[5/7, 10:31 AM] S REZA ✍️: 🤷‍♂️ *ADDININMU* 🤷‍♀️ ( *By S REZA* ) ☀️ * *BISMILLAHI RAHAMANUN RAHIM* *ADDININMU* *PAGE* 👉0️⃣1️⃣ (Labarin ya fara kamar haka) Kai gaskiya innah wallhi masu kud'i suna hutawa suna jin dad'in su, kinga gidan da mukaje jiya kuws? Wallhi nidai idan na mallaki wannan gidan to nida talauci guma har a bada, yayi can nikuma nayi nann. Innah ta kalleshi cike da gajiya da wannan surutun nasa Ta ce "To dame zakayi kud'in ance kanemi aikin gomnati kace kai badomin aikin gomnati kayi karatuba, to a haka zakayi kud'in? Kuma ance kafara zuwa kasuwa ka ce kai bayanzu ba, kazama daga wancan gidan sai wannan anya kuwa rayu zata yu a haka Abdul jabari? Abdul jabar wanda ya komar da sunan sa izuwa A J ya ce "Innah aikin gomnatin ne babu wani samu, nikuma da nakeso na zama shahararran mai kud'i a cikin garinnan sai kawai naje na kama aikin gomnati!! Ya ci gaba da cewa, yanzu fa a cikin wannan 'kasar tamu idan ana lissafin masu kud'i bazaki ta'ba jin sunann ma'ai kacin gomnati ba saide Yan kasuwa sabo da haka ni kasuwanci zanyi, kuma ki jira lokaci... Kinga yanzu innah bari na miki misali, yanzu a ce nasamu ai kin gomnati ace ana biyane dubu hamsin, to acikin wata d'aya menene dubu hamsin zata mana, mu uku? Kinga ga kud'in makarantar Nana ga kayan sawa ga abin da zamuci. Sannan ba lallai bane bafa a biyani dubu hamsin d'in, amma in kasuwancine a rana d'aya ma Sai na samu dubu d'ari uku wallhi, to kinga Mai a keyi da wani aikin gomnati, Innah ta kalleshi cikin mamaki ta ce "yanzu Abdul jabaru kana ba d'an kowaba kake irin wannan lissafin wallhi kaji tsoron duni da mutan cikinta, ka rage son gud'i dayawa, yanzu abokankama da kuka taso duk ka zubar dasu saboda tsabar alfaharin ka na banza, kaje kana abota da Yayan manya, yau kaje gidan su wannan gobe gidan su wannan, anya Abdul kana tsoran wula'kancin mutane kuwa? AJ ya ce "To innah in banda abinki yaza'ayi ina talaka kuma nayi abota da y'ay'an talakawa haba ai abumma sam baiyi dai-dai ba...kinga in Nana ta dawo kice ta shanyamin kayannan ana kirana. Kafin inna tayi magana har ya tashi daga zaunan da yake ya nufi d'akin sa ya ciro wayar sa daga caji yana mai ciro wata jallabiya ya d'ora a kan kayan da suke jikinsa kafin ya kalli in na ya ce "Inna watarana sai labari amma dai tabbas zanyi kud'i in Sha Allah. Innah ta ce "Nidai bazan dena maka addu'a ba Allah ya shiryamin kai domin ni harga Allah ina tsoron wannan shegen son kud'in naka ya jefaka a damuwa. A J kuwa yana fita ya hangota a gefen gidan su tana tsaye tana waige-waige kamar mara gaskiya, yana hangota yaji wani sanyin dad'i domin kuwa yasan an dace. da sauri ya 'karaso gurin ta yana mai washe baki, kafin yayi magana ta kamo hannun sa suka shiga cikin wani lungu, ta ce "A J I don't get the money. Kallon yayi da kyu ganinn irin shigar da ke jikinta daga ita sai riga mai siririnhannu sai wando jins wanda ya tsaya mata iya cinya, kana kallon shigarta kasan ba musilma ba ce, cikin jin haushi ya ce "what are you saying? "ai see idont have the money, jin haka yasa AJ juyawa zai bar gurin tayi saurin sake kamoshi ta ce please AJ listing to me? Kallon ta yayi cikin muryar Hausa domin kuwa yasan baji takeyi ba ya ce "in bandama ina son kud'i Mai zaisa na dinga tsayawa da ke kidubi irin shigarki in wani yazo hucewa ya gammu a haka ai shikenan, baride na samu abun da nakeso a gareki wallhi bazaki sake ganinaba. Zarah ta ce "What are you saying? Ya ce "no is not you. Nann take suka fara magana cikin turanci domin kuwa ita bata jin Hausa ko zo in kashaka bata saniba. Zahrah ta ce "AJ saura kad'an Daddy ya kamani kuma nasan yanzu yasan nice nake sata masa kud'i, kuma duk kaine kake sakani. A J cikin rashin tsoro ya ce "kinga ni in bazan samu ba kawai a bar maganar kuma daga yau bani babu ke, na ce miki waya zan sake tawa tayi 'karama mutane suna rainani, yanzu a ce ina da ke amma ina ri'ke irin wannan wayar! Ganinn ransa ya b'aci ne yasa zahrah ta ce "please I'm so sorry I well bring the money for you tomorrow, tafad'a kamar tayi kuka. Tabbas zahrah tana son A J sosai hakanne yasa bata son 'bacin ransa, yayinda shi kuma domin kud'in iyayenta ya keson ta yana amfani da itane kawai domin samun kud'i. da sauri ya ce "Yawwa ko kefa, ta ce "To kayi dariya? Ai kuwa nann yayi dariya tazo da gudu ta rungumshi tana cewa I love you so much my A J, shikuwa bai amsaba sai son ganinn ya cireta daga jikin sa ya keyi. Zahrah kuwa tana zuwa gida ta shiga tinanin yaza'ayi ta samu gud'in nann ta kai masa gashi Daddy na gida. Haka ta tashi ta nufi d'akin Mommy cikin sand'a amma tana zuwa taga Mommy na zaune tana cin uban 'kwalliya kamar wata amarya, komawa tayi da baya ta shiga d'akin Daddy ai kuwa ta samu yana barci. Gurin da tasaba d'aukar kud'in ta nufa cikin sand'a kana ganinn ta kaga mara gaskiy. Wani 'karamin kurido ne a kasan drowan kayan sa, nann take Zarah ta fara jawoshi a hankali ai kuwa tana zarowa taga kud'ad'e masu uban yawa wanda sun ci uban wanda take gani a baya... Ai kuwa saida ta tsorata tsabar yawan kud'in tana cikin hakane wayar daddy tafara ringtone alamar kira, ai kuwa da sauri ta tura abun kud'in ciki ta rufe ta fad'a 'kar'kashin gado wanda yayi dai-dai da shigowar Mommy d'akin sannan Kuma Daddy ma ya farka. Bayan ya amsa wayar ne ya kalli Mommy ya ce Eliza we are you going In this time? Cikin yaransu na tibi ta ce "Sorry sar yanzu I'm coming back now...ta ci gaba da cewa wai dama kana gidane baka fitaba? Daddy ya ce "okay bari nima nashirya mufita munada mitin on this time, da sauri ya shirya Mommy na tsaye har suka fita a d'akin Daddy ya kalli Mommy ya ce "Bari na 'kulle d'akin nann domin kuwa na daina yarda da kowa a gidannan kullum sai an d'auka min kud'i kuma arasa waye ya ke d'auka. Mommy ta ce "Ni kaina ana d'aukar min kud'i Kuma na tabbayi Zahrah ta ce ita ba itaba ce shima Samuel ya ce bashi bane to kaga wazamu zarga acikin su? Daddy ya ce "Samuel ne yake d'aukar kud'in in bashiba to ita zahrah me zatayi da kud'i masu yawa? Mommy ta ce komade waye zamu kamashi. Haka Daddy ya rufe gofar ta waje ya murza ki har sau uku kafin ya saka kin a aljihun...ya d'ago kai ya kalli Mommy ya ce "We zahrah? Mommy ta ce "taje gidan su Usha, ta bashi amsa tana mai rufe gidan gaba d'aya. Zahrah kuwa bayan daddy ya fitane ta zaro abun kud'in sannan ta fara d'iba Saida ta kwasa da yawa domin kuwa sunfi Wanda ta saba d'iba a baya, sannan cikin sassafar tayi hanyar fita daga d'akin, tana zuwa taji 'kofar a 'kulle, ta buga amma taji ko motsi batayi, nann fa ta zubar da kud'in a gurin ta fara rusar kuka. *KANO STETA* *ZAINAB AMBATO* Shahararriyar mawa'kiyar Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce tayi fice sosai a harka yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s, wacce kowa yasan da zamanta a wannan 'kasar tamu domin kuwa tana lokacin ta. Kallon wani video da abokin takun sa'karta yayi nayau Wanda yake caccakar bidi'a da kuma masu yinta takeyi, kallon sa takeyi ganinn yanda ya dage yana bayani akan wa'kar da ta sake jiya, cikin tsananin b'acin rai da jin d'acin abun da yake furtawa ta ce "Yau kuma wanann mutumi harda cikin mutunci a cikin baton nasa!! Kafin tayi magana taji ya sake cewa... "Al'umma wallhi ku guji ai kata bidi'a kuma ku guji masu ai katata, jiya naji wata daga cikin su ta saki wata sabuwar wa'ka, tana cewa...(bagudu baja dabaya kan 'kwanar shehu maulansu). Ya rera wa'kar cikin bar kwaci, ai kuwa nann take Jamar gurin suka kwashe da dariya sannan ya ce "kutsaya kuji, dan Allah wannan begen annabine kodai begen wani? Nann take suka amsa da cewa begen wanine... Kafin ya sake magana Zainab ta kashe wayar cikin tsananin b'acin rai tayi hurgi da wayar tana maijin d'acin abun da yake mata. Tashi tayi ta bar d'akin ta nufi d'akin mahai fiyar ta kamar zata kamar zata tashi sama. Da sallama ta shiga d'akin kamar yanda ta saba, amma taji ba'a amsa mata ba, hakanne ya bata damar shiga cikin d'akin, tana shiga ta tarar da ita tana sallha sai kawai ta juya izuwa d'akin yayan ta, ai kuwa tana shiga ta tararr dashi shima yana kallon wannan video d'in, cikin sauri ta isa gareshi ta ce, "Isa kaga abun da wannan gayan ya sake min ko? Ni bansan mai na tare masa ba, ni bana shiga har karsa amma shi kullam yana bibiyata, in anyi magana ya ce shi Wai mau ilimine, cikin 'bacin rai ISA ya ce "to Ina ilimin yake a nann mutum kullum saide ya tara mutane yana cin zarafin wasu saboda basa bin gungiyar su, in anyi magana kuma suce wai su sunnha sukeyi haka sunna take? Isa ya ci gaba da cewa "wallhi wannan yaron haushi ya ke bani, mutum Dan Allah ya baka ilimi sai kuma ka dinga kallon kowa a banza! in ilimin nanne yasan mun sha kansa domin yaje yayi bin cike a kan wannan gidannamu. Zainab ta ce "Sai su dinga fakewa da cewa mu yan bidi'a ne sukuma yan sunah, Kuma sune suke ai kata bidi'a d'in a bayan 'kasa. Isa ya ce "yanzu to yaza'ayi? Ta ce "Nima zan fara mayar masa da martanine domin in ba hakaba bazai san cewa nima niceba. Cikin jin dad'i ISA ya ce "toma wai meye wannan yaron zai nuna miki in banda dogon gemu kamar bunsuru, Zainab ta ce "Toma wai yaushe a ka san dashi? Shifa albarkacin mahaifin sanema yasa jama'a suka san dashi amma har zaizo yana min habaici to wallhi ina dai-dai da ubansama ba shiba. Haka dai ISA da Zainab suka dinga zagin sa saboda abun da ya musu. *ABDALHA* Cikin tsananin b'acin rai yake kallon 'kanwar tasa cikeda jin aushin abun da tayi ya ce "Waye wannan? Itama cikin dubur-burcewa ta ce "Shine wanda nake fad'a maka zai zo gurinka tin..."tin kafin ta 'Karasa ya katseta da cewa... "Wannan d'an bidi'ar zaki kawo mana gida kice wai shine zaki aura!? Bakiji abun da nace mukuba ko Maryam ta ce "Yaya wallhi bad'an bidi'a ban... "Zakimin shiru ko saina fasa miki baki yanzunnan? Abdullha ya kalli Maryam ya ce "Dabansan ko shid'in wayeba da saiki min 'karya, to bari kiji wannan yaron har ubansa na sani saboda haka daga yau bake bashi karna sake ganinn ku tare kinji na fad'a miki ko?. Ta gyad'a masa kai sannan ya bar d'akin cikin 'bacin rai. Maryam kuwa cikin kuka ta nufi d'akin mahaifiyar su domin sanar da ita komai, tana zuwa ta tararr da sauran Yan uwan nata dukkansu a gaban maman nasu suna d'aukar karatu hakanne yasa ta share hawayenta itama tabi layi domin kuwa tasan babu wanda zai kulata har sai in sun kammala karatun. Abdullha kuwa part 'dinsa ya nufa yana jin mamakin taurin kai irin na Maryam, duk cikin 'kanyansa tafi kowa taurin kai ga rawar 'kafa ba kamar Sadiya da Nusaiba ba. Cikin zuciyar sa ya ce "ni na had'a jini da yan bidi'a a'a bata isaba akan wannan maganar zan iya mugun 'bata mata rai sosai. *ZAINAB VOP* Da sauri ta shiga gurin Mama lokacin ta idar da sallah hakane yasa ta kwashe komai ta sanar Mata abun da abdullha ya sake mata, Mama ta kalleta ta ce "Zainab ke mace ne shikuwa na mijine kinga in kina biye masa zaku zubar da girmanku a gurin al'ummar garine dukkanku, gashi kuma dukkanin ku jagororine a gurin al'ummar ku saboda haka kibarshi karki biyewa wance yayan naki mai zigaki.....📝 _ *PAGE* 👉0️⃣2️⃣ ......... Zainab ta ce "To yanzu Mama haka zan barshi ya cigaba da cin mutuncin mu al'halin kuma duk abun da yake fad'a 'karyane!? Mama ta ce "Zainab karki bari malam yaji zancennan domin kinsan Shima baya 'kaunar su, saboda haka kibar komai a gurina, kinga yanzu in kika biye masa al'ummar gari zasu samu abun fad'a dukda dama batin yanzu akasaba jin kanku dashiba, dukda ke ba beye masa kikeyiba, yanzuma kiyi haguri karkice komai kiyi abun dake gabanki... yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s ne kuma babu Wanda ya isa ya hanaki domin kuwa da albarkar uwa da uba a kanki, kuma ga soyayyar Nana batula 'Yar manzan Allah wanda shine silar saninn ki da al'umma sukaye, kinga ko iya haka ai kinci riba sosai ko? Cikin jin dad'i Zainab ta ce "Sallahu a'lahi wasallam, tana mai shafa wa a fuskarta, sannan ta shiga rera wata 'kasida da tayiwa Nana fad'ima Yar ma'aikin Allah Mai taken *(NANA YAR MA AIKI UWAR GIDAN ALIYU SADAUKIN DA FAYA TSORO.* ) *A J.* VOP Yana shigowa gidan ya tarrar har nana ta gama shanya masa kayan sannan ta 'dora musu girki, Yana shiga ciki inah ta ce "Wai Abdul jabaru meya had'a ka da wasu mutane yanzu suka turo wai ana neman ka? shine na tura Nana kadija akan ta dubo, tazo tacemin Wai wani saurayi ne a cikin mota! Kafin Innah ta rufe baki Nana ta ce "Yaya wanine yazo Wai yace min in kazo nace maka sunan sa salis yazo bai gankaba ka sameshi a gida. Da sauri AJ ya ce "Wa kikace? Nana ta sake cewa "Wai Salis. Ai da sauri AJ ya rungumeta yana cewa "Innah in Sha Allah arzi'ki ne yake kirana, ina wannan gidan da nake baki labarin cewa in na mallaki gidan nahuta, tofa yaron gidanne ranar juma'ar da ta huce muka had'u dashi to shekaran jiya ya gaiyaceni gidansu har mukaci abinci, shima baban sa ya rasu daga shi sai 'kanwar sa sai mamarsu agidan Wallhi Innah in kiga ga gidan sai kin godew Allah!. Innah ta ce "Auda bana gode masa har sai naga gida? Ta cigaba da cewa "wallhi Abdul jabaru kari'ke maraicin ka karka dinga saka kanka a gurin da Allah bai sakakaba, i'na kai i'na abota da d'an masu kud'i har kana fad'a. AJ ya ce "Yanzu Innha dan Allah kallemufa? yana ri'ko hannun Nana yana cewa... Yanzu dan Allah Innah munyi Kama da y'ay'an talakawa, ai wallhi ko daga gani kinsan huce nann, Koda mud'in bamu da kud'i amma ai Muna Kyu ko, saboda haka mude ki dinga mana addu'a kawai. Innah tayi salati ta sanarwa da uban giji kafin ta ce "To dan gidan ku kyu d'in da kake alfahari dashi ai duk nawane shima uban naku ai ni ya gado kukuma kuka gajeshi, Kai Allah dai ya ji 'kan Rabu'u!! Tafad'a kamar tayi kuka. Duk suka amsa da amin. Sannan Nana ta ce "Yaya sabulun wankanafa ya 'kare ga kuma a islamiya ance a kawo kud'in wata? AJ Ya kalli Innah ya ce "To kingani yanzu da bana tare dasu a Ina Zan samu wannan kud'ad'an. Nifa wallhi Inna duk wata sana'ar da zata kawomin kud'i Zan iyayi domin Naga na inganta rayuwar Nana da kuma taki... Sannan kuma akan kud'i zan iyayin duk wani Abu in dai ADDINIMU bai haramtaba. Kede inna kinsan bana sata bana shaye-shaye bana neman mata, duk abun da kukaga inayi to nasan menakeyi. Karatunnan fa nayi, nasan dai-dai da kuma a kasin hakan, shima wannan d'in da yake kirana aiki zan samu a gurinsa shine yasa. Innah tayi shiru tana tinani tabbas abun da yafad'a hakane, baya sata sannan Kuma komai na rayuwa shine yake musu daga ita har Nana d'in, Yana yin duk wata sana'a in dai zata rufa masa asiri. Bata mantawa, yayi san'ar okada, yayi yaron mota, yayi jiran shago ya iya d'in ki, ga ya ta'ba zama Dreban wani mutumi Kuma duk saboda su, to amma abun tambayar ba kullum yake zuwa aikiba kuma kullum baya rabuwa da kud'i, in na tambayeshi yace sana a yayi. Tana cikin tinani taji Yana cewa, yanzu in naje gurin sa zan samu aiki wanda daga yau mun daina cin tuwo a gidanan , ya kalli Nana ya ce "kilissafa min duk abun da kikeso in nadawo zan siyo miki, cikin murna Nana ta sake rungumshi tana ji kwanar yayan nata sosai, ta ce "Allah ya dawo da Kai lafiya Yaya. Itama Innah ta ce "dan Allah kadinga tinawa damu tik inda kashiga karkabarmu. AJ yace karki damu Innata abar alfahari na. Yana fita ya tuno da Zahrah sai yayi dariya ya ce "In banda mahaukaciya ina ta ta'ba jin ana aure tsakanin musilmi da arne! Wai ita aure takeso muyi, baride na gama samun Yan canjina na barki da nemana. Yanzufa wannan yarinyar ta satomin kud'ad'e sunfi dubu d'ari shida, anya kuwa in baban ta ya kamata bazan shiga damuwa ba!? Sai kuma yace kodan ai tana sona bazata ce nine nake sakataba, kumafa babanta soja ne! Ta'b gaskiya rabuwa zanyi da yarinyar nann Yasin kafin ta sakani a matsala, haka ya tare me mashin zuwa gidan su Salis, yana tinanin tayaya zai rabu da ita. *ZAHRAH* *VOP* Take ta zubar da kud'in a gurin ta shiga dukan 'kofar amma bata ko motsi, tin tana d'aukar lamarin wasa har abun yazama gaske, wasa wasa zahrah takai a'wa uku acikin d'akin amma ba wanda ya shigo gidan, nann take tafara rusar kuka domin kuwa ta tsorata sosai ga yunwa dake addabar cikinta ga tsoran abunda Daddy zaimata in ya kamata, domin kuwa tasan da cewa ta kamu. Tana cikin hakane taji dawowar su, harda Samuel da Daddy harda Mommy, da sauri ta kwashe kud'in ta mayar gurin da ta d'auka sannan ta tashi ta koma 'kar'kashin gado ta sake 'boyewa. Ai kuwa cikin sauri Daddy ya shigo d'akin yana shiga ya tsaya cak yana mai bin d'akin da kallo...sai ya nufi gurin da ya ajiye kud'in yana mai bud'e abun ya zubawa kud'in ido kamar mai son gano wani abu, sai Kuma ya koma bakin kofar d'akina yana dubawa kodai bai rufe da Kyu bane, domin kuwa Tabbas an shigo d'akinnan. Kayansa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wando na sojoji, Wanda Zahrah tana ganin sa a haka ta rufe ido cikin tsoro, toilet ya fad'a ya rufo 'kofar, ai kuwa yana shiga itama ta fito, har zata fita sai kuma ta dawo da baya ta bud'e gurin ta kwaso kud'in ta saka a cikin jins d'in dake jikinta dama ya katseta, sannan tayi hanyar barin d'akin Amma ta sake jin 'kofar a rufe. Cikin rekicewa ta saki wani ihuuu d'an 'karami amma tayi saurin toshe bakinta da hannu, sai ta hango kin d'akin a kan kadonsa gurin da ya cire kaya, nann ta d'auko ta bud'e, sai ta dawo ta ajiye da niyar fita sai daji alamar shigowa d'akin, ai da sauri ta koma bayan 'kofar ta 'boye ai kuwa Mai shigowar Yana tura 'kofar yashiga ciki yana shiga ita kuma ta sand'a ta fita, ta nufi d'akin ta cikin rikicewa, tana shiga ta boye kud'in sannan ta saki a jiyar zuciya. Samuel kuwa, yana shiga ya samu gefen gado ya zauna Yana jiran fitowar Daddy, ai kuwa yana zama Daddy na fitowa. Cikin tsananin mamaki da firgici Daddy ya ke kallon Samuel ya ce "Samuel what are you doing in may room? Kafin Samuel yayi magana ya ga durowar kud'in abud'e ga kuma 'kofar d'akin nasa ta ciki ya rufe Amma yaga Samuel aciki gakuma kofar a bud'e. *ABDALHA* *VOP* Zaune suke agaban Mommy dukkanin su, abdalh Maryam da Sadiya da Nusaiba sai autansu nura... Kallon su tayi kafin ta ce "meya had'a ka da Maryam? Cikin tsananin jin haushin abun da Maryam d'in tayi ya ce "Mommy wai wannan yarinyar d'an bidi'a zata kawo mana gida a matsayin mijin aure! Saboda ita mara kunya ce, shine harda cewa Wai in Abba yazo zata sanar masa, Mommy ta ce "Wai ni abdullha kaida babanka bansa me kuka d'auki mutanan ba, sumafa musilmai ne kamar ku, Allah mu d'aya annabin mu d'aya, littafi d'aya muke karantawa wato ALQUR'ANI mai girma, kaga kenann ADDINIMU d'aya, to meyasa don an d'an samu rebewar Kai sai ku dunga ai batasu kuna kafurtar dasu!? Kafin wani yayi magana sukaji ana cewa "Mu ba d'aya muke dasuba, domin kuwa mu bamuyin abun da Annabi Muhammad sallalahu a w s, baiyiba Kuma Allah baice a yiba, saboda haka, nidai zuria'a ta bazasu had'a jini da suba, cewar Abba yana shigowa d'akin. Kafin kowa ya sake mgn Nusaiba ta ce "Ni fa wallhi bana musu kallon musilmai domin kuwa wani lokaci in sukayi wani abun Kamar basa karanta ALQUR'ANI, . Sadiya ma ta ce "Ni Wallhi tinma ba wannan Zainab Ambato d'inba gaba d'aya 'kasidun ta babu wani tsari da ma'ana amma a haka zakika kowa Zainab Ambato Zainab Ambato. Mayarm ta ce... "Ashede kina jin 'kasidar tata da har kika san babu tsari, kafin kowa yayi magana Abba ya ce "Andullahi meya faru? Abdullha ya ce "Abba Maryam ce tazo da wani yaro Wai shi takeso kuma d'an bidi'a ne. Daddy kuwa dama yagama sakarwa abdullha ragamar gidan duk abun da ya yanke a kan 'kannennasa to yayi. Nann shima ya tabbatar mata da cewa Babu ita bashi, in auren takeso ta nemo mari'kin sunna shi zai aura mata, Yana gamawa ya bar d'akin ya nufi nashi d'akin dama yanzu ya shigo. Mommy ta kalli Maryam ta ce "mamana ki rabu dashi tindade Abbanku da yayanki basaso kinji? Kafin ta Kara'sa Nusaiba ta ce "Toma mommy in banda zubar mana da kima yaza'ayi ta kawo mana dan la'ilo tace yazama suriki a gidannan. Itama Sadiya ta ce "Allah da nagan shi da sai na gaya masa maganar da bazai manta da itaba, "Ai kuwa kema da namiki abunda bazaki manta da niba. Ina ruwanki da saurayina? Duk abun da zakuyi ku tsaya a iya matsayinku karku shiga gonar da ba takuba domin kuwa ba tsoran aji kanmu daku nakeba. Maryam tana kaiwa nann ta fito da wayarta ta Kuna qasidar Zainab Ambato mai taken *GANI ASO* , tabar su a gurin ri'ke da baki. Mommy ta ce "Nace kudaina shiga hankarta yanzu tana kan ganuwar girman balaga tanajin kanta yanzu dai-dai daku saboda haka kubarta tayi raruwarta, Kuma karku fad'a wa yayanku tana jin 'kasidar Zainab Ambato kunji? ceke da takaici Sadiya ta ce "Yasin Mommy Maryam ta rainamu, ace agidannan ana jin kad'e-kad'e Kuma kice Kar a fad'awa yaya, shida yakeyin wa'azi akan kid'a babu kyu sai Kuma a samu a gidan sa, ai dolenema yaya yaji wannan zancen, tana kaiwa ta tashi fuuu tabar d'akin izuwa nata d'akin. Mommy ta ce "Allah dai ya sa mudace, Kuma Allah ka barmu a musulumci kuma Allah ka had'a kan al'ummar musilmi na duniya Baki d'aya. Nusaiba ta amsa da amin. *ZAINAB* *VOP* Kallon yayan nata tayi kafin ta ce "Wai kuwa kasan gobe zan bogowa wancan banzan wata 'kasida mai harshen damo? Isa ya ce "Nifa Allah yaron mamaki yakebani shifa burinsa Wai ace shi ma malami Kuma wallhi bai Kai ya had'a kansa da keba, yanzu duk Wanda kacewa Zainab Ambato, d'an izalar da ma Yan 'dariqar bawanda bai San dakeba, shifa, in kace... Abdalh in dai Baki had'a da sunan baban saba Wallhi za'a ce waye haka, Koda acikin masu d'an gelallan wandonne, take suka bushe da dariya dai-dai lokacin MLM wato babansu ya shigo. Kamar yanda d'abi'ar su take ta girmama duk wani babba ta hanyar rusunawa har 'kasa sugaishi haka yanzuma har 'kasa suka rusa suka gaida MLM. Bayan ya amsa ne ya saka musu albarka sannan ya ce "Zainab d'azu su Alhaji Bashir sunce ranar JUMA'A suna gaiyatarki zaki musu majalasi a gidansu zai aurarr da yarinyarsa. Kuma na amince masa, ina fatan dai kinada lokaci? Cikin girmamawa ta ce "to MLM ai koda bani da lokaci tinda suka biyo ta hannun ka ai zan samu lokaci. MLM yayi mata godiya sannan ya ce "Saide wani hanzari ba guduba... Gidan Alhaji Bashir d'in jikin gidan wannan mara kunyar yaronnanne 'dan gidan Shek kabiru. Take isa da Zainab suka had'a baki gurin cewa, Abdalh shek kabir kenann kake nufi? MLM ya ce "eh wannan. gaskiya yaron bashi da kunya ahakan ya kurarin su malamaine Amma suna cin mutuncin mutane, nasan yanda kuke dashi saboda haka kisan abun da zakiyi. Zainab ta ce "to MLM nagode ranar JUMA'A ko? "Eh ranar JUMA'A. Sannan ta tashi ta bar d'akin ciki da jin dad'in haka, Isa dake bayanta ya ce "Ashe a gurin za'a fara jin sabuwar 'kasidar kenann? Ya cigaba da cewa "ya sunann gasidar? Itama cikin tinani ta ce "Sunann ta bud'ad'd'iyar wasi'ka...📝 *PAGE0️⃣3️⃣* .......Cikin mamaki Isa ya kalleta ya ce "Bud'ad'd'iyar wasi'ka Kuma? Zainab ta ce "Eh dama ai nace maka 'kasidar mai harshen damo ce saboda haka kaide ka saurari fitowarta kasha mamaki. Isa ya tsaya yana mata kallon mamaki domin kuwa yasan 'kanwar tasa Allah ya bata ilimi ga dogon tinani, in har ta bugo 'kasida tofa sai tayi dad'i, haka dai shima ya tafi cike da son jin wannan sabuwar'kasidar. *A J. VOP* Mai Okada bai sau'keshi a ko inaba sai 'kofar gidan su Salis. Bayan ya sallami mai mashin d'in ne ya nufi bakin get d'in gidan cike da kwarin gyiwa, yana zuwa ya bubbuga cikin 'kan-'kanin lokaci mai gadin ya bud'e. kafin A J yayi magana mai gadin ya ce "Kaine AJ ko? Da sauri AJ ya ce "Eh nine. Ai kuwa take ya bashi hanya had'i da cewa "yace in kazo ka shiga ciki. Tin daga harabar gidan AJ yake sake bin gidan da kallo sai yaga gidan kamar ya 'kara kyu, kamar ba gidan da suka zo shekan jiyaba, sai da yaje 'kofar palorn kafin ya danna abun da yaga Salis ya danna wancen lokacin kafin ya nemi guri ya tsaya kamar dai yanda sukayi wancen karan d'in. 'Yar aikin gidan ce tazo ta bud'e kamar wancen lokacin, yana shiga ya hango Hajiya zaune a d'aya daga cikin kujerun dake cikin palorn, da sauri AJ ya fara kwasar gaisuwa. Hajiya ta amsa sannan ta ce "Tashi daga 'kasa ga guri ka zauna, babu musu ya zauna yana kallon hanyar da zaiga Salis ya fito. Hajiya ta ce "Salis baya nann dama nice na sa ya kiramin kai, tin ranar da na ganka agidannan kaida my son naji ina son in d'aukeka wani ai ki mutu'kar zaka iya? Cike da mamaki AJ yake kallon hajiya kafin ya ce "Hajiya ni in dai zan samu kud'i kuma ADDINIMU bai hana ba Wallhi ko menene zanyi. Cike da jin dad'i hajiya ta ce "Ok tom kazauna cikin shiri nann da wani lokaci zan fad'a maka wani irin aikine zakayi, kuma zaka samu kud'i sosai domin kuwa in har ka yarda to daga ranar bakai babu ta lauci. Jin abun da hajiya ta ce ne yasa AJ cewa "To hajiya a fara sanar dani aikin mana tin yanzu sai na fara shiri? Hajiya tayi dariya tana kallon sa cikin burgewa ta ce kar ka damu yanzuma kanada wani babban kaso daga cikin kud'in aikin na ka ina zu. Hajiya ta me'ke tsaye ta nufi d'akin ta, shikuwa sai bin ta yake da kallo har ya daina ganin ta. Ai kuwa take ya saki wani dariya yana cewa "kai Yasin AJ ni na daban ne, irin wannan farinjini hk! Yana cikin hakane hajiya ta dawo. Ta mi'ka masa bandir din yan dubu-dubu guda d'aya wato dubu d'ari kenann. Cikin rikicewa AJ ya ce "Haji hajiya Wann wann Wannan nawaye? Hajiya ta ce "Ko baka sone? "Ina so wallhi inaso sosai makuwa. Kai hajiya na gode sosai Allah ya saka da alkairi. Amma hajiya wannan wani irin aikine? Hajiya ta ce "Aikin bashi da wani wahala kaide ka zauna cikin shiri. "Ai kuwa hajiya a shirye nake wallhi. Haka AJ ya bar gidan cikin tsan-tsar farin ciki, kasuwa ya fara zuwa ya musu siyayar kayan sakawa shida Nana da innah kafin ya tsaya a gurin mai kaza ya seyo musu ko d'aya, yaje ya siyo musu yourgot kafin ya nufi gida cike da farin ciki. *ZAHRAH*. *VOP* Fitowa da kud'in tayi ta girga taga dubu d'ari harda tara, aikuwa ta bud'e baki da hanci tana mamaki me yasa ta d'ebo da yawa, take ta saka a cikin jakar school d'in ta, sannan ta shiga toilet ta watsa ruwa gamida sau'ke abun da ta tara a cikin ta tsabar far gaba. Riga da wando ta saka na Adidas sannan ta nufi kiching domin samun abun da zata ci, tana shiga tayi karo da Mommy a ciki tana had'a musu abincin yamma. Cike da mamaki Mommy take kallon ta, cikin yaran su Mommy ta ce "Daga ina kike? "Mommy nadawo tin d'azu zan shiga gida naga kun rufe gidan shine na koma sai yanzu nadawo. Mommy ta bud'e baki zatayi magana taji muryar Samuel a d'akin Daddy yana ihuu ai kuwa suka nufi gurin da gudu. Cikin fushi Daddy ya ke cewa "I see wer is my money? Samuel na kuka yana cewa "Daddy banine na d'auka ba Allah nima yanzu na shigo. Mommy ta shiga tsakanin su sannan ta mi'kar da Samuel ta ce "Samuel what happened? "Mommy I don't no. Ta juya gurin Daddy ta ce "What happened? Cikin fushi Daddy ya sanar da ita komai, sannan ya d'ora da cewa... "Dubu d'ari harda wani abufa ya d'auka. Mommy kuwa ta ce "Amma kuma ai tare da Samuel muka shigo gida, kuma kace ta ciki ka rufe 'kofar d'akin naka, to tayaya Samuel zai iya shiga? Kafin Daddy yayi magana Zahrah ta ce "kokuma Daddy bai rufe 'kofar d'akin da kyu bane shine Samuel d'in ya shigaba. Ai kuwa Daddy ya ce "Yes of course hakane ma. Samuel ya harareta yana jin kamar ya kamuta ya fara tattakata. Mommy ta ce "No inda shine da bazai zauna a d'akin ba tafiya zaiyi. DADDY ya ce "Ya tashi ya dawo masa da kud'i kafin yasa sojojin waje su karkaryashi, Samuel de sai kuka yakeyi, shikuwa Daddy ya kafe akan dole shine ya d'auka. Zahrah kuwa take taji ta daina jin yunwar tsabar tsoro, Daddy baya dukansu sai sun kaishi bango, yanzu da ita ya kama haka zaitama wannan dukun! Sai kuma ta fara tinaninn shimafa Samuel d'in tasan dole sukwaso riki dashi in ya warke. Take Kuma ta tuno da rabin ran nata tana jin in ta kai masa wannan kud'in ai za'a daina renashi tin da zai siya babbar waya. Take ta nemo number sa ta ai ka masa da Kira. *ABDULLHA* *VOP* Da sauri ya 'karasu gurin Abba yana mai d'an du'kawa kad'an ya ce "barka da yamma Abba gani?. Cikin sanyin murya da ta Saba da karanta ALQUR'ANI mai girma Abba ya ce "Abdullha kaga yanzu mutane suna ta magana a kanka akan zaman ka haka, kasan ba mutum baya cika mutam har sai ya ajiye iyali, yanzu fa kai ba 'karamin mutum bane, duk in da kashiga a 'kasar nann ansanka, kai harma wasu 'kasashien, kuma kaga kai ne mai yiwa mutane wa'a zi a kan aru'ke sunna a bar bidi'a, Amma kuma kai bakayiba shin hakan zai yu kuwa?... Saboda haka abun da nakeso dakai shine kafitar da wacce kakeso ka yi sure domin al'umma su sake ganinn ka da kima. Abdullha ya dubi mahaifin nasa ya ce "Gaskiyane Abba, amma Abba duka-duka shekarata nawa da har zan fara maganar aure? Shekara tafa 26 zuwa da 27 Amma Zan fara zancen aure. Abba ya ce "Abdullha ka duba matsayin ka ba shekarunka ba, yanzufa mutane masu shekara. Arba'in ma girmamaka sukeyi, saboda haka nidai yanzu umarni zan baka akan ka fitar da wacce kakeso a cikin wannan shekarar. Abdullha ya ce "Tom Abba tindadai kace umarnine in sha Allah Zan fitar. Abba wato shek kabiru kabuga, malimin sunna wanda yayi suna wajan ru'ko da sunna a fad'in duniya, wanda tin yaronsa wato abdullha Kabir yana 'karami yake tafiya dashi duk in da zashi kuma yake ja masa a'ya awajan wa'a zi. Har take yanzu shima abdullha yazama jigo ga al'umman dake tare da ma haifin nasa. Abba ya saka masa albarka sannan ya tashi ya tafi. Abdullha kuwa gidan sa ya nufa yana shiga ya fad'a toilet yayi wanka sannan ya zauna ya fara rera karatun ALQUR'ANI mai girma cikin muryarsa mai sanyin dad'i, saida yayi izufi biyar (5) sannan ya shafa addu'a kafin ya zauna ya shiga tinanin maganar Abba... To ni yanzu daba soyayya na keyiba ina ni ina wata budurwa! Nann take Aisha ta fad'o masa a rai, amma yayi tsaki yana cewa, wannan yarinyar batada kamun kai, haka dai ya dinga tufka da warwara, harma yayi banza da maganar ya kama har kokin gaban sa. Take yatina da cewa abokin safa ya gaiyace shi gurin bikin sa, amma ba wa'a zi zaiyiba zaije gurin walimar ne, walimar da uwar amaryar ce ta shirya, haka ya tashi ya shirya domin halartar gurin, kafin lokaci ya 'kure, domin kuwa abdullha yana kiyaye Al'kawari. *ZAINAB*. *VOP* Washe gari ta shirya tsaffff domin zuwa wani taro biki da a ka gaiyaceta zatayi qasida a gurin, Saida taje gurin Mama suka gaisa, sannan ta ce "Mama ina Aisha ne? Mama ta ce "Sun fita da Isa wai zata rakashi kasuwa. "Ok tom mu zamu je majalisi sai an jima zamu dawo, nann take Mama ta saka mata albarka sannan tamusu fatan nasara kafin ta fita, tabi d'akin mlm shima yasaka mata albarka kafin ta fita. Tana zuwa waje taga halifiyar tata wato Maryam wacce duk wani taro ko mauludi in an gaiyaceta to tare suke zuwa, wani lokaci ma in Bata da time ita take turawa. Maryam tazama tamkar 'kawace ga Zainab sannan kuma yarinyar ta. In ana cikin hadaya na yabon Annabi Muhammad sallalahu a w s, girma take bata sosai, in kuma a zahirine ko a gida, zaka gansu acikin wasa da dariya. Haka suka tafi cikin wasa da dariya. Suna isa gidan, matar da ta kirata tazo da gudu ta rungumeta tana kuka cike da mamaki wai yau gata ga Zainab Ambato. Ta ce "Zainab Ambato wallhi na kasance duk anguwarmu nafi kowa son ki da 'kasidunki, domin kuwa duk wata sabuwa gasidar ki in tafito sai na d'auko ta, tin kafin yarinyata ta samu mijin aure nayi Al'kawarin sai na gaiyatoki walimar auran kuma, gashi Allah yayi. Matar harda kuka, yayin da yarinyar matar ma tazo ta rungumeta sunata saka mata albarka. Ita kuwa Zainab Ambato me take in banda mamaki cikeda farin cikin ganinn irin wannan tsan-tsar soyayyar. nann fa al'umma maza da mata suka fara murnar ganinn ta sai zuwa sukeyi ana hoto. Da kyir aka samu a ka barta ta fara gabatar da majalusinta. Nann fa duk 'kasidar da ta fara sai kaji muryoyin al'umma tamkar sune sukayi, haka zatayi shiru al'umma sunayi kuma basa mantuwa, uwar amarya kuwa babu kunya ta ce yau ranar farin cikin tane, tafara rera 'kasidar Zainab Ambato kamar ita tayi. Ana cikin hakane a kazo kan 'kasidar da ta saka kwanannan wato *GANI ASO*. zokaga al'umma. Ana cikin ha sai ga ango da abokansa... Angon shi kad'ai ne sai mutum biyu acikin abokannasa... Kana ganinn su kaga malamai aikuwa nannn al'umma suka hango Shek abdullha d'an gidan Shek kabiru kabuga. Nann fa suka fara mamakin mai ya kawoshi nann bayan bayason wannan wa'ke-wa'ken, tin daga nesa suka fara jin muryar mutane ana jin wa'kar Gani aso, dai-dai gurin da take cewa, ( *narantse da ilahumma ma'aiki bani da wani wanda nakeso ya maa'aiki Allah shine masanin zuci da baki, sanda nakemassa masoyin sa ma'aiki)*. Nann take abdullha ya tsaya agurin ya kalli angon ya ce "Salim kace min walima za'a yi agurinnan? Salim ya ce "Sorry Shek wallhi nima bansan za'a gaiyato mawa'kiya ba, "Amma ai kasan yarinyar da ganima yar bidi'a ceko? Inji abdullha cikin tsananin b'acin rai. Salim ya ce "Kaga mutane na Kallon mu dan Allah muje muzauna sai muyi magana. Abdullha ya ce nine zanje na zauna Ina kallon kad'e-kad'e da rare-rare? Salim ya ce "a'a za'a tsaya da shi yanzu please dan Allah? Saida abdalh yaga mutane sun fara kallon su kafin yabar maganar ya nufi gurin da a ka ware musu wato an kwaye. D'aya daga cikin abokin angon me suna Yusuf ya ce "Wai ita wannan yarin yar ahaka zata 'kare rayuwarta da kad'e-kad'e da rare-rare bazatayi aureba? Abdalh ya ce "To waye zai auri wannan ai rashin wanda zai aurane yasa kaganta haryanzu. Salim ya ce "Haba kau wallhi wannan da kuke gani ba matar yara bace, ai ba kowane zai iya tin karar ta da batum aureba sai de manya malamai wallhi. dai-dai lokacin da abdallha ya bud'e baki zaiyi magana ita kuma Zainab Ambato ta kai idonta gurin take idinsu ya had'u a guri d'aya, Saida sukaiwa juna kallon minti d'aya kafin suka kawar da idonsu. Yayin da abdullha yakejin mugun tsanar abun da takeyi kana take Mata kallon rashin kamunkai. Ita kuwa Zainab idonsu na had'uwa tamai kallon 'kiyayya kafin ta kalli halifiyarta ta ce "Jeki sakamin wa'kar bagudu bajadabaya, wato wa'kar da abdullha ya musu Randi a kanta jiya. Ai kuwa dama wa'kar sabuwace kowa soyake a zo kan wa'kar domin kuwa WAQAR tayiwa mabiya shehu dad'i. Ai kuwa ana sawa al'umma suka d'auka, nann take suka fara fitowa da hoton shehu Mata damaza samari da 'yan mata, ko ganinn Zainab d'in ma bakayi. Saide kaji ana cewa... ( *BAGUDU BA JADABAYA KAN 'KWANAR SHEHU MAULANA).* 📝 *PAGE* 👉4️⃣ ______________Muryoyin al'umma ne kawai ketashi agurin ana bin wa'kar kamar sune suka rerata, ita kuwa Zainab sai kallon gurinda Abdalh yake takeyi tana son ganin wani irin yanayi zai shiga. Abdullha kuwa yana ji tasaki wannan wa'kar ya kalli abokin nasa cikin tsananin b'acin rai ya ce "Nagode da abun da kamin sannan kuma in harkana so na cigaba da zama anann to sai an kori wannan mawa'kiyar. Angon ya kalli Abdalh sannan ya ce "Haba Shek abdullha kasanfa banine na gaiyatotaba uwar amaryar ce, kuma tana gurinnan kaga kuwa banida ikon korarr ta. Abdullha najin haka ya mi'ke tsaye ya bar gurin cikin tsananin jin haushin abokin nasa. Tin da yake ba'a ta'ba cimasa fuska irin wannan ba, wato saboda ta ganshi agurin shena tasa a ka sake Mata wannan wa'kar ko!!? Haka Abdalh ya dawo gida cikin tsananin jin haushi, dama mukullen mutar na hannun sa, sai kawai ya tafi yabar su. Duk abun dake faruwa a kan idon Zainab, dama tasan bazai zaunaba hakanne yasa tayi amfaninn da wannan damar ta kore shi. Bayan ta gama rera 'kasidar ne kuma ta koma wa'a zi a kan zaman aure tsakanin ango da amarya. Tana musu tini da irin zan auran Nana fad'ima Yar ma'aikin Allah .s a w. Yanda tayi ha'kuri agidan mijin ta, sannan tamusu tinida da, rayuwar manzan Allah da yayi da iyalan sa, haka dai Zainab ta dinga kawo musu abubuwa da manzan Allah yayiwa matansa. Daga 'karshe ta rufe da salatul fati. Abokin ango da ango sai mamaki sukeyi ganinn yanda ta dinga fad'ar irin abubuwan da ma'aurata ya dace da suyi domin koyi da sunnonin Annabi Muhammad sallalahu a w s azaman aure. Haka mutane suka dinga mata ihisani harda ango da kansa saida ya mata, haka uwar amarya ta rasa inda zata sakata tsabar murna. *A.J POV* Da sallama ya shigo gidan baki har kunne, ba kowa a tsakar gidan hakanne yasa ya sake doka wata sallamar, dai-dai lokacin Nana ta fito daga wanka, ta amsa sannan ta tsaya da bokiti a hannu tana kallon ledodin da suke hannun sa, cikin mama ta ce "Yaya wannan kumafa daga Ina? "Kafin ya bata amsa Innah ta fito daga cikin d'aki tana cewa "lafiya kuw... "Lafiya lau Innah kawai taga abun da bata saba gani bane shine ta tsaya sai tayi surutun nata da tasaba. D'akin Innah ya huce yabarsu tsaye suna kallon sa. Ya ce "Innah wallhi mugodewa Allah domin ni mai sa'a ne! Ya shiga fito da abubuwan da ya siyo , dai-dai lokacin Nana ta iso gurin bayan ta d'aura hijjabi a kan tahul d'in da tafito dashi daga wanka. Ganinn doguwar riga Amaya ne yasa ta d'auka tana cewa yayana amma wannan tawace ko? A.J ya ce "Ai Nana daga yanzu mun fi 'karfin irin kayan da muke sawa a baya duk kyatar dasu zakiyi kifarasa na zamani. Cikin tsananin mamaki Innah ta ce "Yanzu Abdul jabaru bazakamin bayaninn yanda kasamu kud'ad'an nannba, har sai na tambayeka? Cikin farin ciki A.J ya ce "Innah amma ai tinkafin na tafi na miki bayani ko? Kuma kinsande A.J baya sata, saboda haka kawai kimanta da komai Allah ne ya dubemu. Haka dai Innah tayi shiru domin kuwa tasan tinda yace to hakane, nann fa Innah ta shiga cin kaza ba kwa-kwatawa, haka suka kasance cikin farin ciki wannan ranar. Bayan komai ya kammala ne ya d'auki wayarsa yaga kiran Zarah, saida yaja tsaki sannan ya kirata yana cewa, yarinya yanzu kuma ai nahuce ajinki, nasan yanzuma zakicemin ba'a samu bane, kuma ke ya dama. *LA'DIFA. SALIS. POV* Da gudu ta fito daga cikin palorn gidan nasu tana mai kirin sunann mai gadin nasu tamkar ita ta rad'a masa. IRO!... IRO!... IRO!... Wanda shikuwa iro tin kiran farko ya taso daga sallamar sallha da yayi ya fito da gudu yana cewa "hajiya karama Dan Allah kiyi haguri wallhi yanzu na idar da sall... Cikin tsananin b'acin rai ta ce "Wai Kai wani irin wawane Kai baka da hankali ne? Shin saunawa zan cemaka karka sake barin wani ba'ko in dai magidanci ne ya shigo cikin gidannan? Cikin sabawa da irin abun da Lad'ifa ta kema dukda kuwa yakai ya haufeta, bata duba wannan domin kuwa wani lokaci ma harda mari ta had'a masa. Ya ce "Allah ya huci zuciyar ki wallhi saideko ina sallha ne ya hajiya Babba ta shigar dashi amma Dan Allah a gafarceni bazan sakeba in Sha Allah. Cikin masifa ta ce "Kama sake mana wallhi in har ka sake barin wani mutumi ya shigo wannan gidan koda kuwa Hajiya Babba ce ta saka to abakin akin ka, ya bud'e baki zaiyi magana ta ce "bana son jin komai kadai ji me nace maka, nonsense. Tana fad'a ta bargurin ta nufi cikin gidan domin cin mutuncin mutumin da yazo neman auran mahaifiyar tasu. IRO Maigadi kuwa wani hawayene suka zubo masa daga fuskarsa, tabbas ya gaji da cin zarafin da wannan yarinyar take masa, badan bashi da abinyiba in yabar gidannan da tin ba yanzuba ya bar aikinnan. SALIS tasamu yana zazzagayawa acikin palorn da alamar ita yake jira, aikuwa tana zuwa ta ce "Brother muje wallhi yau sai mutumin nann ya san bamuda mutunci. Suna cikin hirarrsu cikin nutsuwa dimin kuwa tasan yarannan nata bazasu dawo yanzuba, saboda zuwan wannan bakon natane yasa ta aikeso gurin da bazasu dawoba har ya tafi. HAJIYA Babba kenannn, mace mai tarin dukiya wacce mijin ta ya rasu ya barta da yara biyu mace da namiji, Salis da Lad'ifa. Ita kuma tana son kara aure amma sukuma sun hana ta, saita gama boye musu komai daga 'karshe sai sun gano, dayawa wasu mazan domin dukiyarta suke son auranta wasu Kuma domin Allah, yanzu haka yaranta sun koremata manema sama da goma. Wasuma sai ana gobe aure wasu tin zuwa d'aya wasu sai abu yayi nisa, wasu ma sai sun dakesu wasu kuma suyi ikirarin kasheshi in har ya aureta, ita kuma tana bu'katar yin auran. Yanzy haka wannan ma magar da akeyi an saka rana, suna cikin haka taji shigowar yaran nata. Cikin mamaki ta me'ke tsaya tana kallon fusko-kinsu ganinn yanda suka murtuke fuska, ta ce "Salis ina aiken da namuku? Bai ko bata amsaba yayi gurin da mutumin ke tsaye ya ce "Wallhi kafin na irga uku karna kara ganinn wannan fuskar taka a nann! Cikin tsananin b'acin rai Hajiya ta ce "Salis ba dakai nake mgn bane? Lad'ifa ta ce "Malam badakai akeyi bane? Ko sai ka ruga a guje? Hajiya Babba ta fashe da wani irin kuka tana cewa Wallhi in har kuka korishi to saina tsine muku dukkanku. Dai-dai lokacin da Salis ya kai uku a irgen da yakeyi. Ai kotakan maganar Hajiya baibiba yayi kan bazawarin da gudu, itama Lad'ifa tabi bayansa. Ai kuwa gogan naku yana ganinn haka ya dau nakare. Hajiya Babba sai ihun kiran sunann su takeyi. Shikuma bazawari tsabar gudu ya manta da cewa yazo da mota, domin kuwa ya huce bakin get da kudu, ai kuwa IRO Maigadi Yana ganin sa ya kibud'ewa, harsai da suka iso gurin. Salis da Lad'ifa suka kalleshi cikin tsananin b'acin rai suka ce "Wallhi daga yau in ya sake zuwa gurin Hajiya Allah sai sun halakashi, haka ya ce wallhi bazai ma sake nuna yasantaba, haka dai suka razana shi har ya d'auki motarsa ya bargidan cikin fargaba. Salis da Lad'ifa suka juyo gurin IRO Maigadi suka sake cemasa karya sake barin kowa ya shigo in ba hakaba hmmm!!. Iro ya ce "To yalla'bai wannan yaron da kace in yazo a barshi ya shigofa? Salis ya ce "banda wannan abokinane. Haka suka shiga cikin gidan Lad'ifa ta cemasa "Wallhi brother bana son ka da wannan yaro, nifa Allah ban yarda da shiba, kana ganinn sa kaga d'an matsiyata, kafin Salis ya bata amsa sun iso d'akin Hajiya. Suna tura kofar d'akina suna iskota a gefen gadon ta kifa kanta sai kuka yakeyi, Salis ya ce sorry Hajiya bamasu..."Bana son jin komai a gareku kutashi kubarmin d'akin tin kafin ku 'Karasa kasheni!! "Lad'ifa ta ce "Hajiya kiyi hagur..."Kufita daga d'akina na ce!!! Ta fad'a cikin kuka had'e da ihuu!. Haka suka fita suna jin kukan nata harcikin zuciyarsu. Bayan sunfitane hajiya ta sake fashewa da wani sabon kukan tana cewa "Bakusan abun da nakejibane, duk abun da yafaru dani bazan yafe mukuba, tana kuka tana fad'a, ai kuwa take ta tino da yaron da yazo jiya, da har tafasa abun da tayi niya amma tinda suka sake mata wannan abun to dele sai ta aikata sede ran kowa ya b'aci. Take ta sheye hawayenta ta shiga kiran Salis tana nemo murmishii ta ya'ba a kan fuskarta duk domin ta nuna musu cewar ta ha'kura. Ai kuwa da kudu suka karasu har suna ture junann su. Ganinn Hajiya na murmishii ne yasa suka kalli juna cikin tsananin mamaki. Lad'ifa ta je da gudu ta fad'a jikin ta tana cewa kokefa Hajiya Allah yasa dai kin huce? Shedai Salis baice komaiba sai kallon ta ya keyi. Hajiya bata bata amsaba sai ta ce "Inaso muyi mgn daku ta nutsuwa? Hakanne yasa suka nutsu ta ce... "Shin meyasa bakwa son nayi aure? Duk sukayi shiru, sai Hajiya taci gaba da cewa...yanzu abun da zanyi haramne ko mekyu? Namma sukayi shuru, hajiya Babba ta ce, aure aure aurefa nace zanyi amma kuka hanna!! Shin kunaso na jefa kaina a cikin masifane? Shin kunaso nafad'a cikin tsinuwar Allah ne? Shin abun da zanyi ADDININMU yayi hani da aikata hakanne?. To tunda de bakwaso nayi aure, naha'kura Amma da sharad'i. Cikin tsananin farin cikin jin cewar ta ha'kura suka kalleta suka ce kokefa Hajiya, sannan ki fad'i sharad'in ki komenene zamuyi? Hajiya ta ce "Kin Tabbatar? Suka had'a baki cikin zumud'i sukace "Eh mun yarda. *SARAH POV* Saida tama kira yakai talatin (30) Amma bai amsaba hakanne yasa ta saki wani tsaki mtsiiiiiiii sannan ta bud'e Data ta hau online, tana cikin chatting ne misalin qarfe 6 na yamma taga kiransa, saida tayi kamar bazata d'aga ba amma taga ita zata cutu sai kawai ta d'aga hadi da cewa "A.J kodai namaka laifi ne? Cikin 'kosawa ya ce "Naga kiranki Allah dai yasa an samo? Saida ta share hawayan ta sannan ta ce "Eh ansamo. Jin haka yasa AJ ya me'ke daga zaunan da yake ya ce "Ar you serious? Jin ya saki fuska yasa ta d'anyi dariya sannan ta ce "eh yanzuma suna gurina aina zamu had'u sai na baka? Amma daga shi bazan sakebako? Domin wannan ma fa saura kad'an Daddy ya ganni? Cikin tsananin farin ciki A.J Yace "No-no dagashi baza'a sakeba, amma yanzu kibari zuwa safe sai mu bud'e in kinje school ko? Ta ce "no gobe bazanje school ba kawai muhad'u yanzu inason ganinn ka? "Ok amma kinsan bazan iya zowa kofar gidankubako, saboda wad'annan sojojin masu Kama da suci babu? Sarha ta yi dariya sannan ta ce "Kadaina tsoransu baruwansu da kai aikin su kawai sukeyi. "Tom yanzu de muhad'u a WADATA makert sai ki bani. Sahra ta ce "ok bari na shirya. Haka suka kashe wayar yayinda sarha ta shirya irin shigarta wato riga da wando, yau ko hularma da tasaba sawa bata sakaba gashin kanta yasha wanji ya kwanta har kafadiun ta sannan ta nufi kofar d'akin nata zata fita. Dai-dai ta tura shima yaturo, kana ganinn irin turowar da yayi kasan ransa a mugun'bace yake, cikin tsananin tsoro ta kalleshi ta ce "Samuel Lafiya? Kafin ta rufe baki ya d'auketa da wani wawan mari, kasan cewar babu wani girma da sukebaiwa juna, sai kawai itama ta zabga masa mari, cikin yaransu ta ce "Bakada hankali ne zaka mareni, ko Daddy bai ta'ba marinaba... "Ai bata an karaba ya sake d'auketa da mari har biyu, sannan ya nunata yana cewa.......📝 *PAGE👉5️⃣* ..................Cikin tsananin b'acin rai Sameul ya nunata da hannu cikin yaran su na tibi ya ce "Oya tell me waye ya shiga room d'in Daddy? Jin tayi shiru ne yasa ya sake zare mata ido ya ce "Tell me waye ya bud'e d'akin Daddy? Cikin rashin kunyar da tasaba Sarah ta ce "Waye zai shiga in bakaiba... 'barawo kawai kuma in kasake ta'bani Allah sai na had'aka da Daddy tif. Ganinn yayo kantane yasa ta fita dagudu izuwa d'akin Mommy ai kuwa shina sameul d'in yabi bayanta. Tana zuwa ta fad'a jikin Mommy tana kukan karya had'i da cewa... "Mommy Kinga Samuel wai meyasa na tona masa asiri a kan ya d'auka ma Daddy kud'i, kuma nace masa banice na fad'a ba shine yabini hard'aki yana dukana. Mommy ta kalleshi ta ce "Sameul get out in my room? Ya bud'e baki zaiyi magana ta sake cewa ai se get out in my room? Had'i da nuna masa hanyar fita, tana cewa... Kasan dai tinda aka kamaka to dole sai ka fito da kud'in... Yaro baya jin magana kaine daga wancan clop sai wancan ba dole ka koma sataba, kana biyewa yaran banza a unguwa. Haka mommy tacigaba da masa fad'a har ya bardakin yana tafiya yana aiyana abun da yafaru kamar an shirya Masa. Mommy ta kali Sarah tace "Kema nace kidaina shiga harkarsa bakiji ko? Duk ranar da bama gida ya kamaki ya kark-aryaki babu ruwanmu don kinsan ba han kali yakeda shib... Ai kafin Mommy ta rufe baki saiga Daddy re'ke da hannun Saumel ya na ihun kiran sunann mommy cewa... Eliza!!... Eliza!!... Eliza!!...cikin tsananin mamaki Mommy da Sahra suke kallun sa. Mommy ta bud'e baki daniyar tambayar ba'asi ya katseta da cewa... "Eliza luck at this sameul Ashe bai fita harkar wannan yaron masu yin sallhanananba!? Na fad'a masa babu shi babu duk wani yaron Hausa domin basa da hakali, yanzu haka ma shine yakesa yake sato mana kud'i? Cikin kuka da ba'kin ciki Samuel ya ce "waini Daddy yaushe na d'auka maka kud'i, nazo zan shiga d'akin ka naganshi abud'e shinafa nashiga kuma i suwet to God ina shiga kaima kana fitowa. Daddy ya ce "Sameul karna sake ganinn ka da yaran Hausa masu sallah bana so? Sameul ya ce "Allah Daddy his my class ment kuma... " I see is okay bana son ganin ka dasu. Ok sameul ya Yana hararr SARAH wacce tayi mutuwar tsaye tana jin abun da Daddy kecewa. Mommy ta ce "I don't like all Muslims... Samuel kafita hanyarsu, mutanan babu abun da kuka had'a dasu, mutanen da suke zagin Addininmu, babu ruwanku dasu, in ba so kuke raina ya 'baciba karnaji karna gani. Tana kaiwa nann ta bar d'akin cikin 'bacin rai. Shikuwa Daddy saida ya tabbatar musu da cewar zai cigaba da tarkon mai d'auka masa kud'i kuma zai Kama, sannan ya cigaba da fad'a musu cewar Hausa masuyin sallha ba abokan zama bane. Ita kuwa sarha duk abun da suke fad'a yana shigane ya fita, domin kuwa ita bataji bata gani a kan A J. Tashi tayi dai-dai lokacin kiran sallha yayi ita kuma ta nufi wadata market gurin AJ. Sameul kuwa yana fita ya tarrar da abokin sa Umar wanda Daddy ya ce karya sake ganinn sa tare da d'ansa. Yana fitowa suka kama hanyar su tazuwa gurin da suka Saba. Yayin da Sameul yake mamaki ya a kayi haka, shida bai d'auki kud'i ba yau amma an kamashi, nann ya shiga tinanin kodai Sahra ma tana d'aukar kud'in me!!? To amma anya ita zata saci kud'in Daddy kuwa!? Nannn tai ya keta tinani, daga 'karshe dai yace zai bibiyeta yaga ina take zuwa. *LAD'IFA. SALIS POV* Hajiya Babba ta ce "Nayarda bazan yi surenba Amma sai kun cikamin wannan sharud'an? "Muna jinki Hajiya cewar Lad'ifa tana murmishii. Ta ce "Abun da nakeso daku shine... Salis kafito da matar aure, kekuma Lad'ifa zaki koma waje ki 'karasa karatun ki. In dai kun amin ce to nima na Amin ce, in kuma ba hakaba wallhi watarana saide ku nemeni kuga bananan agari, zan tafi nabar muku gidan naje can wani guri nayi aurena, tinda ADDININMU bai haramta ba, ta 'Karasa tana hawaye. Cikin tashin hankali Salis da Lad'ifa suka juyo suna kallon juna, ita dai Lad'ifa nata da sau'ki domin kuwa zata iya, shikuwa Salis cikin muryar tausayi ya ce "Haba hajiya aurefa kikace? Yanzu Dan Allah ina zan iya wani zaman aure yanzu!!? Jin haka yasa Lad'ifa fashewa da dariya ta ce "Haba bro sai kace wani mace wai yaushe zaka iya zaman aure. Hajiya ta ce "to in bazakiyi to wallhi aurena sainayi, da sauri Lad'ifa ta ce "No hajiya Babba mun yarda zamuyi! Da sauri salis ya kalleta ya doka mata harara sannan ya ce "Hajiya Wallhi nifa ban shir... " Kafin ya karasa hajiya Babba ta tuna da wani abu sai ta ce... "Naji kuje zanyi tinani. Sun tashi zasu tafi hajiya ta dawo dasu had'i da cewa ina wannan yaron da kukazo gidannan dashi har ka ce abokinane? Cikin sauri Salis ya ce... "Ok AJ? Hajiya Babba ta ce " Eh shi. Kafin Salis ya ce wani abu ta ci gaba da cewa... "Ina son ka kiramin shi zan bashi aiki, domin naji Kuna maganar cewar shi yanzu aiki ya keso ko? Cikin jin dad'i Salis ya ce "Good hajiya wallhi dama ina so namiki maganar yaron, amma wannan wawan bazawarin naki... Da sauri ya ri'ke baki yana cewa I'm sorry na mantane. Ya ci gaba da cewa wallhi hajiya yaron yana burgeni, gashi ba dan kowaba sai tsafta, in kika ganshi yasin zakiyi tinanin dan mai kud'i ne, amma y'ay'an talakawa ne sosai, saboda haka Hajiya muna godiya sosai, yanzuma gidan su zanje na kirashi. Ita dai Lad'ifa tinda ta ga A.J har zuciyar ta gayan bai wani burgetaba dan ita tana jin har yabar gidan bama zata iya masa maganaba, haka dai Hajiya ta tashi ta nufi d'akin ta tana zancen zuci. haka Salis ya nufi gidan su AJ. ( *IN BAKU MANTABA A BAYA SALIS YA JE HAR GIDAN SU A.J YA KIRASHI, SHINE YAZO GURIN HAJIYA BABBA HAR TA BASHI WANNAN KUD'IN AKAN ZAI MATA AIKI, TO KUNJI DALILIN KIRAN, DAMA KUMA SALIS YA CE MASA HAJIYA CE TAKE KIRAN SA. MUJE ZUWA)* *A.J POV* Har ya gaji da jiranta amma shuru bata zoba, ya kira number ta amma no amsar, yana dai tsaye a gurin har a ka fara kiran sallar magariba, nann ya ganggara yayi, yana cikin sallar ne yaji wayarsa na 'kara. Bayan ya idar ya ro'ki Allah yasa Hajiya ta kirashi gobe, sannan ya ce Allah yasa kud'in da sarha ta sato masa sukai dubu hamsin (500k) cikin zuciyar sa ya ce "Ai kuwa Nana zan baiwa wannan wayar tawa, Innah kuma na siya mata 'karama nikuma naje na siyo maikyu. Yana cikin Addu'ar ne yasake jin 'karar wayar sa, hakanne yasa ya fita daga masallacin kafin ya d'aga. *SARAH POV* Tin tana harabar gidan su take kiran wayar sa, amma baya d'agawa har ta iso gurin da zasu had'u, tana sake kira ya d'aga, ta bud'e baki zatayi magana ta hangoshi yana isowa gurin. Kana kallon fuskarsa zakaga hasken musulunci irin wanda ke fita daga goshin duk wani musilmin da ke tseda sallharsa, hoton tabon sallahr dake goshin sa ta 'kurawa ido, dukda duhun dare ya farayi amma hasken gurin bai hanna ta hango abun da yake bata sha'awa a goshin nasaba. Cikin sakin fuska ya 'karaso gurin dad'in da yin sallama wacce shikaidai zaiji kayarsa. Kallonta ya keyi kamar yanda Itama take kallon sa. Cikin d'an 'bata fuska ya ce "Meyasa yau baki saka hulaba kika fito da kanki a haka? SARAH ta ce "sorry I'm forgetting. Kallon ta ya sakeyi yaga kamar tayi kuka sai ya ce "lafiya kuwa naga kaman kinyi kuka? Sarha ta ce " Samuel ne ya cuceni d'azu. take ta kwashe yanda sukayi da shi ta fad'a masa, amma bata sanar dashi akan d'aukar kud'i bane. Tin da yake bai ta'ba jin sontaba ko tausayin taba sai yazu, cikin ransa ya ce yanzu ma haka duk a kainane!!! Afili kuwa ya ce... "Ok sorry stop crying. Da sauri ta kalleshi jin yau shine yake bata ha'kuri, ta tsayar da kukan... Ta ce "please AJ dan Allah kana sona? A.J ya ce "please yanzu duk ba wannan ba, kinga dare nayi bani kud'in ki koma gidan kar Daddy ya dawo bai gabkiba. Cikin sauri ta ce "please AJ amsar me. Kana sona? A.J cikin jin haushi ya ce "Yes Sarah I really love you, kibani kinga dare nayi? Da gudu ta rungumshi had'i da cewa I'm so happy to you my AJ. Lokaci d'aya tsikar jikinsa ta tashi, in ka gansu a haka zaka rantse da Allah Sarah babu wando a jikin ta, domin kuwa wandon ruwan tokane kuma iya cinya ya tsaya, ga kuma yanda jikin su ya had'u da juna kamar irin suna cikin wani yanayi. Da sauri AJ ya janyeta daga jikinsa had'i da cewa... "Na fad'a miki cewar Wannan abun babu kyu a *ADDININMU*, please karki... "Cikin sauri ta ce " muma babu kyu a namu addinin amma in dai da wanda zaka aurane babu laifi. Cikin sauri ya ce "To mu koda kuwa an saka muku ranane in dai ba'a d'auraba to babu kyu, saboda haka kikiyaye, ADDININMU da naku a kwai babban ci, ta bud'e baki zata sakeyin mgn ya ce "please ina kud'in dare nayi kingama an kusa kiran sallar isha. Cikin jakar da tazo da ita ta sa hannu ta d'auko kud'in ta mi'ka masa. AJ ya zaro ido waje Yana kallonta ya ce "Sarah sarh sarhh wannan kud'in nawaye? Ganinn yanda kud'in suka bud'e masa ido, nann fa ya rikice ya shiga tambayarta. *ABDULLHA POV* Tin Yana mota yake tinanin irin cin mutuncin da abokin sa ya kaishi a ka masa, cikin ransa kuwa yana kallon lokacin da take kallon sa har wani hararra take masa. Palorn Mommy ya nufa tin kafin ya 'karasa ya fara jin kamar sauti ko surutan mutane, yana isa ya tsaya chak Yana kallon abun mamaki. Maryam ce tsaye cikin shigar 'kanana kaya ta kunna waqar Zainab Ambato ita da wasu 'kawayanta mata guda biyu, kasan cewar Mommy bata gidan, Nusaiba da Sadiya ma duk tare suka fita da Mommy. Daga ita sai nura d'an autansu, sai 'kawayan nata guda biyu. yayinda d'aya ta tashi suke bin waqar ita kuwa d'ayar tana chatting a waya. Dukkansu basu ga shigowar saba tsabar sunshiga hadaya, Saida yayi a'kalla mt5 yana tsaye yana kallonsu, yama rasa mai zai fara musu, sannan sai mamaki ya keyi, da gaske agidan su a keyin kad'e-kad'e da rare-rare!? Kuma Maryam! Lokaci d'aya haushin abun da Zainab d'in tamasa da kuma abun da ya tarar d'in suka had'e masa yanzu, yanufi gurin da suka jona wayar, yana zuwa ya cire wayar daga cikin abun speaker d'in, baiyi wat-wataba ya buga wayar da 'kasa. Ita kuwa Maryam jin an katsemata yasa ta juyo da niyar zagin qawar tata, a tinaninta itace ta kashe. Ai kuwa tana juyowa sukayi ido hud'u da shi, kafin kace me ya d'auke ta damari, had'i da bin kawayen nata. Sukuwa basubi ta kan jakokinsu ba da ta'kalmin su, ita daiyar ma harda gyalenta da wayarta. Haka suka fita da gudu, shikuwa ganinn sun gudune yasa ya dawo gurin Maryam, itama ta nufi d'akin ta da gudu tana kiran sunann Mommy. Dai-dai ta turo 'kofar zata rufe shima ya iso d'akin, kafin ta tura ya rigata, ya turo, hakane yasa ta fad'a a tsakiyar d'akin. Nann ya cire hular kansa,. Sannan ya zare wayar caja dake d'akin ya shiga lamta mata, tana ihuuu yana zabga Mata, saida ya mata shegen duka kafin ya ce "Bade ke mai taurin kaiba muje zuwa ina dai-dai da ke... tsabar kin raina mutane kizo har gida kina kunna mana wa'ka!? Ya kara d'aga wayar ya labtamata, har saida Maryam ta daina kuka tsabar azaba. *AJ POV* Sarah waye ya baki wannan kud'in!? Yafad'a yana 'kura mata ido? Sarha ta ce "please 'kar'ba in kuma bakaso tom na koma dasu?. AJ ya kar'ba ya 'kirga yaga dubu d'ari dai-dai, kallonta yayi ya ce "To amma yanzu yazaa..." Zamuyi waya kar Daddy ya dawo yaga bananan. Haka ta sake rungumarshi sanna ta tafi, ta barshi tsaye yana kallon ta. Shima cikin kasala ya kama hanyar gida.....📝 * *PAGE* 👉6️⃣ ............ A.J. Duk yanda yakai da son kud'i yaukan yaji ya tsorata da wannan kud'in, shi babban tashin hankalin sama shine... kar Daddy ya kama Sahra ita kuma tace shine yake turata. Haka ya shiga gida jiki babu 'kwari. Ko sallama baiyiba ya shiga gidan nasu yana tinanin mafita, Nana ce kad'ai a tsakiyar gidan tana cin abinci, hakanne yasa ta tsaya tana kallon yanayin yayan nata. "Yaya Lafiya kuwa kake?. Shikuwa A.J baima san tanayiba. Ganin bai bata amsa ta ce "Yaya kiran sallar isha fa a keyi kuma naga kashigo gida? Cikin hanzari ya dawo daga tinanin na sa ya ce "Sorry na mantane yanzu zanje nayi. Tana kallosa ya bargidan da alama dai wani abun na damun sa. *SALIS POV* Kallon 'kanwar tasa ya keyi cikin soda ƙauna, tinda suke tare da ita basa ɓoyewa junann su komai domin kuwa ko saurayine yazo gurinta tofa saita sanar da shi haka shima, dukdade shi baitaɓa cewa yana sonwata yarinyar ba. Akaro na farko kenann yakejin bazai iya sanar da ita abun da ke ransaba, saninn halinta na kushe zaɓin wani. Cikin zuciyar sa ya shiga tinann abun da yafaru yanzu minti kaɗan da suka huce. Tsaye yake a 'kofar gidan su AJ yana jiran yaga yaro ya aikeshi ya kira masa AJ, kasan cewar yakira wayar AJ ɗin bata shiga. Yana tsaye ya ga yaro yazo shiga gidan, nann take ya sanar da yaron cewar in ya shiga yace ana neman AJ. Bayan kamar minti 2 yaron yazo ya ce wai bayanann amma ga ƙanwarsa wai zataga kowaye in yazo sai a faɗa masa. Salis ya ce "ok. Sannan ya kira yaron ya masa ihisani. Cikin gidan kuwa Innah ce ta ceda Nana taje ta dubo kowaye, domin kuwa sunsan A.J da abokai kuma duk yaran masu kuɗi. Hakanne yasa ta saka hijab ta nufo ƙofar gidan. Leƙowa tayi ta hango baƙar mota a fake a ƙofar gidan, gakuma mutum a jingine a jikin motar, hakanne yasa ta nufi gurin sa. Tana zuwa tayi sallama haɗi da gaishisa. Salis da yake danna waya, ko kallonta baiyiba ya ce "Idan A.J yazo kice masa Salis ne yazo kuma kuce yasameni a gid... Maganar tasa ce ta maƙale a bakin sa sanadiyar tozali da fuskar Nana. Cikin rikicea ya ce "am am am kikace baya gida ko? Nana ta ce " Eh baya gida amma yanzu zai dawo. Ai take Salis yayi mutuwar tsaye jin wata sassaiyar muryarda tamasa magana da ita. Ya ce "To kice Salis ne yazo neman sa, Kuma kice yazo gida yanzu. Nana ta ce "to zan fad'a masa, tana faɗa ta juya ta nufi gida cikin takunta na yan mata masu natsuwa. Salis kuwa neman fad'uwa ya keyi ganinn yanda take tafiya kamar zata karye, haka ya bar ƙofargidan cikin begen Nana. Sauke ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tinanin. Laɗifa ta ce "bro lfy kuwa tin ɗazu kazo Kanata tinani kuma kayi shiru? Salis ya ce "sis ina maganar da hajiya Babba tamana ɗazu? Laɗifa ta ce "Maganar aure ko maganar yaronnan abokin ka ɗan talakawannan? Salis kuwa cikin ranshi ya ce "Allah ya sa ban faɗa mataba da wallhi bazata goyi bayana ba. Afili kuwa ya ce " maganar aure... Na yarda zanyi domin kuwa nasamu wacce na keso. Cikin mamaki Laɗifa ta ce "Yanzu-yanzu daga kaje gidansu A.J ka dawo kace min kasamu matar aure? Salis ya ce "Yes haka Allah yake abun sa. Laɗifa ta ce "Tofa!! Lallai koma wacece ta iya kamu, tabaɗa had'i da yin dariya sannan ta ce "ya sunann ta? Salis ya ce " ban saniba, bata faɗa min ba. Laɗifa ta ce "To yanzu dai muje mu sanarwa da hajiya Babba, kaga itama saita dena maganar aurannan nata ko ya kace? Salis ya ce hakane tashi muje?. Haka suka jera suna tafiya Laɗifa na tsokanar sa, wai wata yarinyar tayi WUFF da shi a cikin lokaci kaɗan. *ABDALH POV* Cikin tsananin ɓacin rai ya bargidan ya nufi gidan sa wanda ke unguwar hotoro ɗan marke, yau ransa in yayi dubu to duk sunɓaci, baisan yazaiyi da Maryam ba, a'ce wai ƙanwarsa da suke uwa ɗaya uba ɗaya itace keyin rawa, rawa da waƙar ƴan bidi'a!!?. Yanufi gidansa da niyar bazai dawo ba sai gobe domin a'san yanda za'a yi da Maryam, kawai aure za'a Mata. Wata zuciyar ta faɗa masa, ai kuwa ya aminta da hakan. Maryam kuwa bayan Abdalh ya fi ta, ta yunƙura da niyar tashi amma Ina, take ta sake rusa ihuuu, hakanne yasa nura da tin shigowar yayan nasu yagudu,. ganinn yanda fuskarsa ta ɓaci. Dukda nura bashida ƙarfi haka ya taimaka mata ta miƙe tsaye ,ya kwantar da ita a kangado. Abin dariya amma ba damaryi, haka ya gintse dariyarsa ganinn yanda takeyi kamar wacce a ka ɗaye fatar jikin ta, ga ihuu da takeyi. Ganinn kamar nura nason yin dariyane yasa cikin kuka ta ce "Wallhi nura in kasake naji dariyarka saina kusan karkaryaka. Shikuwa nura jin yanda tayi maganar cikin kuka da rakici ne yasa dariyarsa kufcewa, aikuwa ya saki dariyar, haɗi da sakin ta ta faɗa kangadon da ƙarfi. Aiku mai neman kukane aka jefeshi da kashin a waki, nann take kuka ya dawo sabo, tadin buɗe baki tanayi, shikuwa nura yabar ɗakin yana dariya. *ZAINAB VOP* Dariya takeyi wacce rabon da tayi irin ta harta manta. Kallon Isa tayi ta cigaba da bashi labari. "To bayan ya tafine mukayi wa'azi sauran abokan nasa harda wani kafeni da ido, Nikuwa ko ta kansu bambiba. ISA ya kwashe da dariya sannan ya ce "Amma fa kin burgeni Wallhi, wani abuma saigobe in munje kusa da gidansa gabatar da walimar da zamuyi, nifa Allah har na matso naji wannan sabuwar wa'kar da kikace zakiyi mai taken bud'ad'd'iyar wasi'ka. Zainab ta ce "Yanzuma zan je na ƙarasa aikinta, ai i'na sane da Al'kawarin da na ɗaukarwa mlm. Isa ya ce "Ɗazu Aliyu yazo wai ya kira number ki baki ɗaga ba? Zainab ta ce " Oo!! Allah sarki ban sanar dashi batun zuwana walimar bane, Kuma kasan idan i'na kan aiki bana ɗaka waya, Allah dai yasa baije gurin mlm ba? ISA ya ce "Nima agurin mlm ɗin na ganshi, kuma nasan maganar ce ta kawoshi, kuma zakigani mlm zai miki mgn. ISA ya cigaba da cewa "To Zainab in kina sonsa kawai kiyarda ayi auran mana tindade shi yace ko yaushe kika shirya?. Zainab ta miƙe ta bargurin haɗi da cewa Yaya zamuyi mgn anjima yanzu inada aiki. *LAƊIFA SALIS. POV* Salis ya ce "No Sistar karmu sanarwa da hajiya tukunna, saboda ban samu mun yi magana da yarinyar ba, kibari nann da kwana biyu lokacin mun shirya da ita. Lad'ifa ta kwashe da dariya sosai kamar zata faɗi sannan ta ce "Kai bro karfa kodai kaima irin mazannanne masu tsoran Mata? Salis ya ce "Dama a kwai mazan da suke tsoran Mata!? "Hh mana ga ɗaya ma a gabana. "Haba yarinya aini jarumin mazane, ke bama niba duk mai irin sunan Salis to yanmata ma shakkarsa sukeyi. Laɗifa ta ce "Tom zade mugani .Haka suka bari sai ya shawo kan yarinyar. ( Wanda ya kasance ranar ne A.J yaje gurin Hajiya) *A.J POV* Bayan ya dawo daga sallar isha ne ya shigo gida, cikin kwarin gyiwa domin kuwa zuciyar sa ta bashi tabbacin kawai yaci kuɗin domin Sarah bazata tona masa asiri ba. Kallon Nana yayi ya ce "NANA goba zan baki wayata iyah kuma zansiyo mata ƙarama, amma fa bance ki dinga tara number samari a waya ba, kuma kullum sai na Kar'bi wayar naduba, kin yarda? Da sauri ta barcin abincin da sukeyi tare da yayan nata ta ce "Yaya wallhi na yarda, ni daga number ka sai number Innah sai kuma number kadija ƙawata shikenan. AJ ya buɗe baki zaiyi magana yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga number Hajiya wacce ta bashi akan zata kirashi, da sauri ya ɗaga yana cewa hello Hajiya?. "AJ hajiya Babba ta Kira sunann sa ta cikin wayar. "Na'am" Hajiya ta ce "Kazo gida misalin qarfe goma na safe, kuma banason Africa time?. "Angama Hajiya in Sha Allah zanzo. Amma hajiya kituro Salis sai mutafi tare da shi? Da sauri Hajiya ta ce "no banason yasan da zuwanka, Kuma karka sanarmasa da cewa kazo kuma duk aikin da na baka karka nuna masa komai kaide yardarka kawai nake buƙata. Cikin sauri AJ ya ce "An gama ranki shidad'e, yanda kikeso haka za'a yi. Nann ya kashe wayar dai-dai lokacin inah ta fito daga bayan gida. Ta ce "Yanzu Abdul jabaru inayin magana kafini baki, kacemin kai baka sata, yanzu a ina kasamu kud'ad'an nann da kake cewa zaka siyamana waya? AJ ya ce "Yanzu Innha fisabillhi sokike mu ƙare a wannan talaucin? Abun arzuƙi ya samemu amma kicewai... to Innah in baki son wayar ai sai kibarta, yanzu ki dubeki daga jiya zuwa yau dan Allah baki ji kinfi samun kuzariba?kinci kaza kin sha yourgot ga kaya mekyu, amma bazaki samin albarkaba. NANA ma ta amsa da cewa, mudai innah muna son wayar please yaya kabani taka kaji?. Haka innah tayi shiru badan batada da abun cewaba sai dan anfita baki. Washe gari, kamar yanda A.J ya ce, ya siyowa Nana layi, yabata wayarsa, itama Innah yasiyo Mata ƙarama da layinta, yayinda shima yaje shagon siyarda waya ya siyo wayarsa mai kyu. Ƙarfe goma na safe dai-dai aka tafka saɓani tsakanin Salis da A.J. yayinda Salis yake kan hanyarsa ta zuwa neman soyayyar Nana. Shikuma AJ yaje domin jin wani aiki Hajiya zata bashi. *A.J. SALIS POV* Kallon Hajiya babba yakeyi cikin tsanani mamaki, haɗi da kallon jakar kuɗin gaban sa. AJ ya ce "Hajiya ban fahimci abun da kikenufiba?. Cikin shawƙin abunda ta keji ta ce "Yes kamar yadda kaji na sanar dakai, aure nakeso muyi da kai amma cikin sirri, karkowa yaji, in har ka amin ta, kasanar dani duk abun da kakeso tin daga kan miliyoyin ɗari da kuma gida da kuma mota, zan mallaka maka. Sanye take da dokuwar riga sai gyale fari. Kallon sa takeyi ganinn shima ya zuba mata ido. Cikin jin kunya ta ce "ina u'ni? Salis kuwa ganinn irin shigar da tayine yabashi damar kafeta da ido, yana jin sonta har zuciyarsa. Bai ankaraba yaji tana cewa "Yaya ɗin AJ bayanann kunyi saɓani yanzu ya fita, amma in yadawo zance masa wannan da yazo jiya yazo neman sa. Tana kaiwa nann ta juya zata koma ciki. Cikin sauri salis ya ce "Ji'mana, bagurin sa nazoba gurin ki nazo. Ta ɓangare ɗaya kuma yana tinanin meyasa bata riƙe sunann saba. Cikin mamaki Nana ta nuna kanta da cewa ni?. Duk da uban fankoki da asi da suke aiki a palorn hakan bai hana AJ jiƙewa da zufaba. Cikin rikicewar ya ce "Hajiya aure fa kikace? Kuma dani!?... gaskiya bazan iya ba, yazanyi da salis wanda agirme. Ya girmeni kuma abokina wanda yake temakamin a komai, amma na auri uwarsa!!? Ina Hajiya dan Allah kibar wannan zancen Please. Ya ƙarasa yana kallon jakar kuɗin da yasan in har ya mallakesu to tabbas shida talauci har abada. Salis ya ce "Yes gurinki nazo. Nana ta juya tana neman wacce salis ɗin ke magana da ita, domin kuwa tanada tabbacin bada ita yakeba, domin kuwa babu haɗin kwanda da gula. Kayanda kejin sama tasan ba na ƙananan yara bane, bare motar da yake jingine a jikin ta. Cikin mamaki ganinn yanda take ta dube-dube ne salis ya ce "Keɗayace a gurinan, kuma dake nake...kamata yayi a ce kiyi maraba da zuwana domin da alkairi nazo....📝 _ *PAGE* 👉7️⃣ ............... Kallon jakar kuɗin yakeyi yana aiyana abun da zai faru in ya mallake su. Cikin ransa yace "Anya kuwa in nabar wannan garaɓasar ban cutuba!?. Zuwa wani lokaci ya ɗago ya kalli Hajiya Babba sannan ya ce "Yanzu dan Allah hajiya meyasa kikeso ki aureni?. Hajiya Babba tayi dariya sannan ta ce "Banice zan aurekaba kaine zaka aureni...Kuma ba wai in ka aureni shikenan bazaka sakeyin wani auran bane, a'a zaka auri wacce kakeso, amma kafin nan zan baka labarin abin da yasa zanyi aure. Cikin gamsuwa da abunda ya ce Nana ta ce "Ok tom barka da zuwa. Salis ya gyara tsayuwar sa sannamallak "Barkade...da fatan dai ba dole namikiba? Nana ta ce "kusan dai hakan...yanzu dai kafaɗi abunda ya kawoka tunda kace gurina kazo, kafin innah ta fito nemana?. Cikin dariya Salis ya ce "Afito nemanki fa kikace kamar wata ƙaramar yarinya?. "Eh dama ai ƙaramar yarinyar ce baka gani bane?. "Dan Allah karki ƙara kiran kanki da ƙaramar yarinya, kallekifa kin isa aure amma kice wai yarin ya ceke?. "Cikin jin kunya Nana ta rufe fuskarta haɗi da cewa... Please dan Allah zan tafi gida.? Salis yace "Muga wayar ki?. Ya mata wannan tambayar ne ganin wayar a hannuta. Ita kuwa Nana tinda a ka bata wannan wayar haryanzu bata barta ta hutaba. Hajiya Babba ta ce "Nakasance tin ina yarinya Allah ya ɗoramin wani irin ciwo, wanda tin kafin na kai mizanin aure a kamin. Na kasance daga cikin mata harijai wato masu mutuƙar sha'awa. Hakanne yasa iyayena sukayi saurin aurarr dani, aurena uku (3) zan faɗa maka abun da yake rabani da mazajena. Har Allah yayi na auri mahaifin su Laɗifa, shima ɗin dan Allah yayishi jarimin gaske ne, shiyasa zamanmu yakai har lokacin da Allah ya amshi abinda. Lokaci ɗaya AJ ya zaro ido waje jin abunda Hajiya ke faɗi. Ya ce "Hajiya menene harija? Hajiya tayi murmushi tana jin wani matsananci sha'awar yaron na ƙara taso mata a duk lokacin da yayi magana. Zaro ido waje Nana tayi ta ce "Mezakayi da wayana? Salis ya ce "kinga rufe bakin kar..."ai kafin ya ƙarasa ta rufe fuskarta tsabar kunya. Haka ta ciro wayar ta bashi, domin kuwa babu fuskar masa musu, domin kuwa ya mata kwarjini sosai. Bayan ta bashi sannan ta zuba masa ido domin ganin mai zaiyi da ita. Hoton ta da AJ ne a gaban wayar. ganinn yanda sukayi kyau ne yasa ya ce "Kunyi kyau sosai kamar ba keba ya ci gaba da cewa "Badan AJ ya girmekiba da sai ace ko ɗin ƴan biyu ne. Dariya tayi tana jin daɗin yanda ya yabesu. Number sa ya saka mata sannan ya ƙwada kira ko tanada kuɗi, aikuwa sai gashi ta shiga, yayi seveng number sa da (my sweetheart) sannan ya nuna mata. Haɗi da cewa wannan number nane zamu dinga gaisawa. Hajiya Babba ta ce "Karka damu duk zan sanar dakai. Taci gaba da bashi labari. Yanzu haka shekarar Alhaji huɗu da rasuwa, kuma tun baya ya rasu yarana suka hanani yin wani auran, kuma sunsan da cewar addinmu bai hanaba amma duk wanda yazo sai sun korheshi. Jiyama sun koriwani, shine yasa nayi amfani da kai domin cimma wani burina, inaso ka yarda babu abun da zai faru, domin kuwa ADDINIMU bai haramta ba. Zamuyi aure na shekara ɗaya, Sannan zan baka miliyoyin hamsin da gida harda mota... sannan babu abun da zai shiga tsakanina da kai har muyi wannan shekara ɗaya ɗin, abin da nakeso shine Karka sanarwa da kowa, harda kakarku domin kuwa nasamo labarin ka gaba ɗaya, iyayenku sun rasu, daga kai sai ƙanwarka sai kakarku, to banaso susan da labarin, da so samunema wata ƙasar samu tafi mufara yin wats ɗaya kafin mudawo, kokuma kawai zan cewa su Salis na ɗaukeka a matsayin yaron gidana, zaka dinga zuwar min aike da cefane. Kaga kassmu damar shiga ɗakina duk lokacin da na kiraka koda kuwa kana inane?. Nana bata tsaya karanta abun da yayi seveng number ba, domin ita duk a tinanin ta kawai yasa number ne bai ajiye taba. Hakan ne yasa ta karɓa tana cewa "Tom zan shiga gida? "To sai kinga kirana. Batace komaiba ta shige gida, shikuma ya tsaya yana Kallon ta har ta shiga gidan. Sannan shima yayi murmushi ya huce gida. Yana hanya yana tinanin hirarr da sukayi. A.J. Ya ce "Shekara ɗaya kawai? Hajiya ta bashi amsa da cewa "Eh shekara ɗaya. Amma bazan baka kuɗin gaba ɗaya ba, zan baka miliyoyin biyu yanzu, bayan shekara ɗaya kuma zan baka sauran, amma gidan da nace shima zan baka, motarma saboda gudun tambaya da zan baka, amma yanzu itama motar sai bayan aure. "Waiyoooo daɗin kasheni AJ ya furta a zuciyarsa sannan ya ce "Hajiya na yarda, amma ki bani miliyoyin biyun yanzu, sai kuma ki kaini gurin gidan nawa. Hajiya ta ce "wannan duk mai sauƙi ne, amma ai ban gama kafa maka sauran sharuɗan da suke cikin auran ba?. AJ ya ce "i'najinki. Hajiya ta fara bayani kamar haka...."In na fara karkace komai sai na kammala sai kayi tambayar ka? AJ ya ce "Kede Hajiya muje bayani. "Duk lokacin da na nemeka to ko a i'na kake ko me kakeyi zaka bari kazo?. Sannan wasu lokutan a gidana zaka kwana kuma a ɗakina, zan sanarwa da mai gadi cewar in kazo yabuɗe maka koda cikin dare ne. Ba kai ba kula wata macen ko wacece harsai auranmu ya ƙare. Karwani yasan wannan labarin koda kuwa Salis ne, ko abokanka, ko ƙanwarka, koma de waye. In kayarda gobe inada gurin da zamuje a ɗaura auran. Abun da Hajiya Babba bata saniba shine...duk wannan bayanin da takeyi, shi AJ kuɗin kawai yake hange, amma abu ɗaya ya tsaya masa a'rai, wato kwana a gidanta. Tayaya!? AJ ya tambaya? Hajiya ta ce "Karka damu duk wannan mai sauƙine, nidai karka bari Salis da laɗifa suji wannan zancen? AJ yace "ya yarda. Nann take Hajiya ta ce "bani acont number ɗinka yanzu na tura maka?. Nann take miliyoyin biyu suka shiga acont ɗin A.J. kallon message ɗin yakeyi, tamkar ya ƙwala ihu tsabar daɗi. Haka ya tashi ya fita, tsabar ruɗewama ya manta da maganar gidan. Hajiya Babba kuwa, duk abinda yaron keyi sake ɓurgeta yakeyi, badan tana tsoran saɓon Allah ba, kuma tin tana yarinya batayiba, da babu abun da zaisa bata zuba masa magani a ruwa don tayi amfani da yaron ba. Tabbas tana buƙatar na miji kuma, yaranta sun hanata, akan ta je ta aikata haram ƙwara tayi haka, tinda ADDINIMU bai haramta ba. Tawani ɓangaren kuma tana ganinn tsan-tsar son kud'i da ƙuruciya da suke damun AJ. A.J. Yana fita sukayi karo da Laɗifa zata shiga palorn. Shi AJ tsabar rikicewane yasa bai gantaba. Ita kuma laɗifa tsabar zuciyarta ce take suya tsabar halin da take ciki. Tabbas yau tayi gamo, tana tafiya tana tinanin abun da yafaru tsakanin ta da shi, wanda tanada tabbacin ba musulmi bane. sai kawai taji tayi karo da mutum. Kallon-kallo sukewa juna, yayinda laɗifa kejin kamar ta zabga masa mari. Aikuwa cikin rashin iya magana da wanda suka girmeta ta ce "Wannan wani irin wawancine da dabbanci!!, kana tafiya baka kallon gabanka!?. Kafin ya bata amsa ta sake cewa...waima uban me ya kawoka gidannan da ranar Allah?