*AMEERA DA ADAM* _*( By S-REZA✍️)*_ *(Writer of Uwata ce cela. Meera & Nusee* ) _Sadaukarwa ga marubuciyar arziƙi. Yau na cika alƙawarin da na ɗauka. Wannan page ɗin naki ne ke ɗaya (Kahdija Candy)_ *Bismillahi Rahamanin Rahim!* *PAGE 1️⃣* Ƙarar homm ɗin mutar da ta ƙara ji a karo na babu adadi ne ya sa ta bar naiman abun da da take yi ta nufo hanyar waje har ta na haɗawa da sassarfa. Zaune ta same shi a cikin motar ya na kallon hanyar fitowa da ga cikin gidan ya cika ya yi fam kamar zai fashe. Fuskarsa ta ƙara kalla a karo na biyu taga yanda ya haɗa rai kaman haɗuwar gaggarumin hadari a cikin watan ogosta. Da sauri ta buɗe ƙofar mai zaman banza ta shiga tana cigaba da satar kallonsa. "I'm sorry honey wayata na ke ta naima tun ɗazu bansan inda na jefata ba ne shi yasa na daɗe. Ameera ta faɗa ta na gyara zamanta a cikin motar. Ko kallonta bai yi ba yaja mota mai gadi ya buɗe musu get suka ɗauki hanya. Har suka iso babban asbintin babu wanda ya ƙara magana acikinsu. Kallonta ya yi a karon farko tun bayan shigarta cikin motar ya ce "Shiga ki fito ina jiranki idan kinje ki tsaya naiman wayarki karki fito da wuri.Ya faɗa ya na kawar da kansa daga gareta ganin ta kafeshi da banyan idanunta. Kallonsa ta yi ganin har yanzu fuskarsa a haɗe ta ke da ga ɗan abun da ya faru. "Wai wannan haɗe fuskar na meye dan Allah? Na baka uzuri nafa, please dan Allah muje tare wallhi ni kunya zuwa ni ɗaya nake yi please honey. Ta faɗa ta na kamo hannun angon nata cikin shagwaɓe murya. Kallonta ya yi ganin yanda ta ƙara haske ga y'ar rama da yagani a jikinta. Sosai ya ke lura da yanayinta kwana biyu ganin duk ta canja, hakan ne ya sa ya ce dole sai sunzo asibiti domin yanayin nata ya na bashi mamaki. Yana son matarsa sosai kaman yadda yasan itama tana sonsa, sai dai ya lura saboda zuwa asbintin nan da bata so ne yasa take son ɓata masa rai! Badan shine ya matsu da zuwa asbintin nan ba da ba zai shiga ciki ba. Kuma yasan tunda har ta fara haka tofa ko ya barta ita kaɗai ba zuwa zatayi ba. "Fito muje" shine abun da ya ce ya na cire hannunta a jikinsa sannan ya fita itama ta fito suka jera izuwa cikin asbintin. Kasancewar likitan abokinsane ya sa tun kafin su isa cikin asbintin ya kirasa ya na sanar da shi isowarsu. Koda suka isa gaban likitan bayan sun gaisa Adam ya fara masa maganar abun da ya kawo su. "Ta yi fari ga wani irin taurin kai da takeyi yanzu ga rama idan na tambayeta ta ce wai ita lafiya ta ke, abun da yafi bani mamaki ma shine yanzu abu kad'an za'a mata ta fara masifa, ƙunci kamar ba itaba, to tun ba yau ba nake mata maganar muzu asibiti taƙi, sai yanzu na samu ta yarda, inaso a dubata idan ma ta kama gado za'a bamu to. Likitan yayi dariya ya na faɗin babu batun bada gado in sha Allah abun arziƙi ne. Koda likitan ya sa tayi fitsari domin ya gwada ko ciki ne gareta domin abun da ya fara zuwar masa kenan lokacin da ya haɗa ido da ita. Ita kuwa Ameera tashi ta yi ta nufi toilet ɗin dake cikin ofecc ɗin domin kuwo fitsarin. Gwajin farko ya nuna tana ɗauki da ciki. Tsabar murna Adam bai san lokacin da ya rungume likintan ba. Ita kanta Ameera abun yazo mata a bazata domin bata taɓa kawo ciki gareta ba. Sosai farincikin ta ya fito fili ta na kallon Adam kamar wanda ya fita daga haiyacinsa tsabar farin ciki. Kamota yayi a gaban likitan ya fara surfa mata addu'a ya na shafa cikin kamar ya samu kan motarsa. Sosai yake cikin farin ciki kana ganinsa zaka gane hakan. Riƙo hannuta ya yi suka fito bayan likitan ya gama sanar dasu yanda zasu kula da cikin ɗan wata guda, harda sanar da Adam cewa har yanzu cikin bai bar lokacin laulayi ba sai yayi haƙuri . Adam kuwa ji yake ba ma laulayi ba koma me ye zai jure a kan wannan cikin. A cikin motama dai da hannu ɗaya yake tuƙi hannu ɗaya kuma ya rike hannunta kamar wacce zata gudu. Saida suka tsaya suka sayi magani kafin suka wuce gida. Suna isa gida ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ta na jinta kamar wata sarauniya, ga mukuma yanayin ƙuncin da take yawan tsintar kanta a cikin kwana biyun nan. Haka ya rike hannunta suna tafiya a hankali har suka isa cikin ƙaton falon nasu. Zaunar da ita ya yi a kan kujera sannan ya nufi kicin ya ɗauko rowa mai sanyi ya buɗe ya kafa mata tana sha ya na kallon yanda ruwan ke shigewa ta maƙogaronta, yana ji a ransa yanzu wannan ruwan zai dangana ga yaronsa dake wannan cikin, sosai murmushi ya samu mahalli a kan fuskarsa. Bayan ta gama sha ya zauna kusa da ita ya ce "Jikina yana faɗa mini ba lafiya kike ba ashe dai rabone mai girma a tere da ke. Dariya ta yi tana jin barci na son kamata. Wayarsa ya ciro ya fara kiran ƙanwarsa kasancewar mahaifiyarsu ta rasu daga shi sai ƙanwar tasa ka ɗai suka rage, mahaifinsu kuwa tun ƙanwar tasa na ƙarama ya rasu. Ta na ɗagawa ya ce "Kadija albishirin ki? "Goro fari tas-tas" ta faɗa cike da zumud'in son jin mai yayan nata zai ce mata domin tasan da jin haka to abune mai daɗi. " Ameera na dau'ke da ciki har na wata guda. Da ƙkarfi kadija ta kwaɗa wani uban ihu ta na cewa "Da gaske Yaya? Bai ko bata amsa ba ya kashe wayar yana kallon Ameera da har barci ya fara tafiya da ita. Afili ya ce "A she ba a banza ba wannan saurin fushin naki da kikeyi na kwana biyu. Ganin haka yasa ya ɗauketa gaba ɗaya ya nufi kicin ɗaki da ita ya kwantar da ita sannan ya fita yana mai ci gaba da kiran ƴan uwa da abokan arziƙi. Da misalin ƙarfe biyar na yamma Amerra ta faraka, ko da ta farka sai ta farka da wani irin ciwon kai, ga kuma wani ɓacin rai da mai barci ke tashi da shi musamman barcin yamma. Ta na fitowa falo ta ganshi sanye da kananan kaya na adides masu ruwa kore sosai kayan suka zauna a jikinsa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki, ga kuma falon wani ƙamshine ke tashi shima dai a'lamar ya gyara ko ina. Ya na ganinta ya nufo gurin yana sakin murmushi haɗi da kiran sunanta. "Honey kin tashi? Muje ki yi wanka kafin a fara kiran salla saura kaɗan na gama abinci, ina fatan barccin ya isheki ko? Tun lokacin da ya fara magana take jin ɓacinran da ta tashi dashi yana ƙaruwa, haka kawai taji bata son yin mgn, sosai take daurewa karta ce komai domin tasan ba magana mai daɗi zatayi ba, hakan ya sa ta kasa cewa komai sai yatsine fuska da takeyi. Shi kuwa ganin haka yasa ya nufota yana dariya. Bakinsa ya kai da niyar sakar mata kiss a kuncinta amma ta ja fuskarta ta na had'e fuskar harda tsartar da yawun bakita kamar wanda yayi mata kiss ɗin. Da mamaki Adam yake kallonta ganin abun da ta yi. "Lafiya kuwa kike honey? Ya faɗa ya na kallonta domin yasan abun da tafi so kenan a duk lokacin da zai fita daga gida ko idan ya dawo Koda ya dawo da ɓacin rai ne to ita zata masa, amma yanzu tun kafin yai mata tana kawar da kai. Bata ce komai ba ta nufi ɗakin ta domin ɗazu a ɗakinsa ya kwantar da ita, tana shiga ta faɗa toilet ta yi buroshe sannan ta yi wanka tana jin har lokacin ɓacin ran bai bar kantaba. Shikowa Adam uzuri ya yi mata ganin daga barci ta tashi gashi Kuma bata da lafiya. Sauri ya yi ya gama gyara komai kafin shima ya sake wanka sannan ya ɗaura alaula ya fito sanye da jallabiya. 'Dakinta ya nufa ganin bai ganta a Palo ba. Yana shiga ya ganta a kwance tana kallon sama ba barci take ba. Kallonta ya keyi yana jin tausayinta sosai ganin yanda ramarta ke sake fitowa fili. "Honey kiyi alaula kiyi salla kafin na dawo na yi mana girki mai daɗi yau na hutar dake Kuma...Tun kafin ya ƙarasa ta tsayar dashi domin ya kaita bango, shi bai san bata son yin magana bane. Cikin ɗan ɓacin rai ta ce "Dan Allah ya isa! ni nace maka yinwa nake ji ne? Fisabililahi kazo sai surutu kake mini wai kayi girki, to ni nasakaka, ko nace Adam kayi kirki ne, dan Allah kaje Kaci kayanka ni bama abinci zanci ba yau a ƙoshe nake. Ta na gama faɗa ta bar masa ɗakin ta fito Palo ta zauna tana jin wani haushi wanda bata san daga ina yake zuwa ba. Adam kuwa mutuwar tsaye ya yi ya saki baki da hanci yana kallonta har ta bar palon. Shi dai baiga abun da yayi ba, kuma Ameera da ko musu bata iya masa idan ya yi maga amma take masa irin wannan magana da ihu harda kiransa da Adam!. Shima fitowa yayi daga ɗakin domin an fara kiran sallah. Kallonta yayi ganin yanda ta haɗe rai ka rantse wani abu a kai mata. Ita kuwa ta na ganinsa ta kawar da kai ta tashi domin barin gurin. Adam kuwa bai karaya ba ya ce "Sorry honey nasan duk barcin yamma ne, dama ana magar cewar babu kyau barcin yamma, yanzu dai ki daure kiyi alaula kiyi sallah kinji. Kallonsa tayi tana jin magana a bakinta amma ta daure har ya fita daga gidan. Ba domin maganarsa ba itama ta nufi toilet ta ɗaura alaula ta fara gabatar da sallar la'asar (Asar) kafin ta fara gabatar da magrib. Tana idarwa ta koma ɗaki ta sake kwantawa domin wani sabon barcin take ji. Adam kuwa yana dawowa ya nufi kicin saida ya gama fitowa da komai kafin ya shiga ɗakinta domin kiranta suci abinci. Cikin mamaki yake kallonta ganin tayi shigar barci ta kwanta abunta harma barci ya fara mata nisa. Cikin kwantar da murya ya fara kiran sunanta haɗi da bubbuga mata gadon duk dan karya ɓata mata rai. "Honey honey honey hone..."Inna'ilai wa inna'ilaihi raju'un! Wannan wani irin masifane, yanzu dan Allah barcin ma bazaka barni nayi ba fisabililahi, wannan wani irin shiga haƙƙin mutum ne, ko ka manta zunubin da mutum yake samu idan ya tashi wani yana barcci ne, ni nace maka yau bazanci abinci ba, ko ana dole ne cin abincin. Cikin sanyi murya ya ce "Haba honey ya za'ayi ki kwanta bakici abinci ba Kuma gashi ba kya da lafiya, ai ko kaɗan kici sai kisha magani ko? "To wallhi bazanci ba idan kuma dolene sai naga wanda zai sakani na ci, na ce maka na ƙoshi-naƙoshi ko dolene. Ta ƙarasa tana fashewa da kukan takaici Kai ka rantse da Allah dukanta a kayi. Sosai take jin barcin kuma harga Allah bata jin yunwa hasalima bata son ganin kowa a kusa da ita, yanzu haka ji take kamar dukanta ya keyi. Shi kuwa Adam gurin yin gwaninta zai rarrasheta harda kamota zai kwantar da ita a jikinsa amma ta wani ƙwace jikinta ta miƙe tsaye ta ƙara fashewa da wani sabon kukan ta na kiran sunan Umma tana ihu! "Wai ni dolene sai mutum yaci abincin ne? na ce maka na ƙoshi-naƙoshi Kuma barci nake ji dan Allah ka rabu dani waiyoo Umma! Ta na faɗa ta yi waje tana cigaba da kukan kamar wacce a ka sanar mata cewar unman ce ta mutu. Shima bayan ta yabi yana kallon wani sabon salo daga wajan matar tasa. Wai to mai ya ke damunta ko dai har yanzu barcin yamman ne bai saketa ba. Ganin ta zauna a palon ne yasa ya ɗauko kulan abinci gaba ɗaya ya nufo gurin ta ya na faɗin "kinga ko cokali uku kikayi sai kisha magani ki kwanta in ba hakaba zakisha wahala kodan cikin dake jikinki please honey ki daure. Yana ajiye abincin Ameera da har yanzu bata daina kukanba ta ɗaga kulan abincin ta buga da ƙasa tayi booll da kulan ta na faɗin. "Idan ma wannan abincin na maitane to wallhi bazanci ba,ni barci nake ji na ce maka na koshi bazan ci ba. Ta na faɗa ta koma gurin daining tebul ɗin ta kwaso sauran abincin da abun sha da ya haɗa musu suma tayi watsi da su tana gamawa ta koma ɗaki tayi kwanciyarta abunta, cikin minti kaɗan barci yayi awun gaba da ita. Shiru Adam yayi yana kallon ta batare da ya hanta komai ba har ta maba zubar da komai na abincin, shi kan Adam izuwa yanzu yasan ba wai barcin yamma bane yasa ta wannan haukan, anya kuwa Ameera ƙalau take, daga yau ɗaya kawai ta canja daga Ameeran da yasani izuwa zuwa wata aba da ban. Shi yanzu damuwarsa rashin cin abinci da batayi ba ne, rabonta da cin wani abun tun rana kafin su fita asibiti. Haka ya zauna saida ya gyara ko ina da ta ɓata kafin ya shiga ɗakin ganin har tayi barci yasa ya ja mata bargo ya fita izuwa masallaci domin yin sallar isha. Zuciyarsa yana jin izuwa gobe in sha Allah zata daina wannan ƙuncin. Har ya dawo daga masallaci barci takeyi, yaso ya koma ɗakinsa ya kwanta amma yayi tunanin kar Kuma ta tashi cikin dare tana neman abinci. Hakan yasa ya kwanta yana buƙatarta amma yana tsoran masifa, haka ya kwanta yana ta tunanin kyautar da Ubangi yayi musu a wannan lokacin da suke buƙata, kaman ya rungumota amma ya haƙura har shima barci ya ɗaukeshi. Da asuba shine ya fara tashi tun kafin yayi mata magana motsin sa ya tasheta, domin dama wani lokaci ma ita ke tashin su sallar Asubahi. Ko kallonsa batayi ba ta shiga toilet ta ɗaura alaula Koda ta fito bata ganshi ba, ta hau kan dadduma ta tada sallah. Tana idarwa ta koma barci ba tare da ta cire hijab ɗin jikinta bama,ga yunwa ta na ji amma barci ya hanata tashi. Haka tana kwance har ya dawo. Ganin ko daddumar bata naɗe bane yasa ya naɗe yana kallon irin kwanciyar da tayi. "Good morning honey" ya faɗa yana hawa kan gadon domin komawa barcin. Jin shiru yasa ya kai kallonsa fuskarta ya ga ashe har ta koma barci. Da mamaki yake kallonta , iKon Allah wannan barcin dai anya kuwa na lafiya ne Ameera. Kasancewar safiyar litinin ce yasa bai so komawa barci ba amma baccin ya sa ce shi. Misalin karfe shida daidai na safe Ameera ta farka tana jin wata a zababbiyar yunwa kaman an mata sata a cikinta,ɓangare ɗaya kuma ga wani irin ƙunci da yafi na jiya da ta tashi da shi! Kallon gurin da yake kwance tayi sai taji bata son ganinsa a kwance, haka kawai taji barcin da yakeyi ɓata mata rai yake. Wayarsa ta ɗauko ta duba lokaci ganin shida saura yasa ta ajiye wayar ta na tunani. Tashi ta yi ta na kallonsa kamar ta rufeshi da duka ganin yana barci. Kicin ta shiga ta haɗa tii (shayi) mai kauri da zafi ta ɗauki kick ta fito falo ta zauna tana ci. Zumbur ta miƙe kamar wacce aka tsurkula ta shiga d'akin domin ita har yanzu barcin da yakeyi ya tsaya mata a rai haka kawai. Ta na shiga ta nufi gurin da yake, ta ɗauki filo ta fara buga masa ta na cewa "Malam ka tashi ka tafi aiki, ko wani Namiji yana gurin aiki amma kai sai barcin a sara kakeyi tun jiya dadadare kake barci kamar wani mace malam wallahi sai ka tashi ka tafi aiki, yana ƙokarin tashi amma taƙi ba shi damar hakan sai cigaba da buga masa fulo takeyi. Shi kuwa Adam cikin barci yaji ana dukansa yana son tashi amma sai ƙara danneshi a keyi Kuma ba'a daina dukansa ba. Da ƙyar ya iya tashi zaune yana kallonta sai ajiyar zuciya takeyi kamar wacce tayi gudu. Sosai yake kallonta ganin ta kafeshi da ido tana jiran yace wani abu. Wayarsa ya lalubo ya duba lokaci ganin shida da minti biyu ne yasa ya d'ago kai ya kalleta ya ce "Yanzu ƙarfe shida shine kike cewa kowani Namijin arziƙi yana gurin aiki? Ƙarfe shida fa Ameera? wai lafiya kike kuwa. Cikin masifa dake cinta ta fara magana bilhaƙƙi da gaskiyarta "Eh wallahi sai ka tashi, wani irin barcine haka tun dare har yanzu ana yinsa sai kace barcin a sara, ni dai wallhi sai ka tashi ka tafi aiki yanzu nake so kuma. Adam ya ce "Wai honey me ke damunki ne, yanzu ko mai gadin gurin aikin namu bai tashi ba amma ni zan tafi gurin aiki, Ko wanka banyi ba banci abinciba haka kikeso na tafi gurin aikin? "Su sauran ma'aikatan an faɗa maka abinci sukeci suke zuwa? ko wankanma dolene sai kayi, Malam wallahi ka tashi ka fita dun kafin raina ya ƙara baci. Cikin karaya ya ce "To kisamamin wani abun kafin nayi wanka. "Babu abunda zan girka kuma bazakayi wankan ba,ni dai kawai kabar gidan koma ina zakaje kaje bana son ganinka ne a gidan gaba ɗaya. Haka Adam ya miƙe ya ɗauki doguwar rigarsa ya saka, ita Kuma ta na biye dashi a baya riƙe da filo ta na cigaba da maganganu "Ni bana son Namiji rago kullum barci-barci sai kace mace, kawai ka fita gurin aiki. Sai da ta kaishi har ƙofar falon fita kafin ya ce "Kinci abincin ne ke? Cikin tsiwa da matsuwa da ganin yabar gidan ta ce "Ina ruwanka da naci ko banci ba. Tana faɗa ta tura shi waje ta rufe gidan tana Jan tsaki. Tsaye Adam yayi a waje daga shi sai doguwar riga sai yanzu ya kula da ko takalmi ma babu a ƙafarsa wayarsa ma a ciki ya baro ta, afili ya ce "Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un! Wai me ke damun honey ne, anya kuwa ba sauyamin ita a kayi a asibiti ba, to idan ba haka ba menene matsalar daga jiya zuwa yau na kasa sakewa a gidana babu damar nayi gwaninta. Ya na laluba aljihunsa yaji babu makullin mota, sannan babu ko sisi da zai hau mashi izuwa gidan ƙkanwar sa, kasancewar babban abokinsa take aure. Ko da yazo mai gadi barci yake yi abunshi haka ya buɗe get ɗin ya fita yana kallon titin tsit sai ɗai-ɗaikun mutane masu tafiya a ƙasa. Sai da ya daɗe kafin ya samu mai mashi ya hau izuwa gidan su Najib. Koda suka isa ya tsaya a bakin get d'in gidan yana bugawa, amma sun kai minti biyar babu wanda ya amsa harma mai mashin ɗin ya fara magana, suna cikin haka mai gadi ya buɗe get ɗin da masifar katse masa barci da a kayi, domin yasan dai masu gidan suna ciki. Amma ganin Adam yasa ya saki fara'a yana masa barka da safiya. Cikin jin kunyar ganinsa a haka da mai gadin yayi ya ce "Kamin mgn da Najib yanzu please. Ko da Najib yaji cewar Adam ne da sauri ya fito yana mamakin zuwansa da sassafennan dama jiya kadija ke sanar masa da cewar Ameera tanada ciki kodai ba lafiya bane. Kafin Najib yace komai Adam ya ce "Please sallami mai mashin ɗin nan yana faɗa ya shige gidan ya bar Najib da mamaki ganinsa a birkice. Ameera kuwa bayan fitan Adam palo ta koma ta zauna ta ɗauki shayinta ta fara sha, jin yayi sanyi yasa ta koma kicin ɗin, ta ƙara haɗa wani, zata ɗauki keck amma taga ya ƙare, ita kaɗai sai kumbure-kumbure takeyi, tana jin haushin komai ma shi kanshi gurin da a ke ajiye Keck ɗin ganin babu saida ta rufe gurin da ƙarfi har yana tsagewa. Firiza ta buɗe ko zata samu super commando domin shine drink dinta shima ganin babu yasa ta ture firiza ɗin da ƙarfi har yana faɗuwa ko ta kansa bata biba ta duba bredi shi Kuma taga saura kaɗan Kuma ya d'an bushe hakan yasa tayi wurgi dashi ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta nufo gurin mai gadi. Tsabar masifa na cinta ma ko sallama bata yi ba ta fara buga ƙofar ɗakin kamar ɗakin ne yayi mata laifi. "Baba mai gad...Baba mai gadi!... Da sauri baba mai gadi ya fito yana amsawa domin ya gane muryarta. "Na'am hajiya lafiya dai ko? "Saboda nazo kiranka shine kake tambayar lafiya? Ok idan da lafiya ban isa kiranka ba kenan ko? Na ce ban isa kiranka ba kenan ko? Jin yayi shiru yasa ta harareshi sannan ta ce "Aikenka zanyi kuma saura kamin shirme kuma wallahi ka dawo yanzu! Tabna faɗa ta jefa masa dubu ɗaya ta ce "Abu mai laushi zaka sayomin yanzunan karka ɓata mini lokaci. Ta na faɗa ta juya ta fara tafiya ta bar baba mai gadi da buɗe bakin ganin sabon lamari daga matar gidan nasu. Matar da ko ɗaga ido ta kalleshi bata yi, bare har tai masa ihu barema aike, shi dai tun da yake a gidannan bata taɓa zuwa ta aikeshi ba, wani lokacin dai Adam ke turota ta ce inji Adam ka sayo abu kaza. Ganin zata shige be kuma gane aiken ba ne ya ce "Hajiya wani abune mai laushi bansan wanda zan sayoba? Tun daga gurin da take ta nufoshi cikin masifa kai ka rantse zaginta yayi, har tana haɗawa da gudu ta iso gurinsa ta ce "Kai baka da ilimi ne baka san abu mai laushi ba har sai ka tambaya to kaje ka sayo goriba ko rake tunda baka da lissafi, yanzu abu mai laushi har sai an faɗa maka in banda samun guri, to wallhi kaje ka sayo min yanzu ina jiranka. Ta na faɗa ta juya fuuu ta nufi ciki ta bar baba mai gadi tsaye yana juya kuɗin yana nazari to meye abu mai laushi! Kuma da sassafe haka, anya kuwa hajiya lafiya taka. Haka dai ya fita badan yasan me zai sayo ɗin ba. Ita kuwa Ameera bayan ta koma ta nufi gurin da firizan da tafaɗar tana son ta ɗaga amma ta kasa, tati-tayi amma ko motsashi ta kasa, haka ta dawo ta zauna tana jiran baba mai gadi domin taga mai zai kawo mata, domin ita kanta bata san me takeson ci ba, ita dai tasan Abu mai laushi take marmari, idan da za'a yankata bata san me take son ci ba, kuma bata son cin bredi hakan yasa bata ce masa bredi ba. Najib da kadija cikin mamaki suke tambayar Adam lafiya dai yazo a haka. Cikin rashin sanin abun yi ya ce "Wallahi babu lafiya gidana tun jiya ba lafiya. Da sauri kadija ta ce "Mai ya samu Ameera ɗin Yaya? Wani abun ne ya samu cikin nata? Shi Adam har ga Allah harma ya manta da cewar cikene gareta. Cikin su'butar baki ya ce "Au wai dama ciki gare ta? Da mamaki Najib da kadija suka Kalli juna jin abun da ya ce. "Yaya ina ce kai da kanka jiya ka kirani kace Ameera nada ciki ko dama tsokana ta ka keyi? Kallonsu yayi ganin sun kafeshi da ido sai ya sunkuyarda kai ya ce "Eh gaskene kawai sha'afa na yi. "Ban gane ka sha'afa ne ba, wai wani abu ne yake faruwa ka fito ko takalmi babu ga shi ko kayan arziƙi babu a jikin ka, yanzu kuma wai kace ka sha'afa ne lafiya kuwa? Najib ya faɗa yana ƙara nazarin abokin nasa. Cikin murya tausayi Adam ya fara cewa "Wallhi tun jiya da muka dawo daga asibiti Amerra ta sauya, dana tun kafin jiyan ta zama abu kaɗan fushi da masifa, to daga jiya kuma abun ya ƙaru komai nayi masifa, idan nace taci abinci masifa,idan na tasheta a barci faɗa, yanzu haka itace tace wai na tashi na tafi gurin aiki, nace mata lokaci baiyi ba wai wallhi sai na fita, ta barni na sake kaya ko naci abinci ma wallhi taƙi, harfa waje ta rakoni tana dukana da filo. Ya ƙarasa kamar zaiyi kuka. Dariya kadija ta yi tana cewa "IKon Allah ita Ameeran ce harda dukanka? To ko dai nata cikin ne yazo mata da ƙunci da ɓacin rai? "To Kuma sai tayi ɓacin ran harda ni mijinta? Adam ya tambaya cikin rashin yarda. Kadija ta ce "Ta to wallhi yaya in dai irin wannan cikin ne to mutum koma waye sai ta masa, wani lokaci ma idan bata samu abokin yi ba to kuka zata fara ita kaɗai ko kuma ta samu wani abu a gidan ta huce a kansa, irin wannan yanayin mata da yawa na shiga irin sa, Kuma suna shan wahala sosai dole sai kayi haƙuri, dama ai Yaya ka sha faɗin cewar idan Ameera ta samu ciki zaka tarairayeta kamar ƙwai, to kaga haka zaka daure. Cikin mamaki Adam ya ce "Wai dama cikinne yasa wannan abun? Nifa duk inace barcin yamma da tayi ne yasa ta haka, yanzu dan mace nada ciki sai ta fara masifa Fisabililahi! Najib ya ce "Ai kawai abokina haka zaka daure, yanzu dai ka shiga kayi wanka ka fito muci abinci anjima kadija sai taje gurinta kar a barta ita ɗaya a gida kaga babu daɗi. Adam ya tashi ya tafi ɗakin da suka nuna masa yana tafiya yana mamakin wannan lamari, yanzu kawai sai mace ta fara masifa saboda ciki, shi bai ta'ba jin wannan labarin ba. Tana zaune idonta ƙurr a ƙofar falon Mai gadi ya turo ƙofar falon hannusa riƙe da leda, idonta a kan ledar domin ganin mai ya kwaso mata. Shi kuwa baba mai gadi jikinsa har rawa yake domin yasan dole sai ya she masifa barin ma yanzu da ya ƙara haɗa ido da ita ganin yadda ta kafe ledar da ido. A zuciyarsa ya ce "Yanzu fisabililahi ki aiki mutum ba tare da kin sanar da shi abun da zai sayoba, fatan kawai ki wahalar dani, yanzu nasan dole sai na koma. Jin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin ƙarasawa gabanta ya miƙa mata ledar kamar zai faɗi. Karɓar ledar ta yi ta na ƙoƙarin buɗewa, ganin ledar na mata gardama ne yasa ta yaga ledar tana jin ƙamshin abun da ke cikin ledar, cikin mamaki take kallon abun da ke ciki. Ɗagowa tayi ta kalleshi kafin ta Kara kallon abin da ke ciki ta ce... Kubi S-REZA a hankali kusan bai saba baku kunya ba. *Whatpad* Salis m Reza *One love💘* *One house🥰* *Comment's 🤝* *Shering please👏* *Love my all fan's😍* *S-REZA typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* _*(By S-REZA✍️)*_ *(Writer of Uwata ce sila. Meera & Nusee)* *PAGE 2️⃣* ...."Baka da hankali ne me ye wannan ɗin haka? Ta yi tambayar ta na turo masa ledar gaban sa. Cikin tsananin tashin hankali Baba mai gadi ya ce "Hajiya ƙosai ne na gani ana soyawa a ƙarshen layi to shine na sayo miki domin wallahi ban san wani abu mai laushi bayan wannan ɗin ba a irin wannan lokacin. Lokaci ɗaya taji kwaɗayin ƙosan a rainta amma tsabar masifar dake cinta sai cewa ta yi "To dan tsabar gidadanci sai kawai ka sayo mini ƙosai saboda kaga ana soyawa a ƙarshen layi ni nace ka sayo mini ƙosan ne? Baba mai gadi yayi shiru yana sauraronta. Jin ta yi shiru ta faɗan ne yasa shi ɗako kai da nufin kallonta sai kawai yaga tana cin ƙosan. A zuciyarsa ya ce "Ikon Allah a she ana so! Ganin haka yasa Baba mai gadi meƙewa ya bar palon ba tare da ya ƙara cewa komai ba. Ameera kuwa sosai taji ƙosan ya shiga ranta hakan yasa ta ɗauki guda ɗaya ta ci, jin yayi mata daɗi sai kawai ta cigaba da ci har bata san lokacin da Baba mai gadi ya bar palon ba. Tashi ta yi ta koma kicin ta ƙara haɗa shayi ta fito palo ta zauna ta sha kayanta sosai sannan ta ƙulle sauran ƙosan ta koma ɗaki ta sake kwantawa ba tare da ta gyara gidan ba, tana kwanciya barci ya ƙara ɗauketa. Tana cikin barci taji ana kiran sunanta hakan yasa ta miƙe fuska a haɗe ta nufi hanyar waje. Koda ta buɗe sai taga Kadija ce hakan yasa ta ɗan saki fuska. Cikin yanayin barci tai mata maraba sannan ta juya izuwa cikin gidan. "Ameera ta Adam yau dai Allah ya amshi addu'o'in mu ya bamu baby da muke ta nema. Kadija ta faɗa lokacin da ta zauna. Murmushin yaƙe ta yi tana jin babu daɗi a ranta. Ganin haka yasa Kadija sake cewa "Kawai sai mukaga Yaya da sassafe wai kin kora shi aiki ko taƙalmi babu a ƙafarsa kamar ɗan gudun hijira hala wani laifin yayi miki? Kadija ta faɗa duk domin ganin ta jata da hira ganin kamar ranta a ɓace yake. Daidai lokacin Ameera ta ce "Kice gulma ce ta kawoki gidan ba komai ba, ina ruwanki idan ma laifin yayi mini, shima zai dawo ya sameni daga cewa ya tashi ya tafi aiki shine zai ɗauki ƙafa yaje gidanki yana kai miki ƙara ke ga uwarsa ko uwata ko? Shine harda zuwa ki kuma zaki ɗauki mataki ko? To gani dan Allah ki ɗauki mataki nice na koreahi. Tana faɗa tana ƙarasowa gaban Kadijan cikin tsananin ɓacin rai domin har ga Allah abun da Adam ɗin yayi ya sosa mata rai, daga cewa ya tafi aiki shine harda zuwa ya kai ƙaranta kamar wacce tayi wani abun laifi. Cike da tsananin mamaki Kadija ke kallon Ameera wacce ada ko iya magana ma batayi da ita tsabar kunya, hasalima wani lokacin har faɗa take mata cewar ki saki jikinki dani ni ƙanwar mijinki ce ba yayar mijinki ba, amma haka Amera zatayi dariya ta kawar da kai. Ganin Amearan a gabanta kamar zata saka mata hannu ne yasa tayi ƙarfin halin cewa "Ameera ni kike faɗawa haka dan na tambaye ki? Cikin harzuƙowa ta ce "An faɗa miki ɗin uwata, ke ɗin banza kika iya shigowa gidana da niyar gulma bakiji kunya ba sai ni ce zanji kunyar faɗa miki gaskiya to na faɗa ko ƙarya nayi ba gulmar kika zo yi ba, ina ruwanki da tsakanina da mijina, mijina ko mijinki? Duk yadda Kadija ta kai da tayiwa Ameera azuri amma sai take jin wannan ba laulayin ciki bane, wallahi kawai iya shige ne da alama asalin halintane take baiyana wa yanzu,to da ma a ce laulayin ciki ne ai nata cin mutuncin yayiwa, dama itama Kadijan ba haƙuri gareta ba. Hakan yasa Kadija faɗin "Ya isa haka ƙaramar mara kunya, ke har kin isa nazo gidan Yayana kina zagina, to ƙaryane baki koreahi ɗin bane? Kuma idan bai zo gidana ba duk duniya wayakeda shi da ya wuce ni, wato zakiyi ƙarya da ciki kina cin mutuncin munatane ko, to wallahi ƙarya kike yi yarinya. Kadijan ta faɗa itama ta na cire mayafin kafaɗan ta tana ɗaurawa a ƙuƙunta alamar shirin faɗa. Kasancewar su ɗin kusan sa'anye ne domin ko Kadija zata girmewa Ameera to sai dai ko irin da shekara ko watanni, domin ko auransuma tare a kayi, kuma dukkanninsu babu wacce Allah ya baiwa ciki sai yanzu da Ameera ta samu. Jin abun da Kadijan ta faɗa ne yasa Ameera jin kamar an watsa mata garwashin wuta cike da fushi da jin cewar a zo har gidanta a naimi buɗe mata ido, ga kuma duk ƙuncin da take ji yazo ya tsaya mata a wuya bata son magana sam, hasali ma ita bata son ganin kowa a kusa da ita, hakan yasa ta ɗauke fuskar Kadija da mari wanda Kadijan batai tsammani hakan ba, shi yasa marin ya shige ta da kyau. Ji kake tass tass tass har sau uku. Sannan ta chakumeta ta watso ta waje ta rufo ƙofar gidan ta tana cigaba da zagin ta. Ita kuwa Kadija tsabar shigan marinne yasa bata ma san lokacin da a ka watsota wajenba, sai ji tayi ta ƙara buga kanta a jin abun da bata san ko meye ba, ai kuwa take ta baje a gurin sumammiya. Cike da ɓacin rai Ameera ta ɗauki wayarta domin kiran Adam ta sauke masa kwandon masifar amma taji wayar na ƙara a cikin ɗaki. Sosai wannan karan ranta yayi mugu-mugun ɓaci, azo har gida a naimi cimata kashi. Ɗakin ta shiga ta ɗauki wayar tana ji kamar ta bugata da ƙasa, sosai take jin ɓacin rai fiye da kullum, ji take da Adam zai shigo gida yanzu da sai ta kusa ɓallashi tsabar ta kaici, yanzu kenan duk abinda sukayi sai yaje yana sanar da ƙanwarsa tsabar rainin hankali, to ko ita an faɗa masa bata da ƙannen ne, to Allah ya kawo shi gidan lafiya, ita kuma wannan ta nuna waje sai na yi maganinta bata san wacce ni ba. Haka ta zauna tana jiran shigowar sa. Adam kuwa haka ya saka kayan Najib ya ɗauki motar Najib ɗin ya tafi gurin aiki, kasancewar Najib ɗin yau ba zai fita aiki ba saboda bashi da lafiya. Koda yaje gurin aikin yana ta tunanin halin da matar tasa ke ciki idan kuma ya tuna da cewar Kadija tana gidan sai hankalinsa ya kwanta. Yana aiki yana tunanin Allah yasa zuwan Kadija gidan yasa Ameera ta dawo asalin Ameeran sa, sosai halin da ta sauya yake damunsa daga jiya zuwa yau duk ya fita a haiyacinsa gashi yana son kiranta yaji halin da take ciki amma wayar tasa tana gida haka yaci gaba da aiki yana tunanin rikicin Ameera. Ta kai minti ashirin a gurin kafin Baba mai gadi ya hango ta a kwance a gurin, hakan yasa ya nufo gurin da sauri domin yasan da shigar ta gidan. Cikin tashin hankali yake runtumawa Ameera kira bayan ganin jini ya wanke mata gaban fuska gaba ɗaya. Sosai yake kiran hajiyar tasa, jin bata amsawane yasa ya nufi ɗakinsa ya ɗebo ruwa a buta ya watsa mata,ai kuwa watsawa ɗaya ta ja wani dogon numfashi haɗi da buɗe ido. Daidai lokacin kuma wayarta ta fara neman ɗauki. Da sauri Baba mai gadi ya ɗaga haɗi da zaiyana halin da Kadijan ke ciki tun kafin ma yaji wanda ke kiran. Cikin tsananin tashin hankali Najib ya ke tambayar sa waye shi ɗin? kuma a wani guri suke? a rikice Baba mai gadi ya sanar da shi cewar shine mai gadin gidan Alhaji Adam kuma suna cikin gidan. Ita kuwa Ameera ta na zaune ta haikince a Palo tana jiran shigowar sa sai taji Mai gadi na mata irin wannan kiran, far ko ta tsorata domin da ihuu ya kirata, har tayi nufin ta fita ta sauke masa buhun masifar dake cinta, amma tana buɗe ƙofar idon ta yayi gamo da aika-aikan da tayi , hakan yasa tayi saurin rufe ƙofar palon ta koma batare da mai gadin ya kula da itaba. Sosai ta tsotsa da ganin irin jinin da Kadijan ke fitarwa, zaunawa tayi tai shiru tana tunani, ko dai turata ɗin da tayi ne ta faɗi a kan ƙarfe, take jikinta yayi sanyi, amma har yanzu ƙasan zuciyarta zafi yake mata. Tana zaune a gurin har taji isowar ƙarar motar, ko bata leƙa ba tasan Najib ɗin ne yazo ya tafi da ita asibiti bata ko iya loƙowaba har suka bar gidan. Misalin huɗu da rabi Adam ya turo ƙofar gidan haɗi da sallama yana wurga idanunsa cikin palon domin ganin ta ina zai hango ta. Ganin bai ganta bane yasa shi nufar cikin ɗakinta yana kiran sunanta "Honey..."Honey. Daga cikin kicin yaji ta amsa da "Na'am Honey welcome back. Har ya juya zai nufi kicin ɗin ya hango wayarsa a gefen gado, hakan yasa ya je ya ɗauka ya nufi waje cike da mamakin sauyin matar tasa, yana tafiya yana godiya ga Kadija domin yasan itace ta lallasheta. Yana shiga palon ya ganta sai girki take yi ita kaɗai ta haɗa zufa. Yana shiga ya rungumota ta baya yana faɗin "Waye ya saki girki keda baki da lafiya Honey? Murmushi tayi haɗi da cewa "Ni lafiya ta ƙalau kawai girki nake marmari kuma na gargajiya. Adam ya ce "To me kike dafawa ne haka? Cikin ƙosawa ta ce "Kaje waje idan ya ƙarasa zaka gani ai. "A'a ai tunda Allah yasa