[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA💋* NA *S REZA* ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... *SADAUKARWA* Na Sadaukar Da wannan Page ga Masoyan littattafaina, Ina alfahari daku, *S REZA* ❤❤CAKWAKIYAR SOYAYYA💋❤. PAGE 0⃣2⃣ ......... Tun daga ranar Shikanan Kullum Se sun Had'u agun Da'ake koyar darawa,Kuma Kamal, beta6a ganinn Suba. Sun kai kwan 5 Sunayi ɗan har tafara koya. Yau ma kamar Kullum Suna cikin aikin koyar darawan Cikin Farin ciki da nutsuwa Domin kuwa Basma Tana gane Abin da ake koya mata Kamal tin yana Shigowa, school d'in yan kullama, Sukafara Sanar dashi Chewa Basma tana can gun Amar Yana koya mata rawa, Aikuwa ko class beshigabaYanufi gun da a ke koyarda Rawa. *Waye kamal?* *Kamal Jamil* Shine Asalin Sunansa sunan Abbansa Alhaji Jamilu. Kamal Subiyu ne agurin Mahaifinsu Shida Qanwar sa Khadija. Kamal irin Yan iskan nan ne masu yiwa budurwa, dole, Babu Wanda, besan, Kamal ba,dik chikin school d'in, Har yara yake dasu domin kuwa yanada nera Abin da yaha dashi da, Basma,Tin wata Rana a school ɗin su da Sukayi. Wani program 📺, kuma yafito, amastayin mijinta Shikenan ya takura mata wy shi a dolematar sace. Ita kuma Basma Allah ya sakamata tsoran sa, Azuciyarta,kuma shid'in mugun matsoracine. (Zakusan hakan anan gaba kad'an) Wannann shine labarin Kamal. *Cigaban labarin* Kamal basuga zuwan saba sai jin maganar sa sukayi cikin isa yace,"Wato ke taurin kai kikeji ko dik abin da nake cemiki bakiji ko yanzu abin yabar cikin makaranta yadawo bayan makaran tako, kuma Ace Namiji shine yake koyamiki rawa?" Dik Wannann maganar da yakeyi Sunyi cirko-cirko Suna kallon sa Shikuma Se zagayasu, yakeyi yana wasa da, glas d'in dayake hannun sa. Yace"Wannann ɗin waye?" yana nuna gun da Amar yake. cikin rikicewa Basma tace,"Mallamina ne." Kamal yace."awace makaran ar?" Tayi shiru, Kamal yace"Kije kikoyi yan da akeyin girki ba Rawa ba daga yau in har. na kara ganinnki da Wannann Gayan yana koya miki rawa Sai kiyi dana sani" Yana kai wa nan Yakoma dabaya, yabar Gurin. Bayan yatafi Amar yace"Dama kina da aure shine baki sanar daniba?" Basma tace "Nice zan auri Wannann mahaukacin?" Amar Yace"To meya hada ki dashi?" Basma tace"Tin watarana damukayi program 📺 yafito a mijina Shikanann wy shi dole yana sona ni matar sa ce yan zu haka, Shekara 3 kenan Yana takuramin." "to meyasa kikayi Shiru kuma?" inji Amar. cikin Tsoro tace "Kai kai!! Walhi tsoran sa nakeyi." A'mar yace"Toni zan kawar da Wannann tsoran nasa daga idon ki." da sauri ta d'ago Kanta tana kallon sa,yace "eh Gobe ki kira shin Gun da zamuyi Rawa,zan sa yadena baki Tsoro." tace "kajifa yace in ya kara ganina ina koyan rawa zan ga abin da zemin." A'mar yace"Nide ga abin da nacemiki, in kuma kinaso in barki kicigaba da tsoran sa neto fine." tace "no Zan kirashi." *WAYE Amar* Amar, Shi Kad'ay iyayan sa suka haifeshi,Allah yayiwa Mahaifiyar sa rasuwa tin yana ɗan karami mahaifinsa Bai kara aureba,Domin yace, Ya hakura, da yin aure har abada, Yaransa Kad'ay ya i'she shi rayuwa. Mahaifin Amar, Yanada, Ilimi sosai yana koyar wa sannan sunada rufin asiri,Subaza ace mu masu kud'iba, kuma ba talakawa ba,Amar, Yarone, Mezuciyar neman na kasan sa, Yana dafushi in har a ka taboshi sannann ya iya rawa Sosai, domin kuwa, Dik makarantar babu wanda besan shiba, Yanada aboki guda 1 wato Sadam Irin mutanann ne. Masu abin dariya, Zeyi wahala, Kagan shiyana fishi , Abotar su tana tafiya yanda baku tinanin Amar farine ba sosai ba sannann yana da fara'a gashi da Saukin kai sunan babansa professor 👨‍🏫 Salisu, *(Abin da baku jiba, agameda shi,kubiyo ni a Cikin labarin Zakiji shi S REZA)* Bassma tunani takeyi, akan abin da Amar yagayamata Anya kuwa zatadena jin tsoran, Kamal kuwa Kode baisan waye Kamal bane? mugune bashi da mutinci ɗan akuya ne, Zai iyayinkomai akaina Har tashiga gida Bata yan ke hukun i ɗaya ba,tana zuwa bakin get d'in Gidan su Senaga ta Saki fuskar ta Tanufi gidan Wani Tanga memen Gidane Wanda Yakai gari guda. *(Tambayar da nafara yiwa kaina, Shine anyakuwa, nan Shine gidan su? abin da yasa nayiwa kai na wannanTambayar kuwa shine, Irin man yan motocin Danagani a fake, a harabar gidan, ita kuma Kullum a kan , ace6a takezuwa school kokuma, keke napeng)* Wani yaro Nagani, yafito daga chikin Farlon gidan Dagudu alamar yaganota yana zuwa yafad'a jikin tayana mata, welcome back Anty Basma, itama dariya takeyi tana cewa "Thanks my bro" Tad'aukeshi suka shiga Ciki. Abin da ya bani mamaki, shine Lokacin da Tashigo Gidan Wani, d'an matashe, Wanda Suke kama, a 'Kalla zaikai, Shekara 40 ko da 44. Yana ganinn ts yataso Ya rungumeta Yana mata, welcome, itama rungumeshi tayi tana "Thanks my daddy" Cikin Farin Cikin ganinn ta yace,"Haw is the school?" Tace "Daddy Ni walhi Yau school babu dad'i Yana jin haka, ya jawota kan jin yarsa, yana mata magana,"Meya faru my baby?" Cikin Sha'ko6a tace"Daddy Babu komy fa,kawy de nagaji ne, Rawar da mukayi yau ce walhi mun sha wahala." Dariya daddy yayi yace"Amma ai kin fara iyawa ko?" Bata bashi amsaba, Tami'ke tana nufar wani d'an Garamin kujera da yake Cikin farlon, tana zuwa naga ta kunnann wani d'an Qaramin yanfi Takekuwa Farlon yacika da wata waga Ta Yan USA🇻🇮 Take tafara bin waqar Cikin Yan da a keyin Rawar wakar. Abin mamaki Mutimin da take Kira da daddy, inace ko ze hanata, Senaga yana dariya Yana mata tafi, Shikuma Yaran da yaje yatarota, Lokacin daTashigo, naga yana toshe Gunnuwan sa. Wani mutum naga yafito daga Saman gidan Shida wata mata, da alama dai matar sa ce, Suna karasowaSukace,"Ashe yar baba tadawo"Suma zama sukayi Suna kallonta itakuwa sai taka rawar ta takeyin. *( KAI JAMA'A Wannan wani irin Gidane haka, , kodan bazan ce komy ba kude kubiyo S REZA )* *WACECE Bassma?* Bassma Sammani, shine Asalin Sunannta, mahaifinta Alhaji Sammani Ahuta, Yanada Tarin dukiya. tabam mamaki ɗan siyasane Inda yari'ke man yan mu'kamay a kasa Allhaji Sammani, matarsa guda d'aya ce, Wato hajiya faiza Sunyi auran Zumincine, amman fa nasoyayya, Allhaji Sammani yanada kani Me suna Sani. Sani Tin yana d'an Shekara 12,Rukonsa yadawo hannun yayansa Hajiya faiza,Tin da tahaifi yarinyar ta Sani Yama'yar da ita Tamkar yar Cikin sa baya bari ayi mata Fad'a, Kokuma ihu ,Koda kuwa iyayan natane. Har yayi Aure. Sani Shine ya sha'ko6ata, Wani lokaci Setayi wata 1 Agidan Sani Bata zo gidan mahaifan nataba, Suma. Iyayan nata Sun ji dad'in yan da yake kula musu da 'ya Tin lokacin Hajiya Faiza, 6ata kara samun wani Cikin ba, Shima, Sani tin da ya Auri matar sa. mesuna Zainab Ko 6ari batayi ba,Hakade Rayuwa taketa tafiya. Bassma Wata iriyar, Rayuwa take Agidan, Qaninn mahaifin ta wato, Sani, Bayamata fad'a ko wani abu da zesa Ranta ya6aci yana sonta Sanda Baze ta6abari wani ya ta6ata kuma yabariba Matar sa Wato Zainab Da har tafara, tsarguwa da irin Soyayyar da Yake Yimata,ammda Taga alamar in tace Zatayi wani abu ita zata kawana a rana dole itama tafara Yimata tata Soyayyar Haka iyayan ta zasuyi tafiya zuwa wata 'kasar, har wata 2 ko wata 3, batare da itaba amma ita ko ajikin ta Sede sudin ga yin waya yan zuhakama basa kasar watan su 1 kenann kuma sun kusa dawowa Shekarar Bassma 15, Wata rana Suna Zaune ita da Zainab Suna kallon Hausa film Se gani Sukayi, Sani, wato Megidan , Yashigo Gida Yana kuka, Cikin tashin hankali, yaman ta ma a gaban, Bassma Yake yace... "Yaya Sammani, Sun yi hatsari a jirgin sa Yan zu a ke fad'a" Cikin kuka Yake had'a kallmomin, Kafin suka Zauna a bakin sa. ina lillahi wa inna ilaihi Raju'un!!! Zainab Take fadi Bassma Tasha kuka, iya kuka, amma iya na Wannann lokacin ne, domin ita bata wani saba da iyayan nata sosai ba, gakuma 'kuriciya da take damun ta. Tin daga bayan Rasuwar iyayan ta, kulawar ta, yadawo hannunn Allhaji Sani, Damakuma a hannunn satake, Tin tana garama take son Yin rawa, hakan yasa Allhaji Sani Yashige mata gaba Komy tace tana so Tofa shi a kai yi Kodakuwa, Menene shi. Mutukar kud'i Ze iya siyan sa, Yaruwa sukeyi, rayuwa irin ta turawa baya kunyar yimata komy, itama haka ko a ina ze iya rungumar ta itama haka. Tana da kawa guda ɗaya Wato Lubna, Yanzu haka Bassma Shekarar ta 20 dai-dai Inda Zainab ta hafi, D'an ta mesuna, Sammani Wato sunann Ma haifin Bassma, yanzu haka Sammani shekarar sa 5 yana ta Shida Bassma Tana son yaron Sosai inda Sukecemasa, Little, Basma Batasan Ana kai ta school a mota, Domin ita wy haka tagurane jin hakan yasa Alhaji Sani ya barta. Su Shida 6 ne a gidan Allhaji Sani da matar sa Zainab dakuma yaran su,guda d'aya Wanda Suke cemasa little , Sekuma, ita Bassma, Dakuma Wani daga Cikin dangin su Shima Shida matarsa Sunansa Ali. Matar sa kuma Mariya fart d'in su daban. Wannann shine ta'kaitatcen Labarin Bassma *CIGABAN LABARIN* Washi gari, Dahuri ta isa school Tana zuwa Ta'kira Amar, tace "Gata tazo" Bayan yazo yace "Takirashi a waya tace yazo Yasameta agun da Suke koyar da rawa tana son ganinn sa" taci "ni kuma Bakai kace zakayi masa magana ba?" Yace "ai tare zamuje" Cikin Tsoro ta kirashi ta sanar dashi. Yace OK gashi nannn Zuwa. ________Kamal Lokacin da yaga kiran ta, yayi mamaki Sosai, amma yashre bayan yagama dik abin da tace yace ok "yanzu haka ina kusa dagurin ne." Haka yatabin wayar da kallon mamaki, mezesa takirashi kode 😂 tayar da zata aure shine Haka ya d'auki yara guda 2 acikin yaran sa suka tafi ✋....✍️✍️📝 *LITTAFIN,YADA HAR GITSI DAYAWA,ZAKU IYA BINA KOWA? , BA A FARA KOMY BAFA , WASU JARUMA ZASU BAYYANA AGABA* IN KUN SHIR YA GANEWA MUCIGABA,, ~HAQIGA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️📝🤫~ The end fart 2️⃣ To be continue.... *ALL QALAMI S REZA.. ✍️* *PLEASE COMMENT AND SHER,DAN ALLAH 🙏* ~BY S REZA~ [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *💔💔CHAKWAKIYAR SOYAYYA💔💔 *NA* *S* *REZA** * بسم الله الرحمن الرحيم...* *GARGA'DI* *Ban yarda wani ko wata, Su canzamin labariba Seda izinina.* _________________________ ~DAGA S REZA~ Wannann Book d'in Yazo da Salo Naban mamaki, Kuma Nayi amfani da, Abubuwan ban mamaki, " Sannann Kuma Zakuga, Sauyin, Halayyar Jaruman cikin Littafin, Yasha banban Da namu na hausawa. Kude kukasan ce da, S REZA* *Sannann kuma, Wannann, 'kir-kiranran, labarine, Banyishi DanCin Zarafin kowaba* _______________________ *GODIYA GA ALLAH* *Masha Allah for everything about my life , I'm thank God for everything* _________________________ *PAGE 1⃣. FREE BOOK* 📚 *Dan Allah Kaƙara gudu Domin Bana son Na maka irin Najiya, Domin Wannan Sabuwar Malamar Bata Da kirki inde Har kazo a Makare Wallahi ba ruwan ta Korar ka Zata yi" Wanda ake Zubawa Wannann SuRutun, Kai kace BadaShi a keyiba, YaraBu da ita, Se Suruntun ta take yi Shikuwa Tu'kin Mashin Ɗin Sa yakeyi Ko kallon Tama bayayi. ta Kuwa Bata dena Surutun Ba Har Suka Ƙaraso. Suna Ƙarasowa Kuwa Da Sauri Ta Sauƙa Daga Kan Mashin Ɗin TamiƘamas Kuɗin Sa, Ko Canji Bata tsaya ƘarƁaba Har Tana Haɗawa Da gudu. Shi kuwa Memashin yana ganin Haka ya Soke kuɗin Sa yabar gurin. Dik da Saurin Da Taketayi Hakan BaiHana ta Makaraba Tana zuwa Bakin Class Din Malamar Tasu Tana Shiga. Ai kuwa Tana Shiga Malamar Tace.. "Get out in my class" Ta bude Baki domin yin magana Malamar ta Ƙara cewa.. "ai see get out in my class" Tana nuna ma ta Hanyar Fita Juyawa tayi Ta kalli student Taga Kowa Su yake Kallo.. Haka kuwa Ta juya Tabar Class Ɗin. Basma, Bata da Burin Daya wuce Ace Ta iya Rawa, a. Ci kin school Ɗin a kwak ƁanGarori Daban Daban,ƁanGaran boll Ɗin kwando, Da Ɓangaran Koyar da Rawa ƁanGaran gudu ,, Dik Wani sport Daka sani To a nayi a cikin Wannann school din. Bayan tafito Daga class din Ta wuce Gun Koyar Da Rawa.. Tana Shiga Gurin Ta Tarar Har anyi nisa Da KoyarWar. Itama Tashi ga Layi Bayan Sun Fito Daga Gun Koyar Da Rawan ne Tana Cikin Tafiya Taji ankira SunanTa, "Basma²!!" Tana Juyowa taga Ƙawar Lubna Tace "Haba Basma! Dik Wannann uban Kiran Da Nake ZabGa miki Zaki ce BakiJi niba?. Basma Tace.. "Sorry Wallahi ban jikiba,ina SauRine Bana So Muhadu Da Wannann dan Rainin Wayon" Lubna Tace.. "Waike Dan Allah Bazaki dena Tsoran Wannan Wawan Bane? Basma Tace.. "Abin Da yake Son InBari ne Wallahi Bazan BariBa, Domin Shine Burina ,Bani Da wani Buri Daya huce inzama yar rawa kin Gakuwa wallahi be isa ya hananiba" Kafin Lubna Tayi Magana Sukaji an Ce.. "Da kuwa kinSha wahala, Domin ni A tsari na Matar Da zan aura BazaTayi Rawa Ba" Tace "Kai dakata Ni ba matarKa Bace,Rayuwa Ta Rayuwa Ta ce! Yace "idan naƙara gani,Ko na ƙarajin Ance an ganki agun rawa ko" Kafin ya Ƙarasa Lubna Tace "Tomeza Kayi? Ko kallon ta beyi ba yaci Gaba da Cewa.. "To kisani Cewa ba a nan ba Sekin Shigo Gidana Zan nuna miki", Yana magana yana nuna mata Hannu.. Yana gama faɗa yajuya ya barSu agurin a tsaye. Bayan Yatafi ne Tace "Ban Za wawa Wallahi Saboda...in koya masa Hankali Ma Sena Dage Na koyi rawa" Lubna Tace "Ni wallahi kina ban mamaki Meyasa Bazaki iya MagaNa A gaban sa.. nide Wallahi kin fara bani Haushi" Suna tafiya Suna Zancen, Ita kuwa, Basma Tana Ƙara faɗa wa Ƙawar tata Cewa Zata dena TsoranSa. Suna cikin Tafiya Ne Suka ga taron wasu Student Suna Rawa an saka mutum ɗaya a tsakiya sai Rawa yakeyi Sukuma Sauran student Ɗin Se ihuu Sukeyi Suna Tafi Shikuma Sedagewa Yakeyi Kai da kaga irin Rawar Da Ya keyi Kasan Ya Ƙware. Basma AbinYa Burqeta Taji Ɗan saurayim da yake" Rawan, Rawar Tasa Ta burgeta Ai kuwa " Take itama Tafara Jujjuyawa Kai wai itama Tana irin Rawar Sa. Lubna Tace "Menene Haka Wallahi Zantafi in Barki" Ita kuwa Basma Tace "Ke wallahi Na Samu Me koyamin Rawa Domin Rawar Tasa Ta burgeni" Hakade SukaTafi Tana Yabon Rawar Ɗan SauRayin. Kuma Tace Zata Same Shi Domin Suyi magana. ________A'mar Bayan Sun gama Rawar Dama. Gasa A ka Saka Ta rawa Kuma Shine Ya Lashe Gasar, Bayan Sun Fito Ne daga Cikin MakaranTar Shi da abokin Sa Suna Futowa Sekaji Kowa ya na, "A'mar²" Haka mata da Maza Dama Kuwa yana Ɗan koyawa Muta ne Rawa Amma lokaci lokaci Abokin nasa ne Yake cemasa Kai A'mar Wallahi kai me sa'a ne a Rayuwar Ka... A wannan zamani. Bako wa bane Ze Haɗa Kara tun Jami'a Da Rawa.. Kuma Dik Yadin Ga Samun Nasara ba A'mar Yace " Haba Tinkafin. Ni wasuma Sunyi kaga Kuwa Wannan Bawani Abin Mamaki bane" Abokin Yace "Amma de Ba'a cikin wannann Garin Na Benue state Bako? Haka de Suketa hira har Suka bar Makarantar ________Basma Itade Tasamu malamin Koyar da rawa Kuma Babu Abin da wancen Banzan Ze iya Kuma ni wallahi Be isa Yasa indena Rawaba.. Haka de Take ta Surutunta, Washe Gari... Saboda Tana Son suhadu Dashi ko tsyawa ma yin Breakfast Batayi ba haka Ta Kama Hanyar School. Yau Dawuri Tazo Hakan Yabawa kowa Mamaki Domin Kowa Yasan Ta da Zuwa a Makare Banyan Sun gama Daukar Darasi Ne Takira Lubna Domin Suje Neman Sa. Ai kuwa Tana Zuwa, Lubna Tace "waike Da gaske Kike yi ne dama? Basma Tace ok "Dama ina miki Qaryane?.. Tom Bari kigani" Tana ganin tafara tafiya Itama Tabita Domin Tin da Tace Aikuwa Sefa Taje ________A'mar Wani. hool Ne da a'ke gudanar da Dik wani Abun Da ya shafi MakaranTar, yau ma an gabatar da wata Gasar Rawa ne. Kuma yana Cikin Yan gasar Yana gefe Shida Abokin sa Wato, Sadam, Kuma Kowa Ze iya gaiyato mutane Domin kallon Gasar Hol Din yacika da mutane