( Kasancewar yanzu 12 miyu da mintin 4).( 12:0,4)) Kodan naji Hajiya Babba ta ce tana neman ɗan aiki ko? To Allah yasa dai aikin waje kasamu bana shiga cikin gidaba...dan Allah kalleka har wani tsami kakeyi waikai a hakan saurayi, yanzu haka wannan kayan sunkai kwana uku a jikin ka, koma sunfi haka...bari dai naje naji wani aiki Hajiya tabaka, wallahi badan Salis ba wallhi baka kai ka shigo gidannan ba, nonsense. Abin da Laɗifa bata saniba shine A.J yafita baki, sannan a yanzu yana ganinn dai-dai yake da shugaban ƙasa ma ba itaba, saboda miliyoyin biyun da suke tare dashi, saboda haka ya barta ta gama maganar ta sannan yaga zata tafi ya ce "Yaro man kaza...kalleni da kyu nafi ƙarfin kimin wulaƙanci, domin nibadake zanyi saidai nayi da wanda yafiki, saboda haka kisan da wanda zaki dinga magana, AJ nake bana ɗaukar nonsense. Take ya juya yabar gurin yana jin kansa a sama, domin kuwa yanzu jinsa yake yana dai-dai da uban kowa harda uwar kowa a duniyar nann dan yanada miliyoyin hamsin, yanzu kuma ga biyu a hannusa, afili ya ce "kai wallahi sabuwar waya ma alherice, daga siyan waya yau har tafara ganinn irin wannan message na kuɗi haka, kai Allah ya sakawa Sarah da albarka, dole yau na ɗauketa muje clop domin itama aci wannan banzan da ita. Haka ya tafi gida cikin farin cikin da yafi na jiya. Ita kuwa Laɗifa tsayawa tayi tana Kallon ikon Allah. Ɗan aikin gidan sune zai faɗa mata magana son ransa!! To wallhi an fasa ɗaukar sa aikin, nann take ta nufi cikin gida gurin Hajiya Babba. *ABDULLAH* *POV* Cikin ɓacin rai Mommy take masa magana. "Yanzu Abdalh kana cikin haiyacinka kuwa?! Yanzu da ka il'latata a wani gurifa!? Bakasan mace bace, macan ma budurwa wacce takai ta zama matar wani... ban sanka da irin wannan halin ba sabada haka karka fara, dukan mace!....hakan ya nuna cewar ko aure kayi haka zaka dinga ɗikar ƴar mutane ko?. Abdalh ya ce "Ayi haƙuri Mommy bazan sakeba, Amma fa Mommy rawafa na samu tanayi agidannan harda ƙawayen banza, sun kunna waƙa sai rawa sukeyi. Cikin rashin kunya Maryam ta ce "Wallahi Mommy ba waƙa mukejiba, ƙasidar Zainab Ambato cefa, kuma yabon Annabi Muhammad s a w suke..."kafin ta ƙarasa Mommy ta bige mata baki, tana ƙarasa cewa Sallallahu alaihi Wasallama. Kafin ta ce "Yanzu Maryam ban hanaki ana magana kina saka bakiba?, to ai gaki gashi zan barku tinda kinga kema kinkai ko?. Ai kuwa dama Maryam abu kaɗan take nema ta ɓare baki. Nann take tafara ihu!! "Waiyo bakina waiyoooo bayana Mommy kin fama min ciwo, kuma kin fasa min baki, waiyoooo Allah Daddy. Haka Maryam ta dinga ihuu! Har su sadiya da Nusaiba harda Nura wanda shigowar kenann daga makaranta, suka zo gurin da gudu. Cikin ɓacin rai ABDULLAH ya ce "Wallahi in baki rufe mana wannan ƙaton bakin nakiba zan fasa shi da gaske. Nann take tayi tsit sai jan numfashi takeyi kamar wata me shirin haɗiyar zuciya. Abdalh ya ce "Wallhi Mommy in har na sake ganinn ta tana jin waƙoƙin nann sai ta gane, In ba haka a ke mataba yarin yarnan wallhi saita gagari kowa a gidannan. Mommy ta ce "nima naga alama amma bana son duka, ka ja mata kunne dai. Sannan Mommy tamasa faɗa. Bayan ta kori su Maryam. Sannan ta masa nasiha a kan ya daina nuna ƙiyayyarsa ga mawaƙannan domin itama kakanta wanda ya haifi mamanta ɗan ɗariƙane. Amma Abdullah ya ce " Ai da ba haka ɗariƙar takeba yanzu sun ɗauki abun fiyeda yanda nada sukeyi, suna baiwa wani ɗan adam ɗin matsayin, wanda ni da ke da shi duk mutanene amma suna kaishi matsayin da Allah bai kaishiba, wasumafa har Allah suke kiran sa, in kamusu magana suce wai ƴan haƙiƙa, dan Allah mene haƙiƙa a ADDININMU? Cikin sauri mommy ta ce "Abdalh kaji tsoran Allah yaushe ka taɓa jin sun kira wani da Allah? Shiya kullum nake maka faɗa akan ka dinga iya bakinkan a kan mutanann ka daina faɗar abun da kasan baka da tambas akai. Haka Mommy ta masa faɗa sosai, kafin Daddy yazo, ya masa maganar auran da ya ce masa, amma basu sanar dashi dukan da yama Maryam ba. *A.J* Da sallama ya shiga gida, bayan ya biya ta bank ya ciro kuɗi. Geme take bugawa a wayarta hakanne yasa bataji sallamar saba. Hakanne yasa ya ƙarasa gurin ya kafce wayar daga hannuta haɗi da cewa "Sabon shiga ɓarawo da sallama...ba sabobba ɗan Fulani yayi a gogo. "Haba yaya gashi kasa ammin Game ovar. Nana ta faɗa cikin shaƙwaba, haɗi da turo baki. AJ ya ce "yazu tun safe dana fita abun da kiketayi kenann ko? Ai kuwa kamar yasani, domin kuwa tin kafin Salis yazu har yanzu ya tafi ta cigaba da game ɗin ta, babu yanda innah batayi da itaba akan tazo tayi aikin gida amma sai ta ce ina zuwa innah. Kafin tayi magana innah ta ce... "Maraba da zuwa Abdul jabaru, tinda yanzu ta ganka ai tazo muyi aikin, yarinya tinda tayi waya kuma bata moruwa, ni kaga tawama tinda na ajiyeta bambi ta kantaba har yanzu. AJ yace "Nana kafin na baki wannan wayar me nace miki? Nana tayi shiru. Ya ce "Bani wayar? Nana kuwa da yanzu-yanzu ta saba da wayar ta ce "yaya dan Allah kayi haƙuri wallhi na daina..."Tsawar da ya daka matane yasa ta kasa ƙarasawa sannan ta ciro wayar danufin miƙa masa. Dai-dai wayar ta shiga rabin hannun sa, rabi kuma tana hannuta saiga kira ya shigo cikin wayar number an rubuta my sweetheart.....📝 _ *NASIHA* _ka tarbiyyanci kanka da karatun alƙur'ani, sannan ka saka soyayyar Annabi S.A.W a zuciyarka, sannan ka saka soyayyar iyalan gidansa za ka rabautu duniya da lahira_. *ADDININMU* *PAGE* 👉8️⃣ ............Kasan cewar lokacin misalin ƙarfe sha ɗaya zuwa sha biyune yasa A.J Baiga sunan mai kiran nataba, itama kanta cikin mamaki take kallon wayar domin kuwa har ta manta da cewar Salis ya saka mata numbar sa. A.J ya ce "Waye mai kiranki? Rikicewa tayi domin kuwa ta rasa mai zatace. "Badake nake mgn ba? Sai a lokacin ƙarya ta samu nasarar isowa bakin ta, ta ce "Ɗazu ne naje gidan su kaɗija na nuna mata wayana, shine tace nabata numbar na idan tasa kati zata kirani, to inaganin itace. Ta ƙarasa maganar kamar tayi kuka. Kasan cewar A.J yasan halin Nana, kuma yasan bata kula kowa, sannan kuma yaga kwata-kwata ma yau wayar ta shiga hannun ta, sai kawai ya ce "Karna sake jin ance waya ta hanaki aiki, in ba hakaba Allah sai na ƙwace. Nana ta ce " I'm Sorry yaya bazan sakeba, sannan ta harari gurin da innah ke wanke shinkafa. Ai kuwa caraf suka haɗa ido. Inah ta ce "Eh ai da yake ni kika rena shi yasa, ga wanda ya miki faɗa amma ni kike harara, to wallhi ahir ɗin ki mara kunyar banza, ai Allah yasa Abdul jabarun baibar gidan ba. A.J Kuwa yana shiga ɗakinsa ya fito da dubu hamsin (500) ɗin da ya ciro a bank, ya zuba musu ido yana aiyana cewa yanzufa yabar matsayin talaka ya zama ɗan ƙaramin mai kuɗi, wata zuciyar ta ce kai ai kafi ƙarfin ƙaramin mai kuɗi sai babba, take ya kwashi kuɗin ya watsa sama yana dariya, yana jin yanda kuɗaɗen ke sauƙa a kansa kamar ganye, sannan ya ciro sabuwar wayar da ta zama masa alkairi a cewar sa ya kira sarha. *SARAH. SAMUEL* *POV* Cikin ɓacin rai Samuel ya kalli abokinsa Umar cikin English ya ce "Umar ban taɓa jin kunya irin na jiyaba, saboda haka karka sake min haka. "Umar ya ce "Kai Allah nimafa naji kunya amma hakan shine mafita badan wannan yarinyar ba Allah sai munji kunyar da tafi wannan, amma fa yarinyar ta ɓurgeni. Yafaɗa yana kallon Samuel ɗin. Samuel ya ce "Yau zan biyata kuɗin da ta kashe mana, domin banason raini, kasan yaran hausann naku sun iya jisga mutum, yanzu a kan wannan abun da tamin saitayi tinanin ko muɗin matsiyata ne. Umar ya ce "Yes nasan yarinyar batada kunya ga isa, kai itafa tsabar raininn hankalin ta, wallahi samari har tsoran zuwa gareta sukeyi. Samuel ya ce "Rely? Umar ya ce "Yes. Samuel ya ce "Ai kuwa yau zan mayar mata da kuɗin ta, sannan sai na karya wannan record ɗin nata, ya ci gaba da cewa...kasan ni babu ruwana da yaran hausawa domin sam basu iya harkar wayewa ba, amma wannan karan sai na afkuwa wannan yarinyar, kuma sainayi nasara a kanta. Cikin mamaki Umar ya ce "Ban ganeba? Samuel ya ce "ina nufin zan huta da ita. Umar ya ce "Lallai kam bakan taba. Sameul ya ce "Ok nabaka kwana biyar sai ka ganta a gaban motana muna yawo cikin soyayya. Umar ya ce "kwana biyar dai? Samuel ya ce "Yes. Haka suka rabu, yayin da Samuel ya shiga tnanin yanda zai sato kuɗi domin zuwa clop ɗin yau. Haka ya bari a kan cewar zai shiga ɗakin daddy tindade an'masa sharri, sannan ya rasa waye ya saci kuɗin wancan karan. *SARAH* Kallon wani Afrikan Film ta keyi wanda ya ɗauke mata hankali har bata san shigowar Usha gidan nasuba. Zagayowa yayi ta bayan kujerarr da take kallon yayi, ya rufe mata ido ta baya yana dariya ƙasa-ƙasa. Ita kuwa sara cikin masifa ta ce "Samuel I don't like it please..."Kafin ta ƙarasa Usha ya zagayo yana mai haɗe fuskarsu. Cikin murna da farin ciki SARAH ta rungumeshi cikin yaransu ta ke cewa "Usha yaushe a gari? Shine ko ka sanar dani? Ihun da Sarah tayine ya fito da Momy daga ɗaki, ai kuwa itama tana ganinn Usha tazo da gudu ta rungumeshi tana masa welcome back. Suna cikin haka Samuel ya shigo, shima yana ganinn ɗan uwan nasa kuma abokin sa, yazo da sauri yana shiga jikin sa. Nann Sarah ta fito masa da kayan mutsawa sai dariya ta keyi. Usha ya ce "Momy tinda natafi sau ɗaya Sarah taje gidan mu, saboda taga bananan. Cikin sauri Momy ta kalli Sarah wacce gabanta ya faɗi. Momy ta ce "Da gaske? Shikuwa Usha da baisan komai ba ya ce "Yes Mommy domin kuwa haka mama tace min, shinema yasa nazo kodai ba lfy ba. Cikin mamaki Mommy ta ce "To Sarah ina kike zuwa kullum sai kice zaki gidan su Usha? Cikin rashin sanin abunyi ta buɗe baki zatayi mgn sai wayarta ta fara rori. Ɗauko wayar tayi a kujerarr da ta zauna ɗazu. Kwallon number da ta gama zama a kanta tayi, cikin sauri ta ɗaga haɗi da fita daga palorn. Duk binta sukayi da kallo, sannan suka shiga wata hirarr. Yayinda Samuel yake neman hanyar shiga ɗakin daddy, ganinn motarsa batanan sannan sojojin da suke binsama yaga basanan sai kawai masu jiran gidan. Nana kuwa bayan A.J ya shiga ɗakine ta ciro wayar domin duba waye zai haɗata faɗa da ƴaƴanta, kafin ta duba saiga kiran sa a karo na uku. My sweetheart, Shine sunann da tagani a kan wayar, cikin zaro ido da yazama mata ɗabi'a in abu ya bata mamaki ta ce "Kuttt!! Allah ya taimakeni, take ta goge number sannan ta kashe wayar gaba ɗaya ta ajiye ta koma gurin girkin da innah keta surfa masifa daga taga Nana ta kalleta tin ɗazu. *SARAH* Hello my AJ. Hi my Sarah, ya amsa cikin shwƙi da jin kansa a sama. Sarah ta ce "I hope you buy the phone? "Yes my Sarah, yanzuma da ita muke waya. "Waoooo I'm very happy, wacce iri kasiya? Allah yasa de ba irin ta yara kasiyaba? A.J yayi dariya yana jin wani girma na shigarsa sannan ya ce "Sai mun haɗu yau zan nuna miki. Sarh ta ce "Tom mu haɗu yau? Ya ce "Ok yau abokina yana da birthday da daddare, so zamu tafi tare, ar you ready? Cikin jin daɗi ta ce "Yes But I don't know...sai tayi shiru. AJ ya ce "What is your problem? Tana so tace masa batada kuɗi kuma tana jin kunya, sannan tana son tace masa in tayi dare Daddy zai karkaryata, in ba hakaba saide ta kwana a wani gurin. Cikin jan numfashi ta ce "Ok I'm or ready. A.J yayi dariya sannan ya ce "Good Allah ya kaimu lokacin, amma fa kiyi wankan shiga taro. Ya faɗa yana dariya domin kuwa yasan ta wajan ɗaukar wanka. Haka sukayi sallama Sarah tana tinanin yanda zata shiga ɗakin daddy ta ɗauki kuɗi, domin tasan AJ bashi da kuɗi. Nann ta shiga tinanin abun yi, take ta tuna cewar Usha ya dawo zataje ta tambayeshi ko dubu ashirin (200) ya bata sai ta haɗa da na gurin ta. Amma me sai ta tuna da cewar ya ce ya daina bata kuɗi in dai bazata amince da abun da ya umar ceta ba. Nann take ta shirya domin zuwa ɗakin daddy. *ZAINAB VOP* Zaune take a gaban MLM ya ce "Yauwa kin haɗa komai na majalisin yau ɗin ko? Zainab ta ce "Eh mlm. "To Allah yabada Sa'a. "Amin ya Allah. Zainab ta amsa tana meƙewa domin tafiya gurin majalisin da a ka gaiyaceta. Mlm ya ce Abu? Ta ce "Na'am mlm. Mlm ya ce "Jiya Aliyu yazo, sannan ya tabbatar min da cewar zai turo iyayensa, shine nace to dama de kunyi magana dashi? Ya cemin a'a baisamekiba, sai na ce masa yaje zamuyi mgn dake, in kinyarda sai a faɗa masa ya turo, tinda ai Aliyu ɗan gidane kinsan halin sa yasan naki kinga babu wani dogon bincike da zamuyi a kan haka ko? Cikin jin kunya da abun da Aliyu yayi ta ce "Tom mlm Allah yasa hakan shene mafi alkairi. Mlm ya ce "Amin Zainabu abu, Allah dai ya miki albarka, yasa kema naki yaran sumiki abun da kike mn. Ta amsa da amin tana barin ɗakin. Ta ce "Yanzu abun da Aliyu zaimin kenann!? Ni nace masa ina sonsane, take ta watsar da batun Aliyu ta shiga haɗa kayan da zata tafi gurin walimar tata. Ta shirya domin zuwa ɗakin mama suyi sallama kamar yanda ta saba a duk lokacin da zata wani guri da a ka gaiyaceta. Aisha ce zaune a gabon maman nasu, wato ƴar auta a gidan su Zainab. Mama ta ce "Wa cece mahaifiyar Nana faɗima ƴar manzan Allah? S a w? Aisha ta ce "Nana Kadija. "A'wacce rana a ka haifeta? Asha "Ranar juma'a, jimada sani. Mama ta ce "good. Sannan ta ce "Waye ya aureta? Aisha ta ce "Saiyadi Aliyu bin abu ɗalib. "Yaranta nawa? "Yaranta biyar. Mama ta ce "Tom faɗa min sunann su? Aisha ta ce "I'mamu Hasan. Sai imamu Husaini. Sai Musa sai Zainab sai Ummu ƙursum. Mama ta ce "Allah hu akbar!!! Yanzu sai "kafin ta ƙarasa Zainab ta shigo da sallama. Mama ta ce "Anjima zamuyi cigaban kinji? Aisha ta ce "Tom mama. Bayan Mama ta amsa ne Zainab ta ce "Mama ina jin karatunku keda auta, kinga itace zata gajeni in Sha Allah!. Mama ta ce "Ai in Sha Allah Humaira tama sai ta fiku daga ke har yayan naki. Zainab ta ce "Aikuwa dai ga alama, sukayi dariya sannan Aisha ta ce "To ai Anty Zainab kece kika faɗa a waƙarki kuma dama ana mana a islamiyar mu, shinefa na riƙe. Zainab ta ce "To kinji Mama ashe agurina taji. Sukayi dariya sannan Zainab ta ce "Mama zamu tafi kimin addu'a, domin inajin gabana na faɗuwa sosai. Mama ta ce "ki yawaita ambaton azbunanlahu wa ni'imal wakil. Zainab ta ce "in Sha Allah Mama, na gode sai na dawo. Mama ta ce "Zainab nasan unguwar su Shek Abdulh kabir kabuga zakuje, saboda haka banason jin wani abun ya biyo baya. Zainab tayi dariya ta bargidan batare da ta ce komai ba. Fitowa da sabuwar waƙar da tayi, mai suna biuɗaɗɗiyar wasiƙa tayi tana sauraro, wacce jiya da yamma ta bugota, sannan a daran jiya ta gaiyaci masoyanta izuwa gurin majalisin nasu domin anann zata fara sakin waƙar kafin ta saketa a duniya. Ai kuwa masoyanta sun nuna mata cewar zasozo, kodan jin abun da wasiƙar ta ƙunsa. Tin daran jiya take samun saƙonni daga masoyanta akan zasu halarci taron. Wasu kuma suna mata fatan alkairi domin ba a Kano suke ba, bazasu samu damar halartar ba. Haka ta shirya itada halifiyar ta da kuma wani daga cikin halifofin ta maza, suka nufi gurin taron. *SARAH . SAMUEL POV* Samuel ne tsaye a jikin ɗakin Daddy yana sanɗa domin yaga ƙofar a buɗe. Da sanɗa ya tura ƙofar haɗi da leƙawa, baiga kowaba, hakanne yasa ya koma palor domin rufewa koda Daddy yazo sai yayi magana kafin ya shigo. Sarah ce zaune a bakin gadon ta, ta haɗa kaida gyiwa domin tinann shiga ɗakin Daddy, take wata zuciyar ta ce mata, ai Daddy bazai dawo da huriba kawai kije har ki dawo. Hakane yasa ta cire taƙalminta ta nufi ɗakin. Tana zuwa ta tura ɗakin sai ta jishi a buɗe, nann take ta tura kanta babu tinanin komai. Saida ya tabbatar ya rufe palorn kafin ya dawo izuwa ɗakin Momy, ya sameta tana waya, hakanne yasa bai tsaya dubawa ko ita da waye a cikin ɗakinba kawai ya fita izuwa ɗakin Daddy. Tana shiga ta nufi gurin da tasaba ɗaukar kuɗin, amma abin mamaki, sai taga gurin abuɗe, aikuwa ta duba toilet babu kowa ta duba ƙarƙashin gado, nann ma ba kowa. Take ta shiga jiddar kuɗin saida ta ɗiba nasu yawa zata fita taji motsin shigowar mutum. Yana zuwa saida ya ɗan tsaya ya sake kallon ko ina na gidan (wato gefe da gefansa) kafin yasa kai cikin ɗakin, yana shiga ya nufi gurin da yasaba ɗaukar kuɗin, abun mamaki sai yaga gurin a buɗe, nann babu ko tinanin komai ya sa hannu ya ɗiba masu yawa, sannan ya sa a aljihun wandon sa, sannan ya juyo zai fita. Nann yaji takun mutum na dosar ɗakin kuma da sauri. Tana jin motsin shigowar mutum tayi WUFF ta faɗa ƙarƙashin gado gurin da ta saba ɓoyewa, aikuwa sai taga Samuel ya nufi gurin guɗin ya sa hannu ya ɗiba zai fita. Ashe dama shima yana satar kuɗin!? Ta burta a zuciyarta. Da sauri ya faɗa toilet Yana mai jin gabansa na dukan tara-tara, neman yin fitsari a wando ya keyi tsabar ruɗewa... Yana kallo ya shigo ɗakin cikin sauri. Cikin tashin hankali Sarah take kallon mai shigowa ɗakin bayan Samuel ya faɗa toilet. Daddy ne cikin shigarsa na zaman gida alamar dai ya daɗe a gida. Take wani fitsari ya kufcewa Sarah ganinn ya nufo bakin gadon yana amsa waya, ihuu ne ya kufce mata haɗi da sakin fitsari...📝 ? *PAGE* 👉9️⃣ .........Cikin sauri Daddy ya zauna a bakin gadon yana amsa waya. Cikin minti kaɗan ya shirya cikin kayansa na sojoji, baiko tsaya ya kalli abun da ke faruwa a ɗakin nasaba, haka ya fita yana mai gyara rigar sa haɗi da kiran Mommy da ƙarfi! "A'lexa! "A'liza! "Da sauri Mommy tazo haɗi da cewa "Lafiya kuwa? Cikin sauri Daddy ya jefa mata kyin ɗakin haɗi da cewa ta rufe masa ɗaki zasuje Abuja yanzu sun samu kiran gaggawa sai gobe zasu dawo...sannan ya ce idan Samuel ya dawo ta ce ya kirashi. Haka Mommy ta masa fatan dawowa lfy haɗi da kissin ɗinsa sannan ya fita har yana haɗawa da gudu. Mommy kuwa komawa ɗaki tayi batare da rufe ɗakinba. Duk abun da Daddy ke faɗa yana sauraro amma tsabar tsoro ya hana ya fahimci komai, yana cikin hakane yaji alamar zai fita, ai kuwa yazo jikin ƙofar toilet ɗin yana leƙawa har yaga fitar Daddy ɗin, sannan ya sauke a jiyar zuciya yayi hanyar fita. SARAH kuwa lokacin da ihu ya kufce mata haɗi da fitsari sai tayi saurin rufe bakinta, amma fitsarin kuwa saida ya kufce. A kan idonta Samuel ya fito daga toilet har ya bar ɗakin kafin itama ta fito cikin tsoro ta nufi ɗakinta. Tana shiga ɗaki ta faɗa toilet tayi wanka kafin ta fito tana cewa "Walhi daga yau bazan sake satarwa Daddy kuɗiba irin wannan tashin hankali da nake shiga! Haka ta ƙirga kuɗin dubu arba'in da uku (43,000) sannan ta shiga neman kayan da zata saka. *LAƊIFA. SALIS POV* Tana shiga palorn ta tararr da Hajiya Babba sai sakin murmushi takeyi, harda wani lissafi da hannu. Tin daga ƙofar palorn take kiran Hajiya Babba Hajiya. "Wai Hajiya wani irin aiki kika baiwa wannan wawan yaronne!? Allah Hajiya na tsani yaron Please dan Allah a koreshi akawo wani. Cikin mama Hajiya ta ce "Wai wani yaro kike magana a kaine kinzo tin daga waje kina kirana kamar namiki laifi? Cikin tsananin jin haushin AJ Laɗifa ta ce "Hajiya wannan yaron dayafita daga gidannan mana dashi nakeyi Please wani aiki kika bashi? Kafin Hajiya tayi magana saiga Salis ya shigo yana ƙoƙarin zama laɗifa ta ce "Bro please dan Allah ka fita a harkar yaronnan, kaga abunda yamin yanzu kuwa!? Zaginafa yayi harda cewa wai wai yafi ƙarfin yayi dani! Yana ɗan aiki to Walhi sai ya bar gidannan tinda ba gidan ubansa bane. Cikin kwantar da murya Salis ya ce "Haba my sister meye na ɗaukar zafi haka, Allah yaron baida wata damuwa kece dai kike son saka abun a ranki amma karki damu A.J mutumin kirkine. Cikin fushi Hajiya ta ce "To naji zan koreshi tundade kince bakya sonsa, amma bari kiji na faɗa miki... wallhi nima zanyi aure ko kunaso ko bakwaso, tinda na fahimci saboda ina goyan bayankune shine kuke son Sai kun kasheni da raina ko!? To na gode. Cikin mamaki Salis da Laɗifa suke kallon Hajiya domin jin abun da take faɗa. Cikin ƙarfin hali Salis ya ce "To yanzu Hajiya ina ruwan auranki da aikin AJ? Sannan ma meyakawo zancen zakiyi aure bayan muna magana a kan ɗan aikine? Sai a lokacin Hajiya Babba ta fahimci katoɓararr da takusa ta tafka. Ai kuwa cikin sauri da rikicewa ta gyara maganar ta da cewa "To ai nasan halinkune yanzu ina faɗa muku aikin da na ɗauke shi sai kuce ku bai mukuba kumani haka nakeso. Da sauri suka haɗa baki da cewa "Faɗa mana mun yarda? Hajiya Babba cikin farin ciki ta ce "Zai dinga tuƙani duk lokacin da naso haka. Sannan zan dinga aikansa cefane dade sauransu, shikenan fa aikin, ma'ana dai yaron gidana. Da sauri Salis ya ce "To yanzu Hajiya a kan wannan shine kike cewa wai zamuce bamaso?...ai gaskiya ma Walhi daɗima naji kinga shima yaron yanzu sai ya ɗanji daɗi ,Allah ma dai yasa ya iya mota? Hajiya Babba ta ce in bai iyaba za'a koya masa. Ita dai laɗifa bataso AJ yasamu aiki a gidan nasu indai ba aikin gadi bane, amma ya zatayi haka zata haƙura, amma tayi alƙawarin shida kansa zaibar gidan saboda cin mutuncin da zata dinga masa. ( *NI KO S REZA NA CE UMM-UMM FA🤓)* Ta ce "Bro muje nazo da labari? Salis ya ce to muje ɗakina. Haka suka tafi suka bar Hajiya Babba cikin murna ganinn ta shawo kan yaran nata cikin sauƙi. Laɗifa ta ce Bro Inason namaka wata tambaya dan Allah ka bani amsa? Salis ya ce "ina jinki. Ta ce "Shin ADDINIMU ya amince mace musilma ta auri arne? ( KRISTEN) Cikin mamaki ya ce "Ban gane ba? Ta ce "To kaman dai ni Laɗifa zan iya auran wanda ba Musulmi ba? Ta basa maganar dalla-dalla domin taga yana son ɗaukar abun kamar wasa. Salis ya ce "Bana son rainin hankali idan zakimin bayani yanda zangane to kimin in ba hakaba Allah zan koreki waje tinda naga bakida abun faɗa sai shirme. Cikin serus ta ce "Bro Walhi sonsa nakeyi... tin jiya da na haɗu da shi har yanzu ban manta dashiba, kuma inajin zuciyata namin zafi duk lokacin da na aiyana cewa babu aure a tsakanin mu, ganin ba ADDINIMU ɗaya ba. Salis ya ce "Waye... kuma yaushe kuka haɗu... kuma me ya haɗaku??? Cikin rashin tsoro da kuma saboda yayan nata wajan sanar masa da duk wani sirrinta ta fara bashi labari abun da ya haɗata da shi kamar haka... Laɗifa ta ce "Jiyane a clup munje taya zee-zee bikin birthday ɗinta. "Sai me ya faru? Salis ya sake tambayar ta. "Farine dogo kansa yayi wani irin ɗan iskan aski, zaune muke a teburin gabammu wanda muka cika shi da kayan shaye-shaye (abu buwan sha) dade sauransu, Kasancewar gurin bawai iya mune muke gudanar da fatin ba harda wasu hakanne yasa gurin ya cika sosai. Muna cikin hakane sai mukaga ana ihuu! An zagaye wani teburi, muna zuwa sai mukaga mata da maza ne agurin yayinda ake saka gasar kuɗi... Budurwa da saurayi ne zasu fara yiwa junann su kiss batare da kowa ya taɓa ɗan uwansaba, idan macen ta taɓa namijin to shine yaci, idan kuma namijin ne ya taɓa macen to itace ta ci. Taci gaba da cewa...ana cikin haka layi yazo kansa. Sanda tayi shiru zuwa wani lokaci kafin taci gaba da cewa...Suka saka dubu ashirin-ashiri shida wata yarinya, nann suka fara... yarinyar tsaɓar ta cika cikakkiyar yar duniya batayi komai ba amma shi sai ya ke neman ruɗewa hakane yasa ya faɗi. Sai'a ka fara ihuu!. Shikuma cikin jin kunya ya ce a sakeyi. In ta ƙaice maka zance saida sukayi sau uku duk tana cinyeshi. A'na cikin hakane akazo gurin bada kuɗi, duka-duka kuɗin dake jikinsa dubu sha ukune, kuma dubu sintin zai bata (60,000) nann fa ya rasa yanda zaiyi, shima abokin nasa da alamu dai bashi da kuɗi, amma abokin nasa musulmi ne. Nikuma tun lokacin da nayi ido biyu dashi naji gabana na faɗuwa, take naji gayan ya kwanta min har cikin raina, shinefa na karɓi acont ɗin sa na tura masa dubu ɗari. Kuma tin lokacin bai kiraniba, Allah Bro ina sonsa kuma zan iya komai a kansa. Salis ya saki baki da hanci yana sauraron ta. Saida ta gama sannan cikin ihuu!! Salis ya ce "Ya isaaaaa, harsaida laɗifa taji tsoro. Ya ce "Arne, ɗan iska, ɗan clup, mai bin Mata, wanda ya mayar da iskaci sana'a, shine kikeso!? Wanda kika ganshi yana shan bakin wata shine wanda zuciyarki ta gani kuma takeso ko!? Cikin ɓacin rai ya ce "Karki sakemin maganar wannan wawan yaron idan kuma kika sake to wallhi sai na lahira ya fiki jin daɗi, shin ina hankalin ki da tinanin ki, mutumin da ba ADDINIMU ɗaya ba, kuma ɗan iska!!! Tashi yayi yana nunata da hannu ya ce "Karki bari Hajiya Babba taji wannan maganar kuma kema karki sake mai-maita zance domin bazan miki ta daɗi ba a kan haka. Kibar ganin wai ina sonki ina damu da dawarki, hakan ba yana nuna cewa bazan iya hukuntaki bane. Yana faɗa ya tashi yabar ɗakin cikin mamaki haɗi da fushi. Ita kuma Laɗifa kallon bayansa tayi harya bar ɗakin sannan ta share hawayen da suka zubo mata tun lokacin da ya fara mata faɗa. Ta ce "Kaman yanda nace akansa zan iya yin komai to tabbas hakane zanyi komai koda kuwa ADDINIMU mai yardaba domin nidai ina sonsa. *AJ. SARAH* Gudu-gudu sauri-sauri yakeyi domin kuwa yasan ya ɓata mata lokaci sosai. Wayarsa ce tayi ƙara sau babu adaddi amma yaƙi ɗagawa, saida ya gama shirinsa gaba ɗaya kafin ya ɗauka wayar yana mai ɓoye dariyarsa ganin tarin miss call ɗin ta har guda ashirin da uku (23) da sauri ya fito daga ɗakin nasa cikin shiga irin ta masu zuwa club. Cikin mamaki Nana take kallon yayan nata ganin yanda yayi kyu. Ta ce "yaya ina zuwa ne haka kodai kasamo min Anty ne? "Ya buɗe baki zaiyi magana wayarsa ta sake yin ƙara a karona ashirin da huɗu. Kallon Nana yayi wacce ke fama da figar kajin da AJ ya kawo ɗazu wai sune abincin dare haɗida dankalin turawa. Ya ce "Idan ban dawoba kisaka min nawa a ɗaki komai dare zan zo na ci. Nana ta ce "to yaya amma dan Allah karka daɗe kaji...kuma ka gaida minda Anty na.ta faɗa tana dariya. Jin wayarsa ta sakeyin ƙarane yasa ya amsa da cewa zataji, sannan ya bargidan. SARAH kuwa iya ƙuluwa yau ta ƙulu hakanne yasa tayi alƙawarin saita nuna masa fishinta. Kallon sa takeyi cikin mantawa da laifin da yamata ganin irin wani kyu da yayi. Da sauri ta rungume shi tana mai jin cewar ko ina zasu iya shiga dashi ba wanda ya isa ya raina mata saurayi. Yau kan A.J ya ajiye komai a gefe ya kama hannun ta suka nufi gurin da a ke gabatar da birthday ɗin. Cikin dare misalin ƙarfe 12 Daddy ya dawo gida. Yana zuwa ya nufi ɗakin sa, sai yaga ɗakin a buɗe, hakanne yasa ya nufi ɗakin Mommy yana kiran sunan ta. A'leza! "Da sauri Mommy ta fito aɗaki domin kuwa itama barci ya gagareta, tinda SARAH ta fita bata dawoba, shi kuwa Samuel dama yasaba. Cikin yarunsu na tibi Daddy ya ce "Nace ki rufemin ɗaki lokacin da zan fita amma na dawo naga ɗakina a buɗe? Ya ce gaba da cewa...Shin kunsan irin kuɗin da na ajiye a cikin ɗakin! Kuma kinsan kuɗin waye? Lokaci ɗaya fuskar Daddy ta koma ta asalin sojojin da ransu ya ɓaci. Ya ce "Oyaa muje ɗakin mu duba. Tin daga bakin ƙofar ɗakin sukaga kuridon kuɗin a buɗe, cikin sauri Momy ta ƙarasa zaro kuridon kuɗin. Mommy ta ce "Samuel Samuel Samuel! Sai kawai ta rusa ihuu!. Amma sai taga Daddy na murmishii ya ce "Koma waye yanzu zamu kamashi. Mommy ta ce "Ban gane ba? Daddy ya ce "Tin lokacin da akamin satannan na ƙarshe naga abun yayi yawa shine na faɗawa wani abokina shikuma yabani shawarin nasaka CCTV camera aɗakin zan kama kowaye. To hakane yasa na bar ɗakin abuɗe tin da rana. Cikin mamaki Mommy ta ce "Ar You serus? Daddy kuwa cikin murmushin da yazama na ɓacin rai ye ce "Yes. Nann take ya ɗauki computer ɗinsa da yayi connektin da shi ya buɗe. Kallon abun sukeyi har a kazo lokacin da SARAH ta shiga. Kallon juna sukayi cikin mamaki, basu ƙarasa mamaki ba saida sukaga ta ɗebi kuɗin sannan zata fita, saikuma sukaga tashiga ƙarƙashin gado. Saiga Samuel shima ya shigo, shima bayan ya ɗiba sai ya shiga toilet...haka dai suka cigaba da kallo har lokacin da Daddy ya shiga, har SARAH da Samuel suka fita. Lokaci ɗaya Daddy ya koma tamkar bashiba tsabar ɓacin rai! Ita kuwa Mommy kasa yin mgn tayi tsaɓar tsoro domin kuwa tasan yaude mai hana Daddy karya Samuel da SARAH sai Allah, cikin muryasa ta mazaje ya ce "Ina SARAH? Mommy ta ce "Ba ba ba ta ba "cikin ihuu ya ce "Ina SARAHHHHHHHHH!!!!!!!!!!!!!!? Mommy ta ce "Bata dawoba....📝 *PAGE* 👉1️⃣0️⃣ .... *ABDALLAH.* Cikin tsananin mamaki yake kallon address ɗin gurin da zata gabatar da taron nata, tabbas unguwar sune, sannan kuma ƙofar gidan maƙofcinsa, kenann hakan nanufin yau zatayi rawa da waƙa a ƙofar gidan sa!. Afili kuma ya ce "Jiya taje bikin abokina har ta samu damar cin mutuncina, shine yanzu ma take son ta ƙara samun damar yi a karo na biyu ko!. Kallon sunan sabuwar ƙasidar da tace zata sake a gurin taron yayi, afili ya karanta sunann waƙar. *BUƊAƊƊIYAR WASIƘA.* Take ya saki dariya sannan ya kashe wayar yana mai aiyana cewa kodai shi takeson tama martani. *MARYAM.* Wani ihuu tayi haɗi da kwashewa da dariya irin dariyar da kana gani kasan ta muguntace. Da gudu tazo gurin Mommy sannan ta ce "Mommy albishirin ki? Tayi tambayar cikin dariya. Mommy ta ce "Lafiyar ki kuwa? Kinzo sai dariya kikeyi kamar wacce ta zauce?. Tsabar dariya Maryam ta kasa magana sai kawai ta miƙawa mommy wayar tana cewa... "Mommy karanta kiga Ikon Allah. Bayan Mommy ta gama karantawa ne ta ce "Na gani za'a ayi walima ne a unguwar su yayanki kuma shine abun dariya? Maryam ta ce "To ai Zainab Ambato ce zata gabatar da waƙoƙin ta a gurin, kuma kalli wannan sabuwar waƙar kigani, itamafa agurin zatayi, kuma Allah daga jin sunann waƙar zatayi sweet. Tafaɗa haɗi da cewa ai kuwa baza'a barni a bayaba, dama bamu taɓa haɗuwa da itaba saide daga nesa, yau kan har ƙawance zamu ƙulla. Cikin mamaki Mommy ta ce "Amma ai yayanki ya hanaki shiga lamarinta ko? To saboda haka ban yarda kije ba. Maryam ta ce "Mammy kirabu dashi ni nasan komai, shimafa Allah yana son ƙasidun yarinyar kawai dai..."kafin ta ƙarasa Mommy ta kai mata duka tana cewa ai zai nado mara kunya kawai. Ita kuwa Maryam cikin dariya ta je domin shiryawa. *ZAINAB. POV* Kallon taron al'ummar dake gurin takeyi wanda kusan rabunsu basu taɓa ganinn taba. Cikin farin ciki da ƙwanar mosoyan nata take takowa izuwa gurin da a ka ware domin ta. Gurine wanda a ka masa ado da hotunan Shehu Ibrahim inyasa da dai sauran shehunan su, kowa burinsa ya gaisa da ita, yayinda matakan tsaronta da mai gidan da ya gaiyatona ya haɗasu da ita domin bata kariya, sai tare mutane sukeyi. Ita kuwa Zainab faɗuwar gaban da takeji tin a gida sai ƙaruwa yakeyi. A haka ta ƙaraso gurin sanan ta samu guri ta zauna tana sakin murmushi, halifan ta guda biyu mace da namiji, sune suka zauna a kusa da ita, can zuwa wani lokaci kuma ta tashi ta shiga bin layin duk wani malami dake kurin saida ta gaida shi. Saida malamai suka buɗe taro da addu'a kafin aka fara wa'azi a kan aure. Saida malamai biyu suka yi kafin a ka bata. Manyan malam gurin sai binta sukeyi da ido, daga mai aiyana cewa yau zai gabatar da kansa sai mai cewa yayiwa yaran kamu, sai masu jin cewar wannan ai irin tasu ce. Cikin muryarta mai tsaki wajan yabon Annabi Muhammad S a w. Ta fara da addu'a sannan ta shiga gaida manyan malamai da dai sauransu. Nan fa aka saki kiɗa tafara yin wata ƙasida mai taken.... *INDAI KAASONI BANI DA FAR GABA, ANNABI NA BIKA BAN BI WANIN KABA* Nann fa al'ummar gurin suka ɗauka harda malamen dake gurin. *ABDALLAH* kuwa yana cikin gidansa, yana jin duk abundake faruwa, damuwarsa ta saki wannan waƙar domin da ita zai yi amfani wajen kamata da hujja. Har cikin kunnuwansa muryar ta ke shiga wanda ya nutsu yana jin abun da take cewa a cikin waƙar. Saida tayi waƙoƙi guda uku, izuwa lokacin kowa nason jin wannan sabuwar waƙar, ai kuwa take aka kunnata. Kasancewar babu wanda yasan ƙasidar sai gurin yayi tsit ana sauraron ta. *A.J. SARAH.* Kallon mamaki sarah kebin A.J dashi ganin irin abubuwan da yake sawa a kawo kan teburin su, bata tashi ruɗewaba saida taga wasu daga cikin abokansa yaran masu kuɗi sunzo sun zauna a teburin, kuma suma yace su karɓi duk abun da sukeso. Nan fa sarah ta shiga zare ido, domin kuwa tasan abubuwan da a ka kashe sun fi ƙarfin kuɗin ta. Bayan an gama abun da za'a yi ne, kowa ya kama budurwar da yazo da ita suka fara aikata abunda ke kaisu gurin. Hannusa ta kama ta miƙar dashi sannan ta jawoshi izuwa gurinda ake rawa. kallon ta yakeyi ganin yanda take shafa shi ta ko ta ina, nann shima ya fara mayar mata da mar tani. Tin suna shan bakin juna har A.J ya jawota gefe, suka faɗa kan ɗaya daga cikin do kwayan gujerun gurin. Cikin fitar tunanisa ya fara kai hannusa izuwa ƙirjinta, wanda hakan ya bata damar ƙara tura masa ƙirjin nata, bata an karaba taji hannuwansa a fatar ƙirjinta, ya zame rigar maman ta ya sa hannunsa. Tin da AJ yake a duniya bai taɓa shiga irin wannan yanayin ba, haka ya dinga jinsa kamar ba a wannan duniyar yakeba. Sun kai minti ashirin a haka suna shafar juna yana taɓa ko ina a jikinta kafin ya fara ƙoƙarin zame mata riga, bata hanashi ba har saida ya rabata da rigarta, sannan ya shiga ƙoƙarin cire ɗan gajeran wandon da tasa, yana ƙoƙarin hakane, yaji alamar tana cire masa wando, saida ta cire belt ɗin ta fara jan wandon sai kawai taji ya riƙe wandon sa. Lokaci ɗaya ya miƙe yana kiran sunan Allah, kallon gefe da gefen sa yayi yaga kowa harkar gaban sa yakeyi babuma wanda yasan sunayi, ya mayar da Kallon sa izuwa gurin ta, yaga ƙirjinta duk a waje, da sauri ya jawo rikarta yana kare mata jiki shima ya ɗaure wandonsa, ya ce "Tashi kisa kayanki, yayi maganar ne yana juya mata baya. Cikin kasala da mutuwar ji ta miƙe tsaye tana jin baƙon yanayi na sake shigarta, har ta gama bata ko iya magaba. Saida yaji shiru sanan ya juyo, aikuwa ya ganta tsaye tana kallon bayansa, idonta yayi jaa. Ya ce "Mu tafi? Haka ta ɗau jakarta, suka nufi gurin biyan kuɗi. Cikin mamaki taji ance ai abokansa sun biya dukka. Haka suka fito babu mai magana acikin su sai tinanin abun da ya faru sukeyi. A.J ya ce "Sarah kiyi haguri bansan mai ya kaini harna aikata haka a garekiba, ba halina bane, kuma addinmu ma bai halarta haka ba, kuma ina so na sanar miki da wani ab..."Bai ƙarasa ba ta ce "Karɓa wannan kuɗine nazo dasune domin wannan abun amma basuyi amfani a nann ba, kuma idan na je dasu gida za'a iya kamani, saboda haka kawai ka karɓa kayi amfani da su. Kallan kuɗaɗen yayi yana aiyana cewar ai yanzu yafi ƙarfin su. A.J yayi dariya sannan ya kalleta cikin ido ya ce "SARAH yanzu kece kike buƙatar wannan kuɗin baniba, sannan inason na sanar miki cewa gobe zanyi tafiya zuwa Maiduguri, zanyi wata ɗaya, kuma i'naso ki bani acont number ɗinki, idan na tafi zan sake layi ba lallai mu yi wayaba har mu dawo. Cikin Muryar ta da tun tuni take rawa ta ce "Me zakajeyi? Idan kuɗine ai nace zan dinga kawo maka, Please karka tafi ka barni, bazan iya jurewa ba...tana kaiwa aya kuka ya kufce mata, tana jin kamar ta rungumeshi ko zataji sanyi. Ya ce "Sarah ki daina kuka ba zama zanyiba zan dawo, Please kije gida kar Daddy ya gane baki dawoba. Haka yayi Sa'a ta tafi amma ta ce ba gida zatajeba gidan su Usha zata kwana, hakanne yasa ya rakata har ƙofar gidan sannan ya ciro kuɗi masu yawa ya ƙara mata, ya ce ta ɓoye har yadawo. Ita dai zara sai kallon sa takeyi tana tinanin kode yayi kuɗine!, sannan tana jin cewar kamar in ya tafi bazata sake ganin saba. Haka ya juya yabar gurin yana mai jin tausayin ta domin kuwa yasan sun rabu kenan har a bada. Haka itama ta shiga gida cikin rashin kwarin gwiwa. Yana shiga ɗakinsa ya fito ya shiga bayan gidansu ( toilet) wanda ke tsakar gida, yana wanka yana aiyana cewa yanzufa daga yau na daina wanka a irin wannan bayan gidan, wanda kana wanka ƙasa na hawa ƙafafunka. Har ya gama ya fito yana aiyana abubuwa da yawa. Saida yazo saitin ɗakin Nana zai huce yaji kamar ana magana, hakanne yasa ya dawo da baya ya kara kunnansa, tabbas magana akeyi amma baya jin me a ke cewa, amma idan anzu gurin yin dariya dariyar tana fitowa. Saida yayi kamar ya shiga ɗakin amma ya fasa yana mai tinanin kodai kallo takeyi, haka dai ya bari a kan da safe zai tambayeta. Yana shiga ɗakinsa yaga abincin sa, ya buɗe yaga namane sai dankali ɗan kaɗan naman kazar ya fishi yawa, sai kawai ya ɗau cinyar kaza ɗaya yasa a baki yana taunawa yana kallon lokacin da bakinsa dana Sarah ke haɗuwa, tashi yayi ya fita ya ɗaura a laula ya gabatar da magariba da isha. Nana kuwa Salis ya samu nasarar shawo kanta, yayinda suna gama waya zata goge number sa, idan ya kira kuma saita ga ba kowa take ɗagawa, kokuma suyi wayar dare, tabbas ta yarda da shi har zuciyarta,. Yau kwana biyu kenann amma taɗan saki jiki dashi ganin da gaske sonta yakeyi. *WASHE GARI. HAJIYA BABBA POV* Tin misalin ƙarfe 8 na safe ta gama shirya komai da za'a buƙata na ɗaurin aure, tin daga kan waliyan ango da kuma waliyanta, gamida gaiyatar mutanan da basu santaba. Ta gama tanadar komai, yayinda ita yayanta wanda suke uba ɗaya shene wanda zai jagoranci auran, shi kuma AJ wasu iyayen bogi aka samo. Misalin ƙarfe goma na safe Hajiya Babba ta kira yaranta Laɗifa da Salis. Kallonsu tayi sannan ta ce "Kamar yanda na sanar daku cewa yau zamuje Abuja domin tabbatar da in gancin ma'ai katan da a ka ɗauka a kamfanin ku, da banyi niyar zuwaba amma na samu kira yanzu wai dole sai naje. Saboda haka zan tafi, amma yau zan dawo. Cikin sauri laɗifa ta ce "Haba Mommy yanzu kece zakiyi tuƙi tin daga Benue har Abuja? Mommy ta ce "No tare zamu tafi da AJ. Kafin Laɗifa tayi magana SALIS ya ce "Tom Mommy amma fa dan Allah karki kwana Please ku dawo da wuri. Laɗifa ta ce "Yanzu Mommy wannan yaron har ya iya tuƙin da zai jaki har Abuja? Gaskiya nidai ban yardaba. Hajiya ta ce "To kizo ki kaini? na ce kizo kikaini, tindade bakison ya kaini, waima dan Allah menene yaronnan ya mikine? Kafin Hajiya Babba ta rufe baki Laɗifa ta ce "Zaginafa yayi yana matsayin ɗan aki amma kice wai me yamin. Salis ya ce "Hajiya dan Allah ki rabu da ita, idan kin shirya kawai muje mu rakaki mota. Hajiya Babba ta ce "Nagode Salis Allah ya maka albarka, bari yaron ya ƙaraso domin shima yanzu tafiyar ta sameshi. Salis ya ce "Kekuma bari kiji na faɗa miki, dama kinsan tin jiya ina tunanin zancen da kikamin ko? To ki cire idonki a kan A.J idan ba haka ba Allah ranki zai ɓaci. Cikin mamaki da rashin kunya Laɗifa ta ce "Yanzu kaima yaya kana goyan bayan wannan yaron? Har kana cewa zaka ɓatamin rai, cikin kuka tayi sama ɗakinta tana cewa ita walhi saide duk abunda zasu mata suyi amma Walhi saita kori wannan yaron daga gidannan. AJ kuwa tin safe Hajiya Babba ta kirashi a kan ya shirya domin goma da rabi zasu tafi, hakanne yasa tin safe ya shirya ƙaryar da zaiwa inah da Nana. Bayan sun gama karyawane shida Nana, ita kuwa Innah sai fama takeyi har lokacin. Ya kalli ƙanwar tasa sai ya kejin kamar idan ya tafi wani abu zai samesu. Cikin sanyin rai ya ce "Nana?. "Na'am ta amsa tana jin yanayin muryar da yayi mata maganar. "Inah. Ya sake kiran sunan innah wacce ke tura naman kaza a baki. Itama ta ɗago ta ce "Ya a kayi Abdul jabaru? AJ ya ce "Innah zanyi tafiya yau, kuma zanyi kwana uku kafin na dawo shine nake tinanin idan na tafi kaman wani abu zai sameku? Cikin sanyin murya innha ta ce "Ina zaka kuma me zakaje yi? Cikin irin ƙaryar da ya shirya musu ya ce "Inna ai dama nace miki na samu aiki, to ogan gurin aikin namune ya zaɓomu mu biyar akan zamuje wani aiki. Kuma Innah muna dawowa shikenan mun zama manya a gurin aikin. Inah ta ce "To Abdul jabaru wannan wani irin aikine haka? AJ ya ce "Innaaaaah!! Haba mana irin wannan tambaya kamar yar jarida, kinsan dai bana sata bana shaye-shaye bana... "Kafin ya ƙara sa ta ce "Naji, ba sai ka ƙarasa ba, ta ci gaba da cewa... kai yanzu badama na maka faɗa sai kamin wannan zance? To sai mutum yana yin sata da shaye-shaye zai jefa kansa a damuwa? To Walhi Abdul jabaru na gaji da irin wannan ɓoye-ɓoyen da kakemin, yanzu komai fa a gidan nann yazama na masu kuɗi, hatta ruwan da muke sha, kuma nace wacce sana'a kakeyi kace kai baka sata baka shaye-shaye kuma..."Kai inann haba dan Allah!, ni har kin fara sakamin ciwon kai, yanzu gashi har nafara makara, nidai kimin addu'a kawai inah ta. Ya faɗa yana kamo mata hannu alamar wasa. Ita dai innah haka ta bishi da ido har ya tashi zai fita, ita dai jikinta na bata kamar AJ na ɓoye musu wani abune, saida ta ga zai fita kafin ta iya buɗe baki ta ce "Allah ya dawo da ku lfy. "Amin my amarya ko kefa. AJ ya faɗa domin ganinn ya kawar mata da kokwanton da ke ranta. Aikuwa tayi murmushi tana cewa, kaide Abdul jabaru halinka sai kai, sai kuma wannan mara kunyar ƙanwar taka mai kama da ifiritai. Nana tayi dariya ta ce "Ooo innah, yanzu ni mai kuma namiki da kike haɗani da jin sin aljannu? AJ ya ce "Nana tashi muje ki karɓo muku saƙo. Haka suka fito yayinda innah ke faman surutu ita kaɗai. P .O .S .Sukaje shida Nana ya ciri kuɗi dubu hamsin (50,00) Kafin ya ce mata "Wannan kuɗin bance ki nunawa innah ba, ki barsu a gurinki, duk abunda kuke da buƙata kawai ki siya. Nana ta ce "Wai yaya zaka daɗene haka? Kuma waye ya baka wannan kuɗin? Ni dai gaskiya nimafa kafara bani tsoro kamar inna!? AJ ya ce "Bana son dogon surutu, kede kiyi abun da nace miki. Haka ta ƙarɓa ta tafi, yayinda takeda tarin tambaya da zata masa idan ya dawo, sannan itama jikinta na bata cewar idan ya tafi bazai dawoba. Koda tazo gida haka ta ɓoye kuɗin batare da innah ta ganiba. A.J kuwa yana shiga gidan, Hajiya Babba da Salis suna fitowa daga cikin palorn gidan. Cikin fara'a Salis ya ce "Babban yaya har ka iso kenann? A.J ya ce "babban yaya kuma!? Salis ya waske da cewa ka iya mota kuwa? "Cikin wannan surutun nasa ya ce "To ai ni saide mota ta iyani, nida nayi aikin gidan biredi, kuma nine Mai kaiwa shago-shago. Hajiya Babba ta ce "Lallai kam kune masu iya mota. Salis ya ce "To ka tuƙa Hajiya a hankali domin ita ba biredi bace. Haka sukayi dariya kafin Hajiya Babba da AJ suka shiga motar, iro mai gadi ya buɗe musu suka fita cikin farin ciki......📝 [ *PAGE* 1️⃣1️⃣ ....... *A.J*. Tin da suka shiga motar yake tinanin mokomarsa idan an ɗaura wannan auran. Tafiya sukeyi suna ɗan taɓa hira jifa-jifa, Hajiya Babba kuwa ruƙon Allah ta keyi a zuciyarta a kan aurannan ya ɗauru kar a samu wata matsala ko ɗaya. Ita dai tasan abunda zatayi ba haramun bane, ADDININMU bai haramtaba, sannan ta wani ɓangaran ma sunna zasu aikata, to amma shin A.J yasan nufinta a kan wannan auran!. Awani ɗan ƙaramin gida suka tsaya, Hajiya Babba ta ce "Wannan shine gidan malamin da zai ɗaura mana auran, na sanar dashi komai kaide abun da nakeso shine...duk abun da zaice maka kace eh. A.J ya ce "Angama hajjaju makkatu. Bayan malamin ya gama yiwa A.J duk wata tambaya ne sanan ya ce su jira har lokacin sallar a'zahar tayi idan sun idar sai a ɗaura. Haka kuwa a kayi bayan sallar a'zahar al'ummar da suka gabatar da salla a wannan lokacin suka sheda auran Abdul jabaru da amaryarsa maimuna Aliyu (Wato Hajiya Babba) a kan sadaki dubu ɗari ɗaya. Shedu suka sheda waliyai suka amince al'umma suka ƙarɓi goran ɗaurin aure. Bayan an ɗaurane mlm ya kira A.J ya tambayeshi akan cewa shin da amin cewarsa a ka ɗaura wannan auran? A.J ya ce "Eh da yardasa kuma da amin cewarsa. Shide mlm yana ganin abun kamar ba mai yuwa bane domin kuwa yasan Hajiya Babba tin mijinta na raye. Haka suka shiga mota izuwa hotel domin a can zasu kwana kafin gobe subar ƙasar a yanda Hajiya Babba ta shirya kuma sai sunyi wata biyu kafin su dawo. Bayan sun kama ɗakine Hajiya Babba ta ce masa bari taje ta dawo. Tana fita ta huce gurin masu sayarda kazar amarci, ta sayo guda biyu sannan ta sayo musu lemo da ayaba da dai sauran abubuwan da zasu buƙata a daran. A.J kuwa Hajiya Babba na fita ya shiga toilet ya watsa ruwa yana cewa "Kai jama'a yanzu dai da gaske na zama maikuɗi! Tinda nake ban taɓa shiga ɗakin hotel bama amma wai yanzu gashi ni kaɗai zan kwana a kan wannan makeken gadon. Yana faɗa ya faɗa a kan gadon yana mai sakin wata dariya irin ta wanda suka samu sauyin rayuwa kamar sa. Yana cikin wannan hali tinanin Sarah ya faɗo masa. Ya ce "Allah sarki Sarah bazan manta da keba, idan burina ya cika kece ta farko da zan fara mallakawa mota. Yana faɗa ya saki dariya yana kallon kansa ganin daga shi sai tahul ne yasa ya tuna da cewa ashefa baida kayan sawa. Tini ya mayar da na jikin sa kafin ya tada sallar magariba domin kuwa har wani gurin anyi. Kasan cewar sun daɗe a gidan malam. (Baisan cewar zaman da sukayi a gidan mlm Hajiya Babba ta shirya kanta bane🤓) Hajiya Babba. Da sallama ta shigo ɗakin riƙeda ledodi a hannunta har guda huɗu. Kallonsa tayi ganin yanda yayi da fuskarsa alamar damuwa. Ta ce "AJ angon hajiya lfy kuwa? AJ yace "Ina kika sakamin layin wayana? Hajiya ta ce "Ai sai mun koma gida zan baka saboda kar a damemu muna cin amarci. Cikin AJ yabada wani sauti gooo. Ya ce "Ina son nayi waya da Innah ta da ƙanwata? "Ok kabari Saida safe. Kafin yayi magana ta ce ga kazar amarci na siyo mana kazo muci domin shima yana cikin dokokinmu. Kasancewar dama yunwa ya keji sai ya ce "Ikon Allah yanzu cin kazarma a cikin doka yake? Hajiya tayi dariya sannan ta buɗe musu kazar suka fara ci yana mata surutu ita kuwa Allah-allha take taga sungama ta samu kanta, domin yanda takejin idan bata yi komai yauba to abubuwa zasu lalace mata. Bayan sungama Hajiya Babba ta ce "Tom Sai mutashi mu gabatar da Sallah? A.J ya ce "ai lokacin isha baiyiba. "Ok tom yanzu dai ga kayan barci kaje kasaka nikuma zanyi sallar magariba da isha kafin ka fito. AJ ya ce "No ai ni da wannan kayan zan kwanta karki damu. Hajiya Babba ta ce "Shima yana cikin dokokinmu. Ai kuwa da sauri ya ƙarɓa yana faɗawa toilet domin sakawa. *BAYAN MINTY TALATIN* "Ban gane cewa a ɗakinan zaki kwana ba? Cewar AJ yana kallon Hajiya Babba cikin mamaki. "Eh ai dama nace maka aɗaki ɗaya zamu dinga kwana idan har naso, kuma kayarda. Cikin rikicewa Ya ce "Amma ai kince babu abunda zai shiga tsakaninmu har mu cika shekara ɗaya ko? "Eh amma ai idan naso to sai anyi domin shine auran idan har babu kulawa ai auran ya zama aikin banza. Shin ma wai in tambayeka? Yanzu idan bamu kulawa da junan ai Allah sai yayi fushi damu domin munyi wasa da sunnar annabin sa. AJ ya ce "Nifa bana gane duk wannan zancen naki, idan har sai wani abu ya shiga tsakaninmu to walhi na fasa bazanyi ba, ai ba haka kikacemin ba. Ya cigaba da cewa...kince saboda yaranki subar damunki zakiyi kuma gashi kinyi amma zaki fito da wani batun daban. Hajiya Babba tayi wata almurar dariya wacce ita kaɗai tasan munufarta kafin ta ce "Shi aure bawai ana yinsa dan adinga kallon juna bane, nasan kasan komai amma kana nuna kai yarone, karka damu duk yanda kason yi kayi a kwai igiya uku har a gun Allah kayi ibada kuma Annabi zaiyi alfahari da kai. A.J ya ce "No-no Hajiya Salis abokinane kuma shine ya sa har na sanki kuma kece kika haifeshi!! Walhi na fasa zan sakeki yanzu afasa auran. Hajiya Babba ta ce "Tom ko ka sakeni ai an riga da anɗaura kuma komai daran daɗewa zai sani, kuma kayi a sarar kuɗinka, sannan zaka dawomin da wanda na baka. A.J yayi shiru yana tinani kafin ya ce "Hajiya nayarda amma dan Allah kar wani abu ya shiga tsakaninmu zan biyaki kuɗinki amma nidai bazan aikata wannan abun Kunyar ba, nifa banayin abunda ADDINIMU yayi hani dashi. Yana maganar yana jin idonsa nawani yaji-yaji alamar barci. Hajiya ta ce "Ok tom shikenan bari nayi wanka saina fita izuwa nawa ɗakin gobe sai a raba auran kaikuma kabani kuɗina. Tana maganar tana sakin dariyar mugunta. Tana fitowa ta sameshi har yayi barci. Afili tace "Kai Nagode wa Allah, ashe nayi dabara kamar nasan bazai yardaba, inama guda huɗu nazuba maganin ba biyuba kaga da har gobe zaikai yana barci. Ta cigaba da cewa...kai ina kallon halak amma a hanani. Take ta cire kayan jikinta ta hau gadon ta fara shafa shi har ta rabashi da kayan jikinsa. Kallon sa takeyi tana jin tsikar jikinta na tashi domin kuwa an daɗe ba'a gamuba. Cikin ƙwarewa da abun ta fara shfashi tako ta ina, sannan ta fara aiwatar da gudirinta. *GIDAN SOJA* *POV* Sarah kuwa bata samu wadatatcen barciba domin kuwa AJ ya barta da muguwar buƙata, gakuma tinanin abunda yace wai bzai dawoba sai wata uku, kuma ba lallai suyi wayaba har ya dawo. Misali qarfe bakwai na safe, yan gidan su Usha sun fito yin breakfast, sukaga Sarah, nan ta musu ƙaryar cewa itace tacewa Mommy zata kwana anan. Babu yanda ba'a yi da itaba akan ta tsaya taji abinci amma ta ce wai ana kiranta a gidane. Haka ta bar gidan cikin sauri, domin bataso Usha ya dawo ya sameta domin shi kaɗai yasan tazo gidan, kuma dayake tin safe yafita booll. SAMUEL kuwa duk yanda yakai da yasake ganin wannan yarinyar ta jiya ya rasa, da a lamun dai bata zoba, kuma yana son ya mayar mata da kuɗinta, hakanne yasa ya tsaya jiranta har ɗayan dare, ganin batazo bane yasa ya samu wata rarinya yaransu shida Umar kowa ya kama tasa suka rage zafi, amma yau baiyi wannan gasar tasu ta kiss ba. Hakanne yasa suka kwana a ɗakin da ya kama musu ɗin. Dasafe ya tashi ya sallami yaran matan da suka kwana dasu sannan ya yi sallama da Umar ya na cewa Allah yasa Daddy ba'a gida ya kwana ba. Da sanɗa ta tura ƙofar get d'in gidan amma ta jishi a rufe, hakanne yasa taje ta ƙaramin get d'in ta tura, sai ta ganshi a buɗe, ai kuwa ta tura kanta, tana ganin motar da Daddy ke fita da ita a fake saida gabanta yabada rass!. Haka ta shiga sojojin na kallon ta itama tana kallon su, domin kuwa Daddy ya ce duk wanda yadawo karsuce masa komai a cikin SARAH da Samuel. Haka ta shiga gidan ba wanda ya ganta, har ta shiga ɗakinta, ta ɓoye kuɗin da AJ yabata, sannan tayi wanka tasa kayan barci ta nufo palor domin karyawa. Tana zuwa taga Mommy da Daddy zaune suna hira sama-sama. Ta gaishe su, sannan ta fara haɗa ti. Tana cikin haka Samuel ma ya fito daga ɗakinsa dagashi sai singlet da gajeran wando, alamar dai ya kwana a gida. Sarah ta kalleshi sannan cikin zuciyarta ta ce "Ashede shima yana satar kuɗin amma zaice wai ƙarya a kamasa, Allah dai yasa Daddy ya kamaka ido da ido, walhi da nayi murna mugu kawai. Kallon da ya watsa matane yasa tayi ƙasa dakai tana tura masa baki. Saida suka gama breakfast kafin Daddy ya kira manyan sojojin sa na hannun daman sa wanda tin jiya ya sanar musu da abunda ya faru. Bayan sun shigu palorn ne ya je ya rufe ko ina harda kicin sannan ya ce Mommy ta shiga ɗaki. Amma ta ce ba inda zata. Sarah and Samuel sai kallon mamaki sukeyi ganin wannan mugayen sojojin da ko dariya basayi riƙeda bulala, ya buɗe baki zaiyi magana Daddy cikin harshin English ya ce "Waye ya shiga ɗakina a cikinku jiya da yamma? Nan fa suka fara kallon-kallo domin kuwa babu alamar wasa a fuskar Daddy dama kuma sunsan halinsa. Sarah ta ce "Walhi Daddy Samuel ne . Shima Sameul ya ce itace, nan fa suka fara musu. Sai Daddy ya ɗauko vedio ya nuna musu, tindaga shigar Sarah harda na Samuel. Nan fa ido ya raina fata. Cikin ɓacin rai Daddy ya shiga zane Sarah sauran sojojin kuma suna zane Samuel, daddy ya ce "Ina kike kaimin kuɗi idan kin ɗauka? Amma Sarah ta kasa magana sai ihuu tana Mommy!! Mommy Amma Ina Daddy sai labtamata yakeyi, ita kuwa sai ihu takeyi amma ta kasa magana. Ganin haka yasa Daddy ya saurara da dukan nata ya ce "idan bata fito masa da kuɗin saba wallhi saiya karyara. Sarha cikin tsananin zafin duka ta ce "Daddy zan faɗa zan faɗa. Haka take tacewa amma ta kasa faɗa hakanne yasa Daddy cigaba da dukanta harsaida tace Daddy AJ AJ AJ. Cak Daddy ya tsaya da dukan ya ce "What? Teell me waye AJ? Cicin tsananin wahala sarah ta kwashe komai ta sanarwa da Daddy, akan cewar shine yake turata ta sato masa kuɗi. Ai kuwa take ran Daddy ya ƙara ɓaci jin cewar AJ ɗinma musilmi ne. Take yace ta miƙe ta kaishi gidan su AJ ɗin. Mommy ma Sai kuka takeyi ganin irin dukan da Daddy ke ma Sarah kamar ba mace ba. Ɓan ɓangaren Samuel kuwa tini yace hotel yake zuwa da kuɗaɗen. Ai kuwa Daddy yasa a ka ɗaureshi aka sakashi a ɗaki. Sarah kuwa dan dolema ta meƙe suka shiga mota, Daddy ya kira station akan suzo gidan sa. Haka Sarah jiki duk jini ta kama nunawa motar sojojin nann gidan su AJ. Ai kuwa babu ko sallama suka shiga gidan yayinda Daddy ke waje Yana jiran fitowar AJ. NANA da Innah kuwa suna ƙoƙarin karyawa sukaji parking ɗin motoci a ƙofar gidan su a lamardai balafiya ba. Basu an karaba sukaga sojoji ta ko'ina sun zagayesu gawata yarinya kuma a gabansu sai kuka takeyi. Cikeda tashin hankali innah ta saki kofin shayin dake hannuta, batasan sanda ta meƙw tsayeba. Wani soja ne yayi Maganar da tasa inah rusa wani uban ihuu!! Cikin harshen English ya ce "Ina AJ? Ai kuwa Innah ta ce "Waiyoooo Allah jama'a ku taimako mana yan fashi da safen Allah! Wani mari da wani soja ya batane yasa jinta da ganinta tsayawa na hucin gadi. Jikake tsit kamar ba'a halarci Innah a wannan gurinba. Sojan ya dawo da kallonsa gurin Nana wacce tini itama ta fita a haiyacinta. Ya ce "Ina AJ? "Ba babb ba ba ya ya, ta manta da cewar sojan baya jin Hausa domin kuwa a rikice take gakuma Innah a ƙasa a sume, ga kuma itama ta kasa magana. Ai kuwa sojan ya sake cewa ina AJ? Da ƙyar Nana cikin Hausa ta iya haɗo kalmar bayanan. Ai kuwa sojan nan ransa ya mugun ɓaci ganini sai Hausa suke masa, ai kuwa ya tsinka mata mari sannan ya ce "Menene batanann?. Ya mai-maita abun da tace? Sai alokacin Nana ta tina da cewar ashefa baya jin Hausa tsabar shigar mari. Aikuwa cikin turanci da saurin baki haɗi da kuka ta ce "Bayyanan yayi tafiya jiya kuma bamu san ina ya tafiba. Ai kuwa sojan ya gane metace sai kawai ya ce "Ok tinda bayanann Bari mu tafi daku idan yaji kuna hannunmu ai zaizo koma ina yaje. Sojan ya faɗawa Daddy ai kuwa Daddy ya shigo gidan yana zagin sauran sojojin akan mai sukeyi bazasu kawowa ƴansanda suba. Sannan ya ce "Ni na tsani duk wani musulmi koda kuwa macece, idan har tana Salha to wallhi babu mutunci, mutanan da suka mayarda kisa ba'a bakin komai. Nidai ADDINIMU bai aminta da kisaba amma yau sai na nunawa wannan A.J ɗin cewar ADDININMU ba ɗayabane, shege inama shi muka kama. Haka Daddy ya sa aka watsawa innah ruwa ta farko sannan a ka yi waje dasu.....📝 *Oooo ni Allah!! Kaima AJ Ina kai ina taɓa irin wannan bala'in. Allah sarki innah da Nana😓.* *PAGE1️⃣2️⃣* .........Haka sojojinnan suka tasa ƙeyar Innah da Nana har bakin motar Police ɗin da suka iso gurin, al'ummar unguwar kowa yafito yana kallon ikon Allah, wasu daga cikinsu kuwa kuka sukeyi ganin yanda Innah tayi kamar wacce bata cikin haiyacinta. Nana kuka Innah kuwa ta kasa magana tsabar ruɗewa. Babu ko imani suka turasu a cikin motar sannan sukayi gaba. Ana zuwa police station babu wani bincike saboda ganin wanda ya kawosu, haka Daddy yasa aka turasu cikin sell sannan ya kalli police ɗin daya ƙarɓi ƙarar ya ce "Kar a sake a bada belinsu harsai yaron yazo gidana da kansa. Cikin sauri police ɗin ya ce "Yes sir. Daddy ya bar police station ɗin cikin ɓacin rai. Bai taɓa kawo cewar Sahra zata iya satar masa kuɗiba, dama yasan saide wani ya zigata wanin ma wai musulmi mai Sallah shine yake tura yarinyata tana satar min kuɗi!! Haka Daddy ya shiga mota yana tinanin idan ya kama A.J Allah ne kaɗai yasan abunda zai masa. *SALIS. LAƊIFA. POV* Bayan Hajiya Babba da A.J sun tafine Salis ya koma cikin gidan domin yin mgn da laɗifa, amma taƙi buɗe masa ƙofa, hakanne yasa ya kira Nana yace mata yana zuwa, dama sunyi a kan zasu haɗu idan AJ ya tafi. Aikuwa bai bar ƙofar gidan ba sai wajan ƙarfe biyu, sannan ya ce zai tafi, amma gobe da safe zai kawo mata kyutar bazata. Haka sukayi sallama ya tafi gida cikin farin ciki. Laɗifa kuwa abubuwan ne suka haɗe mata biyu. Ga haushin A.J da takeji wanda batasan meyasaba, gakuma haushin hanata zuwa club ɗin da Salis yayi jiya, tabbas taso taje tasake haɗuwa da wannan gayan, kodan tasamu sukuni a zuciyarta . A kowani lokaci idan zatayi ƙoƙarin kawar da tinaninsa sai taji soyayyar sa na ƙaruwa a zuciyarta. Tana cikin hakane wani tinani ya faɗomata, aikuwa afili tace "Tabbas shine Walhi shine, take ta shiga wanka domin kuwa gurinsa zataje, to amma ai tamasa rashin mutunci, take abunda ya faru tsakanin ta da Umar abokin Samuel ya shiga dawo mata a kanta. Fitowarta keda wiya daga gidansu ƙawarta Yusra wacce ke unguwar su Umar ɗin ne ta hango wani saurayi shida wata budurwa a jikin motarta suna hira. Kallon gurin tayi cikin tsananin mamaki ta ce "Yusra kinga irin abubda yasa bana son zuwa unguwar ku ko? Yanzu-yanzu daga ajiye motar har wani wawa ƙazami zai ɓatamin Itaki? Ai kafin Yusra tayi magana har Laɗifa ta kai gurin da Umar ke tsaye. Yana cikin hirarrsa irin ta mayaudara yaji muryarta tana cewa "Uban waye ya baka izinin tsayuwa a jikin motana?. Dagashi har yarinyar da ya tare yake zuba mata ƙarya akan cewar motar sace suka juyo suna kallon ta. Kafin suyi magana ta ci gaba da cewa...inbanda hauka da rashin tunani daga ganin mota sai kawai ka zoda wani ƙazamin kayanka ka jin gina ajiki, kalleka fa kamar wani ɗan almajiri wai kai saurayi har kana kawo budurwa jikin motana. Cikin jin kunya Umar ya kalli yarinyar da ya gama shirya mata ƙarya, zaiyi magana taja wani dogon tsaki mtsiiiiiiii sannan ta bar gurin. Laɗifa ta ce Mlm kobazaka ma tsa bane? Umar kuwa ya kasa magana tsabar kunya haka ya bar gurin motar yana sosa kai ya kasa magana, amma abunda tamasa ya tsaya masa a'rai. Laɗifa tace "Sune irin ƴan isakan samarin da suke zuwa wajan ƴan Mata da yaudara, kukuma kuna jin zancen su saikuyi sauri kuce kun amin ta dasu, daga baya kugane ashe matsiyata ne. Yusra ta ce "To mlm bansan iskanci ni kinga ina kula irinsune? Kuma wannan ma ai ɗan unguwar nann ne kinga gidansu can? Laɗifa ta ce "Au shi ƙaryar tashima har a unguwarsu yakeyi? Yusra ta ce "Tom kindai gani. Ajiyar zuciya Laɗifa ta sauke tana tinanin cewar to idan taje gurinsa me zatace masa! Nan take ta kawar da wannan tunanin ta shirya domin zuwa gurin Umar. Tayi niyar zuwa a yau amma ta bari sai gobe. *SALIS* yakira number Nana a karo na babu a dadi yana son sanar mata dacewar bazai samu damar zuwaba sai da yamma, amma ba'a ɗauka, hakanne yasa hankalin sa ya kasa kwanciya, kuma ga yasan A.J baya gari, tin jiya Hajiya Babba ta kirashi tace masa zasu kwana a can sai yau zasu dawo, hakanne yasa Salis ya nufi gidan su Nana, domin yasan Nana bata barin waya da nisa hk. Abuɗe ya samu ƙofar gidan, hakanne yasa ya samu yaro ya tura ya kira masa Nana, aikuwa yaron ya ce "Wasu sojoji da ƴan sandane suka zo ɗazunnan suka kwashe su itada innar su, kuma sunada yawa. Ganin Salis bai fahimci abunda yaron kecewa bane yasa ya ƙarasa gurinda yaga wasu samari na zaune. Tambayar su yayi gameda abinda yaron ya ce. Aikuwa nan take suka sanar masa da komai. Cikin tashin hankali Salis ya tambaye su wani police station aka kaisu? Sukace walhi basu saniba. Haka Salis ya shiga bin duk wani police station da yasani amma ko ina yaje zancen ɗayane wato basu san inda a kakai suba. Yayi yawo a cikin Benue MKD amma bai samu gurin da a kakai suba, hakanne yasa ya dawo gida yana tinanin shin mesukayi haka harda sojoji!. Washe gari laɗifa ta shirya izuwa gurin Umar. Dama ƙawarta Yusra sun daɗe da barin unguwar, hakanne yasa bata ma san inane a salin gidan ba. Bayan tazo unguwar ne ta kalli unguwar taga an sakeyin gine-gine, sai tarasa gane wannene gidan. Tana nan tsaye saiga wata rarinya kusan sa'ar ta zata huce. Laɗifa ta ce "Jimana yarinya? Yarinyar ta kalleta ta ce "Wacce yarinya? "Idan bakeba wacce agurin nann ko kina nufin keba yarinya bace? Cikin jin haushin sunan da takirata dashi na yarinya tazo har gabanta ta ce "Kalleni nafi ƙarfin kikirani da yarinya walhi, domin na huce nann, duk abunda kike taƙama dashi inadashi sabada haka karki sake cemin yarinya. Laɗifa ta buɗe baki da hanci tana kallon ƴar ƙaramar yarinyar da kecewa tanada komai. Ai kuwa ta ce "Ina komai ɗin yake anan kina tafiya kamar wata sabuwar kamu babu ko kintsi, hakanne kuma baza'a kiraki da yarinya ba? Nan fa yarinyar ranta ya ɓaci ta ce "Uwarki ce mara kamun kai! Kalli irin shigar da ke jikinki ko gyale babu bare hujjabi wai a hakan ke musulmace! Kai Allah ya wadaran irinku da basa ɗaukar ADDINIMU da muhimmanci...ai bata rufe bakiba taji sauƙar tagwayan mari... Jikake tass-tass. Itama zata rama Laɗifa ta riƙe mata hannu tana cewa "Idan kika sake wannan ƙazamin hannun naki suka taɓani sai kin gane Allah ɗaya ne. Aikuwa hankalin mutanan dake kusa da gurin ya dawo kansu ganin Hadiza riƙe da kumatu. Da mamaki suka nufo gurin ganin yau ansamu wacce tafi Hadiza rashin kunya harda marinta. Ai kuwa Hadiza ganin ƴan unguwar su sunga marin da a kamane yasa ranta ya ƙara ɓaci. Duk unguwarsu kowa tsoranta yakeyi daga maza har mata, batada kunya ko kaɗan ga rena na gaba da ita. Kafin laɗifa ta ankara taji sauƙar mari har biyu. Dai-dai mazan sun iso gurin. Nann fa faɗa ya ɓarke da kyar aka rabasu Hadiza sai zagin ta takeyi tana cemata karuwa. Laɗifa kuwa ranta yayi mugun ɓaci, wani saurayi ne yazo yana tambayar ta meya haɗata da wannan mahaukaciyar? Laɗifa ta kasa magana sai jan nufashin ɓacin rai takeyi. Ana cikin haka ne Umar yazo gurin wanda shiɗin yayane ga Hadiz. aikuwa yana ganin laɗifa ya ganeta da sauri ya iso gurin da take ya ce "Amm umm, alamar dai yana son tuno sunan ta. Ai kuwa laɗifa na ganin sa taganeshi. Umar ya ce "Kaman nasanki? Amma maiya haɗaki da wannan yarinyar har kika biye mata kuna faɗa, ƙanwata ce batada kunya? "Wai saboda na tambayeta shekenan zatamin rashin kunya! Umar ya ce "Kidaina biyewa irin wannan yaran barinma ita da kowa yasanta a unguwar nann bata da kirki, nima yayanta bata barniba. Amma ina zakije? Cewar Umar? Bata bashi amsaba, tsabar haushin abunda ya faru, kuma tayi alƙawarin saita ci uban wannan yarinya dukda kuwa ƙanwarsace. Haka ta shiga motar tamasa alamar ya shigo, ai kuwa ya shiga, suka bar unguwar. Tun lokacin da tayi magana ya gane itace yarinyar da Samuel yake nema, amma bai gane itace ta masa wannan cin mutuncin ba domin kuwa abun ya ɗan daɗe. A bakin titi ta tsaya sannan ta kalleshi ta ce "Ina fatan ka ganeni ko? Umar ya ce "Eh naganeki...kece ta club ko? Laɗifa taji daɗin da bai tuna abun da tamasa ba. Ya ce "Jiya munje domin biyanki kuɗinki amma bamu haɗuba lfy kuwa? "No jiya banje ba... sannan wani kuɗi? Dama ni auro na baku? "A'a Samuel ne yace muje ya biyaki. "Samuel Samuel, ta mai-maita sunan a ranta sau biyu sannan tace "Please yanzu ina zan ganshi? Umar ya ce "yanzu dai bazaku haɗuba saboda baya gari, amma zan baki number sa, kuma kema kibani taki number zan masa bayani dama shima nemanki ya keyi. ( Yamata ƙaryar cewar yayi satane😆) Cikin jin daɗi ta bashi number ta sannan Itama ta amshi ta Samuel ɗin da kuma ta Umar ɗin. Aikuwa ta zaro kuɗi ta bashi haɗida masa godiya sannan tayi gida. Yayinda Umar ya girgiza kai alamar dai da wani abu a ƙasa. *HAJIYA BABBA.* *A.J* Haka ta rabashi da komai na jikinsa ta cigaba da gudanar da sunna. Tabbas Hajiya Babba tayi mutuƙar ƙoƙari wajan danne zuciyarta daga aikata zina. Hajiya Babba tanada mutuƙar juriya domin kuwa ita ɗin ta daban ce acikin mata. Abun da yafaru da ita da AJ kenann a wannan daran. Tin tanayi ita kaɗai har A.J ya fara jin sauyin yanayin sa, ai kuwa yana buɗe ido ya saukesu a cikin na Hajiya Babba akansa. Abunda AJ bai taɓa yiba kenann. Cikin tashin hankali yayi ƙoƙarin tashi amma yaji babu hanya, gakuma abun sa acikin.....h. Tin A.J yana ina biye mata dayake ta shayar dashi abubda baiyi tunaniba, sai ya ce yagaji amma ta ce ita bataji komaiba, tin A.J na jurewa harfa ya kasa domin kuwa takai shi bango, da ƙarfi yake ƙoƙarin tureta amma yaji sai wani nishi takeyi alamar fa ita yanzu za'a fara. Tin yana jin daɗin abun har ya fara jin komai ya tsaya masa. Ai kuwa ya ce "Please Hajiya Walhi na gaji zan mutu! Yayi maganar kamar yayi kuka. Inaaa Hajiya bata san meyakecewa ba. Ai kuwa ya kurma wani uban ihuu haɗida cewa "Waiyoooo Allah zan mutu walhi zan mutu ki taimakamin nagaji abuna zaifita, walhi na gaji. Ai kuwa Hajiya Babba ta ce "Please walhi yanzu na fara samun gamsuwa ka ƙaramin minty talatin. Cikin kuka A.J ya ce "Walhi bazan iyaba dan Allah kiyafeni na tuba kuma wallhi bazan iya ko minty ɗayaba? Kai AJ fa kuka yakeyi sosai yana baiwa Hajiya hauƙuri. Hajiya Babba kuwa da takejin kamar yanzu ma sha'awar ke ƙara zuwar mata tayi WUFF ta koma. Ai kuwa AJ tin yana ihuu har ya daina muryarsa ta dashe sai ajiyar zuciya ya keyi. Tin yana iya jin abun da takeyi har ya saki jikinsa aikuwa Hajiya Babba ta samu damar yin komai yanda takeso. Shikuwa gogan naku numfashin sa ne ya ɗauke take ya suma ko numfashi bayayi. Madam kuwa batasan ɓarnar da tayiba sai aikin gaban ta takeyi😲........📝 *PAGE* 1️⃣3️⃣ ....... *HAJIYA BABBA.* Saida ta ji komai zam-zam daga gareta kafin ta sauƙa tana mai jin komai ya mata dai-dai, lumshe idanuwanta tayi tana jin wani irin nutsuwa na shigarta ta ko ta ina, afili ta furta... Auran namiji mai jini a cika shine rayuwa, kai gaskiya addinin musulunci yayi wajan halarta auran ɗan cikinka, kai A.J Allah ya saka maka, aure kuwa mutu ka raba, yau ɗinnan ma zamu bar ƙasar domin kuwa bana son komai ya taƙura mana daga cin amarci. Hannunta ta kai tana shafo angon nata domin taji ko yana jin me take cewa, ita a tinanin ta shima idonsa biyu. Sai taji kamar ma a sanƙare yake, ai da sauri ta sauƙo daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin. Mai zata gani!. Ganin A.J tayi a kwance kamar babu numfashi, ai da sauri ta hau kan gadon tana mai taɓa ƙirjinsa ko zataji yana motsi. Toilet ta shiga ta ɗebo ruwa ta watsa masa, amma bai farkaba. Ita kanta ta manta da cewa babu komai a jikinta. Ruwa mai sanyi ta haɗa sannan ta je ta ɗaukoshi kamar wani ɗan jinjiri. Dama ba komai a jikinsa, ai kuwa ta tsoma shi a cikin ruwan, itama ta shiga ciki. Ruwan take ɗiba a hannunta sannan ta zuba masa a kai, saida tayi sau biyar ana shidanne ya saki wani dogon ajiyar zuciya, wanda yasa Hajiya Babba yin wani murmushi. Buɗe idonsa ya keyi a hali har ya saukesu a kan ƙirjin ta wanda idon nasa ya tsaya a haka yana kalllonta kamar yasumu tibi. Tariyo abunda ya faru yakeyi wanda cikin lokaci kaɗan ya fahimci abunda ya faru. Kafin yayi magana yaji hannuwata a wani ɓangare daga jikinsa. Sai a lokacin ya sake dawowa cikin haiyacinsa, ganin dagashi har ita tsirara suke, ya meƙe tsaye wanda yayi dai-dai da miƙewar Hajiya Babba itama, aikuwa sai gasu tsirara shida ita, wanda lokaci ɗaya A.J ya koma cikin abun wankan yana rufe ido. *ZAINAB VOP* Kowa dake gurin ya nutsu sosai domin kuwa waƙar ta ɗau hankalin mai sauraro. Kaman yanda ta ce, sunan waƙar buɗaɗɗiyar wasiƙa, tabbas hakane, buɗaɗɗiyar wasiƙarce, domin kuwa tayi maganganu masu kamada tanayi da wanine ko wasune. Ana cikin haka, manyan mutane suka fara mata ihisani, wasu suna mata kyutar guɗi wasu mota wasu kuma addu'a. Saida ta gama tsaf, suna cikin haɗa kayan su zasu tafi, taji ana kiran sunan ta cikin dariya. Da gudu Maryam ta ƙaraso gurin haɗi da rungumeta ta na cewa "Saiyada Zainab ni masoyiyar kice sosai tin ba yauba naso in ganki amma Allah baiyiba. Cikin mamaki Zainab take kallon Maryam domin kuwa tasan ta, Kasan cewar duk family Shek Kabiru kabuga, ba ɓoyayun fuskoki bane ga al'umma. Amma Zainab ta kawar da mamakin ta ce "Aiya ya kk? Maryam ta ce "Ina lfy ya ƙoƙari da haƙuri da mu? Zainab tayi jimmm! Sannan ta ce "Haƙuri ai sai ma'aiki...mudai muna kwai-kwayansa ne. "Hakane...to yanzu zan iya samun number ki? Ta faɗa har yanzu tana murmushi. Zainab ta ce "Ba damuwa. Sannan ta bata wayar tana satar kallon Maryam ɗin, tana ganin yanda yarinyar ke kama da Abdalha kamar an tsaƙa kara. Saida Maryam ta gama sa sunan sannan ta kira, tana kira sai taga wayar na ƙara, ta ce "Maryam shek Kabir kabuga. Itama ta ce "Zainab A Ambato. Maryam ta ce "Waye baisankiba a faɗin Nijeriya? Zainab ta ce "Shek Kabir kabuga shine ma haifinki? "Kin san shi ne? Tafaɗa domin taga me Zainab ɗin zatayi. Zainab ta buɗe baki da nuyar yin mgn sai tayi ido biyu da Abdalha wanda ke fitowa daga cikin gidansa ganin al'ummar gurin sun ragu, ai kuwa dama idonta gurin yake kallo, ai kuwa shima dayake yafito a zuciye sai kawai ya kai kallonsa gurinda yake tinanin zai ganta. Ai kuwa yana ɗaga kai sai suka haɗa ido. Kallonsa takeyi tana jin faɗuwar gaban da takeji tun da tazo yana ƙaruwa. Da sauri ta kawar da kanta tana haɗe fusaka. Yayinda ita kuma uwar surutu wato Maryam. Ganin Zainab ɗin bata bata amsa bane yasa ta cigaba da cewa...shine ma haifina kuma karkiyi tunanin ko nuɗin irinsuce, a'a ni ba haka nakeba, ni kowa nawani mutuƙar ADDINIMU ɗaya, saboda haka karki damu ni fan ɗinki ce kuma..."Bata ƙarasa ba tayi ido biyu da Abdalha dake tsaye a kusa dasu yana binta da wani kallon da yasa cikin ta ya bada ƙuuuuuu. Ai bata an karaba taga yana dariya haɗi da buɗe mata ƙofar gidan gaba alamar ta shigo sutafi. Cikin tashin hankali Maryam ta gyaɗa masa kai kamar zatayi kuka. Abdalha kuwa yayi kamar zai fito daga cikin motar ai kuwa Maryam bata ko tsaya tayiwa Zainab sallama ba ta nufi gurin abdulha ta buɗe motar ta shi sannan shima ya shiga yana mata murmushi yaja motar yabar gurin. Take Zainab ta saki wani dariya mai kama da murmushi, sannan ta ce "Kagama duk wani muna furcinka, ni nafi ƙarfin tarƙonka, Kuma indai nice ina dai-dai da ku. Tana gama faɗa tacewa masu haɗa musu kaya suyi sauri su gama Ta samu kyautar mota, guda biyu a gurin, hakanne yasa ta ce da halifiyar ta ta da ta hau ɗaya daga cikin sabbin, shima ɗaya na mijin da sukazo tare haka, ita zata hau wacce sukazo da ita. Tana kan hanyarta ta tafiyane ta kira, yayanta Isa ta sanar masa da cewar Abdalh fa yana shirya mata wani abun. Nann take ta faɗa masa duk abunda ya faru tsakanin ta da Maryam. Ai kuwa yace karta yarda da yarinyar, sannan kuma ta san irin mutanan da zatana hurɗa dasu. Haka suka gama wayar yayinda Isa yake tsokanarta da cewar, wannan waƙarfa sai ta jawo kace nace, kuma fa waƙar tabada salo. Baifi minty ɗaya da kashe wayartaba, taga wasu motoci guda biyu sun shiga gabanta, ɗaya ta hagu ɗaya ta dama. Hakanne yasa ta yi saurin taka burki. Aikuwa kafin kace me...har sun sauƙo daga motocin, sun buɗe nata motar, ɗaya daga cikin su ya buga mata ginɗin bindigar dake hannusa, ai kuwa nann take ta suma. Suka bar motar tata a gurin suka kwashe komai na cikin motar sannan suka sakata a motarsu suka bar gurin. *ABDALLH* *POV* Bai tsaya a ko ina da Maryam ba sai gida. Bai ce mata komaiba har suka shiga cikin gidan. Ɗakinta ta nufa cikin tsoro amma Abdalh ya daka mata wani abun tsawa wanda yasa tayi saurin dawowa baya tana riƙe siket ɗinta dake ƙoƙarin kadata. Hannunta ya kama ya shiga parlon Daddy ai kuwa ya samesu dukkaninsu harda Mommy da su Sadiya. Da sallama ya shiga hannusa na cikin na ta, kafin a amsa masa sallamar ya yi wurgi da ita sannan ya ce "Gatanan Momy kince a daina dukanta ko!? To na barta ban daketaba amma daga yau bazata ƙara amfani da wayaba, kuma daga yau ban yarda konan da ƙofar gida tajeba har sai an dawo hutun makaranta. Abdalha Yana maganar hansa na masa kamar ya kamo ta ya karkaryata. Alhaji kuma Shek wato Daddy. Shek Kabir kabuga babban malamin sunna na ƙasar Nijeriya wanda ko ina an san dashi wajan baiwa addinmu wato addinin Musulunci gudun mawa sosai. Ya ce "Abdalha samu guri ka zauna. Babu musu Abdalha ya zauna yanayi kamar ya mari Maryam wacce ta fara kuka jin abunda ya ce. Tabbas tasan duk abunda Abdalha ya ce a kansu to Daddy baya musu, hakanne yasa ta fara kuka tun yanzu. "Menene yasa kace bazata sake reƙe wayaba? Cewar Shek yana kallon magajin nasa. Nann take Abdalha ya kwashe komai ya sanarwa da shek. Sannan ya cigaba da cewa...ranarfa Daddy rawa nazo na samu sunayi a palorn ƙasa itada wasu ƙawayanta, sun kunna waƙoƙin wannan sha-sah-shar yarinyarr. Shek ya kalli Maryam ya ce... *GIDAN SOJA* Tin daga harabar gidan sauran sojojin da ke gadin gidan suka fara sara masa cikin sauri domin kuwa sunga yanayin ogan nasu babu sauƙi. Reƙe yake da hannun Sarah yana janta da ƙarfi sannan yana kiran sunan matar tasa, wacce itama tinda suka bar gidan take kuka ganin yana neman kashe mata yara. Ta wani ɓangaran kuma itama tana tunanin yanda Sarah ta saba da wani har yake turata ta sato kuɗi, domin ita a tunaninta AJ ɗin ba musulmi ne. Taso ta buɗe Samuel ya fita, amma sojoji ne har guda huɗu agurin suna gaɗinsa. "Eliza!...Eliza!...Eliza!? Da sauri Mommy ta fito daga cikin ɗaki ta na mai share hawayen da suketa mata zirya. Jefa mata Sarah yayi sannan cikin yare ya ce "Luk at Yaron masu Sallah ne yake sakata ta sato mana kuɗi, yanzu gashi yaron ya gama tara kuɗin ya bar gari, hatta uwarsa da sister ɗin sa basu san inda yakeba... Ya gudu ya barsu. Ya ci gaba da cewa...damafa haka yaran musilmai ɗinnan suke, basuda hankali saboda sunsan iyayensu talakawa ne. Kuma ƴan uwansu basa taimaka musu, sai kawai suzo su ɗinga yiwa yaran mu irin haka ko! Daddy yayi maganar yana nuna mommy kamar itace AJ ɗin. Cikin tsananin mamaki Mommy ta ce "Muslim? For this house? My daughter! No-no is laya. "Ina uwar tasa take? Daddy ya ce "Na kaisu sell har sai yadawo idan har yana son iyayansa. "Thank you. Sannan ta kama kan Sarah ta buga da jikin kujera sannan tace "Musulmi da yarinyata!? Kinsan suwaye mutanana, to duk cikinsu babu na kirki, wallhi da nasan kina tare da yaron da saina sa an ci ubansa tun ba yanzuba, kuma Walhi idan har ya saka ƙafa a gidannan sai ya biya komai sannan anci uwarsa. Idan kuma baizoba Walhi mamarsa da ƙanwarsa saide su mutu a cikin sell. Shegu ɓarayi matsiyata dagin marasa mutunci. Walhi na tsani musulmai na tsani duk wani abu da ya shafesu, bana son ganin su, na tsanesu! Natsanesu!!!!!!!! Ta ƙarasa cikin ihuuu!!. Ta cigaba da tattaka Sarah kamar zata kasheta. Jin hakane yasa Sarah fashewa da wani irin kuka, ga kanta da ya fashe, ga wani biyu-biyu da take gani tsabar tashin hankali, sai ihu takeyi amma Mommy bata tsayaba. Sameul kuwa jin abunda Mommy ta kecewane yasa ya fasa faɗar abunda yayi niya. Duk da yana cikin ɗaki amma yana jin duk abunda Mommy ke cewa domin kuwa ihuuu takeyi. DADDY yasa a ka fito da Samuel ya haɗa su a guri ɗaya shida Sarah sanan ya fara magana cikin faɗa da nuna cewar komai sukaji da gaske yakeyi. Ya ce "Samuel daga yau zuwa kwana shida ka nemomin duk inda kake kaimin kuɗi, kuma bazaka fita ko inaba, zan baka wayarka domin duk wanda kake kaima kuɗin yaji halin da kake ciki ya kawo mun kuɗina, kuma idan kuɗin ya huce kwana shida hammm! Sunanka Sorry. Kuma daga yau a cikin ɗakin kusa da kicin zaku dinga kwana dukkanku. Ya dawo kan Sarah ya ce "Kekuma daga yau bazaki ƙara fita ko ina ba, har sai A.J ɗin ya kawo min da kuɗina kuma har gidannan, sannan ke bazan baki wayarkiba, kuma abinci sau ɗaya za'a baku, har zuwa lokacin da kowa zai kawo min kuɗaɗena. Kai Samuel duba ɗari takwas zaka biya. Kekuma tinda shi wanda kike kaiwa kuɗin musulmi ne, kuma shege to miliyon uku zai biya harda dubu ɗari biyar, idan ba hakaba wallhi saide karya dawo Benue. Haka Mommy ta goyi bayan sa, domin kuwa Momy ta tsani musulmai fiyeda Daddy. Haka kuwa a kayi, Samuel da Sarah a ka turasu a wani ɗakin da babu komai a ciki saide hasken gulob guda ɗaya. Kuma ɗakin haɗe yake da toilet. Ɓangaren su Nana da Innah kuwa tunda a ka turasu sell babu ko mutum ɗaya da yazu domin dubasu, harzuwa wannan lokacin Innah batayi maganaba sai hawaye dake bin fuskarta. Tun safe har qarfe biyar na yamma babu abunda a ka kawo musu da niyar suci. Nana kuwa tin tana kuka harta fara tunanin dalilin me a ka kawosu. Ta kalli Inna ta ce "Innah Kodai yaya yana sata ne? Batayi tunanin Innah zata bata amsa ba ganin tin ɗazu tana mata maga bata um bata um-um. Sai a lokacin inna tayi magana cikin muryar tsufa da kuma yunwa da damuwa haɗida fargaba ta ce "Nana babu shakka Abdul jabaru sata yiyi, domin kuwa in ba sataba baza'a mana irin wannan cin mutuncin ba! Tana faɗa hawaye na wanke mata fuska, Nana ta ce "A'a Innah Walhi yaya baya sata saide ko shari a ka masa. Cikin kuka Innah ta ce "Nana a'i'na ya samu kuɗin da yake mana komai? A ina ya samu kuɗaɗen da ya siya mana wayoyi? Shin ya taɓa faɗa miki cewar ga irin san'ar da yakeyi? Wani lokaci ma nama kawai zai ce muci, muba ƴaƴan kowaba. Idan na tambaye kekan ki kinji abunda yake cemin... Ni bana sata. Bana bin mata bana shaye-shaye bana komai!! !!!!!!!!! Ina ta ƙarasa tana cewa haka yake cemin, ashe kuɗi yake sata shine yanzu ya tafi ya barmu da masifar!!! Ta share hawaye ta ce "Tabbas yasan da haka shine yasa ya gudu ya barmu!!! Nana tayi shiru tana tunani. Can ta ce "Tabbas Innah yaya yana ɓoye mana wani abun, ranar da zai tafi ya bani kuɗi, wato jiya, masu yawa na tambayeshi yace min wai ƙara tambayarsa. "Inna ta ce "Yanzu da zaitafima munce ina zaije, yamana ƙaryar banza, gashi tunda ya tafi bai kiramuba, shikuma idan an kira bata shigaaaaa. Inna ta ƙara fashewa da wani kuka mai ƙarfi wanda yasa ɗaya daga cikin ƴan sandan daka musu wata tsawa wacce tunda suka shigo yake zaginsu da aibatasu wai suna mata amma suna sata, kasan cewar shima ba musilmi bane. Haka yake musu tin ɗazu. Shiru sukayi suna haɗewa a guri ɗaya domin har sun fara tsoran sa....