorin abinda kaima baka samu ba, ko dan ance g'wanau bai jin warin jikinshi sai na wani... Kiyi hakuri Aunty Jidda, ba fitsara nai miki ba.. Amma kinfi chanchata a kiraki da JUYA sama dani, ban fa ja da ikon Allah ba.. Na fad'i raina ne kawai,kiyi hakuri in na 6ata ranki.. Ta karasa tana mata murmushi. Kan su Huwaila ta dawo, "Bari kuji,ba wai dan ina da lokacin ku bane zan tanka muku,kai ta girgiza,"nasiha ce,Kila tai muku amfani,, D'uk k'yaun ka,d'uk dukiyar ka,da d'uk wata K'awa ta duniya, mud'in kika rasa halin k'warai, wallahi, "u r nothing, don babu ma ta fiki mat'sayi gun Allah, "Ku kuna kawai hoping 4 dis Duniya, wacce ba komai acikinta face t'sant'sar nadama,da da na sani. Ku sani... "Wani yana chan a k'wance a asibiti ba lafiya,kila ma ko kudin sayan magani bai da shi, wani gidan sa yau ko na safe basu samu abinci sun sa a bak'in sallati ba,wani ko kud'in gidan haya bai dashi, amma ku Allah d'uk ya baku wannan. "Sosai k'yawawa ne Ku,farare" hurul ein" koh? Da ido ta kafe su, jin basu tanka ba yasa ta k'ada kai. Tabbas banni k'yau, sai d'ai ku sa ni, ban ta6a dana sanin hakan ba,cos ina duban na kasa dani sannan na gode Allah,saboda yayi min Ni'imar da bai ma wasu ba, yai muku k'yaun da bai ba wasu ba,ya baku lafiya da bai bawa wasu ba,ya baku d'uk wani farin ciki na duniyar nan, "mind you, ba fa wai dan yafi son ku bane ya muku hakan? Kai ta girgiza,"no,wal lahi talaka,daya riki Allah da manzon sa,sai ya sami mukami babba a gun Allah wanda ku ba d'ayan ku ba zai samu ba. "Domin da kanshi yace wanda yafi wani a guna shine wanda yafi tsoro na,ba wai wanda yafi dukiya da k'yau ba, amma "instead of you to thank Him,,umm..um u r ungrateful... Kun gode mishi ne ta hanyar gorantawa wanda ya tauye. Ku sani,ak'wai mutuwa, "and wallahi,you will leave all these behind. " In kin ta6a jin "k'aruna" wanda a tarihin duniya ba ai mai kud'in shi ba, ba kuma za ai ba, amma da ya mutu sile biyar bai tafi da ita ba,daga shi sai halinshi, yanzu kam arzikin da komai babu, da an turmusa ki kabarin ki k'yaun shi zai fara zag'wanye wa,karshe ki zama kasa abar takawa. "Kinga ba bu Alfari,babu Dukiya,babu k'yaun,yanzu kam sun zama kasa. "Toh ku fad'an, wanda zai zamu haka a gaba,meye nashi na tunkaho da wannan duniyar?? Kai ta girgiza.. "Malamai,wallahi you better seek ur "Jannah" sannan ku gode Allah da baiwar da ya muku, ta hanyar fad'in Alhamdulillah, ba wai ta gorantawa wanin shi ba,da nuna isa da fariya.. Shiru tai, jin sallamar Abba cikin gidan, tunda yaci ka'ro da motar AAA ya sanar shi su Momy ne jikin shi yai sanyi, sai d'ai daga shi har AAAn sun sha mamakin jin gidan t'sit sai tashin nasihar Fure cikin nut'suwa. A hankali ta tashi tai gun Abban d'uk suka bita da ido. Kayan hannunshi ta k'ar6a cikin girmamawa tana leka wa, sai ta dago da murmushi, "har kullum ina alfari da kasancewar Abban mu makanike mey ci da gumin shi, kun ganshi nan, a kullum cimarmu mai dad'i ce, dan ta Abba ba mai cin k'wananen abinci, burinshi ya samu ya kashe su kanmu, dan haka a kullum ya zama abin alfaharin mu,dan haka ne nake yaki da d'uk mai neman taka min shi... Jin kuka zai K'wace mata yasa da sauri ta lafe a gefen kafad'ar Abban,d'uk sai ya kara kaunar Furenshi, tabbas sun cika yara na halali,masu takama dashi