na dawo baki gama ba to sai dai na tayaki mu ƙarasa. Adam ya faɗa yana ƙoƙarin zagayowa ta gabanta. Ita kuwa Ameera gaba ɗaya ma bata son ganinsa hakan yasa cikin masifar dake cinta da take ta dannewa ta ce "To sai kazo ka dafa kai ɗaya haba mana dan Allah na ce Kaje waje yanzu zai ƙarasa kazo ka dameni to gama kicin ɗin nan ka dafa harda kanka. Tana faɗa ta bar masa palon cikin ɓacin rai. Shi kuwa Adam da sauri yabi bayanta yana bata haƙur a kan wallahi zai fita, ita kuwa jin haka yasa ta ce yayi wanka zai kaita sufa makert zata sayo abun sha domin duk irin wanda take so ɗin sun ƙare. Jin haka yasa shi amsawa da sauri ya shiga ɗaki domin yin wanka ita kuma ta koma kicin domin ƙarasa aikin nata. Tun lokacin da Ameera taji fitar Najib da Kadija tasan asibiti zasu nufa, hakan yasa ta fita da sauri ta samu mai gadi taja masa kunne akan kar ya sake ya sanar da Adam komai, kuwa da wasa ya sake ya ji to sai ya bar aiki a gidan. Shi kuwa Baba mai gadi jin haka yasa ya riƙa bakinsa da hannu a lamar ya kulle bakinsa. Gurin da Kadijan ta ɓata da jini tasa mai gadin ya wanke sannan ta shiga ɗaki ta ɗauki wayar sa tasa a jirgi (plane mode) sannan ta shiga kicin domin yin girki. Ko kafin ya fito daga wanka itama har ta gama girkin ta zuba a plas ta rufe ta jera su a dainin tebul sannan itama ta shiga ta ƙara shiryawa. Yana fitowa itama ta fito cikin shigar abaya baƙa ta yane kanta da mayafin a bayar sai kuma baƙar jaka mai shigen kayan sai taƙalmi ja mai irin adon duwatsun gaban abayar. Batayi kwalliyaba amma ta ɗan shafa hoda, sosai tayi kyau ga ƴar ramar da tayi ya ƙara fito da haskenta. Shi kuma sanye yake da riga da wando flawa yad masu ruwan ganye, sai hula mai shigen kayan sosai shima yayi kyau dukda bai wani tsaya ya gyara kansa sosai ba. Kallo ɗaya tai masa ta kawar da kai ta nufi hanyar fita. Amma jin tambayar da yayi mata ne yasa hantar cikinta kaɗawa. " Wai ni Kadija har ta tafi ne daga zuwanta? Duk da razanar da tayi bai hanata dakewa ta ce "Eh ai bata dade ba ta juya wai tana sauri. Ta faɗi maganar hankalinta a kwance kamar batayi komai ba. Adam ya ce "Ok ai ina shigowa gidanan daga irin tarɓar da na samu nasan sister tazo gidanan. Ya faɗa daidai lokacin da ya ɓude mata motar ta shiga shi kuma ya zagayo ɓangaren direba ya shaga yana cigaba da yabon sister ɗin tasa. Ita kuwa Ameera ƙara ɓaci ranta keyi jin da gaske dai gulma ya kai mata shine yasa tazo. Sai yanzu ma take jin daɗin abun da ya faru da Kadijan Allah ma ya ƙara maganin masu gulma, sai yanzu ma take jin bata tsoron ya sani domin ko ya sani ai maganin magulmaciya tayi. Ganin ya ɗauko wayarsa zai sa a caji ne yasa ta kalli wayar taga har yazu a jirgi take hakan yasa taji daɗin cewar babu yanda za'ayi ya sani har sai gobe dan uban magulmaciya. Sosai ta cika tayi fam a cikin motar jin yadda yake ci gaba da yabon kirkin sister ɗin tasa jin yaƙi dainawa ne yasa ta ce "Wai dan Allah ko dai mu koma ne kaje ka ɗauko wannan kadijar sai kaci gaba da mata godiyar ne, haba dan Allah ni kazo ka dameni kamar wani kai ne kaɗai mai ƙanwa. Jin haka yasa Adam yin shiru yana kallonta ganin tana ƙara ɓata rai. Bayan sun shiga sun maga sayan komai da take buƙata ne sun zo hanyar fita daga cikin supar makert ɗin sai ledar hannun wata ƙaramar yarinya ya suɓuce daga hannun yarinyar bai tsaya a ko ina ba sai a ƙafar Ameera, take ledar ta wargaje kayan ciki suka watse wanda Ameera ta je taka gurin da ake sauƙa, sai kawai bata ankaraba ta taka gwanganin matar ai kuwa sai ji kayi tayi sama ta dawo tim a kan gurin. Da ƙarfi ta saki iho wanda kowa na gurin saida ya tsaya yana kallonta. Da sauri Adam ya iso gareta yana mata sannu ya ɗagota tana kuka wurjanjan domin kuwa ta bugu. Kuka take yi tana kallon gurin da yarinyar ke tsaye da uwarta ko irin su zo domin ɗagata ma babu wacce tayi. Ai kuwa cikin ɓacin rai da zafin ciwo yasa tana tashi ta nufi gurin da yarinyar take babu wata-wata ta ɗauke ta da mari hanu bibbiyu. Tana kuka tana marin yarinyar a gaban uwarta, wacce hakan yasa itama yarinyar rushewa da kuka, Amera na kuka yarinyar ma tana kuka. Uwar yarinyar ce tayi kan Ameera domin ramawa ƴarta amma Adam yayi saurin shiga tsakiya yana baiwa mata hakuri. Ita kuma Ameera baki yaƙi mutuwa sai zagin uwar yarinyar take yi, itama uwar yarinyar na ramawa kamar zasu buɗa. Ganin haka yasa Adam juyawa ga Ameera ya ce "Wai wannan wani masifane ina miki magana amma bazaki saurareni ba. Amma Ameera sai ƙundumawa uwar yarinyar asher take yi. Uwar yarinyar ta ciro wayarta da ke ruri ta ɗaga ta na ɗagawa ta ce "Abban Hanifah ka shigo ciki wata mara kunya ce ta bari Hanifah. Ta na faɗa ta sauke wayar tana jin yadda Ameera ke cigaba da kutuntumu zagi kala-kala tana surfa mata. Babu yadda Adam baiyi da itaba amma taƙi yin shiru ƙarshe shima ta shiga surfa masa nasa masifar tana faɗin "Kana kallo zata kasheni baza kace komai ba sai ni da nazo ƙwatarwa kaina ƴanci shine zakace na yi shiru to wallahi baka isa ba idan ma bakinku a haɗe yake to nafi ƙarfi ku, Banza mara kishin matarsa kawai. Yau kam iya kunya Adam ya gama jin kunya jin irin zagin da take masa a cikin mutane. Ana cikin haka sai ga wani gurjejen mutum sanye da rigar sojoji yana zuwa ya nufin gurin yarinyar da suka kira da Hanifah ya na zuwa ya rungumota ya fara lallasheta haɗi da tambayar waye ya taɓata kuma mai ya faru. Ai kafin yarinyar ta fara magana uwar yarinyar ta kwashe ƙarya da gaskiya ta sanar masa harda cewa wai ita da mijinta ne suka daki Hanifah itama harda zabga mata mari sannan ta rushe da kuka tana riƙe ƙunci. Ai kuwa wannan sojan jin haka yasa ya na juyawa ya ɗauke Adam da wani lafiyayyen mari ya riƙe kwalar rigarsa ya dinga zabga masa naushi, dukansa yake yi yana ihu yana ƙara masa, ita kuwa Ameera ganin haka yasa da gudu ta nufi gurin motarsu ta shiga, amma ganin kamar za'a biyota ne yasa ta fita daga motar ta tare mai a daidaita ta shiga ta bar gurin gaba ɗaya. Sai da wannan sojan yayi wa Adam ɗan banzan duka wanda har sai da bakinsa da hancinsa suka fitar da jini kafin ya barshi yana tambayar matartasa ina ita matar mutumin take. Nan suka naimi Ameera sama da ƙasa basu ganta ba, sannan sojan ya kalli Adam ya ce "Daga yau ka ƙara dukan matar wani dan ubanka idan baka da hankali, yana faɗa ya ƙara takurinsa a ruwan cikinsa sannan ya kama hannun matarsa da ƴarsa suka bar gurin. Sai da ya bar gurin kafin mutane suka zo da sauri suka ɗaga Adam ɗin dake ta zubar da jini ta baki da hanci. Sosai ya daku ko tsayuwa ma baya iya yi, hakan yasa suka saka shi a mota suka nufi asibiti...✍️ Kubi S-Reza a hankali labarin na daban ne. *Whatppad* Salis m Reza *One love💘* *One house🥰* *Comment's🤝* *Shering please👏* *Love my all fan's😍* *S-REZA typing...✍️* _*AMEERA DA ADAM*_ *(By S-REZA✍️)* *First class writer's asoo..* 3️⃣ ...Ɓangaren su Kadija suna isa asibitin suka samu taimakon gaggawa kasancewar har zuwa lokacin da suka isa bata farka ba. Shi dai Najib ya na ta mamakin abun da ya samu matar tasa, tsabar tashin hankali ma bai ko tsaya ya tambayi mai gadin abun da ya faru ba. Ya kai kaman awa ɗaya a tsaye yara jira kafin wata daga cikin likitocin ta fito ta kira shi. Ko da ya iso sun gama shiryata an saka mata bandeji agurin sannan an saka mata ruwa ta na barcin wahala. Kallo ɗaya yayi mata yaga yanda ta rame ga kuma a lamar rashin jini a jikinta domin kallo ɗaya za kai mata kaga tayi fari. Nan likitan ta sanar masa akan za'a ƙara mata jini bayan ta farka, kasancewar jininsa group O ne yasa ya je a ka ɗiba a nasa. Bayan an gama ne ya fito yana son kiran Adam domin sanar da shi halin da ake keci ganin har lokacin bai ga Ameera ko Adam ɗin ba. Haka ya kira numbar Adam ɗin amma ba'a ɗagawa ya masa kira har sau huɗu amma babu amsa, hakan yasa ya bari zuwa an jima. Ko da ya koma ɗakin da Kadijan take kwance ya ga har yanzu barci take yi sai kawai ya fita izuwa masallaci. Ko da ya dawo ya sake kiran Adam amma yazu yaji number a kashe, sosai yanzu abun ya fara bashi tsoro. Sai yanzu kuma ya tuna cewar Adam fa a gida ya bar wayarsa, har ya yanke shawarar zuwa gurin aikin Adam ɗin amma yayi tunanin kar kuma ya tafi ita kuma Kadijan ta farka baya nan, hakan ne ma yasa ya zauna har sai ta tashi ta sanar tashi abun da ya faru. Koda mai keken ya sauketa bata tsaya bashi guɗi ba tayi hanyar shiga gida da gudu, tana zuwa ta tura ƙaramin get ɗin ta shege ciki da gudunta. Mai keke kuwa ganin haka yasa ya biyo bayan ta yana masifar bata isa ba wallahi. Mai gadi dake zaune yaga ta wuje da gudu ya bita da mamaki baki a sake yana ganin ikon Allah na sauya rayuwar wannan baiwar Allahn cikin lokaci kaɗan. Yana cikin mamakin yaga mai keken ya shigo har cikin gidan yana zage-zage. Mai gadi ya tare shi yana tambayar sa. Nan mai ɗan sahu ya sanar da shi cewar kuɗi zata bashi. Dama a kwai sauran canjin kuɗinta a gurin mai gadin na ƙosan ɗazu hakan yasa ya tambaye shi nawa ne kuɗin sai ya cira ya ba shi. Ita kuwa Ameera ta na shiga palon ta fara sauke ajiyar zuciya ta cire ɗan kwalin a bayar da ke kanta sannan ta samu guri ta zauna tana riƙe bayanta gurin da ta bugu. Firiza ta nufa domin ɗau kan ruwa mai sanyi sai taga frizan a dungware a ƙasa socket ɗin ma baya jikin wuta, ga kuma babu komai a ciki, sai yanzu ta tuna da cewar a shefa kayan freza ɗin suka tafi sayowa. Komawa ta yi ta zauna ta ciro wayarta ta latsa kiran numbar Honey, amma taji wayar a kashe, sai ta tuna da cewar a she fa ita ce ta ka she masa wayar. Sai kuma tunanin Kadija ya faɗo mata kasancewar saboda su Kadijan ta kashe wayar. Afili ta furta "Oo ni Allah na Ameera me yake faruwa da ni ne! Yanzu fa sai ace wannan duk laifinane bayan kuma ni duk ba laifina bane. Sai kuma ta miƙe tsaye ta fara ƙoƙarin kuka tana kiran sunan Adam. "Allah dai yasa Honey ya ƙwace ya gudu daga hannun wannan mugun, Allah yasa bai ji masa ciwo ba, waiyo ni Allah Honey na mai ya kaika faɗa da sojoji! Sosai kuka ya kufuce mata tana yi tana kiran sunan Honey ganin kukan ba zai kaita bane yasa ta fita waje da sauri sai kuma ta dawo ta ƙara surar jakarta da ɗan kwalin ta har ta kusa isa ƙofar waje sai kuma ta dawo da baya ta zauna ta dafe bayanta da yake mata wani ciwo. A fili ta ce "Allah ya isa tsakanina da wannan Hanifah ɗin shegiyar yarinyar, kimin laifi amma saboda ubanki soja ne sai kawai baza'a hukunta ki ba, ai kuwa wallahi ƙaryane sai dai idan ba Ameera kika taɓo ba. Ta shi tayi ta leƙa wajen cikin gidan ta ƙwaɗawa mai gadi kira, bayan yazo ta sa ya kwashe abincin da tayi tace yaje ya cinye. Da murna mai gadi ya kwashe abincin ya fita da shi ya na godiya. Ɗaki ta koma da niyyar sake wanka tayi alaula kafin Honey ya dawo ganin magrib na dosowa. Ɓangaren Adam kuwa ana zuwa da shi asibiti bai ko yarda an kwantar da shi ba ana gama wanke masa ciwon bakinsa ya sallamesu ya fito daga asibitin bayan sun rubuta masa magungunan da zai siya, sai da ya biya ya sayi maganin kafin ya koma ya ɗauki motarsa ya nufi hanyar gida. Yana cikin tafiya ya ɗauki wayarsa domin kiran Najib yana danna kiran sai yaga kiran ya dawo. Sai da ya duba yaga wayar a jirgi. Sosai yayi mamakin hakan domin dai shi da kansa bai sa wayarsa a jirgi ba, Nan take Ameera ta faɗo masa, girgiza kai kawai yayi yana kiran numbar Najib ɗin bayan ya cire wayar daga jirgin. Tana shiga Najib ya ce "Hello Adam" shima ta ɗaya bangaren ya amsa da cewar "Kana gida ne? Cikin ɗacin rai da ɓacin ran da Najib ɗin ke ciki dalilin jin duk abinda ya faru daga gurin Kadija ya ce "Wallahi Adam ka bani mamaki, wato saboda kar ma na kiraka na sanar da kai abinda matarka taiwa Matana shine ka kashe waya, kuma tsabary rainin hankali kana iya kirana ka tambaye ni wai muna gidane ko? To kaje gida ka ajiye mini motana kuma wallahi ka sani ba zan bar wannan cin mutuncin ba, ko mai ina za'a je sai dai aje. Yana faɗa ya kashe wayarsa yana jin wani ɓacin rai ganin irin halin da matar tasa ke t. Tsabar masifar dake cinsa ma har ya manta da cewar matar tasa ƙanwar Adam ɗin ce. Cikin tsananin mamaki Adam yake sauraron abokin nasa jin abun da yake cewa, jin ya kashe wayar ne yasa ya fara salamulai a fili ya na cewa "Innalillahi wa Innalillahi raji'un! Meye Najib ya ke faɗa ne, wai Amera ce ta daki Kadija ko meye. Nan dai ya shiga kiran sa amma a kashe, haka ya nemo numbar Kadija itama a kashe, take hankalinsa ya ƙara tashi gabansa yana faɗuwa, domin tun da yaji muryar Najib a haka to yasan ransa ya ɓaci sosai. Gidan su Najib ɗin ya fara zuwa amma mai gida ya sanar da shi ai tun safe da hajiya Kadija ta fita shima Najib yabi bayanta basu dawo ba. Motar ya bari a gidan sannan ya nufi gidan sa cikin ɓacin rai yana jin yau sai ya ɓata wa Ameera rai, dan tsabar bala'i ma a ƙafa ya taka har zuwa cikin gidan Ko da ya tura get ɗin ya shiga sai yaci karo da mai gadi ya saka kulolin abinci a gaba yayi tagumi yana kallon cikin babbar kular kamar zaiyi kuka. Yaso ya wuce ciki amma ya ƙarasa gurin mai gadin yana tambayar sa Amera ta dawo ne? A tsorace mai gadin ya dawo hankalinsa yana miƙewa yana masa barka da zuwa cikin yanayin tsoron yanayin da ya tarar da shi. "Eh Hajiya ta dawo tun ɗazu tana ciki ma yanzu haka" Har Adam ɗin zai huce sai kuma ya dawo da baya yana kallon cikin kular abincin da kyau ganin abun da ke ciki. Ɗan wake ne a kayi amma ya dame ya zama kamar ƙullun tuwo, ko kyawun gani babu. Lokaci ɗaya Adam ya gane cewar abincin da tayi ne ɗazu kafin su fita. Zai magana mai gadi ya ce "Mai gida hatsari kayi ne? To Allah ya kiyaye gaba ya tsare tsau-tsayi da a'sara. Adam ya amsa da Amin yana nufar cikin gidan. Ransa a ɓace ya tura ƙofar palon gidan nasa yana ƙoƙarin danne zuciyarsa akan abun da take saƙa masa game da matar tasa. Yana shiga ya fara kiranan sunanta cikin kakkausar murya. "Ameera "Ameera. Kafin ya rufe baki sai ji yayi an rungume shi ta baya tana faɗin. "Sannu da dawowa Honey ya jikin ina dai fatan lafiya kake ko Honey mai sukai maka? Ta dinga jero masa tambayoyi kamar zata yi kuka domin kuwa tun lokacin da ta dawo ta kasa sakuni sai kaiwa da komowa take yi tana jiran ya dawo duk ta damu. Cikin ɓacin rai ya ce "Bana son zancen banza Ameera me ya haɗaki da kadija ɗazu da tazo? Yayi tambayar cikin ihu da ta kaicin abun . Ai kuwa Ameera jin haka sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinsa da kyau ta fara faɗin. Ni ina gida ina tunanin halin da kake ciki duk na kasa sakuni amma ka shigo kana mini ihu harda kiran sunana da Ameera a kan abun da ban san faruwansa ba, hasali ma ni a kaiwa laifi amma kazo baka ji kan zance ba ka hauni da faɗa wato kafi son ƴar uwarka a kaina ko? Cikin sauri da jin shirmen zancen ta ya sake cewa "Mai ya haɗaki da ita? "Nifa ban san komai ba kawai dai ni naga tazo yin gulma ne shine kawai nace ta fita min daga gidan mijina tunda gulma ya kawo ta shine na turata waje. Da sauri Adam ya fincike ta daga jikinsa ya ɗan turata baya haɗi da faɗin. "Kadijan zaki kora daga gidana baki da hankali ne, kuma itace zata miki gulma har kina iya faɗa mini cewar gulma tazo, kuma wai gidana, to wallhi mutuƙar..."Ai kafin ya ƙarasa Ameera ta ƙwalla wani uban ihu sanadiyyar turata ɗin da ya ɗanyi ta faɗi a tsakar palon. "Waiyoooo allana Umma na! Waiyoooo cikina bayana ya kasheni! Inna'ilaihi na shiga uku!. Sosai take kuka bilhaƙƙi da gaskiya harda hawaye. Ganin haka yasa Adam saurin ƙarasawa gurinta yana ƙoƙarin ɗagota. Take ta fara kai masa duka tana faɗin"Ni ka rabu dani ka barni ni dai sai ka kaini gurin Umma. Sosai ta burkice masa gashi taƙi ta barshi ya taɓata، sai faɗin cikinta da bayan take wanda hakan yasa Adam tsorata karfa wani abun ya sami cikin nata. Jin tunanin da yazo masa ne yasa gabansa faɗuwa, da sauri ya sunkuya ya kinkimota suka nufi ɗaki. Yana shiga ya kwantar da ita yana cigaba da bata haƙuri akan ba zai ƙara ba hakan ma kuskure ne. Lokaci ɗaya tayi shiru tana ajiyar zuciya, ganin haka sai kawai shima ya kwanta a kusa da ita ya ruƙo hannunta ya fara faɗin. "Kalli abun da kika ja a kai mini ɗazu duk a dalilin taurin kanki, dan Allah Honey ki rake wannan fushin wallahi ina cutuwa kinji? Shiru tayi tana kallonsa batare da tace komai ba domin ita har ga Allah bata ga wani abun da tayi na fushin ba, hasali ita batayi wani laifi fa. Jin tayi shiru ne yasa ya ɗaga rigarta yasa hannunsa a cikinta ya fara shafawa yana cigaba da faɗin. "Wannan Babyn yazo da rikici sosai, duk yabi ya sauya min mata kamar ba Ameera da Adam ɗin da suka kafa tarihin soyayya ba, dan Allah ki dawo kamar da kinji Honey? Ya faɗa yana kai idonsa ga fuskarta jin bata ce komai ba. Yana kallonta yaga tana lumshe ido alamun barci zatayi. Shi kuwa take yaji yana buƙatar ta jin yanda ta sake masa jiki. Sai kawai ya shiga rabata da kayan jikinta yana cigaba da shafa daga cikinta zuwa sama, sosai itama yanayin yayi mata daɗi sai kawai ta sakar masa jiki tana bashi dama. Sosai ta manta da komai ta saki jiki suka samu natsuwa domin itama tana buƙatar hakan. Bayan komai ya wakanane ya jawota jikinsa yana saka mata albarka sannan ya faɗa toilet yayi wanka haɗi da alaula ya fita Masallace. Ganin fitarsa yasa itama miƙewa ta shiga toilet ɗin. Bayan sallar isha suna zaune a Palo suna kallo ta kwantar da kanta a kan cinyarsa shi kuma hannunsa na cikinta yana shafa ta ce "Honey wallhi gurin dana faɗi ɗazu har yanzu zafi yake min kamar ma fa karyewa nayi a gurin? Da sauri ya ce "Na gani? Haka ta juyo masa kan kwankwason ta tana nuna masa. Ya ce "Sorry ba karyewa bane kawai dai kin ɗan bugu ne. Cikin shagwaɓa ta ce "Allah zafi fa yake min sosai bana iya ko sunkuyawa gaba ɗaya. Adam ya sake shafa gurin ganin bai ga alamar komai ba ya ce "To sorry zai dana in sha Allah kuma zan sayo miki magani gobe sannan zan samo miki wacce zata ɗan dinga tayaki wasu ayyukan na gida sai ke ki dinga hutawa ko? Dariya tayi tana faɗin amma dai ba a cikin danginka zaka nemo ba ko? Domin bana son raini Allah, kuma karka samo ƙazama Please. Sai a lokacin Adam ya tuno da kadija lokaci ɗaya ya saki salati yana faɗin Honey Kadija fa tana asibiti kuma bamuje ba? Take Ameera ta haɗe rai tana kallonsa. Take ya ɗauko wayarsa ya nemo number Najib kira ɗaya ya ɗaga haɗi da sallama. "Najib kuna gida ne ko har yanzu kuna asibiti? Adam ya tambaya cikin harɗewarmurya? "Mun dawo gida tun ɗazu. Najib ɗin ya bashi amsa kamar wani abun bai faru ba. "Ok tom ina kadijan lafiya dai take ko? ganinan zuwa yanzu Please. Yana faɗa ya kashe wayar ya miƙe ya shiga ɗaki ya sauya kaya ya nufa hanyar fita daga palon yana sauri kamar zai tashi sama. Yana zuwa ƙofar palon yaga ƙofa a rufe, yana juyowa ya ganta tsaye ta riƙe ƙugu tana haɗe rai. "Lafiya dai kika rufe ƙofar? Ya tambaya cike da mamaki. "Babu inda zakaje a darannan ka barni ni ɗaya wallahi. Itama ta faɗa tana ƙara tsayawa a gurin da kyau. "Gidan Najib fa zance dubo Ameera kuma kece silar zuwanta asibiti, kuma babu wanda yaje nidake, Please dan Allah zo ki buɗe min na tafi yanzu zan dawo. Cike da mamaki ta ce "Wato nice sila ko? To kai da kaje ka kai mata gulmar cewar Ina dukanka kullum, kuma ina hanaka sakewa a gidan kafa? ni bance komai ba sai ita magulmaciyar, to Allah komai dai me zakace bazaka tafi gidan ta a darannan ba. Jin haka Adam ya ce "To zo mu tafi tare Please bana son tashin hankali, naji har kin fara ce mata magulmaciya ce. Ameera ta tayi dariya ta ce "Babu inda zanje wallhi kuma kaima haka muna tare har gobe. Sosai ransa ya kai ƙarshe da ɓaci yana jin wallahi ko danneta sai yayi ya ƙwaci ɗan makulli ya tafi , bayajin zai samu sakuni idan baiga halin da kadija ke ciki ba. Kallonta yayi da kyau yana jin wani ɓacin rai na zuwar masa, da sauri ya ƙarasa gabanta yana tattaro natsuwarsa a guri guda ya ruƙota da ƙari ya mannata a faffaɗan ƙirjinsa ya matseta sosai...✍️ _Ban fara ganin ra'ayoyin ku bafa. Comments dinku shine ƙwarin guiwa na_ *Kubi S-REZA a hankali* Whatppd Salis m Reza *One love 💘* *One house 🥰* *Comment's 🤝* *Shering please 👏* *Love my all fan's 😍* *S-REZA typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* 4️⃣ *(By S-REZA✍️)* _*(Writer of Uwata ce sila)*_ *PAGE4️⃣* ....Ya fara magana cikin sanyi-sanyi kamar mai tsoron kar wani ya ji. "Ba daɗewa zan yi ba yanzu zan dawo dan Allah ina so kema ki shirya mutafi tare nasan idan ta ganki zata ji daɗi shima Najib zai gane cewar ba laifinki bane please Honey?. Adam ya ƙarasa yana riƙo hannunta kamar zaiyi kuka. Yana gamawa ta zame jikinta batare da tace masa komai ba ta juya ta nufi ɗakinta ta barshi baki sake yana kallonta. Haka dole ya haƙura da zuwa gurin Kadija ya dawo Palo ya zauna yayi tagumi yana tunanin lokacin baya tsakanin sa da Ameera, lokacin da suke soyayya irin soyayyar da zakaga masoyan har kama da juna suke yi, tsaɓar soyayyar da suka sha a baya shine yasa ake kiransu da Ameera ta Adam, ko kuma wasu suce Ameera da Adam. Yana cikin wannan tunanin sai gata ta fito cikin shigar kayan bacci. Kallo ɗaya yayi mata ya kawar da kansa gefe. Ta na zuwa ta ce "Honey ta shi muje mu kwanta na kasa bacci ne? Ta faɗa da ɗan rigima a muryarta. Ta shi yayi ba tare da yace komai ba ya nufi ɗakin yana shiga ya kwanta kansa na kallon sama. Itama irin kwanciyar da yayi tayi tana kallon gurin da idonsa ke kallo. "Honey na dameka ko? Baka san yanda zaka yi da ni ba ko? Tayi maganar ba tare da ta kalle shi ba. Sai a lokacin Adam ya juyo ya kalleta ya sauke ajiyar zuyace kafin ya ce "Wai duk abinda da kikeyi dama kina sane kenan? Jin haka yasa itama juyowa sukayi ido biyu kasancewar basu kashe wutar ɗakinba. "Meye nake yi wanda bai dace ba ko kuma nayi laifi? Itama ta tambaye shi tana jin yanayinta na sauya wa . "Babu komai" ya faɗa sannan ya sauƙa daga kan gadon ya kashe wutar yayi shirin bacci ya haye katifar ba tare da ya ko ƙara bi ta kanta ba, itama daga haka bacci yayi wuff da ita. Washegari da wuri Adam yayi shirin zuwa aiki daga nan kuma zai biya ta gidan Najib ɗin. Sosai yake sauri yana Allah-Allah kar wannan matar ta kawo masa wata matsalar da safen nan, tsabar sauri ma bai ko tsaya ya karya ba ya nufi kicin gurinta yana sanar da ita ya shirya zai tafi. Yana shiga ya tatdata kwance a cikin cikin ɗin tana baccinta hankali kwance yaso juyawa ya fita amma dai ya ƙaraso yana kiranta. "Honey Honey lafiya kuwa kike? Jin haka yasa Ameera farkawa tana sauke idonta a kansa. Kafin tayi magana ya ce "Idan bacci zaki yi ai da kin tsaya a ɗaki amma sai kizo kicin ki kwanta. Yana faɗa Ameera ta fashe da kuka tana faɗin. Indomi da ƙwai nakwson ci kuma nazo naga babu ƙwai shine bacci ya ɗaukeni kuma ni yunwa nake ji sosai. "Ok tom yanzu dai bari na aiki mai gadi ya sayo mana ƙwan sai ki dafa ko? Ameera ta ɓata rai sannan ta tsayar da kukan shagwaɓar ta ce "Wai dan Allah dole ne sai kaje gurin wannan yarinyar ne, to ni dai wallahi yau bana jin daɗi ina son zama da mijina a gida, kuma gashi cikina ma yana ɗan murɗawa haka kawai ka tafi ka barni ni ɗaya a gida ai kuwa ba zai saɓu ba. Cike da mamaki yake kallonta ya ce "Me kike nufi? Da sauri tun ma kafin ya rufe baki ta bashi amsa "Abun da kaji shi neke nufi. Jin haka yasa ya ce "Ai kuwa baki isa ba, dele na tafi gurin aiki, zan ajiye miki kuɗin ƙwan a ɗaki sai ki ba mai gadi ya sayo miki ban yarda ki fitaba na faɗa miki. Yana kaiwa nan ya juya ya fita daga kicin ɗin cikin sauri. Ai kuwa tabi bayansa tana masifa. Ganin yaƙi tsayawa ne sai ta bishi da gudu. Shima yana juyawa yaga ta nufoshi sai kawai shima ya saka gudun. Sosai take jin bata so ya tafi ya barta a gida, ganin ya sa gudu yasa ta ƙara dagewa. Har cikin harabar gidan bata dai binsa ba, ganin haka yasa bai ko bi ta kan motarsa ba ya na zuwa ya nufi gurin get. Shi kuwa Baba mai gadi cikin mamaki ya hango amarya da ango suna tseren gudu, hakan yasa ya saki baki ganin uban gidan nasa ya dage da gudu. Kasancewar get ɗin a rufe yake yasa ko da Adam ya ƙara so gurin yayi-yayi ya buɗe taƙi har saida Amera ta cim masa. Tana zuwa ta riƙe masa riga tana haki!. "Biyoni mutafi cikin ruwan sanyi" Ta faɗa ba tare da tunanin mai gadi na kallonsu ba. Jin haka yasa Adam fara lallaɓata babu yanda baiyi ba amma ta kafe akan ita Allah yau ba zai fita ba. Jin haka yasa ya haƙura suka koma gida. Suna shiga ta sake shi ta nuna masa kan kujera tace ya zauna, ai kuwa babu musu ya zauna. Itama zama tayi tana kallonsa ta ce "Na faɗa maka ƙwai nake son soyawa da indomi kuma kasan bamu da ƙwai a cikin ko? Cike da ɓacin rai ya zaro kuɗi yace gashi kije ki ba mai gadi ya sayo. Ai kuwa cikin masifa ta ce "Ni zaka wulakanta akan na tambayarka kudi Honey? Shine har da watsomin wato irin ga matsiyaciyar nan ko? To wallahi nafi ƙarfin wulaƙancinka akan wasu banzayen kuɗinka kuma bana so. Tana gama ta tashi fuuu ta nufi ɗaki ta ɗauki kuɗi ta fito ko hijjabi babu ta nufi hanyar waje. Tana zuwa ko takan mai gadin bata ko bibi ta nufi hanyar waje da kanta, kasancewar a kwai wani mai ɗan shago inyamuri a ƙasan layin nasu. Tana zuwa cikin fushi ta ce abata ƙwai kret ɗaya. Ya ƙarɓa ya fara suba mata a leda sai taga wani ɗan ƙarami tace a sauya mata yayi ƙarami. Shi kuma yace ai ba'a sauya wa sai dai idan kiret ɗin gaba ɗaya za'aa sauya. Jin haka Ameera ta ce "To wallahi sai ka sauya mini, na sayi abu da kuɗina amma kace wai ba'a sauyawa kai ɗin banza. Tana faɗa ta sa hannu ta ɗauki guda ɗayan zata sauya da kanta, ai kuwa malam inyamuri ya yi sauran mayar mata da wanda ta saka masa yana cewa "Hajiya nace miki ba'a sauyawa sai dai idan wani kike so gaba ɗaya amma dai bazamu zake ko ɗaya daga ciki ba. Ai kuwa cikin tsananin ɓacin rai da masifa Ameera ta ce "To wallahi sai an sauya min ko kai ɗan gidan uban waye, kai ɗin banza ni da kuɗina amma na bari a cuceni. Tana faɗa ta zagayo ta gaban shagon da kyau sannan ta nufi gurin ƙwan. Kallo ɗaya za kaiwa wannan inyamurin ka gane ba ƙaramin ƙaton mutum bane amma tsaɓar ƙarfin hali na Ameera sai take ƙoƙarin ture shi ta ɗauki ƙwan, ganin yaƙi turuwane sai kawai ta ɗauki nata kiret ɗin ta watsa masa ƙwan a fuskar sa tana faɗin"Tsinane kaine matsiyaci gasunan gaba ɗaya kaje ka dama da shegiyar matarka. Adam da ya saci hanya zai gudu ya hango abun dake faru da matar tasa. Da gudu ya ƙara so gurin yayi saurin shiga tsakaninsu ganin inyamurin ya dososa cikin ɓacin rai. Ita kuwa ganin Adam a gurin sai ta ƙara ƙaini gurin zagin mai shagon. Sosai Adam ya ba shi hakuri sanan ya biya shi kuɗin ƙwan wanda da kyar ya haƙura domin kuwa ta masa wanka da ƙwan gabaki ɗaya jikinsa. Haka Adam ya kamo hannunta suka nufi gida. Suna shiga palo ya juyo da ita ya sauke mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu. Sai dai kamar walƙiya kuma kamar a mafarki yaji sauƙar maruka fiye da guda biyu a kumatunsa wanda yasa bai ko iya tsayawa ya duba daga ina marin suka fitoba. Ta gama zuwa har ƙarshe ta gaji bazata iya ba ta gaji. Cikin mamaki da tsoron Adam yake bin ta da kallo ya riƙe kuncinsa, kasa yin magana yayi sai kallonta da ya keyi. Jin yaƙi cewa komai sai ita ta fara magana cikin tsananin ɓacin rai da fitar da abun dake ranta. Dama cike take da abun da yayi mata na jefa mata kuɗi ga kuma rashin shigar mata faɗa da bai yi ba sai wani haƙuri yake bayarwa shine kuma yanzu tsabar samun guri zai wani mareta. "Wallahi nafi ƙarfin a wani ya wulakanta ni koma a inane, ka fita ka tarar ana faɗa da matarka kai baka shigar mata ba sai kawai kai ma kazo gida ka hau dukan jaka ko? Ai iyayena jaka suka ajiye maka da zaka daka alokacin da kake so to wallahi baka isa ba. Cikin ƙarfin hali Adam ya ce "Ni kika mara Ameera? Yanayin yanda yayi maganar sai da gabanta ya faɗi amma ta dake ta ce "To laifin waye? Mai yasa zaka mareni a kan waccen wawan arnen? Ba tare da yace komai ba ya nufi ɗaki ya shiga toilet ya sake wanka ya sauya kaya ya fita daga gidan gaba ɗaya. Itama Amera wayarta ta ɗaga ta kira Umma ta ce abawa Nana ƙanwarta kuɗi ta sayo mata ƙwai tazo mata da shi yanzu tana son cine kuma na gidan ta ya ƙare ne ga kuma Adam baya gida. Ai kuwa babu jimawa sai ga Nana ta kawo mata ƙwan. Koda nanar tazo taga yanayin yayar tata sai take tambayar ta lafiya kuwa. Ameera ta sanar da ita babu komai amma nanar ta so dagewa son jin komai. Nan take Ameera ta hauta da masifar cewar ina ruwanta, ko itama ta zama magulmaciya ne. Jin haka yasa Nana yin shiru da bakinta. Ameera ta ce ta shiga kicin ta dafa mata indomin ɗin. Kawai sai taji komai ma baya mata daɗi, sosai take jin ƙunci a ranta idan ta tuno da abun da ya faru ɗazu. Cikinta taji ya murɗa alamar yunwa sai kawai ta kwaɗawa Nana kira . "Nana wai har yanzu baki gama dafa indomi ba kawai? Ko rufe baki batayi ba sai ga Nana ta fito da alamar ta gama. Nan suka zauna suna ci Nana tana bata labarin saurayin ta wanda a ka saka musu rana da shi ta ce "Anty Meera kinsan Allah Nasiru bai da kirki kumafa tsabar rashin Kunya har cikin gida ya shiga da kansa wai ya fasa auran, Allah ma dai yasa Baba baya gida ai da anyi abun kunya. Ameera ta ce "Ni ban taɓa ganin soyayya irin wannan ba kullum faɗa kullum kuma sai wani daga cikinku yace ya fasa, an ya a haka aure zai yiwu kuwa Nana? Nana tayi dariya ganin ta fara cin nasarar sakƙo da yayar tata ta ce "Waifa kawai dan an faɗa masa cewar an ganni da wani a tsaye kuma wallahi ƙaryane shine shi kuma yana zuwa ya hauni da masifa kamar wata matarsa ko ƴarsa, shine nima na kasa jurewa har sai da muka yi dam e shine ya ce wai ya fasa, amma jiya ya dawo zance dake baida kunya. A kwanakin baya idan Nana tazo wa da Ameera da irin wannan maganar haƙuri take bata domin babu wanda bai san irin soyayyar Nana da Nasiru ba soyayya ce wacce su kaɗai suka san nufinsu, in dai yazo zance tofa sai sun raba gari, amma zuwa gobe kamar ba'ayi ba. Sun kai shekaru biyu a haka har dai a ka saka ranar, wacce yanzu haka kullum idan yazo ko ita tace ta fasa ko shi ya faɗa, to shekaranjiya ne abun ya girma domin har cikin gida ya shiga yana faɗin ya fasa. Shi Nasiru bashi da haƙuri kamar yadda itama Nana haka, amma duk da haka wani irin so sukewa junansu wanda basa iya yin fushi mai tsayi da junansu. Ameera ta ce "Buɗe kunnuwanki da kyau kiji abun da zan sanar miki. Nana ta ɗaka kai ta kalli yayar tata ta ce "Ina sauraronki. Lokacin da Adam ya isa gidan su Najib ya tarar da Najib ɗin shima a gida domin har yanzu ba shi da lafiya. Da kunya ya ƙarasa ciki yana senne kai! Ganin yadda suka tarbe shine yasa yaji daɗi domin basu nuna masa komai ba daga kadija har NAJIB ɗin. Zama yayi a gurin da kadija ke zaune yana kallon bandejin dake ƙoshinta, kafin yayi magana itama take tambayarsa ciwon fuskarsa. Nan take ya zauna ya faɗa musu komai irin dukan da ya sha a gurin soja, sannan ya tambayi kadija abun da ya faru. Itama haka ta kwashe komai ta sanar masa bata ɓoye ba. Sosai Adam yaji tausayinta ya sanar mata cewar wallhi itace duk ta hana shi zuwa da masifa iri daban-daban. Sai a lokacin NAJIB ya ce "Maganar gaskiya Ameera ba da sanin ta take yin wannan abun ba, wallhi cikine yake sakata duk wannan abun, lokacin da kadija ta faɗa min farko nima na ɗauka rainine da iya shege sai da na tsaya nayi bincike sosai nagano abubuwa da dama akan masu ciki, hakan yasa nayi mata uzuri, to kaima dole sai ka ƙara hakuri kuma ka bita a hankali. Yanzu dai ka samo mata ƴar aiki domin samun sauƙin wasu abubuwan. Adam ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Najib jin wai harda yin bincike...