📝 ? *PAGE1️⃣4️⃣* ......Police ɗin ya kallesu cikin ƙas-ƙanci da cin mutuncin ya ce "Idan baku rufe mana baki a'nan ba sai na gyara muku zama yanzunnan, kodan kunci sa'a tunda kukazo babu wanda ya taɓaku shine har kuke samun damar cika mana kunne da surutu, to karna ƙara jin tarinku agurin nann idan ba hakaba kuma...babu ruwana da ku matane cin ubanku zanyi tunda ai ku ɓarayine. Cikin tsananin tsoronsa Innah da Nana suka ƙuntse kukansu suna takurewa a guri ɗaya. Haka Innah da Nana suka wayi gari a cikin seel ɗinnan babu ci babu sha, sannan babu wanda ya zo garesu. Misalin ƙarfe 8 nasafene Nana ta ce da Innah "Innah yunwa nakeji bazan iya ba a kwai kuɗi a gida da yaya ya bani zanje na ɗauko sai mu dinga siyan abinci. Innah ta ce "Nana addu'a kawai zamuyi in ba hakaba bamuda kowa in ba Allah ba, sannan kike maganar zuwa ɗauko kuɗi yaushe yayan naki ya baki kuɗin? "Ranar da zai tafine kuma sunada yawa, zasu ishemu harda Berlin kanmu, bari na ƙwada zuwa ko Allah zaisa ya barni. Innah ta ce "Nana daga yau har zuwa lokacin da zan mutu a cikin wannan gurin to wallhi bazan ƙara taɓa komai na Abdul jabaru ba, indai shine zai fitar dani, kokuma kuɗin satar da ya saba samowa to na ƙwammace mutuwa a haka, saboda haka nidai babu ruwana da komai da ya shafi Abdul jabaru, tunda har zai iya jawo masifa ya gudu ya barmu, to haƙura! na haƙura!!! Inna ta ƙara maganar ƙirjinta na mata wani irin zafi, ga hawaye da ya wanke mata idanu. Nana ta ce "Haba Innah dan Allah karkici haka, shima yanzu ai bakisan halin da yake ciiiba dan Innah ki yarda da yaya bazaiyi abunda kike tunaniba, Please ina ki yafe masa dan Allah!? Itama ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Innah wacce kana ganita kasan bata cikin haiyacinta. Inna ta kasa magana sai kuka takeyi tana shafa gadon bayan Nana. Nana ta ce "Innah yunwa wallhi ina jin yunwa zan mutu! rabona da abinci tun jiyafa! Please ki yarda naje na ɗauko kuɗin dan Allah Innah ta? Tafaɗa tana ɗagowa daga cinyar Innah tana riƙe ciki. Domin itama yunwar takeji kamar ta yi ihuu amma haka ta danne ta ce "Nana idan har zasu barki kije to kije ki samowa kanki amma nidai ƙwara na mutu yau ɗinnan, tashi kije Allah yasa ya saurareki. Nana ta ce "Amin. Bakin sell ɗin tazo tana kallon ƴansanda da suke kaiwa da kawowa a gurin, shikuma mai jiran nasu yana tsaye da wani alamar dai wata maganar sukeyi. Sai ta rasa me zatace masa domin ya sauraretNa, ai kuwa ta tuna ba Hausa ya keji ba, domin tunda sukazo bataji yayi Hausa ba. Ta tsaya a bakin gurin ta ce "Am am am yalla'bai". Bai jiba. Sai ta ɗaga muryar ta ce "Oga. Nan ma baijiba alamar dai zancen nasu ya ɗauki hankalin sa. Sai ta sake cewa "Ogaaaa! Da ƙarfi wanda yasa dukkanin yan sanda seda kowa ya juyo yana kallon ta. *LAƊIFA. SALIS. POV* Haba Umar meyasa baka sanar dashi ba? Cewar laɗifa tana waya da Umar tana sanar masa da cewar ta kira number Samuel amma ba'a ɗagawa, shikuma yana sanar mata da cewar ai Samuel baya ɗaga baƙuwar number. Yanzu ina zamu haɗu domin zuwa gidan nasu?, cewar Laɗifa? Umar ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce "Bazai yiwu muje gidansu yanzuba amma dai ki tsaya zan kirashi zuwa gobe domin ina tunanin bai dawo bane? Cikin muryar da kana ji kasan tayi zurfi cikin soyayya ta ce "No Umar please yanzu nakeso muje, wallhi ina son ganin sa, idan ban ganshiba a kwai matsala? Umar ya ce "Ok tom kisameni a unguwar mu sai mu tafi yanzu. Ai kuwa cikin sauri ta ce "Tom jost minti goma. Haka da yamma Salis ya koma gidan su Nana ko an sakesu amma yaga har yanzu basu dawoba. Nan fa hankalin sa ya tashi domin zuwa yanzu yasan babu lafiya sosai. Haka ya zauna a gurin har zuwa wani lokaci kafin ya bar gurin cikin rashin kwarin gwiwa. Washe gari ma da safe ya kira number Nana amma no amsar, haka ya koma gidan ya sake ganinn sa a rufe kamar yanda ya rufe jiya, domin farkon zuwansa a buɗe ya samu ƙofar Shine ya rufe. Yana tunanin kamar ya shiga gidan amma ya tsoro, yana cikin hakane wani tsohon abokin AJ yazo hucewa, wanda ganin Aj yana abota da yaran masu kuɗine sukuma yana ja baya dasu yasa suka rabu da yaron, amma har zuwa wannan lokacin suna gaisawa da yaron mai suna kamal. Zaune suke a cikin motar Laɗifa Umar ya sanar mata halin gidan su Samuel a kan iyayensa basa son musilmai, ko shima da suke abota iyayansa sunyi dashi amma yaƙi, kuma har yanzu idan abban su ya gammu tare saiya kusa karyashi, nima idan nasake ya kani ubana zaici, kuma babban soja ne. Laɗifa ta sauke a jiyar zuciya sannan ta ce wannan duk mai sauƙine, indai zan samu ganin sa. Umar ya ce "nima bansan meyasa baya ɗaga min wayaba (Umar baisan an kama Sameul ba) SALIS ya ce "Salamu alaikum? Kamal ya amsa da "w slm. "Dan Allah ko kasan ina a ka kai masu wannan gidan? Kamal ya ce "Walhi nima tin lokacin da abun ya faru bansan ina a ka kaisuba, na je duk police station ɗin dake kusa damu amma shiru shine na haƙura. "Yauwa ko ka san wani soja ne a kace yazo ya tafi dasu? Ko kasan gidan sa? "Kamal da yasan komai tsakanin A.J da Sarah tin ba yanzuba. Ya ce "No ban san gidan sa. "Salis ya ce " Ok yanzu amma ai kasan yaron gidannan ko? "Eh nasan shi abokina ne sosai. "Ok tom zaka biyoni zuwa gida ka rakani mu shiga cikin gari neman inda a ka kaisu? Kamal ya ce "Ok ba damuwa. Domin kuwa yaga alamar Salis ɗin ba wanda zai tsaya yiwa musu bane, gakuma yaga kamar a rikice ya ke. Bayan sun je gida ya ɗauki motarsa ne suna cikin tafiya yaji wayarsa na ƙara, yana dubawa yaga Hajiya Babba. Bai ɗagaba saida ya samu gefen titi ya tsaya kafin ya fito da wayar. Saiga wani kiran ai kuwa yana ɗagawa ya ce "Please Hajiya ina A.J? Abun da yaji Hajiya Babba na cewane yasa ya tsaya da maganar tasa yana mai sauraron ta har tagama. Ya buɗe baki zaiyi magana ta ce "Ku kula da kanku bazan daɗeba ka kula da laɗifa. Kutttttt yaji ta kashe wayar. Dafe kansa yayi yana jin wani ɗacin abunda yake faruwa daga jiya zuwa yau. Yaso ya sanar wa da Hajiya Babba cewar ya samu wacce ya keso, amma yanzu gashi babu Nana itama Hajiya Babba tana zancen sai tayi sati ɗaya ko fiye da haka. Salis bai kawo komai tsakanin Hajiya da AJ ba kawai suka cigaba da tafiyarsu shida kamal. Saida sukayi yawo sosai kafin a hanyar dawowarsa suka ga wani police station kamar dai ba'a aiki a cikin sa. Kamar bazasu shiga amma kamal ya ce "Su shiga su tambaya ko Allah zaisa a dace. Suka shiga ciki suna raba idanu. Wani ɗan sanda suka gani shi kaɗan a bakin mushigar gurin, ya tambaye su wa suke nema? Kamal ya masa bayanin abunda ya kawosu, ai kuwa ya ce "ba nann a ka kawosuba. Salis zaiyi magana police ɗin ya haɗe girar sama da ta ƙasa, ya ce ba nan bane. Ganin kamar dai suna ciki sai Salis yasa hannu a aljihun sa ya ciro kuɗi masu yawa ya kama hannun plec ɗin ya saka masa. Ai kuwa ya washe baki yana sanar musu da cewar suna ciki. *GIDAN SOJA*. *POV* Kaman yanda Daddy ya ce sau ɗaya zai dinga basu abinci haka a kayi, tin jiya har yanzu sau ɗaya ya basu abinci, amma kowa nasa. Sannan bai baiwa Sameul wayarsaba sai yau, ita kuwa dama Sarah ya ce bazai bataba. Washe gari Daddy yasa a ka buɗesu ya shiga ya baiwa Sameul wayarsa yana ƙara faɗa masa cewar kar kuɗinsa ya huce kwana shida. Yana kallon Sarah jikinta duk yayi sanyi ga har yanzu kuka takeyi amma ya kawar da kansa ya bar ɗakin sanan yasa a ka rufesu. Ai kuwa Daddy na fita Sarah tayi wajan Samuel tana cewa "Please Samuel call A.J for me please? Samuel kuwa ko kallonta baiyiba yasa buɗe wayarsa yana kallon tarin miss call da aka masa, domin kuwa Daddy bai kashe wayar ba. Number Umar ya fara kira, ai kuwa kira ɗaya Umar ya ɗaga haɗi da cewa "Haba Samuel ina ka shigane muna ta kuranka amma no amsar? Samuel ya ce "No yanzu babu lokaci, nann ya kwashe komai ya faɗawa Umar. ai kuwa Umar ya zaro ido yana cewa "harda Sarah? Sameul ya ce "Please yanzu meye abun yi? Umar ya ce "gaskiya kuɗin da yawa, amma ina wannan yarinyarr da kace zaka sameta? Samuel ya ce "Ka haɗu da itane? Umar ya ce "ai jiya tare da ita muke nemanka. Nann Umar ya kwashe komai ya sanar masa. Take Samuel ya saki wani ajiyar zuciya ya ce "Good! Aikinka na kyu, yanzu ka kira ta ka sanar mata da komai sai kawai tazo ta fitar dani? Umar ya ce "kai haba da huri haka? Ai sai kasa ta renaka, bari kawai nasan me zan ce mata, zatazo ta fito da kai. Haka sukayi sallama yayinda Umar ya ƙara mamakin daddyn su Samuel gaskiya baida kirki, ƴaƴan samafa kenan bare ƴaƴan wasu, kai gaskiya zuciyar kafirima batayiba. Haka dai ya cigaba da tsorata da lamarin mutumin, sannan yana tausayawa Sarah Sosai. Sarah ta ce dan Allah ya kira mata A.J? Cikin tausayin ta da ya faraji tin jiya ya kalleta ya ce "Please Sarah waye Aj? Sarah ta ce "His my boyfriend. "Like Haw? Sarah ta kwashe komai tsakanin ta da AJ ta sanarwa yayan nata sannan ta ɗora da cewa...i love him so much, please Dan Allah kiramin shi. Haka ya bata wayar tasaka numbar AJ ta Kira, amma bata shiga haka ta dinga kira amma babu alamar zata shiga. Samuel ya ce "Haba Sarah wai wai!! Meyasa zaki yarda dashi? Yanzu haka kuɗi yayi ya gudu ya barki. Yanzu ga halin da kike ciki....✍️ I' *PAGE1️⃣5️⃣* ......Kinsan ba'a yarda da musilmannan domin basu da kirki burinsu kawai su cuci mutum su gudu su barshi saboda haka nifa dama bana yarda dasu, ko Umar da kike ganinmu tare nasan irin zaman da nakeyi dashi, amma ke kin ɗauki yarda kin baiwa wanda baya ƙaunar ADDINIMU, nasan shi baya sonki kawai yayi amfani da kene ya biyawa kansa buƙata ya ware. Kuka Sarah takeyi tana tunanin maganar da A.J ya mata ranar da zasu rabu! Cikin zuciyarta ta ce "kenan da gaske A.J ya tafi bazai dawo ba!? Wani irin kuka ta sake tana mai jin ƙaunar AJ ɗin na ƙara mata yawo a duk sass-sassan jikinta... Tabbas ta yarda da AJ kuma tasan zai dawo gareta, domin tasan yana sonta. Sai kuma ta tsya cak tana tunanin tunda suke tare ya taɓa cewa yana sonta kuwa!? Bama wannan ba, shin mema yace min ranar da na bashi kuɗinnan!? "Kiriƙe wannan kuɗin domin yanzu kece kike buƙatar su, sannan ki bani acont number ɗinki zan turomiki wasu. Tabbas haka yace mata. Kenan da gaske yayi kuɗi ya gudu!? Gashi ya bar gidan iyayensa! To dama haka halin musilmai yake! Haka sukeyi!. Sai kawai ta fashe da kuka wanda yasa Samuel kamota yana rarrashin ta. Sannan ya ce "Yanzu a ina zaki samu miliyon biyu? Sarah ta ce "idont no. Kafin Samuel yayi magana wayarsa ta fara ƙara hakanne yasa ya ɗaga yana kwantar da Sarah a kan cinyarsa yana cewa Hello. *HAJIYA BABBA. A.J* Hannu takai tana son buɗe masa idon nasa wanda ganin ta tsirara ne yasa shi rufe idon, ganin yaƙi buɗe idonne yasa ta ɗauki shi cak tamkar wani ƙaramin yaro ta kaishi kan gadon tana kwantar dashi. Ai kuwa da sauri ya jawo bargo yana rufe tin daga kansa har ƙafafun sa. Hajayi tayi dari sanan ta ce "Angona lokacin sallah fa yayi ka tashi idan munyi sallah sai mu koma barcin. Yana jinta amma yayi shiru yana jin cewar wannan matar ta gama dashi har a bada. Wankan tsarki tayi sannan ta ɗauro a laula kafin ta fito ta saka kaya sai murmushi takeyi, tana tunanin sauran mazajan da ta aura. Mijinta na farko. Ko sati basuyiba ya saketa domin kuwa har kuka saida yayi dukda lokacin tana ƙarama, idan ya fara kwanciyar aure da ita baya ko a'wa ɗaya zai gaji yayinda ita kuma a wannan lokacin batama san me a kayiba, hakanne yasa a ka raba auran. Sai tayi dariya tana tuno mijinta na biyu. A daran farko. Bayan sun gama duk wasu sharuɗa da ADDININMU ya tanada ga duk wasu sabbin aure. Ya ɗauko kaza yana zumuɗi, haka ya dinga bata harsaida tagoshi kafin shima ta bashi. Ganin ita ɗin bazawara ce yasa bai tsaya yin wata-wata ba domin shima bazawarine, yana ganin ai sun san komai. Haka cikin nuna zaƙuwarsa ya fara sarrafata. Ai kuwa itama Madam wacce dama takawo iya wuya, sai kawai ta fara mayar masa da martani. Bai kawo komaiba domin kuwa yasan ai dama ita bazawara ce. Haka dai ango ya shiga duniyar ma aurata yana ta aiki. Saideme? Aifa ango yaga duk abunda yakeyi baijin ihunta ko wani a lama da zainuna tana gamsuwa. Sai ya ƙara dagewa! Amma fa duk ɗaya. Saida ya gaji sosai amma yaga idon Madam Carr a kansa a lamar kafara ne kodai kana shirine? Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana. Ogafa ya fara raba ido yana mai haɗiyar wani yawu muƙut. Haka Hajiya Babba ta jashi kan gadon ta cigaba. Nann fa ya fara kokuwar ƙawtar kansa amma ya kasa, ga kuma ya gama jigata domin kuwa babu wani ƙarfi a jikin sa. Itafa Hajiya tin tana jin yana magiya har yasaki baki yana ihuuu!. "Dan Allah kiyi haƙuri walhi zan mutu na gaji kibarni haka. A ta ƙaice dai, bawan Allah bai farfaɗo ba saida gari yawaye sosai sannan ya buɗe ido ya ganshi a gadon a sibiti. Aikuwa ba wata-wata ya saketa yace ba zai iyaba. Haka Hajiya Babba ta dawo gida ta cigaba da zaman zawarci har na shekara ɗaya da watanni kafin wani yazo. Saida biki ya rage sati ya ce yafasa, alamudai yaji labarinta, haka wani baƙo wanda ba ɗan garin nasuba shima saida abu ya kusa aka zugashi shima yace ya fasa. Ai kuwa bata rufe wannan shekararba Allah ya kawo mata uban ƴaƴan ta. Dariya tayi bayan ta dawo daga tunanin, ta tuno da mijin ta mai iyawa da ita, bawai dan tana gamsuwa ba, a'a dandai yafi sauran. kafin ta tada sallah. AJ kuwa yanajin ta har ta fara sallah yayi sauri ya shiga toilet, domin kuwa duk hankalin sa na kanta, yana kallo tanata murmushi. Yana shiga ya tsaya yana Kallon jikinsa daga sama har ƙasa kafin ya ce "Na shiga uku ni AJ!! Ina kuma sankuɗina ya kaini! dama haka a keji idan anyi aure? To meyasa wasu mazan suke cewa daɗi a keji!? Nidai wallhi matarnan kasheni tasoyi, idan ya tuno irin wahalar da yasha, domin kuwa abarsa har wani zafi take masa, tin tana iya tsayawa har ta lanƙwashe. Ya ce "kai wallhi bazan iya da wannan abunba, ni wallhi sai najima na tsani aure indai haka a keji mutum ya kusa mutuwa, amma fa da farko yaji daɗi. Take ya tuno da ranar da sukaje clup da Sarah ranar da yakusa keta mata haddi. Afili ya ce. Kenan itama da nayi haka zanji wannan a zabar!? "Allah sarki Sarah ko yanzu tana wani hali na rashini!? gashi ko kiranta banyiba...ooo!! Allah sarki innah ta da Nana, kwana guda ban jikuba, ku kwantar da hankalin ku na kusa yin kuɗi, duk zaku huta, gida zan siya mana babba wanda komai sainasaka mana. Haka dai yayi wankan tsarki kafin yayi a laula, sai kuma ya rasa kayan da zaisa, domin kuwa tsirara ya shiga toilet ɗin kuma gashi ba komai a toilet ɗin. Haka ya keta bin jikinsa da kallo, kafin ya buɗe baki ya ce "Amiƙomin kayana. Hajiya Babba dake zaune ta idar da Sallah tana jiran fitiwarsa. Ai kuwa ta saki dariya jin abunda yace. Tashi tayi ta ɗauki sabbin kayan da ta siyo musu jiya shida ita, domin kuwa ta shirya da safe zasu bar ƙasar. Ɗauka tayi ta nufi toilet ɗin, baiji tafiyartaba sai ji yayi an buɗe ƙofar an shigo. *ABDALHA POV* Shek Kabir kabuga ya ce "Maryam wato kin rainamu ko? Kina son mayar damu mutanan banza a idon al'ummar ko? Muna hani da ai kata bidi'a amma a dinga samunsa a gidanmu, me kike tunanin za'a ɗaukemu!? To daga yau kaman yanda yayanku ya ce...babu ke ba zuwa ko nann da bakin get, sannan wayar ma ai dama shine ya siya muku, to bani wayar? Ya miƙa mata hannu babu a lamar wasa, ai kuwa ta bashi har izuwa lokacin kuka takeyi. Sannan ya kalli Sadiya da Nusaiba ya ce "idan har naga wayar wata a hannuta to kuma waya ta haramta a hannuku. Yana kaiwa nann ya miƙe yabar ƙurin cikin ɓacin rai. Yana fita Maryam ta faɗa cinyar Mommy tana kuka. Mommy ta tureta haɗi da cewa "Ai maganin wacce bata jin maganar uwarta, ai saida na ce karkije tunda yayanku baya so, amma kikace sai kinje. Abdalha ya miƙe ya kalli sauran ƙanyan nashi ya ce "Kunji abunda Daddy ya ce ba saina ƙara muku wani ƙarin bayaniba. Bai jira cewarsu ba yabar palorn Mommy na binsa da harara. Yana fita Maryam ta sake fashewa da kuka tana cewa "Wannan ai san kaine me ya hana a karɓe wayoyin su Sadiya idan ba ni kaɗai a ka tsanab..."Kafin ta ƙarasa Mommy ta bige mata baki haɗi da cewa "Mune muka tsaneki ɗin? Nusaiba harda Nura suka kwashe da dariya suna barin ƙurin , yayinda Sadiya ta zauna tana mata faɗa da kuma sanar da ita illar aikata bidi'a, dukda tasan Maryam ɗin tafita sanin komai abinda ya shafi addinmu, domin kuwa duk gidan bayan Daddy da Abdalha. To tafi kowa ilimi harda Mommy kuwa, saide Mommy ta faɗa mata saninn littafin addini wanda itama tayi amma ba kamar Momy ɗinba, domin kuwa har yanzu suna ɗaukar karatun litattafai a gurin Mommy ɗin, wanda sukeyi kowani dare, ranar asabar da Lahadi kuma harda rana, kasan cewar ba su kaɗai take koyarwar ba harda wasu daga cikin matan unguwar su. Ita kuma Maryam tana koyar da matan aure da ƴan mata karatun Alkur'ani mai girma kullum da daddare. Cikin ɓacin rai ta ce da yayar tata "Ya isa haka mlm saidinawa masu jiran ganin an min wani abu suyi dariya, to wallhi duk baƙin cikinku dani saide ku barni amma wallhi nida Zainab sai mun zama ƙawaye, kuma ku zuba ido kugani, abu kamar mutum yana gidan kaso. Taja wani dogon tsakiii mtsiiii sannan ta bar gurin. Mommy da yayar tata Sadiya suka bita da kallon mamaki. Abdalha kuwa yana fita ya tararr da Daddy na jiransa a waje, take ya sanar dashi cewar yaje masallacin da shek ɗin yakeyin wa'azi duk ranar juma'a da yamma kafin ayi sallar magariba. Akan yaje yayi shi zaiyi tafiya zuwa Zariya sai kwana biyu zasu dawo. "Ok Abbalha ya masa sannan ya masa fatan dawowa lfy. *ZAINAB. VOP* Mama ce tare da Aisha da kuma Isa da malam tareda halifiyar Zainab ɗin da kuma namijin halifan nata. Mama ce ta ce "Mlm ku sake kiran numbar nata. "Mama wallhi numbar bata shiga kingani? Isa ya faɗa yana nunawa mama wayar. Malam ya ce "kumata uzuri baku saniba ko ta tsaya yin wani abunne. Hakanne yasa duk suka tsaya a wajan suna jiran ta. Wasa-wasa har ƙarfe shida da rabi, babu Zainab babu dalilinta. Nann fa hankalin su ya tashi. Gefe ɗaya kuma ga masoyanta mazauna unguwar au ( wato waɗanda suke unguwa ɗaya da ita) suna jiran dawowarta, domin kuwa sunji daɗin waƙar da ta sake ɗin. Hakafa har aka idar da sallar isha. Take Isa ya shiga tunanin abunda ta ce masa ɗazu. Ai kuwa cikin yarda da abunda zuciyarsa ta ɗarsa masa ya ɗauko wayar sa, dama a recording take, take ya ce "Mlm inada tabbacin Abdalha Kabir kabuga ne ya sa ceta, kokuma ya sa aka kamata, kode ɗaya daga cikin su, domin kuwa tace ya turo ƙanwarsa ɗazu. Ai kuwa ya kunna musu yanda sukayi da ita.ai kuwa take suka yarda, amma Mama ta ce "Isa karkaje kayi abunda bakada tabbaci a kai, kaga baka da tabbacin abunda kake son ai katawa. Take Isa ya fita bai tsaya ya saurari mama ba. Yana fita ya tararr da masoyan nata a ƙofar gidan su sai ɗaga hotunan Shehu nannsu haɗi da na Zainab ɗin, sannan sun kunna sabuwar waƙar sunayi domin kuwa har wasu sun riƙe waƙar. Baiyi wata-wata ba ya sanar musu da cewar Abdalh Kabir kabuga ya sace Zainab dalilin waƙar da tayi. Aikuwa nann take suka fara zaginsa, domin kuwa maganganun da tayi a cikin waƙar tamkar dashi takeyi, dama kowa yasan takun saƙar dake tsakanin su. Ai kuwa cikin daran labari ya bazu ko ina akan Abdllah Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa.haka dai duk inda ka shiga, dama abune na sanannun mutane, ɓangaren sada zuminta talabijin zancen a kayi. Yayinda rikici ya ɓarke tsakanin ƙungiyoyi guda biyun, garin kono ko ina zancen akayi, wasu na cewa ai dama batada kunya, meyasa zata zageshi a cikin waƙarta, ai ƙwara haka. Yayinda wasu suke cewa ai dama ita bata taɓa masa martaniba shikuwa indai zaiyi wa'azi saiya saka da ita, to mezaisa dan tamasa ɗaya ya tsargu. Rikici dai mara dalili da tushe, abunda yaƙara raba kan sauran ɗan abunda ya rage daga ƙungiyoyi guda biyon. Wasu mazauna kabuga yan ƙungiyar Zainab ɗin suka haɗa kai domin zuwa gidan Shek Kabir kabuga ƙwato Zainab...✍️.📝 PAGE* 1️⃣6️⃣ .......Haka samari majiya ƙarfi ƴan ƙungiyar Zainab suka doshi gidan Shek Kabir kabuga, bakajin komai sai zage-zage da ikkirarin cewar sai an fito musu da Saiyadar su kokuma kowa yaji a jikinsa. Ɓangaran Isa kuwa, gaba ɗaya hankalin sa ya tashi, tun yana kiran numbar ta tana shiga har yakoma kira yaji ance tana kashe, nan fa ya shiga kiran duk wani babba da yake a ƙungiyar tasu, dama manyan malamansu yana sanar dasu cewar Abdalha Kabir kabuga ya sace Zainab saboda waƙar buɗɗiyar wasiƙa, kowa hankalinsa ya tashi, haka dai kowa ya kasance cikin mamakin lamarin har zuwa washegari. *ABDALHA POV* Yana barin gurin Daddy ya koma gidansa ya shirya ya tafi gurin da zai gabatar da wa'azin. Haka ya gabatar da wa'azi sosai wanda yasa al'ummar dake gurin kowa ya jinjina masa domin kuwa wa'azin a kan iyaye matane yanda suke sakaci da yaransu, harda mazan ma. Yayinda wasu daga ciki suke mamakin sa ganin komai idan zaiyi irinna mahsifinsa ya keyi harta muryar su, idan kana sauraron karatun su, bazaka taɓa babbace muryar Shek Kabir kabuga da kuma ta ɗansa Abdalha Kabir kabuga ba. Saide ko idan kana kallonsu. Kaman dai yanda yasaba yauma bayan ya gama wa'azin saida yayi tsokaci a kan ƴan waccer ƙungiyar, musammamma waƙar da sukayi ɗazu, domin kuwa tsaf yaji waƙar har ƙarshenta. Saida ya caccakesu sosai kafin ya yi addu'a ya rufe karatun. Gidan su ya nufo daniyar zuwa suyi magana da mommy. Kaman yanda yayi tsakanin, hakane kuwa ya faru, domin kuwa yazo ya samu Sadiya ce ke koyawamatan da Maryam ke koyawa karatu. Cikin faɗa ya ce "Ina Maryam? "Wallhi yaya anyi-anyi tazo ta koya musu karatu amma tace wai bazatayi ba. Abdllah ya ce "Ina take? Yayi maganar cikin tsananin ɓacin rai. "Tana cikin ɗakinta ko abinci taƙici, ko fitowama taƙiyi. Cewar Sadiya tana kallon yanayin yayan nasu. Da sauri Abdllah yayi ɗakin Maryam cikin zafin rai!. Ya kai hannu zai buɗe ɗakin yaji Nusaiba ta kwalla masa wani uban kira har bakinta narawa, ita kanta Maryam da take cikin ɗaki tana karatu saida ta tsorata domin kuwa da ƙarfi takira sunan nasa. "Yaya Abdalha!!!!!!!!!. "Cak ya tsaya cikin ruɗewa domin kuwa yasan babu lafiya, itama Mommy da take ɗaki tana koyawa Nura karatu saida ta fito. Hakama Sadiya da ita da ɗalinbanta saida suka tsorata. "Da sauri ta ƙaraso gurin da yayan nata yake hannunta na rawa ta nuna masa abin da tagani yanzu ana yayatawa. Karɓa yayi yana dubawa, dai-dai mommy da Maryam duk sun iso gurin. Suma kallon wayar sukeyi suna duba abinda ke cikin wayar. A kiɗime Mommy ta kalli Abdalha wanda ya kafama wayar ido yana kallo. Tabbas bazaka gane halin da yake cikiba, domin kuwa babu alamar yaji tsoro ko mamaki, ko firgici. Mommy ta ce "Abdalha me nake gani? Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy tayi maganar bakinta na rawa kamar zatayi kuka ba. Cikin zuciyarta ta ce "ya Allah karka nunamin wannan ranar. Maryam kuwa wani irin dariya ta bushe dashi tana cewa "To ai basai an tambayaba, ninasan yaya son Zainab yakeyi kuma bazai iya faɗa mataba shine ya sace ta, ai kuwa abun zaibada citta, kunga kafin ya dawo da ita soyayya tayi nisa. Ta ƙarasa maganar tana mayarwa da Nusaiba wayar sannan ta juya zata koma ɗakinta. *NANA* *POV* Cikin mamaki ƴansanda suke kallonta jin yanda tayi maganar cikin ihuuu. Wannan ɗan sanda da ta kira da wannan ihune ya nufo gurinsu cikin ɓacin rai, yana zuwa ya wanke mata fuska da mari, kafin ta ankara ya ƙara mata, wanda yasa Nana faɗawa jikin Innah ta saki wani kuka mai ƙarfi, itama Innah kuka takeyi. Cikin muryarsa da suke tsananin tsoro ya ce "Dan uwarki ko ance miki nann gidan ubankine da zaki dinga magana yanda kikeso, yana maganar yana buɗe gurin da makullin hannusa ya tura ya shiga, ya ɗago Nana daga jikin Innah ya ce "Wato ke mara kunyar ko? Banace karna ƙara jin muryarku anann ba? Duk abunda ya ke cewa inna bataji domin bada Hausa ya keyiba. "Kunci sa'a ku matane amma Walhi da sai kunsan kun shigo nann. Yana kaiwa nann ya turata ta faɗi kafin ya harari Innah yana ficewa daga gurin. Haka Nana taci kuka har tana ciwonkai, sannan ga yunwar da ta ƙara rikice mata ciki. Haka suka zauna a gurin har, bayan sallar la'asar. Izuwa wannan lokacin kuwa har Nana ta daina kuka tsabar azabar yunwa, ita kuwa Innah kwanciya tayi tana jin kamar kayan cikinta zasu zubo, idonta a kafi tana kallon sama. Suna cikin haka sukaji ana kiran sunan Nana. "Nana... "Nana... Nana? Dukda cikin rawar baki yake maganar da kuma sauri, amma hakan bai hana Nana gane muryar waye ba. Tana ji amma ta kasa magana jitakeyi kamar tana magana amai ne zai zibo, ita kuwa Innah batasan ma me a ke cikiba. Da sauri Salis ya ce da ɗan sanda ya buɗe masa gurin da sauri, amma police ɗin ya ce "Ai ba haka sukayiba, sunyi a kan kawai zai gansune ya tafi, da sauri Kamal ya ce da ɗan sanda Please dan Allah ka taimaka baka ganin halin da suke cikine? Police ɗin zaiyi magana SALIS ya ƙara zaro kuɗi ya miƙa masa haɗi da cewa Please ya buɗe. Ai kuwa take ya buɗe musu, Salis ya yi kan Nana yana kiran sunanta, yayinda Kamal kuma yake ɗaga Innah. Ganin suna ƙoƙarin fita dasune yasa police ɗin cewa "Lfy kuwa ban gane ba? "Asibiti zamu kaisu baka ganin yanayin sune? Cewar kamal yana kallon police ɗin. Wani irin zaro ido police ɗin yayi yana cewa "Kai! Kai! Kasan kuwa me kake cewa? To wallhi idan har nabari kuka fita dasu to nabar aikina kenann, yanzu ma lokacin ku ya ƙara kuzo ku fita karku jamin masifa, yana faɗa yana jawo ƙofar zai rufe. SALIS da Kamal sunyi yin duniya amma ya ce bazasu tafi dasuba, mutanan da sukayi sata, cikin mamaki suka ce "sata!! Police ɗin yaga alamar fa suna son jawo masa masifa ne, nan danann ya rufe gurin yana cewa idan baku bar gurin ba kuma za'a haɗa daku. Da kyar dai police ɗin ya barsu a kan zasu dinga kawo musu abinci, safe rana dare, shima a kan zasu dinga biyan sa. Haka Salis suka yarda, take sukaje suka siyo musu abinci da magani suka kawao musu. *A.J .HAJIYA BABBA* *POV* Aruɗe ya kalleta domin kuwa ta tsorata shi, da sauri ya karɓi kayan da take miƙomasa ya juya baya yana sakawa ransa a ɓace. Saida ya gama sosai kafin ya buɗe ƙofar toilet ɗin ya fito yana wani haɗe fuska. Kan abar sallar da yaka tayi shima yaje ya tada sallah ko kallon inda take bayayi. Bayan i idar ne ya ɗaga hannu yana addu'a wanda ni (S REZA bansan me yake roƙaba) Bayan ya idar da addu'ar ne ya kalli Hajiya Babba cikin haɗe fuska ya ce "ina wayata? Hajiya Babba ta tasu tazo har gabansa sannan ta ce "Good morning angona, da fatan ka tashi lfy.tana faɗa tana ƙoƙarin zama a kusa dashi. Cikin sauri ya miƙe tsaye haɗi da cewa "Please dan Allah kibani waya wallhi Innah ta zan kira ban saba kwana ba tare da suna kusa daniba, Please dan Allah kiyi haƙuri karki ce wannan ma yana cikin kwangilar mu Please? Aj ya ƙarasa Maganar kamar zai sa kuka. Hajiya Babba kuwa wannan abun da yayi sai yamata kyu, domin kuwa tana son ganin namiji na shaƙwaɓa, abun burgeta ya keyi. Cikin kwantar da muryar, kamar wata budurwa kai ka rantse da Allah cewa ba itace ta haifi laɗifa da Salis ba ta ce "Haba mijina acikin wannan asubar zaka kirasu ai sai kasa suyi tunanin ko ba lafiyaba, kabari zuwa safiya sai ku gaisa kafin mu tafi, Please yanzu kaje ka huta nasan a gajiye kake, Please, ta ƙarasa tana kawar da hannusa da ya miƙo mata tin ɗazu a kan ta bashi wayar. Tabbas da alamar dai AJ bai gane me hajiya take nufi da cewar kafin su tafiba, shi yayi tunanin ko kafin su tafi gidane. Hakanne yasa ya kasa cewa komai domin kuwa kewar su Nana ce ke damunsa, gakuma sabon al'amari da yakeji a tare dashi yanzu tsakanin sa da Hajiya Babba. Anann kan daddumar ya kwanta yana tunanin abuwa masu yawa wanda zaiyi idan ya gama cinye wannan kuɗin. Sai gani yayi itama tazo kusa dashi ta kwanta tana haɗe fuskokinsu, ai da sauri ya miƙe zaiyi magana ta ce "A cikin sharuɗanmu babu raba shin fiɗa mutuƙar zamu kwanta tare. AJ ya ce "Amma ai baki faɗa hakaba, kuma ai yanzu ba barci zanyiba, kawai zan hutane. Ya faɗa yana tuno suman da yayi ɗazu. Ta ce "Ai na faɗa maka cewar zamu kwana duk lokacin da naso, sannan kuma ai koda ba barci zakayi ai ni matar kace ADDINIMU bai haramtaba, ladama fa zaka samu. Ya ce "Walhi kaina kemin ciwo. Ta ce "Aiya sorry muje mu kwanta babu abunda zai faru. Haka yana ji yana kallo ta ɗiorashi a kan gado sannan itama ta hau ta ja musu bargo, suka faɗa barci mai daɗi irin na miji da mata. AJ gaba ɗaya a takure yake domin kuwa duk ta manne a jikinsa, shikuwa duk sai yaji ya kasa cigaba da barcin. Misalin ƙarfe bakwai da wasu ƴan mintina yaji alamar tana ƙoƙarin tashi, sai ya rufe idon sa domin karta gane cewa baiyi bacceba. Tashi tayi tana sauƙe idan ta a kan fuskarsa sai taga ya ƙara mata kyu. Miƙewa tayi ta saka hijab sannan ta fita. Bayan kamar minti goma ta dawo lokacin shikuma yayi dube-dubensa ko zaiga ina ta ajiye wayar sa amma ya rasa. Tana shiga saiga ɗaya daga cikin ma'aikatan hotel ɗin reƙeda tire na abincin su. Bayan sunci ne Hajiya Babba tace ya shirya da huri zasu tafi. Haka AJ bai ƙara mata zancen wayarsaba ya shirya cikin shigar wasu sabbin kaya da tabashi. Fita ta sakeyi ta kira Salis ta sanar dashi cewar wani aiki ya kamata saboda haka bazata dawo yauba, ya kula da laɗifa tare zasu zauna da AJ amma bazasu huce sati ɗaya ko biyuba, tana jin yana tambayar ina AJ amma ta kashe wayar damin kuwa batason komai ya shiga tsakanin ta da angonta. Haka suka fito daga cikin hotel ɗin suka shiga motar da sukazo da ita sukaje gidan malamin da ya ɗaura musu auran suka ajiye motar. Cikin mamaki AJ ya ce "Bada motar zamujeba? "Cikin basarwa ta ce "Ina zamuje da motar? "Shima cikin ƙosawa ya ce "Gida mana ko a motar haya zamu tafi? "Sai a lokacin Hajiya Babba ta tuna da cewar a shefa bata sanar dashi da maganar tafiyar bafa. Juyowa tayi da kyu ta kalleshi sannan ta ce "Ƙasar zamu bari amma ba nisa zamuyi muna cikin Africa ina so mu samu Kamar sati biyu ne kafin mudawo kaga lokacin mun ci amarci sosai kaima idonda ya buɗe. Cikin mamaki da rashin tsammani AJ ya ce "Tafiya waje sati biy!! Ina bazan iyaba, tayaya zanyi sati biyu batare da naga Innah ta da Nana ba, no ai babu wannan tsarin a cikin sharuɗanmu? Kuma koda da wannan bazan iyaba, Ni no no no, ya ƙarasa yana kirkiza mata kai haɗida jadabaya kamar zai ruga da gudu. Hajiya Babba tayi shiru!!! Sai zuwa wani lokaci ta kalleshi cikin murmushi ta ce "Shekara ɗayane kwangilar mu ko? Aj ya ɗaga mata kai alamar eh. Hajiya Babba ta ce "To idan har ka yarda muka bar wannan ƙasar har mukayi sati biyu to idan mun dawo gida, wata biyar zamuyi shikenan kaci kuɗinka miliyoyin hamsin. Ina jiranka yanzu, idan kuma baka yardaba to muje gida muyi shekara ɗaya ɗin. Ta ƙarasa tana sakar masa murmushi!!!!....?? PAGE* 1️⃣7️⃣ ........*A.J* Shuru yayi yana kallon Hajiya Babba kafin ya buɗe baki ya ce "Kina nufin idan munyi sati ɗaya shikenan saura wata biyar? "Eh saura wata biyar amma fa shima da sharaɗi? A.J ya ce "Wani sharaɗi kuma bayan wanda nake ciki? Hajiya Babba ta kalleshi da kyu kafin ta matso kusa dashi kamar zata shiga jikinsa ta ce "Sharaɗin guda ɗaya ne kawai idan har zaka yarda? Taci gaba da cewa... Banaso kayi waya da kowa har sai mun dawo, abun nufi shine bazaka kira kowaba har mu dawo, kuma..."Bata ƙaraba ya ce "Na yarda. Cikin mamaki take kallon sa kafin ta ce "kayarda? Ya ce "Yes na amince, amma inaso zanyi waya da Nana yanzu? Hajiya Babba ta ce "Badamuwa. Haka ya shiga kiran numbar Nana amma bata shiga, sai ya kira number Innah itama dai bata shiga. Nann take hankalin sa ya ɗan tashi domin kuwa yasan Nana bata barin waya babu chaji, saida takira yakai sau goma amma dai bata shiga. Har ya haƙura sai ya kira number Sarah, itama dai ga numbar ta shiga amma no amsar, haka ya dage da kira amma dai duk ɗaya, sai kawai ya rubuta ɗan ƙaramin text message ya tura mata sannan ya miƙawa Hajiya Babba wayarta kafin suka fara tafiya. Basu samu damar tafiya a ranarba dalilin babu jirgin da zaitashi, sai zuwa gobe. Ai kuwa washegari haka suka tashi da sassafe bayan ansha amarci, suna zuwa basu daɗba jirginsu yabar Nigeria izuwa ƙasar *MOROCCO*. Ɓangaren su Salis kuwa, da ƙyar sukaci sa'a police ɗin nan ya amince zasu dinga kawo wa su Innah abinci sau uku a rana, hakanma saida sukayi ciniki da police ɗin, domin kuwa yace idan har a ka kamashi to wallahi korarsa za'a yi. Haka dai har su Innah sukayi kwana huɗu a cikin sell ɗin nan amm Daddy baibi ta kansu ba. Salis da Kamal kuwa kullum sai sunje, dukda basa wani samun damar yin magana dasu, domin kuwa police ɗin yace idan a ka gansu to da matsala. Ananne Salis ya tambaye police ɗin a kan waye ya kawosu police station Kuma a kan meye? Nan police ɗin ya sanar dashi komai game da Daddy, wato ya ce "Comomda Deniel ne ya kawo..."Ai bai ƙarasaba Salis ya miƙe tsaye ya ce "What!! Daniel? Shima police ɗin cikin mamaki ya ce "Yes Kasan shine? Salis bai tsaya amsa masa tambayar ba ya bar cikin police station ɗin cikin sauri kamar zai faɗi. Shikuwa ɗan sandan ganin irin razanar da Salis yayine yasa yayi tunanin kodai Salis ɗin yasan Daniel ɗinne!?. *GIDAN SOJA* Yau kana huɗu kenann da kullesu Samuel wanda yayi dai-dai da kulle su Innah da Nana a cikin sell. Har kawo wannan lokacin Daddy bai ƙara zuwa police station ba, sannan bai ƙarabi ta kansu Samuel da Sarah ba. Yanda ya shirya a ransa shine...kwanakin da ya basu na cika zai ɗau hukunci a kansu. Su kuwa Innah da Nana ya barsune a kan har lokacin da shegen yaron zai dawo, idan kuwa bai dawoba, to tabbas kamar yanda ya ce abaya saide su mutu a haka. Har yamatsu yayi ido biyu da wannan A.J ɗin, domin kuwa tun kafin ya ganshi har ya tsaneshi. Samuel kuwa sun gama shiryawa da shi da Laɗifa da kuma Umar a kan zasu kawo kuɗin gobe. Bayan haka kuma sun shirya a kan Samuel ɗin zai gudu daga gidan bayan komai yayi dai-dai. Ɓangaren Sarah kuwa acikin wannan kwana huɗu tarame sosai kuma kullum sai sun kira number A.J amma har yanzu bata shiga. Tayi kuka har ta godewa Allah. Samuel kuwa yanzu mugun tausayin ta yakeji, domin kuwa yasan halin Daddy tsaffff zai zaneta a kan kuɗinsa. Kaman yanda yace sau biyu za'a ɗinga basu a binci a kullum, tabbas hakanne, idan kuwa an kawo Samuel zaice Sarah tace itama tace yaci. Haka dai zasu zauna suci don dole. Wannan ɗan zaman da sukayi har sunyi shaƙuwa sosai wanda da basuyi ba.... Ko wannan su yanzu tausayin ɗan uwansa ya keyi, yayinda Samuel yake shirya yanda zai gudu da ita batare da Daddy ya saniba. kallon ta yayi cikin yaransu na tibi ya ce "Sarah yanzu idan wannan kwana shidan ya ciki AJ ɗin bai zoba ya zakiyi? Cikin kuka da yazama mata aiki ta kwanta a jikin yayan nata ta ce "I don't no! ban saniba, amma inaji a jikina cewa AJ zai dawo gareni, domin kuwa yana sona. Samuel ya ce "Sister saura kwana biyu fa? kina tunanin zaizo a cikin kwana biyu? "Ban saniba! Ta baɗa tana kifa kanta a kan ƙafarsa tana fashewa da wani irin kuka mai cin rai!. Tabbas Sarah tana son AJ sosai, domin kuwa ita har yanzu zuciyarta bata yarda a kan cewar kuɗi yayi ya guduba, amma wani ɓangaren daga zuriyar ta tana sanar mata irin son kuɗin AJ ɗin, tabbas tasan aj sosai, tasan halalin sa na san kuɗi, domin yana faɗa mata cewar... "Sarah duk wani abu da zai kawo min kuɗaɗe to tabbas zanyishi mutuƙar ADDINIMU bai hanaba, inason naga nayi kuɗi sosai kodan na taimakawa Innah ta da ƙanwata da kuma matar da zan aura da kuma ƴaƴana. Sannan zan iya yin komai wajan kare mutuncin family na, zan zamar musu bango a rayuwarsu, bazan barsu suyi kukan rashinaba koda kuwa zan ƙarar da rayuwata a kan hakan. Da sauri Sarah ta tashi tsaye bayan ta dawo daga tunanin ta ce "No no no AJ bai guduba, bazai iya guduwa yabar family ɗinsaba, a kwai abun da ke faruwa, AJ baisan an kulle su Innah ba da ya sani zaizo koda kuwa Daddy zai yanka shi. Ta ƙarasa da cewa akwai abunda ke faruwa!. Samuel ya kamota yana kuka yana mata sorry. Amma yaƙi sanar da ita cewar harda ita zasu gudu, domin yasan bazata yardaba. Haka dai ya rarrasheta har yayi sa'a tayi shiru tana bai cigaba da tuno magan-ganun Aj akan kuɗi da kuma family ɗin sa. *LAƊIFA. UMAR. POV* Kallonta yayi ya ce "Gaskiya ni bazan iya zuwa gidannan ba, domin kuwa mutumin yasanni, kuma ya tsani musulmai sosai, bai ƙaunar addinin Muslunci koda kuwa a gurin kasuwacine bare har wata mu'amala ta haɗashi dasu. Cikin jin haushe da kuma ganin tsoron Umar ɗin Laɗifa ta ce "Kaide wallhi anyi raƙon na miji a gurinnan, gaka dai namiji iya namiji amma sai shege tsoro. Umar ya ce "Aini da kika gani inada kiyaye lafiyata harta ƙanwata Hadiza a bokiyar faɗarki to itama tsoranta nakeyi domin kuwa wallhi yarinyar tamkar mai aljannun, tasha faɗa da maza kuma tayi nasara a kansu, shiyasa ake tsoranta daga maza har mata, kema dande baki santa bane da har kika biye mata. Laɗifa ta ce "Au dama aljannun gareta!? Ta ƙarasa tana zaro ido. "Eh tanada su masu shegen ƙarfi ma kuwa. Ya faɗa yana dariya. Laɗifa ta ce "Kaga yanzu dai faɗa min gidan su Samuel ɗin da kuma sunan Daddy ɗinsu ni zankai tinda kai matsoraci ne. Ta faɗa tana kawar da wancen zancen da sukeyi. Umar ya zaro ido waje ya ce "Kece zaki kai kuɗin!? Bakiji abun da nace ba? Ta ce "Please faɗa min bana son wasa? Tafa da alamar da gaske take. Umar ya fara address ɗin gidan sannan ya ce "Sunan sa Comamdar Daniel! Cikin rikicewa da nuna alamar mamaki ta ce "What!? me ma kace Daniyal ko wane!? Shima Umar meƙewa yayi cikin mamaki ya ce "Eh Daniel na ce kin san shine!? Cikin tashin hankali Laɗifa ta ce "Umar zan kiraka bari naje gida Please, zan nemeka anjima. Bata tsaya taji mai zeceba ta bar shi agurin baki a sake yana binta da kallon mamaki. A fili ya ce "Ninasan bazata iya zuwa gidan wannan ƙaton arnan ba, domin kuwa kowa yasan ƙiyayar sada musulmai a garin nan, ƙwafa yayi yana ɗan taɓa baki irin ko a jikin sa kafin shima ya bargurin cikin jin haushen ta barshi da hawa keke. *ABDALHA. POV* Kafin Maryam ta rufo 'kofar d'akin nata har Abdalha ya kamota, kan kace me ya ɗaga hannu ya zabga mata mari, cikin ɓacin rai da jin haushin abunda ta ce ya ce "Ni abokin wasan kine da har zaki kalli idanuwa kice wai sonta nakeyi!? Ya faɗa yana ƙara ɗaga hannu da niyar ƙara mata wani marin, sai sukaga mai gadin gidansu ya shigo har palorn gidan cikin kiɗimewa abunda bai taɓa yiba. Ganin haka yasa Abdalha ya mayar da kallonsa izuwa gurin mai gadin. Ya buɗe baki da niyar fara yiwa mai gaɗin faɗa a kan shigowa gidanne domin kuwa sun hanashi shigowa, koma me zaiyi ya tsaya daga waje. Mai gadi cikin rawar baki yace "Ranka shidaɗe, ga wasu samari nan sunzo sai bub-buga ƙofar gida sukeyi suna kiran sunan ka suna zagi wai a fito musu da Zainab. Cikin tashin hankali Mommy ta ce "Ai kagani abunda nake gudu kenann, me ya kaika sace ta!! Shinma wai saceta ɗinne zaisa ta daina waƙoƙin kodai mai!? Mommy ta fara faɗa tamkar zata ari baki. Maryam da Sadiya da kuma Nusaiba da Nura, sai kuka sukeyi, domin kuwa izuwa yanzu suna jiyo ƙarar dukan get d'in gidan. Su kuwa ƴan matan da sukazo ɗaukar katu, jin abundake faruwa ne yasa, suma suka fara ihuuu, domin kuwa ƙarar dukan git ɗin da ƙarfi sukeyi. Abdalha kuwa hankalin sa ya tashi ganin irin kukan da Mommy da kuma sauran ƙanƴan nasa sukeyi, sannan kuma ga magan-ganun da mommy ɗin keyi. Shi gaba ɗaya ma abun ya ɗaure masa kai, bai masan ta ina zai faraba. Afili ya ce "Tabbas wasu suna bibiyata!! Take ya ɗauki waya ya kira police station ya sanar dasu abunda ke faruwa a gidan su. Suna jikin haka saiga kiran Shek Kabir kabuga, kallon wayan Abdalha yayi wanda shi tsabar ruɗewama har ya manta bai kirashiba. Ya ɗagawa Shek Kabir kabuga ya ce "Abdalha ina ka kai musu yarinya!? Shin dama abun da kake shiryawa a kanta kenan!? Shek yayi maganar cikin ɓacin rai domin kuwa yanzu ya fara ganin saƙonnin da kuma kira akan samari sunje gidan sa. Nann aka fara kiransa har saida ya kashe waccar wayar tasa. Shiru Abdalha yayi yana mai jin kansa na sara masa. Azuciyarsa ya ce me ke shirin faruwa ne! Harda Daddy. Yana cikin wannan tunani yaji muryar daddy na cewa "Abdulhi bada kai nake bayaniba!? jin aldalha baiyi magana bane yasa Daddy cewa Abdullah..."Kit yaji an kashe wayar. Daddy yabi wayar da kallo yana mamaki, kenann da gaske Abdalha ne ya saceta!?. Abdalha kuwa yana kashe wayar yayi hanyar fita ba tare da yayiwa kowa maganaba. Jin kiran da Momy kemasa ne yasa ya tsaya yana kallonta, kafin Mommy tayi magana ya ce "Momy bansan me zanceba ban saniba!, ni dai abun da nasani shine tabbas ana bibiyan rayuwana, amma koma waye zan gano!. Cikin ɓacin ran jin maganar da ya ke cewa mommy ta zabga masa mari ta ƙara masa sannan ta ce "Tsabar ka rainamu, ina ji yanzu kuna magana da Daddy ka kashe waya batare da kace komai ba. Nikuma ina maka magana kana fita yanzu kuma kana min wani zance saban. Shin da gaske kaine ka sace ta!? Mommy ta tambayeshi tama mai ƙara fashewa da wani kukan. Abdalha ya riƙe gurin da mommy ta mareshi yana jin abunda tinda yake Mommy da Daddy basu taɓa masaba amma a kan ta amma mareshi. Yanzuma shiru yayi domin kuwa tabbas baisan me zaiceba, abinda yasani shine ana bibiyar rayuwarsa....✍️ * *PAGE* 1️⃣8️⃣ *Babu editing* ..........Cikin tsananin mamaki Abdalha yake kallon Mommy wacce ta ɗaga hannu ta mareshi a kan abunda batada tabbacin sa, ya kalleta cikin mmk ya ce "Momy ban saniba bansan komai ba wasune suka saceta amma ni bani bane pls Mommy ki yarda dani karki bari zuciyarki ta aminta da wannan zancen. Momy ta kalli ɗan nata cikin tausaya masa tace "Shin me ya kaika gurinta lokacin da abun zai faru? "Mommy bansan komaiba kamar yanda na sanar miki, kuma nuda kaina zan gano komai pls ki yarda dani. Yana gama faɗin haka yabaar gidan cikin tsananin mamaki abubuwan da ke faru kamar wani shirin Film. Lokacin da Abdalha ya isa ƙofar gidan nasu har police ɗin nan sun kama na kamawa sauran kuma sun gudu, kallon police guda biyu da ke jikin ƙofar gidan nasu yayi wanda a ka bari domin basu tsaro yayi, kallon su yayi cikin takaici domin kuwa kallo ɗaya ya musu ya gana ba musilmai bane, a zuciyarsa ya ce "Tabbas wannan shirine kuma zan kawo ƙarshensa yau. Police ɗin dake nufoshi ya ɗagawa hannu a lamar bayan tsaron nasa , amma police ɗin yace ai hakan umarnine dole sai yayi. Haka badan Abdalh yasoba suka shiga motar shida ɗan sandan suka fita. Ɓangaran gidan su Zainab kuwa har yanzu babu labarinta, yayinda Isa ya dinnga yaɗa cewar Abdalha ne ya saceta kuma tabbas yanda labarin ke bazuwa idan kagani dole ka yarda. Ƴan gurgiyar Abdalh da sukaga abun ya fara yawa sai suma suka fara mayar da martani akan ai shi Abdalh baɗan bidi'a bane yana amfani da ilimin sa, saide kaga majalista ta samari daga hira sai zage-zage sai faɗa. Har takai ta kawo wasu daga ciki suna tono tsoffin asirin wata gurgiyar. Budurwa da saurayi aboki da aboki mata da miji, malami da ɗalibai, uba da ƴaƴansa, maƙofci da maƙofci, dukkan su mutuƙar ba kungiyar su ɗayaba to Tabbas sanadiyar wannan abun Kai ya ƙara rabuwa. Kai abundai ba'a cewa komai domin kuwa lamarin ya gawarta. *SALIS LAƊIFA POB* Cikin sauri kamar zata tashi sama tsabar ruɗewa ta banko ƙofar palorn tana ƙoƙarin haurawa sama, sai tayi ido biyu da Salis yana zagayawa a ɗakin cikin tashin hankali. Da gudu ta ƙaraso gurin da yake ta buɗe baki zatayi mgn, cikin harɗewar murya ya ce "Com com comand Comandar Daniel ne ya kullesu?. Ya ƙarasa maganar yana kallon laɗifa wacce Salis ɗin ya ƙara sakata a cikin duhu domin ita bata gane me yaceba, ta daiji yace Daniel amma fata fahimci gaban ba. Ta ce "Pls Yaya banji me kace ba, itama ta faɗa tana kallon cikin idonsa? Salis ya ce "Gajiya Babba dole ta dawo yau ɗinnan domin kuwa a kawai matsala?. Laɗifa ta ce "Pls Yaya sanar dani abunda ke faruwa ban ganeba fa? Ni nashigo da maganar Comandar kuma kaima naji kana min shin wani abun ya haɗoka dashi ne? Cikin sauri Salis ya fasa danna kiran numbar Hajiya Babba ya dawo da kallonsa izuwa gurin Laɗifa ya ce "Me zaki sanar min akan Comandar ɗin? Da sauri Laɗifa ta ce "Shine baban wannan yaron da nace maka inaso wannan Kristen ɗin..."Ai tin kafin ta ƙarasa Salis ya ce "No no no, ya miƙe tsaye yana kallonta wacce itama ta miƙe tsaye ya ce "Bakida hankaline kin matan waye Daniel da har zakije kifara soyayya da yaronsa ko? Kafin ya samu matsayin Comanda ma ya muka ƙare dashi bare yanzu...damade baki sanarwa da yaron cewar kina sonsaba? Ya tambayeta yana son yaji tace masa bata sanarba. Cikin kuka ta ce "Wallhi Bro bansan shine babansa bane ban saniba, ta faɗa tana ƙara fashewa da wani sabon kukan. Salis ya ce "kin faɗa masa? Ta ce "Eh harma mun zama... Da sauri Salis ya ce "Yanzu haka shine ya kulle yarinyar da nakeson aura tare da innarta basu san hawaba bare sauƙa, kuma ya ce bazaibada Berlin ɗinsuba sai yaga wanda yake nema. Ta ce "Pls bro mukira Hajiya Babba? Ai kuwa take suka shiga kiran Hajiya Babba amma bata shiga. Itama laɗifa ta shiga kiranta da wayarta, amma duk ɗaya. Salis ya kalli laɗifa ya ce "Akwai matsala domin kuwa Hajiya bata ƙasar nannn tin jiya number ta bata shiga. Laɗifa ta ce "To ina yaron da suka tafi tare? Sai a lokaci Salis ya tuna da cewar a shefa Hajiya tare da A.J suka tafi, sai kawai ya nemo numbar AJ ɗin domin kuwa yasan tunda ita bata ƙasar to shi yana 9j. Da sauri ya shiga kiran numbar amma shima yaji bata shiga. Kallon juna sukayi suna mamaki, laɗifa ta ce "To ko zamuje gidan su yaron mu tambayeshi da gaske Hajiya tabar 9j? Cikin ɓacin rai Salis ya ce "Dan Allah malama sunansa AJ ba yaroba! Ko bai girmeki bane? Kuma bari kiji yarinyar da zan aura ɗin ƙanwarsa ce, kuma itace a ka rufe a police station itada innar su, kuma Comandar ne sannan kuma AJ ɗin yake jira ya dawo kafin ya sakesu. Wani abu taji shuuu ya shiga kunnenta kafin taji alamar iska, ta ce "Ok sai yanzu na gane abunda ya sakaka a tashin hankali a shedai saboda soyayya ne ba dan abunda wancen tsohon arnan ya manaba. To walhi bazamu taɓa haɗa jini da wannan matsiyatan ba, har kake cewa wai ita zaka aura to dan ubanta tazo gidan mu gani. Cikin kwantar da hankali ya ce "Yanzu dai ni bama wannan ba, yanzu meye abunyi? Ta ce "kawai ka manta da su domin banaso mu ƙara shiga sabgar wannan ƙaton arnan. Abunda Salis bai saniba shine, laɗifa ta gama haɗa kuɗin da zata ƙwato Samuel domin kuwa ta so ta sanar dashi gaskiya amma jin shina Musa soyayya ce ta kaishi sai kawai tayi fuska a kan kowa yaji da damuwarsa abunda Basu samaba. Salis ya ce "Ban gane na barsuba! Kinaji nace matar da zan aura amma kice wai na barta? Jin tambayar da tamasa yasa ya shiga tunani, tabbas abunda ya kamata ya fara sani kenan Amma ya manta. "Wai ma me sukayi har ya kaisu police station suna mata? kidan yaga su ɗin musulmai ne ba addininsu ɗayaba. SALIS ya ce "No suma basu san me sukayiba domin bai sanar musuba, amma dolema na sani yau ɗin nan, ya kamata muga AJ. It's dai laɗifa waya ta ɗauka tana kiran Umar domin ita dai bazataje gidan su Sameul ɗin ba. *GIDAN SOJA* Da sauri Daddy ya shigo palorn yana kiran Mommy Eliza! Eliza! Kai da jin irin kiran kasan cikin ɓacin rai yake, itama Momy ɗin da sauri ta fito daga ɗakin tana cewa "I'm coming sir. Tin kafin ta ƙaraso ya ce "Zuwa gobe naba yaranki a kan su kawo min kuɗaɗena kokuma namu hukuncin da babu wanda zai yarda cewar nune ubansu, barinma wacce muna fukar da ta ɗauki kuɗinan tana kaiwa musulmi wanda nakejin da nayi ido biyu da su ƙwara a ce bani da idon, bazan taɓa ƙwanar mutanananba na tsanesu , Walhi inajin idan na kama wannan yaron AJ to tabbas zan iya kasheshi. Cikin tsananin ƙiyayar da sukewa musulmai itama mommy ta ce "Ni sonake ka kaini police station ɗin da kakai ƴan uwansa na fara zuwa naci mutuncinsu tukunna Amma kace wai ba hakaba. Daddy ya ce "Yanzu haka daga chan nake, nasa an ci ubansu sannan ance wai ana kawo musu abinci, nasa an kori police ɗin da yabada umarnin shiga da abincin, yanzu haka nasa wani mai kula dasu ɗin kuma nace masa duk wanda yazo gurinsu ya barshi ya shiga amma ya kirani. Cikin jin daɗi Mommy ta ce "God! Idan ma yaronnane yake kai musu abincin ai zamu ganeshi. Daddy ya ce "Nima hk nake tunani kodai yaronne?. Samuel da Sarah kuwa duk abunda akeyi suna ji. Kuka Sarah takeyi tana cewar Pls Samuel call AJ please. Shima kansa Samuel ɗin yana son yaga waye wannan AJ ɗin, sannan shima yana kiran numbar Umar amma no amsar. *HAJIYA BABBA AJ POB* Tafiya sukeyi a bakin wani ƙaton hotel ɗin da suka kama a ƙasar morocco mai ɗauke da sunan *HALIDYS HOTEL* Kusan duk wanda ya gansu saiya ƙara kallonsu domin kuwa kana ganin su kaga uwa da ɗanta, amma yanda suke a manne da junane zaisa ka ƙara kallonsu domin kuwa sunyi kama da masoya, bakin ƙofar hotel ɗin suka tsaya kafin Hajiya Babba ta kalleshi cike da tsananin sha'awar sa da kullum take zamar mata sabuwa da kuma yanda yake iya jure buƙatarta fiye da sauran mazan da ta zauna dasu. Kallon fuskarsa tayi wacce kana gani kasan yana cikin damuwa sosai ta ce "Aj angon Hajiya Babba inji yaranta! Yanzu idan muka koma Nijeriya yazamuyi da su Salis da laɗifa? Domin fa ni gaskiya ko mun koma 9j to Muna tare dan bazan iya nisa dakaiba. Idan bai mantaba yau suke kwana huɗu kenan da zuwa Morocco sannan kuma yana jin cewar daga wannan kwana baƙwaɗin tofa komai zaifaru bazai ƙara kwana batare da yaga Nana da Innah ba harma da Sarah waccce yanzu yake yawan mafarkin tana cikin wani hali na taimakonta. Ya ce "Ai bamuyi cewa zamu zauna a gidankiba idan mukakoma Naiger, kodan saboda yaranki, saboda haka a gidanmu zan zauna. Hajiya ta ce "Yanzu idan na ce muyi sati biyu a matsayin shekara ɗan da nace maka idan yaso tun. A nann na baka kuɗinka muna zuwa Najerya sai kawai ka ci kuɗin shin zaka yarda? Ka daiyi tunani miliyon 50 a sati biyu ba wasaba....📝 *INA KUKE S REZA FAN'S?⁉️⁉️⁉️* A kwai wani tsohon littafi na da na rubuta, mai suna so ne. Tom na sake dawo muku dashi domin wanda basu karantaba su karanta. Littafin soyayya ne. Soyayya mai taɓa zuciya, littafin da masoyana suka dameni akan na sake dawo musu dashi. Tom in Sha Allah zan dinga haɗa muku da wannan na ADDINIMU zai dinga zuwar muku a tare, domin farin cikin ku. Littafin *SO NE* Littafine da ya ƙunshi soyayya mai tarin abubuwan allajabi, mai rama tsakanin masoya. Ku kasance da littafin domin suna tare da littafin *ADDINIMU* kuma dukkansu free ne, domin jin daɗin ku🥰🥰 *ADDINIMU*.da. *SO NE?* ❤️ * *PAGE* 1️⃣9️⃣ ........Kallonta yayi da kyu cikin wani sabon mamakin da tun da suka haɗu take bashi ya ce "Hajiya ban gane me kike nufiba? Hajiya Babba ta kalleshi cikeda maradin sa ta ce "Inaso muyi sati biyu a nan in yaso muna komawa 9j shikenan kaci kuɗinka? "Kina nufin daga haka mun gama auran kenann? Hajiya ta ce " Eh haka nake nufi. Cikin tsananin mamaki da farin ciki AJ ya shiga tinanin abubuwan da zaiyi idan ya mallaki wannan kuɗin fayan kwana goma. Hajiya ta ce "Bakace komai ba? Ya ce "Na amin ce, saura kwana goma kenan ko? Hajiya ta ce "Eh hakane. Tinda sukazo ƙasar Morocco Hajiya Babba bata ga farin ciki a fuskar angon nataba sai yanzu, domin kuwa ya dawo kamar ba AJ mai surutu da abun dariya da fara'a ba, tashi tayi ta kama hannun sa tana masa alama da ido. Kaman yanda suka saba kullum Hajiya saita buƙaci mijin nata sau huɗu a rana, wani lokaci ma har fiye da haka, shikuwa gogan naku tun bai saki jiki da itaba har ya ware shima ya ɓarzi abarsa domin kuwa da yana tsoro kar wani abu ya faru, idan yaran ta sun gane, amma da yaga ita ko a jikinta sai kawai ya fara abubuwan da takeso, dukda kuwa yana shan wahala domin kuwa wani lokacin har fita yakeyi a haiyacin sa. Yauma abun da ya faru kenann domin AJ ya nunamata cewar yau fa yana cikin farincin, warewa yayi suka sha love da ƴar tsohuwar abokin nasa, amma fa saida ya gaji ya barta, saida yaji ta gamsu kafin ta yayyafa masa ruwa ya farka. *SALISU* Yakira numbar AJ ya kai sau goma amma bata shiga, sai kawai ya nufi police station ɗin cikin sauri domin kuwa gabansa na faɗuwa. Da sauri ya shiga gurin yana kallon sabon ɗan sanda da ke tsaye a gurin ba wanda ya saba ganiba, kasan cewar police station ɗin tsohone babu wasu ma'aikata a guri sai ƴan kaɗan hakanne yasa gurin ko mai gadi babu. Ɗan sandan ne ya tareshi yana cewa "Lfy daga ina me kake ne? Salis ya ce "Wasu mata da suke cikin gurinnan ɗazu sunake nema Pls?. Cikin mamaki ɗan sandan ya ce "Kaine AJ? Salis ya mai-maita suna kafin ya ce "Pls ina police ɗin da ke gurin ɗazu? Cikin ɓacin rai police ɗin ya ciro waya yana dannawa kafin a ɗaga ya ce "Police ɗin dage gurin nann kuma an koreshi a aiki, sukuma wanda kazo nema an sake musu guri. Cak Salis ya tsaya yana kallon police ɗin cikin mamaki, Salis ya buɗe baki zaiyi magana ya ji ɗan sandan na cewa "Yes sir ga wanda yake kawo musu abincin yazo, ina tsammanin ma shine AJ ɗin. Police ɗin yayi shiru yana ƙamewa a gurin kamar wani gunki yana sauraron abunda a ke cewa daga cikin wayan. Saida ya gama jin abunda a kace sannan cikin tsan-tsar girmamawa ya ce "Yes sir an gama. Salis dai sai kallonsa yake cikin mmk. Yana gama wayar ya kira wasu ƴansan dan ai kuwa nan take suka maƙala masa onka, suka turashi a cikin sel ɗin da su Innah suka fita. Yana tambayarsu lfy lfy amma ina saida suka turashi. *LAƊIFA POV* Salis na fita daga gida itama ta shiga ɗaki ta shirya ta ɗauki ATM card ɗinta ta shiga kiran numbar Umar. Bayan Umar ya ɗaukane ta sanar dashi cewar yazo ya karɓi kuɗin ya kai. Cikin murna Umaru ya amsa kafin ta sanar masa da gurin da zasu haɗu. Shuru tayi tana tunani. Shin meyasa Salis yafi damuwa da matsalar su yarinyar da zai aura! Bayan ga matsalar da nakeciki, kuma yasan cewar ina sonsa. Wata zuciyar ta ce "Shima saboda yana sontane, kamar wacce take zance da wani ta ce "Ok hakane shima sonta yakeyi ko, shine yasa ya manda da tawa matsalar ki, to Walhi nima saide duk abunda zaifaru yafaru, badai abunda yafaru a faya bane zai ƙara faruwa muda Daniyel to walhi muje zuwa. Tana kaiwa nann ta nufi gurinda zasu haɗu da Umar. Jiniyar motocin sojojine ya karaɗe ilahirin unguwar da mamu wasu mutane a cikinta sai ƴan ƙalilan kasan cewar a bayan garin gurin yake. Babu mota ko ɗaya da ta sabu damar shigowa gurin kasan cewar gurin baida girma kuma ga wata tsohuwar mota a gurin ita kadai ma ta ciki gurin. Parking sukayi sannan sojoji suka fara durgowa daga cikin kowacce mota. Babban sojojin barinki garin wanda a wannan watan yake cika shekaru biyu da samun ƙarin girma daga wani muƙamin zuwa wani, wanda a Yanzu haka shine Comandar ɗin duk wani sojo dake wannan state. Kama yanda kowa yasani mutumne mara imani ga tsan-tsar kishin addinindu wato addinin Christian, mutumne mai ƙiyayya da duk wani wanda ba ɗan addinisuba, hakanne yasa ya samu matsala da manyan ƴan kasuwar dake garin Benue sts. Baya samun yabo daga sauran addinan dake garin amma kuma duk wani ɗan addininsa yana jin daɗin abunda yakeyi, domin kuwa baya barin a takasu koda kuwa sune basu da gaskiya. Ƙiyayar sa tafi ƙarfi a kan masu bin addinin musulunci domin kuwa sune yake ganin sunfi yawa, bugu da ƙari matemakinsa ma Musulmi ne, mai suna Faruƙ. Comandar Daniyel kenan wanda ke zaune a ɗaya daga cikin gidan da kwamnati ta mallakamasa yanada mata guda ɗaya mai suna Eliza wacce sukecewa Momy, sai yara guda biyu mace da Namiji. Samuel da Sarah. SAMUEL ne babba yabata shekara huɗu. Yayinda dukkanninsu sukayi kama da Eliza sosai domin kuwa Elixa fara ce sosai ga iya cin uban wanka kamar matar shugaban ƙasa. Yanda mijinta ke ƙin musulunci sai ita ta damashi ta shanye domin kuwa ita ƴar gidan wani babban fasto ce wanda duk faɗin garin babu kamarsa. Daniyel yana son yaransa sosai, itama Mommy hk, amma yafi son ƴar autar su, wato SARAH. Lokacin aihuwa Sarah Saida a ka findda rai da mommy domin kuwa ta wahala, hakanne yasa bayan ta aihu yasa a ka cire mata ma haifar gaba ɗaya a kan ya daina ai huwa. Eh tabbas yana son yaran sa amma hakan baya hana idan suka taɓa masa martaba tofa sai sun gane shiɗin rainun ɗajine. Shine ya fara sakar ma yaransa kuɗi daga baya kuma ya daina sukuma suka shiga satar masa batare da yasabi. a kan kuɗi zai iya komai haka a kan addinmsa ma zai iya yin komai. Wannan kenan. Bai ko tsaya an buɗe masa ƙofar motar kamar yanda a kasaba, da sauri ya fito daga cikin motar yana nufar cikin ɗan ƙaramin Police station ɗin. Tin lokacin da da ƴan sanda sukaji jiniyar motocin suka miƙe tsaye suna ƙamewa a gurin kamar wasu gunkuna. Shikuwa Salis cikin tsananin tashin hankali yake abin wajan da ido ko zai gano waye zai shigo kodai Daniyel ne, ai kuwa kafin ya rufe baki sai gashi yana shigowa cikin takunsa na mazajen da suka shiga in da rakwaye basu iya shiba, cikin takunsa wanda ke gigita masu da sun hangoshi. Bai tsaya tambayar kowaba ya nufi gurin da Salis yake a ƙulle, cikin umarnin na shugaba a gurinsu yasa a ka fito da Salis. Tin kafin a durƙusar da shi a gaban sa ya ɗaga ƙafarsa ya buga masa wannan shegen ta ƙalmin nasu, kafin Salis ya ɗago ya ɗauke shi da mari, ya ƙara masa ya ɗagashi ya kwasheshi ya faɗi a rufa ciki, tsabar a zaba yasa Salis kasa yin ko da ihuma. Cikin zafin rai ya ɗago Salis da niyar sake kwasheshi. Chak ya tsaya yana binsa da kallo kafin sakeshi yana nuna shi da hannu cikin mamaki. Ya ce Salisu? Kafin Salis yayi mgn ya sake cewa "na You again? *ABDLLAH POV* Eh tabbas baiji daɗin sace Zainab da a kayiba, amma kuma baiji hakan ya bashi wani haushiba. Yana zaune yana jin yanda abubuwan suke ƙara rikicewa a yanar gizo-gizo. Yana cikin haka yaga kirin shek Kabir a karo na babu a dadi, tuno abunda yafaru tsakanin su yayi jiya a gidan su. Yana ɗagawa Daddy ya ce "Kazo gidan yanzu ina son ganin ka? Bai tsaya jin komaiba ya kashe wayar. Zaune suke dukkanin su a gaban Shrk Kabir kabuga. Abdllah Sadiya Nusaiba Maryam Nura sai Mommy. Cikin yanayin da yake nuni da cewa babu wasa ya kallesu ya ce "Abdalha kabani mamaki! Dama ashe a kwai wani abu tsaka ka da wannan ƴar iskar yarinyar wacce bata samu tarbiyaba, wacce bata san girman manyaba! Waccce ke rwwa da waƙa a gaban maza! Wacce take aikata saɓo ta sigar isgilanci, har ina kiranka kana katsemin waya a kan karna maka maganar ta ko? To naji kuma ka saurareni da kunnab basirar ka. Kaman yanda kasani ni dai bana amfani da duk wani abunda Allah da manzan sa basuceba, kuma duk inda ka je ka kaimusu yarinya to ina mai sanar dake yan ɗinnan kaje ka dawo musu da yarinya? Kuma nagaji da zagin da mutane suke maka akan zaman ka haka, idan kai abun bai damunka kaida ma haifiyar taka to ni yana damuna, saboda haka kaje gidan mlm Aliyu ka ga ƴarsa idan tayi ko batama mun gama mgn da mahaifinta mun tsayar da rana, idan kaga dama kaje ka ganta idan ma bakaga damaba ruwanka. Kowa shiru yayi yana sauraron Daddy domin kuwa abun ya basu mamaki, kenan daddy ma ya yarda cewar mommy da Sadiya suna bin Daddy da kallo ganin zai bar ɗakin. Tinda take Tare da mai gidan nata bata taɓa tsayawa tayi masa magana cikin zafiba, dukda bata son wannan ƙiyayar da yake nunawa ga abokan takun saƙar dasu. ta ce "Kabiru? ba daddy ba, ba kuma Maryam ba ba kuma Abdalha ba hatta Nura dake ɗan yaro saida ya kalli Mommy jin yanda ta kira sunan Daddy. Taci gaba da cewa... "Na gaji! Walhi na gaji da wannan baƙin ƙiyayar da kunewa junanku. Muna Musulmai ƴan uwa ɗaya Amma duk kun raba kahunanku, wasu suna yiwa wasu kallon kafurai, har takai ta kawo yanzu kana nema kayiwa yaronka aure da ƴar gidan mutumin da kowa yasan halin matarsa a garinnin. ADDININMU ɗaya al'adar mu ɗaya yaranmu ɗaya Allah mu ɗaya, annabinmu ɗaya, shin me mukeso muzama!?... Yanzu kazo ka hau kan maganar da kaji anayi a gari a kan shine ya saceta, baka tsaya kaji daga gareshiba ka yanke hukunci, shin hakan..."Ya isa haka ya isa . Cewar Daddy Yana ɗaga mata hannu ransa a mugun ɓace. Ya ce "Badai kince kin gajiba, to ga hanya nann daga ke har ɗan naki ai ban ɗaurekuba, kunada damar da zakuje duk inda kukikeso a cikin ƙasar nann. Yana kaiwa nann ya ce "Indai a kan su kike zance to damar kice. Ya juya yabar gidan gaba ɗaya. Gaban Mommy ne ya faɗi, yayinda Abdalh ya ɗago ya kalli Mommy ya kalli daddy, Sadiya ma kallon daddy tayi tana riƙe ƙurji. Abdalha ya ce "Dan Allah Mommy kibar wannan zance kar a je wani abu ya faru, ina dai nune zanyi duk abunda yakeso, badai aure bane zanyi. Kuma zan fito da Zainab. Cikin mamaki suka kalleshi har suna haɗa baki gurin cewar dama kaine ka saceta ɗin? Mommy da sauran yaranta suka haɗa baki. Abdalha ya ce "Eh nine kuma kamar yanda ya ce yau zan fito da ita, amma dan Allah Mommy ku fahimcen... "Kafin ya ƙarasa Mommy ta fashe da kuka....📝 * *PAGE.* 2️⃣0️⃣ .........Cikin mamaki suke kallon juna yayin da Comandar Daniyel ke bin Salis da wani irin kallon tsana yana nunashi da hannu. Cikin tsoro da fargaba Salis ke kallon sa yana jin tamkar a ce mafarki yakeyi ba gaske bane. Da sauri Comandar Daniyel ya kamo hannun Salis cikin tsanin ɓacin rai da ƙiyayar da ke fitowa daga fuskarsa cikin harshin English ya ce "Waye kai? Yayi tambar cikin rashin mutunci kai ka rantse da Allah baisan waye Salis ɗinba. Cikin mamaki Salis ya ɗago kansa ya kalleshi sai kuma ya sun kuyar da kansa ƙasa bai iya magana ba. Ganin haka yasa Comandar Daniyel cewa "Wato bayan duk abunda ya faru tsakanin mu daku saida kuka sake shigowa rayuwarmu ko? Wai ku meyasa musilman nan bakuda tunanine, Walhi na tsaneku bazan taɓa sonkuba, bana kwanarku. Sai kuma yayi shiru ya kalli Salis ɗin ya ce... "Waye AJ? Kuma me nene haɗinku da shi? Cikin tsananin ɓacin rai Salis ya ce "Abokinane kuma bansan ina yake ba a halin yanzu. Cikin jin haushi ya ce "To idan har kuna son fita daga Hannuna to sai kun kawo min shi kuma yau ɗin nan ya faɗa yana karewa Salis ɗin ido. Salis ya ce "Pls wai me Aj ɗin yayi? "Wani wawan mari yaji ya sauƙa daga gefen daman sa wanda kafin ya an kara an sake ƙara masa. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Ina AJ na tambayeka ba wai nace kaima ka tam bayeniba, kasan waye Ni kuma kasan abunda zan iya akan duk wani musulmi... Waima ba ubanku yayi muku iyaka da niba!? Bashi da kansa yace babuni babukuba? Akan wannan addinin naku addinin da yace yafi masa wanda ya tashi yaganshi a cikiba. To Walhi na tsaneku daga ku har duk zuri'ar ku, kuma Walhi in dai baku fito da wannan yaron ba kaima sai na ɓatar dakai baza'a sake ganin kaba har gaba da abada. Yana gamawa ya bar gurin ya shiga motarsa sauran sojojin suka take masa baya suka bar Salis a gurin. Daniyel yana zuwa gida ya tararr da wani sabon tashin hankalin. **HAJIYA BABBA*AJ* Zaune take tana rangaɗa kwalliya yayinda shi kuwa uban gaiyar ke tsaye yana bata amsar ta bayar da ta ke masa. "Nima yau gaba ɗaya bana jin daɗin jikina sosai sai naji gabana na faɗuwa wani lokaci. AJ ya ce "Nima har zuwa yanzu ban dai jin hakaba amma in Sha Allah komai lafiya. Ta ce "To amin Allah yasa hakanne, amma dai yau inason muyi waya da su Salis ko hankalina zai kwanta. AJ ya ce "Eh to hakanma dai-dai ne. Take ta ciro waya ta kira laɗifa, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga haɗi da cewa "laɗifa lafiya...kafin ta ƙara da laɗifa ta ce "Hajiya ina kika je ne, ta faɗa kamar tayi kuka. Saida hajiya Babba ta sauke a jiyar zuciya kafin ta ce "Laɗifa fatan dai kuna lfy ko? Cikin muryar shaƙwaɓa ta ce "Dan Allah Hajiya ki dawo Walhi min yi kewarki Pls and pls dan Allha mun gaji, waima kuna inane? number ki bata shiga tun lokacin da kika tafi. Hajiya ta ce "Ina lafiya very soon zaku ganni..."Waima to Hajiya inane kikaje? Bakince Abuja zakujeba wai ma dan Allah yanzu kina ina? Cikin son kawar da zancen Hajiya ta ce "Ina Salis? Dama de yana zuwa aikin bai tsaya wasa ba? Cikin ƙwantar da hankali ta ce.... "Hajiya ai Salis ya zama ɗan soyayya, domin kuwa yasa rayuwarsa a cikin damuwar da tafi ƙarfinsa. Cikin sauri ta ce "Ban gane ba? Wacce irin matsala? Laɗifa ta ce "Yanzu haka yana hannun Daniyel... "zumbur Hajiya Babba ta miƙe tsaye haɗi da cewa "Wani Daniyel? Laɗifa da take jin ita ai hakan shine samuwar muradinta ta ce "Comandar Daniyel dai Daddy brother. Cikin wani tashin hankali Hajiya Babba ta ce "No no karna ƙara jin haka daga bakinki, Walhi ƙarya yakeyi bai isa a karo na biyu yaci mutuncina na barshiba. Cikin Muryar da tasa ita kanta laɗifar tsorata Hajiya Babba ta ce "Menene ya haɗasu? Shi Salis baisan waye Comanda Daniyel bane, kodai bashi da hankaline baisan me yakeyiba kodai ya manta da abunda Daddy yace muku ne? Laɗifa ta ce "Haba Hajiya wannan fa ba wani abun tashin hankali bane, ai shima Comandar Daniyel ɗin ai ya isa da mu...."Ya isa da uwarki nace ya isa da uwarki! Walhi laɗifa kikiyayeni banza mara mutunci ke idan har kinada hankalima har zaki ƙara kallon wannan ƙatin arnan da idon mutunci, mutumin da ya kasha ɗan uwansa saboda ya bar addinin ƙarya izuwa na Gaskiya, to Walhi ki shiga hankalinki, kuma ina hanyar dawowa gobe gobe in Sha Allah!, Wlhi wannan karan sai yasan dadayanzu ba ɗaya bane,. Tana gama wayar ta kashi tana haɗa wani uban zufa, kallon wayar tata tayi ta danna kiran numbar Salis amma bata shiga. Kallon AJ tayi tace gobe zamu koma 9j. AJ tin lokacin da Hajiya Babba take yin wayar ya nutsu yana jin me take cewa. Lokacin da yaji sunan Comandar Daniyel sai yaji kamar yasan mai wannan sunan amma ya kasa tunawa, yana da niyar idan tagama shima yayi waya da Innah ko Nana kokuma Sarah wacce izuwa yanzu kullum sai yayi mafarkin ta. Amma yanda yaganta cikin ɓacin rai yasa ya fasa tambayarta. Cikin wani murya ta ce "Walhi wannan mutumin sai yagane cewar yanzu bada bane, da ba dan yamma tayiba da yau zamu tafi, bazan barshiba Walhi. Shidai sai kallonta ya keyi yana jin shi a wani yanayi, shin murna zaiyi kodai baƙin ciki, yanzu kenan idan sun koma sai sunyi wata biyar ɗin kafin yaci kuɗin! (Kai AJ sarkin son kuɗi) afili ya ce "Hajiya mubari mu kammala sati biyun mn kinga ai komai zaifi tafiya saiti ko? Cikin tsananin fushi da bai taɓa gani a fuskartaba ta ce "Kasan wacce masiface ta tasomin a gida!? Kasan me yake shirin faruwa? To gobe zamu tafi bazan iya zamaba. Tana faɗa ta shiga ɗaki ta ciro masa wayarsa ta bashi tace ga wayarka nann zaka iya kiran kowa. Ganin haka yasa AJ yin shuru yana buɗe wayar yasa sabon layin nasa na wannan ƙasar kafin ya shiga kiran numbar Nana. *ABDALHA POV* Kuka Mommy keyi taƙi ta tsaya ta saurareshi ganin haka yasa ya miƙe tsaye sauran ƙannan nasa suka bishi da kallon mamaki, yayinda Sadiya tayi ƙarfin halin cewar "Yaya me zaisa ka sace..."hannu ya ɗaga mata yana barin ɗakin cikin tsanani ɓacinrai, domin kuwa ransa yayi mugun ɓaci sosai, harma baisan meye abunyiba. Tunawa yayi da maganar daddy "Kaje ka fito musu da yarinya a duk inda ka ɓoyeta kuma mun gama magana da baban yarinyar da na zaɓa maka, indan kaga damar zuwa ruwanka idanma bakajeba to bazamu fasa daga ranar da muka yankeba...Na gaji da maganganu da mutane keyi a kanka, idan kai bai damunka toni yana damuna...Kin gaji ko to idan kin gaji daga ke har yaranki ai ga hanya nan kunada damar zuwa duk inda kukaga dama acikin ƙasarnan. Ajiyar zuciya ya sauke yana shiga motarsa, tafiya ya keyi yana tunanin abunyi. Nan ma maganar Mommy ta dawo masa kansa. "Komai ɗaya Al'adar mu ɗaya, yarenmu ɗaya Allahnmu ɗaya Annabinmu ɗaya, ADDININMU ɗaya Amma kunɗauki tsana kun ɗora a kan junanku, Walhi kuji tsoran Allah domin wannan abun ba addini bane. "Kallon agogon hannusa yayi sannan ya koma gidan sa domin shiryawa zuwa gurin su. "Haba mlm yanzu dawanne kakeso muju da ɓatar ƴata kakeso kokuma da wannan masifar naka!? Shi wannan yaron da kuketa zargin shine ya saceta shin kunyi magana dashi ya ce shine ya saceta ne? Kudinga yiwa kanku a dalcifa, ni yanzu damuwata kawai yarinyata ta baiyana koma waye yaje shida Allah, kaikuma Walhi idan na ƙarajin kace wani abu a kan wannan yaron to Walhi sai na saɓa maka, banza mara zuciya. Mama ta faɗa tana nuna gurin da Isa yake staye yana ƙara zuga mahaifin nasu akan cewar Abdalh ne yasaceta shi kuwa mlm dama a sama yake ya tsani mutanann baya son duk abunda zai haɗa shi dasu, yanzuma jiyake da yanada dama da ya tashi duk wani ɗan aƙidar su Abdalh ɗin gaba ɗaya kowa ya huta. Mama ta ci gaba da cewa ...."Gashi tunda abunnan ya faru kuna gida babu wanda yafita domin nemanta amma kunzo kuna ta zancen banza a kan yaronda inada tabbacin baima san suwaye suka ɗauketaba. Ni dai Allah ya bayyana min yarinya. Cikin tsananin faɗa da yasa muryarsa har rawa takeyi mlm ya ce "Walhi kin yi ƙarya ba a gidannan ba! Dama na lura dake bakison kuji ana faɗar laifin wannan yaron ko? To Walhi bari kiji kotu ce zata rabamu da wannan yaron mutuƙar yarinyata bata dawo gida yauba, ga alamu sun nuna cewar shine ya saceta, kuma har yanzu daga shi har uban nasa wanda shine mai ɗaure masa gindi babu wanda ya fito yayi magana. Shegu dangin tsiya munafukan Allah, Walhi sai sun tozarta idai irin wannan rayuwar satar yaran mutane itace halaiyarsu. Caraf isa ya cafe da cewar... "Walhi haka sukeyi, kwanakin baya ma haka yaran da suka ɓata a hanyar school ance sune suka sacesu. Momy ta ce "wallhi kuji tsoran Allah domin wannan abun da kukeyi ba shine mafitaba, dama kishin neman ilimi kukeyi da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yayi alfahari daku, bawai zagin juna kuba, idan anyi magana kuce kune nagari, Walhi addinmu bai koyar damu cin mutuncin ɗan adam ba, ɗan adam ɗin ma wai musulmi. Kuma yanzu gashi ai kunju daɗi tinda gashi sai raba kawunan al'umma kukeyi, kullum tashin hankali kuma duk kune dalilin hakan, yara marasa sanin ciwon kansu sai zage-zage sukeyi a gari. Cikin ɓacin rai mlm ya ce "Walhi ki kiyayeni ki fita daga idona "Nidai a je a nemomin yarinyata shine kawai, ai ADDININMU baiyi hani da sace yaran mutanebako? Kuma Walhi sai munje kotu. Yana kaiwa nan ta rushe da kuka, isa da mlm suka fita suna cewa ai shine ya saceta kuma sai ya fito da ita. *ABIN DUBAWA. TUNANI MAI KYU* Waya ya ɗauka ya danna kira, sai da ta kusa tsinkewa aka ɗaga. Kafin ayi mgn ya ce "Gani nazo gurin wani gidane? Ya ce "Ok gani kubuɗe min get ɗin ina ƙofar gidan. Bayan ya shiga da motar tasa ya fito ya nufi wata ƙaramar hanya da ita ce kaɗai zata sadaka da cikin palorn gidan. Yana shiga ya ƙara kiran numbar taso suka ce ya dawo baya, ba'a wannan gidan sukeba dama sun kwadashi ne ko tafe yakeda ƴan sanda, cikin mamaki ya ce "Bayan munyi mgn daku maizaisa nayi ƙarya? Ta cikin wayar a kace ayi haƙuri shek ɗan gidan Shek kasan yanzu duniyar ce ba'a yarda da kowa. Ya nufi gurin da sukace masa, bayan yaje ɗaya gurin da suka cemasane ya shiga gidan domin ƙofar gidan a buɗe take, ya ce "Ina take? Da sauri sukace tana ciki! Ya ce "Damade baku taɓataba?, nann suka fara sun guyar da kai alamar aikin gama ya gama. Yana tura ɗakin da tage ya tsaya chak cikin mamaki haɗi da zaro ido waje. Da sauri ya fito daga motar ransa a ɓace ya shiga kiran matar tasa "Elixa!!! Kafin ya rufe baki idonsa ya sauƙa a kan wasu samari guda biyu, zaune a cikin palorn nasa. Cikin tsananin mamaki ganin harda musilmi a cikinsu ya ce "Meya kawo su? Mommy ta ce "wai kuɗin Samuel sukazo biya shine nace sujira ka kadawo. Cikin mamaki daddy yake binsu da kallo haɗida zubawa shigar wannan ba haushen da kallon tsana domin kuwa doguwar riga ce a jikinsa sai hula mai kyin gaske. Ya ce "Suwaye kuɗin? menene haɗinku dashi? kuma yaushe ya baku aron kuɗinsa?. Kowa yabar gida tabbas gida ya barshi! Yau dai ga Hajiya Babba tareda AJ a ƙasar 9j. Kana kallon fuskar Hajiya Babba kasan babu annuri ko kaɗan, harma wani jajaja fuskarta keyi. Yayinda shi kuwa AJ ya buɗe ido yana kallon ƙasar tasa wacce bai taɓa barintaba koda kuwa na kwana ɗayane Amma yanzu harna kwanaki biyar. Mota suka shiga izuwa gida, yayinda AJ yake kallon komai kamar a mafarki. A ƙofar gidan Hajiya Babba sukayi parking ta ce "Ya fita yaje gida in yazo anjima zata kirashi, kuma zata tura masa kuɗin idan ta shiga gida. Kasan cewar da yamma ne sai kawai AJ ya ce "To angama dama nimanna matsu naga Innah da Nana. Saida tafiya wani shafi yayi musu soyayya mai yawa kafin ya nufi unguwar tasu. Tin daga bakin layin unguwarsu yaga ana ta kallonsa sai kawai ya bar hakan akan irin kayan dake jikinsane yasa, yana tafiya baya ko kallon kowa kamar yanda ya saba a da bare yanzu da yake ganin shima wanine, suma ƴan uwarsa da yake sun san halinsa na ɗaukar kansa yafikowa yasa babu wanda tanada mgn sai kallonsa da sukeyi. Kallon ƙofar gidan nasu yayi a buɗe, sai kawai yasa kai ya shiga yana sallama haɗida zabgawa Innah kira cikin muryarsa dake nuna cewar yayi kewarsu sosai.....