a d'uk yadda yake.. Tashi Maryam tai tana goge hawaye tai gun su Abban,d'uk sai ya hau lallashin su.. Ba zata suka t'sinkayi muryar Ya Suleiman. By Feenat Ja'afar. [5/18, 12:31 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 56_"Yanzu kam komai ya kare ai.. Dan haka ku tashi tun da guntun mutuncinku Hajiya ku tafi,d'uk din su ba wacce akai ma auren sadaqa.. Rayuwar y'anci muke yanzun, haka nake bid'ar ganin k'anne na ciki.. T'sit sukai ba mai mot'si cikin su, ciki ya karaso cikin bacin rai, da dan k'arfi yace "ku tashi nace koh?.. T'saki Rukayya tai, kan ta hau neman tashi, "Ga'iyar... Saukar mari taji yasa da sauri tai shiru ta zauna d'ai d'ai rike da gun,Momy ce. Hannu ta nuna ta dashi, "ka'r na kara jin bak'in cikin zancen wani anan... D'uk k'allonta suke cikin mamaki musamman Huwaila da Rukayya da Fure. "yanzu Momy akan wa'enan Mat's... Wani marin ta kara sakar mata,wanda ba shiri ta g'imtse baki tana shafa gun.. "Ki kiyaye ni,in ba zaku iya shiru ba ku tashi ku ban gu. Kamar masu jira da suka d'au jakukkuna sukai waje suna kunkuni. Ita d'ai Aunty Maryam ido ne nata, yayinda Aunty Jidda takaicin duniya ya isheta ganin abinda Momy tai,gashi tace bata yafe ba in ta tofa tun suna gida. Hawaye Abban ya goge ma su Fure kan ya juya ya koma yana mai kiran Ya Suleiman, fatan shi a wanye lafiya. Tashi Momyn tai tazo inda su Fure suke, ido kawai Fure ta zuba mata, Maryam kam kai ta k'auda, dan Allah yaga taki jinin Momy. Hannu ta daga zuwa fuskar Fure dake hawaye, da sauri ta rint'se ido tana mai jiran saukar mari a kuncinta,yayinda da sauri AAA ya ju ya baya shima ya rufe ido.. Sai d'ai har wani lokaci bai ji saukar mari ba,hakan yasa ya d'an ju ya. Abinda ya gani ne ya sashi juyowa gaba d'aya, Momy ke sa hannu tana goge ma Fure hawayen fuskarta tare da girgiza mata kai halamar ta d'aina kuka, da sauri ya sau ajiyar zuciya tare da washe baki yana murmushi. Kan Maryam ta koma wacce ta zumburo baki tai gefe da kai... "Kuyi hakuri kunji ya'yan nan.. Takanas nazo bikonku ku koma... Nasan ba ku samu yadda ya dace ba a zamanku na baya ba gun mu.. Ban rike ku sirikai ba sam, amma ku kun rike ni uwa... Shiru tai tana k'allon su,wanda su ma k'allonta suke baki sake, wai Momy ke basu hakuri? Kuma cikin sanyin murya? Ido Fure ta ka'rkad'a, tana fatan in mafarki ne ma lalle ta wat'sake... Tamkar Momy tasan tunaninta ta ruko hannunsu tana murmushi suka zauna. Chan ta nisa ta fara magana,"Furera... Ido Fure ta rint'se, a ka'ron farko da Momy ta ta6a kiran sunanta.. Hakuri ta fara basu dasu Umma cikin nuna nadamar abinda tai musu,da alkawarin ba maimaici InshaAllah. Tun suna ganin abin kamar da wasa har suka ware da yardar lalle Momy tai nadama,sai rarrashin Hussein take dake kuka tana fad'in "wannan na Umman ku ne, nawa mai gidan gashi nan.. Tana nuna Hassain, kamar mai jira shima ya kama kuka,baki sake tace "au,au,kaima hakan take? Banda murmushin jin dad'i ba abinda Fure ke yi, a hankali ta daga kai ta k'alli gun da AAA yake,shima idonshi akanta yake,tuni ta hau mishi godiya cikin yaran su nasu kadai da kurmanci, ido ya lumshe mata halamun ya ji dad'i.. Sai ta kawar da fuska tana murmushi. Tasan wannan aikin na AAAn tane, a karshe yai nasarar gashi har gidan Momy tazo wai bikon sun a zahiri