yan school dama de Baƙin Da Suka Zo kallon Gasar Kafin a fara ne... Suna hira Shida Sadam Wani daga Cikin Malaman School din Yazo gunDa suke Yana zuwa Ya dafa A'mar Yace "Amar meyake faruwa.. Kunanan Ana ƙoƙarin Fara gabatar da gasar kukuma Kuna Hutawar kuko? A'mar yace "Wani irin Hutawa Malam. Bayan Har yanzu takadduna Sunƙi Haduwa niburina Yanzu na kammala. P. H. J. Dina amma malam kaƙi Bani gudunmawa" Malamin yace.. "Haba A'mar Dik wata nasara DaKasani A Hankali a ke samunta Amma kai naga a lama da Hanzari kake Son taka, kayi haƙuri Ka d'an ƙara jira" A'mar Zeyi magana malamin Yace "kar ka damu. Yan zu de yakamata kumatsa kusa... Sannan ya barSu a gurin" "ok gamunan Zuwa" Kafin Subar Gun da suke Ne Sega Tanan Da Saurin Ta Tana Zuwa Tace "Barkan kuda rana" Kafin A'mar Yayi magana. Sadam yace "Barka yanmata me kikeso? Basma Tace Sunana "Basma Najib Nima 1 daga Cikin student Din wannann makarantar Kuma. Ina Son.. Kakoya min Rawa ne Domin Munada gasar rawa da za muyi Kuma nima ina ciki... Sannann Kuma irin Rawar Da naga Kanayi Jiya ita Nake Son kakoyamin" Tin Tana Cikin maga nar Sadam yake cewa a cikin Zuciyar sa. Wannann irin Zuƙeƙiyar budurwa amma Ita rawa ta keson koya Kuma Tarasan Meko amata Rawa Se namiji Haka ita Kuma Tachi gaba da cewa "please ina son inci gasar domin Shine mafarkina" A'mar Yace... "Nikuma saboda cikar mafarkin ki Sena bar nawa ko? Se tace "Bafa A kyauta Zaka Din ga koyamin ba Zan dinga biyan ka please" Sadam yace "Ok dama Biya Zakiyi. To nawa zaki din ga biya Dik Sati? Tace "Zan dinga biyan nera Dubu 5, " yace ki'kara masa mana, Dasauri tace "to zan Din ga biyan dubu 10 Dik Sati" Sadam yace "To shikenann badamuwa Nima abani Wani Abu" Lubna Tace "To kafin a baka wani Abu Sekafara koyamata Tukun, Kaiba da Rawaba kai da Surutu". Sadam Zeyi magana kenan Akakirasu Suka bar Gurin Yana Hararar Lubna , Bayan Sun Shirya in da zasu fara koya mata Rawar gobe. ita Kuma se dariya Take tayi masa Suna juyawa Suka Hadu da Kamal. Yace "Wato ke tauRin kaine dake ko Nace miki Matata Bazata yi rawa ba kekuma kin Dage ko to walhllhi in har nagan ki agunrawa to wallahi Se kingane niwaye.." _________________________ *TO FA GA SABON BOOK NA FARA Me taken Muzuba muga ni Please ina bugatar Addu ar ku a gareni* *NAKUHAR KULLUM *S REZA* *The end part 1️⃣* *To be continue ⏩....* *In naga ruwan comment Zan cigaba Amma in ban ga Comment ba bazan cigaba ba* Please Sher And Comment By S REZA [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... CA'KWAKIYAR SOYAYYA ♥️💘.... PAGE 5️⃣ .........Gurin da suke ya nufa Babu alamar tsoro a tare dashi, Yana zuwa ya nuna Wanda yayi wannan maganar, ya ce " me maka ce? "Shima cikin rashin tsoro ya ce.. "Cewa nayi Zata iya ɗaukar maza guda huɗu.. ai ko ƙarasawa bai yiba. Amar Ya ɗau keshi da wani Mari Wanda har sai da yaga ha'koransa guda 2 a hannun Sa, Kafin kace me, Sauran biyun Sun yo kan sa. Cikin sa'a ya 'kara kaiwa nafar kon naushi Wanda Sai da ya fad'i, Ya kamo na bayan yayi daniyar 'Dago shi Se yaji Saukar wani abu a bayan sa, Yana dubawa yaga Wannann na farko ne daya Zubar masa da ha'kora Shine yataso ze Soka masa wu'ka Shine Basma ta rigashi tabuga masa dutse akai. Nann take yazube , Amar yatara su a guri d'aya, Ya ce waya turoku gurina jiya? Cikin Tsoro Sauran Suke kallon Sa, Ogan nasune ya ce.. "Kai ne Amar?" Cikin tsoro yake Kallon Amar ganin yanda idon sa ya sake color, Amar ya ce "waye yaturoku Gurina? "Shima yana Yiwa ogan nasu tambaya a karo na biyu Cikin Tsoro ogan nasu ya ce.. Kamal Shine ya turomu, Kuma ba mashin yace musataba, Cikin mamaki yake bin Su da kallo ya ce.. Waye kamal? Domin Shi har ga Allah Bai ma san waye kamal ba.Basma ce ta ce.. "Kamal kuma,To meye kamal d'in ya ce muku?" Ogan Nasu ne ya cigaba da bayani. "Ya ce mun Mu biku abaya duk gurin da ku kaje, Sannan ya ce.. Wan da suke tare da ita muyi masa duka, wato kai kenan,ita kuma yace Mu d'auko masa ita mukai masa in da yake.Amar ya ce.. "To meyasa baku Sace ta ba kuka sacemin mashin?" Yana kallon Su. Ogan ne ya ce.. Eh da Mun so muyi hakan amma ruwan da a kafara ne alokacin Yasa muka rabu daku,kuma Mun sace wannann mashin d'inne Domin kar kutafi ku tsaya neman sa har a d'auke ruwa, Amma bakuyi hakan ba. Waya yazaro yakira yan sanda domin Sutafi dasu, bayan wasu lokuta Sega motar yan sandan Sun garaso gurin, Nan take aka Saka musu ankwa akayi gaba dasu. Amar yajuyo Gurin basma ya ce.. Waye Kamal? "Nan take ta sanar dashi, Shine wannan na school d'in nan nasu,Nan take shima ya gano shi, ya ce " Dama har yanzu yana tare da ke ne? Basma ta ce.. "Ni Wallahi har na manta dashi a rayuwata kai ma bana son kasa wannan a ranka please. Cikin 'Dan damuwa ya ce.. To yanzu da kika biyosu nan gurin ke kad'ai in da ban zoba sun miki wani Abu kuma fa? Yana maganar yana 'kar6ar a gogon sa yana sawa a hannu, kafin tayi magana ya cikigaba da cewa, a kan mashin Zakije ki Jawo wata damuwar.Wannann mashin d'in Ina jin sa tamkar wani abune daga jikina, Duk wani Abu naka Ina girmama shi Sabuda haka kar kace a kan mashin kawai. Jin haka yasa yaji dad'i Sannan yace.. Duk da hakan Kin yi kuskure, Kar ki'kara irin haka kinji. Cikin murna tazo dagudu ta rungumeshi ta ce.. Ina sonka Sosai Amar. "Shima rungumar ta yiyi ya ce.. Me too my baby. Haka suka kamo hanya zuwa bakin ti-ti. Seyan Zuma basma Ta tuna da wanda ya kawo ta nan wato me mashin, Amma ta duba bata ganshi ba, Wanda tun lokacin daya ga Basma taje Gurin su sun fara Biyota kamar zasu daketa shi kuma ya tada mashin d'in sa yabar Gurin. Ganin bata ganshi bane yasa suka tafi. Har Gurin da Ta bar su Lubna da direban su me mashin d'in ya kai su, Dama kuma ta kira Lubna ta tambaye ta suna Gurin har yanzu ko dau sun tafi?Inda Lubna ta hauta da masifa kafin ta ce mata suna Gurin. Sallama Suka yi da Amar a kan zeje gurin ƴan sandan Domin jin abin da zai faru motar tashiga tana d'aga masa hannu Shima yana d'aga mata hannun har suka tafi. Tana kallon irin hararar da Lubna take bin tadashi Amma ko kallon ta bata yi ba har suka isa. Gaskiya Basma abin da ki keyi wallahi Babu 'kyau Yanzu gashi kin samun fasa zuwa gurin da mukayi niya Saboda wani banzan dalilin ki.Lubna ce take wannann masifar ganin Basma ta sa Sun dawo gida, Cikin Sanyin murya basma ta ce .."yanzu haka daddy yana nan yana jiran dawowar mu in yaga mun dad'e kin san zeyi fad'a.Lubna ko magana ba batayi ba ta wuce ciki ta barta. ...............BASMA turus tayi tana kallon mutanan da bata san suwaye ba tayi tana kallons u a parlon, Cikin mamakin abin da yakawo su gidan nasu ta bisu da gaisuwa amsawa duk sukayi suna kallonta, Kusa da daddy ta je ta zauna Domin jin abin da ya kawo mutanan,amma kash tayi rashin Sa a domin tana zama sukuma mutanan suna cewa.. "Tom Muzamuko ma se in mun dawo,kuma munji dad'in yanda kuka amshi bu'katar mu mungode sosai"cikin fara'a daddy ya ce.."masha Allah bakomai ai yanzu an zama d'aya ya tashi ya raka su izuwa gurin motar su. Basma babu abin da ta fahimta acikin zancen su, Hakan ne yasa bata bawa maganar wata muhimmanci ba ta cigaba da harkarta .Har cikin d'aki taje ta samu daddy ta ce ..daddy me yakawo Su gidan nan naga kamar nasan su ko daddy? Daddy cikin san yaga ya faran ta mata ya ce.. eh kin sansu amma tun kina yarinya domin tunda kika girma ba suzo ƙasar nan ba sai wannan karan, Kuma yanzum ma sun zone da abin arzi'ki. "Daddy me suka zo yi?" Basma ta tambaye shi domin ita jikin ta yafara bata ba lafiyaba, "daddy ya ce.. Sunzo ne da batun Suna son abasu auranki ga yaran su, Kuma mun amince domin yaran d'an manyane, Yanzu haka yaran ya daga cikin manyan yan kasuwa da suke cikin 'kasar nan, yajuyo yana kallonta ya ce.. daughter in kin auri yaran nan zaki ji dad'i kuma ni burina kenan Saboda haka na yarda da mutanan kuma nace jibi suzo se ayi maganar domin nasan na isa dake baza kibani 'kunyaba ko my daughter? Ya ƙarasa maganar yana kamo kumatun ta yana ja. Basma tun da daddy ya fara maganar ta tsaya tana kallon sa cikin mamaki, Aure kuma! Cikin zuciyarta take cewa, to ma wai haka a ke aure bansan mutum ba to bama wannann ba karatuna fa? anya kuwa daddy yasan me yake cewa kuwa! Jin ana ja mata kumatu ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, Ta ce..daddy "aure fa kace? "Daddy ya ce.. "eh aure nake nufi domin mutane sun fara magana a kanki wai nine na hanaki haure Bana jin dad'in abin da dagin suke cewa a kaina da kuma ke. Yay maganar hawaye na zubowa daga fuskar shi, yacigaba da cewa...Suna zagina sosai nikuma ba wai aure ne bana so kiyi ba, inason in samu wanda zai ri'kemin ke da amana ne kuma inason ki auri me arzi'ki domin kihuta, Hakan ne yasa na za'bamiki shi yaran yan kud'i sosai kuma bawai kud'in baban sa bane kudin sa ne zaki ji dadin zama shi kin ji daughter? Yana kamo hannunta. Basma wannan shine karo nafar ko da taji tausayin daddy, Shine karo na farko da takasa musa abin da ya ke cema ta kuma gashi tasan abin ba me yuwa bane tasan baza ta amince ta auri wani ba in dai ba Amar ba , to amma meyasa ta kasa yin musu? Tambayar da ta keyiwa zuciyar ta kenan. Maganar daddy ne yadawo da ita daga tunanin ya ce... Jibi za suzo tare da yaran se kuyi magana kin ji, in sha Allah zaku fahimci juna dashi , haka tana ji tana kallo daddy ya tashi yatafi amma taka yin musu kuma zuciyar ta takasa amin ta da maganar daddy, haka itama cikin sanyin jiki ta tashi tabar gurin . ...............AMAR Abba Gani ya na kallon abban nasa cikin son jin me zai cemasa abba ya ce.. "Takardun ka natura izuwa gurin wani professor Dayake *ABUJA,* kuma ya duba yagani ya ce in turaka domin takardun sun yi kyau. "Cikin farin ciki ya ke kallon abban nasa da ya rage masa a duniya wanda ba yason 'bacin ransa ,Wanda akansa yake yin duk wani abu domin gobensa, ya ce... Abba wallhi naji dad'i sosai shima abban dad'i yaji yana ƙara jin 'kaunar d'an nasa a zuciyar. Numbar Basma yafara kira domin yayi mata albishir da cewa burin sa ya kusa ciki. Kira d'aya ta ɗaga amma kafin yayi magana ta riga shi da cewa.. Amar kana ina ina son mu had'u yan zu? "Yanzu ina gida nima dama a 'kwai abin da zan gaya miki. Basma ta ce.. To yanzu ina zamu had'u, Amar ya ce.. Zaki iya futowa daga gida? Cikin sauri ta ce.."eh zan iya , nan take yace mata ok tom kizo gurin Shagon Sadam ina gurin yanzu haka ok ta ce sanan ta tashi da sauri. Tunani take yaya zata fita daga gidan nan! Nan take dabara ta fad'o mata da sauri ta fito falor tana zuwa ba kowa sai little, Dasauri ta kamo hannun sa ta nufi d'akin ZAINAB. Tana zuwa ta ce.. Anty little zai rakani gidan su Lubna zan 'kar'bo wayana naman ta da ita a gidan su? "Kasan cewar gidan bawani nisa yasa anty "zainab cewa.. To kuyi sauri domin yanzu Daddy yafita kin ga ba yason yarinka ganin ku a waje kiyi sauri kin ji tana mata hargaɗi da hannu a kan kar su dad'e. ok Basma tace tan kama hannun sa suka bar falon Sai da tabi ta gidan su Lubna Domin taraka kafin suka tafi tare. Basma da Lubna Sun riga Amar zuwa inda suka samu Sadam agurin. Bayan sun gaisane Suka samu guri suka zauna , Kafin Amar yazo Basma Ta kwashe duk abin da sukayi da Daddy ta gaya mata "cikin mamaki Lubna ta ce... To yanzu me abin yi? Tana tambayar Basma? Basma ta ce ..shine nima ban saniba, Bansan yanda zai dauki maganar b... Kafin tagarasa Sai gashi ya karaso , kai da ka ganshi kasan yana ciki. Farin ciki. ..............AMAR Yana gan ku cikin wani irin yanayi , To nazo muku da labari kuna sonji, Cikin farin cikin da yakasa 'boyuwa a fuskar sa yake wannan maganar. "Amma jin abin da Basma ta ce ne yasa ya tsaya cak agurin yana kallon ta. Basma ta ce... Yaka mata muyi Aure Amar , wannan kalmar yaji daga sama tafito daga bakin Basma, Taci gaba dacewa... Saboda kaga jibi masu neman aurena zasu zo gidan mu, kuma Daddy ya amin ce musu, kuma nina ji a jikina daddy na bazai yarda muyi aure da kai ba please dan Allah Amar muje wani guri muyi auran mu Ta karasa tana kuka kamar Ranta zefita . Amar ya ce..Aure kuma Ban gane ba? Yana tambayar ta Cikin kuka ta ce.. Amar bana bukatar ina zaka kai ni ko kuma ina zaka ijiye ni ni dai burina dan Allah muje muyi Aure, Bayan soyayyar ka bana bukatar komai a gareka player. Amar ya ce .. To sai naga ace za ayi aure yanz..."kafin ya karasa ta ce Amar in dai kud'ine matsalar ka zan ji da komai tana kallon shi cikin hawaye. Amar yace "wai kud'i "kafin yayi maga ta ce .. To menene matsalar ka? Tana bin shi da kallon wanda izuwa yanzu kukan takeyi, ganin yayi shiru ne tace.. "Shin Amar kana sona? Zaka aureni?" Amar a karo na farko da zai runguume ta ganin irin kukan da takeyi , ya ce ..tabbas zan aureki, kuma zan baki duk wata kulawa da bakiyi tunani ba , tana jikin sa har yanzu kuka takeyi , tanajin damuwar ta tana raguwa, Ta ce ... Ina sonka Amar ina 'kaunar ka ,shima abin da yake fad'a kenan har zawu wani lokaci Sannan ya saketa. Sannan tace ya a kayi da su Kamal. Yace ban je gurin ba har yanzu amma nasa wani abokina a kan maganar shima police ne. Batace komai ba har ya rako su gunda zasu shiga keke napin sannan suka koma shida Sadam . Duk wannann abin Da a keyi , lubna da Sadam suna gurin amma babu wanda ya iya cewa komai domin Lamari. Na sune su biyu. Amar ya ce.. Sadam Wallahi da matsala shin kasan abin da abba yace min? "Sadam ya ce.. Aa, Nan take ya 'kwashe duk yanda sukayi da abban sa ya gaya masa , Sadam yace. "To meyasa baka gaya mata ba? "Amar ya ce... To tayaya zan gaya mata acikin wannan halin da take ciki ni yan zu ma wallahi ban san abin yiba Sadam ya ce ..Amar wallahi Basma tana sonka kuma son da ta kemaka ne yasa tace kuyi aure please dan Allah kar ka bata kunya pls Amar yace ...sadam bari zan yi tunani a kai ..daga haka babu wan da ya kara magana har suka bar gurin ....✍️📝 *YAU A KE YIN TA ANYA KUWA HANYAR DA BASMA TABI ZATA 'BULLE KUWA ,. Shin Amar Ze yarda ya bar aikin da baban sa ya sama Masa , ya auri Basma ,. Shin waye Wanda DADDY YAZA BAWA BASMA,. KU KASANCE DA... S REZA* HAQIKA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️📝 the end of Part 5️⃣ To be continue..