✍️ *Kubi S-Reza a hankali* *WATTPAD* _Salis m Reza_ *One love💘* *One house📚* *Comment's🤝* *Shiring please👏* *Love all my fan's😍* *S-Reza typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* *5* _*By S-REZA ✍️*_ *(Writer of Uwata ce sila)* *WATTPAD* _*Salis m Reza*_ 5️⃣ ...Cike da tabbacin abun da za ta sanar ɗin Ameera ta fara ce wa "Karki ƙara tsayawa wani ƙaton banza ya ɗora hannunsa a jikinki da sunan duka wai saboda ya kai sadakin ki, idan har ya dake ki kema ɗaga lafiyayyun hannayen da Allah ya baki ki daki ɗan banza, ai ke ɗin ba jakarsa ba ce dan uban sa da zai dinga jibga tun ma kafun ayi auran, Idan kuma ya ce ya fasa auran kema Ki ce kin fasa ai shi ɗin ba autan maza bane. Nana dai ta yi shiru ta na sauraron yayar tata cike da mamaki, sai da ta gama tsaf kafin Nana ta ce "To Anty Meera in sha Allah hakan za'ayi ai dama kinsa bana raga masa tun ma ba yanzu ba, idan yamin ramawa nake bana tsoron da. Bari na tafi gida Umma ta ce kar na daɗe. Nana ta faɗa ta miƙe da niyar tafiya har ta fara barin cikin palon sai ji ta yi Ameera na faɗin "Ke kinsan bana so ina magana ban ƙare ba mutum ya tashi zai ta fi, wannan ai raini ne, dan ubanki yaushe har na fara sakar miki ido har haka da ina miki magana zaki tashi ki tafi? To wallahi idan kika bar gidan nan to kar ki sake dawowa, idan kuwa na sake ganin ƙafarki a gidana Allah sai na karya miki su. Nana tayi mutuwar tsaye tana kallon Ameera cike da mamaki domin da farko ta yi tunanin wasa take yi sai yanzu da ta juyo ta kalli fuskanta sai taga yanda ta ke haɗa rai, kuma cikin fushi take maganar. Ganin haka Nana ta ce... "Haba Anty Meera Umma ce fa ta ce kar na daɗ..."Inji uwar ki itace ta ce haka? Idan baki barmini gida ba sai na ɓallaki banziya munafuka, ai dama nasan munafunci ya kawo ki gidan kuma kin gama. Jin haka Nana ta ƙara ɓude baki zata yi magana amma Ameera ta bita da gudu wanda yasa ta fasa faɗin abun da ta yi niyya ta yi waje tana ihuu! Sosai Ameera ta ji haushin abun da Nana tai mata, bata so a gwale ta haka, tana magana a tari numfashin ta ko a tashi a tafi ko aƙi sauraronta abun na ɓata mata rai sosai da sosai. Tun daga wannan lokacin Ameera ta ƙara zama masifaffiya ta bugawa a jarida, sosai masifar tata ta wuce gona da iri, domin kowa yazo gidan basa wanyewa lafiya, haka ma Adam ya kawo mata mai aiki amma tsabar masifa da bala'i mai aikin ta gudu da kanta, domin har duka take mata, shi kansa Adam yanzu bai cika zaman gida ba saboda rashin son zaman lafiya irin na Ameera. Kadija ta warke amma bata ƙara zuwa gidan ba domin ta ce idan kuka ganta a gidan to Ameera ta sauƙa ne. Yanzu haka Ameera ce ta ce da Adam dole ya ƙara samo mata ƴar aiki domin bazata iya komai na gidan ita ɗaya ba. Jin haka yasa shima ya ce "Sai dai ta nema da kanta amma Ameera ta da me shi da tashin hankali kala-kala har sai da ya je ya samo wata ƙaramar yarinya wacce kana kollonta kasan baƙauyiya ce, Adam ya yi hakan ne ko zata jure abun da Ameera ɗin za tai mata. yanzu haka cikin Ameera watansa biyar harda wasu kwanaki, kana kollonta zakaga ɗan cikin yayi kamar an kifa ɗan ƙaramin ƙwarya. Ya na kan hanyarsa ta dawowa daga gurin aiki ya ga yarinyar tare da mahaifiyar ta suna bara a kan trefik (kan titi) hakan yasa ya tsaya ya kirasu bayan sun zo ya basu sadaƙa sannan ya sanar da su cewar yana so ya ɗauki wannan yarinyar zata dinga ta ya matarsa aiki a gida. Jin haka yasa suka amince kasancewar ita uwar ba wai makanta ce tasa suke yin barar ba, domin kuwa idanunta ƙalau suke, haka ma ƙafadunta, su dai san dalilin su na yin barar, amma dai lafiya ƙalau suke, hasalima ba wani tsufa ita uwar yarinyar ta yi ba. Haka Adam ya sa su Amota har gidansa kafin ya sallami uwar ta koma gurin barnta shi kuma ya shiga cikin da yarinyar. Tun kafin ya shiga ciki yake tsoron abunda zai faru domin kuwa Adam yasan bata shiri da ƙazama ko yan ƙauye. Da sallama ya shiga cikin palon ita dai yarinyar sai binsa a baya ta ke tana kalle-kalle ganin haɗuwar palon da ta shigo. Ganin babu kowa a palon ne yasa ya nufi ɗakinta yana kiranta. Yana shiga ɗakin ya sameta ta a kwance riƙe da waya tana fama da karance-karance littafi, domin yawanci yanzu abun da ta ke yi kenan, idan kuma taso ayi zaman lafiya to Adam ɗin ne ke karanta mata ita kuma tana zaune ta hakince kamar sarauniya, idan baya yi da sauri ta ce ya dinga sauri idan kuma yayi a hankali nan ma tayi ƙorafi. Idan kuwa a kazo gurin dariya tsabar dariya har marinsa take yi wai duk a cikin dariya ne, sai tai ta dukansa tana ƙyaƙyata dariya kamar taɓaɓɓiya, sannan bai isa ya tsaya ya ce ya gaji da kansa ba sai dai idan har itace ta ce ya isa haka. Tana karanta littattafan marubuta da yawa amma tafi son littafin Khadija Candy da Batul Mamun da S Reza. Tabbas idai sun fitar da sabon labari to sai ta karanta domin tana ƙaruwa sosai da littatafan su, yanzu ma haka littafin Khadija Candy ta ke karantawa na *WANI GARI* , sosai karatun ya ɗauki hankalinta harma bata san ya shigo ɗakin ba. Har saida Adam yazo har kusa da ita kafin ta ɗago kai ta kalle shi. Ai kuwa cikin masifar ƙatse mata karatu da yayi ta fara faɗin. "Yanzu fisabililahi haka addini ya ce a shigo ɗaki babu sallama? Kana babba da kai amma har yanzu baka iya yin sallama ba idan zaka shiga guri, ni bana son irin haka dan Allah a koyi sallama kafin dai yara su taru su ɗauki irin wannan ɗabia'ar. Girgiza kai kawai yayi domin izuwa yanzu ya saba jin kalamai masu tsauri fiye da wannan daga bakinta. ya ce "Na samo miki ƴar aikin tana Palo ki fita ki ganta ni zan fita? Kasancewar tana cikin karatu yasa ta ce "Wai dai tazo gidan ba? To wani irin gani kuma zan mata, haba dan Allah wai mai yasa kullum Adam baka son ganina cikin farin ciki ne, saboda ka kawo ƴar aiki sai kawai na bar abun da na ke yi na zo ganinta wato itace ma matar gidan da har sai nazo na gai data. Tana faɗa ta ja tsaki ta koma ta zauna. Ganin bai ce komai ba ne kuma zai juya ya tafi cikin masifa domin bata so tayi masifa bai tanka mata ba, ta fi son ya dinga tanka mata yanda zata sauke masa na yau gaba ɗaya. Ta ce "Malam kazo ka fassara mini wannan yaran da wannan rayinyar take yi a cikin wannan littafin wai yaran Garuk ne. Ta faɗa tana zaune a gurin ta na jira ya zo gurin. Cike da dauriya Adam ya ce "Ban iya ba" yana faɗa ya juya ya bar ɗakin. Ai kuwa ta ce "Wallahi sai ka fassara mini kama isa ka ce baka iya yaran Garuk ba. Ta na faɗa ta biyo shi a baya da gudu har cikin palon ta miƙa masa wayar ta ce "Duba ka fassara min yanzu. Adam ya ce "Wai ke mai yasa baki da hankali ne ba kya ganin baƙuwa ne? Kuma na ce miki ni bamma san wani yare yaran Garuk ba bare ma har na iya fassara wa. Jin haka yasa Ameera kallon yarinyar da aka kawo mata a matsayin ƴar aiki, taso yin magana amma maganar da Adam ɗin yayi mata na cewar bata da hankali yasa ta ji zafi harma hakan ya nuna a fuskanta. Ganin haka yasa kafin ta yi magana Adam yayi saurin cewa "Wasa nake miki Honey kawo na fassara miki, ai yaran Garuk ana mana sabjet ɗin sa a school kuma na iya sosai kawo nagani? Ya miƙa hannu ya amshi wayar yana kallon fuskarta ganin ta na murmushi! "Yawwa ko kaifa wallahi littafin ya na min daɗi ne to kuma ina so naji abun da yarinyar take cewa a gurin ni kuma ban iya yaran ba. Adam ya karɓa ya karanta gurin ya kai sau biyar yana so yasan wani irin amsa zai bata wacce zata yi daidai da gurin. Ita kuma ganin yayi shiru yasa ta ce "Allasarki ba dai shi ma likitan zaginsa ta yi ba dai ko? Ta faɗa da alamar tausayi. Jin haka yasa Adam samun madafa cikin yanayin tausayi ya ce "Eh wallahi nima abun ne yake ta bani mamaki irin zagin da take masa, sosai fa ta dinga zaƙulo manya-manyan zagi kala-kala wanda haramunne ma kayi zagi da yaran Garuk da irin wannan kalmomin. Kai allasarki likita ya zagu? Ameera ta ce "Kai amma Waira bata kyauta ba shi da ya taimaka miki mai ye na zagi, ni har ma littafin ya fita a kaina. Ta na faɗa ta fita daga cikin littafin tana jin babu daɗi. Sai a lokacin ta kalli ƴar aikin ta ce "Wannan mai zubin abun tsoron ce mai aikin gidan nawa? Dubeta fa ka ga kamar ta shekara bata yi wanka ba. Cikin tsawa Ameera Ta ce "Dan ubanki ba kya yin wanka ne? "Cike da tsoro ta ce "I i ina ina ina yi! Ameera zata ƙara magana Adam ya ce "Please honey kiyi a hankali ƙaramar yarinya ce kibita a hankali. "Wannan ƙazamar zaka kawo mana gida Adam? Yanzu dan Allah kai sai ka yarda wannan yarinyar ta zama mai dafa maka abinci da share maka ɗaki da wanke-wanke? Ameera ta faɗa tana matsowa kusa da yarinyar harda toshe hanci. Ita kuwa yarinyar idonta ƙur a kan Ameera kamar mai kallon tv, sosai ta kafe cikin Meera da ido kamar mai gani har hanji, ita dai Ameera bata lura da kallon ƙurullar da take mata ba, shi kuwa Adam tsaf ya kulla harma ya fara tsoron irin kallon. Ganin har lokacin da Amera ta ke juya yarinyar bata daina bin cikin Ameera da kallon bane ya sa Adam saurin jawo da Ameera baya ya na cewa "Honey duk zata iya komai dan Allah ki barta. Ameera ta kalli yarinyar sai yanzu ta kula da fuskar yarinyar gata kyakkyawan gaske sai dai ƙazanta da ya bayyana a jikinta, Afili ta ce "Yaya sunanki? Yarinyar ta ce "Haura" Ameera ta kalli Adam ta ce "Meye kuma Haura kamar wani sunan yan kidnapping? Jin haka yasa Ameera bata sake cewa Kawai ba ta ce "Adam ya kai ta ɗakinta an jima zata kirata ta nuna mata aikace-aikacen da zata dinga yi, kuma tayi wanka yanzu! Shi dai Adam sai bin yarinyar da kallo ya keyi yana ta nazarin ta, sosai wani ɓangare daga zuriyar sa ya ke ƙoƙarin ƙin yarda da yarinyar. Bayan ya kaita ɗakin ne ya nuna mata komai da zata dinga amfani da shi harda toilet da dai komai, bayan ya gama nuna mata ne ya fito sai kuma wata zuciyar ta ce ya ɓoye ya ga wani abu yarinyar zatayi son tabbatar wa ya laɓe daga jikin ƙofa ta baya yana kallon yarinyar. Gani yayi ta zauna a kan gadon ta ɗaga kanta sama tana ta juya idanunta farare a saman ɗakin. Yana tsaye yaga ta miƙe kamar zata fito sai kuma yaga ta ƙara komawa ta zauna, ta daɗe a haka kafin ta miƙe ta shiga toilet, yana dai tsaye sai gata ta fito tsirara aihuwar uwarta, gashin kannan nata sun zubo mata har gadon baya sun zana kamar ba nata ba. Kallo ɗaya Adam yayi mata ya ɗauke kansa yana jin wani faduwar gaba, babu shiri ya juya ya bar gurin yana ɗan ƙoƙarin danne yanayin da ya shiga, sai haɗa hanya ya ke yi yana waigen baya kamar yarinyar ce ta biyo shi. Misalin biyar na yammacin ranar Ameera ta je har ɗakin Haura ta kirata lokacin Adam baya gida. Zama ta yi a kan kujera ita kuma ta nuna mata ƙasa ta tsuguna kafin ta ce "Ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurareni, kar sai na gama kice baki gane wani abun ba. Kafin nan wannan kayan karki ƙara mayar da su, an jima ko gobe za'a sayo miki kaya suma koda an kawo miki ba'a maimaita kaya sau biyu kina jina ko? "Eh" . Da farko dai kin iya girki? Haura ta yi shiru kafin ta ɗaga kai. Ameera ta ce "Dan ubanki magana za ki yi ba ɗaga kai ba. Cikin sanyin murya ta ce "Eh ina yi" "Ok to daga yau girkin gidannan safe rana duk kece zaki yi, bama yin girkin dare, sannan kullum zaki share gidannan gaba ɗaya ki yi mofin ɗin ko ina, ki shiga ɗakuna suma ki gyara su, sannan bana son zama da ƙazanta kullum wanka sau uku safe rana da yamma, kina dai jina ko? Haura ta ce "Eh ina ji" Ameera ta sake cewa "Kin iya karatu da rubutu ko? Haura ta ce "Wani irin rubuta da karatu? Cikin rashin fahimtar tambayar Ameera ta ce "Rubutun Hausa da na Turanci mana. "Na iya na Hausa da na garinmu amma ban iya na tauranci ba. Ameera ta ɗan ƙura mata ido ganin yadda ta kira turancin da tauranci. Ta so tambayar ta wani yarene na garin nasu amma tsabar jin kai yasa ta ce "To tunda kin iya na Hausa ai shikenan. Yanzu tashi ki shiga kicin ki dafa min indomin naji ko kin iya girki. Sannan ina ƙara jaddada muki wallahi wallahi Karki yadda na sameki da munafunci ko ƙarya ko gulma ko ha'incin. Tana faɗa ta buɗe wayarta tana shiga domin fara karatun sabon littafin da ta siya ɗazu na littafin *UWATA CE SILA* na S-Reza. Ko fara karatun ba ta yi ba tana dai karanta jawaban marubucin ne kafin a shiga cikin littafin sai ji tayi ance Anty na gama. Cike da mamaki ta ke kallon indomin wanda sai tiririn zafi haɗi da wani irin ƙamshin daɗi ke fita daga cikin sa. Sosai take kallon Haura ka na ta kalli abincin. Lokaci ɗaya ta ji abincin ya shiga ranta sai ta fasa faɗin abun da taso faɗin kawai ta ɗauki indomin zata fara ci, sai kuma ta kalli haura ta ce "Ɗauki wannan wayar ki dinga karanta min wannan littafin afili ina saura? Ganin bata ɗauka bane yasa Ameera daka mata tsawa ta na cewa "Dan uwarki bada ke nake magana bane? Da sauri Haura ta ɗauki wayar ta ƙura mata ido. "Wai dan ƙaniyrki ina wasa da ke ne? Bazaki fara karatun bane sai na watsa miki wannan abinci? Ta faɗa daidai lokacin da daɗin abincin ke ratsa ƙwaƙwalwarta. Cikin muryar kuka Haura ta ce "Ban iya ba! Cike da mamaki Ameera ta ce "Baki iya me ba? "Karatun" Haura ta faɗi iya gaskiyarta. Cikin tsananin mamaki da rainin hankali Amera ta ce "To dan hancin uwar ki mai yasa da kika ce min kin iya? Haura ta ce "Wannan ne ban iya ba. Ta faɗa tana nuna wayar. Tsabar haushi da takaici yasa Ameera faɗin "To wannan ɗin yaran ubanki ne, ba kece kika ce Hausa kawai kika iya ba, to wannan menene? Haura ta ce "Ai wannan ba Hausa ba ne" Sai a lokacin Ameera ta ajiye abinci ta lailayo wani abun zagi da jin sama zunubi ne ta makawa Haura kafin ta jawo ta ta kwaɗa mata wani lafiyayen mari kafin nan ta ce "Idan ba Hausa bane da yaran ubanki S Reza yake rubutun littafi? Cikin jin zafin marin da yasa saida ta fashe da kuka ta ce "Wallahi ba Hausa bane wani yaran ne da ban, kuma ki duba ki gani. Tsabar takaice sai da ta ƙara mata wani marin har tana ture ta kafin ta duba wayar da nufin dubawa. Cikin tsoro da mamaki haɗi da firgici take kallon littafin da ta siya da rubutun Hausa amma yanzu ya koma wani irin rubutun da bata san ma ko na ina bane. Ga dai sunan littafin da Hausa amma komai da wani irin yare yake wanda bata ma san ta ina zata fara karantawa ba. Ta ke kuma ta yi wani tunani. Ɗazu kafin haura ta kawo mata abinci fa ta fara karanta jawaban marubucin na cikin littafin kuma da Hausa ya ke amma yanzu harda su ɗin sun koma wani yare da ban, sannan shi kansa abincin kamar bata yi minti biyu ba ta dawo wai ta gama, sannan kuma ita dai bata koya mata amfani da kicin ɗin ba duba da yarinyar kamar bata taɓa amfani da irin wannan kicin ɗin ba. Sai a lokacin ta kalli Haura ganin tana kuka ta daka mata tsawa ta na faɗin "Dan ubanki wacce ke? ina kika shiga min da littafina? Ni zaki rainawa hankali, yanzu na fara ƙaranta littafi lami lafiya daga zuwanki sai ya koma wani abun kamar yaran chana! Ina kika shiga min da littafi kuma wacce ke na ce!? Ameera ta ƙara sa maganar cikin ihu da ɓacin rai! Haura ta ce "Wallahi Anty nima haka na gan shi ban san yaya a kayi b, kuma ni ba kowa ba ce Haura c... "Kafin ta ƙara sa sai ji kayi tass ta ɗauke bakin nata da mari. Ameera ta fita daga cikin littafin ta sake komawa, amma dai har yanzu haka yake, take ta kunna Data ta shiga Whasopp domin sake yiwa mai littafin magana ya turo mata wani. Ko da ya turo mata shima dai wanda ya turo mata ɗin haka ne. Hakan yasa ta tambaye shi wai da wani yare a ka rubuta littafin Uwata ce sila? S Reza yayi dariya ya ce "Ban gane ba Haujiya Ameera Ai da yaran Hausa nake rubuta duk littatafai na. Bata ƙara cewa komai ba ta sauƙa a online ta ce da Haura wannan wani yare ne? Ta kafe ta da ido. Haura ta ce "Nima ban sani ba. Cikin takaicin da yazo mata har wuya ta kamo haura ta fara jibgarta kaman an aiko ta, ta na faɗin "Karya keke tsinaninya wallahi kinsan komai wani guri kika shiga a wayar da rubutun ya zama haka kuma sai kin mayar min. Ana cikin haka sai ga Adam ya shigo gidan shima tun da ya fita yake ta nazarin yarinyar, sannan ga surar yarinyar da ya gani ya tsaya masa a rai, sosai yaso ace ya tsaya ya ƙare mata kallo amma ya kasa. Yanzu haka da sauri ya shigo gidan kasancewar tun daga waje yaje jin ihuu Haura...✍️ *Kubi S-Reza a hankali, salon na daban ne* *One love* 💘 *One house* 📚 *Comment's🤝* *Shering please 👏* *Love my All fan's 🥰* *S R-eza typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* *6* *By S-REZA✍️* *PAGE 6️⃣* ....Da sauri Adam ya riƙe Amera da ke ƙoƙarin yin kisa. "Lafiya kike kuwa Ameera? Baki da hankali ne idan kika kashe musu yarinya fa, daga kawo yarinya har zaki naimi hallaka ta. Adam ya faɗa ya na ɗago Haura dake durƙushe ta na kuka. Ita kuwa Ameera dama kaɗan ta ke jira, kafin Adam ya ƙara sa har ta yi tsalle ta shiga tsakaninsu da Haura. Cike da gadara da nuna isa ta ce "Honey wallahi wannan yarinyar bazata zauna a cikin gidannan ba domin ban yarda da ita ba. Cike da mamaki ya ce "Me ya faru? Ameera ta fara magana cikin ɗacin rai da takaici ta na jin yau sai ta nakasa wannan yarinyar. "Daga cewa ta dafa min indomin ɗazu wallahi ko minti uku ba'ayi ba wai har ta dafa, sannan yanzu na ce ta karanta min littafin da na siya ɗazu wai daga bata waya sai rubutun ya koma wani yare da ban? Ameera ta ƙara sa maganar da wata iriyar murya. Cike da tsoro Adam ya ce "Ina indomin da littafin? Sai a lokacin suka kalli gurin da kwanon abincin ya ke, amma wayan babu abincin a cikin kwanan. Cike da sabon tashin hankali Amera ta kalli Haura ta kalli kwanan abinci ganin da gaske babu komai a ciki, ita dai tasan cokali uku tayi kawai a abincin. "Ina abincin ya ke? Ameera ta tambayi Haura cike da dakiwa alamun babu wasa. Cikin muryar kuka Haura ta ce "Ba ke ce kika cin ye ba ɗazu. Take Ameera ta lailayo wani ƙatoton zagi ta makawa Haura haɗi da faɗin "Ubanki ne ya ce miki nine na cinye? Ina ce yanzu kenan na fara cin abincin kika mayar min da littafin wani abu da ban, shine yanzu zakice ni ce na cinye. "Kunga yanzu dai duk ku dagata" Adam ya faɗa bayan ya gama jin duk abinda kowa ya ce. Sosai ya ke ta nazarin yarinyar ganin tana yin komai a nutse ne yasa bai ta da hankalinsa ba. "Yanzu ina wayar da rubutun ya koma wani iri ɗin? Da sauri Ameera ta miƙa masa wayar ta na faɗin "Wallahi ko rubutun aljannu ma iyaka kenan. Adam na ƙarɓa ya ce "To ai ga shi rubutun Hausa ne ba na wani abun ba. Ya faɗa yana miƙa mata wayar. Cike da tsoro ta ƙarɓa tana kallon komai na Hausa a cikin littafin. Adam ya ce "Duk kinzo kin tashi hankalin mutane bayan a she kece ma baki duba ba da kyau ba, ni wallahi na rasa gane miki Honey kullum sai sauyawa kike yi kamar wata wa hainiya, please dan Allah ki bari ku zauna lafiya da wannan rayinyar bata da wata matsala. Adam na gama faɗa ya kama hannun Haura ya tafi da ita ɗakinta ya na faɗa mata cewar sai ta yi haƙuri da Ameera wannan cikin ne duk ya mai data haka, da zarar ta sauƙa in sha Allah komai zai dawo daidai. Ita dai Haura sai sun kuyar da kai take yi ta na sauraron sa har suka iso ciki ɗakin nata. Kallonta ya yi da kyau daga ƙasa har sama yana tuno ganin da yayi mata tsirara. "Gobe idan Allah ya kaimu za'a sayo miki kayan sawa kin ji? Ba tare da tayi magana ba ta ɗaga masa kai. Juyawa ya yi ya bar ɗakin ya nufi gurin Ameera. Tun daga nesa ya hango ta ta na zazzagawa a cikin palon ta je nan ta dawo nan , kallo ɗaya ya mata ya nufi ɗakinsa bai ko bi ta kantaba. Ya na shiga ya shiga cire kayan jikinsa ya na cigaba da tunanin lamarin Ameera da Haura. Sai kuma ya ɗan saki murmushi yana jin anya kuwa Ameera bata fara ganin biyu-biyu ba kuwa. Ya na cikin wankan yaji an banko ƙofar da ƙarfi kamar za'a ɓalla ta. Tsaye yayi yana kallon ta itama ta na kallonsa cikin ido, tsabar masifa da ke cikinta har wani jaa fuskarta ta yi, shi kansa Adam sai da ya tsorata da ganin fuskar tata. Cikin tsawa da ɗaga murya Ameera ta ce "A ina ka samo wannan yarinyar!? Adam ya haɗiye wani yawu haɗe da ruwa a lokaci ɗaya sai ji kake maƙot. Tsabar rike cewa ma ya kasa cewa komai jin yayi shiru ne yasa ta sake daka masa wata tsawar kamar wata uwar sa. "Na ce a ina ka samo wannan tsinaninyar yarinyar da har ina magana zaka riƙe hannunta ku tafi ka barni a tsaye? Ta ƙara sa tana nuna masa wuƙar da ta ɓoye a bayanta tun ɗazu. Adam ya ce. "Am am kinga honey dan Allah a jiye wuƙar muyi magana please... Kafin ya ƙara sa ta kai masa yanka yayi saurin sun kuyawa yana zaro ido ganin fa da gaske ta ke yi. "Honey please tsaya kiji wallahi ba abun da kike tunani ba"...Nan ma bai ƙara sa ba ta ƙara kai masa wani yankan ta na kuka. Ganin haka yasa Adam saurin riƙe hannunta mai wuƙar yana jawo ta jikin sa. Ita kuwa Ameera ganin haka yasa ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana so taga ta luma masa yasan da gaske take. Da ƙarfi Adam yake so ya ƙwace wuƙar amma saboda ba riƙon wasa tai masa ba yasa ya kasa ƙwacewa kuma idan ya dage wani zaiji ciwo a cikin su, hakan yasa ya jawo ta jikin ƙofar ya buɗe yayi waje a guje, itama tabi bayan sa cikin gudu. Bai ma san ina ya nufa ba a cikin gidan shine naiman mafita yake yi, tsabar gudu har yana zamewa a palon ya faɗi, hakan ya ba Ameera damar kamashi, tazo kusa dashi itama ta zame sai kawai ta nifo kansa kuma wuƙar tana hannunta kuma bata nufi ko ina ba sai cikinsa kasancewar ta reƙe wuƙar a tsaye ne tana gudu. Ai kuwa tana faɗa wa sai a kan sa wuƙar bata tsaya ko ina ba sai daidai wuyan Adam Kasan cewar yayi ƙoƙarin kwacewa sai bata sauƙa a cikin ba sai wuya, kafin ka ce me sai jini ya fara tsalle yana malale palon. Cikin sakan ɗaya Ameera ta dawo hankalinta kallon yadda jine ke fitowa daga jikin mijin nata tayi ga kuma babu komai a jikinsa tsirara ya ke. Da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauko masa wanda wanda tsabar sauri da ruɗewa ma bata san sket ɗinta ta ɗauko ba. Ta na isowa gurin taga Haura a gurin tana kuka ta ɗora hannunta a kan gurin ciwon kuma jinin ya daina fita. Da ƙarfi ta chakumeta ta falla mata wasu lafiyayyun maruka guda uku kyawawa sannan ta ce "Ba kya ganin ko kaya babu a jikin sa ne da zaki zo ki tsaya a kansa haka dan uwarki. Ganin Adam na ƙaƙarin mutuwa ne yasa Ameera saurin saka masa sket ɗin, sai a lokacin ta lura a she wani baƙin sket ɗinta ne ma, ai kuwa bata ko tsaya sauya masa ba ta saka masa haka sai kuma ta kalli Haura dake tsaye riƙe da kunci, ta ce "Me kika masa jinin ya tsaya? Haura dai sai bin ta da kallo take yi. "Ba dake nake magana bane? Ameera ta sake faɗa cikin ihuu! "Addu'a nai masa" Haura ta faɗa cikin kuka. Jin haka yasa Ameera cewa taje waje ta kira mai gadi. Ai kuwa take mai gadi ya zo wanda shi kaɗai ya kama Adam ya kaishi mota sannan Amera ta ja mutar izuwa asibiti duka bar Baba mai gadi da jimami da mamaki. Suna tafiya Haura ta shiga gyara gidan abisa umarnin da Ameera ta bata, sosai ta wanke gurin da jinin ya ɓata, sannan sai yanzu ta shiga ko ina dake cikin gidan, ta tsaya ta ƙarewa komai na gidan kallo tana mamakin duk abinda ta gani. Sosai ta baiwa idanunta hakkinsa wajen kallon sabbin abubuwan da bata taɓa gani ba. Tana cikin haka idanunta ya hango wani hoto a palon, da sauri ta ɗauko ta na kallon mutanen cikin hoton. Adam ne da Ameera sun sha kayan ƴen booll riga da wando koraye sun yi kyau sosai wanda Adam ke riƙe da hannun Ameera suna sakarwa kan su murmushi, kallo ɗaya za kai musu kasan suna cikin farin ciki, take yanayin da ta gan shi ɗazu ya dawo mata, sai kawai yanzu ma take kallonsa kamar babu kaya a jikinsa, take ta kai hannu ta na shafa daidai gurin a hoton . Ta daɗe a haka kafin ta mayar da hoton ta koma ɗaki tayi zamanta tana jiran tsammanin warabbika. Cikin ikon Allah a ka wanke masa gurin a kai masa ƙaton bandeji wanda hakan yasa dole sai a asibitin suka kwana daga ita har shi ɗin. Washegari da sassafe ta nufo gida domin ɗaukar musu abinci. Ta na shiga ta fara kiran Haura. Da sauri Haura ta fito daga cikin ɗakinta ta na amsawa. Kallonta Ameera ta yi ta ce "Zan shiga wanka yanzu ki tabbatar kafin na fito kin gama haɗa min komai na abinci? Haura ta amsa da to. A gurguje Amera ta shirya cikin wata ɗinkin doguwar rika Wanda kallo ɗaya za kai mata kaga hango ɗan ƙaramin cikin nan nata ya leƙo kai, mayafi mai kalan rigar ta yafa sannan ta sauƙo cikin sassarfa. Ta na zuwa ta tarar da Haura ta gama komai tana tsaye tana jiranta. "Me keka dafa? Ameera ta tambaya tana kallon kulolin abincin. "Abun da kika fi so na dafa" Haura ta faɗa da murmushi! Cikin mamaki Ameeran ta ce "Ni yaushe na faɗa miki kalan abincin da nafi so? Sannan ma wani abinci ne? Ameera ta faɗa cike da tsan-tsar mamaki. "Kin manta jiya kin faɗa min" Ta faɗa tana dariya a karo na farko tun da tazo gidan. Kafin Ameera ta sake cewa Kamai Haura ta ce "Anty ya jikin nasa? Sai a lokacin ma Ameera ta tuno da abun da ta kwana da shi a ranta. Ta ce "Jiya kin kalli jikin sa ne lokacin da yake tsirara? Ameera ta faɗa domin tun jiya abun ya tsaya mata a rai, tana da kishin mijinta, har ƙara ma ace ita Haura ta gani tsirara ba Adam ba. Ita kuwa Haura da bata kawo hakan komai ba cikin ƴar dariya da take yi tun ɗazu ta ce "Allasarki koba jiya da babu ko kaya a jikinsa ba, nayi mamakin ganin zaki kashi shi ko ba kyau son sa ne? Hauran ta faɗa har yanzu tana dariya. Da sauri Ameera ta ɗago kai tana kallonta. Ta ce "Kenan kinga jikinsa? Haura ta ce "To mutumin da babu komai a ji kinsa ai dole a ga jikin sa" "Gabansa nake magana kin gani? Ameera ta faɗa tana aiyana abun da zata mata idan tace ta gani domin wallahi tazo iya wuya. Sai yanzu Haura ta gane nufin ta, lokaci ɗaya ta tsayar da dariya da ta keyi ta sunkuyar da kai ta ce "A'a ban ga komai ba" Ameera ta sauke a jiyar zuciya ta ce fine for me and you. Sai kuma ta ce "Ɗauko abincin ki biyo ni mota da shi. Tana faɗa ta wuce riƙe da jaka a hannu. Bayan Haura ta gama saka kayan a mota ne zata koma gida amma Ameera ta ce "Shigo motar mu tafi tare. Babu musu ta buɗe mai zaman banza ta zaune suka ɗauki hanyar asibiti.Sun zo daidai gurin da mamarta suke zama bara ne ta hango mamar tata cikin ƴan uwansu mabarata. Kaman tayi wa Ameeran magana amma tasan bama zata iya ba. Daidai lokacin taji Ameera ta taka wani aban burki tana sakin ƙara. Ji kake ƙuuu! Da sauri ta fito daga cikin motar ta nufo gurin da ta kusa bige yaran mai sayar da ruwa da su biskit da abubuwan sha. Ta na isowa gurin ta kamo yaran ta sauke masa mari wanda hakan yasa kowa dake gurin ƙarasowa domin tun lokacin da ta taka burki hankalin kowa ya dawo gurin su. Haura kuwa tana ganin haka ta fita tayi gurin mamarta. "Haba baiwar Allah me ye kuma na duka tun da Allah ya kiyaye ai sai dai muyi godiya Allah ya ƙara kiyaye wa ba sai kin dake shi ba. Ameera da yaron nan ya gama tsoratata ganin yadda ya shiga gaban motar ta har sai da hajjin cikinta ya kaɗa tsabar tsoro. "An dake shi ɗin, na ce an dake shi ɗin, yanzu da na bige shi da kune zaku fara zagina kuna cewa ban iya tuƙi ba, amma yanzu saboda na dake shi zaka wani zo kana maganar banza. "Ayi hakuri dai Hajiya yaro yayi kuskure. Ameera ta ci gaba da zagin yaron kamar zata ari baki, an bata haƙuri taƙi tafiya sai wani ya ce "Wai ke sai ka ce ba musulma ba fisabililahi! An ce kiyi haƙuri an haɗa ki da Allah amma kamar wacce ake ƙara tunzurawa, ko dai ba'a san Tauhidi ba ne? Mutumin ya faɗa yana mai jin haushin yanda ake ta fata haƙuri taƙi haƙura. Ai kuwa ta yi caraf ta ce "Kafura mara sanin Tauhidi tana gida zaman Allah bamu, idan Kafura kake nema ka je gurinta, wawa mahaukaci, an min laifi ba zan fito na faɗa ba.. kafin ta rufe baki mutumin ya ce "Wallahi kin ci darajar wannan cikin dake jikinki amma da nasa yara sun lakaɗa miki na jaka anan banza mara tunanin da haƙuri, yana faɗa ya bar gurin dalilin mutane dake ta bashi haƙuri. Haka Ameera ta dinga zagin mutumin har ta shiga mota, daidai lokacin Haura itama ta dawo, ba tare da ta ce mata komai ba ta ja motar suka bar . Koda suka isa asibitin cikin fushi ta ce da Haura ta ɗauko abincin ta biyo bayan ta. Ta na tura ƙofar palon taga Kadija da Najib zaune a kusa da shi Kadija na ba shi abinci a hankali. Ko sallama bata tsaya yi ba tsabar masifa da fushin da ta kwaso, sosai ranta yayi mugu-mugun ɓaci, ita ta tafi gida domin kawo masa abinci shine har wasu zasu kawo masa ya ci wato ita ta gaza ko...?✍️ Bana ganin comments fa? Ko dai a tsaya da labarin ne? *One love 💘* *One house 📚* *Comment's 🤝* *Shering please👏* *Love all my fan's🥰* *S-Reza typing....