ba mafarki ba,tuni ta kara jinjina wa hakuri. Ai Aunty Jidda tuni ta bi bayan su Huwaila, dan a ganinta Momy ta ma gama badasu gun su Fure, gashi Fure ta sha da ita ba damar magana,sai Taxi suka hau dan da motar AAA kad'ai da Aunty Maryam suka zo, ita kam Rukayya gida ta wuce tana tunanin yadda yau Momy ta mata,kai ta girgiza.. Su zuba toh. Har dare Momy tana gidan ita da AAA, Aunty Maryam ta tafi, sai ga nan Momy tana zukulkular tuwan hatsi miyar d'any'ar ku6ewa tana santi.. Har ta kasa shiru sai da ta tofa. Shi dai AAA bak'in nan kamar gonar audiga dan murna, yasha mafarkin ranar nan sai yau tazo da ikon Allah, fatan shi Allah sa su Aunty Jidda ma su gane. Ba karamin farin ciki Abba yai ba da jin zuwan Momyn,ganin yadda AAAn shi ke farin ciki yasan yau Maryam ta wanke laifinta, hakan yasa Washegari da kanshi ya shirya dan zuwa har gida kara bada hakuri, abinda bai ta6a ba sai kansu Fure. Lokacin Abba ya dawo suna a t'sakar gida kamar kullum Familyn g'wanin ban sha'awa AAA yai sallama. Jin da wa yake tafe yasa su tashi zuwa neman mayafi, da t'sabar kunya shima Abba suka gaisa,dan bai ta6a tunanin zuwa domin gaisuwa ma sirikin nashi ba koh a hanya, asalima shi bai san waye Abban su Fure ba koh a hanya, sai d'ai da mamakin shi yaga Muhammad ne ma, cikin mamaki yake k'allon Abban,shikam murmushi kawai yake. "Wai da gaske ne koh ido na ne Muhammad? Murmushi Abban yai mishi, sai Abban su AAA yace ma Ahmad d'in "lalle ka lalubo zumuncin da Baba na, dama su Furera yaran ka ne? Ikon Allah, gaskiya har naji kunya, nasan da Nasir na raye da yau zan d'au query, shi d'ai Abba murmushi kawai yake. "Ke nan kai ka gane ni Muhammad, kai ya k'ada yace "sosai ma Yaya,tun a auran Furera na gano dangin Nasir ne ke nema, toh a gun d'aurin aure na gano ashe ma kaine Abban Ahmad. Abba yace "ikon Allah, amma baka k'yauta ba Muhammad, sosai Hajiya tai k'ewar ka har ta bar duniya.... Shi d'ai AAA an sashi t'sakiya, ya k'alli Abban su ya k'alli Abban su Fure, da halama yana neman karin bayanin a fiddashi duhu. By Feenat Ja'afar. 庐NWA. 9/29/16, 3:05 AM - Queen Safiyyert馃憫: [5/18, 11:45 PM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 57_Irin firar da sukai ne ya gane sun jima da sanin juna,koh dan yanayin yadda kowa ke tambayar bayan rabuwa. A mota d'ai AAA ya kasa hakuru yai tambaya, cikin murmushi Abba ya sanarshi ai sun san juna da Abban su Fure da jumawa tun zamanin jami'a, a dalilin k'aninshi Nasir sukai sabo sosai,d'uk da ba t'saran shi bane. "Sosai sunyi abota da kawunka,wanda har ya zamana Hajiya ta d'aukaki Muh'd d'in, dake shi Nasir ba mai nisan k'wana bane tun bayanan ban kara ganinshi ba... Kai ya jinjina, yana mai farin cikin wannan rana da jiya,burinshi Furii ta dawo mishi dan zaryar nan d'aurewa kawai yake, amma da kunya. Tuni Abba ya dawo ma su Momy komansu harda karin kud'i a (account), har sashen Mama Momy taje dan jin shawarar irin kayan da za ai ma Fure na suna, dan fa fur tace sai ansha shagali kamar na kowa, sosai Maman tai murna,har ta kasa 6oye wa. Aunty A'i Momy ta bama k'wanigilar had'a kayan goyon Furen, tuni kuwa ta hau 6adda kud'i tana narko ma (Babies) da Furen kaya na azo a ga. Sosai sunyi rawar gani,dan naira ta ci kasa. Baki kawai su Umma suka zira lokacin da kaya