✍️ *ALQALAMI S REZA✍️* *PLEASE COMMENT AND SHARE DAN ALLAH 🙏🥰* ~BY SALIS M REZA~ [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKWAKIYAR SOYAYYA❤❤ NA S REZA ✍ ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma Writers Ƙungiya 'Daya Tamkar Da dubu Farin Cikinmu, Mu Faɗakar Da Al'umma Domin Su Farfaɗo Su Gane Gaskiya Al'umma. Sai Don Al'umma Allah Ya Ba Mu Ikon Fadakar Da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... **DAGA, S REZA* *Wannan littafin yana da sar'ka'kiya yana da hargitsi 'kunshir ya, fahimta mu cigaba domin kuwa, Sai kun bi ni a hankali cakwakwakiyar soyayya. Ba a *ma fara komai ba fa ku kasance da S REZA** 🙏 ________________________________ HAPPY MAULUD 🕌 ❤CAKWAKIYAR SOYAYYA❤. PAGE ⚓️ 3⃣ ...Sun riga shi 'karasawa gurin, Amar yake ce mata "Abin da nake so da ke, Shi ne. In ya zo kar ki ji tsoran shi, ki zare masa idanu, ki gaya masa magana babu abin da zai iya. Ya cigaba da ce mata, kin ga can ya nuna mata. Ɓarin hannunsu na dama, ta bi hannun da kallo, ta ce "Na gan su me za su mini? Ya ce Ba za su bari ya yi miki komai ba." Basma ta ce"Ni gaskiya tsoro nake ji ba zan iya ba don Allah abar shi kawai. Cikin san ya ga ya taimake ta ya ce: "Kar ki saka tsoro a zuciyarki, ba abin da zai iya." Suna cikin haka ne, suka hango motarsa tana zuwa gurin. Amar ya ce: " Ki dage ina kusa da ke, kar ki ji tsoro." Yana gama fad'in haka ya bar gurin, cikin sauri, domin kar ya gan shi. Basma tana ganin ya tafi, tsoro ya k'ara kama ta, ga shi kuma mugun yana zuwa. Kamal tun daga nesa ya hango ta, yana tafiya idon sa yana kanta. Wani irin shu'umin kallo yake bin ta da shi, har sai da ta tsargu. Ta ji gabad'aya ta k'ara tsanar shi. Kamal yana zuwa, ko sallama babu ya ce " Ga ni na zo me za ki mini?" Cikin muryar 'yaniska yake magana, me za ki ban? Fad'a min mana. Basma ta kasa magana sai ja baya take yi, shi kuma yana bin ta.Tana kallon gurin da Amar ya nuna mata cewa ba za su bari ya yi mata, komai ba. Kamal ya cigaba da cewa. "Me kike kallo ne a can ki yi magana mana." Basma suna had'a ido da Amar ya yi mata nuni, da hannu a kan, ta yi magana. Cikin juriya kuwa ta fara magana. "To me za ka yi? Na ce me za ka yi? Ko kana tunaninn ina tsoran ka ne,? To bari ka ji in gaya maka, Na kira ka nan ne domin in shaida maka, daga yau. In har ka k'ara shiga harkata, Wallahi sai ka raina kanka, ban za wawa. In ka isa ka taɓa hannuna, tana miƙa masa hannun, tanabin shi. Yana ja baya, kamar yanda ya yi mata d'azu. Ka ta'ba na ce in ka isa. Tana ƙara tura masa hannunta. Kamal cikin mamaki yake kallon ta. Ya ce " Ke ko kin sha wani abu ne?" Yana maganar alamar storo a fuskarsa. Ya ce "Na ga alama ba kya cikin hankalinki." Za mu haɗu wani lokaci, ya ja yaransa suka bar gurin da sauri. Basma lokacin da ta fara ganinn alamar tsoro a fuskarsa, hakanne ya ƙara mata, ƙwarin guiwar cigaba da abin da take yi. Ta yi mamakin ganin bai iya yi mata komai ba. " Ashe ma mugun matsoraci ne." Ta fad'a a fili daidai lokacin da Amar ya ƙaraso gurin. Amar ya ce "Da ma na gaya miki yanzu ga shi kin gane, ko shi ɗin waye." Cikin jin dad'i, ta ce "Amar na gode sosai." Ta zo da gudu ta rungume shi tana dariya. Amar wani abu ya ji, lokacin da jikinsu ya had'u guri d'aya. Kasa yin magana ya yi, har ta sake shi ta bar gurin. Tana farin ciki ta nufi cikin School. Amar, tsayawa ya yi a gurin kamar wanda aka kafe, shi yana bin ta da kallo. Har ya daina hango ta, kafin ya ja numfashi, ya bar gurin yana murmushi. Tun daga ranar ala'karsu me 'karfi ta shiga tsakanin, Amar da Basma. Rawar ma yanzu ba sosai yake koya mata ba. Ɓangaran Kamal kuwa tuni, yake shirin yadda zai 'bullo mata. Gobe za ba da hutu school kuma gobe za a rufe, school d'in. Kuma shi Amar wannan shi ne, final year d'insa. Suna zaune su biyu suna zancen makomarsu, in aka ba da hutu, ya za su yi. Basma Tun lokacin da ya raba ta, da Kamal take jin sa a a zuciyarta. Hakan ne ya sa, take ganin ya dace su samu mafita. Basma ta ce. Amar, cikin wata irin murya. Bai kar'ba mata ba ya juyo yana kallon ta ta ce. "Wannan k'warin guiwar da ka ba inda da soyayya a cikin ta, ya za ta kasance? Please ina so ka kasance a rayuwata har abada. Amar na yarda da kai please." Tana gama fad'in haka ta tashi ta bar gurin, shi kuma ya bi ta da kallo ya kasa magana. Har ga Allah yarinyar tana burge shi, amma kuma shi halaiyarta ne suke ba shi mamaki. Domin ita ba ta kunyar ta rungume, shi a gaban kowa. Ko kuma ta gaya masa kowacce irin, magana ta zo bakinta. Amma in ba haka ba yarinyar ta yi. Haka dai yake ta tunanin. Abin yi . Amar ne a gaban mahaifinsa, wato Farfesa Salisu. Shi ma a makarantar yake koyarwa, ya dubi yaron nasa ya ce. "Gobe za a ba da hutun school, kuma kai gobe za ka gama gabad'aya. Ina son in sanar da kai cewa, har na sama maka, aiki a Abuja. Domin can na ga za su fi biyan albashi mai kauri." Yana gamawa Amar ya ce. " Baba ni ba zan iya barin garin nan ba!" Wace ce yarinyar nan da nake, ganin ku tare a school?" Ya tambaye shi. Ya ce. Basma ce. "Saboda ita ne ba za ka bar garinnan bako? To ni dai na gama magana. Ba ni da darajar da zan sama, maka aiki a cikin garin nan." Amar ya ce. " No baba zan samu wata makarantar na dinga koyarwa kafin wani lokaci." Abbansa ya ce. "Oho dai in ka ga dama kar ka koyar da kowa, ka tsaya kai ta yawo a gari. Kana koyar da rawa da ba komai kake samu ba." Ya ce "Baba kar ka damu na kusa zama wani abu." Ya fad'a cikin dariya. ______Basma Cikin tunanin abin da zai ce mata ta dawo gida, tana zuwa gida wanka ta yi. Sannan ta fito Parlon gindan ta zauna, tana tunani. Can ta mi'ke tsaye ta nufi d'akin daddy tana shiga ko sallama babu, ta tura k'ofar d'akin. Ta same shi, shi da Little suna shan kankana. Tana zuwa da gudu ta nufo shi, shi kuma ya ware mata hannu ta fad'a jikinsa. Cikin shagw6a ta ce "Daddy ni gaskiya wani abu nake so kai mini." Ya ce " Gaba 'yar daddy me kike so? Ko mene ne, ki fad'a mini a shirye nake da yi miki." Bayan ya d'auki kankana, ya saka mata a baki. Ta ce "Daddy ka san gobe ne za a ba da hutun school ko?" Daddy ya ce " E na sani me ya faru? Ta ce. "Daddy wanda yake koya mini rawa ne, nake so a kawo shi gidan nan. A rik'a biyan shi yana koya min rawa, tun da bai samu aiki ba ka ga sai ait's dinga biyan shi kud'i mai yawa ko daddy?" Ta k'arasa maganar, ita ma tana saka masa kankana a baki. Sai da ya shanye kankanan Ya ce. "Wannan ai ba wata damuwa ba ce, 'yar daddy, kar ki damu ki fad'a masa ya zo ya same ni za mu yi magana da shi kin ji." Cikin farin ciki ta manna masa kiss 💋 a goshi ta ce "I love you my daddy" Tana fad'a, ta tashi ta ri'ke hannunn little, suka fita Izuwa d'akinta. Waya ta d'auka ta kira shi bai d'aga ba. Hakan ya sa ta yi masa text message sannan. Ta kira Lubna ta ce ta zo gida ta same ta za su yi magana. Amar ne tare da Alhaji Sani wato baban Basma , Bayan ya gaishe shi, Alhaji Sani ya bi shi da kallo daga sama har 'kasa, Sannan ya ce. "Ya sunanka?" "Sunana Amar" ya ba shi amsa. Daddy ya ce ya yi kyau. "aikin me kake yi?" "Na kammala P h d yanzu haka ina jiran aikin yi ne." ( SLHAJI SANI FA BEYI KARATUN BOKOBA KAR KU MAN TA) Daddy ya ce. "Wato karanta tsare-tasre ko?" "Amar ya ce. A'a ana nufin 'kididdiga Kenan." Daddy ya ce. "Kana nufin ka ce mini kana da takardun kammala Karatu ko? To ni ba wannan nake son sani ba. Ina son sanin taya kake samun kud'i wani aiki kake yi yanzu?" "Ya ce " ina d'an koyar da rawa Ana biyana." Daddy ya ce. " To daga yau ka daina koyar da kowa. Sai yarinyata sannan za ka dawo gidan nan da zama har zuwa lokacin da za ka samu aikin yi." Cikin mamaki yake bin daddy da kallo. Saboda ya ji ya ce zai dawo nan. Daddy ya ce. " Kar ka damu wannan tsarina ne zan dinga biyan ka dubu 50, a kowanne wata. In dai har Basma ta ji dad'in zama da kai." Jin kud'in da aka ce za a biya shi ne ya sa ya fasa fad'in abun da zai ce sai godiya yake yi cikin jin dad'i, ya tashi ya bar Parlon. Yana fitowa ya kira ta a waya domin tun da ya shigo bai gan ta ba, tana d'agawa ta ce zan kira ka leter "ok" ya ce. Haka ya je ya sami Abbansa ya gaya masa, duk abin da ya faru. Amma bai ce masa a gidan zai zauna ba. Don kar ya yi sa a abbansa ya amince. Washegari haka ya sanar wa da Sadam` shi ma ya yi masa fatan Alkairi. Bayan ya iso gidan ne Alhaji Sani, ya had'a shida Ali` wanda yake cikin gidan A kan ya nuna masa 'barin da zai zauna. Suna cikin tafiya ne. Ali ya ce " Wannan gidan da ka shigo yana da hatsari sosai` za ka iya yi wa kowa laifi har da Alhaji ya bar ka amma kar ka ta'ba 'yarsa." Amar ya ce " Ai kuwa ni ma kar ta mini shirme, domin ni ina zane mutane mutuk'ar suka yi ba daidai. A gurin koyar da rawa." Ali ya ce "Nan shi ne gurin da za ka zauna ba kowa sai kai ka kad'ai. Can da kake gani sashina ne ni da matana, ba na shekararmu 25 da yin aure amma har yanzu Allah bai ba mu haihuwa ba. ( *ALI IRIN MUTANEN NAN NE MASU SHEGEN SURUTU* ) Amar ya ce " To Allah Ya ba ku yana zama a kan kujerar da ya gani a cikin d'akin." Mash Allah! Abubuwa suna tafiya daidai, inda soyayya tsakanin Amar da Basma ta girma kuma Babu wanda ya sani a cikin gidan . Kafin me afkuwa ta afku yanzu ne za a fara, Cakwakiyar yanzu ne komai zai fara faruwa. Yanzu za a shiga labarin asalin abin da zai faru.. 📝✍️ *TO FA! YANZU ZA A FARA RIKICIN ABUBUWA ZA SU FARA FARUWA , KUDE KU KASANCE DA NI* ~S REZA~ ~HAQIQA ALK'ALAMI YA FI TAKOBI ✍️📝~ The end fart 3️⃣ To be continue...✍️ *ALK'ALAMI S REZA..✍️* PLEASE COMMENT AND SHERE DON ALLAH 🙏🤣 *BY S REZA ON LOVE* [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CHAKWAKIYAR SOYAYA* NA S REZA ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... *SADAW KARWA GA* ```MAMAN ADNAN🥰 BADAN HALIN KIBA. WANNA NAKINE KEDA ADDNANM`DAKUMA ABBAN ADNAN🙏``` CA'KWAKIYAR SOYAYA PAGE ⚓️ 4⃣ ....... Amar. Zaune Yake akan Mashin d'insa Yana jiranta, Amma shiru yakai 30mt, Agurin yana jiran ta har yafara tinaninn komawa gida, Se jinyayi tace "Sorry Amar Walhi daddy ne yakeson jin ina zanje, Kuma mezan jeyi Shinefa na shirgamasa 'karya Shine yasa kaga nadad'e, Tana magar nar tana 'ko'karin hawa kan mashin din. Amar yace "to yanzu wani 'karya kikamasa Har yabarki. Basma tace "kai nifa ban iya garyaba, Rasa irin 'karyar dazan Masa ne, shine kawai nacemasa, Zamufita Yawon sha'katawa ne nidakai. Cikin wani mahaukacin Tsoro Amar yataka birkin mashin d'in, Yajuyo yana kallonta, Yace.. "Please Dagaske Haha kika cemasa? Basma cikin dariyar da take 'boyewa Tafito fili tace.. "eh mana Ai nacemaka ban iya 'karyaba Shine kawai nafad'a masa gaskiya, kuma bagashi ya barmuba, Tagarasa tana dariya🥰, Gani tayi yajuya kan mashin d'in Izuwa gida yana cewa "nide Walhi bazan je ba, Meyasa Zaki fad'a masa haka, kin San cewa in har yasan da wani abu a tsakanimu, to Walhi da matsala, Cikin dariya Basma tace "kai Walhi dawasa nake makafa nacemasa, zani gidan su Lubna nefa. Abin dayasa kaga nadad'e, Yace wai semuje Nida Little nefa, nikuma na'kiyarda , Se a lokacin Amar ya jidad'i, yace "kokefa amma Walhi har kin sa gabana yafara Dukan tara² Sun yi nisa Sosai Kafin Suka tsaya, wani gurine irin gurin da masoya sukezuwa, domin Jin dad'in Rayuwar su, Wata iska akeyi mekamada irin iskar damuna, Hadirine Yake haduwa, shine ake kad'a wata iska me shiga cikin Zuciya, Bayan Sun Samu Guri Sunzaunane, Amar yace.. "Basma cikin sanyin murya, tace "na'am. Yazuba mata ido Sannann yace.. "Basma Ha'kiga na yarda kina sona kuma Kina min Zonda ban yitinaninn shi daga garekiba, kin San meyasa nace muzo nagurin? Girgiza masa kaitayi alamar aa, yacigaba dacewa "Basma Ganinakeyi Soyaya nidake bazata yuba, Dubada ke y'ar waye a garinninnn, ina tsoran kar nagama yarda da sotayar ki daga baya a zo a samu Matsalar, Basma Walhi ina son ki, ina Kuma ina miki so banawasaba, Wani lokaci Senaji zuviyata! tana Cemin Basma bamatar aurena bace, Idan naduba irin Soyayyar da, Daddy Yake nunamiki, Walhi senaji kamar Baze yarda da Soyayyar muba, To shine yasa nakiraki nann domin in ji daga bakin ki. Shuruu Basma tayi Sannann Tace.. "Daddy na yana sona kuma kaima kasani, Dik abin da nakeso shine za'binsa, Sabodahaka kar kasa komai a ranka mutugar, Naje masa da zan ce koda wani irine to daddy, Yana yarda, Nide fatana Kari'kemin Amana. Amar yace.. "Inde nine karki damu kece kad'ai a Raina, Sonda nake miji bazan iya had'ashi da nawata ko nawaniba, Karma kisa Wannan azuciyar ki, Amar nakine ke kad'ai, Tagarasa maganar Yana ma'kemurya kamar wani ustaz. Dariya Sosai Basma tayi Sannann itama tayi irin muryar sa ta ce.. "Dama ban sa a rainaba bare kace in cire. Dariya dikkaninn susukayi, Sukaci gabada Hirarr Soyayyar su cikin Farin Ciki. Suna cikin hakane Aka tsinke da ruwan Sama, Ruwa ake yi sosai Hakan ne yasa Suka fito domin tafi gida acikin ruwan. Cek Suka Tsaya Suna kallon gurin da suka ijiye mashin d'in Naso, babu mashin din, Tashin Hankali, Basma tace.. "Ina mashin di'n? Yace.. "Anan gurin fa muka ijiye yana nunagurin da hannu. Hakade aka duba mashin Sama da 'kasa amma babu shi babu a lamarsa. Haka suka hagura Suna jira domin a gama ruwan Su samu abin hawa Sutafi, Acikin ruwan sukayi sa a Suka samu me keke napen Wanda Shima ruwan ne ya tarashi yana kan hanya. ______Daddy Tin dayaga an fara ruwa Amma bata dawoba Han kalin sa yatashi, Ya Kira number ta. Amma bata shiga, Yakasa sakewa, Damuwar sa Allah yasa Wannann ruwan be ta6ataba, Hakan neyasa yadawo harabar gidan yana kallon get d'in gida domin ganinn ko Zata shigo yan zu. Lokacin da Suka garaso Ruwan saman yaragu Se kad'an² Bayan sun salami me keke napeng, Amar ya ce.. Yanzu baza mushiga tare ba saboda Yanxuhaka Nasan Daddy yana nann yana jiran dawowar ki, Saboda haka kifara shiga zan biyoki daga baya. Basma tace.. "Amma dan Allah kar kaima ka dad'e awaje Saboda sanyi, please ina shiga kaima kashigo kaji, Tana maganar tana Rawar Sanyi, Cikin son yaga tashiga Domin tabar Rawar sanyin da takeyi yace.. "Ok no problem yanzu zanshigo, yana fad'a yana mata a lamar tatafi Tana tafiya tana kallon Sa. Tana shiga Daddy yataso da Sauri yana cewa.. Basma Daga ina kike haka? Me yasa baki Kira anzo an d'awkokiba? Cikin son Taga ambar maganar tace... Daddy Sanyi nakeji, haka yakamo hannunta, Har Cikin d'akinta ya kaita Sannan yace.. "Daga yau baza ki gara zuwa koinaba seda dreba, Kuma ita ita Lubna In bazatazo gidannan ba to Bazaki gara zuwa gidan Suba, Yacigaba da cewa kiyi wanka ki sake kayan jikin ki, Sannan kizo kisha mgn, Yakamo hannunn ta ya mannamata kiss 💋 Yace ina jiranki a parlor, yajuya yafita yana jin kamar Kar yagara barin ta tafita. Amar, Bayan ya shiga yayi wanka da ruwan zafi Sannann, ya 'kawnta yana tinann waye yasace masa mashin? Agarin ya Bayan Kuma makullun mashin d'in yana gurina, To koma waye Wannann bibiyata yakeyi, kuma sena gano waye, Dawan nann tinanin yayi barci Basma, Bayan tayi dik abin da Daddy yace, Tafito Parlon Tasameshi yana Zaune, da a lamar ita Yake jira, Tana zuwa ya ce my daughter Ina Kikaja? Hankalina be 'kawnta da Wannann fitar da kikayiba. Ta ce.. Daddy Gidan Su Lubna Naje fa, Haba daddy na ai kasan bana qarya , Toma ni inama zan je, please nide daddy Allah babu inda Naje, Tagara tana kukan Sha'ko6a. Daddy da Izuwa yanzu yagama yarda da ita, Domin kuwa yasan bata masa 'karya yace.. "Sorry my daughter ya isa kin ji , Segashi ya koma rarrashin ta, Hakade har sukaci abin ci sannann yabata mgn tasha, Yace taje ta 'kawnta tahuta Segobe. ______WASHE GARI Tin jiya da daddare Takira Lubna A waya Tashir ya mata garya akan tazo gidan su Tace Zasuje school Domin kar'bar wasu takardu, hakan kuwa a kayi Bayan Daddy yagamajin Dik abin da tace, "Sannan yakira Basma yatam bayeta gaskiya ne? Da Sauri tace "eh daddy tin jiya Naso in gaya maka amma na ban ta, Daddy yace" Tom amma fa tare da dreba Zakutafi, Basma bataso hakaba amma bayanda Tayi suka hagura. Tafiya Sukeyi Kanta yana ga wayan ta Se danne² takeyi abun ta, inda itakuma Lubna take ta zuba Surutu, Kamar an ce tad'ago Kanta Tana d'agowa idonta yasauga akan wasu Samari su biyu A kan mashid'in Amar, Kar tasan su amma amma ta manta in da tata6a ganinn su. Magana tayiwa dreban Akan ya tsaya Ta sauqa Ai kuwa yanemi 'kuri ya tsaya Lubana tana