✍️ *Abin tambaya. Shin meye tsakanin su Hajiya Babba da Comandar Daniyel? Shin ina ne Abdalha yaje? Shin da gaske shine ya sace Zainab? To gadai AJ ya sauƙa a 9j? Me zai faru? Yanzu komai zai warware. KUKASANCE da S REZA. Domin jin me zaifaru.* * *Kafin kufara karanta wannan page ɗin, inaso kutuna abunda nace a page ɗin farko, Pls* 🙏 *PAGE. 2️⃣1️⃣* ......... Innah! Innah! Innah! Cikin murna da ɗokin son ganin Innar tasa yake ranƙaɗa mata wannan uban kiran kai ka rantse da Allah irin ya hangota daga nesane amma bata jisaba. Saboda tsabar ɗoki da AJ keyine yasa bai ko kula da kurarr da gidan ya ɗanyiba, sai kawai ya nufi ɗakin Innah da sauri yana cigaba da kiran sunanta, wannan karan harda sunan Nana yake haɗawa. Cikin mamaki yake kallon ƙofar innar tasa abuɗe gakuma kwanukan abinci da sauran abincin dake ciki alamar dai andaɗe ba'a cikin gidan, da sauri ya fito daga ɗakin Innah ya nufi ɗakin Nana. Yana zuwa itama yaga ƙofar ɗakin abuɗe, har yanzu bai daina kiran sunan Nana ba, yana shiga idonsa ya fara sauƙa a kan kadonta, sai ya hango wayarta a kan gadon, ai kuwa da sauri ya ɗauka yana ƙoƙarin kunnawa, amma wayar taƙi kunnuwa, domin kuwa babu caji. Fitowa yayi da wayar izuwa tsakar gida jikinsa har rawa yakeyi domin kuwa izuwa yanzu jikinsa ya fara aiyana masa mugayan abubuwa a kan su innah. Sai a lokacin yabi ko'ina na gidan da kallo yaga tabbas babu kowa a gidan. Afili ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ina su inna suka tafi!? Cikin zafin rai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran Hajiya Babba, ai kuwa kira ɗaya ta ɗaga, tana cewa "Pls ina zuwa zan kiraka. Tana gama faɗa ta kashe wayar batare da tajira abunda zaiceba. Sai a lokacin kuma ya fashe da wani irin kuka ya ce "No no no yana faɗa yana girgiza hannunsa yana jabaya, ya ce "Noooooooo! tabbas bai yarda da abunda zuciyarsa take cemasa akan su innha ɗinba, hakanne yasa yayi waje izuwa ƙofar gidan su, yana zuwa kuma ya tsaya yana kallon al'ummar gurin cikin rikicewa yarasa abunyi sai kawai ya nufi gurin taron samarin da ke kusa da wani ɗan shago, wanda shi a tunaninsa dai idan bai mantaba bai taɓa zama a gurinba ko kuma yayi musu mgn ko sallama aganin sa su ƴaƴan talakawa shima haka to me slamar zata ƙara musu, saidema idan yazo hucewa ya dinga musu kallon banza yayinda sukuma suka ɗaukeshi mai gyrman kai, domin kuwa sunsan bai ajiyeba kuma bai baiwa kowa a jiyaba sai shegin iyayi da nuna shi wanine. Ko sallama baiyiba ya ƙarasa gurin tsabar a rikice yake ya ce "Ina kuka kaimin Innah ta da Nana Pls? Yayi maganar ne baisan cewar abunda yafito daga bakinsa ba kenann yaci gaba da cewa...Dan Allah ku fito min dasu sune kaɗai gareni pls dan Allah kuyi mgn Walhi zan iya shiga wani hali, idan laifi nayi muku a kaina zaku sauƙe basuba. Kamar haɗin baki yana kaiwa aya duk samarin gurin suka watse suka barshi babu wanda ya tamka masa sai wani guda ɗaya wanda daga gani kasan yafi kowa jin haushin Aj ɗin ya ce "Kai amma Walhi kama raina mana wayo, watoma mune ɓarayin da zamu sace maka u'wa ko? To me suke dashi da har zamu sacesu, kaje can gurin da ka aikata satar ka kanemesu amma ba nann ba. Kasan cewar sunji wai-wai AJ ɗin sata yiyi daga bakin duniya. Saurayin na gama faɗar haka ya bar gurin cikeda jin haushin AJ ɗin. Shiru yayi yana tauna maganar yaron ta ƙarshe wai sata! sata! sata! Haka yaketa mai-maita sunan sata ko zai tuno lokacin da yayita amma ya kasa ya ce "Nine nayi sata!? To a ina! Kuma yaushe! ƙaryane walhi ƙaryane ni ban taɓa sataba saide wani amma baniba. Ya ɗaga kai domin tambayar gayan amma ko alamarsa bai hangoba, ya juya izuwa hagunsa sai yaga yara suna klonsa kamar wani mahaukaci. Tabbas sai yanzu yasan cewar ashe abokima wani ɓangarene da zai dinga taimaka maka a rayuwa, shi baida abokai duk yaci mutuncin su, ya koresu wai abota ƴaƴan talakawa a tare batada amfani. Chak ya tsaya bayan ya tuno da abokinsa Kamal, Wanda babu irin cimutuncin da bai masaba amma kamal ɗin yaƙi haƙura domin yana zuwa nemansa kokuma yaje su haɗu a gidan bredin da yake aiki a da. Da sauri yatashi domin nufar gidan su kamal ɗin amma ya ji ankira sunansa AJ. Chak ya tsaya yana juyowa fuskarsa duk ajiƙeda hawaye, idonsa yayi ja duk ya fita a haiyacinsa. Kadija ce ƙawar Nana wacce itama ta samu labarin abun daga bakin ƴan unguwar domin kuwa kowa yaji lokacin da sojojin suka shigo unguwar kuma suka tafi da su Nana ɗin. "Sojojine sukazo suka tafi da Innah da Nana yau kwana huɗu kenan basu dawo ba kuma bamusan inane suka kaisuba. Ya manta da cewar yarinyar ta ce masa basu san me su Nana sukayiba amma tsabar ruɗewa ya ce "Sojoji! mai sukayi, ya faɗa yana ruƙo hannun kadijar kamar itace zata sanar masa da komai. Ta sake cewa Walhi abunda na sani kenan. Tafaɗa cikin rawar murya domin riƙon da ya mata. Kafin aj yayi magana wani saurayi da yasan AJ tare da Sarah ne ya ce... "Wannan sojan baban wannan arniyar budurwarka ɗain ne yazo ya tafi dasu harda duka da zagin duk wani musilmi dake duniya bama iya kan ƴan unguwaba kuma harda yarinyar a kazo da alamar dai itace ta nuna musu gidan naku, kuma sunzo basu gankaba shene sukayi ram da tsohuwar Allah da batasa hawaba bare sauƙa...sau rayin ya ƙare da cewar damade ba ciki kamataba domin naga itama sai kuka takeyi da alamar dai itama an ɗan samota kafin su fito, kasan fa sojoji basuda tausayi harta ƴaƴan suma tafka sukeyi bare ƴaƴan wasu. AJ ya saki hannun Kadija wanda shi baima san ya riƙetaba, afili ya ce "Soja Sarah baban ta kenan ya kamata ita kuma ta zo nunani. dalla-dalla zuciyarsa ta faiyace masa komai shikuma baisan cewar a fili yake faɗaba, acikin minty ɗaya zuciyar sa ta sanar masa da duk abunda ya faru, kuma yasan hakanne. Rasa wani irin tunani zai farayi daga ciki domin kuwa yasan yakamata yayi tunani amma ya kasa, sai kawai ya miƙe ya nufi gidan su Sarah cikin dakiyar zuciya, yana tafiya yana tuno irin wahalar dasu Innah suka sha a hannun wannan baƙin kafirin da kowa yayi shedarsa wajan cin mutuncin Addinin Musulunci koda kuwa babu dalili bare kuma a ce akwai dalil. Yana tafiya hawaye na wanke masa ido na tausayin su Innah da Nana. *ABDALHA POV* Da sauri Abdalha ya dawo da kallonsa izuwa gurin samarin dake cikin gidan ya ce "Me kuka ai kata mata? Yayi tambayar cikin rikicewa, kafin su bashi amsa yayi gurin da take kwance kamar macacciya ya ɗago fuskarta yaga idonta a rufe, sai kawai ya ɗauketa izuwa matarsa, bai ko ƙara kallon samarinba, ɗaya daga cikin samarinne ya ce "Mlm Walhi taci albarkacinka badan hakaba da daga yau idan akace ta ƙara zagin malamammu a ciki waƙa bazata ƙaraba shegiya kuma har yanzu zamuci gaba da bibiyarta shege ka fasa mara kunyar banza ƴar tasha kawai. ɗaya daga cikin kuma yana ganawa cikin ihuu!. Abdalha baiko bi takansa ba ya hanyar barin gidan. Kasancewar yanzu nemanta akeyi kuma ko ina hotontane ke yawo sai kawai ya kaita gidan likitan sa domin sirri. Tun kafin ya isa gidan ya kira likitan ya sanar dashi cewar yazo gida idan baya gida yanada emergency, likitan ya sanar masa da cewar yana gida yau domin madam ɗinsa bata jin daɗi. Haka kuwa a kayi ABDALLAH ya huce da Zainab gidan likitan nasa. Shine ya ƙara ɗaukarta har cikin gidan bayan likitan ya taimaka masa, likitan mai suna Musa bai ganetaba domin kuwa yanda ta fita a haiyacinta ga kuma rama da tayi sosai, nan take yace da Abdalha zai fara mata al'lura kafin yaje asibiti yadawo zai ɗauko kayan ƙwaji, nan ya tafi yabar Abdalh zaune kusa da ita yana ƙura mata ido cikin tausayi. *ZAINAB VOP* Tinda aka zuba mata wani abu a fuska bata farkaba sai cikin dare. Ihu takeyi tana tambayar a ina take domin kuwa ɗakin yayi duhu. A haka ta kwana a cikin ɗakin babu wanda ya kulata. Washe gari ma sai misalin ƙarfe tara na safe kafin ta ga wasu samari guda huɗu, kowanensu ya rufe fuskarsa da baƙin ƙyelle. Tambayarsu ta farayi cikin kuka domin kuwa harga Allah ta tsorata. "Suwaye ku? Me naimuku Pls Dan Allah karku cutar dani pls? Babban cikinsune ya ce "Tambayarmu ma kikeyi cewar me kike mana ko? To kafin muci ubanki bari mu fara nuna miki dalilin kawoki nan da mukayi shegiya mai kamar ubbanta, masu ƙaryar addini masu son rarraba kawunan musilman gaskiya. Yana kaiwa nann ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunna mata waƙarta da tayi mai sunan buɗaɗɗiyar wasiƙa. Babu wanda ya sake yin magana harsaida waƙar ta ƙare har ƙarshe, kafin ya sake dawowa da ita akaro na biyu. Waƙar ta farayi kenan ya kashe ya kalleta ya ce "Daga yau bazaki ƙara yin wata waƙa irin wannan ba, kin zagi malamammu kinci mutuncinsu hakanne yasa mukace sai mun hukuntaki domin kisan cewar malamai ba mutanan banza bane. Sannan ya ce "Zamu kunna miki waƙar ki dinga fassarata domin kuwa wani guri a har-harɗe tayi maganar. Take Saiyada ta haɗiyi wani yahu maƙot, tayi dauriyar cewar..."Walhi bada kowa nakeba kuma ni nayi waƙarne domin Allah. Saide kawai wani guri da nayi gargaɗi akan wasu, kuma nasan sunji kuma su..."Wani mari taji mai sauƙar ungulu daga gefenta, wanda yasa jinta tsayawa na ɗan daƙiƙu kaɗan, bataji ƙarar wani marin da aka ƙara mataba sai dai taji zafinsa sannan ga kuma bakunansu dake motsi wanda ke nuni da cewar wannan karan dukkansune suke mgn amma batajin me ceke cewa. Tana kallonsu sai nunata da hannu sukeyi alamar dai zasu iya ai kata mata komai a wannan lokacin. Tana haka taji an ƙara mata mari, kafin ta ɗago ta gane waye anyi boll da ita, sake kamo kanta a kayi aka ɗago buskarta ido cikin ido yake mata mgn alamar gargadi dai, yanayi yana nuna mata hannu wanda ko kaɗan batajii abun da ya ce ba. Tunani takeyi shin abun da tace ne ya ɓata musu rai haka da suke mata wannan dukan. Yana gamawa ya ƙara mata mari aɓarin da aka mata na farko. Hakanne yasa taji wani abu shuuu ya huce ta kunnanta ta faɗi agurin ta fashe da kuka. Cikin mamaki taji yana cewa "tsabar raini ki kalli idonmu kice wai wani guri ne kikayi gargaɗi ga wasu! wato malaman mune wasu ko? sai kinsan kinyi da malamanmu mahaukaciya babu wanda zaisan ina kike har gaba da abada dan ubanki, dama nifa na tsaneki walhi ban samu damar ɓatar dake bane tun da sai yanzu, yana kaiwa nann ya barta agurin suka tafi. Haka Zainab taci gaba da zama a gurin har yammma kafin aka zomata da abinci ɗan kaɗan babu ruwa. Bayan nan bata sake ganin suba sai washe gari, wato dai kwananta biyu a gurin. Yauma da safe sukazo kamar ranar farko, suka tarar da abincin da suka kawo mata ko kallonsa batayiba. Babban ya ce "Good Saiyada haka mukeso kar kici abinci kinji? Ya faɗa yana sakin dariya. Kallonsu takeyi cikin wata murya tace "Dan Allah ku barni na tafi gida me kukeso dani kusanar min idan kuɗine zan baku Walhi zan baku koda kuwa nawa kikeso....sannan dan Allah waye yasa ku kumin wannan zalunci? Duk tayi maganar ne babu ko haɗiyar yawu. Ya ce "Ubanki ne ya turomu! Ji kake tass tass tass har sau uku yaci gaba da cewa..."Ke yanzu har kin kai a ce wani ya turomu gurinki! Mune muka turo kannmu, kuma bari kiji ko uban ki wannan mai kama da aljanunnan baida kuɗin da zai bamu bareke ƴar maula. Yana kaiwa ya ƙara mata mari yayi boll da ita, suka fita suka bar mata ɗakin. Tayi kuka har ta godewa Allah kafin ta tsagaita da kukan ta shiga nazari akan Abdalh ne zaisa a mata wannan aikin tabbas shine. Washe garima haka wanda yayi dai-dai da kwananta uku kenan a gidan. Yauma saida taci uban duka kafin suka jawota zuwa parlon gidan ɗaya daga ciki wanda ba shine oganba ya ce "Munaso kibar wannan aƙidar taku daga yau ki dawo tamu ta gaskiya wato sunna, kuma kiyi mn alƙawarin bazaki koma waccar taku ɗinba koda kin koma gida, kuma kin daina aikata duk wani bidi'a da ubanki ya koya miki? Sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi, kana ganinta kasan ta jigata, kwana uku kenan ko abinci bataciba ko maganarta bata fita, tana son tayi mgn amma ta kasa hasalima biyu-biyu take ganinsu, tana son sanar masa cewar koda irinsu ɗari za'a taro bazaisa ta bar kan aƙidarta ba saide su kasheta, amma ta kasa. Ya buɗe baki zaiyi magana ogan nasu ya ce "what!!! Ya faɗa yana kallon wayar hannunsa. Hoton Shek Abdalh Kabir kabugane tare da Zainab da kuma wasu rubutu dake nuni da cewar shine ya saceta, da sauri ya miƙi yana nunawa abokan nasa. Nan take hankalin su ya tashi jin yanda al'umma suka ɗorawa Abdalh, ai basuma naga komaiba saida suka buɗe fexxbookk suka dinga ganin kace na ce ɗin al'umma kuka kowa Abdalh yake zargi. Hakanne yasa ogan nasu dayake yanada numbar Abdalha sai kawai ya kirashi da yamma ya sanar masa cewar tana gurinsu, kuma abunbda yasa suka sanar masa saboda sunga kowa shi age zarg, sukuma suna giemamashi sosai. Nann Abdalha ya tambaye su dalilin da yasa suka saceta, suka sanar masa saboda cin mutuncin malaman su da takeyi ne shine yasa, Abdalha ya musu faɗa sosai haɗi da cewar idan kunaso mutum ya ƙirmamq aƙidarku to kuyi masa nuni da abubuwan kirki da aƙidar taku taƙunsa na tsoran Allah bawai ku biye masaba yanzu wannan abunda kukayi kuna tunanin idan wani yaji za'a yarda cewar ƴan sunnha ne sukayi hk? Kasan cewar sa mlm kuma mai iya sarrafa kalamai yayin wa'azi hakanne yasa jikinsu yayi sanyi suka sanar masa da gurin da suke, yace zaizo washe gari. Duk abunda akeyi Zainab na jinsu kasan cewar an saka wayar a amsa kowa. Suna gamawa ogan ya kallesu ya ce "Mun aikata kuskure Amma kuma ai mun koya mata hankali, ɗayan da waazan da Abdalh din yamusu ya shige shi ya ce "Muɗauketa mu kaita har gida mu nemi yafiyar iyayenta, ɗayan ma yace "Kunga ubanta malami ne yayantama hk itama haka zasu yafe mana? Ogan ya ce "No mubari har Abdalh yazo sai mu bashi ita kunga shi yasan ya zaiyi da ita. Wanda yaɗan ji wa'azin ya ƙara cewa...."to idan mukayi haka kuma ai al'umma zasu yarda cewar shine ya saceta kenan ko? Ogan yace "Munsan yanda zamuyi har komai yayi dai-dai. Wannnan shawarin bayan sun komar da ZAINAB cikin ɗakintane sukeyi. Wani ya ce :"To idan Abdalh yazo da police fa? Oga ya ce "Kumafa hakane. Take ya sake kiran Abdalh ya sanar dashi akan kar yazo da Police. Abdalha yace shi kaɗai zaizo. Hakanma wasu daga ciki sukace basu yardaba sai sun kwada shi, shi dalilin da yasa suka fara nuna masa wani gidan. Suna gamawa kowa ya shiga ɗakin Zainab wacce ko kwance idonta alumshe, suka siyo mata abinci harda nama amma ta kasa ci. Haka suka kwana a kanta suna kallonta idan ta suma su watsa mata ruwa, har washe gari da tayi dogon suma wanda dukkansu suka shiga cikin damawa sunyi tunanin ta mutu, har Abdalh yazo suna tsaye a palorn....✍️ * *PAGE.* 2️⃣2️⃣ *BABU EDITING* ......... Yana zaune agurin yana kallonta har Dr Musu y dawo, kallonsa yayi cikin mamaki ya ce "Har kadawo? Dr ya a'msa da cewa yasa an kawo masa ne. Bayan ya dawo palon gidanne ya zauna Dr ya kalleshi ya ce "Wai shin Abdalha meke faruwa da batun yarinyar da akace kaine kasaceta? Tabbas Dr Musu ya gyrmi Abdalh nesa ba kusaba amma kasancewar shi Allah ya ɗaukakashi fiye da Dr Musu ɗin, sai suka zama tamkar abokai. Abdalha ya ɗago kai babu alamar fargaba ya ce "Itace wannan. Yafaɗa babu alamar wasa. Dr Musa ya zauna daƙwas cikin tsananin mamaki ya ce "kana nufin kace Zainab ce wannan? Abdalha bai bashi amsaba ya ce "Idan ta farka kasa madam ɗinka ta taimaka mata tayi wanka kuma abata abinci sanan ka kirani. Yana gama faɗa ya bar gidan batare da ya tsaya amsa tambayoyin da Dr kesan masaba. Dakallo Dr yabishi cikin sabon salon mamakin lamarin Abdalha. Afili ya ce "kenann shine ya saceta! Sanin ba mai bashi amsane yasa ya koma ɗakin da Zainab ɗin ke ciki da sauri har yana cin karo da kujera. *HAJIYA BABBA POV* Kallon palon nata takeyi cikin tsananin mamaki da abun al'ajabi, ta ce "ooo ni Allah me laɗifa takezon zamane? Ma'aikatan da ke sunkuye a cikin palorn da basu san da shigowar taɓa sunan nan a yanda ta shigo ta samesu. Da ƙarfi ta ƙwaɗawa laɗifa kira wanda yasa ma'aikatan ɗagowa daga sunkuyan da suke suka kalleta, nan take suka fara mata barka da dawowa. Dai-dai Lokacin laɗifa tana sauƙowa daga sama waya kare a kunnanta alamar waya takeyi. HAJIYA BABBA ta nuna gurin da ƴan aiki suke ta ce "Lafiya kuwa naga waɗannan a haka? Cikin wani ihuu da tsan-tsar farin ciki tanufi uwar tata tana cewa "oyoyo Hajiya Allah inace ba yau zakidawo duk na zaci wasa kikemin. Kafin Hajiya Babba tayi magana ta ce da ƴan aikin subar palorn yanzu nan kafin ta ƙirga uku. Haka kuwa suka shiga rige-rigen bar gurin cikin sauri. Hajiya ta dawo da kallonta zuwaga laɗifa ta ce "Me ya faru zaki sakasu irin wannan aikin? Ta ce "Wallhi Hajiya ƴan aikin nann duk ƴan raininn wayone, wai saboda bana gida sai kowacce ta ci wanka suka zauna suna hirarr wai kowacce son yaya Salis sukeyi harda sha warin yanda zasu mallakeshi, cikin mamaki Hajiya ke kallon ƴan aikin ta ce "Wato kuna sha warin yanda zaku mallake min yaro ko? Kuna matsayin ƴan aiki amma kun iya tunanin cutar da ɗan gidako? To dan uwar kowacce daga cikin ku kuhaɗa kayanku duk na sallameku ƴan iska kawai. Hajiya ta ƙarasa maganar tana nuna musu hanyar waje. Yayinda kallo ɗaya zaka mata kagane tana cikin fushine. Nan fa ƴan aikin kowacce ta shiga bada haƙuri a kan cewar Walhi rabi ce ta zigasu( Rabi itace babbar ƴar aikin gidan) Hajaya da Laɗifa basu tsaya bin ta kansuba suka koresu. Yayinda laɗifa ta kira Iro mai gadi cikin isa da cewar ita ɗin itace ta ce "Walhi Iro idan har kabari yarannan suka ƙara shigowa gidannan to kaima a bakin aikinka.tana faɗa ta bar gurin. Shikuwa iro sanin cewar itace matar gidan yasa ya rufe gidan yana cewar in Sha Allah bazasu shigoba. Laɗifa na shiga palor ta tararr da Hajiya na waya, amma tana zuwa ta kashe. "Tashi mutafu? Hajiya ta faɗa tana nufar ƙofar waje. Laɗifa ta ce "Haba Hajiya ko hutawa bakiyiba? "Laɗifa bakida hankali bakisan waye wannan mutumin ba, Walhi zai iya kashe mutum mutuƙar ba addininsu ɗayaba, barinma ace mudulmine. Laɗifa ta zaro ido waje ta ce "Wai Hajiya meyasa baya son musilmai ne? Kuma naga Daddy mudulmine? "Cikin ɓacin rai ta ce "Shiga mota muje, wannan labarin bai shafekiba. Haka suka shiga mota laɗifa dai sai tunanin wannan lamarin takeyi. Batayi auneba sai ganin su tayi agidan su Samuel. Ta ce "Hajiya kekuma zamuyi anann? Hajiya ta ce "Walhi yau za'ayi ta taƙare fito mutafi. Tafaɗa dai-dai tayi fakin a bakin get ɗin ta waje, domin tasan bazata iya shiga gidan ba. *GIDAN SOJA* Umar ne zaune tare da wasu daga cikin abokan Daniyel mutum biyu wanda suka haɗa komai tare a kan sune zasu kawo kuɗin. Umar yayi wata irin shigar da bakowane zai iya ganeshiba, domin kuwa ɗinkin babbar riga yasha ga hula sai sheƙi ya keyi. Ɗaya daga cikin abokan Daniyel ɗinne ya ce "Sorry sir Samuel ba aron kuɗi ya bamuba kuma mu bawai munsan me yayi da ƙuɗin bane, kawai munji labarin abunda ya farune yasa muka haɗa kuɗi domin a sakeshi. Tabbas da kana kusa da Umar da sai kaji yanda cikin sa ke murɗawa, domin kuwa Daddy ya zuba masa ido kamar shine mai yin maganar, kokuma mai son gano wani abu. Daddy babi takan maiyin maganar ba ya nuna gurinda Umar yake ya ce "Wannan fa shima abokin Daniyel ne? Cikin sauri Umar ya ce "A'a Walhi ni bamma sanshiba kawai naga zasu shigone sukace na rakasu, da sauri sauran suka kalli juna domin kuwa ba haka suka shirya cewa ba, ba haka laɗifa da Umar ɗin suka shiryaba. Da sauri Daddy ya kira ɗaya daga cikin sojojin yace ayi waje da Umar. Ai kuwa babu ɓata lokaci sukayi waje dashi suna takashi da wannan ɗan banzan taƙalmin nasu, shikuwa sai ihu yakeyi. Daddy ya dawo da kallonsa izuwa gurin sauran ya ce "kawo kuɗin? Da sauri suka miƙa masa kuɗin a lede kafin ya ce "Elixa ta fito da Sarah da Samuel. Da sauri ta miƙe tayi ɗakin da su Sarah keci ta buɗe ta ce "Kuzo palor Daddy na jiranku. Da sauri Samuel ya meƙe domin kuwa yasan da cewar yau za'a sakeshi. Sarah kuwa kana kallonta sai ka tausaya mata, domin kuwa tashi kuka ta rame sosai, haka itama ta miƙe tana bin uwar Tata da kallon mamaki ganin ko ta kanta batabiba. Nan fa a ka hau kallon kalo tsakanin Samuel abokansa. Daddy ya buɗe baki zaiyi magana kenann sai ga ɗaya daga cikin sojin nasa ya shigo palorn ya sara masa sannan ya ce "Gawani wai sunansa AJ yazo yana nemanka? Ba Daddy ba mommy Samuel da Sarah suka kalli sojan da kyu momy ta ce "Wani Aj? Daddy ya miƙe tsaye ya ce "Shigo dashi. Take sojan ya juya domin cika umarni. Yayinda Samuel ya kalli sara itama ta kalleshi sai ya sakar mata murmushi. Daddy ya kalli abokan Samuel ya ce "Sutashi subar gidannan yanzu kafin yasa ayi fata-fata dasu, danma sunyi Sa'a su ɗin yan addininsu ne. Haka suka fita cikin gudu harda faɗuwa. Daddy ya dawo da kallonsa izuwa gurin Sameul ya ce "Tashi kaje kayi wanka, sannan ya miƙa masa kuɗin aleda wanda a ka kawo, ya ce ya ƙirgasu zuwa anjima ya kawo masa. Ya kalli Sarah cikin tsananin jin haushin ta ya ce "Sarah sorry for you! Kirasa wanda zaki ɗauki kuɗaɗena kubaiwa sai Musulmi! Ya faɗa yana kafeta da ido. Dai-dai Lokacin aka shigo da oga AJ riƙe a hannun sojan. ( *Tofa yau ga aj ga Comandar kuma ga Sarah ga Mommy. Shin me zai faru?)* Kowa miƙewa yayi a palorn harda Samuel domin shima soyake yau saiga waye wannan AJ. Daddy ya kalli Sarah ya nuna Aj ya ce "Shine AJ? Sarah da hawaye suka wanke mata ido ta kalli AJ wanda kana ganin sa kasan yasha kuka. Suna haɗa ido gabansu ya faɗa a tare alokaci ɗaya. Dukda irin halin damuwar da AJ keciki bai hana ya ƙurawa Sarah idoba, yana aiyana kodai rashi lafiya tayi. Tana son tace eh shine AJ amma tana tsoro. Aj kuwa kallon Daddy da mommy yayi na lokaci ɗaya ya ɗauke ido, domin kuwa yasan yau ya shiga hannun manyan arna. SAMUEL kuwa kallon AJ yakeyi cikin mamaki ya ce "Ashema yarone ƙarami, domin kuwa Samuel ɗin ya girmeshi, tawani gurin kuma kallo ɗaya zaka masa kagane shiɗin yana cikin hutu, domin yanayinsa ga kuma farar fatarsa da tasha hutu na kwana biyar a Morocco, haka dai Samuel yaketa bin Aj da kallon tausayi. Bata ankaraba sai ji tayi an zabga mata bari wanda yasa ta rikice ta kurma wani uban ihuu, tana faɗuwa agurin riƙe da kuncinta. Daddy ya ƙara mai-maita tambarsa a karo na biyu. Ai kuwa da sauri ta ce "Shine!. Daddy ya kalli AJ a karona babu adaddi, sai yasa hannu a aljihu ya jiro waya. Kira ɗaya ka ɗaga ya ce "Asaki wannan matan guda biyu sannan kuhaɗa musu da duka. Yana kashewa ya ƙara kiran wani shima ya ce "Ya saki wannan yaron, amma shi kar a haɗa da duka. Yana gamawa ya kalli matarsa cikin ɗacin rai ya ce "Luk at her? Kalli yaronda yake saka yarinyata sata? Wannan yaron, yafaɗa yana yin kan Aj ya shaƙeshi har saida taga ya fara kururuwa kafin ya sakeshi, aikuwa nann take Sarah ta fashe da kuka domin kuwa ta tsorata sosai da shaƙunda aka masa. Daddy ya kamo wuyan rigar AJ ya ce "Meye haɗinka da ƴata? Kai ɗan gidan uban waye a garinnani. Sannan kana musulmi meye haɗinka yarinyata, AJ ya ce "Ina Innah ta da ƙanwata? Yayi maganar cikin sadaƙarwa. Jin haka yasa Daddy kwasheshi ya kalli sojan ya mai a lama da ido, aikuwa ya jashi yabar palorn dashi yayinda Sarah ta kamo ƙafafun Aj tana kuka. Ganin haka yasa Daddy yin bool da ita harsaida ta daki kujerarr palorn aikuwa take goshinta ya fashe amma bata tsaya bi ta kansa taƙara kamo ƙafafun Aj, Daddy ya riƙeta da ƙarfi harsaida aka fita dashi kafin ya juyo da ita ya kwaɗa mata maruka har guda huɗu, ya turata cikin ɗakin da suka fito itada Samuel, sannan ya sa ki ya rufeta. Samuel kuwa na ganin haka ya bar gurin cikin sauri, yana jin tausayi Aj domin yasan yau sai aj ya kwammaci baisan Sarah a rayuwasaba. Itama kanta saran sanin gurinda za'a kai aj ɗin ne yasa ta wannan kukan da riƙe ƙafafunsa. Momy kuwa tayi muwar tsayar agurin tsabar mamaki ganin Aj ɗin ɗan yaro, ita tayi tunani zata ganshi babba ne. Ɓangaren su Innah da Nana kuwa, suna zaune kamar yanda tunda aka sake musu guri suke, Innah na kwance a kan cinyar Nana wanda kana kallon Innah sai gabanka yafaɗi, domin kuwa ta fita a haiyacinta, har wani ƙara tsofewa tayi. Buɗe ƙofar gurin akayi da sauri Nana ta ɗago kai ta kalli ɗan sanda da ke ɗauke da sanda a hannu. Shima kansa ganin irin halinda suke cikine yasa ya kasa dukansu ya shiga lallaɓasu kar wannan tsohuwar ta mutu a hannunsu. "Kutashi ku fit. shine abunda ya ce yana kallon Nana. Haka Nana ta ɗago Innah wacce ko buɗe ido batayi. Ita kanta nanar ba kwari garetaba, sai kawai ta shiga jan innar yayinda ƙadafunta ke jan ƙas. Saida suka fito waje tukun idon Nana ya raina fata domin kuwa ganin gurin da suke. Da kyar ta samu mai keke ya ɗauketa izuwa asibiti. Da sauri likitoci suka amshi Innah, yayinda ta ce da mai mashin ɗin bari ta bitu ya kaita gida ya dawo da ita sai ta bashi kuɗin. Saida taga ɗakin da aka ajiye Inna kafin ta fito izuwa gurin mai keken. Unguwarsu ta faɗa masa ta ce ya kaita. Aƙofar gida ya ajiyeta ita kuwa tana sauƙa ta shige gida domin bataso wanda ya santa ya ganta a yanda take. Gurin da ta ajiye kuɗe taje ta ɗauko dubu ɗaya ta fito ta tsaya daga ciki ta meƙawa mai mashin ɗin, bata ko tsaya ba ta koma ciki da sauri. Tana shiga ɗakinta ta faɗi a ƙasa ta fashe da kuka tana kiran sunan yaya yaya yaya! Wani ɗaci takeji tanajin ta tsani soja da ɗansada domin kuwa tasan basuyi komaiba yayantama tasan baiyi komaiba, tunowa da tayi da Innah sai ta miƙe ta rasa nema zatayi yanzu. Tashi tayi ta ɗibi ruwa aranda ta shiga bayan gida tayi wanka, sosai ta wanke jikinta da har wani wari-wari takeyi, ta fito daga bayan gida ta zaɓi ɗaya daga cikin dogayan rigunann da Aj ya sayo musa ta saka, sannan ta shiga ɗan ƙaramin kicing ɗinsu ta ɗora ruwa domin samar musu abinci.......✍️ *PAGE.* 2️⃣3️⃣ .........Bayan ta kammala komaine ta zauna taci abincin sosai sannan ta shiga neman wayarta ganin lokaci na tafiyane yasa tabar neman wayar ta fito da kuɗin da AJ ya bata gaba ɗaya. Gaba ɗaya tasaka kuɗin ajaka sannan ta shiga ɗakin Innah itama ta ɗaukar mata doguwar riga guda ɗaya da kuma atamba da zani. Saida ta haɗa komai kafin ta tsaya ta ɗan gyara gidan sama-sama. Haka taci gaba dayin komai cikin juriya da jajircewa domin kuwa ita kanta tana buƙatar hutu. Kasan cewar basuda wani ɗan abunda zata zuba gaba ɗaya kayan nasu harda abincin ne yasa ta ɗauki ledar da AJ ya kawo musu kaya aciki tun wancan lokacin, gaba ɗaya ta zuba kayan aciki kafin ta koma ɗakin Innah domin ɗaukar wayar Innah. Dai-dai jikin ƙofar ɗakin Innah taga leda, tinda tashigo taga ledar amma batabi ta kantaba. Ɗauka tayi da sauri tana buɗewa, da sauri ta zuba kayan aƙasa cikin mamaki ta ce "Waye ya kawo! Sai kuma ta gyaɗa kai domin abinda zuciyarta tace mata. Abubuwa ne aciki wanda ke nunida cewar kayan tsaraba ne aciki kala-kala...irinsu lemo ayaba biskit madaran ƙwankwani da dai sauran abubuwa harda kayan shayi. Cikin sauri ta ce "Kode yaya yana garine kokuma ya dawo! Kodai yasan abunda ke faruwa damune amma ya share! Kodai da gaske kuɗin yasata ya gudu yabarmu!?. Ta ce "No Yaya bazai iya ba. Take hawaye ya shiga zubo mata, ta miƙe tabar kayan a haka ta fita daga gidan tana kuka. Farin hijjab ne ajikinta wanda ya rufe mata dukkan jikinta, tana tafiya kamar wacce bata son taka ƙasar. Kowa dake unguwar kallonta yakeyi cikin mamakin ganinta a unguwar, gashi anason yin gulma babu dama, domin kuwa Nana Bama kowane yasanta a unguwarba, ita kuwa batasan sunan kowa a unguwarba saide Kadija da ƴan gidansu. Haka dai takai har bakin titi ta tare me kike izuwa asibitin da Innah take. *SALIS* *POV* Koda ƴan sandan suka sakeshi sai yazo gurinsu ya amshi wayarsa, yana dubawa yaga tarin miss call. Cikin mamaki yakebin numbar Hajiya dake nuni da cewar daga 9j take kiransa. Take ya danna numbar Hajiya Babba yana jin wani farincikin. Dai-dai lokacin da sojan yazo yace dasu Hajiya Babba sushoigo dai-dai wannan lokacin kiran Salis na shigowa wayar Hajiya Babba. Bayan ta ɗaga ya ce "Hajiya yaushe kika dawo? Yayi tambayar cikin farin ciki, domin kuwa harga Allah yana son hajiya ta dawo domin asan abinyi. "Kana ina yanzu? Yaji muryar ta acikin kunnuwansa? "Gani a hanyar gida yanzu zan shigo. Hajiya ta ce "Ban gane ba? Salis da baisan cewar Hajiya taji labarinba ya ce "Yes Hajiya na ɗan je wani gurine amma ganinan yanzu. Yana faɗa ya jashe waya yanufi gida cikin sauri. Ita kuwa Hajiya Babba tayi tunanin ko Salis ɗin yana gudan Daniyel, amma hakan bazai hanata shigaba domin yau tanaso ayi komai a gaban yaransu, kowaji abunda yakesonji. Bayan Hajiya Babba taji ya kashe wayar sai ta kalli laɗifa ta ce "Yau zan ƙarasa baku labarin tsakanin Daddinku da wannan mutumin. Laɗifa ta ce "to Hajiya mu koma gida mn sai muyi labarin agida? Hajiya ta ce "no a gaban sa za'ayi domin kusan asalinsa. Ɗan gajeran message ta turawa Salis kafin suka shiga gidan bayan manya-manyan sojojin sun wangale musu ƙaton get ɗin gidan. Saida yaje ƙofar get ɗin gidan nasu kafin ya ji shigowar message, yana dubawa ya tsaya yaci gaba da karan tawa, afili ya ce "Gidansa kuma! Why? Hajiya. Ya ɗauki a ƙalla awa ɗaya acikin gidan kafin ya shirya yafito cikin shigarsa ta mlm bahaushe. Ɗanyar shadda ce wacce taji aki ga hular kalar kayan, kana kallon Salis sai ka ƙara tsabar yanda shiga tayi dai-dai da surar da Allah ya bashi. Wata motar ya ɗauka yana sauri domin yasan ya makara tundade minty talatin ta bashi. Saida yabi ta police station ɗin da aka kulleshi akan ko wani zai sanar dashi inane a ka kai su Nana, amma kowa na tsoro. Sai kawai yabi ta unguwar su Nana ɗin, yana zuwa yaga gidan a ƙulle, da mamaki ya ce "To kodai shima aj ɗin ya dawone, aikuwa ya shiga kiran numbar Aj amma no amsa, numbar Nana kuma har yanzu bata shiga, haka yanufi gidan da zaije batare da yayiwa kowa magana a'unguwar ba. Dai-dai Hajiya Babba ta saka ƙafarta gidan Comanda Daniyel sai taji wani mugun faɗuwar gaba haɗida jin ƙirjinta nayin wani zafi. Kallon gidan tayi sama da ƙasa kafin ta fara karanto duk addu'ar da tazo bakinta, amma tafi ambaton hazbinalhu wa'ni'imal wakil. Tabbas wannan faɗuwar gaban nata da wani abu da ya shafe ta a cikin gidannan. *GIDAN SOJA* Wanka yayi cikin sauri-sauri , Haka yayi shigarƙananana kaya rigar adides, kallon kansa yayi da kyu yaga yanda ya rame, sai ya ɗauki ledan kuɗin da abokan nasa suka kawo ya fito da kuɗin ya ce "Waoo i love this baby girl so much. Cikin yaran su ya ce "Thanks laɗifa bari komai ya dai-daita zan huta dake kin haɗu sosai, yana kaiwa nann ya bar ɗakin izuwa kicing yana tunanin ƙanwar tasa ko ya zata kaya tsakanin Daddy da kuma aj ɗin. Kallon gidan takeyi ta ko ta ina. Tabbas gidan yafi nasu gyrma amma bai kai nasu haɗuwa ba. Cikin dakiyar fuska suka tura ƙofar palorn itada ɗiyar tata, ai kuwa sukayi ido huɗu da Comandar Daniyel da kuma matarsa wato Elixa. Cikin mama Momy wato Elixa ta miƙe cikin mugun mmk ta ce "Fatima!? Hajiya Babba ta ce "Na'am Elixa!? Comandar ya ce "Fatima!? Dai-dai wannan lokacin Samuel ya nufo gurin, aikuwa sukayi ido huɗdu da laɗifa. Cikin mamaki ya ce "laɗifa! Itama ta kalleshi batare da tace komai ba. Cikin sauri Daddy ya ce "SAMUEL...."kafin yayi mgn Hajiya Babba ta ce "Shima ɗan naka kasheshi zakayi saboda yabi addinin da ba nakaba? Cikin zafin rai mommy ta ce "Fatima karkiyi tunanin ko yanzuma kinfi ƙarfin ƙara ƙarɓar wani hukuncin ne irin na baya. Dai-dai Lokacin Salis ya shigo palorn ɗauke da sallama. Laɗifa ce ta amsa yayinda Elixa ta daja masa wata tsawar da tasa Sarah dake cikin ɗakin da aka mayarta tsorata. "Ƙarka ƙara mana wannan abun a gidan idan ba hakaba Walhi sai kayi ladama. Idon Salis ne ya sauƙa akan wani ƙaton hoto dake cikin palorn wanda iri ɗayane da nacikin palornsu. Baiyi mgn ba dukkda kuwa ya tsaorata da tsawar da mommy tayi. Ɗaukar hoton yayi yana shfa hoton cikin sakin mura. Wata tsohuwa ce manne a jikin hoton wanda duk iri ɗaya ne da na palornsu. Ganin haka yasa itama laɗifa nufar gurin cikin sauri. Daddy ya ce "Kifita kibarmin gida yanzu kokuma nasa ayi miki abinda bakiyi tunaniba kinsan irin matakin da nake ɗauka akan duk wani musulmin daya shiga sabgata? Jin haka Hajiya Babba ta samu guri ta zauna ta ce "Ok tom Ina jiranka? *(Akwai batu a'cikin wannan labarin)* *WASU SHEKARU DA SUKA SHUƊ ABAYA* . Wani ɗan ƙaramin ƙauyene dake cikin local Government ɗin *BOKON* ta cikin Benue st. Ƙauyan mai suna...katunku. kamar yanda kowa ya sani garin garine na tibabe, haka zaluka bakowane kejin wani yareba bayan yaransu na tibi. Akwai ƴan kaɗan da suka samu shiga cikin gari wato *BOKON* kokuma cikin Benue MKD domin samun ilimin zamani. Garin dukkansu ƙabila ɗayane haka zaluka addininsu ɗayane, wato addinin Cirstand. Garin ɗan ƙaramine saide kallo ɗaya zaka musu kasan suna cikin tsanani na rashin wayewa da kuma rashin abubuwan zamani. Zaune suke su huɗu yayinda ɗaya daga cikin take kwance alamar dai batada lafiya, sukuma sauran ukun sun zagayeta suna mgn cikin neman mafita daga ciwon ma haifiyar tasu. Mace ɗaya sai maza biyu wanda kana kallonsu kasan jini ɗaya ne. Cikin kuka macen ta kalli yayun nata guda biyu cikin harshen da shikaɗai ta iya ta ce "Yaya dan Allah koda shagon nakane ka siyar sai mu kaita asibitin cikin gari dan Allah kar mama ta mutu? Wanda a kewa wannan maganar ya sunguyar da kansa ƙasa yana zubar da hawaye cikin tsananin tausayin halinda suke ciki, kafin yayi mgn babban yayan nasu ya ce "Yanzu da mama nada lafiya komai shi zatace, idan anyi magana tace shine mai tausayinta idan kuma anyi laifi saide ta ɗora min koda kuwa shine yayi laifi, Amma yanzu bata da lafiya ance kasiyar da shagonka a kaita asibiti kaƙi. Cikin kuka da takai ci wanda akewa wannan maganar ya ce "Haba Daniyel yakakeso nayi da rayuwata, shagon da kuke ta magana akai menene acikin sa komai ya ƙare, kai kanka lokacin da zakaje zana jarabawarka acikin kuɗin shagonne, sannan kuma tun lokacin da mama take wannan rashin lafiya duk acikin kuɗin shagonne. Yanzu haka babu komai a cikin shagon, komai ya ƙara. Ya faɗa yana kamo hannun mamar tasu yana sake fashewa da kuka. Cikin faɗa yayan nasa ya ce "Ƙarya kakeyi Solomon yanzu da ka siyar da shagon ƙwara mama tamutu!? Cikin sauri Solomon ya ce "Shikenan aje a nemo mai siya, idan ya siya sai mu kaita asibitin. Cikin sauri Daniyel ya fita sai gashi da mai siyan shagon. Aikuwa aka yiwa shagon guɗi naira dubu ashirin da ɗaya, kasan cewar babu komai a'cikin shagon. Haka Daniyel ya karɓi kuɗin, batare da yayi wa ɗan uwan nasa bayanin komaiba, saide yace washe gari zasu tafi cikin garin Bokon domin kaita asibiti. Washe gari tun safe Solomon da ƙanwarsa wato titi suka nemi ɗan uwans Daniyel sama da ƙasa an rasashi, tun safe har yamma babu shi babu alamunsa. Cikin wani sabon tashin hankalin Solomon yake kuka yana kallon mahaifiyar tasu da duk abunda sukeyi tana kallonsu amma babu damar magana. Daniyel da Solomon da titi...yarane ga Ushe wato mahaifinsu, ya daɗe da rasuwa tin lokacin titi tana ƙaramar. Sai mahaifiyarsu suna cemata maman Daniyel. Acikin yaran nasu kuda ɗayane yayi karatu wato Daniyel, domin lokacin ubansu na raye,har yagama Secondary school. Ɗan uwansa kuma yana son karatu amma basuda dama kasan cewar noman doya sukeyi. Haka dai ya dage har ya ɗan buɗe ƙaramin shago agarin wanda shagon yake ƙofar gidansu, kuma a hakan shagon babu kamarsa duk cikin ƙwayan dukda ɗan ƙaramine. Tin da aka kafa wannan shagon Shikenan yayansa wato Daniyel ya ce tofa shine zai ɗauki nauyin karatunsa ga nauyin gida. Haka kuwa a kayi yana noma yana kasuwanci sai Allah ya dafa masa, yake ɗan samun riba dai-dai kwarkwado. Yana son yin karatu amma saboda na yayansa shikuma ya haƙura da nasa. Ana cikin haka shago ya fara jabaya domin kuwa anfi ƙarfin shagon. Ana cikin haka rashin lafiya ya kama mamarsu shine zaije gurin wannan mai magani suje gurin wannan har komai na shigone ya ƙarasa ƙarewa sai kuma ga shi yanzu yayansa yasa an sigar da shagon kuma ya gudu da kuɗin. Kwana ɗaya kwana biyu, babu Daniyel babu alamarsa. Haka Solomon da ƙanwarsa suka cigaba da jinyar mamarsu. Cikin kwana na biyarne, cikin wani dare sai ji sukayi tana musu mgn bayan ta kai wata huɗu batayi magana ba. "Solomon Solomon! Ina kuke ina titi? Haka take ta cewa cikin dare. Da sauri sukazo gareta suna kamo hannuta. Ta ce "Solomon ga ƙanwarka ka kula da ita kuma duk rintsi duk wuya karkubar Addiniku kuzauna acikin ƴan uwanku, sannan shima ɗan uwanka ka sanar dashi akan muhimmancin addinimu Pls dan Allah karku bar addinimu da al'adar mu, kuma kukula da ƙanwarku karka bari ƙiyayar dan uwanka ya shigeka haka yake sai kayi haƙuri dashi. Cikin sauri Solomon ya ce "Mama kin samu lafiya ne? Walhi namiki alƙawarin bazan taɓa barin ADDINIMU ba, namiki alƙawari, itama titi tafaɗa hk. Haka dai Solomon ya ce "Dan Allah Mama ki daina faɗa haka bazakimutu ba muna tare gashi kin warke kin samu lfy. Titi sai murna takeyi tana ganin yanda mamarsu ta samu lfy lokaci ɗaya. Haka sukaci gaba da hira tana basu labari akan muhimmancin addininnasu. Cikin mamaki sukayi barci cikin farinci tati na manne ajikin mamar tasu. Washe gari kamar yanda ya saba da safe yaje gona ya ciro musu doya. Tindaga bakin layin unguwarsu yake jin koke-koke, da sauri yazo ƙofar gidannasu ganin anɗan fara taruwa. Yana shiga yaga titi a gaban mama sai kuka takeyi. Haka shima ya shiga rusar kuka kamar wanda kukan zai dawo musu da ita. Suna cikin wannan hali,wani kawunsu yazo ya ce "Ga mota ankawo wacce zata ɗauki gawar daga nann ƙauyan zuwa cikin gari wato BOKON domin a kaita mutuware kuma kuɗin motar sai an bashi dubu ɗari harda ashirin. ..sannan ga kuɗin wata allura da ake siya domin miƙar da gawar karta sanƙare, ita kuma dubu goma kuma guda biyu akeyi, sannan duk a yau akeso kuma ayanzu.. Sannan idan ankai gawar mutuware duk kwana ɗaya idan gawar tayi dubu ɗaya ne za'a biya, bayan nann kuma idan an karɓo gawar ranar da za'a binneta sai sunyi biki an yanka abubuwa kamar akuyoyi alade da abubuwan shaye-shaye irinsu giya burkutu dadai sauran abubuwan da al'adar su ta tanadar. wannan duk al'adar su ce kokuma na ce Addininsu. Idan wannan gawar takai shekara tofa sai kabiya kuɗin shekara, idan wata ɗaya ne ko biyu kai komai dai nawane. Cikin sauri Solomon ya ɗago kai ya kalli kawun nasa cikin hawaye idanuwansa sunyi jajawur...📝 *Tofa masu karatu kunji wani addinin fa!? Shin yaya Solomon zaiyi? Shin kokunsan waye wannan solomon ɗin?* *PAGE2⃣4⃣* ............Tabbas solomon yasan wannan abubuwan da Uncle ya lissafo duk cikin al'adarsune, tabbas yasan wannan duk al'ada ce ba addininsu bane, amma shi bai taɓa tunanin cewar abun zai zagayo ta kansa ba! Kallon kawun nasu yayi(Uncle) cikin muryar kuka ya ce "Banida kuɗi banida komai bansan ya zanyi ba, yana kuka yana riƙe da hannun titi wacce itama kukan takeyi. (duk wannan maganar cikin yaransu yakeyi wato yaren tibi) Kafin kowa ya sake mgn sai sukaji anshigo gida cikin ihuu! haɗi da ƙara. Suna juyawa sukayi ido biyu da Daniyel wandake rusar kuka ko ganin gabansa bayayi. Da sauri titi ta 'karaso gurinsa ta rike 'kafarsa tana kuka tana cewa "Yaya Daniel mama ta mutu please and please ka ce mata karta tafi ta barni!?. Cikin kuka shima Daniel ya kamota tsam ajikinsa yana rarrashinta,shima Solomon sai kawai ya fad'a jikinsu yana kuku abun tausayi. Suna cikin hk kawun su ya sake cewar "kunsan fa tin cikin dare ta mutu saboda hk dolene ayi wannan alluwar domin karta fara wari agari, kuma kar ta san'kare. Daniye da baisan zancen me a keba ya kalli uncle din nasu ya ce "Kawu meya faru? Tsaf uncle din nasu yasanar masa da duk abunda ake bu'kata kamar yanda ya sanarwa da Solomon. Cikin sayri Daniel ya ce "Uncl a samo mai siyan gonar mu sai kawai a siyar masa kaga ai sai musamu na kaita mutuware? Da sauri Solomon ya d'ago kai ya kalli yayan nasa cikin mmk amma bai ce komai. Tabbas kam indai har ba gonar zasu siyarba to basu da wannan ku'din da zasu iya biya, to amma gonar fa guda biyuce kawai, ɗayama daga ciki ta solo d'in ce da ya siya da kansa tunda sad'ewa. Haka kuwa akayi suka samo wanda zaisiya, akayi cinikin gonar amma solo ya ce banda kayan ciki wato doyarsa, domin kuwa doyar ta nuna harma an fara cira ana ci. Bayan ansiyar ne solo ya samu yayansa ya ce "Yaya ina kuɗin shagon da aka siyar kace zamu kai ma..."kafin ya 'karasa ya ce "Ninasan dama baku damu daniba, wato na ɓata amma kai damuwar ka kud'iko? To 'barayine suka bini abaya, Ina tunanin sunga lokacin da kabani kuɗinne shine suka bini, amma dai basumin komaiba kud'in kawai suka 'kar'ba. Solo ya ce "kayi ha'kuri Allah ya kiyaye gaba. Ya amsa da amin sannan ya ce yanzu zanje na nemo mai motar da zai d'aukemu zuwa cikin gari. Yana fad'a ya bar gurin yayinda solo ya bishi da kallo. Sai wajan ƙarpe sha biyu na rana kafin Daniel ya dawo da wani mai moto har cikin garin nasu. Wanda har gawar ta Bara wari, ƴan gari sun fara surutu, dan gin ubansu kuma babu wanda ya taimaka da komai. Aikuwa solo da Daniel ne kad'ai suka d'auketa domin kuwa harta fara wari kasan cewar ba'a yi wannan allurar ba. Haka dai a ka kaita mutuware, wanda suma da kyar suka yarda suka 'kar'beta akan wai basu kawota da wuriba harta fara wari. Kaman yanda kawunsu ya ce musu duk kwana 'daya dubu 'daya to tabbas hakane. Anan fa hankalin Daniel da solo ya tashi, sukace badamuwa zasu biya. Bayan sun koma gidane, a ranar Daniel ya ce zai tafi gurin aikinsu domin a wannan lokacin har sun fara zuwa zana jarabawar neman aiki. Ya ce "zanje bayan kwana goma zai dawo sannan kuma zai dawo da kud'in da zasu 'kar'bo mamar tasu. Batare da sunce komaiba suka masa fatan dawowa lfy. Kafin ya fitane titi ta ce "yaya kafin mama ta mutu ta bamu sa'ko mu sanar mk? Ya ce "Ina jinku? AI kuwa nan suka kwashe komai suka sanar masa irin wasihar da ta basu. Nan shima ya 'kara musu nashi fa'dan akan addininnasu domin kuwa duk cikinsu yafi su kishin addinin nasu. Yau kwanan Daniel koma sha hud'u da tafiya, amma bakajin ko labarinsa, cikin damuwa da fargaba titi ta kalli solo ta ce "Solo pls yaushe yaya zai dawo? Jin hk yasa kukansa 'kwacewa yana rarrshinta. Wasa-wasa saida Daniel yayi kwana ashirin da 'daya bai dawoba. Ganin hk yasa solo sayarda d'aya gonar yaje ya biya kud'in mutuwaren sannan yazo gida da mamar tasu.anan fa kamar dama jiran beriyan sukeyi, kasancewar dama 'kwayan 'karamine yasa duk wani abu da a keyi a 'kwayan sai kowa yasani. Da 'kyar yayi sa'a ya yanka musu kaji suma guda uku sai kuma kayan shaye-shaye. Aikuwa nan aka fara zage-zage da 'korafe-'korafe. Haka dai ya toshe kunnuwansa daga jin kowani irin zagi daga cikin la'umman garin. Kasan cewar an ɗan sayi gonar da daraja yasa tun kafin yayi komai saida ya ware kuɗin akwatin da ake siya kafin ya ɗan ware wanda za'ayi sauran hididdimun. Cikin yardar Allah akayi beriyar mamarsu batare da ɗan uwansaba. Kamar yanda aladarsu take wajan bikin anayin kwana uku anayi, wasu huɗu wasu biyar kai wasuma har sati guda. Bayan kwana shida da yin beriyar ne solo ya shiga aikin dyarsu sosai shida titi, kasan cewar dama itama ta iya komai na aikin gona, hk suka tone doyar nan sannan ya ce cikin gari zai kaita ya siyar. Haka ya kasance basu da komai a cikin garinnan sai gidansu sai kuma doyar soloda ya gama shiryawa akan zai tafi da ita gari. Misalin ƙarfe tara na dare suna zaune shida titi suna hirar idan solo ya siyar da wannan doye meye zasuyi da kuɗin. Ita dai titi ta ce kawai tindade yanzu basuda gona ga kuma shagon basuma babu kwai su tafi cikin gari da kuɗin sai yayan nata ya fara wani sana'ar itama ta fara. Solo yace "to a ina zamu zauna? Ta ce "Sai mu siyar da gidannan idan munje sai mukama haya. Solo ya ce "idan kuma Yaya ya dawo ya zauna a ina? Titi tayi shiru tana kallon solo. Ya ce "kawai ni zan dinga shiga gari ina yin wata sana'ar kekuma kizauna agida kafin yaya ya dawo. Hk kuwa suka yanke shawarin shine zai dinga shiga gari yana yin kasuwanci. Hk suka cigaba da rayuwar shida ƙanwarsa, yayinda dangin mamansu kowa yayi watsi dasu, shikuwa Daniyel bai sake leƙowa garinba. Haka suka kasance har shekara biyu da daɗi ba daɗi. Haka zaije cikin garin Bokon yayi buga-bugan sa ya dawo ita kuma titi idan tasamu wani aikin koda na nimane sai tayi. Haka dai har jarinsu yayi ƙasa kasan cewar aciki suke komai da komai. Bayan shekara ɗaya. Cikin sauri haɗi da murna titi ke kallon yayan nata da yace mata ”Yasamu jiran shago a cikin gari, saboda haka yanzu itama zata daina noma. Tin daga ranar titi ta daina yin aiki saide itace wanke musu kaya da kuma kula da gida, kokuma idan zasuyi girgi itace zata dafa. Sunyi wata ɗaya da yin haka sai Daniel ya dawo ɗauke da kakin soja ajikinsa, cikin mmk kowa dake garin ke binsa da kallo domin kowa'a karo na farko kenan da wani ɗan cikin garin yayi karatu har ya samu aiki kenan kuma aikin ma na soja. Kai zokuga murna gurin titi da dangin ubansu harda solo. Abunda ya ƙara baiwa mutane mamaki ma shine har star ɗaya ajikin rigar nasa, kasan cewar yayi dogon karatu sosai. Haka dai al'ummar gari suka dinga zuwa kallon sa kai kace wani sabon halittane. Kwanan sa uku a garin yace da su solo da titi zasu bar wannnan ƙwauyan zuwa cikin bokon. Nan fa dangin ubansa sukace su basu yardaba, titi da solo kuwa sai murna sukeyi. Haka sai ya musu alƙawarin zai dinga zuwa yana dubasu idan ya samu hutu daga aikin nasa. Eh tabbas sun samu sauyin rayuwa sosai, domin kuwa yanzu sun daina shan wahala irinta baya. Yayinda titi da solo suka fara zuwa school kasan cewar Daniyel ɗin yanada burin yaga ƴan uwan nasa sunyi karatu. Ɓangare ɗaya kuma solo yana zuwa gurin uban gidansa wanda yake zauna masa a shago, domin kuwa shima mutumin acikin Bokon yake. Lokacin da zasu fara zuwa school ya sanar dashi cewar yanzu sai ƙarfe huɗu zai dinga zuwa, shima mutumin ya ce babu damuwa kuma yana tayashi murnar. Tabbas suna jin daɗin zama da juna tsakanin solo da mai gidansa domin kuwa solo yanada riƙon alƙawari, mutumin ya ɗauke shi da daraja dukda kuwa Addininsu ba ɗaya ba. Ɓan garan Daniyel kuwa bayan ya dawo dasu titi gidan da aka mallaka masane ya zuba musu kayan abinci sosai sannan ya biya musu kuɗin karatun su. Saida ya gama cinye hutun da aka bashi kafin akace zai koma cikin barikin sojoji da zama. Hakanne yasa ya ce dasu titi su zasu zauna ana shi kuma zai koma can. Haka kuwa akayi shine ya koma cikin barikin sojoji dake cikin bokon, sukuma suka zauna awannan gidan. Alhaji Salisu gamji shine uban gidan solo wanda ko titi bata taɓa sanin saba, shikansa solo ɗin tsoran kar yayan nasa yasan cewar uban gidan nasa musulmine ya keyi. Domin kuwa bai mance gargaɗin daya musuba akan karsu sake wata alaƙa ta shiga tsakaninsu da wani wanda ba addininsu ba. Abinda Daniyel baisaniba shine solo ya daɗe da Alhaji Salisu, kuma shi babu ruwansa da cewar wai shi ba musulmi bane tundade yana riƙe masa amana. Shekarar su ɗaya da dawowa wanda tayi dai-dai da ranar da Alhaji Salisu zai aurarr da ƴarsa. Hakanne yasa ya ce da solo yanason yazo gidansa gurin ɗaurin auran. Solo ya ce ya yarda zaizo. Wannan lokacin kuma Daniyel ya sake samun ƙarin girma agurin aiki, hakanne yasa ya dawo gidan nasu da zama, sannan ya tara ƙanyan nasa ya kallesu cikin ido ya ce "Ranar lahadi mai zuwa zaiyi aure sannan matar tasa agidannan zata zauna, kuma yana musu ƙargaɗi akan matarsa, sannan dukkansu ya basu wayoyi sannan ya ƙara tuna musu cewar karsuyi abota kokuma alaƙaga da kowa. Hakanne yayi dai-dai da auran ƴar gidan Alhaji Salisu. Ashe ɗaya daga cikin manya sojojinne ya baiwa Daniyel auran ƴarsa domin ganin juriyarsa dakuna hango kamar a kwai nasara a gaba ta rayuwar Daniyel ɗin. Daniyel Mutum ne mai tsananin kula da addininsa domin kuwa ya yarda da addinin nasa, dukda hk solo ya fisu ɗaukar addinin da serus. Ita kuma titi bata wani damu da addininbama domin kuwa cocima sai ranar Lahadi kawai take zuwa. Zaune suke su uku suna hira irinta yanda zasu ƙaru acikin family ɗin nasu...cikin sauri titi ta ce "yaya wai yaya sunan matar takane? Daniyel ya ce "Compot ne sunanta....sannan bata san raini ko kaɗai kuma bana son naji wani abu daga gareki domin nasan shi solo babu ruwansa...ya ci gaba da cewar yauwa solo inason zamu haɗu da wannan ogan naka saboda inaso kaima ka mayar da shagonka ka zauna da ƙafafunka? Cikin sauri solo ya ɗago kai ya kalli yayan nasa. Ga abun murna amma yazo da abun kuka. Ya ce "no ai kawai ka bani kuɗin sai na haɗa?. Daniyel ya ce "no inaso muyi shawa dashine. Babu yanda solo ya iya, dole ya gaiyato Alhaji Salisu izuwa gidansu kuma batare da ya sanar masa da komaiba. Assalamu alaikum! Alhaji Salisu ya faɗa lokacin da shiga palon gidan su solo. Dukda kuwa yasan suɗin ba musulmai bane. Da sauri titi ta ɗago domin jin abunda baƙon ya ce. Da sauri solo ya rintse ido yana addu'a irin tasu ta coci. Kasan cewar yanzu solo da titi sun zama cikakkun ƴan gari saboda yanzu suna iya jin turanci har su mayar. Tin kafin Alhaji Salisu ya zauna Daniyel ya miƙe tsaye cikin mamaki da ɓacin rai ya nunashi da hannu ya ce "Idan ka sake ka zauna agidannan Walhi sai kayi nadama...✍️ * *PAGE 25* ......Daniyel cikin ɓacin rai yaci gaba da cewa "Nace kafitamin daga gida yanzunnan kafin ranka ya ɓaci!! yana faɗa yana nuna masa hanyar waja. Shi kuwa Alhaji Salisu sai murmushi yakeyi yana ƙoƙarin zama acikin kujerun da ke cikin palorn. Da ƙarfi Daniyel ya sake daka masa wata tsawa wacce tasa dukkansu saida suka tsorata. "I see get aut in my home? Da sauri Alhaji Salisu ya meƙw tsaye cikin tsoro da jin irin tsawar da ya masa ya ce "Da ka tsaya munyi mgn cikinnutsuwa da ka faɗa min laifin me nai maka hk? "I don't like to see duk wani Muslim in my from I don't like you. Sai yanzu ya fahimci abunda yasa yake ta wannan ihun. A ƙalla Alhaji Salisu zai girmi Daniyel sosai amma ya kwantar da muryarsa ganin ya ɗauki lamarin da zafi, tabbas Alhaji Salisu yasa da yawa wasu arnan basa ƙaunar musulmai amma baiyi tunanin harda dangin solo ba domin ganin shi solo ɗin babu ruwansa. Ya ce "Ko zan iya sanin abinda musulmai suka ai katamaka haka da yasa dukkansu kake ɗaukar su ɗaya? Cikin ɓacin rai Daniyel ya kamo solo ya jefashi jikin ahj Salisu ya ce "Walhi idan baibar gidannan ba zan sa a halakashi. Yana faɗa ya bargurin cikin cewa kafin ya fito yabar gidannan. Titi kuwa itama wani kallo tabi Alhaji Salisu dashi irin kallon nan na tsana kafin tabar gurin izuwa ɗakinta. Da sauri solo ya kamu hannun Alhaji Salisu suka bar palon yayinda Alhaji Salisu ke binsa da kallon mamaki. Bayan sunje gidan Alhaji Salisu ɗinne ya ce "Mai gida dan Allah kayi haƙuri da abunda yayana yamaka, Walhi haka yake baya son musulmai ko kaɗan, Ni kaina hk nake, amma zamana da kai yasa na gane ashe duk abunda ake faɗa mann akan ku ba haka bane.domin gaskiya kuna bani mmmk musamman ma kai, saboda hk kayi haƙuri pls? Alhaji Salisu ya ce "Ai yanzu kaine abun tausayi, domin kuwa Allah ne kaɗai yasan idan ka koma gida me zai maka domin naga ransa ya ɓaci sosai, sannan kuma ɓangaran addini nima kaina kana bani mmk domin kuwa ni baka taɓa faɗamin komai game da yayanka ba. Solo ya ce "Eh kayi haƙuri a kwai abunda yasa ban faɗa maka ba. Nan dai alhaji salisu yaci gaba da baiwa daniyel ha ƙuri a kan yayi haƙuri da ɗan uwansa. Kuma ya sanar masa da cewar duk abunda yace yayi to karya masa musu.saida solo ya tashi zai tafi kafin Alhaji Salisu ya ce "Shin ko zan iya sanin dalilin kiran da ɗan uwanka yaymin? Solo bai ɓoye masa komaiba ya sanar dashi akan wai zai bashi jarine shine zai shawarci mai gidana. Alhaji Salisu ya ce "karka damu dama nima na gama shawara da mai ɗakina a kan zan maka free domin kuwa ka cancanta, saboda hk yanzu kaje gidan duk abunda yafaru sai ka sanar min?. Cikin ruɗewa da mmk solo ke kallon uban gidan nasa jin abun dayace. Alhaji salisu ya ce "Addinimu wato Addinan musulunci yana da sauƙi haɗi da tsafta, sannan yanada dokoki haka kuma komai munayinsane cikin hukuncin Allah. Addininmu bai banbance mana kowaba wajan keytatawa, sannan bai sa muna kallon kowa a matsayin mai kuskureba, domin kuwa Allah ne mai shiryawa, mutuƙar mutum ya kyautata mk koda kuwa ba Addiniku ɗaya ba to kaima zaka iya kyautata masa, a koyarwar manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, ya ce koda mutum ya nufeka da sherri to kaikuma ka saka masa da alkairi, duk wani musulmin gaskiya to tabbas ya yarda da wannan. Solo yayi shiru yana jin wani annashuwa na shigarsa, idan ya tuno da kyutar da mai gidan nasa zaimasa, gakuma yanzu wani irin zance da yake masa wanda shi bai fahimci komai ba. Alhaji Salisu ya ce "Karka damu hankali zaka fahimci komai. Cikin bazata Alhaji Salisu yaji solo ya watso masa tambayar da baiyi zatoba. "To ance wai ku musulmai idan mutum ya kashe wani wai shi ɗan aljannane shi yasa ku kashe mutane babu wahala a gurinku, sannan kuma ana faɗa mana cewar addinin musulunci kashe mutane shine aikinsu, sannan ana cemana wai ku ba Allah kuke bautawaba, wai wannan Muhammad (S a w) ɗin kuke bautawa, Ni kaina na yarda da hk amma zamana da kai sai abun yake bani mamaki domin naga halaiyarku ba hk takeba. Amma abunda ya bani mamaki shine bautar Muhammad (S a w) da kukeyi, ko yanzu naji da idan zakayi mgn shi kake cewa ba Allah ba , kuma naga Allah ne kaɗai abun bauta sai kuma wanda shine ya kamata ace kuna kalla wato jesus domin shine maganar Allah. Shin me yasa kuke bautar Muhammad? (S a w), bayan kuma yanzu haka baya raye, kuma shima mutumne kamar kowa, kuma idan an taɓa shi kuke ɗaukar fansa, me yasa tunda shi Allahnkune ba zai dinga kare kuba, kuma mai yasa..."Cikin sauri da mamaki haɗi da murmushi Alhaji Salisu ya katse shi sannan ya kalli solo jin irin fahimtar da wasu addinin sukewa addinin Musulunci. Cikin muryarsa mai ɗauke da sanyin murya irin ta wanda yasaba da ambaton Allah ya ce "Duk wani musulmi da kasani aduniya to Allah yake bautawa, shima kansa Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ɗin ma Allah ya ke bautawa, sannan shine ya koyar damu yanda za'a bautawa Allah ɗin. Sannan kuma shi abunda yasa kaka kamar muna bauta masa kuwa shine...shi wannan Muhammad ɗin da kake gani to duk duniya albarkacin sa mukeci harda shi Annabi Isa Alaihissalam ɗin wato jesus. Saboda Allah da kansa ya ce idan muka zo gareshi da soyayyar annabinsa to tabbas zai karɓemu hannu bibbiyu... Duk wani musulmi da kasani to yana son Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama fiye da kansa, amma duk Allah muke bautawa Bama haɗa shi da kowa wajan bauta domin shiɗin shi kaɗaine, sallah da kaga munayi to Allah muje bautawa, azumi dakaga mukeyi shina ibadane. Solo ya sunkuyar da kansa izuwa ƙasa yana ɗagowa sai ga hawaye suna bin idonsa. Cikin zuciyar Alhaji Salisu ya ce "In sha Allah zuciyar ka irinta masu rabautane da yarda Allah sai Allah yasa ka gane gaskiya yau. Afili kuma ya ce "Solo lafiya kuwa? Cikin kuka ya ce "Walhi mai gida an ɓatar da zuciyoyinmu wajan saka mana ƙiyayar abinda bamuda masaniya akansa, tunda nake ban taɓa zama da wani musulmiba, amma an sakamin ƙiyayar su fiyeda yanda baka tunaniba, ko farkon haɗuwata da kai saida zuciyata ta haneni amma da yake alokacin ina buƙatar taimako sai kawai nace zan ƙwada zamada wanda ba ɗan addininmu ba nagani ko dagaske hk kuke. Alhaji Salisu ya sauke ajiyar zuciya afili ya ce "Allah sarki, dama ai ba'a yankewa mutum hukunci sai ka zauna dashi kasan halinsa. Haka dai Alhaji Salisu ya ci gaba da nunawa solo cewar duk wannan abunda ake faɗa musu akan musulunci to duk ƙaryane, sannan ya ce masa musulmai basa kashe mutane haka kawai saide idan sunci mutuncin addinisu kokuma Allah da annabinsa, to idan hk ta faru to tabbas addinin musulunci ya tanadar da lada mai tarin yawa ga wanda suka kashe wannan mutumin koda kuwa shiɗin waye. Saida yaga jikin solo yayi sanyi sosai kafin ya barshi ya tafi. Bayan ya fitane allhji Salisu ya ɗaga hannu sama ya ce "ya Allah kasa wannan bawan naka yanada rabon musulumta acikin kwanannan, kuma kasa yayansa karya iya hanashi, shima yayan nasa idan yanada rabon musulumta kasa shi a cikin rahamar musulumci. Koda solo yaje gida sai titi tahau shi da surutu da ihu a kan mai ya haɗashi da wannan mutumin. Baiko kulataba ya shiga ɗakinsa yana jin kansa na juyawa, kwanciya yayi yana kallon sama yana tunano abubuwan da mai gidansa ya faɗa masa akan addinisu. Tabbas ya yarda da wannan mutumin sannan shi kansa shedani ogansa baida damuwa baida abokin faɗa, yana cikin hk titi ta shigo ɗakin cikin sauri tana cewa "Solomon kamanta abinda Momy tace mana a kan yin alaƙa da wasu wanda ba addinimu ɗayabako? Cikin sauri solo ya miƙe zaune yana tunowa da nasihar mamarsu, hk titi ta cigaba da tuno masa da abubuwa da yawa. Da sauri solo ya ce "Pls titi is ok! Ya faɗa cikin ihu da yasa titi nutsuwa. Ya ce "ina yaya Daniyel? Cikin rawar muryar tace ya fita. Shima fita yayi yana cigaba da nazarin komai. Yau ranar juma'a ranar da Alhaji Salisu yake aurar da ƴarsa, wanda kowa ke cewa tayi yarinya ganin a lokacin shekararta batafi sha huɗu zuwa sha biyarba, shi kuwa shi yasan dalilin aurar da ita ɗin. A ranar kuma bayan al'umma sun sheda aurarrne kuma solo yazo gurin mai gidan nasa da himmar shiga addinin Musulunci. Alhaji Salisu yayi mmk domin kuwa tun ranar da sukayi mgn bai ƙara ganin saba yau kwana biyar kenan. Cikin mmk yace "Solo kayi shawara da ɗan uwankane? "Idan mutum zai shiga sai yayi shawara da wanine dama? Alhaji Salisu ya ce "a'a ai ka mallaki hankalin kanka. Babban malamin da ya ɗaura auran shene ya baiwa solo kalmar shahada kuma ya ƙarɓa. Ya ce "Ashi'hadu allailahaillallha wa'ashi'hadu anna buhammadur Rasulullah. Shima Solo ya mai-maita sannan mlm ya fassaramasa cikin turanci wato... (ka sheda babu anin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan sane kuma bawansane) solo ya ce eh na sheda. Take kuwa gurin kowa ya ɗau ƙabbara cikin farin cikin cewar yau addinin Musulunci ya samu ƙaruwa. Nann aka tambayeshi wani suna ya keso? Babu wata-wata ya ce "Muhammad! Nan fa al'umma suka ƙara yin kabbara. Bayan an gama komaine anyi wankan shiga musulunci da dai sauran abun da shari'a ta hukunta, saikuma aka fara sanar masa da komai na cikin Addinin. Alhaji Salisu ya ce "Shi indai wannanne zai koya masa komai cikin ƙanƙanin lokaci cikin yardar Allah. Masu masa kyuta nayi masu masa addu'a nayi, haka dai ranar solo wato Muhammad da Alhaji Salisu da iyalan gidan Alhaji Salisu suka kasance cikin farinci da walwala jin cewar ta sanadiyarsu Addinimu ya samu ƙaruwa. Wanda shikuwa Daniyel ranar Lahadi mai zuwane auransa, kuma baisan bidirin da akeyiba itama titi bata saniba. Haka dai Alhaji Salisu ya dinga sanarwa da Muhammad komai nacikin musulunci haɗida koya masa karatun alƙur'ani mai girma, da kuma yanda zaiyi salla da lokutanta da sauran abubuwan da ya kamata ace yayi kafin sallah, irin su Tsarki alaula. Sannan ya sanar masa abubuwan da addinin musulunci yayi gani dasu irinsu....shan giya cin, mushe, zina, cha-cha, zuwa gidan rawa, da dai sauransu. Tabbas Addinin Musulunci addinin gaskiyane, sannan addinine wanda idan ka reƙeshi kuma kayi aiki da hukuncin dake cikinsa to tabbas zaka zauna cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Tabbas Muhammad shine ya faɗi haka lokacin da ya kawo ƙarin karatun da Alhaji Salisu ya masa jiya, kuma dai-dai babu ɓata, saide rashin daidaituwar harshi wanda sai a hankali harshensa zaisaba. Yau kwana biyu da musuluntar solo Muhammad, wanda yayi dai-dai da ranar bikin daniye da amaryarsa. Anyi aure lfy kuma an tashi lfy bayan anyi duk wani abu da za'ayi. Har zuwa wannan lokacin Daniyel baiyiwa solo maganar uban gidansaba kuma bai ƙara masa maganar buɗe masa shagonba. *Bayan wata uku* Eh tabbas titi da Anty wato matar daniye harma da Daniyel ɗin sunga sauyin rayuwar solo amma basu kawo komai ba, idan zasuje coci sai yace bashi da lfy kokuma ya bar gidan cikin wayo. Izuwa yanzu kuwa Muhammad ya fara nisa sosai wajan karatun addini, sannan yana cigaba da zuwa shagon nasu. Sannan kuma ƴar gidan Alhaji Salisu ansaketa har ta sake yin wani auran, amma babu wanda yasan dalilin sakin nata. Saide wani abu dake faruwa tsakanin sa da matar yayan nasa wanda abun ya fara bashi tsoro. Da sauri Muhammad ya fito daga ɗakinsa zai fita izuwa masallacin dake kusada shagonsu domin kuwa baya son rasa jam'i, tin acikin ɗakinsa yayi alaula ya nufo waje. Yazo zai fita yaci karo da titi zaune itada saurarinta wanda dama ya daɗe yana zuwa gurinta. Saida ya kai bakin get sai kuma ya dawo da baya domin ya makara ƙwara kawai yayi a gida cikin ɗakinsa. Saida ya shiga yayi raka'a biyu yana zaman tashiya saiga Anty tazo kiransa domin kuwa Daniyel ne zaune palorn cikin ɓacin rai domin yau ya keso ya raba solo da wannan uban gidan nasa karyaje ya cutar masa da ɗan'uwa. Kuma yayi alwasin idan ya sake ganinsa dashi Walhi sai ransa yayi mugun ɓaci, sannan zasuyi maganar auran titi da wannan saurayin da yake zuwa gurinta. Kasan cewar titi na waje gurin saurayin batane yasa Daniyel tura Anty ta kira masa solo ɗin. Ai kuwa dama basa jituwa domin ita Anty tana son sai sun aikata alfasha tsakanin ta dashi amma shi yaƙi bata goyan baya, a cewarsa lokacin da yake da baiyiba saida ya karɓi musulumci. Tasha binsa ɗakinsa cikin dare amma cikin addu'ar da Alhaji Salisu ya koyar dashi wajan tsare kansa daga sharrin mutum da aljan yasa bata taɓa samun nasaraba. Yanzuma dukda kuwa da ranar aallh ne amma tana fatan ko ɗan wani abu yamata. Babu ko noking ta tura ƙofar ɗakin tashiga aikuwa tsayawa tayi chak tana kallonsa daidai ya ɗago daga zaman tashiya, ya ce Allahu Akbar!!! Cikin mmk firgici haɗida faɗuwar gaba ta buɗe baki zatayi ihuuu domin harga Allah ta tsorata. Amma sai wata zuciyar ta raya mata cewar ai wannan babbar damace kika samu, domin ta gane solo musumta yayi, to bari tayi amfani da wannan damar tinda ance idan suna Sallah ai basa mgn ko cewa komai. Dukda har yanzu a tsorace take Amma ta dage ta shiga cire kayan jikinta, saida tayi tsirara aihuwar uwarta kafin ta nufi gabansa kan daddumarsa shikuma dai-dai zai kai sunjada aikuwa sai gata agabansa.....✍️ [10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA....* ✍️ *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE* 2️⃣6️⃣ ............Yana ɗagowa daga ruku'u ita kuma tana ƙarasawa gabansa, kafin ya kai ga yin sunjjada har ta zo gabansa. Hannu ɗaya yasa ya tureta sannan ya kai sunjadar. Kallonsa takeyi ta na so su haɗa ido amma ko kallon gurin da take baya yi, da sauri ta kamo hannusa ta ɗora a kan ƙirjin ta dai-dai ya ɗago. Kafin hannunsa ya kai ya sake fisge hannusa. Ai kuwa ganin haka ya sa ta rungumeshi ta baya ta na cewa "Pls Solo for only today i realy love yo"...kafin ta ƙarasa taji an banko ƙofar ɗakin an shigo, dai-dai shi kuma Solo ya ƙwace jikinsa ya kai raka'ar ƙarshe. Kallon ƙofar ɗakin ta yi cikin tsoro da firgici, ido biyu sukayi da Titi wacce ta ƙame agurin tsabar ruɗewa domin ita bata ma kula da abun da Solo keyi ba, ita dai ganin Anty da tayi tsirarane ya firgitata. Kafin Anty tayi magana Titi ta kurma wani uban ihuun da yasa Daniyel shigowa cikin ɗakin. Da sauri ya ture Titi ya tura idonsa cikin ɗakin dai-dai lokacin Solo ya sallame sallar tasa. Idonsa bai fara sauƙa a ko'ina ba sai kan Solo da ke zaune a kan wa ta sabuwar dadduma ga wani farin carbi a gabansa, sannan kuma ga shigar farar jallabiya haɗi da ɗan ƙaramin hularta. Kafin yayi magana idonsa ya ƙara sauƙa a kan matarsa dake kakkare jikinta cikin tsoro da fargaba. Da sauri yayi kan Solo ya fara dukan sa yana cewa "Solomon What aryu doying!? Itama Titi sai kuka takeyi tana tsarlle da ihu! Yayinda Anty ta fara magana cikin kuka. Tabbas doka ne *(DOKA)* ga duk sojan da ya daki matarsa amma jin magar da Anty takeyi ne yasa ran Daniyel ƙara tashi domin a yanayin magar ta na nuna cewar solo ne ya nemeta. Shi kuwa zuciyarsa ce ta raya masa cewar ai sun aikata. Ai kuwa a take allurar tasu ta sojojin ta motsa kafin kace me ya kamo Anty cikin fitar haiyaci ya fara dukun ta ita da Solo wanda shi tun-tuni ya suma domin kuwa ya daku. Tabbas Daniyel ya manta da cewar baban antyfa sojane kuma ogansane a gurin aiki domin kuwa ya fishi matsayi. Saida ya tabbatar da cewa dukkansu sun jigata kafin ya barsu ya kamo hannun Titi suka bar ɗakin. Waya ya ɗauka ya kira abokinsa daga cikin susoji akan suzo gidansa. Bayan sunzone ya sa aka tafi da Solo wanda ko farfaɗowa baiyiba, bayan ya sanar musu cewar ya kamashi da matarsa ne. Ita kuma Anty ma haifinta ya kira ya sanar masa da komai akan ya kamata da ƙaninsa kuma zuciya tasa ya dakeso. Kwana biyar da abun solo ya farka kasan cewar an kaishi asibiti. Ita kuwa Anty dama babanta ba a Benue yake aikiba, jin haka yasa akazo aka tafi da ita, domin kuwa yasan halin ƴartasa, hakanne ma yasa bai bari kowa yaji zancen ba. Cikin kwana na shida Daniyel yazo asibitin ya sa aka bashi Solo ɗin. Bayan sunzo gidane ya kama wuyan rigarsa cikin ɓacin rai ya ce "Solo karka cemin wannan mutumin ne yasa ka kwanta da matata? Kar ka ce shine yasa ka koma yin Sallha? Ya faɗi maganar cikin ihuuu!!! Wanda yasa solo fashewa da kuka ya kasa Magana. Daniyel ya girgizashi ya ci gaba da cewar "Kamanta wasiyar mama kafin ta mutu! Shin ka manta da cewar suna kashe mutane! Shin kamanta da cewar sune suka kashe Daddy? Ka faɗamin da gaske ka koma Addininsu? Cikin kuka solo ya ɗaga kai alamar eh. Lokaci ɗaya Daniyel ya dinga sakin hannunsa daga wuyansa yana ja baya a hankali. Saida yayi nisa kafin ya ce "Solo ka haɗa kayanka ka bar min gida idan ba hakaba Walhi saina kashena!! Ya faɗa yana nuna masa hanyar waje. Solo ya buɗe baki zaiyi magana ya sake cewa "Get aut!! Da ƙer Solo ya ce "Pld Daniyel ka tsaya ka sauraren"..."Cikin sauri Daniyel ya fito waje riƙe da wuƙa a hannu ya nufo gurin da yake cikin rifewar ido. Ai kuwa solo yayi waje da gudu babu ko taƙalmi. Titi kuwa mai zatayi banda kuka domin tafi son Solo fiye da Daniyel, amma itama jin cewar ya koma wani addininne yasa taji ya fita mata a rai. Waje ya fita yana kuka yana kiran sunan tati da Daniyel, yanaso su saurareshi amma sunƙi bashi dama. Rabonsa da zuwa shago harya manta, hakanne yasa ya tashi ya nufi shagon nasu. Tsaf ya tsarawa ogansa komai bai ɓoye masaba. Alhaji Salisu bashi haƙuri kuma yace masa in sha Allah zai tayashi domin shawo kan yayan nasa, kar ya damu yanzu yana cikin fushine. Shi dai Solo kawai yana jin sane. A nanne Alhaji Salisu ya sake sanarwa da Solo (Muhammad) cewar an sake sakin Aisha (Ƴar gidan Alhaji Salisu) cikin mmk Solo ya ce "Wai shi sakinnan babu wa hala ne? Alhaji Salisu ya ce "Ai ba daga mazan bane daga itane. Muhammad ya ce "To me take musu? "Babu komai Allah ya kawo mata dai-dai da ita. Muhammad bai ƙara cewa komaiba sai Amin. Bayan wasu lokuta. Alhaji Salisu da Muhammad sunje gidan Daniyel har sau uku, amma ya musu korarr kare azu na ukunma saida ya daki Muhammad, ganin hakane yasa Alhaji Salisu yace ya sake rabuwa dashi harna tsahun wani lokaci. Ɓangaren Daniyel kuwa ya cire solo daga cikin danginsa, sannan ya ƙara yin wani auran ya samu wata ƴar gidan pasto ya sura mai suna Elixa. Titi ma tayi aure da wannan saurayin nata, kuma duk auran basu gaiyaci Muhammad ba amma saida yaje. A auran titi saida yasan yanda yayi suka haɗu da ita amma cikin mamaki ta zazzage shi tace ita bata sansaba, kuma yasan duk Daniyel ne zai zugata, yayi kuka ranar har ya godewa Allah. A kwai ranar da daniye ya je har ƙauyansu ya ɗauko kawunsu shina yaci mutuncin Muhammad, sannan yace babu su babu shi sun barwa masu yin Sallah shi. Ana cikin haka Daniyel ya tattara shida matarsa wacce yanzu itace take sake shiga tsakaninsa da ɗan uwanasa, domin idan Muhammad yazo gidan lokacin da Daniyel baya nan sai ta cimasa mutunci sosai. Suka tattara suka bar cikin garin Bokon suka koma cikin Benue MKD (Makurdi) sannan ga kuma ƙarin girma da Daniyel ɗin ya samu daga gurin aikin nasu. Yayinda Daniyel har yanzu abunda solo da matarsa wato Anty sukayi yake tsaya masa a rai. Bayan susu lokuta Alhaji Salisu da Muhammad aminci ya ƙara ƙarfi sosai, yayinda yanzu haka Alhaji Salisu ya aurawa Muhammad ƴarsa wato Aisha. Cikin yardar Allah komai ke tafiya dai-dai da yanda Allah ya tsara musu. Lokacin da dangin matar Alhaji Salisu sukaji cewar zaibaiwa tubabbbe auran Aisha saida kowa ya ce bai yarda ba, amma abinda Alhaji Salisu ya faɗa musu gameda ƴar tasa ne yasa kowa yaja baki yayi tsit. Bayan ɗaura auran saida Alhaji Salisu da Aisha da Muhammad suka tattara sukaje Beby mkd domin nunawa Daniyel matar ɗan uwan nasa, amma ya ƙara cimusu mutunci harda tsarabar duka domin wannan lokacin ana bashi masu gadinsa domin ya ƙara samun girma sosai. Alokacin ne Elixa ta kama gashin kan Aisha ta na ja domin cin mutuncin, haka dai suka korosu korarr kare korarr wulaƙanci. Hatta gidan Titi itama ta nuna cewa ta manta dashi. Ananne ma yake samun labarin Titi ta aihu ta samu ɗa Namiji. Muhammad yayi kuka Sosai domin kuwa yanzu hk ya yi sauƙar Alqur'ani maigirma, kuma yasan littatafan addini da dama, yasan cewa addinin musulunci bai yarda da ƙin zuminci ba, koda kuwa ƴan uwan naka ba addininku ɗayaba, sannan bai yarda cin mutuncin kowa ba, sannan baice kaima kabari aci na ka mutuncin ba. Hakanne yasa bai watsar da ƴan uwan nasa, dukda suɗin basa ƙaunarsa. Izuwa yanzu Muhammad aizikin sa sai ƙaruwa yakeyi, domin kuwa yanzu komai na Alhaji Salisu yana hannun sa, ya mallaki abubuwa da dama hakan ne yasa yaje ƙauyansu wato Katungu. Yayi alheri sosai, dukda kuwa suce basa ƙaunarsa amma hakan baisa sun ƙi karɓaba. Ga kuma ya samu mata mai sonsa da gaskiya wacce itama ta ke taya shi a kan shirya wa da ƴan u'wansa. Daniyel da matarsa Elixa sunce idan Muhammad ya sake zuwar masa gida Walhi sai sun kasheshi. Domin sunji haushin abunda yamusu. Lokacin da suke cemasa Solomon sai ya ce "Yanzu na bar Solomon na koma Muhammad"...."Ai tin kafin ya ƙara sa shine suka fara zagin sa da cin mutuncin sa, sannan sukayi wannan ikirarin. Kwanansu biyar da dawowa, suka tattara sukaje ƙasa mai tsarki domin bautar Allah. Yayinda Muhammad bai manta da ƴan uwansa ba wajan addu'a, sannan bai manta da Alhaji Salisu ba wajan masa addu'a domin kuwa ya masa komai a rayuwa. Bayan sun dawo gida 9j ne Muhammad da Aisha suka koma Katungu wato ƙauyansu, yayinda suma Alhaji Salisu da matarsa suka ji ƙauyansu cikin garin kano domin dama Asalinsa ɗan canne shida matarsa. A hanyarsu ta tafiya ne suka kunna wa'azin malam shek Kabiru kabuga wanda yayi akan ruƙon abana da muhimmancin har. Aisha ta ce "Walhi ina son wa'azin bawan Allannan "Nima ina sonsa sosai kuma in sha Allah idan kika aihu shene zai zo garinnan domin shan wa'azi. Itama ta ce "Wooo ai kuwa da ka burgeni sosai! Suna cikin hakane wayar Muhammad ta ɗau ƙara, yana dubawa yaga numbar Daddy wato Alhaji Salisu. Da murmushi ya ɗauka yana cewa Aisha "Kinga su Daddy sun riƙamu ƙarasawa"..."kaine Muhammad? Yan wata murya ta fito daga cikin wayar wacce bata Daddy ba ce. "E, h,h,hhe ni ne. Ya faɗa cikin rawar murya. "To ga mota ta yi hatsari mutum biyu ne aciki kuma da alamar rai yayi halinsa sabo da haka yanzu kuzo"..." Ya isa ya faɗa yana tambayar sa a ina sukayi hatsarin? Aisha dake kusa dashi sai tambayarsa takeyi lfy kuwa? Take ya sanar mata komai, aikuwa ta rafka wani uban ihuu kafin ta sume agurin ko mosti bata yi. Kamar da wasa haka Alhaji Salisu da matarsa rai ya yi halinsa, mutuwar da ta gir-giza Muhammad da Aisha kenan. Sai da a ka'sha fama kafin Aisha ta farka. Tayi kuka har saida ta fita a haiyacinta. Tin daga lokacin komai ya dawo hannunta, dama kuma su ba ƴan Benue bane, sannan kuma ita kaɗai ce a gurin babanta. Haka har komai ya huce suka ci gaba da zamansu a gidan da suke ciki. Cikin tsokana da agon na ta ya saba mata ne ya ke ce ma ta "Hajiya Babba, domin kuwa yanzu ta zama Hajiya Babba, saboda dukiyar da ta mallaka, itama dai da ba ta son sunan har ta fara ƙaunar sunan sosai. She karar Alhaji Salisu biyu da rasuwa ne Aishe ta haifi ɗanta na miji, wanda yaci sunan ma haifinta wato Salisu. Daga nan ne Muhammed ya ce su tattara su koma cikin mkd. Ai kuwa haka a kayi suka tattara suka koma gidan su da suka siya a cikin gari. Bayan suna da kwana huɗu, suka shirya domin komawa gidan Daniyel gaisuwa wanda shima yanzu haka ya sake samun wani girmar. A wannan zuwanne fa basu samu Daniyel ba sai matarsa Elixa. Aikuwa take ta hau Aisha da duka har saida ta kasa tashi dukda cikin da ke jikin Elixa ɗin. Shi kuma Muhammad ya na tsoran karya taɓa ta a samu wata matsalar. Amma ganin ta na neman kashe ma sa mata ya sa ya fusgota ai kuwa ta faɗi a kan kujerar dake cikin ɗakin, take jini ya hau zuba, ganin haka ya sa ya ɗauki matarsa sai gida. Washe gari da sassafe ko karyawa basuyi domin kuwa jikin Aisha da baya mata daɗi, dukda sunje asibiti jiya, kuma a jiyan ta farka shine aka sallamesu. Bata liyan sojojine mota har huɗu suka shigo unguwar tasu, ai kuwa babu wata-wata suka kama Muhammad suka tafi dashi. Sai da yayi wata huɗu babu wanda ya san inda yake kafin suka sako shi, shi ka ɗai yasan abin ya ga ni a gurin da suka kai shi. Bayan shekaru da dama lokacin Muhammad ya ƙara samun aihuwa ita kuma ya saka sunan maman Aisha amma suna ce ma ta Laɗifa. Yayinda ita kuma Elixa saida tayi she ƙara shida da aihuwa kafin ta ƙara samun cikin ƴa mace. Yanzu dai itama yaranta biyu Samuel da mai sunan mamar su wato Sarah. Ita kuwa Titi yaranta huɗu uku maza ɗaya mace, amma duk sun koma ga Allah sai ɗan au'tanta shene Usha, wanda shine sa'an Samuel. Har wannan lokacin Muhammad bai dai na neman ya fiyar ɗan uwansa ba, yayin da shi kuma ya yan ke sha warar kashe shi. Kafin wannan lokacin ma ansha rikici sosai da Aisha da Elixa, yayinda kowa yasan yaran kowa amma ba bu wanda ya taɓa faɗa wa yaransa dan gan takar dake tsakanin su. Sunyi iyaka da juna a kan kowa yaje yayi addinin sa, kuma kowa ya ce ya yarda. Ganin yanda Muhammad ya kwaso wasu daga cikin ƴan uwansu na ƙauyan Katungu ne sai musuluntar da su ya keyi ne, shine ran Daniyel ya ɓaci ya ce sai ya kashe shi, domin kuwa a ƙalla mutane sama da goma duk sun musulumta kuma a hakan ma suna ƙara musulunci. *RANAR WATA JUMA'A* Tafe yake shida yaronsa Salis a cikin motarsa yayinda karatun Shek Kabir kabuga ke tashi a cikin motar, kallon yaransa yayi ya na tuna ranar sunan sa saida Shek Kabir kabuga yazo garinnan, murmushi yayi ya na ƙara godewa Allah da ya sa ya gane gaskiya, kuma ya na ƙara roƙon Allah a kan ƴan uwansa. Misalin ƙarfe huɗu na yamma bayan ya taso daga masallacin da yakeyin sallar juma'a, ya na cikin tafiya yaga an sha gaban sa, kafin ya ce wani abu har sun shaƙa masa wani abu sun ɗauke shi da ga cikin motar sun kunna ma motar huta, sannan sun ɗauki wayar sa sun yar da ita a gurin sun tafi dashi. Koda mutane suka zo gurin wutar taƙi mutuwa dole saida ta cinye kafin a ka shiga leƙawa. Bayan an ga wayar sa a gurin ne a ka ga numbar Hajiya Babba sai kira ta ke, sai kawai aka sanar da ita cewar mijinta yayi hatsari motar ta ƙone. Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana kenann. Aisha tayi kuka tayi kuka sosai har sai da ta kwanta jinya. Nan fa Elixa da Titi da Daniyel suka zo har gidan ta a kan wai sai ta fito musu da ɗan uwa, dama ai an ce musulmai ka she mutane sukeyi. Abu fa kamar wasa har saida a kaje kotu, Aisha ta yi kukan rashin kowa na ta, ga ar ziƙi amma sun tashi a babu, domin saida ta ƙarɓi hukunci mai tsanani wanda saida tayi she kara tana jin yar kanta, bayan ta fitone kuma ta ɗauke ƙafa da su, domin taji zafin abinda suka mata. Ɓangare ɗaya kuma bata yarda cewar mijinta ya mutu ba, domin bataga gawar sa ba, kuma jikin ta na bata yana raye amma bata da hujja, amma dai ta ce idan ma ya mutu to ƴan uwansa ne suka kashe shi, tin ta na jiran tsammani har she karu suka jaa, sannan bata taɓa sanarwa da yaran ta komai ba saida wani abu ya haɗe ta da shi Daniyel ɗin, to fa a nan ne suka fara gano wani abun......📝 *Shin wai Muhammad ya mutu kuwa?... Lailai a kwai ƙura a cigaban labarinnan* 😀 *Comments And shering* *S REZA ✍️* [10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE* 2️⃣7️⃣ ......Haka ta ci gaba da rayuwar ta daga ita sai yaranta, kuma ta na ci gaba da jan ragamar kasuwancin ta har yaranta suka girma, ba ta sake shiga lamarin ɗangin mijin ta ba, sai she karar da ya samu ƙarin girma na matsin Comandar. Ajiyar zuciya ta yi tana kallon ko wa dake cikin palorn san'nan ta ɗora da ce wa "Yau dai yaran ka da na wa ko wa yaji dan gan takar dake tsakanin ka da ɗan uwanka da kasa a ka kashe, kuma yanzu so na ke ka sanar min abun da ya sa ka kulle min yaro? Matsiyacin banza wanda ba zai gama da duniya lafiya ba. Samuel da Salis da Laɗifa harda Sarah da ke cikin ɗaki a ƙulle duk sunji labarin da Hajiya Babba ke bayar wa kaman a ta tsuniya. Elixa ce cikin masifa da jin haushin labarin da ta bayar a gab yaransu ta ce "Wallahi ƙarya kakeyi Aisha baki isa ki kashe mana ɗan u'wa kuma kizo ki dawo mana da zance baya ba, kuma ki fita kibar mana gida kafin ki ƙara ƙarɓar wani hukuncin da ya fi na baya. Ta ƙarasa ta na nu na mata hanyar wa je. cikin ihu!. Comandar Daniyel ku wa mutuwar tsaye ya yi tsabar mamaki da tsananin ƙiyayar da ke wa duk wani wanda ba addininsu ba, harma ya rasa me zaice. Kafin kowa ya yi magana Samuel ya ce "Daddy dama kana da ɗan u'wa namiji shine baka taɓa sanar damu ba? Cikin abunda ya gama cin ransa ya ce "Kar ka ƙara haɗani da duk wanda ya koma yin Sallah, ba ɗan u'wana ba ne, kuma walhi idan ka ƙara min maganar sa sai na sa an koya maka hankali. Cikin tsananin mamaki Samuel ya ce "Daddy wa ye a'cikin ɗakin tsaro? Ko dai shine? Kuma yan zu ma naga ka sa a kai wannnan yaron da a ka kawo yanzu? PLs Daddy dan Allah idan shine kayi haƙuri ina tausaya masa walhi tun lokacin da na ganshi kullum sai na je na ganshi pl"...Ai kafin ya ƙarasa ya ji an ɗauke shi da mari, an ƙara ma sa, Momy ma ta haɗa ma sa da na ta. Kafin ka ce wani abu har sun fara dukan Samuel ta ko ta ina, har saida ya faɗi a ƙ a sa. Sarah da ke cikin ɗakin da a ka kulleta kuwa itama ta shiga tunanin wannan mutumin da Samuel ke maga a kai, tabbas itama tin ba yanzu ba ta na jin mutumin kamar ta san sa, domin kuwa ga kamar sa da maman Usha shk, saide shi yanayin yanda ya koma kamar ma haukaci ne ya sa baza ka taɓa gane komai a kansa ba, kuma gashi taga AJ ma can a ka kaishi, a take ta saki wani ihuu wanda yakaraɗe gidan gaba ɗaya duk girma sa, ta ke ta faɗi a gurin a sume. Hajiya Babba da Salis da Laɗifa sai kallon ikon Allah sukeyi, yayinda gaban Hajiya Babba sai faɗuwa ya ke yi tun da ta shigo gidan. Jin abunda Sameul ke faɗa ne yasa dukkansu kallon junansu, yayin da Laɗifa tayi gurin da a ke dukan Samuel ta na bada haƙuri. Ai sai ji kayi tass itama Momy ta ɗauke ta da wani gigicacan mari wanda ya yi dai-dai da sakin ihunn Sarah. Da sauri Hajiya Babba tayi gurin Laɗifa ita ku ma Elixa (Momy) ta yi ɗakin da Sarha ke ciki, shima Daddy ya bi bayan Momy ya yin da shiku wa Samuel ya tashi da sauri ya nufi ɗakin da a ka kulle Aj. Ganin haka yasa Salis bin bayansa cikin sauri. *NANA POV* Har cikin ɗakin da a ka kwantar da Innah ta shiga, ta samu an ɗora mata ruwa sai barci ta ke yi, kallon fuskar ta ta yi taga duk tayi baƙi ga shi kayan jikinta duk sunyi baƙi, ta fita a haiyacinta sannan ga fuskarta da ɗan kumburi, sauke kayan abincin da tazo da su ta yi sannan ta samu guri ta zauna ta na tunanin yayan ta, sai kuma ta fara tunanin kayan da ta gani a ƙofar ɗakin Innah, wa ta zuciyar ta na sanar mata da cewar ko dai AJ ya dawo ne! Haka dai ta zauna ita ɗaya tana tunanin rayuwa, sai yanzu ma ta tuno da Salis. A zuciyarta ta ce "Allah sarki ko yanzu ya na ina o hoo!. Haka dai har washe gari inha bata farka ba. Washe garine likitan ya sanar mata da cewar Innah ta na buƙatar jini. Cikin tashin hankali Nana ta ce "Pls likita a ɗiba na wa idan zaiyi? "No kema kanki kina buƙar jinin amma ki biyoni zansan abun yi, yana faɗa ya na binta da kalllo. "Me nene sunan ki? Likitan ya tambayeta bayan sun shiga office ɗin sa. "Nana. "Wannan mamar ki ce? "A'a kaka ta ce" "Ok Tom me ne ne ke damun ta? "Nima ban sani ba. "Ko kinsan ta kamu da hawan jini? "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Ta ke ta fashe da kuka ta na ce wa "Wallhi bata sani ba. Da ƙyar ya samu ta yi shiru ya ce "Ku ƴan wacce unguwa ce? Cikin ƙosawa da tambayar ta ce "Pls likita zata samu lfy kuwa? Shima cikin son jin wannan daddaɗar muryar ta ta ya ce "Ai lafiya Allah ne ka ɗai ke bada ta, am'ma za mu yi iya ƙoƙarin mu sai kuma mu barwa Allah ikonsa. Hk dai Dr ya ci gaba da kula da Innah ba tare da ya am'shi ko sisi daga hannunsu ba. Itama dai ta na son yin magana am'ma ta kasa domin kullum idan ya zo sai ya kafeta wannan manya-manyan idon na sa. Haka dai har kwana huɗu am'ma Innah bata farkaba, an sa ka mata ruwa har sau biyu. Yayinda a cikin kwana ukun nan har Nana ta fara sake jiki da Dr domin yanzu ta na ɗan biye masa idan yazo ɗakin haka zasu ta hira kamar sun san juna. *ABDALHA POV* Tinda ya fito daga gidan Dr ya nufi gidan sa ya shirya domin zuwa gidan da Daddy ya ce yaje. Duk abun da ya ke yi ya na tunanin halinda Zainab ta ke ciki, shin wai yanzu ta ya ya zai sanar wa da mutane cewar ba ni ne na sa ceta ba! Afili ya ce "Komai zai yi dai-dai. Da sauri ya yi wanka ya shirya cikin shigar sa ta manyan kaya sannan ya ɗauki wayar sa yana son kiran abokinsa am'ma ya ji yanzu haushin kowama ya keji. Yayi tunanin bi ta gidan su Dr domin duba wa ko Zaiban ta farka am'ma ya fasa. Jin yanda ransa ya ɓaci ne ya sa ya kunna karatun ma haifin sa cikin suratul Maryam. Haka karatun na yi shima yana bin muryar cikin sanyi da nutsuwa har ya ƙara sa gidan. Dai-dai zai shiga gidan shi kuma ma haifin yarinyar wanda ya ke shima babban malamin addinine shi kuma zai fita. Ganin motar Abdalha ne ya sa shima koma wa da baya. Bayan sun gaisa Abdalha ya ce "Daddy ne ya turoni wai kana nemana? Cikin karannci da dattako ya ce "To-to kazo gurin ƙanwar ka kenan ko? To ai hakan yayi dai-dai kuma na yi farin cikin hakan sosai, Allah ya muku albarka bari na turo maka ita! Shi dai Abdalh bai ce komai ba har mai gidan ya shiga ya na ta saka musu albarka. Saida ya ɗauka mintunan a ƙalla goma kafin yarinyar ta shigo palorn cikin ɓacin rai da rainin wayo ta banko ɗakin ta ce "Am'ma dai Walhi anji kunya...bayan an gama yiwa al'umma wa azi a kan cewar bidi'a babu kyu, kuma masu aikatawa ma ba malamai bane am'ma shine ka sace ɗaya daga cikin su, bayan kowa yasan cewar kai da ita ba shiri kukeyi ba, shin me ka je ka ai kata mata? Bayan kun gama komai shine zaka zagayo ta nan wai kana sona ko? To Allah ya kiyaye ni na auri ɓarawo, kuma muna cikin addinin! Kafin Abdalha ya ce komai sai ga u'war yarinyar ta fito, kana gani kasa itace ta zugo yarinyar ta ta, itama ta ɗora na ta..."To duk faɗin 9j waye baisan da cewar kaine ka sa ce ta ba, kuma ka fito musu da yarinya ba shine ka lallaɓo gurin ƴa ta to Walhi bada niba. Sai a lokacin Abdalha ya ɗago kai ya kalli u'war da ƴar sannan ya ce "Ina u'ni Momy? Cikin jin haushin yanda ya yi banza da su ta ce "An iya ladabin banza, da de bamu san halin ka bane sai ka nuna ma na kai ɗin na Allah ne, am'ma munsan komai, abin da na keso da kai shine kaje ka sanarwa da mahaifin ka cewar karama a fara wannan auran ina ba haka ba zasu ai kata da na sani, kuma ka ce"..."ka fin ta ƙarasa Abdalha ya miƙe tsaye ya ce "Sai anjima, bai jira cewar suba ya bar palon cikin mamaki da tsananin ɗaurewar kai. Sukuma suka cigaba da ai bata shi da kuma cin mutuncin sa. *ZAINAB POV* Da sauri ta sauƙo daga kan gadon da take ta na bin ɗakin da kallo, sai kuma ta kalli jikinta taga ba kayan da ke jikin ta kenan ba, ɗaga kanta ta yi sai taga ledar ruwa wanda ya ƙare a rataye, har yanzu bata gano komai ba, sai ta ji wani ciwon kai mai ƙarfi ya sameta dalilin tunanin da ta fara yi, ai da sauri ta riƙe kanta tana rufe ido. A hankali ta ji ciwon kan yana ƙaruwa har kan ya ma ta nauyi sosai, jin sai ƙaruwa ya ke yi ne ya sa ta kurma wa ni ihuu ta na reƙe kanta wanda ta ke jin kamar zai rabe biyu. Da sauri Aisha matar Dr Musa ta shigo ɗakin ta na kiran sunan ta. Al'lurar da Dr Musa ya bata akan idan ta farka da kuka ko ihu ta mata ne ta ɗauka ta ƙara mata ganin kamar bata cikin haiyacinta. Ai kuwa ta ke ta ƙara komawa barci, ita kuma ta kira mijinta ta sanar masa wanda shima ya kira Abdalha ya sanar masa. Tin kafin ta buɗe ido komai ke dawo mata kaman dai mafarki, hakanne ya sa ta farka ɗauke da addu'ar ta shi daga barci *(Subuhana rabbiyal lazi a'ha ya'na ba'a dama a'mata na wa i'laihim nishur)* Ta na buɗe ido ta sauke shi a kan babban maƙiyinta, wanda a faɗin duniya shine mutum na ɗaya da ya shiga rayuwarta ya keson tauwatsar mata rayuwa, rintse idon ta sakeyi ta na sake tunano komai da ya faru. Tabbas ta tuno komai kuma ta yarda da cewa ba mafarki ta keyi ba. "Ƙwatsam ta ji sauƙar muryarsa a kunnuwanta "San'nu kina lfy? Ya jiki? Babu abun da ke damunki ki. Dr Musa ma ya ɗora da cewa "San'nu me ke damunki yanzu? Cikin dauriya da jajircewa ta ce "Gida na keson zuwa yanzu. Ta faɗa ta na haɗe fuska. Abdalha ya ce "Gida ba yauba sai kin samu lfy. Shima ya faɗa ya na haɗe fuska. Da sauri ta kai kallonta zuwa gurin da ya ke, ai kuwa suka haɗa fuska cikin ido, yayinda ko wa ya ɗaure fuskar sa kai ka ce ba shine ya gama mata sannu ba. Sun kai minti uku a haka kowa yana kallon juna kuma fuskoki a haɗe babu mai murmushi. Dr Musa da Aisha kuwa sai kallon ikon Allah sukeyi ganin wani irin sabon lamari, wai yau Abdalha Kabir kabuga ne ta re da Zainab Ambato a zaune a guri ɗaya, kuma da a lama wani babban lamari ne a tare da su. Domin shi Dr Musa baisan ta ya ya Zainab tazo hannun Abdalha, ko dai dama soyayya sukeyi a tsakanin su ne, sai kawai ya ɗauki rumut ɗin tv ya kamo wani tasha da suka gabatar da wani abu da ya ɗaure masa kai. Ganin dai har yanzu kallon juna sukeyi ka ka ce faɗa zasuyi tsabar ƙyayar da ke tsakanin su. Dr Musa ne ya ce "Eh kawai ki bari ki ƙara samun lafiya sai kawai ki tafi gida kinji? Ya ƙara maganar ya na kallon saura lokaci kaɗan a fara mai-maita abunda ya keso gani. Cikin sauri dukkansu suka kawar da kansu yayinda Zainab ta sa ki wani siririn tsaki wanda babu wanda ya ji sai shi Abdalh da ya ga bakinta. Abdalha ya ce "Dr Musa karka damu na gama magana bazata je ko ina ba. Ya na faɗa ya miƙe tsaye zai fita. Yayinda itama Zainab ɗin ta fara ƙoƙarin ta shi daga kan gadon batare da ta yiwa kowa magana ba. Ganin haka yasa shima da wo wa ya na kallon ta. Ta ce "Dr na gode sosai zan tafi nasan yanzu ana nemana a gid"... Ai kafin ta ƙarasa ta ji ana nuna hoton Abdalha a tv ɗin da Dr Musa ya kunna tun ɗazu, a kan ya sace wannan shahararriyar mawaƙyar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, wacce kowa ya santa da suna Zainab Ambato. Sannan kuma yanzu gashi mahaifinta mai suna Malam Adam, wanda shima babban malami ne wanda ya yi suna a faɗin duniya gaba ɗaya, ya kai ƙararr ɗan gidan Shek Kabir kabuga wato Abdalha Kabir kabuga, ya miƙashi kotu a kan zargin sa ce masa yarinya. Kallon tibin da ke ɗauke da hoton Abdalha da Zainab ɗin ta yi, sai kuma rubutu da ke nuni da ranar da za'a shiga kotun. Cikin tsananin mamaki ta kalli Abdalha shima ya kalleta kafin ta kalli Dr Musa wanda shima ya ke son ƙarin bayani domin kuwa abun ya ɗaure ma sa kai sosai....📝 *Barkan mu da ranar Juma'a🕋 Allah ya amshi ibadunmu. Amin ya Allah* *Labari na tafiya dai-dai kuwa?* [10/21 22:05] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE2️⃣8️⃣* .........Dr Musa ya meƙe tsaye da ga kujerar da ya ke zaune ya ce "Jiya muna kallo nida Madam naga wannan sanarwar shine abun ya bani mamaki kuma na ce sai na tambaye ku domin kaina ya ƙulle walahi, shin da gaske ne kai ne ka sace ta? Ya ƙara sa maganar ya na kallon cikin idon Abdalh wanda shi kuma ya ke kallon Zainab wacce har idonta ya cika da ruwan hawaye. Cikin kuka da ya kuffce ma ta ta ce "Ba shi ba ne ya sa ceni, ha salima saboda shi a ka sake ni, amma ni ban san dalilinsa na yin hakan ba! "Babu wa ni dalili na wa kawai na yi ne domin Allah da ku ma wanke kaina a idon duniya domin ko wa na tunanin ni ne na sace ki. Dr Musa ya ce "Shek kabuga ni fa ban gane me kuke ce wa ba fa, dan Allah kusanar min da komai, amma to idan ba kai ba ne to su wa ye? Nan ta ke Abdalh ya kwashe komai ya sanar wa da Dr Musa, sannan ya ɗora da abunda ya faru lokacin da ya je gidan su yarinyar da mahaifinsa ya tura sa domin su ga juna. Da sauri Dr Musa da Zainab da Aisha suka kalleshi jin abun da ya ce. "To su yaran da su ka sace ta me ta musu?Cewar Dr Musa cikin mamakin lamarin? "Wai sabo da waƙar da ta yi ta buɗaɗdiyar wasiƙa. "To suɗin ƴan gidan uban waye da har zasu mata wannan jan aikin!... Kai kuma ka barsu suka tafi baka sa police sun ka ma suba? Cikin kukan da ya fara fin ƙarfin ta ta ce "Dan Allah inaso na tafi gida ni ɗaya, domin nasan me zan ce wa malam ya fahimce ni, kuma kaima zaka fita da ga zargin da al'umma su ke ma ka, amma dai ni ka ɗai zan je gi da kuma yanzu. Ta ƙara sa ta na fashewa da wa ni sabon kukan. Abdalha ya ce "No tare zamu tafi domin nasan abun da zanyi ko mai ya yi dai-dai kamar yanda na ce a baya. Zainab dai bata yarda ba har sai da Dr Musa _yasa_ baki kafin ta yarda zasu tafi da Abdalha amma sai da daddare domin idon gudun idon mutane. Haka suka yanke akan zasu tafi ɗin. Ɓan garan gidan su Abdalha ku wa kaman yanda ya amsa musu cewar shine ya sa ce Zainab haka ko wa ya hau ya zauna daram, harda Momy wacce izuwa yanzu basu gama shirya wa da mai gidan nata ba tun abun da ya faru a kan Abdalh wancan lokacin. Suna zaune kamar yanda suka sa ba duk bayan sallar magariba ranar juma'a domin gabatar da karatun littatafan addini da Momy ke ƙara koya musu a duk yan macin ranar. Cikin sauri har yana ƙoƙarin zame wa ya shigo gidan cikin tsan-tsar ɓacin ran abun da ke tafe da shi ɗin, tin kafin ya ƙara so ya fara ce wa "Ina kike ke mai ɗaure wa wannan yaron ginɗi! Yanzu me hakan ya haifar wannan wani irin abun kunya wannan yaron ya ɗauko mana, yanzu a ke sanar min da cewar wai Abdalh ya je gidan Shek gurin yarin yar da na turashi wai yarinyar ta ce bazata auresa ba, saboda abun da ya aikata. Yanzu kuma gashi wai wannan malamin ƙar yar ne wai ya kai Abdalh kotu akan sai ya fito masa da yarinya. Yanzu dan Allah wannan wani irin abun kunya ya ronnan ya je ya kwaso min, a ce wai ni Kabiru gabuga ne ɗana zai je neman aure wa ni gidan amma a faɗin aibunsa! Shek Kabir kabuga ya ƙarasa maganar ya na mai nuna Momy kamar ita ce Abdalha ɗin. Cikin tsan-tsar tashin hankali Momy ta ce "Kotu fa ka ce Malama? Ta faɗa ta na miƙewa tsaye. Cikin mamaki Maryam ke kallon Daddy jin wai yarinyar ta ce bata son Abdalh. Ita dai ta san Nana ta na son Abdalh sosai, kuma tasan irin addu'ar da takeyi a kan ta samu Abdalha amma yanzu a ce wai yarinyar ta ce ba ta son sa! Kai saide ko an zuga ta kokuma dai a kai wani abun a ƙasa bayan haka. Ta na cikin tunani ta ji Daddy na faɗin. Ni dai Walhi ba zan je kotu na tsaya ni da wannan banzan dattijon ba, bansan komai ba sabo da haka shi da ya je ya taro abun sa shi ne zai jagoranci kayarsa, ha ka kawai yaro lokaci ɗaya ya zo ya zama wani iri, to wallhi xan mutuƙar saɓa masa in dai a kan ƴan bidi'ar nanne, bana sonsu bana ƙaunar ganinsu bare wai har na je na haɗu dasu a kan na sace musu yarinya. To idan na je na ce musu me? Na ce musu dan Allah suyi haƙuri? Ha ka dai Daddy ya dinga sarfa masifa ta idan ya shiga ba ta nan ya ke fitaba, ƙarshe dai ya ƙare da kiran Abdalh amma no amsar, hakanne ya sa ransa ƙara ɓaci, domin yaso Abdalh ya zo ya sanar da shi gidan uban wa ya kai musu yarin ya domin shi dai Daddy bai yarda cewar ya sa ce ta ba, kawai ya masa haka ne domin ransa ya ɓaci. Ɓacin ran Daddy yau kam ya ɓaci, nan Momy ta ke sanar ma sa da cewar ai yau kwana biyu kenan ma Abdalha baizo gida ba. Ita dai Maryam ta shi ta yi ta bar gurin izuwa ɗakinta domin kiran Nana, dan ida kam ba ta yarda cewar Nana ce da kanta ta ce bata son Abdllah ba. Ai kuwa ta na shiga kira ya shigo wayar ta, sunan kamal ne ya baiya na a kan wayar, (kamal wanda Abdalh ya raba su tun da ɗaɗe wa, a she basu rabubu) "Sorry Man mu na palor muna ka ratu ne wayar kuma ta na ɗakina. Kamal ɗin ya ce "Ok ba damuwa, amma dai yau zaki zo ko? "Yes yau ina so zaka rakani wa ni guri, amma fa ni zanzo na sameka. Cikin ɗan tsoro ya ce "Ko dai babban yaya ya dawo ne? "Dariya ta yi sannan ta ce "Kai dai bari! Ina ga fa magata ta zama gaskiya. "Ban ga ne ba? Yayi tambayar cikin rashin fahimta? "Idan muka haɗu zaka gane, ta faɗa ta na ƴar dariya ƙasa-ƙasa. Shima dariya ya yi kafin ya ce "Allah babban yaya yana shiga hakkina fa. Ya sake buɗe baki zaiyi magana ta ce "Zan kira ka anjima. "Ok tom i'm werting. Suna gama wayar ta daka wani tsalle ta na cewa Yes komai na tafiya dai-dai. Numbar Nana ta nemo ta danna wa kira, ai kura ƙara ɗaya a ka ɗaga. Kallonta ya ke ganin har yanzu kukan ta ke gashi lokaci sai tafiya ya ke. Ba ta re da ya ce ma ta komai ba shima ya kifa kansa a kan matuƙin motar yana jira ta gama kukan kafin su shiga. Cikin kuka ta ce "Ba ka tsoran kayi karo da babanna ko ya ya nane? Bai bata amsaba ya ce "Idan kin gama ki fito mu tafi domin yanzu haka a na jiranane?. Yayi maganar dai-dai ya fito daga cikin motar. Ganin haka ya sa itama Zainab ɗin fitowa tana bin bayansa domin har ya yi gaba. Sai da ya je zai shiga gidan kafin ya tsaya ya na kallon wani ƙatoton hoton da ke ɗauke da suna kamar haka... *SHEK IBRAHIM INYASS* Kallonsa ta yi ganin abun da ya ke kallo. Ai kuwa shima ya kalleta sai kawai ya taɓe baki a lamar norting. Itama kallon hoton ta yi kafin ta kai hannu ta shafo fuskar hoton sannan ta fara tafiya shima ya bita a baya yana saƙe-saƙe a zuciyarsa. Acikin gidan ku wa Isa da mlm ne ke shirya yanda zaso tona wa Shek kabir kabuga a siri domin kuwa har ga Allah ya tsaya musu a rai, ga kuma wannan ɗan iskan yaron nasa wanda baya ganin kowa da mutunci, yaron da kullum idai zaiyi wa'azi sai ya zagi ni, wai a ce shine ya sa ce min yarinyar da banda kamar ta amma wai kice nayi haƙuri, sabo da ban da hujja ko! Mlm ya ƙara sa ya na nuna gurin da Nama ke zaune ita da au'ta Aisha sun sha kuka har sun gaji. Cikin tsananin ɓacin ran da bata taɓa nunawa a gidan ba tun da sukayi aure da mai gidan na ta ta ce "To ai Walhi mlm Adamu ba ka ɓurgeni ba tundade bakaje kayi gaba da gaba da shi Shek Kabir kabuga ɗin ba domin nuna masa cewar shiɗin ba komai ba ni kamar yanda kake faɗa, walhi baka bani bamaki ba, kullum abu ɗaya to Ni wallahi na ga ji bazan iya da wannan ƙiyayyar taku ba wacce babu komai a cikin ta sai son zuciya . Kafin Malam ya gama mamakin jin sunan sa daga bakin matar ta sa har ta ɗora da ce wa. "Yanzu gashi yau kwana ɓakwai kenan babu taƙa mai-main labarin Zainab ko kuma labarin gun da ta ke, amma kai da muwar ka sai ka tozarta wani, wato kai hakan ma daɗi ya maka, tunda zaka cimutuncin wani ko, to wallhi mutuƙar wani abun ya samu ƴata to kaine sila, domin ka ba ma ta a samota kakeyi ba, kuma walkhi mutuƙar baka janye wannan ƙarar ba sai na lalata komai walhi. Mama ta ƙara sa ta na fashe wa da kuka, ai kuwa kamar malam jira yake ta gama shima ya ɗora da cewa... "Eh lailai sai yau na tabbatar da cewar kema kina tare da su, kuma yau na tabbatar da cewar duk abun da ke faruwa ke ce kika bada hanya, yanzu duk irin cin mutuncin da wannan yaron bayan nawa kemin nida ɗiyata har kin manta, haka wannan yaron zai dinga cin mutuncin mu ya na ai batamu harma ya na ciremu daga cikin addinin namu amma wai kice na ji daɗi da abun da ya yi? To walhi idan har ta tabbata cewar wannan yaron shine ya sa ce Abu to walhi sai ya yi mamakin irin hukuncin da zan masa kuma"..."Ai kaji gun da matsalar ta ke, kenan ma baka da hujjar cewar shine ya saceta, kenan za to kakaye, kuma zato mene a addinance? Mama ta katse shi da wanan tambayar. Cikin ɓacin ran jin yanda ta ƙatse shi ya ce "Yanzu ni kike ɗaga wa murya a gida ko wa yana ji domin kare wanda ke son cutar da ɗiya ta? Har kina cemin ina yin za to! Ya ci gaba da ce wa... To ki sani mutuƙar ta tabbata hakan to kema sai kinyi da na sani walhi, domin a kan hakan zan iya tsinke zaran da kike wasa dashi har kike ɗaga min murya. Ai da sauri isa da ke tsaye a gurin jin abun da Mlm ya ce ya riƙe baki yana nadamar wannan abun da ke faru wa a tsakanin iyayen nasa. Mlm na gama faɗin haka ya bar gidan cikin tsan-tsar ɓacin rai. Ita kuwa mama jin abunda ya ce sai ta fara cewa dan Allah mlm ka tsinki ai ban hanaka ba kuma ban riƙekaba. Mama ta dawo da kallon ta izuwa gurin Isa ta ce "Yanzu kaji daɗi hakan ko burin ka ya cika ko! Ta na faɗa ta ɗauki Aisha suka shiga ɗaki ba ta ko tsaya jin maganar da Isa ɗin keyi ba. Jama'ar gari ku wa ko wa abun ya bashi mamaki jin cewar Mlm Adamu ya kai shek Kabir kabuga ƙara kotu. Tabbas abun ya gir-giza ko wa, daga ƴan ƙungiyar su Zainab ɗin harma na su Abdalha ɗin, ko wa ya san dai a kan ɓatar Zainab ne, kuma har zuwa yanzu babu wata hujja da zata nuna cewar ba Abdllah ɗin ba ne ya sa ceta ba, domin kuwa tun da abun ya faru ba'a ƙara jin sa yayi wani wa'azi ba, kokuma ya fito ya yi magana a kan hakan ba. Hatta ƴan ƙungiyar tasu wa su duk jikin su yayi sanyi domin wasu sun yarda da cewar shi ɗin ne ya saceta, hakanne ya sa wasu ƴan a da'war suka dinga yaɗa zan can cewar ya ɗau keta ya gudu da ita ne. Domin ko masallacin da ya keyin sallar juma'a kuma ya yi wa'azi a masallacin to wannan jum'ar babu wani da ya saka shi a ido, gaba ɗaya ma dai ba'a ganin sa yanzu, kenan dai ya tabbata shine ya sa ce ta. Yanzu dai kowa na jiran ranar shiga kotu tazo domin a je a ji Shari'a tsakanin malamai da malamai, wato shari'ar ilimi, tsakani Malam Adamu da shek Kabir kabuga. Wasu da yawa dan kawai gulma zasuje, wasu kuma domin jin gaskiyar lamarin. *( To koma dai mai zai faru muje cikin labarin domin jin gaskiyar lamarin mu dai ƴan kallo ne)* *GIDAN SOJA* Gudu Samuel ke yi sosai, wanda saida yayi tafiya mai tsayi tsakanin part ɗin su da gurin da aka kai AJ ɗin wato ɗakin *TSARO* Duk gudun da Samuel keyi da shiga lungu haka Salis ke binsa domin shima maganar da Samuel ɗin yayi yasa ya fara zargin wa ni abun. Dai-dai Sojojin da suka shigar da Aj ɗakin zasu fito, su kuma suna ƙaraso wa gurin, kasan cewar Sojojin sun tsaya koya wa Aj hankali. Ai kuwa Samuel ya na zuwa bai tsaya jiran komai ba ya tura kai, shima Salis da ke bayan sa ya tura kai. Ka san cewar sojojin basu san da zuwansu ba, kuma basuyi tsammanin ma bayan mai gidan da kuma matar gidan wani yasan da gurin ba. Ya nayin yanda suka shigo ɗakin ne da ƙarfi yasa ɗaya daga cikin sojan wanda ya ke gaba faɗuwa, su kuma sauran suka shirya biddigarsu. Ganin haka ya sa Samuel da Salis ɗaga hannuwa sa ma suna ƙara shiga cikin gurin. Ganin Samuel ne ya sa ɗaya daga cikin sojan ya ke tam bayar sa lfy? Cikin tsoro da far gaba ya ce "Daddy ne ya turoni wai ku fito da wannan yaron da kuka shiga da shi yanzu? Ta ke Sojojin suka kalli juna kafin wannan wanda ya faɗi ɗin ya ce "Get aut!!! Ya yi maganar cikin ihuuu! Domin kuwa bai yarda da Salis da ya gani da ga bayan sa ba. Ganin kofar a buɗe ga kuma wata zuciyar da ta turashi izuwa cikin ɗakin da suke da tabbacin a nann komai ya ki, zuciyar sa na tabbatar masa da cewar bazasu iya harbin sa ba. Ai kuwa kafin ka ce me Salis ya nufi ɗakin da gudu, wanda yayi dai-dai da shima Samuel ya shiga, hakan kuma yayi dai-dai da sakin bulet da ɗaya sojan yayi. A lokaci ɗaya abu guda uku ya faru. Shigar su Salis da Samuel cikin ɗakin tsaro, da kuma sakin bulet ɗin da ya sumu ɗaya a cikin su, da kuma ƙarasowar su Elixa da Hajiya Babba da Sarah wacce dama suman ƙarya ta yi domin a buɗe ta, da laɗifa da Daddy. Ƙarar bulet da ƙarar da ɗaya daga cikin Salis da Samuel ya sake ne yasa sauran mutanen dake cikin ɗakin tsorata, harda AJ wanda tsabar duka har ya fita a hai yancin sa. Cikin mamaki Elixa taga raronta jikin jini yana kurma ihuu! Yayin da Salis ya kai kallon sa izuwa cikin ɗakin domin tabbatar wa da zuciyar sa abun da ta ke cemasa...📝 *Anya kuwa kuna tunanin abunda na ke tunani?* *Ku ci gaba da bina a hankali, kuma kuci gaba da min uzuri,* *Yanzu kun rage yin comments fa?🙄* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE2️⃣9️⃣* .........Ko wa da ke cikin ɗakin tsorata ya yi saboda ƙarar harbin bindigar, hakan ne ya sa gaba ɗaya suka cure a guri ɗaya ko wa na neman hanyar da zai tsira da rayuwar sa, shi ku wa Salis lokaci ɗaya idon sa ya sauƙa a kan abokinsa wanda ya ke gefe ɗaya cikin tsananin wahala. Da ƙarfi ya kira sunan sa ya na ƙarasawa gurin da ya ke. Da sauri Momy ta ƙara sa gurinda Samuel ke kurma ihuu domin harbin da a ka masa a ƙafar dama. Shima Daddy da sauri ya je gurin ya na kamo yaron nasa cikin tashin hankali. Yayinda ita kuma Hajiya Babba ta bi bayan yaron ta domin jin kiran sunan AJ da ya yi. Itama Sarah cikin kuka tayi gurin ɗan uwan nata haɗi da rushewa da wani sabon kukan. Ita kuwa Laɗifa tsayawa tayi a bakin ƙofar ta rasa gurin wa zata je, domin ganin jini a ƙafar Samuel ya tasher mata da hankali, hakanne ya sa ta tsaya ta na kallon sa cikin damu wa, ai kubwa bata san lokacin da kuka ya kuffce mata ba tana rufe bakin ta kar kowa ya ji. Da sauri Salis ya ɗago Aj da ga kwancen da ya ke yana kiran sunan sa AJ...AJ... Amma ina AJ ko magana ma yakasa domin kuwa ya daku ba da wasaba, shi kuwa sai gir-gizashi ya kayi ya na ƙara kiran sunansa, kuma yana tunanin me ya kawo AJ ɗin cikin wannan gidan! Daddy ku wa ganin Hajiya Babba na ƙoƙarin shiga ɗakin ne yasa da sauri ya sha gaban ta ya na tambayarta ina zata je? Cikin tsananin ɓacin rai da tsanar da ta kewa yayan mijinta ta fara surfa masa masifa ta na cewa idan bai bata hanya ba zata zabga masa mari, ai kuwa Hajiya Babba ta man ta a gaba wa take domin kuwa ranta yayi mugun ɓaci idon ta duk sun rufe, har wani ruwa ne ya cika a cikin idanuwan na ta. Kafin ta gama rufe baki taji sauƙar mari guda biyu hagun da dama. Cikin ɓacin rai da ganin komai ya lalace ya nunata da hannu ya fara magana cikin fushi. "Walhi saina kashe ki idan baki bar gidan nan ba, shegu dangin tsiya, ai dama nasan mutuƙar mutam ya zama mai yin salla to shikenan kun gama shanyeshi, to dan uwarki harda ubanki ki bar gidannan ko kuma na sa a"...Bai ƙarasa ba yayi ido biyu da Salis reƙe da AJ ya fito daga cikin ɗakin. Da sauri dukkansu suka kai kallon su izuwa gurin da Salis ke tsaye. Da sauri Sarah ta bar gurin da Samuel ke ihuu har zuwa yanzu wanda dukkansu kuka sukeyi an kuma rasa wanda zai ɗauke shi izuwa asbiti sai ihuu sukeyi. Da sauri ta ƙaraso gurin ta na mai kamo hannun AJ ɗin cikin wani sabon kukan. Sai ji kayi itama Daddy ya ɗauke ta da mari sannan ya turata waje, yana ƙara tabbatar ma da cewar babu ita babu AJ.sojoji ku wa Tinda sukayi wannan harbin suka shiga cikin tashin hankali ganin Samuel suka samu ba Salis ba, sannan tunda Ogan na su ya zo bai ce musu komai ba sai yanzu. Ya basu umarnin fita da Samuel. Ai kuwa da sauri sukayi waje dashi. Hajiya Babba kuwa ta na riƙe da hannu a kunci. "Eh tabbas shekarun da ya wa, kuma abubu wa da dama sun sauya, sannan kuma yanayi ya sauya ha ka zalika duk wani abu mai rai to tabbas yana ƙara girma ne, sannan abu mai muhimmanci baya taɓa gushewa da ga mahalli da. Tin lokacin da ya yi ido biyu da yaron da ya shigo ɗakin jikin sa ya sanar masa da cewar tabbas yau Allah ya karɓi addu'ar da suka daɗe sunayi, ya na cikin kallon yaron ne har yaron ya taso riƙe da ɗaya yaron da a ka shigo da shi ɗa kin nasu ɗazunnan. Kukan da yazo masa ne yasa ya kasa yiwa yaron magana har ya fita. Yana cikin haka ne yaji muryar da ba zai taɓa mantawa da itaba koda kuwa mutuwa yayi kuma ya dawo wannan duniyar bare kuma bai mutu ba. Tabbas baiyi niyar tashi ya fito gurin ba, amma jin yanda yayan nasa yake cin mutuncin Addinin nasa da kuma yana jin cewar Allah ne ya turo wannan ranar domin ta zama warakar damuwar da suke cikin Sudan ƴan u'wansa, hakanne ya sa ya miƙe daga gurin da yake zaune cikin wa su kaya yagaggu sun gama fita a haiyacinsu ga tarin gashi da ya gama mamaye masa fuska, gashin kansa yayi jaa ,sannan ya mur-murɗi, ha ƙoran sa sunyi jaa sun fita a haiyacin su, gaba ɗaya kamarsa ta canja, daga gurin da kake zaka hango ƙashin ha ƙaƙƙarin sa a waje. Ganin yayi hanyar fitane yasa sauran mutum ukun da suke ciki suma miƙewa suka biyo bayan sa, suma cikin irin halin da yake ciki. An fita da Samuel, shi kuma Salis yana tsaye a kusa da Daniyel ya kafeshi da ido, yayinda Hajiya Babba tayi kan Salis cikin tashin hankali tana kiran sunan AJ. Lokaci ɗaya Hajiya Babba ta fita a haiyacinta tana ƙoƙarin kamo ƙafafun Aj domin fita dashi sai suka tsikayi muryarsa cikin rawar mur yaya ce " Ai ais Aish Aisha? "Timm ka keji Hajiya Babba ta saki AJ ya zube a gurin tsabar ruɗu da harƙizi da suka dirar mata a lokaci ɗaya. Da sauri ta juyo domin kuwa tabbas bazata taɓa mantawa da wannan muryarba har gaba da abada. Tana juyowa sai taga fuskokin mutane har guda huɗu a bakin ƙofar ɗakin, amma hakan bai hana ta gano fuskarsa ba cikin sauri da ruɗani ta nufi gurin sa bata iya ko magana ba tana nunashi da hannu. Salis da laɗifa sai kallon Hajiya Babba sukeyi domin su dai basu gane waye wannan mutumin mai kama da wanda baya cikin haiyacin sa ba, suna kallo har Hajiya Babba ta rungumeshi dukda irin kayan da ke jikin mutumin. Shi kuwa AJ jin yanda a ka sakeshi ne yasa ya saki wani ihuuu yana buɗe idonsa cikin wahala, domin kuwa tsabar duka har saida ya suma.da sauri Salis ya zo gareshi ya na kiran sunan sa. Cikin mamaki Salis ya duba cikin ɗakin amma baiga Daniyel ba, ai kuwa da sauri ya tashi domin fita waje, ai kuwa yaji ƙofar ɗakin a rufe, ya kalli ƙofar da kyu, ya ja da baya ya zo da gudu ya daketa amma ko motsi batayi ba. Abun da kamar wasa har yayi har ya gaji amma dai ƙofar na ƙulle. Cikin wata iriyar murya wannan mutumin ya ce "Ya ƙulle ƙofar ne ko? dama nasan bazai barmu mu a gidan nan cikin kwanciyar hankali ba tabbas kashemu zaiyi baida imani, dama ya sanar min cewar duk ranar da wani yasan ina raye to tabbas zai kashe ni kuma ya kashe ku. Duk wannan maganar yanayi ne a bakin ƙofar da suka zo domin fita. HAJIYA BABBA ta kalli Salis da Laɗifa ta ce "Sa sa Salis shine ba ba ban babanku, shine babanku. Tana faɗa ta sake fashewa da kuka, yayin da Salis da Laɗifa harma da Mlm AJ suka kai kallonsu gurin mutumin, suma sauran ƴan ɗakin da mamaki suke kallon yaran da kusan kullum sai mutumin ya basu labarin cewar ya bar yaransa da matar yan zu baisan a wani hali suke cikiba. Lokaci ɗaya dukkansu kuka ya kuffce musu, sun kasa zuwa gurin baban na su, sai tuno irin wahalar da yashe sukeyi da kuma tuno abun da ke faruwa yanzu sukeyi. Hannu ya ware musu alamar ku taho gareni ai kuwa dukkansu suka nufeshi suna kukan farin ciki. Alokaci ɗaya Mlm AJ ya sake jin wani sabon ciwon da baisan daga ina ya fito masa ba, shin wai shi yanzu a wani hali yake ne, kuma yaji ana zancen kisa, to har dashi za'a kashe! Lokaci ɗaya ya nemi ciwon da ya keji ya rasa, ya fara tuni Innah da Nana. ita kuwa Hajiya Babba za mu iya cewa harga Allah ta ma manta da wanzuwar wani mai suna AJ agurin. Sun kwashi lokaci suna koke-koke kafin suka ƙara shiga ƙoƙarin buɗe ƙofa amma shiru. Hakanne yasa suka haƙura suka zubawa sarautar Allah ido. *(Shin kuna tunanin Daniyel zai buɗesu? Kodai a ciki duk zai haɗa ya kashe kamar yadda ya ce? To wai ta yaya zasu fita daga cikin gurinnan, ga shi dukkansu kowa na ciki😪 Tom koma dai menene muje zuwa domin ganewa idon mu)* Ganin Muhammad ya fitone yasa Daniel za me jikin sa ya fita daga ɗakin sannan ya sa ɗan mukulli ya rufesu ta waje sannan yayi cikin gidan cikin sauri. Ya na shiga palon gidan nasa yaga har angama cirewa Samuel bulet ɗin an masa aiki agurin ana ƙoƙarin ɗaurewa. Da sauri ya da katar da sojan daga aikin da ya keyi, sannan ya ce ya kira masa sauran sojojin da suke gidan gaba ɗaya. Cikin minti kaɗan sukazo, dukkansu ya sanar musu da cewar zaibar wannan gidan nasa izuwa gidan sa da ke cikin Bokon, kuma gaba ɗaya har da iyalansa zai tafi, saboda haka a je a shirya yanzu-yanzu, ya ware mutum biyu ya ce su tsaya. Bayan waɗan can sun tafi ya kalli sauran ya ce... "Ku biyu zaku tsaya a nan idan mun tafi kamar da awa ɗaya ku sakawa gidan wuta kuma kubi bayanmu, idan an tararr daku kuce gobara ce. Haka suka yanke shawara sannan suka shiga haɗa kaya, komai na amfani saida suka ɗauka, cikin lokaci ƙanƙani Sojojin sun gama haɗa musu kayan a mota harda sauran motocin gidan duk dasu zasu tafi. Ran Daddy ya gama ɓaci ji yake kawai ya kashesu kowa ma ya huta. Sai da a kazo tafiya kuma a ka duba sama da ƙasa amma babu Sarah babu dalilin ta. Anduba gidan ko ina amma babu ita, kuma harda ita a ka dawo palon. Nan fa hankali Elixa ya tashi domin kuwa ta damu, aka tam bayi sojojin kodai ta fita ne sukaje su basu ganta ba. Cikin tsananin ɓacin rai da kuma ganin tana son ɓata musu lokaci Daddy ya ce kawai su tafi su barta. Momy ta ce "To idan itama tana gidan fa har ta ƙone? Cikin haushi ya ce "To idan ta ƙone ni na ƙone? "To wallhi bazan tafi na barta ba. Da kiyr dai Daddy ya fita da baki harta yarda cewar wai kafin sojojin su kunna wutar zasu sake dubata. Haka suka tattara suka bar gidan daga su har kayansu shima Samuel sai ihu ya keyi a kan a barshi a nan amma ina.. ( *to fa )* *NANA POV* Lokacin da a ka sallamo su Dr ne ya ɗaukosu har gida a cikin motarsa, Innah sai shi masa albarka takeyi domin kuwa tabbas sun samu kulawa sosai a gurin sa. Innah ta war-ware sosai , yayinda Nana da Dr abota tayi nisa domin har waya ya siya mata , sannan ya saka numbar sa a kan zasu dinga gaisawa, itama ta saki jiki dashi sosai. Shi kuwa Dr so ya ke sai hankalinsu ya ƙara kwantawa kafin ya gabatar da kansa a gurinta, domin yarinyar ta tafi da imanin sa, idan yana kallonta har tsarguwa takeyi, daɗin sautin muryarta kuwa har wani amsa kowa ta ke masa a cikin kunnuwan sa tsabar yanda takeyin maganar kamar bazata yi ba, ɓan garan tafiyar ta kuwa, shi dai a ganinsa ko ɗawisu saide tazo Nana ta koya mata. Hakanne ya sa baya gajiya da kallonta. ( *Kai Dr ai dama duk wata Nana ai duniya ce walla)* *ABDALHA . ZAINAB POV* Karo sukaci da Mlm Adamu wanda ke ƙoƙarin fita daga gidan nasa cikin ɓacin ran da matar sa ta ƙunsa masa. Kallon Zainab ɗin ya yi daga sama har ƙasa kafin cikin sauri ya ce "Zainabu ke ce? Bata tsaya bashi amsaba ta fashe da kuka tana rufe bakin ta. Ai da sauri Mlm ya kamo hannuta ya ce "Ya isa haka ya isa, muje ciki Alhamdu lillh masha Allah! Mlm ya dinga hamdala yana riƙe da hannun Zainab, shi kuwa Abdalha na biye dasu sai bin cikin gidan ya keyi da kallo ganin sai shiga da fita a keyi ta ɗaya ƙofar, domin kuwa gidan ƙofa biyu ne. Har suka ƙarasa cikin palon sannan ya fara kiran matar tasa wacce dama itama yanzu ta shiga ciki. Isa ne ya fara shigowa palon sai Mama wacce har yanzu ranta a ɓace yake. Kallon-kallo a ka far yi tsakanin Isa da Abdalha, domin kuwa yana shigowa idonsa ya sauƙa a kansa, itama Mama shi ɗin ta fara gani. Da sauri Zainab tayi gurin mama tana kuka tana cewa Moma na yi kewar ki. Itama Mama lokaci ɗaya kukan ya kufce mata, ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana rusar kuka. "Ban gane ba ubam me ya ka wo ka gidan mu? Cewar Isa yana nuna Abdalha cikin mamaki. Sai a lokacin Mlm ya ganshi. Ai kuwa kafin Isa ya ƙara cewa wani abu Mlm ya fara nashi cikin fushi. "To ai dama na faɗa cewar wannan ɗan gidan matsiyatan ne ya saceta amma wannana mai taurin kan ta ce zato na keyi. Ya faɗa yana nuna Mama wacce batama san cewar da ita ya ke yi ba.Ya ci gaba da cewa...."bayan ka gama tara mutane kun zageni kai da uban ka to mai ya kaika ga sace ƴata? Ai dama haka halin su ya ke, wato yanzu ya ji cewar zan kai ubansa kotu shine ya dawo min da yarinya, to walhi duk da haka sai ammana sharia da ku. Ganin Abdalha har yanzu bai nuna koda tsoroba ya sa mlm nufo gurin da ya ke yana cigaba da aibata shi. "Ka fita min daga gida, kuma kaje ga sanar wa da uban naka cewar wallhi zuwa kotu nanan gobe. Cikin tsawa Isa ya ce "Wai dan ubanka bada kai a keyibane ka tsaya sai kallon bakin mutane kakeyi?. Kaman yanda Abdalha ya saba koda kuwa Daddyn sa ne yake masa faɗa, to baya iya cewa komai, kuma idan har bai gaisa da mutum ba haka kana cikin faɗan zai gai da ka. "Ina uni Mlm? Cewar Abdalha yana daga tsayen da yake. Cikin jin haushe Mlm ya ce "Riƙe gaisuwar ka ba na so tashi ka barmin gida, ba ga irinta nan ba, gaisuwa a tsaye kamar zai giasa da sa'an sa, yanzu wannan itace tarbiya, wannan shine yaron da ya ke tara mutane da sunan wa'azi? Mlm na cikin faɗa ya ji Abdalha ya miƙa wa Mama na ta gaisuwar. "Ina u'ni Mana? Sai a lokacin Mama ta ɗago da Zainab ta ce "Lfy yaro...tare kuke da ita? Abdalha ya buɗe baki zaiyi magana Zainab ta ce "Eh tare muke shine ya sa a ka ƙarɓoni daga gurin mutanan da suka saceni.....📝 PLs Comment *By S REZA* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA ✍️* *First Class writer's asso* *PAGE3️⃣0️⃣* ......"Ban yarda da wannan zancenba kuma ba zan taɓa yarda ba, idan ma wani abu ya miki kike ɓoye wa to walhi ba zan taɓa bari wannan yaron da kowa ya gama yarda cewar shine ya saciki amma yanzu ki ce wai shine ya sa a ka kar ɓoki! Ka tashi kabar min gidan tun kafin raina ya kai ga ɓaci. Cewar Mlm yana nuna Abdalha cikin tsan-tsar ɓacin rai. Mama ta ce "Am am Zainab bamu gane me kike nufiba? "Eh Mama kamar yandda kikaji na ce bashi bane ya saceni wasu mutanene kuma shine ya je ya ƙarɓon"..."Ya isa haka! Cewar Mlm...Ya zata muma irin mutanan da yake tarawa a gari da sunan wa'azi ya raina musu wayone? Wato saboda yaji na ce zan kai ubansa kotu shine ya fito da ke har ya shirya miki ƙarya kekuma kika hau kika zauna ko? To ga saƙo zan baka ka kaiwa shi mai sa ka yin komai ɗin ka ce masa... Duk da yarinyata ta fito sai munje kotu an'mana iyaka tsakanin gidana da gidan sa, domin sai an mana shari'a! "Haba mana Mlm sai kace ba musulmai ba... Musulman ma kamar ba malamai bai! Yanzu wannan abunda kukeyi shine zai ƙara haɗa kan addinin Musuluncin ko kuma zai ƙara rabawa!? dan Allah Mlm ka zauna mu saurari wannan yaron muji da mai yazo? Ta ƙara sa ta tana yin ƙasa da sauri ta. "Waye malamin? Wancan ne Malami? Wallhi Kabir kabuga ba malamin gaskiya bane, burinsa sai ya tarwatsa Addinimu kuma Wallhi nidai bana ganinsa da wata kimar malumta, kuma wannan yaron ya barmin gida kafin na dawo, nine zan zauna na saurare shi, kotu ne kuma dole sai anje. Mlm na kaiwa ya bar palon cikin ɓacin rai. Isa ya ce "Yallaɓai sai a tashi a bar mana gida ko? "Walhi isa idan na ƙara jin bakinka a gurinnan sai na mugun saɓa maka, wato ubanka yamin kaima kamin ko? Ban isa na ce maka a'a ba ko? Isa ya ce "No Mama dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara cewa komai ba kinji!. Zainab kuwa tinda Mlm ya fara magana sai kuka takeyi tana jin babu daɗi a ci mutuncin ubanka a gabanka, ta ɗaga kai ta kalli Abdalha sai taga murmushi ma yakeyi abubsa. Shi kuwa tun lokacin da Mlm ke faɗa sai kawai ya tuno da mahaifinsa,. Azuciyarsa ya ce "Anya kuwa tsakanin Daddy da Mlm babu wani abu a ƙasa bayan rabuwar haƙida, idan bai mantaba shima Momy ce take hana Daddy amma kullum sai ya yi maganar Malam Adamu. Mama ta kalli Abdalha ta ce "Yaro bamu labarin abunda ya faru? Abdalha ya ce "Kaman yanda abun ya shiga kunnuwan al'ummar gari da ma duniya cewar nine na sace Zainab, to haka nima abun yazo kunnena, duba da cewar ranar da abun zai faru mun haɗu da ita amma bamuyi wata magana ba, sannan na shiga tsananin tashin hankali ganin yanda labarin ya nuna zahirin nine na saceta, bayan ni kuma ban taɓa saka haka a rainaba, hasalima nine mai jawo hankali ga masu irin wannan halayyar. Abun da ya fara bani mmk shine lokacin da naji Daddy shima ya yarda da cewar nine na saceta, lokacin ina gida tare da Momy saiga samari sunzo har ƙofar gidanmu akan saina fito musu da ita, ana cikin hk Daddy ya kirani akan sai na fito musu da yarinya. Hakanne yasa nikuma furta musu cewar nine na saceta. Da sauri Isa ya ce "Nidai nasan shine zai saceta gashi kuma ya faɗa da kansa"..."Kallon da Mama ta masa ne yasa ya ƙuntse sauran maganar tasa yana rufe baki. "Tun daga wannan lokacin na shiga tunanin yanda zan gano komai domin nayi tunanin anyi hakane domin ɓatani, har washe gari ban gano komai ba. Bayan abun da kwana biyu har lokacin banyi magana da kowa ba tsabar bansan me zance ba, ina zaune naji kira a a waya na, ina ɗagawa naji ashe waɗanda suka kamata ne. Take ya kwashe komai ya sanar musu,bai ɓoye ko mai ba. Cikin kuka Mama ta sake rungumo Zainab tana faɗin "Allah sarki Zainabu Allah zai saka miki koma suɗin suwaye, domin ke baki musu komaiba, kai kuma Allah ya maka albarka mungode sosai, sannan idan Zainab ɗin tayi wanka ta ci abinci zan sakata tayi magana da sauran ƴan gungiyar tata domin suji gaskiyar lamarin, sannan ka sanar wa da iyayenka cewar anga yarinyar? Abdalha ya ce "a'a babu wanda ya sani daga ni sai Dr Musa sai matarsa. Mama ta ce "To idan zaka tafi gida sai ku tafi da Isa ya rakaka domin ayi musu bayani yanda zasu fahimta. Abdalha ya ce "A'a Mama karki ji komai nasan yanda zanyi dasu har komai yayi dai-dai. Mama ta ce "Karka damu ai yanzu an zama ɗaya, idan yaje ɗin zasu ƙara tabbatarwa ne. Kafin Abdalha ya ce wani abu Isa ya ce "Haba Mama ki barshi tinda ya ce komai zaiyi dai-dai mana? Mama ta ce "To sai kaje idan kuma zaka nuna min cewar ban isabane to?. Sai kuma yayi shiru yana sunkuyar da kansa. Da wannan damar Mama ta fara musu nasiha cikin iya lafazi da yasa dukkansu gano kuskuransu. "Haƙiƙa Allah subhanahu wata'ala yana kallon duk wani abu da muke ai katawa, duk wanda ya yi wa musulmi ɗan uwansa maganin damuwarsa babu shakka Allah zai saka haske a cikin ƙabarin sa, sannan duk wanda ya haɗa mutanan da suke gaba shima tamkar ya musuluntar da mutumne, shikuwa musulumtar da kafiri zuwa ga Allah ladan sa yafi duniya da abunda ke cikinta, addininmu wato addinin musulunci yana tsafta ga sauƙi, shin idan har mutum zai haɗa kan masu yin gaba zai samu lada fiye da duniya da kuma abinda ke cikinta shin to mecece duniyar kuma meye a cikin ta! Inada tabbacin cewar wannan ƙiyayyar da kukewa juna daga gurin iyayenku maza tasamo a sali... Shin ko kunsan da cewar wannan abun da kukeyi ga ba ce kukeyi? Isa da Abdalha da Zainab kowa yayi shiru. Mama ta ɗora da cewa "Tabbas ga ba kukeyi, kuma duk mai gaba a addininmu mutuƙar ya mutu bai tubaba babu shakka babu Allah zai masa hukunci mai tsanani... Zainab Isa harma da kai Abdalh nasan dukkanku kunyi karatu kuma kunsan gaskiya amma sai kuma ku ka ta keta!? Karku manta yanzu kune jagororin al'umma, dan Allah ku bani haɗin kai domin dawo da ADDINIMU ya zama guda ɗaya, ya zama addinin da Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaiyi alfarari da shi harma damu wanda muka tashi tsaye akan sa? Inaso dukkanku kuyi yaƙi da faɗin Allah a kan iyayenku domin dawowa dasu hanyar gaskiya, amma bance kuyi wa iyayenku rashin kunya ba, ku tausasa kalamamku a garesu koda kuwa suɗin ba musulmai ba ne, cewar Allah subhanahu wata'ala. Shin kun manta da rayuwar Annabi Ibrahim Alaihissalam ne? Dan Allah karku bari wannan ɗinbin alkairi ya huce mu, dan Allah ku taimaki musulman da ke ƙanƙashinku suna koyi daku, ku dinga fassara aya dai-dai da faɗin Allah, ku daina raba kawunan musulmai, Walhi kullum sai na zubar da hawaye idan na ji yanda musulmi ɗan uwansa yake cin mutuncin musulmi... Har ta kai ta kawo wai wani musulmin baya cin yankan wani saboda kawai ba aƙidarsu ɗaya ba, wasu kuma basa Sallah a masallacin da ba na ƴan aƙidarsu ba, wasu kuma basa aura taiya tsakanin juna mutuƙar ba aƙida ɗaya sukeba, hatta makaranta wai idan har ba makarantar ƴan aƙidar su bane to bazasu kai yaransuba bare kuma su kansu, a hakan kuma wai dukkkanmu musulmai ne. Dukkan musulmi ɗan uwan musulmi ne, amma yanzu abun yazama ba haka ba, domin kawai son zuciya irin na malamammu. To ina kira a garemu walhi muji tsoran Allah mu san cewar komai da mukayi yana kallonmu kuma zamuje garesa. Yanzu dukkanku kumin alƙawarin amincewa da zaku yi magana da iyayenku cikin gaskiya da biyayya? Duka suka amsa mata da cewar sunyi alƙawari, Isa da Abdalha suka gaisa kowa ya baiwa kowa haƙuri. Yayinda Abdalh ya jinjinawa Mama yana jin cewar idan suka haɗe da Momy aguri ɗaya to tabbas ADDINIMU zai ƙara samun jajir-tatun masa acikin sa. Mama ta ce "To yanzu dai Isa ku tashi ku tafi kunga dare nayi? Suka miƙe zasu tafi Mama ta ce "Kije ki rakasu mn? Ai kuwa Zainab ta miƙe cike da farincin yanda Mama ta dawo dasu hanya. A tsaye bakin motar Abdalha suka tsaya ganin Zainab ta fito yasa Isa cewa bari ya ɗauko wayarsa a ɗakinsa. Yana tafiya, dukkansu sukayi shiru Zainab ta ɗaga kai ta kalleshi taga shima ita yake kallo, ai da sauri ta kawar da kanta gabanta na ƙara faɗuwa. Sai ta tsinkawo muryarsa na cewa "Kin san wa cece Maryam? Da sauri ta ɗago tana kallonsa wanda har yanzu kallonta ya keyi, shiru tayi tana tuno a inama ta taɓa jin wannan sunan. Ganin ta kasa tunowa ne yasa ya ce "Maryam Kabir kabuga ƙawarki? Sai yanzu ta tuno da ita, sai kawai ta saki murmishi ta ce "Ban santaba sai a wannan ranar. Yana son ya ce mata wani abu amma ya kasa sai kawai ya ce "Dama ba kwayin waya da ita ne? "No bamayi. Ta bashi amsa tana kallon Isa da yake isowa gurin. Isa na zuwa Abdalha ya ce "Kice da Mama na gode? Itama ta ce "na gode. Tana tsaye a gurin har suka tafi, dai-dai za asu fita daga gidan shikuma ya shigo gidan shima cikin motarsa. Ganin motar Aliyu yasa Isa ya ce da Abdalha ya ɗan tsaya dan Allah. Abdalha na zaune har ya dawo ya ce muje. Abdalha ya ce "Ko dai shima yayanku ne baga kamar zai girmeka ko? Isa ya ce "Eh ya girmeni, amma a bokinane, kuma ba ɗan gidannan bane amma dai yanzu ya zama ɗan gida. Abdalha ya ce "Ya maka faɗa da yagammu tare ko? Isa ya ce "No ai baima ganeniba. Abdalha sake cewa "to me ya zoyi a darannan tunda kace ba ɗan gidan bane? Isa ya ce "Inaga dawowar Zainab ne ya riskeshi kasan shine wanda zai aureta, angama magana yanzu rana kawai a ke jira a sa. Da sauri Abdalha ya kalli Isa sai kuma ya sun kuyar da kansa, bai ƙara jin me isa ya kecewa ba har saida isa ya taɓashi a lamar ina zai kaisu, domin kuwa wata hanyar ya ɗauka. Cikin suɓutar baki Abdalha ya ce "Kuma za'ayi auran da ita? Da mamaki Isa ya kalli shi domin shi harga Allah harma ya manta da sunyi wata maganar aure, kuma yanzuma bai fa himci me yake nufiba sai kawai ya ce "Aura da wace? Abdalha ya waske da cewar "Aure da yarinyar da kake so mn?. A haka suka iso ƙofar gidan su Abdalha ɗin. *NANA POV* Tinda suka dawo Innah batayi maganar AJ ba, hakanne yasa Nana ce wa "Wai Innah bakiji maganar da na ce miki cewar nazo naga kaya a gidannan bane, kuma ina tunanin yaya ne ya kawo ba? Innah bata tamka mata ba. Ta ci gaba da cewa "Wai dan Allah Innah haka zamu zauna mu biyu bazamu tafi neman yaya ba, nifa harga Allah jikina yana bani cewar wani abune ya sameshi, kuma wannan abunda a ka mana nasan ba laifin sa ba ne, dan Allah Innah mn uje nemansa!? Ta ƙasa maganar cikin sha ƙwaɓa. Innah ta kalleta cikin nuna cewar ko a jikina ta ce "Idan zaki tafi nemansa ga hanya nann, sannan kuma mutuƙar Abdauljabaru ya dawo gidannan to tabbas zama a gidan ya ƙare kenan, koda kuwa shi ba zai bar gidan ba, to tabbas ni zan bar masa gidan domin kuwa gidan ubanku ne. Innah ta fashe da irin kukannan da a ke cewa kukan baƙin ciki, tabbas bazan manta da abunda yaronnane yasa a kamin ba, kuma Allah sai ya saka min, dukma inda ya shiga to in sha Allah sai ya ɗan-ɗani irin abunda ya sa a ka mana. Nana ta faɗa jikin Innah tana kuka itama ta cewa "Dan Allah inna karki wa yaya baki, Walhi bakin ki zai kamashi domin kuwa matsayin u'wa kike a garemu, kuma dan Allah idan yaya ya dawo ki tsaya ki fahimceshi na san halinsa walhi zai fahimtar da ke, karki yanke hukunci cikin fushi dan Allah Innah! Cikin tsan-tsar ɓaƙin cikin abun da wasu gin-gima gin-giman arna suka mata ta ce "Arne kuma soja wanda baisan Allah ya ce Annabi ya ce ba shine ya shigo har gidana ya ɗaya hannu ya mareni bai duba tsufana ba, Arne!.. Arne!.. Arne!.. Arne!... Wanda bai sai mutunci ba shine ya mareni duk saboda Abduljabaru, kuma tunda abun ya faru bai zo ba, badan wannan yaron da ya dinga taimaka mana da abinci ba da basu san yanzu a wani hali muke ciki ba. Innah tayi magar tana tuna lokacin da sojan ya mareta. Nana ta ƙara cewa "Dan Allah dai kiyi haƙuri bari na je gidan su Kadija na tambayeta ko da gaske yaya ɗin ya dawo. Innah dai bata ce mata komai ba har ta fita reƙe da wayar ta, tana kuma tuno Salis ko ina ya shiga, gashi ita ta manta da numbar sa da sai ta kirashi kodai shima ba lfy ya ke ba! Kallon Kadija takeyi har ta gama sanar mata da komai abunda ya samu AJ ɗin lokacin da ya dawo. "Lokacin da yaki labarin kuka ya dingayi har yana faɗuwa, kuma duk u'nguwarnan anrasa wanda zai tai maka masa koda da maganar aiziƙi ne, to ana cikin hakane wani ɗan shaye-shaye mai suna Bala ya zo gurin ya sanar masa da cewar wai wannan sojan babban wannan yarinyar da nake ganin ku tare ne yazo tare da yarinyar tana kuka ta nuna gidanku wai...wai...wai...Kadija ta kasa ƙaras sauran maganar da Bala ɗin ya ce tsabar kunya da nauyin maganar, wacce itama tunda taji maganar har kwanciya rashin lafiya tayi tsabar kishin da tayi da yarinyar. "Kadija faɗa min koma meye dan Allah karkiji komai? Kadija ta ce "Wai ci ci ci ki ciki ya mata shine babban yarinyar ya ke nemansa....📝 [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA... ✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE3️⃣1️⃣* .....Da gudu ta bar gidan bata tsaya sauraron kiran da Kadija ke mata ba har tana cin karo da mamar Kadijan zata shigo ɗakin bata ko bi ta kan ta ba ta kwasa da gudu sai gida. Ta na shiga gida ta tarar da Innah a gurin da ta barta, da sauri ta faɗa jikin innar ta na kuka ta na toshe bakinta. Cikin tsorata da halinda Nana ta shigo gidan Innah ta ce "Nana me ke faruwa? Waye ya taɓaki? Me a ka miki? Cikin kuka Nana ta ce "Innah wallhi walhi yaya ya dawo kuma kuma kuma! Sai ta kasa ƙarasawa ta sake fashewa da wani kukan. Cikin jin haushen abubda take cewa Innah ta ce "Saboda ya dawo shine kika shigo min gida da kuka kamar wacce a ka daka? To saime idan ya dawo, ai dama ni nasan babu inda yaje yana cikin garinnan, kuma in sha Allah sai Allah ya saka mana akan abinda ya sa aka ai kata mana. Cikin rashin sanin abunyi Nana ke kuka tana tsoran sanar wa da Innah abunda taji kuma kar taje abun ya ɓata mata rai! Sai kawai ta ce "Wannan sojan ne ya zo ya kamashi, wai saboda ya dawone yasa aka sakemu. Innah ta ce "To wai dan ƙundun ubansa me ya ha ɗashi da arne? Ina ruwansa da marasa sallah da har zaije ya jawo mana irrin wannan azabar? Nana ta ce "Yanzu dai Innah zanje nemansa Kadija ta ce min tasan unguwarsu harma gidan sojan, saboda haka zamuje tare kinji? "To walhi idan kikasa ƙafa kika bar gidannan da niyar zuwa neman Abduljabaru to ina tabbatar miki cewar bazaki dawo ki sameni a gidannan ba, zan tattara kayana na barmuku gida na shiga duniya ƙila a cikin duniyar na samu waɗanda zasu iya zama dani, dama ai nasan ba gidana bane gidan ubanku ne saboda hk zan bar muku gidan. Da sauri Nana ta rugomo Innah ta na kuka tana bata haƙuri a kan cewar ta fasa zuwa, "Pls Innah ki daina irin wannan zancen bai da ceba samm! Cewar Nana ta na kuka. Innah ta tashi ta bar gurin izuwa ɗakinta tana tunano ma haifin su Nana ɗin. Ganin haka yasa itama Nana bin bayanta ta na kuka, ai kuwa ta na shiga sai ga kiran Dr. Tana ɗagawa ya ce "Ina wa je! Nana ta ce "Innah Dr ne yazo wai yana wa je? Innah ta ce "Tashi kije amma karki daɗe, kuma ban yarda da zuwa ko ina ba. Dr kuwa yau dai ya zo da ƙarfin sa domin baiyana abunda ke cikin zuciyarsa a gurin hasken rayuwarsa. *GIDAN SOJA* Addu'a suka duƙufa yi dukkansu domin Allah ya kuɓutar dasu daga hannun wannan ƙaton arnan, ko wa ya manta da komai sai addu'a, wasu kuma suna karatun qur'ani. Muhammad da sauran ƴan uwan nasa wanda suma kaɗan daga cikin ƴan cikin ƙauyan Katungu ne da suka musulunta shine fa Daniyel ɗin ya haɗa dasu, sannan yaje ƙauyan ya sanar wa da iyayensu cewar ai dama idan ka ƙarɓi musulimci kuɗi a ke yi da mutum, saboda haka Solo yaje yayi kuɗi da yaransu. Hakanne yasa suka ƙara ƙiyayyar Addinin Musulunci, wanda har wasu da ɗan dama sun fara nuna buƙatarsu ta shiga addinin saboda yawan zuwan da Muhammad ɗin keyi cikin ƙauyan Katungun, amma yanzu duk sun ƙara jin sun tsani addinin da ma mutanan cikin ta. Hakanne yasa suka fara kashe duk wani ko wata Musulmi da ya shiga yankin nasu. Yanzu dai cikin ƙauyan Katungu babu dama wani musulmi ya shiga. Muhammad, Umar, Usman, Salis, Hajiya Babba, Laɗifa, AJ. Sune a cikin ɗakin rai bakwai(7) kuma dukkansu musulmai. Ko wa ƙoƙarin karanto duk addu'ar da tazo bakinsa ya keyi, banda Laɗifa wacce tun da ta shiga jikin mahaifin ta take ta kuka har yanzu, Hajiya Babba ma kam izuwa yanzu ta saddaƙar domin bata manta abunda ya ce mata ba, ga kuma ƙarar tashin motocin su da sukaji alamar sun tafi. *(Tofa!)* Gudu sukeyi sosai wanda yasa suka isa cikin garin Bokon da wuri, dubada yanda jiniyar motocin nasu ke tashi a dukkan hanyar da suka biyo, kowani mai abun ha wa ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Abun da ya ɗaure wa kowa kai ku wa shine...suna shigowa unguwar da yake ɗin suka ga al'umma a tsaye a bakin gidan, ga kuma hayaƙi da ke tashi. Ko da suka ƙarasa sai sukayi gamo da abun mamaki. Gidan wani ɗan kasuwa ne ya kama da wuta hakan yasa ya laso na kusa dashi, shima ya kamo na kusa dashi, wanda kuma gidan Comandar Daniyel ne a tsakiyar su. Ko kafin ƴan agajin suzo har kowani gida ya gama cinye wa tass. Ganin sojoji yasa sauran al'ummar dake tsaye a gurin suna kallo kowa ya ɗau na kare. Cikin tashin hankali Elixa ta fara rusa ihu har ta manta da ita ɗin wacece, ihu ta kayi tana faɗin irin dukiyar da ta ajiye a cikin gidan, su kansu sojojin mamakin wannan abun sukeyi, domin ai ba wannan gidan bane ya ka ma ta a ce ya ƙone. Shi kuwa Comandar tsabar ruɗewa bai san lokacin da ya tun kari wutar ba, duda cewar wutar ta gama cinye komai amma har yanzu tanada zafi. Kamo shi a keyi yana ƙwacewa ana ruƙoshi yana shiga. Da sauri ya ya tsaya cak yana wani tunani. Waya ya ciro ya kira ɗaya daga cikin sojojin da ya bari a wancen gidan, ai kuwa tana shiga suka ɗaga. Da sauri ya tambaye su cewar sun ƙona gidan ne? Cikin tabbatar da cika umarnin su sukace "Yess sir. Ai da ƙar fi Daniyel ya ce "Nooooooo a kashe wutar yanzu-yanzu kafin ta cinye gidan?. Cikin rawar baki suka cce "Ai muna saka wutar muka bar gidan domin kar a kamamu. Ta ke Daniyel ya sulale agurin a sume ya na sakin wayar tasa. Elixa kuwa sai ihu takeyi tana kiran sunan mijin nata. Da sauri sojojin suka saka Ogan nasu a mota suka kama hanyar asibiti, shi kuwa Samuel zafin bulet ya hanashi gane a wani hali suke ciki ne yanzu. Suna cikin tafiyane wayar dake cikin motar tayi ƙara a lamar kira daga Captain. Wato Captain ɗin dukka sojojin Benue sts, domin shi dama Comandar ne na iya barikin da yake. Da sauri na hannun damansa ya ɗaga. Cikin umarni aka buƙaci Daniyel a cikin garin Benue sts yanzu-yanzu. Ai kuwa bai tsaya jin me zai ce masaba ya kashe wayar. Cikin sauri sojan ya sanarwa da Elixa abunda ke faruwa. Cikin tashin hankali ta ce "An ƙona wancan gidanne? "Sojan ya ce ""eh an ƙona. Ai ta ke ta sake sakin wani sabon kukan, sai yanzu taga wawtarsu na sawa a ƙona gidan. Sojan ya ce "Yanzu fa dole saide muje offece ɗin Captain idan kuma ba haka a kwai matsala. Da sauri Elixa ta kalli mijin nata cikin jin haushin shawarar da ya basu ta ɗauki ruwa mai sanyi ta watsa masa, ai kuwa ya saki wata ajiyar zuciya yana far kawa da da wani ihuu! "No Pls don't se Yes Please Elixa don't . Cikin ruɗewa ya fara faɗin (ƙaryane karkice min gaskene dan Allah Elixa karkice hakane) Cikin tashin hankali ta ce "Pls dan Allah ka nutsu kaji halin da muke ciki. Nan fa Daniyel ya rikice, ganin haka yasa Elixa sanar masa da umarnin Coptaing. Chk ya tsaya da kukan yana kallon dreban nasa, sai kuma ya kai kallonsa izuwa hanyar da suke bi, ta ke cikinsa ya bada wani sauti. Bai ƙara cewa komaiba har suka shiga cikin Makurdi. Saboda tabbatarwa Elixa ta ce da dreban yabi ta ƙofar gidan nasu sugani. Ai kuwa suna shiga unguwar suka tarar da ƙofar gidan cike damutane, ga ƴan kwana-kwana har sun isa gurin sun fara aikinsu, sannan kuma kamar motar sojoji suka hango a gurin harda police, nan fa hankalinsu ya ƙara tashi. Ta ke Elixa ta shiga tunanin idan Sarah tana cikin gidan fa! Shikuwa Daniyel gabansa ne ya shiga faɗuwa yana tinanin Allah dai yasa dukkansu kowa ya ƙone, domin kuwa idan har ba hakaba to tasa ta ƙare, lokacin da ya hango motar police da sojoji kuwa take yasa suka juya da mutarsu suka koma hanyar da zata sadasu da office ɗin Captain. *SARAH POV* Da gudu ta fita ta ƙaramar ƙofar gidan kasan cewar dama tasaba bi ta gurin idan zata fita, kuma duk gidan babu wanda yasan tana da makullin ƙofar. Gidan su Usha ta nufa babu ko taƙalmi a ƙafarta, dukda cewar tsakanin gidan su Usha ɗin da gidansu a kwai ta zara hakan baisa ta hau abin hawaba. Sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa gidan. Mai gadin gidan na ganin ta a cikin wannan halin ya buɗe mata get yana mai cewa sannu. Bata ko tsaya bi ta kansa ba ta shiga gidan da gudu. Tana shiga palorn gidan sai ga mamar Usha ɗin wato Titi cikin shigar ta zata fita unguwa. Da gudu ta faɗa jikinta tana kuka tana nuna mata hanyar waje. Jin kukan ta ne yasa Usha dake ɗakinsa shima ya gama shiryawa kenan da alamar dai tare zasu fita. Da gudu-gudu ya sauƙo yana ƙarasowa gurin yana mai jawo fuskar Sarah ya ce "Menene? Me a ka miki? Itama Titi cikin tsoron kodai wani abune ya samu ƴan gidan nasu ta ce "Sarah meke faruwa ne? Ki nutsu kiyi magana mn? Da sauri Usha ya ɗau ko ruwa ya bata, ai kuwa take ta sha kusan rabi, wanda dama tana buƙatar ruwan. Sai a lokacin suka kula da yanayin ta, tayi baƙi ta rame ta koma kamar wata ƴar almajira. Alokacin Titi ta ƙara shiga tashin hankali. Usha kuwa ya jawota jikinsa yana kwantar mata da hankali. Sai da ta ɗan samu nutsuwa sannan ta ce "Anty Titi kinsan Solomon? Zumbur Titi ta miƙe tana nuna Sarah cikin tashin hankali ta ce "Me ya faru? Sarah ta ce "Yana raye bai mutu b"...Ai kafin ta rufe baki Titi ta ruƙota jikinta tana neman ƙaryata ta ce "Me kikesone kicemin? Ta ke Sarah ta kwashe dukan abunda ya faru ta sanar wa da Titi da Usha. Cikin tashin hankali Titi ta ce "Solomon bai mutuba? Yana gidan ku? No ƙaryane wannan ban yarda ba. Cikin mamaki Usha ya ce "Dama bayan ke da Daddy kuna da wani ɗan u'wa ne? Da sauri Titi ta ce "Yes mu ukune amma ɗayan ya mutu, wanda shine mafi hankali da tausayi a cikinmu, duk lokacin da na tuno da Solomon sai nayi kuka, idan na tuna da abunda ya faru a tsakanin na da shi kullum sai nayi kuka, yanzu gashi ya mutu "No bai mutuba sai de ko yanzu Daddy ya kashe su, amma idan kina son ki ga ɗan uwanki kizo muje gida walhi yana can kuma Daddy zai kashe su. Ai da sauri Titi da Usha suka bi ta a baya, mota suka ɗau ka suka nufi gidan cikin tashin hankali, wanda shidai Usha abun ma mamaki yake bashi, domin har yanzu bai gano komai ba. Koda suka isa gidan suna zuwa sojojin da suka saka wutar suna barin gurin, ai da sauri Titi ta kira ƴan kwana-kwana, shi kuma Usha ya nufi police ɗin yan sanda, su kuma police jin cewar gidan Comanda ne yasa suka kai zan cen sama, ai kuwa kafin ka ce me, sai ga motocin ƴan sanda haɗi da na sojoji, suna zuwa suka tarar da motar ƴan kwana-kwana har sun iso sun fara aiki. Titi ta tabbatar musu da cewar a kwai mutane a cikin gidan, hakanne yasa suka fara aikin cikin sauri, yayinda wasu daga ciki kuma suka shiga cikin gidan. Wutar sosai ta ke ci, hakanne yasa wanda suka shiga ɗin suka kasa gane ko wacce hanya da zasubi domin shiga gidan, kana ganin wutar kasan sakawa a kayi dubada yanda ko ina keci. Abun mamaki an duba ko ina na gidan babu ko wa, kowani loko da saƙo anduba babu wani ɗan adam hakanne yasa suka fito suna sanarwa da Titi, ai kuwa ta ke Sarah ta sake kwatanta musu inda ɗakin yake. Ai kuwa cikin ikon Allah suka ga ɗakin, suka ɗauki wani abu mai kama da zare wanda da irinsa suke buɗe ƙofa. Saida suka sha wahala sosai kafin ƙofar ta buɗu. Ai kuwa saiga bayin Allah a yashe a gurin, wuta ta kusa cinye saman ɗakin wasu daga ciki sun suma, wasu kuma sun fita a haiyacinsu, har wuta ta fara faɗowa daga sama a kansu. Da sauri a ka fara fita dasu cikin sauri. Suna zuwa ƴan sanda suka kwashesu a ka sakasu a motoci a ka nufi asbiti da su...📝 *Muje dai zuwa* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA ✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE3️⃣2️⃣* .....Da sauri a ka ƙarɓesu a asbiti Titi ta ce "Usha da Sarah su zauna a gurin su Salis ita kuma tananan zuwa yanzu. Tinda ta fita bata dawo ba, sai lokacin Usha ya ce da Sarha ta shiga toilet ɗin asibitin tayi wanka, ita ku wa sai kallon fuskar AJ takeyi wanda idunsa ya kumbura ga kuma bakinsa shema kumbure tsabar duka, batasan lokacin da wasu diraran hawaye suka biyo kuncintaba. Usha ne ya sake yin magana a karo na uku, sannan ta kalleshi ta ce "Wannan shine AJ Daddy ne yasa a ka masa hk. Tana faɗa tabar gurin cikin kuka ta nufi toilet ɗin shi kuwa Usha yabi ɗan yaron da a kace shine AJ da kallo. A fili ya ce "To shi kuma AJ ɗin me ya kawo shi gidan da har za'a haɗa da shi, sannan yana mamaki ganinsa ƙaramin yaro. Ɗakin da su Sarah suke a ciki ne a ka kwantar da Salis da laɗifa da AJ. Sai kuma ɗaya ɗakin a ka kwantar da Muhammad da Hajiya Babba wacce duk tafisu jigatu wa domin ita wuta ta faɗo mata daga sama. Sai Umar sai Usman. Hannun yayan nata ta kamo a cikin na ta, sannan ta ɗora a fuskarta tana rusar kuka tana cewa "Pld Solo ka tashi walhi ina buƙatar ka a rayuwata Pls And pls, kuka takeyi sosai wanda kana gani sai ka tausaya mata tsabar yanda ta fita a haiyacinta, tana cewa "Dama ashe kana raye, dama baka mutuba? PLs Solo. Amma ina baima san tana yiba. Likitane ya shigo ɗakin yana mai bata haƙuri a kan ta daina kuka anjima kaɗan zai farka babu abunda ya samesa, da kyar dai Titi ta bar ɗakin. Da kudu-kudu ta shiga motarta ta bar asibitin tana tafiya tana kuka har ta isa gurinda zataje. *DANIYEL POV* Suna isowa yasa aka wuce da Samuel asbiti domin har yanzu kuka yakeyi yana kiran zafi zafi. Cikin tsoro ya tura ƙofar office ɗin ya shiga, yana shiga ya tarar da manyan Sojoji a zaune a gurin ko wa fuskarnan a murtuƙe, kasa zama yayi sai bin kowa da kallo ya keyi. Caraf idonsa ya sauƙa a kan Titi wacce ke zubar da hawaye tsabar rikici. Ɗaya daga cikin sojojin ne ya umarce sa da ya zauna, ai kuwa da sauri ya zauna yana ci gaba da kallon ƙanwar tasa cikin mamakin me ya kawota nan gurin. Wani ya kalli Titi ya ce "Mai-maita abinda kikace a kan ɗan uwanki? Ai kuwa cikin kuka ta fara zaiyano komai da tasani akan ƙulle ɗan uwansu da yayi, sannan ta ɗora da wutar da yace a saka a gidann, sannan ta ce "She kara kusan ashirin kenan yana kulle wai dan saboda kawai ya koma yin Sallah, kuma bama shi kaɗan ya kulle ba mutum uku, sannan kuma ya kamo family ɗinsa suma ya haɗa a gurin zai ƙone. Titi ta ƙara sa tana fashewa da wani sabon kukan. Kowa dake gurin suka zubawa Daniyel ido cikin tsan-tsar mamaki, da yake a cikin gurin harda Musulmai. Wani ya ce da Daniyel "Kaji abinda a ka ce shin hakane ko ba haka bane? Ya ce "No No is my brother"..."Na ce hakane ko ba haka ba ne? Cewar sojan cikin ɓacin rai wanda shima musulmi ne kuma a gaba dashi ya ke?. Ganin yaƙi yin maga ɗayane yasa Captain ɗin cewa ya cire rigar jikin sa, ta ke ya cireta ya ajiye. Captain ya ce "A tafi dashi kafin oga ya zo( Wato shugaban sojojin gaba ɗaya) haka a ka tafi dashi ya na sanar musu da cewar ƙaryane shi daii bai yi komai ba. Captain ya ce da Titi ta koma asbiti idan har oga yazo za'a nemeta daga ita har ɗan uwan nasu, haka ta amsa cike da jin daɗin za'ayi adalci. *ABDALHA POV* Kallon su tayi tana son tabbatar da abunda Isa ya tsara mata ta ce "To Abdalha kasan da cewar ba kaine ka saceta ba to menene yasa kace kaine? Abdalha ya ce "Momy idan nafito na ce bani bane nasan babu wanda zai yarda dani shine yasa kawai na ɗauki laifin. "Yanzu dai ai tafito ko? Ya ce "Eh Momy "To masha Allah tundade yanzu ta dawo kuma cikin ƙoshin lfy ko? Isa Abdalha suka haɗa baki ƙurin cewa Lfy lau ta dawo. Momy ta ce "To yanzu bari na kira Abbanku sai ka masa bayani domin har yanzu fushi ya keyi da kai sosai. Tin daga nesa Shek Kabir kabuga ya fara ce wa "Duk naji bayanin da kukeyi kuma ka sani idan ma kayi hakane da wata manufa to ina dai-dai da kai, kuma ka ce da wannan yaron dake kusa da kai ya tashi ya bar min gida bana son ganin sa. Cikin mamaki suka kalli gurin da Daddy ke sauƙowa rai a mugun ɓace. Abdalha ya kalli Isa shima Isa ya kalleshi sai Abdalha ya dawo da kallonsa izuwa gurin Daddy. Ya buɗe baki zaiyi magana saiga Sadiya da Nusaiba da Maryam duk sun fito daga ɗakunan su dalilin jin Daddy na faɗa. Basu kula da baƙon dake tare da Abdalha ba saida suka nemi guri zasu zauna idon Nusaiba ya sauƙa a kan Isa da ya kafesu da idu. Ai da wani irin tsalle Nusaiba ta meƙe tana mai kare jikinta kasan cewar kayan barci ne a jikin ta. Itama Sadiya ta miƙe a kunyace ta bar palon. Ita kuwa Maryam guri ta samu ta gyra zama ko a jikinta. Kallon da Abdalha ya watsa mata ne yasa ta saki wani siririn tsaki ta kawar da kanta daga kallonsa. Kawar da kansa yayi daga kallon ta ya dawo da kallonsa zuwa ga Daddy ya ce "Pls Daddy kayi haƙuri tundade ai yanzu yarinyar sa tadawo kaga ai komai ya wuce. Daddy ya ce "Komai ya wuce amma ya barmin gida domin nan gidan ba gidan ƴan bidi'a bane, idan kuma kanaso daga kai harshi ranku ya ɓaci to? Da sauri Momy ta ce "Tirr da irin wannan halyyar taka, idan har haka sunna ta koyar da kai to tabbas ba sunna kakeyi ba. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana koran baƙo daga gidan sa? Shin yana gaba da kowa? Koda mutum ba musulmi bane yana kywatata zamantakewar su, kuma muma haka ya koyar damu, dan Allah kayi aiki da iliminka ka ganar da jama'a gaskiyar da kuke ɓoyewa? Daddy ya ce " Bakisan waye Adamu bane shiyasa kike cewa shi ɗin mlm ne . Da sauri Momy ta ce "Kenan a kwai wani abu a tsakanin ku bayan babbancin aƙida? Daddy bai tsaya saurarontaba ya bar palon cikin ɓacin rai. Momy ta baiwa Isa haƙuri sannan ta musu wa'azi mai ratsa zuciya, sannan Isa ya bar gidan cike da tunanin to meye tsakanin Mlm da Daddy. Ita kuwa Maryam duk abunda a keyi tana zaune a gurin tana jin komai dama ita kaɗai ce ta fita Zakka a gidan, domin babu ruwanta da wannan faɗan nasu, sannan ta kafe Isa da ido duk ta hanashi sakewa a gidan har saida ya fita. Tana zaune a kan gadon ta suna chatintg da Nana yayin da Nana ta sanar mata da cewar mamarta ce ta ce wai idan suka yiwa Abdalha haka to ko anyi auran zai dinga ganinta da mutunci shi fa yasa muka masa wannan cin mutuncin. Ita dai Maryam bata ce komai ba alokacin, sai daga baya Nana ta sake kiran Maryam wai har yanzu Abdalha bai dawo bafa? Ita kuwa Maryam ta dinga mata dariyar, to shine fa yanzu take sanar mata da cewar ai Abdalha ya dawo da Zainab yanzu hk ma tana gidan uban ta, hakanne yasa Nana rikicewa sosai domin tana son Abdalha sosai. Suna cikin hira da Nana taji ana buga mata ƙofar ɗaki. A ɗan tsorace ta ce "Waye? Shiru babu amsa sai ta sake cewa "Wai waye ne cikin darannan ke haka ta nufi ƙofar tana surfa masifa Walhi Nusaiba kin cika taƙurawa mutum ke babu dama a ɗauki aron abun ki sai kin hana mutum sakew"...Ai bata ƙarasa ba sukayi ido biyu da Abdalha dake tsaye yana sakar mata harara. Cikin tsoro ta ƙara sa buɗe masa ɗakin tana sun kuyar da kai. Ɗakin ya shiga ya zauna a bakin gadon yana bin ɗakin da kallo cikin nuna ƙyama,. A hankali ta kalleshi ganin yanda yake ya tsine fuska yasa ta saki tsaki wanda yasa Abdalha ɗin jin ta. Suna haɗa ido ta rufe baki tana girgiza kai. "Ina wayarki? Ya jefo mata tambayar da sauri ta ƙaraso gurin da yake ta miƙa masa. Ya ƙarɓa ya shiga gurin numbobi ya dawo gurin hotuna. Ganin ya rasa yanda zaiyine kuma baisan mai zaicemata ba ya miƙa mata wayar, kafin ta ƙarɓa kiran Nana ya shigo. Yana son ya tambayeta numbar Zainab ne amma ya kasa. "Wacece mai kiranki cikin dare? "Ƙawata ce" Bai ƙara cewa komaiba ya kama hanya zai fita Maryam ta ce "Yaya wani abun kake sone? Bai ce komai ba ya bar gidan gaba ɗaya izuwa nasa gidan duk ransa a ɓace. Washe gari cikin garin Kano da ma kewayanta gaba ɗaya suka tashi da labarin dawowar Zainab Ambato. Hausawa suka ce wai gani da ido shine sheda. Ai kuwa dai sai ga Zainab da kanta tana bada labarin komai da ya faru cewar ba Abdalha bane ya saceta shine ma ya cetota daga gurin su. Cikin ƙanƙanin lokaci saƙon yazo ko ina, ƴan jarida da gidajen rediyo dana tv duk sun saka hirar, kasan cewar ƴan jarida ne da kansu sukayi hira da ita. Tofa ana wata sai ga wata. Bayan samun wannan labinrin ne kuma Mlm Adamu ya ce shifa sai an masa iyaka da shek Kabir kabuga, saida ɗan sa Isa ya tsaya sosai kafin abun ya lafa. Ƴan gari kuwa kowa yana jajanta abun, to meyasa Abdalha zai ceceta kodai yana sonta ne. Aliyu kuwa tuni ya nemi da iyayensa akan a saka ranar bikinsa da Zainab domin jikinsa nabashi cewar zai iya rasata. Ai kuwa babu wata-wata a ka saka rana wata uku masu zuwa. Labarin bikin ya bazu ko ina. Lokacin da Nana da mamarta sukaga wannan labarin na dawowar Zainab sunyi ta kaici sosai, domin kuwa sunsan yanzu Abdalha ya musu nisa. Abdullah kuwa Daddy ya haƙura da duk abunda ya faru, amma har yanzu babu shi babu Mlm Adamu. Sannan ya sake umartar Abdalha ya koma gurin Nana amma ya ce ina shi dai yanada wacce ya keso, idan aka ce wacece sai ya ce ai basu gama dai-daitawa, yayinda shima isa ya tsunduma soyayar Maryam sosai da sosai, hakanne yasa ya sanarwa da Zainab, ita kuma da yake yanzu suna waya domin tinda ta dawo ta kira ta kuma kusan kullum sai sunyi waya, ta bashi numbar Maryam kuma cikin ikon Allah itama ta ƙware masa, amma soyayar ta kasa baiyana. Soyaya ya ce mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin Maryam da Isa wanda ta wuce katance. Nusaiba da Sadiya kuma dukkansu kowacce ta fitar da zaɓinta har an saka rana nan da wata biyu masu zuwa. Zainab kuwa daga dawowarta ta sake yin wata ƙasidar mai zafi wanda yasa kowa hawaye saboda tayi ƙasidar ne akan tarihin Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, tayi bayanin yanda yake zamantakewar sa da al'umma. Tabbas ƙasidar ta karɓo a gurin bayin Allah. Amma ai masu iya magana sunce ranar wanka ba'a ɓoyan cibi. Isa da kansa ya tun kari Abdalha da zancen soyayar sa da Maryam, ai kuwa Abdalha yaji daɗi domin wannan hanyar itace mafi dacewa da zasubi su gano ko dai wani abun ya taɓa faru ne a baya. Abdalha nason ya masa maganar Zainab amma yasan babu kyu nema a cikin nema, domin kuwa an saka ranar Zainab,. Amma haka ya daure ya sanar masa da cewar yana son Zainab. Cikin mamaki Isa ya ke kallon Abdalha domin bai taɓa kawo haka a ransa ba. Abdalha ya sanar masa da irin sonsa yake mata tun ba yanzu ba, Isa ya gamsu amma ya ce kasan dai auranta yanzu bai huce wata biyu ba. Haka dai suka sanarwa da Mama ita kuma ta ce ya fara tuntubɓar Zainab domin kuwa itace ta kawo Aliyu kuma Aliyu ɗan gidane, ga kuma an kusa, ita dai batasan abun yi ba. Bai samu Zainab sunyi mgn ba ya tunkari mahaifinsa da maganar? Zaune suke a palon harda su Maryam da Nura wanda ke karatu a gaban Nusaiba ya na bada hadda. "To muna sauraronka wacece kuma ƴar gidan waye a ƙasar nan tamu? Shek Kabir kabuga ya faɗa yana washe baki domin jin ƴar gidan wani shahararren malamin a cikin malaman sunnha ya samo. Itama Momy murmushi ta keyi tana jiran jin sunan surukar tasu. Ita kuwa Maryam da tasan kwanan zancen domin kuwa Isa ya sanar mata da komai, sai rintse ido takeyi kamar itace zata sanar musu ɗin. Abdalha ya ce "Am am damafa fa kowa bace sai sai sai amma Zainab Ambato ce ƴar ƴar gidan mlm Adamu. Ya faɗa yana shafa ƙyeyarsa Tsint palon yayi harda Nura dake karatu domin sunji sunan wacce ya kira, ita kanta Momy saida ta tsorata, Sadiya kuwa ido ta ƙwalalo waje, Maryam kuwa rintse idon ta sakeyi tana karanto addu'o'in da suka samu damar isowa gareta. Shi kuwa Abdalha ɗagowa ya yi domin ganin fuskar Daddy...📝 *Please comment ɗinku shine zaisa mugama da wuri* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA... ✍️* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE3️⃣3️⃣* ..... Daddy ya haɗe fuska babu a lamar wasa ko sakin fuska tsanar ɓacin rai ne kawai ke yawo a kan fuskarsa, tashi yayi ya bar palon ba tare da ya tanka wa kowa ba. Daddy na fita Momy ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Abdalha wanda idonsa duk sun cika da ruwan hawaye ganin yanda Daddy ya ƙi tamka masa. "Abdalha me kake nufi da wannan batun na ka? Kanada hankali kuwa? Kana ganin yanda tsakanin ku da ita babu jituwa amma zaka bijiro da wannan zancen har kana iya kallon ƙwayar idon Daddy ka ce wai ƴar gidan Malam Adamu kakeso, to ko ni ban aminceba domin wannan abun zai iya haifar da rikici mai tsanani wanda dukkanmu ba zai mana daɗi ba. Cikin karyewar murya ya ce "Sorry Momy amma gaskiyar kenan na faɗa muku, kune kuka tambayeni wacce na ke so kuma ni ita nakeso kuma ita zan auura, sannan kuma yayan ta wato Isa shima sun dai-dai ta Maryam, saboda haka Momy dan Allah ki goyi bayan wannan abun domin mu kawo ƙarshen wannan matsalar. Maryam najin abunda Abdalha ya ce ta miƙe tsaye da gudu ta bar palon, su kuwa sauran kallon ikon Allah sukeyi wai Maryam da Isa, to ya zatayi da wanda ta ce shi takeso. Abdalha na faɗar haka ya tashi ya bar Momy sake da baƙi ta hanci tana kallonsa. "Abdul" Abdul" Momy ke zabga masa kira amma ya sakai ya bar gidan cikin jin haushin wannan ƙiyayyar da ke tsakanin iyayen nasu. Motarsa ya shiga da niyar zuwa gidan sa, sai ya tuno da zancen Mama "Su iyaye ba abin wasa bane, Addinimu bai amince da ƴaƴa su dinga tsaurara kalamamsu a kan iyayeba koda kuwa suɗin suna aikata abinda Addini bai yarda da shiba, ba'a kace kamusu biyeyya akan abunba, sannan ba'ace ku tausasa kalamanku agaresuba. Shiru ya yi yana tabbatar da wannan zance sai kawai ya fito daga motar ya koma cikin gidan. A zuciyarsa yana cewa yau wa'azi na zai fara daga gida, kuma in sha Allah sai kowa ya fahimceni. Momy ku wa mamakin jin abunda Abdalha ya ce ta ke yi, wai Maryam ma sun dai-daita da Isa. Kallon Nura Momy tayi ta ce "Nura kira min Anty Maryam yanzu. Da sauri ya miƙe yana ɗan sakin dariya. Kafin Nura da Maryam su zo Abdalha ya shigo cikin palon kai a sunkuye. Yana zama saiga Maryam ta re da Nura ta sakoshi gaba yana kuka. Da sauri Nura ya nufi gurin Abdalha ya na share hawaye domin kuwa yasan shikaɗaine zai rama masa. Kafin Abdalha ya ce wani abu Sadiya ta ce "Yanzu-yanzu daga shigar sa ɗakinki har kin sa kashi kuka, kawai dan ya je ya miki wasa, kinji kunya walhi. Cikin rashin kunya ta ce "To ni abokiyar wasar sa ce da zaije har ɗakina yana min dariya, ko ni ɗin mahaukaciyar ce? Maryam ta faɗa tana ji kamar ta ɗauke Sadiya da mari. Momy ta kai kallonta ga Maryam ta ce "Kin kyuta Maryam, kici gaba da cin zalin ƙaninki karki fasa. Momy na faɗa ta dawo da kallonta izuwa ga Abdalha. Maryam da Sadiya kuwa sai hararar juna sukeyi, Sadiya tana jin cewar yau da Abdalha baya gidannan da sai ta saukewa wannan yarinyar abunda ke kanta. Abdalha ya sharewa Nura hawaye yana kallon Maryam. Momy ta ce... "Karna ƙara jin wannan maganar ta auran ka da Zainab da kuma shi Isa da Maryam ɗin, kuma ka tashi ka je ka ba Daddynku haƙuri yanzu nann? Momy na faɗa ta miƙe zata bar gurin Abdalh yayi saurin cewa..."Momy ina sonta kuma ita nakeson aura, shin hakan bai dace bane? Cikin tsananin mamaki ta ce "Eh bai daceba, kuma karka sake min wannan maganar, kema kuma karna sake jin kiyi magana da shi yaron. Momy ta faɗa tana nuna Maryam cikin ɓacin rai. Da sauri Maryam ta gyaɗa kai tana jin cewar ai ku wa ba zata saɓu ba. Cikin ƙarfin hali Abdalha ya ce "To Momy a kam me? Ya ci gaba da cewa..."Haba Momy karkema ki zama karmar Daddy mana, kecefa kike ƙaramin ƙaurin gyiwa akan abunda muke aikatawa, amma yanzu kema kina so kiyi hani da abunda Allah bai hanaba. Dan Allah Momy ki tayani shawo kan Daddy ya gane cewar badon ɓacin ransa zanyi ba. Momy ta kalli Abdalha taga hawaye sun wanke masa fuska ta kawar da kai ta ce "Abdalha duk abunda zaka aikata mutuƙar babu yardar iyayenka to wannan abun ba zai taɓa albarkaba, kuma kaima kasan da haka, amma yanzu abinda na keso da kai shine..."Kaje ka samu amincewar daddynku idan har ya yarda to nima na amince. Abdalha ya ɗaga kai ya kalli Momy ya ce "To amma Momy kema ki tayani masa bayani mana ko zai sauƙo da hanzari? Da sauri Momy ta ce "A'a yanzu idan ba sokake dukkanmu ran kowa ya ɓaciba to ka je da kanka. Abdalha ya ce to Momy na gode sosai kuma zan dage da addu'a domin Daddy ya yarda. Momy ta katseshi da cewar "Ita yarinyar ta yarda zata aureka ne? Kuma iyayenta sun amince? Abdalha ya sauke wata a jiyar zuciya ya ce "itama mahaifinta ne kawai matsalar, amma mamarta ta yarda. Saide kuma.... Sai yayi shiru yana sosa ƙeya. Momy ta ce "Uhum sai de kuma me? Abdalha ya ce "Momy har yanzu fa ban ban sa sa nar mata ba. Momy ta ce "Ban gane baka sanar mata ba? Kafin Abdalha ya yi magana sai jin dariyar Maryam sukayi. Dariya ta keyi sosai ka kace sabuwar kamu ce. Ta ce "Momy Yaya fa yana nufin bai sanarwa da Zainab ɗin cewar yana sontaba. Sadiya ma abun ya bata dariya amma ta shanye kayarta a cikin ta. Galala Momy ta ke bin Abdalha da kallo ta ce "Da gaske? Ya harari Maryam ya ce "Umm, amma ai tasan ina sonta kuma itama haka dama kawai kune nakeso kuyarda. Momy ta ce "Allah dai ya kyuta. Tana faɗa tabar musu palon itama Maryam ta tashi da gudu ta koma ɗaki. Abdalha ya saki dariya yana kamo hannun auta Nura suka nufi ɗakin Daddy. Haka dai Abdalh ya ci gaba da shawo kan Daddy amma Daddy ya ce "Mutuƙar shine zai masa aure to bazai aura masa ƴar gidan Malam Adamu ba. Ɓangare ɗaya kuma har zuwa yanzu bai sanar da Zainab cewar yana sontaba, amma dai yana nuna mata alama kuma itama tana gane wa. Sai a kayi Sa'a itama ta na sonsa, saide kuma ya makara domin yanzu haka lokacin auranta matsowa ya keyi. Abdalha kuwa shi ya ma manta da cewar an kusa auran Zainab, burinsa ma hsifinsa ya yarda sannan ya tunkareta. Yanzu haka auran Zainab ya rage wata guda da kwana huɗu, amma har yanzu babu wani canji a gurin Daddy. Abdalha kuwa yanzu hira sukeyi da Zainab ta waya Sosai, amma dai bai furta mata kalmar soba. Haka suma Sadiya da Nusaiba auranmsu saura wata ɗaya da kwanaki. (Wannan kenann) *BENUE*. *ASIBITI* Cikin aminci Allah jikin marasa lafiya yayi sauƙi. Yau kwanansu shida a asibitin kuma yaune za'a sallamesu. Dama dukkansu jikinsu yayi sauƙi Hajiya Babba ce dai tafisu shan wahala, sai kuma Laɗifa itama da ta samu buguwa a ƙafarta. A.J kuwa lokacin da ya farfaɗo sunan Innah ya fara kira yana mai sakin wani sabon kuka, amma sai yayi ido biyu da Sarah a bakin gadonsa tana sakar nasa murmushi. Tin baya sake mata hardai ya fara bata haƙuri domin kuwa kunyarta ya keji, kullum idan sun zauna sai yata bata haƙuri ita kuma ta ce ta haƙura ai dama bai mata komai ba. Cikin kwana biyu har suka sake sakewa da juna, Sarah kuwa duk lokacin da ta ganta a gaban AJ ɗinta sai wani sanyin daɗi ya mamaye ta. Tana son AJ sosai sonda bata san asalinsa ba, tanada tarin tambayoyi da take son masa amma tsabar farin cikin da take ciki na ganin sa cikin ƙoshin lafiya yasa duk ta tattara ta ajiye a gefe guda. Titi da yayanta Muhammad kuwa kuka suka sha sosai tana bashi haƙuri akan abunda ya faru, shima yace babu komai. Salis ma ya samu sauƙi so yake a sallamesu yaje ga masoyiyarsa, laɗifa kam ganin babu wanda yaji ciwo sai ita sai kawai ta ƙara lanƙwaɓewa sai zuba shaƙwaɓa takeyi, Ga kuma haushin yanda taga Sarah na mannewa AJ kamar ta sanshi, sannan ga ɓakin cikin rashin Samuel ɗinta, ko yanzu yana wani hali harbin da a kamasa!. Umar da Usman ma duk sun dawo haiyacin su. Cikin sauri Dr ya shigo ɗakinda suke tare da wasu manyan sojoji, suka yiwa Titi da Muhammad tambayoyi game da Daniyel da kuma abunda ya faru. Ai kuwa Titi ta kwashe komai ta sanar musu. Dr ya basu sallama sannan a ka haɗasu da masu kula dasu harna tsahon lokaci, kuma suka tabbatar musu da cewar za'a buƙaci ganin su a kowani lokaci. Dr ya kamo hannun Salis ya ce "To Allah ya ƙara lafiya , saide a dinga kula da Hajiya domin na kula tana cikin damuwa, kuma idan wani abu ya faru za'a iya nemana. Salis ya saka masa numbar sa sannan sukayi sallama. Anfito za'a tafi AJ ya ce shi abarshi ya tafi gida domin kuwa har yanzu a tsorace yake. Yasan meye aure kuma yasan meye mutuwa kuma ya gane cewar yanzu idan bai rabudasu Hajiya Babba ba to tabbas a kwai matsala, wata zuciyar kuma tana tuno masa da miliyan hamsin ɗinsa. Salis ya ce "No kazo muje gida idan kayi wanka kaci abinci ka huta sai na rakaka? Sai a lokacin komai ya dawowa Hajiya Babba. Ai kuwa cikin sauri ta ce "A'a ai tunda kaji yace gida zaije to ai kawai abarshi ya tafi, domin ko ya biyomu bazai samu nutsuwa ba, kawai ya je, Allah ya kiyaye hanya. Hajiya ta ƙara cikin rawar murya kamar mara gaskiya. Laɗifa ma ta ce "To dama me zaije ya mana a gida bayan suma sunada nasu gidan, kawai ya tafi abunsa. Ta faɗa tana hararansa. Sarah da Usha da Titi dai basu san me a ke cewa ba amma sun lura da cewar AJ ne keson tafiya gidan su. Muhammad ma ya sa baki a kan yazo amma Hajiya Babba ta ce sam bazaije ba, abun ya bawa Salis maku. Ya ce "Wai Hajiya ko kin manta da cewar AJ dreban kine? Cikin sauri ta ce "Eh na sani yanzu na bashi hutu harya warware. Kafin Salis ya sake magana Sarah ta ce "Pls My AJ karka ƙara tafiya ka barni dan Allah Pls kazo mu tafi. Take Hajiya Babba ta kalli AJ shima ya kalleta, sai kuma ya tuno da dokokin auransu, ita kuma gabantane ya faɗi jin kamar Sarah ta san shi. Laɗifa ce ta ƙwace hannun AJ daga na Sarah ta na cewa "Rabu dashi ya tafi umma ta gai da Aish. Cikin dabara Hajiya Babba ta yiwa AJ magana da ido alamar ya tafi zasuyi magana ta waya. Haka kuwa a kayi badan Sarah ta soba suka nufi gidan Hajiya Babba baki ɗayansu. Kowa yayi wanka sannan Muhammad da su Umar suka je shagon aski a ka gyara musu fuskoki aka dawo gida aka fara hirar bayan saduwa amma banda Hajiya Babba. Hajiya Babba ɗakinta ta shiga ta rufe da maƙulli sannan ta fara zuwa da dawo a cikin ɗakin cikin neman mafita. Afili ta ce "Na shiga uku ni Aisha wannan wani irin masifa ne ke nufoni, yanzu dai a zahirin gaskiya inada aure kuma gashi tsohon mijina ya dawo, to yanzu a ƙaidar Addinimu ko da nasa AJ Ya sakeni to ai dole sai an ƙara ɗaura wani aura. Wata zuciyar ta ce "To kawai ki sanar masa da cewar kinyi aure amma mijin ya mutu sai kawai a ɗaura muku wani auran. Ajiyar zuciya tayi sai kuma ta ce "To Salis da Laɗifa fa ai sunsan banyi aureba, kuma idan suka sani a kwai matsala. Cikin tashin hankali Hajiya Babba ta fashe da wani sabon kuka tana ɗoraj hannu a kai tsabar rashin ma fita. Muhammad kuwa ganin Hajiya Babba mata gurinne ya kalli Salis ya ce "Ina Aisha? Kafin yayi magana Titi ta ce "Solomon Pls".... Kafin ta ƙarasa Salis ya ce "Pls Anty Titi not Solomon is Muhammad. Ya faɗa cikin wasa ai kuwa dukkansu suka fashe da dariya, Titi ta ce "Ok Oga Salis naji Muhammad. Titi tayi gyara murya ta ce "Wai Hajiya ita aisha ɗin tunda solom or sorry Muhammad ya tafi bata sake yin wani auran bane? Ko dama Addinin naku baya yarda idan mijin mutum ya mutu yayi wani auran? Gaban Muhammad ne ya yanƙe ya faɗi, domin kuwa tambayar da ya keson ya yiwa Salis da laɗifa kenan amma ya rasa ta ina zai fara....📝 *TOFA! ANA WATA SAI GA WATA* *BY S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE 3️⃣4️⃣* .....Da sauri Salis da Laɗifa suka kalli juna alamar farincikin da suke ciki jin abunda sukayi yau zaiyi rana. Salis ya saki ajiyar zuciya ya na tuno irin rikincin da suka sha a kan hana mahaifiyar tasu aure ashe hakan alkairine a rayuwarsu, idan bai mantaba zai iya ce wa sun kori zawarawa da samari sa ma da guda goma sha, wasuma badan Allah suke zuwa ba sai domin dukiyarta, amma Allah yasa bazasu bari tayi wani auranba, sunyi haka ne badan ko suna tabbacin mahaifin nasu zai dawo garesu bane, sunyine domin basa so su tashi batare da mahaifiyar suba, ko kuma su tashi da ƴan u'ba ba. Itama Laɗifa tunanin da takeyi kenan. Salis ya ce "Anty ai bata yi wani auran ba, mune muka hanata domin masu zowa neman auran na ta duk saboda dukiyarta suke sonta. Cikin mamaki Titi ta ce "Jesus kuna nufin kuce duk tsahon wannan lokacin batayi aure ba? Laɗifa dake kusa da Muhammad ta kwanta a kan ƙafarsa tana ce wa "Ni dama jikina na bani Daddy bai mutuba zai dawo shine yasa mukace bazatayi aureba har sai ya dawo. Muhammad ya faɗa dogon tunani a kan matar tasa... Anya kuwa Aisha zata iya kaiwa wannan lokacin batare da na miji ba! Yasan wacece ita, ita ɗin wata irin halittace a cikin mata wacce irinsu basu da yawa, ita ɗin ta kasance mai tsananin buƙata, wacce ta rabu da maza a kan rashin biya mata buƙatun aurataiya, amma yanzu ta iya kaiwa wannan lokacin ta na matsayin harija! Salis ya buɗe baki zaiyi maga saiga mai gadi ya shigo yana sanar musu cewar sunyi baƙi mutum biyu a waje. Salis ya ce "Je ka shigo da su. Muhammad ya kalli Sarah waccce ta yi nisa cikin tunanin rayuwa ya ce "Sarah lafiya kuwa? Zo nan kusa da babanki kinji? Cike da damuwa a fuskarta ta zo kusa da shi ta zauna, itama laɗifa ta miƙe tana mai kallon Sarah cikin mamakin yanayinta,. A zuciyata ta ce "karde ace wannan yarinyar tunanin AJ ne ya sa kata a haka, koma de meye zan bigi cikin ta. Kafin kowa ya sake magana saiga Samuel tare da abokinsa Umar sun baiyana a cikin palon yana ɗingisa ƙafarsa. Da sauri Sarah ta miƙe zuwa gareshi, bata tsaya duba lafiyarsaba ta faɗa jikinsa tana fashewa da kukan da itama kanta bata san dalilin yin saba. "PLs ina Momy And Daddy? Ta tambaye tana mai jin kewar su a cikin ƴan kwanakinnan. Shima Samuel ɗin kuka ya keyi yana mai ta kaicin halin mahaifannasu. *SAMUEL POV* Tinda a ka kaishi asibiti bai ƙara ganin Momy ko Daddy ba saida ya yi kwana huɗu, kafin Momy ta zo. Nan take ta sanar masa da halinda mahaifinsu keciki, a kan an kulleshi a gidan sojoji wai har sai ogansu yazo, sannan an hana kowa ya ganshi. Yana jin haka ya kalli Momy ya ce "Kema da sa hannunki a ka rufe Uncle Solomon? Ya yi maganar cikin ɓacin rai, lokaci ɗaya Elixa taji shakkar yaron nata amma ta dake ta ce "Yes so what? Nice ma na bashi wannan shawarin domin kuwa abunda yayi kuskure ya aikata, kana addininka tun na iyaye da kakano amma lokaci ɗaya ka koma wani"..."Is Ok!!! Samuel ya katse ta cikin ihuuuu!. "Nima zan koma Addininsu idan yaso nima kumin haka! haka a ka ce idan mutum ya koma wani addinin a masa? Momy kunyi kuskure kun aikata abinda bazai taɓa gyaruwa, a da irin wannan abun dama kasheshi kukayi ko kum"... "Wani wawan mari ta sauke masa bata duba cewar yana cikin halin jinyaba. Kan gadon tahau tsabar ɓacinrai ta kamo wuyan rigarsa ta fara maga cikin tsan-tsar jankunne da gar-gaɗi ta ce "Samuel Walhi idan har ka kuskura ka ƙara furta wannan maganar Walhi saina kasheka a cikin ɗakinnan, bakada hankaline kasan halinsu ne? Karna ƙara ji ko gani, kuma itama Sarah ina sane da ita, Walhi sai na ɓata mata rai, har ka kalli cikin idanuwana ka ce zaka kina yin sallar, don't try again. Ganin yana ka-ce-na-cen ƙwace kansane yasa ta sakeshi tana mai kiran Dr. Samuel kuwa cikin zafin da ciwonsa ke masa ya shiga shafa wuyansa yana kakarin amai. Bayan Dr ya shigone Momy ta ce "Dr karka kuskura ka bar yaronnan ya fita daga asibitinna koda kuwa ya warkene, koda kaga ban dawoba? Dr ya ce karki damu za'ayi yanda kikace? Samuel na jinsu har Momy ta bar asibitin batare da ta ƙara ce masa komaiba. Acikin daran ya karɓi wayar wata noss ya sa Numbar Umar, da mamaki yaga Numbar ta fito da suna, bai ce mata komai ba ya ɗan na kiran sa. Ai kuwa kira ɗaya Umar ya ɗaga yana sallama. Samuel ya ce "Umar nine? Umar najin muryarsa ya tashi daga zaunan da yake izuwa tsaye ya ce "Samuel? "Yes Umar kana ina yanzu? "Ina gida lafiya kuwa? Me ya kai wayar zee"... "Samuel ya ce "Umar saurari abinda zance maka? Cikin tsoro Umar ya ce "Wai lafiya dai ko? Kafin Samuel ta ƙara maga Umar ya ci gaba da cewa... Wai naji ance gidanku ya ƙone Allah dai yasa ba kowa a ciki? Samuel bai tsaya amsa masa ba ya sanar da shi duk abunda ke faru kuma ya ce yazu da yamma yasan yanda zasuyi. Umar ya ce " A wani ɗaki kake? Ya faɗa masa shi kuma yace zaizo in sha Allah. A haka sukayi sallama. Bayan sallar la'a'sar Umar ya shigo har cikin ɗakin da Samuel ya ke. Lokacin da yaga bandeji a ƙafar Samuel ya yi tunanin ko hardasu wutar ta ci. Da sauri ya zo gareshi yana mai ƙurawa ƙafar dake ɗauke da ciwon ido cikin mamaki Samuel ya ce "Umar Pls muyi abunda ya dace domin banaso na sake kwana a asbintinnan. Umar da ke son sanin dalilin ganin ƙafa a ɗaure ya ce "Karka damu, inada budurwa a cikin ma aikatan asbintin kuma nayi magana da ita. Samuel ya kalleshi ceke da tuhuma a lamar dai har yanzu yana sheƙe a yarsa ko?. Ai kuwa haka a kayi da sa hannun wanan noss ɗin Samuel ya bar asbintin. Gidan su Umar suka wuce ai kuwa babu wata-wata Haɗiza ƙanwar Umar tana ganinsu ta ja ta dake a kan arne ba zai shiga musu gidaba.To fa! Samuel dai bayajin me take cewa amma dai yasan hanashi shiga takeyi duba da yanda take hararansa, gashi kuma ɗakin Umar ɗin a cikin gida ya ke. Umar ya gama sakewa Hadiza ta rainashi domin kuwa ita bata tsoran sa, zata iya kamashi da dambe a gaban kowa. ( Dama dai baku manta da Hadiza abokiyar faɗan Laɗifa ba?) Babu ko hijjabi a jikinta kanta babu ɗan kwali ko hula, sai doguwar riga wacce ta matseta, rigar ta gama baiyana surarta ta ƴa mace. Lokaci ɗaya Samuel ya kafe ƙijin yar yarinyar da kallo ganin yanda take sarfa musu rashin kunya, gashi ta sa hannu biyu ta tare ƙofar gidan a lamar dai bazasu shigaba. Samuel bai iya cewa komai ba sai bin ta yake da ido yana jin mutuƙar buƙatar yarinyar. "Arne a gidan mu Walhi bazata saɓuba, ko dan kasan baba baya gari? To naga shegen da zai shiga gidan? Ta faɗa tana wani girgiza kamar wata barbar mace. Umar ya ce "Haba diza ta bakya ganin irin halin da yake ne, walhi bashi da lafiya kuma gobe zai tafi kinji? "Walhi saide ya mutu indai sai ya shiga gidannanne, caf ɗi jam arne ɗin na bari ya shiga mana gida ai walhi ƙarama kare ya shiga , arnafa waɗanda basu yarda da Allah da manzansa ba, a'a walhi a ƙara gaba. Haɗiza ta ƙara sa tana kawar da idonta daga na Samuel ganin irin wani kallo da yake mata. Ta ce "Shege mai idon mayu wallhi Hadiza taci dubu sai ceto. Ganin haka yasa Umar cewa su tafi gidan su wani abokinsa. Ai kuwa Hadiza ta biyosu tana ce wa "Wooo atafi can ba dai nan ba dangin marasa salla dangin masu cin kara da alade andai yi a sara maye jikan mayu. Hakanne yasa ƴan unguwa suka fara taruwa a gurin domin an san halin Hadiza. Ganin haka yasa Umar saurin jan hannun Samuel suka bar unguwar. Samuel kam gaba ɗaya ya shiga sosai da lamarin yarinyar, shi baima san Umar nada ƙanwaba sai yau gata mara kunya , ai kuwa irinsu akeso masu irin wannan wayon, lallai kam ta kwana gidan sauƙi, dole nema ya ɗan-ɗana zumar wannan yarinyar. Yana tunani har suka ƙaraso gidan bai saniba. Ai kuwa suna zuwa shima gayan yana dawowa akan mashin ɗin sa. Shima yasan Samuel ɗin hakanne yasa ya ƙarɓesu hannu bibbiyu. Samuel ya sanar da Umar abunda ya faru, kuma ya ce yanaso gobe su tafi gidan su Laɗifa domin Sarah ta na can. Lokaci ɗaya Umar ya ranƙaɗa wani salati yana sanarwa da Ubangiji jin irin abunda iyayen Samuel ɗin suka aikata akan ɗan uwansu ya bar Addininsu. lokacin ɗaya Umar ya ƙara tsorata da halin Daniyel game da ƙiyayyar Addinin Musulunci. Ta wani ɓangaren kuma yana jin ta kaicin zamowar laɗifa da Samuel ƴan uwa, gashi bai aiwatar da nufinsaba. Haka dai Samuel ya dinga bugar cikin Umar akan Hadiza har ya gano komai game da tsoranta da yakeyi. Shi kuwa Umar ganin irin halin da Samuel ɗin keciki sai bai kawo komai ba dukda yasan halinsa na tabbatar da abunda ya gani yana son. Washegari suka hau mashin ɗin abokin Umar ɗin ya kawosu har gidan su Laɗafa. *AJ .POV* Tafiya yake cike da ɗinmun dana sani a cikin rayuwarsa, yanzu shi babban damuwarsa ta ya ya kuɗaɗensa zasu fito. Babu komai a hannunsa da ga shi sai kayan jikinsa wanda su ɗinma Usha ne ya ɗauko masa daga cikin kayansa, fuskarsa anyi bandeji ga gefen bakinsa shima a rufe, gaba ɗaya fuskarsa a gumbure take. Kana kallon AJ kasan baya cikin haiya cinsa tsabar wahalar da yasha a hannun Sojoji. Tsakanin asbintin da unguwarsu a kwai nisa amma haka ya tako a ƙasa yana tafiya yana tanƙaɗi kamar ɗan ƙwaya. Ya daɗe yana tafiya kafin ya iso layin unguwarsu. Tsayawa ya yi a bakin wani gida yana kallo gidansu daga gurin. Lokaci ɗaya ya tuno da abunda wannan gayan ya sanar masa cewar an kama su Innah da Nana. Tunaninsa izuwa yanzu an sakesu ne kodai har yanzu suna a ƙulle? Kafin ya kaiga yin tunanisa ya hango wata baƙar mota ta tsaya a ƙofar gidan... Gaban sa ne ya ƙara bugawa kamar zuciyarsa zata fito. Ya ƙurawa motar ido yana son ganin wanda zai fito daga ciki. An ɗauki tsawon minti goma sha biyar kafin ya ga Nana ta fito, sai kuma yaga wani saurayi shima ya fito daga motar. Lokaci ɗaya yaji wani sanyi a ransa ganin Nana. Sai kawai ya nufi gurin cikin ƙwarin guiwa. Tin kafin ya ƙaraso yake ganin yanda Nana ke dariya da a lamar dai koma waye wannan to sun saba dashi sosai, amma a ransa yana jin baya son haka. Kafin Nana ta baiwa Dr amsar tambayarsa idonta ya sauƙa a kan yayanta, shima ya sauke fararan idanunsa a kan na ta. "Ya ya!!! Ta faɗa da ƙarfi ta na nufar gurin da yake. Kasa rungumar sa ta yi ganin fuskarsa duk ciwuka, sai tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa kuka na son kufce mata, sai tasa hannu biyu ta rufe bakinta dai-dai kukan ya kufce. Juyawa tayi ta shiga gida da gudu tana kuka tana zuwa ta faɗa jikin Innah ta na cewa "Innha ya ya ya ya ya dawo gashi a waje. Lokaci ɗaya gaban Innah ya faɗi amma ta kawar da kai ba tare da ta ce komai ba saina wani dogon tsaki da taja. A waje kuwa AJ da Dr ne a ka fara kallon-kallo, AJ na son tuno a ina yasan shi, shi kuma Dr yana mamakin ganinsa a nan. "Dama shine yayan Nana! Ganin AJ ya kasa tuno inda ya sanshi ne sai Dr ya miƙa masa hannu ya ce Dr Lurwan likitanku. Lokaci ɗaya ya gano shi, bayan sun gaisa Dr ya ce "Zaka iya shiga gida ka huta saboda jikinka, idan ka samu nutsuwa sai muyi maga babban yaya. Babu sallama ya shiga gidan jiki a sanyaye. Yana shiga Innah ta meƙe tsaye kamar dama jiransa ta ke. "Walhi idan har ka kuskura ka shigo gidannan ni kuna zan bar maka gidan ka? Ta na faɗa ta shiga ɗakinta ta fara haɗo ƴan tsummokaranta. AJ na tsaye a gurin har ta fito da kayanta a ɗaure a ɗankwali. "ka fita ka je duk inda kaga dama mu zamu iya rayuwa a matsayin da Allah ya ajiyemu ba sai mun kai kanmu inda Allah bai nufemu zuwaba. AJ ya buɗe baki zaiyi magana Innah ta katseshi da cewar "Idan har ka sake ka furta maga ta shiga kunnuwana to Allah ya isa ban yafeba, kuma mutuƙar kana gidannan to ni ya haramta a gareni, ba dai kai kace a kan kuɗi zaka iya yin komai ba, to kaje ka nemi kuɗinka mukuma ka barmu a inda ka ganmu, zamu rayu cikin talaucin da muke ciki. Innah tana maganar hawaye sun wanke mata ido, aduk lokacin da zata furta wata kalma to tana tuno irin cin mutuncin da wannan arnan ya musu , da kuma zaman da sukayi a ƙulle, ga zaman asbiti duk a kansa. AJ da Nana suma kuka sukeyi duk sun kasa cewa komai tsabar tausayin kakar tasu... "Idan kuma har so kake sai kaga bayana to Abduljabaru gani dan Allah ka zo ka kasheni sai ka ci gaba da abunda kake ai katawa, a ce ka rasa da wa zakayi a bora sai ƴaƴan arna, to ni dai na fa ɗa walhi bazan taɓa yafewa ba. Ta ƙara sa tana dur ƙushewa a gurin nunfashinta na fita kaɗan kaɗan. Da sauri Nana tazo ta rungumeta ta zaunar da ita tana bata baki akan ta manta abunda Dr ya ce ne. AJ kuwa na tsaye a gurin duk ya fita a haiyacinsa yana jin tausayin Innah ji yake inama ana dawo da hannun agogo baya da baiyi wannan kasadar ba, Allah ya isan da ta masa yake ji na masa yawo a kai, lokaci ɗaya kansa ya fara juyawa, take shima ya sulale a gurin tamkar macacce. Ai da sauri Nana tazo gareshi ta rungumoshi tana kiran asalin sunansa " Abduljabaru" "Abdul". "Abdul dan Allah ka tashi karka tafi ka barni Pls yaya. Tana cikin haka ita kuma Innah ta ɗauki ƙullin kayanta ta bi ta bayansu ta bar gidan ba tare da sun saniba......📝 *Da yardar Allah zan koma yin posting kullum har mu kammala, domin an dameni a kan a gama wannan labarin to in sha Allah zamu kama shi yanzu. Amma fa yin hakan dole saida gudun mawar na ƙaramin ƙwarin guiwa ta hanyar comments da addu'o'in ku. Ina alfarari da ku S REZA na kune* *ADDININMU is a Normal* *book* *By S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE3️⃣5️⃣* ..........Kuka Nana takeyi ta na mai gir-giza AJ wanda har zuwa yanzu bai motsa ba, Tashi ta yi cikin sauri ta ɗebo ruwa ta watsay masa ta na binsa da ido kamar wacce bata taɓa ganinsa ba, ganin bai motsa bane ya sa ta ƙara watsay masa ruwan a karo na biyu. Wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke ya na mai buɗe idonsa a kan Nana, sai kuma ya riƙe kansa ya na jin yanda kan ke juya masa, hannunsa ta kama ta na masa sannu cikin kuka. Ya buɗe baki ya ce "I'na Innah? Sai a lokacin Nana ta kai kallonta gurin da ta bar Innah ta na ce wa "Ga ta ce"...."Tsaya wa ta yi da hannun na ta a yanda yake ta na bin gurin da kallon mamaki. Da sauri ta miƙe da gudu ta shiga kiran innar ta ko ta ina. Da gadu ta ƙara fitowa ta na ce wa "Yaya Innah ta gudu walhi bata gidannan ta taffi. Ta na magar ta na kuka. Da sauri AJ ya miƙe tsaye yana nufar waje da sauri riƙe da kansa dake mugun sara masa. Itama Nana tabiyo bayansa ta na kuka. Ya na fita ya ci karo da Innah a ƙofar gidan a duƙe tana kuka tana sharar hawaye. Da sauri ya faɗa jikinta yana fashewa da kuka ya kasa magana, itama Nana ta na zuwa ta faɗa jikinsu ta na mai sakin nata kukan. Kuka sukeye duk su ukun babu mai rarrashin wani a cikinsu, inna ta shiga shafa kan AJ tana mai jin tausayin sa a ranta. Cikin kuka ta fara magana "Tabbas bazan iya tafiya na barkuba domin bakuda kowa sai ni, kaman yanda nima bani da kowa saiku, amma tabbas Abduljabaru ka ɓata min rai wanda bazai musaltuba, amma na maka uzuri kaman yanda mahaifinka ya ce min a kanka, tabbas kai ɗin ɗan arziƙine, ka ɗauki nauyinmu alhalin kai kanka kana buƙatar mai tallafa maka, cinmu shmmu suturarmu gurin kwanan mu duk kaine, amma ka ƙi ka tsaya ka faɗa min gaskiyar sana'ar da kakeyi, sannan meye ya haɗa ka da wannan ar'nan? Allah dai yasa ba da gaskene sata kamasa ba? Shin Abduljabaru me kake ɓoye mana a tattare da kai? Muna son sanin gaskiya amma dan Allah kar ka ƙara mana ƙarya? Cikin kuka AJ ya ce "Tabbas Innah nayi muku ƙarya wanda yanzu haka ta sakani a halin da na sani, kuma tabbas yau zan sanar muku da komai a kan kuɗin da nasamu, amma dan Allah Innah karki gujeni kisan cewar duk abun da na ai kata danku nayi pls innah? Innah ta ce "Innalillahi wa inna i'laihim raji'un, Allah dai yasa ba wani abun kaje ka ai kataba, shin ka manta lokacin da kake cemin AJ baya sata? AJ baya neman mata? AJ ba zai aikata duk wani abun da Addininmu ya yi hani da shiba? To Allah dai yasa baka ai kata ko ɗaya daga cikiba? AJ ya ƙara jin cewar lallai ya aikata kuskure, ita kuwa Nana ta ke ta tuno da zancen Kadija na cewar ya yi wa yarinyar cikine, sai kukanta ya ƙaru domin izuwa yanzu ta fara yarda da hakan. AJ ya ce "Innah mushiga gida sai muyi zancen a ciki. Bayan sun shiga gida Nana ta ɗora ruwa saida yayi zafi sannan ta juye a bokiti ta ɗauka izuwa banɗaki. Saida AJ yayi wanka sannan ya ɗauki kayan adides riga da wando ya saka sannan Innah ta ce yaci abinci tukunna. Itama innar wanka tayi tazo ta zauna kusa da angon na ta ta ce "Abduljabaru kaji tsoran Allah karka sake ɓoye mana damuwarka, kasani duk abunda ya sameka muma ya samemu, duba fuskarka tunda ka shigo na ganka a haka saida gabana ya faɗi, yana daga cikin abunda yasa kaga na kasa tafiya na barku, kullum addu'a'ta Allah yasa kana lafiya ya kuma dawo mana da kai gida lafiya a duk inda kake, haƙiƙa kullum cikin dare sai na tashi na roƙi Allah a kanka, amma a fili ina nunawa Nana cewar bazan yafe makaba domin ta gane cewar abunda kayi ɗin ba dai-dai bane. Inna ta ƙara sa ta na ruƙo hannunsa tana mai kallon fuskarsa dake a kumbure. Inna ta ce "Bari kaji halin da muka shiga a dalilinka? Take Innah ta kwashe komai abunda a ka musu ita da Nana, tun daga marin da a ka fara mata a cikin gida izuwa gidan ƴan sanda da a ka kaisu, ga cin mutuncin da ƴan sandan suka musu, da taimakon da Salis ya musu shida abokin AJ ɗin, har sallamosu da a kayi, sannan ta ɗora da zamansu a asbiti da kuɗin da Dr ya kashe a kansu da irin kulawar da ya basu, aikuwa dai inna labarin ne ya ƙara dawo mata da komai sabo ta ci gaba da kuka ta ce "Tabbas Allah yayi i'nada sauran numfashi a duniya badan haka ba saide ka dawo kaga bana duniya, bansan lokacin da Nana ta kaini asbiti ba ban sani ba! "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! AJ ya dinga furtawa yana mai sakin kuka da jin tausayin inar ya ƙara rushewa da kuka ya na ce wa "Walhi duk nine sila, ba haka nasoba dan Allah Innah ki hukuntani na cutar daku a kan son abun duniya, waiyo ni Abdul na kusa kashe ahalina da kaina. Ganin irin sambatun da yake ne yasa Innah fara bashi haƙuri a kan cewar haka Allah ya tsara zai faru ya bar kuka. Da kyar ya tsaya yana kallon Nana wacce duk sai yaji wani irin rauni a zuciyarsa jin irin halin da ta shiga, ya kafeta da ido yana jin kamar ya ɗauketa ya sakata a cikin sa ko zata huta da wannan kukan da yake sakata, rungumeta yayi yana shafa kanta da bayanta yana saka mata albarka ita kuma tayi luf a jikinsa tana jan hanci. Innah ta yi shiru tana tunanin me AJ zai ai kata ya sa shi irin wannan halin. Sai da suka nutsu kafin AJ ya fara magana kamar haka... "Kuskure na farko da nafara yi a yanzu shine wannan mutumin da ya sa a ka kaiku gidan ƴan sanda to yarinyarsa ita ɗin budurwata ce. Gaban Nana ya bada wani darammm tana jin shikenan ta tabbata. "Amma ni ina sontane badan komaiba sai dan dukiyar iyayenta duk da kuwa suɗin ba musulmai bane. Ita kuma ta na sona tsakani da Allah, sai nayi amfani da son da takemin nake turata ta sato min kuɗi a gidan su. AJ ya sanar dasu komai dake tsakanin sa da Sarah, duk yawan kuɗin da ta bashi saida ya faɗa musu har zuwa lokacin da a ka kamata. Ya sanar musu irin ƙiyayyar da mahaifinta ke yiwa Musulmai, saida ya gama komai Innah ta ce ... "To saboda baka son ya kamaka ne yasa ka gudu shi kuma ya zo ya tafi damu ko kuma kana cikin garinnan kaiwai dai ka ɓoyene? AJ yayi shiru yana tsoron sanar dasu asalin abunda ya jawo wannan tashin hankalin. Shin to aure zaice yayi ko kuma me? Shin da wani ido zai kalli inna ya ce yayi aure, auranma mahaifiyar Salis, kai no bazan iya ba, kawai na je na saketa sai ta auri tsohon mijinta ni kuma ta bani kuɗina amma dai ba zan tona wannan sirrin ba. "Abduljabaru kayi shiru kuma muna sauraron ka. Firgigitin ya dawo da ga tunaninsa yana kallon Nana da ta ƙura masa ido da a lamar dai a kwai magana a bakinta. AJ ya ce "kaman yanda na sanar da ke cewar aiki aka ɗaukemu izuwa ƙasar Niger kuma duk mun dawo lafiya. Ya faɗi maganar wacce daga ji kasan ƙarya yayi. Ya ci gaba da cewar bayan na dawo na samu labarin abunda a ka muku shinefa na je gidansa, to a can ya sa a ka rufeni muda wasu mutane. Haka dai AJ ya sanar dasu abin da ya faru a gidan Daniyel a kan ƙonesu da zaiyi, har zuwa asibitin da a ka kaisu da kuma shigowarsa yanzu. Amma bai sanar musu da cewar shida baban su Salis bane kawai dai ya haɗa ne domin wanke kansa, ya haɗa da dukan da yasha a hannun sojoji. Nann ma dai wani kukan suka sha jin wai ƙonesu a kaso yi, suma sun tausaya masa sosai,, kafin Innah ta ce "To Allah dai ya kiyaye gaba, yanzu sai ka keyaye, babu ruwanka da yarinyarsa, ka fita a harkarta, AJ ya ce "In sha Allah Innah. Innha ta ce "To aikin me kukaje yi a Niger ɗin? Cikin ruɗewa ya ce "Amma am dama fa wani uban gidanmune ya ce muje tonun zinare wai ana samu sosai, shinefa ya fara bamu kuɗi wai kowa ya sallami iyalansa kafin mu dawo. "To yanzu kun samo zinaren ne? "Eh mun samo amma babu yawa saboda bamu daɗe ba. "To Allah yayi albarka, yanzu sai ka tsaya ka nutsu kasan me kakeyi. Nana da AJ sukayi dariya jin wai kasan mekakeyi. *HAJIYA BABBA POV* Numbar AJ ta shiga kira amma ana sanar mata cewar a kashe ta ke, ta ma rasa wani irin tunani zatayi yanzu, kawai ta samashe ya saketa ta bashi kuɗin sa kowa ya kama hanyar gabansa, to ya zatayi da Muhammad. A fili ta ce "Kai co na! Rashin haƙuri baiyiba kwata-ƙwata ma sati nawa da yin auran! Shekara nawa nayi ba tare da namij ba, amma na kasa jure wannan lokacin, a'she dai Salis da Laɗifa taimakona suke sonyi amma na ƙi yarda, na shiga uku ina zan sa kaina. Ɓangaren su Muhammad kuwa Salis ne ke bashi labarin irin cigaban da suka samu a harkar kasuwancinsu da irin nasarorin da suka ƙara samu. Shima Muhammad ya jin-jinawa matar tasa. Haka sai suka dinga hira sosai a kan rayuwa, Titi da su Samuel ma duk sun saki jikin su Umar da Usman duk an kaisu ɓangaren da zasu zauna kafin su huta zuwa wani lokaci a shiga Katungu. Titi ma a gidan ta kwana ita da Usha. Nann fa Laɗifa da SAMUEL suka fara zama a tare. Ita dai a zahirin gaskiya tana sonsa shi kuma a da yana sha'awar ta ne kawai, yanzu kuwa sai yaji duk babu koɗaya kodan ita ɗin jininsace. Hakanne yasa a zaman da sukayi bai wani sake da itaba sai Usha ne ma yake ɗan janta da hira, shi kuwa gaba ɗaya hankalinsa yana ga surarr jikin Hadiza. Sarah da laɗifa a ɗaki ɗaya suka kwana hakanne ya ba Laɗifa damar gano komai dake tsakanin ta da AJ domin kuwa ta bigi cikinta. A wannan lokacin Laɗifa ta sake yarda da cewar AJ kawai yana bin ƴaƴan masu kuɗine ya na manne musu kuma daga yau idan ta ƙara ganinsa a gidansu walhi sai ta wulaƙan tashi. Washe gari bayan sun gama breakfast wanda Hajiya Babba ta kasa cin komai kasan cewar ta tashi da ciwon kai, ga kuma abincin da bata son ganinsa kamar zatayi a'mmai. Bayan sun gama ne Hajiya Babba ta kalli Salis ta ce "Zaka rakani gidan su AJ domin zan kai masa gudun mawa kaga abun da ya sameshi shi bai kamata a barshi haka ba ko? Cikin sauri Salis ya ce "Ok Tom Hajiya amma Abba ya ce zan rakashi gidan abokinsa ki bari idan mun dawo sai na kaiki? Da sauri Sarah ta ce "Na san gidan zan rakata? "Muhammad ya ce "Hajiya bazaki bari ki sake hutawa ba? Ko dai zamu koma asbiti ne? Naga yanayin jikin naki ,ko a kira Dr yazo? Ta ce "No karka damu yanzu zan dawo kuma ba wani ciwo da nakeji. Hajiya Babba da ta ke jin cewar bazata iya cikekken minty biyar batare da sun haɗu da AJ ba ta yi saurin ce wa da Sarha "To ba damuwa idan har zaki gane gidan ai sai mu tafi. Laɗifa kuwa da take takaicin wannan abun ganin Sarah tayi hakane domin taga AJ, shi kuma Salis yayi hakane domar har ya dawo ya je yaga wannan shegiyar ƙanwar AJ ɗin da ya ce yana so. Ai kuwa a zuciyarta ta ce "Yau dai zan sai naga wannan yarinyar kuma naga shi AJ ɗin a ina ya ke, daga nann kuma na ci masa mutunci. Da sauri ta ce "Hajiya nama zan rakaku? Hajiya Babba da bata son a sirinta ya tonu ta ce "No Auta ki zauna a gida yanzu zan dawo? Laɗifa ta ce "Haba mana zan iya takawa fa ƙafar bata ciwo yanzu na warke fa? Muhammad ya ce "A'a auta keda Samuel ku zauna a gida har mu dawo domin kuna buƙatar hutu, ga Anty Titi tana tare da ku kinji? Jin haka yasa ta ce "To amma ku dawo da wuri Pls?. Salis da Muhammad da Umar da Usman suka tafi gurin abokin Muhammad wanda shiɗin malamine domin nemo hukuncin auransa da matarsa shin auran yana nann ne tinda bata ƙara wani auran ba, ko dai sai an gyara auran duba da an daɗe ba'a tare. Bai sanar dasu abunda zaijeyi ba shi kaɗai ya barwa kansa hakan. Hajiya Babba da Sarha ne a bakin gidan su AJ da safe. Hajiya ta ce da Sarah "Shiga ki ce ana sallama da AJ? Sarah ta kalleta ta ce "Ok i'm Coming. Ƙarasawa gurin mai shayin unguwar ta yi ta ce da yaron da yazo siyan shayi yazo ta aike shi. Gaba ɗaya ƴan gurin suka zuba mata ido domin kuwa turanci tayi. Yaron da bai san me take cewa ba ya ce "Mai shayi ana maka magana wai zata siya shayi? "Gaba ɗaya suka kwashe da dariya mai shayi ya ce "Hajiya na nawa kikeso? Sara ta ƙara Mai-maita abun da ta ce sai akayi sa'a wani ya gano abunda ta ke nufi shikuma ya sanarwa da yaron. Ai kuwa take yaron ya tafi kiran AJ ɗin. Suna tafiya kuwa sabuwar hira ta ɓarke a kan taiburin mai shayi. Wasu na yaba irin kyun da yarinyar ke dashi, wasu kuma suna zaginta saboda arniya ce, wasu kuma na gulmar me tazo yi gidan su AJ domin dai basu ganeta ba, kuma basu manta irin tashin hankalin da ya samu gidan su AJ ɗinba a kan idonsu. Tasaye suke a jikin motar su, Hajiya Babba na jin kamar ta shiga gidan tsabar ruɗewa. Sanye da jallabiya fara ya fito ƙafarsa ko ta ƙalmi babu, yana fitowa ya ci garo da Sarah domin itace ta farko jikin gidan nasu, sai kuma ya ga Hajiya Babba. Da mamaki yake kallonsu, sai kuma ya kawar da mamakin nasa domin kuwa yasan dama doke ta nemeshi . Lokaci ɗaya ya kafe Sarah da ido wacce itama shi take kallo idonta har ya fara cikowa da hawaye. A hankali ya ƙaraso kusa da ita wanda yayi dai-dai da ƙamshin tirarensa na fashion ya shiga ƙofofin hancinsu dukkansu. Take Sarah ta lumshe ido, ita kuwa Hajiya Babba tsabar damuwar da take cikima sai taji bata son wannan ƙamshin turaran nasa, take tashin zuciya ya fara zuwar mata. Kallon juna sukayi ita da shi sannan ya ce "Kinsan Sarha ne? Yayi tambayar ne cikin mamaki? Domin shi dai bai san asalin komai ba. Ta ce "Eh amma ba wannane ya kawoni ba, ta faɗa tana mai jin a'mai na ƙoƙarin zuwar mata? Ya ce "Eh dama nima ina son muhaɗu domin kuwa a kwai ma tsala? Kallon Sarah Hajiya Babba tayi sai AJ ya mata a lama da bata jin Hausa. Hajiya ta buɗe baki ta ce.....📝 [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* _*Bansan da wani irin alƙalami zan rubuto muku ɗinbun godiya da irin addu'o'in ku a gareniba, tabbas LITTAFIN ADDININMU yana samun yabo sosai a gareku makaranta ina godiya sosai da sosai.*_ _*PAGE3️⃣6️⃣*_ ..........Ta ce "Bana son wannan ƙamshin tiraran naka pls kaje kacire wannan rigar kazo muyi magana? AJ ya kalli jikinsa sannan ya kalli Hajiya Babba sannan ya dawo da kallonsa izuwa ga Sarah wacce tunda ya fito ta kafeshi da ido ko rin tsawa batayi. Juyawa yayi ya koma cikin gida ya cire rigar ya sako wata jallafiyar sannan ya fito. Yana fitowa bai ce musu komaiba ya ƙarasa jikin motar ya na cigaba da kallon Sarah. "Ta ce ina wayarka? Kuma me ya kaika gidan Comanda Daniyel? Hajiya Babba ta watso masa wannan tambar. Acikin jimilla ɗaya ya bata amsar tambayoyinta. "Babu ruwanki wannan bai damekiba faɗi abunda ya kawoki? Shima ya bata amsa cikin tsananin jin haushin halin da ta jefashi. Da mamaki Hajiya Babba ta kalleshi sai kuma ta kawar da kai gefe tana danasin abunda ta aikata, yanzu wannan ɗan yaron shine har na yarda ya sanni a matsayin ma ce! Inalillahi wa inna i'laihim raji'un! Ta furta a zuciyarta kafin ta koma serus ta ce.... "Kaman yanda mukayi wannan auran ba tare da kowa ya sani ba to haka nakeson yanzu-yanzu ka sakeni na baka kuɗinka kuma karka sake ne ma na, sanan duk wata alaqar da ke tsakanin ka da Salis itama inaso ta yanke daga yanzu, zan baka kyutar gida kubar wannan unguwar domin bana son wani abu ya ƙara shiga tsakanina da kai har a bada. Da ɗan mamaki AJ ya ce "Ai dama a cikin sharuɗanmu harda gida a ciki saboda haka ba kyuta zaki baniba hakƙinane, sannan kuma nima nafi son hakan, amma kinsan fa a tsarin Addinin Muslunci dole sai an ɗaura muku wani auran kafin zamanku ya halarta keda shi mijin naki, kenan ya zakiyi? Hajiya Babba da gaba ɗaya kanta ya ɗau zafi, ga kuma taga kamar yanason yin amfani da wannan damar ya raina mata hankaline ta ce "Wannan ba damuwar ka ba ce, kaidai ba damuwar ka kuɗi ba? AJ ya ware hannu haɗi da karkatar da wiya alamar yes. Ta ce "Ok yanzu nawa ne sauran kuɗin naja? Ya ce "Gidaa nafi buƙata a yanzu, sannan kuma kuɗi inaso ki bani miliyon hamsim idan kinga zaki iya ? Ya faɗa yana haɗe fuska kamar yanda tayi. Cikin tsawa ta ce "Kai ɗan matsiyata walhi kai baka isa ka iya tonamin asiriba kayi kaɗan, kaiɗin banza miliyon goma zan baka ai bamu gama cika watannin da muka yankeba, saboda haka idan kaga dama ka amsa idan bakaga danaba ka barshi aurene dai ya ƙare tunda mijina ya dawo? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar tana buɗe gaban motarta ta ciro wayarta ta ce "Bani account numbar ka yanzu na tura maka, suma ta kardar gidan nazo dasu, inaso daga nan ƙarna sake jin labarinka. Cikin jin jewar shawar da zuciyarsa ta bashi tayi ya ce "Idan har kina son saki daga gareni kuma nayi nisa dake har abada to inada sharaɗi? "Sharaɗinkan na banza, walhi yaro sai ka sakeni kuma yanzu idan ba hakaba walhu sai kayi da kasanin sanin Aisha Salisu. AJ ya ce "To shikenan tinda kince haka, zaku iya barin ƙofar gidannan yanzu kafin na tara muku jama'a kuma ki sani auranmu zai baiyana ga duniya, kuma zaki bar gidanki kidawo gidana ki tare, badai sai na sakeki za'ayi auran ba to muzuba mugani? Yana faɗa ya juya zai shiga gida. Ai da sauri Hajiya Babba ta kamo hannunsa ta yi ƙasa da murya cikin sanyin rai ta ce "AJ karkamin haka ka tuna cewar aurannan fa dama munyishi a cikin kuskurene kaga rabuwar shine mafi dacewa, kokai bazakaso ace kaine mijin uwar abokinkaba, kaga Salis bazaiji daɗiba pls kayi haƙuri kafaɗi sharuɗan naka? Hajiya Babba ta ƙarasa maganar da muryar roƙo kamar zatayi kuka. AJ yayi shiru yana tunano irin dukiyar da ta mallaka, sannan yana tunano irin wahalar da yasha kuma duk itace, sannan ya tunano su Innah yanajin cewar wahalarsu ta ƙare a rayuwa, ya tuno lokacin da take bashi umarni kuma tace a cikin sharuɗan auransune. Afili ya kalli gurin da Sarah ta ke yaga har yanzu su take kallon ko magana batayi, take yaji gabansa ya faɗi ganin irin kallon da take masa, lokaci ɗaya yaji wani tausayinta sai kawai ya lumshe ido yana son sanin alaqar Hajiya Babba da ita ɗin. Ya ce "Sharuɗa na guda ukune? Idan kin yarda yanzu zan rubuta miku saki na baki idan kema kin bani nawa? Hajiya Babba ta haɗiyi wani yawu muƙut ta ce "Ina jinka? *SALIS POV* Gaba ɗaya hankalinsa kacoƙan ya tattara izuwaga Nana ya na son yaje yaga a wani hali suke, shin bayan da suka fito daga gidan ƴan sanda ina sukaje? Anya kuwa lfy? Gashi numbar ta ta daina aiki. Har sukaje gidan abokin Daddy suka dawo bai daina tunaninta ba. Afili ya ce "Yanzu lokaci yayi da Hajiya zata san da magar aurane tunda Daddy ya dawo, kokuma na fara sanar da Daddy. Haka dai ya keta saƙe-saƙensa shi ɗaya, ya bari a kan zaije gurinta da yamma. Ɓangaren su Muhammad da Umar da Usman kuwa, izuwa yanzu sunce sumafa sun matsu da son zuwa gida suga iyayensu, domin kuwa dukkansu babu mai aure. Hakan yasa Muhamd ya yanke cewar suyi haƙuri zuwa gobe sai su tafi. Sunyi yawo sosai a cikin gari, duk gurin da Muhamd yaje indai ansanshi sai kowa yayi mamaki. Lokacin da sukaje gurin abokin nasa kuwa yana ganinsu ya fara Ambato sunayen Allah cikin tsoro. Sai da yaji yayi maga kafin ya nutsu. Bayan yaji duk abunda ya faru ne ya shiga mamakin rashin imanin Daniyel, a ce ka ɗaure mutum kusan shekaru har ashin(20) saboda kawai ya koma addinin Allah. To walhi sai anyi masa hukumci ai samun matsayi ba hauka bane. Malam fa ya shiga surfa faɗa yanajin abunda a kaiwa abokin nasa babu daɗi, domin kuwa ko bayan abotar dake tsakanin su ai shiɗin musulmine, musulmi kuma ɗan uwan musulmine. Da ƙyar dai Muhammed ya taushi Malam har yayi shiru, sannan ya ce "Ni Walhi na yafe masa duniya da lahira, in de domin abunda yaminne za'a masa hukumcin to walhi na yafe. Cikin mamaki Malam ke jijjiga kai ya ce "Eh laillai kam kaci sunanka Muhammad domin kuwa wannan shine irin halin mai sunanna, kuma haka yayi mana nuni da muyi, rama kairi d ga wanda ya aikata maka shirri yin hakan imanine, haƙiƙa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama zaiyi alfarahi da kai, kuma wannan halin naka shine ya kamata adinga yin koyi dashi. Malam ya ci gaba da cewa ..."A kwai wani maƙofci da Manzon Allah ya taɓayi wanda ba musulmibane baya ƙaunar mudulmnci da kuma musulman gabaki ɗaya, tsabar ƙiyayarsa da manzan Allah, kullum idan yayi shara a gidansa sai ya tattara ya watso gidan Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama, shi kuma idan ya watso sai ya kwashe. Sai Manzon Allah yaga kwana biyu wannan kafirin bai watso masa sharaba sai ya tambaya ko lafiya kuwa kwana biyu baya jin ɗuriyar maƙofcin nasa? Sai a ka shida masa cewar ai bashi a ke binsa kuma bai biyaba shine a ka kamashi a ka kulle. Manzan Allah Sallallahu alaihi Wasallama sarkin tausayi Sarkin adalci ya bada wannan kuɗin masu yawa a kaje a ka fito da wannan mutumin. Bayan ya fito ya tambaya cewar waye ya fito da shi? Sai a ka ce masa Muhammad Rasulullah. Sai ya ce "Shiɗin ne ya bada kuɗin da a ka fito da Ni? A ka tabbatar masa da haka. Ai kuwa take kafirin ya miƙa wiya ya musulunta. Take su Muhammad da Umar da Usman da Salis suka ce Allahu Akbar! Malam ya ci gaba da cewa "Haƙiƙa Muhammad kaiɗin masoyin manzan Allah kuma da yardar Allah bazaka taɓa wulaƙanta ba, daga kai har zuri'arka. Nan dai malam ya masa bayani game da matarsa cewar idan har tayi wani auran to zata zaɓane ko shi ko waccen mijin nata, idan kuma batayi wani auran ba to auransu yananan kawai dai zasu cigaba da zamantakewar su a matsayin ma'aurata ne. Muhammad yayi godiya sosai sannan ya tambayeshi labarin malamin su wato shek Kabir kabuga. Malam ya sanar masa da cewar yana nan lafiya, kwanan ma zai aurar da yaransa mata guda biyu. Muhammad ya ce "Ikon Allah malam har zai aurarr da yara. Sun daɗe a gurinsa ya ƙara jaddadamusu cewar suma su Umar da Usman so je gida domin a sanar cewar sunraye. Bayan sun dawo gidane Salis ya shiga wannan tunanin nasa. Ya na cikin haka Muhammad ya shigo ɗakin nasa ya na cewa yazo suje su siyo kayan siyayyar da su Umar ɗin zasu tafi dashi. Tashi tayi suka tafi duk su huɗun. Samuel da Laɗifa da Usha kuwa hira suka sha sosai daga nan Usha ya bar gidan itama Titi ta shiga cikin tadomin ɗora musu abinci. Samuel ya taso daga kujerar da yake yazo kusa da ita ya ce "Laɗifa wannan shine gidan Uncle Solomon? Ta ce "Sunansa Muhammad from today or call him Daddy? Samuel ya ce "Ok Daddy. Laɗifa ta ƙara matsowa kusa dashi sosai ta ce "Yes gidanmune munada irinsu sama da goma a cikin garinnan sannan kuma munada camfanunuwa guda takwas biyu a nan biyu a Abuja uku a kano sai ɗaya a Lagos, amma na Abuja da Lagos sune manya-manyan. Samuel yayi shiru yana tunani sai ya ce "Waye ya baki kuɗin da kika kai gidanmu ranar? Ta ce "Nawane ai inadasu a account ɗina? Ya ce "Waye yake baki? Ta ce "My Momy And my brother. Bai san lokacin da ya ce "I love U so mouc my lovelly Sister. Itama ta ce "Me too my brother. Sai kawai yaji shikenn kaya ya tsinke a gindin kaba. Ya riƙe hannunta yana kallon ƙwayar idonta, yana son yayi amfani da wannan damar ya karya mata tata zuciyar, ai kuwa ya samu nasara domin kuwa take tayi ƙasa da kanta tana mai jin wani yanayi. Ya ce "Ar you serus You love me? Ta yi ƙasa da kai tana jin faɗuwar gabanta na ƙaruwa. Bata an karaba taji ya ɗago kanta ya saka bakinsa a cikin bata. Ido ta zaro tana kallon idonsa da yayi jaa. Da kyar da ƙwace bakinta ta na ce wa "Pls Samuel babu kyu a Addinimu karka sake? Ya ce "Sorry tsabar son da nake miki ne yasa amma kiyi haƙuri bazan ƙaraba. Haka dai ya dinga mata zantukan soyayya wanda yasa Kaɗifa jinta a duniyar sama, har ta saki jiki dashi sosai. Soyayyar gur-gwaye kenann. *AJ POV* AJ ya ce "Idan kin yarda zaki bani miliyon hamsim da gida haɗida takardun gidan, kuma karki bani wanda yake kusa da ku, in da sosamunema ba'a cikin garinnan ba. Idan kinyi haka sai kuma... ki samu wani daga cikin yaran aikin ki yazo gidanmu a matsayin shine ogana, ya sanarwa da Innah ta cewar shine ya bani wannan gidan, sai ya bani takardun gidan a gaban ta, a haɗo da mota sabuwa, idan har kin yarda to yanzu zan rubuta miki saki ko nawa kikeso daga kan ɗari har zuwa ɗaya. Hajiya Babba ta ce "Matsiyaci kaine talaka wanda baisan mutunciba kuma in sha Allah sai ka wulaƙanta. AJ ya ce "Walhi kika sake yin magana to sai dai milion sittin? Cikin jin tsanarsa ta ce "Idan uwarka da ubanka sun isa sai suzo su kwatar maka, wawa ɗan talakawa dama Laɗifa tana cemin kaiɗin ba ɗan arziƙi bane amma naƙi yarda kuma zakagani. Ya ce "To farashi ya ƙaru sai kin bada sittin Walhi! Hajiya dai baki bai mutuba tana jin duk itace ta jawa kanta.lokacin da zatayi aure yaranta sun hanata taƙi hanuwa, ta ɗauki Wannan tsinanan yaron aiki Laɗifa ta hanata amma taƙi. Ta ke ta turawa AJ miliyan hamsin ɗinsa, shi kuma ya ce "Walhi bazaiyi sakiba har sai ta ƙara wannan goman. Haka dai tana zaginsa har ta tura masa. kasan cewar bashida waya yanzune yasa baya ganin message sai har ta nuna masa daga wayarta, ai kuwa saida yaga tabbacin shigarsu sannan ya ce "Ki turo Salis gobe da motar tawa sai ya karɓa miki sakin?ya faɗa yana ɓiye dariyarsa. "Hajiya Babba tana jin kamar ta zabga masa mari ta ce "Na faɗa maka babu kai babu yarana walhi idan wanan maganar ta je kunnuwan wani to kotuce zata rabamu da kai, kuma ka bani takardar sakina na tafi? Ta ƙara sa tana miƙa masa hannu? AJ da zuwa yanzu yake ganin komai kamar a mafarki ya ce "Tabbas bayan wiya sai daɗi walhi, in sha Allah mafarkina akan su Innha zai tabbata. Take ya ɗauki takarda ya damɓara mata saki ɗai-ɗai har uku sannan ya miƙa mata ya ce "Yanzu ya zakice da tsohon mijin naki? Kinga dai dole sai an ɗaura wani auran. Hajiya Babba bata tsaya jin komai ba ta fusge takardar ta shiga mota ta buɗe wa Sarah ta shi ta bar gurin cikin ɓacin rai da danasani. *SARAH POV* Tin da suka fara maganar take binsu da kallo, tabbas bata jin Hausa amma ta lura da cewar sunsan junansu kuma kamar faɗa sukeyi, ganin irin haɗe fuska da kowanensu ya keyi. Ganin haka yasa ta fara nazarin abunda sukecwa, ga takarda da AJ ya bata, kuma taga kamar AJ ɗinne yayi nasara domin taga yana dariya, taso ace tanada waya da sai ta naɗa ta kaiwa Laɗifa ta fassara mata amma yanzuma ta riƙe wasu kalmomi guda huɗu kuma tanada tabbacin akansu suke zancen domin taji sunfi ambatar su. Suna isowa gida Hajiya Babba tayi ɗakinta cikin sauri, ita kuma ta nufi ɗakin Laɗifa cikin sauri. Tana shiga ta samu laɗifa na chatintg. Ai da sauri ta faɗa a kan gadon tana sauke a jiyar zuciya. Laɗifa da basan da shigowar ta ba ta ɗan tsorata. Ganin Sarah ya sa ta ajiye wayar tata ta zo kusa da ita ta ɗagota sai taga hawaye a kumatunta. Kafin Laɗifa tayi magana Sarah ta ce "Pls Laɗifa me a ke nufi da .....📝 *Hammm. To wai shin wasu abubuwa huɗu Sarah ta riƙe a cikin hirar AJ da Hajiya Babba. Samuel fa yaji nera. To fan's ɗin AJ yau dai aure ya rabu, shin kuna taya AJ murna kodai?* *Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...,✍️* *First Class writer's asso* *PAGE3️⃣7️⃣* .......Mai a ke nufi da Aure? Sarah ta tambayi Laɗifa cikin tsoron amsar da zata bata, koda bata jin hausa amma bata yarda da wannan kalmarba. Shiru ta yi ta na son gano mai Sarah ke son faɗa domin Hausar ta ta bata wani fito yanda za'agane ba. Laɗifa ta ce "Sake faɗa niji ban ganeba? Ta ce "Aure da saki mai ake nufi da su a English? Sai a lokacin ta gane mai ta ke nufi. Ta ce "Waye ya ce zai aureki? Laɗifa ta faɗa cike da matsuwa. "Pls Laɗifa let me no ina son sanin kalmarne kawai? Sai ta yi dariya sannan ta sanar mata da abunda aure ke nufi da kuma saki da English. Sarah ta yi shiru ta na tunani sai ta ce "Amm Hajiya your Mother tasan AJ ne dama? Laɗifa ta ce "Wannan shegen yaron ai Hajiya ta taɓa ɗaukarsa aiki a matsayin drebanta harma sunyi tafiya tare, ke idanma a kansa kike wannan tambayar to walhi karki yarda shi, shiɗin ɗan iskan gaskene yana bin yaran masu kuɗi yana musu ƙaryar soyayya domin ya samu kuɗine. Sarah ta kawar da kanta gefe tana jin wata faɗuwar gaba ta ce "Hajiya tayi wani auranne bayan ɓatan Uncle? Cikin jin haushe ta ce "A'a batayi aureba, amma ke meyasa kike ta wannan tabbayoyin? "Noting. Ta bata amsa tana miƙewa ta bar ɗakin. Ta daɗe tana tunani kafin ta yarda da abunda zuciyarta ta bata, kuka tayi sosai tana ta kaicin wannan halin na AJ. Tabbas tasan yana son kuɗi amma bata kawo zai iya auran babbar mace kamar Hajiya Babba saboda kuɗiba. Taso ace tanada waya da sai ta kirashi ya sanar mata da gaskiya, dukda wannan abun sai taji ta ƙara sonsa . Hajiya babba ku wa ta na shiga ɗakinta tashiga dube-dube ta ɗauko wata tsohuwar jakarta ta buɗe ta zazzage komai dake ciki, ta shiga dubawa har ta gano takardar da take nema. Ta ɗauki wayarta ta kira Numbar da take buƙata, bayan ta sanar masa gurinda zasu haɗune ta kashe wayar tana sauke a jiyar zuciya. Palon ta fito lokacin su Muhammad basu dawoba sai ta koma ɗaki ganin laɗifa da Samuel da Usha a palon. Shigarta dakin baifi da minti biyar ba saiga Anty Titi ɗauke da shayi ta shigo ɗakin nata. Titi ta ce "Aisha wai lafiyarki kuwa? Naga gaba ɗaya kamar baƙya cikin kwanciyar hankali, kodai za'akoma asbiti ne? Ta ce "No Titi i'm Ok. , Kawai dai nima bansan me ke damunaba. Ta ce "Ok to ga shayi kisha naga baki karyaba? "Hajiya Babba ta ce "Walhi bana jin yunwa bana sha'awar cin komai bari zuwa anjima idan anyi abinci sai naci. Titi ta ce "No kiɗan sha shayin mana ai ba abinci bane? Haka dai Hajiya Babba ta ɗan sha kaɗan sannan ta sake ce mata zata fita wani guri amma yanzu zata dawo. Ita dai Titi haka kawai Hajiya Babba take bata tausayi barinma yanda taji ance wai batayi wani auranba, ga kuma yanzu tunda mijin ta ya dawo ta ƙara shiga damuwa. *AJ POV* ATM ɗinsa ya ɗauka ya fito ya kalli Innah da Nana ya ce "Lokacin da mukaje tonon zinaren gol ɗinnan ko? Innah ta ce "Ina jinka? Ya ce "mun samo fa sosai amma da yake ogan namu mugu ne sai ya ce wai muje zai nememu. Kumafa masana abun sunce idan zai bamu sai kowa ya mallaki gida da mota hardama na jari? Innah ta ce "To ai sai kuyi haƙuri indai rabonkune zai nemeku tunda ya ce zai nemeku ɗin. AJ ya ce "To Innah Allah yasa dai da gaske ya ke? Kuma ana bani nawa zamu bar unguwar nan zan siya mana ƙaton gida mukoma. Innah ta ce "Au wato dai bazaka daina wannan shegen son kuɗin naka bako? Abduljabaru ina guje maka ranar da kuɗi zasu jefaka a damuwa. Nana ta ce "Haba mana inna wannan ai hakƙinsane kuma ai ya sha wahala a baya kinga yanzu ai sai jin daɗi. Ta ƙarasa tana faɗawa a kan innar. Itama innar tayi dariya ta na cewa "To amma dan Allah Abduljabaru ka sake kula da mutuncin ka da kuma namu, domin a dundiya babu abu mai wahalar samu kamar mutunci yana zubewa shikenan, idan baka samu wannan kuɗin ba ka koma aikin ka na gidan bredin nann dan Allah karka sake jawo mana abun magana. AJ ya taɓa ATM Ɗinsa dake jikin sa a zuciyarsa ya ce "Innah kenan ai yanzu saide ma ni na samo dareba ya dinga tuƙani. Afili kuma ya ce "Ok Innah, yanzuma gidan bredin zanje domin susan na dawo. Har zai fita sai kuma ya dawo ya ce "Yauwa Innah da ma akwai sauran kuɗin da ogan namu ya bani lokacin da zamu tafi, yanzu zanje na sayo waya da layi idan naga ya rage to zan zo da ɗan abunda yasamu, kar sai na kawo ki tsareni kina cewa a ina na samo kuɗi. Inna ta ce "To a dawo lafiya amma dai karka daɗe kaga dai ba lafiya gareka ba? Haka ya bar gidan cikeda jin komai yazo masa cikin sauƙi. Yana fita ya tare mai mashin ya je bank ya ciro kuɗi masu yawa, ya je ya sayo waya ƙirar samsung. Ya siya layi ya tsaya bin layi domin yin welcome bak. *SALIS POV* Suna dawowa daga siyan kayan da su Usman zasu tafi dasu, yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya ya sa hula ya nufi gidan su Nana. Tafiya ya keyi yana addu'a Allah dai yasa suna lafiya kuma sun dawo gida. Da mamaki ya ga ƙofar gidan a buɗe sai ya tsaya yana jiran ko zaiga yaro. Yana tsaye a gurin bai ga kowa ba sai kawai ya koma cikin motar yana jiran ko Allah zai kawo wani. Kamar daga sama yaganta tana tafiyarta irin ta kamammun matanan, tafiya takeyi kamar bazatayiba, babu a lamar sauri a cikin yanayinta kumu da alamar a hakan sauri takeyi. Ganin zata shiga gidan batare da ta kula da motar tasa bane yasa ya yi saurin fitowa daga motar ya ce "Nana? Sauri takeyi ta shiga guda domin ta ɗan daɗe a gidan su Kadija, taje sunsha hira kuma kadijar ta sheda mata cewar tana son AJ, itama tayi murna domin tasan halin kadijar tanada kamun kai gashi bata tara samari. Sauri take ta sanarwa da Innah wannan maganar domin tasan Innah zatayi farinciki sosai, sauri take ba ta ko kula da motar dake kusa da gidan nasuba sai jin Muryar da bazata taɓa mantawa da itaba ta shiga cikin kunnuwanta. Tsayawa tayi ba tare da ta juwoba. Sai da taji ya ƙara cewa "Nana?. Ƙara sa gabanta yayi ya ce "Nana ina kika shiga kwana biyu nazo bana samunku? Kallon sa tayi cikin ido sai kuma ta sun kuyar da kanta ƙasa tana jin wani tausayinsa ganinn yanda yayi da fuskarsa. Ta ce "Na'am ina uni? Salis ya ce "No bawannan na tambayekiba. Ina kika shiga? Nana ta ce "Bari nayi magana da Innah sai ka shigo, tana faɗa ta bata tsaya jin mai zaice ba ta wuff ta shige gidan tana jin wani sanyi a rannta na ganin sa cikin ƙoshin lafiya. Da mamaki Innah ta ce "Allah sarki yaron kirki Salisu ko? Ya ce "Eh Innah fatan dai kuna lafiya? Innah ta ce "Lafiya lau muke, ai sai muka nemeka bamu gankaba muna ta addu'ar Allah yasa dai ba wani abun suka maka ba, domin nasan basuda imani kasan fa duk wani arne to babu wani imani a zuciyarsa. Salis ya ce "Ai nima ku nake ta tausayi kar ko sun kaiku wani gurine domin na koma gurin ban samekuba na dawo gida kuma ba kwanan. Innah ta ce "Ai kaide yaro Allah ne yayi muna da sauran rayuwa a gaba. Nan inna ta kwashe komai ta sanar war Salis har abinda AJ ya sanar musu na cewar yarinyar mai gidan yake turawa ta sato masa kudi shine ya kamata ita kuma ta nuna gidansu shikuma Abduljabaru baya nan yatafi Niger shida uban gidansa shinefa yasa a ka tafi damu. Salis ya yi shiru yana tunani , kenan Sarah AJ ya ke turawa! to dama a kan haka Daniyel ya kama su Innha! kenan abunda yasa AJ yaje gidan Daniyel kenann. Salis ya ce "Ok to yanzu ina AJ ɗin yake? Innah ta ce "Wai me yasa bazaku na kiransa da sunan da iyayensa suka yanka masa na sunanaba sai wani AJ to me AJ ɗin take nufi? Wata ƙilama sunan wani ƙaton kafirin ne kamar dai shi wanda ya kullemu ɗin, ni bana son naji ana cewa aj, ga suna mai sauƙin faɗa nann amma sai kun wani bawa kai wahala. Salis da Nana sukayi dariya ya ce "To ai Innah aj ɗin ya na nufin Abduljabaru ne, anyi hakanne domin sauƙin faɗa. Inni ta taɓe baki ta ce ku dai kuka sani. Innah ta ce "Ina ɗaya yaron da kuke zuwa tare dashi gurinmu a gidan ƴan sanda? Salis ya ce "Ok Allah sarki nima ai ban san saba dama a unguwar nann yake. Innah ta ce "Allah sarki yanada kirki. Salis ya ƙara cewa "Innah ina AJ ɗin yake? Ta ce "Allah sarki ya je ya sanar da gidan bredin da yake aiki cewar ya dawo, ko zasu sake ɗaukarsa, kasan yaxu na masa faɗa a kan shigewa yaran masu kuɗinnan, domin gujewa jin mutuncin al'umma. Salis ya ce "Ban ganeba! Inace Hajiya ta ɗauke shi aki! To ko yace bazaiyi bane? To amma ai ɗazu tazo gidannan kuma tace zata bashi wani abun to me ya faru kenan? Afili ya ce "Ok to Innah idan ya dawo ace nazo ban ganshiba kuma zan bawa Nana numbar na sai ta bashi. Innah ta ce "To zata sanar masa a gaida gida. Ta faɗa ganin ya miƙe zai tafi. Ya zaro kuɗi ya ajiye wa Innah ya ce "Gashi wannan babu yawa? Innah ta dinga godiya tana saka masa albark. Bayan ya fito ya tsaya ya jin gina a jikin motar sa yana tunanin zantukan Innah. Yaushe AJ yaje Niger? Dama yasan Sarah? To Hajiya batazo gidan bane! Yana cikin haka saiga Nana ta fito riƙe da wayarta a hannu ta ce "Salamu alaikum? Ya amsa sai ya ce "Wato kinada waya shine ko ki nemeni ko? "ban reƙe numbar ka a kaina bane, kuma waccear wayar ta ɓata. Ya ce "Ok baki riƙe numbar na ba amma ni na riƙe taki ko?, lallaikam baki ɗaukeni da wani amfani ba ko? Ta yi ƙasa da kai ta ce "To ai kaine ka tafi baka sake dawowa ba nima ai ban...sai tayi shiru ta kasa ƙarasawa ya ce "Umhum ina jinki? Ta ce "To ban riƙe numbar ka ba. Ya ce to yanzu zan baki tawa sai ki riƙe kuma yanzu. Ta ce "To. Take ya saka mata Numbar sa yayi seveng ya kira saiga numbar nan ta baiyana ya ce "Kema karɓi kimin seve da kanki? Ta karɓa wayar ta yi seve da Nana. Ya duba ya gani ya ce "Ni haka nayi wa nurbarki? Duba kigani? Ya bata ta duba taga yasa my heart. Ta ce "Nagani ya ce "Me nasa? Ta ce "Ai ba sai na faɗa ba? Ya ce "Ni kuma sai kin faɗa? Ta ce "To my heart. Ta rufe ido a lamar kunya. ya ce "Yawwa haka zaki dinga kirana? Nan dai suka sha hira irin ta masoya sosai kafin ya mata sallama ya tafi. Takai minty ashirin a gurin tana jin daɗin zantukan da yamata kafin ta shiga gida. Bayan ya tafi AJ ya dawo ɗauke da kayan abinci masu yawa da kayan shayi, harda nama. Bayan ya zaunane Innah ta sanar masa da cewar wannan abokin nasa yazo wanda ya tai makemu a gidan ƴan sanda kuma harda kuɗi ya bamu? AJ ya ce "Allah sarki to ina ya ke? Nana ta ce "Ya bani numbar idan ka dawo a baka? Ya ce "To bari wayata tayi chaji zan ƙarba . Salis kuwa bai je gidaba saida ya tsaya ya sayowa Sarah da Samuel wa ya ganin duk kansu basudawaya sannan yayi salllar magariba da isha kafin ya nufo unguwarsu. Koda ya iso gida bai samu damar sun zauna da Hajiya Babba ba sai kawai ya ba Samuel tasa wayar ita kuma Sarah saida safe idan zasu tafi Katungu. Ai kuwa Samuel yayi murna sosai ganin babbar wayar da ya bashi. Muhammad ne a ɗakinsa na sama daga shi sai matar tasa bayan ya gama sanar da ita abinda malam ya ce masa game da auransu. Hajiya Babba ta ce "Ƙaryane addinin musulunci ba haka ya ce ba. Da mamaki Muhammad ya ce "To me kike nufi? Ta ce "A tsarin Addinimu sai an ɗaura wani auran kafin zamammu ya halarta. Muhammad ya ce "A'a Addinimu wato addinin Musulunci ya ce "Idan har bakiyi wani auranba to kawai zamucigaba da zamammu ne na ma'aurata, idan kuma kinyi wani auran to zaki zaɓa ko ni ko wanda kika aura ɗin. "A'a ni gaskiya ban yarda da wannan malamin ba, ai koda banyi aureba dolene a sake ɗaura wani auran gudun gujewa wani abun. Da mamaki Muhammd ya ke kallonta ya ce "Aisha ko dai kinyi aurene bayan bananann? Ya tambayeta cike da kokonto a ransa. Cikin tsoro da fargaba da rawar baƙi ta fara cewa "No a'a kawai fa dai ni kawai naga hakan shine dai-dai, kuma ma idan baka yarda daniba kaje ka tambayi su Salis sunema suka hana n"... "Ok Tom kwata kiyi barci ya isa na gane idan mun dawo daga Katungu gobe zamuyi magana. Hajiya Babba wacce kamar jira takeyi sai kawai ta kwata tana jan bargo har fuskarta. Muhammad ya gyra mata kwanciya ya gir-giza kai ya fita. Eliza kuwa koda ta dawo asbitiin aka sanar mata da cewar Samuel ya gudu, sai kawai ta hau zagin kowa dake asibitin , da gyra aka rarrashinta ta haƙura amma ta ce anemo mata ɗanta. Tunani takeyi akan ta barsu a gidan su Solomon ne ko dai taje ta kwaso kayanta domin kuwa tanada tabbacin can suka tafi. Wata zuciyar ta ce "idan kika barsu kuma suka koma yin Sallha fa? Wata ta ce "Ta ɗaukosu ta kaisu gidan babanta, a haka dai ta yanke a kan gobe zataje gidan ta karɓo yaranta. Washegari dukkansu ƴan gidan suka tattara izuwa ƙauyansu wato Katungu, garinda Salis da Laɗifa basu taɓa zuwaba domin gudun abinda zaije ya dawo. Suma kansu su Samuel ɗin sau biyu suka taɓa zuwa, Titi da Usha ma dai bawani zuwa sukeba. Titi da Usha da da Samuel da Laɗifa a mota ɗaya, yayinda Usha ne ke jan su, Titi kuma na gaba, Laɗifa da Samuel na baya. Hajiya Babba da Muhammad da Usman suma suna mota ɗaya. Sai Salis da Sarah da Umar suma a mota ɗaya. AJ kuwa suna zaune bayan sun gama karyawa sai jin sallama sukayi, bayan aJ ya fitane yaga wata dalleliyar mota a waje, ƙirar corola. Wani sanyin daɗi yaji yana mai hamdala a zuciyarsa, dama tun ɗazu tunanin da ya keyi kenan. Bayan mutumin ya shiga ne suka gaisa da Innah yayi kamar yanda Hajiya Babba ta ce masa, ya mallakawa AJ gida da mota harda wasu kuɗadan, ya ciro takardun gidan ya miƙawa Innah sannan ya miƙawa AJ makullin motar....