✍️* *AMEERA DA ADAM* *7* *By S-REZA✍️* *PAGE 7️⃣* ....Wani ƙatoton zagi ta lailayi ta maka ta na isowa gurin ta ture abincin gaba ɗaya ta na faɗin "Dan uban mutum yaya za'ayi ni na je gida ina haɗo wa mijina abinci amma kafin na dawo sai kawai wata ta zo ta na baka babu dalili. Ceke da mamaki Najib da Kadija ke kallon ta ganin ko sallama babu sai zagi kamar wata jikar maguzawa. Najib ne ya yi ƙarfin halin faɗin "Madam sannu da isowa" Bata ko bi ta kansa ba ta shiga haɗa wa mijinta abinci ta na yi ta hararan Kadija da har yanzu bata ce komai ba, domin tun kafin su fito Najib ya ja mata kunne a akan kar ta biye mata domin ita bata da lafiya, hakan ne yasa ta zuba mata ido tana ta kallon ikon Allah. Shi dai Adam ya na kwance wuya a ɗaure ko magana idan zaiyi bata fita. Itama Haura ta tsaya shiru kai a sunkuye kamar munafuka. Ganin haka yasa ta gai sar da Najib da Kadija, suma suka amsa ba tare da sun ƙara cewa komai ba, sai dai suna ta kallon yarinyar. Cike da kuzari ta buɗe kulan abinci har ta na jan tsaki domin taƙi buɗuwa da wuri. Cike da tsan-tsar mamaki take kallon abincin. Ai bata tsaya wata-wata ba ta juya ta cafko Haura ta ƙunduma mata zagi haɗi da mari ta na faɗin. "A gidan uwarki na ce ki dafa min ɗan wake? Ta ya ya honey zai iya cin wannan abun shi da ke ciwon wuya? Haura ta shiga bata haƙuri tana faɗin "Wallahi Anty kece kika ce min kina son ɗan wake shine yasa nayi. Jin haka yasa Ameera ƙara arziƙa ta na cigaba da marinta. Ganin haka yasa Najib saurin ta shi ya na bawa Ameera haƙuri akan ta dai na dukan yarinyar. "Malam babu ruwanka ban saka da kai ba pls ka fita a sabga ta dan Allah na roƙeka!. Ta ƙarasa tana haɗa hannayenta a lamar roƙo, Ameera ta faɗa ba tare da ta ko kalli inda yake ba. Cike da mamaki Kadija ta ce "Kai ma wa ya kaika yarinyar da yanzu kowa yasan bata da hankali ai kawai ka bari ta kashe ta kaga sai burinta ya cika. Tana rufa baki Ameera ta shaƙo mata wuya ta fara faɗin Ubanki da uwarki sune mahaukata ba niba Kadija, wallahi ku fita a idona ina faɗa muku munafukai ƴan gulma kuma wallahi ba zai ci abincin naku ba. Ganin haka yasa Najib ƙwatar matarsa wacce har ta fara ƙaƙarin amai. Sannan ya ce su tashi su tafi ba zai iya da wannan masifar ba. Amma Kadija ta ce bazata tafi tabar yayanta a hannun wannan mahaukaciyar ta kashe mata shi ba. Ana cikin haka likitan da ya masa aikin ya shigo yana tambayar lafiya dai ko. Kafin kowa yayi magana Haura ta yi saurin cewa "Wallahi ba ni bace na soka masa ba itace ta caka masa wuƙa ɗazu wallahi babu ruwana. Ta ƙara sa tana ɓoyewa a bayan Najib saboda tsoron likitan da ta gani sanye da fararan kaya. Chak ɗakin yayi kowa ya mai da hankalinsa kan Ameera wacce itama taji maganar daga sama. Ita har ga Allah ta manta da cewar ita ta caka masa wuƙar, sannan ita bata yarda cewar itace ba. Kadija ce ta fara magana cikin babbar murya ta na faɗin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un! Yanzu dai kowa ya yarda da cewa wannan yarinyar mahaukaciya ce ko? Kuduba ku gani itace ta caka masa wuƙa sannan ta hana a bashi abinci wai a hakan matarsa ce, to wallahi bazamu bari ba, haka kawai ki bijiro da sabon hauka dan kawai kinyi ciki, ko a kanki a ka fara ɗaukar ciki ni banga wani amfanin ki a rayuwar Yaya ba kawai a rabu kowa ya huta da irin wannan abun, ai watarana kawai kashe mana kai zatayi. Kadija ta ƙara sa maganar tana zuwa kusa da Adam wanda ke kwance yana kallo da saurare. Da sunsan abun da yake ji da sun taimaka sunyi shiru, da sunsan abun da ke damun sa da kowa ya ja bakinsa yayi shiru. Najib ne ya fara tambayar Haura a kan tabbatar magar, Haura ta ƙara tabbatar masa, sannan ya kalli Ameera da tun ɗazu ta shiga tunani ya ce "Da gaske kece kika caka masa wuƙa? "Ameera ta kalli Haura sai taga kamar tai mata gwalo, amma da ta kalleta da kyau sai taga kanta a ƙasa a fili ta ce "Wai mai kuke nufi? Saboda yarinya tazo ta ce na caka masa wuƙa shine zaku yarda, to ai ga Adam din ku tambaye shi mana, to ba cake masa nayi ba, faɗuwa mukeyi ni da shi lokacin wuƙar tana hannuna shine ta same shi, amma ni ban caka masa ba. Kuma ita yarinyar da tayi maganar ai bata gurin yaya a kayi tasan nice. Ganin Adam na motsi da kai alamar magana yasa likitan cewa kowa yayi shiru. Ita dai Haura sai bin bayan Najib ta ke yi. Likitan ya ɗago daga sauraron Adam dake magana a hankali ya ce "To yace dukkanku ku tafi gida a bar iya Najib. Likitan ya faɗa yana kallon Najib wanda yasan shine Najib ɗin domin shine kaɗai na miji a ciki. Cikin tsananin mamaki Ameera take kallon Adam wanda ya kafe ta da ido. Afili ta ce "Hardani za'a tafi a barka? Adam ya gyɗa mata kai. Ai kuwa bata ƙara cewa komai ba ta kalli Haura ta ce kwaso mana kaya. Take Haura ta kwashi kaya suka fita. Sosai ranta ya ɓaci da abun da Adam yayi mata, wai ita Adam yake kora saboda abun da ya faru, ita da yayi wa laifi amma itace mai laifi. Kallon Haura ta yi ta ce "Ke yarinyar nan a kwai ayar tambaya a kanki! Bari muje gida wallahi yau sai kin sanar dani uban waye ya turoki gidan nan kuma me ya kawo ki. A wani ƙaramin gurin sayar da kaya ta tsaya suka shiga tare ta ce ta tsaɓi kayan guda shida riga da wando sai hijabi guda uku da taƙalma guda uku sai mayafi. Haura ta ce "Ai mu bama saka hijabi" da mamaki Ameera ta ce "Me yasa? Haura ta sake cewa "Ai mu ba musulmai ba ne addininmu da ban da naku" Ameera ta ce "To koma meye daga yau zaki koma addininmu na Musulunci in dai kina son zama damu. Sannan ma ku wani addini kuke yi? "Addinin garin Garuk " Ameera ta yi shiru tana son tuno a ina ma ta taɓa jin gari mai irin wannan sunan, ganin ta kasa ganowa ne yasa ta ce "A wacce ƙasa? Haura ta ce "Nigeria mana" Ameera bata ƙara cewa komai ba har suka iso gurin biyan kuɗin, ta miƙa ATM ɗinta aka cere sannan ta juya suka fara tafiya. Kaman daga sama taji ana kiran sunanta "Anty Meera. Da sauri ta juyo tana kallon mai kiran nata, cikin mamaki take kallon Nana da Nasiru riƙe da hannun juna suma sun fito daga gurin kayan. Da sauri ta ƙara so tana kallon Haura tana neman ƙarin bayani. Kafin suyi magana Ameera ta fara kallon hannunsu dake cikin na juna ta ce "Nana dan ubanki wannan mijinki ne da har zai riƙe miki hannu? ke kuma gaki ƴar daɗi soyayya kina ganina ma ko a jikinki ko, shi kuma babban ɗan iskan harda ƙara danƙe hannun ko? Ameera ta ƙara sa tana zabga wa Nasiru harara domin ita har ga Allah bata son ƙanwarta da wannan yaron kawai ita baya burgeta. Nasiru yayi saurin sakin hannunta wanda gaba ɗaya ma shi mantawa yayi. Itama kanta Nana bata ma lura da hannunsu na cikin na juna ba har sai da Ameera ta yi magana. "Ku dai wallahi kun ji kunya ace kuna ƴaƴan musulmai amma kuma ɗabi'un arna, kalleka kamar mutumin kirki a fuska ashe ƙaton ɗan iska ne, ke kuma wallahi idan kika sake riƙe hannun wani ƙato wallahi sai Abba yaji kuma Nima sai na ci ubanki. Da sauri Nana ta ce "Anty Meera mana" Ta faɗa tana kallon yanda Nasiru ya sauya fuska, ita tasan halin kayanta bashi da haƙuri ga zuciya, kuma yanzu gaba ɗaya suran nasu wata ɗaya ne da kwana biyu. "Idan kika ƙara magana Allah sai na mareki, banziya mara wayo, an faɗa miki su maza abun yarda ne a irin wannan lokacin, bar ganin wai an kusa auran ku, to idan da gaske ne ya bari ayi auran mana gaba ɗaya. Jin haka yasa Nasiru saurin cewa. "Na gode Nana dama kin kawo ni nan domin a ci min mutunci ko, to na gani na gode. Nana ta ce "No Nasir please ka tsaya kaji. Tayi maganar kamar tayi kuka. Da mamaki Ameera ta jawo ta ta na faɗin "Amma dai ke anyi lalaceceyar yarinya, a kan wannan ɗan iskan yaran kika son yin kuka, yaran da baya jin kunyar taba ki a cikin mutane. Da ƙarfi Nasiru ya ce "Ƙarya kike muna fuka, Karki ƙara kirana da ɗan iska, aure ne ya kawoni gurin ƙanwarki ba iskanci ba idan iskanci na da ba'a zo wannan matakin ba. Kuma wallahi ki san irin maganar da zaki dinga furta min ni ba ƙaninki ba ne, dan ina neman auran ƙanwarki ba shi zai sa na tsaya ina kallo ina cimin mutumci ba. Cikin masifa da rashin control ɗin kanta Ameera harda hawaye ta isa gaban Nasiru wanda a girme zai iya girman ta amma ta daga hannun ta sauke masa lafiyayen mari ta cigaba da faɗin. "Ƙaryane ba lalata ɗin zaka yi ba? dama ku haka munafukan samarin nan kuke ba kwason gaskiya kuma wallahi sai na faɗa kai ɗin banz..."Bata rufe baki ba taji sauƙar mari mai lafiya daga kumatunta na dama wanda hakan yasa ta tsaya tsit. Kafin kace me itama Nana ta ɗaga hannu ta saukewa Nasiru mari mai kyau. Tsit kowa yayi yayin da Nasiru ke kallon Nana cike da mamaki, itama Ameera Nana take kallo a lamar ba zata ƙara masa ba. Nana ta yi ƙarfin halin cewa "Haba Nasiru ko dan wannan cikin dake jikinta ai ka raga mata ko badan niba Please dan Allah kayi haƙur. Nasiru ya ce "Nana ni kika mara akan gaskiya ta? Nana ta haɗe hannu tana bashi haƙuri. Nasiru ya ce "Wallahi Nana ko kece autar mata na fasa auran ki, kije ku zauna da yayar taki. Yana faɗa ya bar gurin cikin ɗacin abun da ya faru bai ko tsaya sauraron yanda Nana ke rokon sa ba. Ameera ta ce "Kinga shiga Mota mu tafi manta da shi dama wallahi bai da ce da ke ba, dubeshi ba mara kunya ga shi ɗan iska. Jin haka yasa Nana faɗin "Dalla Malama sakar min hannu, wallahi nayi dana sanin haduwa da ke a nan gurin. Tana faɗa tabi bayan Nasiru da gudu. Ameera ta yi mutuwar tsaye tana kallon Nana. Sai lokacin ta juya bata ga Haura ba, hakan yasa ta ƙara sa motar ta sameta zaune tana kallon waje. Da sauri Nana ta riƙo hannun Nasiru wanda take bashi haƙuri amma juyowar da zaiyi ya sauke mata mari. Ya ci gaba da cewa "Daga yau karta ƙara nuna tasan shi, kuma zai tura a ƙarɓo masa kayan sa domin ya lura ashe gidan su babu tarbiyya, Allah ma yasa tun kafin ya aura aka nuna masa ya godewa Allah. Nasiru ya juya zai tafi Nana ta ƙara cewa "Wallahi Nasiru Anty Meera bata da matsala bansan mai ya mai data haka. Nasiru ya ce "To ni dai ba zan tsaya ana cimin mutumci a ban zaba, to ko uwar yarinyar da zan aura ta isa ta min wannan cin kashin na barta bare wai yayar ta, kawai kowa ya kama hanyar sa Allah yasa haɗa kowa da masu irin halin gidan su. Nana ta ce "Amin Nasiru! Na ce Amin , idan ka haifu a cikin uwarka yanzu kazo muje ka kwashe kayan ka ba sai gobe ba, in sha Allah daga yau bazaka ƙara ganina bama balle har muyi magana ka je nima na fasa auran naka. Tana faɗa ta juya zata tafi amma Nasiru da maganar da ta faɗa ya ɓata masa rai ya janyota sai gata a jikinsa wanda ita kuma ta sauke masa mari tana janye jikin ta, shima kafin ta anka ya mayar mata da marin , nan take suka fara faɗa dama sun saba ...✍️ *Comments dinku shine ƙwarin guiwa na* *One love* *One house* *Comments* *Shering please* *Love all my fan's* *S-REZA typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* *8* *By S-REZA* *Whattpad* _Salis m Reza_ *PAGE8️⃣* ... Sosai dambe ya kacame tsakanin Nana da Nasiru kowa na furta duk abinda ya zo bakin sa, al'ummar dake gurin ne suka yi nasarar raba wannan rikicin, Nasiru ya shige motar sa ya barta a gurin, itama ta tare mai ɗan sahu ta shiga ta bar gurin cikin ɗacin rai!. Bayan tafiyar su Kadija likitan ya ƙara ma Adam allura sannan ya sanar da Najib cewa in sha Allah zuwa jibi jikin zaiyi sauƙi sai a sallamshi. Najib ya amsa da ok Allah ya kaimu lafiya. Bayan likitan ya fita Najib ya tsaya ya na tunanin maganar Haura ta ɗazu. "Kenan da gaske itace ta soka masa wuƙa! Idan kuwa itace to gaskiya a kwai matsala domin wannan abun nata zai iya zama hauka. Haka dai ya yanke shawarar idan an sallami shi kawai gidansa zai wuce da shi har ya ƙarara warkewa. Su Haura suna isa gida Ameera ta wuce sashinta cikin sauri domin har lokacin abun da wannan yaran ya mata bai bar kanta ba, wanka ta fara yi kafin ta saka wata doguwar riga wanda cikinta ya fito sosai a rigar. Ɗakin Haura ta nufa kanta tsaye domin ta sama musu abun da zasu karya da shi. Babu ko sallama ta tura ƙofar ɗakin haɗi da ambatar sunanta. Sai dai taga wayam babu kowa a cikin ɗakin, har zata juya sai kuma taji ana ƙoƙarin buɗe toilet hakan yasa ta tsaya ta na jiran fitowar ta. Kallonta ta ke yi babu ko ƙifta ido tsabar mamaki. Tsawar da ta buga mata ne yasa ta saurin kwaɗa wani uban ƙara na tsoro domin sam bata lura da ita a ɗakin ba. "Ke dan ubanki haka ake fitowa daga toilet a garinku? Ko bakiga tawul a cikin toilet ɗin da zaki rufe jikinki bane? Haura ta rikece ta kasa magana sai ihu ta ke yi. Ganin haka yasa Ameera riƙo mata hannu ɗaya ta juyo da ita da kyau sannan ta sauke mata marin da yasa ta dawo hankalin ta. Ai kuwa cak ta tsaya tana zaro ido. Cike da umarni Ameera ta ce "Daga yau karki ƙara fitowa wanka tsirara? Haura ta ɗaga kai. Ta ƙara cewa "Sannan karki ƙara kwana bakiyi wanka ba? Nan ma dai ɗaga kai ta yi. Sannan Ameera ta riƙe mata kunne ta muɗa ta na faɗin "Daga yau babu ruwan ki da shiga lamarin gidana a kan komai, yanzu kuma na baki minti goma ki sama mana abin kari, saura kuma ki dafa mana ɗan wake dan ubanki. Cikin kuka Haura ta ce "To me zan dafa? "Ki soya doya da ƙwai sai ki haɗa mana shayi ina jiranki yunwa nake ji. Ta ƙarasa tana barin ɗakin. Tana fita Haura ta share hawayenta sannan ta samu ɗaya daga cikin kayan da aka saya mata ta saka, lokaci ɗaya ta saki dariya ganin yanda rigar tai mata chas-chas a jiki kamar dama ita ake jira tazo ta saya. Sosai ta shagala da kallon kanta a madubin ɗakin sai ɓaɓɓaka dariya take yi kamar wata zararriya. A haka dai ta fito tana ta dariya ta shiga kicin. Ameera kuwa sai da ta koma ɗaki ta tuna ashe fa basu da ƙwai s kicin ya ƙare hakan yasa ta riƙe kai ta na sakin gajeran tsaki a ranta, juyawa ta yi da nufin komawa ta sanar da ita cewar ta dafa wani abun sai kuma kira ya shigo wayarta. Ganin sunan Umma ne yasa ta tsaya tana kallon wayar har ta tsinke, tana tsinkewa wani kiran ya biyo baya hakan yasa ta ɗaga haɗi da sallama. "Gani nan a hanyar gidan ki idan ma ba kya gidan to ki dawo yanzu" Umma tana faɗa ta kashe wayarta. Ameera ta saki tsaki ta nufi ɗakin Haura. Kafin ta ƙarass ta hango Haura a gurin daining tebul ta gama jere komai tana goge-,goge na kayan cikin palon. Cike da mamaki ta nufo gurin ta bude kular farko taga doya da ƙwai a soye a guri ɗaya, kula ta biyu kuma zallar ƙwai ne a ka soya da yawa shima da ban. Kula ta uku kuma miyar ƙwai ce da naman kaza ya sha suya har wani ɗaukar ido ya keyi. Sai kuma plas na ruwan zafi sai gwangwanin madara da na suga da na baumbita. Sosai Ameera ta ke mamakin komai hakan yasa ta kai kallonta ga Haura wacce ke ta aikin ta. "Ke Haura zo nan" Ameera ta faɗa cikin tsawa. Da sauri ta ƙara so fuska cike da fara'a. Sai a lokacin Ameera ta kalli shigar da tayi. Rigar tai mata kyau amma rashin iya sakawa yasa basu zauna mata da kyau ba. Cikin sanyin murya ta fara cewa "Keda wa kuka dafa wannan abincin? Haura ta ce "Ni ɗaya ce" "A ina kaka samo ƙwai har kika yi amfani da shi? "A kicin na samu, ai a kwai da yawa" Ameera ta saki ajiyar zuciya ta ce "Yaya ma sunan garin ku? Haura ta amsa da "Garuk" "Kince ku ba musulmai bane ko? Haura ta ɗaga kai. Ta ce "To kuna yin tsafi ne! Ko dai aljannune ku? Haura ta ce "A'a ba aljannu bane. Kuma bama... Kafin ta ƙara sa an turo ƙofar palon an shigo haɗi da sallama. Umma ce sai Nana a bayanta fuskokinsu babu sauƙin kallo ga mai laifi. Da sauri Ameera ta nufi Uama tata cikin fara'a da ɗoki tana ƙoƙarin rungume ta amma Umma ta daka mata tsawa tana faɗin "Sannu shaffiya da mai, wato dan tsabar rashin hankali da gidadanci irin naki sai da kika san ta yadda kika yi har kika raba wannan auran ko? Auran da ya rage wata ɗaya amma yazo kin haifar da tashin hankali a gidaje guda biyu, yanzu ga shi yazo wai dole sai an bashi kayan sa, shi kuma Abbanku yace sai ta samu wani kafin a ba shi kayan sa hakan ya haifar da faɗa harda manya a ciki kuma duk kece kika haɗa a wannan ban zar halayyar taki ta shirme wacce bamu san daga ina kika aro kika yafa ba. Cike da mamaki Ameera ta ce "Ma sha Allah tunda an fasa auran yanzu kowa sai ya huta! Ta faɗa ki a jikin ta. Umma ta kai mata mari amma amma ta kauce ta ce "To Umma dan Allah kuma ku manta da lamarin wannan yaron wallhi ɗan iska ne, hannu fa ya ƙe riƙe mata a cikin mutane fisabililahi! Kuma ma ai indai faɗan Nana da Nasiru ne kowa yasan zasu shirya kawai ku barshi da kansa zai dawo idan har da gaske son nata yake ba iskanci ya kawo shi ba. Cike da takaici Umma ta ce "Allah dai ya wadai wallahi idan ma hannu ya riƙe mata sai ki fara zaginsa ba nasiha ba, haka ake gyara! To yanzu haka Abbanku yana police station duk a dalilin ki. Ameera ta ce "Police station dai? To a kan me? "A kan ya ce ba zai bada kaya ba sai ƴarsa ta samu tsayayye ba. "Cicin faɗa Ameera ta fara "Wallahi wannan mutanan basu da mutunci yanzu a kan kayan lefen da kwata-kwata guda nawa suke da sadakin da ya kawo shine zasu kai Abba police station, to wallhi basu isaba ni dama nasan wannan yaron ba ɗan arziki bane, wallhi ɗan iska ne. Cike da zafin zuciya da Nana ta gama ƙunsa a gurin yayar tata ta ce... "Wai kina ta cewa ɗan isa, me yayi na is kanci ne? Saboda ya riƙe hannuna ne ko? Ta ci gaba da faɗin idan sabo da haka ne to ke lokacin da Adam ya ke nemanki meye bakuyi ba? Ina ce har kowa sai da yasa muku ido tsabar zallar iskanci da kuke yi, wacce irin runguma ce baya miki a gaban mu, ko kina ce mun manta ne, to a gurin ki na koya. Take Ameera ta fara masifa "Yanzu Umma a gaban ki yarinyar nan take faɗa min irin wannan maganar ko? Wato har raini ya shiga tsakanina da ke har haka ko, ni zaki wa sharri, to idan ma haka ne ai ni ya aureni dan uwarki. Umma ta ce "Gani nan uwar tata zage ni yadda kikeso. Haura dai abincinta ta ci sannan ta miƙe ta bar palon. Sosai Nana ta furta abubuwan da ke ranta ita kuwa Umma bata hanata ba domin itama abun da Ameera ta yi ya ɓata mata rai sosai. A haka Umma ta bar gidan ita da Nana tana sanar mata kar ta ƙara shiga sabgar Nana da Nasiru ko da Allah yasa abun ya shiryu. Amma Ameera ta ce "In sha Allah ma ba zai shiryu ba. Hakan yasa itama ta yi fushi ko irin Allah ya tsare hanya ɗin nan ma ba tai musu ba bare ma aje ga batun rakiya. Suna tafiya ta dawo kan Haura ta sauke mata gaba ɗaya baƙin cikin da ta ƙusa, domin kuwa duka tai mata babu laifin fari bare na baƙi, dukda abubuwan kirkir da tai mata. Haka suka cigaba da zama da Haura kullum cikin sabon abun mamaki take yi, har yanzu bata ƙara leƙewa asibiti gurin Adam ba haka bata kira su Umma taji a wani hali suke ba, ko da kuwa jin an saki Abba ne ko har yanzu yana ƙullen ne. Kullum kwanan duniya sai ta daki Haura duk da irin ƙoƙarin da take yi, komai na gidan itace amma kuskure ɗaya zata yi ta sha duka. Izuwa yanzu ta daina mamaki da lamarin Haura domin ta gene cewar su din matsafa ne. Tana kwace a palo kan kujera tana karatun littafin da ta siya na Batul Mamun mai suna uwa uwa ce wanda labarin ya ɗauki hankalin ta sosai, sai murmushi take saki ta na sake juyawa dags kwancen da ta ke. Sosai take mamakin halin yaran innayo, ace yara mata kusan guda shida amma duk babu wacce take taimaka mata gashi kuma mazajensu masu hali. Kwana huɗu kawai ta ɗan ƙara kumbura cikin ya ƙara fitowa ga ƴar ƙiba da ta yi. Sosai ya tsaya ya na ƙare mata kallo daga ƙofar ɗakin duk yayi kewaarta barinma cikin dake jikinta, hakan yasa lokacin da Najib ya ce su wuce gidansa ya ce a'a shi dai yana son zuwa yaga halin da matarsa ke ciki. A hankali ya isa saitin kanta yasunkuyo kusa da kunnenta ya ce "Honey I'm back" Zumbur ta meƙe har tana sakin wayar, ganin sa yasa ta saki tsaki ta na kawar da kanta. Cikin murmushi ya ce "Please Honey I miss you and my baby. Ya faɗa ya na son shafo cikin nata. Da sauri ta ture hannunsa ta na faɗin "Ba kai kace baka son ganinmu ba, kawai kaje ka zauna da su Kadija da abokinka tun da mu bamu da wani amfani a rayuwarka. Ta ƙara sa tana jin furicin da yayi tun a lokacin yana dawo mata sabo. Adam ya ce "I'm sorry honey ba haka nake nufi ba baki fahimce ni bane please I'm sorry. Ya ƙara sa yana kamota ya haɗe jikinsu guri ɗaya. Take ta saki kukan kewarsa da tayi. Soyayyar Adam ta daban ce a cikin zuciyarta ita kadai tasan irin wahalar da tasha na rashin sa. Adam ya shiga shafa cikin nata yana faɗin I hop baby yana lafiya dai ko? Shiru ta yi tana ƙara lafewa a jikin sa. A hankali ta ce "Ya jikin naka ? Ta faɗa tana ɗagowa tana kallon gurin da ya warke sai tabo kawai. "I'm fine jiki yayi sauƙi sai godiyar Allah, ina fatan dai lafiya kike zaune da wannan ƴar aikin ko? Ameera ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba. Hakan yasa ya jata suka shiga cikin ɗakin yana riƙe da ita. Suna shiga toilet ya jata suka yi wanka tare sannan ya shafa mata mai itama ta shafa masa cike da farin ciki. Kayan ƴan boooll na Chelsea mai ruwan blue mai ɗauke da sunan Yokohama a gaban rigar suka saka, sai kuma bayan rigar mai ɗauke da sunan Hazard mai labba goma a baya kasancewar Adam na son mutumin. Sosai cikin nata ya ɗaga rigar har ma rigar na neman yi mata ka ɗan. Nan ya shiga ɗaukar su hotuna wanda sun kwana uku basu yi ba. Sosai Adam ya rungumota a jikin sa yana faɗin Ameera ta Adam ikon Allah! Ameera ta saki murmushi ta ce Adam na Ameera sai ikon Allah! Duk dariya sukayi domin tunawa da lokacin baya da sukayi. Nan take wasan ya sauya kowa ya shiga faranta wa ɗan uwansa, wanda kowa ya nunawa ɗan uwansa yanda yayi kewar ɗan uwansa. Adam sai saka mata albarka yake yi kamar ba gobe. Haka suka sake yin wani wanka suka ƙara saka irin kayan amma wannan karan masu ruwan kunun ɗorawa (yalo). Haka ya kamata suka fito Palo tana manne a jikin sa. Koda suka iso sun samu Haura tana gyara palon hakan yasa ta gaisar da Adam haɗi da tambayarsa ya jiki. Adam ya amsa da sauƙi yana kallon yanda itama ta sauya sosai. Afil ya ce "Hony ke ce kika siya mata kaya ne? Ameera ta taɓe baki ta ce "Yaushe zan iya zama da tsama-tsama, ai ya zame mini dole na saya kafin ka dawo kar a kashe ni da tsami. Ya ce "God bless you my beautiful wife, kinyi ƙoƙari gaba ɗaya ma ni na manta ne da batun tafiyar, yanzu kalla yanda ta yi kyau ba kamar lokacin da tazo ba. Ameera ta kawar da kai tana faɗin "Kin gama abincin ne? Tayi tambayar duk da kuwa tasan abinci kamar ma ba girkawa a keyi a cikin gidan ba. "Eh na gama tun ɗazu kafin Yallaɓai ya shigo" Bata ƙara cewa komai ba suka nufi gurin abincin. Nan Ameera ta zuba musu a flet ɗaya suka fara ci. Suna cikin ci ne Haura zata wuce wa ta kusa da su zata shiga kicin Adam ya bita da kallo. Sosai hankalin sa yayi gurinta wanda ya manta da cewar Ameera na kallonsa. Kallon gurin da yake kallo tayi sai taga Haura na tafiya, tsabar mamaki sai taga kamar tana karkaɗa masa ƴan ƙananan mazaunan ta ta ke yi! Take taji gabanta ya faɗi, lokaci ɗaya wasu banzayen tunani suka fara zuwar mata. Ɗan buka cokalinta tayi a cikin flet ɗin wanda hakan ya dawo da Adam daga kallon tv dan ya tafi. Bai san lokacin da ya furta "Kisa saka kaya " Cike da mamaki Ameera ta ce "Wani kaya kuma zan saka? Adam ya waske da faɗin kisa ke kaya mu je mu sayo abubuwan da babu a gidan, in yaso itama wacce yarinyar sai a ƙaro mata kayan ko? Ameera ta yi shiru tana kallonsa har sai da ya tsargu. "Lafiya dai wannan kallo Honey karfa ki hango muni na? Afili ta ce "Ka bari sai gobe yau bana jin daɗi sosai" "To Allah ya kaimu lafiya matar Adam ita kaɗai babu ƙari" Kafin Ameera ta ce wani abu sai ga Haura ta sake fitowa daga kicin riƙe da flet ta nufo gurin da suka. Tun daga nesa ya kafeta da ido har bai san yana sakin murmushi ba. Shi tun lokacin da ya ganta tsirara to koda yaushe idan ya ganta to a haka yake ƙara kallonta, ga kuma dama ita bata saka hijabi gashi doguwar riga ce mara nauyi siririya a jikin. Ameera ta saci kallon Adam ai kuwa ta ga harda murmushi yake saki, sannan ta kalli Haura sai taga kamar itama murmushin take masa harda ma huro masa isa da su kanne ido ɗaya. Take Ameera ta ƙware tana ta famam tari! Hakan yasa Adam jawota jikinsa yana mata sannu. Haura kuma ganin haka tayi saurin ajiye abincin da ta kawo ta tsiyayo mata ruwa ta zo ta kusa da Adam tana miƙa masa ruwan ya bata. Lokacin da Adam zai karɓi ruwan sai taga kamar murmushi suke yi, sai taga ya riƙe hannunta ɗaya ya jawota jikinsa yana ƙoƙarin hade bakin nasu...✍️ *Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. Kunga ana samun posting babu ɓats lokaci, so kuma ku daure kuna yin comments da shiring dan Allah ina yin ku .* *One love* *One house* *Comment's* *Shering please* *Love my all fan's* S *-REZA typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* *9* *By S-REZA* *WHATTPAD* *Salis M Reza* *PAGE9️⃣* .... Sunanta da Adam ya kira ne ya sa ta dawo hankalinta, sai wani zazzaro waje take yi kamar wata munafuka. "Sorry Karɓi ruwa ki sha Honey Please ki dinga cin abinci a hankali kinji? Adam ya faɗa ya na kai mata ruwan saitin bakinta. Babu musu ta karɓa ta kafa kai sai da ta shanye ruwan kafin ta fara sauke ajiyar zuciya ta na kallon Haura wacce tun ɗazu take fama da sannu-sannu. Ta shi ta yi daga gurin ta nufi ɗaki domin so take ta samu damar yin tunani. Sai da ta kusa shiga ɗakin sai ta juyo da nufin ganin yanayin da suke ciki. Ai kuwa ta na juyowa sai taga kamar Haura ta yi saurin sauƙa daga kan cinyer Adam ɗin ne, shi kuma taga kamar shima Adam ɗin gyara jikinsa ya ke yi. Haka ta shige ɗakin har zata zauna sai kuma ta fara leƙe daga cikin ɗakin kasancewar daga cikin ɗakinta ana iya hango wanda yake daining tebul. Ta na leƙowa sai taga Adam ne kaɗai a zaune a gurin, afili ta furta "Muna fiki Allah yasa na kamaka da laifin cin amana ka gani, wai ma to me yake nufi ne!. Adam kuwa sai da ya tsaya ya cika cikinsa sosai har yana tambayar Haura a ina ta iya girki har haka mai shegen daɗi. Ita kuwa sai ta yi murmushi ta ce "Babu wanda ya koya mata da kanta ta koya. Adam ya kalleta ya ce "Da kanki kuma? "Haura ta amsa da kai. Haka har ya gama lokacin itama ta gama cin nata ta koma ɗaki. Shima yana gamawa ɗakin nasa ya nufa amma sai yaji kamar Muryar mutane biyu a dakin Haura ɗin, hakan yasa ya nufi ɗakin cikin sanɗa. Ya na zuwa ya kara kunnen sa domin saurara, ya kai minti biyu bai ji komai ba hakan yasa ya fara shawarar buɗe ɗakin. A hankali ya tura ƙofar ɗakin yana leƙawa. Zaune ya hangota ta dafe kanta hawaye na zubowa daga cikin fararan idanunta, da a'lamar wanka zata shiga domin ɗaure take da wani ɗan ƙaramin tawul wanda tun ranar da Ameera ta ce ba'a fitowa wanka tsirara yasa ta fara ɗaurawa. Da sauri Adam ya ƙara so gurin da take ya na tambayar lafiya? Da sauri Haura ta ɗago kai sai ga hawayen jini na fitowa daga idanunta ta. A ɗan tsorace Adam ya ce "Inna'ilaihi! Jini ne fa yake fitowa daga idon ki, ya faɗa yana ƙoƙarin komawa baya domin ya tsorata ainin. Da sauri ta fara goge jinin tana ƙaƙalo murmushi ta miƙe tsaye. Ai kuwa ta na miƙewa tawul ɗin ya kwance kafin ta tare shi ya dangane da ƙasa. Adam ƙamewa yayi agurin ya kasa kawar da kansa yayin da ita kuma Haura ta yi saurin shigewa toilet ta na barin tawul ɗin a gurin. Sai a lokacin ya dawo hankalin sa ya sauke a jiyar zuciya yana juyawa ya bar ɗakin cike da rashin ƙwarin jiki. Washegari ma kafin su ta shi Haura ta gama haɗa musu komai na kari, hakan yasa suna tashi daga barci suka nufo daining tebul ɗin suka zauna suna cin abincin cike da jin daɗin sa. Ameera ta ce "Honey zaka kaini gida yau idan ka dawo daga aiki sai ka biyo mudawo. Adam ya kalleta kafin ya ce "Kin ce yau zamu ƙarowa wannan yarinyar kaya ko kin manta ne? Ta ke ta ce "An fasa ƙaro mata kayan wanda ta samu ma ta gode. Adam ya ce "No ba za'a yi haka ba, idan na saukeki ni zan je na sayo mata kayan. Da ƙarfi Ameera ta ce "Na ce an fasa sayo mata kayan ko bakaji bane? Wai Adam me kake nufi ne da wannan yarinyar ne naga kana shishige mata da yawa fa, wallahi zaka yi mata sanadin barin wannan gidan. Da mamaki Adam ya ce "Ina shige mata kuma? Haba honey me kike nufi da zantukanki, ashe baki yarda da ni ba har yanzu. "Eh! Wallahi ban yarda da kaiba in dai akan mace ne ban yarda da kai ba, kuma na faɗa maka karka kuskura ka ƙaro mata kaya, ni nasan kalan kayan da suka dace da ita. Adam dai bai ƙara cewa komai ba har ya kammala cin abincin sa kafin ya koma domin shirin tafiya aiki. Cikin ƙanƙanin lokaci ya shirya cikin ƙananan kaya sai zuba uban ƙamshi yake yi kaman anyi ɓarin turare a jikin sa. Ya yi nufin shiga ɗakinta ya kirata amma ya hango Haura ta na goge-goge a palon hakan yasa ya nufo ɗaya daga cikin kujerun palon ya zauna yana kallon ta. Haura kuwa da tun zamansa ta kula da shi sai gaba ɗaya ta kasa sakewa da irin kallon da taga yana mata, ita ta kasa gane masa, haka abun da ya faru tsakanin su jiya ya ƙarasa taji kunya sosai, hakan yasa ta miƙe zata koma ciki idan ya fita ta dawo ta ci gaba. Amma taku ɗaya ta yi ta tsinkayo muryarsa yana kiran ta da kee. A ɗan tsorace ta amsa da "Umhum" Sai kuma ta tsaya tana kallon sa. "Nan zaki zo. Ya faɗa da ɗan ƙarfi wanda yasa ta ɗago ta saci kallon fuskarsa. A hankali ta ce gani. Sai da ya gama kallonta sama da ƙasa kafin ya ce "Kije ki shirya zamu fita dake yanzu, kuma karki ɓata mana lokaci. Haura ta ce "Tom" Ta na faɗa ta miƙe daga zaman da tayi a ƙasa tana barin gurin. Bata daɗe da shiga ba sai ga Ameera ta fito cikin shigar wani Les uban su, domin kallo ɗaya ka ɗai less ɗin ke buƙata a gane nauyin kuɗin sa. Ta sha kwalliya kamar ka sace ta ka gudu, ga cikinnan yayi turtsitsi a gaba. A hankali take sauƙowa tana ƙoƙarin yafa ɗan ƙaramin mayafin da ke hannunta fuskar nan tata a murtuƙe babu ko a lamar fara'a. Tun daga nesa ya zuba mata ido ko rsintsawa baya yi, sosai ya yi suman tsaye yana kallon matar tasa kamar an sauya ta, har ta ƙara so gurin yana tunanin lokacin baya da ta taɓa irin wannan wanka kafin su yi Aure wanda ranar tsabar kyau har faɗa suka nai mi suyi domin shi Adam bai san lokacin da ya rungumota ba ita kuma bata tsammaci haka daga gare shi ba domin basa haka a rayuwar soyayyar ta su. Ita haushi ma ya bata da irin wannan kallon hakan yasa ta ce "Wai dan Allah me ye wannan ɗin, kaman wacce bata saba yin wanka ba, yanzu fisabililahi idan wani ya gani ai sai ya zata bana maka kwalliya ne sai wata-wata. Adam da ya dawo daga tunanin sa ya ce "Honey kenan ai ke kullum wankanki idan kin yi Allah ƙara rikitani kike yi, kalleki fa kamar wata amarya. Ya faɗa yana ƙara sawa kusa da ita ya shiga shafo cikin nata kamar ya fito da yaron dake ciki. Ganin abun nasa ba na ƙare bane yasa ta ce "Wai zamu tafi ne ko dai sai ka gama wannan abun na ka? Adam ya ce "No mubari wannan yarinyar ta fito domin tare zamu tafi, idan na ajiyeki sai mu ƙarasa da ita mu sayo kayan. Take gaban Ameera ya bada wani darararammm! Jin kamar zata faɗi ne yasa ta naimi guri ta zauna tana kallon sa. "Kenan da gaske Adam yake yi a kan wannan yarinyar! To me yake nufi da haka! Haka dai bata ce masa komai ba har Haura ta fito cikin shigar ta na doguwar riga babu mayafi sai kanta da ta yane, sosai rigar ta amshi jikinta sai sunne kai take yi kamar tai wa sarki laifi. Da kyau Ameera ta kafe yarinyar da kallo ta na so taga ko a kwai wani abu na daban a jikin yarinyar da bata san da shi a gurin mata ba ne. Haka suka shiga motar gaba ɗayan su ba tare da Ameera ta ce komai ba. Har suka isa gidan shi kaɗai yake zan censa domin Ameera kamar ma bata cikin motar. Fitowa ta yi ta na miƙawa Haura jakar hannunta alamar ta ƙarɓa su tafi. Adam ya ce "Tare da ita fa zamu tafi ko kin manta ne? Ai kuwa dama abun da take jira kenan, dama tana so ta ji ko yana da kunya ko baida ita, jin ya nuna mata tsan-tsar rashin kunya ne yasa cikin harziƙowa ta ce "Tunda ita ɗin ƙanwar uwarka ce ai dole ku tafi tare, yarinyar da ba maharramarkaba itace zaka ce min wai tare zaku tafi, dama naso naga ƙarshen rashin ta idon ka ne, kuma ka nuna min, dama na lura gaba ɗaya ka manne ma wannan yarinyar to wallhi ka sani sai ta bar gidan nan ko kaso ko baka so ba. Adam da ransa ya gama ɓaci jin har tana zaginsa ya ce "Ni kike zagi akan nace zan je da ita na sayo mata kaya? Ya tambaya cikin ɓacin rai! "Ameera ta ce "Ni dai ban zageka ba sai dai ko kaine kaji zagin amma babu inda wannan yarinyar zata bika har ga Allah! Ta na faɗa ta dakawa Haura tsawa dake zaune a cikin motar tana sauraron su. Haka kuwa ta fito daga cikin motar riƙe da jakar tana komawa gefe ta tsaya. Tana fita Adam ya tada motarsa ya fuzgeta a guje ya bar unguwar ba tare da ya ƙara ce mata komai ba. Afili Ameera ta ce "Idan ka ga dama karka tsaya har wata uku kana gudu. Kunnen Haura ta kamo ta murɗe tana faɗin "Shigiya dan gin arna wata ƙikama karuwa ce ke, ko kuma wani abun ki kai wa mijina har yake neman damuwa da ke. Haka suka nufi gidan kunnen na hannunta Haura kuwa ta kasa ko yin ihu sai rintsaye ido da ta yi. Sai da suka zo shiga gidan kafin ta sakar mata kunne tana shiga gidan nasu da sallama. Sosai ta yi murna jin an saki Abban nasu, sai dai abun da ya ɓata mata rai shine jin cewar wai auran Nana da Nasiru yana nan wai sun shirya. Afili ta ce "Kai wannan yaro ina ga wallahi maye ne ko dai yana da dangi mayu! Haba duk irin abubuwan da suka faru amma ya dawo, anya Umma wannan yaron alkairi ne a gurin Nana kuwa? Umma ta yi saurin faɗin. "In sha Allah Nasiru alkairi ne kuma shi ba maye bane, sannan ki dinga iya bakinki a kan abun da zai fito daga ciki, sharrin maita bata da sauƙi. Ameera ta saki guntun tsaki ta na faɗin "Wannan auran dai kawai ganganci za'ayi, ya za'ayi yaro kullum dukan ta tun kafin ayi aure amma hakan ace wai shi zata aura, anya Umma kun duba wannan lamarin da idon basira kuwa? Umma ta kafe Ameera da ido ta ce "Wai ke manene matsalar ki da wannan yaron ne? Ameera ta yi caraf ta ce Dukan ta da ya ke yi, kinga duka ko a addinin Musulunci haramunne namiji ya daki matarsa. Kinga Umma in sha Allah zan kawo miki wani littafi mai suna Addininmu mu wanda S-REZA ya rubuta nasan in sha Allah zaki ƙaru sosai littafin yana faɗin abubuwa da dama a kan addininmu, nima ban daɗe da fara karatun sa ba. Umma ta ce "Allah ya tsareni da karatun shirme da ƙarya, tun da banyi ba sai yanzu, idan sanin addini ni to ga Alkur'ani mai girma ko sauran littatafai irin su Mahuwul Islam da ƙawa'idi Ahadari. Ameera ta ce "To ai daga cikin su ake ɗaukowa a rubuta. Umma zata ƙara magana sai ga Nana ta shigo tana sallama. Tana haɗa ido da Ameera ta zo da gudu tana faɗin anty Meera albishirin ki? Dama ke naso na fara sanarwa da wannan albishir ɗin. Ameera ta ce "Kinga ni ɗagani karki ƙarasa baiwar Allah. Nana ta kalli Umma ta ce Umma ɗan bamu guri, Umma ta ce "Ko baki faɗa ba ta shi zanyi ai! Bayan Umma ta fita Nana ta kalli Haura kafin ta yi magana har ta miƙe zata fita. Ameera ta ce "Munafuka ai da kin tsaya kinji gulma. Nana ta ce "Wai wacce wannan ɗin ne? Ameera ta ce "Wannan bai shafe ki ba. "To ai naga bata kama da mijin naki ne bare nace ƙanwarsa ce ko ƴar uwarsa. Amma ta ce "Wai Nana a ina kika koyo munafunci da gulma da Gutsiri tsoma ne? Ganin zata fara masifarne yasa Nana faɗin. "Anty Meera kin san me? Ta ce "Sai kin faɗa " Nana ta gyara zama ta na faɗin "wallahi wai harda makulli mota zai haɗo min a sabon lefen da zai kawo, wai yana so ya bawa mara ɗa kunya. Ameera ta ce "To ai idan yana so ya burge ko kuma yayi abin da wasu basu yi a wannan layin ba to jirgi zai baki, domin mota tsohon yayi ce, ko baki faɗa masa cewar Adam ya haɗe lefena da sabuwar mata ba ne, kuma shi bai taɓa shiga har cikin gidan iyayena ya ci musu mutunci ba, ko kuma yasa a kulle ubana a police station ba, to shi wannan in bada rashin kunya har ya iya ƙara haɗa ido da mu dan gyatumarsa. Nana da izuwa yanzu ta gana ƙuluwa ta ce "Ta ce to anty ko dai ɓakin ciki keke min ne da wannan abun arziƙin?...