cewa"lafiyakuwa? Basma tace.."zaku iya jirana kokuma kuje zan sameku a cen, kokuma de, Zamuyi waya, Tana bad'in haka tafita daga motar Me mashin ta samu tanuna masa mutanenn da zedingabi a baya har in da suka tsaya, me mashin zeyi mgn tace.. Kar kadamu Zan baka komanawane jin hakanne yasa yayi shiru. Waya ta ciro tskira Amar amma no Amsar, Shikuwa me mashin 'Kara bin mutanann da tanuna masa yakeyi. _____SMAR Zaune Suke Shida abokin sa wato Sadam Yana gaya masa cewa an sace masa mashin Kuma shide baya tinaninn kowa, "amma abin da mamaki, in ji Sadam Bayan ya gama jin dik abin da yace.Amar Ina zuwa yace yana barin gurin, Yabar wayar sa a gurin Bayan ya tafine Kiran Basma ya shigo waryar har sau uku amma Sadam be d'aukaba, akira na hud'un ne , yayi dede da ya iso guri da Sauri yad'aga domin kuwa katin waya Yaje siyiwa domin kiranta. Amar naga mashin d'inka please kazo yan zu gashi ma ina bin su a baya dan wkayi Sauri, Abin da tace kenann lokacin da Taji an d'aga kiran, Cikin mamaki yace.. "Basma are you ok? "Tace please I'm ok dan Allah kazo dawuri, yace kina ta ina yanzu? Yagaya masa inda Suke sannan ya kashe wayar, Ko mgn beyiwa Sadamba Shima yafito yanemi me mashin Suka nufo gurin A wani gurin Samarin Suka Tsaya, Da a lamar gurin ogansu sukazo. Tsayawa sukayi da Nasu mashin d'in Suna kallon su. Setaji ogan Nasu yana cemusu.. "Meya baku cire number ba mashin d'in ba? Amma kun San Wannann gangancine, Kuma kun biyo cikin gari Dashi bakuda Han kali ne? Waya kuje gurin masta yan zu yacire wannan lambar, yana nuna musu da hannu a kan su hau mashin d'in sutafi. Dik abin da Suke Fad'a Basma tana jin su, Dataga alamar Tafiya zasuyi kuma gashi Amar bezoba Se kawai Tanufi gurin su. Tana zuwa tace.. "Barkan ku wannan Mashin d'in mune, Sekuma tayi shiru Don ganinn irin kallon da sukeyi mata , ogan Nasu ne yataso tana nufota yana cewa "ina lasisin sa Yake? Ina takardun sasuke? Basma tace.. Kamar yaya? Ogan yace.. "Idan kika nun amin ai se mubaki mashin d'in, d'aya daga cikin yaran sa yace.. "Ke megida yana Tambayar ki, kibashi amsa mana? Oga se'kara nufota yakeyi itakuma tana jabaya, Yana wani lashe baki yana cewa.. Haba 'yan mata kiyi magana mana, ya kai hannu da niyar ta6a bakinta yaji an ri'ke hannunn, Kafin yayi magana, Amar yace.. Dan Allah kuyi hagu ri, yaja hannunn basma Suna tafiya yana cemata kar kidamu mashin d'ina ze fito, Basma tace "baga mashin d'in ba allha muje mu kar'ba yana janta tana Wannann maganar Sukuma ogan Nasu yana ganinn Amar yatafi da ita yakecemasa, kai yaro ai da kabar ta mun d'an mayar da yawunmu irin wannan tso'kekiyar yarin ya, Daga Gani kaima kana 'kawsar raban kako? Kai anyama kuwa zata iya, 'DAUKAR nawyin mutum 4 Kaga in Muka Mure kaima seka 'kawshi sauran, ammafa gaskiya, Kai bakada tsuciya in de har bakazo mun 'kawshi ganimaba, yana fad'in haka suka 'kawshe da wani irin dariya Amar dik abin da sukecewa acikin kunnenn sa, Dikda suma d'in sun yine domin yaji. Cek ya tsaya, domin jin abin da Sukace na 'karshen juyowa yayi yana kallon yan da Suke faman dariya, ya kalli Basma itama shi take kallo. Ya cire a gogon Dayake a ma'kale a hannunsa ya bata yace bana son ya 'kar ye, kijirani.... ✍️📝💪 **Tofa 🤔😃😃 inaga* *Amar Ze gama dasu 💪* * The end fart 4️⃣ To be continue... *HAQIGA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️📝* *PLEASE COMMENT AND SHER DAN ALLAH 🙏🥰,* *NA KU HAR KULLUM S* ~REZA~ [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA* *Story and writers...* ✍️ *S REZA* ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... *I'M BACK AGAIN, PLEASE MY FANS SORRY FOR AVERTING 🙏❤* *I* *LOVE ALL MY FAN'S* 🥰🥰 CAKWA KIYAR SOYAYYA❤ PAGE 7⃣ ...........Basma Tashi tayi tanufi gurin Daddy domin Tasanar dashi komai, Amma kash!! Tayi rashin sa'a domin tunda sassafe yabar gidan bata sani ba. Amar gida yaje Sukayi sallama da Abban sa bayan yamasa fad'a akan yakula da kansa kar ya biyewa abokan banza, Dade sauran su. san nan yanufo gidan su Basma domin yin sallama da Alhaji Sani. Misalin Qarfebiyu na rana Amar yakaraso gidan, Dede lokacin Daddy yana 'ko'karin fita shi da Ali. Ganin Amar d'auke da A'kwati ne yasa suka tsaya. Bayan ya'karaso gurinsu ne yasunkuya har kasa ya gaishe su, San nan Ya Sanarwa da Alhaji Sani Abinda ketafe dashi, Wato yasamu aiki zetafi. "Allhaji Sani yataya shi murna had'e da fatan nasara, San nan ya masa ihi'sani Suka shiga mota suga bar gidan. Basma Duk abinda Sukeyi a kan idonta har lokacin da Amar yasa k'afa yabar gidan Taso ace sunyi sallama amma gashi ya tafi ko kallon gurin da nake ma beyiba, Har ya hau mashin d'in da Sadam ya kawo shi a kai yatafi, Fashe watayi da wani irin kuka Taji Aranta !Anya kuwa Amar yana santa? ahaka takoma d'aki taci kukan ta Iya san ranta. *_________WASHE GARI* Dawani irin matsanan cin ciwon kai ta tashi, Takasa walwala kana gallonta kasan akwai abinda yake damun ta, Daddy ne da kansa yaje har d'akinta yataso ta. Babu irin tambayar da beyi mata ba a kan abinda ya ke damun ta amma ta ce " Babu komai, Haka daddy ya hakura badan ya yarda ba. Tun da suka gama breakfast tashiga d'akin ta taci gaba daga in da ta tsaya, Ta manta da cewa yau ne Za a zo maganar sa ranar ta. Wasu motoci ne guda biyu Suka shigo harabar gidan, Motoci ne masu d'auke da Tam barin wani abu wanda nide bangane menene ba Bayan sun yi parking ne dukkanin su suka fito a tare su hud'u ne maza ukku se mace guda d'aya. Kana kallon su kasan Sun jik'u da naira, Ga wani irin Kama da sukeyi dukkanin su. Banyan sun shiga cikin parlon ne A ka tar6esu da abubuwan marmari, Nan take suka ci abinda zasu iya ci, Bayan Angama cin komai ne Allhaji Sani ya ce" Tom masha Allah daya kawo mu wan nan rana , Duk dacewa tun zuwanku na farko muka gama yin duk abinda yada ce, To yanzu Allah yakawo mu yau da muke fatan Cika muku alqawarin da muka d'auka, wani abokin Alhaji sani da ya gayyato ne ya ce" Tom mash Allah Sabida haka muna jira daga gareku Shin kun shirya akan base mun saka bikin da nisaba ko kuma dai kuna da d'an gyare gyaren dazakuyi? Dasauri macen Cikin su tace"Aa bamu da wani abu da yarage, mu ku muke jira san nan kuma bamaso a saka ranar da nisa. Haka kuwa akayi bayan sun bada sadaki ne aka saka ranar biki a kan wata biyu masu zuwa Abisa yarjejeniyar b'anga rori guda biyu, a haka Suka ci gaba da wani hirar akan kasuwanci . Misalin hud'u Suka kama hanya suka tafi da fad'in cewa zasu turo yaran nasu yazo domin su fahimci juna kafin lokacin. *___________BASMA* Duk abinda a keyi bata sani ba tana sama d'akin daddy tana barcin dole, wanda bayan tasha kuka ne ya d'auketa.Jitayi ana tashinta amma kamar a mafarki ganin abin kamar azahiri ne yasa ta bud'e idonta` a hankali wanda suka yi jazur tasauke su a kan Lubna. Ganin itane yasa ta tashi da sauri tarungumeta tagara fashewa da kuka, ita kan ta Lubna ta tausaya mata sosai. Bata rarasheta ba barin ta tayi seda tayi me isar ta. San nan basma ta ce" *LUBNA* yatafi wallahi yatafi ya bar ni, yazan yi? Duk cikin kuka take wan nan Maganar. *LUBNA* Takamo hannunta ta ce" please dan Allah kidena kuka haka ai zedawo Ba tafiya yayi ba yana sane dake Kuma ai yagaya miki shekara daya fa kawai zeyi yadawo please kibar wannann kukan kin ji. *LUBNA* kallon ta takeyi tana tausaya mata` ya zanyi in sanar mata da cewa an saka ranar ta da wani? Wanin ma bamusan waye ba, anya kuwa *BASMA* zata iya jure jin abinda zataji daga bakina?,Tambayar da *BASMA* ta watso mata ne yasa hanjin cikinta juyawa "Ta ce..sun zo an saka ranar ko? Sanar da ni cewa an saka ranata kar ki 6oyemin ko mai *LUBNA*, Da gaske abin da nagani afuskar ki gaskiya ne Shin daddy ya bayar dani? Tini *LUBNA*tarasa abin da zata ce mata Se gyad'a mata kai kawai ta keyi kamar qadan gariya. Nan take *BASMA* Tazube agurin tamkar babu numfashi atare da ita, ita kuwa *LUBNA* Metake in banda ihu da kiran sunann *BASMA. BASMA BASMA* Amma ina ko motsi batayi ....✍️📝 WAN NAN SHINE MAFARIN QADDAARAR SU GABADAYAN SU , shin kokun San waye wan da a ka saka musu Rana da Basma? shin Kun San cewa Kamal Yana Raye Kuma yace se ya au reta? KU kasan ce da S REZA..✍️ *KUYI HAKURI* *ABISA JINA SHIRU KAWNA 2, ABUBUWA NE SUKA* *MIN* *YAWA DA FATAN ZAKU MIN UZURI* 🙏🙏🙏 The end of part 7 To be continue..✍️ *PLEASE COMMENT AND SHERE DAN ALLAH* 🙏🥰 *BY S REZA* [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKAWKIYAR SOYAYYA💋❤💘 Writer by. S REZA.. ✍️ ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... I love all my fans😍 Ca kwakiyar soyayya❤ PAGE 6⃣ ..........Tafiya yake yana tinanin abin yi, Shin idan suka gudu da ita su kaje su kayi aure to shi kuma karatun safa? Kuma gaskiya ina son ta ina sonta, bazan iya jure wani ya aureta ba mutu'kar ina raye. Horn yaji ana masa tabaya Har sau huɗu amma beji ba se a nabiyar ɗin. Ya na juyowa su kayi ido huɗu da Ali, da mamaki Ali yake kallon sa yace.. "ina kake kallo haka ana tayi maka horn amma shiru? Amamar yace .."walhi ban jiba Sorry. Allhaji sani da yake cikin mota yaga an tsaya kuma yasan halin Ali da surutu, hakan ne yasa ya leƙo yana yiwa Ali magana akan suzo su tafi. Shikuwa Ali har ya fara yiwa Amar surutu in da yake cema sa "tare muke da abban Basma, in gida z aka kazo mu 'karasa" Ammar yace .."aa nagode nima yanzu zan ƙaraso." Ali ya na shiga motar Allhaji Sani yace .."kaida waye a waje?" Ali yace.. "nida Ammar ne yaran da ya ke ko yawa Basma rawa." Alhaji Sani yace "gida zeje? "Eh waigida zeje in ji Ali, Alhaji Sani yace .."to kace masa ya shigo muta fi ai kuwa haka a kayi da kamar yayi ƙarya yace ba gidan zeje ba kuma seya fasa ya shiga suka tafi. Sun shigo layin unguwar su kenan suka hango taran mutane a wani 'kofar gida, dama kuma megidan abokin Allji Sani ne, kasan cewar babu ta in da motar tasu za tabi tahuce ne yasa suka tsaya, dikkanin su fitowa Sukayi daga cikin motar domin jin abin da yake faruwa. Suna ƙarasowa sukaji , wani ɗan saurayi agurin yana cewa .."Wai me kake nufine nifa ban ganeba? "Alhji Sani Yana zuwa gurun abokin nasa yaje yace.." mlm Bala mayake faruwane? Wan da a kakira da mlm Bala ya ce "wai wannan yaran ne yace yana son binta wato ƴar sa kenan, yaci gaba da cewa.. Wai in be aureta ba. Kafin ya ƙarasa Saurayin ya tare Shi da cewa.. "Ina son Auran ta kuma itama tana ƙau nata ku tam baye ta kuji yana nuna gurin da yarin yar da a ka kira da binta take. Alhaji Sani cikin Sanyin murya yacee..."Yaro na yin soyayy ba kuskure bane, amma kuma yin aure bada izininn uba ba wan'nan shine kuskure, ya ciga bada cewa Saurayin , shin mene ne aikin ka? Yatam baye shi, Saurayin yace .. "Na kammala Degree, ya bashi amsa a ta'kaice. Alhaji sani yace.. Wato Degree, To da Degree zaka ciyar da ita? Saura yin yace ''yan laɓai idan na samu ai kin base komai ya tafi de de ba." Alhaji Sani yace "Shin kai baka yi tunanin yanda a kayi a karene ta har takawo hakaba? A makaran ta me tsada a ka sa mar mata da iliminta, dik mutumin da ze iya haka to yasan yanda ze ta fiyar da gidan sa. Shin bama wan'nan ba kai yanzu a haka zaka iya tafiyar tan da iyali bakada ai kin yi , yaka mata kayi tinani dan saurayi. kafin Saurayin yayi magana sejin akayi yarinyar tace.."to ai ni ma ina son sa kuma mu bama bu'kar tar dik wanan'n abubuwa" cikin mamaki mutanann gurin suke kallon ta , Sannann alhaji Sani yace.. "Yan zune ki ke ganin haka yarinya, kar ki biyewa saurayi Kibar maganar iya yanki domin in hakan ya kasan ce babu wata riba da zaki samu. Saurayin yace wa Alhaji Sani "bama bu'katar wani 'boye-'boye kafito fili kafad'a mana abin da kake nufi? Cikin jin haushin yaran Alhaji Sani ya ce... Kari fe min bakin ka na shirme haka, waye kai a ina kake dik wan'nan ba shine abin da muke soba. Idan uba ze ba da auran 'yar sa gayaro to ya tabbatar yana da wata madafa domin komai ya tafi cikin nutsuwa. Yaci gaba da cewa Soyaya ai kowani matashi ma ai yana yin ta, amma in baze iya d'au ke d'awai niyar yarin ya ba ai ya zama a banza. Gaba d'aya dik saboda irin kune ya sa zama nin na ya lalace. Ya cigaba da cewa... Mu idan zamu aurar da yaran mu muna so musamu wa 'yen da zasu iya d'au ke damuwar sune bawa 'yenda daga 'kwana biyu zasu nad'e hannun su suce ya zan yiba, kai ma kuma ina ganin kana cikin su saboda haka kabar nan gurin. Yana nuna wa saurayin hanya. "Cikin rashin Kunya sau rayin yace "ba damuwa nina san abin da zanyi ai." Alhaji Sani "yace koma meza kayi kayi yaran ya ta fi yana surutan sa. San'nan ya dawo gurin baban yarinyar yace... "Kar kada mufa haka yaran zamanin na suke, mlm sani wato baban yarinyar ya ce.."badamuwa nagode sosai. Sannan suka koma motan dik su ukun suka tafi. Dik abin nan da yafaru a'idon ammar, Haqik'a Alhaji Sani dik magan ga nun sa gaski yane to yan zu me kenan hakan yake nufi? Maganar da Alhaji sani ya yine ya sa ya dawo daga tinanin nin sa. Kun ga irin samarin zamanin ko , se ka gama shan wahalar ka da yarin yar ka wani cen yazo ko aikin yi babu, wani ma zaman banza ya keyi wanima dan shaye-shaye ne, se yazo yasa yarinya ta fara sonsa , kuma kana aura masa kwana 2 zece ya gaji. Har suka 'kara so gida abin daya ke ta fad'a kenan. In da shima Ali dama sarkin surutu ne suka cigaba. Bayan sun 'kara so gidane tin kafin Kowa ya fito Ammar ya fito ya nufi sa shin sa da yake cikin gidan kana ganin sa kasan wani abu na damun shi. Ze shige d'aki kenan yaji maganar ta. Juyo wa yayi ta ce.."kagama shiryawa ko? Domin gobe da Asuba zamu tafi" Kallonta yayi da'kyar ya 'ka 'karo murmushi ya yi mata , Sannan ya d'aga mata kai alamar eh ya gama shirin be jira ta 'kara cewa komai ba ya shige d'akin nasa. Basma ganin kamar dawa ni abu da yake damun sa yasa taji babu dad'i, amma kuma tinda de ya amin ce zasu yi aure to ai shi kenan, bayan auran zata mantar dashi dik wata damuwar sa, da wan'nan tina nin ta koma d'aki tana jiran dare yayi ta fara shirya kayan ta. Ammar yana shiga d'aki kan kujera ya zauna yari' ke kansa yana jin yana juya masa. Tashi yayi Domin jin 'kiraye² sallar magariba. Bayan yayi sallar ne ya zauna shiru yana tinani, kafin ya 'kira wayar Sadam yace "yana so su had'u." Basma 12:00 Na dare dede. Take Shirya kayan ta, Gashi tana 'kiran number sa yaki d'agawa. Ta 'kirashi ya kai Sau 20 amma no amsar. Kuma bata dena 'kira ba. _________Ammar Zau ne yake yana kallon 'Kiran wayar ta amma ya kasa d'a gawa. magan ganun d'azu suna dawo masa cikin kansa!mumu na bu'katar musamu wanda ze iya d'aukar d'awai niyar yaran mune ba wanda daga kwana biyu zena d'e hannu yace yazan yi ba ko kuma ya dun'kule hannu ya kwanta ba. Wan'nan magan ganun se suke masa yawo, San'nan ya 'kara tinawa da maganar Abban sa. Acen garin *ABUJA* . Na turawa da wani professor takar dun ka kuma gaskiya yayi mamaki domin takar dun sun burgeshi yanzu haka ya bu'kaci ka tafi *ABUJA* Yarasa abin yi wanne zebi ina lillahai wa ina ilaihi raju'un abin da yake cewa kenan. Basma Ganin ya'ki amsa 'kira yasa ta tura masa text message kamar haka ( *Nagama shiryawa Allah yasa kaima haka, kai nake* *jira)*. Ammar yana zaune ya rasa mafita yaga Sa'ko ya shigo, kobe duba ba yasan itace , yana gama karan tawa shima shima ya mayar mata. Basma tana jin sa'ko ya shigo