📝 *Kunsan ranar Lahadi bana typing amm gashi yau na muku* *Anya masu karatu wannan sirrin zai ɓoyj* ? *To kunjifa a adddinin su Hajiya Babba sai an ɗaura wani auran ko a wani addinin ta ke ohooo🤗* *Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata* *By S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE3️⃣8️⃣* .... Innah da Nana harma da AJ duk bakunannsu sunƙi rufuwa tsabar farin ciki da abun alherin da ya samesu, Innah ta kamo ƴan jikokinta guda biyu ta rungumosu tana saka musu albarka kamar ba gobe. Kallon kuɗin da mutum ya ajiye musu a cewar sa wai AJ ɗin ya kama wata sana'ar. Nana ta ce "Shekinan yaya yanzu babumu ba zama a wannan gidan. Ta faɗa tana jin wani sanyin daɗi na ratsa zuciyarta. Innah ta ce "Kai amma gaskiya wannan ogan naka ɗan arziƙine Allah ya saka masa da albarka. Dukkansu suka amsa da amin sannan AJ ya kwaso wannnan kuɗin ya ƙirga su naira dubu ɗari biyu ne dai-dai. Innah ta ce "To Abdauljabaru kaga dai yanda Allah yayi damu cikin lokaci ƙan-ƙani sai ka sake nutsuwa domin kaima yanzu Allah ya baka naka, kuma ba ruwanka da surutu domin kasan halin wannan zamanin namu ana jinka da ɗan abun harziƙi sai kaga ana neman halakaka. "AJ ya ce "Haba Innah a naira dubu ɗari biyun za'a wani damu dani, to walhi a wani gidan ma wannan shine kuɗin abincisu na rana ɗaya. Innah ta rafko salamulai tana tafa hannaye a lamar mamaki. Haka dai tai masa faɗa sosai kafin ta ce masa ba yanzu zasu koma gidan ba sai ya fara sana'a tukunna, AJ da yake son a gobe subar unguwar ya ce "No no no ai kawai tattarwa zamuyi gobe-gobe mubar wanga unguwa, sannan ya ce yanzuma zasu tafi da Nana domin ganin gidan. Innah ta ce "A wani unguwa gidan ya ke? "Innah ai ba a kusa muke ba can wajan gidan kwamna nefa. "Har kusa da gidan kwamna, to ai naga gurin yayi nisa, to amma Allah dai ya kyuta. Haka Nana da AJ sukayi wanka suka shirya izuwa sabon gidansu. A'jinkin takardun gidan ya duba yaga sunan unguwar da gidan harda Numbar gidan. Gidane ɗan dai-dai mai ɗauke da ɗakuna shida, sai toilet a kowani ɗaki kicin guda ɗaya palon biyu babba da ƙarami, sai filin gidan mai ɗan girma sai gurin da motoci kamar huɗu zasu faka. Gidan yayi asalin haɗuwa, da a lama dai sabon gidane domin babu komai a ciki. Haka suka dawo cike da shawƙin gidan. A ranar kuma suka ƙara fita da Nana domin siyan wasu kayan su fara kaiwa gidan batare da Innah ta saniba. Dubu ɗari biyun da Hajiya Babba ta basu ya haɗa da sauran kuɗin da Hajiya babbar ta bashi tun kafin su tafi Cemeron ya haɗa suka shiga kasuwa da sabuwar motarsa. Duk gurin da yaga wanda ya sani sai ya sauƙe glas ɗin motar ya ɗaga musu hannu, masu mamaki sunayi masu tambayar junansu nayi. Burin AJ kenan a ce yau ya mallaki gida da mota ga kuma kudaɗe masu yawa, burinsa ya ganshi a cikin mota wacce kowa ya ganta sai ya ƙara kalla. Yana cikin tafiya wata zuciyar ta ce masa "Yanzu meme burinka na gaba? Yayi shiru yana tunani sai kawai yaji wata zuciyar ta ce "Sarah ce burinka na gaba, ta maka hallacci ta soka da zuciya ɗaya. Afili ya ce "No ƙaryane ba gaskiya bane ba zai taɓa faruwaba Addininmu ba ɗayaba. *HANYAR KATUNGU* Salis ya kalli Sarah wacce gaba ɗaya tayi nisa a cikin tunanin da takeyi, izuwa yanzu ta haɗa komai da zai tabbatar da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba. To amma yaushe kuma a ina? Batasan hawaye na mata zirya afuskartaba tana jin wani sabon son AJ ɗin na shigarta, ita koma me zaiyi tana sonsa, tana haka har saida taji Salis ya kira sunanta. "Sarah! Sarah!. Da sauri ta goge idon ta ta amsa da "Yes Bro? Sai ya ciro wayar da ya sayo mata ya miƙa mata ba tare da yace mata komai ba, amma yana lura da ita ta gefen ido. Hanunta tasa ta karɓa tana kallonsa, domin jin ƙarin bayani. "Wayar ki ce idan muka dawo kije kiyi welcome bak. Taji daɗin kyutar har cikin zuciyarta, amma a fili sai ta kasa nuna masa cewar taji taɗin sai kawai bata ce komai ba ta ajiye wayar a kan cinyarta ta ci gaba da kallon waje. "Sarah inason muyi magana da ke akan saurayinki, kuma banaso kimin ƙarya? Lokaci ɗaya ta ɗaga kai ta kalleshi sai kuma ta gyara zamanta da kyu tana kallonsa yana tuƙinsa kamar ba shine yayi maganar ba. "AJ saurayinki ne, ni kuma a bokinane to saboda haka inaso na miki tambaya akansa? Ya sake yin maganar yana cigaba da tuƙinsa. "AJ abokinka ne? Itama ta tambayeshi tana kallon kyawawan i danunsa da ya zubasu a kan ƙwaltar da suka tafiya? "Eh abokinane sannan kuma yayanane. "Yayanka kamar ya? Sai kuma ya waske ya ce "AJ yana turaki ki ɗaukarwa Daddy kuɗi ki kai masa ko? Da sauri ta sake kallonsa ta ce "Eh amma waye ya sanar maka? Ya ce "Bani labarin haɗuwarku da rabuwarku? Sarah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai bamu rabuba har yanzu muna tare, amma naji Laɗifa ta ce min wai ya taɓa yin aiki a gidan ku ko? "Eh yayi aiki amma fa aikin bai kwana ko ɗaya ba sukayi tafiya da Hajiya, to bayan ya dawo n... Sai kuma Salis yayi shiru yana tunani ya ce "Innah ta ce yaje Niger baya gida a ka kamasu, kuma lokacin yayi dai-dai da tafiyan da sukayi tare da Hajiya, kuma shi baima san ko tare suka dawoba. Ya ce "Lokacin da Daddy ya kamaki AJ yana gari? Itama ta shiga tunanin ranar rabuwarsu da AJ ta ƙarshe. Idan bata mantaba ranar har kuɗi ya bata bayan sun dawo daga club, kuma a washe garin ranar ne a ka kamata, kuma dama ya ce mata zai tafi ba laillai ta sake ganin sa ba. A yanzu kam Sarah ta gama yarda da cewar AJ aure sukayi da Hajiya Babba auranma na kuɗi. "Ya ce min zaiyi tafiya ne, bayan haka ban sake ganin saba sai da yazo gidanmu. Nan Sarah ta bashi labarin haɗuwarsu da AJ har zuwa ranar da suka rabu. Salis ya ce "AJ yanada kirki matsala sa ɗaya shine son kuɗi, amma banda wannan gayan ya iya zama da mutane ga sakin fuska ga iya mu'a'mula da mutane, amma a kan kuɗi zai iya yin komai indai ba zai taɓa mutuncinsaba to amma ya akai yake turaki satar kuɗi!? Sarah tayi shiru tana tunanin kodai a addininsu idan mutum ya aure mamar a bokinsa ba wani abu bane! Ko kuma Salis ɗin bai sani bane, to ko dai ta sanar masa! Haka dai ta keta saƙe-saƙe, shi kuma Salis sai yabon halin AJ yakeyi, tawani gefen kuma yana haɗawa da Nana. Kamar ta tambayeshi sauran abu guda biyun da ta riƙe a hirarr su AJ da Hajiya Babba amma tana tsoro. To me ma zan tabaya bayan komai ya baiyana kansa. Ɓangaren su Samuel da laɗifa kuwa sukam soyayya suke zubawa babu kunyar kowa, domin izuwa yanzu Samuel ya zubar da makaman yaƙinsa yana son laɗifa ta shiga daga cikin zuciyarsa tukunna. Hajiya Babba kuwa dukda irin damuwoyin dake cunkushe a zuciyarta hakan bai hana sarkin ɓarayin duniya barci yayi wuff da itaba. Tafiyar a'wa ɗaya da wasu ƴan mutuna sukayi sai gasu a bakin titin da zai sadasu da cikin ƙwayan katunku. Babu laifi yanzu ƙauyan sun samu burji har cikin gari. Usman da Umar da Muhammad tun daga nan suka fafa kalle-kalke domin kuwa garin ya koma musu kamar ba shiba. Titi ce da yake ita tazo tin bayan samun wannan burjin sai ta dinga nuna musu hanya har suka shigo cikin garin. A tsarin dokar garin Katungu duk wani musulmi idan ya sake ya shiga cikin garinnan tofa ya zama gawa, tun labarin da ya riskesu na cewar Solomon ya mayar da yaransu masu yin Sallah kuma an kashesu. Duk wanda ya ɗaga kai ya kalli jerin motocin to fa ko mai ya keyi sai ajiye ya biyo bayansu. Kafin su ƙarasa cikin tsakiyar garin har sama da mutane ɗari maza da mata sun biyosu, wasu da abun duka wasu kuma domin ganewa idanunsu. Lokacin da motarsu ta tsaya a tsakiyar garin kuwa mutanene suka zagayesu kaman dai a'na wani taron. Garin ko kaɗan basa son baƙo, shi yasa duk wanda zai shigo sai an sani domin tsaro. Titi da Usha ne suka fara fitowa ai kuwa ana ganin su kowa bakinsa ya washe domin idan har tazo tana musu wani ɗan isaninn, amma ita idan zatazo to a mota ɗaya take zuwa, ko shi Daniyel lokacin da yazo mota ɗayace. Ganin haka yasa kowa ya fara komawa gurin aikinsa. Saida a ka watse saura ƴan kaɗan kafin Titi ta kalli Uncle ɗinsu ta sanar masa da halin da a ke ciki. Da sauri ya ce "Ina suke? Kafin Titi ta fara magana har ya fara ihuuu yana sanar musu da cewar Tena da Gumma sun dawo. Kafin kace me, saiga mutanen da suka tafi sun dawo domin jin abunda Uncle ɗin ke cewa. Tena da Gumma irin mutanennene da ko sun mutu ba'a saurin mancewa dasu saboda sunan da sukayi a garin. Ganin haka yasa Titi cewa su fito. Ai kuwa dukkansu suka fito harda Hajiya Babba da sai yanzu ta farka daga barcinta, gaba ɗaya tayi lakwas. Tena wato Usman shine ya fara fitowa sai kuma Gumma wato Umar. Sai Solomon Muhammad. Kafin kace me, an'hau koke-koke, ma haifin Usman yazo ya rungumi sa yana fashewa da kuka, shi dai Usman jira yake yaga ma haifiyarsa da ƙanwarsa guda ɗaya da suke tare. Cikin yaransu na tibi ya ce "Baba ina mamana da ƙanwata? Baban ya sake fashewa da kuka ya sanar masa da cewar a ciwon zuciyane ya kasheta, kuma ta mutu da burin idan har ta sake ganinn Solomon sai ta kasheshi. Usman yayi kuka sosai ya ce ƙanwarsa fa? ita ma a ka sanar masa cewar tayi aure gurin aihuwa ta mutu. Nan take Usman ya fita a haiyacinsa yana kuka kamar ƙaramin yaro. Umar kuwa duk gaba ɗaya uwa da uban sun mutu, sa ƙaninsa guda ɗaya wanda ya rage masa, shi ɗinma cikin rashin lafiya yake. Haka ya huce gidan nasu ya tarar da ƙanin nasa a kwace cikin ciwo. Ai kuwa ƙaninn ganin sa ya ganeshi, yayi kuka haɗida murna da farin cikin sake ganin ɗan uwan nasa. Su kuwa su Muhammad ganin haka sai suka nufi gidan Uncle ɗinsu. Samuel da Sarah harma da Usha ba wani sanin su a kayi sosai a garinba domin basa zuwa, hakanne yasa suka zama baƙi, amma hakan bai hana matar Uncle ɗin nasu ganesuba. Tini jama'ar gari suka gama shirya yanda zasubi Muhammad har gida su kasheshi domin sun san da cewar shine ya sace su Gumma. Shigarsu gidan bada daɗewa ba aka fara dukan gidan wai sai an fito da duk wasu masu yin Sallah an kashe. Shi kuma Uncle ɗin nasu lokacin ya fita izuwa gidan Sarkin garin ya sanar masa da abun da Titi ta sanar masa a kan cewar duk wannan abun Daniyel ne ya haɗa. Matar Uncle ce da Titi suka fito suna bada haƙuri amma ina suka ce Walhi sai an kashesu. Ana cikin haka sarkin garin ya iso gurin cikin bada umarni ya ce kowa ya tsaya, aikuwa kowa yayi tsait. Ya ce "Duk a tattara a je fadarsa harda su Muhammad ɗin da su Gumma da Tena. *Elliza* Koda ta iso gidan ta tarar da shi a rufe sai ta fara dukun gidan tana zagi. Jin haka yasa mai gadi fitowa yana tambayar waye? "Cikin English da yaransu ta fara maga wanda har tagama mai gadi bai gane ko abu ɗayaba. Ganin tana kiran sunan Sarah da Samuel ya sa mai gatin da bai san ko suwayeba ya ce "Hajiya ba nan gidan bane. Yana faɗa ya koma ciki ya rufe gidan yana jin haushin ta zu ta tasheshi daga barcinsa. Haka ta bar gurin cike da tunanin ina kuma suka tafi. Ɓangaren Daniyel kuwa. Tinda a ka rufeshi a wani ɗaki babu wanda ya ƙara bi ta kansa. Ba'a hanashi ci ko sha ba. amma bai isa ya leƙa ko nan da wajeba ko kuma yayi amfani da waya ba har sai ogan nasu yazo. Haka yake rayuwa shi ɗaya cikin wannan ɗakin ga ac ga fanka ga abinci mai rai da lafiya ga ruwan wanka ga kayan sawa amma a hakan yana jin kansa a taƙure. Yana cikin wannan halin ya tuno irin halinda su Solomon suka shiga, suda ba kullum suke samun abinciba ga babu wanka sai kusan watannani biyu za'a sakar musu da ruwan toilet. Azuciyarsa ya ce "Ooo my GOD! Why why why!. Zaune suke a fadar sarkin garin dukkansu. Bayan Muhammad ya gama basu labarin komai ne sannan a ka tambayi su Umar suma suka tabbatar da cewa hakane. Kowa dake gurin mamaki ya kamashi harda shi kansa Uncle ɗin nasu. Dama kowa yasan halin Muhammad tin lokacin yana ƙwayan yanada haƙuri ga kawar da kai a abun da babu ruwansa, ga kuma baya ƙarya, idan har ya faɗi magana to ana tabbatar da gaskiyasa. Su Usman suka ƙara da yabon halin Muhammad ɗin harda irin halayyar sa na gaskiya. Daga ƙarshe suka gabatar da Salis da laɗifa a matsayin yaransa sai Hajiya Babba a matsayin matarsa. Sai kuma su Sarah da Samuel matsayin yaran Daniyel. Nan fa sarki ya tambayi dalilin zaman yaran Daniyel a gurinsa. Nan suka sanar musu da ƙoƙarin kashesu da yayi kuma ya gudu. Gaba ɗaya garin kowa ya tausaya musu, kowa na tsinewa Daniyel, badan shiɗin soja bane da shi sarkin da kansa zai sa a yanke masa hukumci. Koda suke ba musulmai ba amma suma addidinsu bai amince da zalunciba. Sunyi niyar su dawo a ranar amma dole saida suka kwana. Hajiya Babba kam ba haka tasoba shima kansa Salis yaso ace sun koma, ita kuwa Laɗifa a fili take nuna bata son garin. Muhammad kuwa farin ciki ba'a musaltawa suma su Usman da Umar haka kana ganin su kasan suna cikin farinciki duk da cewar rashin iyaye ba ƙaramin abu bane . Nan fa a ka fara raba abubuwan da a ka kawo, kusan kowani gida saida suka samu nasu tsarabar. Dama kuma haka yakeyi duk lokacin da yazo garin to kusan kowani gida sai sun samu kasonsu. Washe gari da safe suka shirya zasu tafi. Salis ya bawa Sarkin garin kuɗi masu yawa, Uncle ɗin suma haka, sai su Umar da Usman suma Salis ya ce idan suka huta sai suzo har gida su sameshi, haka suma ya musu kyauta , kowa dake ƙauyan saida ya yabawa Salis da irin kyutar da yayi, itama Hajiya Babba ta ɗan rabawa mata cikin juriya da halin da take ciki. Haka suka tattara suka kamo hanya cikin jin daɗin yanda abun yazo da sauƙ. A hanya ya ke sanarwa da Daddy Muhammad cewar ya lura kamar fa Hajiya bata lafiya, hakanne yasa yace to su huce aasbiti batare da ta saniba.....📝 *hammmm garin daɗi a kusa* *Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata* *By S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE3️⃣9️⃣* .......Kamar Hajiya Babba tasan maganar da sukeyi sai ta ɗauki wayarta ta kira Dr Lurwan a kan yazo gida ya sameta bata jin daɗi. Ganin sun ɗauki hanyar asbitine ya sa ta sanar musu sewar ai ta kira Dr yana zuwa gida yanzu. Gidan Anty Titi a ka fara zuwa saida suka tsaya mijinta yazo suka gaisa da Muhammad da Hajiya Babba. Shima dai ya jinjina wannan lamarin na Daniyel. Samuel da Sarah sukace zasu bi su Hajiya Babba hakan ne yasa suka tafi tare. Koda suka isa gida kowa ya nufi ɗakinsa cike da gajiya da yunwa. Shi kuma Salis ya kira Numbar Nana har kiran ya tsinke bata ɗaga ba sai ya sake kira a karo na biyu, saida ta kusa tsinkewa ta ɗaga ta na sallama. Sarah da Samuel suka shirya domin zuwa yin welcome bak, Laɗifa ta ce zata rakasu. Salis ya basu mota ɗaya ya ce su tafi da ita. Haka Samuel ya tuƙasu suka bar gidan. Suna fita Dr ya shigo ya tarar da Muhammad shi kaɗai a zaune a palo ya na tunani. Ganinn Dr yasa ya haura sama domin kira Hajiya Babba. Cikin mamaki yake jin kuka na tashi daga cikin ɗakin na ta. Tsayawa ya yi yana saurara da kyu ya tabbatar da kukantane sai kuma ya tura ƙofar ɗakin ya shiga kamar mai tsoron shiga ɗakin. A sunkuye ya sameta a bakin gadon ta na rusar kuka kamar ba gobe. Cikin mamaki ya ce "Aisha" Da sauri ta ɗago haɗi da share hawaye ta tana kallonsa cikin tsoro. "Lafiya ku wa? "Cikin rashin sanin abun cewa ta ce "Kaina ne kemin ciwo kuma ya kusa dainawa, ta faɗa tana miƙewa daga durƙushen da take. Kallonta ya ke yi da mamaki ya ce "Dr yazo ya na palo ya na jirranki. Ya na faɗa ta bar gurin da sauri ta na ɓoye wayar dake hannunta. Muhammad ya bi bayanta yana gir-giza kai. Dr ya tambayeta abun da ke damunta ta sanar masa shi kuma ya sanar mata da cewar kawai damuwa ta saka a ranta da tunani saboda haka idan ma wani abunne ke damunta to tayi ƙoƙarin magance shi. Hajiya Babba ta ce "Kai Dr to maganar abincifa? Kwata-kwata fa bana son cin komai a cikin ƴan kwanakinnan, ga saurin tashin zuciya wanda ni duk ban saba da suba, ga shegen barci. Da Hajiya Babba tasan maganar da Dr zai faɗa mata kenan da bata sanar da shi waɗannan abubuwan ba. Cikin wasa Dr ya kalli Muhammad da Hajiya Babba a tare ya ce "To ko ƙaruwa a ka samu ne Alhaji? Ya faɗa yana sosa kai cikin jin kunya. Lokaci ɗaya gabanta ya faɗi ta furta ƙaruwa?! Me ne ne ƙaruwa? Ta yi maganar a zuciya fatar da ta san ta fito filiba. "Ina nufin ko dai juna biyu k"...."Ya isa haka Dr mun gode tashi ka fita munji sai anjima. Hajiya Babba ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai da tsoro. Da mamaki Dr ya meke zai fita daga dakin ganin yanda lokaci daya hajiyar tasa ta koma kamar mara lafiya. "Dawo ka zauna. Yaji muryar Muhammad babu a lamar wasa. Muhammad ya kalli hajiya ya ce "Kin sanar masa da damuwar ki amma kuma tun kafin ya gama sanar miki da damuwar kin koreshi mai hakan ke nufi? "Daga kawai na ce masa bani da lafiya sai ya fara haɗani da ciki! Bashi da hankali ne? Ko an faɗa masa aikin likita haukane? To walhi sai ya barmin gida yanzunnan dan uwarsa. Hajiya Babba ta inda take shiga bata nan take fita ba, hakan ne ya sa Muhammad nazarin ta sannan ya kalli Dr ya ce "Wannan abubuwan da ka lissafo ma ta, shin da gaske alamune na masu ciki? Dr ya kalli Hajiya da ta tsaya da zage-zagen ta na kallonsu ya ce "Eh Alhaji wannan alamunne na shigar sabon ciki. Cikin rashin wa sa Muhammad ya ce "Inaso yanzu ka gwada min ita domin tabbatarwa? "Da sauri ta fara surutai marasa kan gado domin kuwa ita kanta sai yanzu ta ke gano wasu alamu da Dr ya ce. "Alhaji ai dole sai tayi fitsari tukun zamu auna da shi? Muhammad ya kalleta alamar ta je tayi fitsari. Da sauri ta ce "To. Ta na haurawa Muhammad ya bita a baya domin shima yanzu ya gama yarda da cewar ta na ɓoye masa wani abunne. Ko da ya shiga ɗakin ya tarar har ta ɗebo ruwa a kwalbar turare zata juya. Sai kawai ta ganshi a gurin a tsaye ya na kallonta. Tsabar tsoro ta saki kalbar ta na kallonsa. "Aisha mai ke ke ɓiyemin? Sanar dani komai kafin mukai ga aikata haramcin? Ya ƙara cikin wata muryar da tasa kukkan gaɓoɓin jikinta yin sanyi. Kukane ya kufce mata ta na kallon sa cikin so sa ƙaunarsa. Ya sake cewa "ki sanar dani komai ni mai tsaya mikene da yarda Allah karkiji komai, ko kin mata alƙawarin da na ɗaukarwa ogana kuma babana Salisu ne? Ganin ta yi sanyne yasa ya ce "Sanar sani komai karki damu nasan ki kuma nasan abunda zaki iya aikatawa da wanda bazaki iyaba. "Hajiya cikin kuka ta ce "Babu komai walhi ban aikata konaiba pls. "To shikenan yanzu tinda har bazaki sanar min ba to kiyi fitsarin Dr na jiranki? Ta ce "No pls karka min haka dan Allah? "Ok to idan har kin yarda da ni kuma kinsan zan iya rufa miki asiri to ki sanar min da komai. Cikin kuka ta fara cewa... "Nayi Aure! Kuma kuma ku ku ma mun rabu da mijin shekaran jiiya, amma babu wanda yasan da auran. Ta ƙarasa ta na fashewa da wani irin kuka mai tafiya da imanin mai sauraronsa. Lokaci ɗaya Muhammad ya ji ɗakin na juya masa, sai kawai ya ƙura mata ido yana kallon yanda ta ke kuka kamar an zare mata nufashi. "Saboda kinyi wani auren ne kike kuka ko saboda kin samu ciki? Ko saboda rabuwar da kukayi, kuma wani irin aurene wannan wanda kowa bai saniba? Sanar min da gaskiya Aisha? "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Wannan wani irin abun kunya ta kwasowa zuri'ar ta? Ta ma rasa ta ina zata fara masa bayani tsabar kunyarsa da ta keji. Ya ce "Aure kikace kinyi ba wani abun kunyarba, to menene abun tsoro a ciki? Idan ma nine kike tunanin zan damu to karma kisa komai a ranki domin da ma a tsarin Addinin Musulunci shekara huɗu ya bayar ga macen da mijinta ya tafi bai dawoba ta yi aure mutuƙar bazata iya jurewa ba, to bare kuma ke da nasan kin fita daban a cikin sauran mata. Hajiya Babba ta ce "Dan Allah banaso su Salis susan da wannan zancen? Muhammad dai badan zai iya hakan ba ya ce ya yarda. Hajiya Babba ta kwashe komai da ya faru tsakanin ta da AJ har zuwa ranar da ya saketa da kuma kuɗin da ta bashi. Sannan ta ɗora da cewar...."Walhi abokin Salis ne sun shaƙu sosai domin shinema ya ka woshi gida har na ganshi walhi ina kunyar su san da wannan zancen. Muhammad sarkin haƙuri ya ce "Yanzu dai kema baki saniba ko kina da ciki ko a kasin sa ko? Ta gyaɗa kai. Sai ya ce "Je kiyi fitsarin ki kawo masa ya na palo. Ya na faɗa ya fita ya bar ɗakin cikin wani yanayi. Dr Lurwan ya ce "Zuwa gobe zan kawo muku da sakamakon in Allah ya kaimu. "No yanzunnan zaka kawo mana. Dr ya ce "Ok an gama in sha Allah kuwa. Ya na tashi zai fita saiga Salis ya fito daga ɗakibnsa bayan ya gama waya da Nana. Suna haɗuwa Dr ya bashi hannu ya na tambayarsa ƙarfin jiki. Ya amsa da lafiya Alhamdu lillh. Sannan Dr ya bar gidan cikin sauri. Salis ya zauna a kujerar da ke kallon Hajiya Babba zaiyi magana Muhammad ya ce "Dama ba tare kuka tafi da su Sarah ba ne? Kallon fuskokinsu ya yi yaga a lamar damuwa sai ya haɗiye maganar da yazo da ita ya ce "Daddy me Dr ya ce yana damun Hajiya ? Ta ke cikin Hajiya ya murɗa ai kuwa da sauri ta riƙe cikinta ta haura sama tana jin kashin na ƙoƙarin fitowa. Cikin dauriya Muhammad ya ce "Kawai zazzaɓi ne ba komai ba, kuma ya tafi ya kawo ma ta magani. Salis ya ce "To Allah ya sawaƙe. Daga haka ya tashi ya fita daga gidan dama a shirye ya fito. Muhammad ya yi shiru ya na tunanin abun yi yanzu! Ya zama dole yarannan suji, ai ba zina suka aikataba, saboda haka dole suji, kuma asan abinyi wannan ba maganar ɓoyewa ba ce, domin tabbas a kwai kura-kurai a cikin auran da ma sakin da a kayi. Salis na fita gidan su Nana ya nufa cikin rashin kuzari domin yaso a ce yau ya yi magana da iyayensa a kan yarinyar da zai aura. Zaune ya ke a cikin motar bayan ya kirata ya sanar ma ma da cewar ya na ƙofar gida. Kallo Innah ta yi sai kuma ta fashe da dariya ganin yanda unnar ke kallonta tin ɗazu. "Innah ko dai kina koyan kwalliya irin wannan kallo haka? "Innah ta yi tsaki ta kawar da kai ge fe ba tare da ta ce komaiba. ""Innah dole nefa sai kin koyi kwalliya domin idan muka koma sabon gidanmu to fa wanka zakici irin ta hajiyoyinnan. Sai a lokacin Innah ta magantu ta ce "Wai ni a cikin raya guda biyunnan da suke zuwa gurinki wannane ne ya keyi da gaske? Domin ya kamata a ce izuwa yanzu munsan wanda ke zuwa da gaskiya? Nana ta tsaya da ɗaurin kwalin ta ce "To da an faɗa miki da wasa suke zuwa? Kuma ai diukansu ina so. Ta yi maganar cikin tsokana. Inna ta ce "Au to sai ki haɗa su ga ba ɗaya ki aura rasa kunya. Yanzu waye yazo a cikin su? Dr ne ko Salisu ne? Nana ta ce "Wai Innah ina ruwankine? Ko kina son ɗaya daga cikinsu ne? To Salis ne, ta faɗa tayi hanyar fita da ga ɗakin. Innah ta dawo da ita da cewar "Idan kin fita ki toromin shi yanzu zamuyi magana. Kallonta ya keyi har ta ƙaraso bakin motar bai ɗauke kansaba. Har ga Allah bai san irin don da ya kewa Nana ba, a koda yaushe cikin tinaninta ya ke, dik lokacin da ya ɗaga kai ya kalleta sai yaji wani sanyi na daban a cikin ransa. Da sauri ya buɗe murfin motar haɗi da sakin murmushi mai sanyi. "Kinyi kyu sosai kamar na saceki na gudu. Ya faɗa ba tare da ya amsa gaisuwar da ta ke masa ba. "Na gode sosai . Kaima kayi kyu fiye da nawa. Itama ta maryar masa da amsa ta na jin daɗin kasan cewa da shi. "Ni ne nayi kyu kallenifa ko wanka banyiba? "Ni dai kamin kyu sosai. "To nagode. Sai ya kafe dara-daran idanunta da kallo batare da ya sake cewa komaiba. Itama ta tsinci kanta da kallonsa ta na jin shwƙin da bata taɓaji ba. Sun ɗauki lokaci a haka kafin motar babban yaya ta nufo gurin cikin gudan sa da yasa ba a duk lokacin da zai shigo unguwar ta su. Daga nesa ya ke binsu da kallo har baisan lokacin da ya daki motar Salis ɗin dake pake a gurin ba. Zuciyarsa ce ta hau tsalle ganin Salis da Nana a irin wannan yaninnda ba sai ka tambayaba kasan masoyansa. A ranar da yamma Dr ya kawo musu saka mako, kuma ya nu na tana ɗauke da ciki na tsawon sati uku. Hajiya Babba ta yi kuka har saida Muhammad ya ja mata kunne akan cewar ai hakanne zaisa yaran su gano cewar a kwai matsala. "Dan Allah a zubar da wannan cikin? Cewar Hajiya Babba cikin kuka? "Karki sa ke kice zaki fara ai kata kuskuren zubar da ɗan sunna, Idan har haka ta faru to walhi zakiyi mamaki. Wannan yaron walhi sai kin haifeshi domin da ubansa kuma kike zancen kar su Salis su sani to tayaya zaki raini cikin a gidan da suke? Kuma ya zama dole a sanar da uban ya ron. Cikin sauri da tsoro ido ta ce "To dan Allah ka ɗauki cikin a matsayin naka sai kawai muce bayan dawowarka muka samu, idan na ai'hu sai mu riƙe yaron ba tare da kowa ya saniba, Pls dan Allah kamin wannan alfarmar dan darajar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama. Hajiya ta ƙarasa ta na kamo ƙaffun Muhammad. "Dan Allah kamin rai ka rufamin a sari walhi kunya zanji bazan iya kallon Salis da Laɗifa na ce na auri yaronnan har ya min cikiba, dan darajar Allah ka taimakamin? Ta na kuka kanta a sun kuye a ƙasa tana na damar wannan auran da tayi, wanda take jinsa tamkar a ce ciki shige ta je tayi. Ganin Muhammad ya yi shirune ya sa ta ƙara cewar "Dan Allah ko a zubar da cikin ko kuma mu karɓi yaron a matsayin namu? Dan Allah ka zaɓi ɗaya, walhi nayi na da ma, na tuba....📝 *Tofa! Muhammad sarkin tausayi da yafiya, shin wanne kuke ganin zai zaɓa a cikin alfarmar da Matarsa ta nema?* *GA AJ GA SALIS* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *S REZA....* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣0️⃣🔕* ....."Shin Aisha i'na hankalin ki da tunanin ki suka ta fi? Wannan abun da kika ai kata ba haramun ba ne, Addininmu bai yi hani ba amma gaba ɗaya kin hana kan ki sukuni haba Aisha!? "Eh na san ba haramun ba ne, am'ma wallhi na kwam'maci da na ai kata haramun ɗin da wann! "Subhana lillahi! A'uzu billahi! Aisha ba ki da hankali ne? Kinsan mai kike faɗa kuwa? Ko kinyi hauka ne? "Ban yi haukaba am'ma na tabbatar zan yi hauka idan har Salis da Laɗifa suka samu wannan labarin. Hajiya Babba ta ƙara sa ta na sake fashewa da wani sabon kukan. Muhammad ya na so ya rarrashinta amma ya rasa mai zai ce ma ta sai kawai ya fita da ga ɗakin cikin damuwa. Ya na jin yan da take ihun kiran sunan sa am'ma ya fita da ga ɗakin. Kuka take yi sosai kai ka rantse da Allah dukanta a ke yi. "AJ ka cuceni ka tuna min asiri ci ki! Ni ni ni Aisha ɗauke da cikin abokin ɗana? Allah ka sa na mutu kafin ganinn ranar tonun wannan asirin! Muhammad da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin ya shigo cikin ɗakin cikin wa ni sabon salon tashin hankalin ya ce... "Ya zama dole uban cikin da ke jikin ki ya san da wannan zancen, sannan dole yaranki suma susan da wannan abun arziƙin, bazan bi ye miki ki sake ai kata wa ni kuskuren ba, wanda kika yi a bayama ya isa haka, ki gode wa Allah ba cikin shege ba ne, walhi i'na ta ya ki murna da Allah ya tsareki da ga aikata alfasha. "Sannan ki sa ni wannan kukan da saɓon da ki ke yi ba shine ma futa ba. Ya na faɗa ya ƙara barin ɗakin jin a lamar da wowar su Sarah. *AJ POV* Idon sa a kan su ya fito da ga motar ta sa ya na bin Salis da wani irin kallon tsoron kar abin da zuciyarsa ta aiyana masa ya tabbata. Salis da Nana da suka ji ƙarar dukan mutar da AJ ɗin ya yi ne ya dawo da su daga duniyar soyayar da saku ta fi. Suna ganin AJ Salis ya saki murmishi ya na kallon fitowarsa da ga cikin motar da ya ke mamakin ganin sa cikin sabuwar mota. Ita ko Nana kunya ta ji domin ba ta so ya ganta a halin da ya same su ba. "Lafiya Malam? Mai ya kawo ka gidan mu? Kuma gurin ƙanwata? AJ ya faɗa ya na haɗe fuska tamkar bai san wa ye Salis ba. Ci ke da mamaki Nana da Salis suke kallon sa ganin babu a lamar wasa a fuskarsa. Cikin tsawa ya ce da Nana "Ɓace min a nan kafin na fasa miki baki yanzu! Ai kafin ya ƙara sa har ta shige gida cikin kuka. Ya dawo da kallonsa izuwa ga Salis wanda ya yi mutuwar tsaye ya na kallon ikon Allah. "AJ Ka na cikin haiyacinka ku"..."Salis ka bar ƙofar gidannan yanzu Please? Ya faɗa ya na ƙoƙarin kawar da abun da ya zo masa zuciya. "Wani abu ya faru ne da Hajiya ta zo gidannan? Ko dai Laɗifa ta zo ta ce wani abu a kan soyayyar mu da Nana? Salis ya yi wannnan tambayar ne domin yasan Hajiya Babba ta ce zata zo gidan su AJ. Kuma yasan Laɗifa ce ka ɗai tasan ya na son Nana. Cikin sauri AJ ya ka tsaye shi da ce wa "Ka yi haƙuri Nana ta na da Miji dan Allah kar ka ƙara zuwa ƙofar gidannan. Cikin tsananin ɓacin rai shima Salis ya ce "Ƙarya kakeyi AJ walhi Nana ta wa ce babu wanda ya isa ya rabamu da ita! Cikin fitar haiyaci AJ ya kamo kwalar rigar Salis ya ce "Kai ɗin banza wa ye kai Nana ba sa'ar ka bace, kuma walhi sai ka bar mana ƙofar gida wawa kawai. Ganin da gaske AJ ya ke yi yasa Salis shima kamo rigarsa ya fara turashi. A na cikin ha ka Nana da Innah su ka fito. Dai-dai AJ ya sa ƙarfi ya ture Salis, ai kuwa ya yi baya-baya sai ya faɗa jikin motarsa. Da ƙarfi Innah ta ce "Abduljabaru"...."Abduljabaru"? Amma AJ ko kallonta bai yi ba. Ganin ha ka ya sa Innah ta je ta kamo hannun Salis ta na jansa cikin gidan. Da sauri AJ ya sha gabanta ya na ce wa "Walhi ba zai shiga gidannan ba, kawai ya bar an'guwar nan ga ba ɗaya. Cikin kuka Innah ta ce "Yanzu Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Yanzu bazan maka magana ka ji ba ko? AJ ya kawar da kai gefe ya ce "Innah wai Nana ya keso kuma babu aure a tsakaninsu domin ita ɗin ba sa'ar sa ba ce, kai ga ba ɗaya ma an mata miji. "To ƙarya ka ke yi , sai na bashi ita, kai ɗin banza, Abdul ka ba ni hanya? Amma ko gizau AJ baiyi ba. Cak Nana ta tsaya da kukanta ta na kallon AJ wanda ya ke ta zuba kamar ya zauce. "Babu aure tsakanin mu! An min miji! Wannan maganar ita ce Salis da Nana ke ta nazari. Ganin mutane har sun fara taruwa ne ya sa "Innah fashewa da kuka ta na dukan AJ wanda gaba ɗaya ya fita a haiyacinsa. Shi dai kawai ba ya son ganin salin a gabansa tsabar kunya da tsoro . Ganin ha ka ya sa Salis cire hannunsa da ga na Innah ya na kallon Nana da itama shi ta ke kallo. Kallonta ya ke yi har ya buɗe motarsa ya shiga ya ta da ta ya bar an'guwar ci ke da ɓacin rai da tunani. Ganin ya tafi ya sa Nana sakin wani kuka ta na jin ta rabu da Salis kenan har a bada, AJ ya rabata da masoyinta na gaskiya. Da sauri AJ ya yi kan Innah da sauri ganin ta sume a gurin tammkar ba numfashi. "Innah! "Innah! Ha ka ya ke ta kiranta amma ko motsin ba ta yi. Da sauri ya ɗauke ta izuwa cikin motarsa, itama Nana ta bi yo bayan sa cikin ihun kiran sunan Innah har suka bar an'guwar. Da sauri a ka karɓesu da umarnin Dr Lurwan wanda fituwarsa kenan da ga cikin asibitin zai tafi gida. Sun ɗauki a ƙalla a'wa guda kafin Dr ya fito ya na kallonsu da zuba masa Ido. "Dr Innar mu ta na lafiya dai ko? Dr ya ce "Ku biyoni? Ba musu suka rufa masa baya zuciyoyinsu na dukan tara-tara. "Dr ya kalli Nana ita kuma ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na jin tsoron abunda zai fito da ga bakinsa a kan innar ta su. "Kin manta bayanin da na miki a kan ciwonta a wancan lokacin ne? Nana ta kalli AJ shima ya kalleta. "Dr ta sanar da ni, amma yanzu dai ai ta na lafiya ko? Dr ya ce "zuciyarta ta ƙara samun matsala fi ye da na baya saboda haka dole sai"...."Ya isa haka Dr idan kuɗi ne ko nawa ka ke so za'a baka Please dan Allah karka ce komai. AJ ya katse shi cikin tashin hankali. Ganin kamar baza su fahimci shine ba ne ya sa ya ce "To shikenan karka damu za'a kula da komai. Ha ka suka fito daga gunsa jiki a sanyaye. "Laɗifa" Laɗifa" Salis ke zabga ma ta kira tun kafin ya buɗe palon, ka na kallon sa kasan ya na cikin tashin hankali mara musaltuwa. Laɗifa da Samuel da Sarah da Muhammad su na zaune a palon suka ji wannan kiran na Salis. Ya na shigo wa palon ya ɗauketa da wa ni mari, kafin ta yi magana ya ƙara ma ta. Daddy Muhammad da Samuel su ka yi saurin ta shi su na kamo shi ganin ya na shirin ƙara ma ta wani marin. Cikin ihu da zafin rai ya ke magana "Mai ya kaiki gidan su AJ? Mai kika je kika ce ma sa a kaina? Wato saboda ke Allah ya yi mara kunya shine ki ke tunanin kowa ma haka ya ke? To Nana na keso kuma sai na aureta ko ki na so ko bakya so. Da ga cikin ɗaki Momy ta ji kamar a na faɗa-faɗa a cikin gidan, cikin rashin sanin abunyi ta miƙe ta na nufar palon domin jin muryar Salis. "Kai Salis ba magana na ke maka ba? Jin Muryar mahaifin na sa cikin fushi ya sa ya tsaya da maganar ya na kallonsa dai-dai Momy Hajiya Babba ta ƙaraso gurin. Tsabar mamaki da rudanine ya ha na Laɗifa kuka, ta ri ƙe kuncinta sai bin Yayan na te da kallon mamaki ta ke yi. Wannan shine karo na farko da hannunsa ya taɓa ta da niyar duka, ku ma wai a kan AJ, sanan ita batama san akan mai ya ke bayani ba. "Mai ya ha ɗa ku? Cewar Muhammad cikin ɓacin rai? Salis ya ce "Daddy gidan su yarinyar da zan aura ta je ta yi halinta na rashin mutunci wanda ya sa Yayan yarinyar ya ce ba zasu ba ni ya rinyar ba. Muhammad ya ce "Su ne su ka ce maka ita ce ta je gidan? "Daddy ita kaɗai na sanarwa ina son yarinyar, sannan ko a lokacin da na sanar ma ta ba ta nuna min a'min cewar ta ba, sannan kuma yarinyar ba yar kowa ba ce , hakanne ma yasa ta je gidan ta ci mutuncin su domin kar su ba ni ita. Ya ƙara ya na jin wani ɗacin abun da AJ ya masa har cikin ransa, sannan ya na jin a kan Nana zai iya fafatawa da koma waye ba AJ ba. Sai a lokacin Hajiya Babba ta gano kan maganar. Duk da ta na cikin damuwa amma kuma ba ta so ya ranta su ga no halin da ta ke ci ki, sai ta sunkuyar da kai ƙasa ganin irin kallon da Muhammad ke yi ma ta. "Ƴar gidan wa ye? Kuma wa ni gida ne? Hajiya Babba ta tambaya cikin ɓoye ta ta damuwar, ta yi wannan tambayar ne domin sasanci amma batasan tambayar itace silar wargatsewar komai ba. Nan ta ke Salis wanda dama ɗazu yazo gurinsu da niyar sanar musu da wacce ya keso, am'ma bai samu da ma ba, yanzu kuwa ya na jin da ma ta samu ya fara maga cikin da kiya da nuna cewar tabbas ya na son abunda ya ke faɗa ɗin. "Ba ƴar gidan kowa ba ce, ƙanwar AJ ce Nana sunanta, kuma mun dai-dai ta da juna tun ba yanzu ba, ta na sona nima kuma ina sonta, amma yanzu na je gidan na su AJ da kansa ya ke korata da ga gidan su, Laɗifa mai kika ce masa a kai na? Salis ya ƙara sa idonsa na cikowa ya na nu na Laɗifa wacce har yanzu kallonsa ta ke yi. Ta na jin wa ni irin tsanar AJ a zuciyarta, ta na jin cewar wallhi da ga yau ba zai ƙara zuwa cikin gidannan ba, ku ma tinda dai ya sa Salis ya da ke ta, to walhi sai ta je har gidan ta ci masa mutunci. Tunda Muryar Salis ta ambaci sunan AJ Hajiya Babba ta sanƙare a gurin, duk wasu gaɓobin jikinta suka tsaya chak, ta ma rasa wani irin tunani za ta yi, sai kallon Salis ta ke yi kamar yau ta fa ra ganinsa. Muhammad da har ya gano komai domin jin sunan AJ, kuma ganin yanda Hajiya ta yi suman zaune, ya kalli Hajiya Babba ya ce "To Alhamdu lillh! Muna godewa Allah da yasa abun ya zo ta ha ka, sannan dukkanku ina so ku ba ni aron hankulan ku domin ku fahim ce ni da kyu. Ya fara da cewa "Da farko dai ba Laɗifa ce ta je gidan su AJ ta ci mu su zarafi ba. Hasalima shima AJ ɗin da ya ma ka haka ba'a son ransa ba ne duk borin kunya ne, sannan idan har bai maka haka ba to baisan da wa ni ido zai kalleka ba, kasan halin yaron da shegen son kuɗi. Hajiya Babba ta kurma wa ni uban ihuu ta na ce wa "Idan ka ƙaunaci mahsifan ka karka ce komai , ni na san yanda zan yi, Please And Please? Muhammad ya da ka mata tsawa ganin yanda ta ke abu kamar wa ta yarinya ya ce "Yau sai kowa yasan komai, wai i'na hankalin ki ya tafine? Kina abu kamar ba musulna ba, kamar baki yarda da ƙandara ba, ke bazaki godewa Allah ba ma da yasa kika bi hanya mai kyu? Sarah da Samuel sai kallon ikon Allah su ke yi, ita kuwa Sarah sai ta hau mamaki jin saboda ha ka Hajiya ke kuka, ita duk a tunaninta a addininsu Hajiya Babba ɗin yin haka ba kuskure ba ne ganin kowa ya ƙi cewa komai, ashe dai babu wanda ya san da zan cen sai yanzu. Kasan cewar Muhammad ba kwarewa ya yi a Hausa ba, ya sa idan zaiyi magana sai ya haɗa da turanci. Suma kansu su Salis ɗin idan har za su yi magana da shi to sai su na haɗawa da turanci. "Sakamakon kuskuren da kuka ai kata na hana mahaifiyar ku yin aure ya sa ita kuma ta ga bazata iya jurewa ba, kuma ta na tsoron faɗawa halaka, sai ta yi aure ba tare da kun sa ni ba, ba tare da ma kowa ya sa ni ba. Salis ya yi tsit, Laɗifa ta kalli Hajiya Babba wacce ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na karanto addu'o'in da ta samu ta wawaso. Wa ni irin abu Salis ya ji ya ratsa tsakiyar kansa, sai ya ɗaga kai ya kalli Hajiya Babba domin shi sam bai yarda ba, domin kuwa, yaushe har ta yi auran, bayan da ga shi har Laɗafi a cikin ƙasar nan sukayi karatu, kuma a cikin gidannan su ke ta re da ita, sannan a iya saninsu itama ba ta taɓa yin nisan da har zai kaita ga yin aure ba. Itama Laɗifa tunani ta ke yi kenan, yau she har suka taɓa yin nisa tsakanin su da ita da har za ta yi aure ba su sa ni ba am'ma ta kasa tunowa. Cikin rashin yarda da komai ya sa Salis ce wa "To Hajiya saboda kinyi auranne ya sa kike kuka? Ya yi tambayar ne ba dan ya yarda da cewar ta yi aure ba, sai domin ya ji dalilin kukanta, domin kuwa ya na da tabbacin cewar ba auranne ya sa ta ke wanan kukan ba. Hajiya ta kasa magana sai ta sa ke fashe wa da wani kukan. Kana kallon Hajiya Babba sai ka tausaya mata, ganin yanda ta ke kuka kamar wacce ta aikata haramun, yawu da majina duk sun haɗe mata, idanuwanta sun ja zirr kamar mai ciwon ido, hakan yasan Salis yin wannan tambayar domin sanin dalilin hakan, shi kansa Muhammad sai yanzu ya ke ƙara tausayin matar tasa domin yasan duk gudun kunyar yaranta ta ke yi, domin kuwa tasan ba haramci ta ai kata ba amma kalli irin kukan da ta ke yi. "Wanda ta aura ɗin ne bai kamata ba shine ya sa ta ke kuka? Cewar Muhammad cikin sanyin murya. "Waye cewar Salis cikin sauri, domin zuwa yanzu gabansa ya tsananta faɗuwa. Hajiya Babba ko dai-dai lokacin numfashi ta ya yi ɗaukewar ƴan daƙiƙu kaɗan tsabar kunya da far gabar abun da zai faru. Ita kanta izuwa yanzu Laɗifa ta fara sakin kuka ganin irin kukan da mahaifiyarta ke yi. Sarah ma kukan ta ke yi cikin tausaya mu su. Shi dai Samuel baima fa himci komai ba, sai dai shima ya ji tausayin Hajiya. "AJ abokinka kuma Yayan budurwarka wan da ka ce kaje gidansu yanzu ya koreka to shine wanda Hajiya Babba ta aura, kuma da yardar sa da yar darta harda rabon ci ki......📝 *Ikon Allah sai kallo! Wai ni Hajiya Babba ko dai ta manta da cewar Aure ta yi ba zina ba ne irin wannan kuka?* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *Ƴan fexxbookk ina ganin saƙonninku* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *Duk abinda Allah ya tsara to tabbas ba makawa sai ya faru, fatammu a kullum shine Allah yasa mucika da imani, Allah yasa mu cika acikin addininmu wato addinin Musulunci addinin gaskiya. Amin²* *PAGE4️⃣1️⃣* ......Shiru palon yayi tamkar babu ko wa a cikin sa, ko wa sai nazarin maganar yake yi, zuciyoyi na harbawa da sauri da sauri. Tabbas da gaske Daddy ne yake sanar da su cewar Hajiya tayi aure, auranma wai da AJ! Salis ya kasa magana sai kallon Hajiya Babba yake yi wacce ita kuma ta sun kuyar da kai ƙasa tana zubar da hawayen da na sani. Da ƙarfi Laɗifa ta ce "Wallahi ƙaryane babu wanda ya isa ya ce haka! AJ ɗin banza Wallahi na tsaneshi! Ƙarya yake yi dan uwar da ta haifi uwarsa, kuma yanzu zanje gidan na su yazo ya faɗa a gabana idan ya cika tsinane. Kana kallon yadda take yin maganar kasan ta fita a hayyacinta tsabar tashin hankali. Daddy ya ce "Sai dai idan nine nake miki ƙarya domin ba AJ bane ya sanar daku ba nine? "To koma waye bazan yardaba, wallahi bazan yardaba wanan ma ai cin fuskanne da rainin hankali! Kamar AJ!... Sai kuma ta dawo da kallonta izuwa ga Hajiya Babba tana cewa "Hajiya wai da gaske ne? AJ kika aura bayan duk irin tsaron da muka saka a kan ganin hakan bai faru ba? Da ƙarfi Hajiya Babba ta ce ... "Eh nayi aure kuma na auri AJ sanan yanzu haka ina ɗauke da cikin sa? Hajiya ta faɗa cikin miƙewa tsaye sannan tana jin wani kwarin gwiwa na zuwar Mata. Shima Salis cikin fushin da yazo masa tun ɗazu ya meƙw ya ce "Nooooo! Dan Allah Momy bana son ji dan Allah ki daina faɗin wannan abun kunyar Please and Please na roƙeki Momy? Ya durƙusa har ƙasa a lamar roƙo ga kuma hawaye a fuskarsa. Sarah da Samuel dai izuwa yanzu sun fara tsorata da lamarin nasu. "Wannan ba abun kunya ba ne Salis, domin aure na ce muku nayi ba zina na aikataba, wannan ma kawai ba abin farin ciki bane ace mahaifiyar ku tayi aure kuma harda c"...."Ya isa haka Momy ya isa ya isa bana so bana so? "Yanzu auran AJ shine abun alfahi a gurinki? Abin farincik? Shin Momy ko dai kin manta da waye AJ ne? Yaro ne fa ɗan ƙarami, na girmeshi sosai ma kuwa, amma kije ki aureshi? Wahy! wahy! Momy mai yasa zaki aikata mana haka? Shin kin manta da cewar kinada yara a gabankine? Ya ƙarasa yana sake sakin wani kukan. Laɗifa ta ce "Wannan tsinanan yaron ai ko nu zan gyarmeshi wallahi, amma wai Momy har kike iya cewa kin aureshi? Cikin sanyi rai da a'lamar kuka a muryarta ta ce "Shin Salis lokacin da na ce muku zanyi aure kukaƙi saurarata a wannan lokacin ba kwa tunanin komai? Shin a wannan lokacin ba kuyi tunanin halin da zan shigaba? Har kuka nake yi ina roƙonƙu akan ku barni nayi aure amma ko nayi niya zaku ɓata? Ni kuma na kai adadin da bazan iya jurewa ba shine nayi aure, shin da ba aure nayi bafa!? Hajiya ta faɗa kan kujerar dake bayanta tana sake fashewa da kuka. Kallon mahaifiyar tasu yayi sai kuma ya kalli Daddy wanda ya zuba musu Ido sai ya sunkuyar da kai yana furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yana kaiwa nan ya tashi da niyar barin gurin. Itama laɗifa miƙewa tayi zata bi bayan sa amma Daddy ya tsayar dasu. "Ku dawo ku zauna? Kamar bazasu zauna ba haka suka dawo kowa ya zauna rai a ɓace. Muhammad ya ce "Salis? "Na'am". Ya amsa. "Laɗifa? "Na'am Daddy? Itama ta amsa kamar bakinta na ciwo. "Duk wanan abin kune kuka jawo, domin kuwa mahaifiyarku ta ce zatayi aure amma kunce bazaku yardaba shin wace hujja kuke da ita na hanata yin wani auran? Sanan shi yaron da ta aura ɗin yayi ƙaramine kokuma dai yaya? Idan har yayi ƙaramine to mai ya hana kubarta ta auri babba? Addininmu bai hana auran da tayi ba, hasalima taraya sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne! Saboda haka dan Allah inaso kozo muhaɗu mu rufawa junanmu a'siri, dan Allah Salis da Laɗifa kudawo cikin hankalinku, ita kanta sai yanzu take da tasanin yin auran, kuma tayi ƙoƙari zama babu miji harna tsawon shekaru masu yawo, ya kamata mu ɗaya hannu mu godewa Allah da yasa aure ne ya samar da wannan cikin. Salis ya ce "Nagane Daddy kuma na fahimta na gamsu, amma kuma Daddy naji ka ce harda ci ci....sai kuma ya kasa faɗa yana jin ɗacin abin da zaifaɗa ɗin. "Eh harda ƙaruwa na ciki, amma kusa hakan a ranku cewar Allah yayi sai tayi koda bada AJ ɗin bane, saboda haka kuyi amfanin da tawakalin da a kasan musulmi dashi, ku ɗauka cewar haka Allah yaso. "Amin Daddy amin. Salus ya miƙe ya nufi gurin Hajiya. "Ɗago ta yayi daga sunkuyan da take sai ya rungumeta yana sakin kuka itama haka. Laɗifa na ganin haka ta miƙe ta bar palon cikin kuka tana zagin AJ. "Kiyi haƙuri Hajiya naga ne cewar duk laifinmune, munyi kuskure kiya fe mana mun tauye miki hakinki da Allah ya halarta miki. Jin haka yasa Hajiya Babba ta ƙara rungumo yaron nata tana kuka ta kasa cewa komai sai ɗan dukan bayansa da takeyi. Sarha da Samuel suma kuka sukeyi ganin yanda suke kuka, take wani irin imani ya shigesu ganin yanda suka warware matsalolinsu cikin sauƙi da min dokokin addininsu. Sarah ta kalli Samuel sai ta miƙe tsaye shima ya bita. *HOSPITAL (ASBITI)* Bayan wani lokaci Innah ta farka, aikuwa ta samesu a tsaye a kanta dukkanninsu cikin tashin hankali. Da sauri AJ yazo kusa da ita yana kiran sunanta "Innah? Dan Allah kiyi magana yanzu muna sonki? "Abduljabaru? "Na'am Innah ina jinki? Kimin magana dan Allah? "I'na Salisu? "Innah bayanan" ya bata amsa yana matsowa "Abdul baka ɗaukeni a matsayin komaiba, idan ka ɗaukeni da daraja bazan maka magana acikin mutane amma kayi banza daniba...yaronnan ya taimaka mana nida Nana lokacin da ka tafi kabarmu, amma yanzu na fito na samu kuna faɗa dashi har na maka magana amma Abdul kayi banza dani...to ni dai bazan maka bakiba, abin da zance maka shine Allah ya shiyamin kai yasa ka daina wannan halin naka na taurin kai, sannan Nana ta sanarmin cewar yace yana sonta kuma na amince ko bayan raina Salis shine mijinta, kai kuma kaje kayi abin da zakayi domin kafi ƙarfina, kodan kayi kuɗine to, sannan yanzu ka gama zama maƙaryaci yanzu idan nace maiya haɗa ka da Salisu bazaka sanar dani gaskiyaba kuma nasa"..."A'a Innah wallahi na shiryu na daina komai, sanan shima Salis ɗin bansan lokacin da hakan ya faruba, ki daina cewa dan nayi kuɗine walhin na shiryu . Inaah ta ce "To shikenan Allah ya muku albarka, ka dinga rage zuciya Abdul, sannan ka rage son kuɗi da yawa Abdul, domin wani lokaci ko ka samu kuɗin idan ka rasa wani abun naka zakaji dama Allah bai baka wannan kuɗin ba ya barka da wannan abin da ka rasa. "Dan Allah Innah ki daina faɗin haka banaso jikina na mini wani iri idan kina faɗin haka? Cewar Nana tana durƙusuwa kusa da Innah. Suna cikin haka Dr ya shigo. A ranar a ka sallamesu Dr ya ƙara jamusu kunne akan a daina ɓata mata rai. Ai kuwa suna dawowa AJ ya ce zai ƙarasa kwashe komai da sukeso na gidannan zaikai sabon gidansu domin daga yau bazasu ƙara kwana a gidan ba. Ita dai Innah bata ce komai ba, haka suka shigar da ita ɗakinta suka kwantar da ita, suka fara fitar da kayan da zasu amfana i zuwa cikin mota. Bayan ya tafi ita kuma ta shiga gyaran gidan. Bayan ta gama ta shigo ɗakin Innah tana cewa "Innah karfa kiyi barci kinga magariba tayi? Jin kamar har ta fara barcinne yasa ta ƙara cewa "Innah!!!!!! Ki tashi!? Nam ma taji shiru, Sai taje harkusa da ita ta ɗagota tana cewa "Kinsan barcin yamma babu kyu amma yanzu-yanzu har kin fara? "Cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ta ce "Nana barni na ɗan kishingiɗa ko zanji barcin nan ya tafi? "A'a fa Innah ai kinsan ba kyu. Haka dai dole saida Innah ta miƙe. A cikin daran AJ ya gama kaiwa koma nasu, gobe saide kawai su tare a sabon gidan su. A cikin daran Nana ta tambayi AJ abin da Salis ya masa, amma ya sanar mata da cewar babu komai kawai dai yayi tunanin ko zai ɓata mata rayuwane. Badan ta yardaba tayi shiru, shima ya tambayeta tsahon yaushe suke tare? Ta ce "Tin kafin yayi tafiya zuwa Niger. Yayi mamaki sosai amma ya ce "Kuma kina sonsa? Ta ce "Ai shi yana sona" AJ yayi dariya yana tausayin Nana domin yasan idan har Hajiya taji wannan zancen bazata yarda Salis ya auri Nana ba, ko shi Salis ɗin idan yaji bazai auretaba. A ranar a Restaurant sukaje suka sayo abinci, yauma kowa kazarsa da bam ga kayan sha, Nana kam warewa tayi ta zaɓi duk abin da takeso ta sayowa Innah ma nata. Sunyi siyayya sosai kafin suka kamo hanyar gida. Hira sukayi a daran sosai har Innah tana basu labarin auran iyayensu wato auran mamarsu da babansu, sunyi dariya sosai. Sunci nama sunci abinci sunsha komai dake gurin anaci ana dariya ita dai Innah komai baya mata daɗi. Inna ta kalli AJ ta ce "Abdul yanzu gaba ɗaya ka daina zuwa gidan kawunka kwata-kwata mai yasa? Ɗan Mama-dama ma Nana tana ɗanzuwa. Aj ya ce "Ai Innah kinsan halinsu idan mutum yaje gidan sai kowa ya dinga kawo maka wani ƙablu da ba'adinsa, amma yanzu zan je gobe insha Allah kafin mu tafi! "To Allah dai yasa, kasan shi zuminci yanada daɗi. Nana ta ce "Aini Innah tin ranar da na karanta miki wannan littafi har kikayi kuka to tinda ga ranar na ƙara gyar mama zuminci. "Innah ta ce "Eh wannan littafin da kika karanta mini a kwanakin baya ko?, ni har yanzu baki bani labarin yanda littafin ya kasanceba. Nana ta ce "To ai haryanzu ban gama karantawa ba, ina cikin karantawa ne a ka kamamuba kuma bayan mun dawo sai banga wayarba, dama Kadija ce ta turamin itama wai yanzu bata dashi. Innah ta ce "Kai naso jin yanda zata kasance ko idan ƙanin mahaifin nata ya gano cewar ƴar gidan ƙaninsa ce ya zaiyi? AJ ya ce "Ya sunan littafin? Da kuma sunan marubuciyar? Da sauri Nana ta ce "Sunann littafin *UWATA CE SILA.* Marubucin kuma na mijine sunansa S REZA. Dan Allah yaya ka nemomin Pls kaji? Kafin yayi magana Innah ta ce "Walhi marubucin yayi labin cikin hikima da basira, idan har ka karanta littafin to zaka riƙe zuminci da kyu. AJ ya ce "Ikon Allah! Ai kuwa zan nemeshi kodan na ƙaru. Nana ta ce "A kwai wani mai suna Allaji muɗi acikin littafin wallhi mutuminnan da zan ganshi a fili saina zabga masa mari domin mugune, harda mai sunana Nana. Innah ta ce "Ni kuma uwar yarinyar da kuma wannan shegen Uncle ɗin mai koya mata karatunne sukafi ɓata min rai walhi!, ace kina matsayin uwa amma kiyi sakaci da ƴarki akan wani banzan karatun boko. AJ ya kwashe da dariya ganin yanda inna take ta zabga masifa da fushi har hawaye sun fara taruwa a idonta. Ya ce "Innah!!! littafine fa ba gaskebane har kike kuka? Ya ƙara sa yana tashi izuwa ɗakinsa. Nana ta ce "Yaya a'a wallahi true life store ne wannan domin a farkon labarin ma an faɗa. AJ ya ce "To zan nemo muku saida safe, amma kice Innah ta daina kuka. Ya fita ya barsu suna cigaba da labarin littafin ita da Nana. Shikuma ya fita yana mamakin jin cewar wai labarin na gaskene. Cikin dare Innah ta ke ta faman tari harsaida tasha maganin da Dr ya bata. Da a suba AJ ya tashi yayi wanka ya shiga tunanin rayuwarsa, haka kawai yaji gabansa na faɗuwa idan ya tuno da mahaifinsa , sai kuma ya kama hawaye yana jin cewar akan Nana da Innah zai iya aikata komai, domin yanzu sune komai nasa, yana jin ba zai barsu a cikin wani hali ba mutuƙar yana raye, zai zauna dasu har gaba da abada, yana son ƙanwarsa da kakasarsa sannan ba zai taɓa yarda susan auran da yayi ba insha Allahu! Yana cikin haka a ka kira sallah , saida yabi ta dakin su Innah ya tashesu sannan ya fita Masallaci. Bai dawoba saida gari yayi haske, yana shigowa ya tarar Nana tana haɗa musu abin kari a gindin murhu. Kallon ta ya kayi cikin dariya ya ce "Daga yanzu dai kin huta da wannan banzan itacen mai sakaki hawaye ko? "Da murmushi ta ɗago ta kalleshi ta ce "Wallhi yaya kamar kasan na gaji da shi Allah. Ya ce "Ai amma gama daga yau sai dai muma mu koma ɓangaren gass Allah yasa dai kin iya amfani dashi domin nasan Innah ba iyawa tayi ba? "Kai yaya gass ɗinne kuma kake cewa ban iya amfani da shiba? Ya ce "Idan kin gama ki taso inna zanyi wanka kafin lokacin? Ganin har ta gama Innah bata tashi bane yasa itama ta je tayi wanka sannan ta je ɗakin AJ ta tasoshi wanda shima barcin ya ɗauke shi. Bayan yazo gurin da suke cin abuncinne baiga Innah ba ya ce "Innah fa? "Tana barci bari na tasota. Tana faɗa tabar gurin daidai shikuma kiran ya shigo wayarsa. "Ganin sunan Sarah ne yasa gabansa faɗuwa, har ya fara tunani sai kuma ya tuna ai yayi Welcome back. "Salamu'alaikum" ya faɗa gabansa na cigaba da faɗuwa. "A a a Aj? Sarah ta faɗa cikin kuka. "Cikin rainin hankali ya ce "Please waye a layi? "Sarah ce" Ta faɗa tana danne kukanta. "Wa cece Sarah? Kuma daga ina? "AJ nicefa Sarah zaka ce ka manta da nu n"....kafin ta ƙarasa ya ya ce "Please is ron Number . Yana faɗa ya katse wayar yana sakin dariya. Kafin ya ajiye wayar yaji muryar Nana ta kwala wani uban ihuuu! Tana kiran sunan sa. Da gudu ya shiga ɗakin innar ya ganta a kan daddumar da tayi Sallah a kwance idanunta sun ƙafe ga carbin hannunta shima ya sake ya faɗi. Kallonta ya keyi yana kallon Nana da take ta ihuuu tana jijjiga innar. Da ƙarfi ya ce "Innah!!! Ya faɗa yana juyata sai ta sake jiki alamar ba rai a tare da ita. Lokaci ɗaya ya gane cewar Innah tayi tafiyar da ba dawowa. Nana ta ce "Yaya maiya faru? "Innah ta ra ta ta ta rasu! Ya ƙarasa yana fashewa da wani irin kuka yana dukan kasan ......📝 *Hammm* *to fa!* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣2️⃣* ........"No Yaya a'a Innah bata mutuba ka daina faɗa dan Allah bana son ji...Innah ki tashi dan Allah ki tashi bana son wannan wasan Innah taaaaaa!!!. Nana ta ƙarasa tana ƙara ruƙo hijabin Innar. Kuka take yi sosai AJ ma kuka yake yi yana riƙe da Nana wacce har yanzu kiran sunan Innah take yi. Cikin kuka shima ya fara cewa "Wallahi Innah na daina aikata komai kuma zan sanar miki da gaskiya bana son kuɗin da gidan dan Allah ki tashi. Tabbas dukkan wani mairai mamaci ne, haƙiƙa duk wata rai zata ɗan-ɗani zafin mutuwa, ka na taka Allah na nasa kuma na Allah shine daidai, haƙiƙa rayuwa babu tabbas duk yanda ka kai da lafiya ko ƙarfi ko arziƙi ko mulki ko... ko... ko... ko... ko...koma mai nene to tabbas sai ka tafi, da lafiya ko babu, kana zaune cikin iyalanka ko kana kan hanyar tafiya, kana aikata alfasha ko kana aikata abun kirki, ita dai mutuwa bata jira.(Allah kasa mucika da kalmar La'i'la'ha'illala Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama.) Haka suna kallo a ka sallaci Innah a ka ɗauke ta izuwa gidanta na gaskiya. Ba shakka Innah tayi jama'a, ƙofar gidannasu cike yake dam da bayin Allah, cikin gida kuwa matan Anguwa da sauran da suka samu labarin mutuwar duk sune aciki. Nana kuwa har lokacin kuka take yi, babu irin rarrashin da Kadija batayiba amma sai kiran sunan Innah takeyi tana kuka. AJ ma kana kallonsa saika tausaya masa, domin ya dawo kamar wani kurma sai kallo da ido. Matar kawunsu da yaranta da ya gujesu a baya yanzu sune a zaune a gidan , kawun nasa ma shine mai riƙe hannunsa izuwa mƙabarta. Saida kowa ya watse a ka barshi shi kaɗai a maƙabartar sannan ya fara addu'o'i yana yi yana zubar da hawaye yana faɗar laifukan da ya aikata Mata. Ya kai a'wa guda a gurin kafin ya miƙe zai tafi sai sukayi ido biyu da Salis a tsaye a gurin yana kallonsa shima idonsa ya ciko da ruwan hawaye. Kallo ɗaya AJ ya masa ya kawar da kansa ya kama hanyar tafiya yana jin zuciyarsa na masa zafi. Shima Salis bai ce masa komaiba yabi bayansa. Suna isowa suka tarar har wasu sun fara tafiya, Kawu ne yake karɓar gaisuwa. Gurin da kawon yake suka zauna har yanzu babu wanda ya tam kawa juna. AJ ya sunkuyar da kansa ƙasa yana kuka yana tuno maganganun da sukayi da Innah a daran jiya, a she wasiya take musu. Shi sai yanzu yake jin dama bai samu wannan kuɗin ba sun zauna a talaucinsu, inama lokacin da suke faɗa da Salis da tamai magana yaji, da ba'a kaita asbiti ba da yanzu haka suna cikin sabon gidansu! Inama inama inama. Haka har akayi kwana bakwai AJ bai ce da kowa komaiba harda kawunsu da Salis da Muhammad wanda kullum sai sunzo gurin, abincin da a ke ci a zaman makoki ma duk Salis ne ya ɗauki nauyi, shi dai AJ baisan waye mai bada abincin ba. Kawu da matarsa da yaransa biyu duk Mata suma sun dawo gidan kafin komai ya kammala. Kasancewar ba komai a gidan ne yasa kawun yasa matarsa ta ɗebo wasu kayan nasu irin tukunya da dai duk abin buƙata, haka a kaci gaba da zaman makokin Innah har a Kayi ba kwai. Daga nan ne a ka fara watsewa kowa na komawa mahallinsa. *BAYAN KWANA GOMA SHA BIYU DA RASUWAR INNAH* What!!! Ban gane ba? Mai kake nufi da haka? Cewar Kawu yana kallon AJ cikin tashin hankali da ruɗani. Itama Nana kallonsa tayi tana girgiza kai batare da ta iya magana ba. AJ yace "Eh Kawu da gaske nake na yi aure kuma auran ma na jari ko nace auran kuɗi, auran da Addinimu bai yarda da irinsaba, auran da yanzu haka shine ya sani a cikin da na sani auran ta kaici auran kwaɗayi auran nadama. Ya ƙara sa yana sakin kukan da ki ta damun zuciyarsa. "Wai Abdul duk mutuwar Innar ce tasa ka koma mahaukaci ko dai yaya? Kazo kanata wasu zantukan da ba kan gado. "Lafiya ta lau Kawu, inada hankalina nasan mai nakeyi. "Cikin dashesshiyar muryarta ta ce "Yaya mai kake cewa ne? Ban fahimtaba Please? Kuka ya keyi sosai ya fara magana yace ""Nayi aure nayi aure saboda kuɗi saboda Innah da Nana su ji daɗin rayuwa, wallahi badan kaina nayiba amma yanzu na gwammaci da banyi wannan auranba, sannan na rasa wazan aura sai sa'ar mahaifiyata, uwar abokina wanda shine ya sa na fara ganinn kaina a haka, yamin rana nikuma na masa dare daran ma mai mugun duhu. Nan take ya kwashe komai ya sanar musu bai ɓoye komai ba. Cikin sabon tashin hankali Nana ta ce "Whay wahy whay Yaya? Mahaifiyar Salis mai yasa kayi haka! Ka gama da rayuwarmu Yaya. Kawun ne ya kalli yanda suke kuka duk sun fita a cikin haiyacinsu ya ce "Yanzu ba kuka zakuyiba, ai kace kun rabu ko? AJ ya girgiza kai. Ya ce "To yanzu ku tashi muje gidan nasu domin sanin abunyi, dole ne sai mijinta yasan da wannan zancen saboda kar a je a aikata haramci. Da sauri AJ ya ce "No bazan iya magana dashiba kunyar Salis nake ji na , ga babansa ga Sarah no bazan iya ba wallahi bazan iyaba. Saida sukayi da gaske kafin AJ ya bisu. Ta kardun gidan da Hajiya Babba ta bashi da makullin motar ya haɗo ya tafi dasu. Saida sukazo bank ya tsayar da motarsa ya ce su jirashi. Duk kuɗin dake cikin account ɗinsa ya kwashe ganin kuɗaɗan sunyi yawane yasa ma'aikatan bank kin sukace saidai yazo da jaka, ya ce bashi da jaka. Dole a tasu suka zuba masa ya fito dasu yasa a matar suka kama hanya. A gidan Malam Muhammad kuwa washe garin abunda ya faru dasu ne Salis da Muhammad sun shirya domin zuwa gidan su AJ a sanar da innarsa komai sai kuma suka riski rasuwar Innahr. Hakanne yasa suka fasa yin wannan maganar suka bari har sai yaran sun dawo haiyacin su. Shi kansa Salis da ya tsaya ya kalli lamarin sai ya godewa Allah da yasa aure sukayi ba abun kunya ba. Lokacin da suka dawo gida suka sanar wa da Hajiya Babba itama ta tausaya masa domin tasan yanda yakeson kakkar tasa da ƙan warsa. Sarah ko kuka takeyi wai a dole sai an kaita gurin AJ. Dama kuma ita da Samuel sunzo da batun suna son komawa Addininsu Muhammad. A ranar Muhammad da Salis harda Hajiya Babba sunyi godiya ga Allah, sannan sunce gurin shek Kabir kabuga zasu tafi dasu domin ƙarɓar Musuluncin. Dama ga batun auran yaran sa, sai kawai a yi komai a garin, yayi kewar malamin dama kuma yanaso yaje gurinsa, domin ba zai iya mantawa da shiba. Muhammad da Hajiya Babba sun bari a kan sai sun dawo daga gurin Shek Kabir kafin su tun kari batun AJ. Yanzu dai ana gobe zasu tafi kenan. Salis ne zaune a polo shida Samuel yana ɗan masa bayani game da Addini kafin ya karɓi kalmar sha'hada. "Da farko dai zaka ajiye shan kiya da neman mata, sannan girmama iyaye koda ba musulmai bane...Zaka daina zuwa coci, salloli guda biyar a kowacce rana.... A kwai A'zumi da a keyi a cikin watan Ramadan wanda yanzu haka ya kusa kamawa...sannan ya zama dole ka daina"...."Bai ƙara saba sukaji sallama daga bakin palon gidan. "Yes Samuel ya ce sai suka zubawa ƙofar shigowar ido. Kawu da AJ ne sai kuma Nana da ta ce lallai sai tazo. Mi ƙewa sukayi tsaye suna kallon juna tsakanin AJ da Salis harda Samuel. Kawune ya fara maga "Ko Mahaifinka yana ciki? Salis ya kai kallonsa izuwa ga Kawu ya ce "Eh yana ciki" Nana da take bayan AJ har yanzu bai gantaba sai zuciyarsa da ta ke ta harbawa a lamar dai da mosoyi...? Kawu da Muhammad Hajiya Babba Salis AJ laɗifa Samuel Sarah ne duk acikin palon a zaune kowa ya nutsu yana jiran abun cewa. SAMUEL dai sai yanzu ya ƙara gane waye AJ ɗin. Laɗifa kam idonta kar a kan AJ da Nana, tana jin tamkar ta tashi ta harbe su kowa ma ya huta. Muhammad ya fara magana bayan sun gama sauraron abunda kawun ya ce kamar haka..."To muna mai sake miƙa godiya ga Allah da ya sa komai yazo cikin ruwan san yi da fahimtar juna...sannan muna ƙara miƙa ta'aziyar marigayi ya Innah, Allah yasa ta huta, mukuma idan tamu tazo yasa mucika da imani. Duk palon suka amsa da amin. To sai kuma abu na gaba... Kowa ya ɗaga kai yana kallon Muhammad. Ya ce "Aisha tana ɗauke da cikin sa a jikinta har tsawon sati huɗu yanzu haka. Zumbur AJ ya miƙe yana kallon Hajiya Babba wacce ta kifa kanta a kan cinyoyinta. Da sauri itama Nana ta wrufe bakinta tana ƙoƙarin fashewa da kuka. Salis kam wata iriyar kunyace ta rufeshi. Laɗifa kam tsaki taja ta miƙe ta nuna AJ dake tsaye ta ce "Wallahi saina ga bayanka kuma saika tozarta kamar yanda ka tozartamu, ba dai kai mayen kuɗi ba, to wallahi Allah saiya saka mana , mugu maci amana wawa mara tinani dabba jahili ɗan a kuy"..."Kyeeeee!!! Laɗifa ya isa ya isa! Cewar Salis yana miƙewa tsaye. Da sauri Laɗifa ta bar gurin tana kuka. AJ ya ce "Ta faɗi gaskiya cewar banida tunani bani da hankali jajili maci amana tabbas duk wannan suffofinane, naci amanar Salis, bai cancanci haka daga gareniba. Yana faɗa yana kuka. Sannan ya ɗauko takardar gidan da a ka bashi ya ajiye a gaban Salis , ya ɗauko jakar kuɗin ya haɗa da makullin motar ya ajiye ya ce.... "Ga kayanku nan, basu da amfani a gareni, dama saboda Innah ta nayi gashi ta tafi batare da tamoresu ba. Tabbas Allah yasan irin halin da zata shiga idan har taji labarin na yi aure harda ciki ba tare da ta saniba, Allha ne kaɗai yasan halin da zata shiga. Tabbas Innah kin huta da ta kaicina. Sai kuma ya dawo gurin Nana itama ya fara cewa "Ki yafemin ƙanwata na lalata komai na zubar da mutuncin kanmu a kan kuɗi. Haka dai AJ ya dinga sambatu har saida ya ba kowa tausayi. Kawu ya rasa mai zaice tsabar ruɗewa. Muhammad ya ce "Karka ɗorawa kanka laifi kai ɗaya, ni dai a ganina ai wannan ma abun farincikine , sannan wannan kuɗaɗan sun zama naka harda gidan da motar, wannan hakkin kane har a gurin uban Giji. Nan fa a kayi a kayi da AJ ya ce sam bazai ɗaukaba, Salis ya bashi baki ya ce shifa wallhi saide ya ƙare a talauci, haka ya tashi ya bar gidan cikin kuka, yana cewa "Na karɓi cikina kuma zanyi komai da uba yakeyiwa yaronsa ban yarda a tayani da komaiba, zan nemi nawa na kaina insha Allah! Yana faɗa ya fita batare da yajira komai ba. Nana ta tashi zata bishi Kawu ya tareta. Salis ne ya kaisu gida yana rarrashin Nana. Koda sukaje gidan AJ bayanan ga gidan nasu ba kwamai domin sun kwashe komai sun kai sabon gidan. Salis bai shiga gidan ba dan haka baisan da cewar ba komai a gidan ba. A mota suka tsaya bayan kawu ya fita ya kalleta ya ce "Nana ina sonki karkiyi tunanin wannan abun zaisa na gujeki, ina tare dake har ƙarshin numfashina, sannan ga wannan ki ajiye a gurinki ko zaki buƙaci wani abun? Ya faɗa yana miƙa mata kuɗin da ya ciro. Yana jin kukan da takeyi kaman ya rungumota jikinsa ya rarrasheta, amma ba dana. Ba ta ce komaiba ta buɗe motar ta bar shi yana binta da kallon mamaki har ta shiga gida. Haka ya zauna a cikin motar yana tunanin abunyi. *Comments ɗinku shine abun da* *S REZA* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *S REZA...✍️* *ADM* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣3️⃣* ........Haka Salis ya bar ƙofar gidan cike da damu wa a ransa, baya son ya taƙura Mata, zai bata dan lokaci kafin komai yayi daidai. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ta ko wani ɓangarori. AJ ya koma aikin sa na tuƙa motar bredi wanda suɗinma da ƙyar suka ɗauke shi a kan suna da ma'aikata, yaci sa'ar dai ya taɓa aiki a gidan ne kuma lokacin da yayi aikin basu taɓa gamashi da wani laifi ba. Dubu goma za'a dinga biyansa duk wata ɗaya, haka ya nuna farin cikinsa sannan ya kama aikinsa ba wasa. Ita kuwa Nana kaman yanda Aj ya ce ta kama kanta ta riƙe maraicinta ta nutsu ta mai da hankalinta a kan karatun ta, hakan tayi domin bin maganar Yayan nata. Wayar hannunta ya karɓa ya sayar, da kuɗin wayar ya sayo musu duk wani kayan buƙata domin yace bazai kwaso nasu na da ba. Rayuwa ta yi musu tsanani sosai, hakan kuma baisa ya nunawa ko wa cewar yana cikin damuwaba, harta kawunsu baisan da haka ba, wani lokaci abunda zasucima wahala yake musu, ɗan sauƙin abunma a kullum yana zuwa da bredi kida, daga ƙarshe ma Nana daina zuwa school ta yi, sai islamiyya, shiɗinma dai ana binsu bashin kuɗin wata. Duk da haka ya ce duk lokacin da Hajiya Babba zataje asbiti to baya buƙatar suyi amfani da komai nasu. Da farko Muhammad bai yardaba amma ya ga AJ ɗin kamar hakan yakeso, hakanne yasa komai idan za'a yi sai an sanar masa, albashin sa na farko ma a kan yaron ya tafi, hakan ma dan an rage masa kuɗin ne. Izuwa yanzu rashi da damuwa sun fara nunawa a jikinsu, duk da irin halin da suke ciki bai hana Kadija gabatar da kanta a gurinsa ba, amma ya mata kace kace ya ce idan a kan haka take zuwa gidansu to karta ƙara zuwa. Yanzu yana yawan zuwa gidan kawunsa kuma duk lokacin da zaije sai ya ruƙo musu bredi ya kai musu. Har Wannan lokacin bai manta da Sarah a ransa ba amma yasan babu komai yanzu a tsakanin su, yanzu itama ta daina kiransa , sai kawai yaji baiji daɗiba. Lokacin da abubuwa suka rincaɓe masa sai kawai ya siyar da wayarsa ya sayo ƙarama, kuɗin wayar kuma ya fara siyan kayan jinjiri, sannan ya biya wa Nana kuɗin school taci gaba. (Wannan kenan) *ABDALHA POV* Kamar da wasa abubuwa sun chakuɗe masa, Duk gurin wanda yake ganin zai tayashi domin shawo kan mahaifinsa a kan lamarin auransa amma abun yaci tira. A kan wannan abun yasa iyayen nasa sun samu matsala, yanzu haka mahaifinsa ya cire hannunsa a kansa gaba ɗaya, yanzu haka ya dawo gidansu da zama kasan cewar bashi da lafiya, ciwon zuciya ya sa shi a gaba, Daddy yayi tunanin Abdullah yana yin hakane domin ya amince da auransa , baisan cewar ɗansa ya faɗa cikin kokin love ba. Wayarsa ya ciro yana daga kwancen ya nemo numbar Isa, kira ɗaya ya ɗaga yana sallama. "Yauwa Isa ya kukayi da shi? Yayi tambayar cikin Muryar da kanaji kasan yana cikin wani hali. "Isa yaja doguwar ajiyar zuciya ya ce "Wallhi kunyarsa nake ji, bansan da wani ido zan kalleshiba, bansa ma mai zance masa ba. "Kwana nawa ya rage? Cewar Abdalha yana lumshe idonsa? "Kwana takwas? Ya bashi amsa yana jin babu daɗi ga tausayin halinda Abdalha ke ciki. Azuciyarsa ya furta "Takwas! Sai ya kashe wayar yana jin cewar dama haka a ke ji idan kana son mutu! Gani yake babu wanda ya taɓa jin irin abunda yakeji a kan Zainab, sam bai yarda da cewar wani ne zai aureta ba, yana mata son da zai iya ja da kowa domin mallakatarta, gani yake shi nashi salon son daban yake, duk lokacin da ya tuno da cewar auranta saura kwanaki kaɗan sai ciwonsa ya tashi. Numbar ta ya kira yana jin cewar zai samu mafita daga gareta. *ZAINAB POV* Mutuƙar wannan auran da zatayi zaisa mahaifinta farinciki kamar yanda ya ce, to tabbas zata auri Aliyu badan tana sonsaba, zatabi zaɓin mahaifinta kodan ganin yayi alfahari da ita kamar yanda ya ce, ta yarda da cewar tana son Abdalha kamar yanda yake sonta amma wani ƙaramin abu ya shiga tsakani yayi baƙe-baƙe babu damar kaucewa. Hirar su da shi ta jiya ta tuno lokacin da ya ke ce mata "Kar zuciyarki ta raya miki cewar zaki auri wani baniba, domin haka bazai taɓa faruwa ba, kisa a ranki nine mijinki, bansan soba sai a kanki, haka zaluka bansan komai game da shiba na sa ƙafa ta a ciki, bansan komai ba ban saniba! Ya ƙara sa yana kallon wayar kamar ita zai gani. Kawar da idanunta ta yi itama daga kallon wayar tana jin cewar sonda take masa yafi wannan abun da ya lissafo kawai dai shi ya fito da nasa filine. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin zuciyarta na mata zafi kamar ana ƙoƙarin cirota da ga ƙirjinta. Tashi ta yi izuwa gurin Mama. Tana zuwa mama na magana da watar ƙanwarta da tazo gidan bikin, domin dangi na kusa-kusa duk sun fara zuwa. Ganin Zainab ɗin yasa Mama mayar da hankalin ta izuwa gareta. "Lafiya dai ko Zaiban? Cewar Mama tana jin tausayin ta, domin tasan Zainab bata son wannan auran kawai dai ba yanda zasuyi da Malam ne. Zainab ta buɗe baki zatayi magana kira ya shigo wayarta, ganin sunan Abdalha yasa ta kasa cewa Mama komai sai ta bar ɗakin tana ɗaga wayar. "Isa zaizo dubani inaso kuzo tare ko da ganinki ne nayi ko zan samu sauƙin zuciyata? "Kamar bazatayi Magana ba ta ce "Ba zan iyaba! Bana fito ko ina ina gida, tun ba yauba na sha faɗa maka cewar ba'a barina fita ko ina. "Kinaso na shiga wani haline Zainab? Ya faɗa da wata murya da tasa jikinta ƙara yin sanyi? Kinsan mai nakeji a zuciyata kuwa? Wallhi ji nakeyi idan har ban gankiba zan iya rasa rayuwata? Ya ƙarasa yana tari. "Abdalha dole muyi haƙuri mu rungumi ƙaddara mubi zaɓin iyayenmu domin samun albarkasu, ka daure ka manta da ni a rayuwarka ka zama mai girma-ma zaɓin mahaifanmu domin bazasu zaɓar mana abunda zai cutar da muba, saboda haka kayi haƙuri ka daurewa zuciyarka da rashina yanzu saura kwana kaɗan na zama mallakin wani, kuma daga ranar dole mu rabu, rabuwa ta har abada Please! Tana kaiwa nan kuka yazo mata. Tana faɗa ta kashe wayar tana fashewa da kuka. Da a ce wani ne zai faɗa mata cewar ita Zainab Adam zata iya yin kuka saboda mutumin da tafi tsana a rayuwar ta to da tabbas kallon mahaukaci zata ma koma waye wannan ɗin. Bata damu da duk abunda zaifaru a gurin al'ummar gari ba, mutuƙar zata samu abunda takeso, amma hakan ba zaisa ta yi abunda mahaifin ta zaiyi fushi da itaba kamar yanda ya ce mata. Kulawa da kyautatawa da damuwa da ita da irin soyayya da yake nuna mata ba dare ba rana hakanne yasa itama ta faɗa a cikin soyayyarsa batare da ta shirya ba. Ya bata kulawar da wani ɗan Adam bai taɓa bataba, sannan shine sanadiyar kuɓutarta daga hannun ƴan iskan da suka kamata, bazata iya mantawa da Abdalha a rayuwarta ba, Haka ta koma ɗakin mahai fiyar tata tana ƙirƙiro fara'a ta maka a kan fuskarta. Da ƙarfi Maryam ta saki plet ɗin abincin da ta kawo masa a ƙasa tana kiran sunan Momy. Momy da ke palo ita da Daddy tana ƙara sanar dashi irin halin da Abdalha ke ciki ya ce "Indai a kan auran wannan yarinyar da kowa ya mata shaidar banzanne to wallhi na cire hannuna a kan Abdul, ƴar bidi'a a cikin zuri'a ta! kuma ma yar gidan Adamu! To Wallhi ko mata sun ƙare a gari sai dai Abdul ya zauna a h"....'Ai bai ƙara sa ba suka jiyo ihun Maryam. Kwance suka sameshi a ƙasa yana tari jini na fitowa daga bakinsa idanunsa sunyi jazurr kamar gauta. Ihuu Maryam take yi tana kiran sunan Daddy, hakanne yasa Sadiya da Nusaiba suma suka fito daga ɗakunansu. Kuka sukeyi dukkansu suna kiran Abdalha amma tarin bai tsayaba, duk tari sai jini ya fito daga bakinsa, ana haka Maryam ta hango wayarsa a ƙasa taje ta ɗauka. Haka suka daukoshi dukkansu suka fito da shi izuwa mota. Shek Kabir kabuga kuwa kallo ɗaya ya musu ya kawar da kansa ya na jin cewar ba a'man jiniba ko aman kwata zaiyi shidai ba zai yarda ɗan sa ya auri ƴar bidi'a ba. Nusaiba ce taja motar batare da sun jira dreban nasuba. Maryam da Sadiya ne suka shiga motar Momy kuma ta koma domin shiryowa tabi bayansu. Tinda suka shigar dashi mota Momy ta kira Dr Musa ta sanar masa, hakanne yasa tun kafin su isa a ka shirya tarɓarsu. Momy na shiga palon ta ga ba kowa sai ta nufi sama ɗakin Daddy. Tana shiga ta sameshi yana waya yana dariya alamar dai wanda yake wayar dashi mai muhimmanci ne a rayuwar sa. Cikin damuwa da halin da ta ke ciki ta ce "Haba Shek yanzu wannan abunda kakeyi ya dace kenan bakaga halin da yaronnan ke ciki bane? A'man jini fa ya keyi, ciwon zuciya fa kenan baka tsoran mu rasa shi? Saida ya kashe wayar sannan ya juyo ya kalleta cikin rashin nuna damuwa da zan cen nata ya ce "Idan muka rasa shi ai ba shi kaɗai muka haifaba, kuma karki sake zuwar mini da zancen yaron da ban isa dashiba. Ya na faɗa ya kawar da wannan zancen ya ɗaoko wani yana sakin fara'a a fuskarsa. "Idan zaki iya tuna wa da wani mutumi da ya musulunta yaran Alhaji Salisu, dake garin Benue Makurdi, har Alhaji Salisu ya bashi auran ƴarsa, lokacin da suka samu ƙaruwar yaro na miji har suka gaiyaceni garin nayi wa'azi? Momy ta ce "Eh ai bana manta lokacin domin a ranar na haifi Abdalha. "To amma ba kace mutumin ya rasuba? Momy ta faɗa tana tuno ranar da a ka sanar musu da rasuwar mutumin saida Shek ya kwanta rashin lafiya. Daddy ya ce "Eh haka a ka ce, amma wai a she yana raye bai mutuba, yanzu haka yau ɗinnan yana hanyar zuwa gidannan iji Malam Nura abokinsa. Momy ta waro ido waje ta na cewa "To ina yaje tsawon shekaru? Ko dai ya gudu yabar Musulunci ne? Daddy ya ce "Yanzu haka ma wai da wasu zaiso suma zasu koma ADDININMU. Sannan ya ce "Ki ajiye tambayoyinki har sai yazo domin nima bansan komaiba, abunda nasani dai shine mutumin kirki ya dawo. Daddy ya ƙara sa yana tunano irin abun arziƙin da ya masa lokacin da ya je garin. Daga haka Momy ta dawo da maganar Abdalha, amma Daddy ya ce "Yanzu haka yana cikin farin ciki karta ɓata masa rai. Hakanne yasa ta ce "To zan tafi asbitiin Yanzu idan ka amicen? Amma Daddy ya mata Wani irin kallo ya maka mata ya ce "Yanzu nace miki munada baƙi amma kina zancen tafiya yawo, to yanzu inaso ki kira su Sadiya su baro gurin su dawo domin a haɗa musu kayan tarɓa. Momy ta ce "Wato yarona na gadon asibiti zanje gurinsa shine zakace zanje yawo ko? Ta faɗa tana jin zafin kalmar yawon da ya ce. Daddy dai bai ce komai ba ya bar ɗakin domin zuwa tarɓar babban baƙonsa. Haka Momy ta kira Nusaiba da Sadiya ta ce Maryam ta zauna a gurin Abdalh ɗin. A ranar suka iso garin Kano, amma basu iso gidan Shek kabuga ba suka nufi gidan su Ogan sa kuma sirikinsa wato Salisu uba ga matarsa Hajiya Babba. Su kansu basu san da dawor Muhammad ɗin ba , domin Hajiya Babba tayi hannun riga dasu tun rasuwar mahaifinta da mijinta. Ita Hajiya Babba ganinta dunta iyayen ta suka rasu a hanyar zuwa garin sai ta ɗauki abun tasa a ranta, hakanne yasa ta daina nemansu kwata-kwata. Suma sunyi mamakin ganin Muhammad kuma sunji daɗi da ya zo musu da jikarsu gida. Lokacin da sukaji bayanin auran da Hajiya Babba tayi ne kuma ransu ya ɓaci , amma a ka basu haƙuri da cewar ai yanzu sun rabu da mijin amma tana ɗauke da cikinsa. Haka suka dinga lallaɓata Salis da laɗifa dama su suna ɗan zuwa garin, hakanne yasa suka saki jiki dasu. Samuel da Sarah dai sai bin laɗifa da Salis sukeyi. Washe gari suka shirya izuwa gidan Shek Kabir kabuga.....