✍️ Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. (Bana yin posting ranar juma'a da Lahadi) *One love* *One house* *Comment's* *Shering please* *Love all my fan's* *S-REZA is typing...* ✍️ *AMEERA DA ADAM* *10* *By S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ *PAGE1️⃣0️⃣* ... Ɗauke da mamaki Ameera ke kallon Nana jin abun da ta ke faɗa a kan ta wai baƙin ciki. Cikin sanyin murya ta ce "Yanzu Nana nice ke miki baƙin ciki!? Nana ta gyara zama da kyau domin kuwa ranta ya ɓaci da irin cin mutuncin da yayar tata kewa Nasiru. "To idan ba baƙin ciki ba meme ne wannan? Mutum ya yi abun burgewa amma baza'a ya ba masa ba sai kuma cin mutunci ya biyo baya, haba Anty Meera ni ban san yaushe kika zama haka ba dan Allah ki dawo yadda kike please ki bar wannan halin hassadar da kika ɗauko wallahi bata ɓullewa. Nana ta ƙarasa ta na ƙoƙarin barin tashi ta bar ɗakin. Ameera da har wani kumfar masifa ne ke fita a bakinta ta miƙe ta janyota ta rufe ta da duka tana faɗin. "Wallahi Nana kin yi kaɗan ki rainani har haka, daga faɗa miki gaskiya sai ki fara zagina harda kirana da munafuka magulmaciya, ke ɗin banza yaushe har kika girma kika san daɗin saurayin da zakimin rashin Kunya a kansa. Sosai take jibgarta babu ƙaƙƙautawa. Nana kuwa jin Ameera na ƙoƙarin sumar da itane ya sa itama ta fara mayar mata da martani bata duba ƙaton cikin dake jikinta ba. Cikin ƙan-ƙanin lokaci Ameera ta fara ihun waiyoo cikinta. Sosai ta ke kuka ta na riƙe da ciki. Hakan yasa Umma saurin shigowa ɗakin tana tambayar ba'asi. Amma idonta ya sauƙa a kan Nana ta danne Ameera sai duka ta ke Kamar Allah ya aikota. Da sauri Umma ta rafka doguwar salati ta na isa gurin ta kama Nana ta wanka mata mari sannan ta jefar da ita kefe ɗaya ta yi kan Ameera wacce izuwa yanzu ta ma daina ihun sai numfashi da take saukewa a hankali. Ganin haka yasa kafin Umma ta dawo gurin Nana har ta fita daga ɗakin. Nana na fita Haura ta shigo ɗakin tana tambayar lafiya. Umma da zuwa yanzu duk ta rikice ta ce "Kin iya tuƙa Mota? Haura ta amsa da "A'a ban iya ba. Umma ta ajiye Ameera da take kan cinyarta tun ɗazu ta nufi ɗakinta domin ɗaukar waya ta kira Abban su. Tana dawowa taga Ameera na sauke ajiyar zuciya Haura na mata sannu tana cigaba da rike cikinta. "Waiyoo Allah Umma cikina zan mutu! Ameera ta faɗa tana kallon Umma da take mamakin ganin lokaci ɗaya ameera ɗin ta magantu. Umma cikin faɗa ta fara faɗin "Wallahi kin bani mamaki Ameera, tsabar rashin sanin ciwon kai ki tsaya kina faɗa da ƙanwarki kina ɗauke da wannan tsohon cikin! Koma me zata miki bazaki haƙura ki barta albarkacin wannan cikin da ke jikinki ba, yanzu idan yazo da tsau-tsayi cikin ya samu wani matsalar fa? Ana cikin haka Adam ya ƙara so gidan dalilin kiran da Umma tai masa. Yana zuwa cikin tashin hankali ya sunkuceta izuwa Mota Haura tabi bayansu suka nufi asibiti. Suna fita Umma ta shiga kiran sunan Nana cikin wata iriyar murya wacce kana ji kasan ranta a mugun ɓace ya ke. Sosai ta ke kiran Nana ta ko ta ina amma babu Nana babu dalilin ta, lungu da saƙo na gidan babu inda bata duba ba amma babu Nana hakan yasa ran Umma ƙara ɓaci tana jin yau sai ta kusa sumar da yarinyar nan idan ta ganta. Sosai likitan ya hau Adam da faɗa bayan ceto cikin da suka samu suka yi da ƙyar. Faɗa sosai ya yi masa akan wai a daina wasa da cikin domin wannan da ƙarfi aka mawa cikin wanda hakan yasa sai da ɗan cikin ya juya daga yanda ya ke. Sosai Adam ya shiga amsawa da za'a kiyaye wannan ma baya gida ne shine yasa. Likitan ya ƙara ɗorasa a kan sharuɗa irin na masu tsohon ciki. Ya ce "Kar a barta ta yi wani aiki mai wahala koda shara ko wanki da sauransu. Sannan banda yawo ta zauna guri ɗaya domin ɗan cikinta ya jigata sosai yin wani babban abun zai haifar da damuwa. Sai da yamma aka sallamo su wanda kafin wannan lokacin sai da Haura ta je gida ta dafo musu abinci. A hanya ne Adam yake tambayar ta me ya sameta. Ameera ta yi shiru ta na kallon gefe ɗaya zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Adam ya dawo da tambayar kan Haura ita kuma ta ce bata sani ba. Har suka isa gida bata ce komai ba sai hawaye da ke zubowa a idonta. Sosai ranta ke mata suya zuciyarta na mata zafi tana jin kamar a kwai wani abun da ya kamata ta yi domin taji daɗi. Sai ta ke jin duk duniyar ma ta tsani kowa, kaman babu wanda yake sonta a duniyar. A hankali take tuno komai da ya faru tsakanin ta da Nana. Shi kansa Adam tausayi ta ne ya rufe shi ganin yanda ta riƙe cikin ta ga kuma hawaye da yake zubowa ba tare da tayi kuka ba. Sai yanzu ya ƙara jin tausayin ta ganin ita kuma irin nata laulayin kenan. Itama Haura kaman tai mata kuka tsabar tausayi domin har ta rame sosai. Haka suka iso gidan mai gadi ya buɗe musu get. Kafin ma Adam ya ƙara sa tsayawa Ameera ta buɗe ƙofa ta fito ta nufi cikin gida da sauri. Bata son ganin kowa a kusa da ita, ta gaji da wannan duniyar bata san mai taiwa kowa ya tsaneta har haka ba. Ganin haka yasa shima bai gama saita motar ba ya kashe ta ya fita yabi bayanta yana sanar da Haura da ta rufe motar. Ya na shiga ya sameta ta ƙifa kanta a bakin gado tana shesheƙar kuka. A hankali ya ƙara so kusa da ita ya fara mata magana a hankali "Honey dan Allah ki yi haƙuri wannan kukan ma zai iya kara haifar miki da damuwa keda ɗan cikin ki, please I'm so sorry kinji. Jin bata daina kukan bane kuma bata ɗago ta kalleshi ba ne yasa ya matso kusa da ita ya sa hannu zai ɗagota. Yana ɗora hannunsa a jikinta ta yi zumbur ta meƙe kamar mai jiran hakan. Wallahi babu wata-wata ta ɗauke fuskarsa da mari, ta cakumi rigarsa ta fara zaiyano komai da take jin ya tsaya mata wanda tun ɗazu take jin idan bata amayar ba zata iya mutuwa "Na tsane ku bana son ganin kowa ku fita a sabga ta wallahi bana son ganin kowa mutuwa ma kawai zanyi mai nai muku ina kuke so naje. Ta na faɗa tana cigaba da dukan Adam a ƙirjin sa. Ganin haka yasa Adam ƙoƙarin kwantar da ita a ƙirjin nasa amma ta ƙwace jikinta ta nufi gurin kayan kwalliya ta kwaso su ta watsar a ƙasa, ta ɗauki kwalbar turare ta wurgowa adam wanda yayi saurin kaucewa, ta ɗauko kwalbar mai shima ta wurgo masa tana kuka tana fasa duk abinda ta gani a cikin ɗakin harda madubin da ke gurin kwalliyar saida ta tarwatsa shi, sosai ta koma kamar mahaukaciya , Adam dai da abun nata yayi mugu-mugun bashi tausayi da mamaki ya tsaya yana kallonta har ta yi ta gaji ta zube a gurin tun tana jan numfashi har barci yayi gaba da ita. Sai da ya bari barcin ya fara mata nisa kafin ya ɗauke ta ya kaita ɗakinsa ya kwantar da ita ya nufi ɗakin Haura da nufin kiranta ta gyara waccen ɗakin. Tun kafin ya tura dakin yauma yaji kamar ba Muryar mutun ɗaya yake ji a ɗakin ba hakan yasa shi saurin tura ƙofar ɗakin yana mai kai kallonsa izuwa cikin ɗakin. Cikin tsananin mamaki Adam yake kallon wannan tsohuwar matar mai yin bara nan wato mamar Haura. Zaune ya same su a gefen gadon ga soyayen naman kaza a gaban tsohuwar tana ci tana surutu. Gefe ɗaya kuma Haura ce zaune itama tana cin naman suna ta fara'a da yaransu. Kafin Adam ya ce komai Haura ta ce "Ammi ta ce tazo yanzu ina so idan ka fito na faɗa maka ne. Adam dai bai ce komai ba sai bin tsohuwar da ido yake yi, itama tsohuwar sai kallonsa cikin ido take yi. Ganin haka yasa ya ce "Ok kizo yanzu. Yana faɗa ya saki ƙofar ya fita da mamaki. Shi dai bai yarda cewar yanzu wannan matar tazo ba, to idan ma zuwa zata yi sai kawai ta shigo kan ta tsaye, to shi yasan ma mai gadi ba zai barta ta shigo kai tsaye ba, hakan yasa Adam cewar sai ya tamba yi mai gadi ko shine ya barta ta shiga. Yana tsaye a Palo ta ƙaraso kanta a ƙasa. Kallonta ya ƙara yi sai yaga kamar ta ƙara zama yarinya. Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya aɓoye kafin ya ce "Kije ɗakin Ameera ki gyara komai, a kwai kwalabe ki yi a hankali. Haura ta amsa da "Tom za'a gyara yanzu " Adam na faɗa ya nufi gurin mai gadi. Yana zuwa bai bi ta kansa da ya fara wasu zantukan daban ba ko gaisuwar ma bai amsa ba ya ce "Amm bayan mu wani ya shigo gidan nan yanzu ne? Baba mai gadi cike da mamaki ya ce "Ranka shi daɗe gaskiya babu wanda ya shiga gidan nan bayan ku ukun da kuka shiga yanzu, kuma yau kasancewar ba kwa gida yasa ban je ko ina ba, abinci ma Haura ce da ta dawo ɗazu ta kawo min har nan, ai Allah ya sakawa wannan yarinyar bata gajiya kamar a gogo. Adam bai ce komai ba ya bar gurin yana girgiza kai alamun nazari. Koda ya koma ciki yana shiga sai yaga kamar ƙiftawar mutum, amma bai ga kowa ba hakan yasa ya nufi ɗakin da yasa Haura aiki ɗin domin yaga ko ta fara. Yana shiga yaga ɗakin tsaf-tsaf a gyare komai an mayar da shi mazaunin sa kamar ma ba'a komai a ciki ba. Cikin wani sabon mamakin yake bin ɗakin da kallo ganin Haura ɗin bata ciki. Afili ya furta "Hasbinallahu wa ni'imal wakil! Haka yake ta furta wa yana bin ɗakin da kallo! Sosai izuwa yanzu ya fara tsorata da lamarin Haura. Da sauri ya fito ya koma ɗakin da Ameera ke ciki. Har yanzu barci take yi tana kwance a yadda ya barta. Juyawa yayi ya fito yana son zuwa ɗakin Haura amma yana tsoro hakan yasa ya ƙolla mata kira daga gurin da yake. Ɗan nesa da shi ta tsaya kanta a sunkuye kanta babu dan kwalli ya ce "Inna Ammin na ki? Haura ta ce "Ai ta tafi dama sauri take yi, wai tazo ne kawai ta ganni ko lafiya nake. Adam ya ce "To ta ganki lafiyar kike? Ya faɗa cike da takaici da mamaki. Itama Haura ɗin ɗagowa ta yi sai kuma suka haɗa ido tayi saurin kawar da nata. Adam yayi saurin kallonta a karo na biyu yana ƙara jin shkkar ta. "Suwa ye ku? Mai kuka zo nema a gurin mu? Mai kuke nufi damu? Da sauri Haura ta ɗago ta kalleshi jin abun da ya ce. "Haura ce da Ammi, kuma mu babu abun da muke nema gurinku sannan mu ba cutarku mukazo yi ba. Haura ta faɗa tana satar kallonsa again. Afili ya ce "Faɗi min yanda a kayi Ammin ta ki ta shigo wannan gidan domin kuwa bata get ta shiga ba. Cikin tsabar mamaki take kallon sa. A zuci ta ce "Wannan fa ya cika tambaya. Take Haura ta sanar da shi abun da ta faɗa wa Ameera cewar su ba Musulmai ba ne, kuma ba Hausawa ba ne, sannan su suna yin wasu abubuwan ne ba irin na mutane ba kasancewar suna da tsfface-tsffce. Da ƙarfi Adam ya ce "What! Auzu billahi! tsafi! Kuma ku ba musulmai ba ne? To wani gari kenan kuke. Haura ta ce "A garin Garuk muke kuma yaran Garuk muke ji, yanzu haka muna son komawa amma babu dama ƙaddara ce ta fito damu daga cikin garin wacce kuma bamu da damar koma , hakan yasa muka fara barace-barace- a nan har Allah yayi ka kirani aiki. Adam yayi shiru yana kallonta ganin tana kuka a hankali ya ce "Mai kuka aikata da yasa kuka bar garin naku, sannan yaya a kayi kuka iya yin Hausa? Haura ta yi shiru ta na kallon sa. Sai cen ta ce "Hausa mun koya ne, sannan abun da ya fito da mu daga Garuk labari ne mai tsayin gaske. Adam ya ce "Yanzu abun da nake so da ke shine Ammin ki zata dawo nan gidan da zama , amma ke da ita duk zaku koma wancen sashin. Ya faɗa yana nuna mata wani ƙaramin sashe dake gefe da nasu. Haura ta yi godiya ta miƙe zata tafi amma suka tsinkayo muryar Ameera ta na faɗin "Babu inda zasu zauna wallahi bazamu zauna da ar'na da kafurai a gida ba...✍️ _Kuci gaba da bibiyan S-Reza. Comments ɗinku shine ƙwarin guwa na._ *One love* *One house* *Comment's* *Shering please* *Love all my fan's* *S-Reza typing ...✍️* *AMEERA DA ADAM* *11* *BY S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ *PAGE 1️⃣1️⃣* ..."Haka kawai bayan yarinya ta gama sanar da kai labarin ta ce wa su ba musulamai ba ne amma har kana iya ce wa zasu zauna a cikin wannan gidan, to wallahi ba zata saɓu ba. Ameera ta faɗa ta na ƙarasowa gurin ranta a mugun ɓace. Kafin Adam ya yi magana ta ci gaba da faɗin "Kasan Allah wannan yarinyar zamanta ya ƙare a wannan gidan dan ubanta, mai za'ayi da dangin tsafi da rashin yin Sallah! Ta na faɗa ta fara kamo Haura da ke ɗuke ta na kuka. Cikin kwantar da murya Adam ya fara faɗin "Honey mana! Wallahi wannan yarinyar abar tausayi ce, kuma ba wai ƴar tsafi ba ce, ha ka itama ta tsinci kanta da abun amma in sha Allah zata daina, please dan Allah ki yi haƙuri su zauna na ɗan wani lokaci please Ameera ta Adam. Ya ƙarasa da tsokana a muryar ta sa. Lokaci ɗaya Amera ta fashe da kuka ta na faɗin "Wannan yarinyar tsinaniya ce wallahi! Ba na son ko ganinta a kusa da ni, ba ta taimako na, jiya fa a gabanta Nana tai min dukan tsiya amma ko ta taimaka mini, idan ma kashe ni za'ayi babu ruwanta. Cike da mamaki Adam ya ce "Dukan tsiya! Kuma Nana? To a garin ya ya? Ameera ta ja ƙwafa ta ci gaba da faɗin "Ai kawai ka bar wannan yarinyar Allah inaga ni ce ajalinta ita da tsinannen saurayin nan nata. Adam cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Na ce mai kika mata da zata dake ki? Bata ganin abun da ke jikinki ne, ko Umma bata gidan ne? Wai ma yaushe har Nana ta iya dukan ki? Wai me ke faruwa ne? Sai ma a lokacin Ameera ta ƙara jin taikaicin abun da ya faru ɗin. Ta ke Amera ta kwashe komai ta faɗawa Adam sannan ta ɗora da ce wa "Allah da zarar na aihu ita zan fara tunkara koda kuwa ta na gidan mijinta ne, bazan taɓa yafe wannan cin fuskar ba. Ta na faɗa ta koma ciki ta bar Adam riƙe da baki a sake yana mamaki. Afili ya furta zanje gidan na samu Nana akan wannan maganar, bata da hankali ne zata daki Mace mai tsohon ciki har irin wannan dukan. "Ta shi ki tafi zuwa gobe sai muje azo da Ammin ta ki ko? Haura ta miƙe ta shige ɗakinta yayin da Adam ya tashi ya bi bayan matar sa. Bayan kwana uku Ammin Haura ta tadowo gidan kaman yanda Adam ya faɗa. Sannan babu abun da ya rage daga ɓangaren Ameera domin har yanzu duk abinda ta ce shi ake yi. "Haura..! Haura..! Haura..! Da ƙarfin cin tuwonta ta ke kiran Haura ɗin duka da cewar ta na amsa amma hakan baisa ta daina kiran sunan ba har sai da ta ganta a gaban ta. Ta na zuwa ta ɗauke ta da mari ta na faɗin "Uban me kike yi da zan ta kiranki bazaki zo da sauri ba, tun ɗazu kin barni sai faman ihuu na ke yi kamar zaucecce yi ko? Haura ta yi ƙasa da kai ta na faɗin ki yi haƙuri. Waya ta miƙa mata game da faɗin "Gashi karatun wannan littafin zaki min kuma da sauri domin ba na son ana tsayawa, kuma dan Allah ki mayar da shi wani abun da ban kinji? Haura ta karɓa sannan ta fara karatun. Sosai ta ke karatun kamar wacce ta yi haddar sa, ko tsawa bata yi sai zubo karatu ta ke yi. Daidai anzo wani guri a cikin littafin Mai suna *Addininmu* Ameera ta tsayar da ita ta na faɗin. Yanzu ke a tunanin ki idan kece yaya zakiyi a gurin? Ace mamarki ta auri abokin yayanki, kuma matsiyaci ɗan matsiyata wanda bashi da ko sisi, sannan kuma ɗan ƙaramin yaro wanda bai fi ashirin da biyar ba. Haura ta ce "Shikenan sai kawai na ce masa baba. Ameera ta maka mata ashariya ta na faɗin. Uwar da ta haifeki mai shekaru da dama ta auri wanda kika fi tsana a duniya, wanda kuka ɗauko a matsayin mai aiki bayan kun gama hanata aure a baya sai kawai ta aure shi amma kice wai zaki kira shi da Baba. Haura dai ta yi shiru jin zagin da a kai mata. Ameera ta ce littafin Addininmu ya haɗu ta ko ina, bari gobe zamuci gaba in sha Allah! Haura ta ta shi zata tafi Ameera ta ce "Yawwa zo. Haura ta dawo ta zauna ta na sauraron ta. Anjima zaki rakani wani guri, so ki zauna cikin shiri kar sai nazo ina famam kiranki. Yau sosai Haura ta yi mamakin ganin sai hira ake ta yi da Ameera babu masifa, sosai ta ke mamaki. Haura ta amsa da "Ok tom. Bayan ta ta fi itama ta shiga ɗaki ta kwanta ta na mamakin yanda yau cikinta sai motsi ya ke mata, a haka har bacci ya yi gaba da ita. A hankali ya buɗe murfin motar ya fito ya na dariya yana mamakin abokin nasa. Adam ne ya fara faɗin "Kai dai Allah yasa naka cikin kar yazo da irin nawa, domin na sha wahala ko kuma na ce ina sha. Najib yayi dariya ya ƙara cewa "A'a ai bama iri ɗaya bane, ni dai nawa cikin ƙwaɗayi da barci ne kawai yake saka Madam, domin ita komai ta gani sai ta ce zata ci, kaidai bari wallahi idan Mace nada ciki to mijinta ya fita wahala da shi, ita wahalar kawai na haifeshi ne, amma bayan shi komai Maza ne ke yi. Adam ya ce "Kaɗan ma ka gani mu ai irinmu acikin masa tamkar muke ɗauke da cikin ne. Adam ya faɗa ya na dariya. "Kasan fa ba zan shiga ciki ba ina jiranka a nan ka kawo min na tafi kar Madam ta naimi wani abun bana gida. Najib ya faɗa ya na dariyar zolaya. Adam ya ce "Wa ai wallahi ko baka so sai ka shiga kun gaisa da Ameera, yanzu ta rage wannan fushin, domin tun jiya rabonta da ta yi faɗa da kowa, ai inaga shikenan ta dawo Ameeran da na sani. Haka dai Najib ya amince suka nufi cikin gidan suna hira irin ta abokai, suna shiga Najib ya samu guri ya zauna shikuma ya nufi ɗaki yana kiranta. Sosai ta sha barci wanda hakan ya haifar mata da ciwon kai, ga kuma har yanzu ɗan cikinta na motsa mata sosai, sai taji kamar yawo yake mata hakan ya ƙara haifar mata da zafin kai, sai ta zauna a gefen gadon ta kasa tashi sai zubar da hawaye take yi tana riƙe da cikin nata. Tana cikin wannan halin Adam ya shigo ɗakin ya na kiran sunanta. Da sauri ya ƙara so yana ƙoƙarin roƙota amma jin irin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin ja baya yana kallonta kamar ba ita ta yi maganar ba. Lokaci ɗaya cikin nata ya ƙara hautsinewa wanda yasa ta kurma ihun. Adam ya ƙara matsowa ta ƙara faɗin "Karka taɓa ni. Amma Adam ya yi banza da ita ya kamota. Ai kuwa ta gantsara masa cizon da yasa sai da ya sake ta. Sai kuma ta fara kuka da ƙarfi tana riƙe cikin nata, sai kuma ta fara zagin Adam a kan ya bar ɗakin bata son ganin sa. Sosai ta ke sarfa masa zagi uwa ta uba, harda kai masa duka tana ya tashi ya fita bata son ganin sa. Shi dai Adam bai fita ba sai kallon yanda take kuka ta na riƙe ciki yake yi, duk ta haɗa zufa ta fita a haiyacin ta, bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba, yana tausayin matar tasa sosai, yana jin ba zai iya fita ya barta a haka ba dukda kuwa haka ta ke buƙata. Ameera kuwa wani irin juyi ta ji ana yi mata a cikin ta, ga zafi da kanta ya ɗauka ga ciwon kai, ga kuma wani irin ƙadaici da take ji. Ihunta ya karaɗe gidan hakan yasa Haura da Ammi suka fito zuwa sashin nasu, wanda shima Najib ihun nata ne yasa shi nufar dakin yana kiran Adam. Sosai Ameera ta ke jin a zaba wanda yasa bata iya gane komai, sai zage-zage zage-zage take yi ta na juyi. A haka Najib ya shigo ya na tambayar lafiya? Suma Ammi da Haura suka ƙara so. "Lafiya mai kai mata? Najib ya tambayi Adam da hawaye ke zubo masa. "Wallhi nima haka na shigo na same ta kuma ta hana na taɓa ta. Najib ya kalli Haura da Ammi ya ce "Kuje ku riketa sai muje asibiti bamu sani ba ko aihuwar ce tazo. Suna isa kusa da ita Ameera ta daka musu tsawa ta na faɗin "Kufita min da ga ɗaki bana son ganinku dukkanku karku matso kusa dani! Ammi ta roƙo hannunta da niyar janyota, amma Ameera ta fisge hannunta ta ware iya ƙarfinta ta dunƙulawa Ammi naushi a ciki, ta yi saurin ƙara mata a haƙarƙarinta wanda yasa ta sumewa nan ta ke. Ganin haka yasa Ameera ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon ta na nufo gurin su idanunta duk ruwan hawaye. "Na ce kubar min ɗaki bana son ganin ku tsinannu. Da sauri Haura ta yi kan mahaifiyarta tana kiran sunanta, ganin haka yasa Najib ɗaukerta su ka yi waje. Ruwa ya zuba mata amma bata farka ba, hakan yasa ya ɗauke ta suka wuce asibiti Haura sai kuka ta ke yi. Sosai Ameera ta fita a haiyacin ta, wallhi idan ka kalleta sai ka tausaya mata, ta tsagi Adam uwa ta uba amma yaƙi barin ɗakin, shi dai dole sai ya kaita asibiti ita kuma taƙi yarda. Sosai ta ke dukansa ta ko ta ina a dakin kamar mahaukaciya. Ganin dai kamar bazata daina bane kuma izuwa yanzu dukan ya fara shigarsa domin da ƙarfi take dukan hakan yasa ya shiga ƙoƙarin ƙwace jikin sa amma ta riƙe shi da ƙarfi. Da gyar ya ƙwace jikin sa ya jefata a kan gado ya rufo ɗakin ya fita. Ya fara kiran Najib ya na tambayar sa wani asibiti suke. Najib ya sanar masa sannan ya nufi asibitin ya na tunanin lamarin Ameera. Ya na isa asbintin ya tarar da Haura sai kuka ta ke suna zaune a harabar asbintin suna jiran sakamako daga gurin likitocin. Najib ya ce "Ina ita Ameera ɗin? Adam ya amsa cikin fushi da ƙosawa da komai "Ta na gida taƙi yarda musu asbintin, kuma da dukkan alamu ba haihuwa bace, babu yadda banyi da itaba wallhi ta ƙi! Ni na gaji, wannan cikin ko cikin aljannune iyakaci kenan, haba dan Allah, to ni gaskiya na gaji ba zan iyaba, ni ban taɓa ganin inda ciki yake mayar da mace mahaukaciya ba, yanzu dubi abun da tai wa wannan matar fisabililahi! Adam ya ƙara sa ransa a mugun ɓace. Najib ya ce "Ka yi hakuri wallahi irin wannan abubuwan duk suna faru ga mace mai ciki, kai dai dan Allah ka cigaba da hakuri har Allah ya sauƙeta lafiya. Cikin tsananin masifa da baisan yanada itaba shima ya ce "Wallahi is okay! Na gaji bazan jura ba, idan haka ne kawai aje a zubar da cikin na hakura da shi bana so, haba dan Allah ita kaɗai ce mace mai ciki, ita baza'azo kusa da itaba wallhi wannan duk ƙarya take yi kawai iya shege ne ba cikin bane ya ke saka ta wasu abun. Haka fa ranar wai taje gida ta nemi faɗa da ƙanaarta Nana tai mata dukan tsiya saura kadan cikin ya zube, bayan naje gidan wai Nanar da yake itama shegiyar ce take sanar dani cewar wai saurayin ta ma ya taɓa marin ta, haba Najib wani yaro ya daki mamata dan Allah wannan wani irin cin mutumci ne. Najib dai sai hakuri yake bashi yana tausarsa akan ya bar maganar zubar da ciki. Suna cikin haka likitocin suka fito fuskokinsu cike da alhini! "Ganin likitocin suna ta sunkuyar da kai ne yasa Najib faɗin"Dr lafiya dai ko? Sauran suka tafi suna girgiza kai. Babban likitan da shine ya tsaya a gaban su ya ce "Ƴaƴanta ne ku? Da sauri Najib ya ce "Eh Dr me ya faru ta farfaɗo ne? Dr da bai kula da Haura da ta kafa masa ido tana son jin mai zai ce ba, tun kafin ya fito jikinta ya bata a kwai matsala domin kuwa taji wata jijiya dake riƙe da ragamar rayuwata ta tsanke, tabbas taji bangwan da da ta jingina a jiki yana zaizayewa, taji ƙofar da makullin rayuwata ke jiki ya karye a ciki. Tabbas taji! "Sai haƙuri Allah ya yi mata cikawa sakamakon haƙarƙarinta ya bugu kuma dama ta na fama da gurin. Likitan na faɗa ya share hawayensa ya bar gurin. Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un! Adam da Najib suka haɗa baki wanda yayi daidai da subewar Haura a gurin....✍️ _Inada tabbacin yanzu kun gama gane ina muka dosa. Saƙone mai wahala fahimta wanda sai mutum ya natsu zai fahimta, ba a cika samun marubuta suna rubutu a kan irin wannan matsalar ba, hakan yasa na tsaɓi wannan bangaren. Ina fatan kuna nan tare da Ni?._ Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. *One love* *One House* *Comment's* *Shering please* *Love my all fan's* *S-REZA typing...✍️* *AMEERA DA ADAM* *12* *BY S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ _(Allah ka tsaremu daga sharrin masu sharri, amin ya rabbil alamin)_ Page1️⃣2️⃣ ... Salatai kala-kala Adam ya ke ta ambata cike da ruɗewa da tashin hankali kaman wanda ya samu taɓuwa. Da sauri Najib ya yi gurin Haura ya na taro ta amma ina har ta dangane da ƙasa. Juyowa ya yi ya na kallon Adam da ya ke ta faman salati harda hawaye kaman wanda ya zauce. Da ƙarfi ya kira sunan sa ganin ya na neman zare wa "Adam samo mana ruwa please? Adam ya ƙara so gurin ya na faɗin "Shikenan ta kashi ta, wallahi ta kashe mata uwa. Jin abun da yake faɗa ne ya sa Najib saurin toshe masa baki, ya miƙe ya taɓo mazauna kusa da su da suma suke cikin damuwar tasu jinyyar, ya amshi ruwa ya fara yayyafawa Haura wanda sai da yayi sau biyar kafin ta saki ajiyar zuciya sannan ta fara magana da yaran su. "Cut kut kici-kici ƙuf zam gut vicce akuƙu fut tati, (Ma'ana ita dai a kaita gurin Amminta Amminta take son gani a kaita)Jin basu gane me take cewa ba ne yasa suka sake ta ai kuwa ta shige daɗin da taga an shigar da Amminta. Ta na shiga ta ganta kwance an rufe fuskarta da mayafi, da sauri ta buɗe ta na kallon ta. Sai a lokacin ta ƙara fashewa da sabon kuka tana rungume uwar tata. Sosai Haura ke kuka harda hawayen jini wanda har aka fita da Ammin bata daina kukan ba. Haka aka kwantar da ita a tsakiyar palon gidan nasu Adam da Najib suka yi jugun-jugun yayin da Haura ta ke ta faman ihu ta na ta magana da yaran su. Da sauri Adam ya miƙe ya nufi ɗakin da ya kulle Ameera, ya na zuwa ya buɗe ransa a mugun ɓace. Ya na shiga ita kuma ta taso tayo kansa wanda tana zuwa ya ɗauke ta da mari sannan ya turata baya. Ita kuwa Ameera tun lokacin da ya kulleta ya tafi taci kuka har ta gode wa Allah, ta zageshi yafi cikin carbi. Da ƙarfi ta ƙwallara wani irin ihu domin marin ya shigeta yanda ya kamata, Adam ya fara magana cikin faɗa da masifa. "Burin ki ya cika kin kashe ta yanzu sai hankalinki ya kwanta ko? Ya faɗa ya na ƙare mata kallo yadda ta fita a haiyacin ta duk ta rame tsabar masifa da ta ɗorawa kanta. Lokaci ɗaya Ameera ta ji gabanta ya ba wani rass! Saboda abun da taji. Adam na faɗa ya juya ya fita ya koma Palo ya kalli Najib ya ce "Wai yanzu yaya zamuyi da gawarta kaga su ba musulmai ba ne? Najib cike da mamaki ya ce "Bangane ba musulmai ba ne? To su wa ye? "Irin arnan dajin nan fa suka samu damar shigowa gari. Sosai Najib yayi mamaki hakan yasa ya ce "Ai ni har zan kira Abba domin ai mata sutura a kaita makwanci. Suna cikin haka suka tsinkayo muryar Haura ta na faɗin "Karku taɓa ta yanzu za'a zo a tafi da ita a binne ta a garin mu. Adam da Najib suka Kalli juna kafin Adam ya ce "Waye zai tafi da ita ɗin? "Mutanen garin namu ne sune zasu ɗauke ta. Haura ta ba shi amsa tana nufar gurin da Adam ɗin ke zaune. Ta na zuwa ta ce "Mun gode da taimakon ku a garemu Allah ya saka da alkairi zan bi yan garinmu mu tafi gida lokaci ya yi da zan je gida na amshi hukuncin laifin da muka yi. Shi dai Najib yana ta zuba ido yaga masu zuwa ɗaukar gawar. Adam ya ce "Bazaki tafi ba kina nan damu har abada, yanzu kin zama ƴar gida ba yar aiki ba, idan zaki iya zama damu anan to zan ɗauke ki kamar ƙanwata har tsawon rayuwar mu. Haura ta fashe da kuka ta na faɗin "Bazasu barni ba nima dole tare dani zasu tafi. Ganin yadda ta ke kuka yasa Adam matsowa kusa da ita ya kamo hannunta ya fara bata baki. Sosai Ameera ke mamakin wai ta kashe ta, to wa ta kashe, sai a lokacin ta tuna da cewar ta naushi wannan tsohuwar maiyar matar da ta tsana. Tabbas a ranta taji mutuwar domin bata yi tsammanin faruwar hakan ba, amma ta wani bangaren taji daɗi kunga kenan yanzu sai su bar musu gida . A haka ta fito ta riski Adam riƙe da hannun Haura. Lokaci ɗaya wani irin abu na kishi ya ratsa zuciyarta, take taji wani irin tuƙuƙi na ƙunci ya dirar mata, hakan yasa ta nufo gurin cikin tsananin ɓacin rai mafi ƙololuwa a rayuwar ta. Ta na zuwa ta kama Haura ta finciketa daga cikin Adam da sauri cikin masifa ta fara faɗin "Shigiya karuwa mara mutunci wallhi sai kin bar gidan nan munafuka. Kai kuma wallahi kaji kunya Adam! Kafin ta rufe baki ya fara faɗin "Kinsan Allah Daga yau Haura ta bar ƴar aiki ta zama yar gida, kuma bari kiji na faɗa miki koda kuskure kar hannunki ya ƙara sauka a jikinta in ba hakaba zaki gane kuran ki. Ganin haka yasa Najib saurin zuwa gurin ya riƙe Adam yana faɗin haba kai kuwa Adam bakaji me na ce maka ba ne? Dan Allah kayi hakuri har su zo su tafi da gawar nan Please. Ai take Ameera ta fara magana da faɗa "kai Adam har ka isa na yi magana ka ce min ba haka ba, to wallhi baka isa ba, ita kuma naga uban da zai hanani dukanta. Kuma sai... Kafin ta ƙarasa suka ji wata iska mai haifar da kasala wanda take ya saka su barci. Sun kai minti talatin kafin suka farka suka tarar babu Haura babu gawar uwar tata. Lokaci ɗaya suka fahimci an tafi da ita ne. Ita kuwa Ameera daga haka barccin hawala yayi gaba da ita. Najib kuma ya shiga kwantarwa da Adam hankali akan dan Allah kar ya biyewa Ameera ita ba lafiya ga reta ba. Haka dai Najib ya fita ya bar gidan cikin alhini da wannan abun. Kallon gurin da take kwance ya yi yaji kamar ya rufe ta da duka, tsaki yaja ya nufi ɗakin sa domin yin wanka. Bayan Najib ya koma gida ya sanar da Kadija duk abun da ya faru. Ai kuwa itama abun ya ƙara bata tsoron lamarin Ameera. Ta kalli Najib ta ce "Wai shin anya kuwa ba wani abun ne ya samu cikin Ameera ɗin ba, nifa sai naga nata abun kamar ya yi yawa wallahi, har da kisa? Sannan ni abun da nake tsoro anya mutanann zasu haƙura da kashe mu ƴar uwa da a ka yi kuwa? Najib ya ce "Nima tunanin da nake ta yi kenan, sannan maganar ki gaskiya ce nima na fara tunanin a kwai matsala a cikin Ameera Allah dai yasa kar ya tabbata. "Amin dai! Amma lamarin a kwai ayar tambaya. Kwance ya ke ya ƙurawa fakka ido kai ka rantse ita ya ke kallo, amma hankalin sa ya yi nisan zango ga wannan gurin. Tunanin halin da Haura ta ke ciki kawai yake yi, shin zasu kashe ta ɗin ne ko dai yaya, shin yanzu a ina zata zauna. To shin wai yanzu ta tafi kenan bazata dawo ba, Allah yasa ta dawo ta karɓi Addininmu addinin Musulunci Addinin gaskiya da gaskiya. Ta shi yayi zaune ya na tunanin makomar cikin jikin Ameera kawai asibiti zasu a cire shi in dai zata dawo yanda ta ke. Sai yanzu ya samu mafita, ai kuwa da saurin sa ya tashi ya nufi Palo gunda ya barta a kwance tun ɗazu, ta na nan yanda ya barta. Ya na zuwa ya kira sunanta da ƙarfi wanda tayi saurin tashi a ɗan firkice. Ta na tashi taji wata azabbiyar yunwa wanda cikinta har wani ƙullewa yake yi. "Kije ki shirya zamu tafi asibiti yanzu, kuma karki ɓata mini lokaci. Ya na faɗa ya juya zai tafi. Cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta miƙe ta ce "Honey yunwa fa nake ji ka sayo mana abinci ne? Ta faɗa ta na ɓata fuska cike da zaƙuwa. Adam ya ce "Nima banci abincin ba, ba dai kin kori masu taimakon ki ba, kin san Allah daga yau kullum ke zaki dinga mana girki koda yaushe ko da kuwa cikin duniya ne ke jikinki, kuma yanzu ki tashi mu tafi idan mun dawo sai ki girka mana abinci. Wani irin tuƙukin masifa da bala'ine suka zo mata wanda yunwar da take cin ta hanata cewa komai, sai kallon sa take yi cike da madarar mamaki. Ganin zai juya ya tafi ne yasa ta faɗin "Wallahi babu inda zanje ƙara ma kasani" Cike da ƙuluwa ya ce "Ai kuwa wallhi dole sai kinje. "To sai naga uban da zai saka ni naje. "Haka kika ce? "Eh haka na ce, naga wanda zai kaini asibiti yau. Adam ya ce "Dan Allah ki tsaya har na shirya na fito na sameki. Ya na faɗa ya koma ɗaki yana jin wallahi yau ko me zai faru sai an zubar da wannan cikin kowa ya huta, koda kuwa shi da kan sa zai zubar mata shi da duka. Sauri-sauri ya ke komai domin jikin sa har wani rawa ya ke yi kamar wanda zai shiga filin dambe. Itama Ameera ganin kamar da gaske yake ne yasa ta tashi da gyar ta shiga kicin ta ɗauko sauran abincin jiya ta ɗumama tsabar yunwa ta haɗo da shayin ta mai karo sannan ta nufi ɗakinta. Sosai ta ci ta sha shayin ta yi gyatsa, domin ita cikin ta baya mata zaɓen abinci ko kuma ta ce ita abu kaza take so, ita duk wani abu da take ci a baya to yanzu ma tsaf zata ci, hakan yasa bata da wata matsala ta ɓangaren abinci. Wanka ta shiga tana cikin toilet ɗin taji shigowar sa ɗakin, sai kuma taji ya fita ba tare da yace komai ba. Tana wankan ta na tunanin rainin hankalin sa. A haka ta fito ta shirya cikin duguwar riga ta zaman gida, ta ɗauko wayarta ta shiga karatun littafin ta da ta ke yi. Tana cikin karatun taji shigowar sa sai tashin ƙamshi ya ke yi, sosai ƙamshin nasa ya tafi da hankalinta har sai da ta ɗago ta kalli angon nata. Sosai ta ke kallonsa ganin wani irin kyau da yayi kamar ba nata Adam ɗin ba. "Ta shi mutafi" Adam ya faɗa babu alamar wasa. Sai a lokacin ta dawo daga kallon sa ta ce "Babu inda zanje, yanzu ma so nake na kiraka kamin karatun littafin Addininmu, Please matso kusa kaji rikici tsakanin A J da Laɗifa da kuma Abdullah da Zainab. Ta ƙara sa tana murmushi haɗi da miƙo masa wayar. Cikin zafin rai Adam ya fizge wayar ya ɗaga ta ya raɗa ta a kan yayiss ɗin ɗakin wanda nan take ta wargaje, yaci gaba da faɗin "Ke kin ɗauka wasa nake miki da har zaki wani bani waya nai miki karatu, to wallahi baki isa ba, bari na faɗa miki na rantse da Allah asibiti zamu je yanzu a cire wannan cikin na gaji da masifu iri-iri akan wannan cikin, idan ban cire ba bansan mai zai haifar zuwa gaba ba. Saboda haka tun kafin rayuka su ɓaci ta shi mu tafi. Adam ya ƙara sa yana nuna mata hanyar tafiya. Wai Hausawa suke "Mai neman kuka ne aka jefe sa da kashin awaki! Sosai Ameera take bin wayarta da kallo ganinta a wargaje. Tana cikin haka taji batun wai za'a cire ciki ɗan wata bakwai da wani abu. Tun kafin ta yi magana take jin abun faɗa har wani turarreniya suke wajan fitowa daga bakin ta. Sai da ta miƙe tazo har gaban sa kafin ta fara magana har tana wani zaro ido tsabar masifa "Idan rayukan basu ɓaci ba Allah ya tsine musu! Na ce Allah ya tsine musu! Sannan na faɗa bazan je asibitin ba, wato ma cikin da ke wata bakwai kake batun azubar saboda a garin gaɓa-gaɓa muke ko? kuma wayata da ka fasa min Allah ya"..."Kafin ta ƙara sa ya ɗauke fuskar ta da mari sannan ya turata kan gadon ya shaƙe mata wuya bakinsa har rawa yake "Wallhi sai na kashe ki daga ke har cikin dake jikinki ke har kin isa ina magana kina magana a gaba na ko shakkar idona ba kya ji. Sosai ya sha ƙeta yana jin wani haushin ta kamar ma ya danne ta da filo. Cikin a zaba ta yi sa'a ta mai naushin guwar ƙafa a gaban sa, wanda yasa Adam ƙamewa na wuccin gadi a kanta. Ai kuwa sai gashi ya faɗo kanta kamar babu rai a jikin sa. Da sauri ta miƙe tana tari kamar zata yi amai. Tana cikin haka Adam ya farfaɗo ya ƙara kamo ta tayi saurin make masa hannu amma ya miƙe da sauri ya kamota ya ƙara wanke mata fuska da mari itama ta ɗaga hannu ta sauke masa mari kafin ta fara magana cikin ihu wanda shi kuma Adam har yanzu gaban sa na masa wani irin zafi...