seda tayi murmishi kafin ta bud'e, amma abin da ta gani ne yasa gaban ta fad'uwa ta zaro ido tana karan tawa. Lokaci d'aya idon ta ya cika da hawaye. Dik kanin su babu wanda ya iya rin tsawa domin kuwa kowa da abin da yake damun sa. Misalin Qarfe 7 na safiya, Basma ta saci hanya ta nufo d'akin Ammar kasan cewar 'yan gidan basa tashi she wajan tara. Tana son taje taji shin abin da ya rubuto ma ta gaske ne ko kuma wasa yake mata? Sallama tayi aka bata izinin shiga kafin ta shige ciki. Ammar dama yasan da cewa dole se tazo, Kuma dama shima yana bu 'katar zuwan nata, domin su san abin yi. Guri tasa mu ta zauna tana bin shi da kallo Fuskar ta dik a kumbure , alamar tasha kuka. Kasa yin maga na tayi sebin sa da ido takeyi. Ammar shima de kana kallon idonsa kasan beyi barciba jiya, amma yana had'a ido daita yaji ya tausaya mata, ta sowa yayi yazo kusa da ita daniyar yayi mata magana, Tariga shi da cewa... Haka ne yanzu zaka tafi *ABUJA* Kenan? zaka je domin kayi degree na biyu a can bayan she kara d'aya kuma se ka dawo kayi aure? Shin da gaske ne?" Tana hawaye take tambayar sa. Ammar yace.."yaka mata kema ki gane , ina yine domin abin da gaba zata haifar mana" cikin kukan da ya 'kwace mata tace..."kawai de kace kana yin abin da gaba zata haifar maka, Shin ma wai in ka dawo ni ina ina wan'nan lokacin?" "Ammar yawa ce...''Haba Basma shekara 1 ne fa kawai." Cikin kuka taqara cewa "to acikin wan'nan she karar idan a kamin aurefa? Amamar yace... "Ai kafin ai miki auran zan d'auke ki mugudu, kede abin dana keso da ke shine kifahim ceni" ya kama hannun ta ya ce.. "Basma dan Allah shekara d'aya kawai." "itama cikin kuka tace .. "Ammar kaki ka fahimce ni Aure! Aure!! Aure!!! fa nace maka za a zo nema gidan mu kuma gobe, kuma sun ce dawuri za a yi bikin shin meka keso inyi? nace kazo mugudu ka 'ki pls dan Allah" Tana rok'on sa. Ammar yace "kema dan allah "Kafin ya 'karasa ta fisge hannun ta tabar d'akin tana kuka. "Basma Basma Basma." Amma ina ta tafi. Ko juyo wa ba tayi ba. Kan shi ya ri'ke yana jin yana sara masa, yace... "Shin meya sa Basma baxa ta fahimce niba" Nan take ya fara had'a kayan sa domin barin gida, Seda ya je ya gama sallama da banan sa kafin ya dawo yayi sallama da Daddy wato abban Basma. ________Basma har ta shiga d'akin ta babu wanda ya ganta kasan cewar babu wanda ya tashi har yanzu. 'Dakin ta ta shiga taci gaba da rusar kukun ta, jita keyi kamar taje ta samu Daddy tace masa ita Ammar ta keso, amma tasan hakan ba me yuwa bana ,tasan Daddy baze amin ceba! wani abun ma wai yau ne ze tafi!anya makuwa Ammar yana sona? Tambayar da tayi wa kan ta kenan. Eh Amar yana sonki sosai kuwa. taji wata zuciya ta bata amsa. Wata zuciyar ce ta ce ya ka mata kije kisamu Daddy ki fad'a masa cewa ke gawanda ki keso, kin san yana sonki ,kuma dik abin da kike so shina yana so kinga kuwa ze yarda da ke. Shiru tayi tana tinanin maganar zuciyar ta ta, Kawai se ta tashi tanufi.....✍️📝 *DOMIN GANIN INA ZATA JE KU KASAN CE DA S REZA,YAN ZU A KAFARA* HAQIQA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️ the end of part 6️⃣ To be continue...✍️ ALQALAMI S REZA...✍️ PLEASE COMMENT AND SHER DAN ALLAH 🙏 BY S REZA.✍🏼 [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKWAKIYAR SOYAYYA ♥️ Story and written...✍️ S REZA ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 _Dama na cemuku wan nann labarin se kun bini a han kali domin labarin yanada d'an har GITSI, wannann Page d'in_ na kune masoyan _gas Kiya, in Kun karan ta kar kuyi kuka domin kuwa yanada tarin abin tau_ _sayi_ ,🥰♥️ Sekun zo, بسم الله الرحمن الرحيم... Cakwakiya Soyayya💔🥰 PAGE 8️⃣ …...... **CIGABAN LABARIN* .....Sai me ya faru sanar dani cewa duk abin da naji ana fad'a a kan ki 'karyane pls fad'amin? yana tambayar ta. Ta ce..Amar ba wai na zo gurin nan bane domin in zauna tare da kai, ka san me yasa nazo gurin ka? Bai iya yin magana ba sai kawai ya girgiza mata kai a lamar a'a, Ta ce.. "Jiya professor Salisu ya kirani ya sanar Dani duk halin da kake ciki". *__________TUNANI* Slm nine professor Salis Nake Magana Allah yasa ina magana da Basma Sani ne? eh yallabai nice. Ai nagane ka ya kake ya school? "Lfy lau Basma Shin kokin san nine Mahaifin Amar? "Eh yallabai ya fad'amin na sani Dama ina son in tambaye ka ya Amar d'in yake Yanzu nasan ya nada babban matsayi a aikin sa ko? "Aa basma Amar a halin yanzu ma baya cikin hankalin sa tun daga lokacin da yasamu labarin kin yi aure shikenan komai da komai na shi ya lalace. Kullum yana cikin tunanin ki, Ya ki yayi aiki yana cikin wani hali kullum zancen sa Basma²,Shi ne yasa na samo number ki domin dan Allah ina so kije kiyi masa magana ko Allah zai sa ya dawo cikin hankalin sa.. Ya koma rayuwar shaye-shaye, Yace min yana so zaku had'u tun ba yanzu ba amma nace masa ai hakan be dace ba, To tun daga wannan maganar har yanzu bana samun shi a waya, A halin yanzu ko office baya zuwa, Shi ne yasa na yanke shawara bari in kiraki ko Allah zai sa yaji maganar ki, Dan Allah ki taimakawa wannann yaron nawa, Dan Allah Basma kin ga yanzu komai yana hannun ki, Ya karasa maganar yana kuka. Ita ma da take sauraron maganar kukan takeyi har bata san lokacin da ya kashe wayar ba. Basma Sai da tasha kuka da jin wannann maganar dama A she Amar ba mantawa da ita yiyi ba! To ka ji yadda mukayi dashi, Wannan shine yasa nazo gurin ka. "Amar ya ce...Hakan yana nufin kin tausaya min ne ma kikazo ko? Basma Cikin kuka ta ce.. Ba haka bane Amar.. Ni na yi tunanin kawo yanzu kaman ta da duk wasu lamuranane Amar to ba haka ba..kin d'auka wai ban sani bane A 'kwai yan mata da yawo da suke aure wasu da lilin iyayen su wasu kuma dalilin Al'umar da suke tare dasu, Ya nunata da hannu ya ce.. To hakan bai da ce da ke ba to Domin ni d'in nan ina cikin rayuwar ki, kuma ni zan ji da komai. Cikin wani irin kuka Basma ta ce.. "Ba haka bane Amar, ni yanzu ina cikin farin ciki tare da mijina, Ban san me zan ce maka kagane bane, A halin yanzu ya nuna min soyayya me tarin yawan gaske wannan yasa na fara mantawa da kai...da sauri tsayar da ita wajen d'aga mata hannu, yazo kusa da ita ya kamu hannun ta cikin tsananin bacin rai ya ce.. Yanzu Basma kece kike fad'ar wannann maganar da kan ki? Ki kalli cikin idona ki mai-maita abin da kikace in kin isa, ki kallan nace, ki kalli cikin idona in kin isa, cikin ihuu!! Ya 'kara mai mai tawa, Shin Basma bani bane a cikin zuciyar da har zaki ce wai kin fara mantawa dani? Basma ta ce.. Dan Alla. Kafin ta karasa ya ce.. To me yasa baza ki kalli cikin idona ba, Saboda kar ki fara min hawaye ko? Ta ce.. Aa ni ba haka bane, to tun da na gane me yasa ka kasa fahimta ta?, Cikin ihu Amar ya ce.. "To meyasa kikazo? Wai dan na sha giya ina ruwan ki da rayuwa ta, In na rasa aikina ma ina ruwan ki? Wai ma in na mutu ma ina ruwan ki? "Basma ita ma cikin kukan ta yaki 'karewa ta ce.. "Ai Saboda hakan kar ta faru ai nazo, a wancen lokacin na yanke abin da zakayi yafi maka muhimmanci a kan nace se ka aure ni, dama na fad'a maka cewa ba lallai a bar ni in kai har lokacin da zaka dawo ba, amma kaki ka saurareni ka nuna kafi son ai kin ka, in na kira ka a waya sai dai ka din ga cemin kar na damu kana kammalawa za muyi aure, ka ki ka tsaya ka saurareni, ni kuma ka bar ni da ciwon son ka nayi kuka har babu a dadi, kuma har kawo yanzu babu wan da yasan da soyayar mu a gidan mu, nayi tunanin ka man ta da nine shi yasa naje nayi aurena .. Amma gashi abin da nayi tsammanin zaka zama ga shi duk ka bata, Haka d'in bazan iya jurewa ba. Amar ya kalle ta cikin ha wayen da suka jika masa fuska ya ce.. "Bani da wani abu da yafiki a gurina Basma, indai da gaske kina cikin farin ciki a can in da kike to baki da bu'ka tar ki zo in da nake wai dan nayi farin ciki, koma menene ze faru ni na kasance naki kuma zan zauna zaman jiranki. Yana gama fad'in haka ya tashi ya bar gurin cikin 6acin rai. Basma ta ce.. Amar Amar Amar cikin kuka, amma ina ko juyowa bai yi ba,sai da tasha kukan ta a gurin kafin ta mi'ke tsaye ta nufi motar da tazo da ita ta tafi gida, Tun a han ya take tunanin abubuwa da yawa har ga Allah har ta fara mantawa da Amar a rayuwar Acikin she kara 1 da rabi kawai, kulawar da Abdul yake bani yasa na man ta da shi, to amma yanzu me yake shirin faruwa. ina da auran wani fa kuma ban tambaye shi ba naje gurin wani Astagfurullah! ta furta a fili daidai lokacin da maigadi ya bud'e mata get d'in gidan ta shiga. Zaune yake yana aiki acikin 💻 laptop din sa Amma hankalin sa yana kan ta, tun jiya ya lura da cewa kamar wani abu yana damun ta, Amma yace bari ya gani Ko daisaboda abin da yace mata ne jiya,kuma gashi ya ga har yannzu da a lamar damuwa a tare da ita, hakan ne yasa ya bar abin da ya keyi domin yaje yaji damu war da take damun matar tasa. Ya zauna kusa da ita ya jawo ta jikin sa ya ce.. Basma me ye yake damun ki? Tayi shiru tana jin sa har ya kara maimai ta tambayar sa a karo na uku, Basma tunani ta keyi Akan lokacin da zasuyi aure da shi tun kafin suyi aure take bashi labarin Amar amma bai taba cema ta wani abu ba, kafin ta amince dashi ma, sa take cema sa, Ni zuciyata Amar take so baza ta taba son wani d'a namiji a duniya ba sai shi, Amma be taba damuwa ba, kai a kwai wani lokaci ma bayan sun yi aure ta ce masa, Abdul Wai dan Allah har yanzu baka sanin da Amar ya shiga ba? a wannan lokacin ma sai ya ce mata ni ai ban san shi ba, Gaskiya samun miji irin Abdul a wannan zamanin gaskiya yana wahala, Shin yanzu taya zata iya kallon idon sa tace masa gurin Amar taje, Shin in tayi haka ta kyauta kuwa, shin Abdul ba zai zarge ta ba.Tam bayar da ya 'kara mata ne yasa ta dawo daga tuna nin da ta tafi, Basma gaya min abin da yake damun ki ko dai a kan maganar jiya ne? In dai haka ne to kar ki damu zan sake miki ita, ba dai mota bane kar ki damu, yana maganar yana mata murmushi domin ganin ya cire ta daga damuwar. Amma jin abin da ya fito da ga bakin ta ne yasa murmushin fuskar sa 'bacewa 'bat, a lokaci d'aya fuskar sa ta canja izuwa damuwa. "Jiya naje mun yi magana da Amar, Abin da tace kenan kan ta a 'kasa. Jin yayi shiru ne yasa ta d'ago kan ta ta kalleshi domin ganin wani irin Akswon ya d'au ka,sai dai abin mamaki shima ita ya ke kallo, kafin tayi magana ya ce "Me kikace? "Ba ta mai maita ba ta cigaba da maga kamar haka, kuma ido cikin ido take maganar babu a lamar 'karya.. "A lokacin da nake maka maganar amar, bayan auran mu ka bamu gudun mawa sosai, Amma gaskiya bazan iya man tawa da shi ba, Soyayya ba abin da zaka fara shi bane kuma kadai na a lokacin da ka ke so, ahalin yanzu na koyi komai da komai ne daga gareka, Amma Amar yana ganin ina zaune da kai ne a matsayin haka kawai, Saboda ni duk ya 'bata duk kanin rayuwar sa, har yanzu yana ganin ina 'kaunar sa ne, ni kai na ina jin wani iri, Ni a nan ina cikin farin ciki tare da kai Abdul bai kamata a ce in gaya masa haka ba, Shi kan sa idan yagani zai fahimci haka d'in"tayi shiru tana zubar da hawayen da bata san dalilin zubowar su ba, sannan ta fad'i maganar da ta karasa g rugurguza duk kannin sauran nutsuwar Abdul, Ta ce... Abdul ina ganinn mu kira Amar cikin wannan Gidan namu domin in yaga rayuwar mu zai fahimci ba haka abin yake ba, kaga daga nan sai ya zabi in da zai yi rayuwar sa, Sai kuma tayi shiru tana kallon sa, sai a lokacin ta tuna da cewa ai hakan be dace ba, Sannan ta ce .. Amma fa hakan Sai idan ka yarda. Yayi shiru Yana tunanin wani Abu ya ce...✍️📝 *SHIN KUNA GANIN ABDUL ZE AMINCE MATAR SA TA KAWO TSOHUN SAURAYIN TA CIKIN GIDAN SU DOMIN SU SAKE MASA RAYU WA?SHIN WAI INA KAMAL NE? KU KASAN CE DA S REZA ✍️* MASHA ALLAH. HAKIQA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️ The end of part 8️⃣ To be continue..✍️ Please comment and Sher 🙏🥰 *By S REZA* [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKAWKIYAR SOYAYYA 💔🥰 *Story and writers..✍️* *S REZA* ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* *No Editing* 🙏 بسم الله الرحمن الرحيم... *Giayra ko tsokaci ko Sha wara ko kusku re, Ina maraba da su, han ya a bud'e take. 07063571070 by S REZA* *Cakawkiyar Soyayya* PAGE 9️⃣ ........... *Abdul* Kallon ta ya keyi yayi shiru alamar yana tinaninn wani abu, cen zuwa wani loci ya ce.. Basma yaki ra sunan ta, itama kallon sa take tana son taji me zece. "Idan de han kan ze iya gyara masa rayu war sa to kice masa yazo.Yasa ke run gumota jikin sa ya ce.. Domin farin cikin ki shine nawa Basma. jin abin da yace ne yasa ta 'kara shi gewa jikin sa cikin kukan farin ciki ta ce.. Ina son ka Abdul ina kaw nar ka Abdul. Shikuma yana shafa bayan ta yana cewa "kar kidamu farin cikin ki shine nawa. *_____________AMAR* Tin da ya tafi ya bar ta a gurin gida ya koma cikin ɓacin rai, Ya jawo kayan shaye-shaye sa ya din ga af kawa, ya kai a 'kalla awa 1 yana korawa daga bisani ya zar ce da bar ci. Awan sa 4 yana barci kafin ya tashi, wanka yayi kafin yazo ya zauna a gefen gado yana tinanin dik abin da yafaru tsakaninn sa da Basma 'dazu, Aure aure aure ko to walhi koma waye ya aure ta bazan bar masa ita ba zan jirata har lokacin da zata fito, *_____________WASHE GARI* ranar lahadi wato ranar hutu ga duk wani me aiki a 'kar 'karshin gomnati, misalin garfe 9 nasafe Amar yana kawnce tin da yiyi sallar asba ya koma be tashi ba 'kararr wayar sace ta tashe shi daga bar cin da yakeyi, kamar baze tashiba domin bar cin be i she shiba miga hannu yayi ya d'au ko wayar ko duba sunan ta beyiba ya d'aga sanann ya kara a kunne, muryar da yaji ne daga cikin wayar yasa alokaci d'aya bar cin da yake idon sa ya war tsake, tashi yayi ya ce.. Basma kece? Kin dawo gareni? Ban ji me a kace daga cen ba se jinayi yayi mur mushi!! ya ce... "Wato kina nufin nazo gidan ku domin inga wani irin jin dad'i kukeyi keda mijin ki ko? Basma ta ce "Amar kana ganinn cewa anann ba a cikin jin dad'i nakeba shi yasa kake 'bal 'balta rayu war ka ko? To shi yasa na keson kazo kagani da idon ka domin kasan i dan ina cikin farin ciki da miji na ko bana cikin farin ciki zaka gani da idon ka. Amar ya ce.. To menene ma idan nazo naga hakan? Basma ta ce.. "Seka man ta da komai ka koma gurin ai kin ka domin ka sake wata sabuwar ra yuwa. Amar ya ce..idan kuma be kasan ce haka ba kumafa? Yaka mata kigane cewa zaki kasan cene har a bada a zuciyata ni abin dake son ki fahim ta kenann cewa kece kad'ai wacce na keso kuma dake zan rayu, kema kiduba Basma kin san gaskiya hakan ne yasa kikayi shiru. Basma ta ce..Shi kenann Amar koma menene idan kazo zaka fahim ci komai da komai. Har tayi niyar kashe wayar sekuma taji ya ci.. "Basma da'karfi, mayar da wayar kunne tayi sannan taji yana ce wa.. "Kin man ta kin ce soyayya ba abin tsinta bace kawai? amma yan zu wai kina cewa zaki bani wata dama, ina fatan kin fahim ci maga nata? To yan zu ne nasara ta zata fara. Basma ta ce.. "Ai ita nasara ba haka kawai take zuwa a zau neba se an had'a wata gasa tukun na, bari kuma zaka gani. Tana gama fad'a ta kashe wa yar tana jin gaban ta na bad'uwa, anya kuwa hakan ba kuskure bane!! An ya kuwa bana tagurawa Abdul sabo da naga yana sona dayawa? Namiji a gidan auran mu! Idan kuma daddy ya ji labari fa? Haka de take ta zan cen