ya iso musu, tabbas gidan su AAA sunyi wuta. Haddadiyar walima suka had'a a harabar gidan su AAA, su Fatee kan gaba Wai dan ma ciki yai yawa. Lalle ne bayan wuya sai dad'i, ga nan Fure sai ji da ita da yaranta suke,ita kam bata cewa komai sai godiya ga Allah. D'uk da su Aunty Jidda su basu yadda makaman yakin nasu ba a kanta,amma sosai ta sarara,dan fur Momy ta toshe d'uk wata kofar da zasu muzgunawa Fure, ga kuma tsoron ka'r Abba ya kara k'wata musu ta da. Tuni Maryam ta koma, amma gida daban Muh'd ya sa ta,yanzu kan ita da Hassana sai gani daga nesa. Lokacin arba'in d'in su Fatee ta juye nata, sai abin ya zama biyu,ga shirin komawa gidan AAA,ga jelar gidan Fatee. Tuni likafa ta hau,yanzun kam kowa a dangin Salman nanike mata yake son yi, sai d'ai ita tace ina, wai takai-takai. Huwaila d'ai aure yaki dad'i, dan fur Miji ya juya baya shi sai amarya, wai ta zama chus,ga gida d'aya ya gamasu da kishiyar, da ta hau mata fallin amarci take tada hauka, a haka har ta k'wata ya jibgeta had'i da saki ya kuma bar kasar. Da wannan Momy ta kara tir da wani auren mai kud'in. Yanzu kam Rukayya ita aka sa gaba, dan tuni lakabinta gun su Aunty Jidda ta fara amsa sunan JUYA... Ga kishiya mai dan uban isa da gadara, ita a dole jinin sarauta, ita ke da (remote) a hannu sai yadda tace ai ake yi, da ta nemi yi mata rashin kunya zai taka mata burki,dan fa wai yana ji da Matarshi tamkar t'soka d'aya cikin miya... Ga sharadin Babanta na in ta kaso aurenta toh kar ta tunkari gidanshi, ga Momy tun daga abin Fure da tai mata zuciya itama Momy ta nuna kamar ba ai ruwanta ba.. Tun Rukayya ta shiga t'saka mai wuya, ko ina ba dad'i, ga yaran gidan kadai sun isheta hawan jini, rayuwar dai sai a slow gun Rukayya. Ita kam Aunty Jidda tuni karan nan Abba ya bud'e mata wuta kan sai ta koma gidan mijinta,tunda yace shi bai Saki ba. Karshe tana ji tana gani ta koma gidan da tai rantsuwar ba komai cikin shi.. Wanda a zahiri jarabar uwar mijin su yasa taki auren fur,dan sosai take wanke ta ciki da bai d'uk wai ta cika musu gida ga ba wani fus,.. Amma dake Dan Adam ce ita wai har take huce takaicinta kan wata. ********************** K'wance take cikin d'aki gaba d'aya yau jinta take wani iri, dak'yar ta samu ta lalla6a su Hussein ta basu ball kan su fita sui wasa zata huta. Tana t'saka da bacci ta zabura har tana shirin fad'o wa a gadon, jiri take ji,ganan kuma karar zubar abu,wanda tasan babu tantama daga kitchen ne aka zubo mata (plates) suka fashe. Kawai sai tasa kuka tana mai dan buga gado ba koh hawaye, kai da gani kasan kukan 6aci ne, yara tamkar beraye kullum cikin 6arna suke mata... By Feenat Ja'afar. [5/19, 12:50 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 58_Parlourn tai dank'wali a hannu tana sakar ma su Hassain harara,tuni suka fara raba ido ya 6era a buta.. Hussein da ke a bak'in kitchen rike da ball yace "momma hakuli... Harara ta kara mishi rike da k'ugu, kan tace "mey ya kai ku kitchen? K'allo Hassan yai sai ya k'allo Furen.. Cikin maganar yara suka ce ai ita tace su je sui ball,shine suna ball ta fad'a kitchen ta bigi farantin kofuna.. Kai ta dafe tare da fad'in "oh Allah,, wato g'wari- g'wari kullum zan ta muku kan ku gane ummm? Parlour ne waje? Kai suka k'ada mata. Sai ta fara dube tana "yau