✍️ Comments dinku shine ƙwarin guiwar S-REZA *One love* *One House* *Comment's* *Shering please* *Love all my fan's* *S-REZA typing....* *AMEERA DA ADAM* *13* *BY S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ *Page1️⃣3️⃣* ... "Cikin wa ta bakwai da kwanaki ne ka ke tunanin za ka zubar wai ka haƙura da shi, uban wa ye ya yi cikin? Idan har kasan ba ka so mai yasa ka yi? To wallahi babu wanda ya isa ya zubar mini da ciki domin ina son kaya na, kuma asbinti ne na faɗa na ƙara faɗa ba zanje ba. Ameera na gama faɗa ta fita daga cikin ɗakin ta koma ɗakinsa har lokacin shaƙan da ya yi mata na sa wuyan ta zafi. Adam kuwa shiru ya yi ya na sauraron ta har lokacin gaban sa na masa wani irin zugi kamar tafiyar tsutsa, ya ɗauke wuta sosai ya na jin duk abun da take faɗa amma ya kasa ko kallonta bare ya tamka. Har sai da ya kwashe mintina ashirin a kwance ruf da ciki a kan gadon kafin ya iya tashi ya zauna. Hannu ya kai ya shafo gurin ya ji ko sunanan, jin sun koma ƙanana ne yasa shi saurin leƙawa domin ganewa idon sa, ganin a kwai su kawai sun da ku ne ya sa suka koma ciki sai ya saki ajiyar zuciya ya na ƙoƙarin miƙewa tsaye. Ta na shiga ɗakin taji kamar motsin mutum hakan yasa ta tsaya ta na jiran ganin ko waye domin ita yanzu ba tsoron komai ta ke ba dan uban mutum! Sosai Ameera ta ke ta nazarin maganar Adam wai zai zubar da cikin ta. Toma in banda wa wa a ina a ke zubar da ciki ɗan wata bakwai, cikin da za'a iya haifarsa a kowani lokaci. Kallon cikin nata ta yi sai taga kamar ya na motsi hakan yasa ta shafa kansa ta na tuno watarana kafin ta samu wannan cikin abun da Adam ya ce idan har ta samu ciki. Wa ya ce a hannunsa ya na ta ƙoƙarin tura saƙo izuwa email ɗin Najib cikin gaggawa domin ana buƙatar aiki da shine amma abin ya ƙi tafiya, hakan yasa ya ke ta sakin tsaki babu ƙaƙƙautawa. Ya na cikin wannan halin Ameera ta fito daga ɗakin cikin shigar barci. Ta na zuwa ta zauna kusa da shi ta ce "Please kabar wannan aikin ka taso mu kwanta zuwa gobe sai ka tura masa Honey ka ji?. Ta yi maganar cikin muryar shaƙwaɓa. Adam ya ce "Wallhi cikin darannan ake buƙatar aikin ne idan ban tura masa ba a kwai matsala ne. Jin haka Ameera ƙara lanƙwaɓe murya kamar zata yi kuka ta ce "Uhun Uhun ni dai ni dai Allah ina bukatar mijina a kusa dani yanzu na kasa barci. Jin haka yasa jikin sa mutuwa ya kamota ya kwantar kan cinyarsa ya ce "Ki fa ra barci a nan kafin na ƙara gwada wa ko Allah zai sa adace. Ta na kwanciya ta tura kanta cikin girjin sa kamar zata shige ciki. Ai kuwa ta na kwanciya sak Ƙon na shiga hakan yasa ya ɗan saki karar murna yana godewa Allah sannan ya ɗago da ita ya na faɗin "Gaskiya Ameera ke alkairi ce a rayuwata, kuma keɗin mai sa'a ce, duba daga zuwanki har saƙon da tun ɗazu nake ta fama da shi ya shiga. Ameera ta yi dariya ta na faɗin ba wai zuwana ba ne kawai fa ikon Allah ne. Adam ya yi charaf ya ɗauƙeta sai cikin ɗakin sa kan makeken gadon su. Ya na kwantar da ita ta ce "Wannan irin ɗauka da kake min ko jinjira ma ƙare kenan, har na mazu na samu ciki ka daina daukana irin haka domin nasan zanyi nauyi. Adam ya yi murmushi ya ce "Honey wallhi kullum addu'a na ke a ce yau kina ɗauke da cikina da daga wannan ranar kin daina komai har sai kin haife min shi ko ita ko su. Idan zakije kicin zan goyaki, idan zaki shiga toilet zan goya ki, ke koma me zaki yi to kina baya na. Nifa da sai na kafa tarishin da ba'a taɓa samun mijin da yayi shi ba, domin aihuwar ma tare zamuyi. Ameera ta yi dariya domin ta saba jin irin waɗannan maganganun a kan cikin da ba'a ma riga an samu ba. Ta ce "Ni dai zan so naga ranar da za'a dinga koya ni ko ina na ce zan je. Adam ya ce to ki dage ki ɗauki ciki ko yau ne kiga aiki da cikawa daga bakin masu abun, yana faɗa ya na kamota suka shige bargo ya na ƙara cewa, da Kinga yanda maza ke naƙuda suna taya matansu aihuwa. Kalmar ta ya matansu aihuwa ce ke ta yawo a kan Ameera lokacin da ta dawo daga tunanin. Afili ta ce "Gashi ba'a tayani haifa ba za'a tayani zubarwa. Sai ma yanzu ta ke ƙara tunano irin alƙawarin da yayi akan ta muddin ta samu ciki. Hannu ta kai ta shafo wuyan ta ta ce "Allah ya isa mugu wallahi kasheni yaso yi, wai ma yaushe Adam ya koma haka, ko dan mutuwar da wannan matar ta yi ne, to ai naga ba nice na kashe ta ba, kuma ma ni matar sam ban yarda da itaba ƙara ma da ta mutu. Ta na cikin haka taji ana ƙoƙarin buɗe dakin nata, hakan yasa ta dawo da kallonta izuwa gurin. Adam ne ya shigo yana tafiya a gwale kamar ɗan kaciya hakan yasa Ameera kafe shi da ido ta na son yin dariya, ganin yanda ya haɗe fuska ne yasa ta ƙara jin dariya ya zo mata, ai kuwa ta ke ta saki kayar ta harda tafa hannu ta na nuna shi. Adam kuwa ganin irin dariya da take yine yasa ya ƙara jin wani mugun haushin ta, haka ya shige toilet ba tare da ya tanka mata ba. Ya na shiga ta bishi ciki ta na dariya. Bai ce mata komai ba ya shiga cire kayan jikinsa ya juya mata baya amma da dawo ta gaban sa ta na kallon yanda suka koma kamar ta yara. Lokaci ɗaya ta ƙara sakin dariya harda faɗuwa. Sosai Adam ya kai chan sama mutuƙar ƙuluwa, amma a zabar da ya ke ji ba zai biye mata ba, shi dai hukuncin da ya yanke kawai shi zai aiwatar. Haka Amera ta ke ta faman dariya har ya yi wankansa bata damu da jiƙata da yayi ba, ganin ya kusa gama wankan ne yasa itama ta fara nata wankan ba tare da ta cire doguwar rigar jikinta ba. Adam na fitowa ya saka doguwar jallabiya ba tare da ya saka wando ba, ya kwanta yana kallon sama yana addu'ar Allah yasa dai abun na sa su tashi kar su samu matsala. Ya na cikin haka yaji fitowar ta. Rintse ido ya yi yana jin wani faduwar gaba lokaci ɗaya, hakan yasa ya riƙe gefen zuciyarsa ya na salati. Ameera kuwa tun a cikin toilet ta gama shirya irin muguntar da zata masa badan komai ba sai domin taga yanda zai yi. Ta na fitowa daga ita sai tawul wanda girman cikinta bai sa ya ɗauru sosai ba. Ta na fitowa tazo gaban sa ta ce "Malam ina bukatar haƙkina a gurin ka yanzu. Ita kanta da ta yi maganar taso ta yi dariya domin ganin irin kallon da yayi mata, amma ta dake ta na ƙoƙarin ɗaga rigarsa. Adam da ko magana baya jin zai iya yi ya ce "Idan kika taɓa ni Allah ya isa ban yafe ba. Adam ya faɗa kamar zai yi kuka tsabar takaice. Ameera ta ce "Ban gane Allah ya isa ni da hakkina ba, yo ta ina Allah ya isarka zata bini bayan Allah bai hana ba, kawai ka tashi ko na kwata da ƙarfi na. Ta ƙara sa ta na ɗaga rigar tasa. Idan da tasan irin azabar da yake ciki da tai masa uzuri amma ganin da gaske ta ke yasa Adam faɗin. "Dan Allah kiyi haƙuri. Ameera kuwa cike da mugunta ta ɗage rigar tana ƙara kallonsu tasa hannu ta taɓa, sai kuma ta kama da niyar jansu ko zasu tashi. Ai kuwa Adam ya kurma ihuu wanda yasa Ameera saurin sakin su tana kallon sa. Ganin haka yasa Ameera ƙara dawo da shi ta ce "Malam Allah fa sai na karbi hakkina. Ta ƙara kwantar da shi zata ƙara kamawa jin tana son kashe shi ne yasa Adam faɗin. Idan kika ƙara taɓawa wallahi a bakin auranki!. Kina karawa na sakeki. Ya na faɗa hawaye na zubowa daga idanun sa. Da sauri Ameera ta miƙe tsaye ta saki dariya ta na faɗin, ai ko baka faɗa haka ba ma ba yi zan yi ba, to ina abun ya ke, dama ina so ne kawai na gani ko zasu iya tashi. Ta na faɗa ta nufi gurin kayanta ta ɗauko wata doguwar rigar irin ta jikinsa ta saka bata ko shafa komai ba sai turare, ta zo kusa da shi ta ce "Honey dan Allah ka ƙara ɗauko mana wata mai aikin please ni ba zan iya komai na gidan nan ba, idan yaso wannan karan ka samo mana tsohuwa kaji? Adam ya lumshe ido ya buɗe ya ce "Tom" Amera ta rungumo shi ta na kantar da kan ta a kan ƙirjinsa ta ce "Na gode Honey sannu Allah ya baka lafiya kaji. Ta faɗa cikin seriously. Jin ta yi barci a jikinsa ne yasa ya tashi ya zauna ya na kallonta. Lokaci ɗaya hawaye suka wanke masa idanu idan ya tuno da cewar wai Amera ta Adam ɗin sa ce ta dawo haka, Ameera da bata ko iya ɗaga sautinta a kan nasa, Ameera da take son abin da yake so fiye da shi, Ameera da bata son ko damuwarsa amma wai ita ce yau take son kashe shi. Shi dai har yanzu bai yarda laulayin ciki ba ne wannan, wallahi wannan yafi ƙarfin laulayin ciki domin idan ya tuno abubuwan da ta yi sai ya ƙara tabbatar da cewar ba laulayin ciki be. Azuciyarsa ya ce "To me kenan? Sai kuma ya yi shiru ya na tunani. Shi dai yasan babu komai kuma babu alamar komai a tare da ita. Tashi ya yi ya koma waccen ɗakin ya ɗauki wayarsa ya kira Najib a kan yazo gidan yanzu, amma Najib ya sheda masa cewar baya gida yanzu kuma ba zai dawo ba sai dare ya bari kawai su haɗu gobe. Ya na sauke wayar tunanin Haura ya faɗo masa. Ya ce "Yarinyar kirki mai haƙuri Allah yasa ki dawo muna kewarki. Ya na faɗa ya tashi ya cire wannan doguwar rigar ya saka ƙananan kaya da wando gajere so yake ya kai karar Ameera gurin iyayenta domin susan halin da ake ciki. Ya na gama shiryawa ya fita daga gidan, amma ganin irin tafiyar da ya ke yi ne yasa dole ya dawo domin yasa tabbas kallo ɗaya za'a ai masa a gano a kwai wata damuwar. Kadija ya kira amma bata amsa ba sai kawai ya tura mata da saƙo akan ta saka shi a cikin addu'a. Da yamma da kansa ya shiga cikin domin yasan ita kam ba shiga zata yi ba, shi kuma yunwa ya ke ji, hakan yasa ya shiga ya haɗa musu abinci mai sauƙi. Bai gama abincin ba har kusan an fara kiran magariba hakan yasa ya na jere abincin ya yayi wanka ya fita Masallaci. Kafin ya dawo itama ta ta shi ta kara yin wanka ta fito palo ta na hamma. Ganin abinci a jere yasa ta ja tsaki ta nufo gurin abincin ranta duk a jagule. Ta buɗe ta ga abin da ke ciki sai taji ita kawai ɗan wake ta ke son ci ba taliya ba, komawa ta yi ta daura alaula ta fara Sallah. Bai dawo ba sai da ya tsaya a ka idar da sallar isha. Ya na shigowa ya sameta zaune ta ta na jiransa. Ba tare da ya ce mata komai ba ya zauna ya buɗe abincin ya fara zubawa, ganin bai ce mata komai ba ne ta ce "Honey ya jikin baka? Adam kaman yayi kuka dan takaici, yau she ya ce mata bai da lafiya, idan ma abun da take nufi ne ai ita ce sila. Bai ce komai ba ya ci gaba da zuba abincin sa. Sai ta ƙara ce wa "Honey ni me zan ci ne? Ta yi tambayar domin shima yasan bata son taliya. Adam ya ɗaga kai ya mata kallo ɗaya sai yaga kamar ba fuskar Amearan sa ba tsabar haushin ta da ya ke ji. Ganin dai ba tamka mata zai yi ba ne ya sa ta ce "Wai ina ta magana ka min shiru, kai kasan ni ba wani damuwa na yi da wannan taliyar ba, kuma ka dafa duda kasan bana so, na zo ina maka magana kuma ka yi shiru? Adam ya ce "Abun da na ke so na dafa kema zaki iya zuwa ki dafa abun da kike so. Ameera ta kalleshi ta ce.. "Ok tanan ka ɓullo kuma? To ni ɗan wake nake so ka dafa mini, please shi nake son ci. Ta faɗa cike da bada umarni. Adam ya ci ga ba da zuba abincin sa ba tare da ya ce komai ba. Ta ce "Ba ka ce komai ba fa? Ya ce "Bazan iya ba" "To me ka ke nufi da bazaka iya ba? Kenan haka zan kwanta banci komai ba? Cikin tsananin bacin rai da wannan taƙura shi da ta yi Adam ya ce "Na ce ba zan iya dafa miki ɗan wake ba, idan kina so ki tashi ki yi kayan ki na gama magana. Ya faɗa cike da ƙunci da takaicin ta. Jin haka yasa Ameera faɗin... "To wallahi ba ka isa ni na kwana banci abinci ba kai kuma ka ci, sai dai duk mu kwana a haka. Ta na faɗa ta ture kulan abincin ƙasa ta ɗauki wanda ya zuba a fleet ta ɓarar da wannan ɗin shima, sannan ta ce "Sai dai kowa ya kwana bai ci abinci ba a cikin gidan nan wallahi. Adam da rabon sa da abinci tun safe, tsabar yunwa har wani jiri-jiri yake ji. Kallonn kulan abincin ya yi ganin duk ya zube babu komai sai yaji kamar an cire masa duk wata laka ta jikinsa, lokaci ɗaya ya ji wani irin abu na ɓacin rai da bai taɓa jin irin ba ...✍️ _Comments ɗinku shine ƙwarin guwa na_ *One love* *One House* *Comment's* *Shering please* *Love all my fan's* *S-Reza typing...* AMEERA DA ADAM 14 By S-REZA WHATTPAD Salis M Reza Chapter1️⃣4️⃣ ... Tsabar ɓacin rai muryasa har rawa ta ke yi ya ce "Yanzu abincin da zan ci ɗin shine ki ka zubar Amera? "Ai muddin ka ce bazan ci abinci a gidan nan ba to sai dai kowa ya huta wallahi " Amera ta ƙarasa ta na miƙewa zata bar gurin. Adam ya ce "Haka kika ce ko? Ta juyo ta ce "Eh haka na ce babu wanda zai ci komai yau. Ta na faɗa ta ci gaba da tafiyar ta cike da jin haushin rashin dafa mata Ɗanwaken da take son ci. Sai da ta shige ɗakinta sannan Adam ya iya miƙewa daga gurin ya nufi ɗakinsa da niyar ɗaukar kin mota ya fita waje ya naimi abinci domin ba zai iya kwanciya bai ci abinci ba saboda wata iriyar mahaukaciyar yunwa da ya ke ji. Ɗan makulli kawai ya ɗauka sai ATM dinsa ya na tafiya ya na jin haryanzu jiri na ɗiban sa. Sai da yazo bakin ƙofar palon ya ganta tsaye da makulli ta na masa wani irin kallo. Lokaci ɗaya gabansa ya faɗi domin bai tsammaci ganin ta a gurin ba. Bai ko iya mata magana ba shima ya tsaya ya na kallonta kamar yaga wata halittar. Kallon-kallo kawai suke wa juna kamar wasu abokan karawa. Shi Adam ya na kallonta ne cike da mamakin yadda a ka yi Ameerar sa ta dawo haka, domin ya lura wannan halittar da ke gabansa mai amsa sunan Amera wallahi kashe shi ta ke son yi, domin shi dai zai iya dafa Alqur'ani mai girma a kan cewar wannan ba Ameerar sa ba ce, kallonta yake yi sosai ya na son ya gano wata sheda da zata nuna masa cewar ba ita ɗin ba ce, amma babu alama sai wannan ƙaton cikin dake jikinta wanda izuwa yanzu babu abin da ya tsana kamar wannan munafikin cikin. Ita kuma Ameera ta na mamakin ƙarfin halin sa ne ganin shi yaƙi ya dafa mata nata abincin amma shi ya zo zai fita ya je ya ci ita kuma ko ohoo ko! Dama ta yi wannan tunanin hakan ya sa ta na shiga ɗaki ta yi saurin ɗaukar kii ta fito domin tare shi. Sun kai kusan minti biyar a haka kafin Adam ya ce "Bani hanya zan wuce? "Babu inda zaka je na faɗa maka, idan kuma kana son fita to ka tsaya ka dafa min abin da na ce maka sai ka je duk inda kake so ka sayo abincin ka. Adam yayi shiru ya na tunani. Baida ƙarfi a jikinsa badan haka ba da sai yai mata dukan raba raini kafin ya fita abinsa, ga kuma yunwa da ke ta kiɗan amaja a cikin sa, ga har yanzu gabansa zafi yake masa. Sa ke kallonta ya yi ya ce "Dan Allah wace ce ke? Cike da mamaki Ameera ta ce "Ban gane ba wai ni ka ke tambaya? Adam ya ce "Dan Allah ke wace ce? Mai nai miki kike son kashe ni? "Cike da takaici da mamaki ta ce "Wai ko ka fara shan ƙwayoyin gusar da tunani ne? Au wai kai dama kallon da ka ke min kenan? To ni ce dai Ameera wacce ka sani. Cikin rashin sanin abin yi Adam ya juya ya koma ɗaki harda hawaye. Sai da ya shiga ɗaki amma ya fito ya sameta har lokacin ta na Palo a zauna da alamar dai shi take fako, bai ce mata komai ba ya shige kicin ya tsaya ya na tunanin dame-dame ma a ke buƙata idan za'ayi Ɗanwake! Ruwa ya fara ɗorawa sannan ya buɗe buhun fulawar da ko taɓawa ba'ayi ba, Nan take ya ɗaibi daidai da yanda ya ke tunanin zai masa, sai da ya juye a wata roba sannan ya zuba ruwa sai kuma ya fara tunanin anya ba'a zuba wani abu bayan fulawa? Shiru ya yi yana tunani, gashi kuma ya bar wayarsa a ɗaki kuma baya so Ameera ta taya shi Gashi yana bukatar sanin wani abun, shi tun da kaye bai taɓa ko gwada yin ɗanwake ba, bai ma san dame-dame ake buƙata ba. Kaman zai yi kuka ya shiga tunani, lokaci ɗaya Haura ta faɗo masa arai ya ce "Ina ma ta na nan! Ya daɗe a haka har ma ruwan ya fara zafi sai ya shiga dube-dube a cikin kicin ɗin, ganin babu sarki sai Allah ne yasa shi dole fita domin ɗauko wayarsa ya kira Kadija. Daidai zai fita ita kuma Ameera ganin ya daɗe a cikin ɗin sai ta biyo bayan sa ta gani ko ya fara yin ɗanwaken ne. A bakin ƙofar kicin ɗin suka haɗu ya wuce ba tare da ko yayi mata magana ba. Ita kuma ta ce "Ko ɗanwaken kake dafawa ne? Ta yi tambayar ta na shigewa ciki. Ɗakinsa ya shiga ya ɗauki wayarsa ya kira Kadija amma ba'a ɗaga ba, yana ƙara kira ta ɗaga ta na faɗin "Yayana na kaina barka da dare? "Lafiya alhamdu lillah ya jikin na ki? "Jiki da sauƙi " "Ok please ina so na tambayeki ne cikin gaggawa " "Ok Yaya ina sauraronka Allah yasa na sani" "Adam ya ɗan sai ta muryasa ya ce "Please dan Allah ya ya ke haɗa ɗan wake? Shiru Kadija ta yi ta na jin tausayin yayan nata domin tasan wannan aikin Ameera ne a wannan daran da kowa ke so ya huta amma ita ta wani haɗa shi da yin ɗanwake. Afili ta ce "Yaya bari yanzu na dafa sai Najib ya kawo maka kaji? Adam yayi ssurin cewa "No har fa na ƙwaɓa fulawar kawai ki sanar dani ɗin yanzu pls. Kadija ta ce "Ok zan turo maka yanzu ta message. Ta faɗa ta na kashe wayar Adam kuma ya nufo kicin ɗin yana yi yana duba wayar tasa. Yanzu ma daidai zai shiga itama zata fito riƙe da kofi ɗauke da tii mai zafi. A hankali ta ce sannu da aiki domin ta yi mamakin ganin yanda ya daɗa ƙwaɓar ɗan waken bai yi ruwa ba kuma bayi tauri ba. Ba tare da ya tamka mata ba ya shige yana jin ƙarar saƙo a wayar tasa. Kafin ya buɗe ya kalli gurin da fulawar ta ke sai yaga an ƙwaɓa daidai yanda kawai sai dai a fara zubawa aruwa. Kallon hanyar waje yayi yana jin taikaicin taimaka masa da ta yi. Haka ya shiga jefa ɗanwaken har ya gama sannan ya soya man gyaɗa, dama sunada yaji mai daɗi a ajiye, lokaci ɗaya shina abin ya shiga ransa ga wani ƙamshi dake tashi daga cikin man da ya sha albasa, a gefe guda kuma ga ɗan ƴen tumatur da albasar da ya yanka, sai kuma soyayen naman da ke cikin firiza shima ya ƙara soyawa. Tun tana Palo ƙamshin man da na naman ya cika mata hanci, har wani leƙe take yi tana Allah-Allah ya fito ta fara kaiwa bakinta. Haka ya fito da gaba ɗaya abincin Palo sannan ya koma ya ɗauko mai da naman, sannan ya ƙara komawa ya ɗauko fleet da cokula masu yatsu. Sosai ya ke yin komai cikin sauri saboda yunwa da ke ta hautsuna halittun cikin sa. Sai da ya gama zubawa yana nufin miƙa mata amma tayi wani saurin fusge wa saura kaɗan ya zube ta na ce ko nasa ne. Ita kanta sai da taji kunyar abun da ta yi. Girgiza kai kawai Adam ya yi shima ya shiga haɗa nasa. Sai da ya gama zuba komai ya na ƙoƙarin ƙara yaji yaji tana faɗin ƙara min wannan yamin kaɗan. Kafin ya ce komai ta ƙara ɗauke na gaban nasa domin kuwa ɗanwaken yayi mata daɗi sosai. Ta ce "Ai dama kai taliya zaka ci ko? To kawai ka bar min sauran gobe da safe zan ci, in yaso Kai yanzu sai ka shiga ka dafa taliyar ta ka yanzu ka ji? Ameera ta ƙara sa ta na rufe sauran ɗan wake dake ruwa a robar. Cike da mamaki Adam ya ce "Ban fahimta ba, yanzu kina nufin sai na ƙara shiga kicin nayi girki bayan ga wannan da yawa? Ameera ta ɗago kai baki ceke da ɗan wake ta ce "A'a dan Allah kar mu yi haka da kai! Kaifa ka ce taliya kake so ni kuma na ce ɗan wake kuma ni yanzu gashi ka min nawa ba sai kama ka yi naka ba. Adam ya kalli robar ɗan waken ganin ga ɗan waken da yawa ya ce "Na fasa cin taliyar tunda ai kece kika zubar da wacce na dafa ɗin nima yanzu wannan ɗin zanci. yana faɗa yana ƙoƙarin jawo robar gaban sa, amma Ameera ta yi saurin ɗora hannunta a kan robar ta ce "A'a kar mu yi haka wannan shine zanci har safe please kaima dafa naka ko kuma ka fita kaje ka sayo. Sosai Adam yake jin yunwa domin ya na daidai gurin da zai iya sumewa tsaɓar yunwa. Haka ya na ji yana gani ya mike ya ɗauki wayarsa da makullin Mota ya fita cikin daren domin nemawa cikin sa abun da zai ci. Ya na tafiya hawayen azaba da na taikaci na zuba a idanun sa har bai san lokacin da ya bigi motar wani ba. Ai kuwa da sauri mutumin ya fito yana faɗa da zage-zage shima Adam ya share hawayen sa ya fito yana bawa mutumin haƙuri wanda ya haƙura badan yaso ba. Allah ya taimakeshi bai sha wahala ba domin gurin cin abinci ɗaya ya je ya tarar basu tashi ba. Sai da ya zauna ya cika cikin sa, kafin ya sayi wani ya nufo gida da shi. Daidai yazo gurin da ya haɗu da su Haura wancen karan ya hango mutane biyu zaune kamar kuma mata. Kamar ba zai je gurin ba ya fito daga motar ya nufi gurin yana ɗan tsoro. Sallama ya yi yaji an amsa masa ya na son ya ga ko dai Haura ce. Wasu ƴan matsan mata ne waɗanda baza'a kirasu yara ba kuma baza'a ce musu tsofi ba ne su biyu ya gani wanda hakan ya bashi mamaki ganin dare yayi. Adam ya ce "Bayin Allah me kuke yi anan a cikin wannan daran? Ɗaya daga ciki ta ce "Ai anan muke kwana bamu da gurin zuwa, munada yawa harda yara yanzu haka wasu daga cikinmu ana zuwa ne a ɗauke su sai a dawo dasu da asuba. Adam ya ce "A'uzubillahi! Almajiran ma haka ake muku? Ta ce "To yaya zamuyi haka rayuwa tazo mana da shi" Adam ya ce "Karki wa rayuwa ƙarya baiwar Allah kuma ai da goyan bayanku a keyin komai daku, idan baku yarda ba baza'a mu ta ƙarfi ba ko. Sai matan suka yi shiru. Adam ya ce "Ina wata mata tsohuwa da ƴarta ana cewa ƴar Haura, kwanakin baya ina ganin ta anan amma yanzu bana ganinsu lafiya dai ko? Ɗaya matar da bata ce komai ba ta ɗago ta kalli Adam ta ce ... "Itace kaɗai yarinya mai hankalin da bata yarda da bin kowa amma itama wani mai mota yazo ya tafi da ita wanda itama tun lokacin babu wanda ya sake ganin ta, daga baya ma mahaifiyarta ma ta fita, to har yau bamu ƙara jin ɗuriyar su ba. Adam ya ce "To Allah ya ƙara tsarewa. Suka amsa da Amin sannan ya ɗauko wannan abincin ya ajiye musu ya zaro kuɗi ya miƙa musu ya na tausayin irin wannan rayuwar. Azuciyarsa ya ce to ina yaransu! Ko basa da ƴaƴa ne? Haka dai ya ƙara so gida yana saƙe-saƙe a game da rayuwar waɗannan bayin Allah, wanda ya gudurta a ransa cewar zai taimakesu. Wanka ya fara yi kafin ya shirya cikin kayan barci, sai dai yana kwanciya Amera ta shigo ta na faɗin "Tun ɗazu ina jiran ka a Palo amma dan wulaƙanci shine kana ganina zaka shareni ka wuce ko Adam?" Adam ya bita da wani irin kallo domin kuwa babu komai a jikinta daga ita sai wandon ciki sai rigar mama ga ƙaton cikinta da yake jin kamar ya soka masa wuƙa ya sace kowa ya huta! "Aiyya sorry ban kula da ke bane" "Ai dama bazaka kula ba tsabar wulakanci ai ko baka ganni ba zaka shiga ɗakina ka duba ko lafiya nake. Ta ƙara sa tana hawowa kan gadon, ta na zuwa ta faɗa kansa wanda cikin nata ya tokare Adam ɗin. Kwantawa tayi a jikinsa ta ce "Honey ina fa buƙatar ka sosai a tare dani Allah" Cikin sauri Adam ya ce "Amma kinsan dai bana da lafiya ko? Kuma kece kika jawo komai. Ameera ta ce "Baka da lafiya na me? Wai har yanzu abun bai ware ba ne? Ta faɗa ta na miƙewa daga jikin sa ta na ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ta gani. Da sauri Adam ya miƙe zaune ya ce "Please honey wallahi babu abun da zata iya, rokon Allahn da nake yi Allah yasa baki jawo min wata matsalar a gurin ba. Amera ta ce "To wai ka tsaya na gwada dabara ko zata tsaya mana. Ta ƙara faɗa tana ƙara kai hannu a karo na biyu gabansa. Adam ya ƙara rike hannunta ya ce "Babu abun da zan iya wallahi har yanzu zafi yake min bana ko so a taɓa please kiyi haƙuri. Cike da ɓacin rai ta ce "To ai laifinka ne ka bari na kwada ka gani ƙila ma idan aka yi shikenan ta ware kuma ka samu sauki kawai bari ka gani Allah zaka iya ai ba komai ba ne. Ta ƙarasa ta na cire masa kayan jikin sa, sai da tazo kan wandon Adam ya ƙara cewa "Please honey please?" Ameera ta kawar da kai ta na faɗin "Wai wannan wani irin abun kunya ne dan Allah Honey, kaman wacce zata yankaka ko zan maka kajiya? Kawai fa raya sunnha zamu yi. Tana faɗa ta cire wandon wanda sai da Adam ya saki ƙara domin yaji zafi sosai... Comments ɗinku shine ƙwarin guwa na One love One House Comment's Shering please Love all my fan's S-Reza typing... *AMEERA DA ADAM* *15* *By S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ *Chapter 1️⃣5️⃣* ... Kallon abun nasa ta tsaya yi ganin yanda suka koma kaman na yaro ƙarami, sai kuma ta kalleshi ganin yadda ya rufe ido alamun kunya. Afili ta ce "Wai mai nake gani haka ne Honey? Ta na faɗa ta sakko daga kan gadon ta na jin haushin abun da ta gani ɗin. Ganin ta fita daga ɗakin ne yasa Adam mayar da kayan sa ya kwanta ya na jin kamar ba daidai yake ba. Sosai ya kwanta ya na tunanin abubuwan da Ameera tai masa daga samuwar wannan cikin kawo yanzu. Ya tuna dukan da yasha a hannun soja, ga wuƙa da ta soka masa, ga shi yanzu ta kashe masa gaba, ga abun da taiwa Kadija, ga kashe mahaifiyar Haura da tayi, ga dukan ita Hauran, ga ƴan aiki biyu da suka gudu daga gidan tsabar masifa da bala'i. A haka har barci ya ɗaukeshi ba tare da ya sani ba. Da safe tunda ya tashi Sallah ya shiga haɗa kayansa a cikin ƙaramar jakar sa, sai da ya kwashi duk abun da yake so sannan ya zuge jakar ya ɗauka ya kai bayan motarsa, sannan ya dawo ya ƙara duba duk abin da yake buƙata. Sai da ya gama koshe komai sannan ya ɗaura alaula ya fara nafula kafin lokacin sallar ya ƙarasa. Bayan ya idar ne ya ɗaga hannu yana riƙon Allah ya raba shi lafiya da wannan cikin na Ameera, Allah yasa ta haife cikin yau. Sosai tsabar ruɗewa ma har bai ma san abun da ba zai yiwu ba ma yake riƙon Allah. Bayan ya gama ya ɗauki biro da takarda ya rubuta mata message ya ajiye a bakin gado sannan ya je gaban hoton su shida ita dake cikin ɗakin ya ɗauka ya zubawa ido yana jin hawaye na zubowa daga cikin idanun nasa. Gogewa yayi kafin ya bar gurin ya nufi hanyar fita.Sai da yazo palo sai kuma yayi tunanin zuwa ya duba ta, amma sai ya tuna cewa yanzu haka ta tashi kuma baya so ta ganshi. Hakan yasa kai tsaye ya fita daga gidan yana zuwa ya nufi gurin mai gadi dake alaula ya ce idan ya idar ya bude masa get. Bayan ya sanar da shi ya dawo cikin motar ya zauna yana tunanin ina zaije. Lokaci ɗaya tunanin zuwa garin su Haura ya faɗo masa, sai kuma ya girgiza kai domin bai san hanya ba. Sai kuma tunanin zuwa hotel, shima yaga hakan bai masa ba. Ya na cikin wannan tunanin yaji mai gida ya na buɗe get d'in. Saida ya tashi motar yazo har bakin get kafin ya ƙara juyowa ya kalli gidan yana jin wani irin kewar gidan nasa na ƙara kamashi, a haka ya bar gidan saida yayi nisa sosai kafin ya tsaya a wani masallaci ya bisu Sallah kafin ya ɗauki hanyar barin cikin gari. Ɗanwaken jiya ta ɗauka da niyyar ɗumamawa amma ko da tayi ido biyu da shi sai taga ya fita a ranta, ga kuma yinwa da da take ji. Palo ta fito tana addu'ar Allah yasa Adam yayi musu girki, sai dai tana zuwa taga babu komai a gurin cikin abincin. Ganin haka yasa ta nufi cikin ɗakin nasa ranta a mugun ɓace. Tana shiga ta fara kiran sunan sa amma jin ba'a amsa ba ne yasa ta nufi cikin toilet tana ɗan kiran sunansa. Sai da tazo bakin gadon zata zauna sai taga takarda hakan yasa ta ɗauka gabanta na faɗuwa. Kasa buɗe wa ta yi sai ta tsaya tana kallon ɗakin ganin an kwashi kaya da dama a cikin sa. Juyawa tayi ta bar dakin izuwa nata ɗakin tana tafiya kamar mara lafiya. Sai da taje ɗakinta sannan ta zauna tana tunanin mai Adam yake nufi ne? Ya saketa kome! Sosai ranta ya ƙara ɓaci hakan yasa ta nufi ƙofar gida tana kiran Baba mai gida. Yana isowa ta ce "Yau she ya fita daga gidan nan? Baba mai gida ya ce "Ai hajiya tun da asuba ya bar gidan da Mota, domin yau ba a yi sallar asuba da shi ba. Cike da ɓacin rai Ameera ta lailayo zagi ta maka wa Baba mai gida. Ta ce "Ɗan kaza-kazan ka shine baka zo ka sanar da ni ba har ka barshi ya tafi? Ta shi daga gabana dalla Malam. Ameera ta ƙara sa tana barin gurin cikin ɓacin rai. Sosai baba mai gida ya ji zafin zagin da Ameera tai masa, hakan yasa ya fara kuka, da zarar ya tuno irin zagin da tai masa wanda tun da yake ba'a taɓa masa irin su ba, sai hawaye ya zubo masa. Wayarta ta ɗauka ta shiga kiran sa amma bata shiga, sosai take mamakin abun da Adam ɗin yayi, takardar da ya ajiye ta ɗauko tana son buɗewa ta karanta amma tana tsoro. Nan take ta shiga boɗewa zuciyarta na tabbatar mata da cewar Adam ba zai iya sakin ta ba, ko dan wannan cikin dake jikinta. Tana fara buɗe wa taci karo da jan rubutu hakan yasa tayi saurin ruɗewa ta ajiye takardar tana riƙe ƙirji. Ta ke ta tuno watarana da Adam ya taɓa sanar da ita cewa baya yin rubuta da jan biro idan kuwa yayi to tabbas ba abu mai daɗi zai rubuta ba. Lokaci ɗaya taji ta daina jin yunwar sai ta koma ɗaki ta zauna tayi shiru! Chan ta miƙe ta saki wasu lafiyayyun tsaki ta na fadin "Aikin banza duk nabi na damu kaina, ai nasan Adam ba sakina yayi ba, kuma zai dawo ya same ni sai ya sanar dani ina ya tafi bai sanar min ba. Sosai ta dawo da walwalarta kamar da, ta shiga kicin ta ɗauko supar commando mai sanyi haɗi da Keck ta zauna ta sha kayanta sosai. Wasa-wasa har bayan sallar la'asar babu Adam babu dalilin sa, hakan yasa ta ƙara gwada layinsa a karo na uku amma bata shiga ba. Tun safe babu abun da taci sai kayan sanyi tsabar ƙyuiwayr yin girki. Haka dai Adam har dare layin sa baya shiga shima bai dawo ba. Bata gama shiga mamaki ba sai da taga har dare babu Adam. Nan fa hankalin ta ya tashi domin bai taɓa yin irin hakan ba, duk yanda ta kai da ɓata masa rai to a gida zai kwana. Sosai take ta faman kiran lambar sa amma a kashe. Ta na son kiran Najib ko Kadija ta tambayesu amma duk ta goge lambobin su a wayarta a cewar ta wai bata da amfani domin su din munafukai ne. Haka Ameera ta kwana cikin zulumi da fargoba, da safe ta fito tana ƙwadawa mai gida kira kamar ita ta raɗa masa sunan, sai dai har ta ƙara sa bataji an amsa mata ba, hakan yasa ta tattaro duk wata ɓacin ranta ta shiga dukan ƙofar da ta gani s a rufe. Ganin kamar babu mutu a cikin ne yasa ta juya a fusace zata koma sai idonta ya sauƙa a kan wata ƙaramar takarda a danneta da dutse. Cike da mamaki ta ɗauka ta fara karantawa ("Na so ace na tafi ba tare da na sanar wa da kowa ba, amma naga yin hakan bai da ce ba,shine yasa na samo yaro ya rubuta muku wannan takardar, ngd da komai, amma ba zan iya zama ƴar cikina tana zagina saboda ina neman a ƙarƙashin su ba. Saboda da haka na tafi na barwa Allah komai shi zai taimaka min, ina godiya wa Alhaji) tana gama karantawa ta saki murmushi haɗi da faɗin. "To dama ni banga wani amfaninka a gidan ba, wai shine harda bayarwa a rubuta saƙo dan rashin kunya. Take ta yayyaga takardar ta koma ciki tana mamakin wannan tsohon. Kwana huɗu kenan yau babu ko labarin Adam ita kuma ta kasa sanarwa da kowa hatta iyayenta, gashi a cikin kwana huɗun nan sai taji kamar ana mata motsi a cikin gidan hakan yasa yau ta shirya domin zuma gidan su Kadija daga nan ta je gidansu. Sosai take damuwar rashin mijin nata, kana kallonta zaka hangi damuwa cike fall a fuskar ta. Tafiya ta ke yi tana hawaye har ta zo bakin get ta tsaya tana kallon get d'in dake rufe wanda tasan ko me taci bazata iya buɗewa ba. Ƙaramar ƙofar ta buɗe ta fita sannan ta rufe ta waje, mai keke napen ta tsayar ta shiga tana sanar da shi gurin da zai kai ta. Bayan an kawo ta gidan su Kadija ne ta biya mai keke sannan ta nufi cikin gidan. Ƙaramar ƙofar gidan a buɗe take hakan yasa kawai ta shige ciki ba tare da ta iya ko sallama ba. Mai gadi na ganinta ya taso ta sauri yana tambayar wace lafiya. Amma ko ta kansa bata tsaya biba. Ganin da gaske tafiya take yasa mai gadin saurin shan gabanta ya na faɗin "Malama wacce ke? Me kike nema? Ameera da bata jin zata iya masa magana ta ɗan raɓa zata wuce ya ƙara tareta, ai kuwa ya buɗe baki zaiyi magana ta sauke masa yatsu biyar a kuncinsa wanda yasa shi saurin komawa gefe cike da mamaki, kuma sai a lokacin ma ya gane ta. Ta na shiga gidan taci karo da Najib ya na ƙoƙarin fitowa. Komawa da baya yayi ita kuma ta bi shi da harara. Daidai lokacin kadija ta biyo shi da hula tana faɗin "Yaya na zo ka sauya wannan hular zata fi dacewa da kaya.. bata ƙara sa ba ta gansu tsaye curko-cirko hakan yasa ta ce "Ameera a gidan mu yau? Ta yi maganar cike da mamaki. Ameera da abun da Kadija din tayi ya bata haushi ta ce "Honey nazo nema ina kuka ɓoye shi? Najib da kadija suka kalli juna kafin Najib ya ce komai kadija ta ce "To fa sabon salo waye kuma Honey kamar sunan tsuntsaye? Cike da jin haushi domin tasan wa take nufi amma take faɗa mata magana, ganin kamar suna don raina mata wayo ne yasa ta tafi kanta tsaye ga abun da ya kawo ta. Ta ce "Koma sunan tsuntsaye ne kona dabbobi wannan ke ya dama, yanzu dai abin da ya kawo ni shine ina kuka turashi yau kwana huɗu babu shi babu labarin sa, haka lumbsrsa itama bata shiga kuma nasan kune kuka zuga shi a kan ya bar gida, idan ma yana nan gidan ne to ku fito da shi mu tafi. Najib ne yayi saurin faɗin"Wai Adam ɗin ne kwana huɗu baya gida kuma number sa bata shiga? Najib yayi tambayar cikin mamaki domin ko jiya sun yi waya da shi kuma ya ce ya na gida. Kadija ta ce "To Kinga laifin sa? Haka kawai ya tsaya a kashe shi babu laifin komai ba ƙara ma ya bar gidan yaje gun da zai huta ba. Najib ne yayi saurin dakatar da Kadija ya kalli Ameera ya ce "Kinga zauna muyi magana, bari na kira miki shi, mu ai bamu san baya nan ba. Kira ɗaya Adam ya ɗaga yasa wayar a amsa kowa. Adam na ɗagawa Najib ya ce "Gani a ƙofar gidan ka Allah yasa kana ciki? Adam yayi jim ƙadan kafin ya ce "Eh shigo ina ciki. Sai Najib ya ƙara cewa "Ina fatan Ameera ma tana ciki ko? Adam ya ce "Idan ka shigo sai ka gani sarkin tsoro! Yana faɗa ya kashe wayar. Ameera da ta yi mutuwar tsaye tun da a ka fara wayar ta ce "Wai yana gida da gaske? Kadija ta ce "Wai anya kuwa Ameera kanki ɗaya kuwa? Ko dai kin fara hauka ne, kai gaskiya inaga wallhi aljannu sun shafe ki ne, a she ma mijin naki na gida kika fito kina neman sa. Najib ya ce "Kinga ta shi muje gidan. Kadija ma ta yi wuf ta ce "Wallahi nima sai naje. Ameera kan ita birninta kawai tayi ido biyu da rabin ranta. Motar NAJIB ɗin suka shiga Ameera na jin kamar baya gudu. Suna zuwa bakin get d'in gidan Najib yake ta hom amma shiru, ita kuwa Ameera da tsabar zumuɗi ta manta da cewar babu ma mai gadi a gidan. Najib ne da kansa ya sauƙa ya buɗe get d'in suka shiga da motar. Abun da ya fara baiwa Ameera mamaki shine motar Adam da ta gani a fake a gurin fakin. Sai da ta rufe idonta ta buɗe kafin ta ƙara sa gurin motar ta shafa ta. Ita dai Kadija sai taɓe baki take yi cike da jin haushin Ameera ɗin. Basu ƙara ruɗewa sai da tayi ido biyu da abun da ya tsayar da jin su da ganinsu na lokaci ɗaya daga Ameera har Najib. Suna shiga palon suka tarar da Adam zaune a ɗaya daga cikin kujerun cikin palon, sai Haura da ke kusa da shi ita da Amminta suna cin abinci cikin natsuwa. Shi kuma Adam yana latsa wayar hannun sa. Jin sallamar su yasa duk suka ɗago suna kallon ƙofar...