📝 *MUHAƊU A GIDAN SHEK* *COMMENTS ƊINKU SHINE ABUN ALFAHARINA* *S REZA ✍️* [10/21 22:06] Aliyu Makko: *ADM* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣4️⃣* ........Misalin ƙarfe tara na safiya suka isa gidan Shek Kabir kabuga, kana ganin Shek kasan yana cikin farinciki da zuwan wannan baƙon nasa. Kafin Hajiya Babba ta tafi saida tasa a ka kira yayan mahaifinta Malam Adamu. Tarɓa ta mutunci Muhammad da iyalansa suka samu daga gurin iyalan Shek. Sosai Shek da Muhammad suke cikin farincikin ganin junansu, kana ganin kabuga kasan a kwai magan-ganun a bakinsa. Itama dai Momy tana nunu nata farincikin daidai yanda zata iya. Bayan an kawo musu abubuwan da a ka tana dar domin sune kowa yaci abunda zai iya ci kafi a ka sake sabuwar gaisuwa tsakanin su. A taƙaice Muhammad ya basu labarin abunda ya faru da su tsawon wannan lokacin, kuma ya tabbatar musu da cewar ɗan uwansa ne ya masa. Da mamaki Momy taga Shek na kuka yana tausayawa Muhammad, shima kansa Muhammad ɗin yayi mamaki. Bayan ya gama ne ya fara masa nasihohi a kan wannan jarabtar da ta sameshi. Sosai Muhammad da su Samuel suka ƙara yarda da Addinin musulunci, yanda sukaji irin alkairin da Allah ya tanadar ga masu yafiya idan an cucesu, sosai son Addinin Musulunci ya ƙara shigarsu har suna ji cewar zasu iya komai cikin koyarwar Addinin Musuluncin. Shek ya kalli Salis ya ce "Kardai ka ce min wannan shine mai sunan Alhaji har ya gyrma haka? Muhammad yayi murmushi ya ce "Eh fa shine har ya zama saurayi. Ya faɗa yana dariya dukkansu. Hajiya Babba ma saida abun ya bata dariya, itama Momy dariya tayi tana kallon Salis ɗin da ke sunne kai. Ganin shek na ta kallon su Sarah ne yasa Muhamd gyra zama ya ce.... "Wannan shine babban ɗana. Ya faɗa yana nuna Salis. Sai ya ƙara nuna laɗifa ya ce "Wannan itace auta Ladifato. Sai ya dawo da kallonsa izuwa gurin Samuel ya ce "Wannan kuma shine ɗan gidan yayan nawa, shine babba sai ƙanwarsa gata nan ya faɗa yana nuna Sarah. Sannan ya ɗora da cewa..."Sannan sune suka buƙaci shiga Addinin Musulunci da kansu. Momy da shek da su Maryam da sauran suka amsa da AllahuAkbar! Fuskokinsu cike da annuri jin cewar ADDININMU zai samu ƙarawa. Momy ta ce da Maryam ta je ɗaki ta taso Abdalha. Tayi maganar ne batare da kowa yajitaba. Maryam ta sanar mata da cewar ai tun jiya da sukawo daga asbiti bai fito wajeba, ya ce kar kowa ya dameshi, sannan Dr Musa ya ce a barshi ya samu barci sosai. Badan Momy tasoba ta bar maganar amma hankalinta naga ɗanta. Shima shek ya gabatar da yaransa ga resu. Cikin tsokana Muhammad ya ce "To a cikin su ukun suwaye a maran da za'a aurar? Shek ya nuna Sadiya da Nusaiba. Duk da hakan dai ya ce "Banga magajin Malam ba? Abokin Salis... domin bana mantawa da tsiran sati ɗayane tsakanin su? Da sauri Hajiya Babba ta ce "Ai nasa yanzu ya zama magidanci? Da sauri Momy ta ce "Allah sarki ai bashi da lafiya yanzu haka ma yana ɗakinsa a kwace baisan halin da ya ke cikiba. Salis ya ce "Allah sarki ai ina jin sunansa amma bamu taɓa haduwaba, shine Abdllah Kabir kabuga ko? Yayi maganar ne bayan ganin hoton Abdalha da mahaifin nasa a palon. Maryam ta amsa da eh shine. Daga haka suka ranƙaya ɗakin da Abdalha ɗin ya ke. Sosai suka tausaya masa ganin yanda ya rame ya fita a haiyacinsa. Muhammad ya tambayi mai ke damunsa,? Mai yasa ba'a kai shi asibitiba? Shi kansa shek sai yanzu ya ƙara tabbatar da cewar ciwon ɗan nasa na gaskene ba yanda yake tunaniba. "Ciwon nasa bana asbiti bane na gidane! Cewar Momy cikin wata iriyar murya. Hajiya Babba da Muhammad har haɗa baki sukeyi na tambayar kamar ya? Ganin haka yasa Shek barin ɗakin yana jin wani irin abu na masa ciwo game da ciwon Abdalh ɗin. Take Momy ta kwashe komai ta sanar musu da komai, tun farkon gabar dake tsakanin yaran har ta dawo soyayya. Salis yayi mamaki sosai jin cewar a kan soyayya Abdalh ya koma haka. Da sauri Muhammad ya fita izuwa gurin Shek. Hajiya Babba da Momy ma suka bi bayan sa. Bayan fitarsu Momy suma ƴan matan suka fita. Salis da Samuel kuma suka zauna a ɗakin suna jiran ya farka. Ai kuwa basu wani daɗe a ɗakinba ya tashi. Yana tashi zaune ya fara bin Salis da Samuel da ido. Salis ne ya matso kusa dashi ya ce "Shek Abdalha Kabir kabuga Sarkin soyayya? Ya faɗa da a lamar tsokana? Kafin Abdalh ya sauƙo daga duniya mamakin ganinsu a ɗakinsa Salis ya ɗora da cewar..."Damafa an ce malamai sunfi iya soyayya, domin su ta gaskiya sukeyi shiyasa suke shan wahala...kasan fa ita soyayya tafi wahalar da mai yinta dan Allah kamar dai ku Malamai. Izuwa yanzu Abdalha ya bar mamaki sai tsoro. Kallon Samuel yayi da ya ke ta faman dariya, sai ya dawo da kallonsa izuwa ga Salis. Ya buɗe baki zaiyi magana Salis ya ƙara so kusa da shi ya ce "Kardai a ce tsoro kake ji? Kana jarimi a soyayya amma"... Salamu'alaikum? Cewar Maryam tana shigowa ɗakin riƙe da tiran kayan marmari. Tana shiga saiga Sarah da Laɗifa suma sun shigo. Salis ya kalli Maryam cikin dariya ya ce "Maryam wacece take wahalar min da abokina, ƴar gidan waye a wannan ƙasar faɗa min yanzu muje mu jawo mata a'ya da hadisai? Maganar tasa saida taba Abdalha dariya, sai ya ɗan murmusa yana kallon Maryam a lamar tambaya jin Salis ɗin ya ƙira sunan Maryam. Kafin Maryam tayi magana Abdalh ya ce "Wai dama mazama suna zuwa gurin aure tin aure yana saura sati guda? Yayi tunanin ko ƴan uwan dangin mijin da zasu auri ƙanyan nasane, a tunansa gurin auran sukazo. Saida Maryam da Laɗifa suka sha dariya kafin Maryam ta ce "To ai zaku iya sanin yarinyar da zai aura domin ba ɓoyayya bace? Salis ya ce "Tofa kenan sele ce yarinyae?! Wacece? Ta ce "Zainab Adam ambata wannan mai yin ƙasidun. Da ƙarfi Salis da laɗifa suka haɗa baki da cewa "Zainab Adam? Maryam ta ce "Ƙunsan ta ne? Abdalha kowa da sauri ya kamo hannun Salis ya ce "Kasanta ne? Salis da mamiki da ruɗani ya saki wata dariya yana kallon laɗifa wacce itama dariyar ta keyi. Ɓangaren iyayen kuwa cikin mamaki Muhammd yake tambayar Shek dalilin hana Abdalh auran yariyar. Shek ya faɗa masa dalili Hajiya Babba ta ce "To Wai ita yarinyar ƴar waye? Kuma meye aibunta? indai anyi bincike a kanta komai daidai ai kawai sai ku amince. "Shek ya ce "Yar bidi'a ce, sannan tana mace tana yawon zuwa gurin taro tana kaɗae kaɗe da raye raye, saboda haka nace bana sonta a zuriata. Cikin mamaki Hajiya take kallon Shek domin ta gano shi, ita kanta family ɗin su a kwai masu yin ƙasida, har yanzu gidansu a nayi, kuma a haka mahaifinta ya auro mamarta dukda ba aƙida ɗaya sukeba. Shek ya ci gaba da cewa..."Ga mahaifin yarinyar ba mutumin kirki bane baya ƙaunar cigaban addinin Allah. Cikin gajiya da zancen Hajiya ta ce "Waye uban nata? Da sauri shek ya ce "Wannan mutumin wai malam Adamu? "Da mamaki Hajiya Babba ta ce "Ya sunan yarinyar? "Wannan dai mai waƙar Zainab Adam Ambato. Tsabar mamaki saida Hajiya Babba ta ƙware, shi kansa Muhammad a mugun mamaki yake kallon Shek domin harga Allah ya mutuƙar bashi mamaki. Da sauri Momy ta ɗauko ruwa ta bata, sannan ta ce "Lafiya dai ko? Hajiya ta kalli Shek ta ce "Idan har kanada matsala da mahaifin yarinyar to bai kamata abun ya shafi yaranku ba, saboda haka ga shawara zan baka Malam...Yaranka na cikin matsanancin hali, sannan kuma ita yarinyar da kuke magana a kai yanzu haka rana irin ita yau za'a ɗaura mata aure, kuma ita ɗin ƙanwata ce, malam Adamu kuma mahaifinane, domin shine yayan mahaifina uwa ɗaya uba ɗaya. Kafin shek da Momy su dawo daga duniyar mamaki Muhammd ya tabbatar musa da cewar hakane, wannan zuwan da sukayi ma a family House ɗinsu suka sauƙa, kuma daga nan gidan gidansa zasu nufa. Kafin su sake cewa komai saiga Abdalh da Salis da sauran suma sun fito daga ɗakin Abdalh ɗin, suma Salis ya sanar musu alaƙarsu da Zainab. A wannan ranar Shek Kabir kabuga yaji kunyar da bai taɓa jiba, ya zaki mahaifin matar abokinsa a gaban sa. Muhammad ya bashi haƙuri a kan idan har ya amince da Abdalha ya auri Zainab to kamar anyi an gamane domin Malam Adamu baida matsala. Cikin jin kunya ya amince yana jin cewar hakan ne zaisa Muhammd yaji sauƙin abun da yama matarsa, sannan ya ce "Shida kansa zaije gidan Malam Adamu su samu jituwa. Kowa yaji daɗi yayinda Abdalh ya zo ya rungumi Muhammad yans ta faman godiya. Nan Shek ya gabatar da Muhammad a gareshi da iyalansa, jin cewar Salis abokinsa ne yasa shi cewa "A she niɗin ɗan biyune shene Momy baki taɓa faɗa min ba ko? Ya faɗa yana ƙarasowa gurin Salis. Kowa dariya yayi sosai harda Nura da yake zaune a kusa da Nusaiba. A wannan ranar da yamma Momy da Hajiya Babba da Muhammd da shek Kabir kabuga suka nufi gidan Malam Adamu. Lokacin da Mama taji abunda ke tafe dasu tayi murna sosai, Malam kuwa ganin idon Muhammad yasa ya kasa cewa komai domin kunyar sa da kuma yar tasa wato Hajiya Babba. Dukda bata zuwa Kano Amma hakan baisa ta manta dasuba, yana jin kunyarta sosai. Sai ya saki fuska ya ce ya haƙura a kan duk abunda ya faru. A kayi sabuwar gaisuwa kowa murna da farinciki. Saida a ka nutsu sannan Muhammad ya shigo da batun auran Abdalha da Zainab. Nan nefa Malam Adamu ya ce "To a gaskiya dai yanzu haka saura kwana kaɗan auranta, kuma yaron da zai aureta kamar ɗa yake a gurina idan nace na fasa ai sai duniya tamin kallon mutumin banza. Muhammad ya ce "Hakane to amma Malam ita yarinyar tana sonsa? Lokacin Malam yayi shiru yana kallo Mama. Haka dai mama ta sanar musu da cewar ai dama auran biyayya zatayi, bata son Aliyu kawai dai tabi maganar iyayenta ne. Malam yasa a ka kira Zainab a gaban sa, a ka tambayeta "Shin kina son Aliyu ko kinada wanda kikeso? Nan take gabanta ya faɗi dukda kuwa tasan da zuwan su, domin Isa ya tura mata da saƙo. yanzuma kafin ta ce komai saƙo ya ƙara shigowa wayarta, tana dubawa taga numbar sa ce. Anyi gajeran saƙo kamar haka... Wannan itace kaɗai damar mu, kawai ki gyaɗa kanki a lamar Eh, nikuma zance musu kince kinada wanda kikesone. Bayan ta gama karan tawane ta ɗaga kai sai tayi ido biyu da isa yana mayar da wayarsa aljihu ya sakar mata murmushi. Maganar da Malam yayi ce ta dawo da ita daga abinda ta keyi. "Zainabu karkiji kunya ki sanar danu komai in sha Allah zan baki wanda kikeso. Zainab cikin jin kunya ta ɗaga kai batare da ta ce komaiba. Mama ta ce "Kin ɗaga mana kai mai hakan ke nufi kenan? Hajiya Babba ta ce "Zee Ambato ki buɗe baki kiyi magana? Zainab ta ɗago kai ta kalli Hajiya Babba sai sake sun kuyar da kanta. Ai kuwa caraf Isa ya ce "Wai tanada wanda take so. Isa Malam ya ce sai ta faɗa da kanta. Haka dai akayi da ita ta kasa cewa komai. Daga haka Zainab tabar palon cikin farin cikin jin iyayen nasu sun shirya, tun a wajan ta fara tunanin yin sabuwar ƙasida a cikin satin nan......📝 *Masha Alhamdulillh A shekaran jiya lahaɗi ƙanwata abar alfaharina tayi sauƙar al-ƙurani maigirma. Allah yasa tayi mai amfanar ta da ma al'ummar musulmai baki ɗaya, Allah yasa albarka a ciki, Allah ya ƙara mata basira da juriya. Allah ka haɗa kan al'ummar musulmi baki ɗaya.* *Wannan dalili ne yasa kukaga jiya da shekaran jiya ban muku posting ba. Wannan ma ba yawa sai kuyi haƙuri.* *Zan shiga wata gasa ta manyan marubuta ina barar addu'arku, Allah ya bamu Sa'a, domin ba iya war mubace tsan-tsar addu'o'in kune.🤲* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *S REZA ✍️* [10/21 22:07] Aliyu Makko: *ADM* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣5️⃣* ........Hakan da Zainab ta yi ne ya ƙara tabbatar musu da cewar tanada wanda takeso. Cikin hukuncin Allah komai ya tafi daidai da yanda Allah yaso ya kasance. Malam Adamu da kansa ya zaunar da Aliyu ya tsara masa komai yanda zai fahimcesa, ya tabbatar masa da cewar ya yi haƙuri domin ba zaiwa ƴarsa auran dole ba, da farkoma rashin fahimta ne yasa naso na aikata kuskure. Da mamaki yaga Aliyu na murmushi Malam ya tambayeshi dalili. Ya ce "Ai tun ba yauba na gano Zainab tana son Abdalha, kuma nasan da cewar auran biyayya zatayi...koda hakan bai faruba to babu shekka ni da kaina inada niyar samunka muyi magana a kai...sai dai ina tsoron abunda zai biyo baya domin nasa ba kwajituwa da yaron da takeso din...sannan kuma Abdalh da kansa ya turo Isa a kan ya roƙeni na janye batun Aurena da Zainab kuma na yarda Allah ya basu zaman lafiya sannan nima naji naɗin wannan haɗin kan naku. Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai baki ɗaya, Allah ya ƙarya duk wani abun da zai tarwatsa kan al'ummar musulmai. Malam Adamu ya kamo Aliyu yana hamdala yana amsawa da Amin amin. Haka Malam ya ce duk yarinyar da yaga ta masa a cikin dangi do yaje ya naimi soyayyarta shi kuma zai masa komai na aure. Aliyu yayi murna sosai a haka ya bar gidan yana jin son Zainab amma zai daurewa zuciyarsa kamar yanda ya ce. Kwana biyu da faruwar haka soyayya ta ɓarƙe tsakanin Zainab da Abdalha, duk wata kafar sadarwa labarinne ke kai wa da komowa, al'ummar gari kowa mamakin wannan abun ya keyi, ai jama'a basu ƙara shiga mamaki ba saida sukaji soyayyar Maryam da Isa, nan fa kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa. Masu cewa dama ai tun farko rashin fahimta ce tasa kowa baya ganin kowa da ƙima. Wasu kuma suce ai dama ai Malamai sune masu jefa al'umma a cikin ruɗani domin sunsan gaskiya sai su taketa domin son zuciyarsu. Wasu kuma sai suyi addu'ar Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulmai mu zama addini kuda ɗaya, koda ma nawane to a zauna lafiya babu cinmutuncin juna da wulaƙanta jna da aibata juna. Ranar juma'a a ka ɗaura auran Sadiya da angonta. Sai Nusaiba itama da nata angon. Sannan a ranar ne Sarah da Samuel suka karɓi kalmar shahada. Kowa ya zaɓi sunan da yakeso. Samuel ya koma Ibrahim Sarah kuma ta ce tana son sunan da taji Momynta tana kiran Hajiya Babba dashi wato Fatima. Manyan Malamaine suka halarci taron hakanne yasa Fatima da Ibarahim suka samu kyaututtukan bam'mamaki. Tabbas sunga yanda a ke karamci sannan sunsha wa'azi mai ratsa zuciya, har saida suka zubar da hawaye. A wannan lokacin ne kuma Fatima ta fara tinanin iyayenta tabbas tayi kewarsu tana son ganinsu. Soyyaya ce mai tsafta da birgewa irin ta malamai Abdalh da Zainab sukeyi. Shima Isa ba'a barshi a baya ba domin soyewa sukeyi da Maryam sosai. Duk inda kaga Abdalha to suna tare su huɗu. Salis Abdalh Ibrahim Isa. Suma haka matan Laɗifa da Fatima da Maryam haka zasu tafi gurin Zainab a zauna a ta hira, a nanne Maryam ta ke sanar wa Fatima cewar ai duk wata Fatima to zara sunanta to kawai yanzu sai a koma cemata Zara, kunga an cire S na Sarah an sa Z na Zara. Cikin farinciki Zainab ta tabbatar mu da hakane, ai kuwa a ka koma cemata Zara. Tabbas Zara da Ibrahim sun tabbatar da cewar suna tare da malamai, domin a ɗan kwana goma sha huɗun da sukayi sun san abubuwa sosai. Ibrahim kam ɗan gata ya zama domin kuwa dukkansu ukun ne suke ƙara masa a bubuwa game da addini. Abdalha ya dage da koya masa karatu cikin muryarsa mai tashin daɗi, wani lokacin idan Abdalh na zubawa Ibarahim karatu sai ya ta kallonsa yana jin Allah yasa shima ya iya karatun Alqur'ani maigirma kamar haka. Isa ma haka yake koya masa wasu littattafai na addini Salis ma ba'a barshi a baya ba. Itama Zara haka Maryam wacce dama ita duk cikin yaran shek Kabir babu kamar ta a mata indai ɓangaren karatun ne, haka take rerewa Zara karatu sosai. Haka Malam Zainab zasu kwashe lokaci suna koya mata karatu ga Mama ga Momy dukkansu suna koya mata, domin suɗin sunzama wasu taurari a cikin al'umma. Shek Kabir kabuga da Malam Adamu kam komai ya huce, yanzu lokacin auran yaran nasu kawai suke jira. Mama da Momy da Hajiya Babba suma sun zama ƙawaye sosai suke zama su sha hira. A nanne Hajiya Babba take sanar musu da abunda ya faru da ita na auran AJ da tayi. Mama da Momy matan manyan malamai wanda kowacce kanta ke ceke da sanin hukunce-hukunce da tsan-tsar sanin ilimin rayuwa. Bayanin da suka mata ne yasa hankalinta ya kwanta, ta ɗaga hannu ta godewa Allah da yasa bata aikata abun kunyaba, tabbas zama da Malamai ma wani Makaranta ce. Shima Muhammd ya naimi ƙarin bayani game da auran Hajiya Babba. Shima dai haka Shek Kabir da Malam Adamu suka tabbatar masa da cewar yanzu tana aihuwa to zai iya auratan sannan kuma kuɗin da ta bashi to kuɗin yazama halak ɗinsa. Daga haka suka tattara izuwa gida cikin kewar junansu. *AJ POV* Haka rayuwa taci gaba da tafiya musu cikin haƙuri da irin rayuwar da sukeyi, har yanzu Kadija bata daina nuna masa cewar tana tare dashiba, amma shi ko ta kanta baya bi, yanzu bashi da wani burin da ya huce ya ga ɗansa ko ƴarsa. Haka Allah ya ɗorawa AJ ƙaunar yaron da za'a haifa masa tun kafin yazo duniya. Sosai yake ƙoƙarin sayan komai da za'a buƙata dukda kuwa baidashi amma haka yake hana kansu ya tara. Ita kanta Nana yanzu addu'a takeyi Allah ya sauƙi ajiyar lafiya. Ɓangaren gidan Muhammd kuwa shine ya hana Salis zuwa gurin Nana ya ce ya barta har komai yayi daidai kafin yaje mata da maganar aure. Wani sabon tashin hankali kuma shine... Ibrahim fa gaba ɗaya hankalinsa yayi ga Hadiza domin tun lokacin da ya ƙarɓi Muslunci sai abotarsu ta ƙaru da Umar. Shi kansa Umar yaji daɗin jin abokinsa ya musulunta. Yanzu sun daina zuwa club sannan sun daina zuwa wannan gurin wasan kiss ɗin. Sosai ya mai da hankalinsa a kan karatun Addini. Yanzu haka har gidan su Umar ɗin yake zuwa domin kawai ya ga Hadiza, ita kuwa Hadiza sam bata ganeshiba domin yanzu kullum cikin shigar kamala yake, haka zaluka har yanzu bata daina wannan yawon nata da kuma faɗa da koma waye ba. Shikuwa dukda hakan yaji yana ƙara sonta. Yanzu haka ya shirya idan har Hajiya ta aihu lafiya a ka ɗaura auranta da Daddy to zai gabatar da soyayyarsa ga Hadiza. Yanzu haka Ibrahim da Zara sun mallaki abubuwa sosai da a ka basu lokacin da suka Musulunta, su kansu har mamaki sukeyi. Ɓangaren Laɗifa ma dai yanzu burinta iyayen nasu su shiga magar ta da Ibrahim, saidai yanzu taga yana ɗan ja baya da ita, amma ta bar hakan a kan yanzu baida lokaci ne. Haka shima Umar a kullum soyayyar Laɗifa ke masa baƙe-baƙe a ransa, amma yanzu dole ya haƙura kodan Musuluntar da abokinsa yayi zai bar masa ita. A da yayi alwashin ba zai taɓa bari Samuel ya auri Laɗifa ba, amma yanzu tunda ya koma Ibrahim to an zama ɗaya, zai taushi zuciyarsa ya danne komai ya barmasa, bugu da ƙari ma ƙanwarsace. Haka ɓangaren Zara kewar Elixa da mahaifinta ne ya dameta amma taƙi sanarwa kowa, haka zata shiga ɗaki tasha kuka har ta godewa Allah. Ɓangare ɗaya kuma ga soyayar aj da ta tabbatar da cewar a jinin jikinta take, bazata daina son AJ ba koda kuwa shiɗin ya ce baya sonta bare kuma tana da tabbacin yana sonta. Duk lokacin da zaizo gidannan bata yarda su haɗu, haka ta hana kowa ya sanar masa da cewar ta Musulunta, shi kansa idan yazu sai zuciyarsa ta raya masa cewar yana son ganinta amma ya musu hakan. Allah buwayi gagara misali, Allah mai yanda yaso a lokacin da yaso babu wanda ya isa ya ce ya haka. Ranar Litinin Hajiya Babba ta haifi ƴarta a gida ba tare da zuwa asbitiba, yarinya fara sol mai kama da ubanta. Tabbas a kwai abubuwa masu yawa da mutane da yawa suka shirya aiwatarwar bayan ai'hwar Hajiya Babba. To yau dai Allah ya sauketa lafiya sai mai zai faru? A daran Muhammd ya kira Kawu ya sanar masa shi kuma kawu sai da gari ya waye yazo har gida ya sanarwa da AJ. Daidai lokacin Aj ko karyawa basuyi ba, abunda zasu karya dashi ma babu gashi lokacin tafiya aikinsa ya kusa. Yana tsaye a gaban Nana yana tausayinta itama tana tausaya masa, yana bata haƙurun cewar idan ya fita zai dawo da bredi in Allah ya yarda, kasan cewar yau kwana uku da biyan sa albashi kuma duk kayan jariri ya siya kasan cewar an sanar dashi aihuwa yau ko gobe, kuma bayaso a ce ya gaza. Da mamaki kawun yake kallon gidan ganin babu komai a gidan ga kuma dukkansu suna tsaye suna kuka. Kawar da wannan yayi ya sanar musu da abunda ya kawo shi. Lokaci ɗaya AJ ya daina jin yunwar, da ƙarfi ya ce "Alhamdulillh! Alhamdulillh!! Allah na gode maka. Take ya zube a gurin yayi sujjada itama Nana ta fara tata hamdalar. Gaba ɗaya suka naimi yunwar suka rasa. Nana taso binsa amma ya ce a'a ta zauna a gida, haka badan tasoba ta zauna cike da ɗokin son ganin jininn nasu. AJ ya tattara komai na bybe ya biya ta gidan matar Kawu suka tafi. Koda sukaje babu kunya AJ ya karɓi yarinyar ya ƙura mata ido yana jin sonta na shiga duk wata jijiya dake jikinsa, lokaci ɗaya hawaye suka wanke masa ido ya ƙara jin tsoran Allah a zuciyarsa, tabbas wannan yarinyar Allah yayi ta hanyar aure za'a sameta! Haka ya faɗa a zuciyarsa. Lokacin da Hajiya Babba taji cewar AJ zai shigo sai ta bar jinjirar a gurin ta koma cikin ɗakinta. Aj yaji kaman kar ya ajiye yarinyar tsabar murna, saida matar Kawu ta masa maga sannan ya ajiye yarinyar zai fita. Ta ce "Kunjimu da ɗan ƙaramin uba! To waye zaima yarinyar huɗubar? Ai kunji matsalar ɗan yaro da aihuwa kenan ai dole a samu rashin hankali. Kasan cewar matar kawun ta fara manyanta, yana jin kunyarta hakanne yasa AJ ya sunkuyar da kai yana jin kunyar maganar ya ce "Daddy ne zai Mata? Yana faɗa yabar palon badan ya gaji da ganin yarinyar ba, sai dan kawai karya wuce gona da iri. Koda Muhammad ya zo yaji abunda AJ ya ce yaji daɗi amma hakan baisa ya yanke mata sunan da zaisaba saida ya kira AJ ɗin a ka tambayeshi ya ce "Daddy duk sunan da kaga dama ka saka mata. Daddy ya ce "A'a ba haka za'ayiba. Ganin Daddy yaƙi yarda yasa AJ ya ce "To a sa sunan Innah! Yana faɗa ya kama hawaye domin tunuwa da innar tasa. Haka kuwa a kayi Muhammad ya ma yarinya huɗuba da sunan Innah wato *HAJARA*. Haka a ka shiga sanarwa da ƴan uwa ta ko ta ina. Gaba ɗaya family Shek Kabir kabuga sunzo, harda Nusaiba da Sadiya. Haka suma gidan Malam Adamu suka tattaro gaba ɗaya. A can ɓangaren su Umar da Usman suma sunzo tare da waso mutane da suma suka musulunta. Domin tin bayan zuwansu garin KATUNGU. Muhammad ya raba musu jari mai ƙarfi wanda yasa suma suke kyautatawa wasu daga cikin ƴan garin har suka fara musulunta. Yanzu haka kowa yayi aure a cikinsu, haka suka tattaro suda iyalansu. Ranar suna yarinya taci sunan Hajara Innah amma zasu dinga kiranta da *ILHAM.* Wasu da yawa da suka halarci sunan basu san cewar ba Muhammad bane uban yarinyarba domin kuwa yanda yakeyi zaka rantse da Allah ɗansa ne na cikinsa, Salis da su Abdalh kowa ka gani farinciki yakeyi, sai yau Abdalha ya taɓa zuwa Benue Makurdi, yayi mamakin ganin musulmai da yawa a garin, don zai iya cewa ma musulmai sunfi yawa a garin, ba kamar yanda yaji a ke cewa garin arnane ba, tabbas yayi mamakin ganin yanda Musuluncin yayi ƙarfi a gari. Bai ƙara mamaki a saida yaga ko ina ya shiga ana kiran sunansa a na girmamashi, tabbas yayi mamaki sosai, manya da yara sai kiran Abdalh Kabir kabuga a keyi. Haka ɓangaren Zainab itama zuwa ta na farko krenan, bata taɓa zaton tanada masoya a garin ba sai yau, Zainab Ambato Zainab Ambato duk inda ta shiga, ganinsu tare da Abdul yasa yan garin yandar da zancen da sukaji a na cewa wai soyayya ce tsakanin Abdalha da Zainab. Lokacin da kowa ke cikin farinciki lokacin ne kuma mutum biyu suke cikin tsananin damuwa da wannan rana. Wato AJ da Laɗifa. Ita laɗifa baƙin cikin abunda akeyine ya dameta wai AJ ne ya auri uwar ta har suka aihu kuma a ke taron suna harda murna. AJ kuwa damuwar rashin kuɗin abunyanka, dukda har yanzu babu wanda ya tambayeshi amma yayi alwashin saiyayiwa ƴarsa abun yanka kuma yanzu haka ko sisi babu a aljuhunsa.....📝 **ADDININMU* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣6️⃣* ........ Zama ya yi a gurin yana faman nazari a kan komai dake faruwa a cikin rayuwarsu shida ƙanwar tasa, haƙiƙa suɗin marayune gaba da baya basu da kowa a cikin wannan duniyar, daga shi sai ƙanwarsa sai kuma wannan yarinyar da a ka haifa masa, tabbas sau a irin wannan ranar ya ƙara jin cewar Innah bango ce makingina a cikin rayuwarsu yasan da tana raye zata yi fishi da shi amma daga baya komai zai huce, da yanzu kan cenyarta zai kwantar da kansa ya sanar mata da damuwarsa. Yana zaune a gurin Nana ta fito daga wanka cikin mamaki take kallon ta ƙaraso kusa dashi ta ce "Yaya har kadawo? Yanzu nake shirin tafiya ni da Kadija fa. Ɗago kansa yayi ya kalleta sai kukan nasa ya ƙaru yana tausayin Nana sosai domin duk shine ya jefasu a cikin wannan halin. "Haba yaya yau ai ranar farinciki ce a garemu amma kana zubar da hawayenka for noting Please yaya ka ka ka daiiii na! Itama ta ƙara sa tana kuka domin ta gano dalilin kukan nasa. Rungumota jikinsa yayi suna sakin kuka a tare. Sai da suka yi mai isarsi kafin AJ ya sanar mata da matsalar sa. Ta ce "Yanzu yaya kaman nawane zai siya maka Ragon? Ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali ya ce "Ai ni Nana ko na dubu sha biyar na samu na saiya ai na fita kunya. Nana tayi shiri tana tunani sai ta ce "Yaya bari na shirya Allah zai kawo mana mafita da yardar sa. Aj ya ce "To Amin ya Rabbil Alamin. Yarinya fa taga gata domin kuwa iyayen nata da yawa ga yayu suma ba'a barsu a baya ba. Dangin Hajiya Babba da basu san uban yarinyarba sai tambayar dangin mijin sukayi, ai kuwa matar Kawu ta ce gamu nan, matar Kawu da yaranta biyu sai mamar Kadija da wasu ƴan uwan Matar kawun sune a matsayin dangin AJ. Hajiya Babba ce da kanta ta hana kowa ya sanar dasu waye uban yarinyar. Ai kuwa Laɗifa ta fasa kwai kowa yasan waye mijin Hajiya Babba ɗin. "Wani ɗan yarone wanda koni na girmeshi sannan ɗan matsiyata ne hasali ma yaron gidan Salis ne, daga zarar Salis yazo dashi gidannan shikenan Hajiya ta ɗauke shi suka bar ƙasarnan sukayi aure, yanzu haka yaron ko Naira baya magani, idan kuka ganshi wlhi sai kunyi tir da wannan abun. Laɗifa ta faɗa tana kuka, yayinda Hajiya Babba ta sun kuyar da kai ƙasa tana jin kunyar maganganun da Laɗifa tayi. Take ɗakin ya kaure da salati, kowa na mamaki. Wata daga ciki ta yi ƙarfin halin yin magana, domin kuwa gaba ɗaya danginsu suna mutuƙar girmamata dalilin arziƙin ta. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Yanzu wannan wani irin abun kunyane? Shine tsabar rashin ta ido harda gaiyato dangi, mukuma muka ɗauko ƙafa mukazo wannan wani irin abun kunyane, auran abokin ɗanki harda ciki!!! An shiga uku wai namiji da cikin haihuwa. Nan fa suka mata tatatass wanda har suka gama bata ce komai. A na cikin wannan biki bidurin ne kuma saiga AJ ya shigo gidan riƙe da ɗan ƙaramin ragonsa, ƙafarsa ko taƙalmi babu, dagashi sai wata baƙar riga waice ta kawo masa har idon sau, rigar dai kamar jallabiya, sai fuskarsa da ko gyaran fuska babu, gashi yayi tumu-tumu da lilin kokuwar da sukeyi da ragon. A wannan lokacin gaba ɗaya labarin ya karaɗe cikin domin kuwa kowa yayi tunan daga dawowar Muhammad ne ta samu juna biyu. Duda cewar wasu sun fara tafiya amma dai gidan cike yake da matan manyan mutane da dangin Hajiya Babba ɗin harda su Mama da Momy. Da farko Laɗufa bata ganeshiba domin kallo ɗaya zaka masa ka gane cewar yana cikin tsananin rashi. *ADM* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣7️⃣* ........Kuka ya kuffce mata batare da ta iya furta komai ba ta bar polon zuciyarta na mata zafi da abunda Ibrahim ya ce. Bayan tabar gurin ne Muhammd ya dawo da kallon sa gurin AJ ya ce "To kaji abunda Kawu ya ce ko kanada wacce kake so? Kafin AJ ya ce wani abu har Kawu ya magantu "Ai a kwai ƙanwarsa ƴar wajena ita nakeso na haɗasu kodan zumunci yayi ƙarfi. Muhammad da su Shek suka ce "Masha Allah ai abu yayi daɗi haka a keso! Allah ya sanya albarka ya sa a yi muna raye. A ranar mutanan Kano suka tattara suka tafi, shi kuma Aj a ks mayar masa da dukkan wasu kadarorinsa ko sisi ba'a taɓa ba, saima ƙari da Muhammd ya masa a kan nada. A cikin kwana uku AJ ya koma sabon gidansa bayan yasa an masa sauƙar alqur'ani mai girma. Bayan tarewar sa ne Kawu ya tura babbar ƴarsa gidan su AJ ɗin wai su zauna tare su ƙara fahimtar juna kafin lokacin bikin. Yarinyar mai suna Safarau itama tanada wanda takeso amma tana ganin irin gidan da AJ ɗin ya mallaka sai ta share wancen saurayin nata ta fara neman hanyar da zata samu fada a gurin AJ. Tare suke kwana da Nana kuma Nana ta sakar mata fuska sosai, ko dama suna ɗan shiri da ita amma ba sosai ba, ba kamar ƙanwae Safara'un ba da basa shiri da Nana kwata-kwata. Ɓangaren Kadija kuwa itama kullum tana ziryar zuwa gidan domin neman fada, hakanne yasa Nana ta rasa ya zatayi da Aj ɗin wanda shi ko a jikinsa kuma yasan da cewar duk domin shi sukeyi, lokacin da Safarau ta gane cewar Kadija ma tana zuwa gidanne domin AJ sai ta sake taku, itama kuma kadijar sai ta sake nata takun. Ɓangaren Laɗifa kuwa har ɗakin Ibrahim ta shiga lokacin yana kwance yana waya da Hadiza, wayarma shine ya saya mata, sannan yanzu ta rage wannan rawar kan nata, ta nutsu sosai soyayar Ibrahim ta gama ɗaureta ta ko ta ina, har mamakin wasu abubuwan idan tayi takeyi,, idan tana waya dashi har wani lumshe ido takeyi kamar yana kusa da ita. "Cek ta tsaya tana kallonsa ganin yanda yake murmushi yana juyi a kan gado alamar dai hira tayi daɗi. "Ibrahim! Ta kira sunansa cikin wata muryar da bata san tanada itaba. Ibrahim najinta ya ce "My lovelly i'm Coming now. Yana faɗa ya kashe wayar ya kalli Laɗifa cikin sakin fuska ya ce "My Sister zo ki zauna mana kin tsaya a tsaye? "Shin dama da gaske kake nufin kanada wacce kakeso? Dama ba sona kakeyiba yauda ta kayi kenan? Ibarahim ya ce "Please zo ki zauna muyi magana dan Allha. Yayi maganar yana binta da kallon tausayi. Ba dan tasoba ta zauna kusa dashi tana jiran taji yace duk wasa yakeyi itace zaɓinsa. ya ce "Laɗifa bazan ɓoye mikiba tunda nake dake ban taɓa sonkiba, da farko dai nayi sha'awar ki har na ƙudirta a raina saina sameki kota yaya, amma da naji cewar keɗin yar uwata ce ta jini sai naji hakan ba zai taɓa faruwa tsakanin nina da keba, hakanne yasa na yaƙi zuciyata har na samu nacire abun da nakeji a kanki, yanzu ina miki kallon Fatima ne, inasonki so irin wanda yaya yakewa ƙanwarsa wallhi Laɗifa bansa haka so yakeba saida na haɗu da Hadiza, kallo ɗaya na mata yarinyar ta tafi da imanina ina sonta sosai Please dan Allah ki fahimceni ba yaudarar ki nayi ba. Ladifa ta kalleshi da kyu cikin kukanda ta ke yi ta ce "Dan Allah karka min haka wallhi ban taɓa son wani ɗan namijii a duniya ba in banda kai! Shin kasan tun yaushe nake sonka? Tana kuka ta na ce wa "Tun lokacin da na ganka a club kuna wannan wasan game ɗin kiss tun alokacin na fara sonka kuma har yanzu yi nakeyi amma yanzu lokaci ɗaya kace wata ka keso! Yanzo kodan dangantakar da ke tsakanin mu bazaka iya daurewa ka aurenuba haba Ibrahim! Ibrahim ya matso kusa da ita kamar zai shiga jikinta ya ce "Laɗifa bakisan so ba, haƙiƙa da farko naso na cuci kaina da cewar inason ki, kuma duk sha'awa ce sai yanzu da na haɗu da wacce nake so sannan na banbance so da sha'awa, shi so ba'a masa alfarma ko tilastawa shi ɗin gaban kansa yakeyi a kan abun da yake so, baya shawara da kowa yake shiga zuciya, saboda haka ki daure ki fahimci me cece s"...."Cikin fitar haiyaci da rufewar ido ta ƙatse shi da cewa "Ya isa haka!² bana son jin komai naji kaje ka aureta ba sai kana faɗa min irin abunda kake jima, dama ai haka ɗan Adam yake barinma wanda tun farko zuciyarsa ta fara tashi a cikin duhun jahilcin kafirci, ai dama idan bakayi hakan ba ai baka cika jinin wannan ƙaton arnan ba wanda bai son komai ba sai cuta da zalunci, to ai kai abumma biyu ya haɗa maka uwar da uban duk haka su"...Bata ƙarasa ba taji sauƙar wasu lafiyanyun mari a kuncinta wanda yasa ta saki wani ihuuu mai ƙarfin gaske. Hajiya Babba ce da Muhammd suka shigo ɗakin domin jin laɗifa tana faɗin irin wannan magan-ganun. A wannan ranar Laɗifa tayi na damar wannan furcin nata domin kuwa ba ƙaramin duka tasha a hannun Hajiya Babba ba, dama kuma itama tanada cikinta so take wata tara ya cika kafin ta haifeta, ai kuwa sai gashi yau wata taran ya cika. Shi kansa Muhammd maganar ta taɓa masa zuciya domin kuwa wannan maganar har dashi takeyi ba iya Ibrahim bane, ganin dukan yayi yawa yasa ya hana Hajiya Babba. Hajiya Babba ta ba Ibrahim hakuri a kan karya bi takan zancenta. Ibrahim kuwa a lokacin tunanin iyayensa ya zomasa ko yanzu a wani hali suke ohoo! Ai kuwa dole ya nemo su ko ma a wani hali suke, iyaye ba abun wasa bane, sannan yayi mamakin jin wannan furcin daga bakin Laɗifa, ita batasan cewar abunda yayi daddynta shine yayi naduba, sai kuma ya mata uzuri domin yasan ba'a cikin haiyacinta takeba. Muhammad ya tambayeshi abun da ya haɗasu. Bayan Muhammd yajine ya ce ya sanar masa gidan su yarinyar da yakeso gobe zaiyi magana da Titi za'a je nemomasa auranta shida Salis. Ibrahim yayi murna sosai, sannan Daddy ya ce "kar Salis da Fatima suji abunda ya faru tsakanin ka da laɗifa, itama zan mata faɗa bazata ƙaraba, kuma kar abun ya dameka a cikin fushi ya take. Shi kam Ibrahim zuciyarsa cike da murnar za'a je zancen auransa ya ce babu wanda zaiji ni harna manta ma. *AJ POV* Da sallama ya shigo palon yana raba idanunsa ko zai ganta amma sai yaci karo da Ibrahim zai fita. Gaisawa sukayi yana tambayar ss Sarah. Ibrahim yayi murmushi ya ce "AJ yanzu ta bar Sarah ta koma Fatima, Allah ya nufa mun gane hanyar gaskiya dagani har ita saboda haka ka ajiye sunan Sarah ka koma ce mata Fatima. AJ ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Alhamdulillh Masha Allah! Ina tayaku murnar komawa Addininmu Addinin gaskiya da gaskiya addinin Allah maɗaukakin sarki!. Ibrahim ya ce "Muna godiya sosai. "To kai ya sunan ka? Ya ce "Ibrahim Khalil. AJ yace "Masha Allah sunan kakan fiyeyyan halittu kenan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama! Dukkansu suka shafa harda Muhammad dake bayansu yana jinsu. "Fatima nakeson gani na kirata bata amsaba shine yasa nazo gidan ko lafiy"..."kafin ya rufe baki sai gata ta fito daga ɗakin riƙe da waya a hannu. A zuciyarsa ya ce "Kenan duk kiran da nake mata tana gani ɗaukane bazatayi ba! Kafin kowa yayi magana Muhammd ya ce "Fatima je ki karɓo masa Hajara ya ganta ko? Ya faɗa ne domin yasan abinda ya kawo AJ ɗin kenan wato ganin Hajara da kuma Fatima. Domin kuwa tun ranar da a ka tambayeta wanda takeso ta ji kunya shine Muhammd ya tambayi Ibrahim ko tanada wanda takeso . Shikuma ya kwashe komai ya sanar da Muhammd tsakanina AJ da fatima. Muhammad yayi mamaki sosai jin cewar a she dalilin zuwan AJ gurin su kenan a gidan Comanda Daniyel. "Ok Daddy. Fatima ta amsa tana shiga gurin Hajiya Babba domin ɗauko Hajara. Saida AJ ya sunkuya har ƙasa ya gaisa da Daddy yana mai jin kunyarsa a dun lokacin da suka haɗu. Yana mamakin irin halin sa domin kuwa shiɗin na dabanne Zaune ta sameshi ya ɗora hannayensa a kansa kamar dai kanne ke masa ciwo. Da sallama ta iso cikin palon har gurin da ya ke ta miƙe masa yarinyar tana jiran ya karɓeta ta bar gurin. Ganin bashi da niyar karɓa ne yasa ta ɗaga kai ta kalleshi sai idanunsu ya harɗe a na juna, ai da sauri ta kawar da kanta tana tsaye a gabansa. "Fatima" Ya kira sunanta da muryar da tasa tsikar jikin tashi, taji yanayin sunan kamar shi kaɗai ya iya kira. "Mai yasa bakya amsa kirana ko kin daina sonane? Ko kinaso zuciyata ta buga ne? Shiru tayi tana jin anya zata iya abunda tayi niya kuwa a kan AJ! Son da take masa a jinin jikinta yake, da shi kaɗai ta saba kuma ita son gaskiya take masa. "Kujerar dake kusa dasu ta ajiye Hajara zata fita sai ji tayi ya kamo hannunta ta baya. Chak ta tsaya ta juyo tana masa wani irin kallo, hakan yasa ya saketa batare da ya shiryaba. "Karka kuskura hannunka ya ƙara taɓani a karo na biyu, tana faɗa tabar palon da sauri tana tare kukan da ya zo mata. AJ ya tsaya a gurin yana dukan kansa yana tunanin kodai ramawa takeson yi! Haka ya ɗauki Hajara yana kallonta cikin so da soyayya har ya gama wasa da ita ya kira mai akin gidan ta karɓeta. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ya dinga furtawa har ya bargidan. Haka kullum AJ zai kirata amma bazata ɗaga ba, zai tura mata message zata karanta amma no amsa. Kullum kuma zaizo gidan domin ganinta amma abun ya fi ƙarfin sa, a gida kuwa kullum Safarau da Kadija sai sunyi rikici a kansa, Nana har ta fara gajiya da abun da sukeyi, hakanne yasa taje gidan kawu ta sanar masa shi kuma ya kira AJ yace "Idan yanada wacce yakeso ya fitar yayi aure idan kuma babu to ya shirya da ƴar uwarsa Safarau. AJ yace yanada wacce yakeso, Kawu ya ce "To gobe za'a zo maganar auran Nana sai kaima ka fitar a saka ranar gaba ɗaya. Hakane yasa AJ saida ya sa Salis a cikin lamarin domin baisan ya zaiyi Fatima ta dawo garesa. Salis ya bashi shawara wacce tasa ya yarda da ita ɗari bisa ɗari, kuma yaje yayi amfani da shawar kuma tayi masa aiki yanda yakeso. A washe gari Muhammad da Shek Kabir wanda yazo domin zuwa neman auran Salis ɗin da kuma a bokinsa Malam suka tafi gidan kawu. A ranar a kasa ranar auran Salis da Nana wata shida sai Abduljabaru da Fatima zara suna wata shida. Daga nan a ka wuce gidan su Hadiza, farko ma haifin Hadiza yaso yaƙi yarda jin cewar ɗan gidan Comanda Daniyel ne, domin bazai manta irin cin mutuncin da yakewa ɗansa ba, amma ganin shek Kabir awajan yasa ya amshi abun hannun bibbiyu. Suma dai wata shida a ka saka. A washe gari ne kuma Titi tazo da bayanin halinda su Comanda Daniyel da Eliza suke ci. Dama Muhammad ya naimi indan a ka kai shari'ar tasu amma an rufe duk wata hanya da zaka iya gane komai game da labarin, hakanne yasa ya haƙura domin dai yasan dole yayan nasa ya karɓi hukunci domin yaci amanar aikinsa, shi kuwa yafi duk wani guri domin ya sanar dasu cewar ya yafe masa amma ba ƙofa, sai kawai yaci gaba da masa addu'a. Bayan ta gama basu labarin komai ne sai kowa dake cikin palon ya fara kuka domin tausaya masu. Zara kuwa harda ihuu tana cewa ita sai taga Momy. Muhammad ya ce Yanzu suna inaa? Ta ce "Suna gidana nace suzo muje gidanka wai a'a bazasu iyaba yaransuma da kuma riƙe sun gode! HAJIYA BABBA ita kanta da take mugun jin haushi su saida ta zubar da ƙwalla, sanann tana sake godewa Allah da yasa ita Tata gaddara mai sauƙuce. Muhammad ya ce "No Titi zomuj"..."Na bar Titi na koma Halimatus Sadiya! Ta faɗa tana fashewa da kuka. Mijinama ya ƙarbi kallamar shahada bayan sanar masa da labarinmu, jin irin halin kirkin da kayi yasa shima yace zai koma addinin Musulunci, shima Usha ya koma ADDININMU. Tana kaiwa nan Muhammad ya rungumota yana kuka yana mata addu'a haɗi da saka mata albarka. Ya ce "Sadiya zomuje gidan naki? Ya faɗa yana ji kamar yau zai fara ganin ɗan uwan nasa. Hajiya da Zara da Ibrahim sukace zasu bisu, amma Muhammad ya ce "Dukkansu su zauna yanzu zasu dawo tare da su. Haka kuwa a kayi suka zauna cikin tunani har Sadiya da Muhammad suka fita.....📝 *Tofa! ko dai Comanda ya karɓi hukuncin sojojine, to Salis da Nana dai abu yazo, ina fan's ɗin AJ? Fatima tana gasa masa aya a hannu* 🥰 *Comments ɗinku shine ƙwarin guiwata* *S REZA ✍️* *ADM* *S REZA...✍️* *First Class writer's asso...* *PAGE4️⃣8️⃣* ........ Lokacin da suka isa gidan suka tarar da Usha da Mahaifinsa tsaye a harabar gidan cikin shigar wasu sabbin jallabiyoyi farare haɗe da hulunansu. Wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Muhammad ya sake miƙa gidiyarsa ga Allah buwayi gagara misali mai aiwatar da komai cikin hikimarsa. Yana isa gurin ya ce "Salamu'alaikum? Ya faɗa yana sakin fara'a da murmushi duk a lokaci ɗaya! "Wa'alaikum salam warahamatulla wabarakatuhu". Bayan sun gama gaisawane mahaifin Usha wanda ya samu sabon sunan Musulunci Abubakar Sadiq ya ce "Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda ya haɗamu da mutumin kirki irinka! Tabbas lokacin da Sadiya ta bani labarin ku da kuma abinda ya faru da kai sai naji gaba ɗaya halaiyarka sun bani sha'awa, shine ta ce min wai ai haka halaiyar duk wani musulmin kwarai take mutuƙar zaiyi koyi da ɗabi'un ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama. To ina jin haka sai na je gurin wani malami na masa bayani akan ina son shiga musulunci. Muhammad kam farinciki kamar yayi tsalle. Daga haka suka shiga cikin gidan yana son yin tozali da yayan nasa. Zaune yake ya miƙe ƙafafunsa daga shi sai gajeran wando da senglet fara kansa babu hula ya kafe guri ɗaya da kallo kamar mai tuto wasu abubuwan. Da sauri Muhammd ya ƙarasa kusa dashi yana kiran sunan sa. "Yaya Daniel? Yaya! Yaya!!! Ganin ya kasa juyawa ya kallesane yasa Abukar cewa "Bazai iya maganaba muma munyi dashi amma daga kallon guri ɗaya sai zubar da hawaye. A lokacin ne Muhammad ya kai kallonsa ga ƙafafunsa sai yaga ɗaya ta kumfura sosai ɗayar kuma ta shanye, ya kalli hannayansa suma haka suke, ga kansa da yayi ƙato wuya kuma ya sirance. Cikin damuwa Muhammd ya ce "Mai ya faru dashi haka? Ban gane ba ina Eliza? Yana rufe baki sai gata tafito riƙe da cufi a hannu tana juya abunda ke cikin kofin da cokali. Da sauri ya karaso gurin da take ya ce "Mai ya faru da yayanna? Eliza ta fashe da kuka itama kanta a birkice take, kamar ba itace wannan ma'abociyar kwalliyarnanba. Cikin kuka ta ce "Mutanan Ƙauyan ku ne( wato mutanan KATUNGU) Sune sukazo har gida suka ɗauki wandonsa guda ɗaya, suka ciri gashin kansa shima ziri ɗaya, to tun daga ranar ya fara rashin lafiya duk inda zamuje sai a ce bazza a iya karya a sirin ba, wai a she ƴan uwanan wannan mutanan da ya rufeku tarene suka masa a siri. Muhammad ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!. "Faɗamin abunda ya faru tun rabuwarku da mu? Elixa ta fara cewa "Ya kai wata uku a ƙulle batare da kowa yabi ta kansa ba, bayan zuwan Captain ɗinsu sai ya naimi zama dashi, bayan an karanto laifukansa wanda ya yi a lokacin da ya samu ƙarin girma. Hatta ƙananan sujojin da suke ƙarƙashin sa suma kuka sukeyi dashi. Sannan bayan ku da ya ƙulle a she ya sa an kashe wasu da yawa musulmai sojoji idan an kawosu aiki ƙarƙashin sa, babban amininsa wanda suke aikata aikin tare shine ya sanar da cewar ya kashe a ƙalla sojoji kusan takwas ba tare da laifin komai ba kawai dan sun kasance Musulmai. Da farko ya fara yin musu amma ganin hujjojin da aminin nasa ya kawone yasa ya yarda. Ana cikin wannan sai a ka sake sakowa batun ku a kan ya kulkeku har sama da shekaru a shirin,kuma daga ƙarshe ya rufeku a ciki ya saka muku wuta. To bayan tabbatar da laifinne kuma a take a ka cere musu kayan jikinsu a ka fara hukuntasu da hukunci irin nasu na sojoji. Bayan kwana bakwai a ka fara bin komai da ya mallaka na gidan soja a ka kwace, sannan gidan da yasakawa wuta shima a kace sai an biya domin ba nasa bane. Sannan bayan an gama biya kuma za'a harbesu a cikin barikin sojojin dake cikin gari. Wannan shine hukuncin da za'a masa. Bayan haka suka bamu wata biyu a kan mu biya tarar da a ka cimu, kuma kuɗaɗene masu yawa wanda gaba ɗaya nidashi bamuda koda rabunsu. Daga nan muka wuce gidan Abbana tare da sojoji guda biyu wanda duk inda zamuje suna tare damu har wata ukunnan su cika. A nan muka tattara komai da mukamsllaka amma ko rabin abunda a keso bai kaiba. Mun shiga tashin hankali sosai , muka naimi auro a gurin babanna amma yace baida shi, daga ƙarshe ya ce ko dai Daniyel ya bar masa gida kokuma mu tafi tare. A haka muka cinye wata guda babu komai sai wahala. Cikin rashin tunaninmu da kuma naiman mufita sai muka tafi garin Katungu domin sayar da gidanku dake can. Alokacin da mukajene a she dama suma naimansa sukaye, a ranar da mukaje bamu kai ga hutawaba suka cika gidan suna zage-zage da cewa sai sun ɗau fansa. Babu wanda ya hanasu suka ciri gashin kansa da wandon jikinsa sukace sai yaga abunda zai sameshi. Ganin haka yasa muka baro garin cikin jigatuwa da azabar tafiya. kuma abunda zai baka mamaki komai dake faruwa a gaban waɗannan sijojinne, amma babu ruwansu. Daga nan mukaje gidan wata aminiyata, itama kwana ɗaya ta koremu, to a lokacin ne kuma muka rasa ina zamu dosa. Sai yace muje gidan Titi amma nace a'a kar muje. Dele muka koma gidan babana wanda da gyar ya amshemu a karo na biyu. A nan gidan muka cika wata biyu da kwana tara. A wannan lokacin ne kuma ciwonsa ya zama abun mamaki, domin Bama iya barci kullum abun sai ƙaruwa yakeyi. Hakanne yasa babana ya koremu. A nanne yake tambayata Sarah da Samuel nace suna gidanka. A ta ƙaice dai su kansu sojojin da sukaga halinda yakeciki sukace har sai ya warke kafin ya karɓi hukunci kuma ko sisi basu taimaka mana dashiba. Hakanne yasa mukazo gidan Titi. Elixa ta ƙara sa tana fashewa da wani irin kuka. Kowa ya tausaya masa, Muhammad kam kuka yakeyi yana so ya kamo ɗan uwan nasa amma yana tsoran karya taɓo ciwon nasa ya famashi. Muhammad ya ce asbiti za'a kaishi yanzunnan" Elixa ta ce "Ba ciwon asbiti bane dmon munje sunce basu san me ke damunsa ba. Muhammad ya ce "Zamu tafi dashi gida idan yaso zan kira Usman na tambayeshe waye yayi wannan a sirin, yanzuma dan banzo da wayana bane. Haka dai Muhammd da Sadiq da Usha wanda ya koma Auwal suka fara ƙoƙarin ɗaukar Daniyel amma sai sukaji kamar dutse suka ɗauka, haka sukayi iya yinsu amma sun kasa ɗagoshi daga gasa. Shi kuwa baya iya magana sai hawaye da ke wanke masa idanu alamun dai yana jin jiki. Haka dole Muhammd ya koma gida domin kuwa yau zaije KATUNGU. Koda yaje gida ya tararr har lokaci Zara tana kuka. Ya kwantar musu da hankali batare da ya sanar dasu komaiba. A ranar ya tafi Katungu shida Salis koda yaje garin ya tambayi Umar da Usman zancen waye yayi wannan asirin sai suka sanar masa da cewar ai rabansu da cikin garin Katungu har sun manta domin dukkansu jiya suka iso garin daga cikin Benue sun haɗa ƙafa sun gina babban shago. Su kansu sun shiga tashin hankali da mamaki jin abunda ya faru, domin su tun wa'azin da Muhammd ya musu a kan yafiya sukace sun yafe masa. Nan fa gaba ɗaya su ukun suka shiga tambayar a salin abunda yafaru da kuma waye yayi a sirin amma duk garin kowa yace bai saniba, tamkar dai abun haɗin baki. Haka dai har dare babu wanda yace komai daga musulman harma wanda basu karɓi Musuluncin ba. Haka suka dawo gida batare da sanin abunyiba. Acikin gari kuwa Salis da Muhammd suna fita Zara da Ibrahim suka shiga ɗaya daga cikin motocin gidan suka nufi gidan Sadiya, lokacin Hajiya Babba tana ciki tana fama da rikicin Hajara. Lokacin da suka ga halin da mahaifin nasu ke ciki sai kowa daga cikinsu ya fara kuka, Elixa ta haɗasu gaba ɗaya ta rungume tana kuka. Shiko Commda sai kallon guri guda yakeyi amma yana jin duk abunda suke cewa. Suna gidan har su Muhammd suka dawo, shima yasan dole zasu zo sai yasa bai ce komai ba. Lokacin Sallha nayi ya umarcesu da sutashi suje suyi. Haka Elixa taji abun wani babbaraƙwai babu daɗin ji wai "Ibrahim ku tashi kuje kuyi Sallah. Kasan cewar da English yayi maganar sai ta hau mamaki ganin duk sun tashi. Bata iya cewa komai ba, domin kuwa sai taga gaba ɗaya ma halaiyarsu ta canza ba kamar daba. A gidan Zara da Ibarahim suka kwana suna taya mahaifiyar tasu jinya. Wasa-wasa abu ya rincaɓe, domin kuwa kullum ciwon nasa ƙaruwa yakeyi ga kuma har yanzu babu labarin wanda yayi a sirin, sannan duk lokacin da zasuyi yunƙurin ɗagashi bazasu iyaba. Haka dai yaci gaba da zama a gidan Sadiya sai dai Ibrahim da Zara suzo duba shi. Shima AJ da Nana sunzo sau ɗaya, hakama mutanan Kano duk sunzo, sannan Muhammad yasa a na masa sauƙar alqur'ani. Wannan kenan! *BAYAN WATA HUƊU* kwana huɗu ya rage bikin Zainab da Abdalha da kuma Maryam da Isa, sai kuma Aliyu da wata daga cikin danginsu da yasamo kamar yanda malam Adamu ya ce masa, ai kuwa shine ya masa komai na sadaki. Mutanan Benue Makurdi ne a kan hanyarsu ta zuwa bikin. Jirgi suka hau dukkansu, Muhammd da matarsa Hajiya Babba domin kuwa tun tana kammala arba'in a ka ɗaura musu wani auran, sai Salis da Ibrahim da Laɗifa da Fatima zara da shi kansa AJ ɗin. A cikin wannan wata huɗun ya kama business sosai kuma Allah ya saka masa albarka, Hajara da Nana kuwa sunsan cewar AJ yana ji dasu , ita kuwa Zara har yanzu taƙi sakar masa fuska domin har yanzu basu zauna sunyi doguwar maganaba. Ita kuwa Laɗifa yanzu ba ruwanta da kowa a gidan daga ɗaki sai kuka sai gobe ciwo jibi lafiya. Kullum Hajara tana gurin zara domin wani irin so da takewa yarinyar, kodan jinin AJ ce, ko kuma dan ta na kama da shine. Sosai sukayi murnar ganinsu, angwaye da amarema sai murna sukeyi domin kuwa dama su a je jira a matsayin abokan angwaye da ƙwayan amare. Ɓangaren Nana kuwa jin Abdalh zayi aure yasa ta sami Maryam ta faɗa mata gaskiyar abun da yafaru lokacin da Abdalha yazo gidansu, cewar mamartace ta zugata a kan taci masa mutunci, amma yanzu dan Allah ta bashi haƙuri ya dawo tana sonsa. Maryam ta mata wani irin kallon alamar baki da hankali. Haka Nana taje gida ta fara ma mahaifiyarta rashin kunya, mahaifinta kuwa yaje har gida ya ba Shek Kabir kabuga haƙuri . Ranar juma'a a ka ɗaura auran Abdalha Shek Kabir kabuga da a maryarsa ZAINAB Adamu Ambato. Da kuma Isa Adamu da Maryam Shek Kabir kabuga a kan sadaki Naira dubu ɗari-ɗari. Masha Allah! Alhamdulillh! Haƙiƙa wannnan auran da a kayi ya ƙara haɗe kan al'ummar Musulmai da dama, domin kuwa dama sune jagororin al'umma kuma sun haɗe kansu. Al'umma takotaina sai kiran sunan ango da amarya akeyi. A ranar da yamma a ka gabatar da wa'azi sosai game da haɗin kan al'ummar musulmai. A washe gari suma abokan ango su Salis da Ibrahim da AJ suka haɗa ƴar walima ta angwaye da amare. Sosai aka ci a kasha a kayi ƙasidu da wa'azi masu Ratsa zucoyoyin al'umma. A ranar a ka raka kowa gurin amaryarsa bayan nasihoyi da iyayen nasu suka musu. Da sallama Abdalha ya shigo cikin ɗakin nata yana kallonta ita kaɗai a tsakiyar kado kanta rufe da farin mayafi, tsayawa yayi yana kallonta yana sakin murmushi yana jin cewar yau Allah ya cika masa burinsa bayan doguwar kwa-kwar mayar da a kasha. Abdalha kenan tun daga ƙofar gida ya sallami a bokan nasa a kan cewar yanzu tazama tashi shi kaɗai babu wanda zai kallar masa ita, murmushi ya keyi yana tuno irin tsiyar da suke masa. Bayan sun gabatar da Sallah raka'a biyu kaman yanda shari'a ta zarta, sai kuma kowa yayi shiru yana tunanin abunyi. Haka ya kamo kanta ya fara jero addu'o'in neman zam lafiya a tsakaninsu, ya ɗau lokaci yanayi tana sauraronsa tana jin yanda Muryar tasa take tasiri a zuciyarta. Bayan ya kammala itama ta riƙo kansa ta fara tata addu'ar, sosai itama tayi, kafin Abdalha ya ce "To yanzu Malama nine zan miki tambayoyinne kodai kece zakimin domin naga fa kamar sai kin sake koyar dani. Murmushi tayi ta sunkuyar da kai domin kuwa yau kunyarsa ta keji sosai. A cikin wannan daran Abdalha ya angonce da amaryar sa. Washe gari Su Muhammd suka tattara nasu ya nasu suka koma batare da sunyi sallama da angwaye ba. Sosai Abdalh da Zainab suke zaman lafiya da gyrmama juna da kuma baiwa kowa damar yin zaɓinsa. Sannan Zainab ta ajiye yin ƙasidu, amma tana rubutawa ta bayar a je a rera, kamar yanda Abdalha ya ce idan zata fita koda ina zataje to sai tasa liƙaf, itama hakan ya mata sosai. Soyyaya sukeyi mai tsafta wacce kowasu ma'aurata suke burin yin irinta. Wannan kenan! *BENUE MKD* Sosai Muhammd da iyalan gidan sa suke shirin auran yaransu da ke gabatosu. Umar ne tsaye a gaban Salis da Ibarahim yana sanar dasu cewar yana son Laɗifa amma yana ganin kamar tafi ƙarfin sa, shiyasa yakeso su taimaka su sanar mata. Salis yayi dariya ya ce "Yanzu tsabar rashin kunya ina matsayin sirikinka amma nine zanje naima maka izini ko?. Haka dai suka ce kawai ya cire tsiro ai mace bata fin ƙarfin Namiji. Haka ya shiyar ya nufin gidan domin sanar mata da sirrin zuciyarsa. Wanka yaci sosai cikin manyan kaya ya shiga gidan ya zauna a harabar gidan ba tare da sanin su Salis ba ya tura mai gadi ya kira masa ita. Yana zaune a gurin ya hangota ta nufo gurin idanunta karr a kan ganin ki waye yazo har gida nemanta. Lokaci ɗaya Umar yaji tsoron ya dawo, cikinsa ya ɗuri ruwa sai yakejin kamar ya ruga a guje, lokaci ɗaya cikin sa ya bada guuuuu! Daidai lokacin da ta ƙaraso gurin ....📝 *Congratulations Zainab And Abdalha* *To fa! Umar ko da rabon shan mari😂* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *S REZA ✍️* *ADM* *S REZA ✍️* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE4️⃣9️⃣* ........Tana zuwa Umar ya miƙe tsaye gaban sa na cigaba da faɗuwa. "Umar kaine kake kirana? Tayi tambayar da ɗan mamaki. "Am am umm dama dama na zone a kan. Umar ya kasa magana tsabar cika masa ido da Laɗifa tayi.Ita a tunaninta yazo a kan maganar abokinsa ne, hakan ya sa ta kalleshi cikin wata raunanniyar murya ta ce "Umar kafi kowa sanin irin sonda nakewa Ibrahim domin da kai a ka dinga shiga da fita har na samu na kuɓutar dashi daga shirrin Mahaifinsa, amm ya rasa da abbun da zai sakamin sai auran wata shigiya yar matsiyata, har yana iya ksllon idona yace ita yakeso. Tana maganar tana kuka hawaye na wanke mata fuska. Umar ya sauke a jiyar zuciya jin irin zagin da takewa ƙanwarsa, sannan kuma shi ba wannan zancen ne ya kawoshiba a zuciyarsa ya ke cewa wato batama san cewar Hadiza ce yarinyar da Ibrahim ɗin yakesoba, a fili kuma sai yaji tausayinta ganin tana kuka. "Ki yi haƙuri Laɗifa matar mutum ƙabarinsa in sha Allah kema Allah zai kawo miki miji daidai da ke kawai ki share ki kalli gabanki. "Da sauri ta kalleshi ta ce "Anya kasan so kuwa? Kasan yaya mutum keji idan wanda yakeso ya ce baya sonsa ko kuma wanda keso baisan yanayi ba? A cikin zuciyarsa ya ce "Ai kuwa nine nasan haka.Laɗifa taci gaba da cewa "Ina jira ya auro koma wacece dan uwarrata da kanta zata gudu gidan iyayenta. Duk yanda Umar ya kai ga son sanar da ita sai ya kasa cewa komai sai ma haƙuri da yake bata, a haka ya bar gidan cike da jin haushin kansa. Bayan ya fita daga gidan ya fara dukan kasan yana kiran kansa da lusari mara wayo mai tsoron Mata. Ita kuwa Laɗifa gaba ɗaya ma haushin kowa ta ke ji a gidan, barinma Hajiya Babba da ƴarta Hajara. Tunda a ka haifi yarinyar bata taɓa mata wasaba bare a je ga ɗaukarta, kowa na gidan yasan da haka amma Daddy Muhammd ya ce a rabu da ita domin kuwa yana tausaya mata. Shi kansa Daddy ɗin yaso ya haɗa auran Salis da Zara ne da kuma Ibrahim ɗin da Laɗifa, amma abun ya zama ba hakaba shine yasa yake tausayin ƴar tasa. ( Wannan kenann!) Ɓangaren su Daniyel kuwa ƙafa sai ci gaba takeyi da kumbura daga ƙarshe ma sai yan keta a kayi. Mahaifin Momy Elixa kuwa da kansa yazo ya tafi da ƴarsa a kan zaman su ya ƙare. Haka badan tasoba ta tafi tabar mijin nata dake cikin mawuyacin ciwo. Saidai kuma tana zuwa gidan uban nata taji bazata iya zamaba saboda takura da matar ubanta da dangi suke mata, kasancewar anji labarin yaranta sun koma yin Sallah. Kasancewar mahaifinta babban Pastor ne sai yace dole taje ta dawo da yaran dangin su, ita kuwa ganin yanzu yaranta sun koma rayuwar farinciki da kwanciyar hankali ga annuri dake tashi a fuskokinsu ne yasa ta ce sam bata san da wannan zancen ba. Hakanne ya jawo mata suka a gurin ubanta da matar ubanta domin suna jin cewar itace tasa suka bar addidinsu. Lokacin da Ibrahim yazo gida Sadiya ta sanar masa da cewar mahaifinta yazo ya tafi da ita. Ai kuwa har gidan yaje ya dawo da ita sannan ya musu gargaɗi da cewar su fita a harkarsu. Alokacin da pastor yaga Ibrahim saida gabansa ya faɗi ganin yanda ya cika masa fuska, lokaci ɗaya yaron ya masa wani baƙe-baƙe sai kace ba Samuel ɗinsaba.hakanne yasa ya kasa cewa komai har ya bar gidan. Muhammad ya kira Salis da Ibrahim ya zaunar dasu a kan batun aiki. Ya sanar musu da cewar kafin a ɗaura auransu ya kamata a ce dukkansu sun fara aiki. Ibrahim ya shida masa cewar ai shi takardunsa sun ƙone a wancen gidan nasu. Shi kuma Salis ya ce "Dama shi yana ɗan zuwa saidai ba sosai ba. Muhammad ya sanar masa da cewar kar yaji komai za'a samar masa wata takardae. Ibarahim ya ce "No Daddy takardun sunanan domin gaba ɗaya mommy ta kwashesu lokacin da zamu bar gidan. Cikin ikon Allah kuwa yaje ya tambayi Momy ta kwaso masa harda nata da na Daniyel, Zara kuwa dama ita bata kammala Secondry school ɗinta ba. Take Daddy ya ce da Salis a je campaign su na Abuja a ma Ibrahim intabiyu idan yaci a bashi opiece. Ai kuwa takardunsa sunyi kyu domin kuwa yanada ƙoƙari. Haka a ka masa intabiyu kamar yanda a kewa kowa kuma yaci. Daddy ya mallaka masa gida a habujan domin a can zai zauna da matarsa, sannan Daddy ya ƙara siyan wani gidan ya ce na su Daniyel ne, idan ya warke zasu koma can. Ibrahim ya share hawaye ya ce "Ka manta da cewar a kwai hukuncin kisa a kansa koda ya warke? Kawai kabar siyan gidan Momy kuma zamu zauna tare a gidana, yanzu babban burina shine ace Daddy ya karɓi kalmar shahada kafin su kasheshi. Daddy da Salis suka amsa da amin in sha Allah zai karɓba. *BAYAN WATA BIYU* Zaune yake kamar yanda ya saba a koda yaushe ya ƙurawa waje ɗaya ido yana sauraron maganar da matarsa take masa a kan cewar gobe ne auran Samuel da Sarah dukda kuwa yasan da zancen. Tana maganar ne badan tasan zai amsa mata ba amman dai tasan yana jinta. Da mamaki taga ya gyaɗa mata kai yana son yin maga amma ya kasa. Tana cikin haka Salis da Zara da Ibrahim da Laɗifa da Muhammd da Hajiya Babba riƙe da Hajara da ta fara wayo suka shigo ɗakin suka zauna suna kallonsa. Burinsu shine Daniyel ya furta kalamar shahada kafin ranar Lahadi, domin kuwa sojojine sukazo har gida a kan cewar ko ya warke ko bai warkeba ranar za'a yanke masa hukumcin. Zancen ya bazu a ko'ina har gida rainiyo da jaridu, domin kuwa babu wanda baisan Commanda Daniyel ba a lokacin sa. Babu yanda basuyi dashiba amma ya kasa magana sai kallonsu ya keyi, yau sama da kwana goma kenan suna so ya furta koda kalmar shahada ce amma ya kasa cewa kimai. Ibrahim yaje ya ɗauko takarda da biro wai ya rubuta kalmar shahadar amma ya kasa ɗaga hannayansa ma bare a je ga rubutun. Zara da Momy sai kuka sukeyi. Zara ta kalli mommy ta ce "Pls Momy kema ki dawo Addininmu addinda shine na gaskiya Please! Momy ta gir-giza kai alamar bazata iyaba babanta zai kasheta. Babu yanda busuyi da itaba amma ina Eliza ta ce "bazata iya barin addininsu ba. Haka dai suka bar gidan cikin tausayin halinda suke ciki. Washe gari da safe a ka ɗaura auran Salis da Nana sai Ibrahim da Hadiza sai Abduljabaru da Fatima Zara. Ɗaurin auran ya samu halarta mutane sosai, duk wani maaikacin dake aiki a ƙarƙashin su Salis to saida ya halarci taron, haka shima AJ mai mutane kala-kala. Shima Ibrahim haka ta ɓangaren abokansa musulmai dama wanda basuba sun halarta. Amarya Hadiza tasha kwalliya kamar ba itace wannan ballagazar ba, ta natsu tayi kyu cikin kayanta na amare. Gefe guda kuma ga angonta fuskarsa cike da annuri da kuma damuwa duk a tare da fuskar tasa. Kasancewar ranar juma'a a ka ɗaura auran kuma ranar Lahadi ne Daniyel zai karɓi hukunci irin na sojoji, hakanne yasa a kace sai ranar juma'a ta sama kowace amarya zata tare a gidanta, Auran dai kawai a ka ɗaura. Ɓangaren Laɗifa kuwa sai a ranar tayi ido huɗu da Hadiza ai kuwa kallo ɗaya ta mata ta ganeta, cikin wani tsananin mamaki take Binta da kallo domin ko shekka babu itace wannan mara kunyar yarinyar kuma ballagaza. Ita kuwa Hadiza tana haɗa ido da ita ta ga kamar ta ganeta, domin kuwa ita har ga Allah ta manta da ita, domin kuwa ita batasan adadin mutanen da tayi faɗa ko zage-zage dasuba. Hakanne yasa laɗifa shiga wani hali tana neman Umar akan mai yasa bai sanar mata da cewar ƙanwarsa ce yarinyar da Ibrahim zai auraba har saida a ka ɗaura auran ta sani. Abunka da wanda bai san komaiba sai yaudaran ƴan mata da ya sabayi a baya, bai duba irin halin da take ciki ba a wannan lokacin kawai ya furta mata kalmar da tun safiyar yau yake ta bitarta kafin ya fito daga gida, ya aiyanawa kansa cewar ko kasheshi zatayi saidai tayi amma sai ya sanar da ita. "Tasss" Kakeji ta ɗauke shi da wani gigicacan mari tana nunashi da hannu cikin huci da ɓacinrai..."Baka da hakalune harni zaka kalla kace kana sona saboda na sakar maka fuska ko? To Wallhi idan na sake ganin ka a gidannan saina sa an ɓatar da kai wawa ɗan matsiyata. Tana kaiwa nan ta koma ciki ta barshi a gurin riƙe da kunci yana kallonta har ta shige gida. Murmushi yayi ya ce "Zan iya jure komai a kanki domin kuwa ina sonki!. Ɓangaren Salis kuwa a daran ranar da a ka ɗaura auranne ya saci jiki ya nufi gidan su Nana ganin AJ baya gidan yana tare da su Abdalh da sauran abokansu. Gidan ba mai gadi sai ya sauƙo ya buɗe get da kansa ya shiga gidan, guri ya samu yayi paking sannan ya nufi ciki harda haɗawa da gudu, kasancewar ba'a gidan a ke bikin ba sai bai ga mutaneba sai kawai ya nufi palon domin kuwa ba baƙonsa bane gidan. Yana tura ƙofar palon zai shi sai kuwa yaji sauƙar flet a kan hancinsa, kafin ya ankara saiga gorarr ruwa ceke da ruwa shima a kan goshinsa. Ai da sauri ya saki ƙofar ya koma da baya yana riƙe hancinsa. Safara'u da Kadija kuwa da suke faɗa basuma san da shigowar Salis ɗin ba, ita kuwa Nana a kan idonta abun ya faru, domin lokacin da Safara'u ta jefo plet ɗin Kadija kuma ta sun kuya sai tabi flet ɗin da kallo. Da sauri tabi bayan Salis ɗin. Ai kuwa ta sameshi a bayan ƙofar har hancin yayi ja, ga kuma jini yana zuba. Abun sai yayi kamar abin dariya, amma sai ta dake tana masa sannu. Da gyar ya ce "Kuna kiwon mahauka a gidanku ne dama shine baki sanar min ba? Wannan karan kam sakin dariyar tayi tana ce wa "A'a ba mahaumkata bane. Cikin zafin ciwo ya kalleta ya ce "Au ke abunma dariya ya baki ko? Ta ƙunshe dariyar ta ce "A'a to ma wai kai me ya kawo ka gidan nan a wannan lokacin? Tana maganar tana ɗauko gorarr ruwan tana zuba masa a fuskarsa yana wanke jininn. Sai da suka gama wankewa ya bata amsa da cewar "Rabon hancina ya fashene ya kawoni. Ya faɗa yana matsowa kusa da ita riƙe da hancin da yayi jaaa. Ta ce "Please za"...."Shiiiiiiii. ya katse ta yana ɗoro hannusa a kan bakinta. Ganin yanda ya matso dafda itane yasa jikinta fara rawa tana neman hanyar arcewa. Salis ya matso da bakinsa kusa da nata saura kaɗan ya haɗe sai sukaji an daki ƙofar da sauri wanda yasa duk saida suka tsorata. Da ƙarfi ta tureshi ta buɗe palon ta shiga a kunyace. Lokacin kuwa Kadija da Safarau sun bawa hammata iska sosai, domin kuwa mai rabun batanan. Da mamaki Salis yake kallonsu ganin yanda suka lalata tufafin jikinsu, wata har jinine a bakinta wata kuma a hancinta. Ga kuma palon shima an faffasa abubuwa. Gaba ɗaya kallonsa sukeyi domin kuwa babu wacce bata sanshiba. Ya tambayi ba'asin abinda ke faruwa. Suna cikin tsara masa saiga AJ ya shigo gidan. Cikin ɓacin rai ya ce dukkansu su tattara a darannan subar masa gida. Nana ta ce "No yaya zunzo taya amarya kwana nef"..."Amaryar banza! Ya faɗa ransa a ɓace. Ai kafin kace cass har sun bar palon suna hararar juna. Saida ya rakasu har waje kafin ya rufe gidan ya dawo, yana jin yanda Safara'u ke cewa zata ɗauko kayanta amma bai ko bi ta kantaba. Yana shiga palon idonsa ya sauƙa a kan hancin Salis. Dariya AJ yayi wacce rabonda yayi dariya a gaban Salis har ya manta domin kuwa har yanzu kunyarsa ya keji. "To oga zamu rufe gida? Salis ya ce "Nima a nan zan kwana" Nana ta waro ido waje ta ce "No a'a wallhi ba ruwana. AJ ya ce "To kawai ka ɗauki amaryar mana katafi da ita ba sai kamin tashin kunya ba. Salis ya ce "Tom nidai koma me zakuce Allah bazan tafi da fashenshen hanci ba. Ƙarshe delo a gidan ya kwana...📝 ( *Muhaɗu a gurin harbe Daniyel)* *Comments ɗinku shine abun alfaharina* *S REZA ✍️* *ADDININMU* *S REZA ✍️* *Watpad* Salis m Reza. *Feecbook* Salis m Reza *Arewabooks* Salis m Reza *Gimal* salisuadam115@gmail.com *Whasoop numbar* 08100785178 *Instagram* *Salis m Reza. *A ko'ina inada gurin zanta wa da kowa idan da buƙatar hakan🥰🥰* *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *PAGE5️⃣0️⃣END* babu editing sai hakuru ........*RANAR LAHADI.* Kamar yanda suka faɗa cewar ranar Lahadi ko bai warkeba to zai ƙarɓi hukunci irin nasu na Sojoji daidai da abunda ya aikata. Saidai kuma wani abun da ya baiwa kowa mamaki shine... a washe garin ranar lahaɗi sai kowa yazo ya ga Daniyel lafiya lau babu wannan ciwukan na jikinsa, kansa ya dawo daidai haka hannayensa da ƙafafunsa. Shi kansa mamaki yakeyi domin shima haka ya tashi yaga kansa. Ya buɗe baki zaiyi magaba nannma yaji muryarsa ta fita kamar da lafiya lau, ai kuwa ya fara ihun kiran sunan matar tasa Elixa!. Cikin tsananin farincin Eliza ta kira Muhammd da sauran yaran ta sanar musu cewar Daniyel ya warke. Kowa ka gani bakinsa a washe domin kuwa abun ya basu mamaki. Ana cikin hakane saiga Umar da Usman sunzo gidan tare da matayensu domin Muhammad ya sanar dasu su cewar ranar Lahadi suzo gidan. A nanne Umar da Usman suke sanar dasu cewar wai ai jiya wanda yayi tsfin ya war-ware komai kuma ya kirasu ya sanar masu. Da mamaki Muhammd ya tambaye su waye? Suka kalli juna cikin rashin son faɗan sunan wanda yayi ɗin. Kafin suyi magana Daniyel ya ce "Basai kun faɗa ba ni nasan waye. Muhammad da Sadiya (Titi) da Elixa sukace waye? Daniyel ya ce "Sarkin garin ne, domin kuwa ya sanar dani cewar zanga abinda zai sameni domin kuwa na cimasa mutunci saisai. Muhammad da sauran suka cika da mamaki domin kuwa harda Sarkin a ke neman wanda sukayi a sarin a she shine da kansa yayi. Umar da Usman suka sanar musu da cewar wai sarkin ya ce saboda kaine ma yasa ya karya asirin badan ba da saidai ta ƙare a haka. Jin haka yasa Muhamd sauke a jiyar zuciya yana tausayin yayan nasa. Suna cikin haka ne saƙon Sojojin yazo musu cewar an bashi a'wa huɗu ya gama komai domin idan sukazo tofa komai nasa ya ƙare babu wani ɓata lokaci da zasu jira. Acikin wannan a'wa huɗun sun cinye a'wa guda da koke-koke. Muhammad ya naimi ɗan uwan nasa da ya karɓi kalmar shahada kafin lokaci yayi. Daniyel ya ce "Solomon yanzu babu wani abu da ragemin aduniya kaga koda na koma addininku ai babu wani amfani kawai yanzu ka yafemin duk abunda na maka kaida Titi harda matarka". Muhammad ya ce "Na yafe maka duniya da lahira n Muma Allah ya yafemana kuma kaima ka yafemin, sannan shi Allah mai karɓar addu'o'in bayinsane a koda yaushe, saboda haka dan Allah zan baka kalmar shahada kafurtata kuma kasa a ranka cewar kayi hakanne har cikin ranka. "Nayi Laifuka da dama wanda ko a Addinimu ni ba mutumin kirki bane, saboda hk bazan koma addininkuba, addininda na tarbatar shine addinin Allah, kuma shine addinin gaskiya, kuma addinin mutanan kirki ba irinaba. Anan Daniyel ya fara faɗo irin abubunda ya aikata a rayuwarsa game da Musulmai. A nanne ya ke sanar musu cewar musulmai ne suka kashe mahaifinsu a gabansa hakanne yasa ya ɗau alwashin babu shi ba duk wani mudulmi, daga baya ya gano a she musulmain irin marasa addininnane masu fashi da makami, amma dukda na gano gaskiya naji zuciyata taƙi yarda da musulmai, hakan yasa nake amfani da muƙamina na babban Soja ina kashesu ta yanda babu wanda zai zargeni, to yanzu a hakan ne Allah zai yafemin? Ya ƙara sa yana kuka yana kallon kowa dake ɗakin yana jin abunda yake cewa. "Eh Allah shene kaɗai wanda yakeso idan kayi laifi ka koma gareshi ka tubu, to hakan nasa Ubangiji yaji cewar lallai wannan bawan nasa ya yarda da cewar shine kaiɗai mai yafiya kuma mai jin ƙai. Allah zai yafe masa ya kuma karɓeshi hannu bibbiyu kuma Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yayi alfahari da shi. Muhammad ya shiga masa bayani yanda zai gane cewar babu irin laifin da bawa zaiwa Ubangiji ya kasa yafe masa saidai laifi tsakanin bawa da bawa ko kuma shirka. Itama shirkar malamai sunyi bayani a kan cewar Allah na yafewa mutuƙar mutum ya tuba ya dawo gareshi. Jin haka yasa Daniyel cewa "Na yarda zan koma na yarda na yarda. Kowa dake ɗakin ya ɗau hamdala suna murmushi. Saida Daniyel yaje Muhammd ya koya masa yanda a ke alaula da wanka irin na Musulunci kafin a ka bashi sabuwar jallabiya fara da hularta aka fara bashi kalmar shahada. Itama Momy Elixa ta ce zata koma. Haka cikin aminci Allah da yardar sa da kuma amincewarsa Daniyel da Eliza suka dawo addininsa addininmu Addinin gaskiya. Anan cikin palon Daniyel ya ce "Nima sunan Muhammadu na keso a bani. Ai kuwa Muhammad ya ce "to daga yau ka koma Ahamad, ko da bayan ranka haka zamu dinga kiranka. Haka kuwa a kayi kowa ya kirasa da sunnansa na Ahamad, kuma ya amsa. Ibrahim ya fita ya samo mai hoto ya ɗaukeso dukkansu, sannan ya dinga ɗaukarsu ɗaya bayan ɗaya. A nanne Ahamad ya sanar da Muhammd cewar a kwai ku ɗaɗe masu yawa a account ɗinsa , sannan ya sanar da shi cewar Zara da Ibrahim suma kowannansu ya buɗe masu nasu account ɗin kuma yana sa kuɗi a ciki, sannan ya bashi wasu ta kardu na filayensa da kuma shaidar tabbatar komai ɗin nasane. Muhammad ya ce "Dama Kanada wannan amma kuma ka tsaya neman gurin zuwa kaida matarka? "Idan na nuna cewar nawane to sai sojoji sun kwace domin kuwa haka dokar take. Muhammad yayi kuka sosai yana jin inama da abun da za'ayi a fasa harbe ɗan uwan nasa. A wannan lokacin ne kuma motar Amoka ta sojoji tazo unguwar tare da motocin manyan Sojojin ƙasar ta Nigeria. Haka dai su tattara shi suka tafi dashi, sannan suka naimi mutum ɗaya wanda zaibisu. Muhammad ya bisu har filin gurin da za'a harbesu ɗin. Mutane huɗe ne a gurin an rufe kansu da baƙin ƙyelle sannan an ɗaure hannayensu ta bata. Gurin filine mai girman gaske wanda ba'a iya hango ƙarshensa, saida a ka yi wasu yan zantuka a ka haɗa connecting kafin a ka sakesu suka fara gudu, sannan a ka baiwa sojojin damar harbi. Ahmad yana kudu yana maimaita kalmar shahada da Muhammad ya sanar dashi har lokacin da yaji shigar bulet a jikinsa. Kuka sosai Muhammd keyi lokacin da yaga ɗan uwansa a kwance ba numfashi, nan take ya fara roƙa masa Allah. Haka ya ɗauko gawarsa izuwa gida a ka sallaceshi. Lokacin da Shek Kabir kabuga da Malam Adamu sukaji labarin abun sunyi masa addu'ar samun tsira daga mahaliccin mu, sannan suka jinjinawa Muhammd ɗin da irin ƙoƙarin da yayi. Haka su kaɗai suka yi zama makoki har na kwana uku. Ranar juma'a kuma a ka kai kowacce amarya ɗakinta. Ibrahim da Sadiya Abuja suka huce, Salis da Nana su kuma sabon gidansu da ya ke kusa da tsohon gidan da su Hajiya Babba suka taɓa zama. Zara da AJ kuwa sabon gidansa a ka kaita ita ka ɗai a gidan. Shiru tayi tana kallon zara-zaran yatsun kafafunta tana tariyo komai cikin ranta, tun daga ranar da suka fara haɗuwa da AJ har Kawo yau da take cikin gidan sa. Godiya tayi ga Allah da ta tunoinaemahaifinta da mahaifiyar ta sun karɓu addinin musulunci.tana cikin wannan tunanin ya fito daga wanka ɗaure da tahul. Bai kalketaba har ya gama saka kayansa kafin ya ce "Nasan na miki laifi amma bai kai a ce har zuwa yanzu kina fushi dani ba, na baki haƙuru amma har yanzu magana ma kin kasa min haba my Zara? Yanzuma bata ko tanka masa ba ta shiga toilet itama tayi wanka da alaula ta fito ta sameshi ya haɗa kai da ƙafa yana kallonta. Ganinn hk yasa itama ta zauna tana jiran jin abunda zaice. Tashi yayi ya ce zo mu gabatar da Sallah ta miƙa gudiya ga Allah da ya mallaka min ke. Babu musu tabi bayan sa har palon gidan idan ya shin fuɗa musu darduma ya jasu raka'a biyu. Bayan sun idar ne ya shiga mata tambayoyi game da addini. Cikin mamaki yaji tana bashi amma. Sosai yayi mamakita, sannan ya kamo kanta ya fara mata addu'o'in ta na amsawa a zuciyarta da Amin. Suna idarwa ya kawo musu kayan ciye-ciye amma ta miƙe ta izuwa ɗaki ta hau gado ta barshi a gurin yana kiranta amma ko kallonsa batayiba. Haka shima yaji bazai iya cin komaiba , sai ya bita a baya har ɗakin yana sanar da ita abinci fa zasuci. Haka suka share kwana uku babu abunda yake haɗasu sai gaisuwa da gyaran ɗakinsa , amma bayan wannan bata ƙara shiga sabgarsa. A kwana na huɗune da asuba bayan ya dawo daga Sallha ya nufi ɗakinta yana addu'a a ransa. Ya na shiga ya sameta zaune ta idar da Sallah tana addu'a. Zama yayi a bakin gadon yana jiranta. Tana idarwa bata ko kalleshiba ta ta tashi zata koma kan gado.da sauri ya jawota jikinsa ya na cewa "i'm so sorry my zara dan Allah ki tsaya muyi mugana wallhi na gaji, na miki laifi amma na tuba Please? Kwantawa tayi a jikinsa jin ta kasa kwace jikinta tana dukan bayansa tana jin cewar itama ta gaji da wannan fushin nata domin itama tana cutuwa. "Mai yasa kamin ƙarya? AJ ya ce "Kiyi haƙuri ba sai mun tuna baya ba. Ta ce "Faɗa min yanda komai ya faru? AJ ya sauke ajiyar zuciya domin baya son tuno komai na baya musamman abunda ya faru tsakanin sa da Hajiya Babba. Nan ya fara bata labarin komai har barindin Nigeria da da wowarsu da zuwansa gidansu. Zara na jin haka ta ce "Gaskiya ban taɓa jin labarin mutum mai son kuɗi irin naka ba AJ, kaso ka jefa kanka a cin masifa da bala'i. Haka dai itama ta sanar da shi irin halinda ya jefata bayan tafiyarsa. Harda ƙullesu da a kayi da dukan da tasha. Bayan ta gama ne taga yana kuka sai itama ta fara kukan tana share masa hawaye. Ya ce "Tabbas zara ke ɗin alkairice a rayuwata, na tabbatar da cewar kina sona son da ba'a yin irinsa a wannan zamanin namu, babu abunda zance miki sai godiya da addu'ar Allah ya bamu haƙurin zama da juna. Ta amsa da amin tana ƙara shigewa jikinsa tana jin cewar son aJ a jinin jikinta ya ke. Haka rayuwar wannan mutane ke tafiya cikin so da kwannar junayensu, haka ɓangaren Salis da Nana da Ibrahim a garin Abuja, itama Hajiya Babba da Muhammd da ƴarsu guda ɗaya Hajara suke zaune cikin farinci. *Bayan wasu lokuta.* Muhammad ya sanar dasu Ibrahim wasiyyar mahaifinsu. Suka ce kawai a gida masa masallaci da kuɗin, kowa yayi na'am da maganar da Ibrahim ɗin yayi. Haka suka sayi fili a ka gina Malallacin cikin ƙanƙanin lokaci. Hajara kam ta zama mai gidaje da yawa, yau tana gidan Salis gobe gidan AJ ko gidan Ibrahim watarana ma har kano gidan su Abdalha, ko kuma gidan Laɗifa wacce dole tasa ta auri Umar wanda shima yanzu yana aiki ƙarƙashin Salis. Yanzu haka suna zaune lafiya da ita bayan bidirin da a kayi a baya. Yanzu haka tana ɗauke da ɗan ƙaramin ciki a jikinta, kuma yanzu tana son Hajara sosai, domin watarana da kanta take cewa a bata ita tayi kwana biyu,. Nana ce ta ke sanar da Salis cewa "Nifa har tsoran wannan shigen wayon na Hajara na keyi,gata da ɗan banzar tanbaya. Ai kuwa tana rufe baki sai gata da wani hoto tana ce wa "Mami wannan hotunan da naga anrubuta *ADDININMU* a jiki to wannan mutum ɗayan waye? Ta faɗa tana nuna hoton da ta gane kowa amma banda Daniyel. (Ahmad) Nana ta ce "Ooo Ni wai ke mai yasa ba kya jin magana ne, komai kiga gani sai kin tambaya to"..."Kafin Nana ta ƙara sa Hajara ta bargidan cikin kuka tana cewa "Ita gidan Uncle ɗinta zata tafi kuma bazata ƙara dawo nan gidan ba tunda faɗa a ke mata. Nana da Salis sai kiranta sukeyi amma tayi banza dasu har ta bar gidan. Salis ya ce "Kinga manta da ita da kanta zata dawo ta ce shima Uncle ɗin nata ya mata faɗa, suka kwashe da dariya Salis na ruƙo hannunta yana sakar mata kiss har ya kai ga zarcewa, itama ta shiga mayar masa da martani cikin so da kwanar nunansu. Suna cikin haka sukajiyo Muryar Abubakar ya tashi a barci yana kuka, dole yasa Salis sakinta yana mai da nunfashi ita kuma ta nufi sama gurin ɗan nasu. AJ ya ce "Innah ta sarkin tambaya to wannan ɗin fafinkine. Ya faɗa yana kallon Zara da take kallon Hajara cikin wani sabon mamakin. Zara ta ce "Wai dama wannan hotunan suna nan har yanzu? AJ ya ce "Wannan ai hutunan tarishi ne kinga ai dole mu kula dasu. "Uncle Ya sunan fafin nawa? Cewar Hajara tana kallon hoton har yanzu. AJ ya ce "Innah ta tambayar taki tana yawa. Ai kuwa ta buɗe baki zatayi kuka Zara ta ce "Sorry Innar mu ga Bybe ya tashi je ki ɗauko min shi. Tana jin haka ta miƙe da gudu ta nufin ɗakin da yaron yake. Aj ya kamo ta ya ce You ar the best in my life. Itama ta ce kaine komai nawa mijina. Ya haɗa bakinsa a guri guda yana kallon hoton da Hajara ta zo dashi mai ɗauke da hotunan su dukkan su anrubuta *ADDININMU* aJikinsa da manyan harufa. A fili suka haɗa baki da cewar "Alhamdulillh da kasancewarmu a cikin addininn Musulunci. *Nima S REZA na ce Alhamdulillh,Alhamdulillh. Tammad bihamdillah.* *Ha ƙiƙa littafin ADDININMU ya faɗakar sosai da sosai, babu abunda zance sai godiya ga Allah. I love all my fan's irin sosai ɗinnan, Allah ya ƙara haɗa kan al'ummar musulman duniya baki ɗaya, Allah ka san munafukai a cikin Addinin Musulunci Allah kai mana maganinsu, Allah ka shiryemu , Allah ka tabbatar damu a cikin Addinin Musulunci. Ya Allah suskuran da nayi a cikin wannan littafin Allah ka yafemin, abunda na faɗa daidai kuma Allah ka tabbatar da ladansa a garemu baki ɗaya . Mu kasance da ku wani lokaci masoyana ina sonku sosai da sosai, idan zan dawo zan dawo muku da labari mai zafi irin wanda kukeso da yardar Allah!* *Kar a manta da min addu'a a kan gasar da nece na shiga, kuma in sha Allah idan result ya fito ko ban samu nasaraba zan sanar muku, amma dai muna fatan nasarar🤗* . *Watpad* Salis m Reza. *Feecbook* Salis m Reza *Arewabooks* Salis m Reza *Gimal* adamsalisu331@gmail.com *Whasoop numbar* 08100785178 *Instagram* *Salis m Reza. *A ko'ina inada gurin da zan zanta da kowa idan da buƙatar hakan🥰🥰* *S REZA ikonn Allah*