zan zane ku son rai ba mai k'watar ku... tuni suka fara t'sula mata ihu ganin ta zari tsinken k'wak'wa suna kiran Daddy... Zagaye suka fara ta ma kasa kama su, bak'in nan kuwa yaki mutuwa da ihu tamkar ma d'ukan nasu take. Shigowarshi kenan ya fara jiyo ihun yaran, ko karasa cire mukullin mota bai ba yai cikin gidan... Ina,ai tuni sun galabaitar da ita dan shegen ziliyarsu, kasa tai tana haki tana nuna su bulalar hannunta.. Da d'an gudugudun shi ya shigo, ai suna ganinshi suka runtuma gunshi suna nuna mishi Furen, ganin bulalar hannunta yasa ya fara daga rigunansu ya ga koh ta dake sun. Shiru kakeji sun bar ihun,tuni ya hau fad'a yana ta kiyaye shi kan dukan yaranshi, dan takaici kawai sai ta sa mishi kukan shag'wa6a, harda buga hannu kan (carpet), tamkar yarinya ta koma mishi, sai ya sau baki yana k'allon borin nata,suma su Hussein k'allonta suke d'uk sunyi narai narai da ido. Bai nufa ba ya ji sun sa mishi suma kukan, sai sukai gun Momman d'aya na girgiza mata kai halamar tai shiru sun d'aina, d'aya na goge mata idon da ba koh hawaye. Kawai sai ya harde hannu yana k'allon su. Shiru tai tai tana k'allon su,jin yadda suke ta fadin sun d'aina, cikin shag'wa6a tace "promise? Da sauri suka k'ada kai, sai tai murmushi tare da janyo su.. Tuni kuma aka hau dariya jin chakulkulin da take musu. Kai AAAn ya k'ada yana musu murmushi ya juya kashe mota. Yasan 6arna kenan sukai mata. A kitchen ya t'saya jin hayaniyar su,k'washe fasassun kufunan take tana su mat'sa kar su taka. Kiran su yai suka fita,tuni ya had'a kowa da t'sarabar shi suna t'sallen murna yace su je gun Baba mai gadi kan ya fito suje gun Hasna,da murna suka fita shi kuma yai d'aki. Jin an bud'e d'akin yasa ya k'alli kofar,rufe wa tai kan ta jingina kanta a jiki tana K'allonshi, d'uk ta marairaice mishi fuska halamar ya agaza mata. Rigar da ya cire ya ajiye kan ya tako gunta cikin lallashi, a gefen gado ya zaunar su tai lamo jikinshi. ("My Furii what's wrong?) Uhnmm?.. Cikin marairaita ta hau ta6e baki kamar zatai kuka,tuni ya hau lallashi tamkar Hasna ke gabanshi, rad'a ya fara mata yana ka'r ta sare man tun a su Hussein... Kai ta k'ada, tasan bazai gane ba ne, amma tun yanzun har ta fara galabaita da cikin tun kan yai k'wari. Lallashi yai ta yi kan ta gode Allah da k'yautar da ya kara mata, ka'r ta sare tun yanzun.. Kai ta k'ada, "hutu nake so fa Daddyn su, yaran nan sunki su barni, ni kam a kaisu Allo private ta tun safe sai yamma koh na huta da kiriniyar su Hussein... Dariya yai, kan a hankali ya k'wantarta ya g'yara mata pillow, har da ja mata bargo. Kanta ya shafo yana mai bata (favorite)nata cikin nut'suwa.. Tuni har ta fara lumshe ido da jin dad'in sautin abin. Jin tai shiru yasa yai tunanin tai bacci ne, cikin nut'suwa ya duk'o ya dan bata (peck) tare da g'yara mata bargo. Kayanshi ya d'auka cikin sanda ya bud'e kofar dan gudun kar ya tada ta yai dakinta dan wanka. Da k'allo ta bi bayanshi ganin yadda yake jan kofar a hankali, sai tai murmushi. By Feenat Ja'afar. [5/19, 7:09 AM] Feenat Ja'afar: "JUYA" 漏 Feenat Ja'afar. 59_Hannu takai kan cikinta tana mai shafawa, tabbas bazatai butulci da Allah ba dan ya bata ciki a kusa,ai ma ta raka, tunda su Hasna sun kusa shekara uku,tasan yasan zata iya ne ya bata, fatan ta su rabu