✍️ _Comments dinku shine ƙwarin guiwa na._ *Love all my fan's* *AMEERA DA ADAM* *16* *By S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ *Chapter1️⃣6️⃣* ...Kasa ƙarasawa cikin palon ta yi ta tsaya ta na kallon Haura da ta mai da hankalinta gurin cikin abincin ta. Najib ne ya yi ƙarfin halin magantuwa ya ce "Adam mai zan gani haka? Wannan ba wannan matar da ta rasu ba ce? Adam ya kalli Ammin Haura ya ce "Ba ita ba ce ƴar uwarta ce, ai wacce ta mutu ko dama ana mutuwa a dawo ne? Najib ya ƙurawa matar ido ya na jin sam bai yarda ba wallahi waccer matar ce ga shi komai nasu iri ɗaya. Adam ya ce "Kaga nai mi guri ka zauna karka ruɗar da kanka. Najib ya ƙara so ya zauna yana son yin magana amma ganin idon Haura a kansa sai kawai yayi shiru, itama Kadija ta shiga ta zauna idonta a kan Haura da matar da Adam ya ce ƴar uwarta ce. Sai a lokacin Adam ya kai kallonsa izuwa ga Ameera wacce ta yi suman tsaye gabanta na faɗuwa ta na jin kamar mafarki. Adam ya ce "Honey ƙara so mana kin tsaya kina ta kallon mu kamar kinga baƙi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta na kallon Haura ta gefen ido sai ta ga yarinyar ta ƙara girma da haske ga kuma wani kallo da taga yarinyar na mata. Bata tsaya a palon ba sai kawai ta wuce ɗakin Adam ɗin tana zuwa ta zauna a bakin gado ta fashe da kuka. Sosai take kuka tana jin wani abu na kishi na sokar zuciyarta. Acikin palo kuwa Najib ne ya sauya haurshe izuwa turanci ya ce "Wai Adam mai yasa baka da hankali da tunani ne? Yanzu me ye amfanin sake dawo da waɗannan mutanin cikin gidan ka, kai kasan halin matarka amma sam baka tsaron wani abun ya ƙara faruwa ko? Adam ya ce "Bazaka gane bane, yanzu haka yarinyar bata da kowa a duniya domin ƴan uwanta sun koreta, kuma wannan yarinyar mune sanadin rasa mahaifiyarta sai kuma mu barta ta shiga duniya ta lalace? Cikin ɓacin rai Najib ya ce "To idan taimakon su kake so ka kama musu wani gidan mana, dole ne sai ka kawo su cikin gidan ka, wai Adam mai yake damun ka ne, anya kuwa ƙalau kake Adam. Cikin nuna tabbacin zaman su Haura ya ce "Gida dai nawa ne ko? Kuma ni keda ikon aiwatar da komai a ciki gidana ko? Sai a lokacin Kadija ta ce "Haba Yaya gaskiya hakan bai dace ba, mai laifin ka kai su wani gidan sai ka ɗauki nauyin su amma ba ka kawo su cikin gidan ka gurin da matarka take ba, kuma kai kasan halin da matarka take ciki please ya ya dan Allah ka duba wannan shawarar da Najib ya ba..." "Ya isa haka naji dan Allah ku tashi ku fita ina son hutawa, a kwai dalilina na yin hakan. Najib na jin haka ya tashi ya ce "Adam mu kake kora a gidan ka? In sha Allah kuwa ka kori ɗan halak. Ya na faɗa ya bar gidan cikin ɓacin rai, itama Kadija tafi bayan sa ta na leƙen Adam kamar karta ta fi ta barshi. Suna fita ya kwantar da kansa a jikin kujerar da yake zaune ya na tunanin hukuncin da yake so ya yanke. Sosai yake ta nazarin komai yana jin wannan shine abun da zaiyi ya taimaki su Haura. Haura ce ta miƙe ta ɗauki jakar su itama matar ta miƙe suka nufi ɗakun Haura ɗin. Suna shiga matar tabi ɗakin da kallo cikin yaransu ta fara magana "Yanzu a nan zamu zauna? Dama anan kike tun tuni shine baku nemo ni ba. Ta yi tsalle kamar ƙaramar yarinya ta hau kan gadon tana dariya. Haura kuwa toilet ta shiga ta yi wanka ta fito ta saka doguwar rigar daga cikin kayanta sannan ta nufi kicin domin fara girki. Sosai take girkin tana hawaye, idan ta tuno da amminta. Lokaci yayi da zata aiwatar da burinta sannan ta bar musu gidan sai ta gama lalata komai tsakanin Adam da Ameera kafin ta tafi domin ba zata iya yafe abun da a kai musu ba. Ɓangaren Ameera kuwa tsabar kuka yasa kanta fara harbawa tana jin cikinta na juyawa kamar wanda zai fita. Ganin babu sarki sai Allah ne yasa ta kurma ihuu tana faɗin "Waiyoo cikinta. Da sauri ya faɗo cikin ɗakin yana kiran sunanta. Ya na zuwa ya ƙara so kusa da ita yana tallafo ta da hannayen sa. Sosai Ameera ta fita a haiyacinta har bata san lokacin da Adam ɗin ya kinkimeta izuwa Mota ba. Asibiti suka nufa yana gudu yana mata sannu. Zauna yake a gaban likitan bayan ya gama zaiyana maso komai na cewa a daure a lallaɓata domin idan ba haka ba za'a illata abun da ke cikin nata, domin ta kusa rabuwa da shi. Haka dai lokacin ya faɗa masa cewar ba komai bane kawai damuwa da tunani ne ya haifar mata da ƙunci har cikin nata ya mata wannan irin ciwon. Haka Adam ya fito daga gurin likitan yana jin cewar ko me zai faru sai ya faɗa mata burinsa domin shi yanzu harga Allah ta fita masa a kai kawai hakan za'a yi. A kan hanyarsu ta zuwa gida ne yaga taƙi ko kallonsa shima yayi kamar bai ma san da ita a gurin ba. Ita Ameera tana tunanin wai tun lokacin da ya tafi dama gurin su hauran ya je ko yaya! To yanzu da ya dawo dasu mai yake nufi? To ita uwar yarinyar ma ba ance ta mutu ba me ya dawo da ita? Sosai kanta ya kulle ga wani haushin Adam ɗin da take ji, ji take tana buɗe baki uwasa da take kushewa zata zaga. Shi kuma Adam tuni ya faɗa tunanin yadda zai faɗa mata cewar yana son ya auri Haura ne domin shine kaɗai abun da zai mata ya biyata abun da sukai mata. Suna isa Ameera ta kama ƙafar motar da niyyar budewa amma ta jita a rufe, ta juyo ta kalleshi amma taga ya haɗe fuska ko kallonta baya yi, itama bata ce komai ba sai idonta da ya ciko da ƙwalla tana ƙoƙarin fashewa da kuka. Bai damu ba domin shi dai zuciyarsa ta cika da son auran yarinyar da take masa gizo a ko da yaushe. Ya ce "Magana nake so muyi? Ameera ta yi shiru. Ya ƙara cewa "Dake fa nake magana Ameera? Da sauri Ameera ta ɗago ta kalleshi jin sunanta ɓaro-ɓaro a bakin sa. Take hawayen da take tarewa suka zubo ta ce "Bana bukatar jin komai daga gareka, ka buɗe min ƙafa zan fita. Adam ya ce "Ok tom bari mu shiga cikin gidan sai muyi maganar a can. Da sauri ta fito tana kuka sosai tana so tayi guda amma jikin ta babu ƙwari ga cikin ta da yayi nauyi. Tana shiga palon wani ƙamshin abinci ya daki hancinta wanda yasa ta saurin kallon hanyar kicin. Haura ce sanye da doguwar riga gashi kanta babu ko ɗan kwali sai dai ta yi pakin kan da ribob, hakan yasa ta yi wani kyau wanda ko ita Ameera ɗin sai da yarinyar tai mata kyau. Cikin ɓacin rai da kuka ta ƙara so gurin Haura ta chakumeta ta baya suka faɗi a ƙasa Amera ta fara kuka ta na dukan Haura akan sai ta bar gidan mijinta. Ana cikin wannan halin Adam ya shigo da sauri ya ɗaga Amera yana ture ta gefe ya ɗaga haura yana mata sannu. Ganin haka yasa Ameera ƙara fashewa da kuka ta na faɗin "Allah ya isa tsakanina da kai Adam, wallahi bazan yafe maka ba , mugu macuci azzalumi, ke kuma sai na ga bayan ki shigiya maiya. Ana cikin haka matar da suka zo da Haura ta fito da sauri tana tambayar Haura lafiya dai ko? Kafin kowa ya ce komai Ameera ta ce "Ubanki ne ya faru, ke ba kin mutu ba uban me ya dawo da ke? Matar cikin yaransu tayi magana tana kallon Haura wacce itama ranta ya ɗan ɓaci "Idan kin isa kiyi maganar da Hausa ko da turanci mana yanda zan ji, da na ci ubanki yanzu a gurin nan. Ganin haka yasa Adam saurin kama hannun Ameera suka nufi dakinsa yana bata haƙuri. Suna shiga matar ta hau Haura da faɗa cikin yaransu kamar zata mareta, ita dai Haura sai hakuri take bata, kai tsabar masifar matar harda murɗewa Haura kunne tana ƙara jaddada mata komai. Suna shiga ɗakin ta ƙwace hannunta ta ce "Malam mutukar kana son zaman lafiya to ka kori wannan matar da uwarta, sannan tun ranar da ka bar gida ina ka tafi sai yanzu? Baka kirani ka sanar dani zaka tafi ba, sannan baka sanar dani dawowar ka sai kawai na ganka tare da su? Adam ya ce "In ji wa ban sanar dake ba, na ajiye miki saƙo kuma nasan kin duba, kuma ko mene ne ai ke kika jawo. Bani da lafiya amma kince sai na kusance ki fisabililahi kin kyauta min kenan? Ameera ta ce "To yanzu dai kawai ka kori wannan yarinyar please? Adam ya ce "Kin manta da cewar Kece kika yi sanadiyar mutuwar uwarta, idan na koreta ina zata je? Amera ta ce "Nifa banyi sanadiyyar mutuwar kowa ba, sannan ita wannan matar wacece idan ba uwar tata ba? Adam ya ce "A'a ba ita bace ƴar uwarta ce Kum.." kafin ya ƙara sa Amera ta ta reshi cikin mamaki ta ce "Ƙarya suke maka wallahi ita ce, na rantse da Allah waccer matar ce, karka yarda da su munafukai ne. Sosai Ameera take rantsuwa tana faɗin munafukai ne. Ganin haka yasa Adam faɗin to koma suwaye zan zauna da su. Amera ta kalleshi ta ce "Adam ka dawo hankalinka idan ma baka da shi. Kafin ta ƙara sa ya ce "Auran yarinyar nake so nayi domin na taimakesu. Shiru ɗakin yayi Amera na jin Kamar ba daidai ta ji ba. Adam ya ci gaba"Dan Allah ki bani goyan baya , zan Auurotane domin ta dinga taimaka miki da aikace-aikacen gida please Honey Karki tada hankalin ki? Ɓangaren Najib da Kadija kuwa suna isa gida Najib ya ce "Kadija tabbas Adam ba a cikin haiyacinsa yake ba, wallahi a kwai matsala ina tsoron ko ba wani abu su kai masa ba, naga gaba ɗaya ya sauya. Kadija ma ta amsa da cewar "Nima abun da ya ke ta min yawo kenan, shima yaya mai ya kaishi shiga sabgar su, yanzu Allah ne kaɗai yasan abinda sukai masa wallahi, ni harna fara tausayin Amera kar su rabata da mijin ta. Najib ya ce "Nasan abun da zan yi ina zuwa. Yana faɗa ya fice daga gidan. Ameera ta ce "Mai ma ka ce? Ya ce "Haura nake so na aura kuma cikin wannan satin, ba shawarki nake nema ba na sanar miki ne saboda kinada hakkin sanin hakan, idan kina da bukatar wani abu ki sanar dani domin ba niki za'a yi ba, mun gama magana da su ..✍️ _Comments ɗinku shine ƙwarin guwa na. Littafin baida tsayi zan iya cewa ma ya kusa ƙarewa_ One House One love Love all Typing S-Reza *AMEERA DA ADAM* _17_ *By S-REZA* *WHATTPAD* _Salis M Reza_ _Chapter1️⃣7️⃣_ ... Lokaci ɗaya Ameera ta sa ki wata dariya wacce sam-sam cikin ta babu nishaɗi. Ta ce "Aure dai zaka yi Adam? Kuma Haura zaka aura ko? Sai kawai taci gaba da dariyar ta har tana riƙe cikin ta. Adam ya tsaya yana kallon ikon Allah, to ko dai Ameera ta samu matsala ne! Juyawa ya yi ya bar ɗakin cike da mamakin Ameera. Bayan fitar Adam Ameera ta tsaya da dariyar ta na kallon ƙofar da ya fita ɗin. Da sauri ta juya gurin da ta ajiye wannan wasiƙar ta ɗauka ta buɗe ta na tsaye ta shiga karantawa. _"Bansan yaya zanyi da ke ba, na gaji da duk wannan abun da kike min, basan haka masu ciki suke komawa ba sai a kanki, yanzu zan bar miki gidan zan tafi neman magani bazan dawo ba sai Allah yayi na warke, domin na lura ke ba ƙaunar samun lafiya ta kike yi ba, Karki neme ni domin ba zaki sameni ba har sai lokacin da na dawo. Ga gidan na bar miki kiyi duk abun da kika ga dama da shi._ Ameera ta juya bayan takardar ko a kwai sauran magana, ganin babu komai ne yasa ta saki tsaki tana faɗin aikin banza ashe ma ba abun da nake nufi ba ne duk na bi na tada hankali na. Sosai auran Nasiru da Nana yake ta natsuwa wanda yanzu saura kwanaki shida hakan yasa Ameera ƙara nisanta kanta da ga bikin domin tayi alƙawarin bazata shiga cikin sha'anin bikin yaron da ya ɗaga hannu ya mareta ba. Haka Adam ya je ya sanarwa da Najib da kadija maganar auran sa da Haura, ai kuwa nan take dukkanninsu suka nuna rashin amincewarsu akan hakan, amma shi ya ce yaji ya gani babu wanda ya isa ya hana shi auran ta. Sosai Najib da kadija suka shiga mamakin wannan masifar, yaya daga ganin yarinya sai ya ce zai aureta, ita kuwa Kadija kuka ma ta fara tana faɗin an asirce mata yaya. Ɓangaren Ameera kuwa, duk wani tashin hankali tayi amma Adam ya ce Aure ba babu fashi, hakan yasa ta koma zagin uwarsa da ubansa da suka riga mu gidan gaskiya. Shi kuwa Adam baya ji baya gani. Itama Haura ta yarda da shi domin yana sanar da ita ta amince nan take, hakan yasa ta fara sakin jikinta a cikin gidan ba kamar da ba, domin yanzu mutuƙar Adam baya gidan to bata yarda da cin fuskar Ameera domin wannan matar da take kira da Ɓultuwa ta gama bata shawara sosai a kan Ameera ɗin. Sai dai abun da yake damun Ameera yanzu bai wuce rashin jin daɗin jikinta da bata yi ba ne, domin yanzu cikinta ya shiga wata takwas da kwanaki, hakan yasa tayi nauyi sosai, amma bakinta bai mutu ba. Da ƙyar take tafiya har ta iso palon ta zauna ta na ɗan sakin ƙara a hankali tana riƙe bayanta, waya ta ciro ta kunna data ta shiga neman littafin da zata karanta na online domin ta kwana biyu bata karanta littafi ba, take ta tuno da littafin da take karantawa na Addininmu bata gama karantawa ba. Tana cikin neman littafin taci karo da status ɗin Adam wanda yayi yau. A hankali ta buɗe tana kallo. Hoton Haura ne wanda ta ɗauka a cikin motarsa wanda yake nuni da cewar yanzu a ka ɗauki hoton domin kayan da ya saka ɗazu ne. Take ta saki wayar a ƙasa tana riƙe kanta da yay mata nauyi. Sosai take jin kanta ya riƙe afili ta furta "Adam ni za za k k ki wa"... Bata ƙara sa ba kuka ya kufce mata ta kwanta a ƙasan gurin ta fara kuka harda jan majina. Tana cikin haka ta ji shigowar su palon alamar sun dawo, da sauri ta yunƙura ta miƙe da ƙyar ta nufo gurin su wanda suma jin kukan nata ne ya tsayar da su suna kallonta. Tun kafin ta ƙarasa gurin ta gama ƙare masu kallo. Haura sanye take da rigar abaya baƙa tayi kyau sosai kasancewar ta fara. Shi kuma Adam manyan kaya ne ajikin sa harda hula, sosai kayan suka zauna a jikinsa daram, ga wani annurin farin ciki dake fita daga fuskarsa. Ta na ƙarasawa gurin ta tsinke Haura da lafiyeyen mari ta chakumeta ta na kuka tana girgizar ta ta na faɗin "Tsinanniya maiya mai kukayi wa mijina? Na ce wani irin asiri kukai masa da zai ce ke zai aura, to wallahi Allah ya fiku kuma sai kun bar gidan nan matsiyata dangin arnaku. Haura dai ta tsaya ta na kallon ta wanda badan Adam na gurin ba tsaf zata rama amma hakan yasa itama ta saki kuka wanda yasa Adam ɗin saurin ƙwace ta daga hannun Ameera ɗin ya ruƙo Hauran jikinsa ya tafi da ita ɗakin su. Ganin haka yasa itama Ameera bin bayansu tana kuka, tana zuwa Adam na dawowa hakan yasa ta kama rigarsa ta fara faɗin "Allah ya isa tsakania da kai shege mugu algungumi wanda ba zai gama da duniya lafiya, wallhi sai dai ka sake ni na koma gidan mu a kan ka auri wannan arniyar kuma maiyar. Ganin haka yasa Adam fara tafiya ita kuma tana biye da shi taƙi sakar masa rigar, sai tafiya yake yana janta amma taƙi daina zagin sa, sai da suka zo har palo kafin ya juyo ya dibeta ya ce "Yanzu sakin kike buƙata ko me? Cikin ɓacin rai dake neman hallkata ta ce "Ka sakeni na ce mugu macuci bana sonka ni kawai ka sake ni" Adam ya ce "Tom sake ni sai na sake ki ɗin ko. "Anƙi a sake ka ɗin wallahi sai ka fasa auran wacce yarinyar ko ba ka so. Adam ya ce "Ok tom yañzu sakar min riga sai muyi magana ko?. Sai da yayi da gaske kafin ta sake shi. Ya ce "Honey ba kya jin magana, ban san mai ya mayar dake haka ba, Please ki natsu ku zauna lafiya da Haura, wallhi bata da matsalar komai kuma zata miki biyayya kaman yadda kike so. Ameera ta ce "Ko me zata min bana so, kawai dai subar min gida shine kawai abun da na ke so. Sannan yanzu ka duba ba fa, ɗaukar ta kayi a mota kuka fita ba tare da na sani ba. "No kaya fa kawai na sayo musu ita da waccer matar. Ameera ta saki tsaki tana kawar da kai gefe. Ganin dai bata da alamar sakkowa ne yasa Adam barin gidan yana jin surutunta amma bai ko waiwayo ba. Ɓultuwa ce tsaye cike da masifu iri-iri take zagin Haura akan yaya zata tsaya ta mareta bata rama ba. Ameera ta ce "Ni Allah so nake kawai ya sake ta amma shima yaƙi kina jin fa irin zagin da take masa amma yaƙi furta mata sakin da yake shima wawa ne. Ɓultuwa ta ce "Shi yasa nake so ayi sauri ayi auran domin kinsan idan har ta aihu komai lalacewa zai yi, dole acikin biyu ayi ɗaya ko dai ya saketa kafin ta aihu ko kuma ayi auran naku kafin ta aihu. Haura cikin matsuwa ta ce "To yanzu ya za'ayi Kinga har zuwa yanzu bai ƙara yin maganar auran ba? Ɓultuwa ta ce "Yanzu baki tuna komai da Ammin ki ta yi akan cikin ba? Haura ta ce "Wallahi har yanzu banga komai ba kuma tabbas tana aihuwa zata dawo hankalin ta muddin bamu nemo abun ba. Ɓultuwa ta ce "Duk laifin ki ne, yaya za'ayi mahaifiyar ki na yin abu amma bazaki so sanin komai ba, yanzu gashi ta mutu kuma ke baki san inda ta ajiye komai ba. Haura ta ce "Nifa sai nake tunanin kamar shegiyar matar tasan abun da Ammin tai mata ne yasa ta kashe ta, ai kuwa wallahi muddin na auri mijinta to itama ko dai ta mutu ko ta bar gidan. Ɓultuwa ta kalli Haura ta ce "Kema fa sai kin ƙara dagewa domin Kinga idan har baki aureshi ba har ta aihu to mun shiga uku domin kuwa shima zai dawo hankalin sa, kuma wallahi korarmu zai yi, Kinga kuwa babu inda zamu je. Haura ta yi shiru sai cen ta ce "Idan yazo da kaina zan masa maganar aure kawai nake so muyi"... Cikin sauri ta tareta da cewar "Karki kuskura ki masa magana bari da kansa zai zo. Haka dai Haura ta fasa amma dai ta matsu yazo ayi wannan auran kowa ya huta. Cikin kuka Ameera ta dauki ƴar ƙaramar jakarta ƴar hannu ta na tafiya ta na kuka Kamar wacce a kaiwa mutuwa. Ta na zuwa ƙofar get ɗin gidan taga get ɗin a rufe, ta na gani tasan adam ne ya rufe. Hakan yasa ta zauna a gurin ta ɗaura hannu a kai ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta kafin ta juya ta dawo gidan ta ɗauki waya ta kira Umma har kira biyar amma babu amsa. Ta lalubo lambar Nana ta kira, ai kuwa kira ɗaya amarya Nana ta ɗaga ta na sallama. Take Ameera ta fashe da kuka ta cikin wayar harda ihu da kiran waiyoooo Allah da na shiga uku duk a lokaci ɗaya. Nana da take tare da Nasiru suna shawarin yanda zasu gudanar da komai na dina taji irin kukan da Ameera ke yi. "Lafiya dai anty Meera? Ta faɗa ta na sauraron irin gunjin ihun da Ameera ke yi. Nana ta ƙara cewa "Anty Ameera wai me ke faruwa ne pls sanar mini mana kodai wani abu ne ya samu Adam ɗin? "Dan Allah Nana kizo gidana yanzu Please zan mutu ki taimaka ki zo tare da Umma wallhi Adam zai kashe muku ni. Jin haka yasa hankalin Nana tashi ta kashe wayar tana faɗin ganinan zuwa yanzu. Ta na gama wayar ta kalli Nasiru da ya wani haɗe rai ya na jiran ta kawo masa wata maganar yanzu su hau sama su faɗo. Cikin ɗan rikicewa da halin da taji yayar tata ta ce "Please ko zaka sauke ni a gidan Anty Ameera wallahi ba lafiya ba kaji fa har kuka ta ke yi. Nasiru da yake jira azo gurin ya ce "Wallahi babu inda zaki je koma mai zai faru ai ita da mijinta ne, ko kin mata irin zagin da tai min kuma ta ce bazata taɓa zuwa bikin mu ba, saboda da haka kema ba zaki je gidan ta ba wallahi muddin na isa da ke. Nana ta ce "Ƴar uwata ce fa, kuma yayata amma kake faɗin haka, to koma me tai maka sai ka hanani zuwa zuwa gidan ta?. Nasiru ya ce "Ni dai idan na isa da ke to karki je, ki bari har sai mun gama abun da muke yi na tafi sai kizo. Nana kuwa da hankalinta duk ya gama tashi da halin da yayar tata ta ke ciki ta ce "Gaskiya bazan iya ƙin zuwa gidan yayata haka kawai ba, kuma sai ka bari sai ka aureni kafin ka kafa min sharuɗan zuwa wani gurin da baka so, amma yanzu dai gaskiya sai naje naji halin da take ciki sai dai kayi haƙuri yayata ce bani da kamar ta koma me zata min. Cikin ɓacin rai ya ce "To wallhi muddin kika bar gurin nan bamu gama abun da muke yi ba to babu ni babu ke har abada, kuma aure na fasa domin bazan auri matar da bata jin magata ba. Dama tasan za'ayi haka domin ta lura da take-tsken sa kenan dama. Ta ce "Allah ya sa hakan shi yafi alkairi. Ta na faɗa ta juya zata tafi amma Nasiru ya kamo hannunta ya juyo da ita ta fuskance shi da kyau ya ce "Wallahi idan har kika bar gurin nan aure dani dake ya fasu kenan har gaba da abada. Ya faɗa yana kallon idonta da har ya fara taruwan ruwan hawaye. Kafin tayi magana har sun gangaro kan kumatunta ta ce "Idan ka fasa sai me? Allah yasa kaine kaɗai na mijin da yayi saura a duniya. Ganin zata tafi yasa ya ƙara juyowa da ita ya ce "Wallahi baki isa ki je gidan wannan munafukar yayar taki ba. Cikin jin haushin kalmar munafuka da ya kira Ameera da ita ta ce "Duk abun da zamuyi da kai karka ƙara zagin kowa nawa domin nima bana zagin kowa naka, saboda haka bazan jura ba, kowa ya girmama dangin kowa shine mutuncin. "To ƙarya nake ba munafukar bace? Matar da take cewa ta tsaneni kuma bata sona da ke, to wallahi ni dai sai na ce mata magulmaciya kuma munafuka. Nana ta ce "Sai dai kaine munafiki amma ba itaba..." Kafin ta ƙara sa ya buge mata baki ya ce "Ni kike kira munafuki. Cike da jin zafin buge mata bakin da yayi ta fara magana "An faɗa maka ɗin, kasan babu dadi ni ka faɗa wa yaya ta. Hakan da tayi yasa hankalin mutane fara dawowa kansu, dama kaf anguwar kowa yasan wannan halin nasu. Ƙarshe dai sai da akayi dokeni in dakeka kafin suka rabu kowa yayi alwashin ya fasa auran ɗan uwansa. Shi Nasiru ma harda faɗin yanzu zai turo a karɓi komai da ya kawo mata. Haka Nana ta shirya bata ko sanar da Umma ba ta nufi gidan Anty Ameera ranta a mugun ɓace. Lokacin da ta isa gidan ta tarar da ƙofar a rufe hakan yasa ta kira Ameera ta ce mata gata a waje. Ameera ta kira Adam akan yazo ya buɗe wa Nana gida amma Adam ya ce "Yanzu baya kusa, tunda har ta kori mai gadi ai sai dai tayi hakuri har ya dawo ya buɗe. Ta cikin wayar ta ce "Nana ce fa da Umma suka zo duba ni. Adam ya ce "Idan zasu iya jira har na dawo to su zauna a ƙofar gidan, idan kuma ba zasu iya ba to su koma gida har sai na dawo. Yana faɗa ya kashe wayar. Ameera ta bi wayar da kallo tana jin wai anya kuwa yaji abun da ta ce masa. Take ta shiga ɗakinsa domin dubo ko zata samu wani makullin da ya a jiye na get ɗin. Babu inda bata dubaba a cikin ɗakinsa amma babu komai. Hakan yasa ta koma ɗakin ta, tana duba gurin da yake ajiyar takardun sai kuwa ta ga makullin get, kasancewar tasan irin sa yasa ta ɗauko ta nufi waje wanda Nana take ta kiranta akan ta gaji da tsayiwa. Da ƙyar ta iya buɗewa Nana ta shigo gidan duk ranta a ɓace, ga abun da Nasiru yayi mata ga barinta a waje da a kayi yanzu. Tana shiga suka haɗa ido da yayar tata wacce rabon su da su haɗu ido da ido sun kwana biyu. Take Ameera ta nufo ta tana jin wani sanyin daɗin ƴan uwantaka. Nan take ta fashe da kuka. Nana ma kukan ta kama tana ƙara tuno abun da Nasiru yayi mata. Haka suka shiga cikin gidan wanda suna shiga Haura da Ɓultuwa suna fitowa daga cikin ɗakin su da niyyar kama Ameera su mata gargaɗi a kan dukan Haura da shiga sabgarsu. Turus kowa yayi suna kallon juna, Nana tayi mutuwar tsaye tana kallon Haura da Ɓultuwa...✍️ Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. One House One love Love all Typing S-Reza *AMEERA DA ADAM* _18_ *By S-REZA✍️* *Chapter1️⃣8️⃣* ...Nana ta kalli Ameera cike da mamaki ta ce "Wannan ba wannan ƴar aikin taki ba ce haka? Nana ta yi tambayar ne ganin irin shigar dake jikin Haura kamar wata matar gida, ko ɗan kwali babu a kanta, itama Ɓultuwa ta yi shiga irin ta masu iko da gidan ko masu iko da mai gidan. Itama kanta Ameera abun ya bata mamaki ganin irin kallon da suka tsaya su na mu su. Cike da isa da nuna cewar ita ce Ameera matar Adam ta ce "Ke uban wa ye ya baki izinin saka irin waɗannan kayan a cikin gidana? Ko an faɗa miki nan gidan karuwan da kika saba zuwa ne? Karo na farko da Ɓultuwa ta magantu a kan Ameera kenan, ta ce "Dama gurinki zamu je sai kuma gaki Allah ya kawo ki. Cikin girma da mutunci nake son sanar miki da matsayin mu ya sauya daga ƴan aiki zuwa masu gida, sabo da haka kisan irin kalaman da zaki dinga furta mana, nasan mai gidan ki ya sanar dake batun auran da zai yi, kuma Kin san wa zai aura itace Haura. Kuma ya yi haka ne domin rufin aairin ki na kashe mata uwa da kika yi. Saboda haka idan ba so kike maganar baya ta dawo ba to ki bi wannan auran da addu'a ko kiyi shiru, idan kuma kinƙi...! Ɓultuwa ta ƙara sa maganar da alamar barazana. Lokaci ɗaya ran Ameera ya gama ɓaci, ashe da gaske ya sanar da su, shin dama wai Adam ba wasa yake yi ba ne? Ita babban damuwarta da a ke cewa ita ce ta kashe wannan matar, wato sabo da haka kowa yake kafa hujja da hakan domin auran ko!? Ita dai Nana ta na tsaye ta na sauraron wannan tatsuniyar wai Ameera ta kashe mutum, kuma wai Adam ɗin Ameera ne zai ƙara aure.cikin kukan da yafi ƙarfin Ameera ta ce. "Duk abun da ku kai masa Allah yana kallon ku, tsinannu dangin mayo karuwai, kuma in sha Allah baza ku ci galaba a kan mu bs. Ta na faɗa ta Kama hannun Nana suka shiga ɗaki. Suna shiga Ameera ta ƙara fashewa da kuka ta faɗa kan gado ta na faɗin "Kinga halin Maza ko Nana? Yanzu kamar Adam wai ni zai wa kishiya tsabar zalunci? Nana da ba wannan maganar ta ke son ji ba ta ce "Wai tsaya me ye waccer matar take faɗa ne? Naji ta na cewa kin kashe wata? Ameera ta ɗago ta ce "Wallahi ƙarya suke min, ni bansan yaya a kayi ba sai gani nayi ta faɗi shine suka kaita asibiti suka dawo suka ce wai nine na kashe ta. Nana ta ce "Kamar yaya kikaga ta faɗi? Haka kawai baki mata komai ba? Ameera da ranta ya ƙara ɓaci ta ce "Kaman yadda kika ji dai, nace ban mata komai ba kawai ta faɗi, ban san komai ba na rantse miki da Allah. Ameera ta ƙara sa ta na fashewa da kuka mai mutuƙar karya zuciyar mai sauraro. Duk da cewar Nana ta tausaya mata amma sai ta nuna mata kuskuren ta domin ta fahimci maganar. "Gaskiya Anty Ameera zan faɗa miki wallahi samuwar wannan cikin naki masifa ya zamarwa duk wani na kusa da ke, yanzu dubi fa mijin ki ne zai ƙara aure, kuma nasan duk akan abubuwan da kike masa ne, yanzu gashi sabo da ke Nasiru ya ƙara fasa aurena yau, wanda ban san ma me zan faɗa wa Umma ko Abba ba. Har ga Allah Anty Ameera kin ɓata komai da kanki. Ameera ta miƙe tsaye ta ce "Yanzu kema kin yarda nice na ka she matar ko? Nana ta ce "A irin wannan halin da kika sakawa kanki tsab zaki iya kashe mutum idan kika samu dama. "Ta shi ki bar min gida" Ameera ta faɗa tana haɗe rai. Nana ta ɗago ta kalleta ta yi murmushi ta ce "Yau ina gidan na domin ana zan kwana, kuma gaskiya ce sai na faɗa miki ko me zaki yi. "Da yake gidan na ubanki ne ai dele ki zauna, na ce ki tashi ki fita ko na fitar da ke. Ameera ta faɗa cike da nuna tabbacin abun da ta faɗi ɗin. Nana kuwa kallon cikin jikin ta ta yi ganin yadda yayi wani ƙatoto wai amma a haka zata fitar da ni. Kawai sai na Nana ta gyara zama a bakin gadon ta na faɗin "Anty Ameera yanzu zauna muyi magana ta fahimta dan Allah? Kawai sai Ameera ta fashe da kuka tana ɗora kanta a cinyar Nana. Ita kanta wallahi bata san me ke damunta ba, Duk inda Adam ya je da batun auran Haura babu wanda yake bashi goyan baya, shi kuwa yana jin idan bai aureta ba to tabbas mutu zai yi. Ganin haka yasa ya koma gurin Najib akan shi ne zai zama wakilin Haura. Aikuwa sosai da Najib yay masa kaca-kaca wanda har sai da ta kai su da faɗan fatar baki. Sosai Adam ke cikin damuwa da rashin samun madafa, ga kuma itama haura ɗin ta dame shi da batun auran. Ita kuma Ameera daga ya shiga gidan sai masifa akan sai ya kori su Haura mayu ne kuma karuwai ne. Sosai kansa yayi zafi, yana cikin wannan tunanin ya samo mafita. Gurin wani malami ya je ya zaiyane masa komai dake faruwa akan cewar yarinyar da zai aura ɗin bata da kowa hakan yasa danginsa suka ƙi amincewa da ita, shi kuma yana so ya taimake ta ne. Haka dai Adam ya gama shawo kan malamin shi kuma ya ce zai zama mata wakila. Take Adam ya sanar da shi ranar da za'a ɗaura auran, malamin ya sanar da shi cewa ai ranar ma a kwai ɗaurin aure har biyu da za'ayi, kaga naka zai zama na uku kenan. Wannan tabbacin wakilan