zu cin ta kafin tasamu ta kawar da wannann tinaninn tace ai te makon sa zamuyi in yazo yaganni a cikin farin ciki ze hagura dani yasa ke ra yu warsa. Amar wani irin ihun na sara yayi loka cin da suka gama wayar, ya ce.. Good this is my time, Basma ke tawa ce nasamu dama kuma yan zu zan dama domin kuwa Hausaw sun ce ba a bori da sanyin jiki, take yafara had'a kayan sa dimin tin kararr wannannn yagin nashi, wan da yake yiwa kan sa fatan na sara, cikin zuciyar sa ya ce.. Wai ma waye mijin nata amma fa koma waye wawa ne, she kuma yayi shiru ya ce.. Muzuba mugani. ( *TA KEN LITTAFIN NAMU KE NANNN MUZU BA MU GANI*) *_WAYE ABDUL MIJIN BASMA* Abdul Ibrahim shine a salin sunannsa, Abdul ba wai iyayan sa bane masu kud'i shine me kud'in, Abdul wani irin mutum ne wan da seka zau na dashi zaka fahim ce shi, tin da yake beta'ba yin wani aboki wan da suka shagu dashi ba, ko a school bashi da abokin da suka sha'ku har ya gama school din shi, Iya yen sa basu da hali domin kuwa da kame-kame suka dage har ya kammala maka ran tar sa, in da yasa mu ai ki a wani kamfani kuma shine manajan kamfanin. Daka nann kuma Allah ya te make shi har ya bud'e nashi kamfaninn. Abdul yana daga cikin man yan yan kasuwan da a ke jidasu a wannan 'kasar tamu kuma dik da haka bashi da amin tatce ko mutum d'aya sede ma hai fin sa kokuma matar sa, Abdul yana da ha'kuri sosai domin kuwa an sha a cuce shi a har kar kasu wan cin sa amma ze share, Abdul bawai wawa bane kuma bawai bashi da wayo bane kuma bawai yana jin tsoro bane, yasan abin da ya keyi, kuma yasan abin da yasa ya keyin dik abin da yakeyi, Abdul yana son matar sa sosai domin akan ta babu abin da baze yiba, kafin ta fara son sa yasha wa hala sosai dan har su jayi aure sun kai wata 6 amma bata saki jiki dashi ba, daya Abdul ya iya soyayayya Hakan ne yasa ya man tar da ita waninn ta, yasan Amar, tin da yana jin sunann shi abakin ta tin kafin suyi aure, Amma be ta6a nuna wani abu a kan hakan ba.. Yan zu gashi ya yar da ya dawo gidan su da zama har zuwa d'an wani lokaci, Abdul batare suke da iyayan sa a gari d'aya ba, shi dan a salin *KANO* yan zu haka iyayan sa suna *KANO* ai kine ya kai shi *FCT* wato *ABUJA* babu wan da sukayi sabo dashi a *ABUJA* se de ma ai katan da suke ai ki a 'kar 'kashin sa, Andul sau rayi ne domin zasu iya yin sa anne da Amar amma Abdul se bashi irin she kara 2 ko 3, Abdul dogone ba sosai ba, kuma fari ne yana tara gashi a kan sa, sannan baya yawan murmishi! Abdul de me hagu rine. *WAN NANN SHE NE ASALIN ABDUL*. ______*CIGABAN LABARIN* Amar ne a get d'in shiga cikin gidan tsaye yake yana bin tan ga me men gidan da kallo, Har besan lokacin da megadin ya wan ga me masa get d'in ba, domin kuwa tin kan ya 'ka raso aka sanar da me gadin cewa zasuyi ba'ko, Bayan ya shiga cikin gidan nann ma bin hara bar gidan yayi da kallo, ganinn man yan motocin da suka farke a garejin gidan, Mashiga falorn ya zo ya tsaya, yana kallon wani suna da a kayi a jikin 'kofar da zata sada ka da falorn gidan, afili ya karan ta abin da a ka rubuta wato, ( *ABDUL VS BUSMA*), Lokaci d'aya yaji wani irin kishi ya tsargu masa amma se yayi murmishi yana dan na wani abu da yagani a gefen 'kofar, wato a lamar da mutum a 'kofar. Dama sun san da zuwan sa kuma dama babu wanda ya ke zuwa musu gida, Sede Lubna wato 'kawar Basmar in da itama yan zu haka tayi aure. Atare suka taso hannu su cikin na juna kai da kagan su kasan suna cikin farin ciki, ita ce ta bud'i 'kofar, dede lokacin da shikuma idon sa na kan gofar damin ganinn wan da ze bud'e. Shuru sukayi dikkan su su ukun kowa da abin da yake sa'kaw a zuciyar sa, Babu wan da yayi maga Se kawai Basma tace.. Abar bar ka dazuwa, be am sa mata ba ya bita da kallo se kawai tace.. "Abdul ga Amar, Amar ga Amdul kuma mijina uban yara na, tana fad'awa jikin sa. Amar beyi mgn ba har yan zu, Kuma yaji hau shin abin da tace, Abdul ne ya ce.. "Amar bar ka da zuwa yana miga masa hannu. Be am saba shima ya bi'ka masa hannu ya ce.. Zamu iya shiga ciki? Kanlon juna sukayi Tsakaninn Abdul da basma Sannann suka bashi han ya yashige. Abdul ne ya nuna masa d'akin sa sannan ya ce masa dik abin da yake bu'kata ya sanar da shi in yaso a saka masa a d'akin. *BAYAN A WA 10, WATO LOKACIN CIN ABIN CIN DARE* Zau ne suke a gaban Dayneng tebur domin cin abin cin dare, Amar ya ce.. Ina son a had'amin kofi? "Basma ta ce.. Ai ga kayan had'a kofi d'in nann ka had'a da kan ka, kafin yayi mgn kuma ta ce.. amma bari in had'a maka, cikin sauri Amar ya ce.. "Dama de kin had'awa megidan ki tukunna ko? kafin suyi mgn ya 'kara cewa ai shima kafin yayi aure gworo ne. Basma ta ce.. "Kai ma base kayi auren matar ka tadin ga had'a maka kofi shayi da kuma dik wani abu da ka bu'kata. "Kenann ke bazaki had'a min ba ya tam bayeta yana kallon Abdul wanda jin su kawai ya keyi yana mur mushi!!. Suna cikin cin abin cin Amar yaga wani gula daban an iji ye shi a gefe ya ce.. To shi kuma wannann kulan da ba a bud'e shi ba kufa? Basma ta ce.. Aa wannann wani had'i ne na daban wan da nake yiwa mijina domin yana te makawa lafiyar sa, saboda haka babu ruwan ka da wannann kai de kaci abin cin ka. Amar ya kalli Abdul ya ce ..kai kuma irin wannann abin cin kakeso Abdul ya ce.. "Eh kasan yana gara lfy , Amar ya ce.. Ai to naga ba wani abin cin kirki bane shi yasa, Kasan cewar kular irin wacce dik abin da ya ke cikin ta zaka iya gani ne. Amar ya ce.. Kin tina lokacin da kike bani abin ci a baki kamar wata ma hai fiya ta? Ya tam bayi Basma, lokaci d'aya dikka ninn su suka tsaya da cikin abin cin suna kallon kallo. Ganinn yan da suka tsaya da cin abin cin yasa Amar ya ce.. A can na kenufi, Ai a cen gidan itace ta ke kawo bin abin ci kullum in ban ciba seta din ga bani a baki har se na ce na goshi. Yana fad'a yana cin abin cin sa han kalin sa 'kawnce.. Yaci gaba da cewa nasan Basma ta iya gir ki sosai, Amma abin da ta kemin wani lokaci fita takeyi da kan ta tasiyomin abin cin a waj. "Amar ya isa haka cikin tsawa ta yi maga nar. Amma ina mar ya cigaba da cewa.. Ai gaskiya ta iya had'e-had'e sosai, kuma a cikin soyayya take ga batar min da komai, Shin mema kike yawan gaya min ma a wan cen lokacin? Yana tam bayar ta lokacin da ya kai lomar abin ci bakin sa, bata ce komai ba , ya ce.. Yau wa na tina abin cin masoya, nayi ti naninn zan cigaba da cin irin wannann abin cin a gurin ta har tsawon rayuwa ta, Saboda Amar na kasan ce na Basma ne. Lokaci d'aya Abdul ya tsaya da cin abin cin sa Amma kan sa yana 'kasa zuciyar sa wani irin suya take yi, Amar ya ce.. Yanaga dik kunyi shiru? Ko sabo da nafadin abin da yafaru a soyayrmu? Abdul ya d'ago kan sa ya kalli Amar ya kalli Basma sannann ya ce.."ya naga kin de na cin abin cin? kici mana, yana kawar da tam bayar da Amar yayi musu, Basma tace.. Zan iya barin komai domin ka miji n. Kafin ta 'karasa Amar "ya tsuro da tarin 'kar ya hakan ne yasa bata 'karasa ba, ganinn haka yasa Abdul ya ce.. Tom alhamdu lillha nina goshi zan je in 'kawn ta, ita ma Basma tashi tayi ta nufi bayan sa domin 'kawn ciyar, har sun fara hawa sama Amar ya ce.. Gaskiya bazan iya 'kawna ni d'aya ba domin tsoro na keji. Shi ru sukayi suna kallon juna Sun rasa abin cewa se Basma ta ce.. "Amar wannann gidan nabu bamu da Aljanu babu abin da ze tsorata ka kaje ka 'kaan ta kawai. Amar yace.. Aa ni ban iya 'kawna ni d'ayaba kuma in naje d'aki zan iya shan kayan chaskewa saboda haka kawai, Wani yazo mu 'kaana tare, yana fad'a yana tashi tsaye, Se a lokacin Abdul yayi mgn yace.....✍️📝 **HAHA 🤣🤣🤣KAI JA MA A, GASKIYA CAKAWKIYA TAFARA , DAGA INI 'DAYA HAR YA ISHE SU, TO WAI ABDUL* **ZE JE SU KAWNA NE? KODE BASMA CE ZATA JE😉. KU KASAN CE DA S* ~REZA~ ✍️ HAGIQA ALQALAMI YAFI TAKOBI ✍️ The end of fart 9️⃣ To be continue..✍️ Please comment and Sher 🙏🥰 *By S REZA* [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: CAKWAKIYAR SOYAYYA 💔 Story and writers..✍️ S REZ. بسم الله الرحمن الرحيم... *08100785178*📞 ASLM Ina maibawa masoya chakwakiyar soyayya hakuri bisa rashi jina da kukayi kwanan biyu✌️hakan yafaru ne sakomakon wayata da akadauke🤦🏽‍♂️ amma yanzu alhdul nayi wata nakuma dawo muku ashirye tsaf domin faran tamuku rai💞 GA SABON NUMBER NA.08100785178 S REZA``_ Gamasu bukatar cigabansa sai sumin mgn na sakasu cikin group din chakwakiyar soyayya 👌 *SADAUKARWA GA MASOYAN CAKWAKIYAR SOYAYYA* ❤ Page 1⃣1⃣ Da wani irin sauri ya fito daga cikin motar ko magana bai tsaya yiwa Amar ba ya nufi gurin motar, Ganin ya kasa samun damar d'aure mata bakin ne yasa yake son ya d'auke ta gaba d'aya amma ina taki nustuwa D'aga kansa da zai yi sai ya ga ankusa zuwa gurin da su ke, gashi kuma be cimma ai kin saba, yana ganin ya kusa ya fisge jakar hannun ta ya ruga aguje. Ganin haka yasa Abdul bebi ta kan Basma ba ya bi bayan sa gudu su keyi amma ya kasa kamo shi Amar ne ya iso gurin da take ya tashe ta yana tambayar ta dama de lafiya? Basma tace "Lafiya babu komai fa pls muje kar yayi wa Abdul wani abu." haka kuwa akayi tashi tayi su ka nufi gurin da Abdul d'in suka ruga da gudu. Gudu ya keyi kamar gudun mutuwa domin kuwa yasan in har ya sake a ka kama shi to shikenan tashi ta k'are Yana cikin gudun ne agarin juyawa ya kalli me bin nasa yayi tinti'be take kuwa ya zube a gurin Yana fad'uwa Abdul yana karaso wa gurin domin kuwa babu tazara a tsakanin su. Kafin Abdul ya karaso gurin sa Yazaro wata siririyar wuka yace "Wallahi kana k'ara sowa sena yanka ka kar ka matso." yana nu nawa Abdul wukar Dede lokacin da Amar da Basma su ka k'araso gurin tare Amar ya ce "Abdul rabu dashi dan Allah kana ganin fa wuka ce a hannun sa kar yayi maka illa." Abdul ko kallon Amar beyi ba seda ya d'au kewa Wannan 'bara won hankali tukun se ji kayi ya kufce wu'kar a hannun sa, kafin ya ankare ya zab ga masa wani irin mari guda 3, yari 'komasa kwalar riga ya na zuba masa naushi. Tsabar wahala har besan lokacin da yasa ki jakar ba ya 'kwasa a guje, har Abdul yayi niyar sake bin sa amma "Basma tayi saurin tare shi tare da cewa pls Abdul dan Allah ka barshi haka, cikin kuka ta keyin maganar. Amar ya zo kusa dashi cikin fad'a yake masa maga Haba Abdul baka ga abin da yake hannun sa bane wu'ka cefa, yan zu da ya yan keka fa akan wata jaka jakar ban za zaka je ka salwantar da rayuwar ka. Abdul yace.."Wan'nan ba ban zan jaka bace , Wan'nan jakar abar tinawa ce agareni domin kuwa ita ce kyautar farko da na fara yiwa Basma. Ya mi'ka mata jakar. "Da gudu tazo ta rungume shi cikin kukan farin cikin tana cewa ina son ka Abdul ina alfaharida kai miji na. Amar kuwa iya haushi yaji hau shi ganin yan da suke cikin farin ciki hakan yasa ya koma gefe har suka gama shirmen su acewar sa fa wai shirme su keyi. Ahaka suka dawo gurin moto cin su, Amma Abdul yaso yaji ko wani ne ya turo Wan'nan yaron, Abdul da basma su ka shiga motar basma, Shikuma Amar ya shiga motar Abdul, a haka su ka 'karaso gida. Amar da Abdul suka nufi d'akin su, Ita ma ta nufi d'akin na ta. Yau asabar kuma yau kwanan Amar 5 da zuwa gidan. Suna zau ne shida Abdul a parlorn gidan suna hira, Basma ce d'au ke da tiran Kayan marmari, ta aje musu zata juya tata fi kenan Amar yace.. Basma ya a kayi ne? "bakomai" taba shi amsa a ta 'kaice. Basma tace "yauwa Abdul dama ina son in sanar da kai gobe Zainab da mijin ta zasu zo akan magar da mu kayi da su ranar kuma sun ce yan zu da gaske suke akan rabuwa za suyi na tambaye su akan me suka ce wai se sun zo tukun na zamu ji kuma dama Lubna ma tace "zata zo tare da mijin ta." Abdul yace.. Wai da ma basu ha'kura da Wan'nan maganar ba har yanzu? Tom shi kenan Allah ya kawo su lafiya, Amin tace, tana niyar barin gurin se taji muryar Amar yana cewa.. Yauwa Abdul dan Allah in tam baye ka mana? Abdul ya ce "ina jin ka Amar ya ce Shin kafin Basma da 'yan mata nawa ka ta6a yin Soyayya? Abdul domin yaji meze ce yace "masa ina ganin za su kai uku ko hud'u, ya bashi amsa. Amar yayi murmishi ya ce.."Haka d'in yana nufin Basma ce ta biyar, duk sau ran hud'un ba kasa mu damar auran suba, hakan yana nufin da ka auri wata daga cikin su da baka auri Basma ba ko? Kaga kenan kai kasamu za6i ni kuma bani da za6i, yaci gaba da maganar sa cikin nitsuwa da tau sayin abin da zai furta, ita kuwa basma har idanun ta sun fara cikowa da hawaye. "Ni ban ta6a samun irin wan'nan damar ba, ita kad'ai na ta6a soyayya da ita, kuma da ita kad'ai naso nayi rayuwa ta, nayi burin ace tare zamuyi rayuwar auran mu tare, kuma sabo da Soyayya ta ta gaskiya ce, yana kawo wa nan hawaye suka wan ke masa ido yana kallon Basma wacce tini hawayan ta suka da d'e da yin ambaliya a fuskar ta. Basma ce tayi juriyar iya ce wa "Amar ya kamata ka gane kana wuce 'ka'ida fa. Kafin ta 'karasa Andul yace "Basma kibar shi yayi maganar sa, jin haka yasa tayi shiru shi kuma Amar ya ci gaba da magana kamar haka. Ya kalli Abdul yace.. "Shin lokacin da kaje neman auran Basma ka ta6a tambayar da ko tana da wanda ta keso? To da ace ka tambaya to tabbas zata sanar da kai ni take so nine a zuciyar ta, Ka ga kai dama ka ta6a yin soyayya kaga kenan da a ce ka tam baye ta da kaga kai zaka samu wata se kayi auran ka, to nikuma fa bani da kowa." Kafin ya 'karasa Basma tace..Amar ya ka mata kasan irin maganar da zaka din ga furtawa Wan'nan abin da kake gaya an yishi ne tin a baya sabo da haka duk sun wuce. Amar yace.. Haka ne ko? Wato sabo da ni yaro ne ku kuma man yane ko? Cikin kuka ya ke yin Wan'nan maganar. Yanzun ina son in muku wata tambaya? "Muna jin ka kayi tambayar ka, in ji Abdul wan da tin da Amar ya fara maga kallon sa ya keyi dik jikin sa ya mutu kuma har ga Allah dik abin da Amar d'in yake fad'a gaskiya ne. Amar yace.."Wata yarinya anyi tunanin bata cikin farin ciki ita da mijin ta, Se ya tafi domin tabbatar da haka in kai ne ya za kace? Shin zaka fad'i kuna da wata ha la'kane tsa kanin ku kokuma baza ka fad'a ba? Yaci gaba da cewa.. Idan yarinya tana soyayya da wani kuma taje ta auri wani daban shin shi wan cen meza a cemasa? Kaga kenan zan iya cewa kana da mummu nan hala'ka da wacce nake so rabin rayu wata, "ya ishe ka Amar baka da hankali ne angaya maka hakuri tsuro ne? Cikin ihu ta yi masa maga san'nan ta shigq d'akin ta tana kuka. Shima Abdul d'in hawa yen ya keyi ya tashi ya bita d'akin. Amar kuka ya keyi kamar wanda a ka dake shi, afili yake furta, walhi ina sonki kuma Allah se nasa shi da kan sa ya sake ki, kuma na aureki, dan ke akayi ni nima kuma dan ke aka yini, a haka shima ya tashi ya nufi nasa d'akin. *_________ALHAJI SANI* Zaune suke shida uwar gidan sa wato Zainab hankalin sa a mu tu'kar tashi, kallon Ali yayi wan da shima hankalin nasa a tashe yake yace.. "An ya kuwa Ali bamuyi rashin tunani ba? "Ali yace abin da za'a yi kawai shine mushir ya zuwan baza ta dumin mu tabbatar" Alhaji sani ya ce.. "Gaskiya ina son yarin yata san'nan kuma bazan yarda ni da kai na in selaka ta a tsaka me wuya ba, walhi abin da ya faru da 'yar gidan mlm bala bana son ya faru a kan yarinya ta, gaskiya kashir ya mana tafi ya *ABUJA* gobe kuma bana so ta sani domin muje mu tabbatar da abin da muke tunanin, a haka suka tayar da maganar. *TOFA MENE NE ZE KAWO ALHAJI SANI GIDAN BASMA? SHIN MASU KARATU DAMA DE BAKU MAN TADA 'YAR GIDAN MLM BALA BA WAN CE RANAR DA SUKA 'DAUKO AMAR A MOTAR SU HAR SUKA GA, WANI SAU RAYI WAI SHI DOLI SEYA AURETA, SHIN ME YA FARU DA ITA? ,HAR ALLAJI SANI YAKE TSORAN KAR YA FARU DA 'YAR SA, SHIN KUN SANE DA CEWA BESAN AMAR YANA GIDAN SU BASMA A ZAU NEBA?