lafiya.. A hankali tai bacci cike da kaunar gidan ta da mai gidan. Basu suka dawo ba sai kusan taran dare,da kaya niki-niki. Tana zaune kuma d'uk sai kewarsu ta dameta, sai maka mishi kira take kan su dawo ta huta,murmushi yai,dan suma Hasna ta mat'sa mishi da fad'in Momman ta. Da sauri ta tafi gunta kuwa tana mata oyoyo, kanta ta shafa da yasha (twists-stick) tana mata sannu da zuwa.. Ita kam batta da k'warafniyar su Hussein. *********************** Rayuwar na ta kaima Fure,ta haihu lafiya su Hussein sunyi k'ani, zo kaga k'walo kusa da baby,wai nan d'uk murna suke.. Kawai sai ta tasasu gaba tana k'allo cikin murmushi, AAA na d'aura ma Hasna babyn suna dariya.. Wai yau ita ke da yara hudu a rayuwa??.. Tuni ta fad'a duniyar tunanin da,har AAAn ya kula da ita. K'allonta shima ya hau yi,bai san karan nan da mey zai sakama Furiin shi ba? Ya d'ai san a chan kasan ranshi kaunarta kad'ai ke kara nunkuwa da k'yawawan yaranshi da take sum6ulo mishi, abin sai d'ai godiya ga Allah kawai. K'wanan su d'aya aka sallame su,tuni gida ya debi su Fatee da nata bataliyar uku,yanzu kam zumunci ya kara yawa har sun zama y'an uwan juna. Ita kam Fure bata cewa komai ga Allanta sai godiya a kullum, ga bud'I da take samu gun abincinta, har yau tana nan da bama su (special dishes) d'inta. Yanzu kowa mutuntata koh dan tsoron Momy da Abba dake bala'in ji da ita da iyalanta, ga kuma yadda ita kanta ta bunkasa ta zama hajiyar kanta. Sai gani sai kuma harara daga nesa, dan yanzu bata ragarma uban kowa t'sakanin su Huwaila, take suna fad'a mata d'aci zata basu mad'aci. Sai ya zamo suna shakkar fad'a a gabanta. Sunzo barka har gida suna d'an y'atsinar nan da ta zame musu tamkar dole, aciki suke mata barkar, ita kam Rukayya ji take kamar ta d'auke babyn, d'uk tai laushi. Tashi tai tana sanarsu zata shiga wanka dan tun dazun aka kai mata ruwa. Kai kawai suka daga mata. Ta gama cire kaya zatai wanka ta jiyo maganar su kasa-kasa. "Wa ya ga kaza uwar ya'ya.. Ina ga kan a shekara goma sai ta had'a ma AAA garke.. Cewar Huwaila. Tana jiyo Aunty Jidda na fad'in "su d'ai suka sani, ke meye naki? Dariya Furen tai, tare da fad'in. "Toh fa! "From fan to fire" daga ''JUYA'' na zama "K'aza" uwar ya'ya? Murmushi tai tare da k'ada kai, D'an Adam sai ka barshi, amma sam baya godiyar Allah sai kalilan daga cikin su, w'ankanta ta fara tana jinjina halin Mutum,lalle ne in ta biye ta mutum toh itama sai an kaita an baro. Bata haihu ba an kirata da JUYA.. Ka haihu ance maka Kaza uwar ya'ya. Mutum! Mutum!!, ba mai iya mishi sai Allahn shi kad'ai.... ALHAMDULILLAH. Na gode Allah da yasa naga karshen wannan littafi (JUYA),Ubangi ya sa mu amfana da darrusan da ya koyar mana ciki. Never loss hope,and trust in the power of du'as, InshaAllah Allah will grant you everything you wants as long as it is good for you... In har kaga baka samu ba,toh ka d'auka babu alkairi acikin rayuwar ka kai da abin... Dan With God,everything is possible... MashaAllah... Nafisa Bashir Tanko (Feenat Ja'afar) ke muku fatan alkairi... Muyi Ramadan lafiya, tare da muku albishir na barka da sallah Novel d'in gaba,mai suna.... "A BAK'IN AUREN KI"... Love you all.... By Feenat Ja'afar. 庐NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.. (NWA). Feenat.mywapblog.com