da ya samu ne yasa hankalin sa ɗan kwantawa hakan ya sa ya sanar da su Haura cewar sati mai zuwa za'a ɗaura auran. Sosai Haura da Ɓultuwa ke murna da farin ciki. Ita kuwa Ameera awannan lokacin ta fara ciwo sam-sam. Sosai ta ke shan wahala da cikin ta a wannan lokacin, hakan yasa bata ko fita sosai. Ɓangaren Nasiru kuwa kaman yadda ya faɗa a ranar da abun ya faru ya turo mota domin kwa she kayan sa. Sai dai wannan karan Abba ya ce "Wallhi babu shegen da ya isa ya mai she su ƙananan mutane. Muddin ya fasa auran ta to sai ya tsaya har Allah ya kawo mata wani in yaso idan anyi auran sai yazo ya amshi kayan sa. Jin haka yasa ran Nasiru ɓaci. Sosai fa wannan karan rikici ya ɓarke wanda har iyayen Nasiru ɗin sai da suka shigo zancen. Dama biki ya rage kwana shida, hakan ya sa a ka dinga rikici har sai da a ka cinye kwana biyar ana abu ɗaya, wanda su masoyan har yanzu babu wanda ya baiwa ɗan uwansa hauƙuri ko wanda ya naimi ɗan uwansa, wanda shi Nasiru yana jira ne tazo ta bashi hakuri, itama kuma Nana jira take sai ya kirata ya bata haƙuri. Sosai wannan karan kowa ya ɗauki zafi domin Abba ya ka sa ya tsare, ita kanta Umma abun ya ɓata mata rai ganin yadda iyayensa ke shigewa gaba-gaba akan rashin mutuncin da yaran su ke shirin aikatawa. Haka dai har a ka wuce kwana shida da ya rage amma Abba bai ba da kaya ba. Hakan yasa maganar ta kai ga yan sanda. Suma suga kasa raba wannan rikicin hakan yasa suka turasu kotu. Sosai ran Abba yayi mugun ɓaci hakan yasa ya tare Nana cikin faɗa ya ke tambayar ta yadda abun ya faru. Take ta sanar masa da komai akan wai hanata zuwa gidan Ameera ya yi shine ita kuma taƙi. Sosai ran Abba ya ɓaci har ya na zubar da ƙwalla. Sosai yake tunanin halin da Ameera ta ke ci, komai a ce Ameera, Ameera dai yarinyar da kaf anguwar nan ake kwatance da ita wajan hakuri da natsuwa amma yanzu ta koma hk. Haka Abba ya tanadi lauya suka fara gabatar da Shari'a da dangin Nasiru. Ihu ta ke yi tana riƙe cikin ta da yake murɗawa kamar zai fashe, sai faman kiran sunan Nana ta ke yi, ita kuma Nana da ke tsaye a kanta sai sannu take mata. Sosai Ameera ta fita a haiyacin ta, hakan yasa Nana ɗaukar waya ta kira Umma ta sanar mata da kamar fa aihuwa ce. Hakan yasa Umma faɗin ta kira mai gidan ta ta sanar da shi sai a kaita asibiti. Wani irin ihu da Ameera ta sake yasa Nana saurin ka shi wayar tana mata sannu. Haura da Ɓultuwa kuwa suna gurin gyaran jiki da Adam ya kai su domin kuwa yau za'a ɗaura auran, hakan yasa Ɓultuwa tanai mi da ya basu kuɗi zasuyi gyara irin kitso da lalle da dai sauransu, shi kuma Adam ya ce zai kai su har gurin da a ke yin kitson, haka kuwa ya ɗauke su ya kai su sannan ya basu kuɗi yace su rika a hannunsa, sannan ya biya mai wankin kan. Adam da yake gaban malam wanda za'a ɗaura auran dake gaban nasu kafin a zo kan nasa yaga wayarsa na ƙara, bai so ya ɗauka ba amma ganin Nana ƙanwar Ameera ya sa ya ɗaga ya na tambayar ta dalilin kiran. Nana ta sanar masa da cewar Ameera ce zata aihu. Ai tun kafin ta ƙara sa yaji irin ihun da ta ke yi. A hankali ya ce "Ina zuwa yanzu amma kafin nazo ki ɗauke ta ki kaita asibiti kafin na iso. Nana ta ce "Wallahi ba zan iya ba, kawai kazo yanzu. Adam ya dawo gurin Malam ya sanar da shi cewar har yaje ya dawo ko? Malam ya ce "Eh har ka dawo domin kaga ba'a ma fara wannan ba, sai dai karka daɗe ka dawo da wuri. Ko da ya iso gidan Ameera ta gama fita a haiyacin ta, ta haɗa zufa kamar mai wanka. Lokacin da ya ganta sai da gabansa ya fadi, domin bai taɓa ganin yadda ake naƙuda ba. Sosai tsoron Allah ya ƙara kama shi yana jin ƙaunar mahaifiyarsa a ransa, nan take ya mata addu'a cikin ransa. Bai ankara ba yaji hawaye na zubowa daga idanunsa. Sosai ya ke kallon Ameera wancce take ta shure-shure kamar zata mutu, idanun ta sun tsaya, sai kiran sunan mutane ta ke yi harda sunan sa. Nana ce itama da sai yau ta taɓa ganin naƙuda ta fara kuka dan itama tsoro abun ya bata. Sun tsaya sai kallonta suke yi suna kuka sun kasa bata wani taimako duk jikin su ya mutu!. Adam ne yayi ta Maza ya zo kanta ya kamota da niyyar ɗagota amma ta sake kurma wani ihu ta na kiran sunan Allah. Lokaci ɗaya Adam ya ajiye ta kukan sa na kufcewa ya faɗin "Sannu honey Sannu, in sha Allah ba za ki ƙara aihuwa ba daga wannan I'm so sorry my Honey I love you so much please don't let! Sosai yake kuka ya rungumota jikinsa yana mata sannu. Lokaci ɗaya ya kamota ya ɗaga ta ya nufi Mota da ita, izuwa lokacin Ameera neman sumewa ta ke yi. Nana ta biyo shi da gudu ta na kuka, haka suka bar gidan cikin namijin gudu har suka isa asbinti. Lebo rom (ɗakin aihuwa) aka shiga da ita cikin sauri, da gaske Adam yazo zai shiga amma a ka tsayar da shi a kan ba'a shiga. Haka suka tsaya shida Nana a gurin suna safa da marwa. Nana ce ta tuna da kayan aihuwa hakan yasa ta tambaye shi. Shi ma sai yanzu ya tuna ya ce taje ɗakin Ameera ɗin ta kwaso komai. Ya ce "Kin iya tuƙa mota? Nana ta ce "A'a ban iya ba. Adam ya zaro kuɗi ya bata ya faɗa mata inda kayan su ke. Wasa-wasa aihuwa har ƙarfe biyar babu alamar fitowar jariri. Sosai hankalin kowa ya tashi musamman Adam, ita kanta Nana duk ta fita a haiyacin ta, Umma sai kira ta ke tana tambayar an aihu? Misalin shida na yamma Allah yayi ikon sa, Ameera ta haifo jariranta guda biyu mace da namiji, sai dai ita uwar jini ya ɓalle mata. Sosai lokacin da Adam da Nana suka ji batun aihuwar suka yi murna, amma jin halin da uwar take yasa murna ta koma ciki. Ɓangaren su Haura kuwa an daɗe da gama musu komai amma har yanzu Adam bai zoba, gashi basu da waya. Haka dai su kai ta jiran sa amma shiru, har ran Ɓultuwa ya fara ɓaci da irin wannan abun. Wasa-wasa har shida na yamma suna gurin, ga shi basu san sunan unguwar da su ke ɗin ba. Suna gurin har bakwai babu alamun Adam. Kawai sai suka tare mai keke napen ya kai su gurin da suke bara. Koda suka zo gurin sai suka fara tunanin abin yi, shiru Haura ta yi tana tuno sunan anguwar su Adam ɗin ranar da zata kai musu abinci asibiti. Da ƙyar ta iya tunawa hakan yasa suka tare mai keke napen again suka faɗa masa inda zai kai su. Suna isa suka sallamshi suka tako har zuwa ƙofar gidan. Sai dai ƙofar a rufe take. Haka suka samu gefe suka zauna suna jiran dawowarsa, basu kawo komai ba domin dama Adam ɗin yana rufe gidan yanzu tunda babu mai gadi. Cikin yardar Allah aka tsayar da jinin sai dai ana buƙatar jinin da za'a saka mata domin ta zubar da jini sosai. Haka Adam ya kamata a ka kwashi jini leda biyu bayan gwajin da a kayi masa babu wata matsala a jinin nasa. Bayan an gama kwasar jinin nasa ne Adam ya ce da Nana taje gida gobe sai ta dawo. Taso tayi musu amma ganin yadda ya haɗe rai yasa ta kama hanya. Har zata ta fi ya ce "Dama kin tabbatar kin rufe min gidan ko? Nana ta amsa da "Eh na rufe. Har asuba jinin bai gama shiga ba, a wannan lokacin Adam ne ya kifa kansa a bakin gadon bacci ya ɗauke shi kasancewar jiya bai samu rsintsawa ba. A cikin barccin yake mafarkin wani yazo zai raba shi da Ameera, hakan yasa yayi saurin buɗe ido ya sauke a kanta wancce take kwance tayi fari sosai, lokaci ɗaya yaji wani irin sonta na fusgarsa, ga wani irin natsuwa da yake jin ya samu yanzu. Nana da Umma ne suka shigo ɗakin ɗauke da kayan abinci da ruwan zafi na yiwa baby's wanka, domin Nana ta sanar musu da cewar ta haifi tagwaye mace da namiji. Bayan sun shigo ɗakin ne Adam ya gaida Umma sannan ya ta shi daga gurin da yake. Ummu ta ce "Kaje gida ka watsa ruwa sai ka ɗan huta kafin ka dawo ko? Adam ya amsa da "Ok Umma. Ya fita ba domin zai iya mata musu ba, yana fita ya tuno a she fa bai sanarwa da kowa bafa. Nan take ya kira Najib bai ɗaga ba, ya kira Kadija kira ɗaya ta ɗaga haɗi da yin sallama. Adam ya amsa lokacin da yake shiga cikin motarsa. Kadija ta gaida shi tana jiran taji ya mata batun auran sa da zai yi jiya domin jinsa cikin farin ciki. Adam ya ce "Sister albishirin ki? Najib dake kusa da ita ya ja tsaki ya kawar da kai! Cikin ƙarfin hali ta ce "Goro Yaya na" ya ce "I'm a daddy now! Ya faɗa yana dariya. NAJIB da Kadija cike da rashin fahimta suka haɗa baki gurin ce wa "Me kake nufi? Sai a lokacin Najib ya kula da ya yayi magana. Shima Adam ɗin da makin jin muryar Najib ya ce "Ameera ta aihu ta haifi ƴan biyu yanzu haka muna asibiti. Yana faɗa ya kashe wayar yana dariya. Daidai lokacin ya karyo kwanan anguwar su. Tsayawa yayi a daidai get ɗin gidan sa، kana ganin sa kasan yana cikin farin ciki. Fitowa ya yi ya buɗe get ɗin sannan ya zo zai shiga motar domin shigar da ita ciki sai yaji an kira sunan sa cikin fu shi da ɓacin rai. Ɓultuwa ce ta ce "Adam yanzu dan Allah ka kyauta mamu da ka barmu muka kwana a waje? Tun jiya daga kaimu gurin wankin kai sai ka manta da mu, Allah dai yasa an ɗaura auran?....✍️ Comments dinku shine ƙwarin guiwa na. One House One love Love all Typing S-Reza *AMEERA DA ADAM* _19_ *By S-REZA* *Chapter1️⃣9️⃣* ...Ɓultuwa ta yi tambayar cike da nunu ɓacin ran da suke ci ki. Da sauri Adam ya juyo ya na bin su da kallon mamaki domin shi harga Allah ya manta da su. Haura ya kalla ya ga ta na wani cin magani sai kawai ya ce "Ku yi hakuri na manta ne, amma yanzu kuzo mu shiga ci ki. Haka Adam ya buɗe get ɗin suka shiga shima ya mara musu baya da motar ta sa. Su na shiga Ɓultuwa ta ce da Haura "Kinga yanzu ke matarsa ce, sabo da haka ki je ɗakin sa ki yi wanka idan yaso sai ku fara maganar kafin na zo, kar ki ji tsoron waccer matar ta sa domin yanzu duk ɗaya kuka kin ji dai ko? Haura ta amsa da kai. Hakan kuwa a kayi, ɗakin Adam ɗin ta shiga cikin sanɗa dukda tasan baya ciki amma sai ta tsinci kanta da fargaban aiwatar da hakan. Ta na shiga ta ga babu kowa a ciki, ga kuma ɗakin ba'a gyare yake ba kamar ma dai yau ba'a kwana a cikin sa ba. Haka ta shige toilet duk jikinta na rawa, ta na shiga ta fara cire kayan ta, sai da ta yi tsirara kafin ta sakar wa kanta ruwan sanyi ta na lumshe ido gami da sauke ajiyar zuciya ta na godiya ga Allah da yasa yau ta zama matar Adam. Ya na shiga palon gidan nasa ya nufi ɗakin Ameera domin a ce ya ke so ya yi wanka, sai dai ya na shiga ya fito dalilin ganin ɗakin ba'a gyare ba, nasa ɗakin ya nufa cikin farin cikin yau ya zama baba. Ya na shiga ɗakin ya shiga cire kayan sa sai da ya gama yin zindir kafin ya tura ƙofar toilet ɗin ya shiga ɗauke da addu'ar shiga bayan gida ("A'uzu bika minal kubusu wal-kaba'isu) Ɓangaren Malam kuwa ganin har zuwa lokacin Adam bai dawo ba ne ya sa ya ce "To ko wani zai karɓa masa wakilcin yarinyar a ɗaura suran ne?, sai kuma Malam ya tuna bai san sunan yarinyar ba. Haka dai akai ta jiran Adam amma shiru, ga kayan ɗaurin aure amma babu ango kuma babu wakilin sa, haka dole Malam ya bada haƙurin cewa ina ga dai ba lafiya ba ne. Haka kowa ya watse ba tare da ɗaurin auran ba. Ya na shiga toilet ɗin Haura ta juyo a tsorace da lilin jin karatun da yayi, hakan yasa shima saurin tsorata dalilin da yasa suka haɗa goshi bata tare da kowa ya an kara ba. Ganin sa tsirara yasa Haura saurin juyawa ba tare da itama ta rufe komai daga jikinta ba. Shima Adam ɗin cikin tsoro da mamakin ganinta a cikin toilet ɗin sa ya sa ya yi kamar zai rusa ihu! Sai kawai bakinsa ya shiga furta "Inna'ilaihi wa inna'ilaihi raju'un! Ya na faɗa ya na kallon yadda ta juya masa baya, shima sai neman shagala da kallon bayan ta da yaso yi, amma jin ya na ƙoƙarin kasa saita kansa ne ya sa ya juya ya fita daga toilet ɗin ba tare da ya biyewa ɗaya gada cikin zuciyar tasa dake angiza shi taɓa wani sashe na jikin ta ba. Ta na jin ya fita ta sauke a jiyar zuciya ta na ɗaura tawul da niyyar fitowa. Sai da ta fara leƙowa ta ga baya cikin ɗakin kafin ta fito da saur ta buɗe ƙofar zata fita shi kuma ya kama zai buɗe ya shigo. Ta na buɗewa suka ƙara cin karo har sai da tawul ɗin jikinta ya kunci, amma ta yi saurin taro kayan ta tsaya ta na kallon sa ganin sa shima ɗaure da tawul ya na kallonta da duk ta rikice. "Mai ya kawo ki cikin toilet dina yin wanka? Adam ya watsa mata tambayar ya na bin jikinta da ke rawa da kallo. Sai yanzu yake ƙara tunano lokacin da ya fara ganinta tsirara, sai yau da ya ƙara ganin ta. Jin ta yi shiru ne ya ƙara ce wa "Tambayar ki na ke" Haura ta ce "Wanka nazo yi saboda naga nima matarka ce yanzu shi ne kawai. Cikin ɗan mamaki ya ce "Mata kuma matar wa?! To ya kika zama matar ta wa? Lokaci ɗaya gaban Haura ya fadi domin ba yadda ya saba mata magana ya ke yi yanzu ba, wannan karan Adam ne a gaban ta. Ganin haka yasa kawai Ɓultuwa ta ke son gani domin ita tasan san abun yi. Hakan yasa ta raɓa ta jikin sa har suna gogar juna ta nufi ɗakin su. Ta na zuwa ta sanar da Ɓultuwa cewa ba'a fa ɗaura auran ba. "Cikin tashin hankali ta ce "Kamar ya ƙarya ne wallahi an ɗaura. Haura ta ƙara cewa "Babu alamar ma fa yasan da wani batun aure ma fa. Ɓultuwa ta kalli Haura ta ce "Ina ce dai ita shigiyar matar ta sa ta na cikin gidan? Haura ta amsa da "Babu alamar ta na cikin gidan, anya ma kuwa ba aihuwar ta yi ba. Da ƙarfi Ɓultuwa ta ce "Aihuwar uwarki! Wallahi ba zamu ga wannan baƙar ranar ba, ta ma isa ta aihu ban sa ni ba. Haura dai ta shiga sauya kaya cikin rawar jiki. Ita dai Ɓultuwa sai sake-sake da kwance-kwance ta ke. Idan har aihuwar Ameera ta yi kenan shikenan asirin ya tonu kenan, ita Haura zata san gaskiya, kuma mutanen garin Ƙaruk ma zasu gano ta. Sanin dukkanin sirrukanta ya dangana ne da aihuwar Ameera, lokaci ɗaya ta fara tunanin kashe Adam ɗin shi da Haura sai ta gudu, amma sai ta tabbatar da cewar Ameera ta aihu. Ya na wanka ya na tunanin maganar Haura wai ta zama Matarsa, ko mai ta ke nufi ohoo! Bayan yayi wanka ya shirya ya fito daining tebul ya zauna ya na jiran fitowar Haura ta kawo masa abinci. Ya na zaune sai gata sun fito ita da Ɓultuwa sun nufo gurin sa. Sai da suka gaida shi kafin Haura ta shiga kicin ta kwaso abun da suka dafa ɗin. Haka suka shiga cikin abincin su uku ba tare da kowa ya ce komai ba, sai Adam da ke dana waya ya na murmushi! Ɓultuwa ce ta yi gyaran murya ta ce "Uhumm ahamm! Ya batun auran jinyan an ɗaura ko dai an ɗaga ne?. Adam ya kalleta domin maganar da ƙarfi ta yi. Adam da yake so sai ya gama cin abinci ya nai mi ƙarin haske sai kuma ga shi an hutar da shi. Ya ce "Wai wani aure kuke maga na a kai ne? Ban ga ne ba, munyi maganar aure da ku ne? Nan take Ɓultuwa ta rikice domin tabbas lissafi ya kwafce mata. Ta ce "Jiya kai ne ka kaimu gurin gyaran jiki ka ce zaka gurin ɗaurin aure idan ka dawo zaka zo ka ɗaukomu shi ne ba ka dawo ba. Da ƙarfi Adam ya bigi teburin abincin wanda sai da duk sauran abincin da ke gurin ya zube. Ya ce "Karna ƙara jin wannan banzar maganar domin ban san anyi haka ba, kuma ni na ɗauki Haura domin na taimaka mata ne, muddin na sake jin wannan zancen sai kunbar min gida, wannan wani irin shirme ne haka. Haka Adam ya bar gidan cikin tsananin ɓacin rai. Koda ya koma asbintin Ameera bata farka ba, sai kawai ya nufi gurin yaran ya na kallon su cikin so da ƙauna. A haka har Najib da kadija suka shigo ɗakin. Sosai Kadija ke murna ta na kallon yaran nata. Adam ya kalli Najib ya ce "Wai Kaji wani shirme da yarinyar nan dake aiki a gida na wai ni ne nai mata alƙawarin aure? Najib cike da mamaki ya ce "Eh ai gaskiya ne, nima nan kazo wai a lallai sai na mata wakilci, sabo da na ƙi ne yasa ka fara faɗa min baƙar magana. Adam ya ƙurawa Najib ido ya ce "Najib wallahi Allah ɗaya kenan ko? To na rantse da shi ban san aiyi duk wadannan abubuwan ba. Cike da mamaki Najib ya ce "Adam to wallahi ka kori mutanann daga gidan ka, idan ma taimakon zaka kai musu to karka barsu a kusa da kai. Haka dai Najib da Adam sai mamaki su ke yi. Sosai dangi da abokan arziki ke ta tururuwar zuwa asibiti, sai dai har zuwa yanzu mai jego bata farka ba. Najib ya sanar da Kadija komai da Adam ya sanar masa, itama dai mamakin ta yi ta na faɗin wallhi sai an kore su ko baya so. Ɓangaren kotu kuwa sosai shari'a ta yi zafi inda a ka yanke hukuncin dole sai Nana ta samu miji kafin a baiwa Nasiru duk dukiyar da ya ka she mata, sannan kuma Abba ya shigar da ƙarar babu ɗan su ba ƴarsa, ya ce ya na so a shiga tsakaninsu. Nan ta ke alƙali ya shiga tsakanin Nasiru da Nana kar wanda ya ƙara shiga samgar wani kwata-kwata. Da wannan ƙara ta ƙare. Sai dai kuma Nasiru da Nana da bazasu iya rayuwa babu ɗaya ba. Kwana uku da yi musu iyaka da juna sai ga kiran Nasiru. Da sauri ta ɗaga cikin zumuɗi. Shiru yayi itama haka sai kawai taji ya na kuka, itama kukan ta kama kowa ya kasa magana. Cikin she-sheƙar kuka ya ce "Mai yasa Nana mai yasa ba zaki kira ni ki bani hakuri komai ya wuce ba? Mai yasa kike da taurin kai ne? Nasiru ya ƙara sa yana fashewa da kuka Kamar ƙaramin yaro. Itama cikin kukan ta ce "Mai yasa baka da haƙuri ba zaka manta da komai ba, mai yasa ka bari har a ka shiga tsakanin mu? Sosai suka sha kuka daga bisani Nasiru ya ce "Yanzu kina ina ne? "Ina asibiti kasan Anty Ameera ta aihu ta haifi ƴan biyu Mace da namiji to nice ke zaune da ita. Nasiru ya ɗan yi shiru kafin ya ce "Ma sha Allah! Allah ya raya. Yayi maganar kai da ji kasan ba har zuciyarsa ta ke ba, domin sosai yake jin tsanar Ameera domin ita ce ta yi sanadin komai. Zaki iya fitowa mu haɗu yanzu? Nasiru ya tambaya cike da kewar ta. Itama babu wani tunani ta ce "Ok idan kazo ka kira ni. Ta faɗa ta na jin wani irin wutar soyayyar sa na ruruwa a cikin tsakiyar magudanar zuciyarta. Ta na zuwa ta hango motarsa a wajan asibitin, tun kafin ta isa take sakin murmushi ta na zuwa ta buɗe gidan gaba ta shiga. Ta na shiga Nasiru ya jawota jikinsa ya na sakin nannauyar ajiyar zuciya. Itama ajiyar zuciyar ta sauke tana lafewa a jikin sa, a hankali ya fara shafa bayan ta har zuwa mazaunan ta, sosai yake kashe mata jiki har ya haɗe bakinsu. Itama cikin so da ƙauna ta fara mayar da martani domin kuwa ta yi kewar sa, sosai suka dinga tsotsar juna ba bu kama hannun yaro kamar wasu mayunwata. Cike da jaraba ya kai hannunsa gaban ta amma ta riƙe hannuna ta ƙwace jikin ta daga nasa ta na girgiza masa kai. Nasiru ya ce "No baby yanzu idan har ba haka muka yi ba to shikenan an rabamu, amma idan har muka nuna musu cewar muna son juna ta hanyar aikata hakan zai sa a warware komai a barmu ta re. Nana ta ce "No ba sai ta wannan hanyar ba, a kwai hanyoyi da dama da zaisa a warware ba sai mun aikata saɓon Allah ba. "To wacce hanya ce? Nasiru ya tambaya ya na kafeta da ido. Misalin huɗu na yamma Ameera ta farka, ai kuwa nan Kowa ya shiga barka. Sosai ta yi haske ta rame. Lokacin da a ka kawo mata yaran ta gansu sai kawai ta fashe da kuka, sosai ta ke ƙara godewa Allah da irin kyautar da ya bata a lokacin da take buƙata. Sosai ta ke son ganin Adam ganin baya cikin ɗakin. Haka duk wanda zai shigo idan ta a kan kofa ta na jira taga rabin ran nata ko yaya zata ga fuskarsa domin tasan zai fita farin ciki. Lokacin da ya turo ƙofar ɗakin zuciyarta ta tabbatar mata da cewar mahaɗin ta ne ke tafe. Ya na shigowa idonsa ya sauƙa a kan gaba ɗaya rayuwar tasa. Sosai farin ciki da murna da zumudin sa suka baiyana, ya manta da kowa da ke cikin ɗakin ya nufi gurin matar sa ya rungumota yana jin wani irin farin cikin da ya daɗe bai samu ba. Sosai yake jin ɗumin zazzaɓin jikinta na sauƙa a kansa. A hankali ya ce "I love you my Honey" itama ta furta "I so much love you my Honey. Ganin dai abun nasu ba na ƙare bane yasa Nana ɗan yin gyaran murya. Hakan yasa suka dawo cikin duniyar mutanen dake cikin ɗakin. Ameera sai wani sunne kai ta ke yi lokaci ɗaya kunya ta rufe ta ganin ana ta kallonta. Sai washegari likita ya sallmesu wanda suka tattara suka tafi gida. Sai dai suna shiga gidan suka tarar da wani sabon ta shin hankali a cikin gidan nasu, domin an ɓalle get ɗin an ture shi gefe an shiga gidan. Mutanen garin Ƙaruk ne su sama da goma sanye da irin shigar ƴan garin wato suna suturta iya ƙirjinsu da da gaban su da wata fata mai kama da fatar damun daji. Lokacin da Ameera ta gansu sai da ta tsorata, ita kanta Nana da Kadija a tsorace suke, Adam da Najib ne dai suka yi ƙarfin halin tun ƙarar su suna tambarsu ba'a sin zuwa. Cike da mamaki suka ji wani daga cikinsu ya na Hausa. Haka ne yasa suka shiga daga cikin palon gidan da mutum uku daga ciki. Suna shiga suka tarar da Ɓultuwa an ɗaureta sai zubar da jini take ga wata ƙaramar randa a kusa da ita, wanda ruwa ne a ciki suna kallon abun da take faɗa ta yi ɗin kamar suna kallon Film. Shigowar su Adam abun ya tsaya cak!. Nan da nan mai jin Hausan ya fara magana ya ce "Ba matarka ba ce ta kashe Hatta (Wato Ammin Haura) kuma sannan ba ita ce ta suka maka wuƙa ba duk aikin wannan munafukar matar ce. Ya nuna gurin da Ɓultuwa ke daure. muma munyi-munyi da ita mun kasa, babu irin makircin da bata sani ba, duk abun da ta ke yi bada sanin mu ba ne, sai yanzu da abun da ta yi ya ɓaci yasa muka yanke mata hukunci kisa domin ta shiga gonar da ba'a shiga. Cike da mamaki Haura ta ke kallon Ɓultuwa jin cewar ita ce ka she Amminta. To ta yaya ita da bata gidan!. Sosai Haura ke son jin agarin yaya. Mutumin ya ce "Hatta da Ɓultuwa uwa su ɗaya uban su ma ɗaya, sun taso masu son kansu wato suna son ace sun fi kowa, Hatta ita ce babba amma babansu yafi son Ɓultuwa saboda Ɓultuwa a kwai saurin sabo da mutum. Soyayya ya ce ta fara raba kawunansu, domin wanda Ɓultuwa ke mutuwar so shine yake son Hatta har a ka yi aure. Daga lokacin ta fara ƙulla mata sherri iri daban-daban har sai da a ka kori Hatta da ƴar ta bayan mutuwar mijin ta. Tun da Hatta ta tafi Ɓultuwa take bibiyar ta, duk wanda ya taimake ta kuwa sai Ɓultuwa ta ka she shi, koda kuwa waye. Ko sadaka ka basu a gurin bara to sai Ɓultuwa ta ka she ka domin kuwa ita ɗin tafi Hatta karfin tsafi, domin ita mahaifinsu ya barwa duk surrin sa. Ganin haka yasa Hatta fara tunanin ko zata mallake wani ne idan yazo yi musu sadaka. Ana cikin haka wani yazo ta mallake shi , kullum sai yazo ya bata sadaka amma baifi kwana huɗu ba ta neme shi ta rasa. Daga lokacin ta fara tunanin ko dai akwai matsala ne. Hakan yasa tayi amfani da na'urar tsafin ta ta gano cewar wani ne ke bibiyar rayuwar ta, amma bata gane ko waye ba, daga lokacin ta fara bawa ƴar ta dukkan nin wasu sirrika na tsafi. Sosai su ke wahala har Allah ya kawo ka cikin rayuwarsu ashe kai ne mai taimakon su dukda cewar sun ɗan cutar da kai amma ba sun yi hakan da gaiyya bane domin Hatta mutuniyar kirki ce kowa ya she de ta, Hakan yasa lokacin da a ka ji labarin mutuwar ta sai da kowa yayi mamaki kuma daga lokacin ne a ka dukufa binciken dalilin mutuwar tata sai jiya gaskiya ta baiyana...✍️ _Ya a kayi Hatta ta mutu? Wani irin cuta su kaiwa Adam da Ameera? Ita Ɓultuwa me ye burinta? Shin yaya makomar Haura a wannan Game ɗin? Shi Ameera ta dawo haiyacin ta ko kuwa? Shin Nasiru da gaske son Nana ya ke ko dai lalata ya ke son yi?_ _Wannan amsoshin tambayar duk suna cikin page ɗin Ranar Asabar in sha Allah. Comments dinku shine ƙwarin guiwa na_ One House One love Love all Typing S-Reza *AMEERA DA ADAM* 🔚 _Chapter 2️⃣0️⃣🔚_ ... Lokacin da ka shigo rayuwar su sai Hatta ta yi amfani da tsafin ta domin ka dinga jin tausayin su, sosai kuma hakan ya yi nasara a kan ka. Tun daga lokacin ne kai kuma ka fara sintirin zuwa kai musu sadaka. Ganin haka ya sa ta ƙara ƙarfin tsafin nata a kanka har watarana da kanka kazo akan zaka ɗauki Haura a matsayin ƴar aiki. Lokacin da suka zo gidan sai suka tarar da matar ka na ɗauke da ciki, kuma cikin nata irin mai saka mace ƙunci da masifu ne. Sosai Hatta tayi niyyar hallakar da cikin jikin matar ka domin ta lura bata son zaman Haura a cikin gidan. Duk abun da matarka ta ke yi babu sa ka hannun kowa domin kuwa dama laulayin ciki na iya zuwa da hk, sai dai wasu lokutan Hatta na tura mata aljannu domin su ƙara birkitata. Duk wannan abun Ɓultuwa bata da labari domin Hatta ta ɓoye komai. Ganin irin azabtuwar da Haura ta ke yi a gurin matar ka yasa Hatta dawowa cikin gidan ka, daga nan kuma ta fara kwaɗaitawa ƴarta auran ka, sai ta fara amfani da kai wajan dai na jure komai na matarka, abu kaɗan sai kaima ka ɗauki zafi. Ana cikin haka Ɓultuwa ta gano komai. Sosai hankalin ta yayi mugun ta shi jin wai Hatta ta samu wanda ya taimake su. Daga lokacin Ɓultuwa ta biyo iska tazo gidan domin hallaka mutumin da ya shiga gonar ta. Ko da tazo sai ta rasa ta yaya zata aiwatar da komai domin jikin ka da na matar ka a kwai aljannun Hatta kuma hakan ba mai yiwuwa bane itama ta tura nata aljannun. Duk wani abu da a kayi ta na cikin gidan tana kallo. Ranar da abun ya faru kuwa ita da kanta ta shiga jikin matar ka ta ture Hatta, bayan faduwar ta ta shaƙeta batare da kowa ya sani ba har ta mutu. Bayan mutuwar Hatta kafin labari ya sa me mu ita ce ta fara zuwa ta sanar da cewar kune kuka kashe ta. Sosai muka zo da niyyar ɗaukar fansa amma ganin irin mutuwar da ta yi sai sarki ya ce dole sai an bincika dalilin mutuwar. Haka muka ɗauki gawarta aka fara bincike. Lokacin Haura ta dawo gida sai sarki ya yafe mata komai amma da sharadin bazata ƙara barin cikin garin Garuk ba. Daga lokacin Ɓultuwa ta saka Haura a gaba akan idan har tana son auran ka to zata yi iya mai yiwuwa har ka aureta. Daga nan ta hure mata kunne har suka ƙara barin cikin garin Garuk suka dawo niman, Ɓultuwa ce tai maka kiranye har sai da kazo inda suke ka tafi dasu. Daga nan ta ci gaba da wasan kura da kai har ka furta musu zaka auri Haura. Daga nan kuma ta ci alwashin sai ta rabaka da matar ka. Sai dai hakan ba zai yiwu ba sai idan sun san idda Hatta ta binne sihirin da tai maka wanda idan matar ka ta aihu komai zai wargaje. Baka san komai ba domin har kayan ɗaurin Aure ka yi, wanda da an ɗaura wannan auran da shikenan kun gama shiga hannunta daga ku har ita Haura ɗin. Hakan yasa da muka gano sai muka cire aljanin jikin matar ka domin shine ya tare cikin, cikin ikon Allah kuma ta aihu lafiya. Sosai Haura ke kuka tana zagin Ɓultuwa da yaran Garuk. Ita dai Ɓultuwa bata cikin yanayin daɗi domin har yanzu jini ne ke zuba a jikinta domin kuwa ta a zabtu. Sosai Adam da Ameera ke mamaki wanda ita Ameera harda hawaye. Shima Najib dai sai kallon Ɓultuwa da haura ya ke yi kaman yaga wasu halittun da ban. Kadija kuwa ji take kamar ta kamo shigiyar Ɓultuwa ta lakaɗa mata nata dukan ko zata huce. Ameera ta miƙe ta re da baby ɗaya ta shige ɗaki, itama Kadija ta bita da namijin. Haka mutanen garin Garuk suka tattara suka tafi da Ɓultuwa Adam ya ce abar masa Haura zai zauna da ita , zai ɗauketa kamar ƙanwaraa, lokacin da ya tambayi Ameera itama ta ce duk abun da ya ce ta yarda. Kadija dai ta ce wallahi ita tsoron su ta ke yi, idan zasu biye nata karsu ƙara yarda da su. Amma Adam da Ameera su ka ce karta damu Haura mutuniyar kirki ce. Haka ranar suna yara suka ci sunan su na Hassana da Husaini. Amma za'a dinga kiransu da Salim da Salma. Sosai Haura ta kama kanta a gidan bari na bari yi nayi. Sai yanzu take ganin asalin halin Ameera wanda ta cika da mamaki abun da ya komar da ita masifaffiya. Ameera ta ce "Ai shi ciki babu abun da bai sakawa amma irin nawa shine mafi muni, ya Allah karka ƙara jarabtata da irin wannan laulayin da zan adabi kowa. Haura ta amsa da amin. Sai da su kayi wata ɗaya da aihuwa Adam ya saka Haura a school bayan shawarar da su ka yi da Ameera. Sosai kuwa take ƙoƙari dudda yanzu babu asiri ko tsafi a jikin ta, komai da ƙwaƙwalwar ta ta ke yin sa. Ɓangaren Nana da Nasiru kuwa duk ta inda Nasiru ya biyo Nana ta ƙi yarda su aikata abun da ya ke so.ga shi har yanzu babu wanda yasan suna tare. Ameera ce ta kira Nana ta ce "Nana kina son Nasiru har yanzu? Nana ta fa she da kuka ta na cewa Wallahi ina sonsa sosai, kuma yanzu ban san abun yi ba. Ameera ta bata haƙuri akan zata gyara mata komai kamar yadda ta ɓata. Haka Ameera ta taka taje ta samu Umma da Abba ta fara basu hakuri akan a warware komai na tsakanin Nana da Nasiru. Amma Abba ya ce idan bata bar gaban sa ba zai saɓa mata. Baba ya ce "Koda Nasiru shine kaɗai namiji to sai dai kar Nana ta yi aure. Sosai Ameera ta dingi sintiri daga gidan ta zuwa na su. Ta kai sati ɗaya kafin Abba ya haƙura. Haka ma taje gidan su Nasiru su kuwa ana zuwa suka ce dama su ai yaran su na so, kuma su duk abun da yaran su ke so to suna mara masa baya. Daga nan aka je kotu aka warware sharadin da a kayi a ka ɗaura auran Nana da Nasiru. Sosai Nasiru yazo har gida yana ma Ameera godiya da bata haƙuri a kan duk abun da ya faru. Wata uku da Aihuwar Ameera itama Kadija ta haifo nata ɗan ƙato Namiji mai kama da uban sa. Kallon ta ya yi ceke da mamaki ya ce "Haba honey yanzu fisabililahi kina kallo aiki fa na keyi shine zaki ce na zo na karanta miki novel? Ameera ta ƙwaɓe baki kamar zata yi kuka ta ce "Sabon littafin Kahdija Candy ne fa please ni dai kazo kar a min nisa. Adam ya ce "To wai ko dai wani cikin ne shima mai hana mutum sakewa. Take Ameera ta gwalo ido waje tana dariya. Ta ce "No barshi zan karanta kayana ai bana addu'ar na ƙara yin ciki irin wannan. Adam ya ce "Allah dai yasa kar yaran su ɗauki irin wannan masifar. Ameera ta amsa da amin dai. Suna cikin hirar sai ga Haura ta dawo daga school. Ta na shigowa ta gaisar da su a tare ta na faɗin "Kai Anty yau fa bana gane kai na tsabar yunwa. Ameera ta ce "Gashi kuma ban yi komai ba a gidan, yaran nan sun hanani sa kewa sai yanzu ma na samu suka yi barci. Haura ta ce "Haba dai Anty Allah zan iya faɗuwa fa ko nayi kuka idan da gaske kike. Ameera ta ce "To yi kukan mana mu gani, kinga da sai naje na taso su suma su kalli ƙatuwar Antyn su ta na kuka ko. Sai lokacin Adam ya ce "Wasa ta ke miki abinci na kicin kuma irin wanda kike so. Ba tare da tursasawa ba ko taƙuwara Haura da kanta ta ce tana son ta shiga addinin Musulunci. Ai kuwa Adam da Ameera sun yi murna sosai wanda sai da Ameera ta bata kyautar wata sarƙa mai kyau mai tsada. Bayan musuluntarta aka ce ta zaɓi sunan da ta ke so sai kawai ta ce "A'isha. Sosai take jin daɗin zama a gidan itama kuma ta sake sosai kai ka ce dama a gidan ta taso. Nan dai Adam ya shigar da ita islamiyya sanna shi da Ameera suna ƙara mata karatun a gida. Cikin ikon Allah Nasiru da Nana ko bayan auran babu wannan yawan fadan da su ke yi sai soyayya mai tsafta da suke shin fiɗawa kamar babu gobe. "Zo na tuna miki da wani abu" Adam ya faɗa ya na kallon ganin ta ƙi ƙarasowa gurin. Ya ƙara cewa "Ranar da kika sa soja ya min duka ina kika gudu ne lokacin? Adam ya ƙara sa ya na dariya. Itama dariyar ta yi tana ƙarasowa ta faɗa jikin sa. Ta ce "Ni dai dan Allah a bar dawo da abun da ya wuce. Adam ya ce "To mai sayar da ƙwai fa na ƙarshen kayi? Ameera ta ɓata fuska ta ce "Allah zan yi kuka idan ka sa ke. Adam ya ce "To na ji yanzu babu ajiyar komai ne a cikin? Ya faɗa yana shafa cikin nata. Ameera ta ce "Please Honey Dan Allah ka je ka nemo baba mai gida ya dawo aikin sa. Adam ya ce "Babu yadda ban yi da shi ba wallahi ya ce ba zai iya ci gaba da aikin a gidana ba, amma na ba shi jari kuma na roƙa miki yafiya kuma ya yafe. Ameera ta share hawaye ta ce "Tom Nagode Honey. Haka fara bata haƙuri har ya lallaɓata suka haura sama. Alhamdu lilliha! Anan lissafin Ameera da Adam yazo ƙarshe. Nasan zaku sha mamakin yadda labarin ya zo a haka. To ba komai ba ne sai yanayin labarin. Ya Allah ka yafe mana kuskuren da ke cikin wannan labarin, alkairin kuma Allah ya sada mu da shi. Da wannan nake muka addu'a a duk inda kuke, ni S-Reza ina ƙaunar ku a duk inda kuke Allah ya barmu tare. Albishirin ku masoya littattafan S Reza? Shin kun san wani irin labari zan fara rubuta muku? Hammm ba'a cewa komai. Shin ba dai kunce kuna son labari irin labarin UWATA CE SILA ba? To Tabbas wannan labarin sai ya taka shi chakwakiya da barikanci ta makirci. Ba zan faɗa muku sunan saba sai na gama shiri domin aikin na yi ne😍 Na barku lfy. One House One love Love all Typing S-Reza