* KUKA SAN CE DA S REZA *WASHE GARI* Da wuri basma ta tashi ta fara tar yar ba'kin su da abinci kala-kala, Seda ta kusa kammala girkin ne Lubna ta 'kirata ta sanar da ita cewa baza su samu da mar zuwa ba pls dan Allah tayi ha'kuri, amma zasu zo wata rana, bata ji d'iba haka taci gaba da 'kara girkin. Mesalin 9 nasa fe kasan cewar yau lahad'i ranar hutu ce yasa Amar da Abdul babu wan da ya farka ita kuma se had'a musu abin ci take yi, tana cikin haka ne taji ana matsa 'kararrawar alamar mutum tayi mamakin jin haka domin kuwa tasan basu da wani b'ako, tin da lubna ta sanar mata sun fasa zuwa. Tana bud'ewa ido ta zaro waje cikin mamaki had'e da far gaba da kuma tsoro duk a lokaci d'aya, Daddy ne shida Ali , da gudu tazo ta fad'a jin sa tana dariya, tace "daddy welcome san'nan ta gai sar sa Ali tana basu han yar shiga cikin parlour, tace.." Daddy me yasa zaku zo amma baka sanar da niba" "muna son muyi muku zuwan ba zata ne kuma gashi munyi muku ya me gidan naki?" Dede lokacin da Amar ya tashi da wata shegiyar yunwa, ya man tama daga shi se rigar barci iya guiwa da wani gajeran wandan rigar, yabfito se wata mi'ka ya keyi yana hamma. Dede Daddy ya na tambayar ta cewa ya naji baki tambaye ni little b... Ai be 'karasa ba sukayi ido biyu da Amar wan da ya ke saukowa, shima sud'in yake kallo cikim mamaki da firgici, Daddy ne yayi 'karfin halin tambayar ta cewa shin Wan'nan meya keyi a gidan nan? Cikin kame kame Basma ta ce.. amm amm dama dama whi dad dad.......✍️📝 End of part 1️⃣1️⃣ To be continued.. Please comment and Shere🙏 This is my new number 08100785178. S REZA By S REZA [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CAKWAKIYAR SOYAYYA* *Story and writing..✍️ *S REZA* ©🎆 *Al'umma Writers Asso...✍🏻* _{Al'umma writers,Ƙungiya ɗaya Tamkar Da dubu Farin Cikin mu, mu faɗakar da Al'umma domin su Farfaɗo su gane gaskiya Al'umma sai Dan Al'umma ,Allah ya bamu Ikon fadakar da Al'umma}._ https://www.facebook.com/102282991949826 بسم الله الرحمن الرحيم... *Cakwakiyar* *Soyayya*🥰💔♥️ *PAGE* 1️⃣0️⃣ ........ ABDUL yace" badamuwa bari inje sai mu kwana da shi ai ba damuwa, Kafin tayi magana ya sau'ko daga saman ya nufi d'akin da suka sau'kar da Amar d'in. Basma cikin mamaki tabisu da kallo har suka shige, bata iya cewa ko mai ba itama ta shige nasu d'akin. A cikin d'akin madai kafin suyi barci abubuwan ban haushi ya ke tayi masa, irun su 'kurnanin barci da kuma d'aura masa 'kafa, kuma duk abin da ya keyi Abdul d'in yana jinsa amma ya nuna masa barci ya keyi. Shi kuwa Amar duk abinda ya keyi da saninsa ya keyi wai shi hakan kishi ya keyi. *WASHE GARI* bayan sun kammala breakfast ne, wanda shi ma gurin breakfast d'in saida akayi abinda a kasaba. Abdul ne ya fara tashi ya ce" Basma ni zan tafi office. "Ok nima dama na gama shiryawa zan huce school bari se mutafi tare, kasan cewar dama tana cigaba da karatun ta` Har sun fara tafiya suka ji Amar ya ce" Nikuma me Zanyi to?Sai ka kula mana da gida ko kuma kuyi wasa da teger, Tana nuna masa gurin da d'an 'karamin karan da suke kiransa da tegar. Shima kallon karan yayi yace "Dama kina nufin kun kirani gidan ku domin in yi wasa da tegar ne ko kuma in yi gadin gidan ku? Kafin suyi magana ya ci gaba da cewa to a cikin ku ina so in bi wani, Kallon junan su sukayi San nan Abdul yace " tom ba damuwa tashi mu tafi. Suna cikin tafiya a motar ba wanda yake yiwa d'an uwansa magana, sai cann wani lokaci Abdul ya kalliAmar yace" Ka saka belet d'in ka, Amar ya ce "ok sannan ya ce yanzu a ina zamu ci abincin rana tunda ita matar gidan ta tafi school? Abdul be kalli in da yake ba yace"sai lokacin cin abincin yayi, Amar ya ce" Duk yanda kace ai haka za a'yi. Basma waya ta d'au ka takira 'kawarta domin gaskiya lamarin Amar ya fara bata tsoro. Lubna Daidai lokacin tana duba wani mara lafa wanda ciwon ha'kori yake damun sa, dama ita 'ban garan data karanta kenan. 'Daga wayar tayi had'e da sallama, Bayan ta gama jin duk abinda Basma tace mata, san nan taja wani gajeran num fashi!! tace" "Gaskiya wannan abinda ki kayi baki daidai ba ya za a yi ka kawo shi gidan ki tare da mijin ki wai ke hakan kina son ki temaka wa rayuwarsa? wai ma ina tinanin ki da hankalinki sukaje ne? lokacin da kika yanke wan nan d'anyan hukuncin? Gashi kince jiya yazo kuma daga kwana daya kacel kince yafara baki tsoro, to ina ga yakai sati daya ko biyu? Basma ta ce"Ni zan iya fuskantar duk wata matsala a rayuwa in dai Amar zai koma cikin Rayuwarsa ta da, kuma nasan in sha Allah zai koma d'in. Lubna ta ce "kina ganin Amar zai iya dawowa cikin Hankalinsa nan kusa ?kinsan fa Amar yana son ki bazai yarda Bata bari ta'karasa ba Ta ce "sai anjima ta kashe wayar ta, Taja wani tsakii san nan ta ce" Dama nasan halinki shi yasa ma lokacin da zan kira shi ban nemi shawararki ba saboda nasan zaki iya 'bata min lamari. Idan mun shiga office duk wanda ya tambaye ka kace masa kai aboki na ne, Abdul ne ya ke gayawa Amar haka lokacin da suke shigowa cikin camfanin. Amar ya yace"Idan kuma na gi fad'a fa Nace musu ni ne tsohon Saurayin matar ka Lubna fa? Yaba shi amma ata'kaice, ganin yanda ransa ya 6aci ne yasa shi saurin waskewa, ya ce" Ina nufin in na fad'a hakan baza kaji dad'i ba, Abdul bai masa magana ba ya huce suka ci gaba da tafiya ganin sun shigo ciki, kuma gashi ma'aikata sai gai she shi sukeyi. office ya shiga, ya tarar ta ai'ki a gabansa sosai hakan ne yasa ya d'au lokaci yana ai ki. Amar kuwa ma'aikatan kamfanin gaba d'aya ya tara yana basu labarin cin amanar da Budurwarsa ta yi masa, Daidai lokacin da Abdul ya fito daga office d'insa ne yaga abin mamaki! wato Amar ya tara duk ma'aikatan yana basu labari ,su kuma sai dariya sukeyi suna washe baki. abin bai gama baki mamaki ba saida yaji abinda Amar d'in ya ke cewa, Bama ai so d'aya ko sau biyu ba ai sau da yawa, wani daga cikin ma'aikatan yace" Kenan ta kasan ce har class d'in ku ta ke zuwa a school d'in ku? Kai amma gaskiya yarinyar kirkice, Wata mace daga ciki ita ma ta ce " kuma yanzu tana cikin farin ciki kuwa? Amar yace Ban sani ba amma nasan bata cikin farin ciki, wani ya 'kara cewa" To me yasa bata kira ka ta sanar da kai ba se kawai ta auri wani? gaskiya bata kyu ta maka ba, Wan nan mace ta 'kara cewa "Gaskiya kam bata kyuta ba ai yakatama ace lokacin da a ka saka ranar ta kira ka ta sanar da kai in yaso se kusan abin yi,amma kuma taje ta auri wani gaskiya batayi ba, ta 'karasa maganar tana wani ya tsine fuska. Amar yace" Ba damuwa fa yanzu haka ma yarinyar tana nan a *ABUJA* ita da mijin ta, amma fa wan nan ba komai bane bafa kawai dai ina baku labarin yaudarar da tamin ne. Duk abin da yafaru a kunnensa domin yaji komai Amma ya nuna masa baiji me yace ba. Daya ke Abdul yana da sau'kin kai yasa ko lokacin da ya 'karaso gurin su babu wanda ya ji tsoran kar ya same su a haka, 'Daya daga cikin ma'aikatan ne yace" Gaskiya yalla'bai wan nan abokin naka ya had'u kaji labarin soyayya da ya ke bamu yanda kasan a cikin film wallahi gaski labarin abin tau sayi, Abdul ya ce"Labarin soyayya kuma soyayar wa? Ya tambaye su, Wani ne ya ce "Yalla'bai labarin soyayar abokin sane ya ke bamu, Abdul ya ce" Tom tashi mutafi yana kallon Amar d'in Kafin Amar d'in yayi magana wan nan macen tace"Yalla'bai gashi kuma labarin ya fara dad'i kuma zaku tafi yaushe zaku dawo da shi domin ya 'karasa mana? "Cikin jin haushi yace kowa ya tashi ya koma bakin aikin sa ban san shirme!!... Haka kowa ya tashi yana ganin yanda Ran ogan nasu ya 6aci lokaci d'aya. Bayan sun fito Ne suka biya ta wani kamfani wanda shima na Abdul ne, sai wajen biyar suka iso gida' suna shiga gida Abdul ya ce" Duk ranar litinin bama cin abincin dare a gida muna zuwa restaurant ne muci a can kashirya mutafi zamu same ta a can din. Bayan sun iso ne kamar yanda yace kuwa a cen suka sameta tana jiran su, bayan sun zaun ne an kawo musu komai da suka bugata, se kawai Amar ya kama dariya yana kallon 'kanon abincin da yake gaban su, sai a lokacin itama Basma ta kula da abinda yake yiwa dariyar, nan take itama tafara dariya, dariya sukeyi babu 'ƙaƙƙautawa. ganin dariyar tayi yawa ne yasa Abdul ya ce" Shin zaku iya gaya min abin da kuke yiwa dariya? Sai a lokacin suka d'an tsaya da dariyar, Amar ya kalli Basma ya ce" Kigaya masa,itama tace" aa kai kaga ya masa, haka suka dinga wasa da Hankalinsa hardai Amar ya ce"To bari in sanar da kai abinda mu ke yiwa dariya, yace" Wata rana ne ni da Basma muka tafi wani gidan abinci ,dani yar cin abinci Saida muka ci muka 'koshi, wai a she bata zo da kud'i ba nikuma a wannan lokacin ko nera biyar babu a gurina, haka mukayi tsuru-tsuru muna neman mafi ta, Sai ga kiran Abokina Sadam tofa shine ya zo yabiya mana kudin abincin, Shine yanzu muka tuna muke dariya. Basma ta ce" Ba gaskiya yafa d'amaka ba, tana kallon Amar d'in yanda ya iya shirya wan nan 'karyar kamar gaske! Ya kasance shi maicin abinci da yawa ne in zaici abinci flet ukku yake cinyewa shi kad'ai, To abinda yasa kake muna dariya shine wan nan abincin ba isar sa zaiyi ba koda kuwa duk har da na mu zaihad'a ya cinye Saboda tsabar cinsa. Tana fad'a tana dariya, duk da kuwa uban kallon da ya ke binta da shi alamar kar ta fa'da amma saida tafa. Shima Abdul saida yayi dariya dajin magar tasu, San nan ya ce" To ai wan nan ba komi bane, bari in sa a 'karo maka ko? Haka dai suka cigaba da cin abincin su cikin nishad'i,shi kuma Amar cikin jin kunyar tonon sililin da tayi masa` Bayan sun gama ne suka fito domin zuwa gida. Amar ne ya fara fitowa Sai kuma Abdul wanda suka jero tare da Basma tana rataye da wata jaka a hannun ta na hagu, Dama itama tazo da motar ta, hakan ne yasa tanufi motar ta daniyar shiga,su kuma har sun shige tasu motar sun tashi zasu bar gurin. Basma daidai ta bud'e gidan driver domin ta tashi ta tafi. Jitayi an sha ganta tabaya, kafin tayi ihu kuma an jefar da ita a'kasa daniyar d'au re mata baki da hannu. Abdul dayaga sun kusa fita daga wajan zuciyarsa ta raya masa bari yagani ko itama ta taso?? le'kawar da zaiyi ai kuwa yayi ido biyu da wani 'kato yana danbe da matarsa!!.......✍️📝 *TOFA, ANYA WAN NAN BA KAMAL BANE ?KUN SAN FA KAMAL MA BE HAKURA BA. SHIN ABDUL ZAI IYA TEMAKONTA ?KODE AMAR NE,? KUKASAN CE dDA S REZA.* *End of fart* 1️⃣0️⃣ *To be *continue*.. Please comment and Shere By *S* *REZA*[12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: ───────────────────── *HIGHER STANDARD WRITERS ASSOCIATION®* 📖📚✍️✍️ ───────────────────── https://facebook.com/Higher-Standard-Writers-Association-100702755812959/ ```Alƙalami Ya Fi Takobi``` ___________(✪)___________ *CAKWAKIYAR SOYAYYA* 💋 Story and writern..✍️ S REZA Na sadaukar ga wannan Page ɗin ga mahaifiyata jigon rayuwata 😢 komai nazama kece silar komai. Ina Alfahari dake. (I LOVE`YOU MY MOM) PAGE1️⃣2️⃣ ............Cikin tsawa daddy yake tam bayarta, nace meyakawo wannan cikin gidan nan? yana nuna gurin da Amar yake "Daddy wallhi fa ban san ni fa amm dady "tsawar da daddy yasake mata ne yasa ta sake rikicewa. tarasa me zatace masa kan ta ya ƙulle "Daddy ai abokinane... Cewar Abdul yana sauƙowa daga ɗakin nasu, cikin fara'a yace.. "daddy zuwa babu sanar wa haka? sannun ku dazuwa. daddy Amar Basma Ali, Duk tsyawa sukayi suna kallon sa shi kuwa ko a jikin sa. Abdul yaci gaba dacewa.. daddy Amar ai abokina ne, yazo garin nann yin wani aikine shine muka haɗu dashi, kuma damuka zogida shine itama Basma tace min wai tasan shi, to shine fa mukace kawai ya zau na a gidannan har ya kammala ai kin sa base ya kama hotel ba. Basma da Amar kallon juna sukayi cikin mamakin abin da Abdul ɗin yace "Daddy yan zu shikenan kadena yar dadani kadena sonako? cewar Basma tana ɓata rai. Haƙiƙa Daddy ya yarda da bayanin da Abdul yamasa domin kuwa yasan halin sa. daddy yace.. "haba ƴar daddy ai ban san haka abin yake ba. Yana kama hannun ta suna shiga cikin falorn. Amar kuwa mutuwar tsaye yayi domin har ga allah yagama tsorata sosai, kuma abin da Abdul din yayi yabashi mmk, afili ya ce... Gaskiya gayan nann yahaɗu kuma yan zune ma za'afara wasan. Bayan sun karya kowa yayi hani an. Abdul yace... Ni zan fita zamuyi wani aiki a office amma yanzu zan dawo. nann take Basma ta haɗe rai alamar bataso yatafi Shi kuwa saraii ya ganta amma ya ɗauke kansa kamar be gan taba. Duk abin da sukeyi a kan idon daddy da Ali harma da gogan naku wato Amar. Bayan Abdul yabar gurin itama tashi tayi tabi bayan sa... Tana zuwa tace.. haba Abdul daddy nane fa yazo amma bazaka iya haƙura yau ɗaya ba? yau ɗin ma kuma baranar aikiba haba mn Abdul kokana son Daddy yayi zargin wani abune? "Haba mana a'maryata walhi nima ban so hakan ba kuma ai nace miki ba zan daɗeba yan zu zan dawo, yana gama faɗa ya man na mata kiss a'goshi sannan yatafi yana sauri. Abin yabata hau shi haka takoma gurin ran ta a ɓace. Alhaji Sani ne zaune shida Ali da kuma Amar. Ali ne yace... Amar naji an ce ka kai sati ɗaya a gidan nann ko? "eh gaskiya ne satina guda harda wasu ƙanaki in ji Amar, Ali yace.. "Tom masha Allah hakan yayi. Dama wani abu ne yake tafe damu akan Basma, a gaskiya muna tsoran kar wani abu yafaru muzo muna da mun sani. Ali yace... Ka tina ranar da muka ɗawkoka a mota har muka ga wani abokin Alhaji suna rikici da wani saurayi harya "eh natina nima wannan abin har yanzu ina tina wa dashi in ji Amar kenan, be bari ma yaƙarasa ba. Amar yace... To me yafaru da ita? Se a lokacin Alhaji Sani yayi mgn yace... "Yarin yar ammata auran dole Kuma tasha maganin ƙwari ta kashe kan ta dalilin hakan, Dama kasan tace tana son yaro amma mukuma muka ce baza mu bashi ba saboda bashi da sana'a, Alhaji sani ya cigaba da ba yani kamar haka.. To wannan shine da lilin da yasa na taso domin nazo naga irin zaman da Basma takeyi da mijin ta, in har naga bata jin daɗin zaman to zan raba auran, tin dade itama nasan tana da wan da take so, auran dole nayi mata. Cikin rikicewa da abin da zece ɗin yace.. "dama kasan tana da wan da takeso kuma ka aura mata wani? inji Amar yana tam bayar Alhaji sani "eh nasan tana da wanda take so amma ban san waye ba "To meyasa kasan tana son wani kuma zaka aura mata wani? inji Amar. Alhaji sani yace..."Ranar ɗaurin auran ne Dasafe ita da ƙawar ta Lubna, Suna zancen nikuma nazu zan huce shine naji lubna tana cewa... Haba Basma kar ki cuci kan ki walhi nasan idan har daddy yaji cewa kina da wan da kikeso to na tabbatar baze miki auran doleba. Alhaji Sani yacigaba da cewa... Nikuma da naji haka se kawai na shiga cikin ɗakin nasu, Amma ban nuna musu naji abin da suke cewaba, Bayan mun gai sada ita Lubnan sai nace tazo zan ai keta, bayan tazo sai nake tam bayar ta cewa abin da naji yanzu gaske ne kode ƙar yane? Lubna ta ce..."Daddy mekaji? nann take na mayar mata da abin da naji suna batun sa... To a lokacin abin da Lubnan tace shine yaɓata min rai yasa nakoreta kuma nayi ban za da maganar. Awannan lokacin da kace Amar zai iya zuwa lahira a yau kuma yadawo to da babu abin da zai hana Amar tafiya domin kun ya da kuma tsoro. tam bayar zuciyar sa yakeyi shin meye Lubna tace! Kenan tace masa nine saurayin ta shikuma ya ji haushi? Tam bayar da yakeson yayi yakasa yaji Ali yana tam bayar Alhaji Sani. "To yaya me nene ita Lubnan tace maka? in ji Ali yana tambayar Alhaji sani. Alhaji sani yayi shiru yana kallon Amar, Wanda izuwa yanzu har wata zufa ce take keto masa. Alhaji sani yace..."yarin yar tabani mamaki dakuma rashin tsoro domin kuwa se yan zu nake tinanin abin da tace shi ne gaskiya. Ta cemin... To daddy idan kasan wanda take so ɗin zaka fasa aura mata wannan n? "nikuma jin haka yasa nake ganinn kamar tamin rashin kunya ne, ni kuma nace mata.. "bazan fasa ba ina so de nasan waye shi. Sai kawai naji tace min wai "To ai daddy babu am fanin sanin inde ba auramata shi zakayi ba. Ni kuma jin haka cikin tsawa nace mata tafita min daga ɗaki mara kun yar ban za. Amar tam kar yazuba ruwa a ƙasa yasa don murna, Azuciyar sa yace.. Wai dama ashe Lubna tanada wayo haka gaskiya ta yi namijin ai ki tanada babbar kyuta a gurina. Abin da Alhaji sani yace ne yasa duk kan su suka mai da hankalin su izuwa gare shi. Alhaji sani ya kali Amar yace..Tam bayar ka nake so zan yi kuma dan Allah ina so kafada min gaskiya, Shin ya zaman Abdul da basma yake a cikin gidan nan? domin ni walhi in har naga basa zaman lafiya to zan raba auran ne, kuma zan nemo wannan Tsohon saurayin nata in aura mata tin dade nasan shi takeso, kaga in naje furin lubna zata gaya min gaskiya. Amar jin maganar yayi tam kar sauƙar aradu, Dan tsabar mamaki har rikicewa yayi yace..."Alhaji ni faaa ban san Alhaji allha ni fa "Alhaji sani yace.. "kaga ai ba wai nace zan raba auran haka kawai bane, Nasan Abdul abokin kane kuma nasan baza ka faɗi ƙarya ba, ni de Abin da nakeso shine farin cikin yarin yata. Amar yayi shiru yana tinanin abin yi. Yan zude ga dama tasamu, yan zu zai mallaki abar begen sa, yanzu Basma zata zama tasa, yan zu wuƙa da nama suna hannun sa, jin zuciyar sa yakeyi wasai tam kar ya mallaketa. Ali yace.."kar kaji kunya duk abin da ya ke faruwa kawai ka sanar damu, Amar yace... "Wai dama auran nasu ba na soyayya bane? "eh walhi basu ma taɓa ganin juna ba se ranar auran, Ali ya bashi Amasa. Amar yace..."Shi yasa nake ta ganin abu buwa suna ta faruwa mana, yaci gaba da cewa... Gaskiya duk auran da bubu soyayya do le irin wannan abubuwan su dinga faruwa, yana maganar yana gir giza kai a lamar abin babu daɗi. Han kakin Alhaji Sani in yayi dubu to yau ya tashi. Yace.."yan zude sanar mana duk abin da kaga suna faruwa a gidan kar kaɓoye mana komai, nikuma in de naji babu abin da zesa bazan tafi da ita gida ba kuma daga gida zamu huce cot domin a raba auran, ni kuma in aura mata wan da takeso suje suyi zam su cikin farin ciki. Amar yaji wani farin ci ki haɗe da ƙarin ƙyiwa a kan abin da yakeson yi. Amar yace..."gaskiya daddy zam nasu.......✍️📝😄😄😄 *KAI JAMA'A WAI ME AMAR ZECE? SHIN KUNA GANIN KODA YAYI ƘAR YAY AURAN ZAI RABU? KU KASAN CE DA S REZA DOMIN JIN YAN DA ZATA KASAN CE....✍️*📝 *ITA ƘADDARA KOWA DA IRIN TASA, KAR KA DIN GA HANGEN NA SAMAN KA KA HANƘI NA ƳASA DA KAI YIN HAKAN ZAI SA KADIN GA GODEWA ALLAH🙏 ALLAH MUN* GODE MAKA2 End of part 1️⃣2️⃣ To be continue... PLS COMMENT AND SHERE 🙏 This is my new numbar 👇👇👇👇👇👇👇👇 08100785178. .S REZA [12/23, 6:01 PM] +234 810 078 5178: *CHAKWAKIYAR SOYAYYA*💋 Story and Written..✍️ By. S REZA *Slm masoyan Cakwakiyar soyayya. Daga wannan PAGE din zan yi tafiya saboda haka , bazaku jiniba har sai sabuwar shekara, in Allah ya kaimu, in kuma Allah yasa na dawo to zan cigaba, Ina Allfahari da masoyan littatafai na🙏🏼* PAGE1️⃣3️⃣ ................Kallon Daddy yayi sannan ya kalli Ali sai kuma ya sunkuyar da kansa sannan ya ce... "Gaskiya daddy nima abin nasu yana bani mamaki, tin da nazo gidan nan kullum a cikin faɗa suke, bama wannan ba wallahi wani abune yake bani mamaki" Da sauri Daddy ya ce.."Kar kaji komai sanar dani duk abin da kagani ko kuma kaji" Amar ya ce " Daddy to wallahi basa kwana ɗaki ɗaya" "Ban gane ba? basa kawna ɗaki ɗaya kuma? Inji Ali yana tambayar Amar? "Eh basa kawna ɗaki ɗaya, kuma nayi-nayi na san dalilin hakan amma kuma Abdul yace min babu ruwana hakan ne yasa nima nayi shiru na rabu dasu" "To shiɗin a i'na yake ƙwana? inji daddy. Amar ya sunkuyar da kai ƙasa alamar abin ya bashi takaici, sannan ya ce... "Daddy abin da nakeso daku yanzu kawai ku bari in dare yayi sai kugani da idon ku, zakuga ina zai je ya ƙwana" Haka kuwa a kayi daddy yace tom bari Allah ya kai mu daran "Amen inji Amar yana tashi ya barsu a gurin. Alhaji sani wato daddy, ya kalli Ali yace... Gaskiya In de abin da yarannan yafaɗa gaakiya ne to wallhi babu abin da zai hana ban raba auran nann ba, ace miji da mata baza ƙwana ɗaki ɗaya to hakan mai yake nufi kenan? "Yana nufin basa zaman lafiya kenan, hakan ma yanuna cewa tun kafin Amar yazo haka masuke rayuwar su kenan fako? in ji Ali yana tam bayar daddy, daddy shuru yayi yana gir-giza kai Alamar ran sa ya ɓaci. *_________BASMA* bayan sun gama kar yawa tattara gurin tayi takai kicin sannan ta dawo ta share gurin, Duk abin da takeyi ran ta a ɓace yake saboda abin da ABDUL ɗin yayi mata, yan zu ace daddyna yazo amma wai bazai hagura da aikin yau ba, kuma yau baranar aiki ba. Sosai abin ya ɓata mata rai, wan katayi bayan taga gyara gida sannan kuma taɗora musu abin cin rana. Tana kicin tana aiki taji dawo warsa, afili take magana. Wai wan da yace Zai dawo yanzu-yanzu shine sai yan zu, tin safe sai ƙarfe 2 amma wai yana cemin baze daɗeba "Haba mana amar yata ai gashi nadawo, walhi wani abune ya tareni shine yasa amma ai gani sorry kinji uwar gida, yana maganar yana kama kunnansa a lamar ban haguri. Haka kawai yau takejin tana jin hausin abin da yayi mata, Hakan ne yasa bata kula shiba, sema ƙoƴarin ƙwace jikin ta da takeyi daga nashi, Abdul yace... My amarya lafiya kuwa inata magana kin min shiru? jin bata amsa bane yasa ya rabu da ita ya huce ɗaki domin yin wan ka. Zau ne ne suke dukkan su'akan daynin tebul domin cin abin cin rana, bayan tazubawa ko ita kuma bata zubawa kan taba, kuma dama tin da tazo gurin babu wan da tayi wa magana, kai da kagan ta kasan rain ta'a ɓace yake. Meƙewa tayi da niyar barin gurin ABDUL Yace... "Basma lafiya kuwa ina kuma zakije? bata bashi amsa ba sai ma kallon sa datayi saikuma taci gaba da tafiya. daddy ne yace..."Yar daddy dawo kici abin cin kin ji "Nifa naci nawa tin ɗazu sabo dahaka kawai kuci kayan ku, tana gama faɗin haka tahuce tayi tafiyar ta. Kallon-kallo aka koma yi sta kanin Ali da daddy da kuma uban ƙaiyar wato Amar. Abdul ne ya meƙe ya bita abaya domin rarrashin ta. Bayan Abdul ya fita ne, daddy yayi tagumi irin tagumin hannu bibiyunnan. kallon Amar Ali yayi yace..."Gaskiya ne maga nar ka, ga alama guda ɗaya mun gani tin dade gashi a gaban mumafa kenan "yan zude kunga alama guda ɗaya ko? Tom Allah ya kaimu anjima zaku sha mamaki. Abdul yana shiga ɗakin yayi truss yana kallon ikon Allah, ƙarasawa inda take yayi yana mata magana, Haba Basma menene haka kuma? yazakizo ki kwanta a ƙasa kina kuka sai kace ammiki mutuwa Pls dan Allah kitashi muyi mugana kinj "nide katashi kafita min daga ɗaki kaje gurun wacce tafini agurin ka nide kabar ni nace. Cikin mama ki yake kallon ta jin abin da take cewa, ban gane ba mekike nufi? cikin kuka tace... "Bayan kafita ankira'a wayar ka akace wai ana neman ka a office kuma kace min cen zakaje, sannan kuma kace min yan zu zaka dawo amma tin safe sai ɗazo fa kada wo? Tana gama maganar tafaɗa jikin sa tana rushewa da wanin sabon kukan. Cikin mamaki yake kallon ta, to shi waye ya kira shi! yace...Ni a ka kira? yana tam bayar ta "to zam maka ƙaryane tabashi amsa "tashi kije ki ɗauko min wayar. Tashi tayi tafita domin ɗauko wayar, Abdul mamaki yakeyi to ma wai waye wanda ya kirashi kuma ai shi tin ɗazu yana office amma bari ta kawo wayar ya gani. Da sallama ta shigo ɗakin tana nufar in da yake meƙa masa wayar tayi tana kallon sa. Dasau ru ya karɓi wayar yana bude ta, kurin da in mutum ya kira kokuma a ka kirashi zai gi yanufa, abin mamaki, Gaba ɗaya ma yau babu wan da ya kirashi, Dama kuma shi bashi da a boki koɗaya in kaga yana waya to shida daddynin sane kokuma wasu daga cikin ma ai katan sa. Nuna mata wayar yayi yace... Basma kin gani a yau ma babu wan da ya kirani ta wannan layin, yana nuna mata wayar, itama cikin mamaki ta karɓa taduba. Basma tace kuna fa walhi an kira ka kuma nice da kai na na amsa kira, cikin wasa yace... Kode tsabar kishin nawane yasa kika manta kina ce ko ankirani ne? "Ai ni yanzu nadena kishin ka tin dade kai ma baka kishi na "Nidin ne bana kishin ki? yana tam bayar ta? tace "eh mana tin dade gashi ni ina kuka kai kuma bakayi "to yan zu dan mutun yana kuka kai ma in kayi shi ne kayi kishin sa? yana tam bayar ta, ita kuwa tace "eh mana ai haka shine cikar masoyi duk abin da masoyin ka yayi kai ma kawai sai kayi "tom yan zu bari nima in kama kukan. Nann kuwa shima ya buɗe baki ya fara kukan ummmm aaaa. Ita kuwa me take in ban da dariya. Haka tsakanin mata da miji sai Allah, a haka de suka shirya kamar komai bai faruba. Shikuwa Abdul wannan abun yana ransa, shin waye yakirashi daga office? kuma shi yasan yau tin da yafita yana office bai je ko ina ba, Haka de yake ta tunani a kan abin. *____________AMAR* Murna ya keyi yakusa kama aikin sa, yan zu idan Allah ya kai mu dare daddy ya tabbatar da abin da na gaya masa shi kenan Basma tazama tawa, wani ɗan ƙaramin ihun daɗi yayi yana tsalle a kan gadon sa. Gaskiya ina son Basma ina mata son da babu wani magaluki da zai iya mata, kuma ni walhi babu ruwa na da Auran ta in de har daddy ya gano su to nide wuff! zan yi da ita abuna, wani abu ya tina sai kuma yayi shiru. Shin ma yan zu idan daddy yaraba su kuma yaji ance nine tsohon saurayin ta an ya bazai zargi wani abu ba! shuru yayi yana tinani, jan zuwa wani lokaci yace.. Nasan abun da zan yi bazai gane ba. Zau ne suke duk kan su domin cin abin cin dare. Abin da yabasu mana ki shine, Basma da Abdul sai raha sukeyi suna cikin farin ciki gashi kuma sun zauna a kusa da junann su. Ali da daddy suma abin ya basu mamaki, amma sukayi shuru da bakin su kamar babu komai. Shi kuwa Amar abin haushi ya bashi ganin yanda suke ta dariya har da wani man nuwa jikin sa. Basma ce tace... Wai daddy baka bani labarin Anty Zainab da kuma litil dina bafa? tana kallon daddy "Ai busu san nann muka zo ba, kin san halin shi in da yasan nan zamuzo ai da sai mun zo dashi, in ji daddy yana bata amsar tam bayar ta "to daddy kuba mu shi mu zaina da shi mana, cewar Abdul yana kallon daddy? daddy yace.."Ai muma shi kaɗai ne a gaban mu badan haka ba ai da tini mun baku shi "Amar takira sunan sa a han kali ganin yagi cin abin cin sai jujjuya cokali yakeyi a cikin abin cin... Me yake damun ka? naga tin ɗazu baka fara cin abin cin ba sai tinani kakeyi. Amar lokacin da yaji muryar ta acikin kun nan sa sai da komai na shi ya tsaya na dan lokaci kadan, yanayin yan da takira sunan nasa sai yaji tam kar yau tafara kiran sunan nasa, sai yaji tam kar tafi kowa iya kiran sunan sai yaji tam yace dan Allah ta ƙara kiran sunan koda sau ɗaya tak amma ina bazai iya ba kode inc "Amar lafiya kuwa kake yaƙara jin muryar ta a karo nabiyu wan da tasa tsikar jikin sa tashi "Bako mai walhi ina tinani wani abu ne. daddy ne yafara tashi yace musu sai da safe, shima Ali yabi bayan sa. Bayan ɗan wasu dan lokaci shima Amar ya tashi da niyar tafi sai kawai yaji Abdul yace jirani mutafi, sai da ya kama hannun ta ya man na mata kiss sannan suka tafi shida Amar izuwa ɗakin kwanan su. daddy da Ali basuga lokacin da yayi mata kiss ba, sai ganin lokacin da Amar da Abdul suka shige ɗaki daɗaya ita ma Basma tashi ga ɗaki. Daddy zama yayi a ƙasa daɓas zaman yan bori, Sannan yace.. Walhi ta tabbata basa zaman lafi naga ni da idona, Ali ne ya ɗaga shi domin su shiga ɗaki sayi maga nar a cen. Ali yace...Yan zu Yaya menene abun yi? Cikin fishi daddy yace.."babu abin da zai hanani raba auran nan, ita kadai Allah ya bawa yaya na kuma namasa alƙawarin zan ri ƙeta amana. Amma yan zu in zo in mata auran dole to wallahi bazata saɓuba. Daddy yace... Yan zu kasan me zamuyi? Ali ya ce.. "A'a ban sani ba, amma ga wata da bara Daddy yace.."ina jinka Ali yace..."gobe idon Allah ya kai mu zan ce mata haƙorina yana min ciwo, Kaga zata ce muje asibitin ƙawar ta wato LUBNA tin dade ance itama anan tayi aure kuma har tasamu ai ki a cikin asibitin, kaga idan mukaje sai mu tam bayeta waye wan da Basma takeso a baya kaga in ta gaya mana mukuma sai mu nemo shi, Amma fa kar mu bari Basman ta sani sai de muyi mata bazata, kaga in a ka samo shi sai kawai a'raba wannan auran sai mu aura mata wance. Kaga in a kayi haka shikenan kar muje mu rasa ta. Cikin jin daɗi da wannan maganar daddy yace haka za ayi kaga kuwa in mukayi haka kowa ya huta. Ahaka zuka tsyar da maga na, Sai a lokacin han kalin daddy ya kwanta. *YAU TAKE RANAR LITININ* Bayan sun karya ne Abdul ya tafi office. Ali ne yasamu Basma ya tsa ramata duk yan da suka tsara jiya da daddare, ita kuwa Basma tace... "Allah sarki Allah ya bada lafiya, yan zu kun san wani assbitin ne wan da zakuje na hagori? tana tam bayar su, dede lokacin Amar yafito shima "a'a bamu sani ba zade muje muyi tam baya, da sauri Basma tace..."A'a basai kun jewani kuriba ai Lubna ta nann a garin nan kuma likitan hakorice saboda haka bari in baku Address ɗin ta, haka kuwa akayi bayan ta basu sai kuma ta kallin Amar tace... Amar kaje karaka daddy kaga kai ma sai ku gaisa da Ita, Kafin ya bata Amsa daddy yace masa? yau bazaka je gurin ai kin babe? Amar yace..."Eh yau babu da ai ki "tom muje sai katuƙamu a motar, haka babu musu ya kama hanya yana tafiya yana kallon ta har suka fita daga gidan. Amar ganinn Ali ya cire abin da yasa daga gefen bakin sa ne. wan da yasa baki ya kum bura Alamar ciwo, amma yan zu yacire shi ya yar, hakan ne yasa Amar tam bayarsa, Dama ba ciwo bakin naka yakeyi ba, amma kuma zamuje assbiti? Amsar da Alin ya bashi ne yasa kam motar kufcewa daga hannun sa . Da sauri daddy yace..."kai lafiya kuwa karfa kaje kayar da mufa cikin tsoro daddy yake maganar. Amar ne yace..."me kace yana ƙara tam bayar Ali? Ali yace.. "Eh zamu je mu samu ƙawar ta Lubna zamu tam baye tane shin wanene wannan saurayin nata domin muna raba auran shi zamu aurawa, tin dade babu wani abu da yake shiga tsakanin su kaga basai tayi wannan abun da mata sukeyi in an sakesu ba. cikin in i'na Amar yace... Amm wato dama amm kasan fa amm walhi, yanyi yana sosai kai dede lokacin da suka iso assbitin. Amar yace.. Daddy bari in zo muje Daddy yace..."A"a bari kawai jiramu muna fitowa. Amar in han kalin sa ya gama tashi yanzu shi kenan asirin sa ya tonu, shi ai ba tahaka yasu ayi ba, har ya gaji da tsyawa ya koma cikin mota sai gashi nann sun fito, suna fitowa yaga tuk ran su a ɓace kuma sun zuba masa ido.......✍️📝 🤣🤣🤣🤣 *Kai walhi abum ma abun dariya wai shin meye Lubna tace musu ne?* End of part 1️⃣3️⃣ To be continue... Pls comment and SHERE ~BY S REZA~